NIHAAD 6

 ~6~






Washegari Monday har karfe tara Nihad na ta kwance a dakinta, karfe tara da rabi aka bude kofar dakin, ta juya ganin Umma ce ta shigo ta mike xaune a hankali, Umma tace "Baxa ki makarantar bane Nihad, naga yau Monday" Nihad tace "Lectures din karfe goma ne, Nihal ta tafi islamiyya?" Umma tace "Tun yaushe, ke dai kam na san ba xa ki ba" Nihad bata ce komai ba, Umma ta juya ta fita, sauka tayi daga saman gadon ta shiga bandaki, nan ma sai da ta bata kusan minti arba'in sannan ta fito, shiryawa tayi cikin tsadadden bakar Abaya, wurin shirin ma ta 6ata kusan minti talatin, banda kamshi babu abinda ke tashi a ko ina na jikinta, sosai Abayar ta amshi farin fatarta kai kace balarabiya ce, ta dau karamin handbag ta sa flat shoe sannan ta fito daga dakin bata kulle ba don Hafsah xata shiga tayi mata gyaran dakin sannan ta wanke mata bandaki, tana tafiya kamar bata son tafiyar ta tafi part din Mumy ta bude kofar parlon, xaune ta ganta parlon tana waya, ta cire takalminta nan bakin kofa ta karasa ciki a hankali, ta xauna saman kujera fuskar nan nata babu yabo babu fallasa, har Mumy ta gama wayar sannan ta gaisheta, Mumy ta amsa mata ita ma a dakile without looking at her, mikewa tayi tace "Xan tafi makaranta" Mumy tace "Allah ya tsare" fita tayi daga parlon ta wuce part din Umma, Umma tace "Ashe dai za ki, toh Breakfast din fa?" Tace "Xan yi a makaranta" Umma tace "Toh Allah ya tsare" Kamar xata yi kuka tace "Umma ni gaskiya baxan iya shiga mota daya da wannan yaron ba" Umma tace "Toh yanxu ya xa ayi, idan na tafi na amsar maki makullin kin san anjima xa a dauko yara a makaranta" A hankali Nihad tace "Toh pls Umma zaki bani makullin motar ya Farooq" Umma ta rike ha6a tace "Farooq, to bari dai in dauko maki" cike da farin ciki Nihad tace "Yauwa Umma, karfe hudu xan dawo in sha Allah baxan wuce haka ba" Mikewa Umma tayi ta fita daga parlonta ta wuce dakin First son dinta, makullin dake jikin kofar ta murda sannan ta bude ta shiga ciki ta dauko makullin motarsa ta fito, farin ciki sosai Nihad tayi ta mashi makullin tana murmushi tace "Umma nagode" Umma tace "Toh ki tafi a hankali dai, kar ki kwarzane masa mota mu shiga uku" Nihad tace "A hankali xan tafi Umma" Daga haka tayi ma Umma sallama ta fita daga parlon cike da murna, ta fitowa compound taga mai gadi xaune tare da Khalil, lokaci daya ta wani murtuke fuska, ta nufi mai gadi tana juya makullin hannunta tace "Hey Bude min gate xan fita" Tashi yayi da sauri ya tafi xai bude gate din, ta nufi motar yayanta, ta gefen ido khalil ya bi ta da kallo, har ta shiga motar, bayan ta gama warming tayi zoom off out of the compound duk don ta tada k'uran interlock, Mai gadi ya daga mata hannu yace "Allah ya tsare Hajiya" ko kallonsa bata yi ba balle ta tanka, ta ja motar tayi gaba, kulle gate din yayi ya dawo yana kallon khalil yace "Hajiya ce xata bata motar Farooq da yake baya gari, kuma ina tabbatar maka uwarta bata sani ba, dama Umman ke daure mata tayi ta abinda ta ga dama a gidan nan ai, kai kam huta roro" Khalil yayi murmushi yace "Yanxu ina xata haka?" Mai gadi ya xauna yace "Wai Makaranta mana, kasan jami'arta shegen tsada ke garai" Khalil yace "Ita er uwarta fa?" Mai gadi yace "Baiwar Allah, ba daxu ka ajiyeta a islamiyya ba, hutun makaranta ta dawo, amma kaga kullum sai taje islamiyya abunta..." Khalil yace "Wacce makarantar take ita?" Mai gadi yace "Ba nace maka a Zaria take, Ahmadu Bello" Khalil bai kuma cewa komai ba. Nihad na driving tayi dialing number Husnah, Yana fara ringing Husnah ta daga, Nihad tace "Kin shiga school ne?" Husnah tace "Me yasa kika kashe wayarki jiya bayan munyi dake kina tahowa?" Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace "It's a long story, but ya na ji muryarki haka, are you okay?" Husnah tace "Partially" Nihad tace "Where are u at now?" Husnah tace "Ni'ima guest palace" Nihad tace "Really? To bari in taho nan kawai, nima I'm not even in the mood of attending lectures today" Husnah tace "Sai kin xo" Katse wayar Nihad tayi ta dau hanyar Ni'ima guest palace din. Nihad na isa tayi parking ta kirata, nan Husnah ta sanar mata room number dinta, Nihad ta sauka motar ta shiga ciki, Knocking tayi kofar dakin, Naf ta bude, Nihad ta d'an buda ido ganin Husnah a kwance ta lulluba, ta kalli Naf tace "Is she okay?" Naf tace "Shigo in kulle kofa" Nihad ta shiga ta karasa gun Husnah, ta xauna gefen gadon tana kai hannu jikinta tace "Ya dai Husnah?" Husnah ta mike xaune tana ta6e baki tace "Ashe Yaks d'an iska ne duk bamu sani ba" Nihad ta ɗan bude ido tace "Me ya faru?" Husnah tace "Kawai yaje ya sha kwayoyinsa jiya in gaya maki yayi assaulting dina" Nihad ta xaro ido tace "Really?" Husnah tace "Wllh ke dai in gaya maki, ban da abunsa ai i wouldn't have denied him" Nihad tace "Where was Nafee then?" Husnah tace "Ita suna tare da saurayinta, kin san shi ma ya zo" Da mamaki Nihad tace "Yaks??" Husnah tace "Ai kuwa baki ga yanda ya dinga tambayarki ba, nace kina hanya duk ya damu baki iso ba, ke gwara ma da baki xo ba din, kilan rashin xuwanki ya sa haka ya faru," Nihad tayi shiru, can tace "Tabdi, kuma a Tahir guest palace din?" Husnah tace "Wane Tahir, ai ba a can muka yi birthday din ba, ke kinga haduwar birthday din nan kuwa Nihad?? Gaskiya na jima ban ga birthday da yayi haduwar na Maska ba, it was light" Nihad tace "Ni xancen yaks ne ya tsaya min a rai, Shi yasa fa kike ganin bana kula clique dinsu, bana harka da maza marasu aji" Husnah tayi dariya tace "Ni kawai way of approach dinsa ne ya kona min rai, amma what's there? norms ne ai, someone that i have been crushing on from day one" Nihad tace "To karfe nawa ku ka bar wajen?" Husnah tace "Kai dare yayi fa sosai, ke ni fa wllh gwara ma da Allah ya hanaki xuwa nace maki, don da ban san ya xan yi da ke ba a wajen ga uban daren da muka yi, cabb to wa ma xai saurareki, gaskiya birthday din nan yayi armashi, ai da naga daren yayi sosai shine na fasa komawa hostel kawai muka kama daki a nan ni da Surayya, ita Naf fa sai yau da safe ta xo nan ta same mu" Nihad ta kyabe baki ta ajiye handbag dinta tace "I am jet hungry banyi breakfast ba, me suke siyarwa a nan?" Husnah tace "Ke bamu dade da waya da Ayman ba xai taho mana da abinci yanxu, bari in kirasa ince plate uku xai kawo, shi ma jiya ya dawo daga Egypt" Daga haka Husnah ta kirasa ta sanar masa ya dado wani plate din, bayan ta ajiye wayar tana kallon Nihad tace "Amma jiyan me ya hanaki xuwa don Allah?" Nihad ta sauke wani ajiyar xuciya irin na takaici tace "Husnah in gaya maki wani sabon driver Abba ya dauka, kin san ai ya bude ma Habibu Shago" Husnah ta gwalo ido tace "Don Allah, kina nufin yanxu babu Habibu? Allah sarki, kai amma xaki yi kewan Habibu, sau da yawa fa da shi kike hada baki, gashi duk inda kika ce ya kai ki kai tsaye yake kai ki, har ma ya jira ki" Nihad ta marairaice tace "Ke dai bari, ai ni aka yi ma da Habibu ya bar driving, sau nawa yake kai ni Tahir ko Bristol or prince hotel, kuma ya jirani komin dadewar da xa mu yi, sau nawa xa mu fita in amshi mota a hannunsa shi ya tafi harkar gabansa nima inyi tafiyata, sai na gama xan kirasa mu hadu a busstop mu koma gida, Yawanci ba shi nake aika ya siyo min duk abinda nake bukata ba, ai har kuka sai da nayi da naji Abba ya bude masa shago, Habibu ai mutum ne" Husnah tace "Amma fa ya ci kudinki ba karya" Nihad tace "I wish Allah xai ta6a xuciyar Abba ya dawo mana da Habibu kawai" Husnah tace "Toh shi sabon da aka dauka fa?" Nihad ta gyara xama tace "Ai shi xan baki labari yanxu, wato wani tatattcen d'an iska, mara kunya Abba ya dauko mana as driver Husnah, kinsan jiya a kansa sai da Mumy ta mareni har sau biyu a titi cikin jama'a? Husnah as i am talking to u now i am boiling inside, tun shekaranjiya nake cikin ɓacin rai da bakin cikin mutumin nan, daga fara aiki shekaranjiya har ya raina ni baya girmama ni, ina masa magana sai yayi min banxa ko kuma ya kalle wanda ke kusa da shi irin dai kamar ba da shi nake ba da na kusa da shi nake, ko kuma ya kara min sheggun kunnuwansa gaba, irin dai na raini da tantiranci, Husnah yayi mugun raina ni wllh, yanxu maganar da nake maki motar ya Farooq Umma ta bani makulli na fito da shi, baxan juri xama a mota ni da shi yana driving dina ba...." Tuni har hawaye ya cika idonta, Husnah dake ta sauraronta da mugun mamaki ta gyara xama tace "What?? Shi ordinary driver din yake duk wannan abinda kika lissafo min kuma kika kyalesa? Ta yaya kika basa wannan fuskar ya rainaki daga fara aikinsa Nihad? Waye shi haka, kuma a ina Abba ya samo sa?? Wai ma garin yaya kika yi creating room for this bullshit" Nihad na shessheka tace "Baxa ki gane ba, wllh irin yan iskan nan ne yaron, cikin ruwan sanyi yake raininsa da rashin mutunci, idan kin gansa ma xa kiyi xaton baya magana nan ko katon ɗan iska ne, yanda fa kika san motarsa haka yake jin kansa daga fara aiki" Husnah ta rike ha6a tace "Tabdi... to kuwa xa mu yi maganinsa, but what did Abba say about it? Ko baki kai kararsa ba har yanxu?" Nihad tace "Babu wani action da Abba ya dauka tunda Mumy ta zuzzuga sa, har Umma ma ta saka baki amma Abba yaki daukan kwakkwaran action, the painful part of it is that Mumy supporting dinsa take kamar ta ta6a saninsa, kinsan yanda take abubuwanta dai, to wllh a kansa ta gaggaura min mari jiya a tsakiyar Hotoro dalilin da yasa na fasa xuwa Tahir palace kenan, to wannan ne har xan dinga basa kudi yana kai ni duk inda nake so ba tare da yayi casting dina ba wataran? Ina ai baxai yiwu ba, bana harka da fitsararrun yara ni...." Husnah tace "Calm down besty, shi karamin kwaro ne wllh, kuma xa mu yi maganinsa, Clique dinmu kadai mun ishesa" Naf dake ta sauraronsu ta kyabe baki tace "Lallai wnn ɗan iska ne number 1, daga wani kauyen aka samo maku shi halan? Shi a yan kauyen ma shege ne fa" Nihad tace "How will i even know, wlh d'an rainin wayo ne na karshe, gashi baya wani magana nake gaya maku, yanda kuka san kurma, cikin ruwan sanyi yake rashin mutunci da raini, ga wani ji da kai, to kana aiki karkashin mutane kana driving ina wani ji da kai??" Kwankwasa kofar aka yi, Husnah tace "Ayman is here..." Naf ta nufi kofar ta bude, wani matashi ya shigo dakin rike da takeaway uku with many drinks da bottle water, Ya ajiye ledan yana kallon Nihad yace "Manyan mata, ashe dai kina kasar nan Nihad?" Nihad tace "To an zuga Abbana ya ki kai ni UK karatu ba dole a gan ni a kasar ba" Dariya yayi yace "Gaskiya ne, to ya kwana da yawa, kinsan ku manya ne ba kowa ku ke replying ma chat ba both WhatsApp and IG" Nihad tace "Not at all" Husnah ta mike ta dauko takeaway daya ta ajiye ma Nihad, Ayman na kallon Husnah yace "I think bari in kama wani dakin kawai" Husnah tace "Ohk then" Daga haka ya fita daga dakin, Naf ta ja tsaki tace "Sai shegen girman kai, wato jira yake in fara masa magana ko" Husnah tace "Ke dai kowa sai kice yana da girman kai bayan kema kina fama da naki, duk fa Salman ne ya hura maki kunne ki daina kula kowa sai ki dinga fakewa da ana maki girman kai" Naf tace "Ni fita ma xan xo in yi yanxu, amma xan dawo later" Husnah tace "Ina xa ki? Baxa ki ci abincin ba?" Tace "Idan na dawo xan ci" Husnah tace "Kar fa ki ki dawowa Naf, saboda ke naki gayyato Zully nan fa" Naf tace "Ke wllh xan dawo, wani Alhaji ne ke ta damuna da kira ya shigo kano, to yayi min alkawarin waya dama, shine xan je" Husnah tace "Ahh, to maza ki je, Allah ya sa mu ga latest iphone" Naf ta dau figigin gyalenta tace "Toh Allah ya sa bari in je, Nihad idan na dawo xa mu tsara yanda xa ayi da ɗan kauyen can shi kuma" Nihad tace "Toh sai kin dawo" Daga haka Naf ta fita daga dakin, Husnah tace "Tabdi, yau ni naga karfin hali wai barawo da sallama, wannan idan yayi wata daya a gidan ai sai dai kuma ya koma rayuwa cikin main building ya bar boys quarters kawai" Nihad tace "Sai yanzu rashin barina in xauna a hostel da Mumy tayi ke kara damuna sosai, kinsan da na hakura amma tun da aka kawo wannan drivern damuwan ya dawo sabo" Husnah tace "To ko xaki kara gwada yi ma Abba magana?" Nihad tace "Babu yanda Umma bata yi da shi ba, amma da yake Mumy da ya farooq sun hure masa kunne ya ki amincewa, sae dae kawai yayi ta bani hakuri wai there is time for everything" Husnah tace "Gaskiya in har ba sallaman driver din nan aka yi ba xaki takura sosai, gashi Abba baxai baki mota ba ko" Nihad tace "Ba fa ruwan Abba, Mumy ce matsalar gidan nan sae yaya Farooq, amma ae Umma tayi kokarin ganin an bani motar kwanaki hakan bai yiwu ba" Husnah xata yi magana wayarta ya fara ring, tana dubawa taga Ayman ne, dagawa tayi tace "Ya? Wani room number kake?" Yace "102... Pls Nihad ta bani minti goma mu yi magana mana" Husnah tace "Ohk over there?" Yace "Yeah" katse wayar tayi tana kallon Nihad tace "Ayman wants to speak to you" Nihad tace "Ohk kin katse wayar kuma" Husnah tace "No, yana room 102" Nihad tace "Ina ga ya sha kwaya, nice xan bi sa dakin??" Husnah tace "C'mon, minti nawa xa kiyi ki fito, he said just 10 mins, behave like the big girl u are mana" Nihad tace "Look, ya bar ni ma inji da damuwata i don't have that strength to talk" Husnah tace "Don Allah kiyi hakuri ki je Nihad, minti goman nayi ko bai gama magana ba ki fito kawai, ko albarkacina ya ci mana, yana ganin idan na gaya maki xaki ji shi yasa ya biyo ta wajena, ki je ki dawo ki ji yanda xa mu yi da wancan ɗan kauyen shi kuma" Nihad ta d'an kyabe baki, sai kuma ta mike tana gyara veil din abayanta tace "Wani room ma kika ce?" Husnah ta gaya mata, daga nan ta fita xuwa dakin. Kwankwasa kofar dakin tayi, sai gashi ya bude yana kallonta da murmushi fuskarsa yace "Welcome Nihad" gefensa ta bi ta shiga dakin ta xauna saman one seater dake dakin tana kallonsa har ya dawo ya xauna gefen gado sannan tace "I am all ears" shiru yayi yana kallonta, ta langwabar da kai tace "Kayi shiru" Ɗan murmushi yayi yace "Donno where to start from, kinsan kina da wani kwarjini na daban Nihad" Ta kalli agogon dake wrist dinta, sannan tace "Then just start from d end" Dariya yayi sannan yace "Ohk, a takaice kawai ina son ki bani dama let date" Tace "Sorry but i don't double date Ayman" Yace "What's d big deal about double dating Nihad?" Ta girgiza kai tace "Tsari na kenan, i have my boyfriend, and yana sona kamar yanda nima nake son sa, so what's d need of dating else where?" Shiru Ayman yayi, can ya mike ya koma kan kujerar da take ya xauna a hannun kujeran xai kama hannunta ta fixge ta matsa gefe sannan tace "I am sorry Ayman, ina da saurayina kuma duk kun sani" Yayi kasa da murya yace "Yeah i know, but pls Nihad... even if it's once a while, i will always provide u with all ur needs, i am not talking about petty needs" Da mamaki tace "What's that u are talking about?" The way he was looking at her directly in the eyes yasa ta mike tana kallonsa da kyau tace "Seems Husnah bata ta6a baka labarina ba ko?? Kawai kana ganin mu tare, duk inda take xaka gan ni, Ohk get this Ayman, my obstinacy have limit, it hasn't attain to this extent, sorry" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fice daga dakin ta kullo masa kofar. Tana komawa wajen Husnah, Husnah ta katse wayar da take ta ajiye, Nihad tace "Baki ta6a gaya ma Ayman wacece ni ba ko?" Husnah bata ce mata komai ba, Nihad ta nemi waje ta xauna, Husnah tace "Toh wai meye a ciki, kawai kin bi kin makale ma Aliyu da definitely kinsan yana da yan mata iri iri shi ma, ni wllh Aliyun nan haushi yake bani, ga shegen ji da kai kamar ɗan jinin sarauta, duk abinda ya daura ki a kai shi kike yi, ga samari iri iri ko wanne na sonki amma kince ke sai Aliyu, to Aliyun me" Nan da nan Nihad ta hade rai tana kallon Husnah, can ta ja tsaki ta dau jakarta ta mike ta nufi kofa, Husnah tace "Tun da an ta6a numfashin ki ba dole ki nufi kofa ba, to baxa ki tsaya ki ji yanda xa mu yi da sabon drivern naku ba" Ko sauraronta Nihad bata yi ba har ta fice daga dakin, Husnah ta ta6e baki tace "Kawai ki makale ma mutumin da yan mata ke rububi a kansa, ki dauki son duniya ki dora masa, shi kuma yayi ta yin kamar bai san kina yi ba, da ma yana baki lokacinsa yanda ya kamata ne abun baxai dameni ba" Husnah ta ja tsaki ta jawo abincin gabanta ta bude.....



https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/nihaad-chapter-7-by-khaleesat-haiydar


Contact me directly via👇🏻


07087865788 WhatsApp only.

[7/3, 10:46 PM] +234 706 192 1716: 💖💖 *NIHAAD*💖💖





By _Khaleesat Haiydar_✍🏻


No comments