Furar Danko 76



 76


........Itama cikin farin ciki take musu sannu da zuwa, yayinda Lulu ke amsawa tana nufar Nasreen. “Oh oh mi akaima wannan princess É—in ne haka take É“arnar hawayenta masu tsada?”. Ta faÉ—a tana É—aga Nasreen, zama tai ta É—aurata saman cinyarta. Itako ta lafe cike da shagwaÉ“a da kuka ta ce, “Ba Mommy bace ta daken dan na kira Abbana a wayanta”.


    “Ayya Mommy ita bata san mun É—an ara bane muji muryan Abba. Barta daina kukan bazamu bata chocolate É—inmu ba”. Tai maganar da share hawayen Nasreen ta É—auka handbag É—inta ta ciro chocolate biyu masu daÉ—i da tsada ta baima Nasreen. Tuni ta fashe da murnar dariya ta kaima kuncinta sumbata cike da farin ciki, sai kuma ta É—aga musu chocolate É—in tanai musu gwalo. Hakan ya bama Lulu dariya ta saki murmushi, suma duk sai suka fashe da dariya Æ™asa-Æ™asa. Dai-dai nan Ammah ta idar da sallanta, batai doguwar Addu'a ba ta juyo fuskarta da murmushi mai Æ™yatarwa. Akan Smart da ke zaune kujerar kusa da inda take sallan ta sauke, sai kuma ta maida ga Lulu. Kafin tace wani abu ya saukko a kujerar ya zauna kusa da ita yana gaisheta, ganin haka yasa itama Lulu sakkowa da ga kujerar ta zauna Æ™asan carpet É—in da ke a share tas ga Æ™amshi mai daÉ—i na tashi a falon ta ce, “Ammah ina kwana”. Da sauri Ammah ta girgiza mata kai da miÆ™a mata hannu murmushin É—unbin farin cikinta na sake bayyana ta ce, “A'a zonan É—iyata kinji, taso maza taso gareni”.


    Abin mamaki sai Lulu ta samu kanta dajin kunyar Ammah. Da Æ™yar ta iya miÆ™ewa ta nufo inda take, zata zauna É—an nesa kaÉ—an nan ma Ammah ta riÆ™o mata hannu ta zaunar da ita jikinta sosai. Ajiyar zuciya Lulu ta saki hawaye na ciko mata ido, amma sai ta daure kanta a Æ™asa ta sake gaida Ammah a karo na biyu. Shi Smart ma da abin ya girmesa kasare kawai yay yana kallonsu. Ammah ta riÆ™o hanunta cikin nata tana amsawa da kulawa.tare da É—orawa da faÉ—in, “Ki saki jikinki É—iyar albarka nan gidanku ne, ni É—in ban son ki É—aukeni mamar mijinki mamaki ce dan yanzu kinfi Hydar matsayi a wajena....”


    Cikin waro idanu da Æ´ar shagwaÉ“a ya ce, “Ammah! Hakama zaki ce ina babanki É—in?”. 


   “Kai tafi can ai photo copy ne ba original ba wake ta taka. Anata sabon É—a waketa tsohon É—a”.


     Dariya su Hawwah suka saka, Lulu ta É—ago ta masa gwalo da nuna masa 8-6 da hannu. Lips É—insa ya cije da Æ™aramar harara. A dai-dai nan Mama ta shigo tanama baÆ™uwa lale marhabun. Itama sai Lulu ta gaidata da girmamawa, Mama ta amsa da fara'a tana sanya mata albarka, dan ita dai barta da rashin mutuncinta idan ya motsa ko Umma ta tunzurata. Amma tanada kirki a lokuta da dama, sannan bata saka Æ´aÆ´a a kishinsu inba taÆ™ure ba. 


    Yaranne suka shiga shigowa É—aya bayan É—aya suna gaidata kamar yanda Mama ta basu umarni, sai dai a Æ´aÆ´an Umma Mubarak ne kawai ya shigo cike da zumuÉ—i, dan yaso zuwa gaida amaryar yayan tasu Umma ta taka musu birki akan duk wanda yaje koda a bayan idonta saita tsine masa. Wannan girmamawa da Lulu taga an mata ya matuÆ™ar birgeta, (tana son a girmamata a nuna mata ita mutumce mai daraja) koda Umma ta leÆ™o itama a gatsine wai tana mata sannu da zuwa da É—an habaicin basu fara shiga É—akunan su ba Lulu ba fahimtar komai tayi ba. Hasalima kallo É—aya taima Umman ta duÆ™ar da kanta dan haka kawai take jin Ammah ta mamaye mata ko'ina. Bata taba jin nauyin mutum da kwarjini kamar yanda takeji akan Ammah ba. Ga tsantsar soyayyar ta data hanga a cikin idanun dattijuwar yasata jin wani irin Æ™aunarta ta musamman. Smart da shima yake matuÆ™ar jin farin cikin nutsuwar da yaga Lulu tayi a gaban Ammah ya ce, “Da nasan haka za'amun a gidan nan daban zo ba. Amma ba koma a bani shayi nasha nai gaba. Zaku nemeni ne”.


     “Wake buÆ™atarka balle ya nemeka anan”. Cewar Ammah da murmushi. Fuska ya shagwaÉ“e da faÉ—in, “Ammah! Ammah gara dai ki tarairayeni dan da tsohuwar zuma ake magani”.


   “Ga wanda bai sani ba ba”.


  Ammah ta bashi amsa.


“Shike nan na daina magana. Hawwah bani shayi na Æ™ara gaba, itama fa ku nema mata abinci bamu karyaba muka fito dan zumuÉ—inta”.


     Ammah ta ce, “Kai Hydar dan ganganci. Shine kuma maimakon ka kira waya tunkan ku taho a É—aura muku”.


   “Haba Ammah sai kace wasu baÆ™i”.


“BaÆ™ine mana. Tunda wannan ne karo na farko data fara marabtarmu dan wancan ba'a sakashi a lissafi. ÆŠiyata mi kike son ci”.


     Æ˜asa Lulu ta Æ™ara yi da kanta tana girgizawa da faÉ—in, “Ammah bana jin yunwa ma, abarshi har sai anjima”.


   “A'a bazai yiwu ba Mawaddatan'warahmah. Ƙarfe goma harta gota ace sai kuma anjima”.


   “Ammah bason cin abinci take ba shiyyasa. Idan kika biye nata ma daga nan har dare zata iya kaiwa”. Smart dake Æ™oÆ™arin kai shayin da Hawwah ta kawo masa bakinsa ya faÉ—a. ÆŠan harararsa Lulu tai Æ™asa-Æ™asa bata dai ce komai ba. Shi kuma yay mata murmushin da take kira na mugunta.


   Yana kammalawa ya miÆ™e da faÉ—in shi zaije ya gaida Abba ya wuce, sai anjima zai dawo. Addu'a Ammah tai masa da ta ratsa zuciyar Lulu matuÆ™a harta tsira musu ido. Karo na biyu yaji wani abu ya tsikarar mata zuciya game da ilimin addini, sai kewar mahaifiya data ratsata, itama fa da Mah-mahn ta nada rai da haka zata dinga mata ko? Sai hawaye suka cika mata idanu. Su Ammah daba lura sukai ba Smart ta É—an dubeta cikin jin nauyin Ammah ya ce, “Madam na barku lafiya, duk abinda kike buÆ™ata karkiyi fillanci Ammah taki ce.”


    Kanta ta jin jina masa tana Æ™oÆ™arin maida hawayenta. Da ga haka ya fice ya barsu....


   Cikin Æ™anÆ™anin lokaci aka shiryama Lulu breakfast, yayinda gidan ya É—auki shiru su Asma'u ma sun wuce makaranta. Ammah nata janta da taÉ—i itako tana bata amsa cike da kunya har Hawwah ta kammala tazo ta zauna. Sai Ammah tace suje É—aki ko zata fi sakewa ta karya kafin suje ta gaida Abba da matan gidan dan yau dai ba fita zaiyi ba. Jin haka yasa Lulu cewa bari taje ta gaida Abban dan bata jin yunwa. Hakan yasa Ammah jin daÉ—i, dan haka ta miÆ™e da kanta domin rakata wajen Abban. Hawwah kuma ta shiga tattare kayan tana maidawa É—akinsu...


    Sosai Abbah yayma sabuwar surukar tasa tarbar mutuntawa kamar yanda yake ma sauran. Yayinda Lulu shima ta kasa ko kallonsa dan tsohon ya mata kwarjini sosai. Shima ta gaidashi da girmamawa ya amsa mata da kulawa da sanya albarka. Sannan ya É—ora da addu'a zama lafiya a gare su Ammah na amsawa da Amin cikin murmushi. Basu jima sosai ba dan sunga Lulun dai kunyarsu ta sata kamar takura suka fito bayan ta ajiye masa leda madaidaiciya mai É—auke da turarruka masu tsada da Æ™amshi, sai agogo. Da sauri Abbah yace, “A'a É—iyata maza zoki É—auka. Gaidamun ma da kuka zo kawai ya wadatar mun kumayi farin ciki”. Marairaice fuska Lulu da kanta ke a Æ™asa tai da faÉ—in, “Abbah dan ALLAH karkace haka. Mu albarkanku muke nema, indai bazan sayama Daddy abu dan neman albarka ya dawo min da shi ba kaima haka nake fata daga gareka”. Abba dake murmushi sai ya jinjina kansa da nisawa. Ya ce, “ALLAH yay miki albarka. ALLAH ya tsare gabanki da bayanki....” ya dinga jera mata addu'oi masu ratsa zuciya Ammah na tayashi kafin suka fito.


    Anan kam saita kira Hawwah akan tazo ta raka Lulu kowane É—aki. Hawwah ce tai mata rakkiya, inda suka iske Umma cike fam, amma saboda shawarar da Hajiya Naqiba data kira ta labartama mata zuwan su Lulun yasata dannewa ta tarbeta da fara'ar yaÆ™e, ita kuma Lulun sai ta kasa sakin jiki da ita dan ita kam dai haka kawai taji Ummah batai mata ba, basu wani jimaba Lulu ta ajiye mata Æ™aramar leda ta miÆ™e, sai hakan kuma ya sake zafar Umma. ÆŠakin Mama ma an mata tarba ta mutuntawa, nan ma sai sukafi É—akin Umma daÉ—ewa, dan duk da Mama taji hassadar kasancewar wannan zukeÆ™iyar yarinya Æ´ar masu kuÉ—i ba wani acikin Æ´aÆ´anta ya samu ba ta danne a ranta ko a fuska bata nuna ba, sai godiyar ledar da Lulun ta ajiye mata ya shiga jerawa. ÆŠakin aunty amarya kam tarba suka samu kamar wata Æ™awa. Dan tsokanarta ma taitayi suna dariya. Sunfi jimawa anan fiye da ko'ina kafin su koma É—akin Ammah bayan itama ta ajiye mata ledar, bakuma komai bane aciki sai kayan turaren wuta data É—iba musu da su cin-cin. Itama Ammah ta kawo mata harda turmin zani biyu su Asma'u kuwa kayan kwalliya ta basu jiya da sukaje. Basu zauna a falo ba suka nufi bedroom É—in su Hawwah É—in inda ta maida break fast. Duk da Hawwah zata iya É—an girmar Lulu da ko shekara biyu ne jikinta ta saki da matar yayan nasu, hakan sai ya saka Lulu sakewa abunta dan wayayyace dama kai babu duhu. Duk da ba son cin abincin take ba sai gashi ta saki jiki sunci tare da Hawwah suna hira cikin mutuntawa, anan ne ma Lulu ta samu damar sake jin matsalar Hawwah É—in sosai, a ranta kuma ta É—auki Æ™udirin taimaka mata, dan haka ta amshi address É—in gidan nata a cikin hikima batare da Hawwahn ta fahimta ba. Bayan sunyi sallar azhar falo suka dawo wajen Ammah, cikin hikima taita jan Lulu a jiki ganin bata sakewa idan suna tare, da yake abune daga cikin abinda take Æ™ishirwar samu sai gashi ta saki jikin nata fiye da yanda sukai zato, dan hirar tasu ne ta karkata akan yanda matsalolin fyaÉ—e ke Æ™ara yawaita da yanda wasu ma yaran kan rasa ransu a take ko a cutar da su ta hanyar saka musu cuta, da yanda wasu iyayen kan rasa ransu adalilin hakan kosan É“oyewa saboda kar duniya taji Æ´aÆ´an su tozarta da su kansu. Lulu ta ce, “Wlhy Ammah nakanji kamar na dinga kashe irin waÉ—an nan aladun da hannuna, akwai case É—in wata yarinya da har yanzu yake cimun rai duk da shegen na prison kusan shekara uku kenan, danni duk wanda nasan na samu nasarar alÆ™ali ya turashi prison akan wannan laifin cigaba nake da bibiyasu a prison É—in dan karma ayi amfani da wata dama a sakesu ina nan baki buÉ—e. Yarinyar tana nan ta zama mahaukaciya kamar yanda Nanny É—ina ta kasance kafin mutuwarta....”


    Wasu irin hawaye suka zubo mata masu azabar zafi saboda tuna mata da abinda ya shuÉ—e kuma yake sosa mata zuciya da zama sanadin komai da ake kallon zagaye da rayuwarta a yanzu.........✍️


No comments