Fin Karfi Book 3 Complete

  




   *FIN ƘARFI BOOK 3*



                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 1



Shiri sosai tayi dama Sarkin gayu ce tayi ƙyau ƙwarai dan tana da irin jikin nan da ake ce ma karuwan jiki,ko wane kaya tasa sai ya yi mata ƙyau an ɗebe su sai hotel ɗin da aka tsara haɗaɗɗiyar dinner, wacce abokan Ango suka shirya guri ya yi guri sanda suka isa,jin gaban ta bai faɗi ba yasa ta shiga cikin ƙwanciyar hankali suna zaune an soma ciye-ciye . Can sai taji gabanta ya yi mugun faɗuwa take ta ji komai ya ginshe ta duk da waƙar da mawaƙin keyi da farko ta shiga ranta, amma yanzu sai taji komai ya tsaya mata cak. Da sauri ta miƙe Sadiya da Munira suka dube ta, ina zaki? Ta ce ina zuwa,can bayan wasu ƴan labulaye taje daga inda take tana duban ƙofa. Haka kawai taji cewa yanzun zai shigo.



***      ****     ****     ****

Dady ya fito wanka ya kuma gajiye yake jin shi ba dan bai samu halartar ko ɗaya daga cikin programs ɗin bikin ba da zaya huta ne don yayi azumi yau kuma a wahale yake ya ɗan ja tsaki shima yana tunanin haka nan zaya haƙura asa bikinshi da Zainab ya gaji da azumin nan shi kanshi yasan yana buƙatar mace kuma yana ganin kamar yana da ƙarfin sha'awa shiyasa gara ya yi auren tunda wadda yake so bazai samu ko ganinta ba bare har ya aura.


Shadda kalar blue hularshi da duk kayan da yasa blue ne,rafar ƴan ɗari biyar ya zuba cikin aljihu ya fesa turare ya ɗauki key ɗin Hummer ya fito. A falo ya samu Sunday yana zuba Hollandia cikin firji, ya ce "Sunday kai min ɗaya cikin motar daka goge min", ya ce "Ok sir." Ya ɗauka ya fita yana matuƙar mamakin irin son da ubangidan nashi kema wannan Hollandia ya kamata campanyn ta suyi mishi ƙyauta ta musamman,ko dan tsananin ƙaunar da yake mata."


Gidan su Zainab Dady ya wuce a phone ya kirata ta fito bayan tayi sallama da mahaifiyarta, Hajiyarta tana tsananin son Æ´arta Zainab ta auri Dady ba dan komai ba sai don iyayenshi sun tara, haka kuma shima ya tara sai godiya.


Yana daga cikin mota yana kallonta ta nufoshi cikin wani leshi ɗan gaske mai kalar green yasha ado da zare silba haka sarƙa da ƴankunne suma silba jaka da takalmi sai wani ɗan mayafi ƙarami duk farare ta yi ƙyau sosai sha'awarta ta ƙaru a zuciyarshi, ta shiga motar bayan ya buɗe mata ƙamshin jikinsu ya buɗe su,ta dube shi My dear har na zaci ka fasa zuwa dani, ya ce "saboda me?" Ta ce naga goma ta wuce sannan baka kira phone ɗina ba, ya ce ina can ina tunanin yakamata mu ma azo mana dinner fa dan na gaji da rungume filo yakamata nima nasan halin da nake ciki, daɗi ya kamata ta ce ba na ce maka ba tuni, amma ka ƙi wai na jira ka,Ƙila kafi son ƙwana da filon shiyasa." Ya shafi fuskarshi ranar asabar za'a kawo lefe da komai tunda Allah yasa sun san komai dama nine matsalar kuma yanzu nima ina buƙatar auran,sati Uku zamu sa fa.?"


Cikin zumuɗi Zainab ta ce "Ya yi nima na matuƙar ƙosawa."


Ya dubeta "dame kika ƙosa?" Ta ce "Da abin da yake hana ka bacci." Kai ya girgiza yana mamakin Zainab, Sam batada irin kunyar nan ta mata, ya tuna Pretty ɗin shi, ita kam kowane lokaci ya yi mata wata magana mai ɗan nauyi takan rufe fuskarta da tafukan hannayenta ta ce,kai ko? Ita kam Zainab sai dai ta biyeshi suyi,hakan baya birgeshi yana son mace mai kunya da jan aji.


Suna shiga gurin dinner yaji gabanshi ya faɗi inda sabo ya saba,ba wata Pretty ɗin shi a nan gurin, zuciyarshi ce dai kullum tana ayyana mishi sai gabanshi ya dinga faɗuwa, haka ya raya a ranshi don haka sai kawai, ya shige, sun samu an daɗe da soma dinner, amma duk da haka sai da aka sanar da zuwanshi a matsayin babban abokin ango akan idon Ruƙayya suka shigo, tana dubansu san da suka zarce kusa da ango suka zauna yayin da Zainab ta maida ɗuwawunta gurin da Ruƙayya ta tashi, gaban Ruƙayya ya faɗi ta tsorata da ganin Zainab domin ta gane wacce suka haɗu a saloon ce, ta gode Allah da yasa ta tashi don haka can ta fita duk da tsoron dake cike fal a ranta haka ta zauna a harabar Hotel ɗin tunda ga haske tamkar rana.


Sadiya ta dubi Munira "M Bash har yanzu kusan awa Ruky M bata dawo ba fa." Munira ta ce "Kai gaskiya ki je ki duba ta, tunda ba phone a hannunta bare ma mu kira."


 Son Guy (kamar yadda suke kiran Dady) ya dubi Al-Mustapha.


"Ina neman afuwa Musty bamu samu isowa akan kari ba." Zainab ta ce "Ya hidimomi ango?"


Al-Mustapha ya ce da godiya.


Zainab ta dubi Munira "Amarya ya jama'a?" Munira bata gane Zainab ba, har suka gaisa suka gaisa da Sadiya basu gane ta ba, Zainab ta ce "Naga baku gane ni ba ko?" Sadiya ta ce "Ni dai ina son tuna inda muka haÉ—u." Zainab ta ce "A saloon." Nan take suka tuna ta, amarya sun gaisa da Son Guy inda ya yi mata Æ´ar tsokana. Zainab ta ce "ina É—ayar nan kuma mai gashi?."  Sadiya ta ce "kina nufin RuÆ™y M ko?" Ta ce "Yes ita kam bata zo ba?" Ta ce yanzun nan ta tashi ko ina ta shiga Oho, Zainab ta ce "Ashe zamu gaisa." Munira ta ce "Armaya'u ki je ki duba ta kin san fa RuÆ™y Æ´ar daru ce zata iya tafiya gida."


Al-Mustapha ya ce "Kai Ruƙy ɗin nan tana da shagwaɓa,da ƙyar dama ta zo.


Shiru Dady ya yi yana ƴan dube-dube tamkar baisan mai suke cewa ba, amma kunnen shi yana gurin su,a ranshi kuma sai yaji yana mai tsananin son yaga Ruƙy M ɗin nan, wancan karan ya kuskure ganinta sakamakon wanka da tashi ga, yanzu kan shi sai fa yaga kalarta, shi kam dama yana matuƙar girmama mai sunan ta,yasha alwashin in har ya haifi ƴa mace sunan ta Ruƙayya. Nan ya tuno ma kanshi son Ruƙayya take hankalinshi ya tashi kanshi ya shiga sarawa nan ya ji zuciyarshi ta tsani duk wata mace, duk hirar da Al-Mustapha yake yi mishi sam bai ji ba,sai da Zainab ta ce My dear ya kamata ka duba masu waƙar nan tuntuni sai waƙa suke yi. Nan ya tashi cikin sanyin jiki yana musu liƙi, Zainab ta zuba mishi ido tana tsananin son shi ita ma nan take ta tashi taje tana mishi liƙi, Ango da amarya suma suka taso suna ma su Dady liƙi nan fa guri ya kaure mai waƙa sai rerawa yake yi.


Ruƙy wacce abin duniya ya dama sai gizo Dady ke mata tana ganin san da suke shigowa da Zainab fuskarshi wasai ƙyawun shi ya ƙaru fiye da da, wata kamala ta musamman ta sauka a fuskar shi, ya zama namiji sosai ga wani ɗan tumbin kuɗi da ya fito ya yi mishi ƙyau,a da sam bata son tumbi amma na Dady ya yi mishi ƙyau.


Hawaye suka zubo mata lallai Dady ya karya alƙawari. Ta tuna da yanda suka so juna ashe duk na baki ne,sai yanzu ma tayi wani tunani, gaskiya ya kamata ma ta gane tuntuni dan me ya hana ya neme ta tuntuni bayan rabuwar su? Kuma phone ɗin da ya bata me ya hana shi kiranta akan layin. Har ta tafi makarantar ƙwana? Duk ma shekarun nan da yana sonta daya neme ta, don haka taba kanta baki tare alƙawari sauraron duk wani wanda ya zo da sunan sonta. Kuma daga yau tayi banƙwana da garin Abuja gobe tana tafiya shikenan,in ba kuma M Bash bace ta haihu bata ƙara zuwa bare ta ganshi. Kai tana ganin ma gara ta je ta auri talaka ɗan'uwanta ya fiye mata ƙwanciyar hankali. Ga Nasir tela duk da ya yi aure har da yara uku,yana nan yana nacin ta har tayi degree ita kam yanzu zata daina biyewa ƴaƴan masu dashi ɗin nan,gara Armaya'u da M Bash suna da halin shiga law school ita kam zata je service ɗin ta ya fiye mata tana gamawa ta nemi aiki koma a ina ne kafin Allah ya bata miji, tunani bar katai sun cika ta har san da aka tashi.


Tana ganin mutane sun soma fitowa, sai ta koma can gurin motar da suka zo cikinta. Ta ganin su Armaya'u da sauran ƙawayen suna sallama da Zainab, yayin da Dady dasu Al-Mustapha suka nufo gurin da take. Tsoro ya kamata da sauri ta zaga bayan motocin ta ɓoye bayan wata.


Jikin wadda ta ɓoye ya shiga tana jin san da yake cewa Musty "Musty Allah ya bada zuriya ɗayyiba, kayi ƙoƙarin samun Baby a yau dare na farko." dariya suka saki sauran abokan suna cewa "Gaskiya ne Son Guy." Ya ce Zee zo muje dare nayi fa." Ta na barwa su Sadiya saƙon gaisuwa zuwa ga Ruƙayya, ta zo tana cewa,My dear mu tafi ko? Ya ce shiga, ta tsugunna tana jin su a bayan motar da bata zata tashi bace sai da taji ya tashi motar ta koma bayan wata da sauri.


Yana bari gurin ta miÆ™e tana maida numfashi taje gurinsu Munira dake ta shishshiga mota. Sadiya har tsoro ta ji ta ce daga ina? RuÆ™y ta ce  ku muje kawai basu jima a gidan Munira ba Abokan ango suka Æ™washe su sai gidan Mom. Sun cika su uku Munira M Bash, Sadiya Armaya'u, RuÆ™ayya M Sani, tayi ta yi da safe su biyo kafin su wuce, sun ce to dan ta Æ™wantar da hankalinta, amma ba zasu dawo ba saboda Armaya'u Kano ta nufa, Mom ta haÉ—a su da kayan biki da kuma godiya tare da cewa suyi ma iyayen su ban gajiya. Dan Umma ta zo Hajiyan su Sadiya ma tazo.


Tunda suka dawo bikin Munira kullum maganar aure Umma da Affa suke mata,ita kam ta ƙosa a tura su service. Takardun na fitowa sai taga ita Legos aka tura ta, bata damu ba dan ita burinta shi ne ta matsa daga gidan.


Ta gama cin tuwon ta ƙwashe ƙwanukan har da na Umma ta nufo bakin rijiya tana wankewa, Umma dake cikin ɗakin Affa tasa baki ta kira Ruƙayya, ta amsa tare da miƙewa ta nufi ɗakin.


Gabanta ne ya faɗi san da taga takardar ta a hannun Affa, bayan ta samu guri ta zauna sai Affa ya ce "Ummanki ta sanar da ni zaki tafi Legos?" Gaban Ruƙayya yana faɗuwa ta ce "Eh, can aka tura ni ɗazun naje na amso." Ya ce "A da dai kinje Kano, yanzu ma da Kanon ne ko irin su Katsina jihohinmu na nan Arewa sai in yarda amma ba zan amince ki je gari kamar Legos ba, a'a." Shiru Ruƙayya ta yi har sai da Affa ya gama sannan ta ce "Kayi haƙuri Affa wata tara ne don Allah kayi haƙuri."


Ya ce "Ke ba ajin zancen aure a bakin ki sai dai na karatu,ki sani na matsu naga auren ki, Allah yasan nayi miki yanda zan iya ita wannan ƙawar taki da ku ka je biki,ba gashi ba tayi auran in ma bautar ƙasar ne ai tana ɗakinta zatayi yanzun ko?


Ruƙayya ta ce "Affa su fa karatu zasu cigaba law school zasu shiga dubu ɗari biyu da hamsin, kuma suma wata tara ne zasuyi."


Ya ce koma menene ai yanzu a ɗakinta zatayi shi yi ko? Shiru Ruƙayya tayi Affa ya cigaba da mata masifa kan aure don haka ba batun wani service.


      ***      ***     ****

Goma daidai ta gama tsantsara ƙwalliyarta cikin Ankon bikin Munira da suka yi,ta fito ta shiga ɗakin Umma.


Umma ta ce "To maimakon ki tuna min sannan in sanar da Affanku shine ki kayi shiru." Ta ce yi haƙuri Affa zai ce a'a ne kinsan baya son yawan zuwa." Ta ce ki gaida su, Shagon kusa da lungunsu ta tsaya tayi ma su Mama da su Muhsin tsarabar chizee da bisket. A hankali take tafiya bakin shagon Nasir "Kai Oga gafa mutuniyarka." Inji wani yaron shagon shi "Wa kenan.?" Yaron ya ce "Ruƙayya,kai Oga yarinyar nan aƙwai yanga,dubi tamkar mai tausayin ƙasa , koda yake ai tana da abubuwan yangar."


Nasir ya miƙe daga aikin da yake ya fito ya tsaya suka gaisa ya ce zaya zo da dare. Bayan ta je gidan Murja sun wuce gidan Fati a can ta ce don Allah su roƙar mata Affa ya yarda ta je service suma sun mata ƙorafin aure ta yi musu ƙaryar cewa ai aƙwai wanda suka haɗu dashi bikin Munira kuma shi zata aura.


Kafin ma ta gama service komai zai kammala kuma zaya yarda tayi aikin ta. Sun yanke shawarar kan cewa Ruƙayya ta je ta samu Yaya Amina da Yaya Suwaiba da Yaya Sadiya ta gaya musu su haɗu ranar juma'a kasancewar Affa in ya dawo sallar juma'a baya komawa kasuwa shi ne suke son magana dashi.


   ***    ***    ***     ***

Yasha mamaki da ya samu gidan tamkar kasuwa, ƴan jikokinshi suka yi mishi oyoyo, ya ce biki kuke yi ne a gidan?" Ummansu wacce ta fito dan taran shi, ta ce, sun zo gaida kaine affansu." Ya ce "sai dai bayan masallaci don lokaci ya ƙore,in na dawo sai mu gaisa." Sun mishi sannu da zuwa sannan suka koma suka ci gaba da hirarsu.


Ɗakin Umman shi ma ya shigo suka dinga gaishe shi ɗaya bayan ɗaya Sadiya ce ta soma magana "Affa dama gurinka muka zo." Ya ce to ince dai lafiya? Ta ce lafiya lau dama kan zancan Ruƙayya ne. Muka ce don Allah kayi haƙuri ka barta tayi bautar ƙasar tunda wata tara ne. Suwaiba ta ce kuma Affa ai Auta tana da kamun kai munsan zata tsare kanta," Amina ta ce "Kayi haƙuri Affa wata tara kamar yau ne." Su kuma su Murja da Fati suka ce "Haƙurin da aka yi na shekaru kusan biyar ban dama na secondary ai wata tara bazaya ga gara ba.


Ya ce "To duk naji jawabin ku yanzu, Amma ban ji wacce tayi zancan aure ba,ku ɗauki misali a kanku aƙwai wacce ta wuce secondary dukkan ku? Suka ce a'a, ya ce na mata haƙuri ko ban ba? Suka ce kayi, ya ce, to ta haƙura gara ma da da tsayayye ne da sai na amince.


Sadiya ta ce "AÆ™wai wanda suka  yi magana, haka suka yi tayi kafin daga baya Affa ya ce yana da sharaÉ—in,sharaÉ—in sune zasu É—auki nauyin yi mata siyayya, zuwa kuÉ—in mota dan bashi da kuÉ—i. Ya ce karatun ta ne ya cinye komai harda kuÉ—in da bawan Allah ya aiko mishi da zakka, suka ce mutumin nan ko wanene yana da mutunci, Allah yasaka mai da alkhairi. Umma ta ce Æ™wanakin nan ba'a yi sati uku buhun shinkafa huÉ—u da taliya ya aiko mana gashi nan har yanzu ita muke ci Affa ya ce hakane gashi ya Æ™i mu haÉ—u ina son in mai godiya ba hali. Yaran suka ce Allah ya saka mai da gidan aljanna shima ya biya mishi buÆ™atunshi.


Sun gama yanke shawarar su kowacce zata bada daidai aljihun ta mata kenan sarakan zumunci,Yaya Fati ta dubi Ruƙayya "Auta don Allah gidan mutumin nan na kusa da Bus stop zan aike ki,mai saida litattafan Hausa, ina son wani littafi ne sabon fitowa ne,na je shagon shi ya ce min suna gida.


Ruƙayya ta ce "To ki koma shagon mana tunda yanzun dai nasan baya gida ƙila ma ya kai takardun shago, Fati ta ce "Ke dai baki son zuwa ne bari in zamu wuce zan biya da kaina."


Sadiya ta dubi Fati ta ce "har yanzu kina nan da shegen karance-karancenki É—in nan."


Murja ta ce "Ai in gaya miki sai abin da ya yi gaba in dai Fati ce tunda mijinta ya É—aure mata gindi.


Fati ta ce "Dole ne ya ɗaure min tunda yana ganin amfanin shi, Allah ku kun jahilci karatun Hausa ne kawai, amma yana da fa'ida sosai matsawar za kiyi amfani da abubuwan da ki ka gani na ƙaruwa zaki koyi kula da mijinki yanda zaki zauna da kishiya da dangin miji,ban da wannan ga kalolin soyayyar da zaki ma mijinki koda gurin ƙwanciya ne, sannan....." Dundu Amina ta sakar mata tare da faɗin.


Lallai Fati Yaya Sadiya ki ke gaya ma maganar ƙwanciya da miji?.


Suwaiba ta na dariya ta ce "Allah ya ƙyauta miki Fati." Ita ko Ruƙayya sai tayi waje, Sadiya kuma ta ce "Uhm ni dai ai kallon ta nake yi." Fati ta ce "Kun ji ku da wani abu, dukkanmu ba mata ba ne.


Murja ta ce "kina da wani da yake bayani kan ƙwanciyar ki ara min." Ta ce bari in kinzo gidana sai muyi maganar.


   ***     ***    ***      ***

Ruƙayya ƴar gata sun haɗa mata komai ta tafi garin Legos. Haka aikin nasu ya yi ta cigaba ƙwanci tashi yau sati shida kenan Ruƙayya tana garin Legos, duk waɗanda suke tare tafi shaƙuwa da Nuraddeen M Adam ɗan Kano ne ko yaushe suna tare.


Yau sati ta fito sanye da baƙar doguwar riga gyalenta baƙi takalmi da kuma baƙar jaka. Ta yi ƙyau sosai, Nuraddeen ya dube ta,sai ina Ruƙy, ta ce "Ina son naje saloon gashina ya yi datti ina son na ɗan wanke, ya ce to bari muje, suna tafiya suna labari har saloon bayan an gyara mata ya nemi ta rakashi kasuwa sun shiga gari sosai kafin su ga wani super market.


Gaban Ruƙayya ya yi mugun faɗuwa, ta tsaya, Nura ya ce "Kin gaji ne?" Ta ɗan wayance.


Sosai ma, ina son na huta" ya ce "To mu ƙarasa daga nan sai gida suna shiga idon ta ya sauka akan Dady,yana tsaye yana waya ta ja gyalenta ta rufe gefen fuskanta ta kuma shige ɗaya gefen.


Dady bai kula da ita ba sai dai gaban shi ya yi mugun faɗuwa, waige-waige ya shiga yi tamkar mai neman wani. Lokaci guda kuma ya fita wajen. Sun jima sannan suka fito bata ganshi ba tanata yi ma Allah godiya. Sai dai kuma taji sanyi ganin da tai mishi. Shi kam Dady tana ganin kullum ƙara masa ƙyau ake yi,yaya zata yi da son Dady?.


    ***     ***    ***     ***


Hajja ta dubi Dady sannan ta dubi aƙwatunan gaban ta. Haƙiƙa kaya sunyi tuzuru, sai dai nace Allah yasa kada itama muji shiru irin na wancan lokacin, don wannan karon in bai yiwu ba Allah ƙauye zamu je ma samo maka mata,mun gaji da ganin ka haka,ko so kake sai na mutu? Ya ce "Allah sarki Hajja insha Allahu sai kin goya min ƴaƴa da jikoki."


Ta ce "Allah ya tsare ni in samu ma inga auran naka,ai ko yanzu nagode ma Allah.


Ya ce "To Hajja zan wuce amma ranar juma'a zan zo nan Kaduna don haka zan iso da azumi zan buɗe baki a nan, Please ai min waina da fankasu,in kuma samu Hollandia mai sanyi, ta ce Allah shi kaimu, yanzu ai kayi hankali ba irin da ba, ya ce da me nake yi? Ta ce wancan auren da kayi bai yiwu ba ai kayi rawar kai,nan fa kazo kasa ni gaba kana cewa ga waya in ma Momyn ka magana su wuce da wuri kai kayan lefe,yayi murmushin yaƙe tare da girgiza kai don Hajja ta tuno mishi wani abu mai motsa rai ya ce "Hajja bazaki gane ba ne wancan auren da man aƙwai bambanci,na tabbata inda ace Pretty ce zan aura wannan auren tabbas cewa za kiyi da,ban yi komai ba saboda rawar jiki ya tsura ma window ido tamkar a nan zai ga Pretty ɗin shi a gurin. Wasu ƙananan hawaye suka taru a zagayen ƙwayar idonshi. Ya furta a hankali "Allah ya rage ma aya zaƙi." Ya dubi Hajja har in mutu zan kasance ina son Pretty."


Hajja ta yi data sanin furta mai maganar auran shi na da,


A fili ta ce "Nasan kana son ta Yusufa, ta dalilin ta ka samu hawan jini,baka dangana da yarinyar nan ba sai da aka haɗa da roƙon Allah sannan ka lafa kayi haƙuri,matar mutum kabarin sa, ya ce "Hajja sam ban so ni aka haɗa da roƙon Allah ba wai don na dangana da son Pretty naso a ce son ta ya kashe ni,." Hajja ta ce "Ashsha! Ashsha kul na kuma ji koda bai kashe ka ba ai ya saka rayuwarka cikin wahala tunda in ciwon nan ya tashi duk hankalinmu tashi yake. Ya ce ai Dad shine ya ja min dan da basu cuci Affa sun zalunce shi ba wallahi na san ba zai hana min Pretty ba,kuma banga laifin Affa ba domin an yi mishi FIN ƘARFI, kafin Hajja ta ce wani abu wayar Dady ta shiga ƙara ya duba Hussain ne ya tuna suna can suna jiranshi game da programs ɗin bikin shi. Ya ce "Hello, Hussain sorry kuna jirana ko, ina zuwa. Ya kashe wayar sannan ya kira layin direban shi ya ce ka sameni gidan Hajja a Kabala ka hawo achaɓa kazo ka jani.


Sabi'u ya ce "To ƴallaɓai." Komawa ya yi ya jingina da kujera. Hajja ta dube shi ta ce "Ina ce kace tafiya zaka yi." Ya maida numfashi bazan iya jan motar bane shine na kira direba ya jani. Gaban Hajja ya faɗi ta ce,ba dai jikin ba ne? Ya ƙaƙaro murmushi ya ce "a'a ba jikin bane Hajja,kin san jiki da jini gashi muna yawan zirga-zirga aikin ba hutu,ta ce To bari in baka wani magani na gajiya ne shima na hawan jinin ne, ta miƙe ta shiga bedroom ɗin ta ta ɗauko garin magani ta miƙa mishi.


Gashi kuma kai ba gwanin shan koko ba sai kasha da Yoghurt ko Hollandia naka,ya yi,sai sannan direban ya yi mishi waya ya iso, ya ce to,gami da faɗin Hajja ni zan tafi." Ya ciro kuɗi,ba dai ki buƙatar komai ko? Ta ce a'a ba komai, ya miƙa mata kuɗin da shima bai san iyakar su ba............




🖊️🖊️🖊️

[7/31, 16:44] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 2



Baisan yawan su ba, ya ce "gashi na cin goro, wannan kuma ki ba ma Saude." Ta ce mungode Allah shi albarka ya biya buƙatu. Ya ce amin Hajja nagode, ta ce a'a nice da godiya Yusufa aini sai hamdala da Ubangiji ya barni da raina, da ubanka ne me min komai gashi har mun kai matsayin da ya haifeka gashi kaima kana kula dani, ya ce duk albarkarki muke nema Hajja.


Har waje ta rakashi inda ya shiga mota direba yaja shi suka tafi.


   ***     ***   ***    ***


Yau kam a gajiye Ruƙayya ta taso daga kotun da aka tura ta game da wata shari'a. Bakin gate suka yi kiciɓis da Nuraddeen Kano. Ya ce a'a Ruƙy yana ganin ki haka hula a hannu jaka hannu gari yai sanyi? Ta ce kai dai bari kawai Nuri,yau ɗin nan na gaji sosai fa ta nufi ɗakin su ta shiga sai da ta huta tayi wanka taci abinci sannan ta yi sallah.


Washegari tana ɗauraye after dress ɗin ta da T shirt ɗin ta,Nura ya sameta Ruƙy ina tunanin duk ma yanda za'ayi gobe Friday koda yamma ne zan je Kano, ta ce ka dawo yaushe? Ya ce Sunday ko Monday." Ta ce Kash, nima da ina da issasun kuɗi da mun je sai nima na sauka Kaduna,in yaso in kana dawowa sai na baka adireshin gidan mu sai mu dawo.


Ya ce "Oh muje in kuÉ—in naki sun kasa sai na cika miki dan nima sai a hankali,allwasce É—ina ne na wancan watan ta ce aini nawa tuni sun sha aiki.


Ranar juma'a tunda safe suka soma shiri,tasowar asuba suka yi,dan haka huɗu tai musu a Kaduna. Sun tsaya a garejin Mando nan Ruƙayya ta sauka,Nura ya rako ta inda yake cewa gashi ba waya a hannunki bare in na shigo unguwarku na kira ki. Ya kamata ace kina da waya fa ba girmanki ba ne. Ta yi dariya sannan ta ce Nuri kenan,Ni nan daka ganni ban so na riƙe waya ba ne, Amma ko ada,na riƙe waya a lokacin da sai wanda ya isa ne yake riƙewa, kuma ma yanzun ban ga dama bane, amma ka bari insha Allahu sai dai kaji calling ɗina. Alƙawari zan kiraka da layina, ya ce shikenan.


Mashin ta samu ɗari uku tun daga Mando gareji zuwa Kabala su kenan kuɗin ta dan haka ta ce muje ai gida nazo kuma bana son shiga mota ga hadari yana ta harhaɗowa gara na isa gida akan kari,bana son ruwa ya taɓa lafiya ta. Sun iso daf da shiga Kabala suna kan titin independence aka soma tsula ruwa nan kuma mashin tayi faci. Ruƙayya ta ce "Oh ni Ruƙy ya zanyi kenan? Ta sauka ta bashi ɗari ukun ya ce "Yaya zaki bani duka gashi bamu kai ba? Ta ce ba komai kaje kawai bari na taka, ya ce ga ruwa? Ta ce kar ka damu,tana tafiya duk ta jiƙe.


Tun daga nesa Sabi'u ya dubi ubangidansa "Ƴallaɓai ga wata can tana buƙatar taimako." Dady ya amsa ba tare da ya ɗago ba, ya ce "A taimaka mata." Ya rufe baki tare da faɗuwar gaba irin wacce bai taɓa ji ba, ya kai hange ga yarinyar da Sabi'u ya ce su taimaka mata,da tazara tsakanin su kuma shekaru baƙwai masu ƙyau bai ganta ba, amma sai da ya gane ta. Ko shakka ba zaya yi ba waccan Pretty ɗin shi ce, domin duk da basa tare kuma idanunshi sun daina ganin ta wannan ba zai hana zuciyarshi kullum karanta surar ta ba, haka yake tsarata kullum.


Sanye take da jallabiya doguwa baƙa haɗe da gyalenta,jaka da takalmin ta ma duk baƙaƙe ne,sai dai ta jiƙe sharkaf har ɗiga take yi.


Jijiyoyin jikin Dady suka tsaya cak, komai ya daina kai saƙo a jikinshi lokacin da ya tsinkayi muryar Ruƙayya suna magana da direba yana cewa baiwar Allah shigo mu taimaka miki ta ce "a'a, nagode Malam na kusa gida gashi kuma duk na jiƙe,ka na jiƙa muku kujera." Ya ce, bakomai shigo taimako ne ai."


Sam Ruƙayya bata ga Dady ba kasancewar motar na waje baya ganin na ciki, amma shi Dady yana ganin ta, tana shaga gaban motar gabanta ya faɗi sai dai har ga Allah bata zata da wani cikin motar ba, don haka sai tayi addu'a a ranta dan kar ta faɗa mugun hannu.


Ta ɓalle maɓallan gaban abayar ta cire sai ga riga T.Shirt mai ɗauka da rubutun N.Y.S.C ta bayyana da wandon ta, ta zage jakar hannunta ta ciro rigar sanyin N.Y.S.C tasa ta ɗaura gyale kamar ɗan ƙwali sannan ta ciro hijabi ƙarami tasa ta maida abaya cikin jaka. Ƙamshin da take shaƙa da faɗuwar gabanta da yaa tsananta sune suka tuna mata da wani abu, tabbas duk inda turaren nan ya fito daga gurin Dady ne, domin tun da suka rabu da Dady bata kuma jin ƙamshin nan ba sai yau.


Ya Allah! Ta faɗa cikin wata muguwar faɗuwar gaba, lokacin da ta dubi madubi ta ga Dady zaune a bayanta. Daga nan bata kuma motsi ba sai ƙwatancen da ta dinga ma direba har lungunsu. Ta ce da direba nagode fa, ya ce bakomai." Ta buɗe mota ta fita.sannan ta saci kallon Dady ta rufe ta tafi, zuciyarta cike da mamakin Dady. Lallai duniya wai kamar Dady ya ganta ya share ta, hawaye ya zubo mata tayi nadamar zuwan ta Kaduna a yau.


Shi kam Dady be ma san anzo har Ruƙayya ta fita ba,haƙiƙa jikinshi ya mutu, zuciyarshi ba ta tare dashi,yana tunanin dama Pretty bata yi aure ba,ko ko tayi ta cigaba da karatun a gidan mijinta? Auren ya mutu ne? Ko ko mijinne ya mutu? Ko ko da auren ta? Wanene zai bashi wannan amsar. Ganin Ruƙayya ya tsorata Dady gami da firgita shi, ta taɗo mishi da wata sabuwar muhimmiyar soyayyar ta.


A fili ya ce "Wannan karon ko Pretty tana da aure ko batada shi, koma wanene mijinta sai ya bai mishi Pretty É—in shi,kai koma ta halin yaya ne shi bazaya barta ba,bai san sun iso gidan Hajja ba sai dai ya ji Sabi'u na cewa.


"Ƴallaɓai mun iso." Ga zaton shi gidan su Ruƙayyan, sai yaga gidan Hajja nan ya soma tunanin kodai mafarki ne? Kai ba mafarki bane. Ya dubi Sabi'u ya ce "ina Pretty ɗin fa? Kan Sabi'u ya ɗaure ya ce,wace Pretty kuma ko wacce muka ɗauko? Dady ya ce "Eh," Sabi'u ya ce ai mun sauke gida Ƴallaɓai baka kula bane." Nan Dady ya wayance ya ce "Ok." Ya shiga gidan Hajja ya bar Sabi'u da mamakin halin da Ƴallaɓai ya shiga kan yarinyar nan,a ranshi ya ce koda yake fa yarinyar ta haɗu dole Oga ya ruɗe har magana yake shi kaɗai ina jin shi.


  ***    ***     ***    ***


Yaraf ya zube a kujerar falon Hajja,Saude da ke jira abinci akan centre table tana faɗin "Uban masu gida kasha hanya,in fatan dai baka sha dukan ruwa ba?" Da ƙyar ya ce sannu Saude ina Hajja? Ta ce gata nan zuwa tana ɗauro alwala ne, sama-sama suka gaisa da Hajja don haka ta tasa shi da tambayoyi jikinne Yusufa ko ko gajiya ce?.


Numfashinsa yana sama-sama ya ce "Duk aƙwai." Ta ce "To ai gara ka je asibiti ko? Ya ce "wannan bana asibiti bane ku barni na huta bana son magana." Duk shiru suka yi,yana ƙwance har aka kira magriba, ya yunƙura da ƙyar ya tafi sallah. Hollandia kawai ya ɗaɗɗaka baici komai ba ya kira direba a waya ya zo ya ɗauke shi. Hajja ta yi tayi ya ci abinci kasancewar ya yi azumi ya ce "Kiyi haƙuri Hajja ba zan iya cin komai ba, ina cikin damuwa ki min addu'a." Ido ta bishi da shi har ya shiga cikin mota sam baya tare da tunanin shi, tunanin shi kawai ta ina zaya fara da wannan lamarin.?


A hankali ya ce "Sabi'u kaini gida gurin Momy."


Yana zube gabanta kan kafet ya yin da take zaune kan kujera, gabanta sai faÉ—uwa yake yi saboda bata san dame ya zo ba. Kallonsa tayi yana bata tausayi dan tuni Dady ya mance da ake dariya,ko yanayi su dai ya daina musu.


Sannan ya zama miskilin gaske ga zafin rai da ya koya waɗannan halayen sama taka ya same su tun bayan da ya gama jinyar rashin Ruƙayya, sai dai har Yanzun yana basu girman su tare da musu biyayya.


Ganin bashi da niyyar magana yasa ta ce "Dady menene damuwarka? Ya dubeta idanunshi sun kada sunyi ja ya ce "Momy naga Pretty, Momy Ruƙayya na gani. Shin da gaske ne tayi aure kamar yanda kuka sanar da ni?.


Gaban Momy ya yi mummunan faɗuwa cikin tsoro ta ce "Haka magabatanta suka sanar damu." Ta cigaba "Ka nutsu Dady kaida gobe kamar yanzu ka zama Ango." Dubi yanda gidan nan ya cika da ƴan biki sannan ka zo min da labarin ka ga Ruƙayya me ganinta zaya amfana maka a halin yanzu?"


Ya yi wani murmushi irin na É“acin ran nan ya girgiza kai shi kam yana mamakin yanda kowa ya kasa gane irin son da yake ma Pretty, ya furzar da wani huci mai zafi sannan ya ce.


"Momy aini nama manta da wani labarin zan yi aure, domin dama a rashin Pretty zan auri Zainab, kuma yanzu na ganta don haka har ga Allah na manta da wani batun aure.


Gaban Momy ya faÉ—i,dan tasan zaya iya fasawa don haka sai ta soma lallashinsa.


"Haba Dady yanzu, wannan girmanmu ne,ace wancan karon mu tara mutane abu bai yiwu ba, yanzu ma mu ƙara maimaita na da? Ka tuna burinmu muga ƴaƴanka shekarun mu sun tsawaita. Haba Dady ko so kake sai mun mutu sannan zaka yi?"


Hawaye suka zubo ma Momy abin da ko cikin mafarkin shi baya son gani,wato kukan Momy.


Da sauri ya isa gabanta


"Kimin afuwa Momyna." Ya sa hannu yana share mata hawayen, "Kada ki min haka Momy, abin zaya yi min yawa,ban sama kaina son Pretty ba daga Allah ne,nima na kasa control ɗin kai na ne, Momy ki fahimce ni." Ido ta zuba mishi gami da tausaya mishi, don haka sai ta ce "Dady kai namiji ne mijin mace huɗu,kana da izinin auran Zainab da Ruƙayya har ma da wasu biyu idan kana da buƙata. Yayi shiru na wasu lokuta sannan ya ce "Shikenan ku ci gaba da bikin ku." Ta ce "To amma nafi son ka ƙwantar da hankalinka kada ciwon ka ya tashi,ka bi komai a sannu har a gama wannan ko.? To kawai ya ce mata, ya miƙe ya nufi shashin daya gina wani tsatsaran plate mai ƙyau a cikin gidan nasu.


Kai tsaye bedroom ɗin shi ya nufa ya shige toilet duk da sanyin da garin ya ɗauka sakamakon ruwan saman da ake yi tun yammacin na yau,bai hana shi sakarwa kanshi ruwan sanyi ba sai da yaji sanyin yana ratsashi sannan ya fito mai ya shafa ya saka jeans baƙi da ƴar shirt sannan ya ɗauko wata rigar sanyi jibgegiya mai laushi ya saka yasa hularta. Har lokacin sanyi yake ji, zazzaɓi ne ya sani amma sai ya share ya tsani shan magani ya ɗauki key ɗin mota ya fito.


Yana ƙoƙarin shiga motar,motar Hussain tana shigowa, dole ya tsaya ya ƙaraso kasancewar har Yanzun ana ɗan yayyafi sai ya shiga gaban motar Hussain ɗaya gefen, suka yi hannu, Hussain ya ce Ango ya za'ayi ne? Ni ɗazun na kiraka muna ƙoƙarin tafiya sai kuma ka ce min kana hanyar zuwa Kaduna. Shi ne abin ya bani mamaki tunda nasan yau aƙwai wani program shi ne ka taho? Yanzun dai nace bari na zo naji goben sai mubi jirgi da wuri ko?"


Dady ya É—an takure jikinshi saboda sanyi sannan ya ce  "kune zaku tafi da su SaddiÆ™ saboda ni bana jin daÉ—i zan zo daga bayan ku,ku tafi da su Dad tunda suma jirgi zasu bi, amma fa sha biyu zasu tashi gidana zaku sauka Sunday yana nan munyi waya dashi zaku samu komai, sannan aÆ™wai Abokaina nacan su Sagir matansu zasuyi ma matanku tarba sosai,ba wata matsala ku cigaba da gabatar da komai kar ku damu da cewa sai nazo.


Hussain ya ce "Daka É—aure munje kada ita Zainab É—in ta zama cikin damuwa." Ya ce ,no ba damuwa zan mata waya yanzu ma gurin Dakta zan je,kaje gida ai zamu haÉ—u gobe É—in." Hussain ya ce "To bari na kaika sai na dawo da kai." Dady ya ce "a'a nan kusa muke ka tafi gidan shi zan je.


Hussain ya tafi sannan Dady ya É—auki mota ya fita.


Kai tsaye Kabala ya nufa bakin lungun su Ruƙayya nan ya tsaya. Saboda yayyafi ba yara don haka sai ya kashe motar sannan ya shiga lungun gidan,yana nan yanda yake sai dai ya samu canje-canje,wato ƴar kwaskwarima yana tsaye daf da ƙofar gidan yana jiyo ɗan motsi baisan ko na wanene ba,ya yanke hukuncin ya yi sallama.


Ruƙayya suna zaune da Umma taji gabanta ya faɗi domin tasan Dady ne,dama ƙarfin hali tayi dan kada su Umma su gane tana cikin damuwa,dan haka sai ta daure har suke hira tana ba Umma labarin Legos. Har sai da Affa ya shigo ta gaida shi suka ɗan yi hira kafin kiran magriba. Saboda ruwa tunda ya tafi sallar magriba bai dawo ba ko sun haɗa sallar ne ko kuma ya tsaya sai isha'i ne bata sani ba.


Umma ta dubeta kamar ana sallama ko? Ta ce naji ƙila gurin Affa aka zo,ta ce A'isha tana ɗaki tana sallah je ki tura ta taji,ɗakin ta nufa gurin A'isha ƴar gidan Yaya Sadiya tace je ki waje zakiga wani mutum in ya tambayi ki Affa kice baya nan.


Yana tsaye ta fito tai mishi sannu ya amsa da yauwa ƴan mata, ta ce kana neman Affa ne? Ya ce a'a Ruƙayya tana nan? Ta ce Eh, ya ce kirata ki ce tazo, ta gaya ma Ruƙayya Aunty wai ke ake nema, ta ce kije ki ce mata nayi bacci,ta zo tace tayi bacci, ya yi murmushi sannan ya ce ita tace kice tayi bacci? A'isha ta ce Eh, ya ce "To koma ki ce mata wai Dady ne yace zai jira ta har sanda zata tashi,tana gaya ma Ruƙayya, ta ce shegiya kin ce mishi ne ni nace ina bacci? Ta ce Eh, Ruƙayya ta kai mata duka maimakon ki ce a'a, A'isha ta ce ai na manta ne Aunty.


Zazzaɓi sosai ya rufe Dady amma yana jingine jikin gidan Affa dan ma an samu yayyafin ya yi sauƙi a haka Affa ya shigo lungun haska tocila lokacin kuma goma ta ɗan shige shima Affan sun tsaya sasanta wani aure ne ya ga mutum tsaye gashi ba wutar lantarki. Ya yi gyaran murya sannan ya ce "wanene?" Dady ya tsugunna ƙasa "Affa sannu da zuwa." Affa ya ce yauwa ban shaida ka ba fa." Dady ya ce nine Yusuf,kan Affa ya kuma ɗaurewa ya haska shi da tocila sannan ya ce Wane Yusuf fa? Dady ya ce "Baka gane ni ba Affa?" Affa ya ce "shigo dai muji."sun zauna sannan Affa ya gane shi cikin mamaki ya ce Yusufa ai wallahi ban shaida ka ba sam ganinka nayi kayi min ƙiba.


Dady ya yi murmushi sannan ya ɗan russuna yana gaida Affa, Affa ya ce ya bayan saduwa kuma Yusufa shiru? Dady ya ce tunda muka bar nan bani da isasshen lafiya waje aka fidda ni dana dawo kuma sai harkokina suka koma Abuja, yanzun can nake,ai na zazzo bana samun ka sai dai na bada saƙo gurin mai shagon can."


Affa cike da mamaki ya ce "Dama kai ne ke aiko min da saƙon nan?" Dady ya ce "Nine Affa." Affa ya ce "Madallah to ya iyalin kuma." Dady ya ce "To ana dai niyya." Affa ya ce kana nufin har yau bakayi aure ba?" Dady ya ce "Eh, to gobe ne dai ɗaurin auren." Ya ce "Allah sarki a ina ne? Dady ya ce ba anan bane can ne Abuja." Ya ce "to Allah yasa alkhairi. Yana son ya sako zancen Ruƙayya kuma ya kasa don bai san me Affa zai ce mishi ba.


Ba ya son ya ji Affa ya ce yayi haƙuri,don haka sai yayi shiru. Sun ɗan taɓa hira sannan Affa ya ce "naga kamar kana rawar sanyi." Dady ya ce bana jin daɗi ne, Affa ya ce to kaje kasha magani ka huta zama da ciwo babu amfani, to kawai ya ce amma can ƙasan ranshi yana cewa,ga maganin nan a gidan ka. Sun yi sallama akan zaya kuma zuwa kafin ya tafi.


Da ƙyar ya kai kanshi gida. Kai tsaye sashen sa ya wuce, cikin bargo ya ƙudundune haka ya ƙwana yana rawar sanyi.


Washegari Dad yaga basu haÉ—u sallar asubahi ba, kuma bai shigo ba, gidan cike da baki ya kira layin Dady tayi ringing har ta katse ba'a É—auka ba,kusan sau biyar yana kira,wayar tana falo yana jiyo kukanta amma ba zai iya tashi ba.


Dad ya juya ya kira layin Momy wacce dama tana kan hanyar shigowa, ta ƙaraso bedroom ɗin shi riƙe da wayar ta tana ringing ta ce gani ma dama nan zan shigo, ya ce wai ina Dady ne? Bamu yi sallah dashi ba yanzu har taƙwas tayi bai shigo ba.


Gaban Momy ya faɗi ta ce "Ina jin ƙila baya jin daɗi yana can sashin sa. Ta fita shima Dad ya ɗauko sandarsa ya nufo waje yana dogarawa ne saboda ciwon ƙafa dake damunsa.


BaÆ™in Yola dake É—akin Momy suka fito suna gaida Dad sanda ya fito ya nufi sashin Dady tuni Momy ta kusan shiga, baya falon dan shi kanshi key É—in shi gaya nan akan wani É—an kucilin firji wanda sam saboda Æ™anÆ™antar sa baiyi kama da firji ba,ta nufi bedroom É—in shi,ta matuÆ™ar tsorata da taga yana maÆ™yarkyata akan gado  da sauri ta cire masa bargo tana masa sannu, ta ce haka ka Æ™wana? Kai kawai ya É—aga mata daidai nan Dad ya shigo,ganin jikin Dady yasa tsoro ya kama shi.


Waya ya yima family Doctor ɗin sa,nan da nan sai gashi ya duba shi. Dady mura ce da ƴar damuwa ke damun shi,muran ce ma tasa masa zazzaɓi ya yi masa allurai dan ya samu bacci sannan ya rubuta magunguna. Dad ya ce to ban da abin Son menene na shiga damuwa,kai da zaka shiga sabuwar rayuwa. Momy ta ce ban sanar da kai bane jiya fa yaga Ruƙayya domin hankalinshi tashe ya zo min. Gaban Dad ya yi mugun faɗuwa a zuciyarshi ya ce innalillahi wa'inna ilaihir raji'un.


Kasa magana ya yi har sai da Dakta ya tafi bacci mai nauyi ya É—auki Dady, Dad ya dubi Momy ya ce "Hajiya yanzun ya ya zamuyi ne?  Momy ta ce "Uhm kai dai bari, haka za'a cigaba da biki kawai,in matar ta zo in tana kula dashi Æ™ila ya mance da RuÆ™ayya." Dad ya ce "In ma za'a bashi ba sai ya aura ya haÉ—a su ba."


Ta ce haka ne abin nan ya isheni.  Ya ce bari in angama wannan zan je Katsina filin nan da aka maida gurin sha'anin biki ana bada haya to nan ne gonar tasu mahaifin RuÆ™ayya zan bashi in huta nima bada zalunci nayi ba duk laifin Jega ne shi ya shirya komai, to na haÆ™ura nima cutata ya yi tunda kinga na daÉ—e da sallamar shi macuci ne na Æ™arshe." Momy ta ce "Hakan ya yi sai mu nema masa auran RuÆ™ayya."


🖊️🖊️🖊️

[8/2, 07:44] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 3



Dad ya ce "Ni dai koda ba zan nema mai auran ta ba in basu in huta."


   ***      ***      ***     ***


An É—auro aure amma hankalin amarya a tashe don haka ba'a samu yin biki a can Abuja ba aka tarkato aka taho da amarya.


Dady ya farka bacci, Zainab ya gani zaune gefen shi tayi ado sosai sai dai hankalinta a tashe yake. Ya yi ƙoƙari ya yunƙura ya tashi zaune ya ce "Zee yaushe ki ka zo?" Ta ce "Tare muka zo dasu Dad da Abokanka,tasa hannu a wuyansa, jikinka babu zafi ka ji sauƙi." Ya ce "Alhamdulillahi." ta ce "To zaka yi wanka ne?" Ya ce da ruwa mai zafi. Ya fito wankan su Momy suka shigo duba shi abokanshi ma dana can Abuja dana nan duk sun cika falon shima yana jin su sai dai jikin babu ƙarfi sannan zuciyarshi na gurin Pretty da son ganin ta.


     ***.   ***      ***


Affa ya dubi Umma ya ce "Af har zan fita na manta ban sanar dake ba jiya yaron nan Yusufa da dare ya shigo yake sanar dani É—aurin auren shi,kin ji ikon Allah duk shekarun nan baiyi auran ba."


Umma ta ce "Oh ikon Allah, to Allah ya sanya alkhairi." Affa ya ce "kuma kin ji ashe duk saƙon nan shi ne yake aiko mana ina ta neman mai kawowa ashe shi ne." Umma ta ce aini zuciyata ta raya shi ne domin naga buhun shinkafar nan mai tumatur kuma ita ce yake kawo mana da, sanda yake neman Ruƙayya." Affa ya ce "ai koda aka fasa auran yaso ya cigaba da kawowa na hana tunda suka zo nan da uwarshi nace kada ya ƙara kawo mana komai mungode." Umma ta ce "Allah ya basu zaman lafiya," Affa ya ce Amin.


Duk zancen nan da suke yi a kunnen Ruƙayya abin duniya ya ishe ta sam ita fa da tasan haka zata fuskanta a zuwannan da bata zo ba, duk da tana shirin wai cire son Dady daga ranta, sai dai abin da yake ɓata mata rai shine har yanzu zuciyarta Dady kawai take ma dariya,yaya zata yi ne domin a ganinta shi Dady bai yi mata adalci ba har manta da ita yayi ya ganta ya yi kamar bai ganta ba, ƙarshen wulaƙanci shi ne ya tako har gida ya shaidawa Affanta auran shi ƙila ma da ita yaso ya shaidawa taƙi fitowa daya kira ta.


         ***      ***       ***


Daran ranar Dady ya raka abokanshi na Abuja masaukin baƙinsu dake nan cikin layin su. Yayin da ƴan'uwan amarya suke can sashin su Momy.


Ya dawo ya zauna a falo tunanin shi ɗaya yana son zuwa gurin Pretty,ƙwarai ya so yaje yau da dare sai dai abokai ne ba zasu barshi ya fita shi ɗaya ba.


Sannan bai san yaya zasuyi da Affa ba ita kanta Pretty bai san nufin ta akan shi ba,ga zaton shi Zainab can gurin su Momy zata ƙwana, amma sai ji ya yi an dafashi ta ce "Tunanin me kake yi My dear?" Ya dubeta "Zee me yasa ba zaki je ki ƙwanta ba?" Ta ce Momy ta ce nazo saboda baka jin daɗi don kada ka ƙwana kai ɗaya,na shigo kuma sai na same ka kana tunani." A ranshi ya ce "Kada ki yarda ki san tunanin da zuciyata take yi." Ya miƙe "To muje." Bayi ta shiga tayo wanka, ta shafa turaruka tare da wasu sirrika da Hajiyarta ta bata,dan ma abin bai zo musu yarda suke so ba. Sun so kece raini a bikin musamman ranar dinner aƙwai shiri na musamman da Hajiyar taso tai mata, sai dai Kash! Rashin lafiyar Dady hakan bai samu ba.


Yana ƙwance rigingine ta zo ta ƙwanta kusa dashi tana kiran sunanshi a hankali yayin da ƙamshin daddaɗan turare ke tashi a jikinta.


Cikin natsuwa da hikima ta dinga janshi da hira tare da nuna masa irin so da ƙaunar da take yi masa domin ya samu ƙwanciyar hankali, dangane da fahimta da ta fara yi yana cikin damuwa.


Lamo ya ƙwanta tana jikinshi tana sharar bacci. Shi kam yana tunanin Pretty gani yake kamar bai mata adalci ba, yana ƙwance da wata ba Pretty ba. Yasan yau inda Pretty ce daran nan sai Allah kawai, amma yanda Zee ta nuna zalamar ta ta bashi haushi ace mace ba kara ba kunya shi bai son haka, to amma ba yanda zaya yi tunda matarsa ce sannan shima mabuƙaci ne.


Washegari da safe an aiko musu da break fast daga cikin gida. Shi kam bai ma tashi ba tunda ya yi sallah sai kusan sha É—aya. Ta zauna tana salo a gabanshi ya rasa sam bata birgeshi amma ya ya zaya yi wani sashe na zuciyarshi ya tuna mishi da wani abu da ya faru tsakanin Hussain da Madam É—in shi, ya ce mishi first night É—in su tasha wahala don sai da Dakta ya duba ta,da ya ce mishi nauyi kasa kaji mata ciwo? Sai ya ce kasan ita mace in virgin ce dole tasha wuya." Ya dubi Zainab sai yaji ranshi ya sosu, kenan dole wani ya santa, shi sam dai baiyi sa'a ba, domin bai kasance mazinaci ba.


Shiru kawai ya yi amma bashida walwala. Misalin biyar ya shirya ya nufi Kabala, bayan ya dawo raka abokanshi kai tsaye gidan Affa ya yi da shirin ko ta ƙwana.


Daidai wannan lokacin Ruƙayya ta dawo daga gidan Yaya Suwaiba ita da A'isha,tazo tana cewa Umma ni ƴar gata ce kinga itama Yaya Suwaiba ta cika ni da kuɗi." Umma ta ce "To Allah ya yi muku albarka dukkan ku." Ruƙayya ta ce Ummanmu "Yaya Murja ta sai min waya, Yaya Fati ta sai min layi ta cika shi da kuɗi, Yaya Murja ta yi min shopping Yaya Amina kuɗi kai na gode Allah." Umma ta ce shine abin godiya. Ruƙayya ta ce bari nasa number Nura inji ko yana hanya koma ya zo, Umma ta ce tafiyar dare zakuyi kenan dai? Ruƙayya ta ce tafi ƙwanciyar hankali hanyar Legos ɗin Allah dai ya kaimu lafiya." Umma ta ce Amin.


Tana kira Nuraddeen ya ce saukar su kenan, yake mata tsiyar waya da cewa tazo ta matsa samari sun fito da waya." Ta ce Wayyo Nuri,wa ya gaya maka? Ba ni da saurayi, ya yi dariya Ruƙayya kenan, yanzu ya ya zan kawo kaina unguwarku? Ta ce shiga motar kasuwa ce market in kun iso sai ka hau ta Kabala kuna zuwa bus stop kai min waya sai nazo na ɗauke ka, ya ce bari na hau Kabala ina zan ce,ka ce Kabala in kun zo sai ku miƙo daga Bus stop kuyo ƙasa ka kirani zan fito na jiraka.


Haka kuwa aka yi,nan bakin lungunsu ta jirashi,yana isowa suka tari juna cikin farin ciki da murna har cikin gida suka shiga ya gaida iyayen ta cikin girmamawa. Bai taɓa zaton Ruƙayya ƴar talakawa ba ce sai dai ya jinjina ma iyayenta dattawa ne masu ƙoƙari sun birgeshi yanda suka tsaya ma ƴarsu tayi karatu. Abinci ta gabatar mishi sannan ta shiga shiri.


Suna sallama da su Umma da Affa,aka yi sallama da Affa a waje. Sun fito dan kada su ƙara dare cak numfashinta yaso ya ɗauke,da suka yi ido huɗu da Dady yana tsugunne gaban Affa. A take ta ɗaure fuska sam bata son ganin shi,tana ganin shi mugu ne bashi da adalci. Tunda ganin shi babu abin da yake ƙara mata sai tashin hankali, suka jero da Nuraddeen, shi ko numfashinsa ɗaukewa ya yi ya kasa cigaba da gaishe da Affan, ya shiga ruɗani,ya ya ma haka Ruƙayya da wani?.


Kusa da Affa suka russuna sai mun dawo Affa." Ya ce Allah ya kiyaye hanya,kasa motsi Dady ya yi har suka wuce su. Affa ya ce "Ruƙayya ga Yusufa ko baki gane shi bane?" Ba tare da ta dubeshi ba tace"Oh ban ganshi ba ina gajiya?" Ta wuce cikin ko in kula.


Ba Dady ba hatta Affa yasha mamakin ta,zama Dady ya yi tare da saka kanshi cikin gwiwoyinshi sai da suka kai ƙarshen lungunsu sannan ta juyo ta dubeshi. Tsaki tayi sannan ta kauda kai jikinta babu ƙarfi jakar hannunta ta faɗi Nuri ya dubeta ya ya ne Ruƙayya idanunta ne suka ciko da hawaye cikin rawar murya ta ce bakomai, ya ɗaukar mata jakar ya ce yi sauri gurin da zamu hau motar Legos da nisa sosai.


Sai da suka zauna a mota sun ɗau hanyar Legas sannan ya yi ta janta da hira tare da bata labarin yarinyar da zaya aura sannan ta ɗan washe dan ya kula tana cikin damuwa baya son mata tambaya ƙila ba zata so yasan damuwar ta ba. Tana cikin wannan halin yana dai tunanin duk yanda akayi aƙwai wani abu tsakanin ta da mutumin da ya taras gurin Affanta,dan da fara'arta ta fito tana ganinshi sai kawai ta canza fuska. Kuma shima ya shiga ruɗani sakamakon ganinta.


Affa ya maido hankalinshi gurin Dady ganin shi ya yi zaune ya haɗa kai da gwiwa, ya ce "lafiya Yusufa?" Hannu yasa a kafaɗun Dady yana cewa "Taso haba Yusufa ya ya zaka zauna ƙasa." Jikinshi babu lakka ya tashi jiri yake gani don haka ya yi saurin dafa bango, Affa ya kula da haka don haka sai ya ce, zauna kan dakalin nan.


Dady ya zauna Affa ma ya zauna gefen shi Shiru kusan minti uku sannan Affa ya dubi Dady wanda zufa take keto masa, ya ce " Yusufa ka daina jin jirin?" Ya É—ago ya dubi Affa idanunshi sun kaÉ—a sunyi jajir ya ce ya lafa, sai dai naga Dakta ne saboda hawan jini na keson tashi, Affa ya yi shiru sai yana tuhumar kansa,anya ya yi ma yarannan adalci kuwa?.


In zaya iya tunawa tunda ya hana Ruƙayya Dady ko sunan shi bai kuma jin ta ambata ba, kuma yasan tana tsananin son shi, sannan bai ji daɗin yanda ta nuna mishi ba a yau shi har kunya yaji,yasan kuma har Yanzun tana sonshi hasalima a kanshine taƙi aure.


Ya dubi Dady tausayin shi yaji don zai yi matuƙar wuya bata sanadiyyar Ruƙayya ya haɗu da wannan mugun ciwon ba,haƙiƙa ya yi kuskure domin ba Dady ne ya yi mishi laifi ba Alhaji Mansur ne.


Ya dubi Dady ya ce "Yusufa meke tafe dakai kazo ne dan kai min sallama kamar yanda kayi alÆ™awari?" Wata wawuyar ajiyar zuciya ya saki sai da ya É—an huta na saÆ™wanni sannan ya ce Affa na zo ne dama sai kuma ya tuna kodai RuÆ™ayya tana da aure?  Don haka sai ya yi É—an tsaki ya ce ko da yake gaisheka dama na zo yi. Affa ya É—ago ido dan ganin shin Yusufa da gaske har zuciyarshi ya zo gaida shi ne? Dan tun kan yanda ya amsa ma ya gane yana cikin wani hali,ga mamakin sa sai yaga hawaye suna zuba daga idon Yusufan nan da nan Affa ya ruÉ—e tare da faÉ—in "Subuhanallah me yake faruwa?" Dady ya sauko daga dakalin tsugunnawa ya yi gaban Affa ya rasa me zai ce ya yi shiru sai dai zubar da hawaye yake yi, shima Affa kasa magana ya yi hannu yasa akan Dady yana cewa "Menene damuwar ka Yusufa,sanar dani ko zan iya taimaka maka domin nima ubanka ne." Shiru Dady ya yi dan rasa ta inda zai zancen,kiran sallar da aka yi ne yasa Dady ajiyar zuciya sannan ya É—aga ido ya dubi Affa. Affan ne yace suje suyi sallah in yaso sai suyi maganar cikin tsanaki.


Bayan dawowarsu daga masallaci ɗakin Affa suka yada zango. Shi Affan yasan matsalar Dady Ruƙayya ce to baya son ya soma kawo mishi zancan ta, tunda ya riga ya yi aure, shi kam Dady ya samu natsuwa kaɗan da ya yi sallah don haka ya raya ma ranshi koda Affan zai hana shi Ruƙayya sai ya sanar dashi har Yanzun yana sonta don haka sai ya gyara zama.


Affa ka gafarce ni nasan cewa ka riga ka ƙwaɓe ni da batun Ruƙayya sai dai amma har Yanzun ita zuciyata ke so,ka taimaka min Affa nasha wahala kanta, kada kai min horo da laifin da ba nawa ba laifin wani baya shafar wani na jira Ruƙayya auran ta ya mutu har na gaji sai dai yanzu bansani ba koya mutu ne ya matsa ya kama ƙafar Affa. Don son Manzon Allah kai min agaji."


Jikin Affa babu ƙarfi ya ce "Yusufa haƙiƙa na yanke maka hukunci da ba kaine kayi laifin ba, kuma ina maka albishir da na baka Ruƙayya a karo na biyu duk san da ka shirya ko gobe ne kazo a ɗaura aure. Sannan ina mai farin cikin shaida maka Ruƙayya batayi aure ba karatu tayi yanzu haka tana bauta ma ƙasa ne a Legos.


Daskarewa Dady ya yi a gurin gani yake yi mafarki ne nan ƴan minti na zaya farka haka nan yasan tsokana ce kawai Affa ba da gaske yake ba. Affa ya kula da nufin Dady dan haka sai yace kada ka damu kaje kayi shawara da magabatanka,sam Dady bai san lokacin da ya rungume Affa yana faɗin "Affa kaima Allah ya yi maka abin da ka ke so duniya da lahira, Allah ya jiƙan magabata." Ya miƙe,na tafi Affa sai ka ganni.


      ***       ***      ***


Kai tsaye gurin Momy ya nufa tana sallar isha'i,san da ya shiga yama manta cewa baiyi isha'in ba, koda yake akan hanya ta same shi.


Ya yi ƙwance kan gadon Momy idanunshi lumshe farin cikin shi ya yi mai yawa wai shi ne Affa ya amincemawa ya auri Pretty shin gaske ne ko kuma mafarkin daya saba ne?


Momy ta kai hannu ta dafa ƙafarshi "Yaya dai Babana? Ya ɗago da sauri kuma cikin fara'a ya ce Momy Affa ya kuma bani Ruƙayya, Momy ki tayani murna ina son ta sosai, tayi shiru tana kallon shi gani take ya soma taɓuwa ne,ganin bata ce komai ba yasa ya ce Momy kice wani abu Please cikin sigar shagwaɓa ya yi maganar Momy dariya tayi ta ce kafa girma Dady, ya ce ni dai kimin zancan Pretty,ta ce Nasan ba haka bane janka yake, ya ce "taso muje kiji a gunsa ya ce ko gobe ne na shirya nazo a ɗaura mana aure." Momy ta ce "Haba Dadyna duka fa satin nan aka ɗaura auran ka,shin ya ya za'ayi ka kuma wani? Bayan haka Ruƙayya ma batayi aure ba?" Ya ce "batayi aure ba tama gama karatu, yanzu service take yi a Legos Momy sai kinga yanda Ruƙayya ta zama Pretty ɗin ta sosai. Ya yi sujjada yana ma Allah godiya.


Shima Dad ya yi farin ciki dan kullum burin shi yaga dariyar ɗan tilon ɗana shi dan haka ya ce ba zai yi ƙasa a gwiwa ba goben nan zaya je godiya tare da kai komai, wani satin kuma a ɗaura ma Son ɗin shi aure.


Cikin farin ciki ya tura ƙofar falonshi, Zainab ta dubeshi ta miƙe ta nufo shi My dear ina ka shiga ne ? Ya rungume ta ina cikin farin ciki,itama ta soma murna,sanar dani me ya faru? Ya ƙara rungume ta,an bani Pretty ɗina wai yau nine zan auri Pretty ɗina, cikin sauri ta ture shi tana mishi wani mugun kallo,kasan abin da kake faɗa kuwa,kasan ni wacece ɗin ka kake min wannan maganar?" Ta soma kuka shekaran jiya fa aka ɗaura bikinn mu, amma kace zaka ƙara aure? Wannan wane irin wulaƙanci ne? Haba Dady."


Ya hau kujera ya zauna,ta juya zata shige bedroom, ya ce ke Zainab zo nan." Yanda ya daka mata tsawa shiyasa ta dawo ta zauna ya ce dube ni nan, ta dubeshi kinsan na taɓa ce miki bake kaɗai bace? Cikin kuka ta ce to amma da wuri haka? Ya ce saurareni Pretty ita ce rayuwa ta duk wanda yasan ni yasan halin da na shiga domin ta, ƙarshe ma a rashin tane na aure ki so Please ki bini a hankali kan Pretty komai zai iya faruwa kada ki ɓata min farin ciki na,ya riga ta shiga bedroom ɗin kai tsaye toilet ya nufa,laf ya yi cikin baho yana tunanin Pretty ina ma yana da number ta,ya kirata su sha hira,can cikin nisan da ya yi a tunaninta ya jiyo kukan Zainab.


Cikin hanzari ya fito tana ƙwance kan gado tana kuka. A hankali ya isa gurinta kallonta ya yi tana bashi tausayi ya zauna kusa da ita yasa hannu ya dafata tare da cewa "Zee.. Zee taso kiji." Ya ɗagota ta ƙwanta a kafaɗarshi tana shashshekar kuka ya ce "Zee son da kike min na gaskiya ne kuwa? Ta dube shi cikin shashsheka ta ce me yasa kake shakka? Tayi ajiyar zuciya sannan ta ci gaba "Ka daina shakka akan son da nake ma." Ya ce to in har kina sona dole kiso Pretty,kar ki zaton cin fuska nake miki, tsakanina da Allah nake sanar dake,ko iyayena sanin mahimmancin a gare shi ne dalilin daya sa zasu goya min baya. Zee inda kinsan halin da na shiga kan Pretty bama zakiyi magana ba shawarar da zan baki itace in baki son ta ki koyi yanda zaki sota dan auran ta ba fashi kuma gaskiya ni bazan iya zama inuwa ɗaya da maƙiyina ba,na sani kema ina son ki tunda ni ne na ajiye ki haka auran Pretty ba shi ne zai sa na wulaƙanta ki ko na daina sonki ba,ke dai ki bani goyan baya. Tasan duk abinda ya faɗa hakan yake nufi,garama ta haƙuri dan haka sai ta zame ta ƙwanta akan gadon shima bai ce komai ba ya koma toilet ya ɗauro alwala yazo ya shiga jero nafiloli dan nuna godiyar shi ga Ubangiji.


Washegari tun da sassafe Dady ya taka gidan Affa dan sanar dashi zuwan Dad É—inshi tare da tambayar yaushe ya kamata zuwan nasu ya kama? Da yamma ko da daddare? Affa ya ce da dare bayan isha'i ai zai fi ko?" Dady ya ce to shikenan Affa,yana son bashi kuÉ—i yana ganin kada Affa ya yi faÉ—a, daga nan gidan Hajja ya zarce.


        ***      ***       ***


Saude tana ƙofar kicin kusa da ita wata ƴar matashiyar yarinya ce tana wanke-wanke ya ce "Saude ina ƙwana?" Ta ce lafiya lau uban masu gida yaya amarya? Ya ce lafiya ina uwar gidana? Ta ce tana ciki ai zata ka daina yi damu, ya yi murmushi ya ce da tsohuwar zuma ake magani Ni na isa in yar da Hajja? Ya faɗa daidai lokacin da yake ƙoƙarin shiga falon Hajja, tana zaune kan kujera tana kallon T.V ya yi murmushi sannan ya ce Hajja sarkin kallon T.V ga kuma wannan uban gilashin. Ya ce me kike kallo ne? Ta ce Oho ga dai shi nan Ni ba jin abin da suke faɗa ni keyi ba ina dai binsu da ido, ya yi murmushi ya ce ina ƙwana an tashi lafiya,? Ta ce lafiya lau, ya kishiya ba haushi? Ya dubeta ban gane wa kenan ba? Ta ba haushi nake tambaya,kan Dady ya ɗaure ya ce nifa ban san ta ba, Hajja ta na dariya tace kai dai turawa sun gama dakai komai na Hausa baka san shi ba,to ina amarsu ta ango, ya ce Oh Zainab tana gida ni naji kin kirata da wani suna.


Ta yi murmushi ta ce ba dai kazo karyawa bane? Dan mun cireka a gandu, ya ce ni da wani albishir ma nazo miki, ta ce name? Ya gyara zama na wani auran, ya yi maganar fuska ba wasa,hakan ya sa ta cire gilashin idonta ta tsura mishi ido ta ce ka fahimtar dani kaine zaka ƙara auran ko wa? Da gadara ya ce ni ne nan,kinsan wadda zan aura? Ya ce Pretty.......


🖊️🖊️🖊️

[8/2, 21:24] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 4



An kuma bani ita a karo na biyu kuma insha Allah ranar sati za'a É—aura mana aure.


Ta harareshi kai amma bakada kai duk yaushe kayi auren ko sati ɗaya ba'a yi ba sannan ka soma zancan wani auran? Ya ce Hajja koda mata huɗu na aura a wancan satin aka ce ga Ruƙayya sai na saki ɗaya na aureta,ke ko yanzun da ba'a ɗaura da Zainab ba ko ranar ɗaurin auren ne wallahi fasawa zanyi dan dai sanda na ganta banida tabbacin ko tana da aure ko bata dashi,kar in fasa ya zama tanada aure. Hajja ta ce yaushe ka ganta kuma wayace maka batada aure? Ya yi murmushi ya ce ƙarewar rashin aure ma an bani ita,yau su Dad zasu je gurin Affa a gama komai nan ya koro mata labarin tun daga farko har zuwa yanzun daya je gurin Affa. Hajja ta yi fatan alheri tare da roƙon shi kan ya lallashi Zainab dan kishiya aƙwai ciwo, kayi adalci, ya ce insha Allah.


Kula aka ci mai da waina dan ya kaima Zainab,a phone ya kira Dad ya sanar dashi yanda sukayi da Affa,kai tsaye sashen shi ya nufa ƙwance kan kujera ya samu Zainab Sam bata san ya shiga ba, ya tsaya kanta sai faman hawaye take zubarwa tausayinta ne ya ɗarsu a ranshi,a hankali ya ajiye kular sannan ya isa gurinta ya tsugunna ya ce Zee a cikin taushin murya, da kiranta ta juyo ta dubeshi, shima ya dubeta suka yi wa juna murmushi.


"Haba Zainab menene haka? Kina son ki ganni cikin tashin hankali ne? Ta fashe da kuka, Dady dubi fa da wayewar gari har ka tafi gurin wata kayo break,ba abin da ke ɓata min rai ace ko one week ba'ayi da auranmu ba har zakayi wani Please ka duba fa." Shiru Dady ya yi jin tatsuniyar ta a ranshi ya ce in ma kina tunanin zan fasa gara kin bari, amma a fili sai ya ce hakanan ki zauna kina kuka ƙila ma baki karya ba, hannunshi yasa ya share mata hawaye ya miƙe ina zuwa ya ce mata sannan ya nufi kitchen ya ɗauko plate waina ya zuba mata a baki yake bata tana zuba shagwaɓa ta ce ya yi mata wanka, ya ce to yanda kika ce ai haka za'ayi soyayya aka tsaya yi a bayin kafin daga bisani ya yi mata wankan sannan shima ya yi.


    ***     ***      ***


Su Affa sun tarbi su Dad hannu biyu shagon gidan maƙwafcin Affa nan suka shiga tarihi ne ya maimaita kan shi wato inda aka taɓa karɓar sadakin na Ruƙayya yau ma gasu nan. Bayan gaishe-gaishe sai kuma ban haƙuri ya biyo baya inda Dad yake ƙara ba Affa haƙuri game da FIN ƘARFIN da aka mishi ya nuna cewa ba laifin shi bane laifin Alhaji Jega ne, yanzu haka sun daɗe da yin hannun riga da Jegan sakamakon cutar da ya yi mishi har ta Naira miliyan talatin da biyar ya cigaba da cewa filin nan na farko da na soma amsa gurin mahaifinku gwamnati ta bani,to sun saidashi miliyan arba'in da biyar. Sai ya kawo min miliyan goma wai haka aka saida, yanzun ma nakun ma na maida muku kayan ku,zamu sa lokaci muje in maida muku abin ku cikin bainar jama'a.


Affa ya ce dama ka barshi Alhaji." Dad ya ce "a'a aiko da, ɗin bansan cewa FIN ƘARFI ya yi maku ba, wallahi da bazan shiga abin ba.


Sannan suka koma ga batun yara inda Dad ke cewa Malam Sani Allah dai ya rubuta Ruƙayya dai My Son shine mijinta, Affa ya ce komai ai na Allah ne, abokin Dad ya ce tun ran gini ran zane inji masu hikima, abokan Affa biyu suka ce haka ne.


Dad ya ce sai muje batun sadaki ko? Affa ya ce Naira dubu goma shi ne sadakin dana yanke mata. Dad ya dubi abokinshi ya ce kaji fa Alhaji Bukar lau ƴa ce fa sukutum wai dubu goma, sukayi ƴar dariya sannan Affa ya ce ƙarancin sadaki shine mafi albarka Dad ya ce hakane sai dai har ga Allah naji babu yawa kace dai Allah ya sanya alkhairi kawai muke so,ai naji daɗi sosai ko batun aikin ta dama mu ma muna buƙatar lauya a campanyn Dady ɗin nan Kaduna da na Abuja shi kenan riba biyu, suka yi dariya, Affa ya ce haka ne gida bai ƙoshi ba ai ba'a kaima wasu ba, suka ce hakane.


Dad ya ce to batun rana fa yaushe ne ɗaurin auren? Affa ya ce wannan kuma Yusufa ne mai ajewa dama haka na sanar dashi, Dad ya ce bari na kirashi, daidai lokacin Dady yana ƙwance kan doguwar kujera Zainab tana zaune kan kafet amma ta jingina da jikin kujerar da Dady ke kai,kanta ma yana gefen ƙirjin Dady remote ne a hannunta ta kamo wata channel da ake film ɗin batsa, Dady ya ce No canza mana banason wannan channel ɗin ta ce "haba My dear daga ni sai kai fa,ka bari mu kalla." Ya ce a'a bana cikin masu kallon haramun, wannan haramun ne mutum ya kalli tsiraicin wani, don haka kamo min MBC Action ta soma searching cikin zunɓura baki, wayarshi ta soma ruri,da sauri ya ɗauka don yaji ringing ɗin daya sama Dad ɗin shi ne, ya ce Hello Dad,nan gefen kuma Dad ya ce yauwa munzo da yaushe kake son a ɗaura auran? Dady ya ce Dad wannan Saturday ɗin nake so." Dad ya ce My Son bazaka bari sai week na sama ba? Sannan an buga I.V, Dady ya ce ai Dad bar zancen I.V ko ana gobe za'a ɗaura aure muna da masu buga cart,bana son na kuma rasata ya ɗan kalli sashen da Zainab take, sai ya miƙe ya fita yana cewa Dad kaji? Ya ce shikenan.


Take a nan Dady ya yi sujjada yana mai godiya ga Allah gefen su Momy ya shiga dan sanar da ita, itama tayi farin ciki tare da yi mishi nasiha game da mata biyu, sannan ta ce Ruƙayyan yanzun ta sani? Ya ce a'a bata sani ba zan dai je gidan su a bani number ɗin ta da kuma adireshin gurin da take, Momy ta ce kai Babana burin ya cika, ya ce Momy ai Allah baya bacci, zuwa na hajji sau uku banda Ruƙayya babu abinda nike roƙa gurin Ubangiji sai gashi ya amsa min ya bani ita a lokacin da na soma ɗebe tsammanin samunta, wata ƴar ƙwalla ta taru mishi gefen ido, Momy tausayin ɗan nata ya kamata don haka yana fita alwala ta ɗaura don nuna godiyar ta gurin Ubangiji ta kuma roƙa mishi zaman lafiya, Allah ya kuma kare shi. Shirye-shiryen biki ya kan kama,ana jibi ɗaurin aure abokan Dady da abokan kasuwancin shi dake ƙasashe daban-daban suka soma zuwa, waɗanda basu sami zuwa wancan ba, wasu kuma sai mamaki suke yi me yasa Dady aure biyu? Ya dawo daga masaukin baƙi inda ya sauke su a Darba Hotel. Bayan ganin sun samu komai ya nufi gida yau kam sai ya ji muryar Pretty.


Sai da ya yi shirin bacci sannan ya soma neman layin ta, lokacin tana tsaka da karatun wani Nobel don ɗebe mata kewar damuwar da take ciki ta rasa kullum cikin faɗuwar gaba take a ƴan ƙwanakinnan Nuri ya kan ce mata ta yawaita addu'a sai tace ita dai tana ganin gida kamar ba lafiya. Ta kira su Murja da Fati duk sun ce mata kowa lafiya,to me yasa ranta be mata daɗi?.


Wayarta ta soma ringing takai hannu ta ɗauka,baƙuwar lamba ta gani mamaki ya kamata,dan ba kowa yasan ta da waya ba, ta ɗauka tare da faɗin.


"Salamu alaikum."


Ya Salam! Ita ce kalmar da Dady yaso furtawa ta ce wa yake magana? Ya ce Dady ne Pretty,nan da nan gabanta ya faɗi tayi shiru ta kasa magana, ya ce kinyi murna da jina? Wani irin baƙin ciki taji da ta tuna wai Dadynta. Daya ganta ya yi banza da ita? Dady da ya karya alƙawarinta? Dadyn da yazo har gidan su don gaya mata auran shi? Sai taja tsaki ta kashe, ya kuma kira taƙi ɗauka ya yi ya gaji amma bai daina ba,da ta gaji sai ta kashe wayar gaba ɗaya.


Washegari jajibarin ɗaurin aure duk su Amina sun hallara don yin aiki da wayar Fati Affa ya yi amfani ya kira Ruƙayya, cikin faɗuwar gaba ta ɗauka jin muryar Affa duk sai tsoro ya kamata, shi kenan Umma ta rasu, haka ta raya a zuciyarta, ya ce Ruƙayya ko zaki iya zuwa gida sai ki koma ranar Lahadi." Nan take tace waya rasu Affa? Ya ce a'a babu wanda ya rasu,ko gobe ma zaki iya zuwa, kada ki damu ba wani abu bane.


Sam bata cikin haiyacin ta gani take an É“oye mata ne babu wanda bata kira ba cikin Yayyanta amma duk sun ce ba komai kuma basu san kiran da Affa yake mata ba,kona menene?.


Nuraddeen ta kira take sanar dashi abin da yake faruwa, yazo gurinta suna tattauna maganar ya ce ta ƙwantar da hankalinta insha Allahu babu komai, kuma ta bar tafiyar sai gobe, tun da yau lokaci ya ƙure,


***      ****        ****


Tun Asubahi tana cikin motar mocopolo duk ta ƙosa ta ganta gida dan jin meke faruwa?.


Wayewar garin wato ranar ɗaurin aure ai kada kuso kuga ango wanda dama ƙwana ya yi bai runtsa ba,nafilfili yake yi yana roƙon Allah kar ya kawo sanadin fasa auran. Da safen ne yana fitowa wanka.


Zainab ta kirashi inda take mishi ƙorafin rashin kiranta tunda ta dawo, har ga Allah shi yama manta da wata Zainab baya tuna komai sai Pretty ɗin shi. Ya ce "Kiyi haƙuri abubuwa sun min yawa yasu Hajiya?" Ta ce lafiya,dama ina son kuɗi ne. Ya ce me zakiyi dasu ne? Bana baki dubu hamsin da zaki tafi ba? Ta ce To ai anayin kayan faɗar kishiya kuma ba kai min ba, ya ce aiko ita ma Pretty ɗin ba riga na mata kayan ba tukunna, ta ce to nidai kuɗin zaka bani, ya ce,zan turo miki, ta ce nawa? Abin ya soma bashi haushi ya ce yanda naga dama ya kashe wayar,shi fa haushin ta yake ji itace dai bata sani ba.


Yana gama shiri gurin abokanshi ya nufa can ya yi break. Hira suke suna ta shaƙiyancin su, yayin da gidan su Momy ya ɗinke da jama'a wannan karon har da Hafsi tazo da yaranta guda biyu daga Kalaba inda mijinta yake aiki. Aure kawai za'a ɗaura amma an cika fiye da wancan satin.


Dady kuwa yasaka kaya sun kai kala goma Yana cirewa sai yaga basu dace da É—aurin auren ba, duk da kasancewar kayan sababbi ne. Duk yasa aka siyo su daga Togo aka kaisu É—inki.


A ƙarshe ya haƙura cikin wata shegiyar mai masifar ƙyau, green dark hular dama tare aka kawo su,yana fitowa sai da ya birge abokanshi gurin Momy ya shiga tana cikin ƙawayenta babu wanda Dady bai birge ba, Momy kam Babu wanda ya kai ta farin ciki wannan rana, ɗan ta ya samu abin da yafi so.


Hatta motar da Dady ya hau wannan rana sabuwa ce mai shegen tsada,so kam abokanshi kayan su iri ɗaya suka sa wani farin yadi mai shegen tsada suka ɗinka gaba ɗayansu abin birgewa har da waɗanda ba baƙaƙen fata ba wasu turawa. Su Sadiƙ ne suka ɗinka duk wanda yazo indai aboki ne sai a bashi yasa. Unguwar Kabala ta ɗinke da jama'a tamkar taron idi. Tun daga farkon layin har ƙarshe dole ne sai anyi amfani da lasifiƙa wurin ɗaurin auren.



      ****      ****     ****


Ruƙayya da yake tasowar ƙarfe huɗun Asubahi suka yi kuma motar tayi shegen gudu, huɗu saura suka sauka. Mashin ta hau zuwa Kabala suna kusanto unguwar tasu gabanta ya na ƙara faɗuwa. Sanye take da wani leshi purple ba wata ƙwalliya da tayi amma hakan birge wasu take. Sun ratsa layin nasu cike da jama'a tayi mamaki yau ba juma'a ba wannan ma an watse.


Lungunsu ta sauka ta sallami mai mashin yanda taga mutane suna kallonta sai ta ƙara tsinkewa, tana shiga gidansu taga matan maƙwafta da Yayyanta ai sai ta saki jakar hannunta tana kuma duban ɗakin Affa an ɗaga labule ga dangin babanta maza na Katsina. Yaya Murja ta ce "Oyoyo ga Ruƙayya." Sauran suka fito sun kula a firgice take, ta ce "ina Umma?" Suka ce gata nan a ɗakinta, ta faɗa ɗakin ga mamakin ta sai taga Umma zaune tasha ƙwalliya sai tayi ajiyar zuciya hankalinta ya ɗan ƙwanta ta ce "Wayyo har naji daɗi wallahi nasha ke ce babu a firgice nazo garin nan, wai meke faruwa ne? Yayyanta da suka zagaye da ita suka ce zakiji gurin Affa da ya dawo ba mutuwa bace,sai taji koma menene da sauƙi.


Bayan ta ci abinci sama-sama tayi wanka bata kai ga shafa mai ba, Yaya Murja ta ce Affa nason ganinta, hijabi ta saka kan zaninta iya ƙirji tayi ɗakin Umma yanzu duk maƙwafta sun tafi sai Yayyanta,ta zauna ta gaida Affa ya amsa cike da murna shima yasha ado, ya ce Ruƙayya nasan cewa ke kullum mai biyayya ce ina matuƙar alfahari dake. Shiyasa a yau na ɗaura miki aure ba tare da na nemi izni ko yardar ki ba. Nasan ba zaki bani kunya ba, kanta a ƙasa dama tunda taga ba mutuwa ba ce tasan dai baya wuce haka.


Gabanta yana faÉ—uwa ranta yana raya mata shikenan sun bar juna da Dady. Amma sai taji gara da hakan tunda ita ta kasa sauraron kowa.


Ta ɗago idonta yana ɗigar da hawaye ta ce Affa nagode Allah yasa hakan shine mafi alkhairi,ba zanƙi zaɓin ka ba." Affa ya ce nagode Ruƙayya amma ban ji kin tambaya wanene mijin ba? Ta ce ai Affa ba sai na tambaya ko wanene ba, tunda dai yayi maka nima yayi min." Affa ya faɗaɗa fara'arshi ya ce To albishirin ki. Ta ɗago tana dubanshi bata ce komai ba ya cigaba.


Dadynki wato Yusufa Allah ya yarda shine dai mijinki." Ido ta tsura ma Affa tana tunanin ko mafarki ne...... Shin ba wancan satin taji yana sanar da Affa auranshi ba? Shine ya ganta ya yi banza da ita shine ya karya alƙawarin ta da har yanzu ita tana tare da alƙawarinsu.


Ta dubi zoben hannunta ta girgiza. Affa ban son Dady,da ne na soshi yanzun bazan iya auran shi ba ka zaɓa min wani cikin kuka rurus take maganar.


Affa ya saki baki yana kallon ta,a zaton shi daya faɗa zata hau murna amma sai yaga akasin hakan,. Ya ce "Kina son shi Ruƙayya da,nine na hana a yanzun kada ki damu na yarda nine ma na fara amince mishi. Na ce Affa duk abinda Dad ɗin shi ya yi maka? Ni dai bana son shi, Affa ya ce Kiyi haƙuri Ruƙayya lokaci ya riga ya ƙure,an riga an ɗaura aure,kije nasan insha Allahu ba zakiyi kuka da Dady ba. Ki riƙe shi zaɓina kiyi biyayyar nan dai da kika sa ba."


Ta ce "To nagode Affa." Ta tashi kuka sosai take yi su Yayyanta sun sha mamakin wai Ruƙayya ke kukan bata son Dady. Murja ta ce me yayi miki? Ta ce cikin kuka "babu ni dai bana son shi,ko da ɗin ma dan dai bansan ciwon kaina bane." Su Yaya Sadiya da Yaya Suwaiba tashi suka yi daga gurinta suka ce kar ta soshi shegiya. Amina kuwa dama Dady tai ma waya cewar Ruƙayya tana isowa, ta kirashi ta sanar dashi a waya, haka kuwa tayi yanzu sai ga wayarshi yana sanar da ita gasu nan shi da wasu Abokanshi ya ce kice mata tayi ƙyau dan Abokaina sun matsu su ga wacece wannan ta haukatar musu da gentleman ɗin su? Amina ta yi dariya ta ce "To ƙanina."


Da farko cewa tayi ba zata ba sai da Umma tai mata tatas ta ce ta zauna ɗin,ai mu bamu isa da ita ba sannan fa su Murja suka lallaɓa ta suka gyara ta sosai wani jan leshi suka zaɓo mata cikin kayan ta dan ba'a riga an kawo lefe ba,farin takalmi da gyale suka bata ta fita tana zunɓura baki.


Sun kai su ashirin abokanshi suna sanye da cikin anko na ɗaurin aure,nan taja gyale ta rufe fuskarta. Shi kam Dady wani ƙwarjininta ya ji matuƙa sai yaji yana jin shakkar ta, Sadiƙ ya ce "baki isa ba ai ki buɗe mana fuska mu ganki." Dady kam kasa magana ya yi ya jingina da bango yana kallonta.


Ta buɗe fuska ta ce "Ina wunin ku." Suka amsa suna ta yi mata tsiya ta rikita musu aboki. Ta ƙi magana sai murmushin dole take yi saboda kada ta bada shi,ta ɗan dubeshi ta ɗan ranƙwafa ta ce ina yini? Kamar an sashi cikin aljanna ya ce lafiya lau Pretty na suna ta damun ki ko? Ta ɗan haɗe hannayenta guri guda ta ce ba komai. Abokansa suka ce to sai mun haɗu gurin dinner ta dubeshi yanzun za'ayi dinner ba zaku bari sai lokacin tarewa ba? Suka ce a'a wannan wasu ne suka shirya muku, ta ce To Allah ya kaimu anjiman. Suka tafi suna yaba tsarin yarinyar har sha'awar tarbiyyarta, wasu ko cewa suke kaga wai lafiyayyen jiki? Dole Son Guy ya ruɗe.


Bayan sun tafi ya rage shi da ita ya miƙe yana duban fuskarta. Ta ci magani tamkar ba ita ba, Ya ce Pretty na gashi dai Allah ya......" Ta ɗago idanun nan nata waɗanda suke matuƙar birgeshi, ta ɓalla mishi harara,nan take ya yi shiru ta ce "Dady manyan ƙasa,nifa yanzun ba Ruƙayyan da bace da ka sani, yanzun wannan babu Dady a ranta kamar yanda ya manta da ita, kada kaga cewa Affa ya cusa maka ni,ka ɗauka ina son ka har yanzu? Ya yi murmushi ya ce Pretty kenan,ai ni burina in aure ki,ko ki soni ko ki ƙini Pretty ni mijinki ne nasan kuma ina sonki. Ko? Ta dube shi kamar gaske ya ce da wasa ne?"


Ta ɗan yi murmushin takaici sannan ta ce wannan damuwarka ce nidai bana sonka." Da sauri ya dubeta ta ce Yes,da na soka lokacin bansan menene so ba bansan ƙwalitis ɗin maza ba, yanzun na gane kai ba irin wanda nike so bane." Ido ya tsura mata, maganar ta ta taɓa shi sosai yasa hannu ya shafi fuskarshi sannan ya fesar da wani zazzafan huci, ya dubeta yanzu ya ya zakiyi dani? cikin sanyin murya ya yi maganar. Ta ce "inka gaji ka sake ni ba."


Ya yi murmushi ki sake sabon tunani, domin babu saki cikin auranmu. Ya take yazo gabanta yasa hannunshi ya ɗago fuskarta dube ni nan Pretty ya kausasa murya,sau uku a jere ina zuwa ƙasa mai tsarki ina rungumi ka'aba ɗakin Allah ina hawaye ina Allah ka bani Ruƙayya, Ruƙayya, Ruƙayya nake faɗi, sannan ya bani inyi wasa dake? Sorry ai mutu ka raba ni dake Pretty zan koma wannan shekarar ni dake inyi ɗawafi in kuma rungume ka'aba in gode ma Allah."


Ya saki fuskata ki shirya da ƙyau Sabi'u zai kawo miki kayan da zakiyi amfani dasu gurin dinner ina son a haska min ke yau gidajen T.V na duniya su san nine mijin." Ya juya ya tafi ta ɗaga murya.


"Ba inda zan je don kaji."bai ko juyo ba ya tafi ranshi na suya wai shi Pretty ta ce bata so. Gudun kada abokanshi su gane yasa ya saki jikinshi tamkar baya cikin damuwa.


Ta nufi gida rai ɓace, Yaya Murja ta ce "Haka ki kaje musu turɓunɓun ba ƙyan gani? Fati ta ce ai Ruƙayya har ma da iskanci ke in Dady bai ƙiki ba ai ko bazaki gujeshi ba duk da yana namiji yafi ki komai, ta ce ni ina ruwana da ƙyan shi Ni bana son shi. Amina ta ce munafuka bari ta shige gidan shiru zakuji ta." Ta ce Allah ya kiyaye,nan dai sukayi ta tsokanar ta.


An dawo sallar magriba Affa ya ce kai kowa ta tafi gidanta, Ruƙayya ta soma musu dariya. Suka ce kema ai tazo kanki yarinya." Ta ce "eh dai ai ba yau ba." Dady ya kira Amina........



🖊️🖊️🖊️

[8/13, 08:28] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 5



Ya ce ga direba nan da saƙo, don Allah dinner anjima ya kira su Murja da Fati ya ce su gyara mishi ita,gurin Amina ya amshi lambobinsu. Nan suka kira mazajen su suka ce zasu dinner tamkar haɗin baki kowa ya ce zai zo ya kai matarsa. Wani shegen leshi ne mara nauyi da kuma takalmi da jaka sai gyale ashe ba kayan tafiyar bane, sai da ƴan'uwan suka matsa mata ta shirya. Sabi'u ne ya ɗauke ta su kuma mazajensu ne suka ɗauke su sai gurin dinner wadda aka shirya ta a command sai ka nuna kati.


Sabi'u ya kawo musu katin amma amarya gidan Momy ta ga an nufa da ita duk da cewa dare ne ta gane layin, ta ce da direba yaya kayo nan da ni? Ya ce haka aka ce min." Tayi shiru ta bishi da ido.


        ***      ***       ***


Gidan su Dady tamkar yau ne bikin farko ganin jama'a ta rufe fuska, tana zaune cikin mota. Sabi'u ya kira Ƴallaɓai, ya gata nan, takaici ya cika Ruƙayya. Dady yazo Sabi'u ya fito ya buɗe motar ya shiga jikinshi sanye da suit baƙaƙe. Duk ta cikin gyale take kallonshi ya yi matuƙar ƙyau, fuskarshi babu walwala ya ce "kin iso Prettyna? Yanzun zaki shiga Momy ta shirya ki." Ta dube shi baki buɗe.


"Bana shirya ba." Ya ce bazaki gane ba,zo muje ya jawo hannunta ta fisge, ta ce nifa bazan shiga ba, ya ce to shikenan ya ciro waya ya kira Momy ya ce "kizo ki fito da ita Momy wai kunya take ji." Ta harareshi na ce maka? Sai ko ga Momy har ma da wasu aminanta waɗanda suka ƙoshi.


Ruƙayya mai sa'a tunda yawanci sun so ya auri ƴaƴansu ya ƙi.


Cikin farin ciki Momy ta fito da Ruƙayya ta rungume ta suka yi cikin gida,sai ɓoye fuskarta take yi, wani ɗaki aka kaita wasu mata suka soma shiryata cikin kayan aure irin na arna, ranta ya ɓaci sam bazata iya shiga jama'a da wannan kayan ba, sai da suka kira Momy sannan ta ce Kiyi haƙuri ƴan awoyi ne. Wasu ne suka shirya muku kin ji? Haka ta haƙura aka sa mata riga doguwa mara hannu sai safar hannu tare da na kai shine ma ya rufe kafaɗun ta dogon farin takalmi suka fente mata fuska tare da gyara mata gashi.


Da ta dubi madubi sai da gabanta ya faɗi bata san ita ɗin ba ce ba ita bace. Momy da ƙawayenta sun yaba da ƙyaun da tayi, shi ko Dady sai ya ji tamkar ya ce a fasa zuwa don kar mutane su gane mishi mata. Suka shiga bayan mota aka ja su yayin da sauran motocin suke take musu baya fuskarta babu walwala ta ɗan kallo gefenshi ta ce ai wannan ɗabi'un arna ne, ya ce inji wa kice dai ba al'adar Hausawa ba ce ko larabawa suna sawa,nima ba son raina bane wasu Abokaina ne suka shirya mana har kayan sune suka kawo ta taɓe baki.


Gurin tamƙam sanda suka iso, suna fitowa haske kawai kake gani hotuna ko ta ina, gidajen T.V da masu ɗauka cikin waya. Hannu ya riƙe mata suna tafiya har kujerar da aka tanadar musu, guda ɗaya ce mai ɗan faɗi, suka zauna matsi juna mutane na ƙasa su suna sama P square ne suke waƙa a gurin anyi raye-raye. Kuɗi ake zubawa kamar ƙasa in anzo rawa Dady sai ya janyo ta jikinshi sannan suke rawar.


Haka gurin ya kasance,keck sai da ya ƙwanto da ita a kafaɗunshi sannan yasa mata a baki, haka da zai bata juice wai don mai gabatarwa ya ce ya nuna zai ci da ita, ita kam ɗan russunawa tayi da zata bashi dan bazata iya wannan abin ba, haka da za'a yi musu hoto gaban keck ɗin rungume ta ya yi tsaf. Suka koma suka zauna sannan aka soma ciye-ciye ta tuna da aminanta Armaya'u da M Bash tasan zasu yi fushi da ita in suka ji wai tayi aure duk da ita ma batasan da auran ba.


       ***       ***      ***

Ɗaya saura aka tashi tana son taga ƴan'uwanta ina, waɗannan ai sun yi bacci ma a gidajensu, tunda suka ga abin bana ƙare bane suka tafi. Mun fito muna shiga mota ya dubeni da murmushi na ce "Allah ɗazun dan naga mutane ne shiyasa har na bada kai, ya ce na dai gode.


A gidan su Momy ban zauna ba kaya na canza na ce ni gida zanje Momy ta ce na ƙwana,na ce a'a dole Dady da wasu Abokanshi suka kaini. Sai da suka buga gida sannan aka buɗe musu ina ji Affa ya ce "lafiya cikin daren nan?" Suka ce Ruƙayya muka rako. Affa ya ce "Shirmen banza can ɗin baƙon guri ne da bata ƙwana?" Dady ya ce Momy tayi ta yi taƙi yarda.


Ita dai ta shige sai ɗaki ta cire kaya tasa rigar bacci doguwa ta kitse gashinta kitso ɗaya,ta faɗa gado. Komai haka yake dawo mata tamkar yanzun yake faruwa,ita ce ƙwance a jikin Dady wai mijinta? Ta mirgina ta rungume filo har Yanzun ƙamshin turaren Dady jikinta keyi,ƙamshin da shi kaɗai ta sani dashi tana son Dady shima tasan yanzun yana can yana tunaninta.


Wata zuciyar ta ce kodai yana can tare da matarshi, gabanta ya faɗi haka nema,yana can tare da matarshi yana gaya mata daɗaɗan kalamai,kishi ya turnuƙe ta, Dady yaci amanar son da yake mata, can ta tashi ta ɗauko wayarta bari ta kira wani yaji yanda ake ciki.


Tayi ringing sau biyu yana yankewa ana uku ya ɗauka cikin yanayin bacci yake magana...... Prettyna lafiya na neme ki ban same ki ba? Ta ce kai dai bari wai kasan menene? Ya ce a'a, ta ce aure.........bata ƙarasa ba taji ɗif ta gurin shi ashe shi da chaji ne,ta neme shi ta gaji.


Zuwa can wayar ta soma ringing a zaton ta Nuraddeen ne don haka ko number bata tsaya dubawa ba ta ɗauka tace Nuri kana jina? Gaban Dady ya faɗi, ya ce Pretty wanene Nuri? Itama gabanta ya faɗi ta ce kai mai maganar wanene? Ya ce ki dai yi hankali yanzu ke matar aure ce, shiyasa nike ta neman number ɗin ki ana ce min Number busy ashe kina ta hira da wani ƙato ko? Ta ce kaima kayi da matar ka kada ka dameni, ya ce ki iya da harshen ki kuma ni ina da izinin hira da matata amma ke baki da wannan damar ki kiyaye ina da kishi bana wasa ba. Ya kashe wayar ya jefar da ita can gefe yarinyar nan fa yaga kamar bata son shi da gaske,kai ko bata son shi zai zauna da ita koda zata rinƙa yankar naman jikinshi kullum. Alwala ya yi ya soma gayawa Allah.


Saɓanin ita data shiga kuka rurus wai ita Dady yake gaya ma yana da damar hira da wata mata? To zata nuna mishi mata suna suka tara.


          ***     ***     ***


Da safe sai ga Sabi'u niƙi-niƙi da kayan tea, Ruƙayya suna zaune ɗakin Umma har da Affa ta ce Affa yau zan koma tunda yau Lahadi, gobe ina da aiki." Ya ce "wannan ke da mijinki,ni menene nawa?,ni da zai zo ma yau ki tare gidan shi ai da yafi min." Na ce "Affa ai min agaji in ƙarasa." Ya ce "To ai yarda da haƙuri yana gurin mijin naki ko? Ta ce"shikenan."


Misalin ƙarfe sha ɗaya ta gama kimtsawa ta ce bari inje gidan Amina. Umma ta ce kin sanar da mijinki? Babu ruwa na fa. Ran Ruƙayya ya ɓaci ta koma ɗaki ita dai bazata kirashi ta tambaye shi ba sai dai kar da taje.


Sallamarshi ce ta katse tunani. Umma ta amsa,ta jiyo shi yana gaisawa da Umma, ya ce Affa ya fita ne? Ta ce eh,ya fita. Ai Ruƙayya tana nan cikin ɗakin ta, ya ce to, tana zaune bakin gado ya shigo message take tura ma Nuraddeen tana sanar dashi abin ya faru gareta. Ya shigo da sallama ciki-ciki ta amsa, kamar ta share shi ta dai ce ina ƙwana? Ba tare da ta dubeshi ba, ya ce ban ganshi ba,ta ɗan ɗago ido ta dube shi sanye yake cikin jeans blue da farar t.shirt,ta ɗan kama shi ya yi ƙyau sosai ya fito a Son Guy ɗin shi. Ta ce waye baka gani ba? Ya ce ƙwanan da kike tambaya, ta ɗan taɓe baki ya ce bana son taɓa bakinnan in kika ƙara zanyi maganin ki.


Umma ta zo daidai ƙofar ɗakin ta ce Ruƙayya bari in shiga nan gidan mai ɗanwake." Ta ce Umma kada ki daɗe zan fita ne." Dady ya ce "ina zaki ne." Ta ce sai kaji? Ya yi ɗan murmushi mai sauti ya ce to ai dai sai na yarda sannan za'a ko? Ta yi shiru ya taso ya dawo bakin gadon, ta matsa ya ce Pretty ni kike gudu? Kar dai ki manta ni mijinki ne, ta ɗan taɓe baki, bata ankara ba taji ya kamo leɓunanta ya manna mata kiss, tayi saurin duƙar da kanta yana ta dariya tayi banza dashi.


Wayarta ta soma ringing ta sa hannu ta ɗauka Nuraddeen ne cikin fara'a ta ce "Nuri kaga text ɗina? Ya ce eh, Mustapha yazo yana ce min yaga amarya." Na ce wallahi auren dole akai min, ban san mutumin ba ai kaga kiran da aka yi min ko? Ya ce eh, ta ce To ina isowa har an ɗaura." Ya ce Allah ya yi shine mijinki sai kiyi biyayya." Ta ce nagode, ya ce yaushe zaki shigo Legos? Ta ce nan da anjima ma zan taso, ya ce to sai kin shigo. Dady dake zaune yana jinsu ya ce "mu ga wayar?" Ta ce ina ruwanka da waya ta, ya ce ki bani ko na ƙwata. Ta tura cikin bireziya, ya ce ciro ki bani tayi banza dashi, ya haɗa hannuwanta guri ɗaya, ta ce zan maka ihu ya ce Kiyi mana ya tura hannu cikin rigar ta ya ciro wayar ya tura cikin aljihun shi. Sannan ya ce ba batun tafiya yau sai gobe,in ma mutum ya yi mini gardama in hana komawar. Jin haka sai tayi shiru.


Sallama ta ji kamar muryar M Bash, da gudu ta fito tana oyoyo M Bash ɗina." Munira ta ce kada ki taɓa ni shegiya ina Kaduna ina Abuja har sai dai naga ana nuna bikin ki a T.V ai Mom ma tace tana fushi dake. Ta ce wayyo nima fa auran nan yanda ku kaji shi haka naji shi,zo dai mu shiga. Suna shiga Munira taga abokin mijinta ta ce ashe ma angon yana ciki,ai ban san kaine angon namu ba,sai da na gani ana nuna dinner a ɗin newline, Ruƙayya ta ce zauna ƙawata kina ta zuba, ta ce Armaya'u ta iso?


Ruƙayya ta ce "a'a itama tana hanya ne?" M Bash ta ce eh tana hanya jiya muka shiryo tafiyar ta kira ni da dare ta ce nasan ana bikin ki? Na ce mata na dai gani a Talabijin shine muka ce bari muji laifin me mukayi?" Dady ya ce Gaskiya bata ƙyauta ba kuma babu inda bata kai kati ba sai ku.


Ruƙayya ta harareshi sannan ta ce "ni fa ina Legos, Affa ya yi min waya wai inzo, hankali tashe nazo garin nan,jiya kamar yanzun muna hanya,wai ina zuwa na samu an ɗaura min aure da wanda ban ce ina so ba." Ta soma hawaye,M Bash ta ce "Ni fa nasha mamakin ace kinyi aure bamu ji ba." Dady ya ce "Munira ina angon naki wato shine bai zo min ɗaurin aure jiya ba?" Ta ce to ai yazo maka na wancan satin, ya ce to ni wannan na gayyace shi wancan ai a garin yake. Ruƙayya ta tsani ta tuna Dady yana da aure,duk sai taji ta tsane shi. Ta dubi Munira ta ce M Bash bari in kawo miki ruwa, Munira ta ce ina Umma? Umma ta shiga maƙota, ta fita dan kawo ma M Bash ɗin ruwa.


Dady ya ce "Munira nayi mamaki da Pretty ƙawarki ce." Munira ta ce "wai Ruƙayya Aminiya ta ce ta wuce ƙawa,B.U.K muka haɗu baka ganta gurin bikina ba?" Ya ce sam amma ta taɓa baki labari na? Ta ce kasan Ruƙayya da shegen zurfin ciki, koda wasa ko sunan ka bata taɓa kira ba." Ya ce labari na da ita aƙwai tsawo wata rana zata gaya miki." Ta ce shikenan ina kuma Zainab? Ya ce tana Abuja kin san halin ku na mata wai bazata tsaya ba ta tafi.


Ta ce abinne sati É—aya fa? Ya ce ke da kinsan son da nake ma Pretty a rashin ta ne fa na auri Zee wallahi."


RuÆ™ayya ta shigo da sallama ta ajiye goran ruwan swan water da lakaseera. Umma da Armaya'u suka shigo tara   RuÆ™ayya ta fito da murna ta ce lah Umma a ina kika samo mini Sadiya? M Bash ga Armaya'u, Armaya'u ta ce ashe ta riga ni,É—akin ta shiga itama ta ce ashe angon namu yana ciki? RuÆ™ayya ta taÉ“a baki, ya ce bakinki baya jin horo ko zan gyara mishi zama. Suka yi dariya ban da RuÆ™ayya.


Sun gaisa da Armaya'u take tambayar shi Zainab, ya ce tana Abuja Armaya'u ta ce lallai kaji daɗi mai mata biyu cikin sati ɗaya. Ruƙayya ta yi waje, ya ce ku daina fada naga kamar Pretty batason ana labarin Zee. Suka sa mishi dariya, ya miƙe daidai sanda Ruƙayya ta dawo ɗakin. Pretty zan tafi na barki da baƙin ki,bata tanka ba ta wuce ta zauna Armaya'u ta ce "Ruƙy ana miki magana." Ta ce me zan ce mishi na riƙe shi ne? M Bash ta ce ke dai Allah ya yi ƴar iska." Ya ce kuna nan ne? Suka ce gobe zamu tafi, ya ce Ok,zan shigo zuwa dare. Ruƙayya ta ce baka bani wayata ba, ya tafi yana faɗin da kin ƙwata ai.


Yana tafiya suka hauta da masifa ta ce ba fa sonshi nike yi ba don ma na barshi ya zauna ne shi ne harda ce min zai tafi, Armaya'u ta ce munafuka daga ganin yanda kike mai wannan kallon Æ™asa-Æ™asan kin sonshi,ai wannan gayen baya cikin mazan da za'a gani ace ba'a so. M Bash ta ce Æ´ar iska tana sonshi RuÆ™y munafuka ce kin santa sumumi sumumi da ita. RuÆ™ayya ta ce "ko yana burge wasu banda ni yana da fa mata gaskiya bana son kishiya,auren dole ga kishiya? Ba zan iya ba." Har suna haÉ—a baki "Kada ki iya." M Bash ta ce dama yanzun ya ce mu daina maganar Zainab ba Æ™ya so." Ta ce mukayi dashi? Armaya'u ta ce ke kishiya ce zata baki tsoro? Gara ma ki tashi ki riÆ™e mijinki" M Bash ta ce ballantana Zainab,ni ranar da su Mom da Æ™awatar suke labarinta da Mamanta duk saina raina  mata wayo. RuÆ™ayya ta ce wacece Zainab ki bani labarin ta mana?" M Bash ta ce "Zainab Adam mahaifinta ministane haifaffen Sokoto, uwar ta Æ´ar Gombe ce ni ko bafullatana ce a Yoben Oho,bata da mutunci matanshi uku ance duk sai da ta koresu, harda matarshi ta farko wacce sukayi auren saurayi da budurwa, Æ´aÆ´an ta biyu duk mata Zainab sai Æ™anwar ta Jamila, sauran kishiyoyin data kora sune masu yara maza.


Ance tana ji da Zainab sai dai babu tarbiyya, tamkar karuwa haka Zainab ta rinƙa bin maza, Uban dama an gama dashi, shegen son kuɗi ne da uwar harma ƴar in gaya miki shine aka yi rufa-rufa aka bawa mijinki.


Ruƙayya ta ce "na shiga uku banason kishi da mace mai shige-shige aje a sabauta ni a banza." Armaya'u ta ce ba sai ki nemi tsari gurin Allah ba,ga addu'o'i nan na tsari. Ruƙayya ta ce nidai an haɗani da aiki ina da kishi mai tsanani musamman akan Dady wallahi da ace be aure ba bazan damu ba.


M Bash ta ce "kamar ya ya?" Nan Ruƙayya ta basu labarin farkon haɗuwarta da Dady har zuwa yanda abubuwa suka kasance ta ɗaga yatsun hannunta,kunga zobunan alƙawuran da muka yi ma juna har sau biyu. Armaya'u ku kanku shaidu ne cewa bana kula kowa, amma ba tashi ganin Dady ba sai in ganshi da budurwa, M Bash in bazaku manta ba lokacin da muka je bikin Uncle ɗin ku ban dawo Kaduna da lafiya ba." M Bash ta ce ƙwarai har Mom tasa Dakta ya duba ki." Ta ce kin tuna to lokacin ne na ganshi da wannan Zainab ɗin haka ganina na biyu,dan na uku ma tsabar wulaƙanci ban ganshi ba sune suka ganni suka rage min hanya amma ƙala bai ce min ba har na sauka, shi ne don iko aka ɗaura min aure dashi.



        ***         ***         ***

Sun jinjina labarin data basu, sannan suka bata shawarar yanda zata zauna da mijinta. M Bash ta ce kada ki damu kin san kana naka tsarin Allah na nashi, Allah ya tsara ku biyun ne matanshi.


Armaya'u ta ce ban ma ga abin damuwa ba tun da tasan irin son da yake miki." Ruƙy ta ce ke rabamu da mazan nan munafukai ne yazo ya ce min I love You yaje ya ce mata I miss You." M Bash ta ce koma menene yanzu dai ki dage da shan kankana da aya da dabino,da ƴan kayan marmarin nan muna rainasu, aƙwai aiki zaki gane in kin kama su, kuma akwai wasu sinadarai da Mom ta bani na Arabic ne, Armaya'u ta ce nifa? M Bash ta ce a'a sai anyi bikinki zan baki, ta ce One month fa ya rage, ta ce to zan baki sai kin zo Abuja, Armaya'u ta ce zan zo amma kafin nan zan je in fara amfani dasu kankana ɗin, Ruƙayya ta ce kai ku rabu dani ya ma samu in tare gidan shi bare ma har na tsaya shan wani abu aje a ƙwararraɓa ni, dariya suka saka mata, M Bash ta ce yanzu duk kishi ne matsalar ki,kina shiga hannunshi shiru za'a ji ki tunda kina sonshi. Ruƙayya ta ce zaku sha mamaki aini bana son cin amana, kuma zan nuna mishi mu mata dabanne. M Bash ta ce ina son fita anjima mu ɗan shiga kasuwa.


Bayan sun ci sun sha girkin da Umma tai musu can gurin la'asar suka shirya zuwa kasuwa, Ruƙayya ta ce Umma zamu kasuwa, Umma ta ce ki ma mijinki waya ki sanar dashi, takaici ya cika Ruƙayya su Sadiya suka ce ki kirashi, ta ce ya tafi da wayar ai, Armaya'u ta kirashi da tawa, ta ce ai ban ma riƙe number ɗin shi ba,ke ni ban ma san me zance mishi ba." M Bash ta ce bari na kira number Al-Mustapha ya yi min text ɗin number Dadyn.


A wayar Armaya'u suka kira M Bash ta ce Ruƙy M gashi tana ringing ta amsa tana cewa me zan ce mishi? Ya ɗauka ya ce "Hello," ta yi shiru ya ce "who is speaking?" Ta ce Ni ce, duk da ciki-ciki ta yi maganar hakan be hanashi gane muryarta ba, ya ce Pretty ya ya ne? Ta ce kasuwa zamu je, tana wani ɗaure fuska tamkar tana ganinshi, ya ce to bari na turo muku direba, ta ce daka barshi zamu hau mashin.


Da sauri ya ce kada ki yarda ki hau mashin ki jira ni, ta kashe wayar ranta ɓace ta ce kunji ko ya samu na kira shi har da cewa kar na yarda na hau mashin wai mu jira shi. Armaya'u ta ce yana da gaskiya aje a yadda mishi mata, M Bash ta ce ƙyale ta da Allah da kanta zakiga ta ƙanƙame mijinta. Ruƙayya ta ce sai kuma kuyi,wayar Armaya'u ya kuma kira ya ce su fito, baya suka shiga.


Ruƙayya na ƙoƙarin shigowa bayan suka tura ta ta zauna gurin mijinta, dole ta zauna gaba tana wani zumɓura baki, ta ɗan saci kallon shi a ranta ta ce ya ci sunanshi Son Guy ko yaushe cikin gayu yake, yanzun ma jeans ne baƙi da baƙar riga mai dogon hannu ta ɗameshi, fuskarshi fes sai ƙyakƙyawan sajen da ya kewaye bakinshi zuwa gefen fuskarshi, idanunshi masu hasken nan suna birgeta.


Ya tada mota yana cewa "Wai ke kallon fa?" Gabanta ya faɗi ashe ya gane, ta dake ta ce "Me zan kalla a nan?" Ya yi murmushi sannan ya ɗan ɗaga murya ya ce wace kasuwar zamu? M Bash ta ce Ruƙy wace zamu je? Ta ce ka kaimu Abubakar Gumi, ya ce me zaki siya? Ta ce sune zasu yi siyayya, ya ce baki da kuɗi ne,in ga jakarki,ta ce a'a ni ba'a ganar min jaka,kai ka cika tsokana kayi abin da ke gabanka..........




🖊️🖊️🖊️

[8/16, 08:44] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 6



Ya ce "ai ni kece a gabana komai na Prettyna." Ta kuma shan mur.


Haka ya yi ta janta da magana tayi mai shiru har suka je kasuwa. Shagon wasu masu leshi da materials suka yada zango,ƴanmatane keta siyayya a shagon Dady yana daga ƙofar shagon yana duban Pretty ɗin shi suna taya M Bash zaɓe, duk abinda take yi baya gajiya da kallon ta, komai nata birgeshi yake yi.


Wasu ƴanmata da tun zuwansu gurin suka maida hankali kan Dady ya tafi da imaninsu,ɗayar ta ɗebi wasu lesuka guda biyu tazo gabanshi don Allah Malam muna musu ne wanne yafi ƙyau? Ya ce a'a ni ban san kayan mata ba, ga mata can ƴan uwanku. Sai cewa tayi to kai wanne yafi maka ƙyau? Nan take yasha kunu ya ce ban sani ba. Ya maida dubanshi ga Pretty ɗin shi suka haɗa ido ranta a ɓace a zatonta shi ya soma yi musu magana. Ya shiga falon kun gama? Yana magana yana kallonta ta juya mai kai.


M Bash ta ce ɗaya na ɗauka kayan su nada tsada, ya ce kema Sadiya ɗauki naki, shi kuma ya ɗauki biyu, ya haɗa ya biya suka sa musu a cikin ledoji, shagon wasu inyamurai suka shiga siyen jaka da takalmi ɗayan sai kallon Ruƙayya yake yi.


Dady yana kula dashi, Ruƙayya ta ce,a ɗauko mata ɗan mara tudu ya ce to Baby,su M Bash suka wuce wajen zaɓen jaka ya kawo mata takalmin ya ce "wannan zai dace dake kinada ƙyau fa." Ya tsugunna gabanta kamar zai kama ƙafarta yasa mata. Dady ya ce "tashi ki fito tashi." Ta dubeshi fuskarshi tamkar bai taɓa dariya ba ta miƙe ya ce Munira ku zo muje, suka ce bari in bashi kuɗin.


Ya tasa Pretty ɗin tashi a gaba suka nufi gurin mota,suma suka biyo su a mota sai masifa yake yi shi baya son irin wannan kasuwar, dubi kamar zasu taɓa mace ko baya nan be yarda ta kuma zuwa nan ba. A ranta ta ce ji irin ikon nashi, shi daya tsaya yana magana da ƴanmata amma ita daga gani yana kallonta ya ce su baro kasuwa. Wata super market ya tsaya suka shiga ya ce su ɗibi duk abinda suke so Ruƙayya dai bata yi yunƙurin ɗaukar komai ba tsayawa tayi tana kallon su, Dady ya wuce yana ɗiban abubuwa,sai da yayo leda huɗu aka haɗa aka gaya mishi kuɗin, ya biya duka da ya sauke su ya ce Pretty ga kayan nan, ta ce babu abin da zanyi dasu, ya aje ya ce ki barsu nan, ya figi mota ya yi gaba.


Munira da Armaya'u sai masifa suke yi mata, ta ce tunda ya yi muku siyayya ai dole ne ku dinga goyan bayan shi. M Bash ta ce shegen taurin kan kin nan ki rage shi yarinya da kishiya zaki zauna, tsaki ta ja sannan tayi gaba suka ce shegiya gara ma kinzo kin ƙwashe kayan ki,kishi na cinki,yara suka roƙo suka ƙwashe musu kayan.


     ***          ***          ***


Dare ya aiko Sabi'u ya gaya mata jirgin ƙare baƙwai zata hau zuwa Legos ta shirya da wuri. Tun dare suka yi sallama da aminanta, bayan sun raba dare suna hira, daga sallar asubahi kowa ya hau shiri ya bada mota Sabi'u ya kai Armaya'u tasha ya yin da Munira direbansu zai zo ya ɗauke ta.


A cikin mota ya dubeta,ko ta bashi haushi yana dubeta sai yaji ya huce, cikin sanyin murya ya ce ba gaisuwa Pretty? Ko ba'a sona na ci arziƙin aure ko?" Ta ina gajiya ya Momy? Ya yi ajiyar zuciya sannan Ya ce tace in gaida ki." Bata amsa ba ya ce ina tunanin sati mai zuwa in yazo zan sama miki gida ƙarami ki koma, ta ce ban ce ba,ka barni inda ka ganni, ya ce shikenan na barki, ta ce wayata fa? Ya ce gata,miƙo mata wata sabuwar waya mai shegen ƙyau ya yi, ta ce ni tawa nike so, ya ce tuni nayi ƙyauta da ita har layin ma zan ɗauki komai amma ban da waya da wasu ƙattai sannan ki kiyayi wani Nuri da naga yafi kowa kiranki, kuma inbox ɗin ki ba text ɗin kowa sai nashi in ya yi wasa ba zai ji da daɗi ba kin jini?"


Yanda yake maganar rai a ɓace shine ya hanata yi mishi tsiwa, sai da yaga komai ya kammala har sun soma shiga jirgi sannan ya tafi ita kam tunani take yi a ranta yau gata a jirgi. A can ma tana sauka sai ga wani yazo ya ce itace Ruƙayya? Ta ce Eh, ya ce yazo ne zai kaita gurin aikin su. Abokan service ɗin ta suna ta mata murnar aure dan da yawa sai da suka yi mata ƙorafin rashin gayyatar su, ta ce aure kawai aka ɗaura wannan dinner ma abokan mijin ne suka haɗa, Nuraddeen ne kaɗai ta zayyane ma komai.


Tana ta fama da waya, waya taƙi tayi sai dai wasu daga numbers daga nashi daga nashi daya sa mata ta Mom sai ta Yayyanta da ta Munira da Armaya'u,sai dai nasa number na kira amma ba dai na.


Haka suka ci gaba da gungurawa, kullum Dady zai kirata tana dakewa tana komai, zasu yi magana ko yayi tayi taƙi amsa mishi, amma duk ranar da be bar kira ba bata da sauran ƙwanciyar hankali har sai ya kira sannan zata samu natsuwa. Tuni ya koma Abuja bakin aikin shi ranar da ya koma ranar Zainab ta dawo, duk da irin soyayyar da yaga tana nuna mishi tare da ƙaramar hukumar maji daɗi da take gayyatar shi suna lulawa besa ya kasa gano ƙaramar ƙwasƙwarimar da aka yi mata ba kuma be sa ya manta da Pretty ɗin shi ba wani lokacin ma a gabanta ma zai ma Pretty ɗin waya.


Wata rana da dare misalin ƙarfe goma Ruƙayya ta kira shi don ta sanar dashi gobe zasu yi tafiya gaida wata abokiyar aikinsu a ibadan kuma tayi tunanin ta yi tafiyar ta kawai sai kuma ta tuna doguwar hanya zasu hau don haka sai ta kirashi.


Lokacin sun soma nisa a hanyar ƙaramar hukumar majidaɗi shi da Zainab, waya ta soma ringing cikin kasala ya ɗauka yasa a kunne Hello Pretty?" Yanda taji Muryar shi sai da gabanta ya faɗi ba ko shakka yana tare da Zainab. Ta daure ta ce dama zamu je ibadan ne. Zainab ko tana jin ya ce Pretty ta shiga aika mishi da saƙwanni waɗanda suka sa shi ya kasa magana sai yace zan kira ki anjima, yanda taji muryar shi ma ta isa tasan cewa sunje majidaɗi ne,in ranta ya yi dubu duk sun ɓaci tayi data sanin kiranshi yafi a ƙirga. Daya sani bai ɗauka ba zai fi mata takaicin wannan abun da taji,awa ɗaya tana kuka can wayar ta soma ringing number ɗin shi ne kamar kada ta ɗauka, sai kuma tasa hannu ta ɗauka Muryar mace taji tana cewa "Hello Ruƙayya ke ce kuwa? Menene dallah na kira min miji muna cikin raya sunnah,bana son shiga rayuwar ki ba,ki bari sai kin samu ya yarda ki tare sannan sai ki dinga wannan shishshigin yanzu barni da mijina mu wala, Ruƙayya ta koma ta ƙwanta tare da sa sabon kuka.


     ***        ***        ***


Dady ya fito daga wanka duk komai ya yi na samun natsuwa, amma duk hankalinshi yana gurin Pretty tunda bata taɓa kiranshi ba tun da ta tafi Legos, sai dai shi ya kira ta.


Ya zauna bakin gado ya dubi Zainab ya ce je kiyi wanka. Sannan ya ɗauki waya ya fara kiran Pretty tayi ta ringing tana katsewa, kamar bazata dauka ba sai kuma ta ɗauka tayi zaton ko Zainab ɗin ce ta maida mata martani, sai taji shi ya ce Prettyna takaici ne ya kamata a ranta ta ce namiji munafiki, ya ce kin kira ni ɗazun bana jin ki network kin ana matsalar shi ƙwanan nan, ta kayi haƙuri na kira lokacin da bai dace ba,ka ba matarka haƙuri ka ce banyi da nufi ba kamar yanda ta zata sai ta kashe wayar ta gaba ɗaya ma ta ƙwanta,ya zauna yana ta fassara maganar duk yanda akayi Zainab ta kirata ya shiga dialled calls yaga kam an kirata, Zainab ta fito ya dubeta me kika ce ma Pretty da kika kirata? Ta ce ni ban kirata ba ita ce ta kira kuma na shaida mata bana son haka,ban da rainin wayo sai ta kiraka muna tare?"


Haushi ya ƙara kama shi ya ce "kin san wacece Pretty? Duk ya ruɗe ya ce wallahi sai naci mutuncin ki,yarinyar da nike lallaɓawa shine dan kuturun wulaƙanci zaki ɓallo min Niger. Don yanzu ban san ta inda zan fara ba na samu na fara shawo kanta, ya ɗau wayar ya kuma kira a kashe take. Zainab dai sai da tayi data sanin bata kira Ruƙayya ba, domin ko bacci Dady bai yi ba itama faɗan da yake mata ya hana ta runtsawa asubar fari ya soma shiri.


      ***         ***        ***


Ta dubi Salimat ta ce,don Allah in kun je kice ina gaida Sulafat,bana jin daɗi jiya da zazzaɓi na ƙwana,Salimat ta ce zan gaya mata, Nuri ya shigo ya ya dai amarya? Ance bazaki samu zuwa ba, ta ce Eh, Nuri ku gaida min ita, Salimat wata ƴar sabis ɗin su ce da tayi haɗarin mota hanyar ta ta zuwa gida ranar Lahadi, shine zasu je dubata a Ibadan, sakamakon abin da ya faru shine Ruƙayya bata samu iznin zuwa ba gashi ta ƙwana ba lafiya.


Bacci ya soma ɗaukarta ta ji magana a kanta shugaban su ne da kanshi yake sanar da ita tayi baƙo. Kan ta ce wani abu Dady ya shigo sam bata son ganin shi don sai take jin kamar a gaban ta suke jiyannan. Ta runtse ido ya shigo ya zauna kusa da ita.


"Pretty tashi tashi ki jini." Ta ce cikin kuka "me zan ji? Bakada sauran abin da zaka gaya min,baka dashi Dady na jima da sanin halin maza,kai kana cikin maza masu cin amana da yaudara ga karya alƙawari." Ya dubeta ta kauda kai ta ce"na tsane ka." Ya ce ban ci amanar ki ba ban yaudare ki ba,kin ƙi bani dama na nuna miki son da nake miki nasha wuya a kanki ina sonki.


Ta toshe kunne.


"Daina gaya min ƙarya,bana son ji,bana son ji." Ta faɗi tana kuka sosai,ya rasa me zai mata ya ce to yanzu tashi ki faɗi min hukuncina, laifi dai ko wane iri ne na ɗauka,ya duka saitin fuskarta yana shirin haɗa bakinta da nashi,ta tashi tana kare bakinta cikin kuka take maganar kaje ka sha bakin wata sannan kazo ka daɓa min na ce kaje na bar mata kawai ka sake ni....." Ya rufe bakinta da tafin hannu.


Ya ce "Babu wannan maganar a tsakanin mu." Kuka tayi ta mishi ya durƙusa gwiwa bibbiyu a gabanta dan Manzon rahama kiyi shiru na durƙusa ni mai laifine amma ina roƙon ki kiyi shiru. Ta daina kukan muryar ta har ta dishe ta ce ka tafi bana son ganin ka, ya ce in na tafi zaki huce? Ta yi shiru ya miƙe ya tafi.


Ta yi shiru yanda ya damu ya bata tausayi tasan gaskiyan su Armaya'u ne sai ta dage zata samu mijinta. Tasan tana son shi amma ta kasa hucewa bayan tayi wanka kusan biyu saura tana fashin sallah, don haka ta zauna yanzun ne zata karya,ta soma shan tea ta ɗauko waya ta kunna text ɗin shine suka soma shigowa duk na bada haƙuri ne tare da neman yardar ta na son shigowa anjima, tayi shiru tana tunanin yanda take da kishi da yawa. Koda yake tasan tana son shi da yawa . Ya shiga kiran wayar ta barta tana ta ringing tana katsewa ya yo text yana roƙon ta dan girman Allah ta ɗaga wayar shi,ta ɗauka ya ce don son Manzon Allah inzo kin ji don Allah." Ta ce "Um." Ya ce to gani nan nagode. Ta cigaba da kurɓar tea ɗin da ta haɗa cikin ƙaramin kofi da har yanzu bata shanye ba. Ya shigo ya zauna kusa da ita ya ya jikin? Bata tanka ba ya ce ki min magana zan ji sanyi Pretty yanzun da na sameki be kamata insha wahala ba, kuma kema kin san ko wacce ƴa mace bayan ki zata biyo ina sonki, Ina sonki kin san....." Ta ɗaga mishi hannu "bana so ban so indai kazo gani na ne ka ganni kawai." Ya kai hannu zai taɓa ta, ta ce kada ka taɓa ni,ya ce to yanzun Pretty kin ce baki son na taɓa ki yaya zanyi? Ta ce me zan ji a maganar ka Dady,ƙarya? Tayi murmushin takaici aini Dady na wuce ka tsareni ka tsarani halin maza guda dubu ƙila goma ne ban sani ba,dan haka kayi shiru zai fiye maka sai mu daɗe tare amma in kace dole sai ka tsara ni to gara ka tafi abinka, ya ce to nayi shiru can ya ce ban karya ba, da gayya ta cika mishi ƙaton kofi da tea ta tashi ta kawo mishi bread ta koma ta ƙwanta tana kallon shi ga mamakin ta sai gashi ya shanye tas kuma ya ci bread da yawa, ya ce ruwa Pretty ta tashi ta kawo mishi.


Tana kallon shi ya fito da wayoyi kusan huɗu ya kunna nan aka soma kiranshi ya amsa wannan ya amsa wancan yawanci duk abokan harkar kasuwanci ne ya kira Momy ya faɗa mata yana Legos gurin Pretty ta ce ya bata su gaisa ya ce to ya miƙa mata Pretty ga Momy ta amsa ta tashi zaune har wani ɗan russunawa take yi kamar tana gaban Momy, Momy ta ce ba wata damuwa ko? Ta ce a'a ba komai, ta ce yana kula dake ko? Eh yanayi Momy nagode. Ta ce To ki kula min dashi kinji ƴata kada ki damu namiji tamkar yaro ne yanda kika saba mishi zai ɗore mishi na yaba da tarbiyyar ki, kuma nasan zan samu jikoki masu albarka. Ta ce nagode Momy, ta ce to bashi phone ɗin, ta miƙa mishi suka ci gaba da magana kan abin da ya shafe su,yana ajewa wata wayar ta soma ringing tana kallonshi yaƙi ɗaukar wayar,har aka dena kira suna zaune shiru har uku da rabi ta duba lokacin sallah ya yi nan ya zube mata komai wayoyinshi da makullin mota ya tafi a ranta ta ce ƙila yana da mota ne a nan tunda taga itama da tazo, zuwa aka yi aka ɗauke ta.


Wayoyinshi suka shiga ringing tana É—auka tana gaya musu yaje sallah,can wannan wayar ta É—azun ta É—auki ruri taga an sa my wife ta ce dama wayace ba matarka ba ce? Sai da wayar tayi sau uku tana katsewa taga yakamata ta É—auka ko itama zataji yanda ta ji.


Ta ce "Hello who is on the line." Daga can Zainab ɗin ta ce matarshi ce,ke wacece ki ka ɗauki wayar mijina? Abin ya ɗan sosa ma Ruƙayya rai, ta ce Ok mijinki ya shiga wanka in ya fito me za'a ce mishi? Zainab ta soma masifa ke wacece ina tambaya? Ruƙayya ta ce in baki da saƙo in kashe wayar dan in muna tare dashi bashi ba ɗaukar wayarki tun ɗazun kike damun mu. Sai ki bari sai naga dama ya dawo." Ta kashe wayar.


Zainab ta kira Mamanta ta ce Hajiyata aiki bai yi ba, yanzun fa yana gurinta har tana É—aga waya ta tana gaya min magana.


Hajiya ta ce "amma yana miki wulaƙanci ne?" Ta ce a'a sai dai jiya ne ta kira shi muna tare shine da ya shiga wanka na gaggaya mata magana shine fa ya ƙwana yana masifa, ta ce kinyi amfani da duk kayan da ƴar Nijar ta baki? Ta ce sosai ma bakiga yanda yake fita haiyacinshi ba idan muna tare, ta ce to ki dage kafin ta shigo ki riƙe shi gam, ta ce to ki koma wajen malamin, Hajiyar ta ce ki dai tanadi kuɗi yana baki ko? Ta ce tam ko bai bani ba ai zan ɗiba kuma ba ganewa yake ba naga kamar sun mishi yawa, suka sa dariya har da shewa tamkar ƙawaye.


     ***          ***          ***


Shi kam Dady har dare yana can sai dai ya yi sallah ya dawo, shi ya nemo musu abin da zasu ci,ita kam gimbiyar ƙin ci tayi yana gurinta har sha ɗaya tamkar kada ya tafi duk da basa hira, haka ya nufi masaukin shi.


Ta rungume tana tunanin shi har ga Allah ta ɗan huce,sai dai kishin ne yana damunta ta so ta auri Dadynta ita kaɗai ta kula dashi ta ririta shi ta maidashi abin sha'awa cikin abokanshi amma yanzun su biyu ƙila tana tufka waccen ta zama tana warwarewa.


Jirgin ƙarfe taƙwai zai bi dan haka ya yi sammako saboda suyi sallama,yau ya samu abokan ƙwananta dama su uku ne,ɗayar tayi mishi sannu da zuwa, duk suna sanye da kayan N.Y.S.C Pretty ɗin shi tana sanya takalmi ya shigo, sauran suka gaidashi suka basu guri itama ta ce an tashi lafiya? Ya ce yanda ki ka ƙwana nima haka kuma kin tashi da shirin zuwa aiki nima daga nan sai ofis." Ya ɗan ƙara bata baki duk da bata tanka ba yaji daɗin yanda tayi mishi addu'ar sauka lafiya. Bai koma gida ba kai tsaye ya wuce ofis, biyar saura ya shigo gida .


Zainab bata nan har ya yi wanka, Sunday ya gabatar mishi da abinci ga kuma Hollandia ya gama ya koma falo yana neman layin Pretty ya saba dan kullum sai ta tsinke sau biyu wata ran ma sau uku sannan ta É—auka.


Ya ce Pretty ko ki kira kiji yanda na sauka ko?" A ranta ta ce da kasan yanda na damu in san yanda ka je gida da baka É“ata bakin ka ba. Amma a wayar sai ta ce lafiya ai ita kesa aji shiru. Ya ce to ke yakike? Ta É—an ja aji sannan ta ce lafiya lau, yanda take amsa mishi waya sai ya rasa me zai ce mata.


Suka yi shiru na É—an lokaci ya ce "ina labari?" Ta ce Æ´ar jarida ce ni zaka tambaye ni labari,ya ce to bani na kotu, ta ce ai ba can naje ba. Pretty me Momy ta ce miki jiya? Sai kaji,ka je ka tambaye ta."


Zainab ta shigo sanye da riga da siket sun ɗameta, ƙaramin gyale a kafaɗa hannunta riƙe da jaka da key ɗin mota ta zauna tana faɗin ka dawo ne ashe?" Bai tanka ta ba ya cigaba da wayarshi.


To Pretty tsakanina da ke ai akwai sirri, ta ce to ba san jin kake yi ba, ya ce to ki ɗanyi kissing ɗina I miss You,ta ce "bata nan? Tai maka mana." Zainab taja tsaki duk da bata jin me Ruƙayya ke faɗi tasan maganganun soyayya ne. Ya yi kissing ɗin wayar Ruƙayya ya kashe. Dariya ya saka ganin ya soma ciyo kanta.


Ya tamke fuska sannan ya dubi Zainab


"Ina kika je?" Ta ce a'a gida mana Hajiyata keson gani na." Ya ce shine bazaki nemi izni ba" ta ce tun jiya kaki ɗaga wayata don kana tsoron ƴar gold kada tayi fushi, ya ce shine kika fita ko? To bazan ɗauka ba, ta ce "duk inda zan je sai na gaya maka sai kace auren gargajiya?" Ya taso da faɗa kamar zai bugeta, ya ce ke jahilar ina ce? Wato har ma aƙwai auren gargajiya, to ban san shi ba,in Hajiyar ta koya miki to bazan ɗauka ba,be carefull zanyi maganin ki." Ya fita ta ce borin kunya dan yaga yaje ya ƙwana da waccan ƴar iskar,kai ma sai nayi maganin ka."


    ***        ***       ***


Ƙwanci tashi su Ruƙayya sun gama sabis farin ciki ba wanda ya kai Dady tun ranar da ta dawo baya ma ƙasar yana Italy. Amma ya soma maganar biki,yana dirowa ya yi wanka sai Kabala.


Affa ya samu dan yasan in takan ƴar rigimar tashi ya bi sai ta dinga kawo mai uzuri,sun yanke sati biyu sannan ya sameta da maganar, ta ce ita wata biyu sai ta huta in kuma ya matsa mata sai ta fasa tarewar gaba ɗaya,ai dama dole akai mata, ya bata haƙuri tare da cewa ya yarda sai nan da wata biyun.


Ashe anyi rashin sa'a Umma ta ji,yana fitowa tsakar gida ta fito daga ɗaki tace kaje ka cigaba da shiri Yusuf sati biyun da kuka tsaida ba ƙari.


Bayan tafiyarshi ta yi ma Ruƙayya ta tas tare da cewa sai ta haɗa ta da Affanta nan ta shiga bata haƙuri tare da cewa ta yarda.


        ***        ***        ***


Shiri ba kama hannun yaro duk ɓangare biyun, Ruƙayya ta taka har Katsina, Zaria ta gayyato ƙawayenta na secondary su Amira,su Munira da Armaya'u ba zama ita sati biyu ne tsakanin ta da Ruƙayya za'ayi nata su Yaya Murja da Fati ana ta shirin yanda bikin zai kasance ya yin da su Yaya Sadiya manyan yayye ana ta shirya Auta. Kowa faɗi yake tana da kishiya Mom ɗin su M Bash tazo ta ɗauki amarya dan kimtsi na musamman.


Ƙwananta biyu tai ƙyau ta gyaru har ita kanta tana jin sha'awar mijinta,tana ba su M Bash labari suka yi ta mata dariya ta ce ni tsoro nake kar yaje ya rakwaɓani a banza gara shi yana da wata.


Gefen Dady daga Kaduna har Abuja ya hana jama'a sukuni, gidajenshi ma sun san Pretty zata shigo an gyara ko ina sashenta ya zuba komai.


Zainab ma ya canza mata amma tana ta mita wai amaryar daya gama da ita tun a waje shine yake rawar jiki, ya ce mata ai Pretty ba irin ki bace ke dai dana taya tun a wajen da kin bani, sannan koda ban taya ba ai kin bama wasu. Ranar tayi kuka kuma tayi data sanin yi mishi wannan maganar.


An kawo aƙwatuna har goma sha biyar Affa ya kirashi yana faɗa ya ce kamar hauka? Gashi shine ya yi musu Anko. Bayan su launching, dinner, walima da sauransu.


        ***         ***        ***


Amarya ta tare ɗakinta dake nan Kaduna gidan da Dady ya ƙera cikin gidan su. Bayan an kaita wajen su Momy aka basu amanar ta, aka maida ta ɗakinta kowa ya watse sai ƙawaye,Angwaye sun shigo har da Nuraddeen wanda shima ya rikiɗe ya koma abokin ango maimakon na amarya.


Anyi ɗan wasa da dariya anguna sun bada kuɗin da su Armaya'u suka buƙata na siyen baki, Al-Mustapha yaja Munirar shi suka nufi masaukinshi,ya yin da Ruƙayya ta riƙe Armaya'u wai sai ta ƙwana.


Da ƙyar ta ɓanɓareta ta gudu, Dady yazo yana lallashin ta dama tun da aka soma bikin kuka take yi musamman ranar da iyaye sukai mata huɗubar zaman aure idonta sai da ya kumbura saboda kuka.


Zahiri Ruƙayya tana da tsoro don haka koda Dady ya ce Pretty yo alwala mu gabatar da sallar ma'aurata sai ta ce mishi tana fashin sallah sannan ta ƙi yarda su ƙwanta tare, dole ya bar mata ɗakin,ba dan yaso ba,sai don kada ya ɓallo rikicinta.


Da safe bayan ta sheƙa ƙwalliya da super mai jajayen fulawa ta wuce Dady a falo ta nufi gefen su Momy, shima ya biyo ta yana cewa shine kika wuce ni? Sai ta nuna bata ganshi ba a zahiri kuma ta ganshi waya taji yanayi da Zainab, Momy ta ji daɗin ganinsu haka Dad a can suka yi break sannan suka dawo.


Kusan sati ɗaya kullum Pretty ta ce tana al'ada daya fita sai tayi sallanta, ranar da suka cika ƙwana goma tana ƙwance a falo hannunta riƙe da littafi tana dubawa, Yaya Fati ta bata shi ta ce zai taimaka mata zaman aure.


Dady ya fito sanye da jeans baƙi haka riga, ta kalleshi tana matuƙar son shi sai dai kishi, ya yi mata ƙyau.


Ya zauna kusa da ita ya ce "Pretty har yanzu baki fara sallah ba?" Ta ce lafiya ta qalau haka nake kayana. Ta cigaba da karatun ta, ya ce ko dan baki sona ne shine kike guduna?" Ta ce "zan ƙi yin sallah dan kai ne?" Ya ce ai Allah yana kallon ki fa,bata tanka ba.


Da dare ta fito wanka ta kulle ƙofa sannan ta tada sallah tana tahiyar ƙarshe taji shigowar shi ya yi amfani da wani key ya shigo, gabanta ya yi muguwar faɗuwa ya wuce ya gadonta ƙwanta ya ɗauki littafin da take karantawa mai suna 'TAWA TA SAME NI' yana dubawa tayi sallama kana ta sake tada kabbara. Yana kallon tayi ta sallah tun yana ƙirgawa a ranshi har ya daina. Ya tashi ya shiga toilet shima ya ɗauro alwala daidai tayi sallama ya ce Pretty biyoni jam'i gara in taya ki ko zakiyi saurin gamawa.


Raka'a biyu suka yi har tayi mamakin yanda Dady ya dinga jero musu addu'a ya ce Pretty ta so,taƙi tashi ya kamata ya cire hijabin daga ita sai ɗaurin ƙirji ta ce meye haka Dady bana so fa, ya ce haba Pretty kiji tausayi na ki tuna baya ki tuna dadynki nasha wuya kanki, ta ce "Ni nace ban son ji baka wani sona."


Ya dubeta"ina sonki ina ƙaunarki, nafi son ki da kaina,ki tuna baya." Ta ce kai dai kana son jikinane kawai, ya ce kinyi kuskure,na fara sonki tun baki girma ba,na so ki lokacin da baki mallaki komai na ƴa mace ba, baki da komai na soki badan ƙyaunki ba badan dukiya ba,badan cikar halitta ba, ya ƙara sassauta murya "Nasan da kin soni yanzun ban san me nayi miki ba." Ya ɗaga yatsun shi guda biyu "kalli zoben alƙawarinki yana cin jikina ban cire ba,ban ci amanar ki ba,ki bari mu fahimci juna. Tana shirin magana bakinshi yasa cikin nata ya shiga nuna mata wasu kalolin soyayya masu zafi da gaggawa tana son shi don haka bin shi tayi suka lula. Sai da tafiya ta soma nisa sai ta kasa tsoro ya shige ta ta soma faɗin "yi haƙuri Dady, don Allah ka barni,ba zai iya ba tunda ya jima yana jiran wannan rana, da zafi zafi yake nuna mata soyayyarshi don haka tayi mata nauyi gashi tasha gyara, wannan dalilin yasa tasha wahala ga Ruƙayya da son jiki ko allura bata so amma ganin babu sarki sai Allah nan da nan ta haƙura Dady ya kusan fanshe wuyarshi a kanta. Ta wahalu ƙwarai saboda...........



🖊️🖊️🖊️

[8/21, 06:53] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 7



Saboda yanayin zuwan da Dady ya yi mata. lokaci mai tsawo Dady yana babban birnin majidaÉ—i kafin ya rungume Pretty É—in shi tsam.


Farin ciki da wani shegen sonta ne suke ƙara ratsa shi, tsawon minti goma ya buɗe ido ya dubi fuskarta idonta yana rufe sai dai zufa da hawaye sun ma fuskar kaca-kaca ya tashi zaune ya jawo kanta ya ɗora kan cinyarshi da zanin gado yake share mata fuska yana faɗin "sannu Pretty kin ji Allah ya shi miki albarka lallai ke wata abin alfahari na ce sannu ƴar halak bari nayi wanka kema sai kiyi ko?" Ya gyara mata ƙwanciya ya shiga toilet.


Farin ciki ran Ruƙayya kar ki tona, domin ta zama cikin matan da mazajensu suke alfahari da su ta tattala budurcinta yayin ƴan matancinta, ta kawo shi inda ya dace,bata damu da ciwon da jikinta yake yi ba ga sanyi yana ratsa ta,tasa hannu ta janyo bargo ta rufa,san da ya fito jikinta ya ɗime da zazzaɓi ya ɗan ja bargon tashi kiyi wanka,ta kuma ƙudundunewa haƙoranta suka soma haɗuwa da ƴan uwansu, sanyi ta faɗa cikin ƙerma ya hau gadon shima ya shiga bargon jikinta har rawa yake yi, "innalillahi." Ya dubi agogo ƙarfe uku gashi basu da ko farasitimol wayar Momy ya kira duk ya ruɗe, tana jin ya ce Momy, ta yunƙura don Allah Dady kar ka tashe ta ka rufa mana asiri,bai jira jin zancen ta ba ya sake faɗin Momy, Momy ta ce lafiya cikin daren nan? Ya ce Pretty ba lafiya kuna da farasitimol inzo in amsa? Da safe sai muje asibiti, ta ce ka tsaya a gurin ta bari na zo, ya ce to,ya ɗauko mata rigar bacci mai ɗan kauri ya ce bari in saka miki ga Momy nan zuwa. Da sauri ta tashi zaune ta saka rigar a jikinta, ya je ya buɗe Momy ta shigo da magani Ruƙayya ta kasa kallonta, Momy ta ce kawo mata ruwa tasha maganin, tana sha ta ƙwanta. Can bacci ya ɗauke ta Momy tayi musu sai da safe ta tafi, jikinta ya shige ya ƙwanta ya ɗora kanta saman ƙirjinshi tayi ajiyar zuciya ta cigaba da bacci.


Shi kam yana jin ajiyar numfashinta sonta yana ƙara shigar shi so tsansta mai cike da yarda mai tsafta.


Bai san yayi kuskure ba sai da safe da ta kasa tashi tayi wanka, suna cikin ƴar dabarar yanda zata miƙe sai suka ji sallamar Momy ba kunya ya ce Yauwa Momy taimaka mata, kunya ta kama Ruƙayya ba shiri ta miƙe ta fara takawa cikin dauriya ta shige toilet Momy ba yarinya ba ce ta fahimci komai musamman da taje bakin gadon ta kakkaɓe musu shinfida ta ce in tasha koda tea ne sai ta ƙwanta. Alamar da ta gani kan shinfiɗar ya tabbatar mata ɗan ta ya yi sa'a don haka tace ya kawo sabon zanin gado ta matsa kusa da toilet ta ce ƴata ki shiga ruwan zafi sosai kisa dettol kin ji." A ranta ta ce shikenan mai aukuwa ta auku.


        ***        ***         ***


Ƙwana uku Dady da Momynshi suna tattalin Pretty ɗin tashi, tun tana kunya har ta daina. A gabanta Momy tai mishi faɗa cewa ka gwada mata ƙarfi ne Dady? Shiru ya yi yana shafa kanshi. Ta fito wanka ta zauna gaban madubi tana ƙwalliya tayi ƙyau ita kanta tasan tana amarci,gashin ta sai ƙyalli yake gashi tasa material mai fulawoyi ruwan madara,ta taje kanta gashin ya sauka har kafaɗunta ta soma fesa tararuka Dady ya shigo yana shaƙar ƙamshin turarenta,bayanta ya tsaya tana ƙoƙarin ɗaura ɗan ƙwali ya amsa ya aje.


"Nafi son ganinki haka My Pretty" ya duka ya saka fuskarshi a gefen wuyanta duk suna kallon madubi ya ce kinada ƙyau Prettyna, ta ce na kai kane? Ya ce kenan muna kama, yaushe ne zaki bani Baby shekaru na sun soma shurawa ina son yara." Kunya ta ji ta runtse ido ta ce ko yau ne Allah ya kawo zan baka, ya ce ƴan biyu nake so,ta ce to ka gayawa Allah.


    ***      ***      ***


Wata rayuwa Dady ya nuna wa Pretty ɗin shi a wannan ƴan ƙwanakin nan mai matuƙar daɗi, itama yanzu tasan babban birnin majidaɗi, yanzun haka da take ƙwance saman kujera rungume da filon kujerar layin M Bash take kira dan neman ƙarin bayani akan wasu turaruka cikin kayan gyaran jikin da Mom ta kawo mata.


Bayan ta ɗauka Ruƙayya ta hau mata tsiya da cewa "haba M Bash kamar kun kawo gawa rami keda Armaya'u babu ko waya, Munira ta ce gara mu barku ku ci amarci babu takura." Ta ce muna ci kam lallai garin daɗi yana gidan aure amma sai ansha wuya ake shan daɗi, M Bash ta ce shegiya Ruƙy kinji maji daɗi ne ina fushin da ake yi da angon? Ta ce da kenan aiko da ɗin ma ina son kayana rashin fahimta ne yanzu kuma mun fahimci juna duk wata mata tana bayana, ko bai faɗa ba haka ne. Don haka bata gabana yanzu ma ina gaban turarukan da Mom ta bani ina son kiyi min bayanin su. Turare in zaki ƙwanta ki shafa kaɗan,garin maganin kisa zuma zaki ganta cikin ƴar leda sai kisa ruwa, kaɗan zakiyi amfani dashi zaki sha mamaki. Suna sallama Dady ya shigo ta yarda wayar saman kujera ta miƙe suka maƙale juna ya ce "ina son ki Pretty." Ta ce "I love You My Yusuf ina sonka." Tamkar ya haɗiyeta yaja hannunta suka fita gaban wata ƴar mitsilar mota fara tas ya tsayar da ita sannan yaja hannunta ya saka mata key sannan ya raɗa mata ƙyautar budurcinki nagode,rungume shi tayi.


Momy tana hangen su daga saman bene ranta ƙal farin ciki, ta ce ka nuna ma Momy ma." Ya ce ita ce ta zaɓar miki zan dinga koya miki duk Sunday,Ni kuma menene tukwicina?" Ta ɗan sake shi tayi taku biyu zuwa uku ta juyo ta ƙyafta mishi ido ɗaya tace to night, ya biyo ta yajata jikinshi me zaki bani? Ta ce zan kaika babban birnin majidaɗi zaka sha mamaki.


Ya kam sha mamakin har yaso ya zauce shiyasa ya ce ya fasa barin ta Kaduna kamar yanda da farko ta buƙata. Ya ce ai tana da ɗaki a Abuja Momy tasa baki da cewa kibi mijinki ƴata kar ki damu da kishiya,ke dai ki zama mai biyayya da ƙyautatawa shi ya ɗibi kayan ta aƙwati biyu haka kit ɗin ta da abubuwan ƙamshi na kimtsa jiki, basu samu Zainab ɗin a gida ba ɗakinta ya buɗe mata ta shiga ya taimaka mata gurin gyara ɗakin duk da cewa a gyare yake.


Suka shirya kayanta cikin dirowa, Sunday ya gabatar musu da abinci a dining table sun sha Hollandia kafin suka shige toilet,ƙiri-ƙiri Ruƙayya ta hana Dady ya sanar da kowa cewa yana cikin Abuja duk da ɗinbin jama'ar dake son ganinshi ba cewa tayi kada ya kira su ba a'a idan tana gabanshi ya kan mance kowa da komai sai Pretty.


Zainab sai bayan isha'i ta dawo suna ƙwance kan doguwar kujera duka su biyu, suna kallo tare da ƴan wasanni da suka saba ma juna turus ta tsaya tana dubansu. Kishi da fargaban rashin samunta da Dady baiyi a gida ba ta ɗaure ta ce "Sannunku." Dady ya dubeta rai a ɓace amma sai ya share don kada ya yi mata cin fuska gaban kishiya ya ce "yauwa Zee,ina kika je?" Ta ce naje na dubo Hajiya ta bataji daɗi ba, ya ce Allah ya sauwaƙe ya dubi Pretty ɗin shi da kishi ya hanata ko motsi ya ce Pretty ga Zee ta dawo ta daure ta yunƙura ta tashi zaune suka dubi juna cikin ido,gaban Zainab ya yi mummunan faɗuwa ganin Ruƙayya ta ce, Ruky dama kece kishiyata? Ruƙayya ta ce oh baki sani ba ko? Wallahi ni ce ya ƙwana biyu? Zainab ta haɗiye miyau da ƙyer ta ce lafiya lau ta nufi ɗakin ta lallai sai ta dage kafin ta ƙwace Dady,nan taji tsanar Ruƙayya ta shige ta.


Ruƙayya ta fito daga wanka ta gama shirin ƙwanciya. Yau kam tasan sai dai ta rungumi filonta,tana shirin kulle ƙofa Dady ya shigo ta ce na zata ka ƙwanta? Ya ce a ina? Ta ce ɗakin matarka mana, ya ce a'a,ta tsaya ban gane a'a ba ai can zaka ƙwana ko ka manta ne? Ya yi shiru tazo ta shige jikinshi ka je can haƙƙinta ne ƙwananta ne gobe sai ka raba mana ƙwana in ɗai ɗai ko biyu bazan taɓa so ka zama mara adalci ba don ina son ka zama Yusuf ɗina har cikin aljanna." Ya zuba mata ido in sumbace ki? Ta ce kaɗan kar ka zarme.


Sai da ta ƙwace kanta ta tura shi ta rufe ƙofa kan gado ta faɗa ta rungume filo wasu ƙananan ƙwalla suka zubo mata Dadynta yana tare da kishiyarta.


Da safe ta fito wanka ta zauna gaban madubi in kinga yanda take tsara ƙwalliya sai kiyi tsammanin shi ta karanta a makaranta. Ta gama aka taje gashi wata shegiyar shadda tasa,tasha ado ta zuba ɗauri tamkar zata je liyafa dama gashi har Yanzun lallen amarcinta na nan wata shahararriyar mai dayis tayi mata,wato Sadiya layin ƴan kifi Allah ya yi mata baiwar zana shi tamkar daga India ta koyo,in tayi maka ya yi wata bai goge ba, amarya sak kalolin turaruka ta fesa sai ƙamshi yake tashi.


Dady ya turo ƙofa a hankali ya shigo kayan bacci ne a jikinshi wani abu taji ya tukare ta a ƙirji amma sai ta danne ta rage tsawo, ina ƙwana? Ya shafi fuskarta lafiya Prettyna kin tashi lafiya? Ta ce lafiya, ya ce zo muje dining room,ta ce baka zuwa ofis ne yau? Ya ce zanje, ta ce bakayi wanka ba, ya ce zanyi muje kiyi break ta ce a'a sai kayi wanka yaso ya shiga toilet ɗin ta tace a'a sai dai yaje can inda ya ƙwana.


Ɗakinshi ya nufa sai da ya shirya sannan ya shigo ta fesa masa turarenta sannan ta ce ba haka ake yi ba,kaje ɗakin matarka sannan ka turo ta kirani ya ce ai kema matata ce kije ki kira ta, ta ce sai ranar da ka ƙwana ɗakina,kana namiji Dady sai na koya maka yanda zaka zauna damu, ya fita sai lokacin ya tashe ta daga bacci tun bayan da ta bar ɗakinshi da asubahi. Brush kawai tayi sannan ta fito ya ce je ki kira mana Pretty muyi break.


Ta ƙwanƙwasa ƙofar, Ruƙayya ta leƙo,kizo inji My dear tana wani yanga ita a dole ta ƙwana da miji dariya ma ta ba Ruƙayya, Sai dai ita kam taji zafi da kishin wannan gayun da Ruƙayya tayi gurin cin abinci tana rawar kan haɗa mishi gara a gabanshi shi kam hankalin nan nashi yana gurin Pretty sai taka mata ƙafa yake yi. Bayan sun gama ya yi musu nasihar zaman lafiya, sannan ya fita.


Ita dai Ruƙayya tun da ta shige ɗakinta ta ɗauki waya taga Dady ya lodo mata kuɗi har dubu biyar, shi ta soma kira tai mishi godiya, sannan ta cigaba da kiran ƴan'uwa da abokan arziƙi. Can da rana Dady ya kira ta ya tambayar taci abinci ko? Ta ce shifa? Ya ce Sunday ya kawo mishi amma bai fara ci ba." Ta ce "kaci yanzu zan je naci." Ita kuma taƙi fita ne saboda tana jin Zainab da ƙawayenta ne ko ƴan'uwanta ne Oho sun cika falon.


Biyar dai dai Dady ya shigo lokacin Pretty É—in tashi ta ci gayu cikin material ja, Zainab a saye da riga da wando ita a dole Æ´ar boko, aka je aka rungumo miji,gaban Pretty ya tsaya ta ce sannu da zuwa Babyna ya ce yauwa My Pretty, Zainab ta ja shi zo muje kayi wanka My dear, ya ce Prettyna bari in fito kin ji? Ta danne sannan ta ce sai na ganka.


Ɗaki ta koma ta shiga nazari lallai zama da kishiya sai ka dage, amma zata nuna mata ita za'a ma salo? kissa Zainab ta shiga nunawa yana shiga wanka itama ta shige wai zatayi mishi,tasan yanda take hillatar maza cikin sauƙi ta shawo kansa take ta fita dan cusawa Ruƙayya haushi. Amma kash bata nan ta koma ɗaki, jallabiya Dady ya saka shima cikin saurin yaje gurin Pretty ya zauna dining table yana faɗin har ta tashi Zainab dake tsaye cikin haushin yanda yake ta zumuɗin fitowar kishiyarta, sai ta ce bari na kirata,bata jiraba ta nufi ɗakin Ruƙayya daga ita sai zani ɗaurin ƙirji da ƙaramin tawul a kanta ta ƙwanƙwasa ƙofa sau biyu Ruƙayya ta buɗe Zainab ta cire tawul ɗin kanta tana faman tsane ɗan diddigar gashinta ita dole tayu wankan tsarki, Ruƙayya kizo inji My dear,nasan kin gaji da jiran shi yana can yana neman lada tana magana tana karairaya.


Haƙiƙa saƙonta ya isa ga Ruƙayya sai dai abinka ga lauya sai ta ce to muje. Cikin murmushi ta dafa Zainab ɗin ta cigaba da faɗin kin san duk inda Babyna zai je ya samo lada zan fiso ai naga saurin shi don Allah Zainab ki rinƙa bashi haƙƙinshi yanda ya dace banda sauri." Ta yi gaba zo muje mana.


Haushi ya kama Zainab bata so haka ba,kai wannan ƴar bariki ce sai ta ƙara ƙaimi maimakon taje gunsu sai ta tafi ɗaki ita ko Ruƙayya firij ta nufa ta ɗauko Hollandia mai sanyi ta cika kofi ta miƙa mishi tare da faɗin sha Babyna. Itama kanta tana mamakin yanda tasa mishi suna,kai kishiya tana sa mutum ya yi abin da bai shirya ba. Gayu Zainab tayi ta zauna tana karairaya, amma duk hankalinshi yana kan Pretty ɗin shi yakan manta kowa bare wata Zainab hakan yana ɗaga hankalin Zainab matuƙa. Ya yin da Ruƙayya taga fushi bazai mata ba gara ta zage ta ƙara kanainaye Dadynta hakanne ma yasa ta dage sai da ya kaita gidan aminiyarta Munira M Bash, ta yini sun je gidan Mom inda suka samo tsarabobi masu ƙyau Munira ta cusa mata ra'ayin saka ƙananun kaya ta ce da sune ta ƙara riƙe wuyan Mustapha. Basu bar gidan sai da suka je kasuwa ta ƙwaso wanduna zuwa siket da shegun riguna na ƴan gayun zamani suna shigowa Dady na zuwa,ya ɗauki matarshi sai gida.


A ƙwanakin girkinta Dady ya shiga ruɗu tare da ƙara sonta ya nane mata koda rana sai ya baro komai ya dawo ganinta bata sani ba ya soma shirya musu yawon shaƙatawa duk da ɗinbin aikin dake gabanshi, sai ana gobe tafiya sannan ya ce ta shirya su je Kaduna. Zainab ta soma masifa ya za'ayi ranar girkinta suje Kaduna, ya ce sallama zamu je yau zamu dawo, ta tsaya sororo ina kuma zaku? Ya ce wasu kaya zanje dubawa a England ina da mata biyu ba zanje na zauna gwauro ba ta ce to ai sai kaje dani tunda nice uwargida, ya ce sai wani lokacin yanzun da Pretty zamu je wasu abubuwan suna buƙatar sai da lauya, kuma kin san ita lauya ce sannan......." Ta ce kai dai kace kawai an mallake ka da,da ita kake zuwa? Ya ce to haka ɗin ne.


Umma ta ji daɗin ganin ƴar Autarta yanda tayi ƙyau gwanin sha'awa shima Affa haka yaji daɗi ganin ta ƙwantar da hankalinta yasan suna zaman lafiya daga gani. Momy ma tayi farin ciki ganin cikin ƴan ƙwanakin nan Dady ya yi ƙyau ga ƙwanciyar hankali, lallai Ruƙayya tana kula da shi kuma rai a bashi abin da yake so, duk kan kafet suka zauna tana bakin gado sha'awa suke bata, wani son Ruƙayya take ji a ranta. Ruƙayya ta ce Momy ina wuni? Ta amsa da lafiya lau ƴata,ya ya baƙon guri da abokiyar zaman taki? Ta ce lafiya lau tama ce agaishe ku," Dady ya dubeta da yaushe ta ce a gaida Momy? Harara Ruƙayya tayi mishi, cikin murmushi ta ce ina ruwanka? Momy ta ce ato sanda zata ce kana ina? Ya yi dariya shikenan.


Dad ma ya shigo sun gaisa shi kam ya kasa barma ranshi sai da yace Æ´ata wane abinci ki ke ba My Son? Naga ya Æ™ara zama gentleman ga Æ™oshin lafiya yana yawo a jikinshi." Kunya ce ta kama RuÆ™ayya ta durÆ™usa tana gaishe shi ya ce ai mun gaisa, Dady ya ce tana kula da ni Dad fiye da yanda kake zato ya shafi gefen fuskarta ashe har yanzu tana sona da,ta ce bata sona Momy ta ce bana gaya maka ba dama kaÆ™i yarda. RuÆ™ayya ta É“oye fuskarta cikin cinyar ta. Momy ta ce to maza ku É—au hanya kada dare ya yi muku  a hanya.


Ya bi Dad samanshi dan su É—an zanta harkar kasuwanci. Ya yin da Momy take tambayar ta badai wata matsala tsakanin ta da Zainab? ta ce babu komai.


Sun ɗau hanya Sabi'u direba ke jansu suna baya suna soyewa kanta ƙwance bisa jikinshi tana ta mishi shagwaɓa ita dai yaje da Zainab domin ta ce ita ya kamata ya soma fita da ita ya ce "Haba Pretty in banda ke ban ga matar da zata samu wannan damar ba, sannan ta ce bata so." Ta tashi zaune sannan tasa hannu ta ƙara jan labulen daya shiga tsakaninsu da mai tuƙinsu wato Sabi'u, ta sanyaya murya ta ce "Ni fa nafi son komai kayi adalci saboda mu gudu tare mu tsira tare." Ya ja leɓenta ya ce da ba dake nace zanje ba da yanzun ana nan ana zunɓura min baki.


To dukkan ku Matana ne da wacce naga dama da ita zanje." Ta ce Allah ko zan ji haushi daga baya zan gane kayi adalci ne, ya ce to duk naji bayan na gama mana komai shikenan sai na fasa ko mekike nufi?"


Tayi fari da idanuwanta ina nufin a cikin biyu ayi É—aya ko dai ka tafi da ita ko kuma ayi Æ™uri'a, ya ce kamar ya ya? Ta ce zaka samu paper  ka rubuta zaman gida É—ayar ka rubuta tafiya ka bamu ita zata soma É—auka kafin ni, duk wacce ta É—auki zaman gida shikenan a tafi da Æ´ar'uwarta, hankalina zaifi Æ™wanciya, ya ce Ni dai kin tadamin nawa" ta shiga shafa gefen fuskarshi in Allah yasa dani zaka ba makawa ka riÆ™e wannan.


Zainab kam da suka tafi Hajiyarta ta kirata tana faɗa mata abubuwan da suke faruwa ita kanta Hajiyar ta damu. Cikin masifa ta ce ke wato bakisan yanda zaki ƙwaci kanki ba? To kada ki sake ki yarda idan yazo ki hau masifa kice ke baki yarda ba sai dai ya barku ku duka,in kuma dole ne zuwan yaje daku ku duka,kin ji ko? Tunda yaƙi ki haɗa da masifa da kissa shi kanshi asirin ba daina shi zamuyi ba, canza wani malamin zamu yi. Ta ce to Hajiya.


       ***           ***        ***


Jibgegiyar motar dake ɗauke dasu tayi parking a gurin daya dace cikin harabar gidan suka fito, Sabi'u ya yi gaba da motar ya kaita mazauninsu ita da taƙwarorinta,su kam ciki suka yi da sallama suka shiga falo.


Tana zaune amma bata amsa ba sanye take da atamfa super baƙa da jajayen falawoyi ƙafarta ɗaya kan ɗaya tana girgizata. Tana cika tana batsewa.


Ruƙayya ta dubeta "sannu da gida Zainab su Momy sun ce a gaisheki." Buɗar bakin ta sai tace "yauwa sannu da yawon cin amana,aini ban taɓa fita dashi ranar girkin ki ba." Ruƙayya ta ce "To kiyi haƙuri in girkina yazo kema ku tafi ko ina ne, ta wuce ɗaki cikin takaici.


Dady ya dubi Zainab "ke wai bakida tunani ne kina nufin banida ikon yin yanda nike so da gidana, saboda kada ranki ya ɓaci? Ki maida hankalinki." Ya faɗa yana tafiya, ta ce Allah zai saka min, ya juyo yana dubanta ta nufi ɗakin ta, kalmar Allah zai saka mata ta zauna mishi a cikin rai ko dai gaske ne ya zalunce ta? Ya tuna ɗazunnan Ruƙayya ta dage tana mishi mita wai bai dace yaje da ita ba shi dama tafiyar nan fa ya ƙirƙireta ne don kanshi da kuma Pretty baiga amfanin tafiyar ba in har baije da ita ba. Wanka ya yi sannan yayi alwala kasancewar masallacin da tazara shiyasa sai yayi isha'i, bayan isha'in ne ya tara su dan yi musu ƙuri'a Zainab ya fara ba ta ɗauka sannan Pretty.


Hannu yana rawa Zainab ta buɗe cikin ikon Allah zaman gida ta samu nan ta soma hawaye kan cewa wannan wani munafunci ne aka haɗa don a ɓadda tunaninta, Ruƙayya ta ce Babyna na yarda ku tafi, ya ce ki min shiru ban yarda ba, ta tashi taje ta ɗauko biro da takarda tazo nan ta rubuta da taje har shaida tayi ma ɗayar sannan da tazo ta rubuta tafiya a mai shaidar ɗayar kuma ta rubuta zaman gida,ta ƙudundune ta zuba a ƙasa ya ce ta soma ɗauka,nan Allah ya nuna mata nashi ikon ta rasa mai shaidar ta ɗauki ɗaya sannan Ruƙayya ta ɗauki nata, Zainab ta katseshi da faɗin tab wallahi ban yarda ba.


A fusace Dady ya ce nima banason ki yarda ki ɗauki mataki kin ji ko? Ya miƙe yana faɗin banza mara hankalin kiyi abin da kanki son ranki a biye miki yanzu kice baki yarda ba, to kada ki yarda ɗin wawiya." Ya nufi gurin cin abinci.


Ranar dai ƙwana suka yi rigima har ta kaiga ya shashsheƙa mata mari, tare da buɗe ƙofarshi ya ce taje ɗakinta cikin daren bata bari gari ya waye ba ta kira Hajiyarta tana kuka tana gaya mata yanda abin ya kasance mata, Hajiya ta ce ƙyale shi su tafi. Insha Allah da rigima zasu dawo ko nawa zamu kashe ƴan iska zasu gane kurensu matsiyatan banza,in tana taƙamar asiri ne muma mun iya har gun tsafin da ake son kaini ina ƙi wannan karon zan je.


Zainab ta ce kije Hajiya wallahi na tsani in buɗe ido inga ƴar iskar matar nan baya gajiya da kallonta sai ka ce T.V,ko nauyi na baya ji gani gata amma bashida lokaci na. Wata ran ma in zai kirani da sunan da yake kiran ta fa zakiji ya kirani, Hajiya ta ce kada ki damu,zan gyara masa saiti,ki barsu su tafi ke dai ki tabbatar kin shaƙi kuɗi, ta ce ba wani abu.


    ***     ***     ***


Tunda tayi sallah ta shiga shiri yanzu kam ƙal take jin ta ba wani zargin an ƙwari Zainab, yawancin kayan da suka siyo da M Bash shi ta ɗauka.


Ya shigo ya ce "bari in taya ki kema sai kije ki taya ni." Zainab kam tana É—akinta har suka gama shiri Sunday shine ya fitar musu da kayan Dady ya kira wayar Zainab kamar ta share sai kuma ta É—auka, ya ce ki fito zamu tafi, ta kashe kusan minti biyar ta fito, RuÆ™ayya ta dubeta cikin fara'a ta ce "Zainab zamu tafi." Ta dubeta ta ja tsaki  "Dady gani." Ya ce zamu tafi ne, ta ce nan zakai min sallama saboda ni ba a bakin komai nike ba. To Allah ya kiyaye hanya ta wuce abin ta ta shige É—akinta, ya ce Pretty muje kawai, RuÆ™ayya ta ce a'a kaje kuyi sallama ka bar mata komai, ya ce kinga check nan zan bata taÆ™i tsayawa,ki muje kawai ai na ajiye mata komai abinda babu ga Sunday nan sai ya amso mata dama ganin dama ne yasa zan bata kuÉ—in ba tsoro ba, komai da an mata ta ce an cuceta anyi meye meye?" RuÆ™ayya ta ce Haba don Allah kayi haÆ™uri kaje ka bata."


Ya nufi ɗakin fuska babu walwala, kuka ya sameta take yi ta kifa kanta, tausayinta yaji don haka ya isa gurinta ya kamota ya miƙar da ita ya rungume wani sabon kukan kissa ta saki yayi ta lallashi tare da bata check ɗin dubu ɗari ya ce in basu isheta ba zai sa a ƙara mata wasu cikin account ɗin ta. Ta yi ta janshi da ƴan wasanni dan dai ta nuna ma Ruƙayya itama yana yi da ita, ya ce to bari muje Zee, ta dama ka ƙosa ka tafi ne ko? Cikin shagwaɓa ya ce a'a Zee kece duk sanda muka zauna sai kin ja munyi rigima, ta shiga kissing ɗin shi a baki tana cewa in sun itama aje da ita, ya ce kar ki damu.




🖊️🖊️🖊️

[8/31, 19:10] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 8



Ruƙayya da taga shiru a ranta ta ce namiji sai a barshi,ta samu guri ta zauna ta ciro waya ta soma kiran Armaya'u, "Sadiya ƴan fatakol amaryar shitu," Sadiya ta ce ƴar gidan Dady ai na zaci ni baza'a kirani ai min sallama ba, jiya munyi waya da M Bash take ce min zaga duniya da bebyn naki." Ruƙayya ta ce lallai ma M Bash har ta gaya miki ina ce ma Dady beby?" Ta ce dole ne ta gaya min tunda mun kawo ki ne kina kukan bana son shi, sai kuma a jiki kin koma ce masa beby inye! Ƴar gidan bebynta." Ruƙayya ta ce ta naki ne? Zan haɗa ki da Shitu in ce yayi miki kishiya. Sadiya ta ce don ke kinada ita?.


Ruƙayya ta ce to yanzu dai sai mun dawo, ta ce ku dawo lafiya ki samo tsarabar Baby boy. Rukayya ta ce baki ce twins ba, ta kashe wayar, sannan ne suka fito tare da Zainab tana manne da jikinshi.


Ruƙayya ta miƙe tana faɗin "To Zainab sai mun dawo." Ta yatsina baki ta dubi Dady ta ce My dear sai ka dawo ka kular min da kanka, ya ce kada ki damu Zee nima ki kular min da kanki da gida,bana son yawo mara dalili ta ce dan wannan kada ka damu.


Ruƙayya dai tayi gaba kishi ko a mota sam taƙi sakin fuska sosai ya kula da haka sai abin ma ya soma bashi dariya, ita fa tace sai yaje ya ma Zee sallama, amma kuma sai ta kama shan kunu,ya raya tsokanar ta ya ɗauki wayarshi ya kira yarinyar dake nacin son shi kullum tayi ta damunshi da kira. Tasha mamakin kiran nashi dan bai taɓa kiranta ba, ringing ɗin farko ta ɗauka yace Aysha ƴanmatan gari, ta ce a'a ku ne masu gari Alhaji Yusuf,yau wace rana an kira ni? Ya ce tafiya zamuyi da amarya, shi ne nace bari in kira muyi sallama don kada ki kira waya kiji shiru kin san bana son haka.


Ruƙayya ta warce wayar ta kashe sannan ta tura a jakarta, ya dubeta "Pretty ya ya zaki min haka? Muna sallama da budurwa......." Wani kallo da ta watso mishi ne yasa ya yi shiru tamkar ya ƙwashe da dariya, amma ya dake ta ce tun kan muje airport tsaya in sauka."


Ya ce saboda me? Ta ce nidai na fasa zuwa kaje ku tafi da A'ishan ka da Zainab. Ya jawo ta haba Pretty na,ta ture shi kai na kula na mamajo ne sarkin mata, saura ta huÉ—u, ya ce haba kamar wani bazazzagi? Ta ce kaima gara ba zazzagen da kai,ni da gaske fa nike bazan je ba,ya bar dariyar da yake yi ganin da gaske take.  Ya ce wasa nake miki Pretty kin san ke kaÉ—ai ce My Sweet one, My everlasting, My dear one,kin san Allah da in rasa ki a duniya,gara ace babu rayuwa ta.


Ta harareshi daÉ—in bakin namiji shi kake min,ya ce haba My Pretty kin san wuyan da nasha a kanki kuwa? Bayan ciwo da rashin Æ™wanciyar hankali ga tsabar sha'awa da begen ki,bazan gaji da gaya miki sau uku ina zuwa aikin hajji inyi É—awafi in rungume ka'aba ina kuka ina gaya ma Allah RuÆ™ayya, RuÆ™ayya. Ya ya zaya bani  nayi wasa dake? Ranar da aka É—aura min aure dake sai da nayi azumi uku dan nuna godiya ta ga maÆ™aginmu." Ya É—an saurara sannan ya cigaba, "Yanzu burina na gaba inga kin cikamin gida da yara,don Allah tafiyar nan kar ki bari mu dawo baki bani Baby ba kin ji?" Ta É—an kama kunnenshi É—aya ta É—an ja sannan ta ce "Allah zaka roÆ™a ya bamu masu albarka," ya ce kullum cikin roÆ™onshi nike sannan zan zage damtse a wannan tafiyar kema ki dage,inga kina É—an aman nan na masu ciki,jaye fuska tayi tare da faÉ—in nidai babu ruwana.


       ***.     ****         ***


England suka fara yada zango cikin wani shahararren hotel.


Wai! Naso ace kuna nan a gurin ku ga soyayya da kanta, Tabbas Ruƙayya ta yarda beby ɗin ta ita kaɗai yake so Son ya manta da kowa da komai daga bautar Allah sai ta Pretty itace ta tuna mishi da abubuwan da ya dace ya yi kiran ƴan Nigeria zuwa ƴan kasuwancinshi,yau da suka cika sati biyu yakamata su bar ƙasar amma sai yaji baya son tafiya sai da suka ƙara ƙwana biyar.


       ***        ***       ***


Rayuwarsu ta England ta tsaya mishi a rai ya rubuta cikin ƙundin tarihin sa, haka na Germany su kansu mutan ƙasar sunyi sha'awar su, kasancewar yana da abokan hulɗar kasuwancinshi sai dai ya ce wannan karon ba kasuwanci ya zo ba, don haka ko England bai nemi abokanshi ba, da gaske Dady shi kam ya dage sai ya samu beby, don haka ko yaushe suna garin majidaɗi gashi Pretty ɗin tashi ta shagwaɓar dashi ta ririta shi. Wani lokacin ma in ya matsa mata da maganar samun beby sai tace kaine bakada beby,nikam ina dashi ta jawo shi zo ma inyi feeding ɗin ka. Duk sunyi ƙyau har sun gaji Ruƙayya ga wasu hips sun zauna fata ta goge tayi shar, wani ƙyau kuma da shegen ƙwarjini sai ka dubi Dady.


Don haka sabon kishin sa ne yake cin Pretty É—in tashi ko yaya taga matan turawan nan suna kallonshi tamkar zasu haÉ—iye. Haka nan shima bai cika son maza na kallonta ba.


Daga sati biyun da suka ce zasuyi sai da suka yi sati biyar dan ma Dad yanata waya, My Son ka dawo kan harkokin ka fa,ga kuma Zainab da duk sanda ya kirata ta dinga kuka kenan,wai ita ta gaji da rashin shi,da yaga shi yanada wata ita fa? Yasan tanada shegiyar jaraba ya ce bari ya tausaya mata su dawo. Sun yo tsaraba harda ta tsiya, shi dai Dady yawancin nashi duk kayan beby ne duk da baiga cikin ba yana sa ran samu tunda yasan lafiyar shi qalau,sai na Zainab da su Momy ta matsa mishi yayi musu tashi duk da ya bata iyayen kuÉ—i tayi ta ta.


A gajiye suka iso gida gurin ƙarfe biyu dan sun ƙwana a Legos sannan suka biyo jirgin Kaduna. Zainab ta taresu babu yabo ba fallasa,sun gaisa da Ruƙayya sai dai ta firgita da ƙyan da Ruƙayya tayi. Hatta muryarta ta ƙara zaƙi da sanyi ta ɗaure tasa Sunday ya shirya musu abinci duk tana yi ne bisa umarnin bokansu da ya ce kada ta tare su da tashin hankali ya ce cikin lalama zata shanmace su ta tarwatsa su ta hanyar saka musu sihirin cikin abinci ko abin sha wanda ake buƙatar su ci su biyun a lokaci ɗaya. Taso ta haɗa baki da Sunday sai dai tasan cewa Sunday ba zai taɓa yarda da buƙatar ta ba, amma ko a shegen Hollandian nasu zata zuba musu su sha suyi ta zabga faɗa kamar yanda Boka ya yi ma Hajiya bayani.


Ƙwanansu uku da dawowa suka nufi Kaduna sun cika dangi da tsaraba kowa sai tsiya ake ma Ruƙayya wai ko an samo ne ganin yanda tai ƙyau ƙwana ɗaya suka dawo.


A hanya ne Momy tayi ma Dady waya take tuhumar shi anya Pretty É—in tashi batada ciki kuwa? Ya ce har yanzu indai ba É“oye min take ba, bayan sun gama wayar yake ce mata Pretty me yasa kowa ya ganki sai ya yi min zancen ciki? Ko dai gaske ne?" Ta ce haba dai da baka sani ba? Allah bani da komai nima haka suke ta damuna, ya ce Allah ya amsa bakinsu, ta yi shiru tana murmushi.


Gidan Munira M Bash ma da taje, Munira ta ce Allah kinada shigar ciki dubi yanda ƙirjinki ya cika dam. Ruƙayya ta musa, M Bash ta ce yaushe ki kayi al'adar ki ta ƙarshe?.


Ruƙayya ta ce "aini tunda nayi aure,ko ince tunda na tare banyi al'ada ba,kin san tunda na samu sauƙin al'ada na dena ciwon cikin nan to sai inyi wata uku biyu banyi ba, Munira ta ce ƙila ma ya shige baki sani ba, ta ce a'a M Bash da naji canji a jikina haka Munira ta haƙura ba don ta yarda ba.


Zainab taso sa musu magani cikin abinci ko Hollandia amma Sunday ya bi ya kanainaye komai tare da sa ido kamar yasan me take son yi. Zaman gidan Dady babu yabo babu fallasa, shima kamar ya É—an soma jin daÉ—in zaman nasu tunda yanzun Zee ta É—an rage matsala kaÉ—an,satin su biyu da dawowa daga tafiya Zainab ta ce mishi zasu je garin su Hajiyanta.


Dady be musa ya ce sati nawa zakuyi? Ta ce ba zamu fi ƙwana uku ba, ya ce maimakon kuyi koda sati ɗaya, haushi ya kamata ta ce don ka gaji da ganina komin kora da hali? Ya ce a'a naga ƙwana uku yaushe aka gaisa da dangi? Ya cika ta da kuɗi ga waɗanda ta sata,har ƙofar ɗakin Ruƙayya taje tai mata sallama, Ruƙayya ko har ƙasa ta rakata inda direba zai ɗauke ta zuwa gidansu, tunda da Hajiyarta zasuyi tafiyar,ta shiga motar tana faɗin zaki ci mai garin garinku wannan tafiyar dan ke zanyi ta da bebyn naki,dama kun ishi mutane da beby beby, zan gyara muku zama a ranta take saƙa wannan abun,sun isa suka tadda Hajiyarta har ta shirya don haka ta sauka motar mijinta ta shiga gida, suka rankaya. Bala direban Hajiya shi ne ya jasu suka ɗauki hanyar Minna.


Zahiri ba garin su Hajiya zasu ba,gurin Boka kanfa suka nufa, domin ta kasa amfani da maganin.


       ***          ***        ***


Bayan zuwan su Minna sun ɗauki hanyar Bidda. Suka yanke suka shiga cikin wani ƙursumin daji sun wuce ƙauyuka da yawa har duhun dare ya soma shigowa kafin suka zo wani bakin rafi Zainab ta dubi Hajiya ta ce "Hajiya ba dai ruwan nan zamu shiga ba?" Hajiya ta ce ga masu fito nan za mu bar motar mu hau ƙwale-ƙwale, tsoro ya kama Zainab ta ce na shiga uku! Gaskiya Hajiya mu haƙura mu koma yaushe zan shiga ruwa ban taɓa shiga ƙwale-ƙwale ba, Hajiya ta ce da Allah ni yi min shiru saboda uban wa zan shiga ruwan ba saboda ke ba,sai mun koma ki damu mutane.


Sun shiga ruwa Zainab ga tsoro ga faɗan Hajiya,har suka fita. Daga nan suka yanki wani daji a ƙafa,gurin duk ƙarafa ne irin dutsinan nan masu faɗi can suka hango bukkar Bokan,suna isa Bala ya ce Hajiya ina son yin sallah don na tabbata yanzun anyi isha'i. Ta ce sai ka koma can baya nan ba gurin sallah, ya saki baki yana dubanta nan kuwa ya juya ya ce zan jira ku gurin mota in ma ƙwana ne sai in ƙwana ciki, ta ce haka ya yi,ya juya yana tunanin halin Hajiya shi kam ya kusan barin aikin nan, ya tafi ga yunwa ga gajiya ga rashin sallah.


Su kam suna tsugunne gaban Boka bayan ya zunduma ashar sannan ya hau zagin Zainab kaga Æ´ar tsinanninya Æ´ar abun uba mu baki maganinmu ki ajiye? Ke sarkin tsoro to bama bawa mai tsoro magani, ya É—ago maganin ya nuna mata kinganshi nan  mun saka aljani ya É—auko mana abun mu Æ´ar tselan uwa,sai kuma bada kuÉ—i sannan mu maida miki,mamaki ya cika Zainab da taga maganinta.


Hajiya ta ce godiya muke Boka a yanzun muna neman afuwa a gurinka ka bamu taimako,ya dubi Zainab da idanunsa jajaye bakinsa ɗoyi na fita duk sanda ya buɗe, ya ce in na baki bakiyi ba to zan barki da aljanu su bi min haƙƙina,ƙa'idar maganina sati ɗaya in ya wuce zanyi hukunci ya ce ya kika ce? Ta ce zanyi, ya ce kisa ko rashin lafiya kike son a ɗorawa ja'irin mijinki da matarsa?.


Ta ce nafi son na faɗan suyi ta zabga faɗa, ya ce kin samu gashi,ya miƙa mata maganinshi na farko daya bata ya ce kije kisa cikin abinci ko ruwan sha ki tabbatar sun sha tare lokacin zukatansu zasuyi zafi su dinga jin zafin juna, amma fa in kika bari ɗaya ya ci wanda ya cin shine zai zama mai zafin rai kuma asirin zai karye bada jimawa ba, sannan asirinki zai tonu, Hajiya ta ce Boka matsalar ta yaron gidan dake musu aiki yasa mata ido, ya yi dariya ya kai hannu kan wasu ƙoƙuna ya ciro wani ɗan ƙullin magani ya yi surkulle ya miƙa mata, riƙe wannan zaiyi maganin shegen yaron.


Zaki mallake shi yanda ko uwarshi ki ka ce ya kashe zai aikata bare sama wata magani, ta ce to ya zanyi Boka?


Ya ce "Kiyi tsirara sannan ki shafe jikinki gargaɗi kada ki yarda ya shafi gabanki,da kin yarda ya shafi gabanki sai dai kiyi haƙuri yaron zai amfana dake,Ta dubi Boka da sauri,ya cigaba sosai daga nan zai bi umarnin ki in kuma kika bari maganin ya taɓa gaban yaron zai liƙe miki kema haka.


Hajiya ta ce "to Boka tayi amfani dashi gurin mijinta mana maimakon ta mallake wani sai ta mallake mijinta." Ya ɗaga sauti da ƙarfi kul! Kul! Tayi amfani dashi gurin mai sallah, mijinta yana sallah aljanun mu zasu ƙone in mun turasu gurinshi ke kar ki fara uwarshi tana tsaye kanshi tana yawan yi mishi addu'a.


Zainab ta ce to Boka a canzan wani, ya ce ina ai sharaɗi magani shine dole ayi in an karɓa,in kuma anƙi aga ɓacin rai,ku tashi ƴan tselan uwa maganar kuɗin aiki sai magani ya ci zan fanshe a jikinki,kije da kuɗin ki dinga shan madara rana ɗaya zan zo in shanye peak zaki sha sau uku a rana zan zo miki insha jikinki da zaran kinyi amfani da maganina ya ci,ku ɓace min a nan bari jinnu su kai ku gurin motarku, kafin suyi magana sai jinsu su kai fuu anyi waje dasu sai tif a ƙasa kusa da mota, cikin tsoro Bala ya buɗe mota ya leƙo bai gane su ba saboda dare, ya soma addu'a, Hajiya ta ce Bala ya gane muryarta ya ce Hajiya kune? Suka ce Eh maza tada mota mu bar dajin nan haka suka kamo hanya sha biyu suka zo wani ƙauye, dole suka nemi gidan maigari don ƙwana.


Washegari suka ɗauko hanya a cikin Minna sukayi masauki cikin wani hotel don su ƙwana biyu tunda sunce ƙwana uku Bala ma sun kama mishi nashi ɗakin. Zainab dai ba'a cikin sukuni ta ƙosa a koma tayi gaggawar aikata aikin Boka gashi ya ce ta dinga shan madara zai zo yasha a jikinta abin ya yi mata yawa.


Tun safe suka É—auko hanyar Abuja sha biyu suka shigo dan ma sun samu matsalar mota a hanya. Daidai lokacin Pretty da bebyn ta suna gida suna shagwaÉ“a juna, kullum da Æ™yer yake tashi ofis. Yanzu da suka zube a falo tana sanye da gajeren wando na jeans sai riga É—amamma sai gashin ta gefe ta kama da ribon shima kalar wandon, tayi Æ™yau kanta yana jikinshi yana wasa da gashin kanta,  ta ce beby yaushe zan koma aiki ne? Ya ce an kusa gama ofis É—in ki na Kaduna? Kuma gashi ban son muyi nisa ace sai weekend zan ganki? Ta ce niko nafi son haka saboda nafi son in ganni daga ni sai kai,ya Æ™ara jawo ta jikinshi ina sonki da yawa Pretty har ban san kalar son da nike miki ba.


Ta ce nafi sonka fiye da yanda kake sona, ya ce ban yarda ba Pretty, ta ce me zan maka ka yarda? Ya ce tashi... sallamar Zainab ce ta dakatar dasu dan tuni take kallonsu amma basu san ta shigo ba. Dady ya ce "har kun dawo?" Ta ce Umm ta wuce É—akinta.


Ruƙayya ta tashi tana mata sannu da zuwa kyar ta amsa ta shige ɗaki.


Misalin sha ɗaya Ruƙayya tana ɗakinta bacci ga zazzaɓi wanda ya zamar mata ƙa'ida duk ranar Allah zuwa yamma sai ya sauka taƙi sanar da Dady ne dan tasan zai ce suje asibiti, ita ko bata son zuwa,tasan gajiya ce bata gama sakinta ba.


Zainab ta leƙa kicin taga Sunday yana ta aiki ta koma ɗaki ta haɗa asirin da aka bata,ta cire kaya ta maka a jikinta maimakon shafawa ya ko gangaro ya shiga gurin da ba'a so nan ta tuna da gudu ta shige toilet ta shiga yin tsarki sai dai kash ya riga ya shiga,ta fito da yaƙinin bazaiyi komai ba, tunda ta wanke wayar kicin ta kira Sunday ya ɗauka ya ce Yes Madam za'a kawo wani abu ne? Ta ce kawo min Hollandia mai sanyi ya ce Ok ya ɗauko yana mamakin me yasa yau Madam zata sha Hollandia ita da bata son shi.


Ya tura ƙofa ya shiga bai ganta ba don haka ya nufi madubin ta dan ya aje mata. Ya juyo zai fito suka yi karo, tsoro ya kama shi a yanayin da ya ganta,da sauri ya juya tare da rufe idon shi bakinshi yana rawa ya ce sorry Madam.......katse shi tayi ta hanyar ɗora hannuwanta a kafaɗunshi, fargaba ya cika shi jikinshi yana ta ɓari tsam ta rungume shi tuni shirinta ya soma ratsa shi ya fara miƙa mazantakarshi ta tashi dama ya soma maida martanin abin da take mishi sun lula cikin shagala da ta ɗauke su tsawon awa biyar.


Bayan dawowa haiyacin su sai tsoro ya kama Sunday ya yin da Zainab ta soma kukan ƙarya tana faɗin daga tana mishi wasa shine zai yi mata haka? To zata sanar da Oga nan ya zube yana bata haƙuri yana kuka,ta ce saka kayan ka duk abinda na ce kayi zakayi? Ya ce zaiyi ko menene ta ciro garin magani ta ce wannan cikin Hollandia zaka saka ka tabbatar Oganka da wancan shegiyar matan sun ci, ya ce to ya saka shi a aljihu.


Ya ko saka kuma yanata gadin shi don kada wani cikin su yasha shi kaɗai sai da dare sannan suka zauna dinner Ruƙayya tasha gayu cikin super fara, yayin da Zainab aka sa farin les,ta saki fuska har su Ruƙayya suna mamaki a zukatan su.


Sunday ya yi ta jera abinci a gabansu Zainab ce da maigidan don haka ta soma zuba mishi.


Sun fara cin abinci kafin daga baya ya jawo Hollandia ya yi sanyi yanda Dady yake buƙata don haka Zainab ta zuba mishi ya soma ɗaɗɗaka ya ce Pretty ga mai sanyi fa, ta ce kasan duk yanda nake son Hollandia ƴan ƙwanakin nan ko ƙamshin ta bana son ji, ya ce kin sha da yawa ne ya hau miki kai ko? Ta ce ƙila haka ne, ya ce ni kam koda zan sha goma a rana ba zai ginsheni ba.


Cikin Zainab ya kaɗa kar dai matar nan taƙi sha ta ƙaƙaro murmushi Ruƙayya ke yau bazaki sha bane? Dubi yanda raɓa ke zuba jikin kofin da My dear yasha Ruƙayya ta duba sannan ta ce yau dai banjin sha. Tamkar Zainab ta fasa ihu don haushi, ta rasa me ke mata daɗi ji take kamar tai ma Ruƙayya ɗura,har ma Ruƙayya tasha jinin jikinta shi ko gogan yama daina cin abincin sai faman banƙarar Hollandia yake yi jinshi yake tamkar yana yawo ne a sama dan daɗi. Ruƙayya ta fara tashi tai musu saida safe kafin Zainab ma ta tashi ta nufi ɗakin ta ta kira Hajiyarta ta shaida mata Ruƙayya fa bata sha ba, faɗa Hajiya ta soma tare da zagin Zainab ɗin.


     ***          ***         ***


Bacci mai nauyi ya ɗauki Dady bisa gadonshi ko addu'a baiyi ba daƙyar ma yayi wanka wata sabuwa Zainab tana fitowa dan zuwa ɗakin maigidan sai taga Sunday tsaye a falo,suna haɗa ido saita birkice ta kirashi ɗakinta shima abin da ya hana shi bacci kenan, suka lula cikin masha'a tsawon lokaci mai yawa sannan suka tashi cikin firgici,ya ƙwashi kayanshi ya yi waje yayin ta kama kuka menene haka daga sau ɗaya.


Kiran sallah ya farkar da Dady bayan yayi sallah ya rasa me ya hana Zainab zuwa É—akinsa? Ya san dai ko faÉ—a sukayi zata zo bare ba faÉ—a, Pretty ce gimbiya bata zuwa É—akinshi sai dai shi ya bita.


Yana wanka zuciyarshi zugi take yi tana zafi ya fito ya shirya kan dinnig babu komai sannan mata biyun babu ko ɗaya takaici ya kama shi ya ce Zainab! Ke Zainab, kai Sunday" a firgice suka fito a zatonsu asirin su ya tonu kowa yana ƙyarma ya fito, yanda jikinsu ke rawa sai suka bashi mamaki, ya ce har yanzu babu komai na break fast harna shirya zan fita,kema mara amfani bazaki matsa mishi ya shirya ba? Ya shiga faɗan rashin dalili, suka yi ajiyar zuciya ta soma cewa, My dear kayi hakuri bari inje in duba da kaina tsaki ya yi ya nufi waje.


Wasa-wasa Dady ya canza ya zama masifaffe Ruƙayya ma tsoron shi take,tun daga ranar da yayi ma Zainab duka akan wai ta fita bata sanar dashi ba, bayan yasan tana fitar bai ɗauki mataki ba sai yanzu, yau ita keda Dady ta saba shi ke zuwa ɗakinta don haka koda aka gama cin abinci sai tayi ɗaki gurin cin abincin ma a ɗari-ɗari akeyin shi sai faman harare-harare yake yana jiran ganin mistake Allah dai yasa aka gama qalau. Ruƙayya na tashi shima ya tashi ya yi ɗakinshi. Zainab tayi kitchen gurin Sunday ta ce ya fa shigo tana jiranshi ya ce to.


A ran Dady faɗi yake yau zaiyi maganin Pretty wato ita tana taƙama yana sonta shi ne haƙƙinshi ma sai ya bi ita tafi ƙarfin zuwa ɗakinshi to yau kam bazai je ba,har gurin biyu taji shiru kamar ta share sai kuma da ta ce bari taje tunda yanzun ya zama a lallaɓa. Sai dai tana fitowa Sunday ta gani zai shiga ɗakin Zainab daga shi sai gajeren wando,bai ganta ba don haka ya shige.


Kamar ta tsaya sai kuma ta wuce. A rigingine ta same shi fuskarshi tana kallon silin ta zauna gefen gadon bayan ta rufe ƙofar ya tashi yana hararar ta ya ce waton Ni Ban isa ba ko? Ta ce me ya faru ne? Ya soma ɗaga murya ƴar rainin wayo dole ki ce min me ya faru? Tunda ni kinga ina son ki sai ki ka maidani sakarai sai dai in ina buƙatar ki ni na biki ɗakinki ko? Ta ce to yi haƙuri bebyna sam faɗa baya yi maka ƙyau ta ƙarasa magana tana tura bakinta cikin nashi. Ya yi ajiyar zuciya sannan ya shiga neman lada. Irin Haka Pretty take yi tana lallaɓa shi in abin yazo kanta,ga ciwon da ko'ina na jikinta yake mata zazzaɓin rana duk ta faɗa tamkar ba ita ba.


Shi da kanshi ya tsare ta wai sai ta faɗi mishi dalilin ramarta, ta ce ko faɗan ka Dady shi kaɗai zai ramar dani tunda da ba haka kake ba, ya ce tunda ga kare ba dole ki ce min mafaɗaci ba,kina taƙama ina sonki shiyasa kowacce magana tazo bakin ki sai ki yaɓa min,ta soma hawaye tana faɗin To kayi haƙuri shikenan, ya ce ai dole kiyi kuka tunda Allah ya hore miki idon kuka da bada haƙuri,tama rasa me zata ce ya dinga shiga yana fita sannan ya yi tsaki ya wuce.


Shiru tayi tana tunanin irin wannan hali da Dady ya canza, inda ma abin ya ɗan mata sauƙi ba ita ɗaya yake mawa ba.


Wani sabon lamarin kuma duk sanda Dady ya nemi Zainab dan zuwa garin majidaɗi sai ya zama ba namiji ba,ya kasa aiwatar da komai sai dai ya haƙura bugu da ƙari kullum da dare sai taga Bokan nan cikin mafarkin ta yazo yana amfana da ita ga wani ɗoyi da yake yi ban da liƙewa juna da suke yi ita da Sunday da rana da dare in ba ita keda miji ba.


Abun ya soma damun Dady ya tsare Zainab yana tambayarta me yasa baya amfani a gurinta amma gurin Ruƙayya lafiyarshi qalau? Ta ce itama bata sani ba wai amma da Hajiya ta nemo magani wai ance Ruƙayya ce tayi mata asiri ya yi shiru yana son yayi nazari amma ya kasa natsuwa zuciyarshi tana ta faman tafarfasa tana shaida mishi gaske ne, in ba haka ba yaya za'a ce gurinta kaɗai yake namiji gurin kishiyarta shima mace ne? Wato duk son da yake nuna ma Pretty bata gani ko? Ya tashi fuu ya fita.


Tana ƙwance tayo amai ta gaji ga zazzaɓi, Dady ya shigo a fusace ta ɗago tana dubanshi, tsoro ne ya kamata ganin bata taɓa ganinshi cikin irin wannan fushin ba duk da cewa yana saurin fushi ƙwanan nan amma na yau dabanne. Tsura mata ido ya yi sannan ya girgiza kai,kin bani mamaki Ruƙayya, da sauri ta dube shi tana zaton tun ranar farko da suka haɗu ta ce mishi sunanta Ruƙayya ya maimaita faɗin sunan bai ƙara kiran Ruƙayya ba sai dai Pretty don haka sai taji wani sabon tsoro ya shige ta,ta zuba mishi ido ya ce ashe haka halinki yake? Ashe wa'azin ƙarya kike min ke munafuka ce? Cikin rawar murya ta ce me nayi Dady? Ya ce da Allah ni rufe min baki,wai duk son da nike nuna miki,be ishe ki ba sai kin shiga bokaye da malamai shi ne kika je kika yi ma Zainab asiri kada inyi sunnah da ita sai dai ke ko?


Ta zaro idanu tare da faɗin "haba Dady wannan sharrin daga ina?" Ya ko ɗaga hannu ya wanke ta da mari ji kake tau, ta firgice ta riƙe gurin,Ni ka duka bada haƙƙina ba Dady? Ya ce na mare ki in kika ƙara magana kuma sai na zane ki.. kuka ta cigaba da yi,shi ko faɗi yake shawara ɗaya zan baki kiyi gaggawar zuwa gurin da aka yi sihirin a karya shi tun kafin in yanke hukuncin daya dace a kanki shikenan don Allah ya jarabce ni da sonki, shikenan sai ki maidani ɗan iska, yasa kai ya fita.


Taci kuka har ta gode Allah jikinta ya É—au zafi kafin wayewar gari ta galabaita amma duk da haka ta yanke shawarar tafiya Kaduna. Ta haÉ—a kayan da zata iya É—auka ko wanka batayi ba,ta zura silifas tana fitowa direba ya taso Madam ina zaki je ne? Ta ce a'a ba nisa zanyi ba, ta fita tayi tafiya mai nisa sannan ta samu mota shata ta É—auke ta suka tafi, tasha ta kaita ta shiga motar Kaduna.


Kamar taje gidansu amma sai ta tuna yasan zata ci ƙaniyarta gurin Affansu don haka sai ta wuce gidan su sashen su Momy ta shiga Momy ɗin bata nan ta zube kayan tayi ƙwanciyarta.


Momy ta shigo da jaka ta soma cin karo ta dubi gadonta, RuÆ™ayya ta gani Æ™udundune tana rawar sanyi da sauri ta nufi gadon, RuÆ™ayya lafiya?  Ta buÉ—e ta a wuyanta tasa hannu zafi taji mai tsanani, ta ce innalillahi keda wa kika zo? Duk ta ruÉ—e cikin ruÉ—u ta É—auki waya ta kira likitansu.


Ya ce gashi nan zuwa ta koma gurin Ruƙayya ta ce keda Dady ɗin ku ka zo? Hannu ta girgiza alamun a'a ita kaɗai ta zo. Abin ya ɗaure kan Momy ta ce yasan baki da lafiya ya barki kika taho? Likitan ne ya yi ma Momy waya cewa ya iso........



🖊️🖊️🖊️

[9/1, 13:10] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 9



Ya jima yana mata aune-aune tare da tambayoyi,ya tambayi Al'adar ta,ta bashi amsa tunda ta tare bata taɓa yi ba,don dama tana daɗewa batayi ba, ya ce ma Momy yana son fitsarinta, bayan ta shiga toilet tayo Momy ta kawo mishi sannan ya ɗibi jini, Momy ta ce wannan kumburin na fuskarta fa? Likita ya yi nazarin fuskar sannan ya ce ma Momy Hajiya wannan ba mari ba ne? Ya cigaba wannan babu damuwa mari ne da kuma kuka zai washe,kan Momy ya ɗaure ta maimaita a ranta mari? Yana tafiya Momy ta soma tuhumar ta akan batun mari gaske ne ko ko faɗin likita ne?


Hawaye ya soma bin kumatun Ruƙayya ta ce a'a ba mari bane, Momy tayi ta yi amma Ruƙayya ta ce ba rigima sukayi ba,ta ce to ina direban da kika zo dashi? Ta ce a'a ita kaɗai tazo a motar haya, ta koma ta ƙwanta jikinta na cigaba da rawa, Momy ta ce gashi bai bada magani ba ya ce sai ya dawo zai je yayo test ta kawo mata tea mai kauri,ta ɗan sha Momy ta kira wayar Dady, ya ce Momyna ina shirin kiranki ki ka kirani yi haƙuri yau duk ban kira ku ba.


Ta ce kaini ba wannan ba me yasa ka turo Ruƙayya babu lafiya kuma a motar haya? Zumbur ya miƙe daga kan kujerar shi tuni rannan nashi ya soma zugi a ranshi ya ce motar haya? Babu izni lallai kuwa, amma ya yi ƙoƙari ya ce tanace sai tazo Momy, direban su ya fita Ni ku Sabi'u zai kaini ofis,ta ce wannan ba dalili bane me yasa tunda kasan bata lafiya baka tuƙa kanka Sabi'u ya kawo ta ba,ta numfasa aƙwai abinda ya faru kuke ɓoye min kai da ita domin likita ya ce mari ne yasa fuskarta ta kumbura.


Ni ba mahaukaciya ba ce Dady yanda nasan ka keson Ruƙayya in ba akwai wani abu ba da zaka bar komai ne kuzo tare, amma koma menene ku kuka sani, tunda kunƙi faɗa, ta kashe wayar ta tazo gaban Ruƙayya tana faɗin ke mace ce ke zai ƙwara gara ma ki...... Aman da ya taso ma Ruƙayya shi ne yasa Momy saurin tare ta tare da yin shiru da ƙyar suka isa toilet ta dinga ƙwarara amai tamkar zata amayar da ƴan hanjinta. Hankalin Momy ya yi matukar ttashi ta kuma kiran likitan ta shaida mishi ya ce yana nan zuwa so yake sai ya gama test.


Kafin wani lokaci ta galabaita,tuni numfashinta ya soma ɗaukewa, to amai ya yi yawa ga cikinta bata ci komai ba. Tsoro ya cika Momy ta yiwa likitan waya ya kai sau shida, sannan ya iso gudu-gudu bayan ceto numfashinta sannan yasa mata ruwa tare da allurai cikin ruwan nan da nan ta samu bacci, likita ya miƙa ma Momy takardun yana murmushi ya ce Hajiya ga sakamakon test ɗin yarinya tana da juna biyu.


Da sauri Momy ta miƙe da gaske Doctor? Likitan ya ce tabbas ga shaida nan cikin takardu, alhmdllh ita ce kalmar da Momy take ta faɗi tare da yiwa likitan godiya, bayan tafiyarshi Momy ta je ta zauna kusa da Ruƙayya tana shafa gefen fuskar Ruƙayyan hawayen farin ciki suka zo mata shekaru sama da talatin da biyar basu ji kukan ƙaramin yaro a gidan su ba sai dai na jama'a in sun zo. Wani sabon son Ruƙayya ya ƙara shigar ta, Allah ka bamu masu albarka, ta furta tare da miƙewa, wayarta ta ɗauka ta kira maigidan, ya ce yaya dai Madam? Ta ce goron albishir nake son ka bani, ya ce goro? Ta ce yes,ina sauraren ka. Ya ce to na baki duk abin da kika zaɓa don nasan baki albishirin banza, ta ce ƴarmu Ruƙayya mata Son ɗin ka tana da ciki yanzun haka gata nan, ya ce Alhamdulillahi gani nan zuwa.


Kafin yazo sai da ya kira Son É—in nashi yana murna da faÉ—in congrats My Son ina farin ciki tamkar ranar da likita ya sanar dani cikin ka, Allah ya bamu masu albarka ya kashe wayar.


Dady ya ɗaure haƙiƙa ƙila gatse yake mishi mahaifin nashi,yana nufin ya yiwa Ruƙayya wulaƙanci ba haka ba murnar me zaiyi mishi? Nan ya samu kanshi da tunanin ya ƙyauta mata kuwa? Can kuma wata zuciyar ta ce ita ta ƙyauta maka kenan da tayi sanadin sunnar ma'aiki, ya miƙe yana shirin fita a ranshi yana raya zai matsa sai ta faɗi gurin da taje ta yo asirin nan dan ma ita ce taci albarkacin so.


Bai samu jirgi ba dole Sabi'u ya jashi a mota, sun isa Kaduna ana magriba, don haka shima masallaci ya wuce, yana dawowa gurinsu,sai dai ba kowa, duk suna bedroom É—in Momy can ya tadda Pretty É—in shi tana ta bacci su kuma Momy da Hajja da tazo dubata suna cin abinci.


Ya shiga da sallama yana raba ido suka amsa idonshi ya sauka kanta tana ƙwance da sauri ya isa gurinta a ruɗe ganin ana yi mata ƙarin ruwa gashi ta rame tamkar ta daɗe tana ciwo ya zauna yana shafa fuskarta, Momy haka Pretty tasha wahala? Tana murmushi ta ce kai kayi wauta sannan kana cewa tasha wahala? Bayan kai kasa ta biyo motar haya,suma ta dinga yi min ɗazun, ya ce suma Momy cikin tsoro, ta ce ƙwarai kuwa,ai tunda likita ya yi mata allura shikenan tayi bacci ta tashi ɗazun ta kuma komawa gata dai har Yanzun ya dubi Dad ya ce Dad Allah ya soni da Pretty ta rasu ya zanyi?.


Hajja ta ce ba gani ba inta rasu, ya ce a'a bafa zan iya da tsuhuwa ba, Momy ta ce ai da tsohuwar zuma ake magani, ya ce a'a yanzun an daina sai sabuwa farar saƙa,duk suka saka dariya ya ce Momy me likitan ya ce game da jikin nata? Dad ya soma murmushi dama Momyn taka bata sanar maka ba na kira ka ina taya ka murnar zan samu jika,ya tsura mishi ido, Dad da gaske kana nufin Pretty tana da ciki? Momy ta ce ƙwarai ƙyautar da Ubangiji ya yi maka kenan kana wasa da ita ka barta ta kamo hanya cikin murna ya cicciɓeta tana bacci cikin firgici ta farka tana yunƙurin amai, Momy ta ce ai gashi nan zaka taso aman.


Nan ko ta soma sharara shi har shi sai da shi kanshi ya tsorata likitan dai aka kuma kira yazo ya ce bebyn nan yana wahalar da Maman shi, Dady ya ce Dakta ya ya za'ayi ta daina wannan aman ne? Doctor ya can wannan kam sai dai haÆ™uri  dan bazai dena ba har sai cikin yayi Æ™wari sosai sai dai muyi ta sa mata ruwa kawai.


Bayan likitan ya maida mata ruwan tare da wasu allurai ta koma baccinta, Dady hankalinshi ya tashi su Momy da Hajja suka dinga ƙwantar mai da hankali, Dad ya tafi maida tsohuwa gida, Hajja ta tafi tana mai tausayin Ruƙayya shi kam Dady ya ƙe ƙashe ƙasa ya ce nan zai ƙwana dole Momy ta tafi saman Dad.


Ciwo ance in yaji dare domin a wannan daren har wasiyya Ruƙayya ta soma bari inda take cewa ya yafe mata kuma yasa su Affa da Umma da Yayyanta su yafe mata,ba shiri Dady ya yi ma su Momy waya ya ce suzo Pretty zata mutu,suna zuwa suka sare, domin lokacin da suka zo jikin nata ya yi tsanani tana ta neman gafara sumanta biyu,ruɗewa ta ƙarshe Dady ya yi,kiran sallar farko suka nufi asibiti inda yace da likitan shi dai kam ya haƙura da cikin da ƙyar su Momy suka shawo kanshi ya haƙura aka bar cikin,satin ta ɗaya a asibiti taɗan samu ƙwarin jiki bata cin komai sai tuwon Hajja da miyar yakuwa kullum sai an yo yaje ya amso su Affa da Umma da sauran Yayyanta kuwa kullum sai sun zo Dady ne me gaya musu ina da ciki ne duk abokanshi sun sani kai har Armaya'u da Sadiya duk ya yaɗani don haka kullum cikin ƴan dubiya muke,an sallameni kamar yau washegari ya koma.


Kafin ya tafi sai da ya tada fitina domin su Momy sunce zasu gyara mata sasanta ta koma ta ce ita dai anan zata zauna ɗakin Momy, Momy ta ce shikenan ma nima zanfi son haka don inma kina can zan raba hankali na biyu ne, Dady ya ce shida so yake su tafi tare, ta ce a'a,su Momy suka ɗaure mata gindin zama, bayan fitar Momy ya zauna kusa da ita ya ce Pretty ki dubi girman Allah da girman son da nake miki ki gayan gurin da kikaje aka yo ma Zainab wannan asirin nasa a karya, zalunci ba ƙyau kefa kike min wa'azi.


Takaici ya kamata hawaye ya soma zubo mata ya ce kash kinga matsalar ki to menene abin kuka,Ni ba abinda zan miki, ta ce nifa Dady ban mata komai ba ƙarya kake son in maka? Allah ban san komai game da abin da kake tuhuma ta ba,yaja tsaki aike aƙwai ki da gaddama ne, Allah in har baki faɗa ba sai na haɗa ki da Affa,ido ta tsura mishi a ranta tana tuna kafin aurensu tamkar ya haɗiye ta, yanzun kam gashi zaune yana ƙulla mata sharri,sharrin ma gaya masa aka yi yaci ya auna amma ya hau kai ya zauna, ta ƙwanta tare da faɗin ka gaya masa mana,ta cigaba gaskiya nifa na gaji ban iya faɗa ba bazan iya zama da mafaɗaci ba ka gane? Auren nan babu dole dama sai da nace a'a aka matsa min, wani sabon haushin ne ya kamashi ya ce cikin masifar tashi dama na sani ba sona kike yi ba, to amma ai sai kibar masu sona su so ni ko? Sai kije ki mana mugunta.


Aure kuma da kike faÉ—in babu dole shine kuwa dole domin ba saki cikin shi duk wahala dole ki jure, ya fita gara ma ki faÉ—a min gurin da ki ka yo wannan mugun abun dan kin san ni ba mazinaci bane bare in bi na waje bazanje ina kallon matata kuma batada amfani a gurina ba.


Ya fita ta ƙwanta tana kuka,jin shigowar Momy sai tayi tamkar tana bacci shiru tayi tana tuna kai aure yana da daɗi da wuya, amma wuyar tafi yawa, shiyasa kowa sai ya ce Allah ya bada zaman haƙuri Allah ya saɓa halayya, gaskiya ne ta tuna yanda Affanta da Umma kai har da yayyenta suka yi ta jaddada mata kalmar nan ta haƙuri,lallai dole tayi haƙuri.


         ***        ***       ***


Lokacin da Dady ya isa gida Zainab suna tare da Sunday ya soma zuga mata kira tsoro ya kama su amma sai ta ɓoye shi cikin wardrobe ta fito tamkar mai bacci tana mishi sannu da zuwa,ya zauna ta kawo mishi Hollandia mai sanyi ya ce ina Sunday ya shirya min table ina jin yunwa sosai,ta ɗan daburce,na na aike shi gidanmu, to bari inyi wanka in yaso ke sai kije ki min abinda zan ci tunda kin aike shi me ya hana ki aiki direba? Sunday ba ɗan aike bane,ta ce yi haƙuri,ya nufi ɗakinshi ita kuma ta nufi kitchen sai da ta tabbatar ya shiga ɗakin sannan ta fito ta buɗe Sunday,a sittin ɗin shi ya fito yanda yake gudun yaso bata dariya duk abinda aka ce babu gaskiya aƙwai matsala, Allah ka tsaremu da shiga halaka.


Momy da Dad suna ji da Ruƙayya tamkar ƙwai duk abinda take so shi za a bata har sai ya hau kanta yanzun an tashi daga tuwon Hajja an koma ɗan waken Umma kullum direba sai yaje ya karɓo, Hollandia ko abin har tsoro yake basu dashi take karyawa haka cikin dare, ta murmure sosai, wannan karon Dady satin shi uku sannan yazo.


Ya sameta tayi gayu sosai cikin material mai bulun fulawoyi tayi ɓul,ɓul gwanin sha'awa dan cikin yasata haske,ta ɗaure gashin ta daya sha gyara salon taje aka gyara mata, Momy sun tafi biki ita kaɗai ce a gidan ya zuba mata ido. Ta ce mishi sannu da zuwa ya hanya? Ya ce lafiya lau Pretty gaskiya kinji sauƙi kin yi ƙyau wannan karon zamu koma Abuja ko? Nan take tasha mur,tayi kicin-kicin da rai gaskiya kada ma ka soma babu inda zanje bayan haka ma ina jiran na haihu nayi gaba rayuwa da kai Dady ba zata yiwu min ba, dole in haƙura da kai.


Ya ce haba Pretty yanzun daga zuwa na,kin tareni da wannan maganar ko ruwa baki bani ba,in kina furta rabuwa tsakaninmu,ji nake tamkar kina watsamin ruwan zafi, babu wannan a tsarin aurenmu ki tuna wahalar da nasha a kanki,nasha wahala a kanki, ta ce shi ne yasa yanzun ka ke fanshe wahalar ka a kaina? Ya ce duk mu bar maganar naji baza muje Abuja ba, amma sai mu koma sashenmu in yaso in na tafi saiki dawo nan. Ta ce a'a nifa ba zanje ko'ina ba,me kake son su Momy su ɗaukeni? Ya ce to ni shikenan sai nayi ta zama cikin ƙunci alhalin ina da mata har biyu gaskiya Pretty ki duba dai.


A ranta ta ce tunda kanada buƙata ai dole ka ƙwantar da murya, inda maza suke bata mamaki kenan ko sarki ne yakan hura hancinshi a fada daya shigo gida gaban mace koda sa'ar ƴarshi ce dole ya yi biyayya ya ƙwantar da murya,tana tunani bata san ma har yazo kusa da ita ya zauna ba, sai dai ji tayi ya jawo ta jikinshi tayi mutsu-mutsu alamar ƙwacewa ya ce haba Pretty ki ji tausayi na mana? Ta ce cikin shagwaɓa baka ce nai muku asiri ba? Da yake namiji wawane wani sa'in sai ya ce nima Zainab ce ta ce min ke ce kikayi mana,ta ce kayi bincike ka gane, ya ce ni kaina bana gane kaina ƙwanan nan ban san meke sani yin wasu abubuwan ba,in ina son inyi tunani sai na kasa kome yasa? Ta ce kana addu'a,yayi shiru can ya ce gaskiya bana addu'a akan matsalar.


Ta ce ai kaji matsalar ga addu'o'i nan cikin husnil muslim kana dashi wasu ma suna kanka amma ka kasa, ya ce haka ne zan kula yanzun ya zamuyi? Ta ce likita ya ce fa na huta, ya soma kiran layin likitan ta tsura mishi ido dariya yake bata duk ya birkice sun gaisa da likitan ko kunya yake tambayar likitan ko zai iya kusantar matarsa yanzun don yaga taji sauƙi sosai likitan ya ce me zai hana? Yanzun ne ma zakafi samun natsuwa domin mace in tanada ciki ta kanfi sanda take amarya sai dai ka biya sannu a hankali.


Ya dubeta yana murmushi ina Momy ta je ta ce taje biki nasan ta kusa dawowa ya kamo hannunta zo muje in nuna miki wani abu a sasanmu,ya jata in so ya haÉ—u da so sai soyewa, abinda ya faru kenan, Dady kam ya shiga ruÉ—u. Sanda suka dawo sasan Momy ta jima da dawowa ta ce mijinki yazo ne shiyasa na neme ki na rasa naso in kira wayarki sai kuma na ganta a kan gado.


Kunya ta kama Ruƙayya ta sosa wuyanta ta ce eh dama shi ne yazo,shi kam dariya yake mata ya ce Momy ƴar taki taji sauƙi na ce ko zamu koma tare ne? Ruƙayya ta yi saurin cewa Allah nifa bazan je ba Momy, Momy ta ce in dai zaki bishi to ku tafi,ta ce ni bazan je ba ta turo baki Momy ta ce shikenan daina fushi.


Ƙwana uku ya yi sai sun fita wai gurin likita Momy har dariya suke bata ita za'ayi wa wayo, ya tafi da ƴar nutsuwa tunda tana yawan matsa mishi yanayin addu'o'i duk sati ɗaya sai yazo Momy tasa ta share sashen su in yazo sai ta koma can in ya tafi ta dawo gurin Momy,sai dai shegen faɗan nan na nan amma ba kamar da ba, Ruƙayya anyi ƙyau kamar ta fashe cikin ya fito gwanin sha'awa.


Zainab dai batasan Ruƙayya tana da ciki ba,sai wannan dawowar da Dady ya yi inda yake ce mata Pretty ta shiga watan haihuwar ta zai koma Kaduna kullum ya dinga zuwa Abuja ofis, ta ce ai wai kana nufin Ruƙayya ciki ne da ita? Ya ce au baki sani ba? Ai ta kusa haihuwa, kinga ke kaɗai na manta ban gaya miki ba.


Nan ta miƙe cikin tashin hankali lallai Dady ka kasa nema min magani balle in samu lafiya, amma ita kai mata ciki,koda yake ƙila nice bakason na haihu shiyasa, ya ce ke kada fa ki dameni, kinga nasan kin gama zubar da ƙwayoyin ki a titi zaki min surutun banza kodan kinga ban gaya miki sakamakon da likitan ya gaya min ba to tunda kinso ji yanzu zakiji ya ce bazaki haihu ba sakamakon shan ƙwayoyin hana haihuwa, magani kije can ki nema da kanki nidai tunda nasan lafiya ta qalau shikenan ya sa kai ya wuce.


Mantuwar da Dady ya yi itace ta dawo dashi gida,sai da ya bincike ɗakinshi kaf baiga jakar ba, kuɗi ne Naira miliyan uku da dubu ɗari baƙwai ba canji duk daloline na America zai biya cikon kuɗin wani inji daya siya da wani banki suka yi gwanjo amma ya nemi jakar ya rasa,ɗakin Zainab ya nufa yasan tana nan tana shegen baccinta da ta iya.


Gabanshi ne Ya yi mummunan faɗuwa mai zai gani Sunday da Zainab,sam basu san yana tsaye ba ma da ƙarfi ya furta innalillahi ya nufi gurinsu wani abin da yafi ɗaure mishi kai da sun ganshi amma sun kasa barin abin da suke, ya ɗauki waya ya kira Hajiyar Zainab ya ce tazo yanzun nan ya fito ya ja musu ƙofa don takaici hawaye yana zubo mishi, to dama asirin in sun fara masha'arsu sai sun kai awa biyar sannan zasu dawo hankalinsu kuma shigar su kenan ya dawo don haka har Hajiya ta zo ya ce ta shiga ɗaki gashi nan zuwa, ta zata faɗa sukayi tana shiga ta samu saɓanin haka.


Shi kam jami'an tsaro ya kira a waya sannan ya shiga ɗakin wani abin mamaki tana jansu tana duka suna komawa suna mannewa har sanda jami'an suka zo abin da yake faruwa kenan Hajiyarta sai kuka take yi sai da mutane suka cika ɗakin tankam sannan fa sun cika lokacin su da dukan da ƴan sanda suka dinga musu, Dady ya wuce ya ɗauko jakarshi da yazo nema a gefen gado,ƴan sanda suka tasa su suna kuka, Hajiya tana ta ba Dady haƙuri, ya ce ai haƙuri yana gurinku ko kina ganin zan kuma zama da annoba? Ai Zainab annoba ce kema ki fita kafin nasa a kama ki.


Ya zauna jagwaf akan kujerar ofis ɗin shi ya kulle kanshi ya yi kuka har ya gaji, Sunday yaronshi daya ba amana, Zainab matarshi wane irin ƙwazo ne baya dashi? Amma har sai ta nemi Sunday? Lallai mutum ba abin yarda bane.


Allah sarki Pretty matar da kullum yake zargin ta da yiwa Zainab asiri ya dubi hannunshi yanda ran nan ya wawwanka ma fuskarta mari,ya miƙe ya ji ma sam tsani wannan gidan don haka gidan hutawarshi ya nufa dake area 2 ya shiga ya ƙwanta bai jima ba bacci ya yi gaba dashi ya jima a ƙwance.


Sanda ya farka sai yana jin shi wani irin tamkar an sauke mishi wasu kaya masu shegen nauyi. Yana zaune komai ya dinga dawo mishi sabo yana ta nazarin abubuwa ya É—auko wayoyinshi missed calls barkatai cikin kowacce waya,na sirikinshi sun fi yawa,yana ganin girman mahaifin Zainab shi ne ma dalilin da yasa baya kallon wasu abubuwan da Zainab É—in take mishi a zaman su.


Don haka sai ya soma neman layin shi,sun gaisa inda Dady ya bashi haƙurin rashin ɗaukar kiranshi yana bacci ne ya ce ba komai dama shima ya kira shi ne dan ya bashi haƙuri game da abubuwan da suka yi ta faruwa nan Dady ya koro mishi komai game da irin zaman nasu.


Satar da ta dinga yi mishi kai har yanda ya ɗauki watanni baya iya saduwa da ita duk saida ya zayyane mishi a ƙarshe ya ce ya sake ta saki uku. Sam minista bai damu da hakan ba don shima yau ya gaji yana zuwa gidan zai sahale wa Hajiya sai dai albarkacin ƴaƴanta ta zauna a gidan,shi kam dama yana neman wata ƙanwar abokinshi,bazawara ce kuma yana da tabbacin yarinya ce mai hankali sai ya koma sabon gidan daya jima yana ƙerawa gidan da Hajiya ta ci burin zama,sai dai yasan yanzu kash sai haƙuri.


Garin Abuja ya yi mishi zafi ya tsani gidan nashi, don haka a wannan yammacin ya kira wayar Sabi'u ya shirya musu zuwa Kaduna, Sabi'u ya ce Oga zamuyi dare a hanya. Ya ce Allah zai kare,koda ya shiga gidan É—akinshi ya wuce kai tsaye be koyi wanka ba ya canza kaya ya É—ibi kuÉ—aÉ—e ya fita.


Sun isa Kaduna ana sallar isha'i, don haka suna tsayawa sai masallaci, RuÆ™ayya tana kitchen riÆ™e da kula ta fito zataje É—akin Momy, sai kawai sukayi kiciÉ“is da Dady ta yi sororo tana dubanshi ya tako zuwa gabanta, ganinshi tayi ya rame,ya kamo hannunta, Pretty ina Momy? Ta kalli sashen Dad ya ce tana saman Dad ne? Ta kaÉ—a a hankali ta ce Eh,ya tsurawa hannuwanta ido Pretty hannuwanki sun kunbura ne ko? Nan ma kai ta kaÉ—a ya ce ki zauna bari naga su Momy ya zaunar da ita tamkar mai É—ora Æ™wai kan kanfa. Ya yi sama da sauri,ita kam kullum tana  mamakin Dady tamkar mai aljanu.


Ta miƙe gara ma taje ta gyara musu gefen su don wancan Zuwan da ya yi irin masifar da ya dinga mata,wai shi baya son ƙazanta,tasan zai zo amma bata sa an gyara ba,da tace mishi wazan sa? Sai ya ce mata Oho miki, to Momy ƴan aikin ta bana ƙwana ba ne suna gamawa suke tafiya, girki tafi son tayi da kanta ita ba yara ba bare ta ce matsalar yara ko zasu ɓata gidan da dai sauransu.


Haka ta zage tana ta faman gyara, da É—akinshi ta soma duk da babu wani datti dama, sannan ta koma É—akinta zuwa falo.


Shi kam wannan lokacin yana can yana zayyane ma su Momy abubuwan da suka faru. Sun sha mamaki Momy ta ce ai dama rashin bincike a aure matsala ne, Dad ya ce aini na nemi sani da mahaifinta naji an yabe shi, Momy ta ce mahaifinta zama yake a gida? Dady ya ce shima yau ɗin nan ya ce zaije ya rabu da uwar shima ya gaji, Momy ta ce Allah sarki Ruƙayya nifa nasan zuwan nan ba lafiya ba, Dady ya ce Ni kaina Momy inna tuna marin da nayi mata duk sai naji kunya. Yanzun sai ka bata haƙuri cewar Dad, ya ce dole ma, duk tare suka sauko sun zauna falo suka ce ya kira ta,ya duba bata ɗakin Momy bata toilet bata kitchen yazo yana huci ya ce ban ganta ba, Momy ta ce duba sasanku,nan ya sameta tana ta goge goge ta gama shara da alama duk ta gaji.


Da gudu ya isa gurinta ya rungumo ta "haba Pretty, haba Pretty ya ya zaki zo kina aiki haka bayan kinsan cewa baki da ishasshiyar lafiya, daga yau bana son kina komai kin ji ko? Kallonshi kawai take.


Su Momy sukai mata bayanin komai tare da bata haƙuri akan duk abubuwan da Dady ya yi mata, shima Dady ya ƙara neman afuwa,ta ce ita dama bata riƙe shi a ranta ba,koda suka ci abinci suka nufi sashensu ta kasa sakin jiki dashi, ya ce haba Pretty na ni ne fa dadynki mai son nan naki kin tuna? Ki share komai ki tuno da farkon aurenmu, yanzun na zama naki ke ke ɗaya ko? Ya ɗaga mata gira.


Ta dubeshi da murmushi shikenan Dady komai ya wuce na yafe maka.


"Yauwa My Pretty, nagode."


Ya Æ™ara matsowa daf da ita yana yi mata wani irin kallo mai tattare da tsananin so da Æ™auna. Itama kallon nashi take yi cike da wani irin yanayi mai cike da tsantsar so. 


"Come to me My Pretty,I want as some thing please come." Murya ƙasa-ƙasa yake faɗar maganar,a hankali tabi umarninsa kafin wani lokaci suka shiga farantawa junansu rai, sai gashi sun dawo kamar yau ne daren farkon su na amarci.


          ***       ***      ***


Haka suka cigaba da zaman su shi da Pretty cikin ƙwanciyar hankali da farantawa juna, Allah ya basu ƴaƴa biyu mace da namiji ƙyawawa dasu.


Hankalin kowa ya ƙwanta, kowa sai farin ciki yake, yanzu Dady bashi da wata sauran damuwa. Ruƙayya ta zage damtse kullum faranta ran Dady take. Wannan shi ne abin da yasa iyayensu suka cigaba da yi musu addu'a tare da fatan alkhairi cikin alfahari da jin daɗin zaman aurensu.


Alhamdulillahi


Ƙarshen littafin FIN ƘARFI


Taku Halima Abdullahi K Mashi.

No comments