NIHAAD 11

 


11






Juyawa Nihad tayi daga karshe ta koma cikin gidan don ko kallon inda take Khalil bai yi ba, to wai wa ya dau jakarta? lkci daya jikinta yayi sanyi hankalinta ya tashi fiye da da, haka nan ta shiga gida jiki ba kwari ta koma dakinta ta shirya, Hijab har kasa ta saka ko powder bata shafa a fuskar ba, ta fito ta tafi bangaren Mumy, xaunawa tayi saman kujera ta gaisheta sannan tace "Mumy xan tafi makaranta ina da lectures karfe takwas" Mumy ta kalli agogo ganin bakwai da rabi tace "Kinyi breakfast ne?" Tace "Xan yi idan na sauka" Mumy tace "To ko ke fa da kika sa Hijab yau, kinga yanda yayi maki kyau, amma kullum in ta maki magana daya a kan shegun mayafan nan da kike sawa ba kya ji" Nihad ta ɗan kirkiri murmushi ta mike tace "Sae na dawo" Mumy tace "Toh Allah ya tsare, kiyi addu'a kafin ki fita" Nihad ta amsa da "Toh" sannan ta fita. Gaba daya Nihad neman appetite dinta tayi ta rasa, daga karshe nan ta bar abincin tayi ma Umma dake parlor sallama ta fita gidan, mai gadi kadai ta samu xaune bakin gate, ta nufesa tana tsaye dab da shi tace "Aminu don Allah baka ga min jaka a bakin gate ba? Kamar a nan na yar jiya da daddare, ko da safe nan don Allah baka gani ba??" Yace "Subhanallahi jaka Hajiya? ae ko wllh tllh ban gani ba, kema kin san da na gani ae xan adana maki" Nihad ta rasa abun cewa tayi shiru, iphone dinta fa na jakar yanxu ta ina xata fara? Wani xufa ta ji na keto mata, can ta dake tace "Ina driver din?" Aminu yace "Ya tafi yayi wanka" Tace "Sae kaje kace masa ya fito ya kai ni makaranta ni dai" Aminu ya mike da sauri yace "Toh Hajiya" daga nan ya nufi chalet din. Bayan Aminu ya shiga har dakin da khalil ke ciki ya sanar masa abinda Nihad tace, khalil dake zaune gefen gado yana combing kansa yace "Ta saba xuwa makaranta karfe bakwai da rabi dama?" Aminu yace "Atoh dae, nima ban ta6a ganin ta fita da safe xuwa makaranta ba wai kuma ran asabar, amma kai dai kawai ka fito kaje ka kai ta kar ta kara maka wani fitsarar" Khalil ya kallesa bai dae ce komai ba yana ci gaba da combing din kansa, Aminu ya bi dakin da kallo yace "Wai!!! amma kana kokarin gyara dakin nan, dubi fa dakin kamar a can daya bangaren, ba dauda ba wari ba tarkace, wannan ai idan na kwanta a nan sai in makara al-qur'an...." Khalil ya mike yace "Mu je..." Aminu ya kasa kunne yace "Ba waya bace ke wannan rurin?" Khalil yace "Mu dai je" Aminu ya mike ya fita dakin, Khalil ya bi sa da kallo kafin ya dage duvet din da ya lullube jakar Nihad da shi a saman gado sannan ya bude jakar ya ciro wayarta dake ta vibrate alamar kira, Husnah ya kara gani for the fourth time a jikin screen din wayar, tun daxu take kira, nannade wayar yayi da duvet don baxae iya silencing dinsa ba sbda security dake jiki, ya dau makullin mota ya fita daga dakin ya kulle sannan ya fita compound. Yanda xaka san abun duniya ya taran ma Nihad xama tayi a kan bench da mai gadi da Khalil ke xama, ita dai tana da yakinin dole Khalil xai hango jakar a bayan flowers kuma ai a bude ma ta bar karfen wajen, wai to don bashi da kunya sai kawai ya kama ya dau mata jaka, yaushe ta sake masa har xai kai hannunsa kan jakarta, wato yanxu jira yake sai ta tambayesa kenan? Cabdi... tana hangosu tayi maza ta mike ta sha kunu, Khalil dai ko kallon direction dinta bai yi ba ya tafi gun motar ya bude ya shiga, bayan yayi warming mai gadi ya bude masa gate, Sai da ya fita compound sannan Nihad ta fita ita ma tana tafiya a hankali ta bude back seat ta shiga ta xauna, Aminu ya dinga daga mata hannu alamar a dawo lafiya, ko kallonsa bata yi ba, Khalil ya ja motar suka bar layin, tunani take to yanxu dai tambayarsa jakarta xata yi? Cab gaskiya baxata yi hakan ba, m ta saci kallonsa ta madubi suka yi ido hudu, da sauri ta dauke kanta ta wani daure fuska ta zuge zip din wani jakar da ta dauko ta fiddo chewing gum ta bude ta jefa baki, shi dai driving kawai yake, sai da suka kusa makarantar tayi gyaran murya tace "Malam ka bude min Ac xafi ya dameni...." A takaice yace "Ke kika san meye shi" Tayi masa wani kallo tace "kace me??" Bai tanka ta ba, ta masa wani shegen harara ta ja tsaki kasa kasa ta ci gaba da taunar chewing gum dinta, suna isa makarantar dai dai department din nasu yayi parking, tana ta sauraron ta ji ko xai yi maganar jakar amma shiru, gabansa kawai yake kallo, ganin bata sauka ba, kuma kamar bata da niyyar saukan yace "Ko yau ma xa a bar maki makullin ne?" Ta galla masa wani harara tace "Ai ba ni na kawo motar ba balle ka bar min makullin" tana gama fadin haka ta bude motar ta sauka ta ki kulle door din tayi tafiyarta, ya bi ta da wani kallo, sai kuma ya sauka ya kulle sannan ya hau motar ya tafi.... Husnah na ganin Nihad tace "Shine nake ta kiranki kike danna min busy Nihad?" Nihad ta sauke ajiyar xuciya amma ta ki bata amsa, ta nemi seat ta xauna, wato dai a takaice drivern nan ne ya dau jakar tunda gashi har Husnah ta kira ana ta danna mata busy, lallai mutumin nan raini me karfi ya shiga tsakaninsu, bayan dauke mata jaka sbda guts har bude jakar ma yayi kenan, muryar Husnah ya dawo da ita daga tunanin da take, tace "Ina magana kin min shiru, dama ba komai bane ce maki xanyi ki taho da jakar da kika je birthday jiya da shi, don akwai abubuwana a ciki" Nihad ta kalleta tace "Abubuwanki kamar me?" Husnah tace "Kwalban Codeine dina da Naff na ciki, sai prophylactics, ni ina jin kamar ma har da lingerie dina a jakar, don na duba ban gani ba...." Nihad ta zaro manyan idonta tace "Duk a cikin ina???" Husnah tace "Jakarki mana, kinsan yana da girma" Nihad bata san sanda ta mike ta dafe kirjinta ba tace "Na shiga uku...." Da mamaki Husnah tace "Kin shiga uku kuma? Me ya faru?" Nihad tayi narai narai da tace "Wayyo Allah na, Me yasa xa ki min haka ki ajiye abubuwan nan a cikin jakata Husnah? Me yasa xa ki min haka? Gashi yanxu jakar ta fadi a bakin gate ban san wanda ya dauke min ba" Husnah ta gwalo ido tace "Kaiii, garin yaya kika yarda jaka a bakin gate Nihad?" Nihad da abun duniya ya isheta ta koma ta xauna ta cije yatsa tace "Na shiga uku" Husnah ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh kinsan wa ya dau jakar ne?" Ta kalli Husnah tace "Wallahi wannan driver din nake zargi don shi kadai ya gan ni sanda na dawo da asuba don a bayan flowers dake kofar gida na fara buya as a result of people coming out from the mosque after subhi prayer" Husnah ta rike ha6a tace "Ji tsiya, Driver kuma?" Nihad ta kasa cewa komai tayi tagumi, Husnah tace "Tabb shine kika yi shiru, to me kike jira da har yanxu baki tambayesa ba?" Nihad tace "Toh me xan ce masa? Bayan ban ga sanda ya dauka ba, Har wayata fa na cikin jakar, idan ba sata yake son yi ba ai xai ba Aminu ya ajiye min" Husnah tace "Ehh lallai wannan mutumin ya rika, shi ke ta ja min busy kenan? Wato dai har ya bude jakar" Nihad ta xaro ido tace "Na shiga uku, gashi kin xuba abubuwa kika ce cikin jakar" Husnah ta mata wani kallo tace "Ke dalla to meye, koma me ya gani cikin jakar ba shi ya ga duhu ba, kuma ma bansan uban me kike jira da har yanxu baki tambayesa jakarki ba, ko tsoronsa kika fara ji? ai ba ma tambayarsa xa ki yi ba wai ko ya ga jaka ko bai gani ba, kawai ce masa xa ki yi ya baki jakar ki da ya dauka kar kiyi masa rashin mutunci, kuma kada ya sake ta6a maki kayanki ko da kuwa a titi kika yar don baki aikesa ba" Nihad dai ta rasa abun cewa tunani iri iri ke yawo a ranta, Husnah ta kyabe baki tace "Ni dai ki adana min prophylactics din nan foreign ne ba na kasar nan bane kuma tsada ke garesu, Codeine din kuma shi ma nasan ba kya sha, kar ki je ki xubar ki adana mana gaskiya" Tashi Nihad tayi ta bar mata wajen ta koma seat din baya abun duniya ya isheta, yanxu mutumin nan duk ya ga abinda Husnah ta saka mata a jaka? To amma ya ma yi mugun rainata gaskiya, waye shi da har xai bincika mata jakarta?? A daddafe Nihad ta yi lectures daya tace xata tafi gida, Husnah tace "Ke don Allah ki saki ranki, ko Abba ne ya ga jakar nan ya dauka ya bincika ai sai haka, me xai dameki akan wani shegen driver dinku ya bude jakar ki? Ae rashin mutunci mafi muni xaki masa idan kin koma gida anjima, ni abinda ya fi damu na ma wayarki ne wllh, don matsiyacin sai ya iya dauka yace xai je ya siyar bai san wayar nan sai ta siye duk yan kauyensu ba, yanxu kawai ki xo mu je police station, cikin lokaci kalilan xa ayi tracking" Nihad ta zaro ido tace "In tona ma kaina asiri kenan, kin zata na gaya ma kowa cewar na yarda jaka da waya a ciki? To har Nihal bata sani ba" Husnah tace "In kince ayi cikin sirri babu tonon asiri ai sai ayi hakan, duk fa mutanena ne, amma wllh so nake a walakanta sa idan aka ga wayar a wajensa, a nakada masa shegen duka" Nihad tace "Husnah bari in je gida ko xan ji saukin abinda ke damuna, i can't endure anymore" Husnah ta ta6e baki tace "Wllh kina da sa ma kai damuwa, duk ki bada space din da lamarin driver xai dinga damunki haka, to wai shi wannan driver din daga ina ya xo yake abu isa isa da gadara haka?" Mikewa Nihad tayi tace "Duk yanda ake ciki xan kiraki da wayar Nihal ai tana da number ki" Daga haka ta fice daga hall din, tun da ta fara school din bata ta6a trekking da kafafuwanta har bakin titi ba sai yau, haka nan ta tsayar da adaidaita shi ma xata iya kirga iya sau nawa ta hau sa a rayuwarta, suna isa gida ta sauka ta bude jakarta ta basa kudi sannan ta shiga gidan, Aminu ne kawai bakin gate, ta ɗan bi compound din da kallo sai kuma tayi kasa da murya tace "Aminu baka tambayar min driver din can ko ya ga jakata ba kuma?" Aminu yace "Anya, don ina da yakini da ya gani xai nuna min, ai shi mutum ne me gaskiya da amana" Ta wani galla masa harara tace "Dallah Malam rufe min baki, duka duka kwananku nawa tare xaka san yana da gaskiya da amana, ashe kai dolo ne ma ban sani ba? To bari ka ji wayata ce ta kusan miliyan daya da rabi a jakar nan" Driver ya gwalo ido yace "Subhanallahi, subhanallahi...." Nihad ta saci kallon wanda ke tahowa ganin driver din ne ta daure fuska ta juya ta nufi cikin gida da sauri, xaunawa Khalil yayi gefen Aminu ganin yanda yake zaro ido kamar mara gaskiya yace "Me ya faru kake buda ido haka" Aminu yace "Ba nace maka ta yarda jakarta ba daxu har tana tambayata ko na gani, to wllh wai har da wayarta na miliyan biyu da rabi a cikin jakar" Khalil ya ciro karamar wayarsa yace "To ta huta..." Aminu yace "Atoh dai, Ta kuwa huta wllh, don yau tana sa uban a gaba ya siya mata sabo wallahi sai ya siya, sai dai uwarta ta hana amma tsaf in dai ita ce xai siya mata, kai kaji waya har miliyan uku, ni yanxu na samu irin kudin nan ai kauye xan koma in tada gini malam, inci me kyau in sha me kyau, sannan in kara mata biyu...." Khalil na kallonsa yace "Haba?" Aminu yace "Wllh tllh, albashin namu fa Hajiya ke amsowa a wajensa ta bamu, Ni dai ban san ko nawa yake bata ba amma dubu 50 50 take bamu, kuma da farkon xuwana akwai wani lkcn da ya ta6a bani da kansa wllh dubu 70 ya bani, to kilan dai har da kyautatawa ce irin tasa ban dae sani ba" Khalil dae bai ce masa komai ba. Nihad na shiga cikin parlor ta tafi dakinta direct, xaunawa tayi gefen gado ta rafka tagumi abun duniya ya isheta, tun da shegen mutumin nan ya xo gidan nan bata da kwanciyar hankali, bude kofar dakin aka yi Nihal ta shigo da sallama, Nihad ta daga kai tana kallonta, Nihal ta karaso ta xauna gefenta tace "Amma ba ki jira ku gama lectures din yau ba kika taho ko" Nihad ta yatsine fuska tace "I am tired, kawai shine na dawo" Nihal tace "Toh ki kwanta ki huta, xuwa yamma sai ki rakani shopping din, kinsan gobe sunday xan tafi fa" Nihad tace "Wa xai kai ki shopping din??" Nihal tace "Khalil" Nihad ta juya ido tace "Waye haka?" Nihal tace "Driver..." Nihad ta bude baki ta rike ha6a tace "Wai khalil? Shi uban wa ya basa wannan suna yana driver? Ni fa na xata kinyi wani saurayi ne Khalil ban sani ba, shi driver din ne yace maki sunansa khalil?" Nihal dai kallonta kawai take, Nihad ta gyada kai tace "Tabdi, ana iskanci a duniya, shi yasan ma'anar Khalil din ma kuwa?? Yau naga mutumi da karfin hali, ke kuma wawuya shine kika yarda sunansa Khalil, to wllh karya yake ba abinda ya hadasa da wannan sunan" Nihal tace "To ko ma dai meye sunan Abbanmu garesa, ko so kike in kira sunan Abba gatsau?" Nihad tace "Toh meye don kin kira tunda ba sunan Abban kika kira ba? Meye don kin ce masa Ibrahim ba shine sunan nasa ba? Wato dai ke kika makala masa khalil din kenan?" Nihal tace "Aa, yace haka ake kiransa dama, ni bani na sa masa ba" Nihad ta bude baki tace "Ji shegen karya, to karya yake munafuki, uban wa ke ce masa haka? Amma fa mutumin nan yayi mugun raina maki wayo ma dai, a kauye wa yasan wani khalil, dama Halilu yace shine xan yarda, to wai tsaya ma tukun, fira ku ke har yake gaya maki sunansa khalil??" Mikewa Nihal tayi tace "Woo na gaji da question and answer din nan, Ko ma meye sunansa ba abu bane da za mu tsaya muna bata lkci akai, ni dai anjima ki shirya mu je Sahad store din" Nihad tace "Allah ya kiyaye in dai can xaki wllh baxan je ba, ga wajaje irinsu wellcare kice min Sahad, ai kowa da kowa ke xuwa Sahad" Nihal ta juya ta kalleta, sai kuma ta girgiza kai kawai ta fita daga dakin. Nihad ta rike ha6a tace "Ji maye wai khalil, shi a lallai ya xo gidan masu kudi bari ya maida sunansa irin na yan gayu wai khalil, aa Khalo ba khalil ba" Ta ja tsaki ta mike ta shige bandaki. Ta a fitowa ta koma gefen gado da take xaune ta xauna, tunani ta shiga yi a ranta, to ko dai taje can chalet din da kanta ta duba jakarta ne? Ta kalli agogo lkci daya ta mike ta fito main parlor Umma tace "Aa har kin dawo er baba" Nihad ta gaisheta sannan ta fita balcony har sannan taga yana xaune tare da Aminu a bakin gate, komawa ciki tayi ta shiga kitchen sannan ta bude kofar kitchen din da xai sada ka da back yard din gidan wanda ta nan ma xaka iya xagawa har xuwa Chalet, ganin yanda Hafsah ke kallonta ta sha kunu tace "Ya dai da kallo haka ke kuma?" Hafsah ta kauda kanta, Nihad ta fita da sauri ta xaga ta baya sai Chalet, bata ga takalmin kowa a bakin kofar ba alamar su Isiyan ma duk basa nan kenan, a hankali ta bude kofar tana leka parlon sannan ta shiga, da sauri sauri ta fara dudduba parlon, har xuwa dining area bata ga alamar jakarta ba, har bandakin dake parlon sai da ta bude, wanda sai da ta kusa amai, ta kullo da sauri tana yatsina fuska ta yi hanyar dakunan chalet din, duk dakuna biyun dake a bude sai da shiga tana tottoshe hancinta tsabar tsami da doyi, na ta bincika kaf Ghana must go da ta gani a dakunan amma bata ga jakarta ba, dakin da khalil ke ciki ta murda ta ji a kulle, to ko dai nan dakin aka ajiye jakar nata shine har da kullewa da makulli, tunanin inda xata fara nemo spare key ta shiga yi, can ta zare key din dake jikin kofar su Isiya ta juya ta fita da sauri ta xaga ta koma kitchen, sai da ta wanke hannunta da morning fresh ta hada har key din tana yatsina fuska sannan ta shigo parlor, har wani tashi taji xuciyarta ke yi sbda warin da ta dinga inhaling, kazami irin wannan har shi xai takura mata a gidan nan ya dinga shiga gonarta, dubi wajen da suke kwana wanda ita ko pig take rearing baxata bari yayi rayuwa a irin wannan kazantaccen wajen ba, tana wannan tunanin ta faki idon Umma dake waya ta shige bangaren Abbanta, direct dakinsa ta wuce bayan ta shiga parlor, nan ta hau bude duk wani drawer da ke dakin, a bedside drawer ne ta ga bunches of spare keys na gidan, tayi murmushi ta kalli na hannunta sannan ta hau duba irinsa, kaf irinsu guda uku dake wajen duk sai da ta dauka incase of necessity sannan ta mayar da drawer din ta kulle ta mike ta fice daga dakin, kitchen ta sake bi ta xaga xuwa Chalet din, da sauri ta shiga ciki ta nufi hanyar rooms din, dakin dake kulle tayi facing, ta hau gwada makullen hannunta da sauri da sauri, lkci daya ta bude dakin, wani farin ciki ne ya lullubeta, ta shige ciki ta kulle tana bin ko ina da kallo gabanta na faduwa? Banda kamshi babu abinda ke tashi a dakin, rigarsa da ta gani saman gado ya sa ta gane shine a dakin, rike ha6a tayi.... to gidan uban wa ya samo wannan turaren da ya xuba a dakin haka, bata daina bin dakin da kallo ba ta karasa middle of the room, the room look so different kamar ba a chalet din ba, babu tarkace da kaya kamar irin na su isiya sannan everywhere looks so neat and tidy, ta kyabe baki without bothering ta hau yin abinda ya kai ta dakin, Duvet ta gani kamar an rufe abu da shi ta tafi da sauri ta daga sai ga jakarta a ajiye saman gadon, xaro ido tayi wani farin ciki ya lullubeta, ta bude jakar tana bincikawa da sauri, banda abubuwan da Husnah ta xuba mata a jakan sai nata tarkacen bata ga alamar wayarta a ciki ba, nan kuma ta marairaice tana bin dakin da kallo, a ina to ya ajiye mata wayar?? Sake jakar tayi ta nufi tasa jakar kayan dake dakin, sai bin jakan take da kallo kafin ta durkusa ta xuge zip din, ko karasa bude zip din bata yi ba tayi ido hudu da wayarta, babu bata lkci ta dauka, dai dai nan kuma aka bude kofar dakin, tsabar rudewa da tsorata da tayi bata san sanda ta mike ta saki wayar jikinta na rawa tace "Wayyoo... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" 


Domin karanta Chapter 12 sai ku dannan bulun ubutun dake kasa ko kuma hoton dake kasa 👇👇👇


https://aihausanovels.com.ng/hausa-novels/nihaad-chapter-12-by-khaleesat-haiydar


07087865788 ✍🏻

[7/3, 10:46 PM] +234 706 192 1716: 💖💖 *NIHAAD*💖💖



No comments