Nailah 1
~*(The abandoned flower🌹)*~
*Na*
*Baebee*
~*WRITER OF✍🏽*~
*MUSAYAR BURI*
*YAN DABA NE (The revenge)*
*ZUCIYARMU* *AND NOW.......*
*NAILAH* ~*(the abandoned flower🌹)*~
*Wannan labarin da duk abinda ya ƙunsa ƙirƙira ne, idan yaci karo da rayuwar wani ko wata arashi ne a gafarce ni*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAY*
*PAGE 1*
Ƙauyen Dosan
Ƙauye ne mai matuƙar kyau da yanayi mai daɗi, mutanen garin gaba ɗayansu shuwa Arab ne sai yan tsiraru dake fararen tubawa, wannan ya saka sam ba'a samun baƙin mutum a ƙauyen.
Dukda cewa ƙauye ne; amma akwai makarantar primary da kuma islamiyya da ake koyar da yara a ciki.
1:30pm
Tana fitowa daga ajin su duk sa'aninta dake tsaitsaye suna jiran fitowar yan uwansu suka dare suka bar gurin,sai ƙananan yaran da suka yi dandazo suna jiran fitowarta ne suka shiga binta a baya suna fizgar mata hijab ɗin jikinta ta kowanne ɓangare, yayin da wasu suke jifar ta da ƙasa suna kiran ta da “MAI WATA KALA”
Duk abin nan bata ko juya ta kalle su ba, kan ta a sunkuye yake tana tafiya da ɗan sauri kamar kullum sai dai jin an fizge glass ɗin dake idon ta an yar a ƙasa ya saka ta saurin duƙawa ta fara laluben shi tamkar ba shine a gabanta ba.
Da sauri shugaban makarantar da ya hango abinda ke faruwa ta tagar shi ya nufo inda suke da bulala a hannunsa haka yasa duk yaran suka watse suka ruga.
Yana zuwa ya duƙa ya ɗauki glass ɗin ya bata a hannunta ta amsa ta saka, ganin ko waye kuma tayi murmushi tace nagode sannan ta wuce, sai a lokacin ya juyo kan yan mata biyu da shekarunsu ba zai gaza 14 ba yace “yanzu ku kuna ganin halin da 'yar uwarku take ciki amma ba zaku taimake ta ba, sai ku tsaya kuna dariya”
Basu ce masa ƙala ba sai taɓe baki da suka yi sukai gaba, haka ya saka shi yin tsai yana ayyana lallai duk yadda zai yi sai yayi dan ya fitar da *Nailah* daga ƙauyen nan ya kaita birni dan shi yana zuwa birni yana ganin masu kalar fatar ta watau BAƘA, ƙila a can ta samu kwanciyar hankali.
Ba kamar nan da kowa ke gudunta ba, babu mai zama a inda take, sannan duk ranar Allah idan aka tashi daga makaranta sai yara sun jefeta da ƙasa suna mata ihu har ya kai wata rana ta shigar mata ido shine ya zama silar ciwon idonta ya kasance ganin nata ya zama biji- biji, sai shine ya samo mata glass ɗin da take sakawa wanda yake ƙarfafa mata ganin ta.
Haka suka tafi tana gaba suna bayanta dan ko kaɗan basa so a gane cewa tare suke ko kuma guri ɗaya zasu nufa da ita, Nailah kuwa sauri kawai take yi dan babban burinta ta sada kanta da gida ta killace kanta, tana zuwa ƙofar gidansu ta tarar da Abbansu yana alwalar Sallar Azahar bata ce masa komai ba ta shige dan ta san ko tayi maganar ma ba amsa ta zai yi ba.
A tsakar gida ta ajiye jakarta ta wuce bayi mintina kaɗan ta fito tayi alwala sannann ta ɗauki jakarta ta wuce ɗakinta wanda ya samu shafen siminti sai dai babu ko leda sai tabarma ce a shmifiɗe can lungu kuma yar jakar kayanta ce daga haka kuma babu komai.
Tana jiyo yan uwanta da suka dawo suna ta kai kawonsu a tsakar gida wanda ita sam bata da wannan yancin, Abbansu da kansa yace baya buƙatar ya dinga shigowa yana ganin giccinta a cikin gidan dan haka sai take kafakafa da haɗuwar tasu, tana zaune har mahaifiyarta ta shigo da robar abinci a hannunta tana murmushi tace *Agla* yau kuma ba zaki je ki amshi abincin ki
, gashi na kawo maki ki taimaka man kici ko zan samu nutsuwar zuciya.
Bata kalli abincin ba sai matsawa da tayi ta ɗora kanta a gefen kafaɗar Ommi tace" Ommh kince min komai me wucewa ne ko?
A nutse Ommi ta ɗago kanta tana kallon fuskarta tace" eh ..... Komai yana wucewa, babu abinda yake dauwama a duniya na daɗi ko wahala dan haka kici abincin nan kafin lokacin islamiyya"
Nailah ta gyaɗa kai tare da fara cin abincin tana jin natsuwa a tare da kalmomin mahaifiyarta.
Kamar yadda headmaster ya ƙudurta ya samu mahaifinta bayan Sallar Magriba yana zaune a ƙofar gidan bisa tabarmar kaba, gefenshi kuwa buta ce da ƙananan kofina irin na shan shayi yayi masa sallama, a mutunce Malam Sagir ya amsa dan akwai yar mutunci tsakanin su, bama shi kaɗai ba, duk mutanen garin suna girmama shi saboda irin halinsa na dattako.
Saida ya tabbatar ya mayar da dukkan nutsuwar shi a kansa sannan ya cigaba da faɗin "Malam Sagir dama nazo maka da wata magana ne da zata amfane mu baki ɗaya, akwai makaranta a birni da ake kwana kuma an fi karatu a can shine nace mi zai hana a kai Nailah can tunda a nan an naga kamar bata samun sukunin yin karatu a nutse kaga yadda aka yi mata sanadin idanunta ina jin tsoron abinda zai iya biyo wa baya kuma.
Da yake mahaifin nata ma neman kai yake da ita cikin sauri ya tari numfashinsa yana faɗin ai wannann ba matsala bane shedimasta bari in kirawota ku tafi yanxu ma" yayi maganar yana ƙoƙarin tashi tsaye dan da gaske shi so yake ma su tafi yanzu ɗin, Malam Abubakar ya dakatar dashi da faɗin a'a jiran malam Sagir ai ba yau ba, yanxu nazo ne in sanar da kai kuma in nemi izini idan ka amince sai na tafi da ita zuwa jibi InshaAllah.
Malam Sagir ya koma ya zauna yana kaɗa ƙafa yace to to to ai shikenan Allah ya kaimu jibin lafiya.
Daga haka Malam Abubakar ya miƙe yayi masa sallama ya wuce dan dama ya san Malam Sirajo ba zai hana ba, babu wanda bai san shima neman kai yake da yar tashi ba.
Tunda suka yi maganar ko mahaifiyarta bai sanarmawa ba sai ranar da Malam Abubakar ɗin yazo zasu wuce ya shigo yana ƙwala mata kira, ta fito a nutse tana faɗin lpy dai malam wannan kira tun daga waje.
Ɗakin Nailah ya nuna mata tare da faɗin" ki fito da ita ga shedimastan su zai wuce da ita, mun gama magana zata koma makarantar kwana a can birni.
Da sauri Ommi ta rumtse ido na yan seconds sannan ta buɗe su a hankali sai kuma tayi murmushi mai ɗaci ta juya ba tare da tace komai ba ta shiga ɗakin .... tana haɗo kayanta lokaci ɗaya kuma tana sanar mata inda zata je da kuma abinda zata yi a can wato karatu.
Nailah ta taso cikin wata rayuwa mara 'yanci, haka yasa komai cutarwar da za'a mata bata ko ɗaga ido ta dubi mutum, bata san miye dariya ba sannan ba mutum ce mai kuka cikin sauƙi ba, duk duniya mutum biyu ne suke ganin murmushinta, daga mahaifiyarta sai shugaban makarantar su dan sune kaɗai suke nuna mata kulawa.
Amma a yau sai gashi tana zubar da hawaye, cikin sassanyar muryarta wadda takan yi kwanaki bata furta kalma ɗaya ba tace “Mama nah ina so in zauna dake”
Murmushi mai tafe da yanayin biyu Ommi tayi sannan tace “A'a Nailah wani lokaci mutum baya gane darajarsa sai ya shiga cikin mutane masu daraja, ki je ki nemo darajarki a inda take, ina so in ganki cikin darajarki”
Tana gama faɗin haka ta juya da sauri ta shige ɗakinta sannan ta saki kukan da take ta ƙoƙarin dannewa a gaban 'yar ta.
Juyowa Nailah tayi ta kalli yayarta da ƙanwarta dake gefe ransu fal farin cikin zata bar gidan dan ba ƙaramin ƙalubale bane a garesu idan aka kira ta da yar uwarsu.
Sai kuma ta juya ta bi bayan shugaban makarantar su dake tsaye a farkon gidan yana jiranta.........✍🏽
*Sabon salo, sabuwar tafiya mai ƙunshe da darussan rayuwar yau da kullum sannan mai ɗauke da sassanyar soyayya, free book ne dan masoya InshaAllah*
No comments