NIHAAD 7

 


~7~






Sai bayan la'asar Nihad ta iso gida, bayan ta fito daga wajen Husnah school kawai ta wuce tayi attending lectures daya, mai gadi na bude gate ta shiga gidan ba tare da ta saurari gaisheta da yake ba, tayi parking dai dai inda motar take ta kashe, sauka tayi ta kulle motar tana kallon inda mai gadin ke xama ko xata ga Khalil, ai ko yana xaune, ko da wasa bai kalli inda take ba, sai ma danna torchlight phone dake hannunsa da yake with full concentration, nan da nan taji har ranta ya fara baci, wai wa yayi ma wannan mutumin hanyar xuwa neman aiki a gidansu? har ta juya xata wuce ciki sai kuma ta dawo, fuskarta daure ta nufesu, Mai gadi na ganin ta doso inda suke ya mike daga xaunen da yake yana gaisheta, Babu yabo babu fallasa ta amsa sannan tace "Aminu kuna canza ma tsuntsaye na abinci da ruwa kuwa??" Yace "Ehh Hajiya ko daxu da kaina naje wajen na basu abinci da ruwan" Mai gadi ne ke mata magana amma banda hararan khalil babu abinda take with hatred, how dare him baxai gaisheta ba ma, wani dogon tsaki ta ja tace "Aminu ka sameni wajen tsuntsayen" Daga haka ta wuce fuuu xuwa bayan gidan inda cage din birds din nata suke, Aminu ya kalli khalil sannan ya bi bayanta da sauri, sai a snn Khalil ya daga kai ya bi su da kallo, suna isa wajen tsuntsayen tace "Aminu in tambayeka mana" Yayi kasa da kai yace "Toh Hajiya" Tace "Wai waye ya kawo wancan yaron gidan nan da sunan ya nemi aikin driving?" Aminu yace "Hajiya Habibu ne ya kawosa ae" Da mamaki tace "Habibu??? Habibu dai?" Aminu yace "Kwarai Hajiya" Juyawa tayi ta wuce ta bar sa tsaye a wajen, gida ta shige, Aminu ya dawo bakin gate ya xauna yana kallon khalil dake kallonsa shi ma, yayi kasa da murya yace "Wai tambaya take wa ya kawoka, to ban san ko na kwabsa ba da nace Habibu, kasan fa Habibu mutuminta ne, har makudan kudi tana basa, to duk inda xata kai tsaye yake kai ta har ya jirata, ya sha gaya min maganganu amma yace kar in gaya ma kowa" Khalil yace "Wani magana?" Aminu ya gyara xama yace "Ae otal daddaya ne a garin nan da wajen shakatawa irin ta manya bai ta6a ajiyeta ba... Kai duk dai wani otal dake kano da ya amsa sunansa otal xuwa take, wani lkcn tun safe sae dare xae je ya daukota, Khalil dake ta kallonsa da mamaki yace "Hotel?? Me ke kai ta can?" Aminu yace "Ahaf ka ji ka da wani xance, me ake zuwa yi otal, kuma kaf babu wanda ya sani a gidan nan sae Habibu sae kuma ni da yake gaya ma, kai wani lkcn har Habuja tana xuwa kuma ta dawo a ranan, kasan sha'anin jirgi, peee ta tafi peee ta dawo ita da kawayenta, babu wanda xae sani, duk kowa tunaninsa tana makaranta, ita ce Kaduna, Ita ce legas, patacot.....kai manyan garuruwan kasar nan dai da ka sani babu inda yarinyar nan bata xuwa, babu abinda Habibu bai sani ba game da ita ai, ina ga shi yasa taji haushin barin dreba da yayi" Khalil dai yayi shiru, Mai gadi yace "Atoh ni kallonta kawai nake kyar" Khalil yace "Allah ya kiyaye" Mai gadi yace "Ameen dae" Nihad na shiga bedroom dinta ta ajiye jakarta da mayafi ta dau wayarta tayi dialing number Habibu, yana fara ringing ta nemi gefen gado ta xauna babu bata lkci ya daga hade da sallama yace "Hajjaju Hajjaju ina yini" Tace "Lafiya lau Habibu" Yace "Ya kwana biyu kuma?" Tace "Lafiya lau, Kana ji na?" Yace "Ina ji Hajiya" Tace "Wannan drivern da ka kawo ma Abba, a ina ka san sa?" Habibu yace "Wani abu ya faru ne Hajiya?" Tace "Tambayarka nake kana tambayata" Yace "Ehh Hajiya na san sa, d'an uwa na ne, garinmu daya" Nihad tace "Bana son karya ta ina ya xama ɗan uwanka kana baƙi yana fari??" Habibu yace "Ayya Hajiya ai in dai ka fito kauye daya da mutum ku ka shigo maraya dan uwanka xaka kirasa, haka abun yake ki tambayi kowa ma" Ta kyabe baki tace "Toh abu daya nake so da kai yanxu" Yace "Toh ina ji Hajiya" Tace "Ko nawa kake so xan baka Habibu, in dai kudi ne kar ka ji komai" Shi dai yayi shiru, tace "Kana ji na?" Yace "Ehh ina ji Hajiya" Tace "So nake ka kira Abba ka 6ata sa a wajensa, ka kirkiro wani babban laifi kace yayi a garin naku ashe dalilin da ya sa ya bar garin kenan, kai baka sani ba sai yanxu wani ɗan garin naku ke sanar maka" Jin shirun da Habibu yayi tace "Kayi min shiru?" Da sauri yace "Ehh ina jin ki Hajiya, ina sauraronki" Nihad tace "Good, yaushe xan saurareka?" Yace "Xuwa gobe in sha Allah" Tace "Ohkk" daga haka ta katse wayar ta mike ta nufi window tana jin wani relieve a ranta. Khalil na shigowa parlon chalet din da suke ciki dab da magrib ya dinga bin parlon da kallo, tun safe da ya fito bai sake shigowa ba sai yanxu, kuma kafin ya fita tass ya share ko ina, amma yanxu parlon wani sai yace yara kanana sun shiga sun yi wasa da rana, beside that every where is so untidy, nan kayan wanki, can kayan guga da Isiya ke yi, ga plate din abinci da cups a tsakar parlon, kofar ma a wangale ake barinsa sauro su shiga yanda suka ga dama, Ya dinga kallon Saminu, Isiya da Shafi'u da ke parlon, Kafin ya ce komai Shafi'u yace "Ana ta kiran wayarka tun daxu fa" Kallon direction din da jakarsa yake yayi, sai kuma ya kallesu yace "Amma nace ku yi hakuri ku bar barin kofa a bude sbda sauro, tunda a parlor nake kwanciya ko" Isiya yace "Baka ga fankar ya lalace jiya ba, AC dama tun da ka xo ai baya yi, shhkn sbda sauro sai mu ki bude kofa iska ya shigo" Khalil ya dinga kallonsa, Saminu yace "Haba kai tun da ka zo sai kayi ta abu isa isa da gadara don kaga muna maka shiru, mu kafin ka zo haka muka saba barin kofa gaskiya" Khalil bai kuma ce masu komai ba ya nufi gun kayansa, ya dau jakarsa da blanket, sai tsintsiya da parker da yake shara, hanyar dakuna uku dake chalet din ya nufa, duk suka bi sa da ido har da waigawa, sai da ya bude ko wani daki sannan daga karshe ya shiga na dama, ajiye jakarsa da blanket yayi, duk wani ghana must go da jaka da ya gani a dakin sai da ya cilla sa waje, sannan ya cire dukunannen zanin gadon dake kan gadon shi ma ya cilla masu waje, tas ya share dakin, sannan ya shiga bandaki nan ma ya wanke, ya fito ya bude jakarsa da makulli ya dauko Harpic da hypo ya koma bandakin, bayan ko ina ya dawo yanda yake son ganinsa, yayi wanka ya dauro alwala ya fito, har xai kulle jakarsa sai ya tuna wayarsa ya dauko ya ga miss calls din Habibu kusan 7, ya gama kare ma number kallo sannan ya ajiye wayar ya mike ya fita daga dakin ya sa makulli, ya zira makullin a aljihun jallabiyan jikinsa, babu yabo babu fallasa ya fito parlon ya nufi kofa duk suka bi sa da kallo babu wanda ya iya cewa komai har ya fita. Bayan khalil yayi sallah yana xaune gefen mai gadi sai ga Hafsah ta kawo ma mai gadin abinci, Mai gadi na kallonta yace "Shi ma ki kawo masa tasa abincin nan kawai" Tace "Toh" sannan ta juya ta koma ciki, Khalil ya mike yace "Xan dau wayata da ka sa a caji" Daga haka ya shiga dakin mai gadin ya dauko wayar ya dawo ya xauna, yayi dialing number Habibu ya kai kunne, ba a dauki lokaci ba Habibu ya daga yace "Ranka shi dade" Khalil ya gyara xama yace "Ya kake" Habibu yace "Lafiya qlau wllh, ya aikin?" Khalil yace "Alhamdulillah" Habibu yace "To madallah, kana ji na" Khalil yace "Ina ji" Habibu yace "Wani abun ya hadaku da wannan yarinyar Nihad ne?" Khalil yace "Wani abu kamar me?" Habibu yace "Aa wai ko sa'insa, ko dai makamancin hakan" Khalil yace "Ko daya" Habibu yace "Tohh, akwai fa matsala" Khalil yace "Ta me kenan" nan Habibu ya sanar masa yanda suka yi da Nihad daxu, Khalil yace "xan kiraka anjima" Daga haka ya katse wayar ya amshi abincin da Hafsah ta kawo masa yace "Nagode" Nihad ta fito daga wanka kenan da daddare Mumy ta shigo dakinta, sunkuyar da kai tayi tana goge jikinta tace "Ina yini" Mumy tace "Wa ya baki makullin motar Farooq daxu?" Nihad ta kalleta da sauri, sai kuma ta marairaice tace "Umma ce ta bani" Mumy tace "Ke yanxu Nihad duk wata hanyar da xaki bi ki sani magana shi kike nema a rayuwarki ko?? Kwata kwata baki daukeni bakin komai ba, duk abinda xai 6ata min rai shi kike rawan jiki kiyi, ki kama ki dau mota ki kama  hanyar makaranta without i and ur dad knowing ko Nihad" Nihad ta fara shessheka tace "Mumy u don't want to be considering me, ni baxan iya shiga mota daya da wancan sabon driver din ba shi yasa na amshi makullin motar ya Farooq gun Umma" Mumy tace "A saboda meye baxa ki shiga mota daya da shi ba? Saboda shi ba mutum bane? Kawai don bai baki makullin mota kin tafi gantali ba shine kika dau karan tsana kika daura ma mutumi? He is only trying to protect his job don ai ba a basa umarnin ya baki makulli ba ko" Kuka Nihad take sosai tace "Ko me nace Mumy baki supporting dina, wllh yaron ba shi da kunya, ya raina ni kawai" Mumy tace "Wato yaro ne ma?? Me yasa ita Nihal bata complain a kansa, ina ce shi ke dropping dinta a islamiyya kullum, i even ask her ko taga yana da matsala tace min he is so friendly, me yasa ke baxa ki sauke kanki yanda er uwarki ke yi ba" Nihad ta hade rai tace "Wannan wawiyar me ta sani, ko bai mata magana ba ma ai washe masa hakora xata yi ita tayi masa, baxa ma ta jira ya gaisheta ba ita xata fara gaishesa sbda bata da hankali, pls mumy ki daina sa Nihal a cikin mutane" Mumy tace "Ki bi duniya a sannu Nihad, babban matashi irin wannan sbda yana aiki karkashin Abbanki kice baxa ki gaishesa ba sai dai ke ya gaisheki, me yasa baxa kiyi koyi da Nihal ba, me yasa kika dau duniya da xafi haka" Nihad tace "Ni dai Mumy kiyi hakuri ki bani makullin motar ki yau wllh ina da lectures karfe goma, Ni kuma baxan juri shiga mota daya da shi ba" Mumy tace "Toh xa mu gani kuwa, kuma wllh kika sake xuwa gun Hajiya kika amshi makulli sai na 6abbalaki a gidan nan" Nihad tace "Shikenan ni baxan je makarantar ba kawai" Mumy tace "Ohk ni kike gaya ma wannan ko" Ta fashe da kuka sosai tace "Toh Mumy ya kike son inyi, ni naga kamar ma kin fi son driver din nan a kaina kawai" Mumy tace "Ehh na fi sonsa a kanki, kuma wllh kar ki kuskura ki bari karfe goma yayi maki a gidan nan, sannan shi din xai kai ki, idan kuwa ba haka ba xaki sha mamakin abinda xan maki, tunda ke kin dau girman kan duniya kin daura ma kanki" Daga haka Mumy ta fice daga dakin, Nihad tayi kukanta ma'ishi, taji ta tsani wannan bawan Allah, ta tsanesa... Babu yanda ta iya haka ta tashi ta shirya, karfe goma saura minti biyar ta fito compound, atamfa ce jikinta da wata mitsitsiyar mayafi da ta rataya a wuya, hannunta rike da laptop dinta da jaka, fuskarta a daura ta nufi can inda ta hango Driver din a xaune da Aminu, tana masa wani matsiyacin kallo, cike da isa da gadara tace "Tasowa xaka yi kayi dropping dina a school idan ka ga dama, kai kuma Aminu sai ka gaya masa makarantar tamu" Daga haka ta juya ta bar wajen ta tafi can gun motar, murya can kasa kasa Aminu yace "Iko sai Allah" Mikewa Khalil yayi ya nufi motar, Har xata bude back seat sae kuma ta fasa ta xaga ta bude seat din gaba ta shiga, yanda ta hade rai sai kayi xaton ko dariya bata ta6a ba, shi ma ya shiga motar, suna fita compound Aminu ya daga masu hannu, AC din motar Nihad ta kunna, shi dai bai nuna yasan abinda tayi ba, suna hawa saman titi tayi connecting phone dinta ta kure waka a motar, shi dai driving dinsa kawai yake, bayan kusan minti talatin suna tafiya, ganin tafiyar tasa babu direction, ta wani juya ta kallesa tace "Wai malam baka san inda xaka kai ni bane, ko Aminun bai gaya maka ba?" Tafiyarsa kawai yake pretending he didn't know she is talking duk da yana jinta, rage volume din wakan tayi can kasa, a fusace tace "Malam da kai nake" Ya kalleta yace "Ohk magana kike, wakar ki ce ta hana inji" Ta yi masa wani kallo tace "Da yake kai kurma ne ba dole waka ya hanaka ji, Aminu wai bai gaya maka inda xaka kai ni ba?" Yayi slow down sannan yayi parking yace "Ina ta sauraren kice ga inda xaki ne ai" Buda baki tayi tana kallonsa, Cikin daga murya tace "Aminu bai gaya maka bane?" Yace "Toh ai ban ga Aminu cikin motar ba" She couldn't stop looking at him, ita ba abin ta sauka ba, dakewa tayi tace "Saboda ba kai ke xuba fetur a motar ba shi yasa kake ta yawo da ni a cikin garin kano ba tare da kasan inda xan je ba ko?" Bai bata amsa ba, bata kuma ga alamar xai ce komai ba, wani dogon tsaki ta ja, ta gyara xama tace "Dama harka da ɗan kauye ya gaji haka, idan kaga dama Maryam Abatcha American University of Nigeria xaka kai ni" Without looking at her yace "Ohk sai kin dinga min kwatance" Tace "Ban gane sai an maka kwatance ba, kai dama babu inda ka sani a kanon ka xo ka nemi driving a gidanmu?" Yace "Ehh idan aka ci gaba da nuna min wajajen xan sani ai" Tace "Amma wllh  baka da amfani" Tsaki ta ja tace "Ai sai ka juya kan motar idan dai ba garinku xa mu je ba" yace "In kince aje can din ma ai sai aje" Bude baki tayi, sai kuma tace "Wallahi yaron nan ka raina ni" Sai a sannan ya juya ya kalleta jin abinda tace, ta galla masa wani harara tace "Malam kana bata min lkci xan je makaranta" Yace "Na xata garin namu xa mu" Daga haka ya juya, rai a bace ta dinga gwada masa inda xai bi har suka iso makarantar, ganin yayi parking a waje tace "Malam tada motar nan ka shigar dani ciki, ko duk nan akwai wanda kaga anyi dropping a titi?" ya ci gaba da driving din slowly, dai dai gate din makarantar ya tsaya ya sauke glass din motar, gaishesa security din suka yi, ya amsa ya amshi pass ya shiga cikin makarantar yace "Ina?" Rudely tace "Duk inda ka ga wancan jan motar ta bi kai ma ka bi, bani da lkcn yi maka wani kwatancen" Bai ce mata komai ba, ya ci gaba da driving dinsa, Dai dai wajen da motar ta tsaya ya samu waje yayi parking shi ma, ta ciro wayarta ta kira Husnah, Husnah na dagawa tace "Kin shigo school?" Husnah tace "Ehh, ke kina ina?" Nihad tace "Ku fito parking space ke da su Naf ku sameni yanzu yanzu, ki tabbatar har da Zully xa ku taho" Husnah tace "Ke kika yi driving din yau ma?" Nihad tace "Ke dai nace ku zo sharp sharp" daga haka ta katse wayar, ta zuge zip din jakarta ta fiddo chewing gum ta jefa cikin bakinta tana tauna a hankali, Shi dae gabansa kawai yake kallo, Bayan few seconds ya kashe motar ya zare makullin ya ajiye nan kusa da ita without looking at her, ya bude motar xae sauka, da mamaki tana kallonsa tace "Heyy, meye hakan kake yi? Waye xaka bar ma motar?" Still bai kalleta ba yace "Masu shi" Daga haka ya kulle motar ya juya ya bar wajen, kasa cewa komai tayi sbda mamaki, can ta sauka motar tana bin sa da ido baki bude, sae ga Husnah da Naf with Zully da wata kawar Zully, Husnah ta karasa kusa da ita da sauri tace "Nihad what happened, ya da bude baki haka" Nihad ta kalleta tace "I don't think this guy is okay, ji tafiya yayi ya bar min motar fa Husnah" Husnah tace "Wa??" Nihad tace "New driver din, kiranku fa nayi wai ku gansa, mu yi masa tijara..." Husnah tace "Wai wancan me bakar rigar dake tafiya?" Kasa bata amsa Nihad tayi don da gaske mamaki ne kawai ya cikata, Naf tace "Kawai haka nan ya kama ya tafi babu magana?" Nihad tace "Not at all, ajiye min makulli yayi kusa da ni, nace wa xai bar ma motar, wai masu shi.... kawai ya saka kai yayi tafiyarsa" Lkci daya Husnah da su Naf suka kwashe da dariya har da kyakyatawa, Nihad ta hade rai, Husnah tayi dariya me isarta sannan tace "Gaskiya wannan drivern dan duniya ne, ni ko na so in gansa wllh, ya iya bada amsa dai dai da tambaya" Nihad ta hade rai tayi locking motar ta bar su wajen a tsaye ta wuce aji, bin ta suka yi har sannan suna dariya, a lecture room suka sameta, Husnah ta xauna kusa da ita tace "Anya ba ajiye aikin yayi gaba daya ba" Nihad tace "Toh ni ya kamata ya ba makulli? Ko dama ni na basa makullin?" Husnah ta fashe da dariya har da kife kai.


*Know the frnds of ur kids*



https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/nihaad-chapter-8-by-khaleesat-haiydar


To gain Access to the book Nihad Contact me directly via👇🏻 


07087865788




_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_



Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....

  *tested and trusted*


If interested contact

👇🏻

08052466875 via WhatsApp

[7/3, 10:46 PM] +234 706 192 1716: 💖💖 *NIHAAD*💖💖






By _Khaleesat Haiydar_✍🏻


No comments