Mawahib 7-8

 


7&8








Cikin sanyin jiki ta qarasa shigowa falon,tazauna kusa da Mamy tace"Mamy me a kayiwa Yaya Ashraf tunda yashigo naga kamar yana fishi"


Cikin basarwa Mamy tayi murmushi tace"Fada yake saboda kinfara tsayawa da saurayi, baisan su Alhaji ne suka bawa Nabil damar zuwaba,tun ranar da mukai waya da Yaya Mustapha Abbanki yaje yasamu Yaya Alqali yafada masa komai" 


Ahankali Mawahib tasaki ajiyar zuciya tazauna,tabawa Mamy ledar hannunta cikin dari-dari tana tsoron kartayi mata fad'a,cikin murmushi Mamy ta kar6i ledar tace"Kawo miki yayi?"


Tace"eh, saida nace yabarshi shine yace zai fad'a miki" 


Mamy tace"to inbanda shirme menene naqin kar6a? koba maganar soyaiya Nabil ai yayanki ne,dani da mahaifinsa uwarmu daya ubanmu daya,bazanyi fad'aba danya baki wani abu,bari mugani menene aciki"


Tafadi hakan tana bude ledar,kayan kwalliya ne aciki masu tsada harda turarukan da chocolate dayawa,sai wata 'yar qaramar Envelope da dubu goma aciki,cikin murna Mamy tace"lalle Nabil,wannan uban kaya haka ai kinci qarfin albashin nasa,Allah yasanya Alkhairi,amma ya kikagan shi? ya miki?"


Cikin tsananin kunya taturo dan qaramin bakinta gaba tace"kai Mamy dan Allah....nide kidena min wannan maganar" 

cikin sauri tamiqe zatabar wajan, Mamy tana dariya tace"dawo ki dauke kayan ki,kije kikaiwa 'yar'uwar taki itama"


Cikin shagwa6a tadawo tabude kayan tadibawa Nabiha komai,sannan tatafi zatakai mata.



Nabiha tagama dudduba kayan da Mawahib takawo mata, cikin mamaki tace"Gaskiya kinyi sa'ah Mawahib,yaya Nabil da qarfin sa yafuto,kuma da alama da gaske yake tunda gashi ta wajan iyaye yafara neman,kuma daga gani bashida rowa,gashida fara'ah masha Allah, kinsan wannan kayanfa tsada ne dasu"


Mawahib tayi murmushi tace"nima shiyasa naji yafara birgeni,tunda yazo yaketa bani dariya,gashi bashida shekaru sosai irin mijinda nakeso,ke kinsan meyafaru dazu da yamma kuwa?Yaya Ashraf yadinga yiwa Mamy fad'a saboda na saurari Yaya Nabil,kuma fa Abbana yasan da zuwan nasa"


Nabiha tayi shiru tana sauraron Mawahib,tunda Mawahib d'in tafara magana dayake ita tafita shekaru da wayo, nan da nan ta dauki haske akan dalilin fadan Yaya Ashraf din, tayi shiru saida tagama jin qarshan zancen sannan tayi ajiyar zuciya tace"kinsan abinda nake tunani? Yaya Ashraf fa Ina zargin sonki yake"


gaban Mawahib yayi wata irin faduwa,cikin tashin hankali ta zaro idonta tace"dan Allah Nabiha? Innalillahi...naga takaina"


Nabiha tace"menene abun wani innalillahi...?  kinsan Allah sonki yake,kuma zakice nafada miki"


Mawahib tace"ai yanzu yaga Yaya Nabil,nikam babu ruwana, bazai ma fadamin ba, babu ruwana da Momy kilishi"


Cikin bada qwarin gwiwa Nabiha tace"kinsan Allah,ki ajiye wannan haqurin naki irinna Mamy agefe ki fuskanci rayuwa, wani lokacin idan biyaiya tayi yawa anfi yima is'kanci,kina mata biyaiya kamar itace takawo ki duniya,ni bakiga idan tana sababin tama wayata nake dauka ba?"


Cikin rawar murya Mawahib tace"bazan iyaba Nabiha,itama kamar uwa ce awajanmu, watarana ai sai labari,nan gaba kadan ma zanbar mata gidan har abada inkoma wajan Yaya Nabil maiduguri"


Nabiha tace"to ai shikkenan,saiki daina rawar jikin"

Sai a lokacin Mawahib ta Lura jikinta rawa yake tunda Nabiha tace mata Yaya Ashraf yana sonta, sun dade suna fira daga baya tayi mata sallama tatafi.


Washegari da safe takama weekend ne, Mamy tana gida bataje ko'inaba,itama Mawahib tun safe data gyara musu part din nasu takoma dakinta tagyara shi,tarasa meyasa tun safe gabanta yaketa faduwa,sai Addu'ah taketa maimaitawa aranta, tana gama gyara dakin Yaya Nabil yakira wayarta,tayi zamanta adakin suna wayarsu,

Mamy ce taqwala mata kira cikin sauri tayi sallama dashi tafuto,ganin Mamy tayi dauke da wani yaro yana kuka kad'an-kad'an, ita kuma Mamy sai jijjigashi take,Mamy ta kalle ta tace"d'auko hijabin ki kikai wannan yaron gidan Maman Fati,yanzu ta aiko shi nayi masa allura kuma naga yaron daya kawo shi kamar bazai riqe shi dakyau ba,nace yaje yaturo babba adaukeshi,kuma kinji shiru babu wanda yazo"


Tace"to Mamy"


Sannan tajuya dakinta tadauko hijabi tafuto,hayaniyar datake ji a waje ne yabata mamaki tarasa me'akeyi haka,Mamy ta nufo bayanta da yaron tace"yi sauri ki goyashi kikai matashi yaro yanata kuka tun dazu" 


tafad'i hakan tana dora matashi abayanta, Mawahib tasa zanin goyon tana kokarin goya yaron, tace"Mamy wai hayaniyar menake ji a waje? kosu Daddy ne suke rabon zakka?"


Cikin sauri Mamy tace"riqeshi ki goyashi ni,kin dameni da tambaya sauri nake,CAPTAIN ne yazo, inaso inyi sauri inyi masa ferfesu med'an sauqi"


tana fad'ar haka tayi d'akinta tabar Mawahib atsaye a wajan


Haushi yakama Mawahib,tabi bayan Mamy da kallo gabanta yana dukan uku uku,cikin ranta tace"mukam yau munshiga uku, bala'i yadawo"


tajuya ta kalli yaron dayake goye abayanta yana qishin-qishin din yin kuka,cikin haushi kuma a fili tace"Yanzu fisabilillah Mamy saboda wannan mutumin jikinta yake rawa haka? saikace wani mutumin kirki za'a je anayi masa wani farfesu? wahalalle yanzu haka da wannan uniform din nasa na kullum-kullum yazo"(😱) 


tasake juyawa ta kalli yaron dayake goye abayanta,tatuna maganar qawayenta 'yan makarantar su dasuke cewa goyo yana zubar da Nono, cikin fad'a tafara qoqarin sauke yaron daga bayanta tareda fadin"kaikuma sauko,wallahi bazan goyaka ba"

tasake rage muryarta taci gaba da fadin"Salon d'an nonon nawa duk su zube mijina yarasa na kamawa...."(🙊) 


Qamshin turaren daya bugi hancinta,wanda bata gama tantancewa nawaye ba yasa tajuya bayanta dasauri....,lokaci d'aya idonsu yahad'u dana juna,gabanta yayi wata irin fad'uwa,atake gumi yafara rufe mata fuska,idonta yayi tsilli-tsilli qarara tsoro ya baiyana a cikinsu,Addu'ah take aranta Allah yasa baiji maganganun datayi ba, kallonta yake fuskar nan tasa murtuk babu alamun fara'ah,amma hakan bai hana kyawunsa baiyana ba,kyakykywane ajin farko,kamar kullum yana sanye cikin kakinsa na Soja,kayan yayi mutuqar yimasa kyau,farar fatar jikinsa tabada hadin kai wajan qawata uniform din a jikinsa,agaban rigar bangaren hannun dama an rubuta CAPTAIN ARYAN,gefen hannun hagu kuma an rubuta NIGERIAN ARMY.



Jikinta ne yadauki rawa,cikin sauri tacire idonta daga nashi,gani take kamar wani abu ne yake futowa daga cikin nasa idon yana shigewa cikin nata idon,da sauri ta matsa ta bashi hanya, tayi wuf tafice daga part din nasu,saura qiris ta doka tuntu6e takayarda yaron hannunta,kai tsaye ta nufi get tafice daga gidan, saida taje bakin get din nasu sannan taga sauran mutane sunata daukar kayan abinci kama daga shinkafa har zuwa taliya da macaroni,gakuma wasu sojoji a tsaye agefe kowanne hannunsa daukeda bindiga, cikin sauri ta wuce kai tsaye taje takai yaron gidansu, sannan tadawo gida,tanaji tana gani part dinsu ya gagareta shiga,sai part dinsu Nabiha ta wuce.


Duk yanda sanyin esi ya ratsa dakin Nabiha, hakan bai hana Mawahib cire hijabin jikinta tana sake firfita dashi ba,Nabiha tace"meyake faruwa ne Mawahib naga sai gumi kike hadawa?"


Cikin rawar murya tace"nida Yaya Captain ne...,maganganu nasaki baki inata fada,bansan yana bayana ba,bansani ba yaji abinda nake fada ko baiji ba,amma kunya ta kamani, na aikata abinda ba halina bane Nabiha"


Cikin sauri Nabiha tace"innalillah....Yaya Captain kuma?to me kikace? wacce maganar kikayi?"


Mawahib tayi shiru tana tunanin me zata cewa Nabiha? nayi maganar nono kuma Yaya Captain yajini?kokuma nagama zaginsa tsaf kuma yajini? 


Cikin sauri ta girgiza kanta tace"kede abar kaza cikin gashinta,amma na tabbatar inde yaji abinda nafada,babu abinda zai hanashi dukana"


Nabiha tace"to yau kin janyo mana ruwa, kinganni nan? tunda naji hayaniya a waje nasan cewa shine yazo,shiyasa naqi fita ko nan da can"


Mawahib tace"to yanzu yaya zanyi Nabiha?"


Nabiha tace"wai akenki yayi kikaqi zuwa ne?"


Cikin rawar murya Mawahib tace"nace miki kidena tambayata abar kaza cikin gashin ta,ni wallahi yau babu inda zanje daga nan"


Tana fadar haka ta kwanta a gadon Nabiha tareda shigewa cikin bargo,gaba daya sai taji zazza6i yana neman rufeta.


Ba'ita ce tabar part dinsu Nabiha ba, saida aka kira sallar magrib, taji gidan shiru alamun duka mazan gidan suntafi masallaci, sannan ta lalla6o ta wuce part dinsu da gudu.


 da daddare suna zaune afalo da Mawahib da Abba dakuma Mamy suna kallo, Mawahib tana sanye cikin doguwar riga ta bacci amma mai kauri, su Mamy suna kallo suna fira kad'an kad'an, amma Mawahib gaba daya tunaninta baya kansu, shawara tagama yankewa aranta gara tahada kayanta tatafi maiduguri idan taji labari Yaya Captain yatafi, saita dawo, kokad'an bataji dadin zuwansa ba, ga kuma rashin kunyar data gama yimasa wanda bata saniba yaji ko baiji ba.


Abbanta yayi magana yaji shiru bata saka baki, a hankali yajuya ya kalle ta yace"yanmatan Abba, babu matsala deko?"


Kallansa tayi cikin ladabi tace" Abba babu matsala,amma inaso idan ka amince zanje maiduguri"


Abba Yajuya ya Kalli Mamy yace "lafiya zata tafi?"


Mamy tace"Alhaji nima sai yanzu naji zancen tafiyar"


Cikin mamaki yace"meyafaru zaki tafi,kuma tafiya babu shiri baki sanarda mahaifiyar kiba?"


Wani irin murmushin qarfin hali tayi sannan tace"Abba dama inaso naje hutu ne kafin hutun mu yaqare"


Abba yace"A a Ruqayya,yaushe kukai hutun ai baki gama hutawa ba,sannan ga yayanku yazo d'azu da yamma, kowa yana gida,bai kamata kitafi ba,ni kinyi masa murna ne akan karramawar daya samu?"


Wani irin qullutun taqaici ne yakama Mawahib,yanzu saboda Allah dan Yaya Captain yazo sai ahanata tafiya hutu maiduguri?

Cikin kwanciyar hankali ta shimfidawa Abbannata qarya tace"eh dazu mungaisa nayi masa ala sanya Alkhairi"


Tana rufe baki, aka turo qofar part din nasu aka shigo,wani irin qamshi mai dadi yadaki hancin Mawahib,sanin datayi cewa irin qamshin dazu ne, hakanne ya tabbatar mata da cewa Yaya Captain ne, hakanne yasa koda wasa batayi kuskuren dago kanta ba,cikin sallama suka shigo falon,dukansu su biyun  sanye sukeda wando three quarter, da riga marar hannu alamun kayan shan is'ka ne a jikinsu tunna yamma,gaba daya sai suka saje suka zama abu d'aya,saide fuskar mutum daya data kasance babu wasa akanta.


Mawahib tayi mutuwar zaune kamar ruwa ya cinyeta,saika rantse bata cikin falon.

Cikin farinciki Mamy tace"yan samari"


Captain yad'ora hannunsa akan daya daga cikin kujerun falon yace"Anty Ma-my...."


yakira sunanta a rarrabe,cikin murmushi tace"Captain"


Yaya Ashraf yace"Anty Mamy akwai sauran kunun madarar nan na dazu?"


Mamy tace"akwai, yana dinning bari in dauko muku"

Tafadi hakan tana kokarin tashi, Abba ya Kalle ta yace"yakamata kiyiwa 'ya'yanki fad'an ajiye iyali Maryam"


Mamy takawo musu kunun madarar wanda yaji kwakwa aciki har lokacin da zafinsa,tazuba musu a cup tabawa kowa,ta zauna a kujera tana fadin"to gasunan de Alhaji,inajin saimun fara tallarsu a yanar gizo"


Adede lokacin Yaya Nabil yakira wayar Mawahib,a hankali tasaki wata irin ajiyar zuciya,dama atakure take a wajan,idan tatuna maganar Nabiha datake cewa Yaya Ashraf yana sonta, tasake tunawa da kato6arar datayiwa Yaya Captain dazu, gaba daya saitajita atakure, a hankali tamiqe tanufi hanyar dakinta,Captain Aryan yana shan kunun madara yad'ago da manyan idonsa a hankali yabita da kallo,karaf idonsa ya sauka akan hips dinta,cikin sauri yad'auke kansa.


Shikuwa Yaya Ashraf kasa daina kallonta yayi, har saida yaga ta shige dakinta tareda rufowa.


Mamy tayi ajiyar zuciya ganin Mawahib tabar wajan,gaba dayansu tana lura dasu yanda suka bi yarinyar da kallo, musanman Ashraf da tun shigowar su ya kafeta dawani irin kallo,to shikuma Captain Aryan kallon na menene? a hankali gabanta yafara faduwa,amma data tuna da maganar Nabil, saitaji hankalin ta ya kwanta harta sake sukaita firarsu. 




Sun dade a part din Mamy sannan suka tafi dakin su,Ashraf yafara gyara musu lafiyaiyen gadon su,Captain yana danna wayarsa,d'ayar wayar tasa ce tayi qara, yadauka yana magana a hankali kamar da mace yake magana,Ashraf yayi tunanin Captain din yayi sabuwar budurwa ne, a hankali yadago yana kallon sa saiyaji yana cewa"A a bamu da irin wannan bindigar,idan zaka shigar da bayanan ka rubuta muna buqatar irinta,musanman saboda sababbin ma'aikata wanda zasu kar6i horo ok?"


Daga dayan 6angaren aka amsa masa, sannan ya ajiye wayar.

Ashraf yace"bansan yau zaka shigo gari ba, da nasa yaran nan sun gyara mana dakin,duk yayi datti wallahi"


Hankalinsa yana kan waya yace"nima bansan zan taho ba,kawai nagaji ne,kuma inason ganinka kaida Momy, shiyasa kawai nataho,toko muje gidanka mu kwana tareda wad'ancen sojojin?"


Ashraf yace"Rigima boy kenan....babu matsala mu kwanta kawai gobe saisu gyara mana,wai kasan yarinyar nan Zulaihat kuwa har yanzu tana nan tanata nacin kirana?"


Captain ya ajiye wayar hannunsa yace"karabu da'ita kawai,dan nima ganin farko danayi mata naji tamin..."(😲)


Ashraf yace"but... tabani tausayi, tana kuka tana tambayata meyasa zan yaudareta?"


Cikin rashin damuwa Captain yace"toya zatayi? Kashareta kawai kanemi wata"


Ashraf ya zauna abakin gadon ya kalli Captain yace"amma kasan idan nasake yin wata budurwar kace kana sonta saika raina kanka?"


Captain yace"to idan aka dace Ina sonta ya zakayi? zamu auri mace d'aya ne?"


Ashraf yadauki fillo yadora a cinyarsa sannan yace"wai kai baka ga Mawahib bane?"


Saida ya yatsina fuskarsa sannan yace"wace hakan?"(😲) 


Ashraf yayi masa wata irin harara sannan yace"Mawahib d'in Anty Mamy mana"


Cikin rashin kula Captain yace "Oh..."


Ashraf yace"kamarya oh.....?  wai kana nufin har yanzu kana nan kanaqin yarinyar nan?,ko saboda Anty Mamy yakamata kadena nunawa 'yarta qiyaiya...."


Cikin damuwa ya lumshe idonsa yabude sannan yace"Bansan jin maganar marar kunyar yarinyar nan Ash...,at all ma nibata gabana,ni maqiyin qasata shine maqiyina ba wannan qwailar ba...."(🙊😳😱)










(Captain Anya kuwa?🤔, to muje zuwa de 💃🏼💃🏼) 






Amnah El Yaqoub✍🏻


💗MAWAHIB💗



Writing By Amnah El Yaqoub

No comments