Mawahib 1-2

 


1&2





Mawahib littafin kudi ne, kibiya 500 kacal ki karanta cikin salama 

0164549488 

Amina muhammad 

GTbank 

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 


_____


'Yanmata ne guda biyu suke tafiya cikin nutsuwa,kana ganinsu kasan bazasu wuce shekaru goma sha takwas ba,d'ayar tana Sanye cikin uniform na islamiya,tanada duhun fata kad'an,a hankali ta juya ta Kalli qawar tata, wadda take Sanye cikin kayan gida,babu uniform din ajikinta saide dogon hijab irinna d'ayar,wanda yazo mata har qasa,kalar hijabin ruwan toka yayi mutuqar qawata farar fatarta,Wanda kana gani kasan cewa hutu dakuma Jin dadi ya ratsa fatar tata. 


Jiddah tace"MAWAHIB,kiraba mana musu dan Allah"


Ahankali tajuyo dara daran idanunta wanda yayi kama Dana mejin bacci, ta Kalli qawar tata, sannan tace"musun me Jiddah?"


Wadda aka Kira da Jiddah tace"wallahi musu muke dasu Hassan da Hussainin gidanmu,nace duk unguwar Nan sukadai ne 'Yanbiyu matasa, shine sukace min wai Yaya ASHRAF din gidanku Shima 'Yanbiyu,nikuma nace ba 'Yanbiyu bane, Yaya Ashraf ne kadai yayanku,saboda nide tunda nake dake,Kuma duk yanda nake qawance dake,baki taba cemin kunada 'yanbiyu a gidanku ba"


Saida ta yatsina kyakykywar fuskarta mai cikeda gashin gira alamun batason maganar, sannan ta motsa dan qaramin bakinta Mai launin pink,tace" 'yanbiyu ne,d'ayan baya zuwa sosai shiyasa baki sanshi ba,ai kinsan Yaya Ashraf dinko?,toshima d'ayan kamar kinsan shi,yanda kikaga Yaya Ashraf Shima haka yake,yana Nan kullum yana fama da uniform,basuda banbancin kamanni, komai nasu iri dayane,nikaina idan suka hadu su biyun bana Iya banbance su,saboda komai iri daya suke sakawa,kawai de hali ne kowa da irin nasa"


Cikin mamaki Jiddah tace"ashe Ana Samun 'yanbiyu maza manya kamar Yaya Ashraf,? Amma Mawahib baki taba bani labarinsa ba"


Cikin sauri Mawahib tace"menene hadina dashi dazan baki labarinsa? wannan marar imanin inani inashi?, halinsa daya da mahaifiyarsu,duk yanda kike tunaninsa yawuce Nan,miskilancinsa yayi yawa,baida fara'ah,kenifa bari Kiji Infada miki na tsaneshi, tun saudaya dana ta6a yimasa laifi ya Sumar dani, daga ranar naji nasake tsanarsa"


Cikin sauri Jiddah ta zaro ido(😳)

Tace"nashiga uku Suma fa kikace?"


Cikin tabbatar wa Mawahib tace"suma kuwa,Ina zaune Yaya Ashraf yazo yacemin naje nagyara masa dakin su,Wai ashe shine zaizo daga Abuja,nikuma bansan ranar zai dawo ba,dana gama gyaran saina dan kishingida akan gadon su,nadan dora kaina a wani fillo Mai laushi,Bansan lokacin da bacci ya daukeni ba,daya dawo yaganni a'inda yake kwanciya,kuma nadora kaina akan fillonsa, shine ransa ya6aci,daya damqi gashin kaina bansan lokacin dana saki ihu ba,shine yasaka kaina a cikin sink din toilet dinsu yabude ruwan,nide nasan yasakani a ruwa,amma daga Nan bansake sanin inda kaina yakeba,Sai farkawa nayi naganni a kwance a gadon dakina"


Cikin tashin hankali Jiddah tace"innalillahi....amma Abbanki baice komai ba?"


"Jiddah mezaice tunda sun dauki power sun bashi?,haka itama NABIHA yata6a jimata targade ahannu,shiyasa nida ita bamaso yazo gida, musanman ma ni,na tsaneshi Jiddah"



Jiddah tayi ajiyar zuciya tace"A a Mawahib,kidena fadar haka,koba komai ai dan'uwan ki ne, gidanku daya,sannan kobabu wannan dangantakar,shidin dan'uwan ki ne musulmi, Kuma babu dadi ka dinga cewa ka tsani mutum,Amma Kuma nayi mamakin yanda naji labarinsa a wajanki,saboda su Hassan din gidanmu har cemin sukai idan yazo har kudi yake rabawa mutane abakin get dinku, wani lokacin ma harda kayan abinci,toke menene ma yakaiki kwanciya a gadonsa?"


Cikin sauri tace"Gadonsa ne shi kadai?gadon su ne shida Yaya Ashraf"


Jiddah tace"duk da haka nide Ina kokonto akan wannan halaiyar tasa dakika fadamin,mutumin dazai dinga yin Alkhairi da kudinsa na aljihunsa shine za'a yi masa wannan shedar?"


Cikin taqaici Mawahib tace"to Jiddah aikuma Sai kiyi,ya Ina fada miki mutum bashida Imani kina min maganar wani kudi,kudinsa na banza da wofi...? ni Kinga tafiya ta"


Tana gama wannan maganar tayi gaba tabar Jiddah a tsaye a wajan cikeda mamaki,Jiddah tasaki ajiyar zuciya tabi Bayan Mawahib da kallo, meyake damun qawarta ne?aiko wani taji yana aibata dan'uwan nata kamata yayi ace Sai inda qarfin ta Yaqare,amma suna gida daya,ana Samun wannan matsalar?(🤔)



******



Tana shiga gida, cikin fara'ah megadinsu dayake zaune a kofar get din gidan yace"yanmatan Mamy har andawo daga islamiyar?"


Cikin ladabi tace"Baba Musa nadawo, sannu da aiki"


Bata jira amsar saba taci gaba da tafiya tana qarewa manyan motocin gidan kallo Wanda suke sheqi da daukar ido tundaga ma'adanar su, taqaraso get na biyu, tabude tashiga,anan zahirin gidan yake, gidane hadadde wanda ya amsa sunansa gida,saide bashida fadi sosai,duk da hakan an qawatashi da adon furanni Masu kyawun launi,anan compound din gidan taci karo da mutanan gidan a zaune,manyan mata ne guda biyu, saikuma wata yarinya wacce bazata wuce sa'arta ba, cikin sakin fuska tayi sallama, Nabiha da hankalin ta kekan wayar dake hannun ta, tadago kanta da sauri Jin muryar yar'uwar tata,qawa, Kuma aminiyar ta. 


tace"Mawahib Kin dawo? Ya Sayyadi yayi dorin karatu?"


Cikin tsokana tasaki wani irin murmushi,murmushin yayi mutuqar yimata kyau har hakan yasa dimple dinta guda biyu suka futo sannan tace"anyi dori,Kuma anbada number,tunda yau da niyya kikaqi zuwa"


Hajiya KILISHI datake zaune gefe kan kujerar roba,lokaci daya tabi Mawahib dawata irin harara kamar idonta zai fado qasa,cikin izza da gadara,tareda tsantsar iko tace"   'ya'yan ma'aikata andawo Kenan,INA GANIN IKON ALLAH NI KILISHI,anfita angama yawon gantali andawo,nikam naga mijin wannan yarinya,Kuma fa ahakan ake neman miji nagari..."


Lokaci daya jikin Mawahib yayi wani irin sanyi,Nabiha ta sunkuyar da kanta qasa,alamun bataji dadin furucin hajiya Kilishi Akan Mawahib dinba,cikin sanyin jiki Mawahib tadubi Hajiya Kilishi,babbar mace ce Mai kimanin shekaru Hamsin da biyar,fara ce tas,batada digon baqi a jikinta, hutu dakuma Jin dadi ya boye shekarun ta, bazaka ce takai adadin wannan shekarun ba,tana kyau sosai,saide fuskar ta cike take da qunci da rashin walwala, cikin ladabi ta russuna tace"sannu da hutawa Momy" 


Hajiya Kilishi ta kawarda fuskarta gefe batareda ta amsa gaisuwar ba



Mawahib tasaki murmushi Mai ciwo, sannan ta dubi d'ayar matar datake zaune kusa da Nabiha, wadda a shekaru bazatafi Mamyn taba, tace"Mama sannu da hutawa"


Cikin sakin sakin fuska wadda aka Kira da mama tace"sannu Mawahib"


Cikin sanyin jiki tashige kitchen,kasancewar tasan yau girkin mamyn tane, Kuma Bata dawo da wuri daga wajan aiki ba, tasan har yanzu tana kitchen bata gama wasu ayyukan ba,tana shiga kitchen din kuwa taganta a tsaye tana duba farfesun ganda Wanda qamshinsa yagama cika kitchen din,kallo daya zaka mata ka tabbatar da cewa mace ce Mai aji dakuma tsari,uwa uba yar boko maiji da gayu, komai nata tana yinsa a nutse,manya manyan zobuna ne a hannunta na gold sunkai guda uku,Riga da zanine ajikinta na leshi kanta yana daure da dan kwali Amma duk da haka jelar kitsonta ya sauko harkan gadon bayanta, black beauty ce, kokadan bata kama da Mawahib, launin fatarsu daban, saide sanyin hali dakuma dabi'arsu da tazo daya, a hankali tace"Mamy sannu da aiki"


Batare data kalletaba tace"sannu da zuwa ya makaranta?"


Cikin rashin walwala tace"Lafiya kalau Mamy,bari inje in cire kayana inzo natayaki"


Kallonta tayi a Karon farko ta karanci akwai damuwa a fuskar 'yartata, amma Bata nuna mata komai ba,cikin hikima tace"A a,aina gama komai,dauki wannan salat din kawai kije ki yanka min,Abbanki yace ayi masa kwadon salat kafin yadawo"


Ahankali tasaki ajiyar zuciya,sannan tacire hijabin dake jikinta,doguwar rigar gown din dake jikinta ta atamfa ta baiyana,rigar ta kama jikinta sosai har hakan yasa shape dinta futowa fili,hips dinta yacika rigar dam,saida ta bubbude girkin da mamy din tayi tagani bayan farfesun ganda,harda fried rice,da Alalan dankali, da fried cabbage with meat,a hankali tadauki salat din ta futo daga kitchen din tanufi hanyar part dinsu, Hajiya Kilishi tabi bayanta da kallo,ta Kalli yanda uban Hips dinta suke juyawa acikin rigar kamar da niyya take kad'asu, ta watsa mata wata irin harara tace"ina ganin ikon Allah ni Kilishi"(😂) 


Tajuya ta Kalli matar datake gefenta tace"Sadiya,dole zanyi wa ALQALI magana yaje yasamu shugaban makarantar islamiyar  yaran nan ayi masa magana,ai bazai iyu abar yara suna zuwa makaranta babu uniform ba,suci wannan uwar kwalliya suna juyawa malamai kwankwaso,Kuma ahakan ake neman miji nagari....,bazan Iya cigaba da zama anan ba Sadiya,baqin cikin wannan yarinyar zai Iya illata ni,idan Kinga zaki Iya cigaba da Zaman jiran abincin, to bismillah Nina tafi,wannan horon yunwa har Ina? ai sai asa ulser ta tatashi". 


tana wannan sababin ,tajuya cikeda iko da izza irinta yayan mulki ta wuce part dinta. 


Mama Sadiya tayi murmushin qarfin hali a hankali tace"Allah yarufa asiri"



Sannan tadubi yarinyar ta Nabiha dake gefenta tana daddanna waya, tajuya taga tabbas Hajiya kilishi tashige part dinta, sannan tace"Nabiha yi maza kije kitchen idan akwai aiki a wajan Mamyn Mawahib ki taimaka mata"


Nabiha ta amsa cikin ladabi, sannan tashige kitchen din, Mama Sadiya saida tasake kallon part din Kilishi ta tabbatar de Hajiya Kilishin bataga lokacin da Nabiha tashiga kitchen dinba,sannan tasaki ajiyar zuciya ta wuce nata part din,tun dazu taso tatura mata Nabiha,domin ta taimaka mata da aiki tunda Mawahib din taje islamiya,to amma tsoro dakuma shakkar Hajiya Kilishi yahanata.


Tana shiga falonsu ta ajiye salat din ta wuce dakin ta tayi sauri ta watsa ruwa,ta futo Sanye da riga da wando,ta zauna adaya daga cikin rantsatstsun kujerun falon Masu launin ruwan toka,Sai qananun fillo dasuke Kai,ta dauki remote din esi ta kunna, sannan tafara yanka salat din cikin qwarewa,batafi minti ashirin da zama ba mamy ta shigo falon, tun daga bakin qofa ta qarewa 'yar tata kallo,tana ganin irin dirin da Allah yabata,Riga da wando ne a jikinta baqaqe, wandon gaba dayansa Iya gwiwarta yatsaya,rigar Kuma batada banbanci da vest saboda ko hannu Bata dashi,sai farar hula shara-shara Wanda kana Iya hango tulun gashin da Allah yabata, Wanda ta gajeshi a wajan mamy, a hankali tasaki ajiyar zuciya tace"kin kunna esi kinzo kin saka wannan kayan, banason shirme tashi kije ki sauya kaya,idan sanyi ya kamaki fa"


Cikin shagwaba tace"Mamy Ana Kiran sallah zancire fa"


Cikin tsare gida tayi mata kallo daya,babu musu ta ajiye wuqar hannun ta ta wuce dakin ta domin sauya kaya.



Lokacin sallah nayi kowa yashige dakinsa domin gabatar da sallar magrib,tana idar da sallar ta dauko Alqur'ani tabude tafara karanta inda aka biya mata dazu a islamiya,Bata dade da fara karatun ba mamy taturo qofar dakin ta shigo hannun ta daukeda counter tana dannawa,ta dubi Mawahib tace"kije kikaiwa su Yaya Abinci"


Badan tasoba tarufe Alqur'anin,tafice daga part din nasu zuwa babban kitchen din gidan,ta dauki abincin mama Sadiya tashiga part din tareda sallama,falon nasu yatsaru Iya tsaruwa da kujeru nasu launin dark green,babu tarkace sosai Bayan kayan kallo dayake falon, Kai tsaye ta wuce dinning dinsu ta ajiye abincin, sannan tashige dakin Nabiha,tana zuwa tazube akan gadon ta tace"sarkin danna waya,kina Nan kina sana'ar taki"


Nabiha tayi murmushi tace"to saina zauna shiru dan Allah? aigara indinga danna wayata"


Mawahib tace"hakane Kam,Nima yanzu tunda mungama exam ai yanzu zan maidata qawata"


Nabiha tace"Mawahib yaushe Yaya Ashraf zai dawo?"


Saida ta juya idanunta Mai kamadana Masu Jin bacci sannan tace"wallahi bansaniba Nabiha,jiyama bayan munfuto daga last paper nayi masa flashing, amma bai kirani ba,kikirashi mana idan magana zakuyi"


Ajiyar zuciya Nabiha tayi,cikin ranta tana jinjina maganar Mawahib datace ta kirashi,tayaya ne zata samu qwarin gwiwar kiransa bayan bataga fuskar hakan awajansa ba?

Cikin basarwa tace"to shikkenan,babu damuwa"


Cikin sauri Mawahib tatashi tace"bari inje inkaiwa Momy kilishi abincinta karnayi laifi"


Nabiha tace"wallahi kuwa,bare keda dama kamar qiris take jira"


Sallama tayi mata ta futo daga part din, takoma kitchen dinsu ta dauki abincin hajiya Kilishi sannan tawuce part dinta,gabanta yana tsinkewa.


Da'ita taci karo tana Bude kofar falon,qiris yarage subugi juna, cikin sauri Mawahib taja baya


Cikin 6acin rai Hajiya kilishi tace"Ina ganin ikon Allah ni kilishi, ai saiki dinga nocking kafin kishigo, idan anbaki iznin shigowa saiki shigo tunda bakida iko da part din bare kidinga shigowa Kai tsaye haka"


Ahankali ta sunkuyar da kanta qasa cikin ladabi tace"kiyi haquri momy, dama abinci ne nakawo"


Batareda ta kar6i abincin ba tace"bude nagani"


Cikin nutsuwa ta sauke kwandon dake hannunta, sannan ta bubbude mata abincin,Nan da Nan qamshin girkin yacika wajan,abincin ya tsaru kana gani, kasan girki ne nazamani. 


Yatsina fuska tayi tace"wanne irin gantalallen abinci ne haka zaki debo jiki kikawo min,?da alama kema haka zakije kinayi a gidan naki mijin....,kinga koma dashi kawai"


Babu musu Mawahib tarufe abincin sannan tadauko tanufi part dinsu dashi, tanajin yanda Hajiya kilishi take rufo qofar part din nata da qarfi.


Tana zuwa part dinsu dayake babu Nisa a tsakani, anan taci karo da Mamy tana zaune tana kallo,cikin mamaki mamy ta kalleta tace"yanaga kindawo da abincin?"


"Mamy nakai mata tace in dawo dashi"


Cikin yanayi na rashin damuwa Mamy tace"to Bari inkai mata dakaina"


Mamaki yacika Mawahib, babu musu tabata kwandon abincin, mamy ta karba tafice daga nasu part din tanufi part Hajiya Kilishi. 


Tana zuwa tatura kofar falon tashiga bakinta dauke da sallama,falo ne har falo,yaji kayan qawata gida da lafiyaiyun kujeru milk color,tareda kafet Mai mutuqar laushi dawani daddadan qamshi dayake tashi gamida sanyin esi,can gefe inda dinning yake, anan ta hangi Hajiya Kilishi tana qoqarin hada tea, Kai tsaye ta nufi wajanta tace"yaya ga abincin angama, Mawahib tacemin kince adawo dashi, kiyi haquri Yaya yau dinne munsamu marasa lafiya a asbiti dayawa,Ina shirin tahowa aka kawo wata mata tana naquda,nice natsaya nakula da'ita harta haihu,sannan nataho gida shiyasa na Makara bandawo da wuri nayi abincin ba, amma kiyi haquri Yaya"


Hajiya Kilishi tace"ina ganin ikon Allah ni Kilishi,nace kinyi wani laifi ne Maryam?kawai abincin naki ne yau bazanci ba,kinyi wata shinkafa haka a tsatstsaye bata dahuba,kiyi mana abincin da muka saba Namu na gargajiya kinqi, saina ki na Yan zamani, kega ma'aikaciya,wannan naman gandar daga ganinsa ko silala baiyi ba bare ayi batun dahuba"


Cikin ladabi tace"kiyi haquri Yaya, me kikeso nadafa miki yanzu?"


Hajiya Kilishi ba tace komai ba, tajuya tabar mamy a tsaye a wajan tashiga dakinta,mamy tasaki ajiyar zuciya ta wuce takai abincin dinning, sannan ta futo daga part din. 


Tana komawa part dinsu taga Mawahib a zaune tanashan farfesun data gama a hankali cikin yanga kamar batason ci,Wanda a zahiri ba yanga takeba,haka cin abincin yake, hankalinta yana kan TV, tana ganin shigowar mamy, ta ajiye plate din dake hannun ta takoma kusa da ita ta zauna, ta dora hannayen ta akan cinyar mamy, sannan ta kalleta cikin damuwa tace"Mamy, Wai dan Allah meyasa Momy Kilishi bata sona?menayi mata Mamy?"


Cikin kwantar da hankali mamy taqarewa 'yartata kallo tana ganin tsantsar yanda take kama da mahaifinta, a hankali tace"tana sonki mana,itace tace miki bata sonki?" 


"Mamy bata sona,dazu har cewa tayi wai itakam taga irin mijinda zan aura...,Mamy ahaka zamuci gaba da zama ne komai akai kinayin shiru?har cemin fa tayi wai nima ahaka zan qare danawa mijin idan nayi aure"


Cikin sauri mamy tace"insha Allahu ba'ahaka zaki qareba,mijinda zaki aura lafiya kalau zaki zauna, ba zakiyi irin wannan rayuwar ba"


Ahankali Mawahib tasaki ajiyar zuciya Jin furucin mahaifiyar tata,sannan tace"to Mamy meyasa ke bata sonki?"


"Wai waye yace miki bata sona? Kawai halintane haka, banason tambaya Mawahib,kitashi kije ki kwanta"



Mawahib littafin kudi ne, zaki biya naira 500 kacal, kokuma katin mtn 


0164549488 

Amina muhammad 

GTbank 


08033300034 


No comments