Mawahib 5-6

 5&6






Bayan tagama abinda take bata dawo gidanba saida ta daidaici lokacin dawowar Mamy daga Asbiti yayi, sannan itama tadawo gidan, gashin nan nata kuwa yasha gyara sai qyalli yake,jikinta yayi sumul dashi kamar ka latsa jini yafuto, koda ta nunawa Mamy gyaran da'aka mata koda wasa bata fad'a mata yanda sukai da Hajiya Kilishi ba.



Washegari da daddare suna zaune afalo gaba dayansu,Mawahib tana sanye cikin kayan bacci riga da wando mai santsi,wandon dogone har qasa, sai 'yar qaramar riga, tayafa dan qaramin mayafi a jikinta,amma kana Iya hango yanda sumar gashinta ta kwanta a goshinta.


Abba ya ajiye cup din hannunsa mai daukeda fruit salat, yad'auki remote yana canja channel tareda fadin"dazu su Yaya Ibrahim suka tafi Abuja,sunyi min magana kozan samu zuwa to ayyuka sunmin yawa a office shiyasa nima ban bisu ba,yauce ranar da za'a karrama su ARYAN,yana d'aya daga cikin wanda shugaban qasa zai karrama su saboda qwazonsu a wajan aiki"


Mawahib dake danna wayarta tayi shiru tana Jin abinda Abbanta yake fad'a,a wannan baqin halin na Yaya Captain tarasa yanda akai harya samu yashiga jikin manya gashi hardashi za'a karrama. 


Cikin murna taji Abbanta yana fadin"Alhamdulillah Maryam kinga ma gashi suna nunawa a wannan tashar"


Cikin farinciki Mamy Tace"masha Allah,aikam gasunan,Alhamdulillah, Allah yasanya Alkhairi"


Cikin Jin dad'i Abba yace"ni gaba d'ayama sainaga Mawahib tana juyewa tana yin kama dashi,da idon,da hancin, da bakin,gaba daya na Captain Aryan ta d'auko"


Yajuya ya Kalli Mawahib da hankalinta yake kan waya ko inda TV take bata kalla ba,yace"koba hakaba 'yanmatan Abba?"


Ahankali tasaki wani murmushi mai kamada yaqe...

Sai a lokacin ta kalli tv,idonta ya sauka a kansa,kamar kullum yana nan da kyansa,kwantaccen sajen daya zagaye bakinsa irinna Yaya Ashraf yasake qawata farar fuskarsa kamar balarabe,jan lips dinsa d'an qarami mai mutuqar laushi sai sheqi yake kamar ya shafa musu lipstick,fuskar nan tasa ad'aure kana gani kasan babu wasa kamar ma baya farinciki da  karramawar da akayi masa,yana tsaye qyam ya qame waje d'aya,ga shugaban qasa da kansa yana sake gyara masa rank dinsa,ga manya manyan sojoji daga gefe kowa ya qame a tsaye, saida shugaban qasa yagama gyara masa rigarsa,sannan shikuma yasara masa,sannan aka fadi irin jajircewar dayake akan aikinsa, tareda kyautar kudi Naira million arba'in,anan aka buqaci daya daga cikin familynsa yazo su kar6i kyautar tare,kai tsaye Alqali yatura Ashraf,cikin nutsuwa Yaya Ashraf yataka yaje gaban Aryan din  suka kar6i kyautar tare,bama sai anyiwa mutane bayani ba,ana ganin ashraf wanda basu san cewa Captain Aryan 'yanbiyu neba, yau kam sun sani,tsirarun 'yanmata wanda suka samu damar zuwa wajan taron lokaci daya kallon su yakoma wajan Ashraf da Captain Aryan,kowa mamaki yake dama wannan miskilin Sojan 'yanbiyu ne?


Mawahib tagama qarewa Captain Aryan kallo, taga babu wata kama dasuke kamar yanda Abbanta yafada, banda fari dayake dashi irinnata ita bataga wani abun birgewa a wajan Yaya Captain ba bare har taji dadi dan ance suna kama.


Ganin yanda sauran sojoji suke  qara girmama shi kamar wani nagaske,hakan yasa Mawahib taji wani irin baqin ciki,sai yanzu ne tagane dalilin zuwan Yaya Ashraf gida,a hankali tatashi ta wuce dakinta.


Abba yabi Mawahib da kallo harta shige dakinta,yajuyo ya kalli Mamy yace"madam ya kamata fa asamawa Ruqayya qanne,naga tatafi daki kamar tana fishi,kuma nasan ba fishi take ba, kawai shagwa6a take ji ba'a tafi da'ita wajan taron nan na yayansu ba,shiyasa tatafi d'aki"(🙊)


Mamy tayi murmushi batace komai ba,shima Abba yayi dariya yace"emanah,tana ganin itace qarama a gidan shiyasa take shagwa6a son ranta,inda tanada qanne ai zata rage shagwa6ar"


Mamy tayi murmushi tace"Alhaji kenan,babu wani shagwa6a ita tasan meyake damunta"


Cikin jin dadi yabi ilahirin jikinta dawani irin mayen kallo sannan yace"Allah koh?"


Itama murmushin tasake yi batace dashi uffan ba,saboda tasan ma'anar kallon dayake binta dashi(🙈)


Washegari Hajiya kilishi ce ta kar6i girki,a qa'ida kuma inde itace tayi girki babu wanda take kaiwa part dinsa,saide kowa yaje yadauka,saboda itace babba,Mawahib bataje ta d'auko musu nasu abincin ba,saboda Mamy tana wajan aiki,shima Abba yafita bai dawo ba,ita kadai ce kuma ba yunwa take ji ba, tun safe aketa sallama a gidan,ana zuwa anayi wa Hajiya kilishi murnar karramawar da Captain Aryan yasamu,sai hayaniya akeyi, tana kwance afalonsu tana chat da Yaya Nabil,wani d'an kawunta dake maiduguri tana jiyo surutun mutane kala kala,bata fita d'aukar abincin ba saida taji hayaniyar mutane ta ragu a lokacin itama tagama chat d'inta,rana tayi sanyi, sannan ta futo,tana sanye cikin doguwar riga marar hannu,yadin rigar yanada laushi, daga gaban rigar anyi mata ado da baqin leshi,sai dan qaramin mayafi data d'ora akanta,babu kowa atsakar gidan,kai tsaye ta wuce kitchen tad'auko nasu abincin,futowar ta kenan daga kitchen din adede lokacin Hajiya kilishi tafuto daga part d'inta itada wata babbar mace da alama qawarta ce, cikin ladabi ta rissina tace"Momy Ina wunin ku"


Hajiya kilishi ta amsa a taqaice tace"lafiya"


Ita kuma d'ayar cikin murmushi ta amsa tana bin Mawahib da kallo harta shige part dinsu, saida taga shigewar Mawahib sannan ta maida kallonta wajan Hajiya kilishi tace"Matar Alqali,Ina kuka samo 'yar kyakykywar yarinya haka?"


Hajiya kilishi tace"Hajiya Mariya baki ganeta bane?"


Wadda aka kira da Hajiya Mariya tace"ina zansan wannan yarinyar?  duk zuwan danake bana ganinta,anya anan gidan take kuwa? Kina ganin yarinya jajir da'ita kamar wankan inji? Kiduba kiga wannan uban diri kamar ita tayi kanta,badan da 'yanbiyun samarinki a gidan ba aida nayiwa Farouq d'ina kamu..."


Hajiya kilishi tace" 'yar wajan Maryam cefa,da wanne samarin zaki had'ata?,inaaa! bade 'yanbiyu naba,har abada babu had'i, yanda kika gantannan kullum haka take yawo tana nunawa mutane jiki,ita ga tantiriya,kuma uwarta ce take koya mata komai,idan na kuskura nabari yarinyar nan ta auri d'ana aina kashe kaina, tun yanzu ma kafin ayi mata aure bad'ala iri-iri uwarta take koya mata,to inaga anyi aure? tana saka irin wannan kayan yanzu,idan tayi aure kuma wanne iri kike tunanin zata saka?kinsan 'yar maiduguri ce uwar, idan 'yarta ta auri dana kuma ai shikkenan sai yanda aka min dashi, kiduba kigani de yanda tashiga tafita a wajan malamai da bokaye saida tarabani da 'yanbiyu nah,basu Isa suzo gidan nanba saide kiga sunje part dinta sun tare,Ashraf ma dayazo shekaran jiya danyaga na tsaye masa ne, na Kuma saka masa ido,amma da abinci ma Infad'a miki saide yaci awajanta, to inda nakejin dad'i sauqina d'aya,yarinyar bata gabansu duka su biyun, musanman ma ARYAN...."



Cikin sauri Hajiya Mariya ta katse ta" ke dakata matar Alqali,wai kina nufin yarinyar nan ce 'yar wajan Maryam tagirma haka?"


Hajiya kilishi tace"hmm ai Ina ganin ikon Allah Hajiya Mariya,itace wallahi,ai kallon tsoro kikai mata,bakiga uban nonuwan taba"



Hajiya Mariya tayi ajiyar zuciya tace"to aikuwa matar Alqali tun wuri kitashi tsaye,inba hakaba kiyiwa kanki sakiyar daba ruwa..."


Cikin sauri Hajiya kilishi tace "wa?, Allah yatsare ni,ai har abada babu alkhairi a tsakanin ta da 'yanbiyu na,to Ina alkhairi ga yarinyar da batayi gadon haihuwa ba? Ita kad'ai uwarta tahaifa daga ita babu qari, ita kuwa bana tunanin ma idan tayi auren zata haihu, tunda batayi gadon haihuwa ba,to waima INA UBANTA?, har zuwa yanzu mude bamu ganshi da idonmu ba"(😳🙆🏻‍♀️tofa)


Hajiya Mariya tayi ajiyar zuciya tace"tabdi, aikuwa matar Alqali saiki dage,kuma kisawa 'ya'yanki ido sosai, kinsan maza da jarabar tsiya,da gane-gane, suna qyalla ido idan suka ganta shikkenan,musanman idan wannan dirin nata ya rud'esu,kina zaune saide kiji Ashraf yana cewa shizai aure ta shima Aryan yana fad'in shi zai aure ta...."(😂) 


Hajiya kilishi tayi ajiyar zuciya tace"kada ubangiji ya nunamin wannan baqar rana....to Hajiya Mariya ai bakisan wani abuba,gaba d'ayansu su biyun fa har yanzu basuda tsayaiyar budurwa,abun har tsoro yake bani, shekaru sunata tafiya sunqi aure, musanman Aryan, shi bashida magana, bansan yaya zaiyi yasamu mace ba"


Hajiya Mariya tace"tokode baqar aljana ce ta aure shi?"


Cikin sauri Hajiya kilishi tace"aiko farar aljana ce dole zaiyi aure shima ya ajiye zuri'ah"


"wannan gaskiya ne" cewar Hajiya Mariya, daga nan tarakota get dinsu na farko, sannan tadawo.



******



Da daddare Mamy tagama cin abinci suna zaune afalo gaba d'ayansu, yayanta dake maiduguri Alhaji Mustapha yakira wayarta, bayan sun gaisa yace"Maryam yaronki ne yasani wannan waya, kinganshi nan zaune tun yamma yazo yasani agaba lalle saina kiraki nafada miki shifa yanason Mawahib,yace nafada miki yanason ayi masa izni yafara zuwa wajanta zance "


Mamy tayi murmushi,tasan cewa yayan nata bashida wani da namiji Sai guda daya, sauran duka mata ne, cikin Jin dadi tace"Nabil kenan,yanzu nice nazama haka awajansa? bazai Iya kirana yafadamin da kansa yanason Mawahib ba saide yasaka kakirani kaida kanka Yaya?"


Gaban Mawahib ne yayi wata irin faduwa Jin maganar akanta akeyi,dama Yaya Nabil sonta yake shiyasa taga kwana biyu yana matsa mata da magana idan tahadu dashi a chat?

Bata gama tunanin datake ba taji Mamy tana cewa"a a, batada kowa Yaya, amma Nabil aina gida ne,Allah yasanya Alkhairi, Allah yasa rabon sa ce"


Bayan sungama wayar,cikin jin dadi Mamy ta Kalli Alhaji Isah tace"Abban Mawahib kaji wai Nabil din Yaya Mustapha ne yace afada mana yanason Mawahib"


Abba yayi murmushi ya Kalli gefenda Mawahib take zaune kamar ruwa ya cinyeta,cikin tsokana yace"yanmatana wai zaki aure shi kigudu kibarmu?"


Cikin kunya tatashi da sauri tafice daga part din nasu, tatafi wajan Nabiha. 


Alhaji Isah yayi murmushi yace" To Alhamdulillah, gaskiya naji dadi sosai, Nabil ai yanada hankali,zansamu su Yaya inyi musu maganar,shima saiki fada masa yazo suyi magana shida Mawahib din,idan sun sasanta kansu shikkenan, idan Allah yayi auren dashi,saita qarasa karatunta adakin mijinta"


Mamy tayi murmushi tace"hakane,amma gaskiya ni naso ace saita kammala karatunta sannan zatayi aure,banason irin neman aure da wurin nan,duka-duka ma nawa Mawahib din take?shekara goma sha takwas Alhaji wanne irin aure ne wannan zasuyi?"


Abba yayi murmushi yace"wanne karatu Maryam?yaushe tafara karatun? ko level two bata shiga bafa yanzu tasa qafa a karatun,kicire wannan tunanin aranki inde harshi Nabil din zai barta tayi karatunta ai Alhamdulillah, batun shekaru kuma bawata matsala bane,tawani fannin ma gara hakan, mijinta zai koya mata soyaiya da kansa, sannan kuma kinsan abinda mu iyaye mukeso akan yayanmu qaddara tana zuwa ta sauya shi,kiga abinda mukeso din bai faruba, ke kinaso ace tagama karatu, taqara shekaru, sannan tayi aure,nikuma abinda yake Raina shine naso ace ta auri Yayanta CAPTAIN ARYAN,dukansu dagashi har ita Ina musu sha'awar junansu"


Gaban Mamy ya yanke yafadi,cikin sauri tace"Alhaji kadena wannan maganar Dan Allah, Allah yasa Nabil din yazame mata mafi Alkhairi"


Cikin Sanyin jiki Abba ya amsa mata da "Amin" 



******



Tana zuwa dakin Nabiha tace"Nabiha nadena zuwa wajanki daga yau, ke bakida aiki saiki ki shige daki ki dauki wayarki,gaba daya kin manta dani"


Cikin murmushi Nabiha tace"to yi haquri,nadena, shikkenan? meyake faruwa naganki yanzu goma saura?"


Saida ta yatsina fuskarta sannan tace"kinsan me?wai Yaya Nabil ne yasa kawu Mustapha yayiwa Mamy magana wai yana sona" 


Nabiha tanajin haka tagyara zama tace"ke dan Allah?"


Mawahib tace"wallahi,Nina rasa yanda zanyi,gaskiya ni bana sonshi,amma zan aure shi kodan Momy kilishi, idan tadena ganina ai shikkenan, bazata sake fada mana magana nida Mamy naba"


Nabiha tayi ajiyar zuciya tace"hakane kam, amma gaskiya nide Mawahib nafi miki sha'awar Yaya Ashraf,saboda naga kamar yana ra'ayinki"


Cikin sauri Mawahib tazaro idonta(😳) tace"Rufamin asiri Nabiha,inani Ina 'ya'yan Momy kilishi?,sannan kuma yamin girma,banason tsoho, gara yaro dan ashirin dawani abu"


Nabiha tayi murmushi tace"lalle yarinyar nan, Yaya Ashraf ne tsoho? to bari Kiji wallahi irinsu akeso,sunfi yaran Iya soyayya....wallahi innice ke ko,yanda Yaya Ashraf dinnan yake kulaki,wallahi sainayi soyayya dashi Inga Yaya Momy kilishi zatayi,Yaya Captain nede dama bamu Isa mugwada hakan ba" (😂)


Mawahib tace"Nabiha ko amafarki bana fatan nayi soyaiya da 'ya'yanta, zama lafiya aiyafi zama dan sarki"


Haka suka dinga tattauna zancen har shadaya nadare,sannan Nabiha tarakota, sukai sallama


******


Washegari tun kafin tatashi daga bacci Nabil yakira ta yakai sau biyar tana bacci bata dauka ba,kuma wayar tana silent, saida tatashi taga messages dinsa dayawa,kusan guda hudu, duka babu wanda bai zuba mata kalaman soyaiya ba,kasancewar ta farin shigan soyaiya tafi minti ashirin tana daga kwance tanata aikin karanta saqonnin nasa,daga baya kuma tatashi tayi wanka ta shirya ta futo ta gyara musu gidan,bata dade da gama aikin ba Mamy tadawo kasancewar yau juma'ah da wuri take dawowa,sai bayan ansauko daga sallar juma'ah sannan Nabil yakira ta,sun dade suna waya tun Mamy tana mamakin Mawahib harta dawo ta daina ganin yanda take magana qasa qasa ita Ala dole da saurayi take waya, da abun ya isheta saita Kalle ta tace"Mawahib kije daki kiyi wayar mana"(😂) 


Babu musu tawuce dakinta,saida sukazo sallama dashi ne sannan yake fada mata zaizo gobe,me takeso yataho mata dashi, ta nuna masa batason komai, daga qarshe sukai sallama.


Saida daddare take fadawa Mamy Yaya Nabil zaizo gobe,Mamy tayi murmushi tace"Allah yakawo shi lafiya"


Washegari da sassafe taje tatashi Nabiha daga bacci,cikin Jin dadin bacci Nabiha tace"dan Allah Mawahib ki barni nayi bacci na"


Mawahib tace"kitashi dan Allah Yaya Nabil ne zaizo anjima, yamin waya yana hanya wallahi"


Cikin sauri Nabiha tatashi zaune tace"wai daga maidugurin zaizo?"


Tace"eh,bansan me zanyi masa ba,nahada masa drinks kawai yayi?"


Nabiha tace"haba Mawahib,ya mutum zaizo tundaga maiduguri amma mu bashi lemo, kinsan me? fita zamuyi muyo cefane muyi masa girki mai dadi, kinsan yau momy kilishi ce zatayi girki ba Mamy ba bare muce zamu bashi abincin gida,kuma wallahi momy kilishi abincin gargajiya takeyi, kawai kije kifuto muje driver yakaimu kasuwa muyo cefane mudawo"


Mawahib ta jinjina kanta tace"eh hakane kuma,to bari inje in shirya, kema kitashi dan Allah"


Cikin sauri suka shirya suka fita,driver yakaisu suka siyo abinda suke so, sannan suka dawo gida, suna dawowa ko zama ba suyi ba suka fada kitchen, kasancewar kayan maqulashe suka hada masa nan da nan suka gama kafin ma ace Hajiya Kilishi ta shigo kitchen din, Mamy de taga anata jera girke girke afalo cikin ranta tace"ikon Allah,zamani kenan"


Sai wajan qarfe uku na yamma yazo,kasancewar sa ba baqo ba a gidan yasa kai tsaye Mawahib ta shigo dashi falo,saurayi ne matashi bazai wuce shekara ashirin da bakwai ba. 


batayi kwalliya mai yawa ba,kawai light makeup tayi,tasaka riga da siket na leshi,tayafa mayafi dan madaidaici mai kyau, bayan sun gaisa ta gabatar masa da kayan ciye ciye, babu kunya yaci abunsa sosai, sannan takira masa Mamy suka gaisa, Mamy tadan dade a zaune tana tambayarsa 'yan'uwanta mutanan maiduguri, sannan ta koma daki tabarsu shida Mawahib din.


Cikin nutsuwa yafara yiwa Mawahib magana cikin sigar jan hankali domin kuwa ya lura bata taba soyaiya ba,a hankali a hankali harya dinga janta da zance harta sake dashi,nan da nan ya dinga sakata dariya sai gashi tun kafin yatafi taji ya kwanta mata arai kasancewar sa mutum mai barkwanci, maisata nishadi.

bai dade sosai ba yace zai tafi, kasancewar tafiyar akwai nisa,sai a lokacin takira masa Nabiha suka gaisa,dazata tafi yadauki 5k yabata, Nabiha tayi masa godia sosai, sannan tatafi, ita kuma Mawahib suka qarasa tattauna wa sannan ta futo zata rakashi,sunzo get nafarko ya kalleta yace"to Amarya ta,zan tafi,sai yaushe kenan?"


Kalmar daya fada ta amarya ta, itace tasa Mawahib dariya,har dimples dinta suna futowa, adede lokacin musa megadi ya budewa Ashraf get yasako hancin motarsa ciki,dasu yafara cin karo,tun daga nesa ya hangota tana yiwa wani qato murmushi, lokaci daya yanemi annurin fuskarsa yarasa,ko gama daidaita parking baiyi ba yafuto daga cikin motar ya nufi get na biyu,fuskar nan tasa a murtuke, Mawahib data dago daga dariyar datake lokaci daya tayi ido biyu dashi, mamaki ya kamata,kode Yaya Captain ne yadawo? to ai kuma idan shine yadawo dole zata sani,da tuni qofar gidansu ma yacika da jama'ah, to meyasamu Yaya Ashraf yayi irin wannan daure fuskar?gaba daya saiya koma mata Yaya Captain sak. 


Koda wasa baima kalli inda suke ba yabude get din zai shige,Nabil ya kalle shi cikin mutuntawa yace"barka da shigowa Ina wuni?"


Ba tareda ya kallesu ba yace"lafiya" 

 kamar anyi masa dole, yana shigewa ciki Nabil ya Kalli Mawahib yace"Sojan gidanku yadawo ne? naga shine baya fara'ah, kinsan niba ganesu nakeba"


Mawahib tayi wata dariya Mai kamada yaqe, tace"shine...,"


Saide cikin ranta tana mamakin sauya war Yaya Ashraf zuwa fishi, idan ta cewa Yaya Nabil bashi bane zai Iya tunanin wani abu, shiyasa tayi masa qarya cewa Yaya Captain ne.


Nabil yayi ajiyar zuciya yace"rannan naga bbc sunyi posting din karramawar da'aka musu,naga photon sa shida shugaban qasa, Allah yasanya Alkhairi"


Kanta aqasa tace masa "Amin ya Allah"


Motarsa yabude yadauko mata wata babbar leda fara, yabata yace "ki shiga da wannan ciki,babu yawa yar qaramar kyautata ce izuwa gareki"


Cikin sauri ta girgiza masa kai tace"A a,Mamy zatamin fada,babu ruwana ka barshi"


Murmushi yayi yace"naji, to ki kar6a zankirata awaya inyi mata magana"


Saida taji haka sannan ta kar6a tayi masa godia,yace zaije suyi sallama dasu Alqali sannan yawuce,tayi masa Addu'ah,sannan tajuyo zuwa cikin gida. 




Tana shiga part dinsu, ta tsinci muryar Yaya Ashraf cikin fishi yana fadin"Amma Anty Mamy yaushe tafara karatu da zaku barta tafara sauraron samari yanzu? waye yabata damar kula samari haka anyhow....?"


baima tsaya jin amsar da Mamyn zata bashi ba yajuya cikin 6acin rai zai fice daga part din,yana ganin Mawahib abakin qofa a tsaye da

uwar leda a hannunta yazo wucewa ta gefenta qiris yarage ya bigeta, cikin sauri ta matsa gefe, tsananin mamaki ya cikata dama shima yana fishi haka?(🤔)


Mamy takasa magana tabi Ashraf da kallon mamaki harya fice daga part din,a hankali tasaki murmushi ganin wannan qarfin hali nasa, gaba daya tagama gane inda yadosa,kuma hakan bazai ta6a iyuwa ba,koda ace Mawahib din tana sonshi dole zata haqura dashi, haka inma mazan gidan sukace zasu qullah to bazata yarda ba,saide wannan karon a saketa har abada tafice tabar familyn Alqali.







(wata sabuwa🥺😱)














Amnah El Yaqoub✍🏻


💗MAWAHIB💗


No comments