Furar Danko 89




 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣9️⃣




.......A ɓangaren Alh. Sulaiman Garko yana barin wajen Dada Alh Baita ya kira a waya. Wanda ya shaida masa yana gida yau kam bai fita ko'ina ba. Ya tabbatar masa yana buƙatar ganinsu su dukansu a daren nan dan magana ce mai muhimmanci da shi. Babu musu Alh. Baita ya amsa masa tare da bashi address ɗin inda zasu haɗu. Sannan yay kiran su Hon. Nakowa suma. Cikin abinda baifi awa ɗaya ba suka haɗu a gidan hutawar Hon. Misau dake anguwar Farawa. Tsaf ya zayyane musu komai da suka tattauna da Dada, su kansu sun girgiza da jin wannan ƙulli. Hon. Nakowa ya ce, “Wato su waɗan nan na kula makirci a cikin jininsu yake. Yanzu shima shegen Yousuf ɗin nan ashe tsagerane a haka kamar na ALLAH yana wani sim-sim da kai. To anya kuwa Isma'il bai sanar masa sirrin dake a tsakaninmu ba kuwa?”.

        “Abinda nai tunani kenan yasa ni nemanku da gaggawa. Dan in har zai iya irin wannan ƙulle-ƙullen kamar haka dan kada yarinyar nan ta auri ɗaya daga cikin kai da Tajuddeen to inaji a raina wannan taƙamar da hura hanci da Isma'il keyi nada alaƙa da ya sanarma yaron nan komai kuwa. Dan haka nake ganin plan B dole ne mu canja labarin da ga Isma'il zuwa Yousuf, hakan zai bamu damar jifan tsuntsu ɗaya da dutse biyu, sannan zamufi gigita rayuwar Isma'il ɗin da haukatashi”.

         “Su kuma yarinyar da yaron fa?”.

    Cewar Hon. Nakowa cikin zumuɗi. Duk da Alh. Sulaiman ya fahimci inda ya dosa, amma sai bai nuna masa a fuska ba, sai ma murmushi da ya saki kai tsaye ya ce, “Wannan aikin Dada zata ƙarasa mana shi. Bayan ta ɗauke ta daga wajensa sai muje plan c akansu ita da yaron, dan dama akwai tawa da shi a ƙasa”.

    Nan ma sun gamsu matuƙa. Daga haka suka cigaba d tattauna abinda ya shafesu, musamman game da sabuwar alaƙar da suke shirin sake ƙullawa akan business. Har gabannin asubahi sannan suka watse.....


       __________★


   Yanda Smart yaga rana haka yaga wannan dare ko sau ɗaya bai rintsa ba har akai kiran sallar asubahi. Da kyar ya iya dauriyar fita massalaci. Ana idar da salla ya dawo gidan. Inda Lulu take ya sake komawa. Har lokacin tana a yanda ya barta bata farka ba. Yana tsaka da tunanin tadata ko ya barta har sai ta tashi da kanta kira ya shigo masa a waya. Yayi mamakin ganin Coach, amma sai ya ɗaga. Jin muryar aunty Khadijah saɓanin wanda yay tunani ya sashi sauke ajiyar zuciya tare da gaisheta cikin girmamawa.

        Tambayar data jeho masa akan Lulu ya sashi kallonta, sai da ya ɗan furzar da iska sannan ya bata amsa da “Har yanzu bata farka ba dai”.

    “Alhamdullah to karka tada ita, inasha ALLAH ina nan zuwa yanzu nan. Dan a yanayin da take a ciki bamu da tabbacin bazata sake tashi a firgicen ba. Hakanne kuma ba'aso da ga gareta”.

            Ya gamsu, dan haka yayma Aunty Khadijah godiya ya na yanke wayar. Kwanciya ya ɗanyi a kan sofar ɗakin ya faɗa duniyar tunani, hakan ya Bama barci damar dinga figarsa kaɗan-kaɗan. Tsakanin wayarsa da aunty Khadijah baifi mintuna arba'in ba sai gata tazo. Sosai yaji daɗi da ƙara jin kimar waɗan nan bayin ALLAH. Bayan sun ƙara gaisawa ya fita ya basu waje. Cikin hikima ta tada Lulu wadda ta farka a firgicen kamar yanda Aunty Khadijah tai hasashe, sai dai Alhmdllh cikin ƙwarewar aiki ta nutsar da ita, tare da taimaka mata zuwa bathroom ta sake haɗa mata ruwa mai ɗumi. Shawarar sake gasa jikinta ta bata ta fito. Lulu da komai ke dawo mata dalla-dalla batai musu ba ta shiga ruwan zafin, sai da taji ya ratsata tako ina ta sake samun nutsuwa sannan ta tsaftace kanta ta hanyar wankan tsarki da shi da kansa ya koyar da ita a cikin karatunsu duk da dai dama tanayi makamancinsa bayan period, amma ko randa ya koya matan yasha harara dan yay mata bayani dalla-dalla ne. Ji take jikinta ya mata nauyi sosai, ga tauna da ƙasusuwata keyi. Bata son tuna abinda ya faru saboda ƙunar da zuciyarta ke mata. Da taimakon aunty Khadijah tai salla, bayan ta idar ta jima zaune shiru tana nazarin tushen faruwar komai na daren jiyan.  Kamar wadda aka tsikara ta miƙe da sauri dan ta manta yanayin nata. Komawa tai da sauri ta zauna tana dafe kanta ta cije lips. Ƙaramar ƙarar da tai ya saka hankalin aunty Khadijah dawowa kanta. Ta nufota da sauri tana faɗin,

        “Mawaddat yi a hankali banda garaje kinji”. Bata iya cema aunty Khadijah komai ba sai hawayen da suka silalo mata masu zafi. Cikin muryarta da ke a disashe har yanzu ta ce, “Aunty dan ALLAH ina son ki kaini gida”.

      “Gida kuma Mawaddat?”.

  “Eh aunty, dan na tsani gidan nan da komai na cikinsa. Wlhy idan na cigaba da zama komai zai iya faruwa”.

    “Ki kwantar da hankalinki Mawaddat. A cikin wannan halin da kike ai wannan gidanne yafi cancanta da ki zauna fiye da ko ina. Karki ruɗar da kanki, domin yau ɗinki tanada banbanci da jiyanki. Aliyu mijinki ne, abinda ya faru tsakaninku kuma yanada banbanci da wanda zuciyarki ke kallo a baya. Bawan ALLAHn nan tun jiya hankalinsa a tashe yake da ganin halin da kika shiga, bana jin ko rintsawa yayi a daren jiya, dan ALLAH ki sakama ranki haƙuri ku fuskanci juna wataran zakiyi alfahari da hakan”.

         Kuka Lulu ta sake fashewa da shi tana mai girgiza kanta, “Aunty dan baki san miya faru bane....”

     “Ba sai na sani ba Mawaddat, ki adana wannan sirrinkine. Ni dai fatana ki kwantar da hankalinki ki saurari mijinki. Aliyu mutumin kirkine fiye da yanda kike zato ko tsammani. Ke da kanki zaki bama wani labarin hakan wata rana...”

            “Aunty shi azzalumi ne, macuci ba mutumin kirki ba. Kuma wlhy saina ɗan ɗana masa fiye da abinda ya ɗanɗana min, ni zai yaudara ya sakama disere tablet acikin abu na sha ya min fyaɗe. Natsanesa aunty, bana son sake ganin fuskarsa a rayuwata. Kuma wlhy sai na shayar da shi mamaki, dama sai da Dada ta faɗamin amma na kasa fahimtarta. Yayi hakane saboda yasan gobe zamu rabu. Bazan yafe masa ba, kuma a yau ɗin nan komai ma ya ƙare, ya kuma saurari abinda zai biyo baya”.

       A bazata suka tsinkayi deep voice ɗinsa cikin kunnuwansu dan basu san da shigowarsa ɗakin ba. “Ni ban saka miki komai kisha domin samun biyan buƙatata ba. Sannan aure nayi kamar kowane aure mai daraja da fatan mutuwa ta raba. Amma kiyi haƙuri ki bani dama na miki bayani maybe ki fahimceni kuma ki yarda” ya ƙare maganar yana ajiye tray ɗin hannunsa mai ɗauke da kofin shayi da plate da aka saka soyayyan ƙwai.

        A zafafe Lulu dake masa wani irin kallo na tsantsar tsana tace, “Har abada babu yarda a tsakaninmu. Baka da abinda zaka fahimtar da ni Munafuki, azzalumi, maƙaryaci, mayaudar...”

       “Mawaddat!!”. 

    Aunty Khadijah ta kira sunanta cikin daka tsawa. Yayinda Smart ya lumshe idanunsa har cikin rai kalmomin guda huɗu da suka fito da ga bakinta na ratsa shi. Ƙoƙarin matsawa yay gaban gadon da kofin shayi a hannunsa yayinda aunty Khadijah ke cigaba da mata faɗa. Bai gama tabbatar da takai maƙurar tsorata da shi ba sai da yay ƙoƙarin riƙota tai wata irin zabura, sai dai azaba da rashin isashen ƙarfi ya sata kasa yin kowane irin yunƙuri face sake fashewa da kuka ta furta, “NA TSANEKA ALIYU!!”.

        “INA ƘAUNARKI MAWADDATAN'WARAHMAH”. ya amsa mata da tashi disashshiyar muryarsa yana tsayawa cak, kofin shayin ya ajiye a bed side drawer duk tausayinta sai ya sake mamaye masa zuciya. So yake tai haƙuri ta kwantar da hankalinta ya jera mata kalaman yabo da jinjinar ban girma, sai dai yasan bazasuyi tasiri ba a yanzu gareta, dan haka ya tattarasu ya adana a wani killataccen sashin adana manyan sirrikansa a zuciya. 

          Ganin Lulu na neman sake rikice musu aunty Khadijah tace yaje falo ya jirata. Kusan mintuna biyar da fitar tasa sai gata ta fito. Kallonsa tai cike da tausayawa. “Kayi haƙuri Aliyu ba laifinta ban itama. Wlhy gaba ɗaya a ruɗe take. Dan ma a hakan fa jiya an taimaka mata da wuri shiyyasa al'amarin yazo da sauƙi. Ni yanzu ina ganin mafita ɗaya ce, ka samo wadda zasu zauna tare, sannan dole kayi haƙuri na samu ko Maman Ra'is ce (Aunty Saliha) tazo ta ƙara lallashinta. Dan yanzu ni zanje asibiti ne inada theatre. Insha ALLAH komai zai dai-daita da zarar ta daina jin raɗaɗin a ranta. Sannan ka ɗanyi nesa da itan na ɗan lokaci koda yinin yau ne haka zuwa gobe”.

       “In sha ALLAHU aunty Khadijah. Nagode sosai da ƙoƙarin ki kuma”.


     Sosai aunty Khadijah taji daɗin yanda ya fahimta ɗin. Yayinda tausayin Lulu ke cigaba da ratsata itama harma da shi kansa Smart ɗin. Dan yarinyar tana cikin wani yanayi ne mai ban tausayi. Bayan wucewarta ɗaki ya nufa ya canja kayansa, koda ya fito sai yay tunanin bari ya ɗan leƙata kafin ya wuce, dan gidansu yake son zuwa ya ɗakko mata Maryam ko Asma'u. Kamar zai fice sai kuma dai ya nufi ɗakin nata, ya samu tana toilet, sai books guda buyu da ya gani a saman gadon da pen. Juyawa yay ya fita saboda so yake yaje ya dawo da sauri. Maganar aunty Khadijah na cewar zatai magana da Aunty Saliha tazo yasa shi bai rufe gidan ba, dan yasan sun fisu kusa da nan zata iya yiwuwa ta iso kafin shi ya dawo.. Da'ace bawa yasan gaibu ko abinda zai iya faruwa a bayansa da Smart bazai yi wannan fitar ba. Da bai bar ƙofar gidansa a buɗe ba. Da ya bari har aunty Saliha ta iso kafin ya tafi.......✍️


*_Tofa masu karatu. Mizai faru? Mike shirin faruwa? Amsoshin na a FURAR DANƘO book 2 in sha ALLAHU 👌_*


_Kumin afuwa wannan karon rubutun duk yazo a yanayi na shiririta sai dai godiyar ALLAH. Yau da gobe kenan dan na fiku son naga na kammala gaba ɗaya😭. Amma in sha ALLAH muna gab da hutawa baki ɗaya. Zamu koma part 2 ne dan in numbers na nisa rubutun gundurata yakeyi wlhy🤦.  Amma insha ALLAHU zamu ƙarƙare akan lokaci._*


           

 _Akwai ƙura fa ta gaske a book 2, dan duk wani abinda muke san sani na ƙunshe ne a cikinsa. Kudai kuyi addu'a ALLAH yasa mu koma pages goma goma mu kammala a kwana goma. Kun san fa ina matuƙar son goma😂😂._


         




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*


No comments