Diyam Complete Hausa Novel
[1/2, 8:57 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
To my daughter Haleema, May you forever be blessed.
Bismillahir Rahmanir Rahim
Godiya ta tabbata ga Allah da ya bani damar fara wannan rubuta, ina rokonsa ya bani ikon rubuta alkhairi ya kuma haneni daga rubuta sharri. Allah ya sa wannan rubutu ya amfane ni da duk wanda Allah ya bawa ikon karantawa.
Littafin DIYAM kyauta ne, ina fatan ya zamanto min sadakatujjariya har bayan raina. Na sadaukar da wannan littafin ga masoyana, na fili dana boye.
Diyam is a total work of fiction, in yayi dai dai da labarin ki/ka to coincidence ne ba wai da niyya ba ne.
Diyam littafi nane, mallaka ta ce, duk wanda ya juya min littafi ko ya siyar min ba tare da sani na ba shi da Allah.
Just follow my pen for I assure you, you are going to fall in love with DIYAM.
Episode One
Madaidaicin dakin karatun mai dauke da dalibai 36 yayi shiru bakajin motsin komai sai na takardu, sai kuma very clear voice din lecturer da take gabatar da lecture ga dalibai masu karantar ilimin law a makarantar Blavatnik school a cikin Oxford University. Darasi ne suke yi akan marital laws, inda malamar take yi musu bayani dalla dalla game da dokokin da suka shafi auratayya. Saboda kasancewa daliban sunzo ne daga mabanbanta kasashe, wannan yasa malamar take daukan kasashe daya bayan daya take musu bitar dokokin kasashen da niyyar in sun gama sai su hadu suyi comparing aga wadanne ne sukafi kyau kuma wadanne chanji ya kamata a samar.
A yau ne kuma malamar tashigo kasashen nahiyar Afrika. Ta fara da Nigeria, the giant of Africa. A nutse ta fara karanto wa daliban dokokin da kasar Nijeriya take dasu wadanda suka shafi auratayya. Suna tsaka da daukar darasin ne suka ji snicker, malamar ta dakatar da karatun da take yi ta dago kanta a tare da duk sauran daliban suka kalli sashen da dariyar ta fito.
A extreme end of the class room, sitting alone like an abandoned island, wata kyakkyawar budurwa ce wadda kallon farko in kayi mata daga nesa zaka ce kyakykyawa ce, in ka matso kusa da ita kuma sai kaga tafi yadda kake tunani kyau, as kana cigaba da kallon ta kyawunta yana cigaba da bayyana a gare ka. Da yawa a makarantar ana yi mata kallon balarabiyya amma nigerians suna ganin ta suke fahimtar cewa tasu ce, kabilar fulani ce, kabila mai dangantaka da larabawa. Daga ganinta zaka fahimci ita kanta bata san cewa tayi dariyar ba. Shirun da taji ajin yayi da kuma feeling na cewa ana kallonta ya saka ta dago kanta da sauri, dara daran idanuwanta a bude kuma ta saka su a cikin na malamar da take tsaye a gaban desk dinta. Suka tsaya suna kallon kallo sannan malamar tace mata "why do you laugh? Are you finding this funny?" Ta girgiza kanta da murmushi a gefen kumatunta. Malamar ta koma kusa da podium ta tsaya tana kallonta sannan tace "where are you from?" Still kanta a kasa tace "Nigeria" malamar tace "menene ra'ayinki game da wadannan dokokin na auratayya a Nigeria. Kina ganin sunyi dai dai ko kina da gyara?" Shiru ta sake yi na wani lokaci, sannan tayi karamar dariya tana girgiza kanta, fuskarta na nuna cewa akwai abinda yake damunta, suddenly kuma sai tayi magana "bani da gyara ma'am. Saboda all those laws da kike lissafawa a rubuce kawai suke, maybe for the sake of the likes of you da zasu nema for educational purposes, amma ba wai amfani ake yi dasu ba" malamar looked interested, tace "so, can you tell us the situation of marriage in Nigeria?" Nan take murmushin fuskar budurwar ya dauke, ta hadiye wani abu a makogwaronta sannan ta sunkuyar da kanta tana kallon rubutun da yake gabanta. "You have a very beautiful handwriting kanwata" taji muryarsa a kunnenta as clear as if yanzu yake gaya mata.
Ta dago kanta tace "in Nigeria ma'am, northern Nigeria to be precise, marriage is just like a form of legal slavery" gabadaya hankalin yan ajin ya koma kanta, har wadanda ada suke yan rubutun su yanzu sun juyo suna kallonta. Ta cigaba cikin yaren turanci mai dauke da nigerian accent "tabbas kafin aure akwai kalmomin i love You, amma yawanci a baki suke tsayawa basa karasawa zuciya, daga zarar anyi aure miji will have a feeling similar to feeling din da master yake ji a lokacin daya sayi slave. Like since I pay your dawry it means like I own you, you belong to me. Sai ya manta da cewa shi da matar belong to each other. Wadansu mazan ko first year ba zata wuce ba zasu juye su zamarwa matar like total stranger, like bata taba sanin sa ba a rayuwarta.
"Na sani cewa kusan more than 80% na mutanen mu na arewa musulmai ne, kuma na sani cewa a Alqur'ani ance 'alrijali qawwamuna alan nisa'i' miji shine sama akan mace, amma kuma da ubangiji yayi gaba kadan a Alqur'ani sai yace ya sakawa maza wannan qawwamar ne saboda su ya dorawa nauyin ci da sha da sutura da muhalli. Amma a halin yanzu more than rabin mazan mu basa iya daukan wannan nauyin da Allah ya dora musu. Mata da yawa su suke ciyar su shayar su kuma tufatar da kansu da yayansu wani lokacin ma harda mazajen na su. Mace zata fita ta je office neman kudi ko kuma ta fita saro kayan sana'arta sannan ta dawo ta girka abincin data siyo da kudinta ta, tayi shara da wanke wanke da wankin kayanta dana yaranta da na mijin, kayan kuma da ita ta siya da kudinta, ta taya yaranta yin homework din da aka basu a makarantar da ita take biya musu kudin makaranta, sannan kuma mijin yayi expecting zata kai masa ruwan wanka tayi masa ta shirya shi tayi masa tausa sannan ta biya masa bukatarsa a shimfidar auren su".
"Mace ce zata yi ciki, ta haihu, wata ma hatta ragon suna da kayan fitar suna ita zata siya, ta shayar da dan ta ciyar dashi da komai amma idan rabuwar aure tazo sai mijin yace 'ajjiye min yayana'. Tana ji tana gani, tana kuka yayanta suna kuka, haka za'a raba su mijin ya dauka ko daya ba za'a bata ba, kuma a karshe shi din daya dauka sai yaje ya kaiwa matarsa ita kuma ta azabtar dasu ta bautar dasu saboda ba ita ta haife su ba. Yara da yawa sun rasa ransu saboda irin haka, wadansu sun salwanta, wadansu sun koma almajirai, wadansu yan daba saboda babu tarbiyya, babu soyayyar iyaye". Ta goge hawayen da ya taru a idonta ta cigaba
"That's why am here in Oxford, that's why am studying law. Saboda in tabbatar cewa babu wata mace a Nigeria da zata sake shan wahala a hannun namiji"
"Ohh shut up please"
Duk class din suka juya suna kallon wanda yayi magana. Ta san shi, tana ganin sa a ajin amma basu taba magana ba dan haka ko sunansa bata sani ba kuma bata da interest din sani. Ya juyo yana kallonta yace "just because kin zauna a kusa da wadanda basu ji dadin aure ba bai kamata ki zauna a nan kina fadin maganganu marasa dadi akan kasar mu ba" ta daga gira daya sama tana kallonsa tace "wacce kasa kenan?" Yace "wacce kike magana akanta" tace "you don't look like Nigerian, and definitely not a northerner" yace "ohh but I am" tace "which part?" Yace "Abuja" ta dan rufe bakinta tana dariya tace "but Abuja is not in the northern Nigeria, so you shut up".
Ya kara bata rai musamman ganin dariya a fuskar daukacin yan ajin. Shi dai yasan duk da shi ba dan arewa bane ba amma ba zai bari a zauna a yaga arewa har haka ba, for his mother is from the north, his only sister now lives in the north, his uncle too, dan haka ya san hakkinsa ne ayanzu ya gayawa mutane cewa karyace kawai yarinyar ta shirya musu, maybe dan tayi suna.
Yace "I may not be born in the north, but my mother is a northerner, kuma...." Tace "was she born and raised in the north?" Dan shiru din da yayi yasa ta fahimci no ce amsar sa, ta daga kafada tace "then she too is not a northerner" da sauri yace "her father was" ta sake cewa "born and raised?" Ya mike tsaye, frustrated, yace "what does it matter?" Tace "everything. In kana son sanin halin da al'umma suke ciki you need to live with and study them". Ya sake yunkurowa da niyyar sake kokarin kare mutuncin kasarsa kamar yadda yake tunani amma sai ya zamanto period din ta kare. Yayi kwafa sanda malamar take bayanin cewa zasu dakata anan sai next class zasu cigaba.
DIYAM..........writing
In anyi comments da yawa zanji dadi, kuma zan fahimci ana son in cigaba.
[1/2, 8:57 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Two
Washegari basu da madam Sally, malamar da tayi musu lecture din jiya, a takaice ma lecture din safe kawai suke da ita shikenan sun gama. Wannan yasa suna fitowa kowa ya fara kokarin tafiya gida dan gabatar da al'amuran sa na yau da kullum. Yarinyar jiya ce ta fito a karshe, tana rungume takardu a kirjinta da hannu daya daya hannun kuma tana rike da wayarta, tana ta waige waige kamar me neman wani sai kuma ta fara tafiya a hankali tamkar mai jin tsoron taka kasa.
Daga inda yake tsaye yana hango yadda daliban suke fitowa daya bayan daya. Ya dauko pack din cigarette a aljihunsa da lighter ya kunna yayi mata dogon zuka ya lumshe ido. Deliberately ya riga kowa fitowa saboda yana son ya ga fitowarta, yana son su cigaba da maganar jiya, yana so kuma ya ja mata kunne akan tasan maganar da zata fada tasan kuma a inda zata fada. Ya danyi karamin tsaki. Haka kawai tana neman ta zubar masa da class a cikin mutane dan duk friends dinsa sunsan shi ɗan Nigeria ne kuma zasu dauka abinda ta fada gaskiya ne.
Yana kallonta ta fito, ta danyi dube dube sannan ta taho direct zuwa side din da yake, tana tafiya a hankali tamkar mai kirga takunta wanda hakan ya bashi damar karewa siffarta kallo, 'too beautiful' yayi deciding, 'too beautiful for my taste'. Har tazo ta wuce shi bata ko lura dashi a gurin ba, ya bata dama ta danyi nisa sannan ya yar da cigarette din hannunsa ya bita da dan sauri yace "hey" ta dan tsorata kadan sannan kuma ta kalle shi ta dauke kai ta cigaba da tafiya, ya daidaita takun shi da nata ya sake cewa "hi" ta dakata tana kwallonsa cikin ido ba tare da ko alamar tsoro ba tace masa "Assalamu alaikum" ya dan shafa kansa yana jin duk confidence din da ya ke dashi yana draining. Her eyes makes him uncomfortable. Jin bai amsa ba yasa ta sauke idonta kasa ta cigaba da tafiya. Ya bita a baya yana cewa "my name is Sadiq, Sadiq Abubakar Sadiq" ya sake shafa kansa yace "my God, this is so awkward, I always feel like this duk sanda nake introducing kaina. I hate my name. Na rasa dalilin da yasa iyayen mu suke son lallai sai sun saka wa yayansu sunan iyayen su. I mean, it make the name only circles and remains in the family. I always wish I can change my name" ta daka ta ta tsare shi da ido, ya dauko handkerchief a aljihunsa ya goge fuskarsa duk kuwa da cewa ba gumi yake ba, he obviously looked nervous, duk planning din da yayi na irin maganganun da zai gaya mata ya gudu ya barshi. A zuciyarsa ya gode wa Allah da ya zamanto su kadai ne a gurin. Yayi ajjiyar zuciya yace "I am talking too much, aren't I?" Ta girgiza kai kawai sannan a nutse tace "in my religion, Islam, an bawa mutum damar chanza sunansa in baya so, what you only need to do is ka sayi rago ka yanka da niyyar ka chanza suna, sai ka kira mutane su shaida, shikenan. But I don't know ko naka addinin ya yarda da haka" he was stunned, wato kallon wanda ba musulmi ba take masa, how can she even think that? Ya bude baki zaiyi magana amma ya kasa cewa komai, sai daya hadiye wani abu mai daci a makogwaronsa sannan a karshe yace "I am a Muslim also" ta dauke kanta tace "sorry, my bad" cikin jin zafin maganar ta yace "me yasa kika yi tunanin ni ba musulmi ba ne ba?"
Ta kalle shi tun daga kan brown wind tossed hair dinsa, his cigarette stained lips, katuwar head phone din dake kunnuwansa, shirt dinsa da take dauke da katoton hoton Lady Gaga, wandon sa da yake tsatstsage daga guiwa, zuwa takalminsa da yafi kama dana sojoji, sannan ta daga gira daya sama tace "na farko you don't dress like a Muslim, na biyu nayi maka sallama baka amsa ba, na uku muslims don't complain about their parent's choice of name, Abubakar Sadiq suna ne mai dadi kuma mai daraja" he was speechless, tunda yake ba'a taba yaga shi irin yau ba, me wannan yarinyar take tunani? Wacece ita? Babu abinda yake so a lokacin irin ya hada wa kyakkyawar fuskanta jini da majina. Ya dunkule hannu amma sai jikinsa yayi betraying dinsa har ta juya ta barshi a tsaye, instead, sai yaji bakinsa yana furta "baki gaya min sunanki ba" ta juyo tace "why?" Ya maimaita "why? I just told you my name that's why" tace "I didn't ask you for it" daga haka bata kuma cewa komai ba sai ma kara sauri da tayi.
Ya dunkule hannunsa ya naushi iska, ya rankwashi kansa yana jin haushin kansa sai kuma ya shafa gurin daya rankwasa alamar yaji zafi, gaskiya ya fara sanyi da yawa, har shi mace zata yiwa haka? Who is she?
Daga bayanshi yaga wata yarinya tazo ta wuce shi da sauri tana kira "Diyam!! Wait for me" yaga ta tsaya ta jirata ta karaso sannan suka cigaba da tafiya tare. "Diyam" ya maimaita, how can someone name his child water? Me parents dinta suke tunani? sai kuma ya koma gefe ya samu guri ya zauna, ya dauko sigari ya kunna, ya gyara zaman headphone dinsa ya zuki tabarsa ya lumshe ido yana lissafa hanyoyin da zai rama abinda Diyam tayi masa.
*****. *****. *****
Diyam taji kiran da akayi mata, ta juya suka hada ido da kawarta Judith, kawarta ce tun a Nigeria suka hadu lokacin suna shirye shiryen tahowa UK, a lokacin da suka yi registration ne Diyam ta fahimci cewa Judith tana neman gidan zama sai kawai ta jata suka zauna tare a nata gidan, tare da Murjanatu. Tayi mata murmushi lokacin da Judith ta karaso suka jera suka cigaba da tafiya a tare. Judith tace "if you don't mind me asking, were you talking to that guy?" Diyam tace "yes I was, what about it?" Judith ta danyi dariya tace "it is just that you never talk to anybody" Diyam ma tayi dariya tace "believe me, it wasn't such a good talk. Am sure that guy is never going to talk to me again" suka yi dariya baki daya, Diyam ta dafa goshin ta tace "God, am so boring, how do you guys manage living with me?" Judith tace "it is never easy" haka suka cigaba da tafiya suna hira akan halayen Diyam.
A kafa suka tafi estate ɗin da gidan su yake, suka je block E suka hau lift zuwa fifth floor inda apartment dinsu yake. Judith ta fito da key din hannunta ta bude kofa. Suna shiga a parlor duk suka zube a kasa saboda gajiya. Murjanatu ta fito daga kitchen da spatula a hannunta tana kallonsu, black beauty ce, mai dan karamin jiki, manyan idanuwa da cikar gashin gira. Kana ganinta zata yi maka kama da irin shagwababbun yaran nan wadanda suka taso cikin naira, tace "shi yasa naki zuwa yau. Haka kawai akan lecture daya bazan sha wannan wahalar ba" diyam ta kalleta tace "kinyi missing, alot" Murjanatu ta karkata kai gefe tace "at least ai nayi muku girki ko? So what you should be saying is 'thank you'" Judith ta mike tayi pecking Murjanatu a cheek dinta tace "thank you".
Suna cikin cin abincin, wanda Diyam chakula kawai take kamar mai cin magani tana ta complain din how much she misses abincin gida. Tace "I can give anything, I mean anything, dan in samu tuwo in ci" Murjanatu ta tabe baki tace "niko ko missing tuwo banyi ba, sam dama ni ba sonshi nake yi ba" Wayar Diyam tayi kara ta kalleta kawai ta dauke kai. Judith ta dauka tana kallon sunan mai kiran har ta katse sannan ta ajiye tace "ban taba ganin marar zuciya irin mutumin nan ba, wulakancin da kike masa Diyam ya isa haka" Murjanatu ta daga hannu tace "hey, yayan nawa kike cewa marar zuciya?" Tana yin shiru wayar ta tana yin kara, ta langwabar da kai tace "Please Diyam, kinga ya kira a wayata. Please just for today" Diyam ta harare ta bata ce komai ba, Murjanatu ta daga wayar ta gaishe da wanda ya kira tana kallon Diyam tace "lfy lau take, yanzu muka dawo daga lecture wallahi duk mun gaji yaya. Eh bata zuwa da motar wai exercise ne zuwa school din. Eh shikenan for today. Gata nan tana cin abinci. Bata ci da yawa wallahi yaya, wai tuwo take so. Ah ah ni ban sani ba wallahi. Yaya ni Wallahi ban iya tuwo ba. Okay, sai anjima" ta ajiye wayar tana turo baki fuskarta kamar zata yi kuka tace "wai inyi miki tuwo yau da daddare ince with love from him" duk suka yi dariya, Diyam ta tashi tana rawa tana yiwa Murjanatu gwalo ita kuma ta dauki pillow ta bita da gudu suka shige corridorn da bedrooms dinsu suke.
Diyam.......... writing
[1/2, 9:01 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Three
Bayan tafiyar su Diyam, ya jima zaune shi kadai, yana ta sakawa yana kwancewa yana kuma zukar hayaki zuwa hunhun sa. Sai da ya ga kwalin ya kare sannan ya jefar da shi ya duba agogon hannunsa yayi tsaki ya mike. Cab ya tare zuwa hotel din da ya ke. Yana shiga dakin ya zauna akan gado yana kare wa dakin kallo kamar yau ya fara ganinsa, idonsa ya sauka akan hoton wata yar kyakkyawar budurwa akan study table dinsa tana murmushi. Ya lumshe idonsa ya bude. She have been the reason for everything daya ke ciki a yanzu, for all his pain and his agony. Ya dauko wayarsa yayi dialing number dinta for the hundredth time amma yanzu ma kamar ko yaushe bata dauka ba. He wandered me yasa ba tayi blocking dinsa ba dan gwara ya kira bata shiga ba akan ya kira ba'a dauka ba, meaning ta gani kenan, meaning tasan all what he is going through but she just doesn't care.
Fatima sunanta, Khausar suke kiranta, he had been in love with her for as long as he can remember, maybe tun da yasan menene love din but he failed to tell her. Daga baya kawai sai yaji labarin wai zata auri brother dinsa, that has been the beginning of his agony, wannan ne asalin dalilin fara shan sigarin sa. Yayi iyakacin kokarinsa tun a lokacin dan ganin cewa ya cire ta a ransa and he succeeded a little, but then sai auren baiyi da brother din nasa ba and his brother ended up marrying another. Wannan turn of events din ba karamin faranta masa rai yayi ba, he saw it as another chance na auren wadda yake so.
Shekara guda kenan da faruwar hakan. A cikin shekarar ne kuma yayi failing terribly in his course of study a Abuja, amma sai ya alakanta hakan da cewa dan baya son course din ne, yace yafi son yabi footprints din maternal grandmother dinsa wadda ta kasance lawyer, da kyar yayi iyakacin kokarinsa har ya samu aka barshi ya taho UK karatu duk da cewa iyayensa basu so hakan ba sunfi son ya zauna tare dasu amma saida ya taho tare da daurin gindin kakar tasa, yayi hakane saboda ita, saboda Khausar, for she now lives in UK tare da auntyn su. But sai me kuma? He realized bayan zuwansa cewa ai she is already dating his cousin kuma, wannan yasa ya daura damarar ganin ko sama da kasa zasu hadu sai ya raba wannan relationship din, wannan ya jawo rigima ba yar kadan ba tsakanin sa da cousin dinsa Ayan and he failed miserably. A karshe Khausar looked into his eyes and said "I will never marry you ko mazan duniya sun kare", and that made him mad, so mad that when his aunty tries to resolve the issue he looked into her eyes and said "go to hell".
Sati biyu kenan da faruwar hakan. Tun daga ranar ya hado kayansa ya dawo wannan hotel din da zama shi kadai. Kuma tun daga ranar babu wanda ya neme shi kaf family dinsu not even his Mami.
But wannan duk ba shine babban problem dinsa ba. Problem dinsa shine satin sa daya da barin gidan auntyn sa parents dinsa sukayi blocking dinsa out of their family bank account. Tun tashinsa da wannan account din suke amfani gaba daya gidan, kowa yana da access da shi sai dai kawai a karshen wata kayi bayanin abinda kayi da kudin daka dauka, yanzu babu. Shi kuma ba aikin yi ba, dan haka blocking dinsa daga family account ya mayar dashi almost koboless. Bashi da komai, hatta kayan abinci bashi dasu kuma kudin siyan abincin nasa has almost run out, zuwa karshen satin nan yasan ko na abinci bashi dashi.
Yasan wannan duk hikimar Mami ce, they want to fish him out ya kawo kansa ya karbi laifinsa, shi kuma yana jin tsoron yadda hukuncin sa zai zama, ba zaiji da dadi a gurin daddyn sa ba. Kuma yasan he have lost Khausar for good. Yayi biyu babu. Abinda yake bukata a yanzu shine karfin gwuiwar facing family dinsa, accepting mistake dinsa da kuma repenting, but to do that yana bukatar courage, yana bukatar wani yayi masa magana at least ko fada ne ayi masa a gaya masa yayi ba dai dai ba.
Bai san mai yasa yarinyar dazu ta fado masa a rai ba, Diyam. Ya kwanta ya rufe ido yana tunano fuskarta, tabbas tana da courage. From her looks, yadda take ware kanta daga cikin mutane zuwa yadda turancinta bai gama nuna ba yasan cewa she is from a poor background, maybe irin yayan talakawan nan ne da gwamnati take dauka take basu scholarship suke tahowa kasashen waje suyi karatu. But she really does have courage, daga yadda tayi magana rannan a class da kuma yadda tayi facing dinsa straight in the eyes ta gaya masa maganganu. Har dare yarinyar tana cikin ransa, amma kuma ya kasa yanke mata hukunci a ransa.
Washegari kamar kullum Diyam ta riga kowa tashi. Tayi wanka tayi alwala tazo ta bude al'qurani tana bita har akayi assalatu sannan ta je dakin Murjanatu ta tashe ta tazo ta tayar da sallah. By seven har ta gama komai, ta dumama sauran tuwon jiya ta zauna tana ci Judith ta fito tayi joining dinta sannan Murjanatu ta fito itama, but sai taki cin tuwon ta hada tea da bread ta sha. Suna yi suna hirar abubuwan da suka shafi karatun su, Murjanatu tana ta mitar takura musu da Diyam take yi suke zuwa school a kafa bayan ga mota an ajiye musu musamman saboda zirga zirgar su.
Suna shiga makaranta Murjanatu tana haki ta kalli Diyam tace "you and yaya na deserve each other. Kafiya ce daku da naci akan abinda kuka sa kanku. At the end kuma ku wahalar da wanda yake tare daku. Ni dai daga yau na daina turturing kaina wallahi, motar zanke shigowa koda ni kadai ce" Diyam ta daga gira daya tace "ba sai ki shiga ba, in kin iya driving din" suka yi dariya tare da Judith, ita kuma Murjanatu ta tura baki tayi gaba tana kunkuni ta barsu tunda ba department dinsu daya ba, suna dan yin gaba kadan suka rabu da Judith itama sannan Diyam ta karasa department dinsu ita kadai.
Tun daga nesa ta gane shi. Yana tsaye kamar kullum da headphone a kunnensa da kuma sigari a hannunsa. Ta duba agogon hannun ta taga it is not 8:00 yet amma har ya fara zuke zuke, maybe ko breakfast baiyi ba. Ta dauke kai ganin cewa bai ganta ba dan kamar yayi zurfi cikin tunani.
Har suka yi nisa da lecture din tana ta saka ran ganin ya shigo amma shiru bai shigo ba, sai da aka fara concluding sannan ya shigo dan haka ko zama bai gama ba malamin ya fita, and she felt sorry for him. Suna nan wani malamin ya sake shiga ya gama ya fita daga nan kuma zasuyi one hour break sai su sake wata shikenan. Ta fita ta nemi coffee shop ta zauna aka kawo mata coffee da cake taci duk da dai ba yunwa take ji ba but she just need to eat something saboda suna da wata two hours lecture din, Madam Sally. Tana zaune ta hango wucewarsa yayi hanyar gate. She wonders ina zaije tunda suna da wata lecture din? Sai kuma ta daga kafada tana mamakin me yasa ta damu da business dinsa.
Har suka tashi a ranar bata kara ganin sa ba. Da daddare suna cin abinci ta bawa su Murjanatu labarin encounter dinta da guy din tace "I am just feeling sorry for him. He obviously is distracted, confused maybe" Murjanatu ta harare ta tace "ni dai babu ruwana. Daga tausayi kuma sai muji wata magana ta daban. Kinsan in yaya yaji wannan maganar zai iya harbo nuclear bomb ya tarwatsa Oxford gaba-daya" Diyam ta daga kafada tace "Allah yasa uranium zai harbo ba nuclear bomb ba. I will talk to whoever I want to talk to" Murjanatu tace "you are not going to give my brother a break are you?" Diyam ta mike tsaye tace "no i am not, har sai yayi abinda nace masa" Murjanatu tayi murmushi tace "maybe baki san shi ba kamar yadda kike tunani" Diyam ta wuce daki da sauri tana jin zafi yana taso wa a zuciyarta.
Da safe basu da lecture da wuri dan haka suka yi baccin su sosai. Sai after ten Diyam ta tashi ta fita parlor ta tarar Judith tana kitchen tana hada musu breakfast. Ta dawo dakin ta ta shiga wanka. Tana fitowa wayar ta tana ringing amma ko kallonta bata yi ba ta dauke kanta ta cigaba da shiryawa amma a zuciyarta tana mamakin yadda yake keeping track din komai nata, yasan sanda take da lectures yasan kuma sanda take free. Wayar tana katsewa taji text ya shigo, ta dauka takaranta, sakon barka da safiya ne mai hade da tsadaddun kalaman da sai da suka huda zuciyarta amma sai kawai ta tabe baki ta ajiye wayar. Ita dashi a ga wanda yafi taurin kai.
Diyam......... writing
[1/3, 10:07 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Four
Tana saka kaya Murjanatu ta shigo dakin, daga ganin fuskarta Diyam tasan akwai problem, ta ajiye skirt din hannunta tana bawa Murjanatu data zauna a kan gado dukkan attention dinta. Ta daga gira daya sama tace "me yace kuma?" Murjanatu tace "he asked me about Judith" Diyam ta hade rai tace "what about her" Murjanatu tace "he asked wai bata kawo mana maza gida? Na gaya masa bata kawo wa but he didn't sound convinced." Ta sunkuyar da kanta kasa tace "am afraid he is going to send her away" Diyam ta dafe kanta tana zagaye dakin da bacin rai a fuskarta sannan tace "tell him nace Judith is my friend, if he wants to get to her he will have to go through me. Ni na kawo ta gidan nan, in yana son ya kore ta sai ya fara kora ta tukunna" Murjanatu ta saka hannayenta biyu ta toshe kunnuwanta tace "ba dani ba, bani Murjanatu ba. Uwata ta daina haihuwa ballantana ta sake haifo ni" Judith ta bude dakin ta leko kanta tace "hey girls, food is ready" sai kuma ta tsaya tana kallon yadda suke kokarin kakaro murmushi.
A bayan lecture hall dinsu ta hango Sadiq. Shi kadai kamar kullum, da sigari a hannunsa kamar kullum, tayi saurin dauke kanta ganin yana kokarin juyowa. Amma sai ta tsaya a kofar hall din bata shiga ba tana so taga yau zai shiga ko yauma zamansa zaiyi a waje. Sai da aka kusan fara lecture din sannan ya taho, a gabanta a jefar da sigarin hannunsa ya saka kafa a murje ta, zai wuce Diyam tace " you know smokers tend to die young ko?" Ya kalleta for some seconds, ya busa mata hayakin bakinsa yace cikin husky voice "says who? I can't believe malama kamar ki ta yarda da wannan saying din. Kin manta kaddara? Ina islamiyyar taki ta tafi?" Ta sa hannu ta kade hayakin daya huro mata tace "maybe ni da kai munyi understanding kaddara differently. Tell me why do we pray? Why do we struggle? Me yasa muke neman duniya kuma muke neman lahira in dai har an riga an rubuta komai, me yasa ba zamu kwanciyar mu ba mu jira abinda aka rubuta mana yazo ya same mu. Yes kaddara rubuyacciya ce, major abubuwan da zasu faru a rayuwar mu a rubuce suke but what is in between depend on choices din da muke making. Wannan shine fahimtata. Yes, kamar yadda ka fada shekarun da aka rubuta maka ba zasu chanza ba amma how you are going to spend them depend on you, ko dai kayi spending dinsu healthy and happy in ka daina shan sigari ko kuma kayi spending dinsu with lung cancer in ka cigaba da smoking" ya kalle ta daga sama har kasa yace "go to hell, both you and your preaching" ya shige class din ya barta a tsaye. Taji zafin maganar sa amma sai ta hadiye ta bishi a baya.
Suna shiga class din wani guy ya kalli Sadiq yace "the Nigerian guy. Why do you skip madam Sally's class yesterday, don't you want to depend your country anymore?" Sadiq yayi banza dashi ya shige ya samu guri ya zauna. Sannan yan ajin suka juyo gabaki daya suka zubawa Diyam ido, ta yi gyaran murya tace cikin harshen turanci "abinda na fada rannan gaskiya ne, gaskiya ne based on sani na. Shima kuma musa min din da yayi gaskiya ne based on sanin sa. We may have come from the same country but we live in different worlds. Muna zama cikin different mutane, muna kallon rayuwa from different perspectives. My being right doesn't makes him wrong. You as potential lawyers should know that" duk yan ajin suka kada mata kai cike da gamsuwa sannan ta wuce ta shige seat din karshe ta zauna.
Madam na shigowa ta fara tambayar Diyam "will you like to continue with that day's argument?" Diyam ta girgiza kai tace "no ma'am, it's okay" ta juya gurin Sadiq tace "what about you, are you satisfied as well?" ya gyada kai yace "am okay ma'am. We now understand each other" sai ya juya a hankali ya kalli Diyam, itama ta dago kai suka hada ido and she smiled at him, a take ya fahimci cewa she have the brightest smile he have ever seen.
Bayan sun gama dukkan lectures dinsu, ta fito tana tsaye tana jiran Murjanatu sai gashi ya taho, ya tsaya dan nesa da ita kadan yace "waiting for a friend?" Ta daga murya tace "yeah" sai kuma taga ya zo zai wuce ta, tace "my name is Haleema. Haleema Usman Kollere. But people call me Diyam" ya gyada kai yace "I am Sadiq, Sadiq Abubakar Sadiq. Most people call me Bassam. You can call me that as well".
Tayi murmushin ta mai kyau tace "nice to meet you Bassam" ya danyi dariya yana jujjuya kai yace "You have a beautiful smile, very beautiful. Ban san me yasa ba kya yawan yinsa ba. Ta daga gira daya sama tace "if it is beautiful than it is precious kenan. Abu mai tsada kuma kasan ba'a ko ina ake ajjiye shi ba" ya sake dariya, his eyes twinkling, amma bai ce komai ba, tace "and you. Ban dauka ka iya dariya ba" ya gyara fuskarsa yace "believe me, I do laugh alot. Yanzu ne dai I am in kind of not laughing situation. But na miki alkawari in na fita daga ciki we will laugh more" daga haka ya juya da sauri ya bar gurin.
Yana tafiya Murjanatu tana karasowa. Tana kallon bayansa tace "who is that guy? Amma ya hadu fa" Diyam tayi murmushi bata ce komai ba, Murjanatu ta sake cewa "ko shine rannan kuke maganar sa da Judith?" Suka jera suna tafiya da Diyam tace "yeah shine" Murjanatu ta bata rai tace "then it is official, gaskiya ina taya yayana kishi. Lallai ma Diyam din nan" ta turo baki, Diyam tace "oh ashe baku hadu ba daga ke har yayan naki tunda insecurity yana damunku. Ashe kujerar taku bata kafu ba, ai hausawa sunce fargaba asarar namiji" Murjanatu ta harari bayan Bassam da har yanzu suna iya hango shi tace "ohh dama wancan namiji ne? Ai na dauka macece ta aske kanta ta saka wando. Ai wannan yana ganin yayana zai narke a gurin dan tsoro. Wannan daga ganin sa rainon madara da cerelac ne, yayana kuwa tuwon biski yaci da kunu dan haka ba sa'an sa bane wallahi" Diyam da take ta dariya tace "naga alama kam. Tuwon biskin ne yasa kansa yayi tauri da yawa" ta fada tana lakucewa Murjanatu hanci, Murjanatu tace "ouch, sai kin nane min hancin kinsa na rasa mashinshini?" suka yi dariya baki daya, sannan Murjanatu ta fara rokon Diyam akan ta fita dasu yawo yau da yamma "Please, Please Diyam, this routine is killing me slowly, ai ance taba kida taba karatu ko?" Diyam tace "sai jibi weekend sai muje muyi siyayyar abubuwan da bamu dasu a gida"
Washegari Friday, Diyam tana zaune a seat dinta tana rubutu taji ance "hi Diyam" ta dago tana kallonsa bata ce komai ba, sai kuma ya shafa kansa yace "Assalamu alaikum" tace "ameen wa alaikas salam Bassam" ya kalli seat din kusa da ita yace "can I?" Ta gyada kai ba tare data dago ba. Ya zauna ya fito da book dinsa pretending to be reading amma ita tasan ba karatun yake ba. Can ya ajiye littafin yayi tagumi yana kallonta yace "can I ask you something?" Ba tare da ta kalleshi ba tace "sure" yana taping hannunsa akan desk yace "me yasa ake ce miki Diyam? It means water right? Me yasa ake ce miki water?" Ta daina rubutun ta na kallonsa tace "maybe I am as important as water is to some people" yayi dariya yace "your boyfriend maybe" tayi murmushi kawai. A lokacin lecturer din su ya shigo, ya gyara zamansa yace "boring, boring, boring" ta sake murmushi kawai tana wandering me yake yi a makarantar in bashi da interest a karatun.
Diyam............... writing
[1/4, 10:30 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ Diyam ❤️
By
Maman Maama
Episode five
Yana tashi da safe kamar kullum abinda ya fara yi shine duba wayarsa, hopping to see ko dan text message ne ko da kuwa daga brother dinsa ne amma kamar kullum nothing, ya runtse idonsa ya bude, haushin su yake ji gabaki dayansu, wato suna nufin zasu iya cire shi daga rayuwarsu ko? Suna nufin zasu iya shafe babinsa su manta dashi, wato suna nufin koma me zai same shi basu da problem ko?
Ya sake duba account balance dinsa yaga kudin ciki ko ticket ba zai siya masa ba in ma yace gidan zai koma. Jin dadinsa daya ya biya kudin hotel room dinsa in advance tun kafin suyi blocking dinsa daga family account. Ya jima yana tunanin abinyi sannan yayi scrolling through contact dinsa ya nemo number din brother n sa ya tura masa text message. Ya duba wallet dinsa ya ga cash din daya rage masa, yayi tsaki tare da komawa ya kwanta a ransa yace "makarantar ma ba za'a je din ba". Ya jima a kwance sannan kuma ya mike da sauri ya shiga toilet, ya yanke shawarar abinda zaiyi. Idan ba zasu turo masa kudi ba to shi zai nemi kudi da kansa.
Yana gama shiryawa ya tafi wani sabon mall da aka bude nan kusa da hotel ɗin sa, tunda sabon guri ne yasan suna bukatar ma'aikata dan haka yaje ya nemi aikin salesman, bai sha wahala ba saboda yadda suka ganshi fes fes dashi dan gayu suka bashi aikin, zasu ke biyansa daily kuma pay din babu laifi, at least ya samu kudin abinci kafin komai ya warware masa.
A bangaren Diyam kuwa yau Saturday tun da suka tashi suke aikin sanitation din gidan kamar yadda suka saba yi duk sati. Sai da suka share ko'ina suka goge sannan ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta tsaya gaban mirror tana kallon reflection dinta. She have come a long way. Last year kamar yanzu in aka ce mata zata zo inda take a yanzu she won't believe it, her life have been so fast, so dramatic and so challenging kuma she have succeeded all those challenges har ta kawo inda take a yanzu. Ta dauki mai tana shafawa a hankali tana noticing irin laushi da santsin da fatar ta take kara yi kullum, tabbas weather din London ta karbe ta.
Sai kuma taji tana kewar gida, ta gama shiryawa ta fita parlor ta zauna jiran su gama su fito su tafi shopping kamar yadda suka shirya. Anan ta dauko wayarta tana noticing time sannan ta kira Inna. Bugu daya ta dauka daga dukkan alamu tayi missing dinta itama. Ta gaishe ta, Inna tana ta tambayarta lafiyar ta data Murjanatu, sannan Diyam tace "ya naji ki shiru? Ina rigimammiyar taki ne?" Inna tace "babanta yazo ya dauke ta sun fita" Diyam ta lumshe idonta ta bude tace "ya zo garin kenan?" Inna tace "eh dazu da safe yazo, shine ya dauketa suka fita wai za'a siya mata keke, ko me zatayi da keke tana mace? Yace min ai zuwa nan da wani satin zai samu yazo ya ganku" Diyam ta kawar da maganar ta hanyar cewa "sun shirya kenan, shi da yar tasa" Inna tace "ina fa? Ta dai bishi da kyar. Daga gani ba da son ranta ba dan dai babu yadda zatayi" Diyam ta kwantar da kanta a jikin kujera tana jin duk tension din data bari a Nijeriya yana dawo mata. A hankali tace "ki gaishe ta inta dawo, a gaishe min da Asma'u" suka yi sallama lokacin da Judith da Murjanatu suka fito kusan a tare.
Duk su ukun suka tafi shopping din a tare, Diyam tana driving, Judith a side dinta Murjanatu kuma a baya. Annashuwa suke ji suna ta wake waken su da dararrakinsu. Murjanatu ce tace su je sabon mall din da wata kawarta tagaya mata an bude, nan take suka karbi address din suka saka a GPS ya kaisu har kofar mall din. Suka fito suka yi locking motar suka shiga suna yaba kyau da haduwar gurin. Suna shiga suka ji ance "welcome, what do you want to buy today" suka juya gaba dayansu a tare, idon Diyam ya sauka a kan Bassam da yake kallonsu da murmushi a fuskarsa, for the first time ta ganshi babu cigarette amma headphone din yana nan sai dai ya sauko dashi wuyansa, three-quarters wando da farar riga mai tambarin mall din wadanda suka kama shi suka fitar da ainahin cikar zatin sa. Cikakkiyar sumar kansa a taje a gyare tas. He looks so handsome and matured. Nan take murmushin nasa ya bace, ita kuma ta fara yi tace "Bassam?" Ya shafa kansa ya juya baya yace "damn it" Diyam tayi dariya tana zagayo wa gabansa tace "wow. This is no nice of you Bassam. Mutum mai dogaro da kansa ba sai ya jira an yi masa ba, ka burge ni sosai. And you look good" ta fada tana kallonsa daga sama har kasa. Ya kalle ta shima yace "you don't look bad yourself" tace "thanks" sannan ta gabatar dashi a gurin su Murjanatu wadda tunda ta ganshi ta gane shi ta kuma bata rai take ta zabga masa harara. Amma ba karya, ita kanta tasan kyakykyawa ne.
Shi ya zagaya dasu zuwa gurin duk abinda suke son siya, in sun je kuma zaiyi musu bayanin different brands na abinda zasu siya da kuma banbancinsu. A haka suka yi ta lodar kaya kamar Allah ya aiko su, kayan abinci kayan kwalliya kayan sawa, kayan ciye ciye da kayan shiririta, har sai da Bassam da kansa ya tsorata da siyayyar tasu yana gudun kar su je biya kudin su ya gaza suzo suji kunya kuma shi gashi bashi da kudin da zai biya musu amma dai sai yayi shiru. Amma suna zuwa gurin biya sai yaga ta basu credit card, ya dauke numfashin sa yana jiran yaji ance insufficient fund amma sai yaga an ciri kudin an miko mata card dinta. Nan aka loda musu kayan a manyan ledoji aka bawa labourers su kai musu mota, shi kuma ya bisu da niyyar ya tare musu cab amma sai yaga sun doshi wata lafiyayyar mota sun bude an saka musu kayan a ciki. Ya tsaya yana mamaki, a car? Student? In UK? Who is she? She definitely is not on scholarship kamar yadda ya dauka daga farko. Ya zagaya side dinta ya dafa windown yace "so, this is your car?" Tayi dariya tace "not mine, ara nayi from a friend of mine" tana jin Murjanatu tayi gyaran murya amma bata kula ta ba. Tace "to naga gurin aikin ka, zanke kawo maka ziyara" ya daga kafada yace "it is just a temporary part time job, kafin inyi clearing some situation" ta gyada kai tace "the not laughing situation?" Yayi dariya yace "yeah, one and the same" tace "da fatan ba zai ke hana ka zuwa school ba kamar yadda ya hana ka zuwa ranar Friday" ya kalle ta cikin ido yace "I will come, ko dan in ganki ma" tayi saurin fitar da idonta daga cikin nasa tace "see you on Monday then" suna jan motar daga gurin Murjanatu tace "you really are playing with fire" babu wanda ya bata amsa a cikin su. Daga nan basu koma gida ba sai suka shiga gari yawo, shiga can fita can suna ta bin GPS, suka tsaya wani restaurant suka ci abinci, suka je gidan wata kawar Murjanatu suka yi sallah, basu suka dawo gida ba sai yamma likis.
Da dare Diyam na kwance a kan gadon ta, jikinta likis saboda gajiyar zirga-zirga da sukayi tayi duk da cewa a mota suke. Ita kanta taji dadin fitar duk da dai bata nuna wa Murjanatu a fuska ba, she maintained her serious face. Ta tashi ta dauki ledar sweets da biscuits din da ta siyo da yawa kamar wata yarinya, ta jera su a bedside drawers dinta sannan ta dauko ledar m and m's ta kwanta ta na jefa wa a baki tana duba lecture note dinta.
Wayarta dake gefenta ce tayi kara, tana dubawa taga alert na kudin daya haura wadanda ta kashe musu, ko bata tambaya ba tasan daga inda kudin suka taho. Ta danyi tsaki ta ajiye wayar dai dai shigowar wani text message din. Ta sake dauka ta karanta kamar haka:
For the shopping you went to. Hope baki sha wahala da yawa ba. Kuma da fatan baki siyo sweets da yawa ba dan na sanki kamar shazumamu.
Your Love.
[1/5, 9:23 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Six: The Lucky Ones
Ta kalli jakar alawar kusa da ita ta sake karanta text din sai kawai tayi murmushi, sai kuma ta bata rai ta mike da sauri ta tafi dakin Murjanatu. Ta tarar da ita tana arranging kayan kwalliyar data siyo tace "ke kika gaya masa munje shopping?" Ba tare data kalleta ba tace "sure. Wani abu ne" Diyam tayi tsaki tace "Will you please stop telling him duk abinda nake yi? I need some privacy and some space" Murjanatu dai bata ce mata komai ba har ta yi mata banging kofar ta tafi, sai kuma tayi murmushi a hankali tace "hypocrite". Sai da Diyam ta gama duk abinda zata yi ta yi shirin bacci sannan ta dauko wayarta ta tura masa reply
Thanks
Ta jima tana kallon kalmar, tana so ta kara rubuta wasu kalaman no matter how small wadanda zasu nuna masa irin yadda take ji a zuciyarta a game dashi amma ta kasa. Bata so tayi giving up, not now, not ever. Haka ta tura masa kalmar guda daya ta koma ta kwanta tana jin ranta babu dadi.
Bassam kuma ranar kasa bacci yayi, yayi ta tossing akan gadonsa. Abu na farko daya ke ransa shine sabon aikin daya samarwa kansa, yaji dadin aikin nasa sosai dan shi tunda yake bai taba aikin neman kudi ba, komai yi masa ake yi. Yanzu yasan at least bashi da fargabar running out of money. Abu na biyu kuma da yake ransa shine Diyam, ya rasa dalilin da yasa yarinyar ta tsaya masa a ransa tun encounter dinsu ta farko, he just can't stop thinking about her. A haka har bacci ya dauke shi. Cikin dare ya farka idonsa ya sauka akan hoton Khausar dake kan bedside dinsa, ya saka hannu ya kife hoton ya juya ya cigaba da baccin sa.
Ranar Monday ya rigata zuwa hall dinsu. Sai ya zauna akan kujerar da take kusa da wadda take zama koda yaushe ya dauko littafi yana bubbudawa kamar mai karanta wa amma sam hankalinsa baya kai, hankalin sa yafi karkata zuwa ga kofar da students suke shigowa zuciyarsa tana kara dokanta da son ganinta. Can ya ganta ta shigo, suna hada ido tayi masa murmushi and all his problems melted away. Tun kafin ta zauna lecturer dinsu ya shigo dan haka basu yi magana ba suka mayar da hankalinsu kan lecture. Amma Diyam tana lura dashi yafi mayar da hankalinsa gurin kallonta maimakon gurin lecture, and her heart sank.
Lecturer yana fita ya juyo gaba-daya gurinta yace "so, miss Nigeria, you are from Yobe state, right?" Ta dan bata rai tana kallonsa tace "Yobe kuma?" Yace "eh, rannan kince min sunan ki Haleema Usman Kollere, and I know Kollere is in damagum local government, yobe state" tayi dariya tana rike baki tace "you are amazing" yayi murmushi proudly yace "I know my geography" ta mike tsaye tana zuba kayanta a jaka, shima ya mike, tace "You surely do, but I am not from Yobe. Kamar yadda na fada ranar nan ni yar kano ce, yes, my grandparents na uwa da uba duk fulanin Kollere ne amma ni a kano aka haifeni, kano ne a birth certificate dina dan haka kano nake amfani dashi" suka jera suna fita daga ajin tace "so you are from Abuja, where in Abuja are you from?" Yace "somewhere" ta tsaya a waje tana kallonsa tace "wayo ko? Wato ni na bude baki na gaya maka daga inda nake shine kai kuma zaka wani ce min somewhere ko?" Yace "a,a ke fa kawai kince min ke yar kano ce, kano ai tana da girma" direct tace masa "Municipal. Yakasai. Kai fa?" Ya sosa kai yana kallonta, taga bashi da niyyar fada tayi gaba tace "ohhh, I hate stingy people" ya biyo ta da sauri yace "I don't want to lie to you, kinfi karfin haka. And I also don't want to tell you yet" tace "saboda me?" Ya sake yin shiru. Ta karkata kai tana kallonsa tace "someone as shiny as you must have come from the Villa, not less" yayi dariya yace "You are wrong, ko kusa da Villa ban kai ba" tace "where then?" Ya kalli surrounding din gurin yace "ina zamuje ne naga mun fito waje" ta gane so yake ya chanja maganar tace "cafeteria, yunwa nake ji, I over slept har na makara kuma munyi fada da Murjanatu taki tashina" yayi dariya yace "me ya hadaku?" Tace "girl's stuff, you won't understand" ya rungume hannunsa a kirji yana kallonta yace "stingy, are we?" Tayi dariya tace "ba zaka gane ba fa" yace "okay, let's go. Nima banyi breakfast ba".
Shi yayi musu order abinci, bacon and eggs, da coffee. Suka fara ci sannan yace "so, how did a Fulani girl daga rugar Kollere ta samu kanta a Oxford?" Ba tare data kalleshi ba tace "luck" yace "hmmm?" ta ajiye chokalin hannunta tana kallonsa tace "you talk about kaddara ranar nan ko? To ita ta kawo ni nan, I was destined to be here and here I am. How about you? How did a guy from somewhere in Abuja find himself here" shima yace "luck" ta daga gira daya sama tana kallonsa sannan yace "okay, I was lucky to be born into a wealthy family" tayi murmushi tace "Villa?" Yace "definitely not" sukayi dariya baki daya.
Ranar kusan tare sukayi komai, har suka tashi daga school suka kuma tafi tare, sai daya rakata har bakin block dinsu sannan yayi mata sallama ya tare cab zuwa gurin aikinsa. Yana jin zuciyarsa fari kal kamar takarda, duk wani bacin rai da stress duk ya gushe daga ransa. He is finally finding happiness.
Diyam kuma tana shiga parlon su ta yarda jakarta ta kwanta ta lumshe ido, tana jin Judith ta shigo parlon tana yi mata magana amma sai tayi pretending kamar bacci take yi nan kuwa idonta biyu, lissafi kawai take yi a ranta. Most of the time shi yasa tafi son zaman makaranta saboda in tana can tana mantawa ne da duk wasu problems dinta amma tana zuwa gida sai taji kamar damuwowinta jiranta suke yi a bakin kofa. Jiya da daddare sukayi rigima da Murjanatu, kuma ita tasan Murjanatu gaskiya take gaya mata, tasan yaudarar kanta kawai take yi taki admitting hakan. Ta dauko wayarta tana kallon hoton dake kan screen din tana murmushi, sai kuma ta shiga cikin ta fara kallon pictures tana ta dariya ita kadai. She missed Nigeria sosai, but wannan zaman da take, wannan karatun da take, shine kadai solution dinta a yanzu. Me yasa mutane including Murjanatu suka kasa fahimtar hakan?
Sai bayan la'asar Murjanatu ta dawo. Kafin nan Diyam ta shirya musu pasta saboda tasan Murjanatu tana so duk dan su shirya. Tana shigowa kallo daya tayi wa Diyam ta kara tura baki gaba ta wuce daki, sai da tayi wanka ta shirya cikin riga da wando budaddu kalar ruwan toka da suka kara wa bakar fatar ta kyau sannan ta dawo parlon ta tsaya ta rike kugu tace "shine kika taho kika barni ko? Kuma na tambaya ance min tare da wannan tsinannen Bassam din kuka taho" Diyam ta mike zaune tace "ayyah Fanna, karki tsine masa, kinsan bakin ku dafi ne dashi, kar kisa ya tambade shi da baiyi miki komai ba" Murjanatu ta zauna ta dora daya kan daya tace "tunda yake kula matar yayana ai yayi min laifi, kuma wallahi daga ke har shi ku shiga hankalinku idan ba haka ba yana zuwa next week sai na gaya masa, kuma kunsan sauran" Diyam tace "oh oh, to gaya masan mana, an gaya miki kowama tsoronsa yakeji kamar ke, ni kinsan daga ke harshi dai dai nake daku. Naci nasha tsumin fulani barebari sai dai su ganni su barni" nan kuma suka koma wasan fulani da barebari, sannan suka ci abincinsu tamkar ba sune jiya suka yi fada ba.
[1/6, 10:32 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Seven : The Phone Call
Tun daga ranar Diyam da Bassam suka hade, kullum a school suna tare duk ya daina kula friends dinsa ita kuma dama bata dasu, daga school kuma zai wuce gurin aikinsa, anan zai samu kudin kashewa gobe. Sosai yake jin dadinsa hankalinsa kwance as if bashi da wani problem.
Ranar Thursday suna lunch a cafeteria kamar kullum, Diyam ta tambaye shi "can you tell me about that not laughing situation da kace kana ciki? Because I can see yanzu kana dariyar" dariyar yayi sannan kuma ya hade rai yana jujjuya abincin gabansa yace "I got fired" ta zaro ido tana mamaki, fuskanta cike da concern tace "daga gurin aikinka? When?" Yace "no, ba daga gurin aikina ba, I got fired from my family" ta hade rai tace "your family? Ta yaya za'ayi familyn mutum su kore shi? Me kayi Bassam? What happened?" muryarta tana breaking kamar zata yi kuka ta tambaye shi, ba tare daya kalleta ba yace "nayi laifi, babban laifi, maimakon in tsaya in fuskanci hukunci na kuma sai na gudu na kama daki a hotel nayi zamana. When I did that na saka ran kwana biyu ba zasu wuce ba mami na da Daddy na zasu zo kasar nan, nayi tsammanin zasu zo har dakin da nake, nayi tsammanin karbar wadansu kyawawan mari daga Daddy na kuma yi tsammanin in samu nasiha daga mami amma shiru, basu zo ba ballantana su fada min cewa nayi ba dai dai ba ballantana su kaini gurin Aunty na da nayi wa laifi su saka ni in bata hakuri" ya dago ido yana kallonta cikin ido yace "basu zo ba ba kuma su kira ni ba, they just cut me up, basu zo ba ballantana suyi min maganin problem dina, at least ko shawara ce su bani". Tana kallonsa tace "wanne problem ne kenan? Your smoking problem?" Ya girgiza kai yace "basu san wannan ba ai" sai kuma ya bata labarin feelings dinsa for Khausar, da kuma yadda ya tarar tana dating cousin dinsa Ayan, tun daya fara bata ce komai ba har sai daya gama sannan tace "how old are you Bassam? You know nothing about love, do you? That girl doesn't love you, cigaba da jan magana tsakanin ka da ita ba abinda zai yi sai bata zumuncin dake tsakanin ku. Kuma ni a fahimtata familyn ka ba wai cutting dinka off suka yi ba, suna keeping tabs on you tabbas tunda su suka haife ka and they love you. They just want you to grow up, they want you to make the right decision by yourself daga nan sai su san hukuncin da zasu yanke maka. Kafin Mami da Daddy su zo su baka shawara ni ga tawa, ka koma gurin auntyn ka wadda kayi wa laifi kaje ka bata hakuri on your on ba wai sai ance maka kaje ba, ka bawa cousin dinka hakuri kuyi shaking hands kabar maganar Khausar, you don't know what God has planned for you".
Yayi murmushi yace "I guess you are right, maybe wadda zan samu nan gaba tafi Khausar komai" ya karashe maganar yana kashe mata ido daya. Tayi saurin dauke kanta tana jin zuciyarta tana bugawa da karfi. A take taji abincin ya fita daga kanta, ta ture plate din ta mike tace masa zata je class in ya gama ya same ta a can, ya bita da kallo har ta fita yana mamakin me ya chanja mata mood.
A ranar haka ta wuni tana jin ranta babu dadi, kar dai abinda take tunani akan Bassam haka ne, kar dai he is developing feelings for her, kar dai abinda Murjanatu ta fada rannan gaskiya ne, cewa she is playing with fire. Tana zuwa gida ta tarar da abinda yafi wannan daga mata hankali. Murjanatu ta gani zaune ta zuba uban tagumi, ya yarda jakar hannun ta ta zauna a gabanta cike da concern tace "Fanna? Lfy?" Ta dago tana kallonta tace "yaya ya kira yanzu, wai in gayawa Judith ta hada kayanta ta bar gidan nan kafin weekend" Diyam ta mike "au wai har yanzu bai bar maganar Judith ba? Me ta tsare masa? Akanshi take zaune? Ni ba zan iya korar Judith ba tunda babu abinda tayi min, dama baki gaya masa sakona na ranar nan ba?" Murjanatu tace "ni na ce miki bazan iya gaya masa ba Diyam tsoro nake ji" Diyam tace "mala'ikan mutuwa ne shi da zaki ke tsoronsa?" Daga haka ta figo wayarta daga cikin jaka and for the first time tun zuwan ta kasar ta danna number dinsa, bugu daya ya dauka, bata ko saurare shi ba ta fara zazzaga bala'i "wanne irin mutum ne kai wai? When will you stop playing god? When will you stop making decisions a rayuwar mutane? This is my life and I asked you to stay out of it" I nutse yace "Diyam...." Ta katse shi "kar ma ka gwada yimin dadin baki, bazan kori Judith ba and that is final" yace "am sorry dear, I was just trying to.." tace "trying to protect me? To kayi hakuri but I don't need your protection" ya sake cewa "I was just trying to.....to provoke you into calling me" sai ya kyalkyale da dariya. Ta tsaya tana kallon wayar da mamaki, sannan ta kalli Murjanatu taga ta durkushe a kujera tana ta kyalkyala dariya harda rike ciki, sannan tayi realising abinda ya faru.
Ta jefar da wayar kamar wadda aka ciza sannan ta dafe kanta da hannu biyu tace "oh God, Murjanatu what have you done?" Da gudu Murjanatu ta mike ta shige daki tana dariya ta rufo kofa. Diyam ta zauna akan kujera ta dauki wayar da har yanzu take a kunne tace "this is cheating" har yanzu da dariya a muryarsa yace "kin tuna abinda kika ce min ranar da zaki bar Nigeria? Kin tuna alkawarin da muka yi dake cewa in dai kika dauki waya da hannunki kika kira ni to nayi winning, zan yanke duk hukuncin dana ga dama" ta sake cewa cikin raunanniyar murya, "but this is cheating" yace "in life, my dear, cheating is allowed once in a while" sannan ya kuma dariya yace "see you on Saturday" ya katse wayar.
Ta kife kanta a kujera tana jin hawayenta yana jika kujerar, sai da tayi kukanta ta gama sannan ta dago ta dauki wayarta ta tura masa message
"You always claimed that you play your games fair and square, but this is not fair"
Bayan yan mintina reply ya shigo mata
"Nothing is fair my dear, life in itself is not fair, you just have to be smart and have eyes like an eagle's so that you won't get cheated on. My regards to your lips".
Comments dinku suna kadan, shi yasa typing yake kadan
[1/6, 8:19 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Eight : The Numbers
Ta jima a kwance a gurin, har Judith ta dawo ta shiga kitchen ta fara hada musu dinner, sannan ta tashi ta shiga daki tayi sallar magrib ta kwanta, ita ba bacci ba ita ba ido biyu ba tana ta saka da warwara. Allah ya gani bata son wannan zuwan nashi dan tasan ba zasu kare da dadi ba, zuwa zaiyi suyi ta rigima kuma rigimar da babu inda zata kai su. A nesa nesa dai sai sunfi samun kwanciyar hankali, wannan shi yasa ta zabi tahowa karatu nan kasar dan tayi baya dashi har abubuwa su warware. She don't want to keep hurting herself and she don't want to hurt others. Bassam ne ya fado mata a rai. Poor innocent Bassam, daga ganinsa tasan is from a wealthy family amma duk da haka bata son involving dinsa a wannan drama din, kuma she is afraid that he is already involved saboda irin kallon da yake mata kwana biyun nan. Kar dai ace ya fara son tane. She will have to put a stop to their relationship.
Har daki Judith ta kawo mata dinner kuma ta matsa mata sai data ci, tana ta tambayar ta abinda yake damunta amma sai tace mata family issue ne kawai.
Washegari tana shiga class ta hango Bassam a seat din kusa da inda take zama, sai tayi sauri ta dauke kanta ta samu front seat ta zauna. Bata jima da zama ba taji kamshin turarensa a kusa da ita, bata dago kai ba yace "Are we changing seat?" Still bata kalle shi ba tace "I am" ya koma baya, ana jimawa sai gashi ya dawo da takardun sa ya zauna a seat din kusa da ita. Bata ce masa komai ba ta dauko littafi tana karantawa, shima ya dauko nasa yana flipping through the pages, can ya ajiye yace "can we go and eat? Ni fa yunwa nake ji" bata kalle shi ba tace "you can. Am okay" yace "me kika ci?" Sai ta mike zumbur ta rataya jakarta, yace "ina kuma zakije?" Tace "somewhere quiet" ya bita da kallo baki bude har ta fice daga ajin. Ya ajiye littafin hannunsa yana tunanin a inda yayi laifi.
Har aka fara lecture bata dawo ba. Sai a lokacin yayi realizing cewa bashi da number dinta, dan haka hankalinsa gaba-daya yana gurinta har akayi lecture din aka gama. She never misses her lectures tunda ya santa sai yau. Ya fara tunanin ko bata da lafiya ne? Lecturer din yana fita shima ya fita ya fara nemanta, duk inda suke zuwa tare sai daya je amma bata nan har lokacin wata lecture din yayi sannan ya dawo wai ko zata zo wannan amma itama shiru har aka gama. Ana gama wa ya tafi department din su Murjanatu ya tarar yau sam basu da lecture ma dan haka bata zo ba. Yana futowa ya tare cab sai block dinsu. Ya hau lift har apartment dinsu yayi ringing bell, daga ciki ya jiyo muryar Diyam ta amsa "who is there?" yace "thank God. Bassam ne, Diyam?" shiru tayi bata bude ba, har yayi kamar zai sake danna bell din kuma sai ta bude, fuskarta a hade ta tsaya tana kallonsa kawai bata ce komai ba, ya tsafa kansa yace "You skipped your class and I was worried and thought ko baki da lfy ne" direct tace masa "lfy ta kalau as you can see" tana ganin yadda expression din fuskarsa ya chanja, daga gani tasan bai ji dadin abinda tayi masa ba amma sai kawai ta juya zata koma ciki ba tare data kara cewa komai ba, yace "Diyam?" ta dakata amma bata juyo ba, yace "in kina so in daina kula ki ne just say so ba sai kin tsaya kwana kwana ba, but please don't skip your classes because of me" daga haka taji motsin tafiyarsa. Ta juyo tana kallon kofar duk ranta babu dadi, sam bata ji dadin bata wa Bassam rai da tayi ba but wani abun ya zama dole ne, laifin tane tun farko data fara zama involved with him amma ai a lokacin bata yi tunanin zai yi attaching wasu strings a relationship din nasu ba. Ta dawo ta rufe kofar sannan takoma ta kwanta a doguwar kujera ta rufe idonta tana lissafin yadda next weekend din zai kasance. Haka ta ringa jera tsaki ita kadai a kwance har taji motsi a hanyar corridor din dakunansu, ta daga kai taga Murjanatu a tsaye tana kallonta, nan take ta kara bata rai ta juya bayanta. Murjanatu ta karaso ta zauna a gefenta tace a hankali "Diyam" Diyam ta mike ta dauki wayarta ta shige ciki ta barta a zaune.
Bassam tunda ya bar gidan su Diyam ya saka hannayensa a cikin aljihunsa ya fara tafiya, wani irin zafi yake ji a ransa yana jin zuciyarsa tana kara karyewa, tambayar da yake ta maimaitawa kansa itace me yayi mata? Duk iya tunanin sa in ya dawo da hirarrakinsu baya sai yaga babu inda yagaya mata ko da kuwa wata magana ce marar dadi. Shi akwai wanda ya samu power over him a rayuwarsa irin Diyam? Tun farkon haduwar su baya iya mayar mata da magana, to me ya faru? Babu abinda ya kai ayi maka hukunci ba tare da kasan laifin me kayi ba ciwo. Yana isa kofar hotel dinsa sako ya shigo cikin wayarsa. Ya dauko yana dubawa, for the first time in weeks ya samu sako daga gida, daga brother dinsa, yaji heart dinsa tana racing kafin ya bude amma yana bude wa sai ya tarar babu ko kalma daya a cikin sakon sai hoto, hoton flight ticket.
Yayi ajjiyar zuciya ya jingina da bango, wato babu wata magana kenan a tsakanin su sai yaje gida. Abinda suke bukata dashi shine ya kai kansa gida ya karbi laifinsa. Yayi ajjiyar zuciya ya mayar da wayar aljihu a ransa yace "not now brother" dan bayajin zai bar kasar har sai yayi straightening tsakanin sa da Diyam. Ya tuno da shawarar da Diyam ta bashi na cewa ya je gurin Aunty Hafsat ya bata hakuri sannan ya tafi gida ya kai kanshi. Wani tunani ya fado masa a game da Diyam, anya ba wannan ne dalilin da yasa ta juya masa baya ba?
Washegari Friday, da sassafe Diyam taje school dan ko breakfast bata tsaya tayi ba saboda bata ma son abinda zai hada ta magana da Murjanatu har sai tayi deciding inda zatayi placing dinta. Ta jima a class tana duba takardunta amma a can kasan zuciyarta tana duba ta inda Bassam zai bullo. Tana nan a zaune har aka zo aka sanar cewa lecturer din ba zai samu zuwa ba, a dai dai nan Bassam ya shigo, suna hada ido tayi saurin dauke kanta amma ta kasan idonta ta hango shi straight ya taho gurinta, ta fara kokarin harhada takardunta pretending to be busy har yazo daf da seat dinta ya tsaya, da dan karfi yace "why? Menene dalilinki na cutting dina off? Laifin me nayi?" Bata ce komai ba amma sai taji wani abu ya rike a tsakiyar cikinta kamar mai jin yunwa, nan take jikinta ya kama karkarwa har takardun hannunta suka zame suka zube a kasa, ta sunkuya tana kwashewa shima ya sunkuyo yana taya ta, sunkuyon da tayi yasa rolling din veil dinta ya kunce gashinta ya zubo ya rufe mata fuska ya sauka akan hannayensa. Still yayi yana kallon tsaho, baki da santsin gashin, ya daga hannunsa ya mayar mata da gashin bayanta tare da bude mata fuskarta, a lokacin ya lura da how red fuskarta da idonta sukayi, sai kawai yaji tashi zuciyar tayi melting, yaji kamar bai kyauta ba da ya daga mata murya har ya bata mata rai. Ta mike ta warce papers din hannunsa ta ajiye a gefe tana gyara veil dinta yace "am sorry Diyam but dan Allah ki gaya min abinda nayi miki" ta dauki takardun ta ta zagaye shi zata wuce ya rike jakarta yace "saboda na fada miki am in trouble da family na shine zaki juya min baya?" Da sauri ta juyo tana sauke manyan idanuwanta da suka yi ja a kansa, she looked shocked, bata taba zaton zai yi linking wannan abin da labarin sa ba, ta warce jakarta tace "is that what you are thinking? tunanin da kake yi a kaina kenan?" Ya daga kafada yace "then tell me otherwise, me nayi miki" tace "babu abinda kayi min Bassam" ta danyi shiru kamar mai tunani sannan cikin karyayyiyar murya tace "am just not who you think I am. Am sorry" ta juya da sauri saboda hawayen da taji yana taho mata. Kafin ta kai kofa ya kuma rike jakarta, ta juyo ta zuba masa jajayen idanuwanta yace shima da raunanniyar murya "ko ba zaki cigaba da kulani ba, at least give me your number yadda zan ke jin halin da kike ciki ko a waya ne, ko physically ba zamuyi magana ba at least....."
"Number?" Ta katse shi "wacce number zan baka Bassam? Ohhh I have so many numbers a cikin wannan kan nawa" ta fara lissafa masa da yatsun hannunta "kaga na farko 24 itace number din shekaru na, 3 itace number adadin yayan dana haifa a duniya, 2 itace number of times I was divorced, 8 itace shekarun yar karamar yarinya ta, infinity shine number of times my heart was broken and 0 is the tolerance I have for other hear breaks. So tell me, wacce number zan baka a cikin wadannan?"
A hankali jakarta ta zame daga hannunsa saboda yadda gaba-daya jikinsa ya saki, tamkar numfashin sa aka zare gaba daya. Ta tako zuwa dai dai fuskarsa tace "like I said, am not who you think I am".
Har ta fita daga ajin bai motsa daga inda yake ba.
You did not see that coming, did you?
[1/7, 7:40 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Nine: The Gamer
Tabbas maganar da Diyam ta fada wa Bassam bashi kadai ta taba ba, har ita. Tana fita daga ajin taji kanta yana wani irin juyawa kamar zata fadi, duk reality din rayuwar ta yana dawo mata. Tun da tazo UK take living in a dream yanzu kuma ta farka, gobe kuma zata kara farkawa tunda gobe zai zo bata san kuma da wacce zai zo ba. As far as he is concerned yayi winning over her dan haka zata bi abinda yace kenan. Ta samu jikin wata bishiya ta jingina tana mayar da numfashi, a nan taji karar shigowar text wayarta, ta dauko a jaka ta bude taga wanda take tunanin ne ya aiko mata da message
"Tell him I say hi, kafin inzo mu gaisa gobe"
Ta sake karantawa, ta nanata amma ta kasa making sense of it. "Him?" who is him?. Wata karamar murya a can kasan zuciyarta tace "Bassam" ta zame ta durkushe a gurin, so he knows about Bassam? Abinda take ta gudu kenan gashi nan bata yi escaping ba. Amma ta yaya yasan labarin Bassam? "Murjanatu" muryar ta sake fada mata.
Ta mike and for the first time ta tari cab saboda yadda take ji ba zata iya tafiya a kafa ba. A motar ma dunkule wa tayi dan ba zata iya zama straight ba saboda wannan abin daya dunkule mata a ciki har yanzu bai saki ba, sai da drivern yayi mata magana sannan ta san sunzo, ta bashi kudinsa ta shiga ciki. Tana bude kofa idonta ya sauka akan Murjanatu a zaune tana facing kofa, suna hada ido Diyam tayi realising gaskiya, ba Murjanatu ce ta gaya masa ba. Murjanatu ta mike tana twisting hannunta tace "Diyam, yaya yasan kuna tare da wannan yaron" Diyam ta bita da kallo bata ce komai ba, Murjanatu ta cigaba "wallahi bani na gaya masa ba, I wanted to tell you tun jiya ya kira ni ya tambayeni wai waye kuke yawo tare dashi a school nace masa ni bansan kina yawo da kowa ba, he said in bangaya masa ba in yazo sai na sani. To dazu kuma ya kira yace min nayi masa karya kuma sai na gane kure na" still Diyam bata ce komai ba, kallonta take kawai tana lura da yadda tsoro ya fito baro baro a kyakykyawar fuskarta. Ta taho ta zagaye ta zata shiga corridor Murjanatu ta mike ta rike hannunta tace "Diyam am sorry akan maganar shekaran jiya, wallahi bansan betting kuka yi a kan wani abu ba, ni kawai cewa yayi min zamuyi playing game, yana so in nuna miki da gaske yake zai kori Judith, please Diyam kiyi hakuri bana son alakar mu ta baci a saboda wannan" ba tare da Diyam tace komai ba ta zare hannunta daga na Murjanatu ta shige dakinta ta rufe kofa. Direct toilet ta shiga, ta cire kayanta gaba-daya ta shiga shower ta kunnawa kanta ruwan dumi. Ta lumshe idonta tana jin dadin yadda ruwan yake sauka a kanta, tana jin duminsa yana narkar da daskararriyar zuciyarta, tana jin jijiyoyinta suna warewa suna aikawa da sakonni kwakwalwarta. Ta tuno abinda Murjanatu tace "a game" of course it is all a game, shi komai a gurin sa ai game ne. Ta tuno wata magana daya taba fada mata shekaru da dama da suka wuce
"Diyam, life is like a game of chess, the secret to winning is to observe the movements of your opponent, think deeply and make your move"
Amma abinda ya kasa ganewa shine a yanzu bashi da opponent din, shi kadai yake buga game dinsa, kuma ya kasa realizing cewa a haka zai zo yayi hurting others, innocent mutane kamar Bassam. Ya kasa realizing cewa duk abinda take yi tana yi ne for him not against him. Shi kawai burinsa yayi winning, no matter the cost. Ita kuma burinta shine ya ajiye wannan game din ya duba reality, ita bata son wannan game din nasa mai ban tsoro, dan last game din da ya buga didn't end well, it ended with someone in jail for life, someone very important to her.
Ta kashe shower din ta fito ta daura dogon towel sannan ta dauki karami tana goge fuskarta da dogon gashinta dashi, a ranta tana kokarin placing kanta in his place daga nan sai taga menene next move dinsa. Amma duk iya kokarinta ta kasa guessing menene zaiyi a next move dinsa. Ta fito ta dauki wayarta data ajiye tana dubawa, sai a lokacin tayi realising cewa for the first time tun zuwanta kasar yau ne rana ta farko da bai kira ta ba, hakan yana nufin yayi fushi da ita, fushi kuwa mai tsanani. Ita dai tasan har ga Allah bata fara kula Bassam saboda wani abu ba, ta fara kula shine saboda maganganu marasa dadi data fada masa a farkon fara maganar su, wannan yasa ta sauko da niyyar ta wanke kanta a gurin sa kuma sai abota ta shiga tsakaninsu. Ita tasan ko da da digon zarra bata jin wani feeling a kan Bassam wanda ya wuce na mutumta juna da aminci.
Ta shirya cikin doguwar rigar zaman gida, ta kwanta ta dauki pillow ta dora akan cikinta ta rungume, sai a sannan ta tuna cewa ko breakfast bata yi ba amma kuma yunwa is the last thing a mind dinta. She just want to know wanne mataki zai dauka, she just want to make sure ba zaiyi hurting kowa ba akanta. Tana nan kwance ita ba bacci ba ita ba ido biyu ba har lokacin sallar zuhr yayi, tayi alwala ta sauke farali sannan ta fito parlor, babu kowa dan haka tashiga kitchen ta dafa noodle ta zauna akan stool taci sannan ta wanke plate da tukunyar data bata ta dauki bottled water ta fito parlor ta zauna tana sha. Dai dai nan Murjanatu ta fito itama da shirin tafiya school. Ta dan zauna a gefen Diyam amma bata ce komai ba. Diyam ta mike ta shiga daki ta dauko dogon hijab ta saka tayi hanyar waje, har ta taba kofa taji Murjanatu tace "Diyam" sai ta juyo ta dawo kusa da ita ta zauna ta rike hannayenta a cikin nata tace "don't worry. He won't hurt you, not while am here". Sai kuma ta tashi ta fita da sauri.
Tana fita ta tari cab, since ta kasa sanin wanne mataki zai dauka ita zata dauki nata matakin da kanta. Bata san hotel din da Bassam yake ba dan haka direct mall din da yake aiki ta tafi. Tana kallon irin kallon da mutanen gurin suke yi mata kuma tasan yana da alaka da dogon hijab din da ta saka amma bata kula su ba ta cigaba da harkokin gabanta. Customer care ta tafi ta tambayi matar gurin agame da ma'aikacin su mai suna Sadiq Abubakar Sadiq. Daga farko kin bata wani information tayi a kansa for security reason, sai da tayi mata karyar ita friend dinsa ce ta yi loosing phone dinta ne kuma tana nemansa emergency concerning harkar karatunsu, sai da matar tayi checking taga sunan makarantar da kuma department din da Diyam din ta gaya mata yayi tallying da information din Bassam sannan ta gaya mata cewa bai shigo yau ba, amma ta gaya mata sunan hotel dinsa. Godiya Diyam tayi mata ta fita ta nufi address din da aka bata. A reception ta tsaya tasake yi musu bayani irin yadda tayi wa waccan matar amma suma suka hana ta hawa sama instead sai suka kira dakinsa through intercom, yana dauka Diyam ta karbi phone din tace "Bassam? Diyam ce. Can you come down for a minute? Ina son magana da kai please" daga can barin Bassam bai ce komai ba dan ji yake kamar in yayi maganar ma voice dinsa ba zai fito ba, sai kawai ya ajiye wayar. Diyam ta ajiye itama a ranta tana kissima cewa yayi fushi ne shima. Amma sai ta kasa fita, sai ta samu guri ta zauna tayi folding hannayenta ta zuba idanunta akan kofar lifter da take ta sunturin kai mutane sama da sauko dasu. Tafi minti sha biyar a zaune sannan ta mike cikin sanyin jiki da niyyar fita, a lokacin ne kofar lifter ta bude ya fito. Sweater ce a jikinsa mai hade da hula wacce ya jawo ya rufe kusan rabin fuskarsa dan haka ta kasa karantar emotions dinsa amma sai taga a idonta kamar ya dan rame kadan. Ya tsaya a gabanta ba tare daya ce komai ba, tana jujjuya hannayenta tace "Bassam magana nake so muyi please in babu damuwa" ya danyi gyaran murya sannan direct yace "are you married? A yanzu nake nufi" da sauri ta girgiza kanta tace "of cause am not" ya gingina kai sannan yayi hanyar waje ba tare daya kuma cewa komai ba ita kuma ta bishi a baya.
Baya suka zagaya, suka jera suna tafiya a tare, suna taka kafafuwansu a tare, amma daga ka gansu kasan akwai tension a tsakanin su. Wani garden suka shiga sannan suka je cikin wata rumfa suka zauna, gurin very quite duk da cewa akwai mutane jefi jefi suna hutawa a gurin, can kuma dan nesa dasu kadan swimming pool ne a zagaye ta fitulu mutane suna wanka a ciki. Ta daga ido tana kallonsa taga shima itan yake kallo, suna hada ido yace "uhumm? Ina jin ki, kince kina son magana dani" tayi kasa da nata idon tace "Bassam am so sorry ban gaya maka all these before ba, nayi haka ne saboda banyi tunanin da akwai bukatar in gaya maka din ba, yanzu kuma nace zan gaya maka ne saboda ka fahimci dalilina na daina kula ka, kasan cewa am doing it for you" ya katse ta "for me? How is that so?"
Ta bude baki zata yi magana wayar ta tayi kara. Ta dauka tana dubawa wa, "Inna" ta danyi murmushin takaici ta ajite wayar, of cause Inna, of cause gurin Inna zashi ya shirya mata wata dramar kuma, tun dazu abinda take tunani ga amsar ta bayyana yanzu. Tasan wannan ba kiran Inna ba ne ba dan tun da tazo kasar nan Inna bata kiranta dan tace ita bata gane wannan lissafin lokutan dan haka sai dai ita Diyam ta rinka kiransu ko kuma in Asma'u tana gida sai ta kira.
Har wayar ta katse bata dauka ba a take kuma aka sake kira, Bassam ne ya daga wayar ya ga sunan da yake kira yace mata "ain't this important? Ba innar ki bace?" Ta karbi wayar ta daga kiran, sai kuma ta saka a handsfree yadda Bassam zaiji abinda ake cewa, maybe abinda zai ji ya taimaka masa wajan fahimtar ta. Tayi sallama, daga daya barin inna tace "Haleema ya karatun? Ya 'yar'uwar taki?" Diyam tace "lfy lau muke inna ya kuke?" Inna tace "uhmm. Ni ina naga lfy kuwa? Kullum hankalina a tashe, ni dai har yanzu zuciyata bata kwanta da wannan karatun naki a kasar turawa ba Diyam" Diyam ta lumshe idonta tace "Inna ba mun gama wannan maganar ba tun kafin in taho? Inna ke da bakinki kika nuna hakan da nayi shine dai dai, yaushe kuma kika chanza ra'ayinki " Inna tace "zancen lokacin da na chanza ra'ayi duk ba shine mai muhimmanci ba, abu mai muhimmanci shine na chanja ra'ayin nawa. Ni ban yarda da zamanki a kasar waje ke kadai babu miji ba, dan haka cikin biyu zaki zabi daya, ko dai ki hakura da karatun ki dawo gida ki zauna a gaba na ina kallonki har lokacin da kuka shirya auren naku ko kuma a daura auren yanzu in yaso ya taho kuyi ta zaman tare, tunda shima yana da nasa harkokin a nan kasar". Diyam ta shafa fuskarta ta taji ta dauki zafi kamar mai zazzabi, ta kalli Bassam taga ita yake kallo shima fuskarsa cike da tambayoyi. Inna tace "kina jina shine kika yi shiru ko?" Diyam tace "Inna bashi wayar muyi magana" Inna tace "wa?" Diyam tace "nasan yana nan a gabanki Inna saboda kalmomin da kika fada ba kalmomin ki bane ba, nasa ne, shi yazo ya gaya miki su, to gwara ni ya gaya min a kunne na inji" Inna tace "au, wato abinda Ingilan ta koya miki kenan? Tun yanzu Diyam?" sai kuma suka ji muryar wani a background, can kuma sai ga muryarsa fes ta fito, very deep and very clear, yace "yes, I am here" Diyam ta hadiye wani abu a makogoronta cikin rarrauniyar murya tace "this is not the agreement, ba haka muka yi alkawari ba" yace "ba haka mukayi alkawari ba and yet you broke the promise" da sauri tace "I didn't, believe me I didn't" yace "we will see about that, tomorrow" daga nan suka ji shiru ya kashe wayar.
[1/8, 10:49 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Ten : The Beginning
Diyam ta dauke kanta tana kallon wani mai yankan fulawa da yake ta aikin gyara flowers din gurin suna kyau. Amma sam hankalinta ba'a kansa yake ba, hankalinta yana gurin yadda zata fita daga wannan trap din ne, a hankali tace "not again, not now" Bassam yace "what?" Ta juyo tana kallonsa kamar yanzu ta fara ganinsa kafin tace "Bassam. What do you understand by the word Love?" Ya karkata kai yana kallonta sai kuma yayi dan murmushi yace "that is a one million dollars question" tace "just answer it, kai me kake tunanin shine love" yayi shiru tsahon minti biyu yana tunani sannan yace "feelings. Love is a feeling of deepest desire for something. Like kaji kana son kasancewa tare da wanda kake so din" ta gyada kanta tana murmushi tace "yes you are right, love can be that but lust can also be that. Sometimes mutane suna zama confused akan bambancin love the lust. To me zan iya cewa abinda ka fada is just one aspect of love. Ta gyara zama tana kallonsa cikin ido tace "zan baka labari na Bassam, maybe a karshe you will understand the true meaning of love, you will understand kuma abinda yasa nake son yanke alaka ta da kai sannan kuma maybe it will help you find redemption". Ta koma ta jingina da jikin kujera tana kallon yadda ruwa yake tsiri a wani fountain kusa dasu. A hankali ta fara tariyo rayuwar ta.
Sunana Haleema Usman Kollere. Wannan shine labari na.
Kamar yadda na gaya maka asalin iyayena yan rugar Kollere ne dake karamar hukumar damagum ta jihar Yobe. Inna ta da baffana 'yanuwa ne, kakanin su daya. Da kakana na wajen uba da kakata ta wajen uwa uwarsu daya ubansu daya. Innar mu su biyu ne kacal agurin mahaifiyar su daga ita sai kanwarta Yakumbo Hafsatu sai tarin 'yan uba da suke dasu kasancewar mahaifinsu yayi aure aure da yawa, kusan sa'anni ne su biyun kuma tun suna yara Allah yayi wa mahaifiyarsu rasuwa ta tafi ta barsu a hannun kishiyoyi su kuma sukayi caa a kansu suka mayar dasu bayinsu, ganin ana neman hallakasu yasa kakana na gurin uba, Hardon rugar mu, ya karbo su a gurin ubansu ya kawo su gidansa gurin matarsa Inno wadda itace kakara ta gurin uba kuma ita kadai ce matarsa ta hada su ya yayanta ta rike.
Hardo yana da yaya hudu. Kawu Isa shine babba wanda muke kira da Alhaji Babba, sai kawu Mamman, sai baffana Usumanu, sai kuma autarsu Fatima wadda tsakanin su da baffana akwai nisa sosai dan kusan sa'ar Inna ta ce. Haka suka taso su shida a tare, idan ba wanda ya sani ba babu wanda zai ce Inno da Hardo basu suka haifi Inna ta da Yakumbo Hafsatu ba. Allah ya yi wa hardo arziki a rugarsu sosai, dan kaf rugar babu wanda yake da garken shanun da yakai nashi cika da manya manyan dabbobi, amma wannan bai saka ya hana yayansa karatu ba duk da dai mazan ne kawai suka yi kuma suma iyakacin su secondary School, duk wanda ya gama a cikinsu sai hardo ya debi shanu ya siyar ya bashi kudi yace "tafi birni ka nemi arzikin ka acan". Allah Babba ne ya fara shigowa Kano da niyyar neman kudi, aikuwa Allah ya buda masa yana fara juya kudin da aka bashi sai gashi kudi sun ninka kansu, Allah ya bashi baiwar iya kasuwanci dan haka nan take ya kafa kansa a kano, ya gina katon gidansa a sharada ya nemi aure anan rigar mu aka bashi ya tare da iyalinsa. Lokacin da Kawu Mamman ya tashi barin rugar mu sai Alhaji Babba ya nemi ya taho Kano gurinsa dan ya buda masa shima ya samu ya kafa kasuwancin sa, wannan ya saka har yau gidajensu suna nan a jere da juna kowa da iyalinsa kamar gida daya kawai gates ne daban daban.
Baffan mu, tun yana dan ƙaramin sa suka kulla soyayya da wata da ake kira zainabu a cikin rugar. Tun suna yi aboye har abin ya fito fili kuma maganar taje kunnen Inno. Ita Zainabu ta kasance ta fito daga wani family da tun asalinsu tun kaka da kakanni an riga anyi musu tambarin maita a garin wai wani kakan kakansu maye ne, to wannan tambarin shi ya biyo generations har kan mahaifiyar Zainabu da ake kira da yaya Ladi sannan ya sauka akan yarta Zainabu. Amma duk acikin generation din da yake cikin rugar babu wani wanda zai bada labarin sanda akayi waccan maitar ko kuma tabbacin cewa anyi din amma har lokacin tambarin yana nan. Labari yana zuwa gurin Inno wadda kusan ita take juya kowa har shi kansa hardo saboda kafiyarta akan magana, ta kira baffa tace masa "kul, daga yau babu kai babu Zainabu" sai Baffa ya dauke kai kamar ya bar maganar amma ina.... Zainabu ta riga ta kafa rassa a zuciyarsa.
Lokacin daya gama secondary school dinsa sai Hardo ya debi dukiya ya bashi kamar yadda ya bawa yayunsa yace "tafi birni kaje ka nemi arzikin ka" amma sai Baffa ya debi wani abu daga cikin dukiyar ya mayar wa da Hardo yace gashi a je a nemar masa auren Zainabu in yaso sai ya tafi da ita birnin. Ai kuwa nan da nan dangi suka dauki maganar "Manu zai kwaso mana dangin mayu" Zainabu tana dandali akaje har can su Inna ta da gwoggo Fatima da kawayensu suka yi mata atule, tana zuwa gida ta tarar Inno ta saka yara sunje suna ta jifan gidan su wai mayu ne su sun chinye kurwar Manu. Bakin cikin wannan abu ya saka Yaya Ladi ta hada musu kayansu cikin dare suka bar garin ba tare da kowa ya sani ba. Wannan abu ya tayar da hankalin Baffa na, ya shiga damuwa sosai dan ance har rufe kansa yayi ya daina yiwa kowa magana ya daina cin abinci sai sumbatu da kiran sunan Zainabu, daga nan sai magana ta koma cewar tabbas Zainabu mayya ce dan gashi nan ta kama masa kurwa, akayi ta jike jiken magungunan mayu har dai daga baya ya warke. Sai daya warware sosai ya koma kamar babu abinda yake damunsa sannan ya karbi kudin da Hardo ya bashi ya taho kano neman kudi kamar sauran yan uwansa. Amma maimakon yabi sawun Mamman ya tafi gurin Alhaji Babba shima, sai yaki ya tafi cikin garin kano unguwar Yakasai ya sayi gida madaidaici ya boye sauran kudinsa yana kuma fita neman wani kudin. A hankali sai ya fahimci cewar yana da fasaha ta bangaren kanikanci dan sosai yake jin dadin aiki a karkashin wani bakanike, kuma cikin ikon Allah sai ya yi dace mutumin yana kokarin siyar da garejinsa dan haka Baffa ya dauko ajiyar kudinsa suka yiciki ya siyar masa, nan da nan ya fara wannan sana'a, ya debi yara sunayi shima yana yi da kansa kuma Allah ya saka masa albarka nan take guri ya bunkasa. Ya cigaba da tara yan kudadensa ya hada lefensa yayi komai ba tare da kowa ya sani ba sannan ya koma gida yana neman azo a nema masa aure ya samu mata a kano, nan take Hardo ya aiko aka nemi aure anan bayan layin da gidan sa yake, aka bayar akayi komi sannan matan su Alhaji Babba tare da kanwar Inno da sauran yan'uwa da suka taho daga Kollere suka zo kawo kaya amma suna zuwa sai suka tarar da yaya Ladi a matsayin uwar amarya. Ashe bayan tahowar su sai da Baffa ya yi ciku cikun da ya samu labarin inda suka taho kuma ya biyo su ya sayi gida a kusa da inda suke saboda ya zauna kusa da Zainabu sannan kuma ya turo aka nemar masa aurenta a gurin sabon marikin ta wanda aikatau ne yaya Ladi take yi a wajensa shi kuma ya rike Zainabu kamar ya har yake shirin yi mata aure.
Ai kuwa nan take rigima ta balle, mutanen nan da suka zo daga Kollere suka karewa yaya Ladi tas kamar zasu cinyeta danya, ita dai ta zauna tana ta kukan takaici dan sam Zainabu bata gaya mata gaskiyar waye manemin nata ba dan da ta sani da sam ba zata bari ba balle ayi mata wannan cin mutuncin a gaban jama'a. Babu irin sunan da basu kira yaya Ladi dashi ba, wannan ya saka suma mutanen gidan suka tashi suka tare wa yaya Ladi suka yi wa yanuwanmu korar kare aka watso musu kayansu waje. Wannan ya kara tunzura su, suna zuwa Kollere suka bawa Inno da Hardo labarin abinda manu ya jawo musu a take Hardo ya kirawo Liman yace a daura auren Baffa na da Inna ta wadda duk dangi sun san irin kaunar da take gwadawa manu amma ko kallo bata ishe shi ba duk kuwa da irin baiwar kyawu da Allah yayi mata, dan ko kusa ba za'a haɗa inna da Zainabu ba indai ta gurin kyau ne.
A bangaren Zainabu kuwa ana watsewa daga gurin karbar kayan da ba'ayi ba mai rikonta ya kira yaya Ladi ya tambaye ta ita kuma ta bashi labarin duk abinda ya faru wanda yayi sanadin barin su rugar su, a take yayi mata alkawarin zai samo wa zainabu mijin da manu ba zai taba iya zama kamarsa ba. Haka kuwa akayi sati na zagayowa aka daura auren zainabu aka sakata a mota aka tafi da ita gidan mijinta akan idon Manu.
Wannan kenan....
Tun muna yara labari ya iske mu daga gurin makota na irin wahalar da Inna tasha a hannun Baffa saboda kiyayyar da yake yi mata da kuma bakin cikin raba shi da masoyiyarsa da akayi. Wannan ya saka sana'arsa ma taja baya sosai, yana yin samun kudinsa yaja baya sosai amma sam ba ya taba zuwa gurin Alhaji Babba neman taimako sai dai idan shine yazo gidan yaga halin da suke ciki ya taimaka musu. A haka har shekaru suka ja amma babu haihuwa babu labarin ta, ana cikin haka ne kuma Allah yayi wa Inno rasuwa, wannan yasa Alhaji Babba yaje Kollere ya tattago su Yakumbo Amina da goggo Fatima ya taho dasu gidansa a kano, daga nan kuma duk yayi musu aure anan kanon, a shekarar da Inno ta rasu ne kuma Baffa ya sake sabon aure wanda shi kadai yaje ya nemi abinsa tare da taimakon kanin Hardo da suke dasawa sosai, sai bayan komai ya kankama sannan sauran yanuwa suka sani kuma suka nuna rashin jin dadinsu saboda suna taya Inna ta kishi, amma basu kuma sallama auren ba sai da aka kawo amarya suka bude fuskarta suka ga Zainabu.
Inna ta tayi kukan bakin ciki kamar ranta zai fita, ta hada kayanta tayi yaji zuwa gidan Alhaji Babba shi kuma yazo har gaban Zainabu yace da Baffa "mu yanuwanka kaf babu mu babu wannan matar daka aura, babu mu babu duk wani abinda ya shafe ta" amma Baffa ko a jikinsa. Babban abinda ya kara dagawa yan'uwan Baffa hankali shine dan jaririn da Zainabu tazo dashi a hannunta wanda ko yaye shi bata kai gayi ba. Sunansa Aliyu.
Bayan komai ya lafa zama ya cigaba da gudana cikin rashin jin dadi a gidan mu, Baffa yana iyakacin kokarinsa gurin adalci amma Inna gabaki daya ta burkice, ta riga ta sakawa ranta cewa Baffa yafi son Zainabu a kanta dan haka komai sai take ganin kamar zaluntarta yake yi, ko magana sukayi kasa kasa shida Zainabu sai taga kamar gulmarta suke yi, sannan ga rashin haihuwa, dadin dadawa ga dan da Zainabu tazo dashi wanda Baffa ya dauki son duniya ya dora akansa. A bangaren Zainabu kuma, let me tell you about Zainabu, tunda nake a duniya ban taba ganin mutum mai hakuri irin ta ba, irin mutanen nan ne da ko zaka zuba musu kashi aka ba zasu kula kaba sai dai su karkade maka wanda ya taba jikin ka. Dan zan iya cewa idan da akwai hakkin da Inna take dauke dashi a kanta to hakkin Zainabu ne.
Let me tell you about Aliyu. Zuwansu gidan mu Baffa ya chanza masa suna saboda sunan Hardo ne dashi ya ke ce masa Sadauki, Sadauki tun yana jariri kakkarfa ne na gaske dan karfin sa ne ma ya saka Baffa ya saka masa Sadauki. Baki ne, dan kusan kullum ba'ar da Inna take masa kenan "Baƙin munafiki" ko "baƙi mai bakar zuciya". Yana da godon hanci da nannadadden gashi irin na fulani, bayan wadanda kuma bai dauko komai na Umma (Zainabu) ba.
Shekaru suka sake turawa, akayi haife haife da yawa, musamman gidan Alhaji Babba wanda yayi ta aure aure on his quest for samun yaya maza amma in banda second born dinsa yaya Kabir bai kuma samun namiji ba. Goggo na da yakumbo na ma da akayi musu aure daga baya duk suma duk sun haihu, wannan ya kara daga hankalin Inna. Cikin ikon Allah Sadauki yana shekara shidda a duniya Inna ta samu cikina, amma hatta shi kansa baffa bata bari yasan da cikin ba saboda tana ganin kamar Ummah zata cinye abinda yake cikin nata. Sai da ciki ya fito sannan aka gani, Baffa kamar zai zuba ruwa a kasa ya sha saboda murna, yana murna Ummah tana taya shi.
Baffa ya bani labarin cewa ranar haihuwa ta, shi, Ummah da Sadauki ne suka kai Inna asibiti a motar Baffa. Suka zauna suka jira, Ummah tana ta jerawa Inna addu'ar samun saukin nakuda har Allah ya sauke ta lafiya. A lokacin da aka fito dani a zani aka bawa Baffa shi kansa ba zai misalta irin farin cikin da ya samu kansa a ciki ba, ya karbe ni yana nuna wa Ummah wadda take ta goge hawayen taya Baffa murna. Sadauki yazo ya bude fuskata yana kallona, ya shafa fuska ta yana sannan ya gwada hannunsa a jikin fuskar yana ganin banbancin kalar fatar mu, yayi dariya yace "Baffa wannan babyn kyakykyawa ce" Baffa yace "kanwarka ce sadauki. Sunan ta Haleematus Sadiya" Ummah tace "Allah ya raya mana mai sunan Inno" Sadauki yace "to Baffa mai za'ake ce mata?" Baffa ya shafa kansa yace "matarka ce ai, kai Hardo ita Inno, sai ka zaba mata suna da kanka" Sadauki ya yi shiru yana kallon fuska ta yace "Diyam. Diyam zamu ke ce mata Baffa" Ummah tayi dariya tace "to Allah yasa ta zamo mana maganin kishin ruwa" Baffa shima yana dariya yace "ameen". Ummah ta karbe ni saboda Baffa yaje siyan magungunan da aka rubuta, yana tafiya su goggo Fatima suka zo, da sauri yakumbo ta karbe ni daga hannun Ummah tana tofe ni da adduoi, sannan ta juya gurin Ummah tace "kurwarta kur wallahi. Wannan yarinyar tafi karfinki" daga nan suka juya sunayi wa juna barka tare da yaba kyawuna ba tare da sun lura da Sadauki daya hade rai yana ta zabga musu harara.
[1/9, 10:09 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤ DIYAM ❤
By
Maman Maama
Episode Eleven: Family
Daga asibiti gida suka taho gaba-daya. Suna zuwa Alhaji babba da kawu Mamman suka zo, Kawu Mamman yace "zamu tafi da Amina can gidan Alhaji Babba ta zauna tayi wanka a can" Alhaji babba ya kara da cewa "zata zauna a can sai yarinya tayi kwari, daga nan asamu a basu magungunan mayu da kambun baka saboda rigakafi" Baffa dai bai ce komai ba, Ummah kuma ta sunkuyar da kanta tana share hawayenta dan gudun kar Baffa ya gani ransa ya kara baci.
Daga zuwa wanka sai da nayi wata hudu a duniya kafin mu dawo gida. Inna ta gaya min cewa a cikin watanni hudun nan duk juma'a sai Baffa ya saka Ummah ta shirya ita da Sadauki sun taho dan su ganni amma ko da sau daya ba'a taba barinsu sun wuce ko da gate din gidan ba. Kuma ko sau daya bata taba gaya wa Baffa cewa ba a barinsu su shiga ba. Sai ranar nan ya dawo daga garage dinsa ya samu Sadauki yana ta kuka shi wajen kanwarsa zaije sai Baffa ya tambaye shi "ba jiya kaje ka ganta ba?" Sadauki ya girgiza kai yace "ai ba'a barmu mun shiga ba, kullum in munje koro mu ake yi ace Alhaji Babba yace kar a barmu mu shiga" to jin haka ne fa sai Baffa ya tafi gidan Alhaji Babba ya samu uwargidansa Hajiya Babba yace "wannan idan auren kuke da niyyar rabawa sai ku fada min in aiko mata takardarta, idan kuma kuna son acigaba da auren to lallai a mayar min da iyalina gidana" jin haka yasa Inna babu shiri ta fara harhada mana kayan mu dan tasan halin Baffa.
Yadda tsarin gidan mu yake shine, ta garage ake shigowa daga nan sai dan karamin fili mai bishiyar umbrella da flowers a sides, sai bandaki a gurin. Daga nan zaka shiga karamar kofa zuwa tsakar gida. A tsakar gida kana shiga kofar palon Inna ne a farko, babbab palo ne da dakuna guda biyu suna facing juna. Dakin Baffa kofar sa tana kallon palon Inna, an yi stairs a kofar dakin Baffa da niyyar yin dakuna a saman dakunan sa, amma kuma ba'a samu damar karasawa ba. Dakunan umma kuma suna daga can ciki saboda daga baya aka sayi fili akayi su aka shigo dasu, suma kuma exactly tsarin na Inna ne. Sai kitchen da toilet a tsakar gida.
Ina so ka fahimci wani abu guda daya. Allah ya dorawa Ummah sona kamar yadda take son mahaifina, soyayya ta gaskiya marar algus a ciki. Tun da muka koma gida sai ya zamana koda yaushe ina gurinta, in dai har Inna zata ajiyeni to kuwa Ummah zata daukeni in ina hannun Inna ne dai ba zata iya cewa ta bata ni ba. Wannan yasa sau da yawa Inna ko aiki zatayi sai ta goya ni tace "bazan ajiyeki ba kar waccan mayyar ta dauka". Hausawa su kance mai da wawa, amma wannan baiyi aiki akan Inna ba, ita idonta ya rufe akan kishin Zainabu.
Sadauki har dakin Inna yake biyo ni, Inna ta kore shi amma yaki tafiya in ta hankada shi sai ya zauna a bakin kofa yayi ta kuka shi a bashi Diyam dinsa. Ni kuma tunsanda na fara gane mutane babu wanda nake murnar ganinsa irin Sadauki. Dana fara rarrafe kuwa daga na tashi zan tsallake Inna tana bacci in tafi dakin Ummah ita kuma ta dauke ni ta bani abinci tayi min wanka da kwalliya ta gyara min dogon gashina ta goya ni, Ummah har kaya tasiya min ta ajiye a dakinta saboda in tayi min wanka ta saka min tunda Inna ba zata bata ba. Ummah macece mai tsafta sosai da kwalliya.
Lokacin dana fara magana kalmar dana fara iyawa itace "Sadauki", sadauki ya bani labarin cewa ban ma iya fadi sosai ba dan "sholoki" nake cewa, shi kuma sai ya sakani a gaba yayi da dora min kamar karatu, "ki ce Sadauki" ni kuma sai ince "Sholoki" a haka a haka har na iya, ranar dana fadi sunansa dai dai yaje ya dauko bankinsa da yake taron kudi a kasan gadon Ummah ya fasa ya tafi bakin asibitin Murtala ya sayo min yar tsanar roba ya kawo min a matsayin gift. Na karba ina murna, yace "to wanne suna zaki saka mata?" Nace "Shubeya" (Subay'a) sunan wata jaririya da aka haifa a makotanmu a lokacin. Tun daga ranar kullum ina rike da shubeya ta, hatta bacci tare da ita nake yi har nayi wayo.
Akwai ranar da bazan manta ba duk da kankantata. Ina wasa da Shubeya a tsakar gida Ummah kuma tana wanki Inna tana kitchen tana girki. Wata yarinyar makota ta shigo tace min "Diyam wai babyn waye wannan?" Ta nuna Shubeya, nace "yata ce, yata ce ni da mijina Sadauki". Ai kuwa sai ga Inna da saurinta ta fito daga kitchen tace min "me kika ce Diyam?" Na sake maimaita mata tunda ni a lokacin bansan ma ma'anar kalmar miji ba, nan take inna ta ciro bulala a bishiyar tsakar gidan mu ta daga skirt dina ta ringa tsula min a kafafuwana ina ihu tana cewa "zaki kara cewa Sadauki mijinki?" Ummah ta ajiye wankin hannunta ta rugo da gudu takwace ni daga hannun Inna ta shige dani dakinta ta rufe kofa. Inna ta ringa bugun kofar amma taki budewa sai ma dauka na da tayi ta kaini toilet ta wanke min kafafuna da suka tashi suka yi rudu rudu, ta shafa min vaseline ta kwantar dani akan gadonta tare da Shubeya ta.
A waje kuma bayan Inna ta gaji da bugun kofa sai ta dauki waya ta kira gidan Alhaji Babba cewa ga Ummah nan ta dauke ni ta shige dani daki ta rufe kofa ita bata san me take yi min ba. Nan da nan sai ga gwoggona da nake cewa Aunty Fatima wadda akayi dace taje gidan a lokacin, da Adda Zubaida babbar 'yar Alhaji babba wadda a lokacin take zawarci, da wadansu da suke yammata a lokacin suka zo gidan mu suka yi ta bugun kofar Ummah, ai kuwa tana budewa suka rufe ta da duka Inna kuma ta shige ciki ta dauko ni tana duba lafiya ta, a lokacin Baffa ya shigo rike da hannun Sadauki daya dauko daga makaranta, yana shigowa yaga abinda ya faru ya nemi ba'asi kowa ya bashi side din story dinsa, a take zuciya ta ciyo shi ya rubuta wa Inna takarda saki daya, ya kuma karbe ni daga hannun ta ya mika wa Ummah ni.
Wannan yana daya daga cikin abubuwan da har yau Inna ta kasa mantawa a rayuwar gidan mu. A lokacin sai da Hardo da kansa yazo har kano ya sasanta maganar sannan Baffa ya mayar da ita amma da sharadin kar wanda ya kuma daga hannu ya dakar masa mata. Bayan wannan Inna ta rage tsangwamar Ummah sosai sai dai ba za'a taba kiran zamansu da zaman lafiya ba.
Shekara ta biyar a duniya Inna ta haifi kanwata, Asma'u, tun daga nan kuma shikenan babu wata haihuwar. Sadauki bashi da kokari a makaranta, dan yana daga yan karshe karshe a position a ajinsu, amma kuma Allah ya bashi fasaha a kan kere-ƙere. Wannan yasa kullum daga ya dawo daga school zai shirya yabi Baffa zuwa gareji, kafin wani lokaci Sadauki yasan kan mota sosai dan zai iya kunce inji ya mayar ya hada, duk minor gyaran da aka kawo wa Baffa sadauki ne yake yi kuma ya gyaru sosai. Ina iya tuna lokacin da Baffa yake cewa "Sadauki da ace ni mai kudi ne da kasar waje zan kaika kayi karatu, tunda karatun kasarmu duk theory ne kai kuma kafi gane practical".
Ranar nan ya dawo daga makaranta na tafi da guduna na rungume shi ina masa oyoyo, ya ciro alawar da ya siyo min da kudin taran sa, wadda yasan in dai ya shigo babu ita to sai nayi masa rigima, na karba nace "Nagode Sadauki" ya kamo kunnena yace "daga yau hamma Sadauki suna na" na gyada kai ina murza kunnen da yaja, Ummah ta harare shi tace "sai son girma kamar gwambo, ga kuma mugunta" ni dai na wuce dakin Inna da sauri na kai mata sweet din nace ta bude min. Ta karba tana tambayata "waye ya baki?" Nace "hamma Sadauki ne" ta kamo kunnena da sauri tana daga muryarta yadda Ummah zata ji daga waje tace "hamma wa? A gidan uban wa ya zama hammanki? Babu hadin danga da garafuni kar in kara jin kince masa hamma" na saka kuka saboda zafin da kunnen yake min nace "na daina Inna" ta sake ni na fita da gudu gurin Ummah ina share hawaye na, ta dauke ni ta dora akan cinyarta ta bude min alawar tana rarrashina. Daga ranar ban kuma cewa Sadauki hamma ba shima kuma bai kuma cewa in gaya masa ba
Shekarar da aka saka ni primary Sadauki ya shiga secondary, dan haka a lokacin Baffa ya siya masa keke yake zuwa akai. Ni kuma Baffa ne da kansa yake kaini a motarsa tunda makarantar mu babu nisa kafin ya fita amma ranar nan sai na saka rigima nace ni a keken Sadauki zan ke tafiya, nan take Sadauki yace "Baffa ka barta, kaga hanya daya ne sai in ajiyeta in an taso kuma in biya in dauke ta" Inna tace "kaji mugunta, salon kake kayar da ita a hanya kullum? In banda mugunta ga motar ubanta sai ace ta hau keke? To ba zata hau din ba" na makale kafafa ina kakalo hawaye, Baffa ya tsaya yana kallon Inna saboda yaji zafin maganar ta amma saboda muna gurin sai kawai yace "bishi ku tafi, Allah ya kiyaye hanya" Ummah tace "ka bi a hankali, kar kaje kana wannan rawar kan naka ka jefa ta a kwata" ni kuwa sai tsalle da murna, ya dora ni a gaban sa ya saka na rike kan keken sannan ya taka keken muka tafi. Muna barin layin mu na saki kan keken na fara kokarin mikewa tsaye, ya rike ni da hannu daya yace "ki zauna Diyam, zaki fadi fa" na ture hannunsa "ka tsaya kaga abinda zamuyi, irin na titanic, nice rose kaine jack" na mike na bubbude hannayena, ai kuwa kafin yayi managa na zame zan fadi, garin rikeni shima ya biyo ni sai gamu a kasa a kan kwalta, guiwowina duk sun daddauje goshina ma haka. Na dage kuwa tun karfina na ringa zunduma ihu, yayi rarrashin duniyar nan naki inyi shiru, haka ya dauko ni da hannu daya ya jawo keken da daya hannun muka taho gida.
A bakin gate muka tarar da Baffa yana shirin fita. Yana ganin mu ya taho da saurin sa ya karbe ni a hannun Sadauki ya dora ni a saman mota yana duba ciwon da naji. Tun kafin Sadauki ya bada labarin abin da ya faru sai ga Inna ta jiyo kuka na ta fito da sauri tana cewa "ai dama sai da na fada, yaron nan babu komai a zuciyarsa sai zallah mugunta, gashi nan yaje ya jefar min da yarinyar ya cuce ni" Baffa ya juya kanta shima da nasa fadan sukayi tayi, basu san sanda Ummah ta fito ta dauke ni ta wankemin ciwon da naji ba ta chanza min kaya sai ji sukayi tace "baban Diyam ko zaka kaita chemist a duba ciwon sosai?" Baffa ya juyo yana kallonta yace "Allah yayi miki albarka Zainab" tayi murmushi tace "ameen, Nagode". Sannan ta cewa Sadauki "kaima sai ka bisu a duba hannunka" sai a lokacin duk muka lura cewa shima yaji ciwo a hannunsa yana ta jini, yayi saurin nuna jarumta ta hanyar cewa "babu komai" amma Baffa ya tilasta masa sai da ya bimu.
Na jima da wannan tabon a goshina, duk wanda ya tambaye ni sai ince "Sadauki ne ya kayar dani a keke".
Writing......
[1/10, 9:56 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Twelve: My Brother, My Friend.
"Diyam, ba zaki cigaba da cin abincin nan ba sai nazo ko?" Na daga kai ina kallon Inna da take zazzare min ido cike da barazana. Na debi shinkafa a chokali na kai bakina ina taunata da kyar saboda koshin da cikina yayi ji nake kamar zanyi amai. Na shawabe fuska "Inna wallahi na koshi, nasha tea, naci bread, naci kwai, bazan iya cin shinkafa ba kuma amai zanyi" tace "kiyi aman, sai ki zo ki cigaba da ci" na kalli kofa da sauri saboda motsin mutum dana gani, ta gefen labule na hango Sadauki sanye da uniform dinsa, muna hada ido yayi min alamar in taho da hannunsa, na ture abincin na sunkuci jakata zan fita Inna ta fizgoni ta dangwarar akan kujera tace "in kika fita daga dakin nan sai na yanke kafafuwanki" ta harari kofa tace "bakin munafuki, babu inda zakuje tare" ta kara dangwara min kwanon shinkafa a cinyata.
Muryar Baffa na jiyo a tsakar gida "kai kai kai, Sadauki wai baku tafi ba har yanzu? Ai kun makara, ina Diyam din?" Nayi saurin ajiye kwanon amma hararar da Inna ta jeho min yasa na dauka na cigaba da rikewa. Baffa ya leko yace "ke Diyam, ki fito ku tafi mana kin makarar dashi zaki sa a dake shi" Inna tayi charaf tace "ya tafi kawai kar a hukunta shi a makarantar su. Diyam bata gama karyawa ba" na ajiye kwanon nace "na gama Baffa, tun dazu na gama Inna ce ta hanani fitowa" na zagaya ta gefenta na fice daga dakin da sauri na rungume sadauki shi kuma ya dauke ni ya dora akan kekensa muka tafi.
Haka mukayi ta fama kullum ba fashi, kullum sai inna tayi ƙoƙarin hanani bin Sadauki ni kuma sai na nace na bishi. Shi zai kaini har class dinmu yaga na shiga sannan ya tafi tasa makarantar. A lokacin dana kara girma kuma sai ya daina dorani a keken sai dai mu tafi a kafa yana jan kekensa a hannu har sai ya kaini sannan shi kuma ya hau ya tafi tasa. Haka islamiyya ma tare za muje, in asma'u ta biyo ni sai in korata ince tabi yaran makotanmu. Sadauki shine yayana, shine abokina, shine kawata, shine abokin shawarata, duk da cewa a lokacin akwai yarinta sosai dan haka duk shawarar ta shirme ce, shima kuma tunda ba wani girmata yayi sosai ba haka zai bani amsar shiririta.
Duk kawayena, na boko dana islamiyya sun san Sadauki, wadda bata sanshi a fuska ba kuwa to tabbas tasan sunansa saboda da wahala in muna hira in iya hada sentence guda ba tare da sunan sadauki ya fito a ciki ba. Duk kuwa sanda wani a ajin mu ko ajin gaba damu yaci zalina ko na tsokani wani ya dake ni to tabbas sai jikinsa ya gaya masa in ya shiga hannun Sadauki, wannan yasa ake shayin tabani ko a yaran unguwa sai dai in na tsokani yaro yayi hakuri dan dole dan sun san cewa sadauki ƙashi daya ne dashi.
Bashi da surutu sam, he is a good listener rather than a talker, ko a gida in dai kaji yana hira to dani ne, ko da Baffa, amma ko Ummah basu cika zama suyi doguwar hira ba. Yana da zuciya da fada in an taba shi ko an taba ni, amma ni din ko daga min murya baya iyayi balle yayi min fada. Kuma duk zuciyar Sadauki, bai taba daga kai ya kalli Inna in tana gayawa Ummah magana ba, sai dai ka gani a fuskarsa cewa ransa ya baci amma ba zai mayar mata ba. Yana da kazar kazar sosai kuma baya zama guri daya, in har baya makaranta to yana gareji in kuma baya can to yana gida yana aiyuka, zai share gidan mu tas ya gyara wa Baffa dakinsa ya wanke masa mota. Watarana nace masa "Sadauki kai baka gajiya ne? Ka kwanta ka huta mana" Sai yace "wa kika taba gani yayi achieving wani abu a kwance? In kana son wani abu you have to work hard to earn it".
Ranar nan, a lokacin ina primary 5, ina da shekaru goma da yan watanni sadauki kuma yana sha shida. Anti Hafsa, wadda muke kira da Mama tazo gidan mu, suna ta hira da Inna ni kuma ina kwance sun dauka bacci nake yi naji Mama tace "ni Addah kullum sai inga kamar kara ramewa kike yi, har yanzu kin ƙi ki kwantar da hankalinki kiyi ƙiba kema" Inna tace "hmmm Hafsa ina hankalina zai kwanta ne bayan wannan mayyar ta sakani a gaba, ita da wannan baƙin dan nata sun hana zuciyata hutawa sam" Mama tayi dariya tana riƙe baki tace "kai Addah, daga ni har ke fa mun sani cewa bafa mayyar bace da gaske, muna sane muke takewa kawai dan mu bata mata rai amma da mayyar ce da ba tini ta cinye ki ba ko ta cinye yayanki? musamman tunda ita bata haihu anan gidan ba?" Inna tace "to ai yanzu gashi danta ya chinye kurwar Diyam ko? kamar yadda ita kuma ta chinye ta baban Diyam, na rasa yadda zanyi da yarinyar nan, nayi fadan nayi nasihar nayi dukan amma abun ya faskara, gashi da shegen naci kamar jinin mayu, bana son mu'amalar yarinyar nan da yaron nan wallahi kullum gani nake kamar zai cutar da ita, kullum in suna tare sai inyi ta fargaba" Mama ta sake dariya tace "bafa mayen bane kin sani kuma. Yara ne, ki barsu suyi wasansu mana, ki kwantar da hankalinki kiyi tayi mata addu'a" Inna tace "idan ba maye bane ta bangaren uwarsa waye yasan waye shi ta bangaren ubansa? Ni fa tunda matar nan tazo gidan nan da yaron nan ban taba jin ko da sau daya ta ambaci mahaifinsa ko wani dangin mahaifinsa ba, ban taba ganin an kaishi dangin ubansa hutu ba. Ni ba dan makota sun tabbatar mun an daura mata aure anan bayan layi ba da sai ince anya ba shege bane ba? To ko ma dai ba shegen bane ba akwai wani mummunan abun da suke boyewa a game da mahaifinsa. Shi kuma babansu ko na tambayeshi cewa yake ina ruwana? Wai ai Allah ma ya hana mutum ya shiga abinda babu ruwansa" Mama tace "to yanzu menene abin yi?" Inna tace "yanzu ni dai so nake ki tambayi baban Diyam tunda wannan satin zasuyi hutu dan Allah ya baki ita da Asma'u duk ki tafi dasu gurin ki suyi hutunsu a can kona samu zuciya ta ta huta kafin su dawo". Mama tace "au yanzu akan agolan kike so ki raba yara da gidan ubansu? To Allah ya sa ya bani din dan kinsan halin mijin naki ba wanda yake gane kansa sai zainabu abu, Allah yasa ma kar yace sai dai in hada har sadaukin in tafi dasu tare" ta fada tana tsokanar Inna, Inna tace "Allah ya kiyaye. Allah ya tsari gatari da saran shuka. Insha Allah ko kofar gidanki ba zai sani ba ballantana ya ga ciki". Ni dai ina kwance ina jinsu, amma sai naji duk raina ya baci saboda babu abinda na tsana irin a kaini wani gidan, saboda bana so a raba ni da Sadauki.
Bayan ta tafi da daddare ina dakin Ummah muna cin abinci a plate daya dani da ita da sadauki. Tana ta loda min nama a gabana wai inci inyi girma in kamo Sadauki. Shi kuma yana ta min dariyar yadda na dage bil hakki nake cin abinci wai kamo shi zanyi duk kuwa da cewa a lokacin ya kusan yin biyu na a girma tunda ni bani da garun jiki shi kuma girma ne dashi. Nace da Ummah "Ummah menene agola?" Tayi shiru tana kallona bata ce komai ba, na cigaba "Inna naji ita da Mama suna cewa wai Sadauki agola ne, sannan kuma maye ne" Inna ta ajiye chokalin hannunta, Sadauki ya kamo hannuna yace "Diyam, agola shine yaron da aka haifa sai iyayensa suka rabu sai uwarsa tayi wani auren ta tafi dashi, mijinta kuma ya rike shi kamar dansa. Kamar ni kenan yadda Baffa ya rike ni amma ba shine ya haife ni ba" nace "to kuma da gaske kai maye ne?" yayi dariya yace "sosai ma kuwa. Yanzu ma sai in cinye ki" ya fada yana yi min chakulkuli ni kuma ina kyalkyala dariya nace "wayyo na tuba kar ka chinye ni" hararar da Ummah ta zabga masa ne yasa ya sakeni muna cigaba da dariyar mu sannan Ummah ta kalle ni seriously tace "Diyam, idan kinji innar ki tana hira da wani, ko cikin yan uwanku ko baffanku, ki daina zuwa kina gaya min kinji? Nima kuma in kinji ina magana da wani kar kije ki gaya mata. Babu kyau kinji?" Na gyada kaina. Asma'u ta leko tace "addah ki zo inji Inna" Ummah ta yafito ta tace "zo Ma'u kici abinci" Asma'u ta makale kafada, Ummah ta dauko cinyar kaza tace "zo ki karba" a hankali Asma'u ta shigo ta tsaya daga nesa ta miko hannun. Ummah tayi charaf ta kamata ta dora akan cinyarta, tun Asma'u tana zillewa har sai gata dumu dumu tana lomar abinci. Muna cikin yi mata dariya nida Sadauki Inna ta shigo da saurinta, ta damki kunnena ta damki na Asma'u, a tare muka saki kara a haka ta fige mu har daki taja kofar ta ta saka sakata.
[1/11, 10:44 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Thirteen: My Saviour
Ranar da mukayi hutu a ranar Mama ta aiko babban danta yaya Mukhtar wanda kusan sa'an Sadauki ne yazo tare da drivern su ya dauke mu. Lokacin Sadauki bayanan sun tafi gidan yaya Ladi shida Ummah, haka na shirya raina duk babu dadi ga yaya Mukhtar yana tayi min jaraba wai in yi sauri ina bata masa lokaci ni kuma Allah Allah nake su Sadauki su dawo kafin mu tafi dan muyi sallama amma ina, haka ya tasa keyar mu yana ta rankwashi na muka shiga mota ina ta waigen ta inda Sadauki zai billo amma har muka sha kwana babu shi babu alamar sa.
Tun daga nan fa shikenan na turbune fuska kamar an aiko min da mutuwa. Da muka je gidan ma da kyar na gaishe da Mama, ta harare ni tace "ke kuma me akayi miki kike wannan bacin ran?" Nan take hawaye ya fara zubo min, na saka bayan hannu na ina gogewa nace "ni gidan mu zan koma" yaya Mukhtar ya dungure min kai yace "yi mana shiru anan, shagwababbiya kawai" ai kuwa nan take na bare baki "wayyo Allah na wayyo Sadauki" Mama ta tafa hannu tana salati "wayyo Sadauki? Dama abinda duk Adda take fada gaskiya ne? To zaki ci ubanki ne ke da sadaukin, babu inda zaki je muna nan dake a gidan nan".
Mama yayanta biyar, yaya Mukhtar ne babba sai yaya Abdullahi sannan Rumaisa wadda take sa'a ta kuma a lokacin kusan itace best friend dina bayan Sadauki sannan Muhsina sai Rufaida yar auta kuma sa'ar Asma'u.
Tunda muka je gidan, ga dai kayan wasa nan iri iri saboda babansu mai budi ne amma ni sam basa gabana, sai in ringa tunanin ina ma tare da Sadauki muka zo, nasan da zai so video game din su Abdullahi. Mama tayi fadan har ta gaji ta rabu dani tace "shegen taurin kai irin na uba" ni dai nayi tagumi ina kallonta. Da Rumaisa kadai muke dan yin hira, shima kuma duk kusan hirar sa ce dan ita din ma mutuniyarsa ce saboda ni, duk sanda taje gidan mu yana yi mata wasa sosai. Ranar nan muna backyard,su yaya Mukhtar suna ball mu kuma muna kallon su. Nayi tagumi sam hankali na baya tare dasu ban sani ba ashe hawaye ne suke bin kumatu na, kawai sai jin saukar ball nayi a goshina, na hantsila na fada bayan bench din da muke zaune, nan take sai ga jini yana zuba daga hancina. Rumaisa ta zagayo tana yi min sannu, na mike ina kallon yaya Mukhtar da yake yi min dariyar mugunta alamar shine ya buga min ball din yace "yanzu sai kiyi kukan mai dalili ai" murya can kasa nace "Allah ya isa na kuma sai na gayawa Sadauki" ai kuwa a guje ya bini har bayan Mama, ta rike shi tana tambayar abinda ya hada mu ga hancina da jini, ni dai ban tsaya bin ta kansu ba na shige daki na rufe kofa.
A daddafe mukayi sati biyu, a ranar da muka cika sati biyu kuwa sai ga Baffa ya sako Sadauki a gaban mota sunzo daukar mu. Ina fita maimakon in tafi gurin Baffa sai na wuce shi na tafi gurin sadauki. Mama ta fito ta gaishe da Baffa tana mita "hutun nasu fa bai kare ba, ni ai ba'a gaya min yau za'azo daukar su ba gashi ko dinkunan su ba'a karbo a gurin tailor ba" Baffa ya daga Asma'u da tazo gurinsa da gudu yace "in an gama dinkin a aika musu dashi gida".
Tun a mota na fara zayyanawa Sadauki duk irin cin zalin da yaya Mukhtar yayi min, tun daga dungemin kan da yayi har zuwa doka min ball da yayi a ka. Baice komai ba sai ya mulmula min goshin kamar yanzu akayi dukan. Bamu kuma tayar da maganar ba ni har na manta ma sai kawai rannan Mama ta aiko yaya Mukhtar ya kawo mana dunkunan da tayi mana ni da Asma'u. Sai da muka gama gwaggadawa muna ta murna ya fito Inna ta biyo bayansa tana bashi sakon godiya zuwa ga Mama, bai yi aune ba sai jin saukar ball yayi a goshinsa, ya hantsila ya fadi a gaban Inna jini yana bin hancinsa. Muka daga kai cike da mamaki sai ga Sadauki yana saukowa daga stairs din saman dakin Baffa, ya tsaya a gaban Mukhtar yace "gobe ma in Diyam ta kara zuwa gidan ku ka sake buga mata ball aka".
Inna tayi kukan kura ta riko shi, amma sai nayi sauri na rike hannunta har ya samu ya zame ya fice da gudu, ai kuwa sai tayo kaina, na ruga sai dakin Baffa na rufe kofa ina leken ta taga. Tayi ta banbamin fada tana debe wa Sadauki albarka "bakin mugu mai bakar zuciya. Allah ya isan sa, idan ya dake ta ina ruwanka? Dan uwanta ne, kai kuma fa? Marar asali" tayi tayi dai babu wanda ya kula ta, ta tashi Mukhtar ta bashi ruwa ya wanke fuskarsa amma sai ya kasa fita wai tsoro yake kar Sadauki ya kuma kamashi a waje. Haka ya koma daki har sai da na fito nace "kayi tafiyarka, babu abinda zaiyi maka ai ya ramamin". Kuma haka ya fita a tsorace amma Sadauki yana kan mota ko kallonsa baiyi ba. Tun daga ranar ko kallon banza yaya Mukhtar bai kara yi min ba.
Yana daga al'adata kullum da daddare dakin Ummah nake zuwa inyi kallo. Inna ta hana amma sai Baffa ya daure min gindi yace "ai homework Sadauki yake koya mata a can din. In kuma kin iya sai ke kike yi mata a daki" Inna bata yi makaranta ba dan haka dole ta hakura. Yes, muna yin homework din in mun gama kuma muyi kallo muyi hira ko Ummah tayi mana tatsuniya. Inna dai ba'a san ranta ba. Wannan yasa ta dage sai data samo mana islamiyyar dare duk kuwa da cewa muna yin ta assuba sannan muyi ta yamma. Baffa yayi magana tace "ai ilimi baya yawa" haka ina ji ina gani kullum nake tafiya islamiyya da daddare. Ni raina baya son islamiyyar nan musamman saboda malaman akwai cin zali kullum zaka gansu suna yawo da doguwar bulala ni kuma babu abinda bana so irin a taba lafiya ta. Ga prefects suma da shegiyar mugunta. Kullum sai Sadauki ya tabbatar naje da wuri saboda kar a dake ni, in lokacin tashi yayi kuma shi zaije ya taho dani saboda kar wani ya tare ni a hanya yaci zalina.
Ranar nan sai na kasa bada hadda. Yasaiyadi ya ware mu ya kira monitan aji uku yace ya zane mu. Haka aka zazzabga min dorina a baya na, gurin ya tashi yayi rudu rudu. Tun da aka dake ni nake kuka har aka tashi Sadauki yazo tafiya dani. Ina fita kuwa na gaya masa duk abinda ya faru, yace in nuna masa wanda ya dake nin a nuna masa muka taho gida. Dama ranar laraba ne, ban san yadda akayi ba sai ranar assabar na tafi makaranta wata yar ajinmu ta tare ni a hanya tace "Diyam, wallahi kar ki je makaranta yau, ana nan an ciro bulalai ance yau sai an zane ki, wai yayanki Sadauki ya tare monitan daya dake ki rannan ya zane shi shida kaninsa. Wallahi yasaiyadi uku ne suke jiranki a makaranta" nan take cikina ya duri ruwa, na juya da sauri sai gida, ina shiga na lallaba na wuce dakin Inna na shige dakin Ummah, nayi sa'a itama bata nan tana dakin Baffa sai Sadauki yana kallo. Na dora hannu aka ina kuka na gaya masa abinda ya faru, yace "zauna. Kin daina zuwa islamiyyar daga yau. Ai ba jakarsu bace ke da zasu saka ki a gaba suna duka kamar ganga. Ina nan zaune a kusa dashi har Ummah ta dawo, ita ta dauka har na taso daga islamiyyar ne dan haka tace "Diyam ki tafi gurin innar ki kar tazo tana nemanki".
Washegari ina kallon Sadauki yana ta yan aiyukansa a saman rufin dakin Baffa, da Baffa yayi masa magana sai yace "Baffa zafi ake yi, hawa zanke yi sama ina shan iska da daddare" yana gama wa sai ya kira ni gefe yace min "idan Inna tace ki tafi islamiyya da daddare ki hau sama kiyi kwanciyarki" shikenan nayi graduating daga islamiyyar dare. Kullum da dare in lokacin islamiyya yayi sai in lallaba in hayewa ta sama inyi kwanciya ta akan katifar da Sadauki ya shimfida min. Daga baya sai Sadauki shima ya fara biyo ni, yazo muyi ta hirar mu muna dariya, ko kuma yazo mana da games din Chess, Watt ko ludo muyi tayin kayanmu. Amma duk kanin mu munsan cewa duk wanda ya juri zuwa rafi to kuwa tabbas watarana zai fasa tulunsa.
[1/12, 11:38 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Forteen : My Boyfriend
Ina ajin karshe a primary Sadauki shi kuma yana ajin karshe a secondary. Mu nan wai muma mun girma a ajin mu sai ake yin irin soyayyar nan ta yarinta. Kowa da saurayinta, amma ni banda ni. Wannan abin yana kona min rai kullum ina ganin ana rubutowa kawayena love letter su karanta suyi replying amma ni babu wanda yake rubutomin.
Akwai seat mate dina lubabatu kuma itace headgirl, ita head boy din mu yake so, kuma dan rainin hankali ni yake bawa wasika in bata wai kunyarta yake jiba zai iya bata ba, ita ma kuma inta rubuta reply ni take bawa in bashi, su basu san haushi suke bani ba gabadayan su.
Ranar nan, ina koro yara aji an gama breakfast sai muka hadu dashi. Muka gaisa yana ta sosa keya ni kuma na fahimci me yake so na bata rai nace "kar ma ka tambaye ni, ni bansan inda take ba" yace "ni fa ba cewa nayi ina neman lubabatu ba, yanzu ba zamu gaisa ba sai kinyi tunanin wani abu?" Nayi gaba nace "oho dai, kai kasani" ya biyoni "dan Allah Halima kina ji ba? Ki ce mata bata bani amsar jiya ba fa" nayi kamar ban jishi ba nayi tafiyata. Bayan naje na zauna a aji na ganta tana ta faman zanen flower a jikin plain sheet, nayi tsaki nace "rashin aikin yi, wai soyayya? Yar karama dake har kin ita rubuta wa saurayi wasika. Allah ya sawake, kuma in baki daina ba sai naje gidan ku na fada" ta harare ni tace "Allah yaso ma dai ni wasika kawai nake rubutawa saurayi na, ke kuma fa? Da kullum kuke yawo ke da naki saurayin?" Nayi galala ina kallonta ina tunanin waye take nufin saurayi na, sai kuma nayi dariya nace "wai Sadauki kike nufi? Bafa saurayi na bane ba, yayana ne to" ta harare ni tace "in yayan ki ne to ya akayi ke fara shi baki? Kuma ai munsan ba babarku daya ba kuma baban ku ma ba daya ba" naji haushin maganar ta na dauki jakata na bar mata seat din na koma wani. Amma kuma sai maganar ta ta tsaya min a raina, wai Sadauki ne saurayina.
Ina nan zaune har aka tashi. Ana ta zuwa daukan dalibai sai ga wata sa'adatu yar A ta leko ta window tace da karfi "Halima Usman ki fito ga wannan saurayin naki yana nemanki" Lubabatu ta juyo tana yi min dariya ni kuma na kara kulewa, na dauki jakata na fita.
Kamar hadin baki sai gashi washegari muka je gidan Mama tare da Inna, muna ta harkokin mu dasu Rumaisa su Inna kuma suna hira, sai naji kamar sun ambaci sunan Sadauki sai na saurara ina jin abinda suke cewa. Inna tace "mtsw, Hafsa ba zaki gane abinda nake nufi ba, ni nake zaune da yaran nan ni kuma nake ganin abinda nake gani wallahi. Ina jin tsoro Hafsa. Bana son abinda nake gudu ya kasance" Mama tace "wai gani kike in sun girma zai iya cewa yana son aurenta?" Inna tace "sosai ma kuwa, ya riga ya shanye ta kamar yadda na fada miki, kuma alamu sun riga sun gama nunawa. Tsoro na Allah tsoro na kar ya furta abinda nake tunani saboda kinsan halin baban su, wallahi indai yaron nan yace yana son yarinyar nan bashi ita zaiyi" Mama tace "chafdi. Kice tsugunne bata kare ba kenan. Allah yaji kan inno, da tana raye wallahi da tuni ta fatattaki yaron nan daga gidan nan. Ni babban tashin hankali na shine rashin sanin asalin sa. Ga tambarin da uwarsa take dashi. Yanzu menene abinyi?" Mama tace "ni so nake kije ki kai maganar nan gidan Alhaji Babba, shi kadai ne zaiyi min maganin fitinar nan wallahi" Mama tace "wanne Alhaji Babba? Alhaji Babba ba zai iya yi miki maganin komai ba saboda kinsan halin mijinki ba lallai ne in Alhaji Babba ya gaya masa magana ya dauka ba. Ke dai addu'a zamuyi tayi, idan har Allah ya rubuta aure a tsakanin su to Allah ya daidaita lamarin" Inna tayi saurin girgiza kanta tace "babu, insha Allah babu, da wanne zanji? So kike zuciya ta ta buga?" Mama tace "ni Adda ba sanin yaron nan nayi sosai ba, gaya min, bayan rashin sanin ubansa da ba'ayi ba yana da wani aibun ne?" Inna ta bude bakinta ta rufe, ta kasa tuna wani laifi da Sadauki yayi mata wanda zata bayar da misali da shi.
Duk a cikin hirar su Inna kalma biyu ce ta tsaya min a raina. "So" da kuma "Sadauki" nayi ta kuya kalmomin a raina ina tunanin ma'anar su. Wai soyayya muke yi ni da Sadauki? Sai kawai naji wani excitement ya lullube ni. I can't wait in bawa Sadauki wannan labarin. Magrib tana yi inna ta ce mu nemo hijaban mu da takalman mu mu tafi gida "kunga yau na jawo muku kunyi fashin makarantar yamma, gwara mu tafi da wuri kar Diyam ta rasa ta daren itama" sannan ta bawa Mama labarin dalilin da yasa ta saka ni a islamiyyar dare. Mama tana ta dariya muka taho.
Muna zuwa gida sallar isha nayi kawai na saka hijab dina na dauki jakar islamiyya ta, Inna ta bani kudi wai ko zanga yara suna siyan wani abu. Nayi mata sallama na fita amma ina fita sai nayi hanyar kofa kamar na tafi sai nacire takalmana na dawo da baya na zagaya ta kofar dakin Baffa na hare saman bene. Ina zuwa na zubar da takalma na a gefe na cire hijab dina na ninke dan kar yayi squeezing na kwanta rigingine na rufe idona ina jin dadin iskar da take kadawa a gurin. Na jima a haka ni ba bacci ba ba kuma ido biyu ba. Sai naji a jikina kamar ana kallona. Nayi murmushi na bude idona a hankali na sauke su a cikin na Sadauki daya zauna ya saka ni a gaba ya zuba tagumi yana kallona cikin hasken farin wata. Yayi murmushin daya bayyana kyawawan jerarrun hakoransa Yace "wato kinji dadin iska ko? Shine har da bacci?" Nayi dariya kawai, nace masa "ya garage din yau, mota nawa ka gyara yau?" Ya bata rai yace "daya" nace "kawai?" Yace "kinsan irin lalacewar da motar nan tayi kuwa?" Nan ya fara bani labarin irin parts na motar da suka lalace da irin yadda ya gyara su, ni kuma nayi shiru ina sauraronsa duk kuwa da cewa ba ganewa nake yi ba, sai daya gama sannan yace "to ya gidan Maman" nace "lafiya lau" sai kuma na bata rai nace "ina sweet dina?" Yayi murmushi ya saka hannu a aljihu ya dauko alawar splash guda biyu ya miko min, na karba nayi masa godiya sai kuma na bare daya na mika masa dayar kuma na jefa a baki. Sai ya zagaya bayan pillow na shima ya kwanta rigingine ya dora kansa akan pillown da nake kwance akai, sai ya kasance shi a kasa yake ba'a kan katifar da nake ba. Yayi shiru kamar bacci yakeyi amma ni nasan ba bacci yake yi ba, nasan kallon sky yake yi kamar yadda nima nakeyi.
Can kuma sai naji yace "Diyam? Yau sky tayi kyau sosai" nayi murmushi ina kallon yadda wata ya cika very full, ga stars ba adadi sun cika sararin samaniya. Sai na juya nayi rub da ciki na tallafe fuskata da hannayena, wannan yasa dankwali na ya zame saboda santsin gashi, gashin ya zubo a fuskar Sadauki, ya saka hannu ya tattare su gefe yana kallona, direct nace masa "Sadauki wai kai saurayi na ne?" Sai ya kware da alawar da yake sha, ya mike zaune yana tari yana bubbuga kirjinsa sannan ya kalle ni da mamaki yace "what?" Na daga kafada nace "nima haka naji ana cewa" ya kwanta rub da ciki irin yadda nayi yayi tagumi da hannayen sa yana kallona fuskarsa cike da mamaki yace "a ina kika ji ana fada?" Na bashi labarin abinda ya faru a school, ya ja hancina har yanzu da dariya a fuskarsa yace "ke kuma me kika ce? Are you my girlfriend?" Na juya na koma rigingine nace "oho" yace "oho? Baki sani ba?" Nace "eh, to kaga ai kai baka rubuta min letter da kalaman soyayya" yayi dariya sai kuma ya rufe bakin sa dan kar ajiyo dariyar tasa daga waje yace "kalaman soyayya Diyam? Naga ta kaina ni Aliyu, Diyam a ina kika san kalaman soyayya?" Nace "a makaranta mana. Ka ga lubabatu headgirl din mu to head boy ne saurayinta, kuma kullum sai ya rubuto mata letter ya bani na bata" yace "ohh, wato abinda kuke yi kenan ko? Head boy saurayin headgirl, ke kuma assistant head girl ke ce budurwar assistant head boy ko?" Nace "lah, ni me zanyi da wannan kazamin?" Ya koma ya kwanta, sannan yace "to ni yanzu me zanyi kenan in ina so in zama saurayinki?" Na daga kafada nace "wasika zaka rubuto min" yace "to ni ban iya ba, ki koya min" nace "kaga, plain sheet zaka samu, sai kayi zanen flowers da pencil, sai kazo ka zana heart da arrow yayi crossing heart din ka rubuta sunan ka a sama nawa a kasa, sai ka rubuta I love You Diyam a saman takardar, a ciki kuma sai ka rubuta min kalaman soyayya shikenan" yayi murmushi mai sauti yace "to ni ai ban iya kalaman soyayyar ba" na bata rai nace "ni ma ban iya ba ai" muka yi shiru gaba-daya muna kallon sky. Can sai naji yace "Diyam. Look at the stars, kinga yawansu ko? To zabi daya wadda kike ganin a idonki kamar tafi sauran dukka haske. Concentrate on it kiyi ta kallonta ita kadai ki manta da sauran, ki saka a ranki kamar babu sauran kowanne star a sky din nan sai wannan wadda kike kallo. A hankali zaki ga sauran sunyi disappearing, zaki ga ba kya ganin komai asararin samaniya sai wannan star din guda daya" nayi exactly yadda yace, sai naga komai ya bace a idona sai star guda daya, yace "do you get it Diyam?" Na gyada kaina da sauri ina murmushi, yace "to haka nake ganin ki a idona, ke kadai kike haske a duniya ta, duk sauran mutane da duhu nake ganin su. You are the only star in my sky" nayi murmushi na maimaita "You Are the only star in my sky" yace "that's right. Ki rike wannan a ranki, ko mai tsanani, komai shudewar zamani, ke kadai ke zaki kasance a raina har gaban abadan" nayi dariya nace "wallahi ka iya ashe. Yayi dadi sosai" yace "to shikenan na zama saurayinki?" Sai kawai naji wata kunya ta lullube ni, nayi sauri na rufe idona da hannayena guda biyu, yace "au wai kunyata kike ji kuma? Bude idon ki gani" na makale kafada, yace "kinga wani abu" nace "naki wayon" sai yakama hannu na da niyyar bude fuskar ni kuma sai na tashi da gudu na fara sauka daga stairs, shaf na manta da cewa buya nayi, na manta cewa gudun makaranta nayi, sai da naji muryarsa a bayana yace "Diyam!!, Come back!!" A daidai lokacin ne kuma idona ya fada cikin na Inna a tsaye a tsakar gida da tray din tea a hannunta. Muka tsaya muna kallon kallo, cike da mamaki tace "Diyam?" Adaidai lokacin da Sadauki yayi appearing a bayana. Ta saki trayn hannunta ya fadi cike da karar data jawo hankalin Baffa da Ummah suka fito a tare kowa daga dakinsa.
Writing.....
[1/13, 9:22 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Fifteen: Baffa
Cikin hanzari Inna ta juya ta koma daki, baya yi second uku ba sai gata ta fito da sharfadediyar dorinar da ta siyo ta ajiye danyi min barazana a duk lokacin dana ki jin maganarta. Da sauri na zagaya na koma bayan Sadauki, na kusa fuskata a bayansa zuciya ta tana aiyana min cewa yau kwanana ya kare, na tabbatar da cewa yana iya jin bugun zuciya ta a bayansa. Cikin tsananin zafin rai Inna ta karaso inda muke tsaye amma sai Sadauki ya sake tura ni baya ya hadani da jikin bango shi kuma ya tokare ni da jikinsa. Nan Inna ta fara dukansa da iyakacin karfinta da wannan dorinar ta hannunta amma ko gezau baiyi ba, shi kawai kokarinsa shine ya kare duk dukan kar wani ya sameni.
Sai da dorinar hannunta ta kakkarye sannan ta yar da ita ta shiga kitchen ta dauko muciyar tuwo, a lokacin ne Baffa yayi sauri ya rike hannunta, sai kuma ta saka kuka tadora fuskarta a kafadar Baffa. Sai kuma yaja hannunta a hankali ya shige da ita zuwa dakinta. Umma ce ta taho itama zuwa inda muke tsaye ta sauke kyakykyawan mari a kuncin Sadauki, kafin ya dago kai ta kuma marin daya side din sannan kuma cikin sassarfa ta wuce dakinta, Sadauki ya bita da sauri yana kiran sunanta "Ummah ta, Ummah ta. Ummah dan Allah kiyi hakuri". Sai ya kasance an barni ni kadai a tsakar gidan. Na durkushe a gurin ina jin kafafuwana suna rawa, sai kuma na dafa bango na mike da niyyar komawa sama in dauko kayana, a lokacin Baffa ya fito daga dakin Inna, nayi saurin komawa na dunkule a guri daya ina cewa "wayyo Allah Baffa kayi hakuri. Na tuba, bazan sake kin zuwa islamiyya ba" yazo ya tsaya a gaba na ya miko min hannunsa yace "zo uwata" na sake ja da baya, ya kama hannuna yace "zo Diyam, ba dukan ki zanyi ba, magana zamuyi kawai" na mike a darare amma sai naga yayi min murmushi.
Dakin sa ya jani muka tafi, ya zaunar dani akan kujera sannan shima ya zauna a kusa dani yana kallon yadda jikina yake karkarwa yace "share hawayenki ki daina kuka, ni ba dukanki zanyi ba kuma bazan bari innar ki ta dake ki ba in dai har kika gaya min gaskiya. In kuwa kika yi min karya, zan zaneki sannan bazan hana innar ki dukan ki ba kuma sauran ke da Allah, kinsan baya son mai karya ballantana mai yiwa iyayensa karya" na gyada kai ina jin dadi a raina tunda yace ba za'a dake ni ba sai in nayi karya, ni kuwa yadda nake ji da jikin nan nawa me zai saka inyi karya? Yace "me yasa innarki ta tura ki islamiyya kika ki zuwa kika buya?" Na share hawayen tunowa da laifi na na islamiyya sannan nace "dukana za'ayi in naje" yace "me kika yi zasu dake ki?" Na bashi labarin abinda Sadauki yayiwa monitan aji uku. Ya jinjina kai yace "to me yasa da akayi haka baki zo kin gaya min ko kumako gayawa innarki ta gaya min in yaso ni sai inje makarantar in basu hakuri shi kuma Sadauki inyi masa fada ba?" Na sunkuyar da kaina ina wasa da hannuna ina tambayar kaina me yasa? Ni da abin ya faru ma it never occurred to me cewa in gaya wa inna, in na gaya mata gani nake fada zata yi min ko kuma ma ta dake ni, besides, bana so ayi wa Sadauki fada akan me yasa ya daki wancan yaron.
Yace "to Sadauki ne yace kike buya a sama?" Na gyada kaina, yace "kuma sai shima yake zuwa kuke zama tare a saman?" Na kuma cewa "eh" yace "to me kuke yi a saman?" Nace "games muke yi" yace "wanne irin game?" Nace "ko chess ko lido ko whot ko kuma...." Sai kuma nayi shiru, Yace "ko kuma me? Kinsan dai kinyi min alkawarin zaki gaya min gaskiya ko?" Nace "ko kuma muyi ta labari" yace "wanne irin labari?" Nace "ko ya bani labarin gareji ko makarantar su nima sai in bashi labarin makarantar mu da kawayena" yayi shiru yana jinjina kai sannan yace "to yanzu ina dankalinki da hijab dinki?" Na nuna sama da hannuna, yace "ya akayi kika cire su?" Nace "hijabin cirewa nayi dan kar yayi squeezing, dankwalin kuma bansan ya zame ba" yace "to me yasa kika sauko da gudu dazu, fada kukayi?" Na girgiza kaina sai kuma nayi murmushi ina tuno kalaman sadauki, Baffa ya sake maimaita tambayarsa yana nazarina, nace "na fada mukayi ba, kunyarsa nake ji shine na rufe idona shi kuma yace sai na bude masa yagani" Baffa ya dan bata fuska yace "me yasa kike jin kunyarsa?" Na dan rufe fuskata alamar kunya Nace "cewa yayi I am the only star in his sky" Baffa ya bude baki da mamaki yace "shi Sadaukin?" Na gyada kaina ina murmushi. Ya jima yana kallona sannan yace "to sai wanne wasan kuma kukeyi a saman?" Innocently na daga hannuna nace "shikenan" ya kuma yin shiru yana kallon na, sai kuma ya gyada kai yace "to yanzu kingakinyi wa innarki dani baffan ki laifi, an tura ki islamiyya kinki zuwa, me zaki ce mana?" Na durkusa a gabansa nace "Baffa kayi hakuri" ya kama hannuna yace "na hakura, saura Inna".
A zaune muka sameta, idonta akan tv amma daga gani ba kallon take yi ba, hallonta daya akan Asma'u tana shafa kanta a hankali ita kuma tana bacci. Na rakube daga bakin kofa ina kallonta, Baffa yaje ya zauna akan kujerar da take kusa da ita sannan ya kirawo ni da hannu yace "me kika cewa innarki?" Na durkusa nace "Inna kiyi hakuri, na tuba, bazan kara buya ba inkin kuma tura ni islamiyya" ta watsa min harara tace "kuma ba zaki kara kula Sadauki ba?" Na sunkuyar da kaina nayi shiru. Baffa yace "tashi ki tafi dakin ku ki kwanta" na tashi babu musu na shiga na kwanta, sai kawai naji ina tunanin koya Sadauki yake ji a jikinsa? Dan nasan ba karamin dokuwa yayi a gurin Inna ba.
A palo bayan na wuce Inna tace "shikenan? Shikenan maganar nan ta wuce? Shikenan ba zaka dauki mataki akan yaron nan da yake neman ya lalata maka yarinya ba?" Baffa yace "nayi magana da Diyam, abinda kike tunani ba haka bane ba. Tabbas shi ya hanata zuwa makaranta saboda wai ance za'a dake ta in taje akan laifin da shine ya aikata ba ita ba. Tabbas Sadauki yayi laifi kuma zan zauna inyi magana dashi kamar yadda nayi da Diyam. Zan fahimci inda yake da kuskure in nusar dashi, inda kuma yayi laifi inyi masa fada" hawaye ya zubo daga idon inna tace "shikenan abinda zakayi masa?" Yace "to gaya min me kike so inyi masa?" Tace "ka mayar dashi gidan ubansa tun kafin yalalata mana yarinya ya cuce mu" ya girgiza kansa yace "Sadauki ba zai lalata Diyam ba, in ma hakan ta faru to mune zamu kasance masu laifi fiye dashi. Yanzu in tambayeki? Me yasa da Diyam ta gudo daga makaranta batazo gurinki a matsayin ki na mahaifiyarta ba sai ta tafi gurin Sadauki?" Da sauri inna tace"saboda ya cinye kurwarta bata ganin kan kowa da gashi sai nashi" Baffa ya girgiza kai yace "saboda a gurinsa take ganin zata samu maslaha in ta zo gurinki problem zata karawa kanta. Yarinyar nan dududu shekarunta goma da watanni a duniya, yanzu ne ya kamata ace kin kara jawo ta jikin ki kin koyar da ita lamurran duniya, amma me? Diyam tsoron ki take ji, komai tayi gani takeyi kamar laifi zatayi a gurinki. Yanzu da ace ma lalata tan yakeyi kamar yadda kika yi tunani ta yaya zaki sani? Kince ba kya son taje dakin Zainab, amma ke kin gaza yi mata abinda Zainab din take yi mata har take nacin zuwa dakin nata, wasa da dariya, kulawa, nuna soyayya, wannan shine kadai abinda Diyam take bukata daga gurinki a wannan lokacin. Ke kika haife ta, dan haka in kika sakar mata fuska zakiyi mamakin yadda zata sake dake itama".
Inna ta kalleshi tace "dama na sani, nasan duk yadda zakayi ka juya maganar nan ta koma kamar laifina ce sai kayi, ni kumana riga na sani, nasan cewa kafi son Sadauki akan Diyam, kafi son agola akan yar data fito daga jikin ka, kamar yadda ka fi son zainabu akai na ni uwargidan ka kuma yar uwarka ta jin, kuma uwar yayanka na gaskiyai" Baffa ya mike tsaye yana girgiza kai yace "Diyam ni na haifeta, Sadauki kuma nina rike shi tun yana cikin tsumman sa dan haka dukkan su yaya nane, babu banbanci. Maganar tsakanin ki da Zainab kuma ke kike ganin haka, ke kika saka haka a ranki. Amma ina son ki bude idonki ki kalli gabanki sosai zaki fahimci ke kadai kike fadanki babu wanda yake amsa miki"
Har ya kai bakin kofa tace "ina neman alfarma guda daya a gurinka" ya juyo amma bai ce komai ba, tace "ina son idan har Diyam ta kammala primary a kaita boarding school" yace "Allah ya nuna mana lokacin".
Writing......
[1/14, 8:43 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Sixteen: My Love
Washegari Baffa da kansa ya tisa keyar mu daga ni har Sadauki muka je islamiyya, ya saka muka bada hakuri sannan shima ya bayar, ya kuma ce duk sanda wani abu makamancin wannan ya sake faruwa su sanar dashi shi kuma zai dauki mataki akan mu. A take kuma yayi Asma'u register ya ce kullum tare zamu ke zuwa da ita . Wannan ya kawo karshen gudun islamiyya ta amma kuma ya kawa hauhawar kiyayyar Sadauki a gurin Inna, yanzu yakasance ko gaisheta yayi bata amsawa shi kuma bai fasa gaishetan ba kullum. Takance "shegen naci irin na uwa, kamar tsohon maye".
A karshen term din muka rubuta jarabawar common entrance. A lokacin shi kuma Sadauki ya rubuta jarabawar shiga ss3, qualifying exam, kuma dukkanin mu munyi nasara. Naci makarantar day science ta nan garin kano. Ina karbowa na taho gida da murnata na kuma yi sa'a Baffa yana gida, suna palon sa shida Sadauki suna lissafe lissfen da suka shafi gareji. Na durkusa na gaishe shi sannan namika masa takardar, ya karba ya karanta yana murmushi yace "very good Inno. Kinyi kokari sosai Allah yasa albarka a cikin karatun ki" nace "ameen Baffa" yace "sai dai ba day science zaki tafi ba, nayi magana da wani abokina wanda yake malami ne makarantar kwana ta yammata dake garin Taura a jahar Jigawa, yace in kaiki zasuyi miki interview in kinci sai a kaiki can" na taba rai cike da confusion nace "taura? Gari ne haka din? Makarantar kwana?" Sai na juya na kalli Sadauki wanda shima Baffa yake kallo yace "Baffa boarding fa kace, Diyam? Baffa Diyam bata da girma manyan dalibai zasu ke cin zalinta kuma...." Sai ya hadiye sauran maganar saboda kallon da Baffa yayi masa, Baffa ya miko min takardar yace "ki kaiwa innarki ta adana miki, gobe da safe ki shirya zamuje kiyi interview din" na karba jikina a sanyaye na wuce dakin inna. Na kai mata ta bude tana gani fuskarta da murmushi duk kuwa da cewa ba wai sanin abinda aka rubuta tayi ba. Na zauna a kusa da ita nace "Inna naci day science, makarantar su Rumaisa" ta ninke takardar ta ajiye tace "Rumaisa ai jeka ka dawo take yi, ke kuma makarantar kwana zakiyi" na fara hawaye nace "Inna Baffa yace wai gobe za'a kaini a gwada ni, inna ni bana son zuwa dan Allah kiyi masa magana kar a kaini" tana kallona tace "saboda me?" Na rike hannunta nace "bana son barin gida Inna bana son rabuwa daku" sai ta zame hannunta daga nawa tace "ko dai bakya son rabuwa Sadauki? Ni kuma saboda shime nake son akaiki makarantar kwanan ko hankalina ya kwanta, kuma idan ba kya ganinsa a hankali zaki manta dashi. Kafin Allah ya taimake mu ya tattara ya koma gidan ubansa" jin haka yasa na fahimci bani da hope a gurin Inna, ba zata rokar min Baffa ya fasa kaini boarding ba.
Dakin Ummah na tafi ina sharar kwalla, ta rike ni tana tambayata, "Diyam lafiya? Wani abu ne yake yi miki ciwo?" Na zauna ina kara sautin kukana nace "Ummah wai boarding za'a kaini inji Baffa, dan Allah Ummah ki bawa Baffa hakuri" tayi ajjiyar zuciya tace "Diyam, ai ba laifi kikayi masa ba ballantana in bashi hakuri, zai kaiki boarding ne saboda yana ganin hakan shi yafi dacewa dake" nace "to ni yanzu Ummah me zanyi? Me zanyi ya fasa kaini?" Tana shafa kaina tace "kiyi addu'a, kiyi fatan Allah ya sa hakan shi yafi miki alkhairi"
Washegari tun da assuba Baffa ya leko yace min in tashi in shirya, karfe takwas na safe muka dauki hanyar Taura, Sadauki ne yake jan motar sai Baffa a gaba ni kuma ina baya ni kadai, wannan yasa na kwanta wai ko za iya bacci amma bacci yaki zuwa ina ta jero duk addu'ar da tazo bakina akan Allah yasa kar inci interview din nan. Su Baffa ma ba sosai suke hira ba sai jefi jefi, shima kuma duk akan harkar garejin su ne. Karfe goma saura muka isa makarantar, aka bude mana gate muka shiga har bakin staff room sannan Baffa ya kira number din abokin nasa wanda shine vice principal a lokacin, inanan dai a kwance yazo, naji suna gaisawa da Baffa sannan Sadauki ya gaishe shi, sai ya bude kofar baya yana kallo na yace "manu wannan kawai bar mana ita za'ayi anan, a aiko mata da kayayyakin ta" Baffa yace "shi kenan kuwa kaga mun huta da sake dawowa" ina jin haka na kifa kaina a jikin kujera na fara rera kuka, Sadauki ya juyo yana kallona yace "wasa suke yi miki fa, ke baki san wasa ba? Ya za'ayi a kawo ki makaranta a lokacin hutu" sai kuma na tuna ashe hutu akeyi, na fara goge hawayena ina cewa "Sadauki bana son makarantar nan" yace "kiyi shiru kar Baffa yaji yayi miki fada" daga waje naji abokin Baffa yana kira na, na fita ina goge hawayena da hijab dina. Staffroom babu malamai sosai saboda ana hutu, office din principal muka shiga, na gaisheta a darare ta kalle ni daga sama zuwa kasa sannan tace "too young" vice ya matsa kusa da ita ta fara yi mata bayanin cewa karamin jiki ne dani amma eleven years nake a lokacin, ya nuna mata birth certificate dina da sauran takardu. Ta gyada kai sannan ta bani wata exam question paper tace in zauna in amsa. Na zauna ina dubawa, obj ce, dan haka nayi ta cike shiririta ta wata question din ma ko karantawa banayi wai ni a lallai so nake in fadi. Ina gamawa na bata na fito raina fes saboda nasan nayi messing up. Baffa ya mike yana kallon vice yace "to ya akayi? I hope taci?" Vice yayi dariya yace "ai ba'ayi marking ba, amma abinda ta rubuta a paper doesn't matter, tunda ina gurin ai babu wani abu, maybe ma ni za'a bawa in yi mata marking. Kawai da lokacin kawo yara yayi ka shirya ta ka kawo ta. Ya dan daki kaina cikin wasa yace "kaga manyan yan boarding" naji kamar in rufe shi da duka dan haushi.
A cikin hutun na harda ciwo nayi. Inna da Baffa kuma duk sunsan abinda yake damuna amma babu wanda yabi ta kaina, sai ma shirye shirye da suke yi. Aka dinkamin uniform, aka siyamin manyan trollies dina guda biyu daya ta kayan sawa daya ta kayan abinci. Vice ya rubutowa Baffa duk abinda ake bukata Baffa kuma ya bawa Sadauki yaje ya siyo min. Akan haka sai da akai rigima da Baffa da inna tace ina ruwan Sadauki da siyayyar makaranta ta? Amma Baffa bai fasa bashi ba. Idan Baffa ya bashi list din sai ya zauna ya kakkara wasu abubuwa yace ai duk zan bukace su, sai da Baffa yace "Sadauki ya isa haka in ba so kake ka talautani akan Diyam ba, muma ai muna bukatar kudi a gidan".
Ranar da zan tafi, tun da na tashi nake yan koke koke na amma Inna ko ta kaina bata bi ba tace "kya yi kya gama. Gata akeyi miki ke baki sani ba". Sai ga Ummah tazo da kanta da kaya cikin leda, da cincin a cikin wani dan karamin plastic container mai murfi tace "Diyam gashi ki tafi dasu makaranta, ki rike addinin ki kinji? Kuma kar kike wasa da cikin ki ki tabbatar kina cin abinci akan kari, duk abinda kika ga ya kusa karewa ki saka ayo waya gida a fada" na karba ina share hawayena nace "to Ummah na gode" Inna ko daga kai bata yi ta kalleta ba.
Sadauki da Baffa ne suka kaini, tun daga gate nake kuka har muka shiga ciki aka gama cike ciken takardu, malamai suna ta tsokana ta wai daga gani na sabun shiga ce. Sadauki ya durkusa a gaba na yana share min hawayena yace "zaki yi ciwon kai na gaya miki. Ki daina kukan nan haka" na rike hannunsa nace "ni karka tafi ka barni" ya kakalo murmushi yace cikin wasa "ai babu hostel din maza" sai kuma yayi dariya shi kadai ba tare dana taya shi ba. Yace "zanke zuwa ina ganin ki. I promise. Amma sai kin daina kuka in ba haka ba bazan ke zuwa ba" na langwabar da kai nace "ai kukan ne yake zuwa da kansa" yace "to kiyi, amma kadan". Ina kallonshi yana ta delaying shiga mota da zasu tafi, har sai da vice ya tisa keyata zuwa class sannan na jiyo tashin motar su. Ina zuwa nayi kawa Jidda, itama yau aka kawo ta tana ta kuka sai class master din mu yace mu zauna a seat daya kuma daga yau mun zama kawaye tunda mune masu kuka a aji.
Duk yadda na dauka rayuwar makaranta zata zo min ba haka tazo ba. Kafin inyi sati na warware sosai ina harkokina, nayi suna a ajinmu saboda kokarina da kuma surutuna. A hostel kuma nayi suna saboda kankantata da kyau na. Seniors suna sona sosai, wadansu su kance ina musu kama da baby doll saboda yar karamace ni babu tsaho babu kiba, gani fara tas kamar babu jini a jikina sai uban gashi mai tsaho da santsi wanda baya kitsuwa sai da kyar. Daga wannan senior din ta dauke ni tace kanwarta ce ni sai waccan ta dauka, ayi tabani kayan dadi ina ci, in an tare yan makara dani sai ace "wannan in aka dake ta ma ai sai a balla ta, tashi ki tafi, karki sake makara" dutse kuwa sai da aka samo wanda yafi komai sauki, sharar verandah sannan aka bani.
Amma fa wannan ko da second daya baisa na cire Sadauki daga raina ba, kullum dashi nake kwana dashi kuma nake tashi. Wani lokaci sai im zauna inyi ta rubuta masa letters ins bashi labarin rayuwar makaranta ta, in zana flowers a jiki da hoton heart da arrow da sunansa a jiki "Aliyu Haidar". Rannan jidda ta gani ta dauka tana karantawa tace "wanene Aliyu?" Nayi murmushi nace mata "saurayi na ne".
Sai da nayi wata daya sannan rannan muna class aka aiko inzo anzo min visiting. Na mike da sauri ina murna a raina ina kwadayin Allah yasa tare da Sadauki aka zo. Ina fitowa aka nuna min bayan staffroom akace inje can. Na tafi da sauri na, banga motar gidan mu ba amma sai na hango Sadauki shi kadai a tsaye ya jingina da daya daga cikin bishiyoyin gurin. Na kwasa da gudu, ya juyo yana kallona yana dariya amma da yaga da gaske jikinsa na nufa sai ya dakatar dani da hannunsa daya sannan ya girgiza min dan yatsa. Na bata rai na turo baki na juya baya nace "ni fushi ma nakeyi da kai" ya zagayo ta gabana kyakykyawan murmushi kwance a kyakykyawar fuskarsa yace "me kuma nayi? Allah sarki Aliyu bawan Allah" na rike kugu nace "ai kasan laifin ka" ya kama kunnensa yace "na tuba, duk da bansan me nayi ba" na nuna shi da dan yatsana nace "ba cewa kayi zaka ke zuwa ina ganin ka ba? Amma shine tunda aka kawo ni ba ka taba zuwa ba?" Yace "aiya, Halima wata daya ne fa kadai" nace "eh, ai duk sati nake so kazo" yayi dariya yace "duk sati ai suma kansu makarantar ba zasu bari ba" ya kama hannuna muka zauna a daya daga cikin benches din dake gurin yace "kinga, visiting card guda uku suka bamu, suna nufin sau uku aka yarda azo ganin ki. In na ce zanke zuwa duk sati ai ko wata ba zakiyi ba cards dinki zasu kare. Kuma kinga su Inna ma si zasu so suxo su ganki ko?" Na danyi murmushi naji ina missing Inna nace "ya suke? Ya Baffa da Asma'u?" Yace "duk suna lafiya, basu san dai na taho ba sai Baffa kadai. Ke kuma fa? Ya makarantar? Ba'a cin zalinki ko?" Ya kama hannuna yana checking ko yayi kaushi ko kanta yace "ba'a saka ki labour? Noma da shara mai yawa?" Na gyara zamana ina wasa da hannuna na bashi labarin duk irin yadda nake enjoying makarantar, yace "wato it sometimes pays to be smallish ko?" Muka yi dariya. Sai kuma ya bani labarin tasa makarantar, yanzu sun shiga ss3, ya fada min an bashi prefect, yace "guess me aka bani" na karkatar da kai ina kallon murmushin fuskarsa nace "labour prefect" yayi dariya yace "you are a smart one, aren't you?" Nace "to kar dai kake cin zalin yayan mutane" ya daga hannu sama yace "ba zalin wanda zanci, kar alhakin su yasa aci min zalin matata" sai kuma naji kunya na rufe ido.
Mun jima muna hira, jin mu muke kamar masu yawo a saman gajimare har sai da aka zo ake ce masa time up sannan muka fara sallama, rai ya fara baci kuma. Yace "hope kayan abincin ki basu kare ba" na gyada kai kawai ina goge hawaye, yace "okay, to bara in koma da sweets din dana zo miki dasu tunda kuka zakiyi" nayi sauri na jawo ledar gabansa na turo baki ina kunkuni. Na bude naga kayan alawa, chocolate da biscuits ne kawai a ciki. Ya miko min kudi yace "inji Baffa, yace ki fada in kina son wani abu" na girgiza kai, yace "to kiyi min dariya mana in gani. Kuma ko sammin sweets din ba zaki yi ba?" na bude ledar na dauko chocolate guda daya na bare na bashi nace "gashi nan, ladan ganin ido"
Share your thoughts akan soyayyar Diyam da Sadauki. Do you think tana dorewa?
[1/15, 8:20 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Seventeen : PS: I Love You
A tsakiyar term su inna suka zo min visiting suma. Sadauki ne ya tuko su amma babu Baffa kuma babu Ummah sai Asma'u Mama da su Rumaisa. Nace "ayyah, Inna da kun sani kun taho da Ummah, nayi missing dinta" babu wanda yace dani ci kanki a cikin su. Ranar nayi murna har na rasa inda zan saka kaina, su kuma suna ta yimin dariya. Suka zo da abinci kula kula muka hadu muka ci tare ana ta hira, amma Sadauki tunda muka gaisa ya koma mota, sai da muka gama cin abincin sannan na zuba na kai masa, ina mika masa kuwa inna ta kira ni in dawo haka na taho bamuyi magana ba. Sai da zasu tafi ya dauko bakar leda ya miko min yace inji Ummah, garin karba naji ya saka min takarda a hannu na sai nayi sauri na saka ta cikin aljihuna, yayi murmushi kawai ya daga min hannu suka tafi.
Bayan na koma hostel ina jejjera kayan dasu Inna suka kawo min, na duba ledar da sadauki ya bani naga dambun nama ne da yaji attaruhu da tafarnuwa, just the way I liked it. Nayi murmushi na dauko takardar daya bani na bude ina karantawa.
My dearest star.
Am sorry ba mu sami damar magana ba, but ganin kina lafiya kadai ya ishe ni farin ciki. Ga dambun nama nan inji Ummah tana gaishe ki.
PS
I love you.
Na dora takardar a kirjina ina jin wani iri. Na sani cewa akwai wani abu a tsakani na da Sadauki amma bai taba furtawa direct ba sai yau. And it feels great. A hankali nace "I love You too Aliyu".
Haka rayuwa ta cigaba da kasance wa, har cikin ikon Allah muka shiga third term na js1, a lokacin shi kuma Sadauki suke zana ssce dinsu. Kullum in naga yan ss3 dinmu suna exam sai inta yiwa Sadauki addu'a, Allah ga Sadauki nan, Allah ka bashi sa'ar exam din nan. Wannan term din gaba daya baizo min visiting ba. Sai ranar da mukayi hutu suka zo daukana shida Baffa, ko dan ma kwana biyu ban ganshi ba? Sai naga ya kara girma ya kara kyau.
Naje na shige gaban mota na barshi da daukan kaya yana sakawa a booth, Baffa kuma ya tafi zaiyi signing dina out. Na dauko powder da lipstick ina shafawa wai duk kyalliyar zuwa gidan ne, sai kawai naji kamar ana kallona, nayi sauri na kalli mirror muka hada ido dashi, ya tsaya da jaka a hannunsa kawai ya zuba min ido ta mirror, muna hada ido sai kuma kunya ta kamashi yayi saurin dauke kai kunya a rubuce a fuskarsa. Dariya kawai nayi wai namiji da kunya.
A cikin hutun ne muna gida na fara period. Ranar ina kwance a dakin Ummah ina tashi kawai naji danshi a kasana, na saka hannu na shafa kawai sai naga jini a hannu na, na kalli Ummah naga itama ni take kallo. A lokacin Sadauki yayi sallama nayi sauri na koma na zauna ina boye hannu na a baya na, ya tsaya daga bakin kofa yana kallona yace "ke kuma lafiya kike rarraba ido kamar bera a buta?" Ummah tace "ina ruwan ka da ita, tsabar sa ido me kazo yi ma gida a yanzu?" Ya shigo yana cewa "babu aiki a garejin, shine nazo gida in huta. Diyam tashi ki bani abinci" na kwabe fuska kamar zanyi kuka Ummah tace tana nuna masa kofa "tashi ka fita" yace "Allah ya baku hakuri, daga tambaya?" Sai ya mike ya fita yana waige na.
Yana fita Ummah tace "tashi in gani" na mike, tace "kin san menene?" Na gyada mata kai. Tabbas nasan jinin haila da hukunce hukuncen sa tun a islamiyya, na kuma kara sani a kansa a makarantar boarding. Akwai yan ajin mu da suke yi, kuma seniors din mu ma sunayi dan sukan aike ni wajen wata matron in siyo musu pad, amma ban taba tsammanin zaizo gare ni ba ni Diyam, at least not now, ni ban shirya girma ba gaskiya. Ummah ta saka ni naje drawers dinta na dauko wasu undies data siyamin da niyyar in zan koma makaranta zata bani, ta saka na dauko pad itama a dakinta takoya min yadda ake sakawa sannan tace min inje toilet in gyara kaina. Ina dawowa na tarar ta gyara inda na bata a kujerar ta, sai kuma ta zaunar dani ta sake yi min bitar wankan tsarki da sauran abubuwa da suke shafi haila, ta kama kunnena tace "babu wasa da maza daga yanzu, babu wasa da Sadauki" nayi kyar kara sannan ta cika min kunne na. A lokacin Sadauki ya shigo yace "ya naji ana ambatar sunana?" Sai kuma ya kalli irin zaman da mukayi yace "hirar me kuke yi ne haka?" Na tabe baki zan saka masa kuka ya juya yace "na fita, in tayi tsami zanji".
Sai da muka gama maganganun duk da zamuyi da Ummah sannan tace min in tashi inje in gayawa Inna. Na zaro ido nace "Inna? Ni bazan iya gaya mata ba" tayi dariya tace "ai kuwa sai kin gaya mata. In baki gaya mata ba ke da ba'a gida kike zaune ba ta yaya zata sani?" Nace "dan Allah Ummah kije ki gaya mata" tarike baki tace "ni? Babu ruwana, ke zaki gaya mata da bakin ki" naji duk hankalina ya tashi, sai tace "bara in baki shawara. Kinga, yanzu ki tafi dakin ta, ki saka pad a jikin pant ki ajiye akan gado inda tana shigowa zata gani. Da kinji ta taho sai kiyi sauri ki shiga toilet ki buya".
Haka nayi kuwa, na ajiye akan gado sai da naji ta taba kofa sai nayi sauri na shige toilet. Na jima aciki,a tunani na ta fita sai na fito ai kuwa sai gata azaune a kan gado ta tasa pant dina a gaba, nayi sauri zan koma toilet tace "ke! Zo nan" na dawo ina karkarwar jiki na tsaya. Ta nuna pant din tace "wannan na waye?" A hankali nace "nawa ne" sai kuma tayi shiru tana kallona sannan tace "yaushe kika fara?" Nace "dazu" sai ta zaunar dani itama ta dora daga inda Ummah ta tsaya a nasiha da bayanan sabon yanayin dana samu kaina a ciki. Sai data gama sannan tace "saura kuma in sake ganin kun rike hannu ke da wancan bakin munafikin".
Muna gab da komawa hutu exam din su Sadauki ta fito. Alhamdulillah, ya samu nasara sosai. Duk da dai ba distinction ya samu ba amma ya samu credits a duk subjects din daya kamata. Mukayi murna sosai. Sai da jamb ta fito sannan murnar mu ta koma ciki, yayi kokari nan ma, sai dai bai samu points din ake bukata ba a mechanical engineering wanda shine abinda yake so ya karanta. Ranar haka ya wuni ransa babu dadi, ni kuma harda kuka na zauna inayi masa, Ummah kuwa dariya tayi tace "wa kuka taba ganin ya samu abinda yake so lokaci daya? Kuje jami'ar ku tambayi daliban kuji wadansu da yadda suka samu admission din. Ko kuma ku samu mutumin daya ke da daukaka ya baku labarin yadda ya samu daukakar tasa. Babu wani abu mai kyau da ake samun sa cikin sauki".
Baffa yana duba takardar yace "babu komai Sadauki, kar ka damu, akwai next year ai insha Allah sai ka sake gwadawa. In the meantime kuma zan nema maka computer school kayi diploma kafin ka sake jamb din".
Ayi hakuri da wannan.
One love 😘❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Eighteen: Saghir
Assalamu alaikum masoya littafin Diyam. Kafin mu cigaba zan danyi wani jan hankali a game da masu cewa in bar labarin da muke akai yanzu in koma gurin Bassam da Diyam. Ina so ku fahimci wani abu, shi littafin nan gabaki dayansa labarin rayuwar Diyam ne da irin wahalhalun da tasha har ta kai stage din data hadu da Bassam, wanda kusan shine karshen labarin. Na fara ta can ne saboda ina so ku samu glimpse of yadda rayuwa ta juya mata saboda in kara increasing curiosity dinku.
PLEASE stop asking me to summarize and get back to labarin Bassam. This story is not about Bassam but about Diyam.
Shekara tazo ta wuce. Lokacin na cika shekaru goma sha uku shi kuma sadauki yana sha tara. A cikin ta babu abinda ya ragu sai ma karuwa da abubuwa suke yi a tsakani na da Sadauki, musamman yanzu da yake jin sa ya kara zama saurayi tunda gashi har ya kammala diplomar sa a computer science. Ya sake zana jamb, kuma wannan karon yaci abinda ake bukata din, sai dai kuma cikowar dalibai masu neman admission da kuma rashin hanya yasa ya gaza samun admission din, Baffa yaji takaicin wannan abin dan yana ganin hakan kamar gazawa ne daga bangarensa a matsayinsa na uba.
Ni kuma a bangare na, na kammala jss2 lokacin ina da shekara goma sha uku amma ina nan jiya i yau, babu abinda na kara a girman jiki sai dan tsaho da kuma hankali. A lokacin kam zan iya cewa duk wanda yake tare damu ni da Sadauki yasan something is going on, including Baffa, Ummah da Inna. Baffa baice komai ba, haka ma ummah, basu taba encouraging din mu ko discouraging din mu ba. Babban problem din, kamar yadda duk muka yi tsammani shine daga gurin Inna dan sosai take nuna kiyayyar ta ga tarayya ta da Sadauki.
Hutun da muka zo na third term din jss2, ina shiga palon Ummah hannuna rike da Asma'u da take ta murnar gani na, na tarar da akwati a ajjiye a kofar palo. Bayan na gaisheta nace "Inna wannan kayan fa?" Ta hade rai tace "naki ne, hutu zaki tafi" naji zuciyata ta buga nace "hutu Inna? Ban gama ganin ku ba fa ina zan tafi hutu kuma?" Ta harare ni tace "gidan Alhaji Babba zaki tafi, in muna son ganin ki mu zamu zo mu ganki" nayi ajjiyar zuciya a boye, dan dai sharada? Nasan Sadauki ko da adungure zai je ya ganni. Kwana na daya a gida na tafi sharada. Ni da Rumaisa ne zamu je muyi hutu a can yayin da Inna ta yi mana rakiya. Rumaisa tana ta murna saboda ita kam tana son zuwa gidan Alhaji Babba. Ni kuma ina yake saboda kar Inna ta harbo jirgina na plans din da mukayi da Sadauki.
Now, let's talk about Alhaji Babba da family dinsa.
Kamar yadda na fada Alhaji Babba shine babban yayan su Baffa, shi ya fara zuwa Kano neman kudi kuma a lokacin yafi dukkansu dukiya, dama baffan mu ne baya. Allah ya jarrabi Alhaji Babba da mugun son yaya maza sai kuma ya hana shi su, wannan yasa ya kasance mai aure aure duk a tunanin sa da burinsa hakan zai saka ya samu cikar muradinsa. Matarsa ta farko yar uwa ce daga Kollere, ya daya ta haifa masa Adda Zubaida, daga nan bata sake haihuwa ba sai ya auri Hajiya Babba wadda tashin farko ta haifa masa muradinsa na ɗa namiji wanda muke kira da hamma Saghir. Hajiya Babba jinin sarautar kano ce, hamshakiyar macece mai mulki da izza wadda hatta kishiyoyinta inka gansu a gabanta zaka iya dauka cewa yaranta ne. Bayan shi ta sake haihuwar mata biyu, Aysha da Salma. Daga Hajiya Babba kuma sai Hajiya Yalwati wadda tafi duk sauran matan yawan yaya kuma wannan shine kadai abinda yake zaune da ita a gidan. Hajiya Yalwati kawar Inna ta ce dan haka duk sanda muka je gidan a dakinta muke zama, kuma nima saboda babbar kawata a gidan, Murja, yar Hajiya Yalwati ce dan haka nima na zama yar dakinta. That plus daga ni har Inna babu wanda yake iya jurar mulkin Hajiya Babba. Sauran vacant space din guda daya kuma na mai rabo ne, wannan ta shiga wannan ta fita.
Hamma Saghir shine da daya tilo da Allah ya bawa Alhaji Babba, dan haka zama bayyana cewa dan gata ne bata lokaci ne. An haife shi tun kafin Baffa na yasan zai auri Inna ballantana a haife ni, dan a lissafi ya bani shekaru goma sha shida da watanni. A kullum idan naji mata suna lissafa siffofin mijin da suke so su aura sai inga kamar lissafin kamannin hamma Saghir suke yi, fari, dogo, kyakykyawa, mai saje, marar son surutu, mai kudi, mai class blablabla. Hamma Saghir is all that and more. Labari ya zo min cewa makarantar da hamma Saghir yayi ma kanta daban take da ta sauran yaran gidan dan Alhaji Babba cewa yayi "a samo min makarantar da yayan masu kudi suke zuwa a garin nan, ita zan saka Saghiru" a haka yayi primary da secondary dinsa, sannan aka saka shi a buk yayi degree a economics ya fita da pass. Alhaji Babba yace "ba wani abu, dama an saka ka a makarantar ne saboda ka samu ilimin juya dukiya ba wai dan ka nemi aiki da takardun ka ba". Sai kuma Alhaji Babba yayi masa irin abinda Hardo yayi masa shima. Ya debi dukiya msi yawa ya bashi yace "tafi ka nemi arzikin ka" Saghir ya gyara zama yace "China zan tafi Alhaji, tunda can ne cibiyar kasuwanci ta duniya a yanzu. In naje sai in nemi Company in saka hannun jari a ciki. Maybe kafin shekara sai kaga nazo na bude nawa Companyn"
Haka ya shirya aljihu fal kudi ya tafi China, daga nan ba'a kara jin labarinsa ba har sai da ya shekara uku sannan sai gashi ya dawo daga shi sai jakar kayan sa yace "yan damfara na hadu dasu Alhaji, gaba daya kudina sun salwanta da kyar na tsira da kudin jirgi na dawo gida" Alhaji Babba yace "kasuwanci ya gaji haka dama, yau riba gobe faduwa hakan kuma ba zai saka mu karaya ba" sai ya debi wadandu kudaden ya kuma bashi, shi kuma ya karba yace "Dubai zan tafi wannan karon inke saro kaya ina aikowa dasu gurinku kuna siyar min". Wannan karon ma tunda ya tafi ba amo ba labari ko waya babu, amma sai iyayen suke boyewa kullum suna nuna kamar yanayi musu waya "abubuwa ne suka yi masa yawa amma yace yana gab da zuwa gida". Yazo gidan kuwa bayan shekara biyu, sai dai wannan karon ko akwatin kayansa bai dawo dashi ba ballantana kudi "Dubai bata karbe ni ba Alhaji. Kudi na gabaki daya sun salwanta ba bu abinda ya rage a hannu na" Alhaji Babba yace "kasuwanci bai karbe ka ba Saghiru. Dole sai mun zauna munyi maka adduoin neman sa'a sosai. Kuma ina kyautata zaton akwai nasara sosai a rayuwar ka shiyasa kake samun tangarda" Hajiya tace "musamman ma shi da yake da tarin makiya, gaskiya kam sai an hada da addu'a".
Bayan an gama rarraba wa malamai kudi sunyi adduoi, sai kuma Alhaji yace "gwara ka zauna a kasar nan saboda muke ganin abinda kake yi muna kuma baka shawara" amma sai Saghir yace "gaskiya Alhaji ko zan zauna a kasar nan to ba'a Kano ba, saboda anan an saka min ido dayawa". Haka rayuwa ta cigaba masa, yau yana wannan garin gobe yana wancan duk da sunan neman kudi, in kudin hannunsa sun kare ya dawo Kano ya karbi wadansu ya kara mai.
Tunda nake bazan iya cewa ga ranar da hamma Saghir yazo gidan mu ya gaishe da Baffa wanda yake kanin babansa ba ballantana Inna da take cousin din babansa kuma matar kanin babansa. Ni kaina ganin da nayi masa a duniya a lokacin bashi da yawa sai dai a jikin katon hoton sa dake kafe a main palon gidan.
A ranar da muka je gidan, kamar yadda muka saba, part din Hajiya yalwati muka fara zuwa muka ajiye kayayyakin mu muka huta sannan muka fita muka zagaya muka gaishe da sauran matan gidan. Bayan mun dawo palon Hajiya Yalwati ne Inna take tsokanar Murja "Murja ya na ganki a daki ne yau kamar matar kulle? Tunda muka zo gidan nan banga kin fita ko babban palo ba?" Hajiya Yalwati tace "uhmm ina zata fita taje, boss din su yana gidan? Tun safe nace musu suyi zamansu a daki kar wadda ta fita in ba haka ba sai kiga an dawo da kumburarriyar fuska ya kama su ya mara, komai akayi ai shi laifi ne a wajensa, magana ma mai karfi in sunyi cewa zaiyi sun hana shi bacci duk ya hada su yayi musu duka. Kuma ban isa inyi magana ba" Inna tace "wai Saghir kike nufi? Yazo garin kenan. Oh ni yaushe rabon da inga Saghir?" Kamar da hadin baki kuwa sai gashi ya shigo palon. Ya dafa kujera daga tsaye yace "Hajiya barka da gida" Hajiya Yalwati tayi yake tace "Barka kadai Saghir, anzo lafiya" yace shortly "lafiya lau" sai ya juya zai fita, Hajiya Yalwati tace "ga gwoggonka fa, gwoggo Aminan baffa Usman" ya dan juyo yana shafa kai yace "lah gwoggo ai ban lura ba. Ya gida? Ya Baffa?" Inna tayi murmushi tace "lafiya lau Saghir, ya kasuwa? Allah yayi jagora" yace "ameen" sannan ya fice ba tare daya ko kalli inda muke zaune ni da Rumaisa muna kokarin gaishe shi ba.
Yana fita Inna ta juya tana kallon Hajiya Yalwati tace "kai masha Allah. Saghir ya zama babban mutum sosai" Hajiya Yalwati ta tabe baki tace "eh fa. Yo mutumin da yake kokarin cika shekara talatin a duniya ai kuwa dole a kira shi da babba. Ni in dai gatan gaskiya kuke yi masa ma aure ya kamata kuyi masa maybe ko ya haifa muku jika namiji" Inna tayi dariya tana tafa hannu, Hajiya Yalwati tace"a'a to bai isa auren bane ba? Ko dai kuyi masa aure wallahi ko kuma ya dauko muku abin kunya dan duk abinda yake aikatawa a garuruwan da yake zuwa muna sane, in munyi magana kuma ace hassada muke yi masa" Inna ta watso mana harara ni da Rumaisa, sum sum muka tashi muka basu guri dan munsan ma'anar hararar.
Muna fita Rumaisa tace "zo mu tafi palon Hajiya Babba" na makale "ke ni bana son zuwa gurinta tayi ta mulka mutane tana kallonsu sama sama" ta kuma jan hannu na "dalla can kizo muje, wani abu zan nuna miki". Muka je muka sameta a dan karamin palonta tana kishingide yar aikinta tana yi mata tausa. Muka sake gaisheta sannan muka zauna a gefe muna kallon tv. Muna zaune ya shigo, yana shigowa na kama hannun Rumaisa da niyyar ta tashi mu basu guri amma sai ta rada min "ki bari muyi kallo" na koma na zauna na zubawa tv ido. Ya zarce gaban Hajiya ya zauna. Tace "kaje duk ka gaishe su?" Ya yamutsa fuska yace "naje" sai kuma yace "Alhaji har yanzu bai fito bane?" Tace "na gaya maka ai baya jin dadi ya kwanta. Wani abu kake bukata?" Yana shafa kai yace "dama kudi nake nema, akwai wasu kayana da aka kawo min daga porthercout shine nake so inje in karbo" tace "kaje drawer ta ka gani ko zasu ishe ka" ya mike zai tafi Rumaisa tayi sauri ta gaishe shi, ya dan bata rai yana kallon ta sannan ya amsa, wannan yasa nima na gaishe shi, ya amsa a ciki ciki irin irritatingly dinnan. Hajiya tace "ba ka gane Diyam ba" ya juyo ya kalle ni yana yamutsa fuska yace "bangane taba. Yar uwar mu ce?" Hajiya ta danyi dariya tace "Diyam fa, babbar yar baffan ka Usman" ya danyi shiru sannan yace "ohh, that little baby da akayi jegon ta anan? Wannan mai cika mana gida da kuka?" Hajiya tayi dariya tace "ita fa" ya dan karkata kai yana kare min kallo sannan yace "sam ban gane ta ba. Bata kama da iyayenta" Hajiya tace "ai kuwa Diyam kamar su daya da innar ta, dan karamin jikin ne dai ta dauko na babanta" ya sake kallo na yace "no Hajiya, gwoggo Amina ai kyakykyawar bafulatana ce, wannan kuma sai naga tana min kama da bararoji" gaba dayan mu sakin baki mukayi muna kallon sa har hajiyan, tace "bararoji kuma Saghir? Diyam kuwa ai kowa yana yaba kyanta" ya sake kallona sannan ta tabe baki yace "still, ni ban gani ba".
Another character added. Saghir. Tell me your feelings about him[1/18, 9:45 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Nineteen: Inna
Haka ya shige daki ya bar mu da budadden baki. Na kamo hannun Rumaisa muka fito da sauri.muna fitowa nace "what? Lallai ma mutumin nan" Rumaisa tana murmushi tace "ya hadu ko? Shi yasa nace miki kizo muje mu ganshi" nace "au wai kina nufin saboda mu ganshi kikajawo ni dakin nan? Meye abin kallo a gurinsa? Wai dan wulakanci nice bararoji" Rumaisa tayi dariya tace "au wai haushi kikaji? Ke baki san wasa ba? Wasa fa yake miki dallacan" na bata rai nace "it doesn't look like wasa yake min, har cikin ransa abinda yake nufi kenan" Rumaisa ta bagarar da maganar tace "to ya kika ganshi? Ya hadu ko?" Na tabe baki nace "ko kusa da haduwa baije ba" tace "ko dai don idonki ya rufe, Sadauki ya tare gaba ya tare baya" nayi murmushi ina jin sanyi a raina nace "yanzu kika kamo hanya yar gari" ta bani hannu muka tafa. Rumaisa ita kadai ce wadda nake zama muyi hirar Sadauki sosai da ita, tasan komai akan yadda muke ji a zukatan mu. Muka samu guri muka zauna, na bata labarin tsarin da mukayi da sadauki na cewa zai ke zuwa zance gurina a matsayin saurayina. Ta rike baki tana zaro ido tace "Diyam? Ba kwajin tsoro? Ba kya jin tsoron a kama ku?" Nace "relax. Kinsan dai gidan nan akwai yammata da yawa ko? Kuma duk suna fita zance so babu wanda zai gane, he will be just one saurayi among others, kuma I will make sure duk wanda yasan fuskarsa bai ganshi ba, ballantana kadan ne a gidan nan suka sanshi".
Ranar da Sadauki ya fara zuwa gurina a ranar na bashi labarin encounter dina da hamma Saghir. Ya bata rai yace "kar ki sake shiga harkar sa, duk hanyar da kika san yana bi ma karki kara bi ta gurin ballantana ya sake gaya miki wata maganar banzan". Duk sanda yazo zai gaya min next time da zai sake zuwa, dan haka ni nake fita da kaina in shigo dashi. A gefen dakin mai gadi muke zama, wanda yau da gobe sai muka zama very friendly dashi. Duk ranar da Sadauki yace min zaizo bai taba sabawa ba, koya wuce time din da yace zaizo to kuwa yan minutes kadai zai kara saboda traffic. A wannan lokacin na kara fahimtar cika alkawarin Sadauki, in dai yace zai yi abu to kuwa tabbas zaiyi din sai dai in wani abu ya faru beyond his ability.
Tun ranar da hamma Saghir yace min bararoji bamu kuma haduwa ba, nabi shawarar Sadauki dan haka ko muryarsa naji a guri to bana shiga, inkuwa tsautsayi ya biyo dani ta hanyar da yake to zanyi saurin chanza hanya. Rumaisa ce mai nacin zuwa gurinsa wai burge ta yake yi. Sai ranar nan bayan nayi ten days a gidan, muna tafiya da Rumaisa zata rakani in shigo da Sadauki sai muka hango Saghir a can packing lot, yasha farin voile sai kyalli yake yi kuma daga inda muke muna jin kamshin turarensa sannan muna jin muryarsa yana ta sirfawa baba audu zagi akan wai bai wanke masa motar daya saka shi ba, dan tsohon Allah sai hakuri yake bayarwa kansa a kasa amma kamar kara zuga saghir yake yi "tsabar iskanci da rashin mutunci wajan awa guda kenan nace ka wanke min mota ta amma saboda ban isa ba shi yasa kaki wankewa ko?" Baba Audu yace "kayi hakuri yallabai, Alhaji ne ya saka ni in gyara masa gurin da yake shan iska yana so ya fito anjima" yace "dalla yi min shiru, wallahi in kayi wasa kafin in koma porthercout sai kabar gidan nan. Ka kiyaye ni wallahi" dan dattijo ya durkusa yana ta bada hakuri. Ban san lokacin da naja wani uban tsaki ba, Rumaisa tayi saurin toshe min baki ta jani bayan flowers "rufa ma kanki asiri Diyam. Tsaki? Hamma Saghir? Wallahi in yaji ki zai balla ki" nace "ai kuwa daya gane cewa shayi ma ruwa ne" ta girgiza kanta tace "Sadauki ne dai takamar ki ba wani ba, amma kiyi tunani, do you really want to get him involved with hamma Saghir?" Na juya ina kallonsa, tabbas Sadauki na is very brave and fearless, amma saghir is not his match dan at least ya bashi shekaru goma, ga kudi ga kuma gata. Dan haka hada shi rigima da Sadauki will be like putting Sadauki in trouble. Na ja bakina nayi shiru sannan muka zagaye ta bayan sa muka fita daga gidan.
Sai three days to resumption date din mu sannan Baffa yazo da kansa ya daukeni zuwa gida. Matan gidan sun hada min goma ta arziki wai tsarabar boarding. Amma ni sai naji duk boarding din ta fara isata amma inaji inagani haka aka daukeni aka mayar dani. Sanda muka dawo next holiday shima ina zuwa na tarar da kaya na a ajiye, ban damu ba na shiga harkokina ina tunanin ai sharada ba nisa amma sai naga inna tana hada nasu kayan ita da Asma'u tace "Kollere zamu tafi, mun kwana biyu bamu je mun gaishe su ba musamman yan uwana da muke uba daya nan take naji bakin cikin duniya ya ishe ni amma haka Baffa ya debe mu a mota gabaki daya har su Ummah muka tafi, naji dama dama saboda ganin da Sadauki ne, amma bayan munje mun kwana daya a gidan Hardo da sabuwar matarsa sai naga su Baffa suna shirin komawa suna ta sallama da mutane, na bishi soro da gudu na rungume shi ina kuka nace "Baffa dan Allah zan biku mu koma tare" ya rike fuskata yace "kiyi hakuri uwata, ba tare daku zamu koma ba ku zaku zauna ku zagaya yan uwan innarku na gurin babanta" ai kuwa a take na kara wani kukan dan ni in akwai abinda bana so a lokacin to zama a Kollere ne. Suka tafi, Baffa da Ummah da Sadauki, suka barmu ni da Asma'u mun rike juna muna kuka, Inna ta tabe baki tace "sai suje ai suci uwar da zasu ci a gidan".
Mune daga wannan gida mu koma wancan mu kwana anan mu tashi anan muna ta ziyarar yan uwa har sai da muka yi sati biyu, Asma'u ta dan ware amma niko alamar warewa banyi ba, ranar da muka cika sati biyu Baffa yazo daukarmu ashe wai yayi wa inna waya akan mu shirya zaizo mu tafi ita kuma taki. Yana zuwa ta lissafa masa sauran gidajen da bamu je ba shi kuma yace baisan magana ba, "Diyam makaranta zata koma nan da sati daya, kamata yayi taje gida ta huta tukunna" Inna tace "wanne hutu zatayi a gidan? Taje dai gida mayun gidan su cigaba da lasheta" Baffa ya gyada kai yace "in har mayun gidan basu cinyeta ba a tsahon wadannan shekarun, to kuwa ke a garin wannan yawon naku zaki kaita gurin mayun" nan take sai rigima, inna tace ai Baffa yace yan'uwanta mayu ne. Hardo ya goya mata baya yace "to in bata kaisu sunga yan'uwanta yanzu ba sai yaushe?" Wannan yasa Baffa ya shiga motarsa yayi tafiyar sa, yace duk sanda muka gama yawon ma taho a motar haya.
Bamu koma ba sai two days to komawa ta makaranta, dan haka a gurguje na shirya shima kuma dan na samu Ummah ta fara harhada min wasu kayan kafin inzo. Dan haka wannan hutun ni da Sadauki sai gani da ido.
A hutun second term ne Baffa ya buga kafarsa yace babu inda zanje hutu, shima yana so ya zauna dani. Nan take rikici ya balle a gidan mu, Inna ta fito da abinda yake zuciyarta na kiyayyar ta a dangane da dangantaka ta da Sadauki, tace "sai dai bayan raina wallahi, wannan yarinyar indai ni na haife ta ba zata auri wannan yaron ba" Baffa yace "saboda me? Menene dalilinki na cewa haka?" Tace "Saboda bana sonsa, na tsane shi tamkar yadda na tsani uwarsa kuma bazan taba yarda in hada jini na da nasu ba" Baffa yace "to shikenan dalilin naki? Kishi ne kawai dalilin naki? To kuma in Allah ya riga ya rubuta akwai aure a tsakanin su fa? Fada min ya zakiyi?" Tace "sai in sallama ta, in dai ta aure shi to babu ni babu ita har abada sai dai ta nemi wata uwar bani ba" na durkushe a gurin da nake ina kuka kamar raina zai fita. Ina da karancin shekaru a lokacin amma nasan muhimmancin Inna a gurina, nasan darajarta ta wuce in hada tada kowa a sauran mutane, amma kuma nasan irin zafin son da nakeyiwa Sadauki, nasan irin soyayyar da shima yake yi min da kuma irin kyawawan halayensa shida uwarsa. Menene laifinsa.
Ta cikin hawayena na hangoshi ya shigo gidan da kayan da yake zuwa gareji dasu a jikinsa duk sunsha bakin mai. Ya tsaya yana kallon mu kawai, Ummah tayi masa alama da hannu cewa ya fita, sai ya ajiye kayan hannunsa ya juya har yakai bakin kofa sai kuma yajuyo yana kallona fuskarsa cike da concern.
Wannan hutun sam ba ajin dadi nayi shiba dan sai dana gwammace ina ma wani gidan aka kaini dan sosai Inna ta mayar dani matar kulle, ko tsakar gida bata bari na in fito daga dakin mu sai palon ta, Baffa ma sai dai in ya shigo in ganshi in kaishe dashi. Yar islamiyyar da nake zuwa in nazo hutu itama ta hana ni zuwa. Asma'u ce kadai abokiyar hira ta duk da ita lokacin bata da hankalin fahimtar me yake faruwa sosai. Rannan ina kwance a daki sai gata da takarda a bakin zanin ta ta miko min a hankali tace "inji Sadauki, yace kar Inna ta gani wai zata dake ki" na karba da sauri zuciyata tana muradin jin abinda yace, na bude na karanta, kalma uku ce kawai "how are you?" Naji hawaye ya taho min, shi concern dinsa akai nane, shi halin da nake ciki shine damuwarsa.
Ranar nan muna gab da komawa makaranta Baffa yana palon Inna yana cin abinci ni kuma ina zaune kusa dashi na dora kaina a kafadarsa, a gurinshi ne kadai nake samun hope. Sallamar Sadauki muka ji a bakin kofa, nayi saurin kallon kofar amma sai naji Inna tace min "tashi ki shiga daki" kamar zanyi kuka na shiga dakin amma sai na makale a bayan labule. Ina kallonsa ya shigo ya durkusa a gaban Baffa ya ajiye wasu takardu yana yi masa bayani akan wata mota da suka siya zasu gyara su siyar. Amma ni ba abinda yake fada nake ji ba fuskarsa kawai nake kalla, sai naga ya kara kyau fuskar ta dan canza min, sannan na lura da abinda ya chanza, ya fara tara saje. Nayi murmushi na durkusa a gurin ina cigaba da kallon sa har ya gama maganar da yakeyi. Sannan ya juya side Inna ya gaishe ta duk da yasan ba amsawa zatayi ba. Bata amsa din ba har ya mike, sai daya je bakin kofa sannan ya juyo ya kalli kofar dakin mu, muka hada ido sai ya lumshe idonsa ya bude sannan yayi murmushi ya fita. Yana fita Baffa yace wa inna
"Amina ni dai bazan gaji da gaya miki cewa ba kya kyautawa ba, kina dora kiyayya akan tushe marar dalili. Su yan uwan namu da suke kara zuga ki kike ganin kamar baki da masoya kamar su duk ranar da babu raina su zasu fara gudun ki keda yayanki, zasu fara ganinku kamar wasu responsibilities a gurin su. Ina ji miki tsoron wannan yaron da kike wulakantawa shine zai zama gatanki ke da yaranki watarana idan babu raina. Shi ɗa na kowa ne."
Sai da lokacin komawa ta makaranta yayi sai naji sam bana son tafiya, duk da cewa zaman gidan kamar zaman kurkuku nake jinsa amma haka nan naji bana son rabuwa da gidan. Kamar ko wanne term, wannan karon ma Baffa da Sadauki ne suka tafi dani. Sai bayan da muka dauki hanya sannan Baffa ya fara magana
"Sadauki, Diyam ku bude kunne sosai kuji abinda zan gaya muku. Tun a gida naso yin magana daku amma saboda rigimar iyayen ku yasa na bar maganar nace mayi a hanya daga ni sai ku. Na farko, kun bani mamaki gaba dayan ku kuma kun bani kunya, yanzu har kunyi girman da har za ace an fara rigima akan auren ku? Yaushe aka haife ku gabaki dayan ku? Waye kuke tunanin zai yi muku aure yanzu? Ba dai ni ubanku ba. Musamman kai Sadauki kai da kake namiji, so nake kayi karatu mai zurfi kazama wani yadda wata rana zan kalle ka ince 'yes, that's my son'. Ke kuma Diyam, ko a ranki kada ki saka cewa zanyi miki aure yanzu. Sai kin gama makaranta kin shiga jami'a sannan in Allah ya kawo miji a lokacin sai inyi miki aure da sharadin zaki kammala karatun ki a gidansa, in kuma mijin bai samu basai kin kammala duk lokacin da Allah ya kawo shi sai ayi miki auren" yayi shiru muma duk mukayi shiru, sannan ya dora "in Allah ya kaimu lokacin, kun zama abinda nake fata zaku zama, kuma ya kasance har lokacin kuna son auren junan ku, to ni zan yi supporting dinku. Saboda dukkanin ku yaya nane, nasan halayenku kuma zanyi alfahari daku a matsayin surikai na. Kuma hausawa sunce da arziki a gidan wani gwara a gidan ka. Amma ku sani, daga ni sai Zainab ne zamu goyi bayan wannan hadin, ke Diyam a gabanki kinji kalaman da innarki ta fada, kuma da gaske take, kuma ni bazanyi miki fatan kiyi aure babu saka albarkar mahaifiyarki ba dan haka wannan shine challenge dinku ku tabbatar kafin lokacin dana fada muku kun yi kokari kuma kun dage da addu'ah kun juyo da hankalin ta ta amince."
[1/19, 11:35 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Twenty: The Two Corpses
Tunda muka koma school nake lissafin kwanaki ina jiran zuwan Sadauki dan nasan wata daya yake yi yazo ya ganni, kuma nasan bashi da karya alkawari sam. Lissafi na yana cika kuwa na fara saka ran ganinsa. Ina zaune kuwa a class sai ga baba mai kiran alkhairi yazo kirana. Na tashi na bishi da sauri jidda tana tsokana ta dan tasan lissafin zuwan wanda nakeyi. Muna fita daga class din na tsaya na kara gyara fuskata ta glass din window, ina lura da yadda sabon kitson da na saka akayi min jiya ya kara fitowa wa da kyawun fuskata. A gefen staffroom na hango shi a kasan bishiyoyi kamar kullum in yazo. Sai dai amma dama matsa kusa sai naga kamar ba shiba, kamar Sadauki na baikai wannan girma da iya daukar wanka ba. Sai na tsaya daga dan nesa nayi sallama. Ya juyo kyakykyawar fuskarsa dauke da murmushinsa mai kyau, na rufe baki ina dariyar murnar ganinsa nace "ashe da gaske kaine, sai naga kamar ba kai ba" ya harde hannayensa a kirjinsa yana kallona yace "lallai Diyam girma yazo, yau ke ce da yi min sallama bayan da tahowa kike da gudu ki wuce kirjina?" Na dan jawo hijab dina na rufe fuskata ina jin kunyarsa, ya saka hannu ya bude fuskar yace "yanzu in taho gari ya gari dan inga fuskarki kuma sai kiyi min rowarta ki rufe? Kinyi min adalci kenan?" Na danyi murmushin jin kunya sannan na kalle shi daga sama zuwa kasa. Ya zama cikakken saurayi sosai, hatta sajen sa ma ya zama complete kuma yayi masa kyau sosai. Gani nake duk samarin duniya babu wanda ya kaishi kyau a lokacin.
Sai kuma na rike baki nace "wai!! Sadauki ina zaka kai girma ne? Sai wani jin karfi kake kamar zaka dauki duniya" yace "ya kika ji sunan? Aliyu fa aka ce miki. Kin manta shi asalin mai sunan duniya kaf ta shaida karfinsa da jarumtakarsa? Sannan kuma akayi min lakani da Sadauki, kin san kuwa ko a cikin mayaka to duk wanda aka kira da Sadauki ina nufin jarumi ne shi a cikin jarumai. Ingarman namiji kenan" nayi dariya ina rufe baki, yace "what's funny?" Nace "wai ingarma, sai kace wani doki" shima sai ya tayani dariyar.
Na sunkuyar da idanuna ina wasa da fingers dina, mukayi shiru na wani lokaci sannan na dago kai na muka hada ido, na turo baki na buga kafa a kasa nace "ni ka daina kallona haka" yace "fada min menene shirrin, sai wani kara kyau kike yi kullum" na bata rai nace "bayan bana girma. Kuma wallahi ina cin abinci sosai" yayi dariya yace "girman zaizo ne Diyam. You won't know sanda zaki girma kawai sai dai ki ganki kin zama katuwa" nace "ni tsoro nake ji?" Ya bata rai yace "tsoron me? Nace "kai gashi nan ka zama kato, gashi kuma zaka tafi jami'a, kar kaje kaga manyan yammata kace ka fasa dani" ya jingina da jikin bishiya yana kallona, yace "Diyam" na dago muka ido yace "you have no idea how much I love you, do you? Ke din fa zuciyata ce, sonki kuma jinin da zuciyata take bugawa ne yana zagaye ilahirin jikina. Ta yaya mutum zai iya rayuwa babu zuciyarsa. Idan kinga Sadauki ya daina sonki to numfashin sa ne ya bar jikinsa. Idan kinga na rabu dake Diyam to kirjina aka tsaga aka cire zuciyata daga ciki. Nine ya kamata in kasance cikin tsoron watarana zaki rabu dani, ina tsoron idan innarki ta ki amincewa dani Baffa zai hanani aurenki, ina tsoron in kin girma zaki samu wani wanda ya fini kudi wanda ya fini asali kice kin fasa dani" na girgiza kai na nace "never, ba dai Diyam ba, Diyam ai kai take so tun kafin ta san menene so, da kai ta saba da kai kuma za tayi rayuwa insha Allah. Rayuwa babu kai will not be only unbearable but also unimaginable. I can't imagine Diyam without Sadauki" sai ido na ya kawo kwalla, yace "zaki fara kukan ko? I am here and I am going no where"
Muka zauna akan bench ya fara bani labarin gida, ana yake gaya min Baffa ya siya masa fili, yace "filin fa babba ne sosai, wai ashe for years yana tara min kudin aikin da nakeyi masa a garage shine yakara akai yasiya min. Yace duk sanda natashi yi mana ginin gidan mu sai inyi akai. Sannan kuma ya fara bani salary a garage kamar sauran ma'aikata" nayi murmushi nace "inye, kaga masu albashi" ya daga gira yace "ya kika gani?" Nace "Baffa ya kyauta. Allah ya saka mishi" yace "ameen. Problem din da nake fuskanta daga Ummah ne, tun ba yau ba kinsan nake fama da ita akan ta kaini dangin babana taki, ni kuma yanzu ina ganin kamar har da rashin su a tare dani ne yake kara kiyayyata a zuciyar Inna, ina so su shiga rayuwata Inna ta gansu tun yanzu amma kullum Ummah tana ce min wai ba yanzu ba, wai lokaci bai yi ba. I just hope ba zai zama too late ba" nace "it won't be, ni nasan Ummah kuma na tabbatar tana da dalilinta".
Ya sunkuyar da kai yana kallon kafarsa fuskarsa da alamun damuwa, naji nima zuciyata babu dadi sai nayi niyyar saka shi dariya nace "Sadauki kaga wani kwaro zai shigar maka ido rufe idonka inga ni" sai kuwa ya biye min ya rufe idonsa, sai kuma na shagalta da kallon fuskartasa. Fuskarsa bata cika tsaho ba kuma ba za'a kirata da zagayayyiya ba. Gashin girarsa mai cika ne da laushi kamar yadda gashin kansa yake, dogon hancinsa da kofofin suke budewa da sauri da sauri a yanzu alamun bugun zuciyarsa ya karu, madaidaicin bakinsa mai dauke da lips a slightly lighter than his dark skin color kuma suke zagaye da kyakykyawan sajensa mai laushi da kyalli, abinda yafi ɗaukan hankalina a fuskarsa sune zarazaran gashin idonsa da suka yi kama da irin wanda yammata suke sakawa a gidan kwalliya.
Sai kuma nayi dariya, ya bude idonsa yana kallona yace "what? Ya fita?" Nace "wallahi gashin idonka irin na yammata ne" ya bata rai yace "Diyam kin raina ni Wallahi, dan kinga gurin kwana na ko?"
Sanda aka zo min general visiting sai naga anxo har da Ummah wannan karon, abinda ba'a taba yi ba. Naji dadi sosai muka zauna mukayi ta hira, muka ci abinci har da Baffa. Da zasu tafi kawai sai na fara kuka, abinda na dade banyi ba. Baffa yace min "ki zama yarinyar kirki Diyam, ki rike addinin ki kuma ki dage da addu'a akan komai ya same ki. Allah yayi miki albarka" sai na rungume shi ina kuka, yana dariya yace "yau kuma shagwabar kaina tazo?" Ya cire hannu na daga jikinsa, Ummah tace "zo ni ki rungume ni tunda shi baya so" na sake shi kuwa na tafi na rungume ta, sannan na juya na rungume inna itama. Ina kallo suka shiga mota suka tafi, sai naki kamar wani part nawa ya tafi tare dasu.
Kafin muyi hutu Sadauki ya sake dawowa. Wannan karon shida wani abokinsa suka zo kuma shine karo na farko da Sadauki ya fara introducing dina a gurin abokinsa, Ahmad Muhammad, na rike sunan ne saboda a ranar mun jima muna musu akan Ahmad da Muhammad duk suna daya ne. Sai kuma mukayi hirar carrier, shi Ahmad yace babu abinda yake so ya zama inya girma irin dan sanda, yace "duk ranar da na zama commissioner of police duk wadannan yan iskan da suke yawo a gari sai na rufe su" Sadauki kuma yace "ni kam whatever zan zama nan gaba a rayuwa will have to do with cars. Ni ina da wani passion sosai akan motoci" sai suka tambayeni ni kuma fa? Na girgiza kai na nace "I don't know gaskiya" Ahmad yace "with time zaki yi finding your place in the society kema".
Tunda hutu ya kusa nake jin babu dadi kamar wadda zanyi rashin lafiya amma kuma ciwon yaki zuwa, haka nayi exams din duk babu dadi. Ko kitson hutu banyi ba. Ranar hutun kuwa sai jidda ce ta hada mana kayan mu ta kai mana bakin gate. Har ta dawo ina kwance akan gado kawai naki hawaye yana bin fuskata, tazo ta tsaya tana kallona tace "kuka kuma Halima? Wani abun ne yake miki ciwo?" Nace "zuciya ta ce babu dadi jidda, ji nake kamar bani da lafiya amma kuma lafiya ta kalau, gaba na sai faduwa yake yi jidda" tazo ta rike ni tace "to ai addu'a zaki ke yi, innalillahi wa inna ilaihir rajiun , ba wai kuka ba" na fara yi kuwa sai naji naji dadi. Muka fito tare akayi assembly aka sallame mu kowa yana murna bandani.
A ka'ida duk ranar hutu kafin a bude gate su Baffa suke zuwa, amma yau sai naga an bude ana ta daukan sauran dalibai bandani. Na samu kofar wani class na zauna idona akan gate din makarantar amma ko motar da tayi kama da tamu ban gani ba. Har aka zo daukan jidda tazo tayi min sallama ta tafi. Har akayi sallar azahar shiru. A lokacin I was beyond crying kawai dai a zaune nake kamar mutum mutumi. Can sai ga wani malamin mu yazo inda nake yace "Halima? Ki zo anzo daukanki" na mike jiki ba kwari na bishi ina ta baza idon ganin Baffana ko Sadauki. Muna shiga staffroom sai naga Abba, baban su Rumaisa. Na tsaya kawai ina kallonsa yace "Diyam babu gaisuwa?" Sai na durkusa na gaishe shi malaman gurin suna ta kallona. Ya tashi da kansa ya zuba min kayana a motarsa sannan yace min inzo mu tafi, sai da muka shiga mota sannan nace "Abba ina Baffa yake?" Ya dauke kansa yace "sun taho motar su ta samu matsala, shine yayi min waya ni kuma na taho daga gumel yace dan Allah in biyo in taho dake" na gyada kaina kawai ina forcing zuciyata ta yarda da maganar sa.
Har muka shiga Kano bamu kara magana ba, na kwantar da kaina na rufe ido na kamar bacci nake yi amma ido na biyu. Na bude ido na kallon inda muke naga ba hanyar gida bane ba nace "Abba ba gida zamu tafi ba?" Yace "zan karbi wani sakona ne anan akth" na koma na kwanta. Ina ji muka shiga asibitin har mukayi packing, na daga kaina kadan ina kallon inda muka tsaya "Accidents and Emergencies" sai kuma ido na ya hango min wata kamar Aunty Fatima a tsaye a kofar gurin, sai na bude kofa na fita idanuna suna kara tabbatar min ita din ce amma zuciyata ta kasa yarda. Ina zuwa kusa da ita na lura kuka take yi, na bude baki zanyi mata magana sai na hango Inna a cikin hall din, Mama ta rike ta tana ta rusa kuka kamar ranta zai fita. Kamar mutum mutumi haka nake tafiya har nazo kusa dasu, sai naji muryar Ummah daga gefena tace "Diyam!!" Na juyo na zube idanuna a kanta, she looked old, ban taba ganinta a irin wannan yanayin ba amma kuma babu hawaye ko digo a idonta, "Diyam" ta sake fada sanda ta karaso kusa dani ta miko hannu da niyyar rungume ni amma sai ta sulale ta fadi kasa ta suma akan kafafuwana.
Tsayawa nayi kawai ina kallonta yayinda jama'a da ma'aikatan asibitin sukayi kanta. "Addah" naji muryar Asma'u a bayana, na juyo lokacin data karaso da gudu ta rungume ni
"addah mun shiga uku, Baffa da Sadauki sunyi accident kuma duk sun mutu"
Na cire hannunta daga jikina na dan tura ta kadan ina kallon fuskartada take cike da hawaye, sai kuma naji wani abu yana fusgata zuwa wani daki da naga wani doctor ya fito daga ciki yanzu. Na tura kofar dakin ina kallon gadaje guda biyu da suke a cikin dakin, sannan na kalli wadanda suke kan gadajen. Gadon farko wanda yake kai an lullube shi har fuskarsa. Gado na biyu kuma an rufe shi zuwa kirjinsa. Sadauki. Daga inda nake ina iya hango jinin daya jika sumar kansa ya bata katifar da yake kai.
[1/21, 2:47 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤ DIYAM ❤
By
Maman Maama
Episode Twenty One : The Two Corpses 2
Na dauke idona daga fuskarsa na mayar kan daya gadon da yake gaba na, sannan a hankali na taka na isa gaban gadon na saka hannu biyu na yaye sheet din da aka rufe mutumin. Idona ya sauka akan Baffa, kamar Sadauki shima gashinsa a jike da jini amma fuskarsa tas da ita babu emotions kamar mai bacci, na jima ina kallon sa dan ina jin ban taba yi masa cikakken kallo irin na yau ba. Kofa aka bude daga bayana wata nurse ta shigo da sauri tace "what .. ?" Sai kuma tayi shiru, ta karbe sheet din daga hannuna ta mayar ta rufe shi sannan ta kama hannuna ta jani kamar wata robot ta fita dani. Gurin su Inna ta kaini, wadda har yanzu take jikin Mama tana ta kuka, hannun ta daya rike da Asma'u. Nurse din tace "tare kuke da wannan yarinyar?" Inna ta kalle ni, da alama sai yanzu ta lura da zuwa na asibitin, tayi sauri ta jawo ni tana gyada wa nurse din kai tace "yata ce, yata ce" cikin kuka. Sai kuma ta rungume ni tana kara sautin kukanta.
Mama tace "haba addah, ya zaki saka yara a gaba kiyi ta wannan kukan haka? Da wanne zasu ji. Dan Allah ki rage wannan kukan inba so kike kema ki yanke jiki ki fadi ba" ta jawo ni daga jikin Inna ta zaunar dani a kan benchi ta rike fuskata tace "kai kiyi kuka kinji Diyam? Kiyi ta karanta innalillahi wa inna ilaihir rajiun" na gyada mata kai ina kallonta. To ni kukan me zanyi ne bayan nasan mafarki nake yi? Yanzu zan farka amma bana so in farka din sai Baffa da Sadauki sun tashi.
Wata nurse naga ta fito daga wani daki da sauri ta kira doctor sun koma tare, sai na samu kaina da mikewa na bisu amma ban shiga ba sai na tsaya a bakin kofar ina kallon ciki ta glass din jikin kofar. Ummah na hango akan gado, nurses biyu da likita daya a kanta suna ta kokarin bata taimako. Sai kuma ta fara convulsing, idanunta suka kakkafe doctor din yana ta kokarin reviving dinta amma sai jikinta ya saki. Ina kallo suka yi ta aaunata sannan doctor din ya kalli nurse din data dauko takarda da biro yace "time od death: 4:35" sannan ya bude kofa ya wuce ni jikinsa duk a sanyaye.
"Death" na maimaita. "Ummah, Baffa, Sadauki" na fada a hankali ina jin kaina yana juyawa. Na bi bayansa a hankali naga ya tafi gurin su Inna yayi musu wata magana, sai naga Inna ta saki hannun Asma'u da sauri ta rufe bakinta ta durkushe a gurin, Mama tana ta salati ita ma su Aunty Fatima suna tayata. Da sauri Inna tazo ta wuce ni ta shiga dakin da Ummah take sai kuma ta sake fitowa da sauri ta hada kanta da bakin kofar tana kuka kamar ranta zai fita. Tunda nake a lokacin ban taba ganin Inna cikin tashin hankali irin na yau ba.
Muryar yaya ladi na jiyo ta shigo gurin. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. La haula wala quwata illah billah. Wayyo Usumanu wayyo Aliyu, yanzu aka kira ni akace sunyi hatsari an kawo su nan. Ya jikin nasu? Ya kuke ta kuka haka?" Kowa ya kalleta sai dai ya kara kukansa, ta rike kafada ta "Halima? Ina marasa lafiyan suke? Ina Zainabu kuma? Ya banganta anan ba?"
Nurses ne su biyu suka zo suka kamata suka jata gefe, duk suma a diririce suke suna yi mata magana, bana jin me suke cewa amma can naji ta saka wani kuka mai ban tausayi sannan ta wuce mu da sauri ta shiga dakin da Ummah take. Alhaji Babba ne da kawu Isa suka shigo gurin, Alhaji Babba yana fada
"menene hakan duk kun cika asibiti da koke koke? Kukan zai dawo dasu ne? Kun kuma san babu kyau yiwa mamaci kuka ko? Fatima ki riko yaran ke kuma Hafsa ki kamo Amina mu zamu taho da gawawwakin ayi musu wanka ayi musu suttura tun kafin magrib tayi".
Wannan maganar tasa ita ta dawo dani cikin hayyacina, lokaci daya naji reality din mutuwar ya doke ni. Na juya da sauri ina kallon kofar dakunan da gawawwakin suke. "Baffa!!" Na fada da iyakacin karfina "Sadauki!! Ummah" Aunty Fatima tayi saurin rufe min baki na da hannunta tace "kul Diyam, ba'a yiwa mamaci ihu". Sai na mayar da kaina jikinta na kwanta na rufe ido ba tare da na sake cewa komai ba. Nasan dai mun shiga mota sannan mun fita, sai kuma naji mun shiga gida mun shiga daki an zaunar dani akan kujera. Sannan ne na bude ido ana ganni a palon Inna, Asma'u tana zaune kusa dani tasha kuka ta koshi, ina jiyo tashin sautin kukan Ummah sama sama amma ban juya ba ballantana in kalli inda take.
Muryar Alhaji Babba naji ya shigo gidan, ya daga labilen palon Inna yace "a dauke carpet din palonsa sai muyi masa wanka a can" na runtse idona ina so hawaye ya fito min amma babu. Muna nan zaune sai muka ji hayaniya kuma, muryar Alhaji Babba "ku fita da ita daga gidan nan, ai tun sanda ya aure ta mun gaya masa babu mu babu ita, dan haka yanzu ma babu mu babu ita" sai muryar yaya ladi tana kuka. Ji nayi kamar in tashi in shake shi, how dare he said that a ranar da Baffa ya bar duniya? A ranar da Ummah ta bar duniya?" Rigima sosai har makota suka fara taruwa, sai ga dattijon mutumin da har yau yaya ladi take gidan sa yazo yace "a gidan aurenta za'ayi mata suttura kamar kowacce matar aure, kai kuma baka isa ka hana ba in kuma zaka iya to ka dauko yan sanda" ganin mutane suna ta kallonsa accusingly ya saka Alhaji Babba ya ja baya ya bari aka shigo da gawar Ummah. Na tambayi kaina to ina Sadauki kuma?
Tare akayi musu suttura, shi a palonsa ita a nata, sannan aka zo aka fita dasu ta gabanmu a tare. Na bi su a baya nayi musu rakiya har bakin gate sannan na tsaya ina kallo aja jera gawawwakin su akayi musu sallah a tare aka dauke su zuwa gidan su na karshe.
Na koma gida ina tafi ina hada hanya. A tsakar gida na durkusa a cure a guri daya ina kara tambayar kaina ina Sadauki? Ji nake nima inama dai mala'ikan mutuwar zai zo ya hada dani. Mama ce tafito ta ganni a gurin, sai ta dauko tabarma ta shimfida mana muka zauna ta jani zuwa cinyarta na kwanta. Anan mukayi sallar magrib, sai ga yaya ladi ta fito tazo inda nake ta shafa kaina tace "sannu Halima, Allah yaji kansu yayi musu rahama, shi kuma Aliyu Allah ya bashi lafiya" na dago kai da sauri na ina kallonta sai naji tace wa Mama "zan koma asibiti inga halin da yake ciki" Mama tace "to Allah ya jishe mu alkhairi" nace da Mama "waye a abibitin?" Tace "Sadauki mana" naji wani abu mai nauyi daya tokare tun daga zuciyata zuwa makogwarona ya janye, numfashi na ya fara fita da sauri nace "Sadauki? Ba tare suka mutu ba? Na dauka ko an kai gawarsa wani gurin" ta rike hannuna tace "Sadauki bai mutu ba ya samu buguwa ne a kansa shi yasa doctors sukayi sedating dinsa. Baffanku kuma tun kafin a kawo su asibiti ya cika, Ummah kuma tashin hankali ne ya saka ta yanke jiki ta fadi, jininta yayi mugun hawan da cikin yan mintina ta mutu" naji wani abu yana sauka daga kai na zuwa kafafuwana. Sadauki is alive. Then there is hope for me.
A daren ranar banyi bacci ba, muna kwance ina rungume da Asma'u da take ta jera ajjiyar zuciya saboda kukan da tasha, sai da naga ta samu bacci mai nauyi sannan na zame jikina na fita palo, Inna na gani zaune akan sallaya ta rufe fuskarta da hannayenta tana kuka a hankali, sai na wuce ta na shiga toilet nayo alwala nafito nima na tayar da Sallah, yau shine daren Baffa da Ummah na farko a kabarinsu kuma nasan suna bukatar adduoin mu sosai. Har na idar da sallolina Inna tana kuka, sai na kwanta akan sallayar na dora kaina akan cinyoyinta sannan nima na samu kuka yazo min.
Washegari yan Kollere suka zo, gida ya cika taf ana ta karbar yan gaisuwa amma babu wanda naji ya kuma maganar halin da Sadauki yake ciki, yaya ladi ma kuma ban kuma ganinta ba duk kuwa da cewa jama'ar Ummah suna ta zuwa gaisuwa suma. Inna dai kam tayi kuka kamar idonta zai fita kowa yashigo gidan sai ya tausaya "uwargidan sace kuma uwar yayansa". Sai dare na ajiye tsorona na tambayi Inna "Inna ya jikin Sadauki kuwa?" Ta kalle ni ta dauke kai, "ban sani ba" ta fada tare da cigaba da jan carbin ta.
Ranar da akayi sadakar uku ranar munga mutane, dan ko ranar mutuwar gidan baiyi wannan cikar ba, ranar yaya ladi tazo akayi adduoi da ita, sai da aka gama ta tashi zata tafi na bita a baya nace "yaya ladi ya jikin Sadauki?" Ta juyo ta kalleni tace "da sauki Halima, jikinsa da sauki" sai ta juya tayi tafiyarta. Alhaji Babba ya shigo bayan an gaishe shi yace "Amina zamu saka a gyara muku guri a can gidana, idan anyi bakwai sai ku koma can ku zauna ke da yara saboda nan din ba zaku ji dadin zama ba ku kadai. Allah ya ji kansa" akace ameen sannan akayi masa godiya ya tashi ya tafi.
Zuwa yamma I have taken all I can, ji nake nima kamar nawa jinin zai hau irin na ummah nima in mutu, an gama adduoin kuma an mayar da gidan kamar gidan biki sai ciye ciye ake da hira da dariya. Na shiga dakin inna na bude jakar ta na dauki kudi na saka hijab dina na fixe ba tare da kowa ya lura ba. Adaidai na hau direct na tafi asibitin malam, naje har emergency room nayi sa'a kuma visiting hours ne dan haka na tambayi nurses Aliyu Usman Kollere nake nema sai suka ce inje aminity room 3. Da sauri na na tafi, zuciya ta tana jin kamar zata kara sauri tayi gaba ta riga ni shiga dakin.
A kwance na same shi da drip a hannunsa daga alamar har yanzu allurar baccin akeyi masa, fuskarsa da dan fada kuma tayi haske, kansa a nade da bandage. Babu kowa a dakin sai shi kadai. Na karasa ciki inajin wani irin tausayinsa yana saukar min, na zauna a gefen gadon na kamo hannunsa nayi intertwining fingers din mu. Ya dan bata rai sai kuma yayi blinking ya bude jajayen idonsa yana kallona, ya kakalo murmushi mai nuna yana jin ciwon yinsa yace "you are here" na gyada kai nace "am here" yace "waye ya dauko ki daga school?" nace "Abban su Rumaisa" yace "good" mukayi shiru kuma can sai yace "ya jikin Baffa?" Gabana naji ya fadi na zuba masa ido, wato bai ma san abinda yake faruwa ba? Ya sake cewa "yaya ladi tace min ya samu karaya ne shine aka kai shi asibitin kashi. Shine kuma duk kuka tafi gurinsa ko?" Ya sake kirkiro murmushi "dama nasan Ummah tafi son Baffa akaina shine ta tafi jinyarsa ta barni, in kin koma ki gaya mata nayi fushi, nima tawa matar tazo ta ganni" na cije lebena ina danne kukan da yake so ya kwace min, sai yace "don't cry please, everything will be alright"
Na gyada kaina nace "yes Sadauki, everything will be alright. Ka koma kayi baccinka" ya lumshe ido yana kara rike fingers dina a cikin nasa. Mun jima a haka ina kallon fuskarsa ina jin wani irin yanayi yana kara shiga ta a kansa, nayi kokarin zare hannuna daga nasa sai ya kara rikewa a hankali cikin bacci yace "don't leave me please, stay with me please" sai ya dora hannayenmu akan kirjinsa sannan ya dora daya hannun ya sake rike wa.
A haka yaya ladi ta shigo ta same mu, ta tsaya tana kallon mu sannan ta girgiza kanta tace "an mutu an bar muku gadon wahala".
[1/21, 10:27 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Twenty Two : Birthday Gift
Abinda na tarar a gidan mu dana koma banji dadinsa ba, harkoki kawai ake yi ana wadaka da abinci, wato shi wanda akayiwa mutuwa shi kadai ta shafa ko? Shi kadai yasan me yake ji? Wato mutuwa ba zata zamo izna ga sauran mutane su nutsu su daina biyewa duniya ba? An bubbude koina har palon Baffa mutane ne a ciki, bedroom dinsa ne kawai a rufe.
Dakin mu na wuce da niyyar in kwanta inji da abinda yake damuna amma sai na tarar da yammata ne fal a dakin, suna ta dauke dauken hotuna da kallon videos a waya suna kyalkyatar dariya. Ko magana banyi musu ba na fito da shiga part din Ummah, babu kowa anan kofar palon ma a saye take dan haka na tura na shiga na mayar na rufe. Direct dakin Sadauki na tafi na bude na shiga. Dan karami ne dai dai size din dakin mu ni da Asma'u, katifa ce kawai a dakin sai wardrobe, standing fan, sai kuma tarkacen takardu a gefe. Sai hoto guda daya a jikin bango. Na tsaya a gaban hoton ina kallonsa kamar yau na fara ganinsa, Ummah ce da Baffa a zaune akan kujera, sai Sadauki a durkushe a gaban baffa sai ni kuma akan cinyar Ummah da shubeya a hannu na.
Na tuna sanda aka dauki hoton da wata sallah ne lokacin Inna tana da cikin Asma'u, babu yadda Baffa baiyi ba ita ba akan tazo ayi hoton taki tace sai dai yaje mu dauka daga ita sai shi sai ni. Shi kuma yaki. Na zauna a gaban hoton ina jin kewarsu tana kara mamaye ni, ina jin kamar inyi rewinding din rayuwar mu ta dawo baya in cigaba da ganin su, in cigaba da ganin Sadauki a gidan mu. Inna tuna cewa Sadauki bai san anyi mutuwar nan ba sai inji zuciya ta duk ta narke, bansan yadda zai dauke ta ba, ina gudun kar wani abun ya same shi shima. In na tuna yanzu bashi da kowa a duniya sai inji kamar in tashi in koma asibitin in zauna a wurinsa. Hope dina daya shine na yaya ladi zata kaishi gurin mahaifinsa tunda nasan dole zata san waye shi, in ma bata sani ba shi wanda ya hada auren ai zai sani. Amma kuma in nayi wannan lissafin sai inji zuciya ta ta kara tsinkewa saboda tunanin rabuwa da Sadauki. Kuma what if shi uban baya bukatarsa? What if shine yakori Ummah da jariri yace baya so?
Anan dakin bacci mai nauyi ya dauke ni saboda kwana ukun nan duk bana samun bacci mai nauyi. Na jima ina yin baccin sai naji magana kamar a tsakiyar kaina ance "Diyam? Uban me kike yi anan?" Na tashi zaune ina mitstsika ido amma na kasa bude idona saboda fitilar da aka haske ni da ita. Aunty Fatima tazo ta kama ni muka mike "tun dazu ake ta neman ki, babu inda ba muje ba duk hankali ya tashi mun dauka an sace ki ne" nace "kuyi hakuri, bansan bacci ya dauke ni ba, hayaniya ce ta yi yawa acan ni kuma ina so in zauna ni kadai" sai kuma sukaji tausayina, amma inna sai da tace "kuma ki rasa inda zaki je ki kwanta sai nan dakin? Ba gwara ki tafi makota ba?".
Sai da aka sake kwana biyu sannan na kuma samun dama na tafi dubo Sadauki, wannan karon tare da Rumaisa muka tafi kuma sai da na saka tayi min alƙawarin ba zata gaya wa kowa ba. A zaune muka tarar dashi yaya ladi tana ta fama dashi akan yaci abinci. Tun a fuskarsa na gane yaji dadin zuwana sosai. Yace "kun taho da waya? Ina son in kira Ummah, ina so kuma inji ya jikin Baffa" na girgiza masa kai nace "bani da waya ai ka sani, kuma bansan zaka bukata ba shi yasa ban karbo wata na taho da ita ba" ya jingina kansa a jikin gado yana runtse idonsa yace "a gurin da muka yi accident aka dauke min waya ta, ita kuma wannan tsohuwar wai tata ta lalace" na jawo kujera na zauna ina karbar kwanon abincin daga hannun yaya ladi nace "duk suna lfy Sadauki, ummah cema tace inzo in duba mata kai. Kasan ba zata iya barin Baffa ba Musamman yanzu da bashi da lfy" ya gyada kai yana murmushi yace "ji nake yi kawai ina so in ganta" ina kallon Rumaisa ta tashi ta fice daga dakin. Na zuba masa tuwon alkama miyar danyar kubewar da yaya ladi tayo masa na zauna ina bashi a baki, ba musu yake karba idanuwansa a kaina ko kiftawa baya yi har sai da ya cinye wanda na zuba masa tas, yaya ladi tace "oh, tun safe nake fama da shi akan yaci abinci yaki ci, shifa yace inyi masa tuwon amma shima ya bar ni da abina, amma da yake ke kece gashi nan ai ya cinye tas" ya juya yana kallonta yace "baki iya tarairayar miji ba ne shi yasa" da alama so yake suyi wasa irin yadda suka saba amma sai ta kasa mayar masa, sai ta hau tattara kayan gurin ta fita dasu.
Na saka tissue ina goge masa bakinsa sai ya rike hannun yana kallona cikin ido yace "kin rame, kinyi duhu, idonki sun kumbura" na kirkiro murmushi nace "ka manta daga makaranta na dawo, kuma exams muka gama bama samun isashshen bacci" ya saki hannuna yace "fada min gaskiya, ya jikin Baffa, is it bad? A ina ya karye?" Na kasa kallon idonsa nace "a hannu ne kuma da sauki" yace "hannu kuma? I thought kafa ce ma saboda shi yake driving" na dago ina kallonsa da mamaki dan nasan Baffa hardly drives in dai da Sadauki a motar. Nace "me ya faru?" Ya sunkuyar da kai yace "rami muka daka sai taya ta fashe, daga nan motar ta fara a dungure akan titi, sai data daki wata bishiya sannan ta tsaya" na gyada kaina ina rike hawaye na.
Muna komawa gida muka tarar da inna a tsakar gida tana alwalar magrib tace "daga ina kuke?" Rumaisa tace "makota muka shiga". Shikenan bata kara ce mana komai ba.
Washegari bayan nayi sallah na kwanta akan kujera amma ba bacci nake yi ba, na rufe idona ne kawai saboda bana son kowa yayi min magana a lokacin. Ina ji akayi ta hidimar abinci sannan aka fito palo aka baje kowa yana ci ana ta hira, cikin hirar naji Inna tana bawa yan uwanta da suka zo daga Kollere labari:
"Wallahi in gaya muku, daga zuwanta da yaron nan ya dauki son duniya ya dora akansa, komai Sadauki komai Sadauki, ni na dauka ko rashin haihuwa ne ya saka haka amma sai gashi bayan na haifa masa yaya har biyu amma sadaukin nan dai ya fiye masa duk su biyun. To in ba asiri ko maita ba me zai jawo haka? A ce agolan da aka haifa a wani gidan koma a wani titin ne oho, tunda babu wanda yasan ubansa amma ace yafi yayanda mutum ya haifa da cikin sa? Ai shari'a tsakani na da zainabu sai a lahira za'a karasa ta. Tun yaron nan yana dan mitsitsinsa aka fara bashi mota a gidan nan, kullum 'sadauki zo ka kaini guri kaza, Sadauki zo muje guri kaza' nayi magana amma a banza tunda dama ni ba jin magana ta yake yi ba. Shine ranar nan yace "Sadauki zoka kaini Taura mu dauko Diyam' to gashi nan bai kaishi taura ba ya kaishi lahira" naji kaina ya sara, ina so in tashi in gaya mata cewa ba Sadauki ne yake driving a ranar ba amma nasan ba yarda zata yi kuma zata tambayeni wa ya gaya min.
Wata ta tambayeta "to ina yaron yake yanzu?" Tace "yana asibiti yana karbar magani, kinsan irinsu bada wuri suke mutuwa ba" sai na tashi tsam na wuce su na shiga daki. I can't take sunan sadauki da sunan mutuwa a sentence daya, not now da nake ganin ya samu sauki sosai. Not now da nake ganin nafi bukatar safiye da koyaushe.
Washegari akayi sadakar bakwai. Jama'a sun taru sosai bangaren Baffa da na Ummah, ga kuma makota da abokan arziki. Yaya ladi ma da sassafe tazo ta bude dakin Ummah inda mutanen su suka zauna. Ana gama yin adduoi aka yi sadaka sai kuma kowa ya fara watsewa, har yan Kollere ma duk sun gama shirin su ana gama wa suka yi sallama suka dauki hanya. Muma kuma sai Inna ta fara hada mana kaya amma ni sai na koma na zauna a tsakar gida na takure a guri daya ina sheshshekar kuka. Yanzu shikenan barin gidan mu zamuyi? Gidan da aka haife mu muka tashi a ciki, me yada zamu barshi mu koma gidan wasu mu zauna a karo? Bayan muna da rufin asirin mu. Ina kallo aka fara fita da kayan mu ana zubawa a motar da Alhaji Babba ya aiko da ita.
A lokacin ne kuma ya shigo. Kansa still a nade da bandage hannunsa kuma sanye da carnula. Ya tsaya yana rike da kofa for support idanuwansa a kaina, na mike nima ina kallonsa ina hango tsantsar tashin hankali a idonsa. Ko ba'a gaya min ba nasan ya sani. "Ina Ummah?" Ya tambaye ni da wata irin murya, sai na fara sheshshekar kuka na kasa ce masa komai. A lokacin ne Inna ta fito da wani akwati a hannunta ta ajiye tana kallonsa tace "sun sallamo ka kenan, dama yanzu nake tunanin yadda za'ayi a fitar maka da kayanka zamu rufe gida" ya kalleta kawai sannan ya sake mayar da dubansa kaina yana kallon yadda nake kuka babu sauti, hawaye wani na korar wani. Sai ga yaya ladi ta shigo afujajan, tana ganin shi ta sauke ajjiyar zuciya "yanzu shine ka fito daga asibitin ka taho nan Aliyu?" Kallo daya yayi mata sai ta saka kuka itama.
Na tafi a hankali har inda yake tsaye na rike hannayensa a nawa, sai kuma na dora kaina a kirjinsa a hankali nace "Sadauki Ummah ta tafi ta barmu, Baffa ma ya tafi ya barmu, sun mutu Sadauki ba zamu sake ganin su ba. Mu dasu sai dai muyi musu addu'a kuma sai kuma a lahira in munje muma"
Baice min komai ba bai kuma yi magana ba amma ina jiyo yadda zuciyarsa take bugawa kamar zata bar jikinsa, ya saka hannu ya ture ni daga jikinsa ya fara tafiya kamar zai tafi dakin Ummah sai kuma ya juyo, yayi kamar zai fadi na tafi zan rike shi sai ya dakatar dani da hannu daya daya hannun kuma ya dafe kirjinsa dashi. Ya dan jima a haka sannan ya sake straightening ya doshi hanyar waje, da sauri ni da yaya ladi muka rufa masa baya muna kiransa amma sai Ummah ta damko rigata a dawo dani baya "in kika bar gidan nan sai na kakkarya ki" ta harari waje "muma duk marayun ne, mun rasa iyayen mu kuma mun hakura".
Sai daga baya na fahimci ashe wasu kawayen Ummah ne suka je duba shi a asibiti shine suka yi masa gaisuwa, basu san cewa bai sani ba, shine ya gudo daga asibitin ya taho gida dan ya tabbatar. Ni dai a bangare na zan iya cewa tunda akayi rasuwar nan banyi kuka mai yawa irin na ranar nan ba dan a tsakar gida na zauna nayi tayin abu na, ina kukan tausayin kaina ina kuma kukan tausayin Sadauki. Menene makomar mu ? Menene makomar soyayyar mu? Babu wanda ya kula ni sai Asma'u da take makale dani tana taya ni kukan itama.
Can naji Inna tana cewa "su kenan kayan sun kare, in muna bukatar wani abu ko Diyam sai tazo ta daukar mana tunda babu nisa" Mama tazo ta tashe mu ni da Asma'u "ku daina kuka kunji? Ai ba barin gidan kuka yi ba gaba-daya zaku dawo in innar ku ta gama takaba" na gyada mata kai kawai. Muna ji muna kallo aka tisa keyar mu zuwa waje aka rufe gidan, a raina ina tunanin kayan Sadauki fa? Kayan Ummah fa? Ai bamu kadai muke da gidan ba tunda dai a tunani na Ummah tana da gado dan haka Sadauki ma yana da gado kenan.
Ina shiga mota kamar ance in kalli side sai na hangoshi a tsaye a jikin bishiyar da take opposite gidan mu, hannayensa a rungume a kirjinsa, idanunsa a cikin nawa. Nayi kamar zan fita sai Inna ta tura ni ciki ta shigo ta rufe kofa. Driver kuma ya tayar da mota muka tafi. Na juya waiwaya baya ina hangoshi ya matso tsakiyar layin mu yana kallon motar mu har muka sha kwana na daina ganinsa. Na juyo idona ya sauka akan dashboard din motar, agogo na kalla,time 3:15 date 25th August and it occurred to me cewa yau ne ranar Birthday dinsa, a yau ya cika shekaru ashirin cif a duniya. So young and so alone. Sai na rufe fuskata da hannayena ina sake wani sabon kukan.[1/22, 11:13 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤ DIYAM ❤
By
Maman Maama
Episode Twenty Three : Shared Strength
Assalamu alaikum wa rahmatullah
Ina neman afuwar wadanda littafin Diyam ya saka kuka a kwana biyun nan, ina rubutu ne dan in faranta muku badan in bakanta muku ba. Amma ina so ku sani ita rayuwa is full of ups and downs dole sai ansha wuya sannan za'a sha dadi. Ina so duk sanda kuke karatu ku saka a ranku cewa kirkirarren labari ne, non of this happened in real life duk da cewa zai iya faruwan. But labarin Diyam kirkirarren labari ne.
Daki ne aka bamu a gidan Alhaji Babba, dakin a babban palon gidan yake. Ciki daya ne da banɗaki mai dauke da gado da wardrobe a ciki, asalin dakin an yi shine saboda baki in sunzo daga Kollere anan suke dauka amma sauran matan gidan kowa in tayi baki to part dinta suke tafiya. Muna zuwa matan gidan duk suka firfito harda Hajiya Babba da kanta, aka zauna a palo ana ta kara yiwa juna gaisuwa da kuma jajanta abinda ya faru sannan aka saka yan aiki suka kara gyara mana dakin aka kai mana kayan mu can sai kuma kowa ya watse ya bar mu mu kadai.
Nina fara tashi na shiga dakin da aka bamu ina kare masa kallo, babu laifi yana da girma kuma da toilet a ciki amma kuma it doesn't change the fact that aro aka bamu, aron kuma da nia ganina bama bukata. Na tuna yawan dakunan da suke gidan mu, Inna daki biyu da palo, Ummah daki biyu da palo sannan ga dakin Baffa ciki da palo ga kuma dakin waje, amma wai duk mun ajiye su mun dawo daki daya mun zauna da sunan taimako, taimakon me? In taimaka mana za'ayi ni a ganina ai food stuff ya kamata ake kai mana can gidan mu kamar monthly haka ko duk sanda aka samu dama, ko ake bamu kudi muna siyan abin bukatun mu da kan mu amma ba gurin zama muke bukata ba. Kuma ko kudin ne ma ni aganina zamu iya kula da kan mu ba sai mun dogara da kowa na. Yes, Baffa ya mutu amma bai bar mu fakirai ba, ya bar garejin sa da yake running for over twenty years, zamu iya cigaba da running kayan mu da kan mu, Sadauki can do that tunda yasan komai dashi ake komai kuma duk costomers din Baffa sun san shi.
Ni a ganina da mun yi zaman mu a gidan mu mun dora Sadauki akan komai kuma nasam as hard working and dedicated as he is zai iya yin komai. Ya cigaba da zamansa a gidan for security tunda za'a ce ba zamu zauna mu kadai babu namiji ba, in ma kuma Inna bata son zamansa a cikin gidan tana ganin ba muharramin mu bane ba zai iya zama a dakin waje ai, kuma yadda yake da kwarjini din nan babu wanda zai kawo mana raini a unguwa. Sadauki yana da gado a gidan da garejin, so it will be a mutual relationship wanda ni nake ganin mu zamu fi benefitting akan sadauki.
Ina ta tunanina har Inna ta shigo tana ta jera mana kayan mu a wardrobe din dakin, Asma'u tana tayata tana kuma mitar cewa wardrobe din tayi mana kadan sai dai mu bar wasu kayan a cikin akwati. Bayan sun gama na tashi na sake goggoge dakin na wanke toilet na jera mana toiletries dinmu da kuma kayan shafe shafen mu, sannan nayo wanka da alwala nazo nayi sallah tare da jera adduoin neman nasara akan Inna in samu ta saurare ni ta kuma yadda da shawara ta.
Da dare sai ga kwanukan abinci nan daga duk matan gidan kowa ta zubo ta aiko mana dashi, Inna ta karba tayi godiya amma daga ni har ita ba wani cin kirki mukayi ba Asma'u ce ta danci da yawa. A lokacin da muke cin abinci ne naga chance dina na magana da ita dan haka na zayyane mata duk tunani na da plans dina na kara da cewa "inna in mukayi hakan kamar mun dogara da kan mu kenan, ba ruwan mu da abinda za'a bamu da abinda ba za'a bamu ba. Duk wanda ya ke ganin zai taimaka mana saboda zumunci sai yaje har gidan mu ya taimaka mana in ma ba'ayi mana ba bamu da damuwa tunda muna da abin hannun mu. Inna dan Allah ki duba maganar nan".
Tunda na fara ta ajiye spoon dinta tana kallona har na gama sannan ta fara girgiza kai tana kallona tace "yayi daidai Diyam, ya kamata a jinjina wa wannan tsarin naki. Amma bara in tambayeki, sanda kike yin wannan tsarin mune a ranki ni da Asma'u ko kuma bakin yaron can? Iye? Wato bakin cikin ki shine mun taho nan gidan an raba ki da shi shine kike so mu koma saboda ku cigaba daga inda kuka tsaya ko? Kuma ke yanzu a tunanin ki duk duniya in rasa wanda zan dauki ragamar rayuwata ni da yayana in bawa sai wannan yaron? Bani da yan uwane? Ko shi mahaifinku bashi da yan uwan da zasu kular masa da sana'arsa su kuma kular masa da iyalinsa? Ai ina sane na karbi shawarar Alhaji Babba ta cewa mu dawo gidan sa mu zauna saboda in raba ki da wannan yaron. Ina so ki saka a ranki cewa Alhaji Babba yayi mana mutunci yayi mana karamci daya dauko mu ya kawo gidan sa cikin iyalinsa saboda baya son mu zauna mu kadai cikin kunci da kewar mahaifinku dan haka daga ni har ku kamata yayi mu gode masa mu kuma yi iyakacin kokarin mu gurin faranta masa. Maganar gareji kuma shi Alhaji Babba da yake da mutum ne mai budadden ido kuma wanda ya san mutane na tabbatar zai san abinda ya dace ayi dashi. Magana ta karshe Diyam, daga yau sai yau, kar ki sake yi min maganar yaron nan".
Bayan na kwanta na jawo bargo na lulluba sai na tambayi kaina ko a ina Sadauki zai kwana? Ko a wanne hali yake ciki? Sai kawai naji baccin ya dauke daga idona baki daya. Babu abinda ba zan iya bayarwa ba a lokacin dan in samu in san halin da yake ciki.
Kwanan mu biyu gidan Alhaji Babba kuma so far bamu da matsala. Muna samun kulawa da sympathy sosai daga jama'ar gidan amma ni a gurina na gaji da "Allah sarki" da "kuyi hakuri kunji" da kullum akeyi mana wanda babu abinda yake rage min a zuciya ta sai ma kara karyar min da ita da yake yi. Sannan kuma ga tunanin Sadauki daya addabi zuciya ya kullum sai karuwa yaje yi har cikin baccina wanda da kyarnake samu nake yi amma mafarkin Sadauki ne, ko inyi mafarkin rayuwar mu a baya ko kuma inyi mafarkinsa wai shi kadai a titi, har ganinsa nake yi a kwance abskin hanya ruwan sama yana dukansa duk kuwa da cewa nasan yaya ladi ba zata rabu dashi a titi ba, akwai makotan mu da akayi zaman mutunci dasu nasan ba zasu barshi a titi ba, akwai kuma marikin Ummah nasan shima ba zai bar Sadauki a titi ba, wannan sai yasa nayi tunanin to in duk wadannan ba zasu barshi a titiba why Inna? Ita me yasa ta barshi a titin ba tare da ko kayan sawa ba, wacce irin zuciyace da ita? Me yayi mata mai zafi haka?
Bayan mun kwana hudu Mama tazo dan ganin yadda mukayi settling down, ta kuma taho mana da yan abubuwan da take ganin zamu bukata. Bayan sun kebe da inna ne take cewa "ni kuwa Adda ina so muyi magana dake a kan yaron nan dan wajen zainabu. Wallahi ranar nan ba karamin tausayi ya bani ba ke kuwa dan Allah ki sauko da zuciyarki akan sa, ji nakeda zainabu kukayi kishin ku kuma zainabu yanzu kasa ta rufe fuskarta haka zalika shima wanda akayi kishin a kansa, shi kuma yaron ina ruwansa?".
Inna ta kuta tace "ni yanzu wani abu kika ga nayi masa, ko kallon banza banyi masa ba ballantana tsawa ko hantara. Abinda nace shine babu ruwa na dashi yayi gabas inyi yamma tunda wanda ya haɗa din ya raba yanzu. Ba shikenan ba." Mama tace "amma at least magana mai dadi ma ai sadaka ce musamman ga maraya, yaron nan bashi da wani gata fa yanzu sai Allah" Inna tace "wai ni Hafsa kin manta da irin wahalar da nasha ne a dalilin uwar yaron nan, kin manta da irin kiyayyar da aka nuna min saboda ba'a aure ta ba? Saboda ita ake so bani ba? Kin manta? Kin manta har sakina akayi a kanta aka kuma dauki yata aka bata. Babu irin kokarin da banyi ba dan in jawo hankalin mijina zuwa gareni amma har ya bar duniya idanunsa ita suke kallo, zuciyarsa baki daya tana gunta duk kuwa da cewa nice uwargidan sa, nice uwar yayansa, ni ce yar uwarsa kuma ni ce wadda ya aura a budurwa ita kuma bazawara. To yanzu sai kiga laifina dan nace bana bukatar duk abinda ya shafe ta? Dan nace bana son ganin abinda zai tuno min da ita?"
Mama tayi ajjiyar zuciya tace "shikenan. Allah ya kara sanyaya miki zuciyarki amma zan sake tuna miki da cewa yaron nan yana da gado a dukiyar da hamma Usuman ya bari, dai dai abinda zaki samu shima haka zai samu shida yaya ladi. Dan Allah Adda a fitar musu da abinsu a basu kinsan shi gado wuta ce, annabi ya fada cewa da mutum yaci gadon maraya gwara ya cika cikinsa da wuta." Inna tace "wannan kuma masu rabon gadon ai sunsan wannan karatun, kuma nasan zasu basu abinsu duk samda aka zo rabawa" Mama tace "yaushe za'a zo rabawar? Ai yanzu ne yake bukatar su, tunda kin ki daukarsa ai kamata yayi a raba gidan a bashi kason uwarsa sai ya fitar da kofa ya zauna a ciki" Inna tace "wai ni Hafsa ki gayamin kina baya na ne ko kina bayan yaron nan ne?" Mama tace "ina bayanki Adda, wannan kuma shi yasa nake gaya miki gaskiya".
A haka mukayi sati biyu a gidan, kallo daya zaka yi min kasan gabaki daya hankali na baya tare dani duk na kara ramewa dama ni ba jiki ba, kullum ina cikin tunanin halin maraicin da muka shiga ciki da kuma tunanin halin da Sadauki yake ciki. Ko wajen gate bani da damar fita saboda kullum ina tare da Inna ko aike na waje ba'ayi saboda akwai yan aiki da masu gadi. Rannan naji Hajiya Yalwati da tazo dakin mu tana cewa "wannan yarinyar kuwa anya ba sai anyi mata rubutu ba? Ita kadai sai inga kamar tana zabura" Inna tace "haka take yi wallahi, ina lura da ita ko baccin kirki bata yi" nan Hajiya Yalwati ta saka ni a gaba da nasiha akan yarda da kaddara mai kyau da marar kyau sannan tace inzo muje dakinta ta bani littafin wasu adduoi da zasu taimaka min. Naje na karba kenan na taho ina hanyar dawowa sai ga Murja da sauri tazo gurina tace "Diyam wai kizo wani yana kiranki a waje" nayi sauri na toshe mata baki muka matsa can gefe na tambayeta waye "to ni ina zan sani, mai gadi ne dai yazo ya a kiranki sai ya ganni ya fada min, wai wannan wanda yake zuwa gurinki sanda kika zo hutu" naji wani adrenaline rush yazo min, nayi kamar zan tafi dakin Inna sai kuma na dawo da baya na zare hijab din jikin Murja na saka nace "Please kar ki gaya wa kowa yanzu zan dawo" sai na wuce da sauri ita kuma ta bini da ido.
Da sauri na nufi inda muke zama in yazo, ji nake kamar inyi tsuntsuwa ko zanfi sauri. Tun daga nesa na hangoshi kuma na gane shi sannan naji dadin ganin sa sosai. He looks good, and that was all that matters to me a lokacin. Ina karasawa na lura da kayan jikinsa sababbi ne kuma masu kyau, he smells good too. Sai dai fuskarsa ce tayi betraying emotions dinsa dan idonsa ya fada ciki sosai kuma zagayen idonsa yayi baki alamun baya samun isashshen bacci. "Sadauki" na kira sunan sa da karyayyiyar murya, bai amsa ba sai murmushi da yayi min mai kokarin boye damuwarsa. Muka karasa zagayawa bayan dakin maigadi, Sadauki ya zauna akan ginin suckaway, wannan ya bani damar ganin gefen kansa inda akayi masa dinki. Na zauna nima a kusa dashi ina fuskantar sa kawai sai hawaye suka fara zarya a kumatu na, bai hanani kuka na ba sai ma ya miko min handkerchief dinsa na cigaba da kuka na, sai dana gama na share hawaye na sannan yace "dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, ke din dama kuka baya miki wahala" nace "Allah yaji kan Baffa da Ummah" yace "ameen. Naje na kai musu ziyara kaburburan su. Suna kwance a sides din juna kuma ina fata da zaton suna aljanna a tare" sai naji dadi sosai a raina, dadin yadda naga ya dauki abin nima sai naji na samu courage din facing rayuwa a koya tazo min. Nace "kai kuma fa? Wanne hali kake ciki? A ina kake a zaune?" Yayi murmushi yace "ina gurin Alhaji Bukar (mutumin da yaya ladi take gurinsa) and they are treating me well, too well even. Ya gaya min cewa zai kaini gurin mahaifina, ya san shi ashe" na bude ido da baki "wow. Congratulations Sadauki, yaushe zaku je?" Ya girgiza kansa yace "I don't know. Ban san shi ba Diyam, bansan waye shi ba and for all I know zata iya yiwuwa ma bai san nayi existing ba, zai iya yayi denying dina yace ni ba dansa bane ba" Nace "amma ta yaya zaka sani in baka je ba? Nasan Sadauki na babu abinda yake tsoro just go kayi clearing doubt dinka and move on" ya gyada kai yana kallona yace "so I have your blessings kenan ko?" Nace "of cause you do".
Sai kuma na tambayeshi abinda yake raina tunda na ganshi "Sadauki me yasa kazo? Bayan abinda Inna ta tayi maka bayan yanzu babu Baffa kuma gashi ka samu wani mai rikon gashi kuma zaka je gurin babanka, me yasa kazo gurina? Ba ka gudun a wulakanta ka?" Ya dan bata rai yana kallona yace "me yasa ba zanzo ba to? For starters I love you, always have and always will. Na biyu duk abinda ya faru dani babu abu daya da yake laifinki dan haka baxanyi fushi dake akan abinda ba ke kika yi min ba. Na uku Baffa, a gurina darajar Baffa ta wuce in yi fushi da iyalinsa dan babu ransa, sannan........" Sai yayi shiru yana kallona, nace "sannan me?" Ya sauke idonsa kasa Yace "sannan lokacin da mukayi accident din, he looked at me straight in the eyes ya ce in wani abin ya same shi in kula daku ke da Asma'u".
Na sunkuyar da kaina inajin sabbin hawaye suna zubo min. Yace "amma bansan ta yadda zan iya kula daku ba Diyam, innar ku bata so na na sani, bansan ta yadda zan iya juyo da hankalinta ta soni ba tunda bansan abinda nayi mata wanda ya saka bata son nawa ba balle in daina. Diyam ina tsoron kar lokacin auren ki yayi in nema a hana ni akan dalilin da ni kaina ban sani ba, I don't think my heart can take that". Mun jima muna hirar yadda future dinmu zata kasance, sai daga baya yace "bara in tafi Diyam kar in jawo miki fada. I just want you to know cewa am okay, dan haka kema ya kamata ki rage wannan koke koken haka ki tsayar da hankalinki guri daya. And everything is going to be alright" nayi murmushi nace "ai na samu strength daga gurinka Sadauki, kayi sharing strength dinka dani" ya mike tsaye yana kallona yace "Aliyu shine sunan, Sadauki shine inkiyar, so ofcause am going to be alright". Muka yi sallama yana yi min alkawarin in sun saka ranar zuwa gurin babansa zai zo ya gaya min saboda inyi masa addu'a.
Shine a gaba ni ina binsa a baya, muna fitowa yayi hanyar gate ni kuma nayi hanyar cikin gida ina waigensa, a lokacin ne kuma aka budewa Alhaji Babba gate ya shigo gidan sukayi clear da Sadauki kafin Sadauki ya fita. Na kara sauri kafin yayi packing Ina jin bugun zuciyata yana karuwa amma ina kama handle din kofa naji muryar Alhaji Babba a baya na yace "Diyam, zo nan"
Not edited. In anga typos ayi hakuri Please.
[1/23, 10:35 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Twenty Four : Red Handed
Na juyo na ganshi a tsaye a gaban motarsa yana kallona, na dawo baya a zuciya ta ina karanto duk addu'ar da tazo bakina na durkusa a gabansa nace "gani Alhaji" ya nuna hanyar gate "waye wancan da na ganku tare?" Nayi shiru kaina a kasa "ya sunkuyo yace "ba'a koya miki in manya suna magana ba'a yin shiru a rabu dasu ba?" Na sake yin shiru ina jin hawaye yana taruwa a idona, ya kama kunnena ya murda, nayi kara na mike tsaye yace "waye wancan nace miki" cikin azaba nace "Sadauki ne" ya sake ni ya kwalla wa maigadi kira, baba audu ya taho dagudu ya durkusa a gabansa yace masa "wanene yace kake barin ƴaƴan iska suna shigo min gida?" Dattijon ya kalle ni sannan yace "bansan baka so ya shigo ba Alhaji, da yake naga duk sanda tazo gidan nan yana zuwa gunta ne na dauka dan uwanku ne" Alhaji Babba yace "babu abinda ya hada mu dashi, daga yau in ka sake barinsa ya shigo gidan nan a bakin aikin ka. Ina fatan ka fahimta" yayi saurin gyada kai "na gane Alhaji, insha Allah hakan ba zai kuma faruwa ba, ayi hakuri Alhaji".
Alhaji Babba ya juyo kaina yace "ke kuma muje gurin Amina ta gaya min idan da saninta kike shigo min da kattin banza cikin gida" na juya da sauri ina tafiya blindly, kafafuwana suna hardewa kamar zan fadi har na shiga dakin Inna na tarar da ita ita kadai da charbi a hannunta tana lazumi, ta dago tana kallona da mamaki "ke kuma lafiya kamar wadda aka koro? Me ya faru" ban bata amsa ba Alhaji Babba ya shigo dakin, ta mike da sauri dan hardly ne ka ganshi ya shigo cikin main gidan saboda part dinsa a waje yake. Yana nuna ni yace "kinsan Sadauki yana zuwa gurinta?" Ta bude baki tana kallona da mamaki sannan ta fara tafa hannu tana salati "Diyam? Yanzu sai da kika jajibo mana yaron nan har gidan nan? Wato duk abinda nake fada ta bayan kunnenki yake bi yake wucewa ko?" Yace "mai gadi yace min dama ya saba zuwa gurinta a duk sanda tazo gidan nan. Wato yar mitsitsiyarta da ita har ta fara jawo mana yaran banza marasa asali da tushe zuwa gida ko?" Inna tace "Alhaji kayi hakuri, anyi an gama insha Allah ba za'a sake ba. Yarinyar nan bata jin magana, babu yadda banyi da ita ba akan yaron nan tun kafin ta kai haka amma taki rabuwa dashi. Yadda kasan yadda Zainabu ta shanye marigayi haka shima yaron nan ya shanye Diyam" Yace "au kice min tafi ƙarfin ki kenan bata jin maganar ki" ya kuma kama kunnena, na saki karar azaba yace "ni in nayi magana ba'a tsallake ta a gidan nan, daga yau sai yau babu ke babu Sadauki" ya sake ni ya juya yana cewa "shi kuma duk sanda ya sake zuwa gidan nan sai ya gane bashi da wayo, sai na rufe shi naga wanda zai fito dashi, sai naga wanda ya tsaya masa a garin nan".
Bayan ya fita Inna ta bini da kallo ina rike da kunnena ina kuka, ta koma ta zauna a bakin gado tana kallona ina jiran ta dora daga inda Alhaji ya tsaya amma sai naji tayi tsaki tace "ba kya jin magana Diyam. Ke indai akan wannan yaron ne ba kyajin magana wallahi" ta dauke kai ta cigaba da jan charbin ta sai kuma tace "zo inga kunnen" na rarrafo nazo gabanta, ta duba kunne na ta shafa min vaseline.
Ranar haka na karasa ta cikin kuncin rai da kunan zuciya tare da fargaba, ni bawai fadan Alhaji Babba ne ya dame ni ba illa furicin da yayi akan sadauki, cewa da yayi zai sa a kama Sadauki duk sanda ya sake zuwa gidan nan, na kuma san alkawarin da Sadauki yayi min cewa zai dawo yayi updating dina akan duk abinda ake ciki dangane da mahaifinsa kuma nasan Sadauki baya karya alkawari idan yayi kuma bana jin zai fara daga yanzu. Option dina daya ne dole in nemi Sadauki in yi warning dinsa kuma in hana shi zuwa duk da cewa hakan yana nufin zamu kara nisanta da juna, amna gwara hakan akan abinda za'ayi masa in yazo din.
Bayan kwana biyu duk na kara diriricewa, ko yaya naji hayaniya a waje sai inji gaba daya hankalina ya tashi inyi tunanin ko Sadauki ne yazo aka kama shi. Rannan dai sai wata dabara ta fado min. Da daddare muna zaune da Inna nace mata "ni kuwa Inna ina so in tambayeki ko muma za'a saka mu a islamiyya ni da Asma'u. Kinga duk ana wuce mu a karatu muna zaune a gida" Inna tace "Wallahi nima zancen islamiyyar nan yana raina tunda muka zo na dauka za'a saka ku amma har yanzu shiru. Amma bari in hafsa tazo sai insa Mukhtar ya kai ku ko kuma in saghir ya zo gari in roke shi ya saka ku" nace "Inna yanzu islamiyya ma sai mun jira wani yazo ya saka mu? In kin yarda kawai in bi su murja in tambayi malaman abinda ake bukata na sabon dauka" ta danyi tunani tace "shikenan, ki bisu din". Ai kuwa na samu chance.
Washegari na shirya na kama hannun Asma'u muka je islamiyya na tambayar mana komai aka yi min bill, kamar yadda nayi tunani sai yasaiyadin yace mu shiga aji mu zauna, dai na tura Asma'u ajin su ni kuma nace zan je in dauko Alqur'ani na daga nan sai na kama hanya. Bani da ko kwandala dan haka na dauki hanya a kafa ina ta zabga sauri kamar zan tashi sama amma a raina sam banga nidan tafiyar ba, nasan gidan Alhaji Bukar inda yaya ladi take anan bayan layin mu yake dan haka nan na dosa, a ringa bi ta lunguna in tsallaka wannan titin in shiga wannan lokon bansan cewa na gaji ba sai da na ganni a kofar gidan, na tsaya a gaban mai gadi ina haki shikuma yana kare min kallo, sai da na gama tsaida numfashi na sannan nace "dan Allah baba Sadauki nake nema. Allah yasa yana nan" ya ajiye radiyon hannunsa yace "dazu ya shiga, bara in dubo miki shi" sai naga ya doshi boys quarters ana jima wa sai gasu sun fito a tare Sadauki ya doso ni da sauri fuskarsa cike da damuwa "Diyam? Lfy? Daga ina kike haka?" Na danyi masa murmushi sai naga yayi ajjiyar zuciya, ya kalle ni yace "kar dai kice min a kafa kika taho" na gyada masa kai sai ya jani zuwa kujerar mai gadi na zauna shi kuma yayi kneeling a gaba na yana mammatsamin kafata yace "me yasa kika taho a kafa Diyam? Ko menene ba zaki bari inzo ba sai ki gaya min? Yanzu da wani abin ya same ki kuma fa?" Nace "You don't understand, gaya maka zanyi kar kazo din ai" sai na bashi labarin abinda Alhaji Babba yace.
Sai naga fuskarsa ta chanja gaba-daya yace "Diyam mai nayi wa mutanen nan ne wai? Su kansu ba zasu taba iya fadar abinda nayi musu ba haka nan kawai suke ji a ransu basa sona" ya dago kai yana kallona yace "Diyam ni nasan ba zasu bani ke ba" nayi saurin girgiza kaina nace "da sauran lokaci ai Sadauki, ka tuno abinda Baffa yace? Sai na gama makaranta na shiga jami'a tukunna? Kafin nan zasu chanja ra'ayinsu zasu fahimci ko kai waye ne. Yanzu ka yarda Alhaji Bukar ya kai ka gurin abbanka tunda wannan zai kara sassauta zuciyarsu tunda suna cewa baka da asali" ya gyada kai yace "you are right. Gobe dama nayi niyyar zanje in gaya miki cewa jibi zamu tafi. Maiduguri yace zamu je" na bude ido ina mamaki, sai kuma na fara sharar hawaye, yace "sarkin kuka, kukan menene kuma kike yi?" Nace "Maiduguri fa da nisa" yace "kuma ce miki akayi a can zanyi ta zama. Nima ai bazan iya zama a can ba zanje in gansu ne kawai in dawo nan ko dan makaranta ta ma" sai kuma ya bani labarin wani abokin Baffa da Baffan ya hada su dan yayi masa hanyar admission, yace "ranan nan bayan nayi welcome back din layina sai ya kirani yayi min gaisuwar Baffa yace min insha Allah wannan admission din dani a ciki. Kinga zan dawo ko dan makaranta ta, besides, ni bazan iya rayuwa nesa dake ba"
Na makale kafada nace "Allah yasa dai kar Borno tayi dadi ka manta da Diyam" yayi murmushi yace "maganar kike so, sau nawa zan gaya miki cewa babu rayuwa a tare da Sadauki in babu Diyam ba. Life without you will not be just unbearable it is unimaginable. I can't imagine me without you". Sai kuma muka shiga hira kamar bamu da wani problem, yana ta tsara min yadda yake yana planning din rayuwar mu tare, hatta fasalin yadda zai gina mana gidan mu a filin da Baffa ya siya masa sai da yayi min. Ga iskar gurin tana yi mana dadi. Jin mu muke a saman gajimare, tamkar together zamu iya facing duk mutanen duniya
Mun jima tare sannan ya duba agogon hannunsa yace "Diyam, tashi maza in raka ki ki hau daidaita ki tafi, ashe lokaci ya tura bamu sani ba". Sai naji kuma kamar bazan iya tafiya ba kamar inyi zamana a gurinsa mu tafi Maidugurin tare amma nasan hakan ba zai yiwu ba, shima ganin yadda na damu sai duk jikinsa yayi sanyi. Ya dauko biro ya kama hannuna ya rubuta min number dinsa yace "ga numberta nan, ba wai rubutawa zakiyi a wani wajen ki boye ba a'a haddacewa zakiyi a kanki, if anything happens kafin in dawo, if you need anything ko menene ki samu aron waya ki kira ni. Kafin ki koma makaranta insha Allah zan dawo. Ki ringa yi mana addu'a" na gyada kai ina karajin jikina yana kara sanyi.
Ya raka ni waje ya tarar min adaidaita ya bashi address ya biya kudin, sai kuma ya tambaye ni in inason kudi. Na girgiza masa kai, kamar ba zai matsa ba yana kallon fuskata sai da mai adaidaitan yayi masa magana tukunna sannan ya ja baya muka tafi. Na waiga ina kallonsa sai yayi murmushi ya daga min hannu.
Daga dan nesa da gidan Alhaji Babba nace a sauke ni, ina sauka na juya da niyyar in karasa sai naji daga bayana ance "Diyam daga ina kike?" Na juya muka hada ido da kawu Isa shida wani mutum suna tafiya a kasa, na durkusa na gaishe su fuskata cike da rashin gaskiya, ya sake maimaita min tambayar, cikin in ina nace "Inna ce ta aike ni gidan Mama" ya gyada kai yace "to ki gaisheta, amma dan sahun ai daya karasa dake ciki" sai nace "zan biya ne ai ta islamiyya in tafi da Asma'u".
Nayi sa'a ina zuwa gida na tarar an taso yan makaranta na shiga cikin su muka shiga cikin gida. Bana jin dadi kuma bana so Inna ta gane dan haka nace da Asma'u ta tafi ta gaya mata mun dawo ni kuma na bi Murja muka tafi part din Hajiya Yalwati. Muna zuwa na kwanta a kujera ina jin kamar zanyi zazzaɓi, Hajiya Yalwati ta tambayeni "lafiya?" Sai na gyada mata kai inajin kamar zanyi kuka, sai kawai ta rabu dani tana tunanin ko Baffa na tuno.
Kwana biyu bayan nan, ranar da nake lissafin su sadauki sun tafi Maiduguri, mun fito zamu tafi islamiyya sai muka tarar da Alhaji Babba, kawu Isa, Inna da Hajiya Babba suna zaune a babban palo da alama magana mai muhimmanci suke yi. Muka gaishe su har zamu wuce sai ji nayi kawu Isa yace "Amina ki daina aiken Diyam ita kadai gwara kiyi wa Hafsan waya ta bawa Mukhtar ko menene ya kawo miki" na kara sauri kamar zan tashi sama, na kusa gate kenan naji an kwalla min kira, na runtse idona na kasa motsi, "Diyam ki zo ana kiranki" murja ta dafa ni tace "number dinki ta fito, good luck, ni nayi gaba"
[1/24, 9:57 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episodes Twenty Five : A Day To Remember
Na juya ina kallon kofar palon amma na kasa motsa kafata ballantana in tafi, Inna na gami ta budo kofa a zuciye tana kallona "ba kiranki ake yi ba?" Na taho a hankali ko wacce gaba ta jikina tana rawa, ina shiga Inna ta tunkuda keyata na durkusge a tsakiyar palon kaina a kasa. Kawu Isa yace "Diyam, shekaran jiya da na ganki kin fito daga adaidaita sahu daga ina kike?" Ban amsa ba kuma ban dago ba, Alhaji Babba yace "idan anayi miki magana kina yin banza da mutane sai na kakkarya ki anan gurin, ba zaki ansa ba" na fara rera kuka "dan Allah kuyi hakuri kar ku dake ni, dan Allah" Kawu Isa yace "ba zamu dake ki ba indai kika gaya mana gaskiya. Ina kika je ranar nan?" na cigaba da kuka na "wallahi Kawu na daina bazan sake fita ba". Na dago kai muka hada ido da Inna ta rafka tahumi tana kallona, nayi sauri na sunkuyar da kaina, tace "ba zata fadi inda taje ba fa, amma ni nasan inda taje, ba zai wuce gurin wannan bakin mayen ba" ta juya tana kallon Alhaji Babba tace "rannan ba kace in ya sake zuwa gidan nan sai ka kama shi ba? To shine ita ta tafi gurinsa tunda shi an hana shi zuwa. Wato dalilin da yasa kika nace sai na saka ku islamiyya kenan ko?" Na girgiza kaina da sauri "wallahi Inna ba haka bane ba, ranar nan ne kawai naje kuma bazan sake zuwa ba" Kawu Isa yace "to me kika je yi ranar? Me ya kaiki gurinsa?" Ina sheshsheka ina kuma wasa da fingers dina nace "ce masa nayi kar ya kuma zuwa gidan nan" Alhaji yace "au saboda nace zan saka a kama shi shine kika je kika gaya masa ko? To in nayi niyyar rufe sadauki kaf garin nan akwai wanda ya isa ya hana ni ne? Yanzun ma kuma zan tura har gidan da yake takama dasu din insa akama shi a dan lallasa min shi yadda nan gaba ko kince masa zaki je shi da kansa zai hana ki" Kawu Isa yace "tashi ki tafi" nayi sauri na mike nayi hanyar waje sai Alhaji Babba ya ce "kar ki fita daga gidan nan. Kin gama zuwa islamiyya ai. Zo ki wuce ciki" na juya na bi inda yake nuna min, muka hada ido da Hajiya Babba wadda tun da aka fara maganar bata ce komai ba tana dai bina da kallo kawai.
Kitchen din gidan na shiga, na rakube a jikin kofa na cusa kaina a tsakanin cinyoyi na, me yasa ni bani da sa'a ne? Me yasa duk sanda nayi wani abu sai an kama ni? Karya sam bata karbe ni ba? Sai kuma na kama addu'ar Allah yasa Sadauki ya tafi dan kar Alhaji Babba ya aikata abinda yace.
A palo bayan na tashi inna tace "na rasa yadda zanyi in raba yarinyar nan da wannan nataccen yaron wallahi. Nayi nayi, Allah ma ta gani nayi iya kokarina amma abin ya faskara, ni farko na dauka soyayyar yarinta suke yi, na dauka in suka fara hankali zasu saki hannun juna amma kamar kara tunzura su ake yi" Alhaji Babba yace "wai soyayya suke yi?. Diyam din yanzu harta isa yin saurayi? Shekarar ta nawa?" Inna tace "sha hudu zata yi nan da wata daya" ya gyada kai yace "ta isa kam. Matanen mu na ruga basu kaita ba ma ake musu aure. Kuma wannan tunda har tasan a raba ta da saurayi ita kuma ta dauki hanya ta bishi to lallai ita ma ta isa auren" inna tayi ƙoƙarin kare ni "ya shanye tane fa, babu maganar wanda Diyam takeji sai tasa" Alhaji Babba yace "anyi daya ai, ba za'a sake biyu ba, mu ba zamu kuma hada jinin mu da mayu ba, yadda bakin cikin Manu ya kashe Inno ba zamu bar bakin cikin Diyam ya kashe Hardo ba dan haka kija mata kunne. Babu ita babu shi, in taki kuma duk abinda ya biyo baya ita ta jawo wa kanta".
Shikenan kamar magana ta wuce, zuwa washegari na shiga harkokina sosai kamar babu abinda ya faru amma cikin raina kuma cikin sallolina ina yiwa Sadauki addu'ar samun nasara, sai inke tambayar kaina ko ya samu mahaifin nasa? Ko wacce irin karba a samu daga danginsa? Hankalina rabi yana tare dani rabi kuma yana gurin Sadauki har ya kwana uku da tafiya. A ranar da daddare aka aiko Alhaji Babba yana kiran Inna, ta dauki hijab dinta ta fita shiru shiru har na gaji da jiranta mukayi shirin bacci ni da Asma'u muka kwanta, amma sai na kasa baccin kuma nayi ta juyi ina jin wata irin muguwar faduwar gaba. Na rasa me yake yi min dadi kawai na tashi na zauna na rafka tagumi sannan sai gata ta shigo, sai kawai naga idonta kamar wadda tayi kuka amma sai ta maze tace "ke kuma me kike yi har yanzu bakiyi bacci ba?" Nace "bana jin dadi ne kawai Inna. Baffa nake tunowa" sai kuma na fara matsar kwalla, ta dauke kai tace in an tuno mamaci addu'a akeyi masa ba kuka ba" sai ta wuce can karshen gado ta zauna ta jingina kanta da jikin gadon, naso in tambayeta in wani abun yana damunta amma nasan ba lallai ta bani amsa ba dan haka sai nayi shiru na koma na kwanta ina kalllon ceiling, mun jima a haka sannan tace min "Diyam Baffanku ya mutu ya huta, mu da muke duniyar mu mune cikin wahalarta" na runtse idona ina tunanin ma'anar maganar ta ta.
Washegari bayan na tashi da assuba nayi sallah sai na koma baccin safe, cikin bacci na kawai naji muryar mama a dakin na farka ina mamakin me take yi a gidan da sassafe? Sai naji Inna tana cewa "ni wallahi Hafsa kinfi kowa sani, bana son yaron nan sam zuciya ta bata sonsa ballantana har inyi sha'awar ya zama surukina amma duk da haka saghir fa...." Sai kuma suka ga ina kokarin mikewa sukayi shiru. Na tashi na gaishe da Mama, sai naga fuskar Inna still akwai bacin rai idonta kamar batayi bacci sosai ba, sai kawai naji ina son inji maganar da suke yi. Sai na bude toilet na shiga na rufe na kunna pampo kamar zanyi wani abu amma sai na dawo na sakakunne na a jikin keyhole.
Sai naji Mama tana cewa "wannan gajeriyar matar tasa ce zata kissima masa, shi kuma ya hau ya zauna saboda son kansa, amma suma kansu sunsan ai Diyam ba sa'ar auren Saghir ba ce ba, ya ninka ta a shekaru fa, gashi da budadden ido ita kuma fa? Yarinyar da junior waec kawai ta rubuta? Akwai cutuwa sosai a hadin su" Inna tace "babu fa abinda ban gaya masa ba jiyan, sai yaji haushina ma wai ina so in nuna ni na haifi Diyam basu ba, wai ita suke wa gata, wai baza ta taba samun miji irinsa ba, wai gata suke yi mata albarkacin zumunci albarkacin maraicinta" ta danyi tsaki tace "ni da ace Diyam ta fi haka girma ne, da ace misali ta gama makaranta ne wallahi da bani da dumuwa. Ni yanzu abinda nake so kice masa idan kinje shine, ki roke shi a bar yaran su daidaita kafin ta gama makaranta".
Na sulale ma zauna a kasa a jikin kofar. Naji dai suna maganar aure, kuma naji sun ambaci sunana sun kuma ambaci sunan Saghir. To tambaya ta anan itace auren wa za'ayi? Aurena za'ayi ko auren saghir za'ayi? Dan kaina ba zai iya daukan aurena da saghir a sentence daya ba ballantana ƙwaƙwalwa ta ta fahimci cewa aure za'a hada ni da saghir. Na wanke fuskata nayi brush na fito ina murmushin yake, suma duk yaken sukayi min har na zauna na fara breakfast sai na lura duk sun zuba min ido suna kallona. Sai na samu kaina da tattauna abincin amma makogwarona yakasa budewa ballantana in iya hadiyewa.
Muna nan zaune babu mai magana sai ga aike aba kiran Mama inji Alhaji Babba, ta tashi ta tafi muka cigaba da zama ni da Inna sai ga wani aiken wai inna taje itama, tana tafiya na rufe abincin gabana na tashi na kwanta a kan gado trying hard not to think, trying hard not to let my brain assess maganar da naji su Inna suna yi. Ba zan iya tuna adadin mintina ko awannin da suka wuce ba sai ga yarinya an aiko wai inzo inji ana kira na a palon Alhaji, na tashi na saka hijab dina still trying not yo think na fara tafiya blindly zuwa part din Alhaji Babba.
Na murda kofar na shiga da sallama. Duk suka dago kai suna kallona kamar yadda nima nake bin su da kallo. Alhaji Babba, Hajiya Babba, Inna, Kawu Isa da kuma Mama. Na durkusa na gaishe su da muryar da a kunnena naji kamar ba tawa ba. Suka amsa sannan duk suka zuba min ido suna kallona. Alhaji Babba ne yayi magana "Diyam a matsayin mu na iyayenki wadanda baki da wadanda suka fimu kaf duniyar nan mun yanke shawara a kanki. Zamu hada auren zumunci tsakanin ki da yayanki Saghir".
"Dama an jima da bani shawarar cewa babban abinda zai saka Saghir ya zauna a guri daya ya nutsu shine in na samu kyakykyawar yarinya na aura masa, tun a lokacin Diyam ce ta fado min a raina na kuma kuduri aniyar hada su aure in ta isa auren, to kuma yanzu ganin har ta fara iya bin saurayi zuwa gidansu na fahimci ta isa auren a yanzu, dan haka za'ayi yanzu. Diyam zaki cigaba da karatu kamar yadda mahaifiyar ki ta bukata, amma ba zaki koma makarantar kwana ba, za'a saka ki a day ki karasa secondary, in kin gama in mijinki ya yarda sai ki cigaba in bai yarda ba kuma shikenan. Bamu saka rana ba tukunna, na kira shi Saghir din nace masa lallai ya hawo jirgi yazo ya gobe ina nemansa, in yazo sai muji tsare tsarensa sai mu samu saka lokacin. Shikenan abinda zan ce miki Diyam, tashi ki tafi".
Na tashi kamar yadda yace, amma sai kafafuwana suka lankwashe na fadi a gurin, Inna da Mama suka yo kaina a tare amma kafin su karaso na sake mikewa na kama hanyar na fice. Bansan ya akayi nazo ba kawai sai gani na nayi a dakin inna, na durkusa a gaban gado gabaki dayan jikina yana karkarwa kamar ana kada mazari amma idona babu hawaye, lallai wani tashin hankalin yaji gaban kuka. Baffa naji ya fado min arai, na tuna maganar sa sanda yake mana fada ni da sadauki "waye kuke tunanin zaiyi muku aure yanzu? Ba dai ni babanku ba" ashe haka maraici yake? Ashe haka rashin gata yake?
A gefe na naga handbag din Mama, na dauka da sauri na bincike da dauko wayarta, babu tsoro ko kadan a raina nayi dialing number din da Sadauki ya bani.
Ring biyu ya dauka, muryarsa as clear as yana gabana a tsaye wannan yasa na samu relief na san at least lafiyar sa kalau. Yayi sallama amma ni sai na kasa magana saboda karkarwar da baki na yake yi, sai kuma kuka ya kwace min. Na fara rera wa ba kakkautawa nan take ya rikice "Diyam?? Ya Salam Diyam kiyi min magana menene? Me ya faru Diyam? Please talk to me" shima kamar zaiyi kukan, na tsagaita nace "Sadauki ka taimaka min, Sadauki aure za'ayi min wai" yayi shiru kamar baiji ba sannan yace "what?!!!" Nace "yanzu suka kira ni suka gaya min, aure zasu yi min Sadauki, wai hamma Saghir zasu aura min" yace da sauri "su? Su waye su? Diyam kar kiyi min wannan wasan bana so" na lissafa masa duk wadanda suke gurin sanda akayi maganar nace "da gaske suke Sadauki, wallahi da gaske suke, Sadauki mutuwa zanyi ka taimaka min". Yace cikin muryar da ban taba jin yayi magana da irinta ba "Diyam listen to me, zan ajiye duk abinda nake yi zan taho kano gobe and I promise you I will not let anything bad happens to you".
Kofa ta bude inna da Mama suka shigo fuskarsu babu yabo babu fallasa, sai kuma suka tsaya suna kallona da waya a hannu ina kuka. Na sauke wayar daga kunne na ina ji a raina bana jin wani tsoro kuma, wanne punishment za'a yi min wanda yafi wannan da aka riga akayi min?
[1/25, 11:53 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Twenty Six : Forever and Ever
Alherin Allah ya kai gun masoya na a duk inda kuke. Ina gani, ina karantawa kuma ina godiya da duk comments dinku, it kept me going.
This page is dedicated to duk wadda za'ayiwa ko kuma aka taba yiwa auren dole.
This page is dedicated to duk saurayin da aka raba shi da budurwarsa ba tare da wani cikakken dalili ba.
This page is dedicated to duk iyayen da suke da ra'ayin yiwa yayansu auren dole. Ina fatan wannan labarin zai saka ku chanza ra'ayin ku.
Ku fahimce ni sosai, auren dole nake nufi bawai auren haɗi ba, akwai banbanci tsakanin arranged marriage da kuma forced marriage.
Mama ta shigo ta karbi wayar daga hannuna tayi cutting kiran. Bata ce min komai ba ta saka wayar a jakarta ta harhada sauran kayanta ta rataya jakarta. Inna tace "ba dai tafiya zaki yi ba" Mama tace "tafiya zanyi, ni ba zan iya kallon wannan kayan takaicin ba, Allah ya bamu alkhairi". Ta juya da sauri ta bar dakin. Inna tayi ajjiyar zuciya dan ta fahimci Mama fushi tayi akan magana ta, tazo ta zauna a bakin gado daga gefena tace "shi kika kira ko? Diyam taurin kanki ne yake jawo miki koma menene akeyi miki. Ke ba kya jin magana ta, da ace tun farko da na hanaki kulashi kin daina ai da bata kai ga haka ba" tayi shiru tana sauraron kuka na, sannan tayi tsaki tace "nima zuciyata ba son hadin nan naki da saghir tace ba kawai dai dan babu yadda zanyi ne, ba wai saghir din ne bana so ba a'a auren ki ne yanzu bana so, duk da dai kamar yadda Alhaji ya fada ana yiwa wadanda basu kaiki bana aure kuma su zauna amma nasan da babanki yana nan da bazai miki aure yanzu ba. To ni wannan shine damuwata. Amma in kika duba ta wani bangaren fa zaki ga gata akayi miki, Saghir yafi wancan yaron da kike ta naci komai, yafishi kudi ya fishi kyau ya fishi asali ya fishi shekaru ya fishi hankali ya fishi wayewa sannan uwa uba gashi dan uwanki. To me kike nema kuma bayan duk wannan" a hankali cikin dasashshiyar murya nace mata "bana son shi Inna. Bana son Saghir Sadauki nake so, bana son aure yanzu karatu nake so. Inna ki taimaka min kar kuyi min auren dole" sai na dora kaina akan cinyarta na cigaba da rera kuka, ta dora hannunta a kaina tana shafawa, a hankali tace "gata akeyi miki Diyam, yanzu ba zaki gane ba sai nan gaba".
Kafin azahar zazzaɓi mai zafi ya rufe ni, ko palo ban kuma lekawa ba ina kwance daki a kudundune ina karkarwa. Ina jin yan gidan suna ta zuwa dubani kuma nasan da yawa daga cikinsu tsegumi ne yake kawo su. Ina jin Hajiya Yalwati ta shigo itama suna ta magana da Inna "amma dai Amina in kika yarda da wannan hadin kun zalinci yarinyar nan wallahi. Saghir in ana so ya shiryu ai gagarumar mace wadda taga jiya taga yau za'a samo a hada shi da ita ba yar mitsitsiyar Diyam din nan ba, ya zata yi dashi?" Inna tace "to wai Yalwati ya kuke so inyi ne da raina ne? Nima fa ba son abin nan nake yi ba amma ya zanyi? Yanzu zan iya cewa da Alhaji Babba ba zai aurawa Diyam Saghir ba? Duk duniya tana da wadanda suka fisu ne ko kuma ni duk duniya ina da wadanda suka fisu ne? Hakuri kawai zatayi nima kuma inyi hakurin sai mu hadu muyi tayi musu addu'a. Duk wannan koke koken nata daga anyi auren fa shikenan. Yara nawa ne akayi musu auren irin haka kuma gasu nan har sun hayayyafa sunyi zaman su" Hajiya Yalwati tace "to ba dole suyi zamansu ba tunda sun hayayyafa? Amma kije ki tambayesu kiji idan har yau abin baya musu ciwo a ransu. Kije ki tambayesu kiji irin wahalar da suka sha kafin su hakura din. To wannan fa wai ina yi miki magana ne akan in mace bata son miji aka aura mata shi to ina ga in shi din ma baya sonta? Kar ki manta Saghir fa bashi yace yana son Diyam ba. Kinsan kuwa ciwon auren wanda baya sonka? Kinsan kuwa irin bakin cikin da zai ta kunsa maka?"
Inna ta dauke kanta gefe tana jin kamar bakar magana ce Hajiya Yalwati take gaya mata. Ita kuwa ita tasan bakin cikin auren wanda baya sonka don har yau tana iya tuno farkon aurenta da Baffa ko kallo bata ishe shi ba, sai gabanta ya fadi data tuno Saghir, idan har Baffa daya tashi ya kuma yi karatu a kauye yayi mata wulakanci saboda baya sonta to ina kuma ga Saghir din da ya gama bude idonsa a kasashen turawa?
Da yamma Aunty Fatima autar su Baffa tazo, ita ta tashe ni zaune tana taba jikina tace "Amina anya kuwa wannan yarinyar ba za'a kaita asibiti ba, jikin ta yayi zafi da yawa fa?" Hmmm shine kawai abinda inna tace tana jan charbi, Aunty Fatima ta bani magani na sha na koma na kwanta tana cewa "wallahi baki ji irin dadin da naji ba dazu da Alhaji Babba ya kira ni take gaya min wannan labarin, kai amma Allah ya sanya alkhairi shi kenan munyi abinmu tuwo na maina. Dama tunda Hamma Manu ya rasu yaran nan Diyam da Asma'u suke raina ina ta tunanin su kinga yanzu shikenan, in akayi auren dai ta dauki kanwarta suje can suyi zamansu kema kin huta, duk inda zai tafi yawon nasa ba sai ya saka matarsa a gaba su tafi tare ba? Itama ma a hakan zata waye din ai" a raina nace kaji wata kuma, ita wayewa ce damuwarta.
Washegari da safe jikina ya danyi sauki sai wani matsanancin ciwon kai da nake ji. Inna ta saka na tashi da kyar ina shan kunun gyadar da Hajiya Babba ta aiko min dashi wai taji ance naki cin abinci. Ina cikin sha aka budo kofar dakin kamar za'a balla ta, duk muka tsorata muka daga kai sai idona ya sauka akan Hamma Saghir da yake haki kamar wanda yayi tseren gudu, Inna tana yake tace "a'a Saghir saukar yaushe?" Ya dauke idonshi daga kanta ba tare daya amsa mata ba ya kalle ni cikin ido yace "dan ubanki, tun wuri kije ki gaya musu cewa ba kya sona tun kafin a makala min ke ki zokina nadama" ban dauke idona daga kansa ba har ya juya ya fice ya bar mana kofa a bude, na sauke kaina kasa na ajiye kunun hannuna, ina jin Inna ta tashi da sauri ta fita tana salati. A hankali naji wata irin tsana, tsanar da ban taba tunanin it is possible ba tana shiga zuciyata a game da Saghir, abinda ya fada bashi yafi bata min raiba akan ambaton ubana da yayi.
Na jawo pillow na kwanta sama sama ina jiyo hayaniya a palo, naji Inna tana tsara musu abinda Saghir yace, muryarta har kakkaryewa takeyi kamar zata yi kuka, sai kuma naji Alhaji Babba yana magana shima amma bana fahimtar me yake cewa sai can naji yace "kai ka haife mu ko mu muka haife ka? To sai an aura maka ita din in yaso in an kaita gidan naka ka kasheta kakawo mana gawarta".
Na runtse idona na jawo wani pillown na dora a kaina na toshe kunnuwana.
Da yamma Mama ta sake dawowa gidan. Inna ta tsara mata abinda dazu ya faru da Saghir. Mama tace "to dama ni abinda ya kawo ni shine in gaya miki in anjima Sadauki zai zo, ya sake kiran layi na yace min zasu zo shida dan uwan mahaifinsa da kuma Alhaji Bukar na garin nan. Abinda nake so ince miki shine dan Allah idan sunzo kema ki fito ki nuna cewa ba kya son hadin Diyam da Saghir, ki karbi Sadauki sau daya dai a rayuwarki ko dan yarki" Inna ta fara girgiza kai "na gaya miki Hafsa, kin sani kuma bana son yaron nan bana kaunarsa" Mama ta fara daukan zafi "Yanzu kinfi son ki hada Diyam da mutumin daya kalli cikin idonki ya gaya miki baya kaunar yarki akan wanda yake binki kamar zai lashi takalmin ki saboda ki bashi yarki? Wacce irin zuciya ce dake Adda?" Amma inna sai ta cigaba da girgiza kanta kawai.
Ni kuma jin maganar Mama sai naji hankalina gaba-daya ya koma kan Sadauki. Sadauki zaizo da gaske? Kuma tare da dan uwan babansa? Kenan ya ga babansa da gaske. Amma kuma har zuciya ta ina tsoron yadda zata kasance tsakanin su da Alhaji Babba.
Muna nan zaune kuwa sai ga kira a wayar Mama, ta amsa sai ta tashi tana saka hijab dinta tace "sun zo, bara inje" amma inna bata motsa ba, ni dai ina zaune ina jin jira, irin jiran da akuya take yi lokacin da aka kaita mayanka. Har wani daci daci nake ji a bakina.
Abinda ya faru a waje kuma shine; Mama ce da kanta ta shigo da Sadauki tare da wani mutum da zuka zo tare daga Maiduguri. Babban mutum ne sosai kuma kana ganinsa kaga babarbare harda tsagun su a fuskarsa. Sai kuma Alhaji Bukar wanda shine asalin wanda ya aurar da Zainabu. Suka shigo tayi musu iso har palon Alhaji Babba ba tare dashi Alhaji Babban yasan ko su waye ba ballantana abinda yake tafe dasu. Sai da yaga Sadauki sannan balli ya fara tashi yace a fitar masa dashi daga gidan sa. Mama ta roka dan Allah a tsaya a saurare su tunda dai suka taho kafa da kafa tun daga Maiduguri ai sun chanchanci a saurare su. Mutumin da hausa bata ishe shi sosai ba sai yana hadawa da turanci ya fara bayanin cewa mahaifin Sadauki ne ya turo shi yayi representing dinsa saboda shi baya kusa, gurin nemawa Sadauki auren Diyam kamar yadda shi Sadaukin ya nema. Nan take Alhaji Babba ya basu short ansa da cewa "ba za'a bashi dinba, kuma Diyam mun riga munyi mata miji. Na gama baku amsa ku tashi ku bar min gidana tun kafin in kira muku yan sanda" Alhaji Bukar yace "shikenan dai? Shikenan maganar 'yan sanda dai?" Alhaji Babba yace "ai gida na kuka shigo, dan haka duk abinda nace kunyi min ya zauna kenan" Alhaji Bukar yace "ai kai abinda baka sani ba shine, in kai baka rufe mu ba mu sai mu tufe ka kuma muga wanda zai tsaya maka ya fito da kai" Alhaji Babba yace "anji din, aure dai ba za'a bayar ba in kaji haushi kamar yadda kayiwa zainabu aure dan munki yarda Manu ya aureta to shima Sadauki ka daura masa aure gobe mu gani" Alhaji Bukar yace "tabbas nayi wa zainabu aure, aure kuma wanda manu baiyi irinsa ba, amma kuma da amincewar ta ba wai tilasta mata nayi ba kamar yadda kake da niyyar tilastawa marainiyar Allah ta auri lalataccen danka. Wallahi indai kayi mata wannan auren sai Allah ya kamaka da hakkinta tun a duniya ba sai kunje lahira ba". Ya mike tare da dayan mutumin daya ke ta mamaki yana tambayarsa dama haka mutanen suke? Anan kuma Aliyu ya girma?
Amma Sadauki sai yaki tashi daga inda yake a durkushe. Sai ya rarrafa gaban Alhaji Babba yace "Alhaji dan Allah, nasan nine ba kwaso na yarda kuma ba zaku aura min Diyam ba amma dan Allah, dan Allah Alhaji kar kuyi mata aure, in dai saboda nine to na hakura na janye neman aurenta please ku barta tayi karatunta, ku barta ta girma ta zabi wani da kanta" Alhaji Babba ya dauke kansa, Sadauki ya sake cewa "in kuma lallai sai kunyi mata aure please not Saghir, ga Mukhtar nan" ya fada yana nuna Mama, "ku aura mata Mukhtar indai har sai kunyi mata auren yanzu but please banda Saghir".
Alhaji Babba ya mike "kai a matsayin ka na waye zaka gaya mana wanda zamu aura mata da wanda ba zamu aura mata ba? To albishirin ka, Saghir din zamu aura mata kuma rana ita yau za'a daura auren idan kaji haushi kaje ka fada rijiya ka mutu".
Ina daki a kwance, na bude idona a hankali ina kallon dakin na lura Inna bata nan. Sai na tashi zaune haka kawai naji ina son in fita waje. Na fito palo sai naga Inna da amaryar Alhaji Babba a can gefe suna magana kasa kasa amma basu ganni ba, sai na wuce su na bude kofar palon na fita waje ina karewa compound din kallo, haka kawai naji zuciyata tana gaya min in tsaya anan wajen. Ban jima ba kuwa sai na hango su sun fito daga part din Alhaji Babba su hudu, manyan maza guda biyu da Mama sai kuma mutumin da ko cikin duhu na hango shi zan gane shi. Sadauki. Su biyun sauri suke yi shi kuma a hankali yake tafiya yana ta waige waige, sai kawai na sati handle din kofar na fita da gudu na tafi inda yake, tun daga nesa ya hango ni sai ya juyo ya bude min hannayensa ni kuma na wuce direct zuwa kirjinsa ya mayar da hannayen ya rufe. Na fashe da kuka ina kankame shi.
A hankali yace "shshshsh, ya isa haka kukan, stop crying please. Wai litre hawaye nawa zaki zubar ne a cikin wata daya?" Sama sama naki hayaniya a compound din amma sai nake ji kamar wani background noice ne akan maganar da Sadauki yake gaya min. "Be strong Diyam, you are stronger than this. Ki zama jaruma ki bude hannayenki ki karbi duk wata kaddara da Allah zai dora miki ki dauke ta a matsayin jarabawa, ki dauka cewa Allah yana jaraba ki ne dan yaga how strong are you for the blessings He plans a head for you. Ki sani cewa Allah yana tare dake a ko da yaushe, kuma ki saka a ranki cewa ni Sadauki zan kasance tare da ke a koda yaushe, this is my promise to you, I will be with you forever and ever, I will love you forever and ever. Always ki saka a ranki cewa an angle is watching over you. Always. No matter what happens and no matter how long"
Hayaniya ake yi sosai yayinda ni kuma nayi luf a kirjinsa ina jin kamar anan aka halicceni, ina jin muryar Inna "ba zaka shika ta ba? Maye" Alhaji Babba "kuyi ta dukansa har sai ya sakar mana 'yarmu" dan uwan baban Sadauki "kar wanda ya taba shi, wallahi duk wanda ya taba shi sai yayi nadama".
Lokaci daya kuma sai Sadauki ya sake ni, ya rike fuskata yana kallona idonsa cike da wani yanayin da ban taba gani ba and then without another word ya kama hanyar waje da sauri, ina jin Alhaji Babba yana bawa yaran gidan umarnin su dake shi amma sai naga kawai kaucewa suke suna bashi guri har ya fita. Ni nasan a wannan yanayin da yake ciki da wani ya taba shi da tabbas in bai kaishi lahira ba to kuwa zai kaishi asibiti.
Yana fita daga gidan naji wani nauyi a zuciyata, wani duhu ya mamaye idanuwana, sai kuma kafafuwana suka lankwashe na zube a gurin unconscious.
Hope ba kuyi kuka sosai ba. Lol.
Love you all.
Chears[1/27, 9:17 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Twenty Seven : Acceptance
Na bude idona a hankali ina kallon ceiling kamar mai son fahimtar yadda aka tsara shi. Kaina yayi min nauyi haka kirjina. Sheshshekar kukan da naji a kusa dani ce ta sakani waigawa ina kallon mai kukan, Asma'u, tayi sharkaf da hawaye da majina da gumi sai kukanta take yi bil hakki. Na tashi hannuna dafe da kaina nace "Asma'u?" Sai ta juyo da sauri ta rungume ni "Adda dan Allah kema karki mutu ki barni" na rungume ta ina dan jijjiga ta nace "bazan mutu ba kinji, ina nan tare dake" sai ta daho kai tana kallona tace "Adda wai Sadauki ya tafi da gaske? Inna tace wai ya tafi kuma ba zai kuma dawowa ba" naji gaba-daya abinda ya faru yana dawomin kaina kamar film, wani kuka ya taho min amma sai na rike shi a nace mata "zai dawo kinji Yar Asama (sunan da yake tsokanar ta dashi) zai dawo wata rana".
Na gyara mata kwanciyar ta a jikina naja bargo na lullube mu tare, sai kuma na fara bitar abubuwan da suka wakana, na hango fuskar Sadauki a idona da irin bacin ran dana gani a idonsa, na tuno kalaman daya gayamin a kunnena. "Be strong" he said, but how can I be strong without him bayan shi din shine strength dina? Yace in bude hannayena in karbi duk wani abin da ya tunkaro ni but how can I do that bayan ya sabar min da kasance wa shield dina? Shi yake tsayawa a gabana ya kare ni daga duk wanda yayi niyyar zalintata, shi ya shagwaba ni inyi duk abinda nake so saboda ina takama ina da Sadauki. Yanzu banj da Sadauki kuma. I felt so exposed. So alone. So scared. Ji naui kamar duk mutanen duniya ne suka hada kansu suke nema su zalince ni. Suddenly sai naji duk duniyar ta ishe ni, to menene amfanin zama a cikinta? Me zan tsinta a cikin rayuwar indai har aka aura min wanda bana so aka ce in cigaba da zama dashi har karshen rayuwata? Sai naji feeling irin feeling din da yammatan da suke kashe kansu saboda auren dole suka ji kafin su kashe kan nasu. Sai naji feeling irin feeling din da yammatan da suke guduwa daga gaban iyayensu suke shiga duniya suke ji kafin su gudu din, ashe dai laifin su kadan ne, ashe dai tura su akayi zuwa limit din da shaidan ya kada musu gansar sa su kuma suka bishi.
Sai dare sannan na tashi na hada sallar magrib da isha saboda wani irin zazzaɓi da ciwon kai da nake yi. Ƙwaƙwalwa ta ta zama blank kamar babu komai a cikinta saboda na rasa wanne tunanin zanyi. Ni dai bana so in shiga duniya saboda I might end up never seeing Sadauki again tunda bansan inda zan same shi ba. Ba kuma naso in kashe kaina saboda nasan wuta zan tafi. Bani kuma da wanda zan kai kara gurinsa saboda su masu shirin yi min auren nan su ne dangin uwata kuma sune dangin ubana, dan Alhaji Babba a lokacin zan iya cewa shi yake juya kowa a family, saboda shi yake da naira. Sai na dora goshina a kasa na fara gayawa Allah, ina rokon sa ya sakamin ga duk wanda ya zalince ni, ina rokonsa kuma ya bani karfi da juriyar daukan duk wata kaddara daya rubuta min.
A kan sallayar na kwanta na lulluba da hijab dina, ina jin Inna ta shigo ta taba wuya na sai kuma ta fita, sai gasu sun dawo da Hajiya Yalwati da Murja, ina jin su suka kamani suka saka ni a mota sannan naji muna tafiya, na dago kai na kalli Hajiya yalwati data rungume ni a cinyar ta nace "Hajiya, dan Allah bana son auren hamma Saghir". A asibitin muna zuwa suka bamu gado, sunce temperature ta tayi sama da yawa dan haka sai na kwana a gurinsu for monitoring, suka yi min allurai ciki har dana bacci dan haka na samu nayi bacci amma cike da mafarkai. Cikin mafarkan da nayi harda wanda na ganni na soka wa hamma Saghir wuka a ciki.
Washegari aka sallamo ni tare da warning cewa jini na yana neman hawa, as young as I was. Muna dawowa gida Hajiya Yalwati ta zauna tana jera wa Inna bayanin likita Inna ta fara sharar hawaye tana cewa "ni in kuna wannan maganar sai inga kamar kuna dora min laifi ne, ni ya kuke so inyi ne wai? Ta yaya kuke tunanin zan je gurin Alhaji Babba in ce masa ba zai aurawa Saghir Diyam ba? Ta yaya? Ga Hafsa ma tayi fushi dani tunda ta tafi jiya har yau taki daukan wayata" Hajiya Yalwati tace "kamar yadda shi da matarsa suka so kansu suke neman hada Diyam da tantirin dansu kema haka zaki so taki yar kice ba za'ayi ba" Inna tace "yanzu zumunci har ya kai haka lalacewa? To ku ku gaya masa mana? Ku gaya masa Diyam tace bata so gashi har tana neman salwanta saboda haka" Hajiya Yalwati ta rike baki tace "ni asu wa? Ina magana cewa za'ayi kishi nake da bakin ciki".
Da rana sai ga abinci kala kala wai inji Hajiya Babba, ko kallon inda suke banyi ba. Ana jimawa sai gata tazo, tunda muka zo gidan ban taba ganinta a dakin ba sai yau. Ta zauna a bakin gado suna gaisawa da Inna sannan ta data jikina tace min "sannu Diyam" kai kawai na gyada mata, tace da Inna "ba zai wuce malaria ba fa, ita ake ta fama yanzu" Inna ta kauda kai tace "likita yace jininta ne yake neman hawa, hawan jini ne yake kokarin kamata" Hajiya Babba ta bude baki tace "hawan jini kuma? Wa likitan ya gayawa?" Inna ta ce "Hajiya Yalwati, ita ta kaita asibitin ai" Hajiya Babba tayi murmushi tace "hmmm, neman magana ne kawai irin na Hajiya Yalwati. Babu wani hawan jini ni na sani" sai kuma ta kauda maganar "kinga fita ma zanyi nace bara inzo in duba ta. Kinsan dazu da safe Alhaji ya siyasa Saghir gidan da zasu zauna, shine yanzu zanje in ga gidan sannan inyi lissafin duk kayayyakin da za'a siya. Wannan abu ai tuwona mai na ne. Kar kiji komai duk abinda ake yiwa yarinya na gata to za'a yiwa Diyam a dakinta. Ni da kaina zan siyo komai tun daga kayan daki har kitchen".
Tana fita Inna ta bita da harara tana magana kasa kasa. Sai kuma ta dauki waya ta kira zuwa can aka dauka ta fara magana "haba Hafsa, wai dame kike so inji ne, da mutuwar mijina ko da auren dolen da za'ayiwa Diyam ko kuma da fushin da kike yi dani? Yanzu Hajiya Babba take gaya min wai an bata kudi zata siyo wa Diyam kayan daki, saboda Allah bake da Fatima ya kamata kuyi wa Diyam siyayya ba? Wannan ai ba hurumin ta bane ba. Gaskiya kizo kije gurin Alhaji sai ki nuna masa kamar baki san maganar ba ki tambayeshi ya bayar da kudin kayan dakin Diyam zaki je ki siyo mata" sun jima suna ta mayar da magana sannan suka yi sallama.
Mama bata zo gidan ba sai washegari, shima tana zuwa tace "ni fa ba wannan maganar ce ta kawo ni ba, zuwa nayi in duba jikin Diyam. Su je suyi ta siya mata koma menene ba damuwa ta bace wannan. Ni damuwa ta shine in dauko yaron nan kafa da kafa in kawo shi har gidan nan amma a wulakanta su har dake a ciki, ni da ban shi nake yi ba dan Diyam nake yi. Kuma wallahi yadda naji takaicin abinda kukayi wa yaron nan ko wallahi da niyya nayi in bashi auren Rumaisa, dan dai kawai yace min a'a ne wallahi da sai dai kawai ki gansu tare da Rumaisa sai kuma inga yadda zaki yi da shi. Suma kuma yan uwansa suka ce a'a ba yanzu zasuyi masa aure ba wannan ma dan rana daya ya tayar da hankalinsa suma kuma ya tayar musu shi yasa suka taho nema masa". Haka ta gama fadanta ta tafi babu wanda ta gaisar a gidan.
Washegari na dan samu sauki babu laifi. Amma zuciyata babu sauki a tare da ita sai ma kara zafi da takeyi kamar ana hura min wuta a cikinta. Inna ta matsamin dole nayi wanka wanda rabona dashi tun ranar da Sadauki yazo gidan. Na fito daga toilet na tsaya a gaban mudubi ina kallon kaina. I can't believe how many things ne sukayi changing a rayuwata in just few weeks? Har yanzu fa ba'ayi arba'in din baffa da Ummah ba amma wai har mutane sun manta dasu, har an shafe babinsu an bude sabon babi na yiwa yarsa aure a shekara goma sha huɗu. Nayi wa yarsa auren da aka san inda ace yana da rai babu wanda ya isa ya ko tunkare shi da maganar danshi ba damuwa yayi da kudin mutum ba ballantana mutum yace ya daina bashi.
Ina cikin saka kaya ne naji hayaniya a palo har da guɗa, sai kuma gasu Murja nan sun shigo inda nake suna ta murna da dariya. "Amaryar Hamma" Salma autar Hajiya Babba wadda ba'a jima da bikinta ba ta fada. Sai kuma suka kwashe da dariya. Kusan duk yayan Alhaji Babba wadanda suke aure dama yammata da suke gidan duk suna nan. Na dauke kaina ba tare dana kula su ba na zauna ina daura dankwali na, "munga kaya masha Allah, kaya sunyi kyau, ko dan gidan gwamna ne iya kacin kayan lefen da za'a kawo kenan" naji wani suka a kirjina "lefe? Nawa?" Sai na kwanta a kan gado na rufe idona. Ina jin murja tace "ku bata so fa, kar ku saka ta kuka" Suwaiba tace "bata son wa? Hamman? Anya kuwa akwai macen da zata ce bata son hamma komai kyanta? Kunya ce dai kawai take ji amma babu ma zancen wai bata sonsa" Aysha tace "ni kam zan so inga yayanku, wow, Diyam kyau hamma kyau, in ina da ciki zanke zuwa gidan ku dan in haifi yaya kyawawa nima" na juya baya na jawo hijab dina na rufe fuskata a raina ina cewa 'ya'ya kuma? Ni da Saghir? Tabbas nasan me akeyi ake samun yayan but I will die first kafin in barshi ya taba ni. For I thought I belong to one, and one alone. Sadauki. Sai kawai tunanin matan da suke kashe mazajensu cikin dare yazo min and it didn't look so bad.
Adda Zubaida ce ta shigo ta kore su gaba-daya. "Manya manya daku kunzo kun saka yar karamar yarinya a gaba kuna tsokanar ta" Salma tace "yar karama ce amma ta kusa shiga layin manya" suka fice suna dariya. Adda Zubaida ta zauna a kusa dani ta dafa ni taji ina sheshshekar kuka tace "kiyi hakuri Diyam kinji? Kiyi fatan wannan hadin ya zamo miki alkhairi. Duk sanda kike bukatar wani abu ko wata shawara ki neme ni kinji? Karki dauka cewa ni yayar Saghir ce ki dauka cewa ni yayarki ce kinji" na gyada mata kai.
Ina nan kwance aka yi ta shigowa da akwatinan ana jere wa a gefe, ina jin daya daga cikin yan aikin gidan da suke shigowa da kayan tace da dayar "ai ga amaryar nan a kwance" sai kuwa suka hada baki suka rangada min wata uwar guda a kaina wadda naji kamar zata tsaga min kan. Sai bayan da kowa ya watse sannan Inna ta shigo ita da Asma'u. Ta tashe ni zaune tana murmushi "tashi Diyam, tashi kiga kayan lefen ki" ta fara bubbudewa, "kinga wadannan sarkokin? Wannan zata yi miki kyau. Kinga pearls din da kike ta nacin in siya miki. Kinga wani lace? Dankari! Wannan ai na zuwa gidan biki ne. Ga takalmin can mai tsini irin wanda kike so" ni dai kallon ta kawai nake yi ko kadan banji zuciyata tayi sha'awar wani abu a cikin kayan ba, na kalli Asma'u data baje a gefe tana ta zaben kayan kwalliya wai duk tana so in bata. Sai kuma ina ta tashi ta fita ta bani guri. Na kalli kayan, akwatuna ne set hudu, pink, purple, peach da blue kowanne kuma da kyar ake rufe shi saboda kaya. Na mika hannu na na dauki wata bra ina kalla a raina nace "ko me suke tunanin zan saka a cikin wannan brazier? Na mayar da ita na ajiye na koma na kwanta na juya wa kayan baya.
Kwana biyu bayan nan ina zaune ina cin abincin da yanzu kullum sai Hajiya Babba ta girka ta aiko min dashi Inna kuma sai ta matsa min naci, sai ga Murja nan ta shigo "Diyam Alhaji yace ki shirya zamu fita yanzu gaba daya" ban kalle taba nace "babu inda zanje" ta daga hannu tace "ni dai yar aike ce". Sai kuma ga Hajiya Babba nan tazo da kanta, taci kwalliya kamar mai shirin zuwa gidan biki tace "innar Asma'u Alhaji yace Diyam tazo muje ganin gida da ita, in yaso in da akwai wani abin da take so sai ta fada a siya" tana fita Inna tace "ki tashi maza ki shirya ku tafi" na bata rai "Inna ni babu abinda nake so, in na gani ma babu abinda zan ce su kara" ta watsa min harara dole na tashi na shiga toilet na wanke fuskata na fito na saka hijab tace "kuma ko dan mai ba zaki shafa ba?" Na dawo na lakuci mai na shafa na juya tace "au dan nace mai shine kika shafa man shi kadai?" Nayi kamar zanyi kuka tace jeki.
Ina fita na tarar da yayan gidan suna ta shiga mota, matan gidan kuma suna gefe a tsaye suna hira. Na tsaya daga gefe ina kallon compound din, na kalli dai dai inda muka tsaya da Sadauki rannan sai naji ina ma dai ranar zata dawo in sake ganin sa at least koda sau daya ne. Na kalli gurin motoci sai idona ya sauka a kansa, cikin normal shigarshi ta dogayen kaya yayi kyau sai kyalli yake yi amma fuskar nan babu annuri ko digo a cikinta. Kallo daya nayi masa naji kamar duniyar ce take kara kuntatamin dan haka na juya na bar gurin na tafi inda yara suke shiga mota sai kuma naji kira da muryar Hajiya Babba "Diyam, ki dawo nan tare zamu tafi dake" na juya kamar zanyi kuka na koma, sai naga sun doshi motar da yake tsaye a kusa da ita, anti amarya tace "Diyam shiga gaba mu sai mu zauna a baya" na tsaya kawai ina kallon su kamar in rufe su da duka har suka gama shiga, shima ya shiga seat din driver ya zauna ya tayar da motar, sai da suka sake yi min magana sannan na kama handle din kofar jishi a rufe ni kuwa na koma da baya na nade hannu na a kirji. Hajiya Yalwati ta leko. "Ki shigo mana Diyam, ke fa muke jira" nace "kofar a rufe take Hajiya" ina jin Hajiya Babba tana yi masa magana, ya dauke kai kamar bai jita ba sannan kuma bayan wajan minti daya sai ya bude lock din. Na bude na zauna a makale a bakin kofa ba tare dana ko kalli side din da yake ba.
A hanya naji Hajiya Babba tana yiwa kishiyoyinta bayani "kunsan halin Saghir da rashin son hayaniya, wai shi ba zai zauna a cikin gari ba saboda kar mutane su dame shi, nace to kai me kanne da yawa? Namiji tilo a cikin mata? Ai dole ko gari ka bari sai kannenka sunje gidan ka, shine Alhaji ya biye masa aka siya masa gidan a can wajen gari, unguwar tokarawa acan zasu zauna" a raina nace 'wato yadda zai samu damar kasheni hankali kwance' ni a lokacin ban ma san unguwar ba sai dai naga mun dau hanyar barin gari, sai da muka wuce 'yan kaba sannan muka sauka daga titi muka shiga unguwar dana lura kamar sabuwar unguwa ce. Tun daga nesa na gane gidan. A house fit for the only son of Alhaji Babba amma ko kadan banji kyan gidan ya burge ni ba. Mukayi packing kusan a tare dasu Murja, na fita na tafi gurin su muka shiga tare amma sai na zame na zagaya bayan gidan nayi zamana akan veranda r backdoor din gidan. Ina jiyo su suna ta hayaniya da iface ifacen su alamar suna cikin nishadi amma ko sha'awar inje inga gidan banyi ba, addu'a nake a raina kar Allah yasa ina da rabon ganin cikin gidan nan in dai a matsayin matar Saghir ce. Naji wata irin kewar Sadauki ta taso min, sau dubu gwara ace in zauna da Sadauki a gidan kasa me yoyo akan in zauna da Saghir a wannan gidan.
Kamshin turare naji, na daga kai sai na ganshi a tsaye yana kallon gefe da alama bai san ma ina gurin ba. Fuskar nan kamar an aiko masa da mutuwa. Nayi saurin share hawayen fuskata saboda bana son ko kadan yaga weakness dina ballantana ya kara rainani. Motsin da nayi ne yasa ya juyo ya kalli inda nake, sai kuma naga ya tako cikin gadara yazo gabana ya tsaye ya kara tamke fuska yace "ke! Me na gaya miki rannan? Ba zaki je ki gaya musu ba sai kin je kin daukowa kanki abinda ba zaki iya ba ko?" Na mike tsaye na karkade hijab dina na juya zan bar masa gurin, ya damko hijab dina ya juyo dani yace cikin barazana "ba dake nake magana ba?" Na zabga masa hararar da nasan ba'a taba yi masa irinta ba nace "su wadanda kake magana a kansu ai sunfi kowa sanin cewa bana sonka, sunfi kowa sanin ina da wanda nake so wanda kuma yake sona, asalima dan su raba ni dashi ne suke neman makalamin kai"
The Game Has Began
It is such a long episode ko?
[1/28, 10:58 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤ DIYAM ❤
By
Maman Maama
Episode Twenty Eight: Destiny
Kafin mu cigaba please let us all take a moment and pray for Maryam Sanda and then pray for ourselves. Allah ya sa wannan hukuncin da aka yanke mata ya zamar mata alkhairi a duniya da kuma a lahirar ta, mu kuma Allah ya kare mu daga mummunar kaddara, Allah ya kare mu daga sharrin shaidan da sharrin zuciya, Allah yasa mu fi karfin zukatan mu a kodayaushe.
Bayan haka ina kira ga matan aure manyan mu da kananan mu, please idan kin tabbatar your marriage is not working, idan kin tabbatar kin je limit dinki na hakuri a gidan auren ki, please walk out of the marriage. Allah ya halatta saki for a reason, wani lokacin rabiwar tafi alkhairi akan cigaba da zaman. It is better a kiraki da bazawara then ki kasance in maryam sanda's shoes.
Sannan iyayen mu dan Allah ku dube mu da idon rahama, ku tausaya mana, dan Allah idan yarinya tazo gida tace ta gaji da zaman auren ta please ku bincika sosai, idan tana da gaskiya kuyi supporting dinta, kar ku tura yarku ga halaka, karku tura yarku zuwa wuta.
Now, let's continue with labarin Diyam maybe anan ma da akwai darasin da zamu dauka.
Da mamaki karara fuskarsa yake kallona, maybe bai taba tsammanin zan iya mayar masa da magana haka ba. Yace "ke? Kin san dawa kike magana kuwa? Ni din ne ma kike cewa za'a makala miki?" Na cigaba da kallon sa cikin ido duk a cikin kokari na na nuna masa cewa bana jin tsoronsa, amma zuciyata in banda lugude babu abinda take yi. Ya daga hannu da niyyar wanka min mari sai kuma ya kalli gidan inda hayaniya take fitowa daga tagogin sama, ya fahimci yana dukana zan tara masa jama'a dan haka sai ya dunkule hannunsa sannan ya sauke, ya nuna ni da dan yatsa yace "in kika sake kika shigo gidan nan sai na karya ki" na fusge hijab dina daga hannunsa nace "not today, kuma ni bani zan shiga gidan ka ba sai dai a shigo dani dan dole" na juya na tafi na barshi anan ina jin dadi a zuciyata, ashe dai Sadauki bai tafi da dukkan Strength din nawa ba, ko kuma maybe a time din wannan hug din ne yayi passing some of his strength and courage to me.
Muna komawa gida na wuce direct zuwa dakin inna, na gaisheta tana ta washe baki tace "kun dawo? Ya gidan?" Na tashi ina ninke hijab din dana cire nace "lfy lau" tace "lfy lau? Shikenan abinda zaki ce? Bayanin gidan zaki yi min inji dame dame aka saka kuma menene ba'a saka ba" nace "Inna ban sani ba nikam, ban shiga ciki ba a waje na zauna" nan fa takama fada, ni kuma nayi shiru har saida ta gama sannan nace "Inna yace inna shiga gidan sa sai ya kashe ni" sai ta girgiza kai tace "fada kawai yake yi, shima fushi yake yi saboda an matsa masa akan maganar nan, daga ke har shi ba kwaso amma abinda mu iyayenku muka hango ku ba zaku hango shi yanzu ba sai nan gaba zaku fahimta".
Washegari ina kwance kamar kullum sai ga aike wai ana kiran Inna, ta tashi ta tafi can kuma ta dawo sai naga cards a hannunta. Ta miko min tana kallon fuskata har na karba na karanta. Katin daurin aure ne, sunana da sunan Saghir, date din kuma nan da kwana uku. Na ajiye su akan cinyata ina jin dan kuzarin dana samu jiya yana draining kawai sai hawaye na ya fara zuba akan cards din. Na tuno abinda Sadauki ya gaya min "how litres of hawaye zaki zubar ne acikin wata daya?" "Be strong" he said, sai na kara karfin kuka na, wanne Strength ne dani kuma bayan bani da gata? Bayan ana so ayi amfani dafarinciki na gurin faranta wa wanda yake da gata? Saboda namiji ne shi nikuma mace? Ko saboda yana da uba a duniya ni bani da? Sai Inna ta zauna a kusa dani ta kwantar da kaina a kafadarta tace "Alhaji yace za'a hada daurin auren da addu'ar kwanaki arba'in din baffan ku, sai bayan daurin aure da sati daya sannan zaki tare, saboda ki samu damar gayyatar kawayenki da sauran shirye shirye". Na dago kai ina sake kallon date din, sai nayi realizing shine date din da za'a yi resuming school.
Tun daga lokacin taste din abinci ya dauke daga bakina, nayi kuka kamar idona zai cire har bana gani sosai, nayi addu'a na gaya wa Allah, kullum kuma sai na gaya wa Inna "Inna bana son auren Saghir" amma kamar busa sarewa nake yi, babu wanda ya dube ni, babu wanda ya mayar da damuwa ta wani abu mai muhimmanci ba kowa sai yace "zata daina ne, daga anyi auren shikenan ai ita mace mai rauni ce" ni kuwa jinsu kawai nake yi dan bana tunanin akwai ranar da zata zo wadda zan ji ina son Saghir.
Ranar Lahadi, 28 September aka daura aure na da Saghir. Ranar tun dana tashi da assuba na shiga toilet na rufe kaina na kwanta kan tiles nake kuka har aka gama daurin auren ban fito ba. Sai da Mama tazo sannan da kyar na bude mata kofar toilet din ta shigo ta fito dani, ta kori duk wadanda suke dakin ta zaunar dani akan gado ta bani Alqur'ani tace "kiyi ta karantawa zaki ji sauki a zuciyarki. Kiyi ta ambaton innalillahi wa inna ilaihir rajiun Allah zai sanyaya miki zuciyarki kuma yasa hakan ya zamo abu mafi alkhairi a gare ki" itama sai ta dauko Alqur'ani ta zauna muke karantawa tare, har sai da hawayen fuskata ya tsaya. Ranar daga ni sai ita muka zauna a dakin, ta saka ni a dole naci abinci duk da cewa da kyar yake sauka cikina. Sai kuma na cigaba da karatun ina jin nutsuwa tana samu na, ina jin karfin guiwar karbar kaddara ta, sannan kuma na gabatar da adduoi ga Baffa da Ummah, sannan na yiwa Sadauki addu'ar fatan alkhairi a duk inda yake. Na kuma samu kaina da tambayar kaina ko ya sani? Ko ya san an daura min aure da Saghir yau?
Kwanakin da suka biyo bayan nan shirye shirye ne kawai akeyi na biki. Hajiya Babba baki har kunne sai shiga take yi tana fita tana ta tsare tsare. Inna babu abinda take yi, gaba-daya tayi wani irin shiru da ita sai dai ta saka ni a gaba tayi ta kallo. Ni kuma na zama kamar mutum mutumi, bana kuka amma bana uhm bana uhm uhm. Mama ce tazo ta debi wasu daga cikin kayan lefe na ta kai aka dinka min, sannan ta yiwa Asma'u itama dinkuna tare dasu Rufaida. Sai tace min "Diyam babu wani abin da zaki shirya ne? Ko yar walima haka ke da kawayenki?" Ban kalle ta ba nace "Mama kawayena ai duk sun koma makaranta, ss1 zasu shiga, ni kuma gidan miji zan shiga, waye zai bar karatunsa yazo bikina?"
Sai tayi shiru bata bani amsa ba amma tana komawa gida sai ga yaya Mukhtar ya kawo Rumaisa, Rufaida da Muhsina sun taho da kayansu zasu zauna har sai an gama bikin. Hajiya Yalwati ta saka aka ware mana daki saboda yan uwan mu da zasu zo daga Kollere zasu sauka a dakin Inna. Ranar Rumaisa ta kawo min waɗansu littattafai guda biyu 'rayuwar aure a musulunci' na daya dana biyu tace "ki karanta zaki samu idea akan zaman aure" na karba kawai nace "Nagode" sai kuma tayi dariya tace "ni ban san me kike yiwa fushi haka ba. Mijinki kyakykyawa, kinsan da ina da crush akan hamma Saghir amma yanzu na hakura tunda ya zama mijinki" na tabe baki kawai a raina ina cewa ina ma dai zamu iya chanjen place da ita? Ita ta zama matar tasa ni in koma ita?
Ana gobe kamu Aunty Fatima tazo da mai kunshi zata yi mana, ranar sunga taurin kaina dan da kyar na zauna akayi min dan haka duk wanda baisan bana son auren ba sai daya sani a ranar. Ana gama wa kuma na saka hannu da gangan duk na damalmala kunshin ya chabe. Aunty Fatima kamar ta rufeni da duka dan haushi amma a haka ta kyale ni. Da daddare tace muje saloon sai na saka mata kuka a dole ta kyale ni kar in tara mata jama'a.
Ranar kamu sai da inna tazo ta sakani a gaba sannan na tsaya akayi min kyalliya. Mun zo zamu tafi gurin da aka shirya dan yin kamun kenan naji wata tayi comment "kunga amaryar kuwa? Yar mitsitsiya" ai kuwa ina jin haka na juya na koma daki a dole sai mai kamun ce ta bini dakin ta kama ni a can. Ranar yini kuwa ni wuni nayi da zazzabi dan haka suka dai suka sha bidirin su.
Washegari kai amarya, tunda safe Mama tazo, yau ne kadai na ganta tun da aka fara bikin. Tana zuwa yau ma duk ta kori su Rumaisa da dama duk sun addabeni, ta saka ni a gaba yau ma muka yi ta karatu kamar ranar nan, tare muka ci abinci mukayi sallah tare kuma sam bata yi min wata magana data danganci aure ba har magrib tayi sannan ta saka ni nayi wanka ta dauko min wani lace fari tas tace in saka. Ta gyara min fuskata simple make up sannan ta saka min sarka da dan kunne tayafa min farin mayafi ta kuma feshe ni da turare. Na zauna a bakin gado ta rufe min fuskata da mayafin sannan ta mike zata fita, na rike rigarta nayi mata tambayar da ta jima tana yawo a zuciyata, nace "Mama Sadauki ya sani? Ya san an daura min aure?" Ta dauke kai tace "ban sani ba Diyam, na kira layinsa baya shiga maybe ya chanza layi ne" sai ta fita, an jima suka dawo tare da wata matar dana fahimci daga baya cewa kanwar Hajiya Babba ce.
Tana zuwa ta bude fuskata tace "Masha Allah. Tubarkallah. Lallai Sagjir yayi dace da kyakykyawar mata. Allah ya baku zaman lafiya, Allah yayi muku albarka, Allah ya baku zuri'a ta gari" Mama tace "ameen". Sai suka kamani a tare suka fita dani. Sam ji nayi zuciya ta dake bana jin wani kuka kuma. Muka shiga dakin Inna anan na tarar da ita tana kwance ashe wai bata da lafiya tun safe. Na durkusa a gabanta tace "Allah yayi miki albarka Halima, biyayyar da kika yiwa iyayen ki Allah yasa kema naki yayan suyi miki. Allah yasa wannan auren shine mafi alkhairi" muka ce ameen muka tashi. Zamu tafi part din Alhaji Babba aka ce mana wai baya nan ya fita tun safe. A raina sai naji ina kewar Baffa, ba zai taba fita ba ranar da yasan zan bar gida in tafi gidan miji. Gidan kawu Isa muka shiga yayi min fada shima, sannan muka shiga mota muka tafi sauran motocin suna biye damu.
Har muka je gidan banyi kuka ba. Muka shiga ciki sannan naji mun fara gawa stairs sannan muka shiga wani palo sai kuma wani daki. Aka zaunar dani akan gado Mama ta rufo kofa tazo ta zauna a kusa dani ta rike hannuna ta fara magana a hankali
"Diyam ki saurare ni sosai kiji abinda zan gaya miki. Yanzu kin zama matar aure, kin bar karkashin iyayenki kin koma karkashin mijinki haka zalika aljannar ki ta koma karkashin mijinki. Bauta zakiyi, amma ki saka a ranki cewa ba Saghir zaki bautawa ba Allah zaki bautawa. Auren Saghir shine kaddararki, shine jarabawarki. Biyayyar Saghir a yanzu ita ce gaba da komai a gurinki in banda addinin ki. Na sami cewa ba'ayi miki adalci ba, na sani cewa iyayen Saghir basu kyauta ba sun kasa tankwara yaron su tun yana danye har sai daya bushe tukunna sannan kuma suka dora hakkin tankwara shi a kanki, duk da kasancewarki mai kankantar shekaru amma ni nasan zaki iya, in dai har zaki yi masa biyayya, ki kula da cikinsa da shimfidarsa, ki kasance mai tsafta mai hakuri da juriya da kawar da kai a lamuransa, to kuwa duk girman kansa sai kin mayar dashi tamkar rakumi da akala musamman tunda kina da kyau kuma shine abinda aza da yawa a yanzu suke so".
Ta jima tana yi min nasihohin hanyoyin da take ganin zan bi in jawo hankalin Saghir ya soni, ni kuma sai nayi wa kaina tambayar "ta yaya zan saka wanda bana so ya soni? Biyayya ga abinda baka so is extra hard right?"
[1/29, 10:18 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Twenty Nine: The Lost Flower
Warning: Emotional Episode
Ta mike zata fita sai na rike zanin ta na kifa fuskata a cinyarta na fara kuka mai tsuma zuciya amma sai tasa hannunta ta cire hannuna daga zaninta ta juya ta fita. Na rufe fuska ta da hannayena ina kuka, ji nake kamar wannan auren shine karshen rayuwata, ji nake ina ma mala'ikan mutuwa yazo ya dauki raina, anya kuwa zan iya yiwa Saghir biyayyar aure kamar yadda ya kamata? Kuma gashi aljanna ta tana defending on wannan auren alakakai din and I so much want to go to jannat idan na mutu, wannan yasa na fara addu'ar Allah yasa in mutu a wannan ranar.
Ina cikin kuka na su murja suka shigo suka zagaye ni, Rumaisa tace "ke baki san yanzu an daina kukan aure bane ba wai? Wannan ai sai ki bada mu in abokan ango suka zo" murja tace "suka zo ina? Wai nan gidan? To ni kam bada ni ba babu wani siyan baki da zan zauna yi yazo ya hada mu ni da amaryar ya huce haushin sa akan mu" Rumaisa tace "ke dan Allah ki daina fadar haka ai sai ki saka taji tsoro". Suna ta hirarrakin su ni dai na mike nayo alwala na gabatar da sallar isha ina kaiwa Allah kuka na.
Ina nan kan sallayar sai na jiyo muryar yaya Mukhtar daga palo, sai ga Rufaida ta shigo tace "wallahi yaya Mukhtar yace duk ku fito mu tafi in ba haka ba sai dai ku kai kanku gida dan shi tafiya zaiyi. Wannan unguwar tasu kuwa ba abin hawa zaku samu ba, angon kuwa in ya zo ko suma kuke ba zai kaiku gida ba" kusan duk a tare suka mike suna harhada kayansu. Na kalle su da kumburarrun idanuna nace "yanzu tafiya zaku yi ku barni ni kadai a gidan nan?" Rumaisa tace "da anjima angonki zai zo, kuma ai naga kuna da maigadi" Murja tace "idan yayi tafiya kiyi min waya sai inzo in taya ki zama, amma in yana nan ba zan zo ba". Yaya Mukhtar ya sake kwala musu kira dan haka suka fice da sauri.
Ina jinsu suka sauka daga bene, ina jinsu suka fita daga palon kasa suka rufe kofa sannan naji sun shiga mota an bude musu gate sun fita, na tashi da sauri na leka ta window na hango hasken motar su har sun dau hanya. Sai kuma na tsaya ina kare wa unguwar kallo, babu gidaje sosai sai kwangwaye wannan ya kara wa unguwar duhu. A bakin gate naga mai gadi a zaune akan benchi da radiyo a gefensa. Sai naji wani irin loneliness sannan kuma naji wani irin tsoro.
Na haye kan gado da sauri sai kuma wani tunani yazo min sai na tashi da sauri na bude kofa na fita. Sai na ganni a cikin wani palo madaidaici wanda aka kawata da kujeru da kayan kallo da adon frames a bango da sauran tarkace. Kofofi uku ne a palon, na fara bude su daya bayan daya ina neman kitchen amma sai naji daya a rufe take dayar kuma wani bedroom din ne kudan irin wanda na fito daga ciki sai banbancin colors. Na sauka daga bene da sauri shima palon ne amma yafi na sama girma da tsaruwa, sai wadansu kananan bedrooms guda biyu da dining room mai hade da katon kitchen. Ban tsaya kallon komai ba saboda yadda jikina yake karkarwa saboda tsoro, na shiga kitchen din na fara bude drawers ina neman abinda ya kawo ni, can naga set dinsu, wukake, na dauki wadda naga tafi kowacce girma na boye a rigata na sake fita da sauri na haye sama. Dakin da aka kaini na koma na tura kofa da niyyar locking amma sai na ga babu key a jiki. Na fara fara neme neme cikin lockers din dakin amma babu key babu alamarsa. Na shiga toilet na duba nan ma babu. Sai na dawo na zauna akan gado kamar zanyi kuka amma tears din sun tsaya, maybe sun kare. A hankali nace "Sadauki, Please come and take me away from here".
Sai na kwanta na dunkule a guri daya, na jima a haka sannan bacci ya fara fusgata ina yi ina farkawa a tsorace cike da mafarkai, wani mafarkin wai Sadauki tazo yace in tashi mu gudu, wani kuma wai Saghir yazo ya zare belt dinsa yace ba yace kar in sake inzo gidan nan ba?
Cikin baccin naji karar bude gate, na tashi zaune a tsorace, sai nayi sauri naje na kashe fitilar dakin sannan nazo na leka window, mota naga ta shigo tayi packing, sai kuma ya fito yana tafiya unsteadily. Ina lura da maiigadi yana gaishe shi amma bai ko kalle shi ba ya taho cikin gidan. Nayi sauri na tura kofar dakin da na ke ciki sannan na dauki wukata na tafi can lokon gado na kudunduna a cikin duvet, naji ya bude kofar palo ya shigo amma banji ya rufe ba, najiyo shi yana hawowa sama sannan naji ya bude kofar dakin da yake kusa da inda nake, sai kuma takunsa yana tahowa sannan naji ya bude dakin da nake, na dauke numfashi na ina kara addu'ar Allah ya dauki raina.
Ya kunna fitila sai can kuma naji ya kashe amma na tabbatar ya ganni, sai kuma naji ya karaso inda nake kudundune ya saka kafarsa mai sanye da takalmi ya dake ni da ita "ke!" Na dunkule hannuna a handle din wukata na mike da sauri ina nuna shi da ita, fuskata cike da hawaye nace cikin murya mai karkarwa "if you dare touch me!" Ya tsaya yana kallona ta kasan ido, da mamaki a fuskarsa sannan cikin wata irin murya da tafi yi min kama data yan maye yace "what? What will you do?" Na sake nuna shi da wukar "in ka kara wani takun kusa dani na rantse I will...." Ya tako step din without hesitation yace "you will what?" Gabadaya jikina karkarwa yake yi hatta wukar hannuna rawa take yi tana neman faduwa, hannu daya yasa ya doke hannun nawa sai wukar ta fadi. Na dunkule a kasa "don't touch me please" sai yasa hannu ya kamo wuyan rigata ya mikar dani tsaye, ya hada ni da bango sannan ya kawo fuskarsa dai dai tawa, wani wari naji daga bakinsa, ba warin kazanta ba amma wani wari marar dadi, nayi saurin dauke kaina yace "mena gaya miki zanyi miki in kika sake kika shigo gidan nan? Kin dauka wasa nake yi dake ko?" Nace "wayyo Allah na, wayyo Sadauki" ya saki wuyana yana kallona "Sadauki? Sunan saurayin naki kenan? To yazo ya nuna sadaukan ta kar tasa in gani" nayi shiru a raina ina fatan zaizo din, yace yana kara matsowa jikina "bana ce miki karki zo gidan nan ba?" Na girgiza kai nace "nima kawo ni akayi, Bani nazo da kaina ba. Please ka mayar musu dani kace ba ka sona" yace "with pleasure. Amma kafin in mayar dake sai na yi musu proving abinda na gaya musu su kaki yarda. Kinyi min kankanta da aure" yana fadin haka sai ya saki wuyana, sannan ya hankada ni na fada kam gado kaina ya bugu da jikin frame din gadon. Na fara ganin dusu dusu a idona amma duk da haka sai nayi kokarin mikewa sai dai nauyin da naji a kaina ya sa na kasa ko motsi. Amma sai na takarkare tun karfi na zunduma ihun kiran Sadauki a lokacin da naji zani na ya bar jikina. Sai kuma naji wani piercing pain daya taho tun daga kasana ya dire har cikin kwakwalwata. Sai muryar ihun ta dauke, numfashi na ya dauke, naga wani haske a idona. The last thing da naji kafin hankali na ya barni shine muryar Sadauki lokacin da yake ce min "everything is going to be alright".
A short episode. But mu fara jajanta wannan lamarin tukunna.
Dear parents, This might be what will happen to your daughter in kuka rufe idon ku kuka aura mata wannan lalataccen dan masu kudin da bata so, ko wannan alhajin da yake zuwa a babbar mota, ko kuma wannan dan uwan naku da yaki aure shekara da shekaru kukayi tunanin bara ku hada su dan inganta zumunci. It might not always be the right choice, especially idan wanda za'a hada ta da shi din ansan bashi da halayya mai kyau. Yaya amana ne a hannunmu, don't trade them for wordly things please.
Yes, addini ya yarda iyaye su taya ƴaƴansu zaben mijin aure, amma kuma bai ce a tirsasa musu ba. Akwai ingantaccen hadisin ma da ya nuna haramcin hakan.
Allah ya sa mu dace.
[1/30, 11:56 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤ DIYAM ❤
By
Maman Maama
Episode Thirty : The Empty Heart
Sama sama nake jin maganganu a kusa dani, a hankali ake maganar amma sai naji tamkar wanda ake hayaniya saboda ciwon da kaina yake yi min. Na kai hannu a hankali na dafe goshina sai naki ance "sannu Diyam. Ta farka" naji muryar kamar na santa amma sai na kasa gane mai ita. Wannan yasa nayi kokarin bude ido na amma sai naji sunyi min nauyi. Na mayar dasu na rufe. Sannan na fara tunani where am I? What happened? A hankali pictures din abubuwan da suka faru suka fara yi min yawo a kaina. Mutuwar Baffa da Ummah, bankwana na da Sadauki, auren dolen da akayi min, abinda Saghir yayi min da daddare. Nayi saurin bude idona sannan nayi kokarin tashi zaune ina girgiza kaina hoping in ganni a gidan mu in ga cewa duk wannan wani mugun mafarki ne nayi. Amma wani irin azaba da naji daga kasana wadda cikin second daya ta gauraye duk sassan jikina ita tasa na koma da baya na kwanta, bana bukatar assurance, wannan ciwon ya tabbatar min cewa ba mafarki nayi ba, ya tabbatar min cewa Saghir raped me. Na runtse idona ina so hawaye yazo min amma yaki zuwa sai wata irin kuna da zuciyata take yi min. Na tuno alkawarin da Sadauki yayi min "ki saka a ranki cewa Sadauki zai kasance tare dake a koda yaushe, kome ya faru dake ko me kike yi ki saka a ranki cewa I will always be watching over you. This is my promise to you" sai nace "where were you Sadauki?" Duk sanda yayi min alƙawari yana cikawa amma ta gaza cika wannan. Na kai hannu zan taba inda nake jin tamkar anyi min tsarki da attaruhu sai naji an rike min hannu, na bude idona naga Adda Zubaida a zaune a bakin gado tana rike da hannuna, nabi dakin da kallo, bakin dakin nan ne dai da aka kawo ni jiya aka ajiye tamkar akuyar da akayi sacrificing dan a kama zaki, dakin da zakin kuma yazo ya karasa destroying rayuwata, ya karasa karbar dan sauran abinda nake rakama dashi.
Na sauke idona kan Adda zubaida da fuskarta take nuna tsantsar tausayi na. Ta kara cewa "sannu Diyam" sai naji wata muryar kuma a gefe na itama tana yi min sannu, na juya naga wata mata da muke kira Uwani, kamar kanwa take a gurin hardo dan haka kamar kaka ce a gurin mu. Na kalli jikina naga doguwar riga ce yar kanti marar hannu. Na koma na kwanta a hankali nace "Adda ki kirawo min Inna dan Allah ki ce nace dan Allah tazo ta daukeni daga gidan nan" ta girgiza kai tace "Diyam ba zan iya ba, bazan iya gatawa innarki wannan mummunan labarin ba. Da wanne zata ji. Na dai gayawa su iyayen tantirin. Su san ga abinda dansu ya aikata" Uwani tace "to ya zasu yi? Sai addu'a" Adda tace "wallahi uwani duk abinda Saghir ya zama a duniya da sa hannun mahaifansa. Basa son laifinsa, soyayyar da suke yi masa ta rufe musu ido ko me yayi basa tsawatar masa. Duk dukiyar Alhaji fa ta salwanta a hannun Saghir kullum in ya di ba ya tafi sai sun kare zai dawo, in muka yi magana ace masa ai kasuwanci yake yi bayan mun san babu wani kasuwanci da yake yi sai iskanci. Sai yanzu kuma da lokaci ya gama kurewa sannan suke son su gyara shi. Yanzu kalli uban kudin da aka kashe aka sai masa auren nan aka sai masa gidan nan aka dauki kankanuwar yarinyar nan marainiyar Allah aka bashi amma dan iskanci shine a ranar da aka kawo ta yayi mata wannan wulakancin ya tattara kayansa ya gudu" uwani tace "au wai tafiya yayi? Ina ya tafi?" Adda tace "to wa sani ne. Da assubar fari ya kira wayata wai in taho gidansa Diyam zata mutu, ina jin gaka nasan yayi tsiyar. Haka nazo na samu Diyam tana numfashi da kyar maigadi ya gaya min tun assuba yaga ya saka akwati a mota ya fice, na sake kiran wayarsa bata shiga. Ni kuwa na kira uwar da uban nace to ga abinda Saghir ya aikata nan kuma ya gudu. Alhaji yayi ta salati, in ba sa'a muka ci ba in anjima kiji shi a asibiti hawan jini ya tashi, kuma hawan jinin mun san Saghir ne ya sama masa. Ita kuma Hajiya Babba saboda tsabar son kai ina gaya mata sai ta kama rokona wai dan Allah kar in gaya wa kowa mu bar maganar a tsakanin mu, in kai Diyam asibiti amma kar in gaya wa kowa. To ni wa zan iya gayawa wannan kayan takaicin ne?".
Uwani tace "hmmm, ni ina bacci ai taje ta same ni wai dan Allah in taho gidan nan in taimaka wa Diyam, ina ji nasan an yi aika aika kenan. Kuma dan dai ya saka mata karfi ne, amma in da a hankali ya bita babu abinda zai same ta" Adda tace "to ina zai bita a hankali? In yayi haka ai bai cika dan iska ba" sai tayi tsaki "ni ban ma san yadda zanyi ba wallahi. Na daiyi mata ruwan dimi na dan gasa ta, ni ba zan iya kaita asibiti ba wallahi wannan ai abin kunya ne, in je ince musu me? This is a rape case zasu iya cewa sai na dauko police" ta sake yim tsaki "Allah wadaran naka ya lalace. Amma ai duk wanda ya sai rariya dama yasan zata zubar da ruwa". Sai kuma ta dauko waya tayi kira. "Hello, sister Asiya dan Allah in kina off ki taimaka min, wata kanwata ce akayi wa aure jiya kuma yar karama ce wallahi.....to kinsan halin maza... Dan Allah in baki address din kizo ki duba min ita" sai kuma tayi mata godiya ta katse, ta sake tsaki tace "this is very uncomfortable wallahi".
Duk maganar da suke yi ina jin su amma na rufe idona kawai dan bazan iya tankawa ba. Addu'a kawai nake jerawa a cikin zuciya ta "ya Allah duk wanda yake da hannu akan wannan wulakancin da aka yi min ya Allah ka saka min. Ya Allah tafiyar nan da Saghir yayi Allah kasa yayi hatsarin mota ya mutu kar ya dawo. Ya Allah ka hada shi da yan fashi a hanya su sabauta shi kamar yadda ya sabauta ni. Ya Allah ka saka ginin gidan da zai sauka ya fado masa cikin dare ya tarwatsa shi kamar yadda ya tarwatsa rayuwata".
Ina nan kwance matar tazo, ina jinta suka gaisa da Adda zubaida da Uwani. Sannan ta zauna kusa dani tace "amarya" na bude ido na kalleta na rufe, tace "kar ki zama raguwa mana. Tashi tsaye mu gani" nayi saurin girgiza kaina sai ta kama kafafuwana tayi bending dinsu, nayi kara saboda jin cinyoyi na nayi kamar wadda nayi frog jump, ta bude rigata tana dubawa tace "babu tear, the place is just sore kuma akwai bruises" ta rufe rigar tace "zanyi mata allurar da zata rage mata pain sannan zan rubuta muku magani ku siyo mata. Sai take amfani da ruwan dumi sosai" Adda tayi mats godiya sai ta juyo tana kallona tace "ina angon? Yazo ya mayar dani gida" ita as a joke ta fada ni kuma kalmar angon ma bata min rai tayi. Har zata fita ta juyo ta sake kallona tace "amma yarinyar nan tayi kankanta da aure wallahi Zubaida. Wai dama har yanzu fulani kuna irin wannan auren?" Ban dai ji amsar da Adda ta bata ba suka fita.
Ranar har dare Adda Zubaida tana guri na, kuma ta saka ni na shiga ruwan zafi sosai sannan kuma ta dafa min abinci mai kyau ta matsamin na ci. Sai kuma ta saka ni nayi tafiya wadda sanda ina yi ji nayi kafafuwana kamar ba'a jikina suke ba. Uwani ce ta zauna ta kwana a gurina washegari sai ga kayanta Alhaji Babba ya saka a aiko mata dasu yace ta zauna a gurina har sai Saghir ya dawo daga tafiyar da yayi. Sai da nayi kwana uku a sama ina jinyar kaina sannan na iya saukowa kasa, ina saukowa daga bene idona ya sauka akan katon hotonsa ya sha shadda army green wadda ta kara haska farar fatarsa, ya turo hular nan gaban goshi fuskarsa dauke da murmushi, sai a lokacin nayi tunanin kamar ban taba ganin murmushin sa ba. Na taka naje har gaban hoton na tsaya ina kare masa kallo sai kuma na saka hannu na ciro hoton na sauke shi kasa sannan na juya shi ya koma kallon bango.
Jikina ya warke, amma tabon zuciyata yana nan kuma banajin zai warke har abada. Saghir kuma kullum zuciyata kara tsananta tsanarsa take yi. Ko mai irin sunansa baba son inji an ambata ballantana shi. Babu sallar da zanyi ba tare da nayi addu'ar neman sakayya tsakani na dashi da duk wanda ya aura min shi ba. Kullum kuma da fargabar dawowarsa nake kwana da ita naje tashi. Ko wani kwakwkwaran motsi uwani tayi sai na firgita ballantana in naji an taba gate. Muna da kayan abinci wadanda aka kawo da sunan kayan gara, kudi kuma duk karshen sati Alhaji yana aiko mana dashi shi dai kawai burinsa in zauna a gidan. Uwani tana tare dani, kuma duk weekend su murja ko su Rumaisa sukan zo su kwanar min biyu, wannan sosai yakan rage min kewa amma a zahiri a zuciyata kuwa empty nake jin heart dina.
Kwanaki suka wuce haka satittika, sai watanni suka biyo baya har nayi wata uku a gidan Saghir amma babu shi babu alamar sa. A ranar da na cika wata ukun ne Hajiya Babba tace mu shirya muje gida mu kwana biyu. Da wuri driver yazo ya dauke mu muka tafi. Tun daga bakin gate na lura da yadda gidan ya chanja, ma'aikata sun ragu, motoci ma haka, gidan kuma yayi datti flowers sun mutu.
A main palo muka samu Hajiya Babba, har da mikewar ta tsaye ta tarye mu da fara'a "sannunku da zuwa uwani" ta jawo ni jikinta zata rungume ni sai na zame na durkusa na gaisheta, ta amsa da fara'ar ta ni kuma na mike na nufi dakin inna ta ina jin missing dinta a raina, ina jin Hajiya Babba tana cewa "Masha Allah, lallai Diyam, wannan girma haka kamar ana hura ki?"
Ina shiga na tarar da Inna tana ta murnar zuwa na itama. Na je na rungume ta tana ta dariya ta dan tura ni baya tace "Diyam kinyi girma haka? Alhamdulillah, naji dadin ganin ki sosai. Ni ina nan ina ta fargabar halin da kike ciki gashi Saghir ance yayi tafiya kasar waje business ya rike shi" na zauna akan gado ina rungume da Asma'u ina dariya. Ta zauna gefe na tana ta yi min tambayoyi game da halin da nake ciki ni kuma ina bata amsa a takaice. Tace "naso inyi miki girki tunda aka ce zaku zo, nasan kina son tuwo amma kinsan bana girki a gidan nan" na kalle ta sai na lura da yadda ta fada tayi baki bakinta duk ya bushe. Nace "inna ku ya kuke ciki? Lafiya dai ko?" Tace "hmm, lafiya lau" nayi shiru dai ina kallonta dan na fahimci ba karshen maganar ba kenan. Sai nace "Inna an saka Asma'u a makaranta kuwa?" Tace "eh an saka ta" sai ta sake shiru, ta jima kuma sannan tace "na jima inata faman bi akan zancen makarantar yarinyar nan, da kyar na samu aka saka ta amma wai ga makarantar da sauran yaran gidannan suke yi sai aka dauke ta aka saka a makarantar gwamnati. Tana kallon yaran zasu shiga mota a tafi dasu makaranta ita kuma sai dai ta tafi a kafa, har kuka sai da tayi min wai ita makarantar su siyama take so amma haka ba bata hakuri saboda babu yadda zanyi"
Naji zuciyata tana zafi nace "to Inna ke ki saka ta ata kudin mana? Ina kudin da ake samu a garejin baffa duk wannan watannin ayi amfani dashi mana a saka Asma'u a makaranta mai kyau" tace "hmmm. Diyam kenan. Wanne gareji kuma kike magana? Tun a lokacin bikin ki nayi wa Alhaji maganar gare jin kinsan me yace min?" Na girgiza kaina tace "yace garejin shi aka siyar akayi miki kayan daki" na bude baki ina kallon ta nace "garejin? Da duk motocin da suke ciki?" Eh kawai tace, na sunkuyar da kaina sannan nace "filin Sadauki fa? An bashi kayansa?" A can kasa ta amsa tace "har dashi ya sayar".
Na tashi na shiga toilet na hada kaina da kofa, rabona da in kira sunan Sadauki tun ranar da aka kaini gidan Saghir amma ni kadai na san me nake ji a zuciyata, I missed him so badly dan tunda nazo duniya ban taba yin wannan dadewar ba tare dana ganshi ba yanzu kuma ambatar sunansa ya tayar min da mikin dake cikin zuciyata. Na tuna ranar da yaje school gurina da murnarsa yake bani labarin Baffa ya saya masa fili, kuma da kudinsa daya tara masa ya siya masa his hard earned money amma wai Alhaji Babba ya siyar. Ban roki Allah sakayya bama saboda nasan tabbas zai yi maybe slowly but surely.
Bayan na dawo dakin ne uwani ta shigo suka gaisa da Inna ta kuma kawo min mangwaro na dana siya a hanya. Inna ta karba tana cewa "wannan mangwaron Diyam ai bai nuna ba aka baku shi" na karba na fara sha ina cewa "yafi dadi ai" sai ta tsaya tana kallona sannan ta juya ta kalli uwani tana girgiza kai sai naga uwani ta gyada mata kai, sai kuma suka juyo suna kallona a tare ina ta rasgar danyen mangwaro. A raina nace "su kuma wadannan menene naga suna magana da ka kamar kurame?".
Not edited
[1/31, 9:21 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman maama
Episode Thirty One : The Broken Heart
Inna ta saka na zagaya na gaishe da mutanen gidan, kuma kowa naje sai ta yi comment akan girman da nayi, ni kuma sam banga wani girma da nayi ba na dai san cewa kirjina ya kara cika amma bayan shi ban kara komai ba. Ina dawowa dakin inna na tarar an aiko min da abinci kala kala daga gurin Hajiya Babba, inna tace "da yake surukar ta tazo shine ta aiko mata da abinci, amma mu yaushe rabon da muga kwano daga dakinta" ni dai bance komai ba na fara bubbuda flasks din zaben abinda zanci, na samu wani farfesun kaji na ja gefe na fara ci. Ina cikin ci Hajiya Yalwati ta shigo, ta kalli lodin abincin tace "hmmm. Ana cewa babu kudi bayan kudin suna can a inda aka ajiye su" Inna tayi dariya tace "ke kam ba kya rabo da bakar magana".
A dakin Inna na wuni, sai da yamma ta tura ni inje in gaida Alhaji, kuma in shiga gidan Kawu Isa suma in gaishe su. Sai a lokacin na fahimci cewa ashe Alhaji Babba bashi da lafiya yana kwance. Ina dawowa sai ga sako dafa Hajiya Babba wai inje an gyara min daki a gurinta inje in sauka a can. Naki zuwa nace ace mata na gode amma a gurin Inna zan zauna, sai nayi sa'a kuma innar bata matsamin in tafi din ba.
Da daddare Inna take gaya min cewa gobe ne zata fita daga takaba, ashe shine dalilin da yasa aka dauko ni. Sai na tambayeta "Mama zata zo goben?" Inna tace "inajin zata zo, wani abun ne?" Nace "dama wata tambaya nake so inyi mata" ta zauna a kusa dani tace "tambayar me fa?" Sai na fara jujjuya hannuna ina feeling uncomfortable, ni ban saba irin wannan maganar da Inna ba dama Ummah ce da sauki. Sai data sake tambayata sannan nace "so na ke inji, wai dama in mutum yayi aure sai ya daina period? Dama matan aure basayi?" Sai ta tashi ta bude wardrobe kamar mai dauko wani abu, ta jingina kanta da kofar tace "yaushe rabon da kiyi?" Nace "tun kafin.....tun kafin biki" tace "wata uku kenan ko?" Na ce "eh" tace "matan aure sunayi Diyam, sai dai in matar aure tana da ciki ne bata yi" naji kaina ya kulle nace "ciki?" Sai kawai ta juyo tana kallo na, na dan yi shiru ina tunanin kalmar ciki sai kuma lokaci daya naji tamkar an ciro zuciyata an buga ta da kasa ta tarwatse. Nayi saurin rike kirjina na zamo daga kan gadon na fado kasa, a hankali na fara kiran innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Inna ta taho da sauri ta rike ni tana kokarin daga ni amma na dunkule a guri daya danji nake yi tamkar idan na mike zuciyata zata fado daga kirjina. Amma hawaye yaki zuwa idona, kalmar ciki ce kawai take yawo a kaina, wai ciki nake dashi ni Diyam kuma cikin ma wai na Saghir wannan wacce irin jarabawa ce, wannan wacce irin rayuwa ce. Har yanzu banyi accepting Saghir a matsayin miji na ba ballantana kuma in karbe shi a matsayin uban yayana. Inna ta rike ni tana cewa "haba Diyam, menene hakan kuma daga maganar ciki? Ciki yar kyautar Allah ne in aka same shi murna ya kamata ayi a kuma godewa Allah" sai na kifa kaina a jikinta ina jan numfashi da kyar. Na rufe ido na ina tunano fuskar Sadauki. Wannan cikin tamkar yayi sealing aurena da Saghir ne, tamkar ya tabbatar da rabuwa ta da Sadauki kenan.
Ranar yadda naga rana haka naga dare. Ina jin ko lokacin da aka daura min aure da Saghir ban shiga irin wannan tashin hankalin ba. Sai bayan nayi salllah asuba sannan nayi bacci dan haka har mutane suka fara zuwa yiwa Inna gaisuwa da kuma taya ta murnar fita daga takaba ban tashi ba, dagabaya ma dana farka sai na yi kwanciya ta har saida naji muryar Mama sannan na tashi na gaisheta. Ta bini da kallo kamar mai accessing dina, wannan yasa na koma na kwanta na lulluba dan ji nake yi kamar duk wanda ya ganni yana iya hango cikin jikina.
Ina kwance Mama ta shigo tace "Diyam taso ki raka ni unguwa" da sauri na mike ina straightening hijab dina dan ba karamin gajiya nayi da gidan da duk mutanen da ke cikinsa ba. Muna shiga muka shiga motar da tazo da ita, Mukhtar yana ja muka tafi sai na gan mu munzo wani asibiti, naji gabana ya fadi ina tuna ranar da aka kaini asibiti naga gawar Baffa, ranar da rayuwata ta tarwatse. Na tambayeta "Mama waye bashi da lafiya?" Tace "ba kowa, ke na kawo kiga likita" sai na sunkuyar da kaina a raina ina cewa Inna ta gaya mata kenan. Da yake asibitin kudi ne dan haka muna zuwa aka dauki jini na for a confirmation test, mu ka zauna jira sai kuma aka kira mu dakin likita, muka shiga suka gaisa da Mama sannan nima na gaishe shi ya dauko result din yana kallona yace "Halima Usman Kollere?" Na gyada masa kai, yace "how old are you?" Nace "14" sai naji kalmar 14 din tana burning a kirjina. Ya girgiza kai yana kallon Mama yace "how comes? Yarki ce?" Ta gyada kai tace "yar yaya tace, mahaifinta ya rasu shine yan uwansa suka aurar da ita ga dansu" ya girgiza kai yana kallona sannan yace "well, she is pregnant. Zamuyi scanning dai muga wata nawa ne sannan muga in ya shiga yadda ya kamata, za kuma mu duba lafiyar mahaifarta in zata iya daukar nauyin cikin" nayi sauri dago kai ina kallon doctor din, da rawar murya nace "doctor please ka cire cikin nan bana so" Mama tace "kul Diyam, kar in sake jin kince ba kyason abinda yake cikin ki. Allah ne fa ya baki ajjiya, ba naki bane ba na Allah ne kuma shi kadai zai karbi kayansa a lokacin da yake ganin ya dace".
Muka je na kwanta akan gado Mama tana rike da hannuna da yake rawa saboda tsoro. Doctor ya zuba min wani abu mai sanyi a mara ta sannan ya fara goga wata roba akai yana kallon screen din gabansa, can sai naji yace "wow wow." Ya juyo yana kallon Mama yace "we are having twins here".
Bayan an gama scanning din mun koma mun zauna yace "gaskiyar magana yarinyar nan tayi kankanta, bayan rashin shekaru gashi kuma tana da kankantar jiki, she can carry the pregnancy but I strongly suggest that kar a barta tayi labor, musamman tunda she is carrying multiple a shawarce da ta kai around 36 weeks ku kawo ta a cire babies din saboda lafiyar ta" Mama ta gyada kai da sauri tace "insha Allah doctor hakan za'ayi" ya tura mu mukayi sauran tests sannan ya rubuta mana drugs ya sallame mu.
Hankalina idan yayi dubu to duk ya tashi, dan tunda doctor yace twins ne bankara magana ba dan in nayi ma inajin muryar ba zata fita ba. Wato ba daya ba, ƴaƴan Saghir guda biyu ne a cikina. Har muka zo gida bance komai ba ina dai jin Mama tana tayi min bayanai da yadda zan kula da kaina da abincin da ya dace in ke ci, ni dai na jingina jsina da kofar mota kawai na rufe idona.
Muna packing su Salma suna fitowa ita da Aysha zasu tafi gidajen su, bana son magana dan haka ko kallon su banyi ba nazo zan wuce ta kusa dasu Salma tace "oh su Diyam manya, kamar ba itace nan take ta koke koke ba wai bata son auren hamma amma gata nan harda ciki. Ni ko zanso inga yadda akayi cikin nan". Sai suka kyalkyale da dariya. Har na taka step zan shiga palo sai na tsaya ina juya kai, it is hardly a gaya min magana inyi shiru and this is not going to be the first time. Na juya na sha gabanta nace "yes bana son yayanki kuma har duniya ta nade ba zan so shi ba ko da kuwa zan haifa masa duk mutanen da suke duniyar nan. Ni ma kuma zanso ace kinga yadda akayi wannan cikin dan a lokacin ne zaki tabbatar cewa yayanku is nothing but a monster, a big for nothing monster". Mama tazo da sauri ta jani muka wuce, amma naji dadi a raina.
Mu da muka zo da niyyar kwana biyu sai da mukayi sati. A cikin satin na fahimci abubuwa da yawa, na farko shine arzikin Alhaji Babba ya ragu sosai, dan naji ana cewa yanzu shagunan sa na kantin kwari ne kadai suke functioning. Abu na biyu Inna tana cikin damuwa game da negligence da take fuskanta a gidan, babu wanda yake daukan abinsa ya bata dan zumunci sai dai idan ta roka, hatta sabulun wanka da wanki sai ta roka za'a bata.
Da safiyar ranar da zamu tafi Inna ta dauko wasu kudi ta bude hannu na ta saka min, nace "kudin menene wannan?" Tace "kudin sadakin kine" na kalli kudin ina jujjuya sannan nace "me zanyi dasu?" Sai tayi murmushi tace "ki sayi wani abu dasu, duk abinda kike so" a hankali nace "ni babu abinda nake so Inna, ni yanzu babu abinda nake tunanin zai saka ni farin ciki, Sadauki shine farin ciki na kuma a yanzu bana jin zan kuma ganinsa har abada" sai na bude hannunta na saka mata kudin nace "ki karbi wannan kudin inna dan Allah ki dauki Asma'u ku bar gidan nan. Ki koms gida ki samo masu rabon gado su fitar wa da Ummah gadonta a gidan mu ki danka a hannun yaya ladi ko Sadauki. Misali in aka fitar masu da dakunan Ummah sai su fitar da kofa daban. Dakunan ki kuma zaki iya saka yan haya a ciki ke kuma sai ki zauna a dakunan Baffa. Kinga kudin hayar zaki iya wani abu dashi sannan kuma zaki samu security yafi ki zauna ke kadai. Kudin nan kuma dubu hamsin sai ki kama sana'a dasu, idan ba zasu isa ba sai ki siyar da kayan dakin ki ko na dakin Baffa ki kara. A yanzu abinda zai sani farin ciki inna shine in ganku a farin ciki" sai naga hawaye yana fita daga idonta, tayi sauri ta goge tace "Diyam. Ni a tunani na abinda nayi miki shine dai dai, amma na rasa me yasa na kasa jin farin ciki a zuciya ta" sai ta dawo min da kudin hannuna tace "bazan karbi sadakin ki ba Diyam. Ki ajiye su, wata rana zasu yi miki amfani" nace "to Inna zaki tafi din?" Nan ma sai ta girgiza kai tace "ba zaki gane ba Diyam".
Sai nayi shiru ina kallonta, sai nayi realizing wani abu, ba wai gidan Alhaji Babba ne bata son bari ba but she is not strong enough to stand on her own, tana bukatar shoulder da zata jingina da ita. Na tuna cewa a kauye aka haife ta a can kuma ta girma ba tare da tayi karatun boko ba, sannan aka aura mata Baffa ya raho da ita kano ya ajiye ta a gida. Tunda na taso ban taba ganin inna da kawa ba, babu wanda ta sani sai Mama da Aunty Hafsa sune kawayenta, in dai Inna ta fita unguwa to in ba gidan su ba to gidan Alhaji Babba ko kawu Isa, gaba daya rayuwarta tayi revolving ne around them. Wannan ne ya kara banbanta ta da Ummah tunda ita Ummah tayi karatu a hannun Alhaji Bukar dan haka ta waye sosai tayi kawaye. Wannan yasa yanzu it will be hard for Inna ta tsaya da kafafuwanta, ko kuma tayi challenging Alhaji Babba. Maybe nan gaba.
A ranar da muka koma gida ni da uwani sai naji gidan yayi min wani iri, kuma nasan hakan yana da dangantaka da sanin da nayi cewa ina da ciki, twins, cikin Saghir. Da dare sai na bude balcony din da yake hade da palon sama. Na tsaya na lunshe idona ina jin dadin iskar da take kadawa, na bude idona naga sky ta cika da stars ga wata ya zama full. A hankali nace "Sadauki where are you?" Sai na tuno abinda ya taba fadamin "You Are The Only Star In My Sky" na shafa marata ina tunanin babies din da suke ciki amma sam banji wata soyayya tasu a raina ba. I can give anything to have them taken away from me. Da Sadauki na shirya haihuwa, dashi na shirya rayuwar aure. Da Sadauki nayi wannan plan din, dashi na shirya zanyi rayuwar aure har in samu ciki har in haifa mana ya'ya. Mace mukayi fatan zamu samu daga farko sai mu saka mata subay'a sunan yar tsana ta, daga nan sai mu haifi namiji mu saka masa sunan Baffa mu kira shi da Junior.......... Ya Allah take my life please, ya Allah end my suffering please. Sai na rike railers din gurin na durkusa ina kuka a hankali. The first tears da nayi shading tun first night dina a gidan.
[2/2, 8:57 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Thirty Two and Three : The Lost Treasure 1 & 2
Sai da nayi kuka na mai isa ta sannan na tashi daga gurin na dawo palo, sai naji zuciyata tayi min dadi dan at least na dan samu relief na zafin da take yi min. Na zauna a kujera ina karewa kayan gurin kallo, kayan da aka ce an siya min with my father's life time earnings. Sai na tuno da yadda kullum Baffa da Sadauki suke fita tun safe suna aiki a gareji basa dawowa sai magrib basu da weekend basu da public holidays kullum cikin aiki suke. Na hango yadda Sadauki yake dawowa a gajiye kayansa duk bakin mai ya bata su inyi tayi masa dariya. Na tuna sanda yake bani labarin filinsa "anan zan gina mana gidan mu ni dake Diyam". Na lunshe idona a hankali nace "Allah ya isa".
Washegari su Rumaisa suka zo, a lokacin ne suke gaya min cewa anyi hutun first term, sai na samu kaina da tambayar kaina 'ko yaushe za'a saka ni a makarantar da akayi min alkawari? Nasan in nayi magana ma yanzu cewa za'ayi ga ciki kuma wacce makaranta zan shiga sai dai in bari sai na haihu.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar min cikin kunci da bacin rai, ga kuma laulayi daya sauko min a lokaci daya, bani da damar inci abinci sai na amayar dashi. Baba son kamshi kwata kwata kona turare ko na sabulu, ga kadaici. Inda Allah ya taimake ni ina tare da uwani wadda take taimaka min sosai dan kusan duk aiyukan gidan ita take yi, sannan tayi min girkin duk abinda nace inaso, wani lokacin kuma ina gama ci zan shiga toilet in amayar dashi gaba daya sannan in dawo ince mata wani nakeso daban. Uwani tana daga cikin mutanen da bazan taba manta alkairin su ba.
Ciki na yana wata biyar, amma in ka ganshi zaka dauka yayi bakwai saboda girma. Lokacin kuma laulayi na yayi sauki sosai. Sannan kuma a lokacin ne muka sake komawa scanning ga mamaki na muna hanya sai ga wayar Alhaji Babba yana cewa da Mama wai a duba masa sex din babies din. Ina jin Mama tana mita "shi Alhaji Babba wai har yanzu ba zai dauki ishara akan wannan son yaya mazan nasa ba? Shin Saghir ba zai zamar masa darasi ba?" Ni dai bance komai ba amma a zuciya ta ina ta addu'a "Allah kasa mata ne, ya Allah kasa mata ne" amma muna zuwa doctor ya duba ya kalleni yace "congratulations, you are having twin boys" na runtse idona, it is official, bani da sa'a a rayuwa ta. Sai kuma nayi sauri nayi istigfari akan sabon da nayi.
Tun a asibitin Mama ta kira Alhaji Babba tayi masa albishir, ai kuwa daga nan direct gidansa yace a kawo ni ya ganni. Muna zuwa muka wuce part dinsa muka same shi zaune a palo shida Hajiya Babba muka gaishe su, yace "Diyam ba dan bani da isassun kuda de ba da kasar waje zan fita dake ki haihu a can. Amma yanzu ma ina saka ran wasu kudade, indai sun samu kafin lokacin haihuwar ki to duk kasar da kike so nan za'a kaiki ki haihu" Hajiya Babba tana ta washe baki tayi min godiya ni kuwa ko ci kanka bance masa ba. Sai ya dauko wasu kudi a envelope ya miko min yace "nasan masu ciki da kwadayi. Gashi kya ringa siyan abinda kike so" nayi godiya har zamu tashi sai kyma ya tambaye ni "kuna waya da mijinki kuwa?" Na girgiza masa kai da sauri ina mamakin tambayar, ni da bani da waya kuma banma san number din Saghir ta yaya zamuyi waya dashi? Amma sai na fahimci wani abu, suma kansu basu san inda yake ba so suke suji koni na sani.
A gurguje muka shiga muka gaishe da Inna, sai na ajiye mata kudin da Alhaji Babba ya bani muka tafi.
A ranar da daddare har na kwanta sai naji yunwa, kuma uwani ta riga tayi baccinta dan haka dole na tashi da uban cikina na sauko kasa. Na karanto adduoi na kunna fitilar palo sannan na shiga kitchen na dauko cornflakes na fara hadawa kawai sai jikina ya bani ana kallona. Nayi saurin juyawa na kalli bakin kofa kawai sai idona ya sauka akan Saghir, ya harde hannaye a kirji ya jingina da kofa ya zuba min ido. Cup din hannuna ya zame ya fadi kasa, na ruga a firgice zuwa back door din kitchen din na bude jikina yana karkarwa na fice daga gidan na rufe kofar ta waje, ban tsaya anan bama sai na kara mai sai dana dangane da katangar gidan sannan na tsaya na toshe bakina da hannuna ina numfashi sama sama, na jima ban tsorata ba irin ranar. Sai da hankali na ya dawo jikina sannan na fahimci a inda nake sai kuma wani sabon tsoron ya sake shigata na koma wajen building din da sauri, na leka tagar kitchen sai naga babu kowa, na zagaya ta gaban gidan na leka palo shima babu kowa sannan babu mota wannan yasa na sauke ajjiyar zuciya. Wato mutumin nan har ya fara yi min gizo kenan ko?
Duk da tsoratar da nayi saboda abu irin na mai ciki sai dana karasa hada cornflakes dina sannan na koma sama na sha a daki na wanke bakina nayi addu'a nayi kwanciya ta a raina ina cewa "aniyar Saghir ta koma kansa". Dasafe kamar kullum bayan na gama karatu na da azkar dina na tashi uwani muka fara gyaran gida tare, muna yi muna hirarrakin mu har muka gama da sama muka dauko kasa, dama mun saba indai mukayi wannan saukowar kuma to sai dare zamu sake hawa dan anan kasa muke wuni. Tana cikin mopping ninkuma ina goge tv kawai sai mukaji motsi kamar ana saukowa daga sama, muka kasa kunne a tare sai kuwa muka tabbatar lallai saukowar ake yi dan haka muka fa eeèra rige rigen neman gurin buya sai kawai ga Saghir ya sauko. Yaci kwalliya kamar kullum, sai kamshin turare yake yi, nayi sauri na buya a bayan uwani ina jin tsanarsa tana karuwa a raina. Kallo daya yayi mana daga ni har uwanin ya cigaba da tafiyar sa zai fita daga palon, sai kuma naga ya tsaya ya juyo yana kallona, amma vani yake kallo ba cikin jikina yake kallo, na saka hannayena na rufe cikin dasu, sai ya juyo ya doso inda nake tsaye yazo daf dani ya tsaya, ya kalli cikin yace "meye wannan?" Na tattaro duk sauran rashin kunyar da take tare dani nace "oho, nima bansan menene ba" muka tsaya muna kallon kallo, ya tsare ni da ido ni kuma naki cire nawa idon daga cikin nasa. Uwani tana gefe tace "kyautar Allah ce, kyautar da babu wanda zai baka sai shi. Sai a karba kuma a gode masa" bai kyalleta ba yace min "so this is your plan ko? Wannan shine abinda kika shirya dan ki zauna a gidan nan?" Na girgiza kaina nace "believe me, a zuciyata bayan kiyayyarka babu kiyayyar abinda tafi karfi irin ta abinda yake ciki na, and one day, ranar dana haifesu a ranar zan baka kayanka and then it will be my turn to run away" ya hade rai yace "su?" Na daga gira daya nace "yes, su biyu ne" ya sake kallon cikin sai kuma ya kalleni yace "Allah ya kaimu. Ranar da zaki bani su din" ya juya kamar zai tafi sai kuma ya tsaya ya juyo yace "ohhh, and I didn't run away kamar wani marar gaskiya, tafiya ce ta same ni" sai daya fita daga palon sannan na sauke ajjiyar zuciya saboda tunda ya tsaya kusa dani na rike numfashi na saboda tsoro da kuma kamshin turarensa da yake kokarin sakani amai.
Uwani ta fara jera min wa'azi. Ba'a yiwa miji haka, namiji shi tarairayarsa akeyi da kalamai masu dadi, hakan shine zai siya miki martaba a idon shi. Nace "shi kuma fa, menene zai siya masa martaba a nawa idon?" Ta bini da kallo kawai ta rasa amsar bani. Na leka ta window ina hangoshi har ya je gate, naga yayi magana da mai gadi sai kuma ya fita daga gidan a kafa. A raina nace "ina motar?".
Bai dawo ba sai dare, ina kitchen ina wanke wanke naji shigowar sa ya haye sama ya shiga dakinsa. Sai ga uwani ta shigo kitchen din tace min "mijinki ya dawo, maza ki zuba abinci ki kai masa" na bita da kallo kamar wadda tayi saɓo. Taga bani da niyya sai ta zuba ta dora a tray tace inje in kai masa. Na dauka kamar gaske na tafi, naje kofar dakinsa na ajiye dai dai bakin kofa a raina ina addu'ar yana fitowa yayi tuntube dashi ya bata kayansa. Sai na shiga daki na na dan zauna kadan dan kar taga na koma da wuri sannan na dawo gurinta.
Haka muka kasance for about a week. Ko magana ta fatar baki bata hadamu kuma kullum d sassafe ya ke fita sannan ya dawo da dare, kuma kullum sai uwani ta saka ni na kai masa abinci ni kuma sai in ajiye a bakin kof inyi tafiya ta, ranar nan naje ina ajiye abincin sai ya bude kofar, na maze nayi kamar wucewa nazo yi shi kuma ya hade rai yace "ke, zonan" na tsaya ina kallonsa yace "ubanwa kike jerawa abinci a bakin kofa kamar dakin bera? Nan an gaya miki gurin ajjiyar abinci ne?" Nayi shiru still ina kallonshi. Yayi tsaki yace "ga tsaurin ido kuwa, anayi mata magana tana tsatstsare mutane da ido. Ki dauka ki shigo dashi ciki nace" na dauka nazo na wuce ta gabansa na shiga, first time dana shiga dakinsa, naga wani table a gefe na dora tray din akai ina lura da irin dattin da dakin yayi, kaya a barbaje har kan gado, takeaway packs sun cika waste basket. Na dauke kaina zan fita ya zauna a bakin gado yace "zuba min abincin" naji raina ya fara baci, wata zuciyar tana gaya min in zuba masa abincin aka in fita da gudu. Na bude na zuba masa shinkafa a plate na dauko miya zan zuba yace "mayar, bana cin shinkafa" na daga kafada na mayar da ita na juye na dauki tray na zanyi gaba yace "menene a wancan bowl din?" Na bata rai nace kwadon zogale ne, ni nayi zanci shine uwani tace in zuba maka wai ko zaka ci" sai naga ya dauke kai yana murmushi, sai kuma ya hade rai ya miko hannu yace "bani" na ajiye tray din na dauki bowl din na mika masa. Charaf ya kama hannuna, na saki bowl din ya fadi akan carpet zogalen ya zube, na fara kokawar kwace hannuna da dukkan karfina amma ko zegau, kuma wai hannu daya fa kawai ya saka ya rike ni. Sai da na gaji da kokawa ta sannan na tsaya ina mayar da numfashi ido cike da hawaye, ya gyara zamansa yace "kin gama kokawar?" Na gyada kaina, yace "good, then listen to me. Am sorry for what I did to you ranar nan. I was drunk" nayi noticing yadda ya fadi drunk din as if it is a normal thing, ya cigaba "bama zan iya tuna details of what happened ba, nasan dai kinyi min rashin kunya kuma ke shine problem dinki baki da kunya, I remember you even threatened me with a knife. But har cikin raina ni banyi niyyar tabaki ba saboda kamar yadda na fada wa Alhaji amma yaki yarda, kinyi min kankanta. Yanzu kin yafe min?" Nayi saurin girgiza kaina, yayi ajjiyar zuciya yace "maybe later. But look on the bright side, babies, har guda biyu. Ni da bansa ran ko daya ba sai gani da guda biyu. Alhaji yace min boys ne ko?" Ban bashi amsa ba sai yayi dariya, the first time da naga yayi dariya, yace "twin boys, in kika haifi twins din nan kin gama biyawa Alhaji bukatar sa ta duniya, you will be his second favorite person bayan ni" ya saki hannuna nayi saurin ja da baya ina goggoge hannun da hijab dina. Yace "Hajiya tace min SC za'ayi miki at 36 weeks ko?" Na dauke kaina nayi hanyar waje yace "how many weeks ne yanzu cikin?" Sai dana bude kofa sannan na juyo nace "oho, ban sani ba, amma ai zaka iya lissafawa saboda kai kafi kowa sanin ranar da akayi cikin" na juya da sauri na fita ina jinsa yana cewa "still with the rashin kunya ko?"
Tun daga ranar ya dan fara kulani, misali in zai fita zai neme ni yace min ya fita, in ya dawo kuma uwani zata saka lallai in kai masa abinci. A lokacin ne nake lura cewa most of the times a buge yake dawowa gida, ni kuma dana ji wannan warin a tare dashi zan gudu. Duk lokacin zuwa asibiti na, Mama ce take zuwa da kanta ta dauke ni muje bata taba fashi ba, kullum kuma tana gaya min "dan lafiyar ki nake yin wannan abin Diyam ba wai dan yayan cikin ki ba, in an haife su dole zan so su saboda jikoki nane amma a yanzu lafiyar ki tafi su muhimmanci". Alhaji Babba kuwa lokuta da dama da kansa yake zuwa har gida wai yazo ganina ya duba lafiya ta, Hajiya kuma kullum tana cikin aiko min da kayayyakin kwalama wai duk cikin nuna kulawa ne, ni kuwa nasan bani suke yiwa ba abin cikina suke yiwa. Sai na samu kaina da tunanin inba sa'a naci ba yadda suka lalata Saghir haka zasuyi wa duk abinda zan haifa, ni kuwa I can't even begin to imagine myself as a mother of yaya masu halayyar Saghir har guda biyu. A haka har cikina ya kai 32 weeks, and that's when it happens.
Ranar wata laraba, Saghir ya dawo kamar yadda ya saba dawowa ni kuma na zuba abinci na kai masa kamar kullum. Ina shiga dakin naji wannan familiar warin dan haka na tabbatar yau ma a bugensa yake. Na ganshi a kwance daga shi sai singlet da gajeren wando yayi dai dai akan gado, na lallaba na ajiye abincin na juya zan fita kenan sai ganinsa nayi a gaba na yana kallona kasa kasa fuskarsa da murmushi, sannan cikin irin voice din da bazan manta ba yace "wai ke kullum sai ki shigo min daki kina wani lallabawa a tsorace kamar dakin dodo, ko ni dodo ne?" Ban bashi amsa ba na chanja hanya sai naji ya damko hannuna ta cikin hijab dina ya dawo dani baya, na fara kokarin ture shi nace "don't touch me" ya maimaita cikin kwaikwayon muryata "don't touch me, shikenan dai kullum don't touch me sai kace wani abin tabawar ne a jikin nata, bayan bata da komai haka aka kawo ta gidan nan, kirjin ma sai dana mammatso su sannan suka fito" naji hawaye yana bin fuskata, na ture shi na bude kofa da sauri na fita palo amma kafin inyi nisa ya kuma kamo hijab dina da karfi ya finciko ni baya, naji bayana ya amsa da karfi na saki kara. Ya zare hijab din yana cewa "ke dai kiyi ta yawo da wannan dogon abin, ke ko zafi ba kya ji?" Na sakar masa hijab din na durkusa a kasa saboda bayana da naji ya kasa mikewa straight, Sai kuma idonsa ya sauka kan dogon gashina da ya zubo har saman bayana ya bude ido yace "well well well, what do we have here. I always have a thing for mata masu dogon gashi" sai ya nannade hannunsa a cikin gashina ya dago ni tsaye da gashin, naji tamkar fatar kan gabaki daya yake cirewa, ba shiri na saki bayana dana rike na kama kaina na saki kara. Ban kuma jin abinda yake cewa ba saboda azaba sai jin muryar uwani nayi tana cewa "Saghir baka da hankali? Ka sake ta mana, baka ganin halin da take ciki?" Sai kuma ya sake ni, uwani tayi saurin rike ni muka bishi da kallo ya tafi dakinsa yana harhada hanya.
Uwani ta kama ni ta kaini dakina tana yi min sannu. Na durkusa a kasa inajin kaina kamar zai tsage da baya na shima ya rike. Sai naga ta dauko wayarta tana waya amma bana jin me take cewa na dai ji ta ambaci sunana da sunan Saghir. Daga nan baccin azaba ya dauke ni. Sanda na farka cikin dare ni kadai ce a dakin a kwance a kan gado, wani irin mugun ciwon baya ne ya tashe ni nakasa mikewa ma tsaye ballantana in fito in nemi taimakon wani, haka nayi ta murkususu ni kadai akan gado ina karanto duk adduoin da suka zo bakina. Ban samu bacci ba sai da aka fara kiraye kirayen sallah.
Sai da gari ya fara haske sannan na lallaba na tashi nayi sallah, nayi azkar sannan na kuma kwanciya akan sallayar na sake komawa wani baccin. Lokacin dana sake farkawa sai naji ciwon kan ya lafa sosai sai bayan ne har yanzu amma shima ba kamar cikin dare ba. Na fito na duba agogo naga 20:32, nasan already Saghir ya fita dan haka na sauko kasa gurin uwani. A zaune na same ta da jakar kayanta a gabanta ga mayafinta a kusa da ita. Na tsaya ina kallon ta nace "wannan kayan kuma fa? Wanki zaki bayar?" Tace min "zauna Diyam" na zauna a kusa da ita tace "dazu da sassafe mijinki ya shigo nan, yazo ya same ni ya kare min zagi tas wai ni munafuka ce na hada shi da mahaifiyarsa. Yace min in fita in bar masa gidan sa kar ya dawo ya same ni" na mike tsaye zan fara masifa "lallai ma Saghir din nan, yanzu ke din zai yiwa wannan rashin kunyar?" Tace "ni dai abinda nasan nayi shine jiya da naga yana neman halaka ki na kira uwarsa, ni kuma abinda yasa na kira ta shine naga halin da kike ciki wai ko za'a zo a kaiki asibiti ko kuma a turo ma'aikaciyar lafiya ta duba ki, ni bansan me ta kira shi tace masa ba shine yazo yayi min wannan diban albarkar" nace "kira hajiyan to sai mu gaya mata abinda yayi, ita zata san abinda zata yi akai" tace "hmmm. Ai yana fita ita din na kirawo, tunda tun farko ai ita ce tace inzo in zauna din, amma dana gaya mata abinda yace sai cewa tayi in tafi can gidan kawai tunda yace baya son zama na anan din. Tace zata samo wata ta turo miki take kula dake" naji raina ya kara baci, hawaye yana bin fuskata nace "wannan wacce irin rayuwa ce, yanzu ace mutum babu yadda za'ayi yayi abu ba daidai ba a gyara masa sai ya zama laifi. Yanzu jiyan da ace ba kyanan Allah ne kadai yasan abinda zaiyi min. Ni ba zan zauna ba uwani, kina tafiya nima binki zanyi, bazan zan zauna ya kashe ni ba" uwani tace "a'a, ba zaki bini ba Diyam, ina tafiya dake cewa za'ayi nazo na kashe miki aure. Ni dai yanzu in naje zan gayawa mahaifiyar ki halin da kike ciki, itace take da hakkin zuwa ta tafi dake".
Ina ji ina gani uwani ta dauki jakarta ta fita, na raka ta har bakin gate ina hawaye tayi sallama da mai gadi wanda har sun saba dashi sosai, na tsaya ina kallonta har tayi nisa sannan na dawo cikin gida na rufe kofa. Na kwanta akan kujera ina tunanin wannan wacce irin kaddara ce ta hau kaina, wacce irin tarbiyya Saghir zai yiwa yayan mu bayan shi kansa ba tarbiyyar ce dashi ba? Ina nan kwance dai har yunwa ta kamani na tashi na shiga kitchen sai na tarar ashe uwani ta ajiye min dumamen tuwon jiya dan tasan ina so. Na dauko na dawo palo na zauna ina ci kawai naji ciwon bayan ya dawo and this time yafi na dare karfi. Yayi ya lafa ya sake dawowa kamar bayana zai rabu da jikina. A haka azahar ta same ni, la'asar ma tazo, sai dari ya fara duhu. A lokacin ciwon bayan ya hade har da cikina da mara ta. Na lallaba na koma sama ina tunanin wannan wanne irin ciwo ne haka tunda ni dai cikina ai bai isa haihuwa ba ballantana inyi tunanin ko nakuda ce. Bayan nayi sallar magrib ne kuma sai na kasa kofa tashi daga kan sallaya ta saboda azabar ciwo, ban taba addu'ar ganin Saghir ba sai a wannan rana na ringa addu'ar Allah yasa ya dawo da wuri ya kaini asibiti, wannan wanne irin ciwo ne haka? Ga yunwa dan tun tuwon safe ban kuma cin komai ba, ga babu waya a hannuna ballantana in kira in nemi taimako.
Shiru shiru babu Saghir babu labarin sa tun ina duba agogo har na daina. Sai kuma kamar daga sama naji tsayuwar motarsa, na daddafa da kyar na mike amma ina tsayuwa sai naji kamar an bude famfo ruwa yana fita ta kasana, nace na shiga uku ni Diyam fitsari nake a tsaye ko me?
Tun daga yanayin yadda yayi packing nasan cewa yau ma ba kalau yake ba, ina jin motsin shigowar sa palo sannan naji ya hawo sama, sai dai banji ya bude dakinsa ba. Na jima ina tattaro karfina sannan na fara bin bango na fita daga dakin. A palon sama na same shi, ya cire rigarsa ya jefar a gefe, ya kure ac ya kwanta a kan carpet. Da rarrafe na karasa inda yake nayi masa magana "Saghir, Saghir" shiru, na dan jijjiga shi, nan ma babu alamar motsi a tare dashi. Da daga hannunsa naji ya saki. Banbancinsa da gawa shine kawai shi yana numfashi. Na fara kuka "hamma Saghir ka taimaka min zan mutu, wayyo Sadauki" amma da wani ciwon ya sake tahowa sai na nemi kukan na rasa. Lallai wani abin yafi gaban kuka.
Na tuna da maigadi a waje dan haka nayi kokarin ganin ko zan iya zuwa gurinsa ya samo min taimako, duk da cewa ba makota ne damu ba. Amma tashi ya gagare ni, kamar kafafuwana sun daina aiki. Na durkusa na kankame kujera yayinda wani irin nishi wanda bazan iya rikewa ba tazo min, ina ji har dan jaririn ya fito daga jikina, na sauke wani numfashi jikina sharkaf da gumi duk da acn da take palon. Na saka hannu na dauko shi, the smallest most cutest baby dana taba gani a rayuwata. Komai nasa irin na babansa ne except dan karamin ɗagaggen bakin sa da yake irin nawa, nayi murmushi ina jin sonsa for the first time yana huda zuciyata. But baya kuka, baya numfashi, aren't babies suppose to cry in aka haife su? Na jijjiga shi, "wake up little soldier" shiru, na dora bakina akan nasa ina hura masa iska irin yadda naga anayi a film amma shiru, na saka fingers dina guda biyu ina danna masa little kirjinsa shima shiru.
Wani ciwon ne ya sake dawo min, babu shiri na jawo rigar Saghir da ya ajiye na dora babyn akai na koma fagen fama har na haifi dan uwansa. Na dauko shi shima ina kallon fuskarsa, kamarsu daya da dan uwansa kamar an tsaga kara. Na dan jijjiga shi da dan saurin karfin daya rage min sai naga yayi motsi ya danyi kuka kadan sai kuma yayi shiru. Na ajiye shi kusa da dan uwansa ina feeling very dizzy, a lokacin ne na lura da jinin da yake malala akan tiles din palon. Na koma na kwanta kusa dasu a ina kallonsu. And it occurred to me that karshen rayuwata kenan, sai naji dadi saboda ina ganin nayi shahada na samu kyakykyawan karshe, my only regret a lokacin shine mutuwa without seeing Sadauki again.
Not edited
[2/3, 9:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Thirty Four : My Savior 2
Bansani ba ko bacci nayi ko kuma suma nayi, amma cikin either baccin ko suman ne nayi mafarki ina tsaye a cikin cincirindon mutane hannayena biyu a rike da babies dina, hawaye yana fita a idona ina kwalla kiran neman taimako amma kowa yana ta harkokin gabansa babu wanda yako kallo inda nake, can sai ga Sadauki yana kutso kai ta cikin mutanen yana tahowa inda nake amma yawan mutanen da suke gurin ya saka yakasa karasowa sai ya tsaya daga nesa yana miko min hannu, kawai sai na zubar da babies din hannuna na kama hannunsa amma ina kamawa sai ya bace ya barni ni kadai a tsakiyar mutane. Na kwalla masa kira "Sadauki! Sadauki!! Sadauki!!!" Amma bai dawo ba.
Ji nayi ana rirrike ni ana ƙoƙarin kwantar dani yayinda ni kuma nake ta yunkuri ina kiran Sadauki. Na bude idona naga nurses suna tura ni akan gadon marasa lafiya, ga Inna tana biye dasu a baya zani a hannu har suka tura ni wani daki suka rufe kofa, sai kuma naji shigar allura a hannu na, daga nan na koma baccin ko suman ne ban sani ba.
Sanda na kuma farkawa I was feeling much better, dan a hankali na bude idona na sauke su akan ledar ruwan da take sakale a jikin karfe sannan nabi tube din da ya taho daga kasanta da kallo har zuwa inda ruwan yake shiga jikina. Na fara karewa dakin kallo ina kokarin recalling abinda ya kawo ni nan. Idona ya sauka akan Inna da take zaune rashe rashe a dandaryar kasa duk kuwa da cewa akwai kujera a dakin. Kuka take da iyakacin karfinta, sai na tambayi kaina "kukan me take yi?". Abinda na fara tunawa shine kyakykyawar fuskar jarirai na, sai naji wani relief yazo min cewa ban mutu ba at least zan sake ganin su, zan dauko su in rungume su a jikina. Sai naji xewa yanzu na sami wani source of happiness din bayan Sadauki.
Nace "Inna" sai naga ta juyo da sauri gurina tana share hawayenta da gyalenta, tazo ta zauna a kusa dani ta rike hannuna wanda babu ruwan a jiki "sannu Diyam" na gyada mata kai kawai, zuciyata tana so ta tambayeta ina jarirai na amma sai baki na ya kasa furtawa. Ta tambaye ni "menene yake miki ciwo yanzu?" Na rasa me zance mata saboda duk ilahirin jikina ciwo yake yi tun daga kaina har yan yatsun kafata. Na tuna irin wahalar da nasha dan ko a mafarki ban taba tsammanin haka haihuwa take da azaba ba, na tuna mafarki na, sai naji ina jin haushin Sadauki me yasa ya rabu dani in the first place, mai yasa duk sanda nake bukatar sa nake samun bayanan?
Inna ta tashi da sauri ta fita, sai gasu sun dawo tare da wata nurse da tazo tana yi min sannu sannan ta auna bp na ta duba idona da hannuna tace da Inna "har yanzu mijin nata bai zo dawo ba? Yarinyar nan fa in ba'a kara mata jini ba za'a iya rasata, gashi har ta fara kumbura. It is a miracle ma da take a raye wallahi" Inna ta karkata kai "nayi ta kiransa wayar bata shiga wallahi, nayi ta kiran mahaifiyarsa ita ma bata dauka ba, yanzu babu wani abu da za'a iya yi mata kafin kanwata tazo? Tayi tafiya zuwa Abuja ne amma tace min yanzu zasu taho ita da mijinta" nurse din ta girgiza kai tace "gaskiya babu wani abu da zan iya yi mata ni dai, jinin nan dai shi za'a kara mata kamar leda uku first sannan kuma muga yadda za'ayi" Inna ta gyara mayafinta tace "bara in fita in je gidan da kaina" har ta kai bakin kofa kuma sai ta juyo "babu komai idan na tafi na barta ita kadai?" Nurse din tace "babu komai, allurar baccin ma zan sake yi mata. Amma kiyi sauri, in babu kudin ma ki samo maza wadanda za'a iya dauka a jikin su" Inna ta sake kallo na sannan ta fita da sauri. Nurse din tazo kaina tana zuko allura tace "ki godewa Allah yarinya, you are very lucky" tana yi min allurar na tambayeta "ina babies din dana haifa?" Ta girgiza kai tace "ban sani ba gaskiya, ke kadai aka kawo ki nan tun cikin daren jiya" daga nan bacci ya dauke ni ina wandering ina babies dina?.
Sanda ma kuma farkawa Inna na gani tana waya tana kuka "wallahi Hafsa babu ko dari a hannuna a yanzu, gashi suna ta tsorata ni da yana yin jikin nata. Naje gidan babu wanda ma na samu duk sun tafi asibiti gurin Alhaji" naji kamar kaina ya kara nauyi,nayi kokarin daga hannuna naji shi kamar ba a jikina yake ba, eyelids dina ma kansu sunyi nauyi. Na sake cewa "Inna" ta ajiye wayar da take yi ta taho gurina da sauri ta rike hannuna "sannu Diyam, Allah zai dube mu kinji? Allah zai dubi maraicinki ya bamu yadda zamuyi".
Kamar amsa maganar ta sai ga wani doctor sun shigo shida nurse, hannunta dauke da ledojin jini guda biyu tazo da sauri ta fara kokarin dauka min. Inna ta mike "jini? A ina aka samu jini" kana jin muryar ta zaka fahimci wani relief a ciki. Doctor ya juyo yana kallonta yace "ba ke kika kirawo wani dan uwanku ba?" Tayi saurin girgiza kai, "ni ban kira kowa ba, ban samu kowa ba da naje gidan" doctor yace "but baki dade da fita ba wani yazo yace dan uwanku ne, mun dauka ke kika turo shi, yace a debi jininsa, kuma muna aunawa muka ga yayi matching, shi leda ukun ma yaso bayarwa mu muka ce kar ya zama affected shi kuma. Ya biya dukkan bills dinku na gado da kudin magunguna duk mun rubuta masa ya biya har da kari wai ko wani abin zai taso" Inna ta koma ta zauna akan kujera "to waye wannan kuwa?"
Nurse din tace "Halima Usman Kollere dai yace yana nema. Ya shigo nan ma ya tarar tana bacci sai ya fita". Inna ta rasa bakin magana.
Nurse ta gama daura min jinin ta juya suka gama rubuce rubuce ita da doctor sannan suka fita yayin da Inna ta zauna tana ta jera addu'a zuwa ga savior dina. "Allah ya bashi abinda yake so duniya da lahira. Yadda ya bude mu Allah ka bude shi shida zuri'arsa, Allah ya biya shi da gidan aljanna" na gyara kwanciya ta ina kallon window, dare ne, meaning na kwana na wuni kenan da haihuwa. Ina 'ya'ya na?
Washegari sanda na farka naji muryar Mama suna magana da Inna, sai kuma hayaniyar su Asma'u da Muhsina. Na bude ido ina kwallon su, they looked like twins, ina twins dina? A tare suka taho gurina suna rige rigen rije hannuna, nayi musu murmushi ina shafa kawunansu, Mama ta taso itama "sannu Diyam, ya jikin naki?" Nayi gyaran murya nace "da sauki Mama" tayi murmushi tace "naji dadin yadda na ganki, da duk hankali na ya tashi, ai mun auna arziki sosai" Inna tace "gashi kinga har ta fara sabewa, amma jiyan nan duk a kunbure take. Wannan mutumin Allah ya biya shi da aljanna" Mama tace "ni nafi tunanin irin masu bin asibitin nan ne suna taimaka wa mutane, maybe ya tarar ana zancenta shine ya nuna kamar dan uwane, tunda dai kinga yanuwan duk mun tambaya sunce basu bane ba". Ni dai ina jinsu ina jiran inji sunyi hirar jarirai na amma shiru. Tare suka kamani suka tashe ni tsaye, na tashi da kyar ina cije lebe, sannan Mama ta hada min ruwan zafi sosai ta kaini toilet da kanta ta gasa min jikina ta kuma saka na shiga ciki. Muna fitowa take ce da Inna "ashe bata karu ba" inna tace "eh fa, haka nurse tace min. To ai yaran ne baki gansu ba yan kanana dasu, ni ko a bakwaini ban taba ganin masu kankantar wadannan ba" Mama tace "Allah sarki. Allah yasa masu ceton ta ne" gabana ya fadi, na juya ina kallon Mama sai naga duk jikinta yayi sanyi, na saki cup din tean data miko min na rufe fuskata da hannayena. Tayi sauri tazo ta rungume ni a jikinta tana jijjiga ni kamar yarinya "kiyi hakuri Diyam, Allahn da ya baki su shi zai baki wadansu. Kuma yayi alƙawarin aljanna ga duk iyayen da ya karbi ran yayansu suka yi hakuri" na kifa kaina a kafadarta nayi ta kuka, sai naji duk ciwon jikin da naje ji ya barni dan wanda nake ji a raina yafi na jikin ciwo. Sai naji muryar da naji jiya ta cewa ban mutu ba ta koma, naji tamkar rayuwa bata da amfani a gare ni. Na rufe idona ina tuno their cute little faces.
Sai da suka samu na tsagaita da kukan sannan suka saka ni a gaba na basu duk labarin abinda ya faru. Gabaki daya suka dauki salati. Inna tace "amma dai Saghir ya cika makaryaci, cewa fa yayi ita ce ta shiga daki ta rufe kofa sai daya ji shiru ya balla kofar ya shiga ya same ta a haka" na matso hawayen idona nace "wallahi karya yake yi. Shi ya kashe min yara na. Ta sanadiyyar shaye shayensa suka rasa rayuwarsu, bazan taba yafe masa ba wallahi". Mama tace "duniya ce Diyam, ki barshi da duniya ta ishe shi darasi shi da iyayen nasa dukka. Tun yanzu ba gashi nan sun fara gani ba" Nace "me ya faru?" Mama tace "ai daya gama mayen nasa ya farka ya ganku shine ya dauko ku babies din ko cibiya ba'a yanke ba ya taho daku gida a gigice, a nan aka jere wa Alhaji Babba su a gabansa innarki kuma Saghir din ya dauko ta tare dake ya kawo ku nan, dan wulakanci kuma babu wanda yayi kara ya biyo ku su ta yayan da suka riga suka mutu suke yi. Sai gashi Saghir yana kawo ku nan aka kira shi wai kuma gobara ta tashi a kantin kwari, shagunan Alhaji Babba gabaki daya sun kone kurmus babu abinda aka fitar, yanzu dai Alhaji ya yanke jiki ya fadi, hawan jini ya tashi, har yanzu yana asibiti unconscious".
Na karbi tean da Inna ta sake hado min na kurba ina jin zafinsa yana kona min bakina. A raina sai nayi wani tunanin irin hikimar ubangiji da take cikin haihuwar wadannan yaran, sannan kuma na saka a raina cewa mutuwar su tamkar wata sabuwar jarabawa ce a gareni, kuma nayi niyyar yin iyakacin kokarina wajen cinta. Twins dina sunzo sun tafi, ko picture dinsu bani dashi sai wanda nayi saving a memory na, kuma bazan taba mantawa dasu ba har in tafi inda suka tafi.
Kwana na biyar a asibitin na warware sai abinda ba'a rasa ba, sai dai something is bothering me deep inside sai dai na kasa magana a kansa. Ina zaune ina cin abincin da Inna ta zuba min ne ina tunanin yadda rayuwata take, kaddara upon kaddara haka take samu na and I wondered wacce kaddarar ce kuma next.
[2/4, 11:21 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman maama
Episode Thirty Five : A Glimpse
Yan uwa da yawa sunzo sun duba ni kuma sunyi min gaisuwar twins dina. Aunty Fatima tazo har sau biyu ita da yaranta, Adda zubaida tazo itama, sai daga baya sai ga kawu Isa nan yazo shida iyalinsa, sai a lokacin yake tambayar inna nawa ne kudin asibitin? Tace masa kawai an biya shikenan sai ya bar maganar ba tare da yaji yadda aka yi aka biya din ba ko kuma waye ya biya ba.
Da dare sai ga Hajiya Babba ita da wannan sister din tata, amma babu Saghir babu alamarsa, su inna suka karbe su babu yabo babu fallasa sannan suka tambayesu jikin Alhaji. Sunce yana asibiti har lokacin amma yana samun sauki sosai. Suka kawo min maltina da fruits. Na gaishe su sai Hajiya Babba tace "Diyam, banji dadin abinda kika yi ba ko kadan wallahi, kinga abinda ya jawo ko? Garin kiyayyar Saghir an kusa a rasa rayuka har hudu" Mama da dama kamar jira take yi tace "me Diyam din tayi" Hajiya Babba tace "innarta bata gaya miki ba? Saboda bata son Saghir bata son haihuwa dashi shine ta shiga daki ta rufe kanta wai gwara ta mutu ita da yayan baki daya, gashi nan yanzu yaran da basu ji ba ba su gani ba sun rasa ransu, ga kakansu can kuma rai a hannun Allah. Dan ma Saghir mai taurin zuciya ne da har dashi zamu hada muyi jinya" naji raina yana min zafi, hawaye masu zafi suka kawo a idona, na yunkura zanyi magana Inna ta dakatar dani tace "kar kice komai" ta juya gurin Hajiya Babba tace "wannan magana ce da Saghir ya fada, ita kuma Diyam ba haka ta gaya mana ba tace a gaban Saghir ta haife yara guda biyu yana sheka uban bacci, babu irin tashin da bata yi masa ba amma ko motsawa baiyi ba" sai sukayi dariya duk su biyun, yar uwar Hajiya tace "kuma yanzu ku da hankalin ku sai kuka yadda da wannan maganar? Wanne irin bacci ne mutum zaiyi har a haihu a gabansa bai san anayi ba?" Mama tace "baccin wadanda suka sha suka bugu mana? Wadannan kam aiko yanka su zakayi sai dai su farka su gansu a lahira" sai kuma suka daina dariyar, Hajiya Babba tace "Hafsa? Wacce irin mummunar magana ce kike jifan dan dan'uwanki da ita?" Inna tace "ba mummunar magana bace ba, gaskiyar magana kenan. Saghir shayeshaye yake yi, kuma wannan shayeshayen shi yayi sanadiyar mutuwar wadannan yaran. Wannan shine gaskiyar magana" Hajiya Babba ta juyo kaina, fuskarta babu annuri ta nuna ni tace "Diyam sakayyar soyayyar mu gare ki kenan? Sharrin da zaki yiwa dan uwanki kenan?" Na girgiza kai na nace "ba sharri bane Hajiya, in baku yarda da magana ta ba ku je gidan ku bincika, ku duba dakinsa na tabbatar ba zaku rasa kayan maye ba, ku duba motarsa ba zaku rasa kwalbar giya ba, in still baku yarda ba ku tambayi uwani ta baku labarin yadda ta kwace ni rannan a hannunsa wanda shine dalilin fara nakuda ta ba tare da lokacin haihuwa yayi ba, in still baku yarda ba ku tambayi mai gadin gidan, ai yana ganin dawowarsa gida kullum a buge yake shigowa" sai suka hada baki suna tafa hannaye suna salati "kuji yarinyar nan yar karama da ita amma ta iya shirya magana irin wannan? Ku kuma iyayen ta kuka hau kai kuka zauna dan kun zama butulu ko? Duk kun manta irin alkhairin da Alhaji yayi muku amma shine yanzu saboda abinda ya same shi har zaku juya masa baya ku dorawa tilon dansa sharrin shayeshaye? Dan kunga Alhaji iftila'i ya fada masa shine zaku juya mana baya?"
Sai ta kama kuka yar uwarta tana rarrashinta. Mama da Inna duk suka tsaya suka saki baki suna kallonta. Sannan Mama tace "Hajiya saratu in kika ce haka baki kyauta mana ba, da Diyam da Saghir duk yayan mu ne amma dole a cikin su in wani ya kauce hanya zamu fada dan gyaransa ba wai dan bata masa suna ba. Bincike ya kamata ayi kamar yadda Diyam tace, wanda duk aka samu da laifi a cikin su sai ayi masa fada dan ya gyara laifukan sa" sai suka tashi cikin fushi suka fice daga dakin. Mama tazo ta zauna kusa dani ta goge min hawayen fuskata tace "kiyi hakuri Diyam, in dai shayeshaye halin Saghir ne wata rana zai yi ne a gaban jama'a yadda babu wanda zai musa". Ni kam zuciyata zafi take yi min, an jima ba'ayi min abinda ya kona min rai kamar wannan ba, ya Saghir zai kala min wannan sharrin? How can they accused me of killing my own babies?
Washegari da safe Hajiya Yalwati tazo itama, tayi ta bawa inna hakuri wai abubuwa ne suka sha kanta ga Alhaji a kwance ga yara ga gida babu kudi. Sai Inna ta bata labarin yadda mukayi dasu Hajiya Babba jiya, sai tace "dalla rabu dasu, waye baisan Saghir yana shaye shaye ba? Amma su kullum sai su ke nuna kamar ba'a sani ba. Yanzu shima uban da ace lafiyar sa kalau kuna gaya masa zai musa". Da daddare muna zaune Inna tana ta mitar cewa tunda muka zo asibitin Saghir bai ko kira waya ya tambayi jikina ba, bai bada ko kwandala ta magani ba bai kuma nemi yaji inda muka sami kudin maganin ba. Tace "wannan wanne irin aure ne?" Na dauke kaina dan bani da amsar da zan bata. Bayan mun kwanta na yi mata tambayar da take raina. "Inna Sadauki kuwa ko yasan bani da lafiya? Yanzu shi ko duba ni ba zai zo yayi ba ballantana yayi min gaisuwar wadannan yaran? In babu aure tsakanin mu ai akwai shakuwa ko? Shi din tamkar yaya yake a gare ni" sai tayi shiru kamar bata jini ba, sai can tace "Diyam bansan inda Sadauki yake ba. Yaya ladi ma da naje nemanta gidan Alhaji Bukar ance min ta tashi kuma basu gaya min inda ta koma ba" na mike zaune nace "nemanta kikaje yi inna?" Tace "eh, naje nemanta da niyyar in bata gadon zainabu na gidan ku kamar yadda kika bani shawara amma ban same ta ba. Bansan ya zanyi ba yanzu". Nayi ajjiyar zuciya kawai ina wondering what happened? Ina Sadauki? Ko yana bornon? Ya samu admission din kuwa ko bai samu ba? Is he doing well? Na lumshe idona ina hangen fuskarsa a cikin kaina.
Washegari bayan an gama duk tests din da za'a yi suka sallamemu, muna shirin tafiya sai ga mutanen gidan Alhaji Babba nan sunzo, har da saghir, a lokacin ne suka fada mana an sallami Alhajin shima jiya, Hajiya Babba tana ta wani yayyatsina tana bata fuska, shi ogan ma a bakin kofa ya tsaya ya gaishe da Inna sannan yace min "sannu" na tattara shi na bawa iska ajjiyarsa. Budar bakin Hajiya sai cewa tayi "amma Diyam gidan ta za'a mayar da ita ba ko?" Inna ta tsaya tana kallon ta tace "ban gane ba" Hajiya tace "ina ganin abinda yafi shine ta zauna a gidanta, sai a tura wata matar haka take kula da ita kafin jikinta yayi kwari saboda kinga shi Saghir kinga babu dadi a barshi shi kadai a gida ba mace" Inna tace "haka ne" sai ta yafa mayafinta ta kama hannuna muka mike, ranta ya baci sosai. Tace "shi Saghir din yasan yana da matar amma tunda ta kwanta kwana bakwai bai waiwayo inda take ba? Shi Saghir din shin anyi masa fada akan abinda tace yanayi ko kuwa haka za'a kuma daukanta a mayar masa in yaso ya karasa kashe ta? Ina son Diyam fa nima ba wai bana sonta bane ba, ina kawaici ne kawai saboda karfin zumuncin da nake hangowa a tsakanin mu amma kuma kunsan wallahi da mahaifinta yana da rai ko soma maganar nan ma ba za'ayi ba ballantana ayi ta" Aunty amarya tace "haba Amina, yanzu kiri kiri a gaban mu kike nuna Diyam taki ce ba tamu gabaki daya ba, yanzu zumuncin har yakai haka tabarbarewa?" Na juya ina kallon Saghir har yanzu yana tsaye da hannayensa a cikin aljihunsa yana bin kowa dai dai da kallo, naji a raina ni kam ko inna ta yarda da komawa ta gidansa ni ba zan koma ba, gwara in shiga duniya yafi min sauki. Na zame hannuna daga na inna na fice daga dakin.
A bakin gate din asibitin na tsaya ina sharar hawaye, sai ga Inna da saurinta ta rike ni, "Diyam ya akayi kika fito ke kadai? Ina zaki je?" Na sunkuyar da kaina bance mata komai ba. Muna tsaye a waje suka fito, Saghir shi kadai ne a motarsa sai Hajiya tace ya dauke mu, nasan a lokacin da inna tana da kudi da ba zamu shiga motar Saghir ba amma dai haka muka shiga muka zauna a baya mu biyu, yana ta wani bata rai irin shi ba haka yaso din nan ba.
Ina zama na kwantar da kaina na lumshe idanuwana ina tunanin ta inda zan fara neman Sadauki, I just want to see him koda bance masa komai ba. Naji ya tayar da motar, sai naji Inna tace "Yakasai zaka kai mu" nayi saurin bude ido na ina kallonta, a raina nace 'finally' Finally Inna ta yi breaking out of her shell zata yi flying, to kawai yace mata ya dauki hanyar gidan mu. Naji mun tsaya na kuma bude idona sai naga traffic light ce ta tsayar damu a gefen asibitin, na dan sauke glass din windown da nake saboda in sha iska tunda babu ac, kamar daga sama naji kamar an ambaci sunana da muryar da ba zan taba mantawa ba, nayi saurin dago kai amma sai naga su inna kamar basu ji kiran ba, and then I smelled him, wani unique smell wanda daga gurinsa kawai nake jin sa, nayi saurin kallon window na and there he was, Sadauki, yana tsaye da hannayensa cikin aljihunsa yana kallona da budaddun idanunsa. Yayi loosing weight sai naga kamar ya kara tsaho, fuskarsa da kansa suna bukatar aski. Na zauna kawai ina kallonsa as the time froze and my heart stopped. He just stood there looking at me, sai kuma na kwalla masa kira "Sadauki!!" Inna ta juyo a tsorace ta riko ni tana tambayata lafiya, na juyo na kalleta sannan na juya da niyyar nuna mata sadaukin dana gani but ge was gone, as if yayi vanishing.
Kuka nake iyakacin karfina ina kiran sunan Sadauki yayinda Inna ta rike ni take tofa min addu'a, Saghir kuma yana bala'i duk da bana jin abinda yake cewa nasan akan kiran sunan Sadauki da nake yi ne ni kuma ban daina ba.
Manage this please
[2/6, 10:06 PM] +234 818 247 0922: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Thirty Six: Mother's Tears
Har muka je gida ina kuka na, though na daina yi da karfi sai ajjiyar zuciya nake yi. Ina jin Saghir yana cewa "wannan Sadauki dama naji ance dangin mayu ne, tunda kin kwallafa shi a ranki ba dole yake yi miki gizo ba? In kuma da gaske shi din kika gani Allah ya bashi sa'ar yi miki magana in nuna masa shi karamin dan iska ne" daga ni har inna ba wanda ya kula shi wanda hakan ya bani mamaki dan nasan inna bata wuce tayi in dai akan zagin Sadauki ne. A raina nace "kaji Saghir din nan da son a sani gaida uwar saurayi a kasuwa".
A kofar gidan mu yayi packing muka fito, na tsaya ina kallon gidan da yake holding so much memories, good memories, Inna ta dauko key a jakarta ta bude gidan ni kuma na dauko mana jakar mu zan wuce ciki naji Saghir yana cewa "anan zan barku ne naga kuna daukan kaya?" Ban kula shi ba sai Inna tace "eh" daga haka itama bata kara komai ba muka shiga cikin gidan.
Na tsaya a tsakar gida na jingina da bishiya ina karewa gidan kallo, ko ina yayi datti dukun dukun. Inna ta bude dakin ta ta shiga sai ta dauko key din dakin baffa shima tazo ta bude. Cikin dakunan basu yi datti sosai ba. Na zauna akan kujera ina tambayarta "Inna anan zamu zauna ko? Ba zamu koma gidan Alhaji Babba ba ko?" Eh kawai tace min sai ta dauki kayan shara ta tafi ta fara share dakin baffa. Na taso na biyo ta zan taya ta tace "ke da baki da lfy kiyi zamanki kawai" amma sai naki, tana share yana ni kuma ina karkade kurar kan furnitures, a haka muka gama gara cikin daki da palon sa, muka wanke toilet dinsa na palo sannan sai gasu Mama sunzo ita da yammatan ta da yake ranar weekend ne babu school, su suka karasa aikin tsakar gida da kitchen da garage. Dakunan umma kuma aka rufo su muka zauna a palon Baffa muka ci abincin da Mama ta taho mana dashi sannan Mama da Inna suka fita su kace zasu je gidan Alhaji Babba.
Bayan sun tafi ne Rumaisa take tambayata "Diyam, bani labarin yadda haihuwa take, naji Mama tana cewa kinyi kokari kin haifi yara biyu ke kadai babu taimako, ya kika ji?" Na girgiza kaina kawai, ni kadai nasan yadda naji, babu wanda zai gane kuma yadda naji din sai wanda ya tsinci kansa a irin hakin dana tsinki kaina. Ba kuma nayi wa Rumaisa fatan shiga halin da na tsinci kaina.
Sai bayan magrib su Inna suka dawo, sun debo duk kayan Inna da na Asma'u, amma duk naga rayukansu a bace suke daga dukkan alamu ba rabuwar arziki akayi ba. Asma'u ta shigo tana ta tsallen murnar dawowa gida, tace "Adda ina son gidan nan wallahi, nafi son muyi zaman mu anan dani dake da inna".
Washegari muka yi breakfast da yan kudaden da Mama ta bamu da zata tafi, bayan nan kuma sai Inna ta fita can sai gata ta dawo da dillaliya, suka shiga dakinta suna ta cinikin kaya ni dai ban bisu ba, daga baya matar ta fita sai gata ta dawo da maza suna ta jidon kayan dakin inna. Set din gadonta, set din kujerunta, kayan kallon ta kai hatta labulayenta sai da aka fita dasu. Katifar dakin mu ce kawai aka kawo nan dakin Baffa sai sauran tarkace kuma ta saka almajirai suka tattara ta zuba su a dakin soro. Sai aka share dakin kuma aka rufe shi. Naje na leka dakin Ummah ta taga naga yana nan yadda yake ko kayanta ba'a kwashe ba. Da daddare naga Inna ta zauna tana ta lissafin kudi.
Kafin sati ya zagayo mun samu tenants a gidan mu, sai akayi yar karamar katanga a tsakanin mu for privacy. Mata da miji ne da kananan yayansu guda biyu Iman da Saudat, da zasu tare sai sukayi fenti suka hada harda gurin mu suka yi mana. Matar mai kirki, irin masu son shiga mutanen nan ce dan tun da suka zo data gama abinda taje yi zata zagayo gurin mu muyi ta hira, in mijin ya siyo wa yayansa wani abu kuwa sai kiga ta dibo ta bawa Asma'u.
Kudin kayan da inna ta siyar, sai ga Mama tazo ta dauke ta suka fita sai gasu sun dawo da lodin kaya, tun daga kan shinkafa har zuwa ashana, sabulan wanka dana wanki kala kala, har da biscuits da sweets da bobo na yara, ta saka aka buga mata runfa daga gefe ta jibge kayan ni na dauka kayan amfanin mune har ina lissafin watannin da zamuyi muna amfani dasu sai naji ta tura Asma'u duk makotan mu ta gaya musu tana siyar da kaya. Kwanon shinkafa kanon fulawa, har gwangwani daya in kana so zata auna maka, manja man gyada barkono babu abinda Inna bata siyarwa. Ta mayar da Asma'u kuma former school dinta, da yake tsohuwar dalibar suce ba'a siya mata form da uniform ba kawai books aka siya mata sai kudin makaranta wanda a take Inna ta biya, Asma'u tana ta murna. Sai naji dadi dana bata wannan shawarar, na kuma ji dadi data dauka.
A bangare na kuwa tunda muka koma gida kullum sai wata makociyar mu ta shigo tayi min wankan jego, wankan runhu take yi min inyi ta kuka wai zafi amma ni kaina nasan inajin dadin wankan. Sosai na warware na dawo haiyacina karfina ya dawo jikina. Inna kullum tana diban kudi ta siyo min nama ta dafa minmai romo ta saka in chinye in shanye romon, ga tuwo zatayi min da dare da safe ta dumama min. Har addu'a nake Allah kar ya kawo karshen wannan zaman nawa. Amma ina....
Tunda muka zo gida babu wanda ya kara bibiyar mu a cikin yan uwanmu, Saghir ko mai kama dashi ban gani ba, hatta aunty Fatima bata zo ba sai mama ce kadai take ziyartaru tana duba lafiya ta. Ta gaya mana itama duk sun daina kulata kuma suna ta surutun wai dan karayar arziki ta samu Alhaji Babba shi yasa muka juya masa baya, bayan mu abinda yayi mana bayan rasuwar Baffa ya dauko mu ya rike mu ya aurar dani ga dansa mafi soyuwa a gurinsa amma duk bamu gani ba saboda mun zama butulu. Inna tace "Allah ai shi yasan abinda zuciyar bayinsa".
Sai da mukayi wata uku a haka, har na gama wanka duk da cewa na wata biyu akayi min. Ranar nan muna zaune da maman iman muna cin wake da shinkafa sai najiyo Inna tana waya, daga jin sunan data ambata nasan kiran daga Kollere ne, ai kuwa tana gama wa naga jikinta yayi sanyi tace min "Hardo ne. Yace yana neman mu duk a Kollere ranar asabar" tun daga nan naji duk wutar jikina ta dauke. Washegari kuwa dai zazzaɓi. Ranar asabar da assuba Mama tazo tare da driver suka dauke mu ni da Inna muka bar Asma'u a gurin maman Iman. A hanya nayi kwanciya ta a mota trying so hard not to think about what the outcome of the meeting might be.
Muna zuwa muka tarar already su Alhaji Babba, kawu Isa, Aunty Fatima da kuma Saghir suna can. Tun kafin mu gama gaishe da Hardo ya fara fada. "Yanzu wato tun kafin in bar duniya har kanku ya rarrabu irin haka? Har zumuncin ku ya tarwatse har haka? Har son zuciya ta son yayanku ya rufe muku ido kun manta da yanuwantakar da take tsakanin ku? Kun manta da tarbiyyar da ni da inno muka baku?" Ni dai ina rakube dama daga can bakin kofar shiga dakinsa, na hango Saghir shima a can daya end din su kuma iyayen mu suna tsakiya. Sai daya gama fadansa sannan yace a tsara masa abinda ya faru, kawu Isa ne yayi bayanin haihuwata da rasuwar twins da kuma abinda ya sami Alhaji Babba na gobara, duk da cewa duk Hardo yasan wannan, sai kuma yayi bayanin shi Saghir abinda yace da kuma ni abinda nace, ya kara da cewa "mu abinda ya bamu haushi shine yadda Amina ta rufe idonta ta goyi bayan Diyam, bayan kowa yasan tsakanin mata da miji sai Allah babu ta yadda za'a gane mai gaskiya a cikin su. Kawai ta hana yarinyar komawa gidan mijinta ba tare da anyi bincike ba. Sannan kuma ta hada kayan ta ta bar gidan Alhaji Babba a lokacin da yake tsaka da bukatar kulawar yan uwansa, ta koma gidan marigayi ta bude ta kafa zaman kanta. Wannan ne yasa muma muka zare ta daga jikin mu".
Hardo ya hada su gaba-daya ya wanke su, yace da mai gaskiya da marar gaskiya duk a gurinsa masu laifi ne, sannan yace "ni yanzu zan yanke hukunci, sai kuma inga wanda a cikin ku zai nuna min cewa ya girma yanzu yayi ya'ya kuma ni bani da iko akan ya'yansa" ya fada yana kallon Inna data sunkuyar da kanta kasa. Ya nuna ni yace "Haleema" nace "na'am" yace "zaki koma gidan mijinki" na runtse ido hawayena yana zubo wa. Ya dora "uwani zata biku ku cigaba da zama tare kamar wancan karon. Zan gaya mata cewa ta saka ido sosai a kanka kai Saghir ko sau daya ta tabbatar da maganar Halima ni da kaina zan karbi takardar ta a hannunka. Sannan abu na gaba shine zaka saka ta a makaranta, zata karasa karatunta na secondary inta gama kuma in kun daidaita a tsakanin ku sai ta cigaba. Ka fahimta?" Saghir yayi gyaran murya yace "na fahimta Hardo, kuma ina godiya" Hardo ya juyo kaina yace "ke fa Halima? Kin fahimta?" Na gyada kaina, yace "ki bude baki kiyi magana mana?" Sai na bare baki na saka kuka. Nan take ya koreni daga dakin yace in tafi cikin gida.
Anan muka kwana, naga Inna ta dan shiga yan'uwanta suna magana sama sama. Ni kuwa babu wanda na kula ina kudundune ina zazzaɓi. Da daddare wai sai ga kira inje inji Saghir yana waje, na tashi naga duk suna kallona dan haka na saka hijab na fita, na dan tsaya a soro na bata lokaci sai na dawo gida nayi kwanciya ta.
Da safe kowa ya shirya zamu tafi, mukayi sallama da mutan gida ina fitowa waje na hango Saghir a tsaye a jikin motar dasuka zo da ita ya harde kafafu yana kada key, na dauke kaina zan wuce yace "babu gaisuwa?" Na juya baya naga kawu Isa yana kallon mu sai na gaishe shi ciki ciki, ya amsa yana murmushi yace "in kin koma gida ki shirya jibi zan zo mu tafi" na faki ido na jefa masa harara na wuce. A raina nace "munafiki".
Mun koma gida da kwana biyu kuwa sai gashi da safe wai in fito mu tafi. Na koma nayi kwanciya ta Inna tace "tashi ki dauki mayafinki ku tafi, sauran kayanki zan hado miki in aiko miki dasu" na fara kuka, sai ta zauna kusa dani ta jawo ni jikinta tace "kiyi hakuri Diyam, nasan wannan duk laifina ne dan tun farko ni na bada kofa har akayi miki auren nan, yanzu kuma babu yadda zanyi tunda igiyar auren ba a hannuna take ba. Kiyi hakuri kinji?" Sai naga kwalla a idonta, nayi saurin goge hawayena ina gyada kai, ta dauko sabuwar waya a cikin kwalinta da sim card ta miko min tace "tun ranar nan na siyo miki wata. Ki tafi da ita, duk halin da kike ciki ki kirani ko ki kira Hafsa ki gaya mana. Uwanin ma munyi waya da ita tace min itama yau zata je. Ki yi ta addu'a kina gaya wa Ubangiji kukan ki, shi kadai ne zai zaba miki abu mafi alkhairi a rayuwar ki".
A mota na tarar dashi a zaune yana jin kida, na kai hannu zan bude baya sai ya danna lock ya rufe, dole na na shiga gaba yaja motar ba tare daya ce min komai ba. Ina ta kuka na kasa kasa har mukayi nisa muka kusa unguwar sannan yace "wallahi ko kiyi shiru da kukan nan ko kuma in sauke ki a gurin nan" nayi shirun tunda nasan ba karamin aikinsa bane ya saukeni a wajen.
A bakin gate ya ajiye ni, ina fitowa ya ja motarsa yayi gaba. Na shiga gidan ni kadai kamar mayya. Maigadi ya taso ya muka gaisa na bude palo na ganshi kamar wanda akayi yakin badar a ciki, kaca kaca, ga used plates nan ko'ina duk sun bushe. Bedrooms ne kadai masu dan kyau suma bawai gyarawa akayi ba amma dai ba'a bata su ba. Na lura cewa abubuwa da yawa were missing a gidan, daga dukkan alamu kayan gidan su suka koma source of income na Saghir. Na kunna tv naga lafiyar ta kalau,na fara tattara gidan kenan naji a tv an sako wakar Westlife ta coast to coast "my Love"
An empty street, An empty house, A hole inside my heart, I'm all alone The rooms are getting smaller. I wonder how, I wonder why, I wonder where they are, The days we had, The songs we sang together Oh yeah
And all my love I'm holding on forever, Reaching for the love that seems so far, So I say a little prayer, And hope my dreams will take me there, Where the skies are blue To see you once again, my love, Over seas from coast to coast, To find the place I love the most Where the fields are green To see you once again, my love
To hold you in my arms, To promise you my love, To tell you from my heart You're all I'm thinking of. And reaching for the love that seems so far........
Sai naji kamar dani suke a wakar with Sadauki as my faraway love. Na zauna akan kujera na kama sana'ar tawa ta kuka. Ina cikin yi uwani tayi sallama ta shigo, sai na tashi da gudu naje na rungume ta.
Tare muka gyara gidan gaba-daya, sannan uwani ta fitar da kudi daga aljihunta ta bawa maigadi yayo mana cefane mukayi girki. Muna gamawa sai ga Saghir yazo ya zauna a palo suna gaisawa da uwani sannan ya ce min "kawo min abinci" Sai na juya ina mamakin karfin hali irin na Saghir, kai da baka bada kudin cefane ba ina kai ina neman abinci? Ina kallonsa ya dauki wayata ya duba, sai naga ya daddanna ya ajiye. Da dare na fito daga wanka ina shirin kwanciya waya ta tayi kara. Na dauka ina duba number din dan number inna da ta Mama kawai nsyi saving dazu a gurin uwani. Na dauka naji muryar Saghir "ki kawo min ruwa dakina" na ajiye wayar nayi tsaki. Har zan kwanta sai kuma na saka hijab dina na dauko ruwan naje na kai masa. Yana kwance ya kashe fitila ya rufa da bargo, na ajiye ruwan ba tare dana ce masa komai ba. Zan fita yace "Diyam" na juyo ina kallonsa ya nuna kusa dani a kan gado yace "come here" na watsa masa harara na juya yace "kin san dai hakkina ne ko?" Na juyo nace "kai wanne daga cikin hakkokin ka ka sauke?" Yace "ki bani chance ki gani. Kuma nasan so far I have been trying my best" na fara tunanin wanne ne best din nasa. Sai ji nayi yace "zanyi Allah ya isa in baki zo ba" na juya da sauri ina kallonsa nace cikin mamaki "are you for real?" Ya daga kafada yace "bani da wani choice ai, ina bukatar ki kin ki bani, bazan iya miki dole ba so my only choice is to do Allah ya isa, ta rago" na juyo kamar wadda aka saka wa remote ina tunanin yadda aljanna ta take kasan kafarsa amma a lokacin babu abinda nake so irin in shake kyakykyawan wuyansa har sai ya daina numfashi. Na zauna a bakin gado na juya masa baya ina jin hawayena yana zuba a cinyoyi na, ina jinsa ya matso ya zare rigata sannan ya jawo ni zuwa jikinsa, ina jinsa yayi duk abinda yake ganin zai iya yayin da ni kuma kukana yake kara tsananta har ya gama abinsa. Ya sake ni yana mayar da numfashi. Na mike zaune na jawo rigata na saka ba tare dana kalleshi ba na mike sai ji nayi yace "shikenan kuma? Ko dan curdle din nan ma, irin falling asleep together din nan na masu aure babu, na juyo ina kallonsa da kumburarrun idanuwana, yayi murmushi nace "shima in banzo ba Allah ya isan zaka yi?" Yace "well, yes" na juyo na dawo na kwanta. Ya matso da pillon sa kusa dani ya jawo ni jikinsa sannan ya jawo bargo ya rufe mu.
[2/7, 4:27 PM] +234 706 813 0709: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Thirty Seven : Abatcha Motors
Da assuba na tashi kamar kullum, na cire hannayensa daga kaina na mike ina kallonsa yana ta sharar baccinsa, ban tashe shi ba tunda ni dai dama ban taba jinsa ya fita masallaci ba, na tafi dakina na shiga toilet na kunna wa kaina shower wai ko zata sanyaya min zuciya, inna wanke jiki na sai in sake wanke wa in sake wanke gani nake kamar duk Saghir dinne a mammanne a jikina, ji nake ina ma ace zan iya cire fatar jikina in sake wata wadda Saghir bai taba ba? Nayo wanka na na fito na saka doguwar riga ta hijab nayi sallah ina addu'a Allah ya kawo min karshen auren nan, sai kuma na chanja nace idan auren shine mafi alkhairi a gare ni Allah ya cire min Sadauki daga zuciyata ya shiryar da Saghir ya saka min sonsa a raina. Ko da banso shi ba at least in rage tsanarsa hakan zai dan rage min zafin da nake ji a zuciyata.
Ina nan kan sallayata har gari yayi haske rana ta fito, sai naji an bude kofar dakin da nake, na juya ina kallon Saghir daya dau wanka yasa gayunsa kamar kullum sai kamshi yake, ya tako har tsakiyar dakin da takalmin sa a kafarsa yace min "ki zo ki bani breakfast zan fita" na dauke kaina gefe saboda wani takaici da ganinsa ya saka min nace "ka kawo abin breakfast din ne?" Yace "ki duba dakina akwai kayan tea sai ki hada min tea, akwai kuma kwai a kitchen sai ki soya min" daga haka ya fita, na tashi nayi abinda yace na kawo masa palon sama yana zaune yana kallo, na zauna ina kallonsa har ya gama ya karkade jikinsa zai tashi nace "mu kuma fa? Me zamu ci" ya tsaya yana kallona yace "babu abinci a store?" Nace "ka ajiye ne?" Yace "bana son maganar banza in babu kawai kice min babu" nace "ai ka fini sanin babun" yace "ku sha tean mana to, kafin lokacin abincin rana ai zan dawo" yayi hanyar waje nace "in baka dawo ba nima zanyi Allah ya isa" sai kawai ya juyo ya kalleni yayi murmushi ya fita.
Bai dawo ba din kuwa. Haka na samu wata guntuwar shinkafa a store muka dafa fara dama uwani tayo guzurin yaji muka ci da mai da yaji. Bai dawo ba sai dare, daren ma sai bayan mun kwanta kuma nasan maybe yayi hakan ne dan kar inyi masa mitar bai ciyar dani ba. Da safe ina kasa muna gyaran gida sai gashi ya sauko, ya leka wajeya kira mai gadi sai naga sun hau sama tare ya bashi akwati ya sauko dashi kuma daga ganin akwatin nasan da kaya a ciki, akwatin cikin kayan lefe nane. Nabi mai gadin da kallo har ya fita sannan na hau saman muka hadu dashi yana kokarin saukowa nace "wancan kamar kayana naga an fita dasu, ko dai ido na ne?" Bai kalle ni ba yace "aro na dauka, zan siya miki wasu idan wadansu kudina da nake jira sun zo" nace "ko aron ne ai ana tambayar mutum kafin a dauki aron kayansa, kuma ni ban bayar da aron ba a dawo min da abi na" yace "ta yaya zamu zauna da kaya cikin akwati alhalin store din abincin mu babu komai? Ai ba kyauta nace ki bani ba aro ne kuma zan biya ki kin dai san ni ba talaka ba ne ba ko?" Kafin in bashi amsa ya fice. Na shiga dakina na tarar duk ya hargitsa min kaya, kusan duk kayan lefe na masu tsadar ya dauke. Bakin ciki ya kama ni kawai sai na zauna ina kuka, sai na tambayi kaina, wai yaushe ne zanyi farin ciki ni kam, yaushe ne zanyi murmushi, irin geniun smile din nan mai zuwa har zuci.
Ya siyo mana kayan abinci sosai, ya kuma bani 10k ya ce kudin cefane "saura kuma a karar dasu da wuri ace min babu" sauran kudin kuma bansan me yayi dasu ba.
Kwana biyu bayan nan, tunda rana naga yana tayi min fara'a sai nasha jinin jikina, da dare ina kwance a daki sai gashi ya bude kofa ya shigo nayi sauri na rufe idona dama fitila a kashe take, yace "Diyam, Diyam" nayi banza na rabu dashi. Sai ya hawo kan gado na sai nayi juyi na fara munsharin karya, irin wannan munsharin mai kamar kakin majina, sai yayi tsaki ya tashi ya fita. Na gyara kwanciya ta a raina nace "sai dai kaje ka rungumi pillow bani ba" and that got me thinking, this is his second attempt a kaina a cikin sati daya da dawowa ta, amma wancan karon wata na bakwai a gidan sa tun randa yayi raping dina bai kuma kallata da wannan maganar ba, menene ya chanza yanzu? Sai nayi realising cewa da yana da kudi yanzu bashi dasu, meaning da yana iya siya a waje yanzu ba zai iya siya ba, wato wannan shine dalilinsa na yarda da dawowa ta irin ga banza ta fadi dinnan ko? Ni kuma indai haka ne bazan yarda ba sai nasan yadda nayi na karbar wa kaina yanci. Sai kuma nayi mamakin kaina yadda nayi realizing Saghir yana neman mata amma ko a jikina wai an tsikari kakkausa, ko kadan banji raina ya baci ba alhalin ko a yanzu da nake matar wani in nayi imagining Sadauki da budurwa ba karamin baci raina yake yi ba ballantana inyi imagining dinsa yayi aure. I can only imagine yadda Sadauki yake ji a ransa a yanzu da make matar wani, har na haihu dawani. Ko ya yake ji? Ko ya yake coping?
Washegari ya tashi yana ta fushi, ni ko kallo bai ishe ni ba. Zai fita yace "zanyi baki anjima, abokaina ne manyan mutane ne sun takura wai sai sunzo sun ganki. Please don't embarrass me, kiyi musu abinci kuma kiyi shiga mai kyau kisa kayan da zasu kara miki girma". Bai jima da tafiya ba dai sai gashi ya dawo da kaji wai duk ayi musu. Mukayi abinci ni da uwani muka jera a dining, muka gyara gida tsaf yana ta kamshi na tafi sama nayi wanka na saka wata doguwar riga ta atamfa, dama ba kwalliya nake yi ba, na saka hijab nayi sallah ina zaune akan sallaya ya shigo yace "gasu sunzo, kuma please ki cire wannan dogon abin" ya juya ya koma, na tsaya ina tunanin menene dogon abin, doguwar rigar ko kuma hijab din?
Na tashi na gyara hijab dina na bishi, suna zaune a palon kasa kusan su biyar duk irin sa, yayan masu kudi masu ji da kansu. Na zauna a hannun kujera na gaishe su suka amsa, suna tsokana ta wai amaryar da ake boyewa, ina kallon Saghir yana ta harara ta nayi kamar ban ganshi ba sai cewa yayi "kin zo kin zauna kin saka mutane a gaba, ba zaki tashi ki kawo musu ruwa ba?" Na fahimci lallai so yake ya dizga ni a gaban abokan sa ya nuna musu ba sona yake yi ba, ni kuwa bai san yadda nake jin haushinsa yafi yadda yake jin nawa ba. Na mike sai cewa yayi "au ina miki magana ba zaki tsaya ki gama ji ba sai ki wani tashi ko?" Na dawo da baya na tsaya a gabansa nace "wanne daga ciki kake so Saghir? In tsaya kayi min fadan ne sai in kawo musu ruwan ko kuma in tafi in kawo musu ruwan sai kayi min fadan which one will you like first". Kusan gaba-daya suka kwashe da dariya. Ya kasa cewa komai ya tsaya yana kallona, sai na daga kafada nace "abinci yana kan dining, you can serve them in ka gama fadan" na juya nayi hayewata sama. Ni kaina nasan na gama da Saghir, amma kuma shi ya jawo wa kansa, me yasa zaiyi tunanin bara ya wulakanta ni a gaban abokan sa? Ko yana ganin hakan zai kara masa class ne a cikin su.
Ina nan zaune naji fitarsu a motoci sai kuma naji yana hawowa, nasan zuwa zaiyi mu yita amma sai naji bana jin tsoronsa, ya shigo har dakina ya karaso gabana ya tsaya, kawai sai jin saukar mari nayi a fuskata, saboda karfin marin har saida na daina gani for some seconds sannan ya sauke min a daya side din. Sai da naji taste din jini a bakina. Ya nuna ni da dan yatsa "ke har kin isa ki ce zaki gaya min magana a gaban abokaina, me kika dauki kanki ne? Wallahi ki bini a hankali Diyam in ba haka ba watarana sai na kai gawarki gida" Ya juya ya fita.
Na rike fuskata na zauna a bakin gado, bazan iya tuna sanda aka taba marina ba, to ni waye ma mai dukana in banda inna itama kuma mostly a kafa take dukana. Hawaye ya fara bin kuncina ina lissafa irin abinda zai faru da ace da ne wani yayi min wannan marin a gaban Sadauki. Nice kuka har magrib ina tayi, daga yin Sallah kuma sai zazzaɓi mai zafi ya rufe ni. Uwani ta hawo taji ni shiru sai ta tarar bana jin dadi sai ta zauna a waje na har saida Saghir ya dawo sannan ta sauka.
Tun daga ranar ban kuma lafiya ba, yau zazzaɓi gobe amai jibi ciwon ciki. Saghir kam fushi yake yi dani sosai ni kuwa ta kaina nakeyi, bai ma kula cewa bani da lafiya ba ballantana yayi tunanin kaini asibiti. Bayan nayi kusan sati ina jinya rannan uwani tace min "Diyam anya kuwa ba zaki yiwa Saghir magana ya kaiki asibiti a gwada ki ba? Ni fa ina ganin kamar juna biyu ne dake" sai naji wani amai ya taso min, naje nayi na gama na dawo nace "ciki fa uwani? Wanne irin ciki kuma?" Tace "ni dai na fada miki, kuma kije a gwada ki gani" sai na hau sama da sauri ina jin kamar labarin mutuwa ta uwani ta fada min, na fada kan gado na kama kuka, na shiga uku ni Diyam, sai na fara addu'a "Allah ka dube ni Allah, Allah kasa kar maganar uwani ta zama gaskiya" amma kuma nasan rabo na da period tun ina gidan mu, ga kuma abinda ya faru ranar dana dawo.
Ina nan kwance Saghir ya hawo yana kwalla min kira, na tashi na same shi a tsaye a kofar dakinsa yace "ki shiga ki gyara min dakina" na wuce shi na shiga na fara harhada uban lodin kayansa duk daya barbaza a dakin, ga zazzaɓi gashi jikina babu kwari saboda amai. Shi kuma ya tsaya a kofar dakin ya harde hannayensa yana kallona. Na daga wata riga kenan naji kamshin turarensa ya doke ni sai amai, da kyar na karasa toilet na fara karara wa sai ya biyo ni ya tsaya a bakin toilet din yana kallona har na gama sannan yace "baki da lafiya?" Bance masa komai ba yace "me yake damunki?" Nace "zazzaɓi" yace "da amai?" Na girgiza kaina da sauri nace "warin turarenka ne ya saka ni aman" yace "amma ai kullum shi naje sakawa baki taba aman ba sai yanzu. Are you pregnant?" Nayi shiru bance masa komai ba sai yayi tsaki "ke bansan wacce irin mace ba ce ke, daga an taba ki kadan sai ciki" naji wani abu ya tsaya min a kirji na wuce shi na dawo daki ina cewa "tunda dai bani na hau kan kaina nayi wa kaina cikin ba ai da sauki. If you hate me that much ka sallameni mana in tafi" ya biyo ni yana cewa "and who says I hate you?" Na tsaya ina masa kallon kar ka raina min hankali, sai yace "idan da bana sonki Diyam da tuni kina gidan ku wallahi ko dan wannan rashin kunyar taki. Kuma yanzu ko dan wannan samun cikin da ake yi ai ya kamata ki fahimci cewa we are meant to be together. Ki kwantar da hankalin ki muyi rayuwar aure kinki, kin ki cire that Sadauki of a person daga zuriyar ki kuma... " Ban karasa jin abinda zai fada ba na fito daga dakin na koma nawa.
Washegari shi ya tashe ni da safe wai in shirya muje asibiti, muna zuwa ya samu doctorn dana lura kamar sun san juna yace "PT zaka mata Please" sai doctorn yayi dariya ya kira wata nurse ya hadamu muka je tayi min. And it came back positive. A ranar nayi kuka kamar idona zai fita.
Tunda muka koma gida ya tare a dakina yana jinya ta, shine bani magani shine yi min sannu da su hada min tea, ni duk na dauka jinyar Allah da annabi ce sai daya sauke bukatunsa a kaina sannan na fahimci inda jinyar ta dosa.
Kayan lefe dai mun cinye su, babu biya babu ranar biya. Sai kuma yazo ya dauki set din kayan kallo na palon sama ya siyar, daga nan sai set din gadon extra dakin da bama amfani dashi a sama, sai deep freezer. Duk abinda aka siyar daga an dan siyo kayan abinci an dan bani kudin cefane bana kuma sanin inda sauran kudin sukayi. A haka har cikina ya tasa yayi wata biyar.
Ranar nan na shiga kitchen na rasa me zan dafa mana na hawo sama na same shi akwance a gado yana daddanna waya. Nace "babu fa abinda za'a ci a gidan nan" sai ya saka hannu a aljihu ya zaro min yadin aljihun na karkade min ya cigaba da danna wayarsa. Sai na samu kaina da tambayar kaina menene role din Saghir a auren mu? Shi aikinsa kawai shine yayi min ciki? Na shigo ciki na zauna a kan bedside nace "Saghir idan ni da kai da uwani mun zauna da yunwa wannan" na nuna cikina, "bai san babu ba" ya kalli cikin nawa sai ya ajiye wayar yace "to wai me kike so inyi? Ni fa ko kudin man da zan zuba a mota in fita bani dashi, ko so kike a ganni a daidaita sahu ake nuna ni a gari? Ko kuma so kike in ke bin gidajen masu kudi ina cewa allazi wahidi? Ko kuma dako kike so in dauka ko lebura ko kuma aikin mechanic? Na fahimci abinda yasa ya fadi mechanic din, so yaje muyi fada inyi zuciya in rabu dashi amma sai nace "eh, so nake kayi duk abinda ka fada indai zaka samu halak dinka. Wai kai ba kayi karatu bane ba? Ina takardun ka, ka karkade su ka fita kane gurin abokan Alhaji su hada ka da connections din da zama samu aiki. At least if you can't be a good husband try to be a good father".
Bansan ya akayi ba kuma ina daki sai gashi da folder din takardu yace zai je gida ya kaiwa Alhaji, sai kuma yace "in na samo kudi a hannun Hajiya sai in taho mana da wani abun a hanya". Ni dai na rabu dashi a raina ina cewa lallai gata mugun abu. Na tuno Sadauki da rashin zamansa a guri daya, tun yana dan karamin sa Baffa ya nuna masa neman kudi. Sai nayi murmushi ina lissafin irin kudin da Sadauki zai tara in dai ya samu hanya.
Ban kuma tabbatar wa cewa Alhaji Babba ya fada kwata ba sai da muka je gidan few days after that. Mota daya ce a compound din, ita ma kuma daga ganin ta nasan an dade ba'a hau ta ba, komai babu, ni sai naga gidan kamar har wani duhu yayi. Shi kansa ya rame, kayan jikinsa sun tsufa, na gaishe shi ya amsa yana ta yake baki. Muka shiga cikin gida suna ta kallon cikina, Hajiya Babba har da yar min da magana wai da Inna ta hanani komawa bayan ni ina son mijina, ni dai bance mata komai ba. Itama naga dakinta yar aiki daya ce kawai kuma itama na tabbatar yan uwanta ne suka dauko mata. Hajiya Yalwati kam Allah ya taimake ta ƴaƴanta manya su uku sunyi nce sun fara teaching dan haka su suke daukan nauyinta da kannen su. Da zamu tafi su murja suka ce zasu bi mu amma Saghir ya rufe idonsa yace babu wadda zai dauka. Sai da muka dauki hanya ne yake cewa wai nauyi zasu dora masa in suka zo. Sai na tambayi kaina 'ba shine namiji ba, babban wa uba? Bashi ya kamata ya dauki nauyin kannensa ba amma shine mai gudun ciyar dasu na kwana biyu?"
Bayan munje gida yake gaya min "Alhaji ya hada ni da wani abokin sa shi kuma ya hada ni da wani mutum daya bude kamfanin siyar da motoci kwanan nan. Gobe zanje interview kiyi mana addu'a. Idan aikin nan ya fada ko? Hmmmm, ba karamin kudi suke dashi ba a gurin nan kuma kinsan accounting na karanta harkar kudin" ni dai nayi addu'a amma bansa ka rai ba saboda bansa ran zai samu aiki irin haka da wuri ba.
And to me surprise, sai gashi washegari da offer. "I nailed it. Diyam, I got it. Wato managern ne da kansa ya ganni, karamin yaro ne mai babbar harka. Kawai few personal questions yayi min shikenan yace 'you are hired' just like that fa, Diyam you are talking to the financial secretary of Abatcha Motors"
[2/8, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Thirty Eight : Subay'a
Na rike baki ina dariya, ko ba dan Saghir ba ko dan ni kaina da abinda yake cikina nayi murnar wannan aikin. Nace "Masha Allah. Alhamdulillah. Amma fa kayi sa'a, abinda mutane sai su dade suna neman aiki basu samu ba amma kai kaga lokaci daya ka samu" yayi dariya yana zama akan kujera yace "maybe mutanen da kike magana akan su basu san inda ya kamata su nemi aikin ba ko kuma basu dace da aikin ba. Kinsan appearance matters alot a gurin neman aiki, yanzu misali ni, kowa ya ganni yasan na chanchanta da post din dana samu" na zauna ina mamakin bragging irin na Saghir, nace "komai fa a rayuwa yana da lokaci, wadanda basu samu aiki ba lokacin samun su ne baiyi ba, kai kuma daka samu lokacin kane yayi, ita rayuwa....." Ya daga min hannu "don't spoil my mood please. Je ki kawo min ruwa" nayi ajjiyar zuciya na tashi.
Ranar daya fara zuwa office ne bayan ya dawo na tambaye shi "to an baka office? Da fatan sun fara baka aiki kanayi" yace "wanne irin aiki kuma?" Nace "rubuce rubuce mana, ba shine aikin secretaries ba?" Yayi tsaki yace "fin sec fa aka ce miki, ni harkar shiga da fitar kudi a companyn ne kawai part dina, besides, ina da mataimaki so shi zaike handling duk aiyuka" nace "so? Kai menene naka aikin?" Yace "who cares about aiki ne wai, what I care about is the salary kuma zasu ke bani mai kyau shikenan".
Tunda aiki ya samu kuma shikenan Saghir ya koma tsohuwar rayuwar sa, inya fita tun sassafe baya dawowa gida wani lokacin ma har sai nayi bacci. Baya zuwa gida a bige, amma hakan bawai yana nufin ya daina bane ba dan sau da yawa in ina gyaran kayansa nakan ji wannan warin a jiki, sai dai bani da wani kwakwkwaran hujja. Yana ciyar damu, duk da dai considering yadda yake kashewa jikinsa kudi baya yi mana yadda ya kamata amma dai muna cin abinci. Shi kuwa kullum cikin sababbin dinkuna yake yakance "gwara mutum yayi dressing sosai kar a raina masa hankali".
Cikina yana ta girma abinsa, ni kuwa babu komai a raina sai fargaba dan kuwa har yau ban manta da wahalar da nasha a waccan haihuwar ba, gashi wannan cikin duk da cewa daya ne a ciki amma tafi wancan cikin girma, wannan yasa tun cikin yana waya bakwai na tattaro kayana na dawo kasa kusa da uwani kuma kullum ways ta tana kusa dani dan am not looking forward to haihuwa ni kadai irin waccan.
Amma lokacin da muka je scanning tare da Saghir, bayan an gama mun zauna sai doctor yace "am afraid ba zaki haihu da kanki ba, dole za'a yi miki cs ne" duk muka bude baki da mamaki, Saghir yace "ta taba haihuwa fa doctor, twins ma" doctor ya dauko takardar scan din yace "tana da abinda a likitance muke kira da placenta previa. A ka'ida in aka tashi haihuwa ɗa ne a farko sai an haife shi sannan sai mabiyya ta biyo baya. But in her case mabiyyar ce a farko sannan dan, meaning ko da ace ta fara labour to placenta ce zata yi blocking babyn yadda ba zai fito ba so babu yadda za'ayi sai dai ayi delivering through cs" na fara kuka, ni takaicina shine yanzu wai yanka cikina za'ayi a fito da babyn ni Diyam, kai mata munga ta kan mu. Saghir yayi tsaki yace "kuma menene abin kuka a ciki? Ke da ya kamata kiyi murna ma babu ke babu wahalar haihuwa. Sai ni aka bari da wahalar kudi".
Alayi fixing date, a week to my edd sai dai da sharadin in naji nakuda kafin lokacin muyi sauri mu tafi. Na dage kullum da addu'a, na kuma gayawa su inna suma suka tayani da addu'a har Allah ya nuna mana lokacin. Mama ce tazo gidan muka tafi tare, dama Inna tunda nayi aure bata taba zuwa gida na ba. Tun a day to aikin mukaje suka bamu gado muka kwana a can, sukayi duk gwaje gwajen da zasuyi sannan washegari sai ga Hajiya Yalwati tazo daga gidan Alhaji Babba, har aka zo aka gama shirya ni babu Saghir babu labarin sa. Naji duk jikina yayi sanyi. Anzo ance lokaci yayi na dauko waya ta and I found myself dialing number din Sadauki, hoping to hear his voice just once more amma naji a kashe na kashe wayar na ajiye feeling so lonely kanar ni kadai ce a duniyar. Mama da Hajiya Yalwati suna ta lallashina suna min addu'a a haka aka shiga dani.
Aikin mai bacci akayi min saboda jini na yaki karbar na ido biyun. Dan haka duk abinda akayi ban sani ba har aka gama aka fito dani dakin hutawa. Anan ne na dan farka kadan naga Inna a zaune kusa dani ta rike hannuna, gefe kuma Mama da baby a hannun ta "Sadauki" na fada cikin bacci, "inna ki kira Sadauki kice yazo ya duba ni" sai na kuma komawa bacci. Sanda na sake farkawa doctor na gani da nurse a kaina, suka yi min sannu daga nan na sake komawa.
Sanda nayi final farkawa kuma babu kowa a dakin sai ni kadai, na bude idona ina ta kalle kalle ina jin kaina yana ciwo sai na hango Saghir a can kusa da window da alama waya yakeyi. Irin yadda naga yana bada respect ga wanda suke wayar yasa ni son sanin ko wanene saboda ban taba ganin yana magana irin haka ba. Sai daya gama sannan ya juyo, muka hada ido yayi murmushi ya nuna wayar yace "my boss. Ya kira yaji ya jikin ki saboda na fada masa za'ayi miki aiki. Yana da kirki sosai. Can you believe he paid for everything hadda karin kudin ragon suna?" Na rufe idona na dauke kai ina jin haushinsa har cikin raina, wato abinda zai fara fadamin kenan bayan an yanka ni an fito da jaririn daya saka a ciki?
Sai yazo ya dafa kafada ta "am sorry banzo ba tun jiya, I am not good at all this emotional stuff ne shi yasa nayi zamana a gida kawai" sai kuma ya juya ya tafi gurin crib din baby ya dauko yana murmushi, na yi kokarin tashi amma na kasa nace "kawo min, menene?" Yayi dariya "au baki ganta ba? Baby girl ce, so beautiful like her mother" this is the first time daya kirani beautiful. Ya karaso ya sunkuyo yana nuna min ita, and he was right, she is so beautiful but tafi kama dashi because she looked just like twins dina, just ta fisu girma sosai.
Nayi murmushi ina jin attraction so much like wanda naji akan twins. Na daga hannu na shafa kanta ina murmushi, yace "inye, Diyam an zama uwa, sai ki daina yi min rashin kunya in ba haka ba zan saka take rama min" ya jima yana ta surutun sa shi kadai sannan ya mayar da babyn cikin crib dinta ya dauko waya yayi ta daukan ta pictures sannan yazo yayi kissing dina a goshi ya fita.
Four days nayi a asibitin. I was so in love with my daughter naji tamkar na samu another reason to live. Sau daya Saghir ya dawo ya tambayi Inna ko akwai abinda muke bukata, ya dauki daughter dinsa sannan yayi min sannu ya fita, and that was all, ko abinci ba'a taba kawo mana daga gidan Alhaji Babba ba. Wannan yasa ranar da aka sallame mu muka wuce gidan Inna, shi ogan ma baisan an sallame mu ba sai daya kira ni naki dauka sannan ya kira uwani tace ai an sallame mu sai kuma gashi a gidan Inna, wai ai ba'a gaya masa zan zo gida ba, ya gama rashin kunyar sa ya fita. Inna tana ta mitar abin, a raina nace "zabin ki ne dai". Tunda Hajiya Babba taje ta dubani a asibiti bata kuma zuwa ba, shima Alhaji Babba ko leke sai yace ace min baya jin dadi ni kuwa nasan dan mace na haifa ne da namiji ne da ko da rarrafe sai yazo.
Kullum in ana kallon yarinyar nan sai na tuno Sadauki, lissafin mu ni da shi shine mu haifi girl mu saka mata Subay'a, to ga girl din kuma na samu amma bata Sadauki ba, gashi ko sunanta ban sani ba duk da nasan yayi mata huduba gaya min ne kawai baiyi ba. Sai ranar suna da safe ya kirani "anyi radin suna a gidan Alhaji. An saka mata Saratu" sunan Hajiya Babba. Na runtse idona ina jin haushin sunan, nace "Allah ya raya, zamu sami wani sunan da zamu ke gaya mata" yace "already na riga na samu, Subay'a" na maimaita cikin mamaki "Subay'a?" Yace "yes, ko ba kya so?" Nace "no, ina so, a ina ka sami sunan?" Yace "my boss called, ya nemi alfarmar duk sunan da aka sawa baby a ce mata Subay'a, and I see no harm in honouring his wish. Besides, shi ya sayi ragon suna" ya karashe maganar yana dariya. Na kashe wayar ina mamakin me yasa boss dinsa zai ce a gaya wa babyn mu Subay'a? Inna ta tambayeni suna nace mata sunan Hajiya Babba ne za'a ke ce mata Subay'a, ta maimaita sunan tana kallona.
An dan taru a gidan sunan babu laifi, duk da cewa yan'uwa ne kadai kuma yanuwana da nasa duk daya ne, sannan ni ba kawaye ba ba makota ba, sai makotan mu na nan gidan da suka shishshigo mana. Abincin suna ma Saghir baiyi ba, cewa yayi ai ba shi yace in taho gida ba dan haka wanda ya kawo ni gidan sai yayi abincin sunan. Ragon sunan ma a gidan Alhaji Babba aka yanka aka soya aka kuma raba sai namu rabon aka kawo mana a kwano. Bayan suna Mama tazo ta dauke ni muka je asibiti, ni na dauka wani check up za'ayi min sai naga an saka min wani abu mai kamar allura a dantsen hannuna ashe abin family planning ne aka saka min na shekara biyar.
Satina biyu a gida Saghir yazo yace ai na warke haka, in shirya in koma. Haka ina kuka ina komai na hada kayana dana Subay'a, Allah ma yaso Asma'u tana hutu nace tazo mu tafi, itama kuma tana shiga mota yace da iznin wa zan tafi da ita? And that kept me wondering if I don't have a say in my own marriage. Shin miji shi kadai ne mai making every decision, ita mace bata da nata ra'ayin? Ko kuma ita mace bata da zuciya ne a kirjinta?
Bayan komawar mu gida ne nayi realizing something, Saghir's weakness lies in his daughter. Yana son Subay'a sosai da sosai dan zan iya cewa yana sonta fiye da komai a duniya. Kullum tana hannunsa sai dai in baya gida ko kuma in zanyi feeding dinta. A lokacin ne kuma aka fara daukan sabon session na makaranta, a lokacin yan set din mu zasu shiga ss3. Nayi wa Saghir maganar komawa ta school sai cewa yayi "ita kuma Subay'a fa? Yaya kike so ayi da ita? Sai dai ki bari sai wani session din kafin nan tayi kwari" sai ya kara da cewa "in kuma kafin nan kin kuma samun wani cikin shikenan" ban mayar masa da magana ba saboda bai san zancen implant dina ba, haka na hakura da zancen makaranta dan babu yadda zanyi, in nace zan kai kara ma bayan sa za'a bi ace in bari yarinya ta tayi kwari.
A lokacin ne kuma yake sanar dani cewa ogansa zai tafi kasar waje karatu "he will be managing the company from there, kin san komai yanzu an mayar dashi computerized ballantana manyan harkoki irin na wadannan mutanen" nayi kamar ban ji shi ba dan ni har na gaji da maganar ogan nan, kullum oga this oga that, oga yace kaza oga yayi kaza, I wonder me suke yi a office din bayan zaman hira.
Manage this please. Ina dan busy ne kwana biyu but I promise you a sweet episode tomorrow insha Allah.
[2/9, 9:39 PM] +234 706 813 0709: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Thirty Nine : The Boss
Bayan Shekara Biyar
Shekaru biyar suka zo suka wuce. A cikin su abubuwa da dama sun faru, na farko Hardo da Uwani duk sun rasu sati daya a tsakaninsu, Hardo ne ya fara rasuwa munje Kollere zaman makoki itama uwani ta kama jinya sannan ta rasu ranar sadakar bakwai dinsa. Naji mutuwar Uwani sosai kusan fiye da yadda naji ta Hardo.
Rayuwata a gidan Saghir babu abinda ya chanza sai abinda ya kara gaba, ya dawo da shaye shayensa, ya kuma mayar da neman matansa openly wanda da yana dan boyewa amma yanzu kiri kiri yake yi musamman tunda kudade suna shigo masa, har gida mata suke zuwa neman Saghir, tun yana yi min karyar cewa abokan aikin sa ne har ya daina. Lokuta da dama kuma yana dora min laifin neman matansa, yace nice na gaza sauke masa hakkin sa shi yasa yake zuwa yake nema a waje wanda ni kaina nasan ina da laifi ta wannan bangaren, nayi nayi in tursasa zuciyata ko yayane in saka Saghir a cikinta amma taki yarda, Sadauki ya riga ya chika duk wani lungu da sako na zuciyata yadda babu wani bugawar da zata yi wanda babu tunanin sa a ciki. It was so hard living with a man while my heart belongs to another. Another din da ban ma san inda yake ba, babu amo babu labarin sa daga shi har yaya ladi. Sometimes sai in samu kaina da tambayar ko wanne hali yake ciki? Ko ya samu admission din yayi karatun? Ko rayuwa tana tafiyar masa dai dai ko kuma akasin haka?
Amma kuma hausawa sunce idan bera da sata daddawa ma da warinta. Ina da laifi a zaman mu da Saghir na sani amma shima ai da laifinsa, at least da ace yana treating dina well da ko ban so shi ba bazan ki shi ba, da zan iya managing in faranta masa as long as nima yana faranta min amma Saghir was doing total opposite of faranta min. Tsawa, hantara, bakar magana and occational duka duk ina samu daga gurin Saghir. Yana ciyar dani, barely, dan duk ranar dana ganshi da leda a hannu ko kuma naga yana yi min murmushi to nasan wani abun yake nema a gurina ni kuma a lokacin zan tayar da tawa tsiyar har sai mun rabu baran baran.
Na koma makaranta bayan na yaye Subay'a, shima da kyar Saghir ya bari har saida na hada shi ta Hardo lokacin yana da rai sannan ya saka ni a wata government school anan bayan layin mu. Na fuskanci challenges da yawa a lokacin musamman saboda kasancewa ta matar aure a makarantar yan mata, kuma duk yan class din na girme musu dan ma bani da girman jiki dan haka da wahala ma ka gane shekaru ma, babu kuma wanda yake yarda nina haifi subay'a musamman saboda tana da girma sosai ita. Har nuna ni ake yi, ni kuwa sai naja kaina gefe nayi facing karatuna kadai wannan yasa har na kammala banyi wadansu kawaye ba sai dai gaisawa kadai.
Inna tana ci gaba da kasuwancin ta, dashi suke ci, sha da sutura ita da Asma'u kuma dashi take biya wa Asma'u kudin makaranta, ta gaya min cewa tunda ta bar gidan Alhaji Babba, kaf yanuwan Baffa babu wanda ya taba daukar kwandala ya bata yace ki siyawa Asma'u ruwa, komai ita take yi musu wani lokacin ma harni take dan dinkawa kaya ta aiko min dashi tunda nawa mijin ba mai yi bane ba. Zai dai dinkawa kansa suttura kamar banza, yayi ta shiga yana fita, mayukan shafawarsa da turarukansa ma kadai abin jinjinawa ne amma ni kayan kyalliya tun na lefe na, da suka kare da wahala yake siyamin wani abu dana yi maganar kayan lefe na ma sai cewa tayi "da uban waye ya siya miki kayan?".
A lokacin da nayi candy a lokacin nake da shekara ashirin da daya, Subay'a tana da shekaru biyar. Har lokacin kuma ina nan jiya iyau, babu abinda na kara a girman jiki sai ma kara motsewa da nayi wadda rannan da Inna take mita naji Mama tace yana da dangantaka da planning din da nake yi, maybe in ya barni zan yi kibar. Sometimes Saghir ma da kansa yana complain "Diyam kina da kyau sosai a fuska, mu maza kuma ba wannan kadai muke bukata ba muna son mace mai lady body parts" yana magana yana nuna irin parts din da yake nufi, nakan bashi amsa da "ai bani na halicci kaina ba, dan haka bani zakayi wa complain ba".
Ranar nan nayi bakuwa, Maman Iman, tazo ta wunar min ita da yaranta da Asma'u na wadda ta shiga ss2 yanzu. Sai Maman Iman ta dauko wasu kulle kulle a leda ta jani bedroom dina ta fara tsaramin
"kinga wannan garin da nono zaki ke sha ko da madara, kamar bayan la'asar haka yadda kafin dare ya fara aiki. Shi kuma wannan gumba ce ki adaba kina cin kayar ki a hankali tana da amfani sosai, wannan kuma na tsuguno ne, ki barbada shi a garwashin wuta sai ki tsugunna a kai ya shiga jikin ki sosai"
Nasan magungunan menene dan kusan duk sanda naje gida sai ta bani irinsu, wani lokacin ina fitowa nake zubawa a kwatar kofar gida inyi tafiya ta. Amma sai nace "maganin menene wannan maman iman? Maganin tajika ne ko kuma na mayu" ta harare ne "a'a maganin sihiri ne. Kar ki raina min hankali mana Diyam, kinsan nawa na saka na sayi maganin nan kuwa? Wannan na tsugunnon da kyar ma na same shi shine na raba biyu na kawo miki rabi amma zaki raina min hankali" nayi dariya nace "maida wukar yayata ta kaina. Amma ki tafi da kayanki kar inyi miki asarar kudi dan wallahi ba amfani zanyi dasu ba" na fada ina dora mata akan cinyarta, ta dawo min dasu kan tawa cinyar tace "wallahi ki gwada ki gani, matar data bani ta tabbatar min da cewa indai kika yi amfani da wannan yadda kika san cingam haka mijin ki zai manne miki" nayi dariya na sake mayar mata nace "bana son ya manne min kamar cingam, ki kara akan naki sai abban iman ya kara manne miki kamar superglue" kafin ta bani amsa aka budo kofar dakin da kallo, Saghir ya tsaya yana kallon mu sannan yace "dan wulakanci kinsan ma dawo amma kika yi zaman ki ba zaki zo ki bani abinci ba" Maman Iman ta gaishe shi, yayi mata kallo daya ya dauke kai fice. Na mike nabi bayansa idona blurry with tears, yaushe wannan zubar hawayen nawa zai kare? Indai har nayi baki, ko kuma shi yayi baki, to kuwa tabbas sai ya wulakanta ni a gabansu, shi yasa har banaso inyi baki indai tana gida.
Washegari muna kasa ina taya Subay'a yin homework dinta sai gashi ya dawo daga office. Ta tashi da gudu ta tafi gurinsa shi kuma ya daga ta sama yana juyata suna dariya. Na gaishe shi ya amsa ciki ciki sannan direct ya wuce dining ya zauna ya zaunar da Subay'a a kan table din ya fara zuba abinci suna hira. Na taso na karba ina zuba masa nace "Subay'a sauka ki zauna akan kujera, na hana ki zama akan table ko?" Ta kwabe fuska tana kallonsa yace "ita da gidan ubanta, table din ubanta kuma abincin ubanta" yana fada yana yi mata chakulkuli tana babbaka dariya, garin dariyar har ta zubar da abincin dana fara zuba masa. Nayi ajjiyar zuciya na zagaye su na wuce kitchen na dauko duster nayi clearing gurin, sannan na sake zuba masa wani. Ban mayi mata fada ba dan nasan indai yana gurin to ban isa ba, maybe a karshe ya kare da zagina a gabanta. Sai daya gama sannan ya kama hannunta suka yi sama sannan suka sake saukowa tare, ya chanza kaya, yace min "zan koma office, muna ta shirye shirye oga zai dawo office ranar monday" na gyada kai nace "a dawo lafiya" a raina ina cewa "gyara ya dawo din ai ko ka mayar da hankali gurin aikin" ni nayi mamaki ma da har yau basu kore shi ba saboda sai yayi sati baije ba, na kuma ji labarin cewa company basa yadda da irin wannan kailular.
Ranar Monday din da yamma, ina daki ina karatun novels a waya ina ta murmushi ni kadai ganin yadda mata suke soyewa a gidan mazajen su, sai naji shigowar sa, nayi sauri na boye wayar dan ya hana ni yace anan nake kara koyon rashin kunya. Ya shigo dakin babu sallama kamar kullum, ya karaso ya tsaya a gaban gado da leda a hannunsa yace "ga wannan ki tashi kiyi wanka ki saka, and please kiyi kwalliya mai kyau, in an jima da dare zamuje party" na zauna ina fito da kayan nace "party? Biki ake yi?" Ya zauna a kusa dani yana cire takalmi yace "no, wani surprise party ne muka shirya wa ogan mu a office, manyan ma'aikata duk kowa zai zo da familyn sa shi kuma za'a kira shi as far ana nemansa dinnan da gaggawa sai yazo zai gan mu" yayi tsaki "ni idea din sam bata yi min ba, tunda akace zai dawo kowa sai wani rawar kai yakeyi kowa yana neman gindin zama". Nayi murmushi kawai ina duba kayan. Doguwar riga ce mai dan karen kyau daga gani nasan an saka kudi masu yawa gurin siyan ta kuma ba dan ni aka siya ba sai dan a burge mutane. Nayi wani tunani, I had never been to a party before, what if naje na kwabsa mishi? What if yaje ya dizga ni a cikin mutane?
Kamar yasan tunanin da nake yi sai cewa yayi "but please Diyam, please don't embarrass me a cikin mutanen nan, my entire reputation depends on this, please don't do anything stupid" na mayar da rigar cikin ledarta nace "if it will make you feel better, ka tafi kai kadai kawai. Ni ba saba shiga cikin irin wadannan mutanen nayi ba" ya bude baki yace "salon a raina ni? Ace bani da iyali? Ki shirya kawai muje Allah dai ya kiyaye ni da jin kunya".
Shi ya dauko Subay'a daga islamiyya ya kaita makotan mu inda naje ajiyeta sanda ina school. Sannan ya dawo yace min in nayi sallar magrib in shirya shima zaije ya shirya. Na tashi na shiga wanka kawai naji jikina yayi wani irin sanyi zuciyata tana ta bugawa, ni duk ji nake yi bana son zuwa gurin taron nan nasu gani nake yi kamar wani abu ne zai faru idan naje amma babu yadda zanyi haka nayi wanka na fito, na shafa mai na saka rigar daya kawo min. Golden color ce da akayi mata agon stones na silver, sai veil silver da stones golden. Ina sakawa Saghir ya shigo yana fadan har yanzu ban gama shiryawa ba, sai kuma yayi shiru yana kare min kallo da sakakken baki. "You look really beautiful" na dauke kai ina kallon kaina a mirror, babu abinda na sakawa fuskata in banda kwalli amma ta fito fes tana kyalli, kayan jikina sun kara haskaka fatata, sai naga ya saka hannunsa a aljihu ya dauko wata sarkar gold ya karaso ya saka min a wuyana, sai kuma yayi kissing wuyan, nayi saurin matsawa ina wayencewa da saka yan kunnayen daya ajiye. Ya sake biyo ni ya dauki comb yana taje min gashin kaina zuwa baya sannan ya saka ribbon ya daure min shi a keya side din hagu ya zubo dashi ta kafada ta yana cewa "let's show them abinda matan su basu dashi" Na cire ribbon din ina girgiza kaina nace "babu kyau fito da gashi ga wadanda ba muharramai ba" yayi tsaki, "ke chafsi ne dake wallahi" a raina nace 'naji din' na daure gashina a tsakiya kamar kullum sannan na nannade shi sai nayi rolling veil din irin yadda naga su Rumaisa yammata suna yi. Sai kawai na tsaya ina kallon kaina a madubi, ban taba ganin nayi kyau irin na ranar nan ba. I looked like baby doll din da kullum ake kwatanta ni da ita. Na rike clutch silver sannan na saka silver hills masu tsinin da suka kara min tsaho. Ya tsaya a bayana yana kallona ta cikin mirror yace "perfect, ina ma kin fi haka girma but hakan ma is okay. Am sure babu wanda zaizo da mata irin tawa".
A hankali muke tafiya, kowa da abinda yake zuciyarsa. Ni tawa zuciyar wani irin bugawa take yi wanka har daci naje ji a bakina, a tsorace nake sosai kamar in bude motar in fita a guje. Har muka je gurin, wannan shine karo na na farko da naje companyn Abatcha Motors. Dare ne kuma kusan duk fitulun gurin a kashe suke saboda basa son idan ogan yazo yayi tunanin wani abu, dan haka a lokacin bazan iya adar da komai dangane da yanayin gurin ba, baya muka zagaya mukayi packing, nan naga duk kowa yana packing ana ta fitowa kowa da matarsa ko budurwar sa. Saghir ya juyo ya kalle ni yaga yadda nake a tsorace yace "bafa cinye ki za'ayi ba, just do as i do. Duk wanda kika ga nayi wa magana sai ki gaishe shi, ba kuma cewa nayi ki durkusa har kasa kina gaishe da mutane ba" na gyada masa kai muka fita a tare, ya zagayo ya zura hannunsa cikin nawa muka shiga cikin mutane. Faran faran muke gaisawa da mutane kowa yana introducing matarsa, Saghir proudly yake nuna ni a matsayin matarsa, ina kuma lura da yadda idanuwa suke bina da kallon yabawa. Sai da aka gama gaggaisawa sannan muka zagaya muka shiga cikin building din gaba ki daya, nan ma babu fitulu sai guda daya dan haka dimly kowa ya samu guri ya zauna ana jiran wanda ya tafi tahowa da oga su dawo.una nan zaune ana dan hira kadan kadan suka shigo, sai aka yi saurin kashe fitila dayar da aka kunna gurin yayi duhu daga ki daya. Muna jinsu suka karaso suna yan maganganu. And my heart stopped at the sound of the voice I heard.
Sukayi unlocking kofar suka shigo cikin inda muke, and I heard one of them said "Mubarak let's hurry up and do this. I am kind of tired" clearly in Sadauki's voice. Na zare hannuna daga cikin na Saghir na mike tsaye da sauri "Sadauki!" Na fada under my breath. Sai kuma lokaci daya fitulun gurin suka kama gaba-daya yan gurin kuma suka hada baki wajan ambaton "surprise!!" Then I saw Sadauki a tsaye a gaba na, idanunsa cikin nawa.
Komai ya tsaya min. Numfashi na ya dauke, na saki jakar dana ke rike da ita a hannuna and ikon Allah ne kadai yasa nima ban bi jakar na fadi ba. Sadaukin ne dai a tsaye yana kallona, my Sadauki. But he has changed alot, he has grown more bigger and more muscular, his dark skin shining as brightly as his bright eyes. He looked more matured, more handsome, more confident and he looked rich. Very rich.
In a flash of second aka zagaye shi, kowa yana kokarin yi masa magana hakan yayi blocking view tsakanin mu, "what is Sadauki doing here?" Shine tambayar dana fara yiwa kaina a lokacin da numfashi na ya dawo jikina. Maganar Saghir da naji a kusa dani ita ta dawo dani hayyacina har na tuna me ya kawo mu gurin, but banji mai yaxe ba saboda voice dinsa sound so faraway kamar daga miles yake yi min maganar, the only sound da yayi filling kunnena shine na Sadauki yana gaisawa da mutane. Na girgiza kaina, trying to clear my head nace "me kace?" Tsaki kawai yayi, ya kama hannuna muma muka shiga mutanen da suka zagaye Sadauki suna gaishe shi tare dayi masa congratulations na kammala karatu. "karatu?" Na tambayi kaina. Menene hadin Sadauki da gurin nan wai? Mu ba zuwa mukayi mu taya ogan su Saghir murnar dawowa daga karatun sa ba? Ya naga kuma anayi wa Sadauki murna?
Ban samu amsar tambaya ta ba na ganmu tsaye a gaban Sadauki ni da Saghir, Saghir ya mika masa hannu yace "congratulations Mr Abatcha, and welcome back to Kano" sukayi shaking hands, nabi hannayen nasu da kallo sannan na sauke ido na akan Sadauki, trying to digest what I was beginning to understand.
Mintsini Saghir ya sakar min a hannu sannan cikin whisper yace min "for God's sake stop staring at him and greet him" sai kawai nabi Saghir din da kallo ba tare da nace komai ba, kamar daga sama naji muryar Sadauki yace "Hello Madam" na juya ina kallonsa, sai naga kamar ya saka wani mask ne yayi hiding Sadauki na, kamar this man is not the Sadauki I knew, this man is Mr Abatcha.
[2/10, 8:57 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Forty: The Masked Man
"Madam?" Na maimaita cikin kokonton abinda kunnena yaji min. Sai ya dauke idonsa daga cikin nawa ya wuce mu ya tafi gaban taron ya daga murya yace "Thank you, all of you. I really appreciate this surprise party and I am really surprised" ya danyi dariya, "but I am sorry I can not stay, I have something really emergency that I need to do. You guys should go ahead and enjoy yourselves. Thank you ones again" sai na juya da sauri yayi hanyar waje, abd without even a second glance at me ya fice daga building din. Da sauri organizers din partyn suka bishi a baya, ciki har da Saghir, nima sai na samu kaina da binsu a baya, hoping to see him again, to talk to him even dan in tabbatar cewa da gaske shi dinne kuma da gaske bai gane ni ba. "Can it be? Ace Sadauki bai gane ni ba ni Diyam?"
Ina fita kofa yana tayar da mota, yaci taya ya bar gurin a guje ba tare da ko ya tsaya ya saurari ma'aikatan sa da suka biyo shi a baya ba. Nabi motar da kallo har ya fita daga gate, sai kuma na zame na durkusa a gaban wata flower bed na jingina kaina a jiki ba tare da ko damuwa da menene zai iya fitowa daga ciki ya cutar dani ba. I only wanted to wake up, wake up from this nightmare where Sadauki doesn't know me.
Ina jin su Saghir suka wuce suka koma ciki suna ta maganganu babu wanda ya lura dani, bayan mintina kadan kuma sai aka fara watsewa kowa yana fitowa yana neman shiga motarsa. A lokacin ne kuma naji muryar Saghir ya na nemana "Diyam! Diyam!" Amma na gaza bude baki ballantana in amsa masa har yazo inda nake sannan cikin whisper yace "what the hell are you doing here?" Maimakon in bashi amsa sai hawaye ya fara kwarara daga idona kamar an bude pampo, ya fincike ni ya tayar dani tsaye yana grinning at mutanen da suke wucewa sannan ya kaini mota ya cusa ni ya rufe kofar muma muka fita.
Ba wanda yayi magana har muka je gida, yana packing ya zagayo ya bude inda nake ya fige ni zuwa cikin gida ya jefa ni a kan kujera yace "me kike tunanin zakiyi archiving ne by embarrassing me a cikin mutane? By trying to destroy my carrier? Oga na yana miki magana ki wani tsaya kina kallonsa kamar statue? Sannan kuma ki fito ki zauna a cikin flowers are you nuts?" Na dafe kaina da hannuna, ni ihun da yake min ji nake kamar zai tsaga min kaina gida biyu. Har yanzu kaina yaki budewa balle in yi tunani. Farkon abinda nake so in fahimta shine me Sadauki yake yi a gurin aikin su Saghir? Kuma har nani suna addressing dinsa as if shine manager dinsu daya dawo daga karatu suka shirya masa party. Can it really be? In kuma har ya kasance haka ne to how comes? Ni dai Sadaukin dana sani sanda muka rabu seven years ago bashi da komai, kuma shekaru biyu bayan rabuwar mu Saghir ya samu wannan aikin then how comes Sadauki yayi kudin da har zai bude companyn motoci a cikin shekara biyu? Bayan wannan kuma shin sun gane juna ni suke playing ko kuma suma kansu basu gane ba? Anya kuwa Saghir zai karbi aiki a gurin Sadauki in har yasan shine? Sai wani tunani yazo min, as we were growing up ni da Sadauki, bazan iya tuna ranar da Saghir yaje gidan mu ba, lokacin ma shi kusan kullum baya kasar. And Sadauki was never allowed to enter gidan Alhaji Babba tun yana dan karamin sa har sai sanda naje nake shigo dashi a boye and even then basu taba haduwa ba. So what I was sure of shine basu san faces din juna ba.
But, me yasa Sadauki zai yi acting kamar bai sanni ba? He did looked surprised akan party din but he did not act surprised to see me there, meaning yasan dangantaka ta da Saghir. And then many things started to become clear to me, sunan subay'a, aikin Saghir. Tabbas Sadauki ya gane Saghir bayan yayi masa tambayoyi a gurin interview wannan shi yasa ya dauke shi aiki even with his pass certificate and lack of experience, kuma shi yasa har yanzu ba'a kori Saghir ba daga aiki duk da negligence dinsa. But why? Ina son insan me yasa Sadauki yayi haka? Is my Sadauki still behind the mask of Mr Abatcha?
Sai bayan na dawo daga tunani na nayi realizing har lokacin Saghir fada yake yi. Na tsaya ina kallon sa ina realizing cewa he had no idea mai ya faru a gurin nan. Shi kawai fada yake na wulakanta ogansa. Nayi gyaran murya nace "Allah ya baka hakuri. Ni ba'a saba cemin Madam bane ba shi yasa na kasa amsa masa. Amma kayi hakuri, nan gaba in ance min madam zan amsa" na mike zan hau sama yace "ina jakarki?" Sai lokacin na lura bata hannuna nace "ta fadi a gurin" nan kuma sai ya koma fadan yar da jaka "tunda bake kika siya da kudin ki ba ai dole ki yar" ni dai nayi wucewa ta sama na barshi a nan.
Ranar yadda naga rana haka naga dare. All I wanted to do is to see Sadauki again and ask him tons of questions da suke zuciyata.
Exactly a week after that. Muna palo ni da Subay'a ina kokawar yi mata kitso tana ta zillo tana kuka Saghir ya sauko daga sama. Ya saka hannu ya dauke ta daga cinyata ya suka hau kujera yana warware mata kitso dayan da da kyar na samu nayi mata shi. "Tunda bata so sai a rabu da ita, ke waye yake takura miki yanayi miki kitso in bakya so?" Ban ce komai ba danni yanzu bana cikin mood na musu da Saghir. Yace "wato idan Allah ya yi mutum shi mai sa'a ne a duniya to bashi da wani sauran stress kuma a duniya. Kinga a office dinmu tun daga dawowar oga yadda ake ta rububi ana shishshige masa kowa yana so ya kafa kansa, ni kuwa babu abinda ya dame ni dasu aikin gaba na kawai nake yi. Amma kinsan ina daki kawai yayi kirana a waya, wai dan Allah in an jima inje airport in dauko shi zai dawo daga Maiduguri, kinsan dan can ne ai, babarbare ne" na cigaba da harkokin gabana looking uninterested, Amma kirjina lugude kawai yake yi nace "hmmm, Allah ya taimaka" ya danyi shiru sai kuma yace "I have an idea, tunda kowa neman shiga yake a gurin oga why not me? Nima ai ina son promotion din. Idan na dauko shi daga airport nan gidan zan kawo shi, you prepare dinner for him tunda dama bashi da aure kuma bashi da gida a hotel yake zama, nasan zaiji dadi, in ya ci abinci anan sai in kaishi hotel din da take zama" na yi saurin juyo wa ina kallon sa, sai na samu kaina da girgiza kaina nace "no" no matter how much zuciyata take son ganin Sadauki nasan ba dai dai bane ba, shigowar sa cikin gidan aure na ba abu ne mai alfanu ba "Please ka zarce dashi inda zai sauka kar ka kawo shi nan" ya mike tsaye yana kwantar da Subay'a da tayi bacci a hannunsa yace "yes, nan zan kawo shi first. Zan fita in yo miki cefane and you cook something nice for him, abincin da kika san mutane irin sa zasu ci" kafin in sake retaliating ya fita. Na zauna a gurin na dafe kaina kirjina yana bugawa da karfi, wata zuciyar tana gaya min cewa in gaya wa Saghir waye ogan sa wata kuma tana hanani har sai na samu Sadauki munyi magana na fahimci inda yasa gaba tukunna. But yaushe zan same shi? Ni a matsayina na matar ma'aikacin sa? Ni a matsayina na wadda yayi addressing as Madam?
Ina nan zaune har Saghir ya dawo da ledoji niki niki ya shiga kitchen ya ajiye, ya fito yace "ga nama can da kayan miya da fruits, akwai wani abu da kike bukata kuma?" Na langwabar da kai "ni yanzu mai zan dafa masa?" Yace "think of something, nima ban sani ba". Daga haka ya fita ya barni.
Sai dana kai Subay'a islamiyya sannan na dawo na shiga kitchen, na saka ledojin a gaba ina kallo, me zan dafa? Kuma wai Sadauki zan dafa wa abinci a matsayin sa na ogan mijina. Lallai life is full of twists and turns.
Sai na tuno da tuwon Ummah da take yi mana muna yara ni da Sadauki. Tuwon laushi miyar yauki sai ta dagargaza kaza a ciki ta cire kashin gaba daya. Sadauki yana so sosai dan har cewa yake yi ayi dan haka na nutsu na fara shirya masa. Na gyara fruit din nayi smoothie na saka a fridge. Zuwa magrib na gama na shirya komai a dining table sannan na fita na dauko Subay'a sai kuma na sake gyara gidan na saka turaren wuta naja subay'a muka hau sama.
A sama nayi wanka nayi mata wanka itama muka yi sallah tare sannan ta kwanta ina yi mata kitson da taki tsayawa ayi dazu, a haka har tayi bacci sannan naji shigowar mota, gabana ya yanke ya fadi na kalli window amma wani barin na zuciyata yace "kul kika leka kallon haramun" sai na kwanta na dunkule a guri daya kamar mai zazzaɓi, naji an tsayar da motar an kuma bude an fito sai dai ba'a rufe ba, naji ina son in san me yasa ba'a rufe din ba. Na jawo pillow na dora a kaina na danne da hannayena amma the next second sai gani na nayi a bakin window a bayan labule ina leka waje.
Saghir na hango a tsaye a bakin mota yana magana dana cikin motar wanda shi bai fito ba, sun jima suna magana a haka, kamar na cikin baya son fito wa yayin da Saghir yake ta insisting akan sai ya fito. Sai kuma naga ya zuro kafafuwansa ya fito Saghir ya rufe masa kofar sai suka jero a tare suka doso cikin gida, yayinda fitilar gaban gidan ta haske min su.
Two men; one fair and the other one dark, fair one din shine mijina amma ni zuciyata dark one din take so; one taller than the other ni kuma tall one din nake so, one younger than the other ni kuma younger one din nake so, one frowning the other one smiling ni kuma me frowning din nake so, one employer the other one employee ni kuma employer din nake so. But the other one is my husband. That was how cruel my was.
For a split second, Sadauki smiled, a smile that went straight to my heart, nayi saurin sakin labulen naja da baya kamar wadda ta taba wuta. Ji nayi kamar an debo wani tarin sonsa cikin trailer an zuba min a zuciyata sai naji tayi min nauyi dan haka na ruke kirjina na zauna akan gado ina ambaton sunan Allah da niyyar ya kawo min dauki a cikin lamari na tun kafin inyi tabewar da zata kaini ga halaka.
Waya ta ta fara ringing, da kyar nayi karfin halin dauka na kara a kunnena Saghir yace ina whisper "mun shigo. Ki zo ki kawo masa abinci" nace "dan Allah Saghir ka bashi kawai, bana jin dadi wallahi" nasan banyi rantsuwa akan karya ba saboda yadda nake jin jikina tabbas nasan akwai zazzaɓi a tare dani, yayi tsaki ya katse wayar. Na koma na kwanta na jawo Subay'a jikina na lullube mu, amma muna fikin kunnena sai yake kokarin zuko min maganganun da ake a palo, wishing to hear muryar Sadauki.
Ina nan kwance kawai naji an hawo saman sai aka bude dakin, Saghir ya shigo fuskarsa kamar zaiyi kuka "Diyam? Me yasa ne wai ke kullum burinki kiga na tozarta a duniya, why?" Na tashi zaune ina girgiza kaina nace "me nayi kuma?" Yace "tuwo. For God's sake tuwo Diyam zaki yi wa wannan mutumin da bana jin ya taba cin sa? Ko ni ba cin tuwo nake yi ba kuma kin sani" nace "cewa yayi ba zai ci ba?" Yace "to ni ina zan iya bashi? Kin san da yadda nayi convincing dinsa ya shigo kuwa kuma kawai sai inkai masa tuwo?" Na tashi na zura jihab dina na fita ya biyo ni a baya.
Yana facing stairs, wannan yasa ina fara sauka na ganshi amma shi kansa yana kasa yana daddanna wayar hannunsa. Na dauke ido na daga fuskarta ina kallon gefe nace cikin wata muryar da naji kamar ba tawa ba "Barka da zuwa" ya dago kai, kallo daya sannan ya mayar da ganinsa kan wayarsa yace "Barka kadai Madam. Ya gida?" Still with the Madam, na fada a raina and my heart hurts. Ban amsa ba na mike naje dining na duba na tabbatar komai yana nan yadda ya kamata sannan na dawo na tsaya ina kallon Saghir da yake ta kokarin yi masa hira nace "ga abinci a table Ko nan za'a kawo muku?" Sadauki ya mike da sauri yace "thank you, zamu ci a can din. Ni am fine ma really, maigidan ki yace sai nazo naci, so I guess I will just have a taste and go" sai kuma ya tafi dining area da sauri Saghir ya bishi a baya, yana zuwa ya dauki plate zaiyi serving kansa sai plate din ya zame daga hannunsa ya fado ya tarwatse, and I noticed that his hand was shaking. Saghir ya kwalla min kira "zo da sauri ki gyara gurin nan" amma kafin in karasa Sadauki ya bar gurin da sauri yayi hanyar waje, Saghir ya kalleni da alamar tambaya na daga masa kafada, sai kuma ya bishi wajen.
Na tsaya da tarin abinci a gaba na ina kallon kofa, so the mask has fallen, my Sadauki is still in there kawai duk pretence ne.
Ina tsaye Saghir ya dawo yace "get a basket ki zuva warmers din a ciki, he is taking it away" naje na dauko na hada masa komai har drink din na rufe, Saghir ya karba yana cewa "Allah yasa ma yaci, wannan mutumi kamar aljanu ne dashi".
[2/12, 6:05 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Forty One: A Stranger in the Dark
Ina jinsu suka fita daga gidan, and some parts of me went with them.
A juya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na koma sama nayi alwala na gabatar da sallar isha sannan na kai kuka na gurin ubangiji na. Bayan na gama nayi shirin bacci na zauna akan gado ina jujjuya waya ta a hannuna, I wish zan iya sanin halin da Sadauki yake ciki, I can't even begin to imagine in dai har son da yake yi min ya kai wanda nake ji a raina a game dashi to kuma tabbas da nice zuciyata bugawa zata yi in fadi in mutu. It hurts so much to meet him bayan shekaru da yawa and not be able to talk to him, to ina ga shi kuma da yake kallona a matsayin matar wani?
Ina nan zaune naji shigowar Saghir, ya jima a kasa sannan ya hawo sama, nayi tsammanin dakinsa zai wuce kamar kullum amma sai naji ya turo kofar dakina ya shigo da tray a hannunsa ya ajiye akan side table ya zauna a kusa dani yana janyo table din gaban mu. "Sarkin yan tuwo gashi nan na debo miki, ko ba zaki ci ba?" Na zuba a plate ina cewa "Nagode" sai naga ya dauko chokali shima nace "au zakaci ne? Bayan baka cin tuwo?" Yace "albarka ta zan saka miki" murmushi kawai nayi zuciyata tana ayyana min abinda yake ransa. Sai da muka gama ci na kwashe kayan na mayar kasa na taho da ruwa da zuba masa a cup na mika masa ni kuma na zauna ina sha a robar ruwan. Sai dana gama na juya naga ya tsatstsare ni da ido kuma nasan irin wannan kallon but not today, I just can't.
Sai na mike zan bar gurin yasa hannu da yawo dani kan gadon, ya jawo ni jikinsa yana mammatsa min kafadu na amma sai nayi saurin ture hannunsa dan ji nake kamar wanda yake doramin garwashin wuta a jiki, kafin in matsa ya saka hannunsa biyu ya juyo dani ina facing dinsa ya jawo fuskata dai dai tasa yana kokarin hada bakin mu, nayi saurin juyar da kaina nace "Please stop, bana so" amma yaki hakura, na fara ture shi kuma yana jawo ni kamar dai yadda muka saba yi duk sanda yazo da bukatar sa, ganin yafi karfina yasa na fara kuka shabe shabe da hawaye ina rokonsa akan ya kyaleni amma yaki, can kuma sai ya sake ni da karfi ya hankada ni baya ya mike tsaye yana kallona da idonsa da fuskarsa da duk suka yi ja saboda bacin rai yace "nagaji, nagaji, nagaji Diyam nagaji. Yaushe ne wai zaki daina guduna? Yaushe ne zamu mori auren mu ni da ke? Tunda akayi auren nan shekara bakwai Diyam in na zauna zan iya lissafa miki adadin lokutan da kika bari na kusance ki suma kuma babu wanda kika kawo kanki kuma babu wanda kika karbe ni cikin son ranki. Ni fa mutum ne, inada jini da tsoka a jikina ina bukatar kulawar matata amma ke na fahimci da dutse akayi taki halittar. Kullum ina bawa kaina hakuri ina ganin kamar zaki dawo hayyacinki amma kin ki, ni Saghir ni da mata suke rubibi na a waje har kawo min kansu suke yi amma ni ne matata take guduna. Na gaji wallahi. Hakuri na ya kai bango" na sauko daga gadon ina goge hawaye na nace "then let me go, mu daina daukan alhakin juna haka nan, auren nan tun farko da aka yi shi ni da kai bama so, igiyar nan a hannunka take, ka saki igiyar ni da kai mu huta da kunan zuciya" sai ya tsaya yana kallo na yace "haka kika ce? To tsaya kiji, lokacin da akayi auren nan ni kaina banyi niyyar zama dake ba wallahi, after what happened on our first night I thought in na sake ki ban kyauta miki ba, nayi niyyar in rufa miki asiri in cigaba da zama dake a haka ina tunanin with time zaki soni. Amma har yanzu kinki sona, kina ganin kamar ban isa ba ko something like that, ni kuma nasan babu macen da ta isa tace bata sona, in na sake ki Diyam kamar kinyi winning a kaina kin nuna min ban isa ba, which is something I won't agree to. Kin san me? Nasan maganin ki. Aure zanyi. I will let you watch as a lady wadda bata kaiki komai ba take away your husband ta marar dani dan lelenta nima in mayar da ita yar lelena a gaban ki, maybe wannan shi zai nuna miki worth dina ki dawo cikin sense dinki" na mike na rike rigarsa cikin rarraunar murya nace "Saghir, ni ban hana ka aure ba, ni ba zan ma damu dan kayi aure ba ka auri duk matar da kake so Saghir but please ni ma ka barni in koma gurin wanda nake so" yace "ohh, wai dama har yanzu baki hakura da yaron nan ba, dama a saboda shi ne kike tayi min wannan wulakancin? Yaron da aka ce min babu wanda yasan inda yake watakila ma ya zama dan shaye shaye ko dan fashi amma ke shi kike so when you already have me?" Nace "so guda daya ne Saghir, kuma Sadauki naje yi wa shi" ya warce rigarsa daga hannuna yace "then you will rot here. Ke da Sadauki sai a mafarki" ya juya ya fita ya barni. Na jingina kaina da jikin bango ina jujjuya kan, sai kuma na zame na kwanta a gurin akan dandaryar tiles. Ina ji hadari ya hado aka fara ruwan sama mai karfi, tiles din dana ke kai ya dauki sanyi amma na kasa tashi ballantana in koma gado in lulluba, ji nake jikin nawa bashi da wani amfani dan haka lullube shima bashi da amfani. Anan assuba ta same ni, sai da akayi assalatu sannan na tashi da jan kafa na shiga toilet na dauro alwala na gabatar da sallah ina kara kai kuka na a gurin ubangiji na dan nasan shi kadai ne zai iya yi min magani, nasan yana gani na yana kuma jina kuma nasan bai manta dani ba dan yafi kowa sona.
A ranar na tashi da mummunar mura da tari, kuma nasan hakan yana da dangantaka da kwanan da nayi akan tiles. Na shirya Subay'a da kyar, na sha magani na kwanta daga nan kuma sai zazzaɓi ya rufe ni. Daga nan sai ciwo, zazzaɓi ciwon kai mura da tari amma Saghir ko leko inda nake baiyi ba ballantana yaga halin da nake ciki duk kuwa da cewa na tura subay'a ta gaya masa yafi a kirga. A haka nayi ta ciwo na, da kansa yake shirya subay'a ya kaita school kuma ya dauko ta yasiyo musu abinci suci kayansu. Ni kuwa sai naji yunwa tana neman illata ni zan tashi insha tea in koma. Har na kwana biyar a haka.
Ranar Thursday na kira Inna na roke ta ta turo min Asma'u tayi min weekend dan ta dan taya ni wasu abubuwan, na gaya mata bani da lafiya ne. Friday sai gasu sunzo har da Inna, wannan shine zuwan inna gidana na uku tunda nayi aure kuma duk duba ni take zuwa yi in bani da lafiya. A kasa muka zauna dan bata taba hawa sama in tazo, tana tayi min mitar yadda duk nabi na kara ramewa tana cewa me yasa banje asibiti ba? Ni kuma sai nayi shiru kawai dan ina ganin fada mata cewa Saghir ba zai kaini ba bashi da amfani tunda nasan ko tayi masa magana ba zai ji ba sai dai kawai ranta ya baci. Sai kuma nayi tunanin ko ingaya mata zancen Sadauki? Sai dai bani da tabbas din yanzu menene ra'ayinta akan Sadaukin bansan yadda zata dauki kasancewar sa a matsayin ogan Saghir ba. Na dai san tana nemansa akan gadon Ummah na gida dan haka dole zan gaya mata amma ba yanzu ba, sai na samu damar magana dashi tukunna first.
Asma'u ce ta tashi ta gyara min gidana tsaf, har dasu turaren wuta, sannan ta shiga kitchen tayi mana girki muka hadu muka ci tare harda Subay'a. Sai naji dadi sosai, maybe ciwon nawa harda rashin wanda zanyi wa magana da kuma yunwa. Ana yin la'asar Inna tayi sallah sai ta tashi ta fara shirin tafiya. Na fara mita "Inna daga yin la'asar? Ki bari mana sai kamar karfe biyar haka sai ki tafi" tace "uhm uhm, wannan gari na damina yanzu sai kiji ruwa ya sauko. Bana son mijinki yazo ya same ni a gidan nan" muka yi tayi mata dariya ni da Asma'u dan mu a gurin mu kamar babu komai dan sun hadu, ita kuma al kunya ce irin ta fulani.
Ai kuwa kamar ta fada da bakin mala'iku sai ga ruwan sama ya sauko, da yake muma daki babu wanda yasan ma da hadarin sai kawai zubar ruwa mukaji. Inna ta fara salati mu kuma muna dariya "yau kwana ya kama Inna a gidan Adda" inji Asma'u, Inna tace "kwana bai kama ni ba, ai komai dare ruwan nan in ya dauke sai na tafi gida, balle ma ba lallai ne ya kai daren ba". Wasa wasa ruwa har magrib, har isha yin sa ake kamar da bakin kwarya, Inna ta shiga dakin kasa inda Asma'u ta gyara dan anan take zama duk sanda tazo gidan saboda basu fiya shiri da Saghir ba, anan tayi sallolinta duk muka zauna muna hira ita dai tana ta bacin rai. Nace "Inna ki bari idan Saghir ya dawo sai ya kai ki a mota tunda ba kya son kwana" ta girgiza kai "ni da bana son ma yasan nazo? Bazan shiga motarsa ba. Allah ya tashe mu lafiya sai in tafi da safen".
Na dauki Subay'a muka tafi sama saboda naji dadin jikina sosai, na tafi da niyyar inyi mata wanka nima inyi, Asma'u kuma ta tafi kitchen tana gyara abinda muka bata. A lokacin Saghir ya dawo, yaga motsin Asma'u a kitchen sai ya leka, yana ganin ta yace "ke! Yaushe kika zo gidan nan?" Ta dan tsorata saboda bata san shigowar sa ba tunda shi dama ba sallama yake yi ba, ta gaishe shi sannan tace "dazu muka zo duba Adda, ni da Inna" yace "ita Addan taki ce tace muku bata da lafiya? ina gwoggon take?" Ta nuna masa daki a ranta tana tunanin yau Inna zata sha kunya in suka hadu da Saghir.
Ya tura kofar ya shiga, Inna tayi saurin tashi duk ta diririce saboda ganin sa haka a cikin dakin gashi tana kwance dan ma dai ba kaya ta cire ba, ya tsaya a tsaye yace "gwoggo Amina barka da zuwa, ashe waccan makaryaciyar cewa tayi bata da lafiya?" Inna tace "uhm uhm Saghir ba karya tayi ba, kowa yaga Diyam ai yasan bata da lafiya" ya daga kafada yace "to ai sai kuzo ku tafi tun kafin dare ya sake yin nisa kuma" Inna tace "mu tafi kuma?" Asma'u data shigo tace "dare ai ya riga yayi, ballantana daren damina? Anan zamu kwana da safe Inna zata tafi ni kuma zan zauna sai sunday" ya girgiza kansa "no, kuzo ku tafi yanzu. A Kano ai dare baya yi ko sha biyu kuka fita zaku samu abin hawa" ya ciri dari biyar ya ajiye a kusa da Inna "gashi ku hau adaidaita" ya juya ya fita.
Suka tsaya cirko cirko suna kallon juna, Asma'u tace "hamma Saghir bashi da mutunci Inna, bara inje in gayawa Adda tayi masa magana, yanzu ina zamu fita a wannan unguwa tasu duk kango? Ga shi har yanzu yayyafi ake yi" Inna ta girgiza kanta, "kar ki gaya mata. Dauko mayafin ki mu tafi. Allah yana nan ai shi zai kaimu gida lafiya" Asma'u bakin ciki ya ishe ta, Inna ma wani irin zafi zuciyarta take yi mata amma bata son gaya wa Diyam, shi da yayi din ai yasan ba dai dai bane kuma Diyam sai dai ta bata ranta kawai amma ba zata hana shi abinda yayi niyya ba, tasan ko bare Diyam ta aura ba zai musu wannan wulakancin ba ballantana ɗan yayanta, ɗan yayan mijinta. Ko Sadauki Diyam ta aura ba zai wulakanta Inna ba.
Mayafan su kawai suka dauka, lokacin karfe goma har ta gota Asma'u dan bakin ciki ko kayanta bata dauka ba suka fita ni ina can ban sani ba, ga duhu ga yayyafi anayi ga uban sanyin da yake kadawa. A bakin gate suka yiwa maigadi sallama, yace "Hajiya tafiya a cikin ruwan nan? Ku bari mana sai da safe ko kuma ayiwa mai gidan magana ya kaiku a mota" Asma'u tace "maigidan ai shi ya kore mu kuma yafi kowa sanin yana da mota".
Hanya duk ruwa ya kwanta haka suka ringa haskawa da wayoyinsu suna tafiya karnuka suna tayi musu haushi, babu alamar mutum ballantana abin hawa har suka fita bakin titi. Suka tsaya suna ta karkarwar sanyi amma babu abin hawa babu alamun sa. Asma'u ta fara kuka "Inna mu koma mu gaya masa bamu samu ba. In baya son mu kwana a gidan sa ba sai ya kaimu gida a mota ba? Ai muma muna da gidan ba'a titi muke ba" Inna dai bata ce mata komai ba. Can bayan sun gaji da tsaiwa sai suka fara tafiya a kafa suna saka ran maybe in sunzo round din yan kaba zasu samu adaidaita a can, ko babur ne ma in suka samu hawa zasuyi in dai zai kaisu gida. A lokacin sha daya na dare har ta wuce. Suna cikin tafiya ne wata mota ta tsaya a bayansu, suka juyo suna tunanin ko taimako ne tazo musu amma sai ji suka yi anyi musu fito, daganan suka gane yan iska ne dan haka suka kara sauri. Aka sake biyo su a baya aka ce "yan mata ji mana" Inna ta kankame hannun Asma'u suna sauri kamar zasu tashi sama amma sai motar ta sha gabansu, aka haske musu fuska da fitila sai wani yace "ashe ma tsohuwa ce da yarinya. Kyakykyawar yarinya" Inna ta tura Asma'u bayanta a lokacin da maza biyu suka fito daga motar. "Haba baba, Menene na boye ta? Rage mata hanya kawai zamuyi fa" dayan yace "kema in kina so sai mu rage miki hanyar amma a boot" suka kwashe da dariya sannan suka yo kan su Inna a tare. Da gudu su Inna suka diba, Asma'u tana gaba inna tana binta a baya mazan suna binsu a baya, daya yace "kunga tsohuwa ita ma ta iya gudu? Lallai itama da sauranta ashe". Basu yi wani nisa ba suka cimmasu suka kama su, Asma'u tana ta ihu, Inna tana ta rokon su su rabu dasu "me muka yi muku yaran nan? Ku sake ta dan Allah marainiya ce" daya yace "nima maraya ne, kinga mun dace kenan".
Sanda suke tisa keyar Asma'u cikin mota ne wata mota ta hawo ta bayan su a hankali, har ta gibta kuma sai tayi reverse da sauri ta tsaya. Asma'u ta fara kokawa dan ta samu karfin ganin taimako yazo mata wannan ya hana su tayar da motar har na cikin bakuwar motar ya fito da sauri ya taho gurinsu. Wanda yake rike da Asma'u ya fara zarowa daga motar yayi masa naushi biyu take sai ga jini a gaban rigarsa. Ba shiri ya sake ta ya shige motar, wanda yake seat din driver yayi saurin tayar da motar dan yana gudun karbar nasa rabon suka bar gurin a guje. Asma'u ta fadi a gurin tana mayar da numfashi cike da tsoro sannan ta juya tana kallon wanda ya taimaka mata, sai taga Inna ma shi take kallo amma maimakon tsoro mamaki ne kawai a rubuce a fuskarta. "Sadauki?" Ta fada da rawar murya "Sadauki!" Asma'u ma ta fada, tabbas, wannan fuskace da baza ta manta ba duk kuwa da cewa rabon data ganshi tun tana shekara tara a duniya yanzu kuwa shekarar ta goma sha shida. Sai ta mike da gudu ta tafi ta rungume shi. "Yar Asama" ya fada yana rabata da jikinsa, fuskarsa dauke da murmushi.
Ni ina can ina yiwa Subay'a wanka naji shigowar motar Saghir, har na gama yi mata wankan na shirya ta nima na shiga nayi na fito na tarar har ta yi bacci na shimfida sallaya na tayar da sallah, sai dana idar sannan na sauka dan in tabbatar su inna basa bukatar komai kafin in kwanta, amma sai naga dakin ba kowa, kitchen ma haka. Wasa wasa na chaje gidan amma babu su babu alamun su, hankalina ya fara tashi na koma sama na dauko waya da niyyar kiransu amma naji ance min "your account is not sufficient to make this call" bank da kudi, da zan kira Inna jiya ma ranta nayi a network dina. Hankalina in ya kai dubu duk ya tashi a lokacin dole na tafi dakin Saghir da sauri na fara buga masa kofa. Ya bude ya tsaya yana kallona nace "su Inna, ban gansu ba, ka bani aron wayarka dan Allah in kira su" yace "sun tafi gida. Ni nace su tafi. Da iznin waye kika gayyato min mutane zuwa gidana?" Na fara girgiza kai na saboda mamaki nace "mutane? Su Inna da Asma'u ne mutane?" Yace "ohh, aljanu ne ba mutane ba?" Ban jira sauran maganar saba na shiga dakina da sauri na dauko hijab dina, nayi hanyar stairs, nima gidan zan bari tunda har zai iya ya kori uwata daga gidan nan toni zaman me zanyi a cikin sa? Da sauri naga yazo ya wuce ni ya riga ni sauka, ban fahimci me yake yi ba sai dana ganshi a bakin kofar fita daga pallon, ya saka key ya rufe kofar sannan ya juyo ya wuce ni hau stairs yana kallona yace "nasan in na ce miki in kika fita a bakin auren ki da sauri zaki fita tunda abinda kike so kenan".
Na bishi a guje ina ihu "ka bude min kofa Saghir, ka bude min kofa nace" sai ma ya shiga dakinsa ya rufe kofa ya rabu dani. Na dawo kasa da sauri ina neman hanyar fita amma babu, duk windows din gidan akwai burglers a jiki, kofar kitchen ta baya kuwa dama tun ina amarya data lalace har yau ba'a gyara taba mun dai a amfani da ita. Sai na kama kuka ni kadai kamar mahaukaciya ina zagaye gidan. Ji nake a raina gwara in kwana a titi a ranar akan in sake kwana a gidan Saghir. A haka har karfina ya kare na zauna na jingina kaina da jikin kujera ina ajjiyar zuciya. A raina ina aiyana abinda zanyi wa Saghir in wani abin ya samu su Inna.
A lokacin ne waya ta tayi kara, nayi saurin dauka na duba naga sunan Inna da sauri na amsa nace "Inna me yasa zaku tafi a cikin daren nan? Kuna ina Inna?" A nutse naji muryar ta, hakan ya kwantar da hankali na sosai tace "ki daina kuka Diyam, muna gida mun iso lafiya" nayi ajjiyar zuciya nace "alhamdulillah. Inna hankali na ya tashi sosai" sayi shiru sai kuma tace "Diyam, Sadauki ne ya kawo mu gida. Ba dan Sadauki ba Diyam yau da bansan me zai same mu ba. Sadauki ne ya taimake ni Diyam a lokacin da Saghir ya wulakanta ni".[2/13, 10:26 PM] +234 818 247 0922: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Forty Two: A backlash
"Sadauki?" Na maimaita cikin tsananin mamaki "a ina Sadaukin ya ganku?" Sai ta bani labarin abinda ya faru dasu bayan sun bar gidan. Wannan ya kara ruda tunani na, me Sadauki yake yi a wannan hanyar a wannan lokacin har ya gansu ya taimaka musu? Duk da bansan a wanne hotel yake zaune ba amma nasan babu hotel a kusa damu, sannan unguwar mu wajen gari ne ballantana inyi tunanin ko wani abu ya fito nema kuma ma ai mutane masu kudi irinsa ba zasu fito neman abu ba sai dai suyi order a kai musu har inda suke. Tabbas ina bukatar yin magana da Sadauki. Amma dai ko menene yake yi a gurin am greatful da taimaka musu da yayi saboda I can only imagine irin horror din abinda zai faru dasu da bai zo din ba, wannan kuma sai ya kara hura wutar kiyayya da nake yiwa Saghir saboda shine ya kusa jefa su cikin wannan halin. Naso in tambayi Inna a game da Sadauki amma sai tayi min sallama tace dare yayi sai gobe zamuyi magana. Anan palo na karasa kwana saboda saman gani nake kamar na kara kusa da Saghir.
Sa safe Subay'a ce ta tashe ni tana neman abinci, da yake ban samu nayi bacci sosai ba shi yasa na makara. Na jata muka shiga dakin kasa mukayi sallah tare sannan muka shiga kitchen na dora mata noodles na soya mata kwai, ina cikin aikin Saghir ya shigo Subay'a ta tafi gurinsa da gudu ya dauke ta suka tsaya a bakin kofa yana kallona yace "me ake dafa mana ne?" Ko kallo bai ishe ni ba, shi har yana da karfin halin pretending kamar babu abinda ya faru? Subay'a ce ta bashi amsa, sai yace "Subay'a mommy fushi take yi da Daddy saboda yace zaiyi aure" na juyo na watsa masa harara, ni har na manta ma da yace zaiyi aure. Ina jin Subay'a tana tambayarsa menene aure, na bar musu kitchen din sai ya biyo ni yana cewa "wai duk kishin ne haka? Ni na taba ganin anyi kishin wanda ba'a so?" Har zan wuce kuma sai na dawo na karbi Subay'a daga hannunsa nace taje kitchen ta dauki abincinta taci sannan nace masa "Saghir ko matan duniya zaka aura ko a tafin kafar Halima. Ni din ce dai ba zaka samu zuciya ta ba wallahi. Kuma su Inna sunje gida lafiya babu abinda ya same su, sun samu wani bawan Allah wanda yasan mutunci da darajar mutane ya taimaka musu kuma ya kaisu har gida a mota, bawan Allahn da basu hada dangantaka ta jini dashi ba" yace "ohh there is that, ashe fushin biyu ne" wato shi a nufinsa har ya manta da abinda yayi. Yace "to yanzu wanene bai san darajar mutane ba? Ni mutum ne mai ka'idoji kin sani kuma, ni bana son a shiga rayuwata sam bana son ake kawo min mutane cikin gidana" nace "gida? Amma dai kasan muma muna da gida ko? Kasan ba'a titi muke ba ko?" yace "sai su zauna a gidan naku kar su zo min nawa gidan, as simple as that" na girgiza kaina nace "ni Saghir bani da sauran karfi, na zuciya da na jiki da zanyi fada da kai, ka fadi duk abinda kake son fada ka kuma yi duk abinda kake son yi. Duniya ce, akwai ranar kin dillanci kuma ina sanar maka da cewa tana daf da zuwa" ban jira abinda zai ce ba na haye sama. Ina jinsa ya bude kofar palo ya fita, na leka naga shi da Subay'a ne suka fita a mota, na sauko kasa da sauri na tura kofa naji a rufe, wato rufe ni yayi daga waje ya tafi da key din.
Ina zama Inna tana kira na, dama tun dazu nake ta zuba idon ganin kiranta amma sai naji muryar Asma'u tace "Adda inna fa kuka take yi tun da muka dawo jiya da dare, tun da taga Sadauki take kuka na rasa dalili" na gyada kaina, ni nasan dalilin, nace "me Sadaukin yace sanda ya dauke ku?" Tace "baice komai ba fa, kawai tsokana ta yayi tayi har muka zo gida. Inna tace masa tana son ganin sa sai yace zai zo watarana" na tambayeta "ya tambaye ki ni?" Tace "a'a" na lumshe ido ina jin hawaye yana taho min. Idan ni ce na hadu da yaya ladi misali nasan abinda zan fara tambayarta shine Sadauki. Ko dai Sadauki ya daina so nane? Duk da dai Saghir yace min baiyi aure ba amma for all I know maybe yana da budurwa yanzu, maybe ma an kusa bikin. Maybe ma yaruwarsa zai aura a Maiduguri.
Nace da Asma'u ta kira Mama ta gaya mata abinda ya faru, ni ba zan iya zuwa in lallashi Inna ba saboda Saghir ya rufe ni a gida. Na san kuma yanzu inna tana bukatar wanda zasuyi magana dashi, musamman wanda yasan abinda tayi wa Sadauki da shi kuma sakayyar da yayi mata.
Ta barshi a titi a lokacin da yafi bukatar gida, shi kuma sai ya dauko ta daga titi ya kai ta gida a lokacin da tafi bukatar hakan.
Washegari Sunday, Saghir ya fita sai gashi ya dawo yana washe baki, ko kula shi banyi ba dan ban damu da insan me ya saka shi farin ciki ba amma sai ya zauna yana cewa "subay'a daddyn ki zai tafi kasar waje, me kike so in siyo miki?" Ta mike da murna tana tsalle tana yi masa list din kaya, shi kuma yana ta dariya, sai ya kalle ni yace "ki hada min kaya, gobe zan tafi oga ya tura ni zanyi signing contract da wani company a can" na dauke kai kamar ban ji shi ba sai yace "dama nan da two months ne tafiyar nan tazo, da da amarya ta zan tafi. Ohh ban fada miki ba ko? Nan da wata biyu ne aure na fa" nace "to ka daga tafiyar mana sai anyi bikin? Ohh na manta, ashe bada kudinka zaka yi tafiyar ba da kudin oga ne kuma dole sai abinda oga yace sannan zakayi tunda kudin sa ne. Mtsww i pity you" da naga dai neman magana yake yi sai na tashi na bashi guri saboda ni bana son rigima dashi a gaban Subay'a, amma kuma sai na samu zuciya ta da jin haushin Sadauki na budawa Saghir da yake yi.
Shi ya hada kayan tafiyar sa da kansa, da safe ya turo Subay'a ta kira ni naje na tsaya a bakin kofa yace "rashin kunyar ki, da rashin biyayyar ki shi yasa har yanzu auren mu yaki daidaita, da ace kin kwantar da kai, kin bini yadda nake so da ba karamin jin dadi zakiyi tare da ni ba. Kinga wannan tafiyar ma oga mu biyu ya biya wa, ni dake, yace in tafi da matata saboda wata daya zanyi kar in zauna gwauro a can, kinga da sai muyi tafiyar mu ni da ke da Subay'a but I guess I will have to go alone" ya ajiye kudi a kan mirror "ga kudin cefane nan, kinsan ni ina tsoron Allah dan haka ina kokarin sauke hakkin ki da yake kaina. Ban yafe ba, in kika fita ko da kofar gida ne indai ba abinda ya shafi makarantar Subay'a bane ba, sai kuma rashin lafiya, Allah yana kallonki in kika ci amana ta in bana nan" nayi murmushin takaici kawai, akwai amsoshi da yawa a raina wanda nake so in bashi amma ganin Subay'a yasa nayi shiru har ya dauki jakarsa ya fita yana cewa "gwara mutum ma ya dan bar kasar ya sarara na kwana biyu".
Tafiyar Saghir da kwana biyu Alhaji Babba ya kira ni a waya, I can't remember last sanda ya kira ni. Na dauka na gaishe shi sai naji muryarsa wani iri yace min "Diyam ki zo gida ina nemanki dan Allah" sai naji wani iri da yace min dan Allah, duk da dai Alhaji Babba yayi sanyi sosai tunda yanzu kusan hannu baka hannu kwarya suke zaune a gidan, bashi da komai sai yan abokai da suke taimaka masa da kuma kawu isa shima da yake dan bashi wani abu, duk sana'ar daya kama sai ta rushe, kullum muka je gidan yana ta cewa makiya ne suka sako shi a gaba ni kuwa deep down nasan inda matsalar dukiyar Alhaji Babba take, kudin mune da yaci, dukiyar marayu daya handame ya hada da tasa dukiyar da yasha wahala gurin nema dan haka sai yayi asarar har tasa dukiyar gabaki daya.
Na tambayeshi ko lafiya? Sai yace inzo dai kawai yana nema na. Na shirya ni da Subay'a muka tafi. Bayan mun gaisa da mutanen gida ne muka tafi palonsa na ganshi daga shi sai riga yar shara wadda duk tayi datti. Na durkusa na gaishe shi sai ya dauko wasu takardu ya miko min. Na bude a nutse ina dubawa a dan ilimi na sai na fahimci takarda ce daga kotu ta sammaci, mai kara shine 'Aliyu Usman Kollere" Wanda ake kara kuma "Alhaji Muhammadu Kollere" sai kuma sauran takardu da suka kunshi photocopy na takardar fili belonging to Aliyu Usman Kollere, da kuma takardar garage din Baffa, sannan anyi list na duk abinda yake ciki da kudinsa da kuma estimate na kudin business din gabaki daya, sai kuma akayi jimullar kudin wanda yawansu sai da yasa na kama baki na. Yanzu wannan ne dama kudin da Alhaji Babba yaci na mu? Wannan shine kudin da akace anyi min kayan daki dasu? Amma mai yasa alhajin yake nuna min a yanzu?
Kamar amsar tambaya ta sai naji yace "Diyam kinga abinda tsohon saurayin ki zaiyi min ko? Yaron da Usuman ya rike kamar shi ya haifeshi kinga sakayyar da zaiyi mana ko? Wai ya kaini kara wai naci dukiyar marayu to dukiyar ta ubansa ce? Ina ruwansa? Kudin nan ba aure nayi miki dasu ba? Ai na gaya wa Amina tun a lokacin kuma ra amince. Takamarsa shine da kason uwarsa a ciki shine yake so yayi min tonon silili" ni dai na ajiye takardun ina kallonsa har ya gama fadan sa sannan kuma sai yace "an ce min in na saka kika yi masa magana zai iya ya janye wannan maganar" na gyada kai, so that's it. Wannan shine dalilin da yasa aka shigar dani maganar. Nace "ni Alhaji bansan inda Sadauki yake ba ballantana inyi masa magana, kuma ma ba lallai ne ya saurare ni ba. Amma shi ne ya kawo takardun?" Yace "ina fa? Babu wanda yasan inda yake fa, lauyoyi ya dauka har guda uku, su suka shigar da karar alkali kuma ya aiko min da sammaci" ba gyada kaina, wato basu san waye Sadauki a yanzu ba. Nace "to ni Alhaji in zanyi masa ma maganar ai bansan inda zan same shi ba" yace "Amina ma tace bata san inda yake ba. Kuma ko number dinsa babu a jikin takardar sai ta lauyoyinsa" na dauki takardar ina kara dubawa sai naga numbobin, na dauki daya a waya ta nace "idan na same shi me zance masa?" Ya gyara zama yace "ki gaya masa ni ba matsiyaci bane ba, kaddara ce ta sauka a kaina da kuma makiya da suka sako ni a gaba wannan ne yasa a yanzu bani da kudin da zan bashi, amma kice masa yayi hakuri muyi aggrement zanke biyansa a hankali a tsakanin mu ba sai munje kotu ba" nace "shikenan Alhaji, zanyi kokarin ganin yadda za'ayi a fahimci juna" yayi ta saka min albarka sannan yace "ashe mijinki yayi tafiya? Sai da aka kawo takardar nan jiya na neme shi sannan naji ma wai baya kasar".
Na fito ina ta mamakin halin Saghir. Sai kuma na koma lissafin wannan lamari. Me Sadauki yake after? Na tabbatar ba kudin yake so ba dan yafi karfin wannan kudin a yanzu. Sai kuma na fahimci wannan shine dalilinsa na tura Saghir kasar waje saboda baya so yayi blowing cover dinsa ta matsayin ogan Saghir, duk da dai yadda ya shirya kai karar ba lallai ne ma a ganshi ba dan lauyoyinsa sun isa su wakilce shi amma me yake bukata?
Sai dana koma gida sannan na kira number din lawyer din. Ya dauka na gaishe shi ya amsa sama sama sai nace dan Allah ina son magana da client dinsa Aliyu Usman Kollere, yace "what for? Bana bada contact din client dina gaskiya" nace "na fahimta, but please ka gaya masa in ya tuna Halima Usman Kollere to tana son magana dashi" ya amsa zai fadi sakona sannan ya katse wayar. Jira jira har dare babu amsa, haka nayi ta duba waya ina karo volume wai dan kar a kira banji ba.
Sai safe around ten sannan kiran ya shigo, lawyer din ne dai yace "yace menene? Ki gaya min sakon sai in gaya masa" na runtse idona ina jin duniyar ma duk tayi min zafi nace "shikenan. Tell him nace dashi nake son magana ba da kai ba in bashi da guts din da zai saurare ni shi kenan na rike magana ta" na kashe watar ina jin zafin Sadauki a raina. Wato bama yason magana dani, baya son gani ba, ya manta dani yake nufi ko me? Ya manta alakar mu? Ya manta alkawarin mu? He said he will love me forever yanzu har forever din tayi? Amma sai wata zuciyar take tuna min da matsayi na na matar wani, wata zuciyar tana so in yi wa Sadauki uzuri na kin saurata ta da yayi, na gudu na da yake yi.
Around 12 wani kiran ya shigo wayata, saida zuciyata ta buga ganin sabuwar number, sai na samu kaina da rike wayar amma na kasa amsawa har ta kusa katsewa sannan na dauka a hankali na kai kunnena idona a rufe nayi sallama, shiru at first, sannan yace "kina son magana dani, ina jinki" muryar Sadauki, as clear as ever. Na hadiye abinda yaki tafiya a makogwaro na sannan nayi kokarin nima in yi irin nasa nace "maganar Alhaji Babba, yana son ayi negotiation. Can you do that?" Ya danyi shiru sannan yace "come to my office tomorrow morning, you know where it is" daga nan ya katse. Sai na zauna da waya a hannu ina mamakin wai da Sadauki nayi magana yanzu, but it sounded as if da wani stranger nayi maganar.
Ranar bana jin nayi baccin awa daya. Da assuba na tashi nayi wanka nayi sallah sai kuma na zauna ina kallon agogo yana ta lakaki yaki yin sauri balle gari ya gama wayewa. Na tashi Subay'a na shirya ta sannan nima na shirya tana ta tambayata inda zanje, na bata breakfast nima na hada tea na kurba amma sai ya tsaya a makogwarona yakasa wucewa. A haka har lokacin kaita school yayi, na kaita sai kuma nayi tunanin is too early inje office din Sadauki dan haka na dawo gida na cigaba da kallon agogo har saida ten tayi sannan na fita. Ina gayawa mai adaidaita Abatcha Motors sai yace "okay companyn motocin nan ko?" Sai da muka isa gurin sannan na kare wa building din kallo, so all of this is owned by Sadauki, how? Na shiga trying not to act like yar kauye, shi kansa building din anyi shine da shape din mota, haka round about din da yake tsakiyar gurin shima siffar mota ce dashi. Sadauki and cars bansan wacce irin soyayya ce a tsakanin su ba. Ina shiga reception din sai na tuno da ranar da akayi party, nayi tunanin ko wasu zasu gane ni? Amma kuma ranar babu haske sosai dan haka ba lallai bane su gane fuskata. Naje desk din receptionist, kafin inyi magana tace "Halima?" Na amsa mata sai ta dauki waya tayi magana a ciki sannan ta nuna min bene tace in hau, na hau na tarar da wata tana jira na sai ta bude min wata kofa tace in shiga, na shiga na tarar da wata mata da name tunanin secretary ce, kyakykyawar gaske gata ta sha make up sai kamshi take zubawa, ta yi min murmushi sai kawai naji ina jin haushinta ba tare da ta yi min laifin komai ba, ta wuce gaba sai naga kamar tana sane take murguda min bombom ta bude min wata kofa da card din hannunta na shiga sannan ta rufe.
Yana zaune a bayan katon table din gaban sa, as majestic as ever, bai ko dago kai ya kalle ni ba yaci gaba da rubutu a takardar gabansa ni kuma ina tsaye sai daya gama sannan ya dago fuskarsa blank yace "welcome Madam, have a seat please" naji kamar in juya in fita daga office din, nayi nadamar dana sani banzo ba amma ina bukatar amsa, ina bukatar ji daga bakinsa cewa ya manta da first twenty years of his life. Na zauna a kan cussion chairs din da suke jere a office din. Ya mike tsaye, sai naga ya kara cika min ido da kwarjini da girma baki daya ya zagayo ya zauna a kujerar gaban table dinsa sannan yace "kince Alhaji Muhammadu ya turo ki akan wani negotiation, ina jinki" naji wani sabon bacin rai, ni na ma manta abinda ya kawo ni kenan, sai kawai hawate ya fara bin fuskata. Nace "abinda zaka ce ma kenan? Irin karbar da zakayi min kenan? Sadauki nice fa Diyam, how can you even......call me Madam?" Sai ya mike tsaye ya juya bayansa ya saka hannu a aljihu yace "menene sakon da Alhaji yace ki fada min?" Sai na mike na nufi kofa da sauri ina goge hawayen fuskata, bai ce min komai ba har naje na kama kokawa da kofa amma taki budewa, na juyo ina kallonsa sannan yace "ba'a fita daga office dina sai nayi wa mutum izni" sai na dawo da baya da sauri na dauki wasu magazines na motoci na jefa masa, na debo tarkacen files din kan table dinsa suma na yi ta dukansa dasu har takardun suka tarwatse a gurin amma ko motsawa baiyi ba, na durkusa a tsakiyar gurin na kama kuka sai ya dawo ya zauna akan kujera yace "menene sakon da zaki gaya min?" Sai dana gama kukana sannan na tashi na zauna na goge fuskata nace "why? Sadauki why? Me yasa kame treating dina haka?" Yace "ya kike tsammanin zanyi treating mayar employee na?" Nace "shikenan? Matsayina kenan? Matar employee dinka? Me yasa ka dauke shi aiki ma? A ina ka sami wannan kudin kuma? I need answers Sadauki, I need to talk to Sadauki not this Mr Abatcha" yace "zaki samu answers dinki in due time. Now me Alhaji Babba yace?" Na goge hawayena nace "nasan kasan bashi da kudi yanzu, bashi da kudin biyanka ko da kuwa kotun koli zaka kaishi, dan haka I think you are just wasting your time" yace "really? To tunda bashi da kudin biya na fili na da gadona sai ya shirya zuwa prison for it. Kullum takamarsa kenan, kullum maganar sa itace zai saka a rufe ni, lokacin yana da kudi ni kuma bani dashi. Ki je kiyi masa albishir da cewa the table have turned, yanzu nine zan rufe shi" na bude ido ina kallonsa nace "you don't really mean that, me zakayi da kudin? Me zakayi da filin Sadauki look at this" na fada ina nuna office din nasa "zaka iya siyan hundreds of wannan filin, kafi karfinsa yanzu" yace "Baffa ne ya siya min remember? I was suppose to build us a house a kan filin nan, gidan mu ni da ke da yayan mu remember?" Sai kuma ya mike ta sake juya bayansa yana kallon window. Mun jima a gaka sannan nace "kayi tunanin abinda Baffa zai so, Alhaji Babba yayansa ne uwa daya uba daya ba zai so ya ganku a court dakai dashi ba, ba zai so yaga ka rufe masa dan uwansa akan kudi ba" ya juyo yana kallona yace "kamar yadda ba zai so a cire ki daga makaranta exactly 40 days bayan rasuwar sa ayi miki aure ba, kamar yadda ba zai zo a siyar da abinda ya kwashe rayuwarsa yana building abar iyalinsa da hamma ba" sai yakuma juya wa sannan yace "kamar yadda ba zai so a raba mu ba" na runtse idona ina jin wound fin zuciyata yana dawowa sabo, kewar Baffa na tana lullube ni, mun jima haka sannan yace "tell Alhaji Babba nace yana da options guda biyu, na daya shine ya bar mana gidansa da yake ciki tunda shi kadai ne yanzu abinda ya rage masa, na biyu kuma shine ya tafi prison for the rest of abinda ya rage na rayuwarsa"
Na mike tsaye, "Sadauki, ubangiji ma yana son rama sharri da alkhairi, kamar yadda kayi wa inna, dan Allah ka bar maganar nan, Allah ma daya halicce mu muna yi masa laifi kullum amma idan muka durkusa muka roke shi gafara sai ya yafe mana" ya juyo yana kallona, his eyes shining, yace "then tell him yana da third option, yazo ya durkusa ya roke ni gafara, ya saka gwuiyoyinsa a kasa ya roke ni in yafe masa kamar yadda na saka guiwowina a kasa na roke shi ya bani aurenki ya hana ni, ya durkusa kamar yadda na durkusa na roke shi kar ya aura miki that monster he calls a son amma duk da haka ya aura miki shi. Yes, I want him to cry and beg kamar yadda nayi in yaso in naki hakura duk da yayi haka sai yaji shima irin yadda naji".
Sadauki yayi tsauri da yawa ko? Lol
Not edited
[2/14, 10:05 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Forty Three : Heartless
Raina ya kara baci, ina mamakin anya kuwa wannan Sadauki nane? Sadaukin da na sani will never do that amma kuma sai nayi wani tunani. Yes, Sadauki yana da kirki da kyawun hali sosai amma bashi da yafiya, musamman idan akan abinda ya shafe ni ne Sadauki bai taba daga kafa ba ko da kuwa waye ya taba nin indai ba Inna ko Baffa ba, na tuno ranar daya doka wa yaya Mukhtar ball aka a gaban Inna. Sadauki bashi da tsoro ko kadan tun a lokacin da bashi da komai ma, ballantana kuma yanzu da yake da masu garin.
Nace "abinda kake so kenan? Abinda kake after kenan? Revenge?" Ya girgiza kai "this is not revenge, this is justice" nace "wanne justice din ne kuma wanda yafi wanda Allah ya riga yayi? Shin in kayi haka Sadauki ka gode wa Allah kenan? Kaga kuwa halin da Alhaji Babba yake ciki a yanzu? Ka kuma duba kaga halin da kai kake ciki a yanzu, kai kanka ka fada, the table have turned, menene kuma saura? Shin in ka yafe wa Alhaji Babba mai zai ragu daga jikin ka? Sai ma daraja da hakan zai kara maka a gurin ubangiji. Yanzu in ya siyar da gidansa ina zai kai iyalinsa?" ya bar inda yake tsaye ya zagawa gurin kujerar sa ya zauna yace "sai su dawo gidan ku ku zauna tare, ai naga kuna da bene, sai su zauna a sama ku kuma a kasa" na saki baki ina kallonsa sai ya danna wani button a jikin table din sai naga kofar dana shigo ta bude, ya kalle ni yace "goodbye, Diyam" na tsaya kawai ina kallonsa ina girgiza kai, I can't believe Sadauki yayi tauri har haka, sai na je na tsaya a gaban table dinsa nace "I don't like this Mr Abatcha da nake gani a gabana, I want my Sadauki back, I want my brother back" sai na juya da sauri na bar office din.
Ina jin matar nan ta waje tana yi min magana amma ban ma fahimci abinda tace ba ni dai na gyada mata kai kawai na fita da sauri. Da saurin kuma na karasa wajen gate na tari abin hawa na shiga muka tafi. Sai da muka bar gurin sannan na saki kukan da nake rikewa, ma dauka hawaye ne kadai nake yi bansan ya fito fili ba sai da naji drivern yace "yammata kiyi hakuri, komai na duniya mai wucewa ne watarana sai kiga kamar ba'ayi ba" a goge hawaye na ina jinjina maganar sa, watarana zanga kamar ba'ayi ba? Yaushe?
Sai dana je gida sannan nayi realizing wani abu guda daya, ni da na tafi gurin Sadauki da niyyar samun answers amma ban samu ko daya ba sai karin tambayoyi da na debo wa kaina. Na sani Alhaji Babba ya zalunce ni kuma ya zalunci Sadauki kuma har cikin raina ban damu ba in wani abin ya same shi a saboda abinda yayi, abinda na damu dashi shine Sadauki, I don't like this person he as turned to bana son wannan hanyar da yake tafiya a kai. Ni da zai aje duk wannan kudin nasa ya koma former Sadaukin da na sani da sai nafi jin dadi.
Na biya na dauko Subay'a sannan muka karasa gida. Muna zuwa na shiga daki na hada mana kayan mu ni da ita a akwati na chanza mata kaya muka fito. Mai gadi yace tafiya zakuyi ne haka Hajiya?" Nace "cikin gari zamu shiga baba iliya, sai Sunday zamu dawo" ya taro mana abin hawa ya saka mana kayan mu muka tafi Subay'a tana ta murna.
Muna shiga gida naga Inna duk tayi wani jeme jeme da ita, bayan mun gaishe ta ta kalli akwatin kayan mu tace "da fatan ba yaji kika yo ba Diyam" na girgiza kaina nace "yayi tafiya ne Inna, shine muka zo gida muyi dan kwana biyu" ta gyada kai tace "duk da haka ina fatan da amincewarsa kika taho gidan. Nasan ba kya son Saghir, kin fada kin kara fada cewa ba kya son sa kuma har yau nasan ba kya son nasa din. Amma kuma rashin son nasa da ba kya yi ba zai cire shi daga matsayin mijinki ba. Ni nasan kiyayya Diyam nasan illolinta, tun zamanin yammatanci na na dora wa zuciyata kiyayyar Zainab kawai saboda baffanku yana sonta ni kuma ina sonsa. Kiyayyar ta karu lokacin da aka aura masa ni ina matsayin matarsa amma kullum sai ya tuna min cewa dole aka aura masa ni, sai ya gaya min cewa ga wadda zuciyarsa take so. Na kara kin ta kuma lokacin daya aure ta ya kawo ta gidan nan duk kuwa da cewa tayi aure ta fito amma bai rage soyayyar ta ba daga zuciyarsa. Sai ma ya dauki wani son daban ya dora akan agolan da tazo dashi har a gurina nake ganin kamar yafi sonsa akan ku yayan da na haifa masa. Sai ni kuma na tsani yaron ba tare daya yi min komai ba. Har yau ni bazan iya fadar wani abu na rashin kyautawa ko rashin kunya da Sadauki ya taba yi min ba. Na tsane shine kawai saboda na tsani uwarsa. A gaban Sadauki zan gaggayawa Zainab magana amma baya kulani saboda ta hana shi tace babu ruwansa da tsakanin mu. Amma haka na cigaba da rura wutan kiyayyar sa a zuciya ta yadda har mutuwar ita kanta wadda ta haife shi da wanda ya kawo su gidan bata wanke kinsa a raina ba a karshe ina ji ina gani na saka rayuwar yata ta cikina a wahala kawai saboda in bakanta masa" sai ta rufe fuskarta ta kama kuka "Diyam ki gafarta min abinda nayi miki,ni na haife ki amma na tauye miki hakkin ki na bawa azzalumai damar zaluntarki" sai na tashi daga gabanta na koma kusa da ita na dora kaina a kafadarta na fara kuka. Ta saka hannu tana shafa kaina tace "nayi nadama, nadama mai tsanani. Maganar baffanku ta tabbata, yan uwanmu sun watsar damu a titi Sadauki yazo ya dauke mu. Ohh duniya. Duk wanda bai godewa rahamar Allah ba to kuwa tabbas zai godewa azabtar sa. Diyam nayi nadama a lokacin da nadama bata da amfani. Wallahi da ace igiyar auren ki a hannuna take Diyam da tun haihuwar ki ta farko zan gutsire auren gwara ki dawo gida ki zauna a gaba na akan auren Saghir. Amma na kai ki na baro ki. Babu abinda zanyi sai dai in nemi gafarar ki" na rungume ta nace "Inna kinfi karfin haka ai, ni dama ban rike ki a zuciyata ba ballantana ki nemi gafara ta. Wanda zaki nemi gafara shine Sadauki. Shi kika fi zalunta ba ni ba" tace " to ni Diyam ina zanga Sadauki? Tunda ya kawo mu nan ya ajiye mu bai dawo ba. A lokacin na gaya masa ina son magana dashi sai yace min zai dawo amma tun lokacin nake zuba idon ganin sa sai dai shiru babu shi babu labarin sa".
Sai na bata labari. Na bata labarin asalin ko wanene Sadauki a yanzu sannan kuma na gaya mata yadda mukayi da Alhaji Babba da kuma irin amsar da Sadaukin ya bayar. Na karashe da "yanzu dai Sadauki yace Alhaji Babba yana da dama uku. Ko dai ya bamu gidan da yake ciki a maimakon kudin mu, ko yayi jail time, ko kuma yaje gaban Sadauki ya durkusa yana kuka ya roke shi gafara a bisa dukkan abinda yayi masa" Inna ta rike baki ta kasa magana. Nayi shiru ina kallon ta ina jiran ta inda zata fara jero tsinuwa ga Sadauki amma sai naji tace "to, kudin nan dai namu ne gabaki daya, ni dai abinda yake hakkina a cikin kudin nan na yafe wa Alhaji Babba tare da fatan Allah zai dubi niyya ta nima ya yafe min wasu daga cikin laifuffuka na. Amma a cikin ku ban tilastawa kowa ta yafe nata ba, duk wadda taga bata yafe ba sai ta bawa Sadauki goyon baya gurin karbo muku abin ku. Shima kuma Diyam kar ki kuma kokarin hanashi karbar hakkinsa, in ma zubarwa zaiyi ai nasa ne ko? Da basu san kina da amfani ba sai yanzu? Babu ruwan ki, ki fita daga harkar" na gyada kaina. Sai kuma ta tambaye mu in mun yafewa Alhaji Babba, nace "ni dama ai ni yace yayi wa kaya da kudin, to in ma ina da ciko na bar masa, wanda ya tara dukiyar ma ya tafi ya barta" Asma'u tace "ni kam in dai har hamma Sadauki zai iya karbar kudin nan to ina son kaso na. Shi da bai taimaka min da komai ba ni ba zan bar masa hakkina ba" na harare ta sai ta daga kafada tace "Inna tace kowa ya fadi ra'ayin sa".
Da daddare tare muka kwana gabaki daya a kan gado daya muna ta hira, Asma'u sai labarin motar Sadauki take yi min "wallahi ban taba ganin mota mai kyau da dadin wannan motar ba. Kai Adda ina ma dai shi kika aura da yanzu a wannan motar za'a ke kaiki unguwa kin huta da dan sahu. Nima in naje gidanki a irinta za'ake kawo ni gida" nayi juyi nace "Asma'u dan Allah ki rabu dani, bashi na aura ba chapter closed" sai kuma nace "motoci fa yake siyarwa. Dole ya hau mota me kyau".
Washegari na shirya, na bar Subay'a anan gidan na tafi gidan Alhaji Babba. Direct part dinsa na tafi tunda yanzu ba sai anyi wa mutum iso ba. Na same shi a zaune yana lazimi, sai da ya shafa sannan ya tambaye ni "Diyam kin same shi? Me yace? Jibi ne fa zamu fara zuwa court" nace "na same shi Alhaji" sai kuma na lissafa masa abinda yace. Ya kama salati, amma wannan yaro anyi asarar haihuwa, yanzu ni tsofai tsofai dani zaice in je in durkusa a gabansa? Sakayyar da zai yiwa rikon da Usman yayi masa kenan? Gwara da Allah yasa bamu bashi aurenki ba Diyam da yanzu da surikin mu zamu shiga Shari'a" ni dai nayi masa sallama na fita ina jinsa yana cigaba da maganganu shi kadai.
A cikin gidan ne zuciyata ta karye. Hajiya Babba ita kanta a jigace take dan yan uwanta sun gaji da taimaka mata. Muka gaisa tace "Diyam baku kyauta mana ba ke da Saghir, yanzu ace tafiya ta same shi amma sai bayan da yayi ta zamuji labari?" Nace "Hajiya ni wallahi bansan be fada muku ba, na dauka duk kun sani" ta girgiza kai tace "ina fa, mu Saghir sai yayi sati ban saka shi a ido na ba sai dai in na kira shi nace ina nemansa. Yanzu idan kunyi waya dan Allah kice masa ya kira ni" nace "to".
Dana shiga dakin Hajiya Yalwati ne na tarar dasu abin tausayi. Aunty amarya dama ta kara mai ta bar yaranta guda uku duk suna gurin Hajiya Yalwati ga sauran yayan da ake bari a gidan duk mata, ga kuma nata yaran dam haka wajan yara goma ne a part dinta, dan abinda manyan ƴaƴanta suke taimakawa dashi da kyar yake ciyar dasu. Ga yara uku sun isa aure sun kuma samu mazaje amma babu halin yi musu auren. Muka gaisa itama tayi min mita "yanzu Diyam shi mijinki ko shinkafa ba zai ke siyowa yana kawowa gidan nan ba?" Ni dai bance komai ba saboda bazanyi alkawarin da nasan ba zan cika ba.
Washegari Saghir ya kira wayata. Dama tunda ya tafi kullum sai ya kira sai in bawa Subay'a su gama maganganun su in kashe. Ranar sai yace ta bani zaiyi magana dani. Ina karba ya fara fada "da izinin waye kika fita kika je gidan Alhaji?" Nace "Alhajin ai shi yayi kirana ya hada ni da Allah da Annabi inje in taimaka masa" yace "ke kuma sai kika fita, saboda kina sauri za'a tura ki gurin saurayin ki ko? Ai Alhajin duk ya gaya min abinda yake faruwa, shegen yaro da bai san darajar manya ba wai har zaice zai kar Alhaji kara ya biya shi gadon uwarsa? Yanzu haka kudin wiwin da yake sha ne ya kare shi e yake neman refill" nace "amma Alhaji bai gaya maka lauyoyi ya dauka har guda uku ba? In kudin wiwi yake nema ya siya mana da kudin daya biya lawyers din dashi? In fitsari abinyi ne kaza tayi mana mu gani" yace "kar ki gaya min magana, kinsan dai dan bana gari ne da tuni zan biya shi kudin sa, ko Mr Abatcha na gayawa a take zai bani kudin in bashi" na girgiza kaina ina jinjinawa rashin sani da hausawa suka ce yafi dare duhu. Sai nace "to ko a daga shari'ar ne sai ka dawo sai ka karba a gurin Mr Abatcha ka bawa Sadauki?" Yace "to kudin ma ba Alhaji yace dasu akayi miki kayan daki ba? Ki gayawa Sadaukin haka in yaso in karar ce sai ya kai ki ke ki biya shi" sai na gaya nasa jimlar kudin, nace "ni nafi tunanin bayan kayan daki na har gidan da muke zaune a ciki da kudin aka siya, sannan aka kara jari da sauran. Dan haka dani da kai za'a gamai biyan kudi".
Da daddare lawyer din Sadauki ya kira ni, wai Sadauki yace kar muje court gobe. Inna tace ai dama babu inda zamuje. Washegari suka zauna a court. Sadauki ma baije ba kamar yadda nayi tsammani, lawyers dinsa ne kawai suka je a madadin sa. Suka gabatar da dukkan takardu da kuma dukkan shaidu da suka tabbatar da wanzuwar garejin da kuma filin, sannan suka kawo shaidun cewa an siyar, har wadanda aka siyarwa ne suka zo sukayi testifying da kansu suka kuma fadi kudin da suka siya. Alkali ya nemi Alhaji Babba daya fito da kudi shi kuma ya tabbatar cewa kudi dai babu su kuma bashi da hanyar samun su a yanzu, sai dai yana neman alfarmar a bashi lokaci yake biya a hankali har ya gama. A take lawyers din Sadauki suka gabatar wa court da shaidar cewa Alhaji Babba yana da gida mai number 43 a unguwar sharada, har da estimate na kudin gidan, dan haka suna so Alhaji Babba ya siyar da wannan gidan nasa ya biya wadannan kudade, a take alkali ya amince kuma ya bawa Alhaji Babba kayyadadden lokaci na siyar da gida shi kuma Alhaji Babba sai ya nuna cewa lokacin yayi kadan saboda sai ya samu mai siya, anyi ciniki anyi komai. A take lawyers suka ce Sadauki yace zai siya, ai kuwa alkali ya bada lokaci yace aje a daidaita a kan price.
Ana fitowa daga court kawu isa ya kira Inna ga Alhaji Babba nan hawan jini ya tashi an kaishi asibiti. Haka Inna ta saka mu a gaba muka tafi dubiya ni dai ba'a son raina ba amma dana ganshi sai naji zuciyata ta tsinke. Yana ta kuka shabe shabe da hawaye. "Yanzu ya zanyi in siyar masa da gidana? Gidan dana gina tun auren fari da gumina. In na siyar da gidana a ina zan saka iyalina kuma?" Sai naji tausayinsa,ko babu komai yayan Baffa ne shi uwa daya uba daya. Sannan ga tausayin iyalinsa ina zasu je? They are innocent. Su zan iya rantsewa basu mori ko kwandala a kudin ba.
Na fita na dauki waya ta nayi ta kiran number din Sadauki bata shiga. Ko kuma blocking dina yayi ne oho. Da daddare kawu Isa yazo gurin Inna, wannan shine zuwansa gidan mu na farko tun da su Inna suka dawo. Yace "kudi dai da za'a bawa yaron nan babu su. Dan ni kaina in nace zan fitar da kudin nan to kuwa tabbas zan kassara kasuwanci na. Gida kuma kamar yadda Alhaji ya fada in ya siyar ya kai iyalinsa ina? Dan haka third option shine a kira yaron nan a bashi hakuri, ku zakuyi mana jagora zuwa gurinsa a sasanta maganar nan as a family tunda shima ai kusan family din ne, shekarar sa ashirin a hannun dan uwan mu".
Ni aka saka in kira Sadauki. Na gaya musu ba dauka zaiyi ba amma suka ki dan haka a gabansu na kira kuma taki shiga din. Sai na tura masa text. "Third option. Kazo a baka hakurin da kake so" na tura masa. An jima kadan yayo reply "tomorrow evening. Gidan Baffa" na gayawa kawu Isa abinda yace sannan ya tafi da niyyar gobe zai zo tare da Alhaji Babba.
Washegari. Inna har dayiwa Sadauki girki tana ta gyaran gida ni dai ina kallonta kawai. Su Alhaji Babba ne suka fara zuwa, sai a lokacin ma yasan akwai yan haya a gidan mu. Suka zauna nan palo aka bawa Alhaji pillow ya dan kashingida saboda babu lfy. Sai after 5 Sadauki ya shigo gidan. Shi kadai, babu wani abu a jikinsa da zai nuna cewa shi mai kudi ne dan shirt da wando ne kawai a jikinsa ko agogo babu a hannunsa. Sai naga ya koma min wancan Sadaukin da na sani ba wai Mr Abatcha ba, kuma ganinsa a cikin gidan mu sai yayi adding to that feeling.
Yana shigowa palon muka hada ido sai ya dauke kai, fuskarsa babu walwala ko ta cikin cokali sai kawai naji gabana ya fadi. Ya gaishe da Inna ta amsa, the first time da naji Inna ta amsa gaisuwar Sadauki. Sai ya samu guri ya zauna yana kallon Alhaji Babba yace "ina jin ka," kawu Isa yace "dama cewa mukayi a kira ka muyi magana. Ayi hakuri a bar maganar nan ta wuce" sai yace "ba kai zaka bada hakurin ba ai" Alhaji Babba ya tashi daga kwanciyar da yayi ya matso gaban Sadauki yace "ka duba darajar rikon da Usman yayi maka, da kuma darajar yanuwantakar da take tsakanin mu ka bar maganar nan. In na baka gidana iyalina kuma ina zan kaisu? Ka duba halin da nake ciki na karayar arziki data same ni ka yafe min kudin nan. Banyi dai dai ba na sani, na aikata maka laifuffuka na sani, amma na hada ka da Allah kayi hakuri ka bar maganar nan" sai naji zuciyata ta karye, hawaye ya fara bin fuskata amma dana kalli Sadauki sai naga kamar da dutse ake magana. Sai ya mike tsaye yana kallon Alhaji Babba yace "na yafe maka kudin gadon Ummah. Amma kudin fili na ban yafe ba dan haka zan aiko a yankar min wani part na gidan ka a maimakon fili na, dama ina da sha'awar yin kiwon kaji sai inyi a gurin".
Na mike da sauri ina kallonsa cikin mamaki. Can his heart really be this dry? Bai jira sauran magana ba yayi hanyar waje na bishi da sauri ma sha gabansa nace "this is not you Sadauki. Ba kai bane wannan. Kai kace minzaka yafe masa in ya durkusa a gabanka ya roke ka and he did just that" ya harde hannayensa a kirjinsa yana kallona yace "ni ba haka na ce miki ba. Cewa nayi in ya durkusa ya roke ni gafara in naki yi masa a lokacin ne zai fahimci irin yadda naji. So, nayi kokari ma ai, na yafe masa rabi saura rabi".
Na dafe kirjina nace "are you this heartless Sadauki?" Yana kallona with straight face yace "do you blame me? Yes, I am heartless because they took away my heart. You are my heart remember?" Sai ya juya ya fice ya barni a tsaye.
[2/15, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Forty Four : Sweet Sixteen
Nabi bayansa da kallo ina jin kamar ya ciro tawa zuciyar ne ya tafi da ita. My chest felt empty kamar babu komai a cikinsa, ji nake kamar in bishi a baya da gudu in rungume shi kamar yadda naje yi sanda ina karama, ina son ya rungume ni nima kamar yadda ya taba yi min a gidan Alhaji Babba, but I couldn't saboda akwai wata igiya data ke rataye a wuya na, igiyar auren Saghir.
Bazan iya komawa palon ba saboda duk bana son kallon fuskokin su. Yes, Alhaji Babba ya cuce ni iyakacin karshen cuta amma kuma still yayan Baffa na ne, kuma va'a taba chanjawa tuwo suna, komai suka yi bazan taba cewa su ba iyayena bane ba. And there is wani satisfaction da ake samu a cikin forgiveness, wannan satisfaction din shi nake yi wa Sadauki kwadayin samu.
Sai na juya na tafi gurin Maman Iman duk da dai ita kuma surutu ne da ita ni kuma a lokacin bana son magana. So nake inyi shiru inyi jinyar zuciya ta. Dan haka ina zuwa sai nace mata bana jin dadi ne ina so zan kwanta, sai kuwa ta bude min dakin yaranta, dakin mu ni da Asma'u a da. Na shiga na kwanta, but sai dakin ya cigaba da dawo min da memories din da. Sadauki's memories, na sake gwada kiran wayarsa still bata shiga. Dai na kifa kaina a pillow na fara kuka. It really hurt to love someone so deep while you are married to another, another din kuma wanda ba ka so.
Sai da akayi magrib Maman Iman ta shigo ta tashe ni in yi sallah. Ayi alwala nayi sallah sannan na koma part din Inna, ina shiga na tarar sun tafi, Inna ta bini da kallo tace "kuka kikayi ko?" Na girgiza mata kai amma sai hawaye suka fito. Tace "me yasa kika masa magana dazu? Ba nace miki ki fita daga maganar ba? Tunda ke kince kin yafe shi ki barsa ya karbi abinsa. Na gaya musu nace Asma'u ma tace bata bari ba".
Ranar sunday, da safe muna shirye shiryen komawa gida ni da Subay'a kamar daga sama sai jin sallamar Sadauki nayi a tsakar gida. Na dakata da folding kayan da nake yi naji Inna tana amsa masa da yake tana tsakar gida ni ina palo, naji ya gaishe ta ta amsa tana tayi masa sannu da zuwa tace ya shigo palo, yana daga labule muka hada ido sai yayi sauri ya saki labulen ya koma yana cewa "basai na shiga ba Inna, dama zan dan shiga dakin Ummah ne" sai Inna ta kira saka mayafinta da kanta ta shiga gurin Maman iman ta gaya mata za'a wuce, saboda sai an bi ta nan za'a karasa dakin Ummah. Subay'a dake kusa dani ta tashi ta leka tsakar gida, sai naji yace mata "Subis, come here" sai ta makale a bayan kofa taki fita, yace "ba zaki zo ba? Dan kin ganni baki babanki kuma fari ko?" Sai inna ta dawo ta tarar dasu tayi dariya tace "Subay'a kizo ki gaishe da babanki mana?" Subay'a ta tura baki tace "ba baba na bane ba" inna tace "ji fitsararriya?" Yayi dariya yace "gado tayi ai" sai Asma'u ta shigo, tana ganinsa ta kama murna tana gaishe shi, yace "yar asama yammata" a raina nace "wato yana iya yiwa kowa magana faran faran, ni ce dai na koma aljana a gurin sa".
Asma'u ce ta raka shi ya bude dakin Ummah ya shiga, sannan ta dawo. Inna ta shigo tana kallona tace "kina jin Sadauki ba zaki fita ki gaishe shi ba?" Nace "baya son ganina inna. ganina a dakin ne fa yasa ya fasa shigowa". Inna tayi shiru kawai bata ce min komai ba ni kuwa zafin da nake ji a raina yasa na dauki kayan na koma cikin daki, amma sai na kasa cigaba da gyarawa na kwanta kawai. Ina kwancen ya dawo, ya leko yayi wa Inna sallama sai ta ce yazo tana son magana dashi. Ya shigo palon ya zauna tace "Sadauki. Ni dai kam bansan wanne kalamai wanda yayi laifi irin wanda nayi maka zai yi amfani dashi gurin rokon gafarar wanda yayi wa lafin ba. Na cutar da kai Sadauki iyakacin cutarwa kuma duk a bisa son zuciyata ba wai dan kayi min wani laifi ba. Amma a karshe sai ya kasance ni din dai nice a wahale. In kace ma ba zaka yafe min ba Sadauki bazan ji haushi ba saboda na cancanci koma menene zakayi min. Amma abinda na sani shine nayi nadama, Sadauki dan Allah...." Sai ya dakatar da ita yace "Inna na yafe miki ai, da ban yafe miki ba Inna ba zaki ganni a dakin nan ba. Maganar ta wuce tsakanin mu har abada" sai Inna ta kama yi masa godiya, har ya sake mikewa zai fita sai ta kira Asma'u, sai kawai zuciyata ta raya min in leka su, naje ta jikin labule ina lekawa sai naga ta kamo hannun Asma'u ta saka a cikin na Sadauki tace
"na hana ka auren Diyam a lokacin da kiyayyar ka ta rufe min ido, amma yanzu ga Asma'u na baka, duk abinda yayi Diyam shi yayi Asma'u har kamanninsu iri daya ne, ina fatan zaka karba kuma wannan zai wanke maka zuciyarka"
Na juya ina dafe kirjina kamar mai kokarin gana zuciyata fadowa kasa. Idanuwana kamar zasu baro mazauninsu ina girgiza kaina a hankali ina cewa "no, no, no" amma sai naga Sadauki yayi murmushi, sai ya cire hannun Asma'u daga nasa ya mayar wa da inna yace "Inna na gode da wannan babbar kyauta da kika yi min, kuma da gaske wannan kyautar ta wanke min zuciyata sosai amma kiyi hakuri bazan iya karba ba. Zuciyata Diyam take so ba kamannin Diyam ko asalinta ba, in na karbi Asma'u banyi mata adalci ba saboda zan tilasta mata zama dani alhalin zuciyata bata tare da ita. Kiyi hakuri idan ban kyauta miki ba amma hakan shine zaifi mana alkhairi a gani na".
Na saki labulen na zauna a gurin ina juya lamarin a kaina. He refused Asma'u, sweet teenage Asma'u, yana claiming that his heart belongs to me, how can that be? Bayan ni kuma I belong to someone else?
Sai yamma muka koma gida, daga nan kuma muka cigaba da lonely rayuwar mu nida Subay'a. Duk da ina kokarin ganin na rage tunanin Sadauki amma kullum tamkar kara min shi akeyi.
Two weeks after that akazo aka raba gidan Alhaji Babba. Aka ja katanga tun daga part dinsa har zuwa bakin gate, sai ya kasance part din nasa da filin compound din dayake gaban part din har zuwa dakin maigadi da gate din gidan duk na sadauki ne. Main house din kuma da sauran abinda ya rage na compound shi kuma na Alhaji Babba, amma ko gate basu dashi dan haka sai katanga suka fasa ake shiga gidan, ko kudin da za'a sayi kofa a saka babu.
Ba'ayi sati dayin haka ba dakunan Alhaji Babba suka zama dakunan kaji, Sadauki ya cika katon palon Alhaji da kuma two bedrooms dinsa da kajin gidan gona, broilers da layers. Compound din kuma akayi katuwar rumfa aka zuba raguna da tinkiyoyi, dakin maigadi kuma ya saka masu kular masa dasu.
Alhaji Babba kuma ya koma cikin gida, dakin da Inna ta zauna nan ya dawo da zama. Washegarin da aka zuba dabbobin da sassafe murja ta kira ni "Diyam wallahi yau bamuyi bacci ba a gidan nan. Yadda muka ga rana haka muka ga dare wallahi, ragunan nan tun magrib suka fara koke koke har garin Allah ya waye sannan kuma kaji suka dauki nasu suma. Ni dai gidan ki zan taho in taya ki zama kafin hamma ya dawo ya kore ni" nace ta taho babu komai. Sai kuma naji babu dadi a raina. Murya, Hajiya Yalwati da sauran yayan Alhaji Babba basuyi wa Sadauki komai ba amma har dasu ake paying. Isn't Sadauki taking this too far? Bayan gudun daukan alhakin wanda baiji ba bai kuma gani ba?
Da dare Sadauki yaje gidan mu. Ya gaishe da Inna sai yace da Asma'u. "Yar Asama kina son gidan gona?" Tace "gidan gona kuma hamma?" Sai ya ajiye mata takardu yace "gashi nan na baki kyauta. Duk karshen wata za'ake kayo miki kudin da aka samu a ciki" Asma'u sai murna da tsalle, yayinda Inna ta saki baki ta kasa magana.
Yana tafiya Asma'u ta kira ni tana son bani labari amma maganar ta kasa fitowa dan murna. Nace "kinga ki nutsu ki fada min, me ya faru?" Tace "hamma Sadauki ya bani kyautar gidan gonar sa da yayi a gidan Alhaji Babba" cikin mamaki nace "what?" Sai ta mikawa Inna tayi min confirming maganar. Har da sunan ta da komai a jikin takardun.
Na kira shi da niyyar yi masa godiya amma shiru wayar bata shiga kamar kullum. Nayi tsaki na yar da wayar feeling very frustrated sai kuma na dawo na sake dauka na tura masa message "ina yiwa Asma'u godiyar kyautar da aka yi mata. Allah ya kara arziki mai albarka" na tura sannan na zauna rike da wayar a hannu ina jiran reply. Can sai gashi ya shigo. Three words
"You are welcome".
Nayi tsaki ina jin haushin sa, amma bansan dalilin da yasa nake jin haushin nasa ba.
Bayawa ko? Sorry, busy weekend
[2/16, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Forty Five: Fauziyya
Murja tazo gidan muka zauna tare da ita, da yake ta gama makaranta kuma tun tuni ana ta zaune gida ba'a cigaba da karatu ba, ita tafi son tayi aure ma. Tace "wallahi Diyam na gaji, na gaji da zaman gidan nan wallahi. Gafa samarin nan ina dasu, kuma duk wanda nacewa ya turo a cikin su wallahi fitowa zaiyi amma Alhaji shiru har yanzu yaki yace wani abu, kuma maganar sa daya wai wasu kudi yake jira su zo kuma duk munsan babu wasu kudin da zasu zo fa. Ni so nake in bawa umman mu shawara duk ace da samarin mu su fito, in yaso kowa kudin auren ta da kuma kudin sadakin ta sai a hada ayi mata kayan daki yadda ya sawwaka kawai. Ai ba sai an kashe mana kudi ba mu auren mu ke so kawai" na jinjina maganar nace "amma biki fa? Gara fa?" Tace "wannan kuma mijin ki zaki yiwa magana dan Allah ya rage matsolancin sa yayi mana. Kudin yadin da yake sawa a jikin sa kadai ya isa ayi abincin biki da shi" nayi dariya nace "kai murja, hadda sharri kuma?" Tace "wallahi ba sharri bane ba kayan da yake sakawa ko sanda Alhaji yana da kudi baya saka irin su. Amma ya bar alhajin da yar shara".
Sanda Saghir yaji labarin abinda Sadauki yayi a gidan su ya kira ni ya zazzage min bala'i. Bance masa komai ba har ya gama sannan nace "ni dai bani na kar zomon ba, ni ratayar ma ba'a bani ba, ka bari in ka dawo sai kaje ka neme shi kayi masa masifar, but I doubt in zaka samu ganin sa dan kasan manyan mutane ba kowa suke bari ya gansu ba" ina fadar haka na kashe, yayi ta kira naki dauka dan nasan cigaba zamuyi daga inda muka tsaya.
Tun ana gobe zai dawo yakira yagaya min "ke yanzu ko dan I miss You din nan ma baki iya gayawa mijin ki ba. Kinga ni kuma har da tsaraba na siyo miki. Ina fatan dai kin tana de ni saboda da kishin ruwan ki zan dawo" sai naji ma abin ya bani dariya nace "duk wanda ka gama samu anan bai ishe ka ba? Mai zakayi da yar mitsitsiyar Diyam?" Bai musa ba yace "naki special ne. Da gaske nayi missing dinki fa" sai na kashe kawai. A raina ina jin inama yayi zamansa a can kar ya dawo?
Banyi niyyar yi masa komai na dawowa ba amma dai sai na daure nayi masa girki, wainar shinkafa na miyar taushe da taji tantakwashi. Na hada masa lemom kankana. Sanda zasu taso ya kira wai zai turo friend dinsa ya kaimu airport ni da Subay'a mu taro shi, nace ni aiki nake yi sai dai suje da Subay'a. Na shirya ta kuwa suka tafi, nima nayi wanka na shafa mai kamar kullum na saka normal kayana na gida nayi kwanciya ta a kan gado.
Ina jinsu suka zo, kawai naji wani bacin rai ya sauko min nayi tsaki na gyara kwanciya ta. An jima kadan Subay'a ta shigo tana ta tsalle. Mommy ki zo Daddy ya dawo, ya siyo min kaya da jirgi da mota" nace "kice kin gode, sannan kice masa ga abinci nan a dining" ta fita na koma nayi kwanciya ta. Sai gasu nan sun dawo tare, na tashi zaune ina kallonsa shima yana kallona, ya kara fari har da kumatu yayi alamar ya huta sosai, yace "shikenan? Babu oyoyo mijin ki yayi tafiya for two months amma ko dan welcome back hug ba zai samu ba?" Nace "na dafa maka abinci, nace maka sannu da zuwa sai menene kuma?" Ya saki hannun Subay'a ya hawo kan gadon sai nayi sauyi na sauka na fita na bar musu dakin.
Na tarar da lodin kayansa a palo, na dauka na kai masa dakinsa na tarar yana shirin wanka, na dauko abincin da nayi masa na kawo palon sama na ajiye sannan na koma kasa muka zuba ni da murja muna ci tace "ke ba zaki tafi gurin mijin ki ba ya dawo daga tafiya? Ke ana neman mijin ke kina wulakanta naki?" "Humm" kawai nace mata sai ga kira kuwa Subay'a tana yi min inzo inji Daddy. Yana zaune a kujera ya hade rai "ki zo ki zuba min abincin tunda ba zakiyi min wankan ba" bance komai ba na zuba masa na kawo table gabansa na ajiye masa. Yace "wai ke ciwon rashin magana ne ya same ki? Na fi so ina fada kina mayar min yafi dadi" nace "ba ciwon rashin magana bane ba, ƴata ce ta girma shi yasa nake shiru a gaban ta" yayi dariya yana kallon Subay'a data zauna ta zuba mana ido. Na juya zan koma kasa sai ji nayi yace "kai! Matar nan wani duwawu naga kina yi fa" nayi saurin kallon Subay'a naga tana dariya sai kawai na girgiza kai na tafi.
Muna kasan Subay'a ta jawo wani karamin akwati da kyar, murja ta tashi ta taimaka mata suka sauko dashi tana cewa "Mommy kinga kayan da Daddy ya siyo min" tana ta bubbuda wa, kayan sawa ne masu kyau da takalma, sai toys, murja tana ta yabawa, sai kuma Subay'a ta koma sama da gudu sai gata da karamar travelling bag mai kyau ta kawo min. "Inji Daddy, wai irin kayan da turawa suke sakawa ne ya siyo miki kema kike sakawa. Ki koma irin su" na bata rai nace "to sarkin surutu" na karba na ajiye, murja ta dan dake ni tace "tashi zaki yi kije kiyi godiya sosai" na mike na tafi amma sai nayi kwana na shiga dakina nayi kwanciya ta.
Sai bayan magrib ya shigo dakin yana kallona ina ninke sallaya yace "zan fita, zan tafi zance" na dauke kaina nace "ba gidan Alhaji ya kamata kaje ba? Ka gaishe su kuma kaga abinda aka yiwa gidan?" Sai kawai naga yayi murmushi yace "au kishi kike dan zanje zance ko?" Na zauna a bakin gado nace "Saghir, na riga na gaya maka tun kafin kayi tafiyar nan ni ko mata goma zaka aura ba zanyi kishin ka ba. Ni da son samu nane ma hudu nake so kayi, yadda zaka bani takarda ta in kara gaba" ya karasa shigowa yana cewa "wato kin ganshi ko? Alhaji ya tura ki kin ganshi ko? To bara kiji, in shi yake zuga kima ki gaya masa, auren ki yanzu na fara. In kinga na rabu dake to mutuwa nayi" ya juya ya fita.
Ranar da wuri na yiwa murja sallama na hau sama tana tsokana ta "wato miji yazo shine zaki tafi turaka ko?" Nayi dariya kawai na tafi, na shirya Subay'a na kwantar da ita sannan nima na shirya na rufe kofa ta nasa key nayi kwanciya ta. Cikin bacci naji karar wayata, na dauka na ga Saghir ne sai na saka ta a silent na juya na cigaba da bacci na, sai kuma naji shi yazo yana knocking, ko kallon kofar banyi ba har ya gaji yayi tafiyar sa. Da sassafe ya bar gidan, a raina nace "Allah ya raka taki gona".
Da yamma sai ga Mama tazo, ni na dauka zuwa tayi gani na sai da naji ta kama yi min fada sannan na fahimci Saghir ne ya kai kara ta. "Diyam me kike nema wa kanki? Kin manta abinda annabi ya fada cewa mata sunfi yawa a wuta? Kuma mafi yawansu sun shige ta ne sakamakon rashin bin aure? Abinda kike so kenan? Wuta kike so ki kai kanki? To wallahi ki nutsu kiyi wa kanki fada. Ganin Sadauki ya dawo ne zaki kuma dorawa kanki kulafucinsa ko? So kike a lahira shi Sadaukin da kike yi saboda shi idan ya aikata aiyukan alkhairi ya kasance a aljanna ke kuma kina wuta saboda shi?" Nace "Mama ni ba dan Sadauki bane ba, Sadaukin da ko kula ni baya yi?" Tace "to ya zaiyi ya kula ki? Matar aure ce fa ke. Ke ai har yanzu ba hankali ne ya ishe ki ba shi kuwa da hankalinsa. Saghir yace shi yana sonki, yana son zama dake, me yasa ke ba zaki so shi ba? Shima Sadaukin nan fa dole watarana aure zaiyi, yadda yake da kudin nan ma sai ki ga ya auri hudu a rana daya. In haka ta faru kuma ya zakiyi?.
Sai dare Saghir ya dawo gida. Yana shigowa palo murja ta gaishe shi ya hade rai yace "ki shirya gobe ki koma gida" tace to sai ya wuce sama. Murja ta kalleni pleadingly, ni kuma na daga mata kafada. Kamar bazan tashi ba musamman ganin ko kallon inda nake baiyi ba kuma dai sai na tashi na bi bayansa. Ina shiga dakinsa naga yana kokarin cire kaya sai na kama masa ya cire nayi hanging rigar sai yace "Mama tazo gidan nan kenan" na rike kugu nace "tunda ka kai kara ta ba dole tazo ba?" Ya zagayo hannayensa a waist dina yace "naga kina neman ki kaini lahira ne shi yasa na nemo taimakon gaggawa" ya shafa fuskata yace "you really are beautiful" na ture hannunsa nace "bararojin kuma?" Sai yayi dariya yace "wai baki manta ba, ai bararoji suna da kyau so it was a compliment" ya saka fuskarsa a cikin gashina yana shakar kamshinsa yace "tell me duk abinda kike so inyi miki" nace "ka bar murja ta cigaba da zama a gidan nan" yace "done. Sai kuma me?" Nayi shiru, yace yana zuge zip din rigata "ba zaki ce in fasa aure ba? Say it and it will be done" na sake shiru na rufe idona ina jin daci a bakina yace "kice 'hamma Saghir Please kar kayi min kishiya" bance komai ba ya daga ni ya dora akan gado, hawaye ya fara bin fuskata yace "kice hamma Saghir ina sonka" nayi shiru sai yayi ajjiyar zuciya yana hawowa gadon yace "watarana zaki fada, ina nan ina jira".
Ina kallon sa yana ta shirye shiryen sa, ni ko su inna ban gayawa zancen auren sa ba sai da suka ji daga gidan Alhaji Babba, Hajiya ta kira ni a waya "yanzu Diyam da gaske Saghir auren nan zaiyi? Shi yanzu kudin da zai kashe gurin auren ya bawa Alhaji su mana ko shago ya bude ya fara dan kasuwanci. Yanzu kina ganin kofar gidan nan ma da kyar Saghir ya saka ta shi ko a jikinsa ma wannan cin mutuncin da akayi wa gidan nan" "sai hakuri Hajiya" shine kawai abinda nace mata.
Har dani akaje aka kai lefe, aka saka rana akayi komai aka fara hidimar biki. Kowa sai mamaki na yake yi wai ni ko a jikina mijina zaiyi aure. Shi kuma Saghir kullum sai ya ce ince masa ya fasa aure ni kuma naki fada. Sai yayi fushi ya daina yi min magana sai kuma dan kansa ya sauko. Sadauki kuma bai kuma bi ta kaina ba, sai dai yakanje ya gaida Inna, kudin gidan gona kuwa account ya bude wa Asma'u ake zuba mata a ciki sai dai kawai su dauko suyi amfani da abinsu".
Satin bikin Saghir yana kamawa Hajiya ta kirani tace ita fa babu wani taro da zata yi, ni kuma sai nace zanyi walima ranar kawo amarya anan gidan Saghir, yadda kowa yazo in an kawo amarya sai ya ganta. Saghir yana ji ya fara fadan wai za'a bata masa gida. Ranar kafi suka zo suna ta daddaga hanci, na saka murja ta nuna musu spare dakin da yake sama suka ce "dama yace ba sai anyi mata komai ba ya saka komai a gidan, gadon ma da cewa yayi kar ayi mune muka ce sai anyi saboda kar a mata gori". Ina jinsu suna gulmar "wannan yar karamar yarinyar ce uwargida?".
Aka daura aure Saturday, Sunday kuma aka kawo amarya. Duk yan uwa sunzo walimar dana shirya, anci ansha sai kuma aka karbi amarya. Ni dai ina dakina basu kawo ta ba nima banje ba har aka gama kowa ya watse. Na shirya Subay'a nima na shirya muka yi kwanciyar mu sai na jiyo hayaniyar maza a waje, ni na manta ma ashe ana siyan baki. Sukayi ta hayaniyar su suka gama suka tafi ninina ta karanta novel din da Rumaisa ta turo min kafin ta tafi, sai ga Saghir ya shigo dakin. Ya hawo kan gadon ya karbi wayar daga hannuna yace "uwargida ran gida" sai abin ya bani dariya ma, yace "ki fito kiga amaryar ki. In ba kyason ta kuma kinyi alkawarin kula dani yadda ya kamata a yau zata koma gidan su" na mike ina saka hijab nace "ta sha zamanta. Tunda ba'a kaina zata zauna ba ni kuwa ina ruwana da ita?" Sai na wuce na barshi a nan. Ina shiga palo na ganta a xaune tana kallon kofar dakina. But unlike abinda Saghir yace na cewa nafita komai ni sai naga kamar ta fini komai except kyawun fuska. Ta fini shekaru, daga gani ta fini ilimin boko, ta fini girman jiki dan duk abubuwan da Saghir yake yawan complain cewa bani dasu ita tana dasu sosai. Tasha heavy make up da wani uban attach har gadon baya. Rigarta kusan rabin kirjinta a waje, na tambayi kaina "a haka akayi siyan bakin?" Na zauna nace "sannu amarya" ta kalleni tana yamutsa fuska tace "yauwa, sannu" Saghir ya shigo ya zauna a kusa da ita, kamar jira take yi sai ta dora kanta a kafadarsa hannunta kuma a kirjinsa. Nayi murmushi ina kallonsu, yace "Halima ga Fauziyya, Fauziyya ga Halima" ya kama jawabin zaman lafiya, baya son hayaniya waye da waye ya gama sai yace "to yanzu amarya zata gama kwana bakwai dinta da musulunci ya bata a matsayin ta na budurwa, daga nan sai kuma ayi maganar rabon kwana. Sai dariya taso kubce min na rufe baki na juya fuska, yace "kina da magana ne, Diyam?" Na girgiza kai, yace "no ki fadi abinda yake ranki, naga kamar kina dariya" nace "kawai dai naji kace budurwa ne, ni kuma da na ganta na dauka bazawara ce" sai tayi sauri ta mike zaune sosai tace "excuse me? Shi da zai aure ni bai gaya miki budurwa zai aura ko bazawara ba?" Nace "ba muyi wannan maganar dashi ba kuma to be frank bani da problem da koma wacece, Allah ya bada zaman lafiya, aci sati daya lafiya, sannan akan sati dayan na kara muku shekara daya kyauta from me to you" sai na mike nace "Allah ya bamu alkhairi".
Ina shiga daki yana shigowa shima, ya jawo ni tace "what? What was that? Wacce maganar banza naji kinyi a gurin can?" Nace "kyauta nayi maka ko ba ka so? Ji nake mai kula da kai a gado kake nema kuma gashi ka samu, ko shekarar tayi kadan ne in kara muku wata?" Sai na kwace jikina nace "and don't touch me kasan ba kwana na bane yau" na haye gado naja bargo.
Ya tsaya yana kallona sai yace "yanzu har tsanar da kika yi min ta kai haka? To shikenan, saki kike nema na sani kuma ba zaki samu ba. Naji, Fauziyya zata kula da gado na amma duk abinda ya danganci aikin gida ke zaki ke yi, wanke wanke, shara, girki da komai" na gyara kwanciya nace "done. Shekara ta nawa ina wanke wanke da shara da girkin? Dan dai karin kwano daya ai ba zai gagare ni ba". Na rufe ido nace "in zaka fita dan kashe mana fitila Please".
[2/17, 8:57 PM] +234 818 247 0922: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Forty Six: New Saghir
Jin yayi shiru kuma bai fita ba yasa na bude idona, na ganshi still a tsaye yana kallona, muna hada ido yace "me nayi miki me zafi haka Diyam? Still akan wannan dan iskan yaron ne ko? Saboda kina sonsa ne yasa kika tsane ni irin haka ko?" Na yaye abin rufar nace "don't bring Sadauki into this, babu ruwan Sadauki da tsakanin mu" yace "saboda an miki auren dole ne dani? It that it? Nima in kika tuna ba son auren nake yi ba lokacin da aka yishi" na girgiza kaina nace "ba dan an tilasta min aurenka bane ba Saghir. Su kansu wadanda suka tilasta min auren naka Inna da Alhaji ai ban rike su a zuciyata ba, babu komai a yanzu tsakanin mu sai kyautatawa da tausayi" yace "ni kuma fa Diyam? Menene nawa a ciki? Nasan ba kya sona but me yasa ba zaki bani dama ba?"
Na mike tsaye ina jin zuciyata tana karyewa nace "you......raped......me" sai jikinsa yayi sanyi, nace "in ka manta da dakin nan yana magana zai tuna maka, na nuna gado na nace "here, anan ka dasa irin kiyayyar ka a zuciyata. I was only 14 years then, ranar baffana kwanansa 47 a kasa and you raped me".
Hawayene kawai suke bin fuskata, ya diririce "Diyam na baki hakuri ai, I was drunk, I wasn't....." Nace "shine excuse dinka? Giya ce excuse dinka? Bayan kuma har yau shanta kake yi? How can you raped me and then expect me to enjoy sexual relationships da kai? Tun ranar gini ai tun ranar zane. Ka dasa tsiron ƙinka a raina sannan kazo ka zuba masa taki when you killed my babies" sai kuka ya kwace min "you killed my babies and you left me to die a asibiti".
Sai ya taho da sauri ya jawo ni ya rungume ni, na fara ture shi amma yaki sakina har na hakura nayi ta kuka na a jikinsa. Yayi kissing forehead dina yace "Diyam ba zan iya dawo da baya ba, amma nayi alkawarin gyara gaba. Kome kike so zan yi miki Diyam in dai zan goge baya, banda saki because I can't. I love you".
Knocking kofa akayi "Darling?" Fauziyya ta fada daga waje, na ture shi na hau kan gado na lulluba har kaina. Ina jinsa ya hawo yayi kissing Subay'a sannan ya fita gun darling din tasa.
Da safe tun dan tashi da assuba ban koma ba, fuskata duk ta kumbura tayi min nauyi saboda kukan da nasha jiya da dare na tausayin kaina da rayuwata. Yaushe zanji dadin aure ne ni? Na gabatar da adduoi na kamar kullum, ina rokon Allah ya bani ikon cin wannan jarabawar da nake ciki ta auren Saghir, idan har zama da Saghir shine mafi alkhairi abu a rayuwata Allah ya rage min kiyayyar sa daga zuciyata. Sannan kuma nayi addu'ar Allah ya bamu zaman lafiya da amarya. Dalilin da yasa na yarda da auren Saghir shine, ina ganin yin auren nasa wata hanya ce ta rage wa ksina tarin zunubin da nake dauka na gudunsa da nake yi, at least in da wata matar nasan wannan responsibility din ya ragu daga kaina.
Ina gamawa na sauka kitchen na fara fere dankali, sai ga murja nan ta shigo mu ka gaisa ta dauka ta fara tayani muna hirar mu, har muka gama na fara soyawa ita kuma tana soya kwai sai ga Saghir nan ya shigo, har yayi wanka yayi kwalliya, murja ta gaishe shi ta fita sai ya jawo stool ya zauna yana kallona "barka da assuba" nace ina kallon sa, yayi murmushi "good morning. Ina jin yunwa a bani abinci" nace "wai da so nake in hada muku kai da Fa'iza sai akai muku sama" yace "Fauziyya ba Fa'iza ba" na dafe kai "sorry. Fauziyya" ya girgiza kai "bacci take, ni kuma yinwa nake ji. Zubo min inci anan kawai" na zuba masa a plate na dora fork na mika masa, ya karba yace "naga Subay'a yau bacci take tayi" na hado masa tea na kawo masa na koma na cigaba da aikina shi kuma yana ci. Sai daya gama ya mike yazo bayana ya rungume ni yana shanshana gashina yace "am sorry Diyam kinji? I promise insha Allah zan saka ki murmushi more than yadda na saka ki kuka" ya juyo dani yace "da ace ina da dama da sai na bude nan" ya dora hannunsa a kirjina "na saka soyayya ta a ciki na rufe da kwado" na ture hannunsa ganin yana neman wuce gona da iri nace "stop it. Amarya tana sama tana jiranka" sai yayi murmushi kawai yace "zan fita. Sai na dawo".
Tare da murja muka gama aiyukan mu kamar kullum, sannan naje nayi wanka nayi wa Subay'a muka sauko muka fara cin abinci sai ga amarya ta sauko. Tana ta wani yayyatsina fuska, sai kawai na tsaya ina kallonta. Babu makeup din jiya, wannan ya sake fito da kamanninta sosai, sai nayi realizing ai na santa ma, tana daya daga cikin matan da suke zuwa har gida neman Saghir shi kuma yana ce min abokan aikin sa ne. Tazo ta zauna murja ta gaishe ta sai naga tana kallona irin kamar tana jira in gaisheta din nan tunda tana ganin ta girme ni. Nace "Subay'a ki gaishe da auntyn ki. Fa'iza ga Subay'a, koda yake nasan kin santa ma ai tun sanda kike zuwa" sai ta bini da kallo kawai. Na tashi na barta a dining nace "ga abinci nan Bismillah"
Na koma sama ina mamakin wannan rayuwar. Ni in nice Saghir ya zanyi in auri saura na, ai sabuwa zanso wadda ban taba testing ba, no wonder yazo yana shashshafa ni da sassafe.
Rayuwa ta cigaba da tafiya, har Fauziyya tayi sati a gidan. A ranar ne kuma Saghir ya tubure. "Babu wata shekara, ban yarda na. Eh an baku dama kuyi kyautar kwana amma sai da amincewar mijin ni kuma nace ban amince ba" na daga gira ina kallonsa a raina ina cewa 'zakayi saki reshe kama ganye kuwa' a dole na na hakura na karbi kwana na. Dokin da yake sai daya sa naji tausayin Fauziyya. Ni kuma kamar an saukar min da bacin rai haka naji nayi zamana a dakina amma sai gashi ya taho. Ina game a waya ya karba ya ajiye yace "me kike so inyi miki ne Diyam? Kuka zanyi ne ko tsallen kwado?" Na juya masa baya nace "duk wanda ranka yafi so" sai ya hawo gadon ya fara yi min tausa. Yace "da gaske fa nake. Say it, anything, yanzu zaki ga anyi miki" na tashi na zauna yace "kudi kike so?" Sai ya dauko bandir din 500 notes ya ajiye min akan cinyata yace "ki shirya gobe in kaiki shopping ki sayi kayayyakin ku na mata, kayan kwalliya, jaka, takalmi anything" na mayar masa da kudin sa nace "ka sayi kayan abinci ka kai gidan Alhaji" ya dawo min da kudin yace "angama. Can we please go to my room? Kinga Subay'a tana nan".
Washegari kuwa ya fita dani, yayi ta lodo min kaya komai ya gani na mata sai ya dauka, "wannan zaiyi miki kyau, wannan ma yana da kyau, wannan zai dace dake" haka dai yayi ta fama. Muna dawowa gida muka tarar babu abinci, bata yi ba tunda girkina ne dan haka na shiga kitchen na dora da yake weekend ne Subay'a tana sama tare da Saghir suna kallo. Riga da wando ne a jikina kaina babu dankwali na daga gashina sama ina ta aiki na ina jin kida a waya ta sai naji kawai wani strange kamshi da ban sani ba, ina juyo wa sai naga wani mutum a tsaye a palo yana kallona muna hada ido sai cewa yayi "Fauziyya tana nan?" Ni kuwa na zunduma ihu ina kiran Saghir, sai kuwa gashi nan a guje ya sauko kafin mutumin ya fita. Ya damko shi yana tambayarsa lfy sai cewa yayi wai shi gurin Fauziyya yazo shi dan uwanta ne kuma ita tace mishi ya shigo. Ranar naga bala'i a gurin Saghir, daga Fauziyyan har bakon nata ya haɗa ya balbale su da fada daga baya ma ya haɗa har da maigadi wanda yayi ta faman rantsuwa a kan cewa shi bai san mutumin ya shigo ba. Ni dai na dauki yata muka koma sama nace ku kare kalau.
Sai da daddare kuma Saghir yayi ta bani hakuri. Nace "duk wanda ya sayi rariya dama ai yasan zata zubar da ruwa. Tun da har ka auri yarinyar daka gama nema a waje ai kasan dole zata kawo maka maxa gida kaima. Duk abinda kayi ai kaima dole za'ayi maka. Haka rayuwa take" ya fahimci magana nake fada masa sai yace "kin san ai dalilin da yasa nayi auren nan ko? So nake kike kula dani yadda ya kamata sai nayi tunanin idan nayi aure kika ga wata tana kula dani kema zaki koya. Wannan shi yasa na auri Fauziyya saboda bana son in auri wata wadda itama bata iya din ba" a raina nace "oh, ita wannan ta iya din kenan"
Rayuwa ta cigaba da tafiya. Saghir har mamaki yake bani yadda yake yi min, gabadayansa ya chanja kuma duk abinda nace to kuwa zaiyi shi sai dai in bance din ba. Na saka shi ya ke kai kayan abinci gidan su, sannan kuma na daina jin warin giya a tare dashi duk da ban tabbatar ko ya daina sha ba. Fauziyya bata da problem, tana dai da daga kai da nuna irin ta fini dinnan amma tunda ta fahimci yadda Saghir yake ji dani sai ta ja baya. Bamu fiya zama muyi hira ba kowa harkar gabansa yake yi. In ranar girkin tane tayi ta iyayi da rawar kai ni kuma in ranar girkina ne Saghir yayi ta rawar kafa, duk da dai ba koda yaushe yake samun abinda yake so din ba dan wani lokacin rufe kofa ta nake in kashe waya, watarana kuma in naje in bata rai har sai ya hakura ya rabu dani. A lokacin ne kuma bikin Rumaisa ya tashi, za'a hada ayi tare dana yaya Mukhtar. Lokacin muna 22 years, tana kuma final year dinta a jami'a.
Bikin yana matsowa na tambayi Saghir sati biyu. Ya rike baki "sati biyu kuma Diyam? Kwana nawa za'ayi ana bikin da har zakiyi sati biyu?" Nace "nice fa babbar kawar amarya. In ina nan ta yaya zanyi shirye shirye?" Babu yadda zaiyi yace "shikenan" amma ina kira Mama na gaya mata zan taho tace "baki da hankali dama? Babu wani sati biyu da zaki zo kiyi, sati daya zakiyi shima kuma dan kina da abokiyar zama ne da ba zan barki ki taho ki barshi shi kadai ba" ranar har kuka nayi, I just needed a break from the house and from Saghir.
Sai satin bikin sannan Saghir ya kaini gidan Mama. Ya kuma buga min warning "saura kuma ki shiga cikin yammata kuyi ta shiririta. Kinsan dai ke mai aure ce ko?" Nace "uhm" a raina ina mamakin wai yau Saghir ne yake kishi na. Ko yaushe zan fara nasa ni?
Munsha bikin mu lafiya mun gama lafiya. Da muka je dinner naga yadda Rumaisa take nishadi da mijinta sai naji wani longing a zuciyata. I missed all this, ni banyi yammatanci ba kuma babu abinda zan adar na bikina. Ranar Lahadi muka kai amarya dakin ta. Litinin kuma na biyo su Inna muka dawo gida tunda satin da aka bani bai kare ba sai nan da kwana biyu. Muna zuwa naji Maman Iman tana soya wainar fulawa sai na aika Asma'u ta karbo min na zauna ina ci.
Ina tsaka da ci sai kawai jin sallamar Sadauki mukayi wai ashe duk mondays yake zuwa ya gaishe da Inna. Na sunkuyar da kaina ina jin wainar ta fita daga raina har ya shigo ya gaishe da Inna da Mama sannan na dago na gaishe shi. Ya amsa yace "ya family?" Sai na kasa reply. Ya mike zai tafi Mama tace "oh Sadauki kaki aure har yanzu? Ko so kake ayi maka kidan tuzuru ne?" Ta tsaya yana shafa kansa, muka hada ido yace "an kusa ai mama insha Allah" Inna tace "alhamdulillah, ai gwara ayi din, aure ai shine cikar kamala da kimar mutum. An sami matar kenan" yace "eh, a can gida ne. A Maiduguri ne" sai naji wainar dana ci duk ta tattaro ta dawo makogwaro na, da sauri na mike na shiga toilet sai da na amayo duk wainar da naci.
[2/19, 5:19 PM] +234 818 247 0922: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Forty Seven : The Messages
Sai dana gama sannan na zauna akan toilet seat na dafe kaina, ina jin jiri yana juyani duk da cewa a zaune nake. Nayi iyakacin kokari na gurin ganin cewa ban yi tunanin maganar da Sadauki ya fada a palo ba sannan na mike na wanke bakina da fuskata na fita, ina tunanin ya riga ya tafi amma ina fita sai na ganshi a tsaye yana kallona yace "ba kya jin dadi ashe? Allah ya sawake" na sunkuyar da kaina ciki ciki nace "ameen" sannan na wuce shi zan shiga cikin daki Inna tace "ba kiji Sadauki yana miki sannu ba? Shine kika wuce ba zaki amsa shi ba?" Na juyo nace "Inna nace masa ameen, ameen, ameen summa ameen,me kuma yake so ince masa" sai kawai yayi murmushi ya juya ya fita, inna kuma ta rufe ni da fada Mama tana taya ta, na zauna kawai nayi tagumi da hannu bibbiyu ina jinsu har suka gama sannan na zame na kwanta a gurin ina jin jikina kamar mai zazzaɓi har Mama tayi mana sallama ta tafi.
Kwana biyun haka na kare su babu lafiya sosai, na so inki komawa saboda bana jin dadi amma Inna ta matsa Saghir ma kuma yace in ma zan zauna sai dai ya dauki Subay'a saboda makaranta ni kuma bana jin zan iya barin ta tare da Fauziyya dan nasan ba kunya ce ta ishe ta ba. Dan haka dole na shirya Saghir yazo muka tafi. A hanya ya kalleni yace "kin kara kiba, baki da lafiya amma kinyi kiba kin kara fari. What's the secret?" Na bata rai nace "what secret kuma?" Yayi murmushi "wai cewa nayi ko Subay'a ce zata yi kani? It is about time, tayi girma da yawa" na juya kai ina kallon titi" I missed my period wannan watan, a lokacin bikin nan ya kamata inyi kuma banyi ba but that doesn't mean anything tunda dama ina missing sometimes. Ina ganinsa yayi packing a bakery suka shiga shida Subay'a suka lodo kayan ciye ciye sannan muka tafi.
A toilet da zan shiga wanka na tsaya ina kallon kaina a mirror, da gaske nayi girma na ciko ta koina musamman hips, abinda da bani dasu sai yanzu suke zuwa kuma. A raina nace "sai yanzu makerin budurci ya tuna dani" after I lost mine long time ago.
Na fito daga wanka kenan ina shiryawa text ya shigo wayata. Na daga sai naga number din Sadauki, a raina nace "really? Ko dai batan kai yayi?" Sai kawai na ajiye wayar nayi shiryawa ta. Saghir ya shigo da magunguna a leda ya bani yana taba wuyana yace "gobe asibiti ya kamata muje in zazzabin nan bai tafi ba, test nake so ayi miki ma dan ni jikina yana bani ciki ne" nace "no fa ba wani ciki" amma a raina sai naji ina son ma ace cikin ne, I was really in need of love, kuma ina ganin haihuwa zata taimaka min sosai" na kwanta na dauki wayata yace "za'a fara karatun ko? Bana hana ba?" Nace "to me zanyi? Babu wani abin yi sai dai mutum yayi bacci ya tashi ya gyara gida yayi girki ya kuma komawa tayi bacci" ya danyi shiru yana kallona kamar mai tunani sai yace "kina son komawa school?" Nayi saurin kallonsa, ban taba tambaya ba saboda banyi tunanin zai bari ba amma raina yana so, ina son in zama abinda baffana ya ke kwadayi, nace "da gaske?" Ya daga kafada yace "why not? In dai zai faranta miki that's what I will do" sai na kama tsalle ina murna shi kuma yana dariya sannan ya jawo ni yace "so? Me zaki karanta?" Nayi shiru ina tunani. Na tuna wani visiting da Sadauk yaje min school shida wani abokinsa and we talked about carrier, a lokaci nace musu bani da choice sai Sadauki yace later in life zan fahimci role din daya kamata inyi playing a rayuwa, but yet still, bani da choice a raina.
Nace "me kake ganin ya kamata?" Yace "anything. Nasan ku mata da son harkar health, zaki iya yin nursing ko midwifery. In ma kuma medicine din kike so sai inyi wa Mr Abatcha magana ya hada ni da wani a samo miki admission" na ture shi ina jin raina ya baci nace "forget Mr Abatcha din nan" yace "why? Shi ya bani wannan shawarar ma fa, ya tambaye ni kina makaranta nace a'a sai yace ya kamata in saka ki. Kinga ai he will be willing to help" na girgiza kaina nace "na fasa karatun" sai kawai ya tsaya yana kallona da mamaki.
Sai da zan kwanta na bude message din Sadauki "ya jikin? Allah ya kara afuwa ameen" nayi tsaki na ajiye wayar na kwanta, sai kuma na tashi na sake karantawa sai kawai na kashe wayar na jawo drawer na saka ta nayi kwanciya ta.
Da safe muna breakfast gabaki dayan mu har Fauziyya, ya ajiye ledar drugs din daya siyo min jiya yace "kina gama cin abinci zaki sha magani, dan naga ashe jiya baki sha ba kwata kwata" nace " in tambaye ka mana Please" ya ajiye spoon din hannunsa yace "ina jin ki" nace "ya sunan ogan ku na office" ya bata rai yace "Mr Abatcha mana" na girgiza kai nace "sunan shi na gaskiya nake nufi. Like sunan da yake rubuta wa in an bukaci sunansa" ya danyi tunani yace "Engineer Aliyu Umar Abatcha" na gyada kai nace "ohh okay" yace "me yasa kika tambaya?" Nace "a bikin nan ne naji ana zancen wani, I tot shine ashe bashi bane ba" yayi murmushi ya fara praising Mr Abatcha "yana da kirki sosai, na girme shi amma mi gaskiya he is my role model. He is very smart and intelligent. Kuma yana sona. Kunga yadda yake korar mutane kuwa duk wanda yaga wasa yake yi ba aiki ba yanzu zai tura maka quiry amma ni ko sau daya bai taba bani ba. Diyam kin tuna sanda ya tura ni Germany? Sai da naje na fahimci ya tura ni ne kawai dan in huta ashe already ya riga yayi sighing contract din. Sai dan workshop dana ringa zuwa kawai" na girgiza kaina a raina nace 'ya tura ka ne dan ya samu damar zuba kaji a gidan ku'.
Munje asibiti anyi min pt and it came back positive. Sai naji dadi, maybe wannan haihuwar ta zamo min silar gyaruwar lamura na. Saghir kam doki har a gaban Fauziyya, ya bawa Subay'a labarin zata yi sister ko brother ita ma tayi ta murna. And yana fita sai gashi da sabuwar waya, yace "wannan tsohuwar wayar taki dai ya kamata ki ajiye ta haka" na karba nayi masa godiya sai kuma ya tambaye ni in akwai abinda nake so. Na zauna kusa dashi nace "so nake kayi wa su Murja aure" ya bata rai, nace "Please, auren suke so wallahi kuma Alhaji bashi da halin yi musu to waye zaiyi musu in ba kai ba? Su ba karatu ba, su ba aure ba me kake tunanin xasu yi?" Yana kallona yace "sai in kinyi min alkawarin kema zaki koma school" nace "sai in kayi min alkawarin zaka daina shan giya" ya daga kafada "na daina fa" na tsare shi da ido sai yace "na kusa dainawa. Seriously na kwana biyu rabo na da ita" nace "mata fa?" Yace "na daina wannan tunda na kara aure ai" sai kuma ya jawo ni yace "tell me, kishi kike yi?" Nace "Saghir ko bana sonka, kai mijina ne, kuma uban yayana, ba zan so kuma yayana su tashi suga babansu da wadannan halayyar ba". Yayi murmushi yace "am getting there".
And two days after that. Ina ta aiyukan gyaran gidana, da yake ni ban damu ba ko aikina ne ko na Fauziyya ni in dai na tashi zan gyara gida saboda bana son kazanta, it irritates me, ina mopping kasa Saghir ya leko ta stairs yace min "ina tsohuwar wayar kine? Naga har yau baki kunna sabuwar ba" nace "tana bedside drawer ta" na cigaba da aikina.
Na gama naje na wanke mop, na dawo ina saka turaren wuta Fauziyya ta sauko ta kunna tv ta kwanta tana kallo. Sai Saghir ya sauko da wayata a hannunsa, I looked at his face and I felt something knot in my stomach. Ya nuna min wayar "waye wannan?" Fauziyya ta mike zaune tana kallon mu. Message na gani a jikin wayar "ya jikin? Allah ya kara afuwa ameen" na girgiza kaina nace "duba ni ake yi, what's there?" Sai yayi scrolling sama, tun message din farko.
"Third option. Kazo a baka hakurin da kake so"
"tomorrow evening. Gidan Baffa"
"ina yiwa Asma'u godiyar kyautar da aka yi mata. Allah ya kara arziki mai albarka"
"You are welcome".
Na daga kafada, ni banga abin tayar da hankali a cikin maganganun mu ba. Ya sake cewa "waye wannan Diyam? Sadauki ne ko? Amana ta kike ci ko Diyam? Wato abinda yasa kike guduna saboda kina samu a wani wajen ko? I always tot, yarinyar nan sai kace dutse, ashe kina da tap din da kike karbar rabonki a gurinsa".
Na zaro ido "wanne irin magana kake yi? How can You even accuse me of that. Menene a cikin messages din nan da zasu saka har ka fadi haka? Yes, munyi magana sanda suke case da Alhaji Babba kuma yayi wa Asma'u kyauta na yi mata godiya. Menene a ciki?" Yace "to uban wanene ya gaya masa baki da lafiya har yake duba ki?" Nace "a gida ya same ni yaje gaida Inna yaga bani da lafiya. I don't even know me yasa nake defending kaina. Dan kana yin abu sai ka dauka kowa ma yi yake yi?".
A girgiza kai idonsa jawur yace "am going to trace him. Am going to enter his number into my phone and call him. In na gano inda yake kuma wallahi sai na daure shi. Sai yasan matata ya taba" ya juya da sauri zai koma sama sai nayi saurin rike rigarsa "Saghir ka tsaya ka saurare ni. Wallahi ba abinda kake tunani bane ba" ya juyo a fusace ya sauke min mari a fuskata, kafin inyi wani abu ya sake sauke min wani a same side. Na rine fuskata ina jin jini yana bin hancina, ganina yayi dusu dusu. Amma still na rike rigarsa i a girgiza masa kaina, ta gefen idona na hango Fauziyya tana dariya, sai ya warce rigarsa ya hankada ni da karfi na fadi, unluckily sai cikina ya bugu da kafar bene, na mirgina gefe ina rike marata da hannun bibbiyu shi kuma yayi sama da sauri ba tare daya kalli inda nake ba.
Na sake kokarin mikewa amma marata ta rike kam sai da kyar na daddafa stairs na mike, tunani na daya shine in Saghir yayi dialing number din Sadauki a wayarsa zaiga Mr Abatcha. And that can destroy Sadauki's reputation a gurin aikinsa. Na juya na kalli Fauziyya da take zaune tana kallo na da murmushi a fuskarta nace "get up from my chair. Munafuka"
Sai na kama bene ina tafiya a hankali nabi Saghir a baya. Ina hawa sama yana fitowa daga dakinsa hannayensa da waya ta da kuma tashi. Nace "ka saurare ni Saghir" bai ce komai ba ya fara daddanna wayar sa. A lokacin mara ta tayi wata irin murdawar da sai da na kai kan guiwowina na runtse idona, sai ji nayi yace
"Mr Abatcha? Menene hadin Sadauki da Mr Abatcha?"
[2/19, 8:38 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Forty Eight: When The Going Gets Tough
Bature yace "when the going gets tough, only the tough gets going" hakane?
It is either you get tough ko kuma kana ji kana gani a tafi a barka.
"Mr Abatcha? Menene hadin Sadauki da Mr Abatcha?" Na dafa bango na mike ina kallonsa kawai. Babu abinda zance masa a yanzu, dama kokari na shine inyi preventing dinsa from finding out kuma ya riga yayi. So magana ta kare kuma.
Ya zuba min ido, "magana nake miki Diyam? Sadauki kike texting ko Mr Abatcha" kallon da nake masa yasa ya tsaya shima yana kallona and then the realization hits him. I saw lokacin da yanayin fuskarsa gaba-daya ya chanza, ya saki wayoyin duk guda biyun suka zube a kasa. His whole world came crashing down on him.
"Mr Abatcha? Mr Abatcha shine Sadauki? When? How?" Ya saka hannayensa duk biyun acikin kansa ya fara zagaya palon da sauri har wani gumi ne yake karyo masa. Idonsa ya ciko da kwalla. Ya taho da sauri ya tsaya a gaba na "you? You were playing me all these years? All these years kina tare dashi dama? My God!" Ya sake dora hannu aka jikinsa har rawa yake sai ya dafa kujera yana mayar da numfashi. Ya jima a haka sannan ya juyo yana kallona sannan yace "ke kika saka shi ya bani aiki ko? I remember ke kika ce inje in nemi aiki. Ke kika saka ya dauke ni without even looking at my credentials saboda ku kasance tare ko? Saboda kuyi controlling dina ko? Is that it?" Na girgiza kai kawai amma kafin inyi magana yace "kar kice min komai, ko inzo in babballaki anan. My God, wannan wanne irin cin amana ne, hatta sunan da zan sakawa yata shi ya zaba min" sai ya fara dukan kansa da hannunsa yana cewa "wawa, dolo, soko, dakiki".
Sai kuma ya zauna akan kujera ya dafe kansa da hannayensa yana girgiza kai. Yace "wato tare kukayi planning din abinda aka yiwa Alhaji ko? Shi yasa ya tura ni tafiya a lokacin. Da aka gayamin sharadan daya saka sai da nayi tunanin me yasa a ciki bai ce in sake ki ya aura ba, ashe baya bukatar wannan tunda already yana tare da ke".
Kamar wuka haka maganganun Saghir suke huda ni. Wannan accusations din yana daya daga cikin abinda na kasa mantawa har yau. Komai zan gaya masa ba zai fahimta ba, amma duk da haka zan gaya masa ruwansa ne kuma in ya dauka in kuma bai dauka ba matsalar sa. I was beyond caring a lokacin.
Nace "sanda Sadauki ya dauke ka aiki bansan shi bane ba, bai taba contacting dina ba, I had no idea yana ina ma har sai ranar da kuka shirya masa party, a ranar nasan shine oganka. Bansan dalilin sa na daukan ka aiki ba, zata iya yiwuwa ya dauke kane kamar kowa, wannan shi yasa ban gaya maka ba tunda ina ganin fadin bashi da amfani. Bamu taba magana ni da Sadauki ba in banda sanda Alhaji ya tura ni gurinsa, a lokacin ma yayi shutting dina out dan haka babu maganar da muka yi sai wadda takaini. Bamu taba waya da Sadauki ba. Texts din da ka gani sune a tsakanin mu. Wannan shine gaskiyar magana" na juya zan bar gurin naji kafafuwana sun rike tun daga cinyoyi na zuwa marata suna min wata irin suka. Nace "Saghir?" Bai amsa ba sai cewa yayi "karki gaya min karyar banza. Wallahi bai isa ba. Baku isa ba daga ke har shi kuyi min wannan cin mutuncin. Sai na nuna masa dukiyar sa ta banza ce wallahi sai ya raina kansa. I will destroy him ko zan rasa raina wallahi." Sai ya shiga daki ya dauko key din mota, zai wuce ni na rike rigarsa nace "Saghir bani da lafiya" ya kwace rigarsa yace "zaki warke ne ma, munafuka" ya fice ya barni without another look at my side.
Na daga rigata naga jini yana bin kafata a dai dai lokacin dana ji tashin motarsa. And I realized something, na rasa cikin jikina kamar yadda na rasa twins dina. And there and then na yanke shawara, na gama auren Saghir.
Nayi kokarin motsawa daga gurin na kasa. Ina so in taimaki kaina kuma ina son in warning Sadauki dan ban san me Saghir zaiyi ba daya fita amma na kasa zuwa ina waya ta take yashe a kofar dakin Saghir. Kafafuwana tamkar sun daina aiki haka nake jinsu sai jini ne yake biyo su zuwa kan tiles. Option dina daya, Fauziyya. Na fara kiranta da dan abinda ya sauwaka daga murya ta. "Fauziyya, Fauziyya" amma shiru, ban tabbatar ta jini ba ko a'a saboda nasan kallo takeyi. Na jima a haka sannan na jiyo hawowarta sama. Tana shigowa palon ta tsaya tana kallo na yadda na hada gumi ga busashshen jini a hancina ga kuma jinin da yake kwance a kasa na sai ta saki purse din hannunta ta taho da sauri "Halima? Me ya same ki haka?" Cikina kawai na iya na nuna mata, ta kama ni ta kwantar a gurin sannan ta koma ta dauko jakarta data yar ta dauko wayarta ta fara kira. Jikina ya bani Saghir take kira sai kuwa mukaji wayar tasa tana kara a kusa da tawa. Ta ajiye wayar tace min "ina ya tafi?" Kaina kawai na girgiza mata, sai tace "ko miscarriage kike yi ne? Ko asibiti zamu je?" Na gyada mata kai sai ta kama ni zuwa toilet dina, ta taimaka min na wanke jiki na amma fa jini zuba yake dan pad ma ba zata rike shiba sai face towel ta bani na saka muka tafi. She half carried my down the stairs sannan ta saka mai gadi ya samo mana abin hawa muka tafi asibiti. Wannan yasa ba zan taba mantawa da Fauziyya ba.
Bayan fitar Saghir daga gidansa ya shiga motarsa ransa a mugun bace, bai taba jin bacin rai irin na ranar ba danji yake kamar ya hada ni da Sadauki ya saka mana wuta mu kone. Sai kawai ya bude aljihun motarsa ya dauko wata tsohuwar ajjiyar sa da kullum in ya dauko zai sha sai ya tuna yayi wa Diyam alkawarin ya daina sha. But yau Diyam din ce da kanta ta bata masa dan haka with vengeance ya shanye kwalbar gabaki dayan ta sannan ya kunna motar ya fita daga gidan ya tunkari kamfanin Abatcha Motors.
Sadauki yana cikin meeting da ma'aikatan sa, meeting din da ba'a ko gayyaci Saghir ba sai assistant dinsa. Sadauki yana tsaka da yin bayanin sababbin dokokin da yake kafawa saboda ma'aikatan da suke incompetent da irin hukuncin da za'a ke dauka akan duk mai karya doka sai ga Saghir ya banko kofa ya shigo, duk suka juya suna kallonsa ya taho yana tangadi ya nuna Sadauki yace "munafiki. Allah ya tona asirin ka yau" gaba-daya gurin suka mike, wasu daga ciki suka mike suka yo kan Saghir amma sai Sadauki ya dakatar dasu da hannu yace "ku rabu dashi" ya gyara zama ya kalli Saghir yace "menene yake tafe da kai?" Saghir ya nuna Sadauki yana kallon mutanen gurin yace
"wannan da kuke gani is not who he is saying he is. Ba sunan shi Abatcha ba sunan shi Sadauki kuma Sadauki shine Mr Abatcha kuma shine saurayin Diyam kuma Diyam kullum sai ta fadi sunan Sadauki ashe shine Mr Abatcha. Shine kuma ya bani aiki sannan ya saka wa yata suna ya siya mata ragon suna. Yazo kuma ya kai Alhaji kara ya karbi rabin gidan sa yayi gidan gona. Sai yau na ga message din sa a wayarta sannan na gane ashe shine"
Wani a gurin yace "do you understand cewa baka making sense kwata kwata?" Sauran mutanen suka kwashe da dariya. Sadauki yayi ajjiyar zuciya ya nuna Saghir yace "Ladies and gentlemen, this is an example of one of the effects of shaye shaye" sai ya kalli security yace "get him out of my sight".
A asibiti akayi confirming fitar cikina. Amma suka ce bai gama fita ba. Sai suka bani wani tablet suka ce zai fitar da sauran. Muna can lokacin tashin su Subay'a daga school yayi, Fauziyya ta koma gida ta dauko ta ta kai makotan mu sannan ta dawo gurina.
Har muka koma gida gurin magrib Saghir bai dawo ba. Na sha tablet din sannan na kwanta, Subay'a tana ta jera min sannu. Na sake trying number din Sadauki bata shiga, duk da dai nasan koma menene zai faru ya riga ya faru. Na kwanta ina ta jiran shigowar Saghir amma shiru har bacci ya dauke ni banji ya shigo gidan ba. Cikin dare wani azababben ciwon mara ya tashe ni, ji nayi kamar raina zai fita gashi daga ni sai Subay'a a daki. Jini guda guda haka ya rinka fita daga jikina. Ban yi bacci ba sai da aka fara kiraye kirayen sallah.
Cikin bacci naji Fauziyya ta shigo dakin tana tashin Subay'a, sai kuma tace min "Daddy fa bai kwana gidan nan ba. Ga wayarsa kuma tana nan. Na kira Kabiru kuma yace basa tare. Ko zaki kira gidan Alhaji kiji ko yana can?" Nace mata to kawai, amma ba wanda na kira. Ita ta shirya Subay'a ta mika ta school sannan ta dawo ta kawo min tea.
Zuwa 12 na dan warware, sai dai weakness sannan kana kallona zaka ga nayi pale saboda ba karamin jini na zubar ba. Na tashi nayi wanka, na fito na shirya sai na tsaya ina kallon kaina a mirror. Na dora hannuna akan marata ina tabbatar wa kaina cewa it is gone. It is dead before it even begins living. It is going to be the last thing da zanyi loosing a sanadiyar auren Saghir. Ina saka kaya na sai na jawo akwati na fara zuba kayana dana Subay'a. Ina cikin zubawa Fauziyya ta shigo, yanayin ta kamar a rude tace "Halima, kizo inji Kabiru" ta fita na saka hijab dina na bita a baya. Yana tsaye a bakin kofa ya kalle mu yace "Saghir yana station tun jiya. Bansan me ya faru ba amma ance security din gurin aikinsa ne suka kama shi suka damka shi a hannun police. Ban san menene charges din ba. Nayi kokarin yin bail dinsa sun hana ni, sunce order ce direct from the commissioner of police cewa kar a bayar da bail dinsa".
Fauziyya ta zame ta zauna. Ni kuma sai na juya nayi hanyar sama. Kabir yace "Diyam ki kira gida ki fada. Maybe Alhaji yana da wani a sama wanda zai saka a fito dashi" na gyada masa kai kawai na wuce. Ina zuwa daki na karasa hada kayana na fito na wuce Fauziyya a palo ta zabga tagumi na je na dauko Subay'a na dawo na sake wuceta. Na shirya Subay'a sannan muka sauko tare da akwatin kayan mu. Fauziyya ta tashi tsaye tana kallon mu tace "ina zuwa haka?" Nace "gida" bata kuma cewa komai ba har muka fita. Mai gadi yayi min sannu da jiki sannan ya taya mu da kaya muka tari abin hawa muka tafi.
Inna tana ganina da akwati tace "lafiya" na ajiye kayan hannu na sannan na gaishe ta, bata amsa ba tace "lfy nace? Lafiya na ganki da tsakar ranar nan da akwati?" Na sunkuyar da kaina nace "Inna na gama auren Saghir" ta saka salati, "shi Saghir din ne ya turo ki gida ko kuma ke kika yi ra'ayin kin gama aurensa kika taho gida? Dama igiyar auren a hannun ki take?" Na girgiza kai nace "Inna Saghir fa...." Tace "Saghir me? Saghir din yanzu ai bana da bane ba. Kika zauna da wancan Saghir din ma ballantana wannan da kowa ya tabbatar ya chanja. Dama tun randa Sadauki yazo nan da maganar aurensa naga yadda kikayi nasan in ba sa'a akayi ba sai kin fito da wata maganar kuma" naji hawaye ya fara bin fuskata, nace "Inna ba a kan Sadauki na taho gida ba, tsakani na da Saghir ne, ni ba zan koma gidan sa ba Inna. Dan Allah karki mayar dani" tace "ina Saghir din?" Na share hawaye na nace "yana police station" ta sake wani salatin "me ya faru? Me yake yi a can?" Nace "Sadauki ne ya rufe shi." Ta mike tace "kuma kika ce ba'a kan Sadauki bane ba. kira min Sadauki yanzu yanzun nan" nace "na baro wayata a can gidan. Kuma ma ba daukan wayata yake yi ba" ta kwalla kiran Asma'u. Tana zuwa tace mata "kira min Sadauki da wayarki" Asma'u tana kallo na da alamar tambaya ta dauko wayarta ta danna kira ta saka a speaker. Har ta gama ringing bai dauka ba sannan ta sake kira shima shiru. Sai kuma gashi ya kira. Ta dauka tasa a speaker naji muryar sa yace "Yar Asama ya akayi?" Tace "Inna ce tace in kira ka. Gata" Inna tace "Sadauki me ya hada ka da mijin Diyam har ka rufe shi?" Yayi shiru, ni kaina sai da nayi mamakin karfin halin Inna. Sai ta ce "tazo gida yanzu tace wai ka kama Saghir ka rufe shi" ya sake yin shiru sannan yace "ita Diyam din ce ta kawo kara ta akan na rufe mata miji?" Nayi saurin girgiza kai zanyi magana Inna ta harare ni tace "eh fa, shine nayi mamaki nace me ya hada ku?" Yace "a ce wa Diyam tayi hakuri, za'a fito mata da mijinta gobe in Allah ya kai mu" sai ya katse wayar.
Na saka sabon kuka "Inna yanzu haushi na fa zaiji yace na kawo kararsa" Inna tace "na sani ai. Haka nake so saboda ki fita harkarsa ki barshi yayi aurensa kema ki zauna ki rike naki auren". [2/21, 12:53 PM] +234 818 247 0922: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Forty Nine : The Utterance
Inna taga ta kanta a gurin jama'a jiya. Duk inda na shiga kowa kokawa yake yi da abinda Inna tayi. But to me, laifin Inna a yanzu guda daya ne, rashin sauraron Diyam kafin ta yanke hukunci bawai hada Diyam da tayi da Sadauki ba. Wannan kuma shine halin kusan 70% na northern mothers. Kullum su dai burinsu shine yarsu ta zauna a gidan mijinta kar ta kashe auren ta dawo gida ta zauna a gabansu. But what if the marriage is not working? What if she is buying her ticket to hell fire instead of paradise a cikin auren?
And Saghir, Saghir yayi laifuffuka da dama a baya but a yanzu laifinsa shine dukan Diyam. Nothing, nothing gives a husband the right to hit his wife. Duk kuma namijin da yake dukan matarsa to ba mijin aure bane ba, ballantana mata mai ciki? Hmmm
Then Sadauki. Na lura Sadauki ya zama shafaffe da mai a gurin readers, sam basa ganin laifinsa komai yayi daidai ne dan ina jin few mutane ne naga sunyi comment akan laifin Sadauki. Sadauki is rather rude and very authoritative. Ba shi da right din da zai sa a rufe Saghir, yes Saghir yazo gurin aiki drunk kuma ya fadi maganganu wadanda babu wanda ya gane in banda shi Sadauki da ake magana a kansa. Abinda ya kamata Sadauki yayi shine yasa ka security su fitar dashi waje, in ya ga dama ya hada masa da takardar kora daga aiki. But bashi da right din kaishi station a rufe shi kuma wai without bail, saboda yana da kudi?
Let's continue
Na rufe fuskata ina girgiza kaina da sauri. "Inna kar kiyi min haka dan Allah. Inna ki tsaya ki saurare ni ki fahimce ni kar ki mayar dani gidan Saghir in na koma wallahi mutuwa zanyi" tace "da baki mutu ba shekara da shekaru sai yanzu da Sadauki zaiyi aure shine zaki mutu?" Sai ta mike zata shige daki nima na mike da sauri na rike hannunta da hannu na daya dayan kuma na daga mara ta da shi nace "Inna nayi bari jiya" sai ta juyo tana kallo na ido a bude, ta taba fuskata da hannunta tace "bari Diyam? Ya akayi kika san bari ne kinje asibiti?" Na gyada kaina nace "naje Inna, su suka tabbatar min da cikin jikina ya fita Inna. Saghir ya fitar min dashi" ta dan bata rai cikin rashin fahimta tace "Saghir? Ta yaya Saghir zai fitar miki da ciki?" Nace "dukana yayi Inna, dukana Saghir yayi ya buga ni da jikin bene ya kashe min baby na, kamar yadda shaye shayensa ya jawo mutuwar yan biyu".
Sai ta kama hannuna muka zauna tace "Diyam, kin tabbatar abinda kike gaya min gaskiya ne? Me ya hada ki da Saghir har ya dake ki haka?" Na shafa fuskata sai itama ta saka hannu ta taba fuskar tawa, side din da Saghir ya mare ni, na dan yamutsa fuska alamar zafi sai naga idonta ya kawo kwalla amma sai tayi sauri ta mayar da ita. Tace "me ya haɗa ku nace" sai na bata labarin messages din Sadauki. Tana girgiza kai tace "me yasa? Me yasa zaki ajiye sakon Sadauki a wayar ki har mijinki ya gani bayan kuma kinsan yasan tsakanin ki da Sadaukin" nace "inna na fada miki menene a cikin sakon nan, babu wata kalma ko daya data kauce hanya a ciki kuma in na goge su ai kamar bani da gaskiya kenan. Ina son Sadauki na sani, amma Allah ne shaidata cewa ko sau daya ban taba tunanin yin sabon Allah da Sadauki ba. Kuma ke kece shaida, Sadaukin nan tamkar dodanniya haka nake a gurinsa, ko kallon inda nake baya yi. Shi dai ya zarge ni ne saboda shi din yasan shi mai laifi ne, abinda yake cikin tasa wayar idanuwa ma ba zasu iya gani ballantana hankali ya dauka" Inna tace "akan wannan maganar ne Sadauki ya sa aka kama shi?" Nace "ni ban sani ba, amma ina jin akanta din ne. Ya dai fita a fusace yace sai ya wulakanta Sadauki, tun daga nan kuma bai dawo ba sai da safe Kabiru abokinsa yazo yace mana yana hannun yan sanda" Inna tayi shiru tana tunani sannan tace "yace za'a sake shi gobe, Allah ya kaimu goben, ya fito sai yazo yayi bayanin dalilin da yasa ya dake ki. Kar ki goge messages din ki barsu saboda shaida a gani cewa babu abin duka a cikin su".
Sai naji raina yayi min wani irin dadi, babu abinda yafi dadi irin a fahimce ka babu kuma abinda yafi ciwo irin ace kana da gaskiya amma a hana ka tsarawa ballantana a fahimce ka. Ina ma dai iyaye zasu ke bawa yayansu wannan damar? A fahimci kowa sai a hada both parties ayi wa kowa fada dai dai da laifinsa? Ba wai ace da mace ki komaki cigaba da hakuri ba tare da ko murya an daga wa shi namijin da yake maltreating dinta ba, wannan tamkar ana ce masa ka cigaba da maltreating dinta ne.
Amma dana fara tunanin abinda zai iya faruwa gobe sai naji duk hankali na ya kuma tashi. Nasan halin Saghir sosai nasan zai iya jujjuya maganar gabaki daya ta koma laifina kuma na tabbatar iyayen mu musamman mazan bayansa zasu bi, musamman in nayi la'akari da irin kiyayyar su ga Sadauki, da kuma soyayyar da suka san ina yiwa Sadauki, tabbas komai Saghir ya gaya musu yarda zasuyi. Ni kuma ba yardar su ko rashin yardar su ce problem dina ba a'a tirsasani in koma gidan Saghir shine problem dina. Na gama auren Saghir, ba zan koma gidan Saghir ba. Wannan is my decision. Ni a yanzu auren Sadauki ko rashin auren Sadauki ko shi kansa Sadaukin basa gabana. Abinda yake gabana shine rabuwa da Saghir.
Inna tace inje in kwanta in huta a daki. Na tashi na shiga ina jin Asma'u tane cewa "Inna amma ba za'a mayar da Adda gidan can ba ko?" Inna tayi shiru bata ce komai ba. Na kwanta kawai sai hawaye ya fara zubo min ina lissafin abin da zanyi in akace sai na koma. A ciki har da guduwa na lissafa amma inna gudu inje ina? Yan uwan uwata dai sune yan uwan ubana sune kuma yan uwan mijina. Sai kawai na yanke shawarar in aka matsa min akan in koma gidan Saghir to zan gudu gurin Sadauki, inje in tuna masa da amanar da Baffa ya bar masa ta kula damu, sannan in tuna masa cewa ni ma fa yar Baffa ce ba wai Asma'u ce kadai yarsa ba. In kuma roke shi daya shige min gaba in kai karar Saghir court alkali ya raba auren mu. Yes, wannan shine abinda zanyi.
Ina kwance Subay'a ta shigo ta kwanta a kusa dani. Sai naji tana sheshshekar kuka, na jiyo nace "Subay'a? Lafiya kike kuka? Wani gurin ne yake yi miki ciwo?" Sai tace "Mommy ki daina kuka kema" na jawo ta jikina nace "ba kuka nake ba Subay'a ido nane yake min ciwo" tace "kuka kike yi ai na sani, naji kuma aunty Fauziyya dazu da tana shirya ni zan tafi school tana waya tana cewa kunyi faɗa da Daddy shine ya dake ki kike kuka, kuma naji dazu kina fada wa Inna Daddy ya dake ki" sai na kasa ce mata komai, lallai yara duk abinda ake yi a gabansu suna sane. Ta goge min fuskata tace "kiyi hakuri Mommy, in Daddy ya dawo zance masa kar ya kara dukan ki".
Sai na dage da addu'a sosai ina rokon Allah ya shiga lamari na ya kawo min agaji. Dan nasan in na koma gidan Saghir to ba rayuwata ta duniya ba har ta lahirar ma tangadi take yi, two zero kenan. Saboda ni dai nasan a rayuwar auren da nayi da Saghir a baya ba karamin zunubi na lodar wa kaina ba ballantana in na koma nasan bazan iya yi masa koda rabin biyayyar da nayi masa ada ba. In kuma haka ta faru to nice a ruwa dan Ubangiji babu ruwansa, laifina daban a gurinsa laifin Saghir shima daban. Kowa littafin sa daban. Dan haka sai na kwana ina kaiwa Allah kuka na.
Washegari tun safe nake saka ran wani abu ya faru amma shiru, ko ya naji anyi motsi sai in tsorata in dauka Saghir ne zai shigo gidan. In naji wayar Inna tayi kara kuwa dai inji kamar zan saki fitsari a wando saboda tsoron ko kira ne a kaina amma shiru. Da safe Inna tayi min farfesun hanta mai romo tace in cinye, na cuccusa da kyar naci dan bani da appetite sam, sai kuma ta fita da kanta taje kasuwa sai naga tayo cefanen green vegetables kala-kala tazo ta hada min miyar ganye mai naman rago ta sani naci da tuwon shinkafa tace zai kara min jini. Daga ni har ita babu wanda yayi zancen Saghir amma dai nasan duk maganar tana ran mu.
Shiru shiru har dare. Har gayi ya waye wani daren ya sake yi. Har aka kwana biyu sannan aka kwana uku, hudu, biyar, sai akayi sati daya. A ranar ne Inna tace "to ni ko Alhaji Babba zan kira ne akan maganar Saghir din nan ne? Kar dai ba'a sake shi ba har yau. Ni kuma bana son in sake kiran Sadauki kar yaga kamar ina damunsa akan sirikina yaji babu dadi" Asma'u tace "dan Allah Inna ki rabu dasu, yayi ta zama mana a cell din wa ya damu ne wai? Itama yanzu ba gashi ta samu kina kulawa da ita ba da yana nan kuwa ba vari zaiyi kije gidan ki kula da ita ba kuma ba lallai bane ya barta tazo nan" Inna tace "Asma'u kenan, ke yarinya ce ba zaki gane ba. Maganar nan fa tana kara jimawa ne tana kara karfi. Dole ya kamata in bincika inji halin da ake ciki" sai ta dauko waya ta kira Hajiya Yalwati, suka gaisa sai take tamayarta ko taga Saghir kuwa? Nan take Hajiya Yalwati tace "dama yanzu nake niyyar in saka kati in kira ki. Me ya hada Saghir da Diyam da tsohon saurayin ta kuma? Tun jiya naji ana ta maganar a gidan nan ni dai ba'a yi min cikakken bayani ba amma na fahimci kamar ko sunyi rigima ne harda su yan sanda" inna tace "Saghir din yazo gidan kenan" Hajiya Yalwati tace "yazo gidan fa, jiya nan ya kusan wuni sai dare ya tafi".
Tunda suka gama wayar Inna ta zauna ta zabga tagumi, sai ajima tayi ajjiyar zuciya ta sake wani ragumin duk tabi ta damu kanta. Nima kuma na damu din amma ba kamar inna ba, ni damuwata shine bansan zurfin sharrin da Saghir yake shirya min ba. Muna zaune kuwa, Asma'u ta kawo mana lunch kenan sai gasu sunyi sallama. Na ajiye spoon din abincin kawai na fara ambaton Allah dan ji nayi zuciyata kamar ta dawo wuyana.
Daya bayan daya suka shigo palo, Alhaji Babba, Kawu Isa, sai kuma Saghir. Inna ta tashi tana musu sannu da zuwa babu wanda ya amsa ta suka zauna. Ta gaishe su babu wanda ya amsa mata, dan haka sai naja bakina naji shiru ban gaishe su ba kaina a kasa. Kawu Isa ne yayi magana "gamu munzo Amina, mun sauke girman mu mu da muke manya munzo mun same ki tunda haka kike so. Kin bamu kunya Amina, Allah yaji kan hardo da inno, Allah yaso ba zasu ga wannan rana ba ba zasu ga wannan bakin ciki ba na abinda suka raina suka rike kamar abinda suka haifa kuma yazo yana yi musu bita da kulli. Amina yanzu ke wato duniya ta bude miki ido ko? Yanzu wato kudi sunfi miki yan uwanki ko?" Nace "Kawu...." Inna ta daga min hannu tace "kar ki sake inji bakin ki" sai ta juya tace "hamma kudi ba komai bane ba akan zumunci da halacci. Amma yanzu ni me nayi da har kake cewa na zabi kudi?" Alhaji Babba yace "me kika yi?" Ya nuna ni yace "wannan bata gaya miki abinda ya faru ba?" Inna tace "ta gaya min, ta gaya min komai har dukan da Saghir yayi mata da barin da tayi ta gaya min" Kawu yace "kuma ta gaya miki labarin cin amanar Saghir din da take yi tare da wannan tsinannen yaron? Ko kuma dama kin riga kinsan wannan labarin?" Inna ta girgiza kai tace "shi Saghir din ne yace Diyam tana cin amanar sa da Sadauki? Zai iya rantsewa da Allah cewa ya gansu suna cin amanar sa? Ko kuma zai iya rantsewa cewa sakon daya gani a wayarta ya nuna wata alama na cewa suna cin amanar sa" Alhaji Babba ya dubi Kawu Isa yace "kaji ba? Na gaya maka dama ta sani sarai. Da hadin bakinta ne akeyi komai. Ba dai yaron yayi kudi ba? Ni kuma na talauce" Inna tace "in kuka ce haka baku kyauta min ba. Yaron nan, duk cikin ku babu wanda ya kuntata rayuwarsa kamar ni. Tun yana cikin zanin goyonsa bana binsa da komai sai harara da muguwar magana amma me? Shine ya dauke ni a lokacin da Saghir ya watsar dani. Ya baku labari? Naje gidansa duba Diyam ya kore mu ni da Asma'u cikin dare ana ruwan sama. Badan Allah ya bude mu ba badan Allah ya kawo mana Sadauki ya taimake mu ba da yanzu babu Asma'u a duniya. Sadauki ne ya taimaka mana. Tun daga ranar kuma nayi nadama mai tsanani na kuma yi alkawarin yin rikonsa tamkar yadda zanyi rikon dana. Wannan ne yasa tun ranar da Diyam tazo min da maganar na kira shi nace ya sa a saki Saghir, sannan kuma na zauna ina jiran shi Saghir din yazo yayi min nasa bayanin inji" Kawu Isa yace "to mu yaje yayi mana bayani, ya gaya mana komai har yadda shekara da shekaru Diyam take tare da tsohon saurayinta, ta saka ya bashi aiki dan suji dadin cin amanar sa, yanzu kuma mun kuma tabbatar cewa duk abinda ake yi da sanin ki Amina. Wato ke naki salon sakayyar kenan a bisa dukkan alkhairan mu a gareki ke da yayanki. To gasu nan mun bar miki su, gaki nan ga duniyar nan ga kuma Sadauki nan. Ba dai kudi ba? Kamar yadda nawa ya kare haka nasa shima zasu kare sai kuma muga wanne sarkin za'a bi. Saghir dai kam ya gama auren Diyam. Dama tursashi muka yi ya aure ta ba'ason ransa ba saboda muna son mu karfafa zumunci da iyalin dan uwanmu kuma muna so mu rufa muku asiri. Taje ta auri Sadaukin mu gani, ba dai mune masu daurin auren ba?"
Na dago kai na kalli Saghir wanda tunda suka shigo yake tsaye a bakin kofa ya rungume hannayensa ya zuba min ido, ina jin idonsa a kaina amma ban kalle shi ba har saida Alhaji ya gama maganar sa sannan na kalle shi.
Sai ya tako yazo gabana ya durkusa yana kallon cikin idona yace "tunda nake a rayuwa ta ba'a taba yi min wulakanci irin wanda akayi min akan ki ba Diyam. Zan rabu dake, amma ba wai dan na hakura na yafewa Sadauki abinda yayi min ba sai dan wadanda suka ce in aure ki sun ce in sake ki. Na sake ki saki daya."
Sai ya dauke idonsa daga cikin nawa ya mike da sauri. Har yakai bakin kofa kuma sai ya dawo yasa hannu ya dauke Subay'a da take kwance kan kujera tana bacci ya dora a kafadarsa ya yi waje. Na mike da sauri kamar wadda aka mintsina nace "Saghir ka bani yata" ya juyo yace "in da ita kika je gidan ba sai ki karbeta ba in gani?" Na bi bayansa da sauri. "Ka bani yata Saghir, Subay'a! Subay'a!" Sai ta farka firgigit a hannunsa ta sauke idonta a kaina. Ganin ina kuka yasa itama ta saka kuka tana miko min hannu "Mommy! Mommy" yana fita waje ya saka ta a mota ya rufe ya shiga da sauri yaja ya bar gidan tun kafin su Alhaji su karasa fitowa".
[2/22, 9:21 PM] Ummy Gugah LING: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Fifty: The Utterance 2
Assalamu alaikum my dear fans. Baki ba zai iya bayyana muku irin godiya ta a gare ku ba a bisa karbuwar da littafi na ya samu a zukatan ku. Nagode Nagode sosai kuma nima ina sonku a duk inda kuke.
A duk lokacin da marubuciya ta dauki biron ta dan rubutu, to tabbas da akwai wani topic a ranta da take son yin rubutu a kansa. Dan haka duk abinda zata rubuta will be akan wannan topic din. Sanda nayi niyya kuma na fara rubuta Diyam abinda yake raina guda biyu ne, na farko shine illolin auren dole na biyu kuma karfin soyayya ta gaskiya. Dan haka duk abinda nake rubutawa akan wadannan abubuwan ne.
So aim din bawai na koyawa mata yanda zasu gyara aurensu bane ba, aim din na nunawa iyaye da sauran al'umma illar auren dole ne. Allah yasa za'a fahimci manufa ta, ba wai ina nufin rayuwar da Diyam tayi a gidan Saghir itace dai dai ba, a'a, ina nuna akwai possibility na samun irin wannan rayuwar a auren da aka gina shi da tubalin kiyayya.
A kodayaushe rubutu na is open for corrections, criticism and suggestions. Duk abinda ka gani wanda kake ganin ba dai dai bane ba zaka iya tuntubata ka nuna min ko kayi dropping comment yadda zamu hadu mu tattauna har a samu fahimta. Amma kuma, ita fahimta hausawa sunce fuska ce kowa da irin tasa.
Godiya ga wata baiwar Allah data yi min wani gyara a last episode, akan maganar da nayi ta cewa "nothing gives a man the right to hit his wife" what I should have said a gurin shine "nothing gives a man the right to hit his wife the way Saghir did" saboda munsan cewa an bawa maza damar horon disobedient wife da bakin sutturar su, shima kuma sai akace kar su taba fuska. Nagode baiwar Allah duk da bansan sunan ki ba. Lol
Kar in cika ku da surutu, ga Diyam...........
Na tsaya a gurin tamkar wadda aka dasa ni, ina kallon bayan motarsa, ina nan tsaye su Alhaji Babba suka fito suka shiga motar Kawu Isa suka tafi ba tare da sun ko kalli inda nake tsaye ina kukan rabani da yata ba. Asma'u ta fito da tazo ta kamani "Adda kiyi hakuri kizomu koma gida, ki rabu dashi yayi ta tafiya da ita din, Allah zai baki wadansu kuma ita din ma da kafafuwanta zata dawo gurinki" ta kama ni muka shiga ciki. Muka tarar da Inna ta zabga ragumi idonta yayi ja, Asma'u tace "dan Allah Inna kar ki wani tayar da hankalin ki, ance musu in babu su ba zamu iya rayuwa ba ne ba? Ai mu kwallon mangwaro muka yar muka huta da kuda wallahi. Da auren Saghir ba gwara babu ba?" Inna tace "hmmm. Asma'u ke yarinya ce. Ba zaki gane ba".
Ni dai sai na wuce su na shiga daki na zauna a bakin gado. All I have ever wanted tun da aka daura aurena da Saghir shine inji sanda zai furta da bakinsa yace ya sake ni. To gashi na samu amma kuma yanayin da sakin yazo min sai yasa naji sam banji dadinsa yadda nayi tunanin zanji ba. Hakan kuma yana da dangantaka da abubuwa da dama. Na farko zargin da Saghir ya sake ni saboda shi, wanda kuma ba gaskiya bane ba, na biyu zumunci daya karasa lalacewa tsakanin mu da yan uwanmu, na uku Subay'a I can't even imagine yadda rayuwar Subay'a zata zamo a gidan Saghir ba tare dani ba. In banda mutuwa menene yake raba uwa da yar karamar yarta? Amma ni gani a raye amma an raba ni da tawa yar. And I asked myself then, shin Saghir yana da wannan damar?
Ranar haka na karasa wuni raina babu dadi. Da nazo sallah kuwa ina dora goshina a kasa sai kuka, zuciyata ta cunkushe gabaki daya, na idar na daga hannuna da niyyar yin addu'a amma sai na rasa me zan roka kuma. Sai kawai na roki Allah daya dubi zuciyata tunda ya fini ni kaina sanin abinda yake cikin ta, na roke shi ya daidaita min lamurana zuwa ga abinda yake shine dai-dai bawai abinda ita zuciyar tawa take so ba, ya saka rabuwar nan da mukayi da Saghir ta zamanto mafi alkhairi a gare mu baki daya, sannan ya bayyana gaskiya ya goge zargi ya kawo daidaito tsakanin mu da yan uwan mu. Na kuma roke shi daya kasance tare da Subay'a a duk inda take.
My life had been full of challenges so far, na fuskanci kaddarori iri iri wadansu naji dadin yadda na dauke su wasu kuma I have made a total mess of them. Amma a cikin regrets dina babu rabuwa da Saghir, na daiyi regretting irin zaman da mukayi amma banyi regretting kuma bana jin zanyi regretting zama na dashi. For more than eight years muna tare dashi amma dai dai da rana daya ban taba jin zuciyata tana sonshi ba, ko da kuwa a cikin ranakun da yake kyautata min ne sai dai inni kiyayyar sa ta dan kwanta min amma ba dai ta tafi ba ballantana sonsa ya shiga. Nayi addu'ar kuma kullum, kullum nayi sallah sai nayi addu'ar idan zamana da Saghir ne mafi alkhairi Allah ya rage min kiyayyar sa a zuciya ta. Dan haka da akayi rabuwar sai nayi taking that as shine zabin Allah kuma ma roke shi ya cigaba da zaba mini.
Na fara zaman iddah a nan gaban inna, ba inda nake zuwa sai kewayen maman iman sometimes inyi kallo musamman in Asma'u ta tafi makaranta, sometimes kuma in zauna anan dakin Inna inyi ta karatu wanda shine yake kara nitsar min da zuciyata ina jina ina zama at ease. Inna ta gayawa Mama abinda ya faru, kuma tazo har gida ta ganni ta kuma yi min nasihohi sosai akan karbar kaddara da kuma shirin facing rayuwar da zata zo min. Tace "in kin gama iddah Diyam makaranta zaki koma. Kar ma kiyi tunanin aure gwara kiyi karatu ki huta kema jini ya dawo jikinki sosai. Sannan ki samu exposure. Kuma ki koma islamiyya ki karasa saukar ki dama kin kusa ko?" Na daga mata kai, tace "sai ki karasa kuma ki fara hadda, ki cigaba da bin sauran littattafan addini suma kina kara buda kwakwalwar ki" nace "insha Allah Mama". Washegari sai ga Rumaisa amarya tazo gurina. Muka wuni tare muna ta hirarrakin mu sai naji hankalina ya kwanta sosai.
Monday Sadauki yazo kamar yadda ya saba zuwa. Last Monday bai zoba ya kira Inna yace wani issue ne ya rike shi a Maiduguri amma tayi hakuri. Wannan Monday din kuwa tun safe naga tana ta haɗa masa kunun aya wai taga yana so, ta dama masa fura itama ta saka a fridge ni dai ina ta kallonta. Yamma tana yi, dama nasan da yamma yake zuwa sai na saka hijab dina na tafi gurin Maman iman muka kafa hirar mu. Bana son ganinsa yanzu kuma nasan kona zauna a cikin daki in yazo sai Inna tace in fito in gaishe shi. Amma muna zaune kawai sai ga baban iman da baki sunzo, dan haka dole nayi musu sallama na fita na koma gurin Inna. Ina shiga naga takalmin namiji a kofar palo, sai na jawo farar kujera na zauna a tsakar gida amma ina zama inna ta kira ni, na bata rai kamar zanyi kuka na tashi na shiga. Yana zaune a kasa, Asma'u kusa dashi da wata takarda a hannun ta tana nuna masa wani abu suna magana a nutse. Ga kunun ayansa nan a cup a hannunsa yana sha. Na zauna a gaban Inna nace "sannu da zuwa" ya dago ya min kallo daya ya mayar da kansa yace "sannu maman Subay'a" sai ya cigaba da yiwa Asma'u bayanin wanda na fahimci kamar takardar jamb ce take kokarin cikewa. Na mike na shiga daki nayi kwanciya ta. Sai naji Inna tace masa "Diyam fa sun rabu da Saghir" naji yace "rabuwa Inna" cikin mamaki, Inna tace "rabuwa fa, ya sake ta" yayi dan shiru sannan yace "ya Salam. Subhanallah. Abu baiyi kyau ba. Allah yasa hakan shi ya fi musu alkhairi" Inna tace "ameen" Asma'u tace "ai rabuwar ma itace alkhairi hamma, wannan auren na Adda ai dashi gwara babu" Inna tace "rufe min baki sarkin magana. Waye ya tambaye ki? Tashi ki fita" ta tashi ta fita. Sadauki yace "na dauka ai ko ganin ku tazo yi" Inna tace "uhm uhm, ai satinta biyu kenan anan. Tun sanda nayi maka wayar nan ai bata koma ba dama. Nan yazo har gabana ya sake ta yasa hannu ya dauki yarsa" yace "Subay'a? Ita ta bashi ita ko kuma shine kawai ya dauke ta?" Inna tace "ina kuwa zata bashi ita? Gata nan tunda ya dauki yarinyar nan kullum sai na ganta tana kuka kuma nasan kukan yarta take yi amma ya zanyi?" Yace "a'a in dai ba ita ta bashi ita ba to zata iya karbar yarta. Ai both islamically da constitutionally bashi da right din daukar yarinyar" Inna tace "to ta yaya za'a karbo ta kenan?" Yace "ba wahala ai. Ko hisba akaje akayi reporting zasu karbo yarinyar a hannunsa su kawo mata" Inna ta jinjina kai tace "mutanen nan sunyi mana ba dai dai ba daga ni har yaran nan, amma yanuwan mune. Bana son cigaba da rigima dasu so nakeyi a samu fahimta a tsakanin mu. Amma zabin Diyam ne" sai ta saka baki ta kira ni. Na gyara hijab dina na fita, sai na ganshi a zaune yana daddanna waya kamar ba shine yanzu suke magana rai rai da Inna ba, na zauna a gabanta nace gani, tace "Sadauki yace za'a iya karbar Subay'a a hannun Saghir in aka gayawa hisba. Kina so a karbo miki ita?" Na juya na kalle shi busy with his phone, at least a matsayin da yake dashi na yayana da muka tashi tare kuma Inna ta bashi wannan labarin ai ya kamata ko magana mai dadi ce yayi min, sai na dauke kaina nace "ina son karbar Subay'a Inna, kuma zan karbo ta insha Allah amma bana bukatar taimakon sa. I can do it on my own" sai naga yayi sauri ya dago kai yana kallona. Yace "how?" Nace "ba kace hisba ba? Ai nasan hanyar hisba din kuma ina da bakin da zanyi musu bayani in naje" Na daga kafada na mike na komawa ta daki.
Daga nan babu wanda ya sake maganar karbar Subay'a ni kuma kullum yarinyar tana raina, kullum zan kwanta bacci sai nayi tunanin ko tayi bacci? In ina cin abinci sai na tunanin ko taci in na tashi da safe sai nayi tunanin ko an tashe ta an shirya ta zuwa makaranta? Kullum kuma a kowacce Sallah sai nayi mata addu'a amma kuma kamar yadda Inna ta fada bana son cigaba da rigima dasu Alhaji Babba, so nake a samu daidaito. Amma daidaiton da baiyi involving komawa ta gidan Saghir ba.
Lokaci ya cigaba da tafiya, har nayi wata biyu a gida. Duk sati ranar Monday sai Sadauki yazo gidan da yamma, in kuma ba zai samu zuwa ba to zai kira Asma'u ko Inna yace musu ba zai zo ba amma ni ko zuwa yayi gaisuwa ce kawai a tsakanin mu, sai sometimes ya kan tambayeni ko da abinda nake so to which I always reply "babu komai. Nagode".
Su Alhaji basu sake kallon inda muke ba ballantana Saghir. Ni kuma sosai na kwantar da hankali na babu abinda yake damuna sai kewar Subay'a. Har yar kiba ta nayi na kara haske.
Ranar nan na hada kayan Subay'a da muka taho dasu gidan, nima kuma ina bukatar kayan amfani dan wadanda nazo dasu sunyi min kadan ga kuma har phone dita tana gidan Saghir. Amma sam bana son zuwa gidan Saghir, duk kuwa da cewa ina son ganin Subay'a amma bana jin zan iya taka gidan dan haka sai na bawa Asma'u ta kai mata sannan na lissafa mata abubuwan da zata dauko min kafin a debo kayana. Tunda akayi sakin inna take cewa za'a debo kaya amma jin su maman iman suna shirin tashi saboda sun kammala ginin su yasa Inna tace a bari sai sun tashi tukunna saboda a samu gurin ajiye kayan.
Asma'u ta shirya taje ta dauko min duk kayan da nake bukata, amma sai tace min Subay'a bata gidan, daga alama gurin Hajiya Babba ya kaita. Sai na fara tunanin to chanza mata school yayi ko kuma dai tana gida kawai? Sai kuma tace min Fauziyya tace in na kunna waya ta zata kirani. Kuma ta bani labarin cewa "kinga gidan nan kuwa Adda? Gaba ki daya ya lalace har wani karni yake marar dadi. Kayanki kuwa in ba'a je an debo su ba to kuwa sai dai a wuce dasu bola. Na tarar da Saghir a gidan ma, yana kwance a palo ni ko kallon sa banyi ba na shiga na dauko abinda zan dauko na fito".
Da yamma nayi charging wayata da daddare kuma na kunna. Fauziyya ta kirani few minutes after na kunna. Muka gaisa tace "Halima yanzu wai da gaske ba zaki dawo ba?" Nayi dariya nace "my fight is over Fauziyya. Na gama. Bai gaya miki ya sake ni ba?" tace "ya gaya min amma ai saki daya ne dan haka akwai chance na zaki dawo din. Ya gaya min komai bayan kin tafi, kuma ni zanji dadi in kika dawo gidan nan. He loves you da gaske, in ma da baya sonki yanzu gaskiya yana sonki. Ya gaya min dalilin da yasa ya aure ni. Ni kuma na aure shine saboda ina son inyi settling down sai yazo da maganar aure ni kuma na karba. But a yanzu halin da yake ciki bayan tafiyarki I don't think Saghir is the right person to settle down with. Sun daura abota shi da shaye shaye. Most of the time ma baya kwana gida, kullum masifa kullum zage zage. Shi ne na kira in gaya miki, for the sake of your only daughter ki dawo maybe zai dawo hankalinsa in kina nan".
Nace "kiyi hakuri Fauziyya, but kamar yadda na fada miki. Na gama. For more than eight years nake tare da Saghir amma babu abinda muka tsinta a ciki auren mu daga ni har shi in banda wahala. Rabuwar insha Allah itace alkhairi. And kar kice baya sonki, tunda har ya zabeki a cikin sauran mata ya aure ki to kuwa tabbas yana sonki. Ki ci gaba da kokarin ki, it will be okay with you insha Allah".
And then one day, lokacin har nayi period biyu ina jiran daya. Monday, ranar da Sadauki yake zuwa sai Rufaida tayi rashin lafiya dan haka Mama ta tafi dubata ta barmu gida ni da Asma'u. Ni nama manta ranar Sadauki yake zuwa dan haka ina zaune a palo ina kallon wani film din hausa da na aro a gurin maman iman kawai sai jin sallamar sa nayi. Na tashi zaune sosai na gyara hijab dina sai gasu sun shigo shida Asma'u tana ta zuba masa surutu shi kuma yana mata dariya. Ya zauna ta gaishe shi ya tambaye ta ina Inna ta gaya masa bata nan. Sai ya dafe kai "kash, yau kice bani da kunun aya kenan" Asma'u tace "lah, sai da tayi maka ai kafin ta fita" sai ta tashi ta dauko masa ta zuba masa yana sha sannan na gaishe shi "sannu da zuwa. Ya office?" Ya kalle ni yace "yauwa. Lafiya lau" and that was all. Naji wani makokon takaici ya tokare ni. It really does hurt to be ignored, especially by someone da kuka saba sosai.
Sai kawai na kara volume din kallo na a raina ina fatan karar zata dame shi ya tashi ya fita amma sai ma naga sun dauko takardu shida Asma'u suna dubawa suna ta magana, kallo nake amma hankali na yana kansu sai na fahimci maganar ssce suke yi tana cewa "ni dai dan Allah hamma ka cire ni daga makarantar mu ka saka ni a government school in yi exams dina a can, wallahi government anfi ci, private basa bayarda da amsa" yarike baki "au kenan amsa kike so a baki? Maimakon kiyi karatu kici da kanki?" Tace "chaf, wadanda ma suka fini kokari basa ci ballantana ni? Yanzu kuma kaga in banci ssce din nan ba jamb dina ta tashi a banza kenan fa sai na sake wata" yayi dariya yace "kinsan kuwa sau nawa na zana jamb? Kuma a karshen karshe dai ban samu admission din dana ke nema ba" sai ta juyo ta kalle ni tace "Adda kema da kin sani kin cike form din jamb din. Kinga sai muyi tare in ba haka ba sai next year kuma" nayi kamar ban jita ba sai naji yace "in kina so sai a kawo miki gobe" na juyo na kalle shi naga yana kallona sai na kalli sides dina kamar me neman wani abu sannan na nuna kaina nace "are you talking to me?"
Sai yayi kamar zaiyi dariya amma ya wani maxe ya dauke kai yace "kina so ko ba kya so?" Nace "ina so, amma karka wahalar da kanka gurin kawo min, zan kira yaya Mukhtar ince ya siyo ya kawo min" ya daga kafada yace "duk daya. Tunda kinci waec dinki ba sai kin sake ba" sai na kalle shi da mamaki, I don't remember telling him cewa nayi waec ballantana zancen naci, nace "ya akayi kasan naci waec?". Sai kawai ya zauna yana kallona. And then all of a sudden sai ganin Saghir mukayi ya shigo palon hannunsa rike da Subay'a. He looked at me then at Sadauki and then at me again. Subay'a ta saki hannunsa ta taho gurina da gudu na bude hannuna na rungume ta ina jin dadi har cikin raina.
Saghir yace "what the f....." Sai nayi sauri na mike nace "Asma'u dauki Subay'a ku fita" dan nasan halin Saghir zai iya fadin komai ko yin komai a gaban Subay'a shi babu ruwansa. Ai kuwa tun kafin su fita ya fara "wato na matsa na baku dama ko? Shine wato zaku cigaba daga inda kuka tsaya? Ba kwajin kunyar duniya ba kuma kwajin ta Allah ko?" Sai Sadauki ya gyara zamansa ya dora kafa daya akan daya yayi folding hannunsa yana kallon Saghir. Ni kuma sai na mike, gabaki dayan su basa gabana dan haka baxan tsaya su bata min raina a banza ba. Nazo zan wuce Saghir ya kamo hannuna "ina zaki je? Munafuka kina wani saka hijabi kamar mumina" nayi kokarin kwace hannuna nace "don't touch me" ya maimaita "don't touch me, don't touch me kullum don't touch me." Sai ya juya yana kallon Sadauki yace "but I did touched her. Dan haka gwanjo nace. Duk inda zaka shiga babu inda ban shiga na fita ba and I left my foot print there" raina ya kai kololuwar baci, ban ma san me zance ba sai ji nayi Sadauki ya danyi dariya yace "are you sure about that?" Na kama kokawar kwace hannuna daga rikon Saghir zuciyata tana tafasa, zan so ace na fisu karfi in hada su duk su biyun inyi ta duka, how dare they talked about me like that.
Saghir yace "of cause am sure kasan a ledarta na bare ta. Sabuwa fil aka kawo min ita and I took her virginity" I froze. What? Ba zan ma iya kallon side din da Sadauki yake ba amma sai naji yace "ita nake so, not her virginity so...." Na kwace hannuna da sauri nayi bakin kofa hawaye yana bin fuskata, kafin in fita Saghir ya finciko hijab dina ya dawo dani cikin palon, ya hada ni da jikinsa muna facing Sadauki, Sadauki ya mike tsaye, Saghir yace "me yasa zaki gudu ne? Dan ke fa ake wannan taron ai ya kamata ki tsaya ki saurara kema ki tofa albarkacin bakinki a ciki. For example, tell him about our first night, tunda yace bai damu ba tell him how I did it maybe zai damu" na fara girgiza kaina da sauri. It is either Saghir is drunk ko kuma kwakwalwar sa ta fara tabuwa. And he said it. "I raped her" and then I saw a flash of fire a idon Sadauki. Saghir ya sake maimaita wa "I raped her the first night da aka kai min ita gida na. That was how she got pregnant for me har ta haifa min twins".
Sadauki took one step sai nayi saurin kwace jikina daga Saghir na tari gaban Sadauki na daga masa hannu "don't. Kar kace wani abu kar kayi wani abu just go" Saghir yace "yeah. Just go. But before you go, listen to this. Na mayar da ita dakinta." Na juyo da sauri ina kallonsa zuciyata tana bugawa kamar zata bar kirjina nace "no, no" yace "yes. Na mayar dake tunda dama saki daya nayi miki kuma shima bada son raina ba. Na mayar dake saboda ina son ki sannan kuma saboda I want him to think of you every night of every day when laying on his empty bed har zuwa ranar da zaki bar duniya ko kuma shi zai bar duniya. Sai inga karshen soyayya".
Inna ce ta shigo dakin da sauri, daga alama taga motocinsu a waje kuma tayi sensing something is wrong. Tana zuwa bata ce komai ba sai ta kama hannun Sadauki ta ja shi da sauri ta fitar dashi daga palon. Kafin su fita ya juyo ya kalleni and I saw a look on his face similar to wanda na gani ranar da zamu rabu a gidan Alhaji Babba. Na juya da gudu na shige bedroom din Inna na rufe kofa.
[2/23, 9:26 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Fifty One : The Will
A jikin kofar na zame na zauna ina jin zuciyata tana wani irin bugawa, ji nake yi kamar zan mutu, kaina yayi wani irin zafi kuma hawaye ya tsaya a ido na. Ban taba tunanin it's possible ka tsani mutum kamar yadda naji na tsani Saghir a lokacin ba. Na fara girgiza kaina ina cewa "no no no" kamar mahaukaciya. I can't even imagine komawa gidan Saghir a matsayin mijina, I can't imagine him touching me again. I would rather die. Ina jiyo maganganu a palo kamar muryar inna amma bana gane me take cewa, sai naji ta taba kofar amma da yake ina jikin kofar sai ta kasa bude wa sai naji tana kiran Asma'u. Sai kuma naji ana knocking kofar. Da kyar na bude idona na matsa daga jikin kofar sai suka bude suka shigo su biyu sannan Subay'a ta shigo itama tana kallo na sai naga Asma'u tayi sauri ta dauke ta sun sake fita.
Inna ta durkusa gabana tana taba wuyana tana magana a hankali amma ni bana jin ma me take cewa. Sai kuma naga ta kama ni ta mayar dani kan gado ta kwantar dani ta juya na riko rigarta sannan cikin muryar da naji kamar ba tawa ba nace "Inna bazan koma ba. In na koma mutuwa zanyi" ta juyo tana kallona sai ta zauna tace "komawa ina?" Sai kawai na bita da kallo, wato Saghir saboda bai daraja ta ba bai ma gaya mata cewa ya mayar dani ba? Sai ta gane me nake nufi tace "cewa yayi ya mayar dake?" Ban iya bata amsa ba sai kuka, sai ta mike tsaye "wannan wanne irin abu ne? Wanne irin ya mayar dake kuma? Suzo nan su kare mana cin mutumci sannan kuma ya mayar dake bayan babu wani mataki da aka dauka? To babu inda zaki koma. Yanzu fa Hafsa take bani labarin wai kawun ku Isa ya bashi Suwaiba" Suwaiba yar kawu Isa ce itama kuma kusan set din mu ce, mun dan girme ta kadan. Lokacin muna yara ita da Rumaisa ne suke crushing on hamma Saghir, murja tana yawan gayamin cewa har yanzu suwaiba tana son Saghir amma ni ban taba ko saka abin a raina ba.
Inna tace "wato su suna can suna kokarin yi masa huce haushi shine shi kuma zai zo nan yace ya mayar dake? To ku biyu yake so ya hada a gida daya ko kuma ya yake so ayi? Ai indai kinga kin koma gidansa to ki tabbatar an zauna ne an hada ku anyi muku fada kowa an bashi laifin sa bawai kullum ace kece da laifi ba" tayi ta fadanta ni dai ina jinta kawai. Amma ni a raina nasan ko anyi mana fadan bana jin zan iya sake zama da Saghir, not after what he did today, not after what he said a gaban Sadauki.
Tuni da Sadauki da nayi sai naji wata irin fargaba ta shige ni. Tsoro nake ji sosai, tsoron abinda Sadauki zai iya yi akan furucin da Saghir yayi a gaban sa. Ina tsoron zuciyar Sadauki, ina tsoron zafin sa, ina tsoron rashin tafiyar sa, considering abinda yaji da kuma yanayin da ya fita a ciki, bansan hukuncin da zai dauka ba. Sai na samu kaina dayi masa addu'ar Allah ya taushi zuciyarsa Allah ya hane shi ga aikata abinda zaizo yayi nadama.
Sai magrib na tashi. Nayi alwala nayi sallah nayi kuka sosai a cikin sujjada ta na roki Allah ya kawo haske a cikin al'amura na. A lokacin ne Asma'u suka dawo ita da Subay'a. Subay'a ta taho gurina da gudu ta fada jikina tana kallona tace "Mommy kin daina kukan? Dazu naga kina kuka" nace mata "na daina subis" sai tayi dariya tace "Daddy ya tafi ko? Dama cewa yayi zai kawo ni gurinki in kwana biyu sai mu koma gidan mu tare" bance komai da akan wannan sai tace "Mommy kullum sai nayi kuka nace da Hajiya ta kawo ni gurinki ita kuma taki. Mommy dan Allah ni kar a mayar dani can gidan gwara in zauna a gurin ko kuma mj koma gidan Daddy na tare" sai na daga ta nace taje tayo alwala tayi sallah.
Na lura ta rame, ta fada sosai tayi baki. Kamar ba'a kula da tsaftarta sosai sannan idonta ya nuna alamar damuwa. Sai na yanke wata shawarar, bawai ni kadai ce bazan koma gidan Saghir ba har da Subay'a ma ba zata koma ba, tazo kenan.
Da dare ina jin Inna tana cewa Asma'u ta kira mata Sadauki, kamar tasan ina son in tabbayda lafiyar sa. Asma'u ta kira switched off, a raina nace nasan za'a rina, amma ban furta komai ba nayi shiru kawai. Nan fa hankalin Inna ya tashi tace "wai me ya faru ne mai zafi a tsakanin su? Ni sam banji dadin yadda naga Sadauki ba tunda kuma ya fita hankalina yana kansa wallahi" ta juyo tana kallona tace "me Saghir din ya gaya masa me zafi haka?" Na sunkuyar da kaina kawai, ni ba zan iya gaya mata kalaman Saghir ba. Jin nayi shiru sai tayi ajjiyar zuciya tace "Allah ya kyauta".
Washegari babu kunya babu tsoron Allah sai ga Aunty Fatima nan da Hajiya Yalwati da kanwar Hajiya Babba wai Alhaji Babba ya turo su su gaya wa Inna cewa Saghir ya mayar dani, a gaya min in shirya sai mu saka rana ni da Saghir din sai yazo ya dauke ni. Ni kawai kallon su na tsaya ina yi cike da mamaki. Inna tace "yanzu Fatima har da ke? Har dake za'a ci amanar marigayi dan bashi da rai?" Aunty Fatima tace "me akayi Amina? Yanzu mayar da auren shine cin amana?" Inna tace "ba mayar da aure ne cin amana ba, rashin kulawa da nuna son kai shine cin amana" sai ta lissafa musu dukkan laifuffukan Saghir wanda ni na gaya mata tace "ni ba wai goyon bayan Diyam nake yi ba ko kuma bana so ta koma dakinta ba, a'a, so nake a zaunar da Saghir shima ta fadi laifin Diyam din sai a hada su kowa ayi masa fada a bashi laifin sa. A ja masa kunne akan dukanta dan ni abinda yafi komai daga min hankali kenan" sai Aunty Fatima ta nuna itama bata ji dadin abin ba tace "ni duk fa bansan wannan ba, ni cemin sukayi Diyam tana kula Sadauki shi kuma Saghir yaji haushi ya saketa. Kema yadda muke dake ai kamata yayi duk abinda ya faru ki kira ni ki gaya min. Da Diyam da Saghir duk yayana ne ai". Amma ita kanwar Hajiya sai ta kama fada, ita wai lallai nayi wa Saghir sharri "babu wani shayeshaye da yake yi balle neman mata" sukayi ta bugawa da inna har tayi zuciya ta tashi ta tafi Aunty Fatima ma ta tafi sai Hajiya Yalwati ta zauna tace sai anjima zata taho. Daga jin haka nasan tsegumi ta zauna yi.
Tace "wallahi Amina karki mayar da yarinyar nan. Yaron nan fa bawai gyaruwa yayi ba. To yaron da baiji kan iyayensa ba ina zaiji kan wani. Shaye shayen nan fa munsan yanayi amma sai a rufe ido ace bayayi. Neman matan nan kuwa yinsa yake yi kamar babu gobe. Ita kanta Fatima da take wannan maganar rannan a gaba na naji tanayiwa Minal yarta fadan kar ta kuma kula shi. Dama Suwaiba ce tasa kuma yanzu sunce sun bashi dan haka ku rabu dasu, in dai abinda Diyam ta fadi gaskiya ne in ya auri Suwaiban ai zasu gani" Inna tace "za kuwa su gani. Ai ni zanso ayi auren nan ma ko dan gaskiya ta bayyana" Hajiya Yalwati tace "gaskiya kam zata bayyana. Tun yanzu ba gashi nan muna gani yana zuwa yana daukan ta a mota ba? Ahau, lokaci kadai muke jira".
Har tana shirin tafiya kuma sai cewa tayi "ni Diyam kuma ta wani zubin banji dadin tahowar nan taki ba. Dama ke ce mai dan saka shi yana dan kawo mana abinci gidan. Yanzu kuwa shiru. Rannan har ya fara zancen aurar dasu murja yanzu kuwa yadda yake a rikicen nan nasan ba lallai ne yayi ba". Inna ta dauki yan kudade ta bata tace ta siyawa yara sabulu.
Da dare sai ga wayar Saghir. Na kalli wayar kawai na dauke kai. Yayi ta kira sai na saka a silent sai ya turo min message "ki shirya. Rana ita yau zan zo mu tafi". Sai na kashe wayar gaba-daya na ajiye.
Washegari wai dan rashin kunya sai ga Hajiya Babba da kanta. Ina ganin ta nayi wa Asma'u text. "Ki dauki Subay'a ku bar gidan nan, sai na kira ki zaku dawo". Ina kallon su suka fice. Tazo ta saka inna a gaba "yanzu ya za'ayi ace kince ba zata koma gidan taba? Yanzu zumuncin kenan? Koma menene ya faru a tsakanin su shi ya hakura ita me yasa ba zata hakura ba?" Inna tace "tace ba zata koma ba. Ni kuma baxan matsa mata ba, matsantawar da nayi mata a wancan karon ma da ace zan iya dawo da hannun agogo baya da banyi ba".
Sai ta kama hannuna ta jani daki muka zauna a bakin gado tace "yanzu Diyam ke kinsan halin Saghir. Kinsan cewa ya chanja sosai saboda ke kuma ya chanja din. Yanzu da kika barshi Diyam Saghir duk ya koma yadda yake da koma fiye da haka. Me yasa ba zaki je ki karasa abinda kika fara ba? Ko dan saboda Subay'a" nace "Hajiya Saghir fa ba wai chanzawa yayi ba. Indai har da gaske ya chanza bai kamata ya koma ruwa ba dan bana tare da shi. Hakan yana nufin saboda ni ya chanza kenan ba wai saboda kansa ya chanza ba. To yanzu kuma in mutuwa nayi fa?" Tace "a hankali ai yake gyaruwar, in kin koma zai cigaba da gyaruwa ne" nace "Hajiya tun farko ba kwa ganin kamar akwai son zuciya da zalunci a cikin dora mim alhakin gyaran Saghir? Ku da kuka haife shi baku gyara shi ba tun yana danyensa ta yaya zaku bani shi bayan ya bushe kuma ku saka ran in kare rayuwata gurin gyaransa?" Tace "saboda munsan zaki iya. Kin fara kuma zaki iya karasawa" na girgiza kaina nace "bazan koma ba Hajiya" tace "saboda me?" Nace "saboda bana son shi Hajiya" sai ta tsaya tana kallona. Sai na tuno da ranar da Saghir yazo gaban inna yace baya son aure na. Hajiya tace "ba kya son sa fa kika ce min Diyam. Yanzu har idonki yayi budewar da zaki kalle ni kice ba kya son Saghir? Koma dai menene Saghir din nan, koma da gaske ne maganganun da kike fada still Saghir dai danuwan ki ne kuma duk kin da kike masa ba zaki taba cire jinin ki daga nasa ba. Mijinki ne kuma, tunda dai yace ya mayar dake Sannan uban yarki ne, ba zaki taba chanja mata uba ba" nace "Allah zai raya ta ko ba a gidan sa ba" sai ta mike da fushi ta fita, ina jinta tana cewa da Inna ina Subay'a zata tafi da ita, sai inna tace "Diyam tace Subay'a ba zata koma ba. Zata rike yarta" nan tayi ta bala'i "wallahi bata isa ba, ita tace ba zata koma ba sannan yar tasa ma ta hana shi?
Da dare inna ta kuma saka Asma'u ta gwada number din Sadauki but still bata shiga. Inna ta kalleni tace "ke baki san inda yake zaune ba?" Na girgiza kai nace "ban sani ba Inna. Sai dai office dinsa na sani" Asma'u tace "ni dai nasan kamar a hotel yake zaune. Amma bansan wanne hotel din ba" Inna tace "to ko Asma'u zan tura office din nasa gobe ta gani? Ni duk zuciyata bata min dadi wallahi".
Washegari Asma'u tana dawowa daga school sai gashi ya kirata. Tace "Inna ga hamma yana kira" Inna tace "to kiyi sauri ki dauka mana kar ta katse kuma? Alhamdulillahi" Asma'u ta dauka tana gaishe shi sai naga ta kalleni tace "tana nan" sai kuma ta mike zata fita, Inna tace "ina kuma zaki je?" Sai Asma'u ta daga mata hannu ta fita kawai.
Shiru shiru, ni dai ina zaune a kan kujera staring into nothingness har Asma'u ta dawo after like two hours. Ta zauna tace da Inna "yace ince miki yana lafiya kuma gobe zai shigo" Inna tace "shikenan? Duk wannan dadewar kuna waya shikenan abinda yace?" Asma'u tace "tambayoyi yayi ta yi min kawai. Akan Adda. Yanayin zamanta a gidan Saghir" Inna tace "ke kuma me kika ce masa?" Asma'u tace "everything. Duk abinda na sani na gaya masa sai dai kuma wanda ban sani ba. Abinda na fahimta shine duk shekarun nan shi ya dauka Adda lafiya take zaune a gidan mijinta" na dauke kai ina lissafin wanne ne abinda Asma'u ta sani wanne ne kuma wanda bata sani ba?
Washegari da safe muna breakfast yazo. Fuskarsa babu annuri ko digo a cikinta ya gaishe da Inna muma muka gaishe shi. Ya kalli Subay'a yace da inna "an dauko tane?" Inna tace "tunda uban ya kawo ta Diyam tace ba zata koma ba" yace "good. Ba zata koma ba. Ita ma kuma Diyam din ba zata koma ba sai dai in har ita ce take son komawar" ya juyo ya kalle ni yace "kina son komawa gidan Saghir?" Na sunkuyar da kaina ina girgiza kaina da sauri, yace "good. Then ki dauki wayarki ki kira shi. Ki gaya masa ba kya sonsa ba zaki koma gidansa ba. In yana son rabuwa ta arziki to ya kawo miki takardar ki within the next three days, in kuma ba haka ba kice masa zaki kaishi kara in yaso alkali ya raba ku".
Ya juyo yana kallon Inna yace "Baffa uba ne a gurina. Dan yadda nake jinsa a zuciyata har yafi yadda nake jin shi kansa wanda ya haife ni saboda Baffa ya bani abinda shi din bai bani ba. Baffa ya bani soyayya, ya bani kulawa, ya bani tarbiyya. And he used his last breath a duniya to tell me in kula daku, and that's what I have been trying to do, and that's what I will continue to do sai inda karfi na ya kare".
[2/24, 8:22 PM] Ummy Gugah LING: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Fifty Two : A Little Game
Inna ta fara sharar hawaye, ita dama kwana biyun nan komai sai kaga ta fara hawaye. "Allah ya ji kan baffan ku. Babu abinda bai gaya min ba sai kace yasan abinda zai faru bayan babu shi. Abinda na wulakanta shine yanzu gatana ni da yayana, wadanda kuma na daukaka fiye da komai sune muka zama abin wulakanta wa a gurin su." Sai Asma'u ta tashi ta koma kusa da ita tana rarrashinta, Sadauki ya mike tsaye yana kallona yace "ki kira shi yau. Gobe ki gaya min yadda kuka yi dashi". Na gyada kaina sai ya juya ya fice.
Ina kallonsu suka gama kukansu amma ni ko hawaye banji a idona ba, maybe ko kukan ya kare ne oho, nidai abu daya da na sani shine baxan koma gidan Saghir ba and that's final.
Sai yamma na samu courage din kiransa. Bugu daya ya dauka yace "ha! Finally. Kin shirya inzo mu tafi?" Na lumshe ido na na bude, ina bitar abinda Sadauki yace min nace "ba wannan dalilin da yasa na kira ka ba. Na kira ne in tabbatar maka da abinda na gayawa Hajiya sanda tazo. Aure na dakai ya kare Saghir. Ba zan koma gidan ka ba saboda rabuwa a tsakanin mu tafi alkhairi akan zaman. Ina neman ka sawwake min. Ka kawo ko kuma ka aiko min da takarda ta nan da kwana uku in kuma ba haka I will have no other choice than in kai karar ka alkali ya raba auren mu" ya yi shiru amma nasan bai ajiye ba, sai yace "are you threatening me Diyam?" Nace "ba threat bane ba, option ne na baka kamar yadda nima Allah ya bani option na ko in hakura in zauna da kai ko kuma in kai karar ka in baka kudin yin wani auren kai kuma ka sawake min" yace "ohh, abinda ya tsara miki kenan ko? Abinda yace ki gaya min kenan? To ki bude kunnen ki kiji sosai nima nawa sakon zuwa gurinsa. Kice masa nace bazan sake ki dinba, idan akwai abinda yafi court ya kai ni can. Amma kafin ku tafi court din bara in fara gaya muku abinda zai fari a can din. Muna zuwa zan zayyana wa alkalin cewa shi wanda ya taimaka miki kika kawo karar tawa tsohon manemin ki ne, na kama ku na hana ku harka shine kuka yi deciding kawo kara ta saboda in sakar masa ke. How about that?" Nace "kai kanka da kake fadar maganar kasan cewa ba gaskiya bane ba. Kuma duk inda alkali yake ai mutum ne mai ilimi wanda zai zai saurari kowa. Ni fa ƴa ce Saghir ba baiwa ba, tunda nace bana sonka set me free please" yace "in nayi haka Diyam ai na bashi abinda yake so kenan, na baku abinda kuke so. Ni kuma nayi alkawarin tunda kuka making fool of me for years sai na dauki fansa. Plus wulakancin da yasa police suka yi min. So here is another message to him. Tell him nace I want my job back, I am kind of out of money yanzu. In ba haka ba kuma zan fara spreading rumors a cikin ma'aikatan sa, and this time around I won't be drunk yadda zanyi passing clear message har su fahimci wanene real Mr Abatcha, suma su fara boye matansu. Kuma harda gishiri zan kara wa maganar" ya karashe maganar yana dariya.
Na cire wayar daga kunne na saboda yadda maganganun sa da dariyar sa suke kara huta ga already wutar da take ci a kirjina. Shin anya kuwa Saghir yana tsoron Allah? Shi karya bata yi masa wuya. Sanda ya dake ni a gida ya nuna yana zargina da Sadauki banji haushin sa ba kamar wanda naji akan maganganun da ya fada ranar nan akaina a gaban Sadauki, it shows cewa abinda yayi din ma bashi da remorse akan sa tunda har fada yake yi proudly a gaban third party. Yanzu kuma maganganun sa sun nuna min cewa ba wai ya mayar dani bane ba saboda yana son aurena ba, ya mayar dani ne to get back at Sadauki. Am not a toy, am a person with zuciya a kirjinta da kuma jini a jikinta. Am not going back.
Da dare na gwada wayar Sadauki dan in gaya masa abinda Saghir yace amma naji har yanzu bata shiga. Haushi ya ishe ni na ajiye ta kawai. Amma sai na gayawa Inna duk abinda Saghir yace akan maganar Sadauki. Ta juya kai tace "wannan yaron baya kyautawa. Shi bai san hukuncin wanda yayi wa wani irin wannan sharrin ba? In kotun za'a je fa shine a kasa dan bashi da wata shaida" sai kuma tace "ni bana son zuwa kotun nan wallahi, zuciyata bata so, yan'uwan mu ne mutanen nan, so nake ayi sulhu a tsakani ba sai kowa yaji ba. Ba ga Suwaiba nan ba an bashi, kuma yana da wata matar a gida me yake nema kuma. In kudin yake so sai a bashi shima in dai za'a rabu lafiya. Ni kotun ce bana so, kuma bana so ya bata wa yaron nan suna a gurin mutanen da suke ganin girmansa".
Nima kuma bana son court din, amma kuma bana son komawa gidan Saghir kuma bana son in watsawa Sadauki kasa a ido ince bazan je ba. Dan haka ranar sai naki bacci na kwana ina gayawa Allah. Kuma na tabbatar ya jini kuma na yarda da cewa zaiyi hukuncin da ya dace.
Washegari da safe Asma'u ta tafi school ni kuma na koma na kwanta in danyi bacci sai naji karar wayata. Na dauka ina kallon number din Sadauki. Sai na jujjuya wayar a hannuna dan in tabbatar da cewa tawa ce bata Asma'u ba. Sai data kusa katsewa sannan na dauka da sallama na gaishe shi yace "ya kuka yi?" Sai da bashi labarin duk abinda Saghir ya fada. Sai kawai naji yayi dariya, yace "that man is so predictable. Ya fadi exactly abinda nake so ya fada. Tell him, na tsorata na tuba nace yayi hakuri kar ya zubar min da mutunci a gurin mutane, kice nace ya dawo ya cigaba da aikinsa ai dama ni ban kore shi ba shine ya daina zuwa. Sannan kice masa kema kin hakura ba kya son zuwa court dashi dan haka zaki koma gidan sa amma kina so please ya baki wata biyu saboda kina so ki shirya sosai" nayi saurin cewa "bazan koma ba" yace "I know. But just tell him that" nace "saboda me?" Yayi shiru sannan yace "do you trust me?" Nayi shiru nima ina lissafa lamarin sannan nace "yes, amma ina bukatar bayani" yace "okay, let me break it down for you. Bana son ke ko Inna ku shiga court dashi saboda kamar yadda Inna ta fada yan uwanku ne babu yadda zakuyi dasu. Sannan kuma ko an kaishi court din karshe kawai raba auren za'ayi and to get even that sai anyi ta faman cecekuce ana saka ki kina bayar da labari kina kara maimaita wa. I don't want to put you through that emotional trauma. You have had enough of your share of emotions. Still kuma in nace zamuyi sueing dinsa for abinda ya fada a kunnena yayi, ba lallai ya samu wani sentence mai kyau ba saboda a lokacin da yayi din akwai aure a tsakanin ku dan haka iyayenki za'a jawo cikin case din for marrying you off that young. Bana son insa Inna cikin wannan maganar. So option dina shine ya zama tsakani na dashi ne kawai ku kuna gefe. And I promise you ba zaki koma ba but for that I need you to call him ki gaya masa abinda nace".
Nace "okay, zan gaya masa" yace "thank you. But please kar ki gayawa Inna. Let it be our little secret".
Ban gayawa Inna din ba kuma ban kira Saghir ba sai washegari. Ji nayi bana son kiran nasa dan haka sai na tura masa text message na fada masa abinda Sadauki yace in fada. Sai kuwa gashi nan ya kira ni na dauka da kyar, yace "it wasn't so hard now was it? Dama nasan zamewa zaiyi ya barki. Ai mutane irin su babu abinda suke so irin su gyara public picture dinsu, ina komawa kuma zanyi requesting karin albashi kuma sai inga in zaiyi denying" yayi ta maganganun sa ni dai bance komai ba har ya gama sannan yace "and you? Mai zakiyi da wata biyu?" Nace "shiryawa nake so inyi sosai" yace "wacce irin shiryawa kuma? Ba kayanki kawai zaki zuba a akwati ba?" Nace "ina so in shirya emotionally, bayan abubuwan da ka fada ranar nan a gaban Sadauki ai you should be greatful da nace zan dawo din ma" sai na katse wayar kamar nayi fushi na kashe ta ma gaba daya.
Daga nan komai ya lafa a bangaren mu. Two weeks after that Sadauki yazo yayi wa inna sallama yace zaiyi tafiya zuwa Canada. Yana shigowa Subay'a ta zagayo ta dawo bayan kujerar da nake zaune. Muka gaishe shi ya amsa sai ya mika mata hannu "Subis come here" sai ta makale. Yayi dariya yace "inna na kawo karar Subay'a, bata gaishe ni" Inna tace "ke! Ba zaki zo ki gaishe shi ba?" Still taki zuwa, zanyi mata fada yace in rabu da ita, yayi wa Inna bayani "dama family na na Maiduguri kusan duk suna Canada, zan danje in yi musu kwana biyu. In naje zan kira ku da number din da za ku same ni da ita should in case ko wani abun zai tashi" Sai Inna ta nuna irin bata ji dadin tafiyar tasa ba, Asma'u harda matsar kwalla yace "ko wata daya fa ba zanyi ba. Just hutawa nake so inyi saboda ina aiyuka da yawa a nan".
Yana fita Subay'a ta zagayo cinyata tace "Mommy bana son mutumin nan" Inna ta kwade ta da muhuci tace "kar in sake jin kince ba kya sonsa, kuma in na sake ganin yazo kin ki gaishe shi ni dake ne. Babanki ne shi, tunda yayan babarki ne".
Sai bayan tafiyar sa Inna ta tambayeni "wai ya kuke ciki ne maganar Saghir? Ni baki ce min komai ba" nace "na gaya masa abinda Sadauki yace in fada masa, shi kuma yace ba zai sake ni din ba sai dai aje court din. Shi kuma Sadauki yace vaya son muje court dasu" inna tace "nima bana so, to amma ai ba zaki yi ta zama da aure aka ba. Dole dai cikin biyu za'ayi daga. Bara ya dawo daga canadan muji".
Sati daya da tafiyar Sadauki muka je gidan Mama gabaki dayan mu. Anan ne muke samun labarin ashe rigima ake tayi a sharada tsakanin Alhaji Babba da kawu Isa. Kawu Isa yayi wa Saghir huce haushi na da suwaiba, har Saghir ya karba ya an fara shirye shirye sai kuma yaxo yace ya fasa ni zai mayar sai kawu Isa ya nuna cewa ba'a kyautawa yarinyar ba, amma as usual, Alhaji Babba ya goyi bayan dansa.
Mama tace "ni tsoro nake ma Allah yasa bai lalata musu yarinya ba, dan labaran da muke ji basu da dadi".
Bayan dawowar mune nayi bakuwa. Fauziyya. Ni ban san ma tasan gidan mu ba sai yau. Na karbe ta sosai muka shiga daki nayi serving dinta abinci da drinks. Sannan tace "muna ta jira kuma har yanzu shiru" nayi dariya kawai, sai tace "ko sai za'a koma sabon gida sannan zaki dawo?" Nace "sabon gida kuma?" Tace "eh mana, ko bai gaya miki ba ya siya mana sabon gida? Sai ta fara yi min bayanin girma da kyan gidan "kowa da part dinshi, part din kowa yayi girman gidan da muke ciki. Yayi order komai na gidan next week za'a kawo su" sai ta nuna min key din mota "kinga ya siya min mota, kema ina jin kina komawa za'a siya miki taki. Shima ya sake wata" na gyara zama ina nazarin ta nace "why are you here Fauziyya?" Tace "ziyara na kawo miki mana. Kuma in gaya miki alkhairin da ya samu mijin mu dan in kwadaita miki komawa gidan. Hausawa sunce the devil you know is better than the angel you don't know. Na zauna dake lafiya, gwara ko dawo akan a kawo min wata wadda ban sani ba".
Bayan tafiyar ta na zauna tunani. Kudi? Lokaci daya? Saghir? Ina ya samu kudi? And I remembered lokacin daya samu aiki yazo yake bani labari yace "financial secretary aka ce miki. Ni nake kula da duk harkokin shige da ficen kudi a companyn".[3/7, 9:06 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Fifty Three : Check up
Sai naji tunani na ya tsaya. I just want to make a sense of wannan abin but na kasa believing abinda nake thinking. Is Saghir helping himself out of Sadauki's money? Ko kuma yana blackmailing Sadauki ne akan wannan maganar? But anya Sadauki zaiyi paying Saghir irin wannan kudin saboda empty threats dinsa? Tun sanda yayi threat din ni ban ji ko alamar tsoro a voice din Sadauki ba. Menene ma kuma dalilin da yasa Sadauki ya mayar wa da Saghir aikinsa? In dai kuwa har Saghir kudin Sadauki yake dauka then he is dumber than I thought.
Koma dai menene ni abinda na sani shine ya kamata inyi warning Sadauki akan ya kula da kudinsa tun kafin Saghir ya debi wanda zai kassara Sadauki ko kuma shi wanda ba zai iya biya ba. Kamar yadda na tabbatar zan mutu haka na tabbatar Sadauki ba zai bar masa ba.
Wayar Asma'u na nemo na dauki number din da naga Sadauki ya kira ta rannan na saka a tawa wayar nayi dialing amma sai taki shiga, naji kamar in jefar da wayar saboda bakin ciki, wato a wannan number din ma sai da yayi blocking dina? Wai me yake tunanin kansa ne? Ni ma na damu, sai sune suyi tayi ai daga shi har Saghir din.
Washegari Saghir yazo gidan. Ya ci kwalliya fiye da yadda yake da sai sheki yake yi kamar tarwada. Sai naga rashin kunyarsa da har zai iya shigowa palon Inna bayan duk abinda yayi mata da kuma sakinna da yayi a gabanta. Subay'a ta tafi da gudu ta rungume shi ya daga ta sama yana juya ta kamar yadda yake yi mata sanda muna gidansa. Asma'u tayi tsaki ta fita. Sai ya dan rissina ya gaida Inna ta amsa masa ba yabo ba fallasa. Sai ta dauki mayafinta tace min zata je unguwa. Ya zauna yana kallona yace "babu gaisuwa gimbiya" na kalle shi nace "yaushe babana ya zama sarki ballantana ni in zama gimbiya?" Yace "ai ba gimbiyar gari bace ba, gimbiya tace ni kadai. Kinsan cewa an bani kyautar budurwa naki karba saboda ke? Ke kinsan wanne irin so nake miki kuwa Diyam?" Nayi shiru ina tunanin irin maganganun daya fada a nan palon a gaban Sadauki, is that his version of love?
Yace "wata biyun nan yayi min yawa please. Ki rage. Ko kuma ince na rage miki da kaina. Na sayi sabon gida, you are going to like it. Zanyi tafiya zanyi two weeks kafin nan komai na gidan ya kammala ina dawowa zamu tare. So, I want you to get ready kafin nan kafin lokacin dan har dake din zamu tare a lokaci daya. Kinga da kin koma ma da dake zamuyi tafiyar nan. Am taking Fauziyya to the honeymoon I promised her, but in kin koma kema sai muyi fixing time ki zabi kasar da kike so mu tafi" na gyada masa kai kawai a raina ina jin haushin Sadauki da yace ince da Saghir zan koma. I don't like this idea at all.
Ya fara duba kayan jikin Subay'a "wannan kayan duk sun tsufa a zubar dasu Diyam. Ga kaya nan na taho mata dasu suna mota sai ta cigaba da amfani dasu" sai ya dora ta akan cinyarta tana ta zuba masa surutu yana dariya, ina jinsu ya fada mata zaiyi tafiya ita kuma ta fara lissafo masa kayan da zai siyo mata. Sannan tace "Daddy dan Allah ka dawo da wuri mu koma gidan mu ni nafi son zama tarr da kai da Mommy" yayi pecking dinta a cheeks yace "ina dawowa zamu koma kinji princess? It is going to be sabuwar rayuwa for us".
Sai naji a raina cewa tunda har yanzu ni matarsa ce then it is my responsibility inji source din kudinsa. Sai nace "kudi ka samu ne masu yawa haka? A ina?" Sai ya watso min wani mugun kallo yace "matse ni sai in gaya miki, kinsan dai tunda kika sanni da arziki na kika san ni ko? Ko kin taba gani na ina gyaran matattun motoci? Wanda ya samu dukiya sama ta ka shi ake yiwa tambayar inda ya samu dan zata iya yiwuwa yankan kai ko fashi da makami yake yi".
Sai da yasa na raka shi har bakin kofa, ya fito da kayan Subay'a jaka guda ya mika min sannan yace "I will be seeing you soon, sweet pie".
Washegari jirginsu ya daga shi da Fauziyya, I didn't even know ina suka tafi sai ya suka sauka ya kira ni yace min sun sauka a Miami, yace in ajiye number din saboda zai ke kira na da ita.
Bayan tafiyar Saghir ne Asma'u ta kammala jarabawarta, tayi candy, sannan kuma hakan yazo dai dai dayin saukar Alqur'anin ta. Wannan yasa ta shirya walima a nan gidan mu ita da kawayenta. Inna ta aika wa duk yan'uwa aka gayyato su kuma ga mamakin mu sai gasu sunzo, sai dai abinda muka lura dashi shine babu jituwa tsakanin iyalin Alhaji Babba da kawu Isa. Aka gabatar musu da abinci iri iri wanda su kansu sai da sukayi mamaki, daga abincin da aka ci har zuwa sutturar da muka saka daga mu har Inna duk sun nuna cewa ba a cikin kunci muke ba. Su Murja sai tambayata suke yi "yaushe zaki koma gidan hamma?" Murja ta jani gefe "dan Allah Diyam in baki koma bama kiyi masa magana ko zaiji maganar ki. Kinga maganar auren nan fa ta tsaya duk uban kudin da yake samu kwanan nan amma yace ba zaiyi ba. Shi kuma kawu isa da muke tunanin tura masa samarin mu shi kuma gashi yanzu ko magana basa yi da Alhaji" nace "wai me ya hadasu ne?" Ta rufe baki tace "ba za'aji a baki na ba".
Kwana biyu da yin walimar Asma'u sai ga Kawu Isa a gidan mu. Mamaki ya ishe ni na tuna ranar da yace sun cire mu a cikin zuri'a ranar da sagjir ya sake ni a gabansu amma yanzu gashi few months after ya dawo da kafafuwansa. Muka gaishe shi ni da Asma'u muka fita muka basu guri da inna. Sun jima suna maganganu kafin muji ya fita sannan muka dawo dakin. Asma'u ta saka Inna a gaba da tambaya "me yace? Me ya faru" Inna tace "ina ruwanki? Suda mai bakin magana"
Sai da Asma'u ta tafi islamiyya sannan inna ta bani labari. "Zuwa yayi yace min wai dan Allah duk yadda za'ayi kar mu mayar dake gidan Saghir. Ashe abinda Yalwati take fada min rannan gaskiya ne, Suwaiba dai har da cikin Saghir a jikinta. Alhaji Babba yace shi lallai sharri aka yiwa dansa, shi ma kuma Saghir din yace ba nashi vane ba kuma yama fasa aurenta ke zai mayar. Shine shi kuma hamma Isa yazo yace kar mu mayar masa da ke in yaso yayi biyu babu kenan. Su yanzu likitan da zai cire cikin suke nema". Nayi shiru ina jin hawaye yana bin fuskata. Na tuno zafin da naji sanda Saghir yayi min sharri a gaban yan'uwan mahaifina amma duk babu wanda yayi komai a kai. Ga zina nan ta kare a gabansu, yanzu sai su ware ni da Saghir waye mazinaci.
Bayan sati ya kuma zagayowa sai ga malam iliya maigadin gidan Saghir ya kirani hankali a tashe. Na tambayeshi sai yace "yan NDLE ne suka zo gidan, sun yi filla filla da komai na gidan wai suna neman kayan maye" cikin tashin hankali na tambayeshi sun samu sai yace "sun samu, a dakin mai gidan sukayi ta fitowa dasu sannan suka samu wasu kuma a motarsa. Yanzu tafiyarsu kenan nima guduwa nayi da ina jin dani zasu hada. Shine na kira ki tunda su basa nan in gaya miki halin da ake ciki" nayi masa godiya na kashe wayar, ina kokarin bawa inna labari sai ga kira ya shigo wayarta daga Hajiya Yalwati tana ta kuka "Amina mun shiga uku. Wai yan drugs ne suka zo zasu tafi da Alhaji. Alhaji Babba fa? Me ya hada shi da shaye shaye?". Nan take Inna ta rikirkice ta saka mu muka shirya muka tafi gidan gaba daya, muna zuwa muka tarar har an tafi dashi ga yan gidan nan sun fito sunyi chirko cirko masu kuka nayi masu salati nayi, yan unguwa kuma ana tsaye ana kallo. Mukayi ta basu baki muna mayar dasu cikin gida har muka samu suka koma ciki sannan aka fara tunanin ta inda za'a bullowa lamarin. Ni dai na fada musu abinda mai gadin gidan Saghir ya fada, dan haka sai muka fahimci cewa neman Saghir suke yi shi yasa suka kama Alhaji. Aka kira Kawu Isa aka gaya masa amma yace shi babu ruwansa "tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka".
Dan abin kunya sai surukan gidan aka nema, ciki harda wanda yake neman auren Murja, su sukayi ta zirga zirga Inna kuma ta saka Asma'u taje ta ciro kudi a account a bawa wancan cin hanci a bawa wancan amma sai da Alhaji Babba ya kwana biyu a garkame sannan suka sake shi da yarjejeniyar Saghir yana shigowa kasar zai danka musu shi a hannun su.
Ranar da Alhaji ya dawo gida haka ya zauna yana ta kuka kamar karamin yaro "ban taba ganin cin mutumci irin wannan ba, wannan yaro mai ya janyo min haka ni Muhammadu. Ankwa hannu da kafa haka aka saka min ana jana a titi kamar wanda yayi kisan kai" sai kuma ya fara yiwa Inna godiya a kan kokarin ta da karfin ta da kudinta gurin ganin an fito dashi. Yana ta kuka har ciwonsa yana kokarin tashi dan haka akayi masa allurar bacci mu kuma muka tafi gida.
What remains a mystery shine yadda akayi yan drugs suka yi suspecting Saghir yana ta'ammali da kayan maye har suka kaiwa gidansa ziyara.
Two weeks after tafiyar Saghir sadauki ya dawo. A gurin Asma'u naji zancen dawowar tasa sai kuwa gashi nan yazo gidan. Ina jin shigowarsa na shige cikin daki na lulluba kamar mai bacci. Ina jin su suna ta hirar su a palo, ya kawowa Asma'u graduation gift na wata desighner handbag da takalmi, ya kawo wa Subay'a yar karamar computer ta yara mai kyau. Ta shigo da murna tana nuna min "Mommy kinga abinda wannan yayan naki ya kawo min, amma ke yace bai siyo miki komai ba" na karba ina dubawa nace "to kije kice kin gode madallah" ta fita na koma na kwanta.
Ina ta so dai inyi masa maganar kudin companyn sa, amma bana son ganinsa dan haka bayan ya bar gidan sai na kara dauko waya ta ban kirashi ba dan nasan ba shiga zata yi ba amma sai na rubuta masa message. "Ka sa ido a kudaden kamfanin ka. I might be wrong. Just taking precautions". Na tura masa. Na zauna da wayar a hannu ina jiran reply, shiru shiru babu. Har na gaji na ajiye ta na tashi na cigaba da harkoki na. Aka jima na sake dubawa babu reply, nayi tsaki a raina nace "ku kuka sani" Sai kuma nake jin haushin kaina for caring a inda ni ba'a damu dani ba.
Saghir yakan kira ni sometimes, in ya kira sai in bawa Subay'a suyi magana. Ko da wasa ban bashi labarin case din drugs ba dan nasan ba karamin aikinsa bane ba yaki dawowa dan ba damuwa yayi da abinda za'ayiwa Alhaji in bai dawo din ba. Ranar nan ya kira na bawa Subay'a suka gama maganganun su sai yace ta bani, na karba yace min "jibi zamu dawo. Ina son ki kawo Subay'a airport ta tare mu. Tace tana son zuwa" nace "okay Allah ya kaimu jibin. Allah ya kawo ku lfy" yace "ameen. Hope kin gama shiryawa dan daga airport sabon gidazamu zarce" na sake cewa "Allah ya kaimu" na kashe. I didn't have the energy or the patient to argue.
Muna gama wayar sai naga Asma'u ta dauki tata wayar tayi kira sannan tace "jibi zai dawo" ta kashe. Ta kalleta nace "what was that?" Tace "Hamma yace in gaya masa ranar da Saghir zai dawo" na saki baki kawai ina kallonta. What was that about?
Ranar dawowarsu na shirya Subay'a tana ta murna muka tafi malam Aminu Kano international airport. Muka tsaya a gurin da aka tanada dan taryar matafiya. Subay'a tana ta tsalle ta kasa tsayawa a guri daya yayin da ni kuma nake ta lissafe lissafen halin da nake ciki. Ni har yanzu ban gama fahimtar kudurin Sadauki na mayar da Saghir aiki sannan da kuma hanani gaya masa cewa ni ba zan koma gidansa ba. Na fahimci kamar yana buying time ne but for what? Me yasa kuma yake son jin lokacin dawowar Saghir?
Muna tsaye akayi announcing saukar jirgin su Saghir, muna tsaye kuma har suka gama checking out suka fito. Na hango shi, as handsome as ever, hannunsa cikin na Fauziyya suna fitowa daga revolving door din gurin. Subay'a ta fara murna "Daddy, Daddy" ya dago mata hannu yana murmushi.
And then as he steps his feet out of the door, police surrounded him. Police, not NDLE officers. Fauziyya ta matsa baya da sauri tana ihu, Subay'a ma ta fara ihun kiran Daddy yayinda shi kuma ya fara demanding dalilin kamashi. Na daga Subay'a na rungume ta a kirjina, muna kallo daga inda muke tsaye aka garkamawa Saghir ankwa a hannayensa aka wuce dashi police car da take gefe tana jira.
Subay'a ta fara jera min tambayoyi "me yasa yan sanda suka tafi da Daddy na? Ina zasu kai shi?" A lokacin naji karar shigowar text cikin wayata. Na dauko ta na duba naga number din Sadauki. Sai yanzu yayi replying message dina. Na karanta "check up" it said.
[3/7, 9:06 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Fifty Four & Five : The Games We Play
"Check up" na maimaita a fili. Nasan wannan kalmar amma a ina? Sai mind dina ta koma baya, back in time lokacin muna yara a gida muna playing game of cards ni da Sadauki a incomplete benen Baffa a lokacin da nake gudun islamiyya ya rama min duka ance in na koma sai an zane ni. A cikin game din ana cewa check up. And it means game over.
Amma wanne game din ne over bayan ni bansan sanda game din ya fara ba? Ya akayi ya turo min wannan text din a dai dai wannan lokacin? Ko dai Sadauki yana da hannu ne gurin kama Saghir?
Kamar ance min in juya baya sai na juya. And I saw him. Yana tsaye ya jingina da jikin motarsa with dark glasses a idonsa and a broad smile on his face yana kallon motar police din da aka saka Saghir a ciki, sai da yaga sun ja sun tafi sannan ya bude motarsa shima ya shiga shima ya tafi.
Da sauri na koma taxi din da nayo shutter nace masa mubi bayan police car din data fita. A hanya drivern yake ta surutai "ai haka police suke yiwa irin wadannan bata garin, in sunyi abu sai su gudu su bar kasar sai a shammace su ranar da zasu dawo azo ayi gaba dasu. Ai wannan commissioner din baya wasa" jin ban kula shiba sai yayi shiru kuma muka cigaba da bin su a baya har na tabbatar cewa bompai zasu tafi dashi sannan nace da drivern ya kaini badawa layout, gidan Mama, muna zuwa na ajiye Subay'a na gayawa Mama briefly abinda ya faru, naci sa'a yaya Sadiq yana gida sai ta hadani dashi muka koma police station din dan muji takamaiman abinda ya faru, for what charges aka kama Saghir.
But ni already jiki na ya gama bani charges din ina dai so ne in tabbatar da zargi na. Ina kuma bukatar wasu amsoshin daga Saghir. Da kyar muka samu desk officer din ya kula mu, amma da muka nemi ganin Saghir Muhammad da aka shigo dashi yanzu sai kawai yayi mana dariya irin mun ma bashi dariya din nan, yace "wannan ai ko uwarsa ce take son ganinsa sai dai ta hakura. Ku koma gida kuyi taja masa charbi dan yau ne za'ayi masa tambayar kabari ta duniya" ya fada yana dariyar mugunta.
Nace "to zamu iya sanin dalilin da yasa aka kama shi?" Yace "ke wacece a gurinsa?" Nace "matarsa" yace "kinsan inda yake aiki?" Na hadiye wani abu a kirjina Nace "eh. Abatcha Motors" yace "to can zaki je ki tambayi abinda yayi, zasu yi miki bayani dalla dalla".
Haka muka hakura muka fito. Yaya Sadiq yana jan motar mama ni kuma ina gaba nayi shiru ina juta lamarin a raina. My deepest fear have come true, wannan case din bana drugs bane ba kuma wani ne daban, case din Sadauki ne, Saghir ya debi kudin companyn Sadauki yayi facaka dasu Sadauki kuma ya saka an kama shi. But what was Saghir thinking?
Gidan Alhaji Babba nace Yaya Sadiq ya kaini, dole inje in fada musu halin da dansu yake ciki in yaso a hadu a san yadda za'ayi tackling lamarin. Ga kuma wancan case din NDLEA da yake jiran Saghir. Sai kawai naji ina jin tausayin iyaye da yan uwan Saghir.
I also needed to talk with Sadauki. Bana ko raba daya da biyu nasan tarko ne Sadauki ya dana wa Saghir shi kuma ya fada head over heels. Wato wannan shine time din daya nema in yi masa buying kenan. Sai kuma na sake tambayar kaina "menene hadin Sadauki da case din NDLEA? I really do hope bashi da hannu a ciki.
Da muka je gidan kuma sai na kasa gaya musu, musamman ganin da nayi suna ta fama da kansu, an dafa wake da shinkafa ana ta lissafin yadda za'a samu kudin mai, sai da naje na bayar aka siyo musu. Sai na ja Hajiya Yalwati gefe na labarta mata. Ta rike baki tana salati tace "gurin aikin sa kuma? Ba companyn Sadauki bane yake aikin ji nake ya kore shi?" Nace "bai kore shi ba, ga kuma abinda ya faru. Yanzu yana bompai. Naje an ma hanani ganinsa" haka na tafi na barta da jimami nace ta gayawa Alhaji da Hajiya. Ni ba zan iya ganin wannan heart break din ba.
Daga nan gida yaya Sadiq ya kaini, na bar Subay'a gidan Mama in yaso gobe in na koma station din sai in biya in taho da ita saboda nasan yanzu in muka he gida ta saka ni a gaba kenan da tambayar ina daddyn ta? Ina police suka kai shi?. Ina shiga gidan Inna tana sallamar wani yaro da yazo siyan kankara ta gane something is wrong, sai data sallame shi tace min "lafiya? Ina Subay'a? Rigima kuka sake yi da Saghir?" na zauna ina cire hijab dina nace "inna Saghir yana bompai" ta saka salati tana tafa hannu tace "masu neman nasa ne suka kama shi? Dama sun san yau zai dawo?" Nace "basu bane ba Inna. Wani case din ne daban, basu gaya min menene ba amma sunce case ne daga gurin aikinsa" na fada ina kallonta cikin ido, nan da nan sai naga ta fahimta tace "Sadauki? Me ya kuma hada su kuma?" Na daga kafada nace "ban sani ba. Sai gobe zan sake komawa inji ko zasu yi min bayani" tace "to ki kira Sadaukin mana ki tambayeshi shi?" Na kwanta a kujera ina cewa "ba zai dauka ba Inna. Dama can baya daukar waya ta ballantana yanzu".
Na jima kwance da idanuna a rufe har aka fara kiran magrib. Ni dai va bacci nake ba kawai ina ta lissafe lissafe ne, Sadauki should have just let me take Saghir to court shikenan a wuce gurin. In na rabu dashi ba dai shikenan ba?
Ina ji da dare Inna ta saka Asma'u tana ta bugawa Sadauki waya amma yaki dauka, daga baya ma sai ya kashe wayar gabaki daya. A raina nace dai dai kenan.
Washegari tun da wuri na tashi na shirya inna ma ta shirya tace gwara muje tare, muka bar Asma'u a gida muka tafi bompai amma muna zuwa muka tarar Hajiya Babba ta riga mu zuwa ita da wani kaninta. Idanunta sun kumbura alamar tayi kuka harta gode wa Allah. Muna shiga ta taho gurina da sauri "Diyam sharri yake masa wallahi, wallahi sharri yake yi masa ina yaron nan zai kai wadannan uban kudade?" Inna ta rike ta tana lallashinta ni kuma na karasa gurin desk officer din da yake on duty. Ya miko min wata takarda wacce take dauke da case statement na case din Saghir, a jiki naga bayanin cewa ya yi transfer din kudi ne daga account din company zuwa private account dinsa. Amount din dana gani sai daya saka kaina ya sara naji kamar zan fadi, mai Saghir yake tunani ne wai? A jiki kuma naga cewa Saghir din ya karbi laifinsa tun a jiyan da aka kawo shi dan haka har an fara shirin tura shi court. Na ajiye takardar nace da officer din "can I see him please" ya kalle ni da mamaki yace "are you sure? He went through some questioning so an dan sassama shi kadan" ya karasa yana grinning. Na juya na kalli inda Hajiya har yanzu take zaune tana kuka Inna tana rarrashinta. Nace "zan ganshi, amma ni kadai" sai ya miko min wani form yace in cike. Na karba na tafi gurin su Hajiya nace musu "sun hana ganinsa, gwara ku tafi gida kawai. Ni zan zauna in cike wasu takardu yanzu zan biyo ku" kamar ba zasu tafi ba sai kanin Hajiya wanda dama tunda muka zo naga yana ta nuna alamar ya gaji yace "in mun zauna ma babu abinda zasuyi mana fa, zasu iya wulakanta mu gwara mu koma gida sai asan yadda za'a bullowa lamarin" sai naci sa'a suka bishi suka tafi ni kuma na koma ciki na cike form din da aka bani, aka kaini wani daki na zauna ina jira, shiru shiru tun ina kallon agogo gar na fara zama frustrated ina jin tamkar na shekara a dakin sai aka bude kofa aka shigo.
Saghir ne, amma kamar ba Saghir ba. Daga shi sai singlet da gajeren wando, fuskarsa babu inda bai kumbura ba dan idanuwansa da kyar suke budewa. Sai kawai naji zuciyata ta karye na rufe baki na kama kuka. Officer din daya shigo dashi yace "na gaya miki ai" sai ya zaunar da Saghir akan benchi ya juya ya fita. Na tsaya kawai muna kallon kallo. Sai can yace cikin wata irin murya "kinzo ne dan ki sakani a gaba kiyi ta kallo kina cewa Allah ya kara ko kuma kinzo ki karasa aikin da tsohon saurayinki ya fara?"
Na zauna ina facing dinsa nace "Saghir me yasa ka daukar masa kudi? Why? In zaka dauki kudin kowa a duniya me yasa zaka taba na Sadauki bayan kasan abinda yake tsakanin ku?" Yace "menene a tsakanin mu din? Ke? Dan ke akayi min wannan abin na sani kuma yayi da dan halak. Sai na rama duk ranar da na bar gurin nan sai na chanja masa kamanni kamar yadda yasa aka chanja min nawa" na girgiza kai cike da takaici, he is still being arrogant, nace "ni so nake in tabbatar, ka daukar masa kudi ko ba ka daukar masa ba? Ina so insan gaskiyar maganar nan saboda in san ta inda zan bullo mata" ya dauke kai yace "I don't need your help. Kiyi tafiyar ki kawai. Ki je ki gaya masa cewa tarkon daya kafa ya kama shaho" na girgiza kaina a raina nace 'he have no idea how much trouble yake ciki' sai na bashi labarin case dinsa da yan drugs. And that broke him down.
Hannu biyu yasa ya dafe kansa, ya jima a haka sannan ya dago yana kallona yace "wannan duk yana cikin irin kiyayyar da kike yi min Diyam? Me yasa baki fada min ba kika barni na dawo kasar? Me yasa kika barni na fada tarkon da makiyana suka kafa min" naji tausayinsa har cikin raina, nace "Saghir, ko daya ba naki gaya maka ne saboda bana sonka ba, naki gaya maka ne saboda nasan in na gaya maka ba zaka dawo ba and that means trouble for Alhaji, wanda babanka ne shi mahaifi dan haka dawowarka yafi maka alkhairi akan kin dawowarka" yace "really? To case din Sadauki fa? Shima kamanin da yayi yafi min alkhairi akan rashin kamani? Waye ya gaya masa zan dawo da har yasa aka tare ni a airport?" Nace "duk abinda zan gaya maka ba lallai ka yarda ba. Amma duk da haka zan gaya maka. Bani da idea akan abinda ya faru tsakanin ka da Sadauki. Na san dai yana buying time for something but bansan menene ba. Kuma ina so kasan cewa zanyi iya kacin kokari na na ganin ka fita daga gurin nan but for that ina bukatar ka gaya min gaskiya. Ka dauki kudin Sadauki ko baka dauka ba? Drugs din da aka samu a dakin ka da motar ka, naka ne ko ba naka ne ba?"
Ya jima shiru kamar ba zaiyi magana ba sannan kuma sai ya danyi murmushi yace "that former boyfriend of yours is smart, na bashi credit anan. Tunda yaron nan ya dauke ni aiki, ina jin ma ai na taba gaya miki, babu aikin da nake yi. Sai ya dauki wani a matsayin assistant dina to duk aikin da ya taso shi ake bawa yake yi and I tot 'huta roro' tunda dai ana bani salary na mai kyau ai bani da problem. Shekara da shekaru, ko banje gurin aiki ba bani da matsala, I should have known tun a lokacin that something is off but ni ta constant monthly income dina nake yi. And then lokacin da na koma aiki, suddenly it was all work for me. A lokacin ne nasan ma how much money ne a cikin account din Company and it was a huge money. Kullum kudi suna shigowa wadansu suna fita, kudi masu yawa. Shi yayi tafiyar sa, and duk takardar da aka kawo zaiyi signing sai a kawo min ace yace inyi a maimakon sa. Duk kudin da za'a fitar ni za'a saka in fitar dasu haka duk kudin da za'a shigar. It was like cewa ake yi Saghir dauki kudin nan. And I saw my chance. Mutumin nan yaci amana ta yayi making fool of me for years, dan haka dole ce ta saka ni na cigaba da aiki under him saboda babu inda zanje in samu din. Dan haka sai na dauka as a revenge for what he did to me kuma dan in kafa kaina nima in daina aiki under him. Nasan zai gani amma kuma nasan yana tsoron kar in bata masa image dinsa with that scandal so I expected him to keep quiet. Da kudin na sayi gidan dana gaya miki na kuma saya mana motoci ni da ke da Fauziyya and I gave some part of the money to Kabir da niyyar zamu hada share muyi business tare. Sauran kuma dasu nayi wannan tafiyar wadansu kuma suna account dina da niyyar su zasu rike mu kafin business din da zan fara ya kankama".
A gyada kai, my mind already thinking ta yadda za'a harhado kan wadannan kudade. Ya cigaba:
"Drugs kuma, wadanda aka samu a daki na, a kasan gadona, ba nawa bane ba. You know I don't do drugs. Na Kabir ne ya bani ajjiya saboda yana da iyali karsu taba masa ni kuma tunda zanyi tafiya shine yace in ajiye masa, a mota ta kuma alcohol zasu samu".
Na gyada kai nace "so, where is Kabir now?" Ya daga kafada yace "ta yaya zan sani tunda ina nan a rufe?" Nace "but ta yaya akayi suka kai mamaye gidan ka?" Yace "I have no idea. Ask that smart boyfriend of yours maybe shi yana da idea".
Na mike tsaye nace "thanks for telling me the truth. Zan je gidan Alhaji zamu zauna muga ta yadda za'a bullowa lamarin. Insha Allah, you are getting out of here. Zamuyi reporting cewa stuffs din Kabir ne ba naka ba." Na juya zan fita sai yace "why?" Na juyo ina kallonsa nace "why?" Yace "why are you trying to help me bayan duk abinda nayi miki? I tot ke celebrating zakiyi ma cewa you are finally getting rid of me" nace "kamar yadda Hajiya ta gaya min rannan. Kai dan'uwa na ne, mijina, kuma uban yata".
Daga bompai gidan Alhaji Babba na koma, a can na same su harda inna duk sunyi jigum jigum har aunty Fatima itama tazo. Na zauna na lissafa musu tas abinda ya faru. Saghir dai ya dauki kudi ba sharri ne akayi masa ba, ya kuma admitting to ajiye drugs a gidan sa amma yace ba nasa bane ba na Kabir abokin sa ne.
Nan take Alhaji Babba ya dauko waya ya kira Alhaji Murtala mahaifin Kabir yana tambayarsa in yasan inda Kabir din yake amma sai yace shima nemansa yake yi bai san inda yake ba, ya dauka ma tare suka fita da Saghir, da yake duk halin daya ne. Nan fa hankalin Alhaji ya sake tashi. In ba'a samu Kabir ba Saghir ne a ruwa.
Out of the confusion na fita waje na zauna a compound. Sai na dauko wayata nakira Fauziyya. Tunda na ganta a airport sanda aka kama Saghir ban kuma waiwatarta ba kuma babu wanda ya kuma kiranta. Bugu biyu ta dauka. "Halima ya ake ciki?" Naji haushin da bata kirani taji ya ake ciki ba sai yanzu? Amma sai nayi mata bayanin duk abinda na fahimta da kuma halin da ake ciki a yanzu. Sai ta tabbatar min da cewa tabbas taga sanda ya ajiye drugs din a day to tafiyarsu yace ajjiya aka bashi but bata san menene ba a lokacin kuma bata san waye ya bashi ajjiyar ba. Sai na ce mata ta shirya ta taho gidan Alhaji itama ayi komai da ita.
Sai can yamma ta zo, tana ta dari dari dan duk yan gidan ba sonta suke yi ba kar ma Hajiya taji labari, tace tsohuwar karuwa ce. Ita ta sake tabbatar musu da cewa Saghir shi ya ajiye drugs din da hannunsa, ta kuma gaya musu zancen gidan daya siya wanda su sam sam basu san da zancensa ba. Tace gidan yana unguwar rijiyar zaki dan haka muka yi shirin gobe zamuje a ga gidan sai kuma a nemi mai siya. Za'a karbi motarta da tasa a hada da wadda yace ya saya da sunana duk a siyar, sai a hada kudin da sauran kudin da yake account dinsa aga abinda za'a tayar kafin a nemi inda Kabir yake a dankashi a hannun NDLEA a kuma karbi kudin Saghir na hannunsa. Sauran kudaden kuma da Saghir ya riga ya kashe bansan inda za'a same su ba. Da Fauziyya zata tafi tace min "Mr Abatcha, ai yana jin maganar ki ko? Zaki iya sakawa ya saki Saghir ko?" And I didn't answer her.
Muna komawa gida na kira shi da wayar Asma'u tunda ba zai dauki tawa ba amma still sai yaki dauka, I guess yayi tunanin Inna ce take nemansa da gaske. Amma ita inna tunda taji zancen cewa Saghir ya dauki kudin Sadauki da gaske sai tayi shiru bata kuma cewa komai ba. But like I told Saghir, zanyi iyakacin kokari na gurin fito dashi so I decided to see Sadauki the next morning.
Da safe muka sake komawa gidan Alhaji Babba, Fauziyya ma tazo za'a tafi sabon gidan Saghir sai nace musu suje kawai, na gaya musu inda zanje. Abatcha Motors.
Na tarar da gurin kamar wancan zuwan nawa ana ta hada hada, sai dai yau kamar gurin yafi cika kuma motocin gurin sunfi nada yawa har bazan iya kirgasu ba, na samu receptionist din nace masa "ina son ganin ogan ku" sai ya tsaya yana kallona yadda na hade rai ya dauki waya yayi magana a ciki sai kuma ya kalle ni yace "ya ga shigowar ki ta CCTV. Yace kije office dinsa. In kika bi nan...." Na daga masa hannu nace "nasan inda office dinsa yake thank you" sai kuma na tafi inajin haushin kaina for being rude ga wanda bashi yayi min laifi ba.
Na ga wannan kyakykyawar secretary din nasa, ta yi min sannu da zuwa sannan tazo ta bude min kofa kamar ranar nan na shiga but sai na bar kofar a bude na tsaya ina kallonsa a zaune yana kallona shima.
Nace "let him go" sai ya taso ba tare daya ce min komai ba yawuce ni majestically ya rufe kofar dana bari a bude. Ya juyo ya samu kujera ya zauna yace "he took, or rather stole my money" nace "kudi, kudi, kudi dai? Shikenan abinda yake da muhimmanci a gurin ka kudi? Look at what you have, lokacin da naga amount din kudin da Saghir ya dauka I tot ya kassara ka but ni banga alamar anyiwa companyn nan ko da scratch ba" yayi murmushi yace "you are right. Amma dai ya dauka. So, dole zai biya in kuma ba zai iya biya ba sai ya tafi gidan maza har zuwa ranar da iyayensa zasu samu kudin da zasu biya masa" na tako nazo gaban table dinsa na tsaya, ina jin kamar in rufe shi da duka. Nace "me yasa? Tarko ne ka dana masa na sani but why? Me yasa? You could have just let me take him to court kamar yadda nayi niyya ya sake ni and that'll be all. Zumuncin dama ai a lalace yake menene saura. Why do you feel the need to lock him up?" Yace "kamar yadda kika ce in kika kai shi court ya sake ki that will be all. Meaning duk abinda yayi miki yayi a banza kenan? What he did to you and said to my face shikenan yayi a banza kenan?" Ya fada with bitterness in his voice, ya cigaba "wannan abinda yayi, kuma ya gaya min yayi, shine greatest mistake dinsa a rayuwa kuma shine abinda zai paying for in prison for as long as possible" na zauna a kujerar da take facing dinsa nace "ni yayi wa, ba kai ba...." Yace "da ni yayi wa da sai abin yafi zuwa masa da sauki" naji zuciyata ta karye nace "Sadauki.....komai ya faru fa ya wuce. Ni duk na yafe kowa saboda a yanzu kowa yayi paying price dinsa. Tun daga ranar da aka kaini gidan Saghir nake addu'a cewa Allah ya saka min akan duk wanda ya zalinceni, kuma a yanzu bayan shekaru duk wadanda suka zalinceni din babu wanda bai karbi hukuncinsa ba. Inna, tun ranar da aka kaini gidan Saghir har yau Inna cikin regret take, har yau bata samu peace of mind ba saboda bana jin akwai abinda yafi ciwo irin ace uwa tayi destroying rayuwar yarta da kanta. Alhaji Babba a yanzu fa bashi da komai, ka tuna dukiya da izza irin ta Alhaji Babba amma yanzu rigar da zai saka ma sai in na debo na Saghir da baya sakawa na aika masa saboda shi ba zai bashi din ba. And Saghir, Saghir fa ta kare masa, ko da bakayi trapping dinsa ya daukar maka kudi ba Saghir already yana da case, NDLEA sun samu drugs a dakinsa dan haka suna nemansa. So you see? You don't have to do anything Allah yana planning komai accordingly" yace "na yarda, kamar yadda na yarda cewa Allah yana using people to furnish other people. Alhaji Babba da kike magana fa har yanzu baiyi regret ba, ko ya taba kiranki ya baki hakuri akan abinda yayi? Har yau da zaki tambayeshi cewa zaiyi taimaka miki yayi ya aura miki Saghir, dukiyarsa kuma cewa zaiyi makiyane suka saka masa hannu. So dole ya cigaba da zama gida daya da kaji da raguna ya cigaba da having sleepless nights for as long as I had, which will be like forever tunda har yau ba baccin nake yi ba"
Na mike tsaye ina jin haushinsa nace "how thick is your skull? In kana furnishing Alhaji su kuma iyalansa fa? Me sukayi maka? Makota fa? Me sukayi maka? Gidan gona tunda ka bawa Asma'u zan saka ta ta chanja masa guri. Batun Saghir kuma za'a biya ka kudinka, za'a siyar da duk abinda ya siya da kudaden sannan a nemo sauran a cika maka a baka kayanka ba shikenan ba?" Ya mike tsaye yana murmushi yace "me da me za'a siyar, gida da motoci? You are kind of late because I already bought the house and one car about two weeks ago" na juyo da sauri nace "what?" Ya gyada kai yace "bayan ya debi kudina I asked someone to track duk abinda zaiyi da kudin, naji ya sayi gida da motoci and I became worried cos zai iya siyar dasu ya biya ni. Luckily for me, sai ga report cewa one of his friends..." Ya duba wata takarda a gefe yace "Kabir, ya saka gidan da mota daya a kasuwa zai siyar, he was in a kind of hurry sai na taimaka masa na siya, yanzu har na zuba yan haya a gidan. Shi abokin daya siyar din yanzu ance min ya gudu ya bar kasar" ya sake murmushi "hard luck for him".
Na dafa kujera na zauna ina kallonsa. Na fahimci lissafin sa tsaf kuma na gane mai ya faru. Saghir ya saci kudi, Kabir set him up with the drugs sai ya siyar da gidan ya hada da sauran kudaden ya gudu. Meaning yanzu Saghir bashi da abinda zai biya ga kuma case din drugs a kansa. Sai na mike ba tare dana sake cewa komai ba har nayi hanyar waje kuma sai na tuna abinda ya faru rannan dan haka na juyo nace masa "open the door" yace "Please Diyam, stay out of it. Let him take the fall. He more than deserve it" na dawo gabansa nace "tell me something. Me yasa ka yafe wa Inna? Inna tafi kowa musguna maka a duniya amma ita mai yasa ka yafe mata?"
Ya dago kai yana kallona yace "she gave birth to you".
[3/7, 9:06 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Fifty Six : A Walk To Freedom
"She gave birth to you"
Maganar ta daki kunnuwana sannan ta wuce har cikin zuciyata, sai naji tamkar ta kunno min emotions din dana ke ta kokarin dannewa a cikin zuciyata, sai hawaye yazo idanuna ya fara zuba kan kuncina a hankali na fara rera kuka sai ya taho inda nake da sauri yace "Diyam....." sai kuma ya dakata ya juya ya koma bayan table dinsa ya danna button din bude kofa yace ba tare daya kalleni ba "good bye Halima".
Na juya nima da sauri na fita ina kokarin goge hawayen fuskata. Na sauka daga stairs din cikin sauri na fita daga building din. So nake kawai in samu seclusion din da zanyi kuka na son raina har in gode Allah. Na tsaya a bakin kenan naga mota tayi packing a gaba na sai driver din ya fito ya zagayo inda nake ya bude min kofar baya yace "oga yace ki shigo a kaiki gida" har nayi tunanin kin shiga sai kuma nayi lissafin gwara inyi kukana a cikin mota ni kadai da ac akan inyi a cikin napep mutane suna kallona.
Na shiga ya rufe kofar ya zagayo gurin driver sannan na masa kwatancen gidan Alhaji Babba muka tafi. Na jawo hijab dina na rufe fuskata nayi kuka na na koshi amma ni kaina bansan kukan menene ba, kukan tausayin kaina ne ko na Sadauki? Kukan abinda ya faru da ne ko kuma wanda zai faru nan gaba? Ko kuma kukan abinda yake faruwa yanzu ne?
Nayi bitar maganganun Sadauki ina son inyi placing dinsa a scale din dai dai da rashin dai dai. A iyakacin fahimta ta tun muna yara nasan kafiya da zuciya sune manyan flaws din Sadauki. And he seemed to be harder yanzu. Ya nutse sosai a cikin kogin revenge yadda har yana kokarin yayi loosing kansa, and I won't allow that.
Nasan duk abinda yayi akan gaskiyar sa yake, babu inda ya kaushe wa shari'a but still Allah da kansa yace yana son bayinsa masu hakuri ni kuma ina so Sadauki ya kasance a cikin jerin mutanen da Allah yake so.
Muna zuwa gidan Alhaji Babba na sauka, drivern ya tambayeni in shikenan inda zai kaini na amsa masa da eh. A dakin Alhaji na same sun yi tsuru tsuru har da Fauziyya. Ina shiga Alhaji ya mike yana tambayata "ya kuka yi Diyam?" Na girgiza kaina kawai na zauna a raina ina cewa 'you are in for a bad news' duk da daga yanayin su na fahimci sunje gidan Saghir sun tarar da yan haya a ciki. Alhaji ya zauna shima, yanayinsa kawai ya isa ya saka mai raunanniyar zuciya kuka, yana cewa "wannan wacce irin mummunar kaddara ce ta afkawa yaron nan? Wallahi ni ko da wasa bai gaya min ya dauki wadannan kudade ba, ballantana ya gaya min ya karbi wannan ajiya. Ba wanda yake neman shawara a gurinsa shi kadai yake al'amarinsa shida abokansa. Yanzu gashi gidan munje mun tarar da mutane sunce su haya suke yi a hannun wani agent suka karba" sai na basu labarin duk abinda na fahimta da maganar, a lokacin da Saghir yake can yana honeymoon dinsa shi kuma babban abokinsa Kabir ya saka gidan da kuma motar da Saghir din ya siya da sunana a kasuwa, ya karbe kudaden ya hada dana wajensa ya gudu ya bar kasar bayan ya bawa Saghir ajjiyar drugs kuma yayi masa chunen NDLEA.
Kowa yayi shiru a dakin har na gama bayani na, sannan na kara da cewa Sadauki yana kan bakansa na cewa sai an biya shi kudinsa. Har na gama babu wanda ya samu damar bani amsa. Sai dana gama sannan Hajiya Babba tace "Allah, Allah mun tuba. Allah in laifi muka yi maka ka dube mu ka yafe mana ka kawo mana sassaci a lamarin nan. Allah ka dubi yaron nan ka fitar dashi daga wannan matsala" ni dai nace "ameen" amma a raina nasan a inda matsalar take. Alhaji ne yayi deciding cewa zai je yaga Saghir kuma zai gaya masa halin da ake ciki. Sai naji dadi dan ni kam I wasn't looking forward to breaking the news to Saghir cewa best friend dinsa ne yayi framing dinsa dan ya cinye masa kudi.
Daga gidan Alhaji gidan Mama na tafi. Ina shiga Subay'a ta taho da gudu ta tarye ni tana cewa "Mommy ina daddy? Kin dauko shi daga gurin yan sandan?" Na jawo ta na rike fuskarta a hannuna nace "Daddy ya sake yin wata tafiyar, amma zai dawo very soon" sai ta saka kuka ita gurin Daddy zata je ita in kira mata shi a waya. Sai da Mama tayi barazanar dukanta sannan na samu tayi shiru.
Muka zauna na bawa Mama labarin duk abinda ake ciki tace "ki fita cikin maganar nan Diyam. Ki barshi shi da iyayen sa suyi ta fama ai tsuntsun daya ja ruwa hausawa suka ce shi ruwa kan doka. Duk halin da Saghir yake ciki iyayen sa ne suka jawo masa dan haka ki barsu su girbi abinda suka shuka da hannun su" sai nayi shiru ina kallon Subay'a tana wasa ina tunanin ko zata daina tambayata daddyn ta?
Sai yamma sosai na shirya Subay'a muka koma gida, muna zuwa na tarar Inna itama dawowar ta kenan sai Asma'u take bamu labarin Sadauki yazo yiwa Inna sallama zai tafi 'business trip'. Na kwanta kawai na rufe idona amma nasan babu wani business guduwa yayi dan kar inyi breaking dinsa.
An saka ranar shari'a Saghir sati biyu bayan kama shi, na shirya na koma bompai gurinsa amma sai yaki yarda ya ganni, officer din yace "ya zama very emotional kwana biyun nan yace baya son ganin kowa" sai na fahimci cewa Alhaji yazo ya bashi labarin cin amanae da Kabir yayi masa, and it broke him, finally.
Tun da aka saka ranar shari'ar Saghir ban zauna ba, nice gidan Alhaji, nice bompai, nice NDLEA, kuma nice kiran Sadauki. Kullum sai na kira shi da yawar Asma'u amma itama sai ya daina dagawa. Sai in zauna in tsara masa message, duk abinda nasan zai saka ya sauko in tura masa amma ko reply daya ban taba samu ba.
During one of my visits to NDLEA ne na samu rannan suka saurare ni, nayi musu bayanin abinda ya faru nayi mentioning sunan Kabir and that cought their attention, ashe dama suna suspecting dinsa amma basu da hujjar kama shi dan haka sun yarda zai iya framing Saghir din but still there is a case, kuma dole someone has to take the fall, Saghir kenan, dole zasuyi convicting Saghir suyi sentencing dinsa har sai an kama Kabir ya kuma karbi laifinsa. I felt relieved, duk da ba wani important improvement bane ba but at least it was a step further.
An siyar da gidan Saghir inda muka zauna, an siyar da tsohuwa da sabuwar motarsa sannan an siyar da motar daya siyawa Fauziyya itama. Sai aka hada da kudaden daya bari account din sa but all that only raised one third of kudin da ake binsa. A lokacin ne na kuma fahimtar cewa Saghir bashi da kowa, bashi da brother dama, cousins din kuma da brother in laws din duk babu wanda yayi zaman arziki dasu ballantana su tsaya masa, uncle din kuma yayi wa yarsa ciki dan haka ko sau daya bai taba shiga maganar ba, daga ni sai Hajiya da Alhaji, ga Alhaji babu isasshiyar lafiya ga kuma tsufa daya kara saukar masa. Yan uwan Hajiya ma duk sun zare hannayensu sunce wannan abin kunyar ba da su ba.
Nima rannan na dawo gida a gajiye Inna ta kalleni tace "daga yau babu inda zaki kuma fita akan maganar nan. In dake ce wani abu irin wannan ya same ki da daga Saghir din har iyayensa babu wanda zai daga ko dan yatsa ne ya taimaka miki, dariya ma zasu yi miki" na zauna kawai nayi shiru, sai tace "ko kin chanja shawara kuma Saghir din zaki komawa?" Nayi saurin girgiza kaina. Bana son Saghir kuma na gama aurensa, that's a fact, but still har yanzu mijina ne, nayi kurakurai da dama a rayuwar auren mu bab sani ba ko wannan kokarin da nake masa zai taimaka min wajen goge wadancan laifukan. Sannan kuma, Subay'a, bata da wani uban daya wuce Saghir duk wani wanda zai rike ta sai dai ya zama uban kara amma ba mahaifi ba, and I am not looking forward to telling her that babanta yana prison, what will happen kuma inta fahimci cewa Sadauki yayi playing role a saka babanta a prison din?
Another dalilina kuma shine Sadauki. Sadauki loves me, for that bani da dobt, wannan kusan shine dalilin da yasa ya gudu saboda kar yaga na damu ya kasa abinda yayi niyya. And I love him, shima bani da dobt a kan wannan dan haka nake so in chanja ra'ayinsa zuwa forgiveness, for his sake, saboda ina gudar masa daukan alhakin wadanda basu da laifi, ina kuma gudar masa dana sani a nan gaba.
Ranar sharia tazo and we all went to the court, na bar Subay'a a gida, wadda a ranar ma sai da tayi min complain din neman daddyn ta. Na samu seat a farko farko na zauna bracing myself for duk outcome din da za'a samu. Muna zaune aka shigo da Saghir, looking very down and defeated, ban taba ganin sa a haka ba. Ya zauna a gurin zaman accused looking down at his fingers.
Sai aka fara gabatar da kara, aka lissafa all charges against him sai lawyers suka fara maganganun su da ba ganewa ake yi ba, nayi ta stressing ƙwaƙwalwa ta ina so in gane mai suke cewa amma sam bana fahimta sai dai in sunyi magana inga alkali ya gyada kai har suka gama. Sannan ya juyo yana kallon Saghir ya tambaye shi "how do you plead?" Ba tare daya kalle shi ba yace "guilty" and my heart went out to him.
A take alkali ya yanke masa hukunci, for the crime of kudin Abatcha Motors daya ci, za'a rike shi a prison har sai familyn sa sun biya kudin, for the crime of drugs, shima zai zauna har sai an kama Kabir.
In both cases he is doomed for life.
Aka gama karanta masa sentence dinsa amma bai dago kansa ba, na fara jin koke koke a baya na. Na waiga naga Hajiya tana kuka ita da kanwarta, sai Fauziyya daga can gefe, sai su Murja sun hada kai ita da sauran yan'uwanta suna yin nasu, and then a can karshen room din na hango wadda banyi tunani ba. Suwaiba. Itama tana nata kukan.
Sai aka taho dashi za'a wuce dashi, ya tsaya yana kare mana kallo daya bayan daya, sai muka hada ido and he smiled. Da sauri na mike na tari abin hawa zuwa gida.
Ranar kwana nayi banyi bacci ba. Washegari Mama tazo suka wuni anan ita dasu Rufaida da Muhsina. Bayan sun tafi da yamma sai naga Subay'a ta shigo da banki irin na kasar nan na yara ta saka a kasan gadon Inna. Nace mata "Subay'a? Banki kika siyo mana?" Tace "eh, kudi zan ringa tarawa a ciki in biya wannan yayan naki kudin sa da yake bin Daddy na" I was stoned, nace "Subay'a? A ina kika ji wannan maganar?" Tace "Mama naji suna hirar da Inna, wai Daddy na yana gurin police sai an biya yayanki kudi sannan za'a fito dashi".
The next day na tashi da wuri na shirya, Inna ta tambayeni inda zanje sai nace "prison" sai ta shirya min abinci a basket tace "ki kai masa".
Da yake anan kano central prison yake, dan haka da kafa na tafi tunda babu nisa da gidan mu. Na jima ma'aikatan prison din suna ta ja min aji kafin su yarda zan ganshi. Sai suka kaini wani guri suka ce in zauna. After waiting for like eternity sai gashi sun fito dashi. He looked very different. Older but calmer. Suka zaunar dashi a kujerar gaban table din da nake sannan wanda ya kawo shi ya matsa baya but yana kallon mu.
Na sunkuyar da kaina ina lissafa fingers dina shi kuma yana kallona yace "my God, you really are beautiful" na dago na kalle shi and he smiled. Nace "ga abinci nan inji Inna" yace "thank you. Dama kinga azumi nake yi" nayi shiru ina tunanin ban taba ganin Saghir yana azumi ba in ba Ramadan ba. Sai yace "ya kika ga sabon gida na? Yayi kyau?" Na kalli surrounding din gurin nace "nan ba gidan ka bane ba Saghir. I am going to get you out of here" yayi dariya yace "how? Zaki saka ni a jaka ne mu tafi gida tare?" Nayi shiru. Yace "nasan maybe, just maybe, zaki iya convincing your lover boy ya yafe min kudinsa, but zaki iya kamo Kabir ki danka shi a hannun hukuma ki saka yayi confessing cewa shi yayi framing dina?" Nace "maybe, just maybe, zan iya convincing Sadauki ya yafe maka, sannan in saka shi yayi amfani da power dinsa to get you out. Nigeria ce fa, with few phone calls an gama komai".
Yayi dariya "not even in your dreams. Ba zaiyi ba. Mutumin da yake son ganin baya na ta yaya zai taimaka min?" Nayi shiru, nima kaina bansan ta inda zan bullowa wannan lamari ba but i am going to try.
Yace "I really did mess up ko? Nayi messing up auren mu. It would have been a great one" nace "not 'you' but 'we'. Tare muka hadu muka rusa auren mu. Ina fatan kuma zaka yafe min my part of the mess" yace "oh, you mean the closed doors ko?" Nayi murmushi. Na juya hannunsa yace "na yafe" nace "thank you".
Sai ya saka hannu a aljihu ya fito da takardu guda biyu yana kallona sarcastically yace "ya sunan ki ma? Ke ce Halima ko kece Fauziyya?" Bance komai ba sai ya miko min daya, naga sunana baro baro a jiki na bude na karanta
Ni Saghir Muhammad Kollere na saki matata Halima Usman Kollere saki daya, in ta samu miji tayi aure
Na dago ina kallonsa yace "daya ne ba yawa, in kika hada da wancan sun zama biyu kenan. Ni kuma na rike daya a gurina with hope that maybe, just maybe, zaki zauna ki jira ni" nayi murmushi yace "not even in my weirdest dream ko? I will just have to keep hoping".
Mutumin daya rako shi ya matso yace "time up" na gyada kaina na mike kamar zan tafi sai kuma na dawo na tsaya a gabansa nace
"For raping me, na yafe maka. For the twins, na yafe maka. For everything, na yafe maka. And I am going to get you out of here"
Yayi murmushi yace "thank you. Goodbye Halima".
Sai na juya da sauri na fita daga gurin, na kuma fita daga cikin prison din, hannuna rike da takarda ta.
Na fara tafiya a kafa ina jin iskar yanayin damina tana ratsani. Wani abu naji ya yaye daga ƙwaƙwalwa ta. I felt a sense of freedom wanda rabon da inji shi tun ranar da aka aura min Saghir. Hatta hanjin cikina ji nayi yana warwarewa tamkar da a nannade yake a guri daya, wani abu daya tokare a makogwarona naji ya sauka at last ina shaƙar numfashi freely.
And I decided that I am going to do the right thing.
[3/7, 9:06 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Fifty Seven: Moving On
A hankali nake tafiya, enjoying my own company, feeling as free as a bird. Wannan feeling din da banji ba lokacin da Saghir yayi min sakin farko sai yanzu nake jinsa. Nayi murmushin da ya shiga har cikin zuciyata sannan a hankali na fara tariyo rayuwar auren mu da Saghir a kaina.
Shi dai Saghir, babban abinda yayi dooming rayuwar sa har ya kai shi ga stage din da yake ciki a yanzu shine rashin tarbiyya. Makauniyar soyayyar da iyayensa suka nuna masa tun yana jariri ita ce silar komai. Sai ya taso a matsayin sangartacce, mai son kansa kuma marar yawo saboda bai san yadda zaiyi ya kula da kannasa ba kwata kwata ballantana har ya kula wani, that including su kansu iyayen nasa. Rashin yawon sa shine ya bawa Sadauki da kuma Kabir damar kai shi inda yake a yanzu.
Na tuno ranar daya ce min bararoji a palon Hajiya, na tuno sanda ya shigo daki a gaban Inna yace baya sona, na tuno abinda ya faru a first night din mu da kuma abinda ya biyo baya, na tuno haihuwar twins, zama na a gida da kuma komawa ta gidansa. Inda ace zan zauna zan iya lissafa sau nawa muka yi magana ni shi inus our first year of marriage. Har zuwa haihuwar Subay'a bata chanja zani ba. Na tuno da yawan comments din da yake yi akaina cewa bani da body parts din daya ke so a gurin mace, year after year, then suddenly lokaci daya ya chanja after ya gama gasa ni for about seven years sai kuma ya dawo yana bani kulawa always commenting on my beauty and the so called body parts din daya ke so wadanda a lokacin na fara developing dinsu. A duk lokacin da naga yana wannan care da comments din nasan inda maganar zata kare, his bed. I remember yadda yake yawan comment cewa I tasted different than sauran matan da yake sharing bed dinsa dasu. And then he said he loves me.
But that got me thinking, it that really love? I mean zaka iya cutar da wanda kake so? Ka dake shi ka aibatashi a gaban mutane ka aibata iyayensa masu rai da marasa rai sannan kace 'you are really beautiful' ka ja shi zuwa gadonka? It that love or something else?
Duk wanda yace baya sonka, ya wulakanta ka a lokacin da baka da physical appearance din daya ke so, sai daga baya kuma daka samu sannan yazo yake kulaka, to me that is not love, that is lust.
Nasan so kuma I don't think I can hurt wanda nake so intentionally. Ko a gurin da ake aibata shima ba zan iya zama ba ballantana ni inyi da kaina. In na bata masa ransa kuwa to tabbas akan wani abu ne da nasan is for his own good. Kamar abinda na kudurce a raina cewa ina so yayi.
A tsakar gida na tarar da Inna da Asma'u suna ta gyaran gida saboda tashin su Maman Iman shekaran jiya. Na gaida ta sannan na mika mata takardar da Saghir ya bani na shige daki, ina jinta ta saka Asma'u ta karanta mata. Sai na zauna a gaban kujerar da Subay'a take kwance a kai ina kallonta a raina ina lissafin whats next a rayuwar mu ni da ita, Allah ne kadai masani amma ni nasan zanyi duk abinda ya kamata inyi a matsayi na na uwa dan ganin cewa ta samu farin ciki koda kuwa hakan yana nufin yin gibi ga nawa farin cikin. The first thing da zanyi shine in mayar da ita school, already tayi missing term guda gashi har anyi hutu ana shirin komawa sabon session. Dan haka na yanke shawarar nema mata school a arear gidan mu in saka ta wadda nasan Inna zata iya biya dan ni koboless nake a yanzu, hatta kudin recharge card ma bani akeyi.
Inna ta shigo ta zauna tana kallona da takardar a hannunta tace "na kira Hajiya Yalwati na gaya mata, nace ta gaya wa su Alhaji" na gyada kai kawai, sai kuma tace "Allah yasa hakan shi yafi miki alkhairi Allah kuma yasa karshen wahalar ki kenan" nace "ameen Inna. Nagode".
Washegari da wuri Asma'u ta fita saboda tana ta harkar neman admission, ina jinsu suna waya da yayanta da sassafe a raina nace "kaga masu business trip". Bayan ta fita nima na fita naje nayi mana register ni da Subay'a a islamiyyar bayan layin mu wadda ake yi safe da yamma. Sai a lokacin nayi dana sani dana yi jamb din nima maybe da yanzu nima ina neman admission din amma yanzu ya wuce ni sai next year. Bayan na dawo ne na tarar da bakuwa a palo tana jirana. Fauziyya. Sai naga duk ta chanja duk babu gayun nan, ga hijab a jiki, the first time da naga Fauziyya da hijab. Daga yanayin fuskarta na gane itama ta karbo tata takardar sai na maze muka gaisa tana ta yiwa Subay'a wasa, ni kuma sai na kira Subay'a na aike ta gurin Inna dan yanzu sam bana son yin hira a gabanta.
Sai Fauziyya ta miko min wata takarda tace "kinga Halima" na karba na bude a raina ina saka ran ganin irin tawa takardar amma sai naga report ne daga asibiti da yake nuna cewa Fauziyya tana dauke da juna biyu. Na ninke na mika mata ina kokarin kakalo murmushi nace "well congratulations" sai ta fara share hawaye tace "zubar wa zanje inyi Halima. Ya zanyi dashi? Na gaya miki nayi aure ne saboda ina son inyi settling down a gidan miji, wannan cikin would have been a good news da ace abinda ya faru bai faru ba, yanzu ta yaya zanyi inyi raising baby alone babu miji babu mataimaki? Kinsan iyayena basu da rai, kuma yanzu ba kowa ne zai aure ni da baby ba, Saghir kuma...." Sai ta rufe fuskarta tana kuka, na taso na dawo kusa da ita ina rarrashinta tace "jiya da yamma naje ganinsa, ya bani takarda wai ya sake ni saboda bashi da ranar fitowa. Bai ma san da cikin ba ban gaya masa ba saboda so nake in zubar dashi" nace "to yanzu ni me yasa kike gaya min? Ba kya ganin cewa kina gaya min ne saboda deep down ba kya son zubarwar kina so wani ya baki shawara yace kar ki zubar?" Ta dago kai tana kallona sai ta gyada kai tace "haka ne, ina son baby na amma ya zanyi" nace "ni ba gashi yanzu an barni da Subay'a ba? Ke da kinyi karatu, ni fa secondary school kadai na gama da kyar, ba zaki iya ki nemi aiki da takardun ki ba ko dan teaching ne ko da private school ce ki ke yi kina samun kudin da zaki rike kanki da abinda Allah ya baki ba? Ni ina ganin in dai ba gani kikayi zaki takura ba to gwara ki ajiye batun aure a side ki samu abinyi first, in mijin yazo along the way shikenan, who knows? Maybe kiga Saghir ya fito nan bada dadewa ba" sai naga hope yazo fuskarta tace "da gaske? Zaki taimaka masa?" Na gyada kai nace "zanyi iyakacin kokari na, amma babu guarantee. Sai dai ina so kiyi min alkawarin ba zaki zubar da cikin ba" ta gyada kai da sauri tace "na fasa zubarwa insha Allah. Allah kuma ya baki sa'a akan abinda kika saka a gaba". Mun jima muna hira sannan na raka ta bakin hanya ta tafi.
Kwana biyu bayan nan da sassafe ina bacci naji ana ta haya niya a tsakar gida, na leko ta window sai naga ma'aikata ne suke ta shigo da kayan gini, na tashi na fito palo na gaishe da Inna na tambayeta "aikin menene za'ayi a gidan nan?" Sai tace "can dakunan za'a gyara sai a zuba kayanki da aka kwaso" ban wani damu da aikin ba da yamma zan tafi islamiyya na leka naga kusan sabo ake mayar da gurin. Hatta plaster da floor an kankare ana sake wasu, an cire ceiling da electric wiring duk za'a sake sai na dawo gurin Inna nace "wannan aikin Inna a ina aka samu kudin yinsa haka?" Bata kalle ni ba tace "matse bakina sai in gaya miki" ban sake cewa komai ba na juya na fita.
Washegari da safe aka sauke katangar da akayi a tsakiyar gidan mu ya koma kamar yadda yake ada. Kwana biyu ana aikin aka mayar da tsofaffin dakunan inna tamkar brand new dan in ba sanin su kayi ba ba zaka gane suba. Maimakon inga an kawo kayana da aka debo daga gidan Saghir sai naga ana shigo da wadansu kayan wadanda ko a ido ka kalla kasan ba class dinsu daya da wadancan nawan ba. Sai na sake komawa gurin Inna "Inna ina wadancan kayan da aka dauko?" Bata kalle ni va tace "na siyar dasu na kara jari" sai na mayar da bakina na rufe.
Asma'u tana shigowa na jata gefe daya yadda Inna ba zata jiyo ba na fara zazzaga mata masifa "ke ce kika ce da mutumin can ya gyara mana gida?" Ta daga kafada "wanne mutumin kuma?" Nace "kar ki raina min hankali kinsan wanda nake nufi ai" tace "the last time I checked shima gidan su ne. Menene laifi a ciki dan na gaya masa masu haya sun tashi za'a zuba kayanki a ciki shine yace a bari azo a gyara gurin tukunna. Daga nan kuma sai ga kaya ya aiko dasu a zuba" na bita da harara nace "kice masa......" Tace "ince masa an gode? To zan gaya masa" sai na dauki katako kamar zan dake ta ita kuma ta fice da gudu.
Wasa wasa ana gama wa da dakunan inna nada muka koma ciki muka tare. Inna da Asma'u daki daya ni da Subay'a daki daya. Na dauko akwatunan kayan sawar mu da muka debo daga gidan Saghir na jera mana abin mu. Subay'a tana ta murna wai munyi sabon gida. "In Daddy ya dawo anan zamu zauna tare dashi".
Daganan kuma aka fara gyaran dakunan Baffa. Aka gyare su tas suma aka saka sababbin furnitures aka barsu a matsayin gurin saukar baki. Inna tayi ta gayyatar yan uwa su zo suga sabon guri, kowa yazo ya gani yayi ta sam barka. Lokacin ne Adda zubaida itama tazo dai ta jani gefe tace "Alhaji ne ya turo ni gurinki. Yace inyi miki godiya sosai akan irin kokarin da kika yi tayi a lokacin shari'ar Saghir. Allah yayi miki albarka Allah ya bar zumunci kuma Allah yaji kan baffanku" nace "ameen. Shi kuma Allah ya fito dashi" "hmmmm" kawai tace, sannan tace "ki samu lokaci kije ki dubo alhajin" nace "to". Sai kuma na kawo mata shawarar da nake ta sakawa a raina tuntuni nace "Adda, a shawarce ku manyan mu tare da Aunty Fatima dasu Inna ku ya kamata ku shiga cikin maganar Alhaji da Kawu. Ya kamata su daidaita haka nan tunda wanda ake rigimar a kansa ma yana can a rufe" tace "zasu daidaita ne, amma ba nan kusa ba kinsan cikin suwaiba ya ki fita har yau, shegen jika za'a ajiye musu, yarinyar ma an kaita Kollere a can zata haihu" na dafe kaina ina jin babu dadi, ina taisayawa yarinyar nan wallahi Saghir ya shafa mata bakin fenti marar goguwa. Yanzu dai yaya biyu za'a haifawa Saghir kenan. Sai na bata labarin cikin jikin Fauziyya, ta rike baki tace "to ai kuwa bana jin mutan gida sun sani".
Duk wannan abinda ake yi shi oga mai gyaran gida ko keyarsa ban gani ba. Ban san ko ya dawo daga so called tafiyar ba ko kuma bai dawo ba. Amma kusan kullum ina jinsu suna waya shida kanwarsa kuma nasan suna gulmata dan sai inga ana maganar ana kallona ana dariya. In naga haka sai in tashi in bar gurin.
A haka har akayi resuming school. Nayi wa inna maganar Subay'a sai tace in bincika makaranta mai kyau sai na gaya mata har na bincika ma na samu wata anan kusa damu wadda zata iya zuwa da kanta. Sai tace da safe in je inji fee dinsu da sauran abubuwa. Amma da safen ina tashi sai naga Asma'u ta tashi itama tana shiryawa nace ina zata je wai "hamma yace in shirya in shirya Subay'a zai zo da wuri muje a sata a school" cikin fada nace "oh dama yana gari kenan. In shi ya haifar min yar ba sai yazo ya dauke ta ba in gani" sai naga duk sun tsaya suna kallona sannan na fahimci nayi rashin kunya a naganar. Nace "amma inna sai ya fara gaya min ai ko? Kulawa ma ai yabawa ce" Asma'u tace "yace ai fushi kike yi dashi. Wai in yayi miki magana ma ba zaki kula shi ba" nace "ya gwada ya gani? Ni ina na ganshi ma balle inki kula shi?" Sai tace "to ki shirya sai kuje tare ku kaita" na tashi nace "bazanje ba ai bai gayyace ni ba".
Ina kallo suka fita, sun jima sannan suka dawo Subay'a tana ta bata rai amma suna zama sai ta fara bani labarin sabuwar makarantar ta, ta nuna min uniform dinta da books din da already aka riga aka bata. Gobe zata fara zuwa fresh. Sai kuma naji dadin kula Subay'a da yayi har ya tuna cewa sabon session za'a shiga ya kamata sata a school. Daganan kuma sai ya ajire driver wanda kullum yake zuwa ya kaita school sannan in an tashi ya dauko ta.
Asma'u ta samu admission a northwest university ta fara karatu. A lokacin ne nima na gayawa Inna kudirina na shiga computer school kafin shekara ta zagayo in nemi admission, harda karawa da cewa "irin wadda Sadauki yayi lokacin da baici jamb ba" wai duk dan ta bari saboda naga yanzu shine favorite person dinta. Amma sai ta tabe baki tace "wato ke lissafin karatu ma kike yi kenan, auren kuma fa?" Naji kamar zan saka kuka nace "aure kuma Inna? wanne irin aure dan Allah dan Annabi?" Sai tace "au baki san wanne irin aure ba? Ai kin kusa gama idda zaki sani a lokacin" kamar ta fada da bakin mala'iku kuwa a ranar sai ga third period dina tazo. Ina cikin saka pad a daki sai gata ta shigo ta kalleni tace "to alhamdulillah!" sai naji duk kunya ta rufe ni. A raina nace "shin wai Inna auren dole zata sake yi min ne?"
A ranar na shirya nace gidan Mama zan tafi in kwana biyu, amma inna ta hana ni tace "islamiyyar fa?" Haka naja jakata na mayar daki na dawo palo na cigaba da zama.
Two weeks bayan nan, ina zaune zaman kallo zaman kashe wando kamar kullum sai jin muryar Sadauki nayi a tsakar gida yana tsokanar Subay'a da sunan da yake gaya mata "Subis" sai na mike da sauri har da dan guduna na shige daki na rufo kofa. Sound proof ne dan haka bana jiyo mai suke yi a palon sai daga baya Subay'a ta shigo ta turo baki, ta zauna a gefe na tace "wannan yayan naki ne yazo" nace "kin gaishe shi?" Ta gyada kai.
Dan rashin ta ido sai ganin kiran sa nayi a waya ta. Na kalli wayar a raina nace "lallai ma Sadaukin nan" ina kallon wayar wannan kiran ya shigo ya katse wani ma ya shigo har ya gaji ya daina. Sai na dauki wayar ina kallon number din. Finally dai anyi unblocking dina kenan. Ya kamata dai inyi saving number din nan, amma wanne suna zan saka masa? Sadauki? Ko hamma kamar yadda naga Asma'u ta saka?
Sai kawai na bude keyboard dina nayi typing "Aliyu" nayi saving. Asma'u ta budo kofa ta shigo tun kafin tayi magana nasan me zata ce "ki zo inji Inna" na dauki hijab dina na saka na fita. Yana zaune can carpet a gefen kujerar da Inna take zaune, an cika masa gabansa da kayan ciye ciye, yayi kwalliyarsa cikin normal kananan kayansa. Nayi saurin dauke kaina daga kansa saboda zuciyata da naji tana kokarin barin kirjina. Na zagaya naje na zauna can nesa dasu nace "Inna gani" tace "baki ji Sadauki yazo ba? Ai dai kya fito ki gaishe shi ko?" Na kalleshi muka hada ido, har da wani langwabar da kai kamar wani abin tausayi. Na dauke kaina nace "sannu da zuwa" yace "yauwa. Ya gida ya makarantar?" Asma'u ta fara bashi labarin school dinsu, yana ta tsokanar ta wai jambite ni dai sai na mike zan bar musu gurin sai yayi sauri ya tashi yace "Inna zan wuce, Allah ya bamu alkhairi" tace "ameen, Allah yayi albarka" sai da ya je bakin kofa sai ya juyo yana shafa kai "ammm, Diyam. Akwai sakon Subay'a a mota ko zaki zo ki karba" nace "Asma'u, bi shi ki karbo mata" sai ta mike tayi hanyar daki tana waka "you know I love it when you call me senorita" ta shige daki ta rufo kofa. Na cigaba da zama na shi kuma yana tsaye a bakin kofa yana kallona sai kawai gani nayi Inna da dauko mafici tayo kaina dashi sai na tashi da sauri na fita.
A garage na same shi a tsaye yana dariya. Na hade rai nace "ina sakon?" Yace "yanzu ke baiwar Allah sai Inna ta biyo ki da mafici sannan zaki zo gurina?" Nace "akwai sakon da zan karba ko babu?" Ya jingina a bango ya rungume hannayensa yace "babu, just want to see you, that's all" nayi shiru, trying so hard not to look at him, yace "ba kya son gani na yanzu ko?"
[3/7, 9:06 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Fifty Eight : Murjanatu
Na dauke kaina gefe nace "tunda babu sakon da zaka bani, Allah ya bamu alkhairi" na juya zan tafi sai ya zagayo ta gabana ya tsaya yace "look into my eyes and tell me ba kya son ganina and I promise you I will leave you alone" na daga ido na kalle shi amma muna hada ido sai nayi saurin sunkuyar da nawa idon kasa saboda wani zazzafan sako daya iso gare ni daga cikin idanunsa, sai na jawo fuskar hijab dina na rufe fuskata dashi, amma ina ganin duhunsa, sai naga ya sunkuyo dai dai fuskata yace murya can kasa "open your eyes and look into my eyes kice 'sadauki bana son in sake ganin ka" sai na juya fuskata daya side din nace "ka bani hanya in wuce, ko ka manta na baro ƴata a daki ita kadai? And she needs me saboda babanta bayanan yana prison" sai ya gyara tsayuwar sa yace "hmmm. Gori zaki yi min kenan ko? Wai 'ƴata'" ya fada yana kwaikwayon magana ta. Bance komai ba sai kuma yace "Subay'a will be fine, nayi miki wannan alkawarin. Na san ba zan taba replacing mahaifinta ba, amma zanyi duk iya kacin kokari na inga na bata duk abinda ya kamata uba ya bawa yarsa. Kar ki manta ina da training din rikon ɗan wani. Ban tashi da ubana ba duk kuwa da cewa yana raye, and still I have gotten the best fatherly care and love"
Na fahimci zancen Baffa yake, sai na bude fuskata ina kallonsa nace "hakane, amma banbancin ka da Subay'a shine shi Baffa bai rufe mahaifinka a prison ba sannan bai yi gidan gona a cikin gidan grandfather dinka ba. No child will ever forget that". Ba tare dana kalleshi ba na wuce shi na koma ciki.
Ina shiga na wuce Inna a palo na shiga daki ina jin zuciyata tana yi min zafi, haushin Sadauki nake ji kuma haushin kaina nake ji. Ji nake kamar wani dan karamin yaki akeyi tsakanin zuciyata da ƙwaƙwalwa ta ko wanne yana gaya min abinda zanyi. Sai na sake jawo jakata na kuma hada kayana kamar rannan na fita na samu Inna a dakinta tana sallah sai na zauna na jira ta sai data idar sannan ta juyo tana kallona, daga yanayin zaman da nayi tasan magana ce a bakina dan haka tace "ya akayi?" Nace "Inna, alfarma nake nema a gurin ki. Dan Allah Inna ina so ki fita daga maganar Sadauki" ta kalle ni da mamaki tace "ban gane ba? In fita daga maganar sa kamar yaya? Wacce maganar kenan?" Sai nayi shiru na kasa bata amsa sai tace "ba kya sonsa ne yanzu kuma?" Na girgiza kaina nace "kawai dai Inna ina son ajiye maganar sa a gefe sai zuwa lokacin da muka sake fahimtar juna tukunna. Kinga shekaru da yawa, abubuwa da yawa sun chanja. Ba lallai ne halayyar sa ta da ita ce a yanzu ba. Ni so nake ki bar mu ni da shi kiyi ta mana addu'a in Allah yasa muka fahimci juna sai mu sanar muku ku saka mana albarka" a juya kanta gefe tace "fushi kike dashi akan maganar Saghir ko?" Nayi shiru, sai ta cigaba "ruwansa ne in yaga dama ya yafe masa, ruwansa ne kuma in bai ga dama ba kuma yaki. Ni ba wai ina matsa miki ki kula shi ko ki aure shiba, ina kokarin gyara abinda na bata ne a baya, ina kokarin bashi abinda na hana shine a baya tare da fatan ko hakan zai rage min laifuffuka na a gurinsa da kuma a gurin ubangiji. Dan haka ni dai shi nake so ki aura, amma zabi yana gurinki in kince a'a bazan ji dadi ba amma ba zan matsa miki ba".
Nace "Nagode Inna" sai kuma na gabatar mata da bukata ta tason zuwa gidan Mama. "Kwana biyu" ta ce min, naso ta barni inyi sati ko ma sati biyu amma taki, haka na hakura na dauki kaya set biyu da safe na tafi tunda ina son zuwan saboda ina so muyi shawara.
Ina zuwa na tarar Rumaisa tazo, na saka ta a gaba da tsokana mai ciki mai ciki ita kuma tana ta jin kunyar Mama, sai da muka kebe tace "wai dama haka ake ji in ana da ciki?" Hmmm kawai nace mata a raina ina cewa wannan kukan dadi take yi, na tuna cikin twins ina 14 years, babu abinda na sani, ga babu miji babu iyaye. Na tuna cikin Subay'a yadda na sha wahalar laulayi, da gorin da Saghir yayi min wai daga an taba ni sai ciki.
Sai da muka samu zama sannan na bawa Mama labarin cewa Sadauki fa ya dawo, bai dai furta direct ba amma ya nuna. Ta daga kafada tace "so? Ji nake murna zakiyi kuma naga kin bata rai" sai na gaya mata kuduri na akansa.
"Ba wai bana son aurensa bane ba Mama, so nake ya kunce kullin da yayi da kansa, saboda jin dadin kansa kuma Subay'a" tace "so kike ya yafewa Saghir kudin da yake binsa?" Na girgiza kai nace "ba wannan kadai ba, so nake ya taimaka masa yayi solving drug case dinsa. Sadauki yana da power, zai iya jan wasu strings ayi closing case din Saghir na drugs, ko kuma ayi tracking Kabir a kama shi asaka shi ya amsa laifinsa. Bayan ya fito dashi kuma ina so ya bashi aikin yi, saboda nasan with that reputation babu ma'aikatar da zasu dauki Saghir aiki ballantana ya samu abinda zai rike yayansa". Mama tace "anya kuwa Diyam wadannan sharadan naki basuyi tsauri ba? Wane ne zai je neman auren mace kuma tace masa sai ya fito da tsohon mijinta daga prison kuma ya bashi aiki? Anya kuwa kina ganin zai amsa?" Na girgiza kaina nace "ban sani ba Mama, shine kuma shawarar da nake so ki bani yadda zan saka Sadauki ya karbi wannan maganar. Ni dai abinda na sani shine zuciyar Sadauki tayi tauri da yawa, ya kasa yafewa wadanda yake ganin sun cutar dani da shi. Kuma nasan gurin Sadauki Saghir yafi kowa baƙi, shi yasa nake so ya yafe masa kuma ya taimaka masa. Nasan in dai har ya iya yafewa Saghir to babu wanda ba zai yafewa ba, in dai har ya taimaka wa Saghir to babu wanda ba zai taimaka wa ba".
Mama tayi shiru tana kallona sannan tace "zuciyarsa tana da tauri tabbas, ke ai kinsan haka tun kuna yara haka yake kuma sai rayuwa ta kara taurara shi. To ni a shawara ta ba juya masa baya zaki yi ba jawo shi kijinki zakiyi. Ki nuna masa irin son da kike masa ki bashi dama ya nuna miki nasa, to shi kansa ba zai san sanda zuciyar tasa zata rissina ba, abinda zaiyi ke kanki sai ya baki mamaki".
Kwana na biyu gidan Mama na shirya zan koma gida Inna ta kirani. "Sadauki yazo dazu, na gaya masa kina nan gidan yau zaki dawo sai yace zai zo ya dauko ki" nace "to" a raina ina jin haushin mai yasa ba zai kira ni ya gaya min ba.
Sai bayan magrib sannan yazo, har na gaji da jira na kwanta a palo ina game a wayata sai ga kiransa "Aliyu" nayi tsaki sai kuma nayi murmushi na daga nayi sallama, ya amsa yace "na dauka ba zaki dauki wayar bama ai. Kin san ni yanzu tsoran ki nake ji fa" nace "naga alama kam. Amma ai ba yanzu ne ka fara tsoran nawa ba dama ka dade kana yi" sai yayi dariya, and I couldn't remember the last time da yayi dariya irin haka. Nima sai nayi murmushi. Yace "ina waje, Please kar kice da Mama ni nazo dan kunyarta nake ji" na tashi na shiga dakin Mama zan mata sallama tace "da daren nan" sai na sunkuyar da kaina nace "Sadauki ne yazo zamu tafi tare" tace "kuma babu gaisuwa? Ki ce masa ya shigo mana" na dauki waya na kira na gaya masa yace "ke ba'a sirri dake? Ban taba zuwa na gaishe ta ba sai kuma in zo in fitar mata da ƴa? Ni kunyar ta nake ji" nace "to ai in bance kai ne ba ba zata barni ba cewa zata yi dare yayi" a dolen sa ya shigo, yana ta sunkuyar da kai yana shafa keya, and I asked myself "wai me yasa maza in suna jin kunya suke shafa keyar su?".
Bayan ya fita nayi wa Mama sallama na bishi a baya. A cikin mota na same shi a zaune a seat din driver. Sai ya bude min kofar gaba yayi min alamar in shigo da hannunsa. Na shiga na rufo kofar sai ya juyo yana kallo na, na sunkuyar da kaina kasa ina feeling uncomfortable. Motar naga kamar tayi mana kadan, space din tsakanin mu yayi kadan, ga motar ta cika da kamshinsa mai shiga har cikin ruhi. Sannan kuma gashi yana min murmushi.
Naji kamar in bude motar in fice. Bai kunna motar ba ya juyo yana kallona Yace "wai ke duk fushin ne haka? Me zanyi ne wai ayi min murmushi ko guda daya ne" sai na kara bata rai na turo baki yace "okay rashin kunyar tana nan ashe kenan. Na dauka an barwa Subay'a" sai ya tayar da motar muka bar gidan.
A hanya yace "kinsa naji kunyar Mama fa, banzo na gaishe ta ba sai da nazo zance" na kalle shi nace "zance? Gurin wa kaje zancen? A kano muke fa ba'a Maiduguri ba" ya dan bata rai kamar mai tunani sai kuma yayi dariya yace "ohhh okay, yanzu na gane wannan fushin na menene. Ai na gaya mata zan zo gurinki dama kuma tace in gaishe ki" nace "kar ma kayi tunanin da nake tunanin kana yi. It is not what you are thinking" yace "yes it is. Hausawa sunyi karin magana suka ce kishi kumallon mata, amma ke naki kishin aman gaskiya yake saka ki. Daga jin muna magana da Inna sai ki kama amai?" Na gane maganar da yake yi nayi saurin cewa "ba fa abinda kake tunani bane ba, bani da lafiya dama a lokacin. To ni ina ma ruwa na da aurenka" yace "okay idan rashin lafiya ta saki amai ita ce kuma ta saka daga nayi miki sannu kika rufe ni da fada?" Nace "kaga nifa bana son ake juya min magana ta" yace "shikenan, an daina" muka cigaba da tafiya sannan yace "na bata labarin ki. I told her ina son aurenki first and she agreed" ya fada yana kallona, nayi kamar ban jishi ba ina jin bacin raina yana karuwa, amma sai ya sake cewa "tana sonki sosai. Tace zata zo Nigeria karshen week din nan purposely saboda ta ganki" na saka hannuna na toshe kunnuwa na ina jin zaman motar duk ya ishe ni. Nace "stop the car" yace "why?" Nace "ko dai ka daina wannan maganar ko kuma ka tsayar da motar nan in fita in karasa a kafa" sai ya kama dariya yace "an daina your highness".
Muna zuwa gida nayi masa godiya, kafin in bude kofar ya kira suna na "Diyam" na juyo ina kallonsa yace "Please in na kira ki ki dauka kinji. Say whatever you want to say in kin dauka din but please kar ki ƙi dauka".
Ranar na jima banyi bacci ba ina juyi. Feeling a familiar warmth a cikin zuriya ta wanda a da naje tunanin ko ba gushe yanzu baya nan. Zuciyata da ƙwaƙwalwa ta suka cigaba da battle dinsa ni kuma na zama confused dan bansan wanne daga cikin su zan bi ba. My heart was telling me in kira Sadauki a waya, in bude masa zuciyata in gaya masa irin zurfin da soyayyar sa tayi a ruhina, while my mind was asking me to hold on, reminding me cewa ba lallai ne in Sadauki ya samu abinda yake so ni kuma ya bani abinda nake so ba.
Washegari da safe bayan na dawo daga islamiyya ya kirani, daga alama a office yake "kinci abinci? Me kika ci?" Nace "kosai Asma'u ta soya mana" yace "yan gayu. Ni kuma kinga yunwa nake ji babu wanda ya damu yace Sadauki ga abinci" nace "Sadauki ko Mr Abatcha?" Yayi dariya yace "all the same" nace "ni banga same ba. Sadaukin dana sani is different from this rich Mr Abatcha" yace "really? To fada min menene bambancin" nace "da farko dai Sadauki baya taba yin abinda zai bata ran Ummah ko Baffa. Ita kuwa Ummah a cikin masu hakuri ma ita daban Allah yayi ta, bata taba fada ballantana har ta kasa yafewa wadanda suka bata mata. Na tabbatar kuma zata so ace yayanta, ni da kai, munyi koyi da ita, ko da bamu zama irin ta ba sai mu kwatanta ko yaya ne"
Ya jima shiru sannan yace "she was a good woman. The best. Bata bata wa kowa, in mutum ya bata mata ma sai tayi kamar bata gani ba duk kuwa da cewa ta gani ɗin. Har gida har daki za'a zo aci mutuncin ta ba tare data yi laifin komai ba and she will always looked at me and said "kar kayi magana, kar kace komai" and I will keep quiet. Amma ranar data mutu kinsan me Alhaji Babba yace? Cewa yayi ba za'a shigar da gawarta gidan mijinta ba as if she were some kind of trash" na goge hawayen daya taru a idona ina tuno wa da abinda ya faru a ranar data chanja gabaki dayan rayuwata.
Nace "sai menene kuma? Hakan ai bai rage ta da komai ba a wajen ubangijin ta, kuma muna saka mata ran cewa yanzu tana gurin da yafi gidan nan kyau da daraja. Kuma nasan da ace zata kalle ka a yanzu zata ce "kar kayi magana, kar kace komai" saboda tana son ka zama mai hakuri mai yafiya irin wanda Allah yake so, Annabi kuma yake alfahari dasu" yace "nasan abinda kike so ki ce, so kike yi kice in yafe musu gabaki dayan su, amma abinda kika manta shine, su fa basu yi nadama ba har yau. Yes, Alhaji ya bani hakuri ranar nan amma daga ni har ke har shi munsan cewa tuban muzuru yayi, na saka shine a corner babu yadda zaiyi shi yasa ya bani hakuri amma a lokacin da yana da dama da ina juya bayana zai daɓa min wuka"
Nace "na sani, amma wannan shi da ubangijin sa, ni da kai na damu ba dasu ba, zuciyarka nake fatan gyarawa and maybe a kokarin haka kaga tasu itama ta gyaru. Kasan abinda na fahimta? Babu abinda yafi saukarwa da mutum nadama irin idan wanda akayi wa sharri yayi sakayya da alkhairi. Take Inna as an example. Ba karamar nadama ce Inna tayi ba kuma a yanzu babu wanda take kaunar farantawa sama da kai" ya ajiye numfashi yace "kina so in yafe musu?" Nace "yes, amma badan ni zaka yafe ba. Dan Allah zaka yafe. Take your time and think over it. Kai da kanka zaka yanke shawarar yin abinda ya dace". Sai ya chanja maganar "yanzu ya za'ayi a kawo min kosan nan zuwa office?"
Kamar wasa few days bayan nan da daddare ina shirin kwanciya ya kira ni "me kike shirya wa bakuwar ki ne?" Nace "wacce bakuwar kuma?" Yace "kin manta nace akwai wadda zata zi gurinki?" Naji duk nishadin dana ke ji ya kau, nayi shiru yace "gobe zata sauka. Jirgin safe. Ni ina da meeting about that time. Ki shirya sai in turo miki da mota kije ki dauko ra a airport" nace "ni kuma? To ni da bansan ta ba ta yaya zan gane ta?" Yace "ki saka bakar doguwar riga ita kuma zata saka milk. You will know her when you see her" na hadiye abinda ya tsaya a kirjina nace "ya sunanta?" Yace "Murjanatu".
Not edited. Sorry for the typos.[3/4, 8:20 PM] +234 703 589 5826: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episodes Fifty Nine & Sixty : The Answers
Da safe na gayawa Inna sakon Sadauki. Tace "to fa! Sai kije ki dauko ta din. Anan zata sauka ne ko kuma a wani gurin daban?" Nace "nima ban sani ba inna" sai tace "to ki kira shi ki tambayeshi mana, in nan zata sauka ai gwara mu sani dan ayi mata abinci ko?" Na kasa kiransa saboda ji nayi duk haushinsa nake ji, sai na tura masa text "a nan zata sauka?" Sai da na fito daga wanka naga reply dinsa, "bakuwar ki ce ba tawa ba. Besides, ni gwauro ne bani da gurin da zan sauke ta".
Karfe goma da rabi yace min jirgin su zai sauka. Karfe goma driver yazo yana jirana. Asma'u tana school Subay'a ma haka, dan haka dole na shirya ni kadai na fita ina ta bace bacen rai. Sai 10:30 muka je airport din a raina ina cewa 'in sun sauka ma ta jira, da waye ya gayyace ta zuwa wajena?" Sai kuma nayi rashin sa'a jirginsu yayi delay dan haka sai da muka jira ma sannan suka sauka. Ina tsaye da bakar rigata da ya umarce ni in saka idona akan kofa ina ganin masu fitowa, mostly turawa ne maza da mata, sai few blacks suma kuma yawanci maza ne sai kuma wasu family da suka fito tare. Sannan na hango ta ta taho, tun daga nema na ganeta saboda kalar rigar jikinta. Waya a makale a kunnenta tana magana tana murmushin da yake bayyana hakoranta, naji kirjina ya buga da karfi a lokacin da zuciyata ta ayyana min wanda suke wayar dashi.
Ta fito waje sosai tana dan dube dube, idonta ya sauka a kaina sai naga ta sake fadada murmushin ta ta katse kiran sannan ta taho inda nake. I was suppose to like nima in tafi inda take sai mu hadu a hanya amma sai nayi tsayuwata pretending as if ban gane taba har ta karaso gaba na tana murmushi tace "Diyam?" Sai kuma na kirkiro murmushi nayi mata ina studying dinta. Baka ce, mai matsakaicin jiki kyakykyawar gaske and every part of her was screaming "I am rich" dan kallo daya zaka yi mata kasan cewa bata san wata kalma wai ita wahala ba. And something caught my attention, kalar skin dinta, manyan fararen idanuwanta, shape din fuskarta da kuma yanayin murmushin ta irin na Sadauki ne. Na tambayi kaina "are they related? Ko hadin gida za'ayi musu?"
Na kirkiro murmushi nace "Murjanatu?" Sai tayi dariya, ta saka phone dinta a cikin karamar jakar da take rataye a kafadarta sannan sai kawai naga ta rungume ni, ta sake ni tana kara kallona tace "wow, you are even more beautiful in person than yadda aka kwatanta min ke" na danyi dariya ina tunanin tsaurin ido na Sadauki da zai zauna yayi wa budurwarsa description dina. Nace "welcome to kano, fatan dai baki sha wahala sosai ba" ta yarfe hannu tace "zafi, haka kullum in muka je Maiduguri nake fama. Kamar ace an ciro mutum daga cikin freezer ne an saka shi a cikin oven. Na kan tambayi Adama, wai haka kaji sukeji in ana gasa su? irin frozen chicken din nan kuma a saka su a oven" nayi dariya a raina ina cewa wannan surutu ne da ita.
Drivern da muka zo dashi ya zo ya fara jan akwatin ta ni kuma sai na mika hannu da niyyar in karbi jakar hannunta amma sai taki bani tace "rufa min asiri, so kike yaya ya gasa ni kamar gyada?" Na maimaita kalmar yaya a raina. So they are related da gaske.
Muna tafiya veil din kanta ya fado kafadarta ya bayyana gyararren gashin kanta, but sai naga bata damu data gyara ba har sai da ni da kaina na gyara mata. She just thank me casually muka cigaba da tafiya.
A hanya muka dan taba hira, duk da dai da yawa daga hirar ita takeyi, a lokacin take gaya min cewa wannan ne zuwan ta kano na farko "in munzo Nigeria gida muke zuwa, Maiduguri, sai Abuja sometimes, mun dai taba zuwa Kaduna once" jin haka sai na fara yi mata bayanin guraren da muke wucewa a hanya, and she looked very interested.
Da muka je gida ina kallonta ina jiran inga tayi wa gidan mu wani kallo haka, ko kuma in an bata abinci inji tayi wani comment marar kyau amma sai naga sam babu abinda ya dame ta, she is the most down to earth person I have ever met. Ta zauna ta harde kafa tana ta cin tarin abincin da Inna ta jera mata tana kuma yiwa Inna hira. Sai tace "ina 'yar Asama? Kullum sai an bamu labarin Yar Asama da Diyam, Diyam this Diyam that. Ko kaya muka saka sai yace "ku kun mayar da kanku turawa, kuyi ta saka kananan kaya, why can't you dress like Diyam?" Ta fada tana kwaikwayon yadda Sadauki yake maganar sa.
Na kai mata kayanta dakina sannan na hada mata ruwan wanka a toilet nace tayi wanka ta huta. Bata tashi ba sai da Asma'u ta dawo daga school, ina jin Inna tana yi mata bayanin bakuwar da akayi sai kuwa naga ta tura baki tana kunkuni, Inna tayi mata warning kar ta sake tayi mata wata magana marar dadi.
Na shiga daki na tarar ta tashi daga bacci tana sallah, na zauna ina jira har ta idar sannan na tambayeta ko da akwai abinda take so. Kafin ta bani amsa Asma'u ta shigo tace "nazo gaishe da matar yayana" sai naga Murjanatu ta kalle ni sai ta cigaba da nineke abin sallah. Asma'u ta sake cewa "matar yaya barka da zuwa" sai Murjanatu ta kalle ni tace "ana miki magana" nace "ke take gaisarwa fa" sai tace "matar yaya naji tace, wanne yayan?" Na gyara zamana ina so inyi confirming suspicio dina Nace "Sadauki mana" ta dan bata fuska tace "waye Sadauki?" Na sunkuyar da kai nace "Aliyu, mu anan Sadauki muke ce masa" cikin mamaki tace "yaya Aliyu? Nice matar tasa kuma?" Nace "well, not legally yet, yace dai an bashi ke an kusa biki" sai ta zauna a bakin gado ta dafe kanta tana dariya tana kallona tace "tsokanar ki yake, he is my brother, my half brother, baban mu daya".
Har dare Murjanatu tana ta tsokana ta. Ina jinsu suna waya da Sadauki tana bashi labari suna dariya sai na harare ta daga ita har wayar tata, ina jinta ta gaya masa wai ina hararar ta sai naga ta saito ni da wayar kamar zata min hoto sai na rufe fuskata ita kuma tayi ta min hotuna a haka.
Sosai Murjanatu ta sake a gidan mu, nan take muka kulla kawance mai kyau a tsakanin mu. Tana ta yimin hirar gidan su, Papa, Mama, Adama, Sa'adatu, Yani. Amma ban taba yi mata tambaya a kansu ba, na saka a raina cewa Sadauki ne ya kamata ya bani labarin su. Na fahimci kuma tana tsoron Sadauki, duk da kuwa na kanga suna yin waya suyi hira amma kamar bata taba ketare maganar sa, bata yi masa musu, kuma tana bani girma sosai saboda shi.
Ranar nan bayan Murjanatu ta kwana uku da zuwa muna waya dashi tace gobe mu shirya gabaki daya zai zo mu fita yawo "mu zagaya da Fanna taga garin Kano" nace "Fanna?" Yace "yes, Murjanatu. We call her that a gida".
Ina gaya musu sai murna, nan da nan Asma'u ta fara making list na guraren da zamuje, aka fara ware kayan da za'a saka da irin kwalliyar da za'ayi. Murjanatu ta kalleni ina yi musu dariya tace "gobe sai na yi miki kwalliya. Asma'u zata rike min ke in kinki tsayawa".
Na dauka wasa suke sai washegarin na fito daga wanka sai gasu da make up kit, nace bana so amma haka suka tilasta min suka yi min kwalliya. Na dauko abaya ta na saka sai Murjanatu ta tsaya tana kallo na tace "wannan rigar is too loose, bai fitar da duk abinda ya kamata ya fitar ba bayan kuma akwai abin" sai ta dauko wani belt a kayanta ta daura min, na kalli kaina a mirror naga yadda hips dina suka fito sosai, ni kaina bansan ina dasu har haka ba, sai na girgiza kaina nace "bazan iya fita haka ba. Mutane zasu ke kallona fa" sai ta dan dake ni a kafada tace "dalla in sun kalle kin sai me kuma? Ke wallahi halin ku daya da yaya Aliyu yanzu zaku fara wa'azi" nayi dariya kawai amma na hakura ne kawai dan bana so in gwale ta amma ni nasan bazan iya sakewa ba sam.
Muna gamawa yazo, muka fita ni dai ina ta rabe rabe a bayansu. Muna fita muka hango motarsa duk da bama ganinsa but I felt his eyes on me sai na kara buya a bayan Murjanatu ina jin kamar zan gurde in fadi har muka karaso inda yake, Murjanatu ta bude min kofar gaba tace "entere" nayi murmushi na shiga ina jin still idanuwansa a kaina amma na kasa kallon side din da yake, sai naji yayi gyaran murya yace da Murjanatu "koma ciki ki samo mata hijab" sai ta kama bubbuga kafa a kasa kamar mai shirin kuka sai yayi mata tsawa "are you still there?" Da sauri ta koma cikin gida.
Nayi kasa da idona ina wasa da fingers dina, still feeling his eyes on me. Sai yace "kinyi kyau sosai Halima. But I can't let people see you like this. Ina da kishi da yawa I might end up fasa wa wani hanci akan hanya. In son samu nane ma bayan hijab har nikab zaki saka ki rufe fuskarki" tunda ya fara magana nake murmushi, ina jin feeling mai dadi a raina cewa nima ina da value. Sai na tuno da ranar da Saghir yake fito min da gashina "let's show them abinda matansu basu dashi".
Ta kawo min hijab din na saka ya saka hannu ya gyara min fuskar hijab din sannan yace "that's much better" sai kuma ya leka waje yace da Asma'u da Murjanatu "duk wadda bata shigo ba zamu tafi mu barta" da sauri suka bude baya suka shigo suna dariya.
Yawo mukayi sosai a garin kano, har gidan sarki sai da muka je muka shiga ta kofar gudu muka fito ta kofar arewa muka ga grand central mosque. Muka je gidan mesium muka je gidan makama da gidan mutan da. Muka hau badala, muka hau dutsen dala da gwauron dutse. Muka je har government house muka yi zagaye a ciki muka fito sannan muka tafi Abatcha Motors.
Murjanatu tace "yau dai finally zanga wannan precious Abatcha Motors din da yake rike yayana a Nigeria. Ko da yake ban sani ba ko ba shi kadai bane yake rike shi ba" ta fada tana mintsini na ta baya. Na juya na harare ta shi kuma yana mana dariya muka shiga building din.
Da yake weekend ne duk babu ma'aikata sai security kamar zasu ci mutum. Muna zuwa suka taso kamar zasu durkusa mana ni dai duk sai naji inajin nauyin su. Ya saka su bude ko'ina a gurin sannan yace dasu Murjanatu su zagaya duk inda suke so mu kuma sai ya saka aka kawo mana kujeru gaban wani fountain muka zauna.
Sannan ya dauko waya yayi kira, da alama abinci yayi mana order. Sai kuma yace min "ranar nan, you asked me some questions. Are you ready for the answers?" Na tuno tambayoyin da nayi masa farkon zuwa na office dinsa. Sai nace "eh. Ina son sani please". Yace "okay. Let's start from the beginning".
"Tun farko na san cewa Alhaji Bukar ne ya hada auren Ummah da mahaifina, amma bamu taba maganar dashi ba saboda ganin kamar umman bata so".
"Sunan mahaifina Alhaji Umar Mustapha Abatcha" nayi saurin cewa "Alhaji Umar Mustapha dai wanda muke jin labarin sa?" Ya gyada kai yace "shifa. Family din Mustapha Abatcha family ne da yayi suna ba'a Maiduguri ba kadai har ma da sauran Nigeriya. Suna da kudi tun asalinsu but kudin Umar Mustapha daban ne dana sauran. Tun yana saurayi ya mallaki kudin da shi kansa mahaifinsa a lokacin bashi da su. Harkar man fetur yakeyi yi, tun yana yin gidajen man fetur a gari gari har ta kai shi ga fara siyan rijiyoyin man fetur din gabaki ɗaya. Bashi da lokacin aure, dan haka ya jima baiyi ba, wannan yasa yan'uwansa, musamman da yake duk yan uba yake dasu dan shi kadai ne a gurin mahaifiyarsa, suka sako shi a gaba, suna saka ran in ya mutu suci kudi. A lokacin ne Alhaji Bukar, tsohon amininsa da sukayi secondary school tare yayi masa tayin auren bafulatanar yarinya Zainab. Shi kuma sai ya karba yana ganin tunda ba auren soyayya bane ba ba zata ke demanding time dinsa ba. Ta gaya masa labarin wanda take so aka raba su and he was sympathetic, yana nuna mata kulawa sosai ita kuma ta kwantar da hankalin ta sukayi zamansu lafiya a nan family house dinsu dake Maiduguri. A haka har ta samu ciki. A lokacin ne kuna ya fara business da Canada yana exporting crude oil daga Nigeria zuwa Canada wanda har yanzu shine sana'arsa, a yanzu yana daya daga cikin manyan dealers na crude oil a kasar Canada.
Tunda zainabu ta samu ciki shikenan kuma sai al'amurra suka cabe mata, gashi lokacin baya zama a kasar ita kuma taji duk duniya babu inda ta tsana irin gidan aurenta, babu wanda bata son gani kamar mijinta, babu kuma abinda take son rabuwa dashi irin cikin jikinta. Ta zama kamar mahaukaciya, sai ta fita da gudu sai an bita ana kamota ana dawo da ita gida, wani lokacin kuma sai ta zauna tayi ta dukan cikin wai sai ta kashe abinda yake ciki. Alhaji Umar yana zuwa ya ganta a wannan halin yasan asiri ne dan haka ya hada malamai aka zauna addu'a da magungunan karya sihiri akayi tayi mata, in abun ya lafa kwana biyu sai ya dawo. Ta sha wahala sosai. Ranar nan cikin dare suna bacci ta tashi tafita ko dan kwali babu ta kama doguwar katangar gidan da aka zagaye da waya da kwalabe amma a haka ta haura ta var gidan cikin jinin ciwuwwukan da taji, Alhaji Umar yana tashi yaga bata nan ya fito yayi ta nema babu wanda ya ganta sai ya dauki mota ya fita hankali a tashe. Cikin ikon Allah sai ya samo ta tana ta tafiya kamar zautacciya a kamata da kyar ya saka a mota daga nan sai airport. A can ya samu yayi mata adduoin ta dawo hankalinta ya sako ta a jirgi ta taho Kano ya kira Alhaji Bukar ya gaya masa, shi kuma sai ya koma ya nuna cewa bai same ta ba. Akayi ta nema har da cigiya a gidajen radio daga baya aka hakura.
Ita kuma ta dawo gurin yaya ladi ta zauna a kano. Har ta samu lafiya sosai aka tabbatar duk sihirin dake jikinta ya fita. Anan ta haife ni, Alhaji Umar yazo da kansa yayi min huduba da suna Aliyu "saboda ka zama jarumi ya sa na saka maka Aliyu" daga nan sai ya datse igiyar aurensa da zainabu, ya kuma roki Alhaji Bukar cewa ya nemo wannan wanda take so din yayi kokarin hada su aure, bayan an samo Baffa kuma Alhaji Umar da kansa ya bashi amana ta. "Dan Allah ka rike shi tamkar kai ka haife shi. Ɗa na kowa ne ai, wata kila ma kai zaiyiwa rana bani ba. Ni dai kawai ina son shi da mahaifiyarsa su kasance safe". Through all those years da nake gurin Baffa ashe duk Alhaji Umar yana biye da rayuwata, kuma yace ko da sau daya Baffa bai taba neman wani taimako daga gare shi ba.
To bayan rasuwar Umma da Baffa, bayan na koma gidan Alhaji Bukar, sai yake gaya min cewa ya gaya wa mahaifina zancen rasuwar, amma baya kasar a lokacin yasan da zaizo gaisuwa ma amma yace a gayamin in saka rana da kaina sanda na ke ganin am ready in gaya masa zaizo Nigeria sai mu hadu a Maiduguri. I fixed the date, sai muka tafi. But cikin rashin sa'a sai ya zamanto shi din wani abu yarike shi a can kasar da yake zaune, Canada, dan haka bai samu tahowa da wuri ba. Ban sami kowa a Maiduguri ba sai step grandmother dina a uncles dina. A lokacin ne kuma kika kirani da maganar za'a hada aurenki da Saghir. Nan take naso in yi musu dan karamin hauka a gidan na dage akan lallai sai an taho anzo Kano an nema min auren ki. Duk kallona suke kamar tababbe, irin suna ganin ban isa aure ba ai. Aka kira Papa aka gaya masa yace a rabu dani, wanne irin aure kuma? Sai na karbi wayar na gaya masa ko dai ya ajiye koma me takeyi yazo ya nema min aurenki ko kuma in kama gabana kuma babu wanda zai kuma jin labari na. Sai na gaya masa ko wa cece ke da dangantakar mu. Wannan ne ya ja hankalinsa. Sai ya bani hakuri akan cewa ba zai iya zuwa ba sai dai mu taho tare da Alhaji Babagana, daya daga cikin uncles dina. Muka taho din kuwa and you know what happened a gidan Alhaji Babba. Sanda muka fita I was beyond broken. Sai nace bazan koma Maiduguri ba, a gidan Alhaji Bukar zan zauna. Na zauna gidan Alhaji Bukar trying to find a solution amma na rasa ko daya, babu irin tunanin da banyi ba ciki kuwa har da in shirya mana visa tare zuwa Canada sai in dauke ki mu tafi can mu cigaba da rayuwar mu. But sai na tuno da kalaman Baffa da yake cewa ba yaso ya bani aurenki in dai babu amincewar Inna a ciki, nasan kuma yadda Inna bata sona in na dauke ki zata hada daga ni har ke ne ta tsine mana kuma ba zamu taba ganin dai dai ba a rayuwa. And I didn't want to put you through that. Sai na fara bincike ta karkashin kasa, Alhaji Babagana ya bani kudi sosai kafin ya koma Maiduguri dan haka bani da matsalar kudi, I followed Alhaji Babba, I watched him a lokacin da ya siyar da garejin Baffa, I also watched him lokacin da ya siyar da filina, I watched him lokacin daya siya wa dansa gida na bishi har gidan na gani. But bayan ya tafi sai na tsaya ina studying gidan, bai yi min ba kwata kwata. Unguwar was deserted dan haka babu security kenan, ko menene zai samu mutum a gidan babu wanda zai sani. Na haura na shiga har cikin gidan sai naga locks din kofofin ba masu kyau bane sosai sai naje na siyo wasu na dawo na cire wadancan na saka sababbin da kaina. But still ban gamsu ba dan nasan wannan mijin naki ba lallai yake zama a gida bake kadai zai ke bari so I hired a gate man for you. Malam Iliyasu" na kalle shi da sauri nace "Malam Iliyasu dai maigadin gidan Saghir?" Yace "yes. Tsohon soja ne yana gadi anan kusa da gidan Alhaji Bukar to sai wanda yake yi wa gadin ya rasu. So I took him zuwa unguwar na nuna masa gidan, mukayi sa'a Saghir din yazo sai na nuna masa shi nace yaje ya nuna masa cewa gurin zama yake nema, yana son zaiyi masa gadi free of charge abinda yake so kawai a bashi dakin mai gadi ya zauna anan. And he took the bait. Nace yace masa free ne dan na fahimci babu yaren da Saghir yake ganewa sosai irin na kudi. So, Malam iliyasu yayi muku gadi, ni nake biyansa duk wata, in return shi kuma yana supplying dina with information musamman abinda ya shafi lafiyar ki"
Ban bar kano ba sai da nayi attending daurin aurenku da Saghir. Daga nan airport na wuce straight na tafi Maiduguri ina zuwa kuma na tarar takarduna sun gama haduwa zuwa Canada dan haka kwana na daya a Maiduguri na tafi Ottawa, capital din Canada inda anan ne mahaifina yake zaune da iyalinsa.
I had been holding on, ina ta gayawa kaina cewa ba gaskiya bane ba, cewa ban rasa ki da gaske ba, but sai a jirgin nayi loosing din sauran hope dina. Gani nake yi na rabu dake kenan har abada and I couldn't picture my life without you, gani nake babu wani sauran meaning a rayuwata. Daga airport maimakon gida sai asibiti aka wuce dani, ji nake kamar tsaga kirjina akeyi da wuka ana yankar zuciyata sala sala. Mahaifin da naci burin gani sai a asibiti na ganshi and the first thing da ya fada min shine "are you this weak? Do you really want to die saboda mace?" Nace "she is not just any woman. She is mine and they took her from me" yace "to me zakayi akai? Zaka kwanta ka mutu ne while tana can tana sabuwar rayuwa da wani ko kuma zaka tashi ka rayu and show them that abinda sukayi is wrong?" And I decided, maybe gwara in rayu din, maybe one day I will be able to see you again, and get you justice from whoever wrong you.
But it was easier said than done. A watannin farko na aurenki I spent more time in hospital than at home. In ina gidan ma kuma ina daki a rufe. Bana kula kowa bana yi wa kowa magana. All I kept thinking about was you, you and you. Kullum tunani na a wanne hali kike ciki? Kinyi missing dina ko kuma kinyi accepting auren ki kin cigaba da rayuwarki da mijinki. Na kira Malam Iliyasu sai yake gaya min cewa Saghir yayi tafiya sai ke kadai a gidan tare da wata mata. And the agonizing months suka wuce, the most terrible times of my life. Ranar nan ina gida da rana kawai sai ga wayar Malam Iliyasu, nayi mamaki dan nasan cewa dare ne ku a wajenku na dauka sai naji cikin tashin hankali ya na gaya min wai baki da lafiya, shi yana ganin ma kamar kin mutu dan yaga maigidan ya dauko ki cikin jini ya saka ki a mota ya fita dake. Papa yana office dan haka message kawai na tura masa na dauki kudi da passport na tafi airport. Ban samu jirgi zuwa kano ba sai Abuja. Sai dana shiga Abuja sannan na samu wani zuwa kano ina shiga kano na kira Malam Iliyasu yace min shi bashi da wani labari tunda kuka fita shiru, sai na wuce gidan Alhaji Babba, na shiga har compound din gidan saboda yadda nake jin raina I was beyond caring akan me zai faru in aka ganni. Amma sai na tarar da gidan a hargitse, hankali na ya tashi and I asked wani mai kula da flowers sai yace min ai gobara ce Alhaji yayi duk shagunan sana'arsa sun kone kurmus babu abinda ya tsira dashi. Sai na tambayeshi game da matar Saghir, sai yace haihuwa ce kika yi amma yaran sun mutu, ke kuma an kaiki asibiti amma baisan wanne asibitin ba. Muna cikin magana Inna ta shigo gidan, ta wuce mu ba tare da ta ganni ba kuma na lura hankalinta a tashe yake, ta shiga cikin gidan ta sake fitowa sai na tura wanda muke tare nace yaje ya tambaye ta ya mai jiki? Anan naji sunan asibitin da kike, ana bukatar jini kuma ita ta rasa kowa duk gidan suna gurin Alhaji da yake asibiti shima. Sai na fice ba tare data ganni ba, na je asibitin da kike na nemo dakin da kike na shiga har ciki na ganki. You were sleeping, kamar allurar bacci aka yi miki. Kin kumbura sosai kinyi fari tas. I stayed a dakin for a while ina ganin kamar in na fita bazan dawo in tarar dake da rai ba but i knew dole inyi wani abu sai na tafi nace Inna ce ta turo ni in biya kudi kuma a dauki jini na, akwai wadda a gurin ta tambayeni ko nine mijinki and it pained me to say no. Aka gwada jini na and luckily sai yayi matching da naki"
Na katse shi "wait, wai kai ka bani jini ranar nan a asibiti?" Yayi murmushi "naki fadar kaina ne saboda nasan yadda Inna bata sona zata iya cewa ba za'a karba ba dan kar in shafa miki maita or something like that"
Kullum ina zuwa in duba ki. Na tabbatar kina samun sauki sosai, ranar nan saura kadan Mama ta ganni na buya duk I doubt ko ta ganni ma zata gane ni saboda ni kaina nasan I looked terrible. Ranar nan nazo sai akace min a ranar za'a sallame ki. Sai na tsaya and I saw you sanda kuka fito, ke da Inna da Saghir da wadansu mata. Kuka shiga motar Saghir ke da Inna kuka tafi and I kept following you a kafa sai danja ta tsayar daku har na karaso inda kuke and I did what I shouldn't have done, nayi miki magana"
Da sauri nace "I knew it. Nasan kai na gani amma inna tace wai aljanu ne suka bude min ido". Yayi murmushi. Ban kyauta ba na sani bai kamata inyi wa matar wani magana ba but I did it.
A ranar na koma Abuja daga nan kuma na koma Canada. A cikin jirgin nayi making decision cewa it is time to move on, tunda ke gashi har kin haihu, seven months after the wedding har kin haihu. Dan haka ina zuwa gida na samu Papa nace "am ready to move on yanzu" yace "good. Sai ka tafi makaranta kayi mechanical engineering dinka" sai nace "ina son karatu amma nafi son business, in yaso sai in hada da karatun da business din duka" yace zai saka ni a harkar Mai, but sai nace masa bana son aiki under him, I want something of my own, yadda zan making name for myself ba wai in jingina dashi ba. Na dauka zaiji babu dadi but sai naga yayi murna, yace wannan ya nuna masa how strong I am. Sai yayi signing check ya bani yace in cike kudin da nake ganin zasu ishe ni in kafa kaina. Na rubuta na mika masa sai ya yaga check din yace "wannan kudin da zan bawa wani ne in tazo neman taimako gurina. Ba kudin da zan bawa tilon dana ya kafa business ba. Sai ya sake signing wani ya miko min yace "multiply that by hundred, ka rubuta kaje ka karba. Allah yasa albarka a ciki".
That was the beginning of Abatcha Motors. I chose Kano saboda in samu damar keeping eyes on you. Cikin few months aka gama komai na fara hiring ma'aikata. A lokacin ne Malam iliyasu yake gaya min cewa kuna cikin matsalar kudi dan yaga aba ta fitar da kayan gidan ana siyarwa. So, I talked to someone who talked to someone har aka gayawa Alhaji Babba cewa ga sabon company nan ana daukan ma'aikata and luckily shi kuma Saghir ya dauko takardunsa ya fito neman aiki a lokacin sai aka turo min shi. A gurin interview din dana yi masa ne na tabbatar cewa bai sanni ba. I gave him a job. Amma ba job bane ba dan baya ma cikin list of staff dina. Salary dinsa daban nake bashi and his salary was just like me giving you money. Ina bashi kudin dana san ya isa ya kula dake.
Ina gab da komawa Canada ne sai yazo office dina yana ta complain wai matarsa ce zata haihu kuma doctors sunce ba zata iya haihuwa ba sai dai ayi mata aiki, gashi sunyo masa bill na kudi da yawa. I was scared kar yazo yaki biyan kudin ki zo ki samu matsala so I paid the money. Har na kara masa da kudin ragon suna da sauran hidima, ranar da za'ayi aikin na kwana ina miki addu'ar nasara, I wanted to go and see you but nasan hakan ba dai dai bane ba sai na hakura nace ya kirani in anyi and I asked him ya sakawa yarinyar Subay'a hoping hakan zai faranta miki ranki.
Daga nan na koma school. Carleton University of Canada. Anan nayi karatu tsahon shekaru biyar na fita da matsayin mechanical engineer. A wannan shekarun ne muka yi bonding sosai da yan uwana. My four sisters, Sa'adatu, Yani, Fanna da auta Adama, wadanda Papa ya bani task din koya musu hankali dan zaman kasar turawa ya saka duk sun koma suma kamar turawan. Yanayin shigarsu da yanayin mu'amalar su. I treated them with fire, but sometimes kuma sai inyi musu sanyi muyi ta wasa da dariya. Maman su kuma ta bani goyon baya sosai gurin koya musu hankali dan dama yanayin nasu duk yana damunta itama turancin ne yasa bata iya tsawatar musu.
All those years, nayi iyakacin kokari na dan ganin na cire ki a zuciya ta amma abin ya faskara. Nayi addu'a, nayi azumi nayi sadaka duk da wannan niyar, daga baya sai na saka a raina cewa wannan shine kaddara ta, zan rayu da sanki a zuciyata amma bazan rayu dake ba. Ban dauka cewa babu abinda ya ragu na sonki a zuciyata ba sai dana dawo, ranar da staff dina sukayi surprising dina da party, I saw you there, I tried pretending but then I saw him holding your hand and I couldn't take it, nasan in ban bar gurin ba zan iya rufe shi da duka dan haka na gudu"
Then one day ina dakina na hotel ana ruwan sama, har na fara shirin bacci sai ga wayar Malam Iliyasu yace min mamanki da kanwarki sunzo gidan Saghir ya kore su, ga dare gashi ana ruwa yana jin tsoron kar wani abu ya faru dasu. I left everything na hau mota na taho unguwar ina tafiya ina dubawa, hankalina a tashe ina tsoron kar in zama too late, sai gasu nan kuwa na gansu already har sun fada hannun mugaye. I couldn't imagine me zai faru da Asma'u idan da Allah bai sa Malam Iliyasu ya kirawo ni ba. That was when I decided to sue Alhaji Babba for garejin Baffa da filina. Tunda rashin mutumci suke ji I decided to show them rashin mutunci".
"Wannan shi yayi stating chain of events din da har suka kai ga rufe Saghir"
"Ina so ki fahimci cewa ban rufe Saghir dan in aure ki ba. Yes, I loved you, I love you and I will take your love with me to my grave but da ace zaman lafiya kuke yi da Saghir da babu abinda bazanyi ba dan ganin cewa zamanku ya dore a tare. I would have given everything in dai zakiyi farin ciki. But after na fahimci irin zaman da kuke yi, after what he said a gaba na ba tare dako digon nadama a muryarsa ba, after ke da kanki kin gaya min cewa ba kya son komawa gidansa then I won't let you. Yes, na barwa Saghir kudina intentionally saboda ina so ya dauka, saboda ina son in samu hujjar rufe shi yayi paying for abinda ya aikata. But I didn't force his hands. Shi yayi making decision din dauka da kansa. And that's what took him to prison bani ba".
"Yanzu na dawo gurinki Diyam. Ina neman aurenki bisa yardarki. Yes, nasan shekaru sunja ba lallai ne kina da feelings for me a yanzu ba. Amma ina so ki fada min abinda yake ranki, in kika karbi offer ta ta aure I will surely be the happiest man on earth, in kuma kika ki karba I will be heart broken maybe fiye ma da wancan karon but I will respect your wish. Bazan matsa miki ba ba kuma zan bari a matsa miki ba".
Ina jiran amsar ki.
[3/5, 10:12 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Sixty One: The Decision
Nayi kokarin dago kaina in kalleshi amma na kasa, tun daya fara magana nake hawayen tausayin rayuwata da tasa, wani gurin kuma inyi murmushi ina jin soyayyar sa tana kara ninkuwa a zuciyata. A karshe sai na samu kaina da tambayar kaina. Shin tsakanin ni da Sadauki waye yafi son dan'uwansa?
But can I tell him that? Anya zan iya gaya masa cewa babu abinda ya ragu a zuciyata dangane da soyayyar sa sai ma karuwa da yayi. Sai jin murtarsa nayi a hankali yace "should I start crying? Ko kuma in durkusa a kan guiwa ta?" Na yi murmushi ina karasa goge sauran hawayen ido na, na bude baki sai maganar ta makale, sai kawai nasa hannayena na rufe fuskata. Ya kama dariya yana cewa "you must be kidding me. Yanzu ni in zauna in gama bude miki zuciyata amma ke sai ki rufe fuska? In ba zaki gaya min bama at least let me look at your eyes in karanto amsa ta a can" na girgiza kaina nace "I can't" yace "wait, wai kunya ta kike ji?" Na bude fuskata nasan "mu fulani kunya ce damu" yayi dariya yace "maybe kin manta, nima bafulatani ne" nace "half ba. Mun bar musu kuma" yace "ni ban yarda ba, ko bani da jinin fulani my heart is fulani. Zuciya kuma itace rayuwa" nayi murmushi ina tuna ranar daya fara fada min nice zuciyarsa a Taura. Yace "I still need to hear it. I need to hear you say you love me. In kika fada then I have tukuici for you. Happiness insha Allah, till eternity. Through thick and thin".
Ina sunkuyar da kaina kasa, murmushi a lips dina, ruwan hawaye a idona, nace "kalmar love can't even begin to describe yadda nake jinka a zuciyata. Sometimes ina jin soyayyar ka kamar tayi waya a kirjina Kamar zuciyata ta cika har tana zuba da sonka. Da sonka aka haife ni Sadauki kuma nasan da shi zan koma fa mahalicci na. Bana jin kalmomi zasu iya bayyana soyayya ta gare ka dan duk abinda na fada ji nake yi kamar yayi kadan" sai yayi sauri yace "okay, will you marry me? Please? Sai a nuna min soyayyar a aikace ko zan fi fahimta sosai" sai nayi saurin jan hijab dina na rufe fuskata saboda nauyin maganar sa da naji. Ban san me yasa yanzu nake jin tsananin kunyar Sadauki ba bayan kuma sanda nake karama bana ji kamar haka. Ina jinsa ya sake jawo kujerar sa kusa dani yace "Please say something Diyam. Am dying here".
Hayaniyar su Asma'u ce tasa na bude fuskata amma ban kalli inda yake ba sai na juya inda na jiyo muryoyinsu. Murjanatu tazo da sauri tana cewa "yaya, wallahi naga irin motar da kayi min alkawari as my birthday gift. Please, please yaya ka bar min ita" sai ya dafe kansa da hannu daya yace "zaki saka min ciwon kai Fanna. Please go and make the noice somewhere else" sai na mike tsaye nace "yauwa an kawo abinci, dama yunwa nake ji".
An jera mana abinci iri iri akan shimfidar da akayi mana akan grass carpet din gurin. Muka tafi mu uku muka fara saving kan mu muna ci muna hirarrakin mu amma hankali na tana kansa yana zaune har yanzu a inda muka zauna da waya a hannunsa. Naji shigowar text cikin waya ta sai na duba naga "Please ki ajiye abincin nan kizo mu karasa maganar mu" sai na juya na kalle shi nace "me za'a zubo maka?" Ya bata rai yace "am not hungry".
Anan mukayi sallolin mu, Murjanatu tana ta yi masa nacin mota sai yace ta bari sai birthday din nata. "Ke ba iya motar ma kika yi ba. In na baki me zaki yi da ita?" Tace "koya min zakayi ai" yace "ni bani da lokacin koya miki mota akwai driving schools ki shiga ki koya a can". Sai da magrib ta gabato sannan muka tafi gida. A hanya Asma'u da Murjanatu ne kawai suke ta hirarrakin su amma ni da Sadauki kowa yana hira ne da zuciyarsa. Ni ina rarrashin tawa ne akan ta yarda da hukuncina a kan Sadauki, ina gaya mata cewa hakan shine abinda ya kamata gare ni, gare shi ga Subay'a, ga kuma zuriar dazamu haifa in muna da rabo. But my heart was weeping tana ganin banyi mata adalci ba. Tana gaya min hukuncina ni zaifi affecting ba wai shi wanda nayi wa ba.
Muna zuwa gida yayi packing a kofar gida su Asma'u sukayi masa sallama suka fita, ina hango Subay'a ta fito da gudu sai kuma ta tsaya tana kallonsa sai ta juya ta koma gida. Ya juyo yana kallona, nasan maganar da zaiyi min kuma kirjina bugawa yake da karfi ina tattaro courage din amsa masa, yace "baki bani amsa ta ba Diyam. In kin amince min ina son zanje gurin Kawu Isa" na juyo ina kallonsa, ina tunanin irin smartness ne Sadauki. Gurin Kawu Isa. Yasan a yanzu in ya nemi aurena a gurin Kawu Isa da gudu zai bashi ko dan ya kara bakantawa Alhaji Babba rai tunda har yanzu basu shirya ba. Sai kuma nayi tunanin hakan da Kawu Isa zaiyi shi zai kara rusa yar guntuwar zumuntar da take tsakanin uncles dina guda biyu. Sai nace "ina son aurenka Sadauki. Zan iya cewa shine greatest burina a yanzu. But, ina son muyi shi akan dai dai. Ina son muyi shi ta yadda nan gaba ba zamu zo muna nadama ba" yace "nadama kuma? Akan me zamuyi nadama?" Nace "have you thought about maganar da mukayi ranar nan? Akan forgiveness?" Sai ya dauke kansa gefe yana kallon waje nace "nima da akayi wa laifin nan na yafe musu. And I felt good lokacin da na yafe din ji nayi tamkar na dauke wani abu ne mai nauyi daga zuciyata. Wannan feeling din shi nake yi maka kwadayi. And Subay'a, ƴata ce at the same time ƴar Saghir ce duk yadda bana son Saghir bazan taba cewa ba shine ya haife ta ba. She will come in between us ko da munyi auren ma she will never forget cewa kai ka rufe mata mahaifinta and that may affect me nima a gurinta zata iya tunanin da sani na akayi komai" yace cikin dacin murya "I didn't lock up her father. Shi yayi signing takarda da hannunsa babu wanda ya tilasta masa" nace "but intentionally ka bar masa ai. Kuma kudin ka ne. You can just walk to the court a yanzu kace ka yafe masa a d that will be all" ya girgiza kansa yace "you seem to be forgetting something. Ba kudina ne kadai yake rike da your precious Saghir a prison ba. Ko drygs din ma ni na daka masa a dakin sa?" Naji zafin kalmar 'precious Saghir' din daya fada amma nasan kishi ne yake yi, sai nace "ba kai ka saka masa ba. Abokinsa ne yayi framing dinsa amma yayi framing dinsa ne saboda ya samu damar guduwa da kudinka da Saghir ya dauka, so it circles back to you. Please Sadauki, you have the power, you can set him free. Saghir yayi nadama. I saw it in his eyes sanda naje gurinsa a prison" yace "nadama? Baki san hausawa sunce kowa ya tuba dan yuwa babu lada ba? Ko zaiyi nadama Saghir ba yanzu ba" nace "Sadauki, Saghir fa....." Sai ya daga min hannu yace "stop, Please stop mentioning his name" sai na fahimci wani abu. Duk maganar da nake Sadauki ba jina yake yi ba, kishi ya rufe masa ido gani yake yi kamar saboda ina son Saghir ne nake so ya fito da shi. Ban kuma cewa komai ba sai na dauki purse dina na bude kofa na fita. Ina jin yana kirana amma ban juyo ba duk kuwa da cewa ji nake tamkar tawa zuciyar tafi tashi jin zafin hakan.
Ina shiga na tarar Asma'u da Murjanatu sun saka Inna a gaba suna ta bata labarin guraren da muka je. Sai na wuce su na shiga daki da niyyar rage marata a toilet sai kawai naga Subay'a a kwance a kan gado, na karasa kisa da ita sai naga kuka take yi a hankali hawayenta yana zuba kan katifa. Naji hankalina ya tashi sai na durkusa na jawo ta jikina nace "Subay'a? Kuka? Me ya faru?" Sai taki magana ta cigaba da kukanta ni kuma nayi ta rarrashinta har tayi shiru Sannan na sake tambayar ta sai tace "Daddy na nake son gani" sai nayi murmushi nace "dan kina son ganin Daddy sai kiyi kuka? Kiyi hakuri kinji? Da weekend zan kaiki ki ganshi" ta gyada kai kawai. Har zan tashi sai kuma na dawo na zauna nace "Subay'a, ranar nan da kika ce min kinji su Inna suna magana akan uncle Sadauki shi ya rufe Daddy ba haka bane ba, bakiji dai dai ba, uncle Sadauki shi yake kokarin fito da Daddy daga prison. Dazu ma maganar da muke yi dashi kenan" sai ta sake gyada kai kawai but she didn't looked convinced. Sai naji babu dadi saboda nayi mata karya amma kuma hakan ina ganin shine zai rage kiyayyar ta ga Sadauki. Ina kuma fatan komai ya dai-dai ta kafin tayi girman da zata gane komai.
Sai da nazo kwanciya naga text din Sadauki "am sorry Diyam, but I can't".
Sai nayi ta juya wayar a hannuna na rasa amsar da zan bashi. A karshe kawai na kasheta na ajiye. Cikin dare na tashi na gayawa Allah bukatu na. I want everything to turn out alright a gurin kowa da kowa. Ina kuma son zumuncin mu da yanuwan mu ya koma kamar yadda yake kafin a hada auren karfafa zumunci tsakani na da Saghir (ko auren bata zumunci ba), sai na roki Allah ya duba zuciyata yayi min zabi mafi alkhairi. Kafin safiya nayi making decision. Makaranta zan koma in cigaba da karatu.
Da safe na samu inna da bukata ta. "Inna maganar makarantar da nayi miki ranar nan. In kin amince ina so in nemi makarantar in sayi form in fara kafin shekara ta zagayo in tafi jami'a" ta tsaya rana kallona, daga dukkan alama maganata bata yi mata dadi ba amma sai tace "Allah yasa hakan shi yafi alkhairi" nace "ameen".
Da yamma sai ga Sadauki yazo gidan. Ya zauna kowa ya gaishe shi sai yake yiwa Murjanatu magana "Papa ya kira. Yace ki shirya ki koma saboda shirin tafiyarki school" ta bata rai, ya daga hannu yace "babu ruwana. Kinsan in baki tafi makaranta ba this year ba aure za'ayi miki" ta turo baki "Sa'adatu ma ba'ayi mata aure ba sai ni?" Yace "okay try me ki gani. Kin dauka wasa nake ko. Su Sa'adatu ai duk karatu suke yi ke kuma zaman banza kike yi zaman kula samari" sai tayi shiru fuskarta kamar an aiko mata mutuwa. Inna tana jin su tace "gwara kije karatun ki. Diyam ma tace makaranta zata koma" ya juyo yana kallona naki yarda mu hada ido sai yace "school? Very good. Ina zaki je?" Nace "computer school zan yi, kafin in samu admission. Tunda kaga yanzu an gama registration har an fara karatu sai next year kuma" ya daga kafada yace "ba duk universities bane suka rufe admission" nace "wacce ce ba'a rufe ba? Kasan kuma banyi jamb ba, so ko ba'a rufe ba bani da hope" yace a hankali "you can go to Oxford. Can nake nemawa Murjanatu, zaku iya tafiya tare" sai Murjanatu ta mike da sauri ta fara tsallen murna. "Haa, har naji dadi wallahi. Please Diyam say yes kinji? Please, please, please".
Sai nayi shiru ina kallon Sadauki wanda shima ni yake kallo, with so many unspoken words a cikin kallon namu ni ina jin haushin wato akan ya yafe wa Saghir ya gwammace ya tura ni wata uwa duniya karatu shi kuma yana jin haushin dan yaki yafewa Saghir na yi choosing in koma makaranta akan in aure shi.
Ba yawa, kuyi manage.[3/8, 12:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Sixty Two & Three : The Bet
Inna ce ta yi magana "au biye mata zakayi? Wani irin karatu zata tafi har wata kasa tayi? Ba gwara ayi auren ba in yaso in ma alhuda huda zata zama sai tayi ta zama ba?" Na kalleta nace "Akwai wanda yazo yace yana son aure na ne Inna?" Sai tayi min dakuwa tace "ku raba ke da yan gidan ku, yanzu zama kike so yayi tayi yana jiranki har ki gama wani karatu? Ko wanne karatu ne ai za'a iya yinsa a gidan miji" sai ya mike yana kallon Inna, ban kalle shi ba but I sensed cewa ransa a bace yake, yace "in karatu take so Inna ki barta tayi karatun ta, in zata je Oxford din ta fada and I will take her there. In kuma bata son ta ta fadi duk wadda take so in dai ina da dama zan kaita" sai ya juya ya fita.
Na mike da sauri nabi bayansa kamar wadda ake fusga ta zuwa gare shi na same shi a gareji nace "Aliyu" ya juyo da sauri yace "what?" Ina kallon yadda idonsa yayi ja nace "kar kayi fushi dani please" ya dawo gabana ya tsaya yace "nasan abinda kike trying to do, kinsan ina sonki da yawa ina son aurenki shi yasa kika yi shawarar tafiya karatu a tunanin ki hakan zai saka na fito miki da Saghir dinki, which I will never do. Na gaya miki kuma nace bazanyi ba, the more you keep mentioning him and showing that you care about him, the more zuciyata take gaya min in barshi yayi rotting there. In da kinsan kina son sa sanda na tambaye ki ko kina son komawa gidan sa sai ki gaya min, I would have supported you, kamar yadda a yanzu zanyi supporting dinki through karatun da kika ce zaki yi. You know why? Because I love you, and to me that's what true love is. In kana son mutum soyayya ta gaskiya shine you care about him and support him, you put his happiness a saman naka, you sacrifice everything just for him"
Naji bacin rai nace "how can you accuse me of that? I don't love Saghir kuma ka sani, ka sani kai nake so, kuma..." Yace "ni kike so? Na dai ji a baki kin fada kin ce kina sona. But am not so sure about that. Saboda duk abinda kike yi is total opposite of abinda na fahimta a matsayin so. Yes, kin soni a da na sani, but yanzu ban sani ba because a yanzu Saghir dinki shine a gabanki, dashi kadai kika damu" nace "ka daina cewa Saghir dina, ba nawa bane ba, bana son Saghir kuma ban taba son Saghir ba kuma bana jin zan taba sonsa tunda har na zauna dashi a matsayin mijina for years amma ban so shi ba. Kai na so, kai nake so kuma kai zan cigaba da so. Son da nake maka ne kuma ya saka nake so ka fito dashi din for your own good, for peace a cikin rayuwar da nake mana burin shinfida wa dani da kai har mutuwa, and that's my version of true love. In jawo ka kan gaskiya even if that will hurt you and me".
Sai naga idanunsa sunyi softening, yana girgiza kansa yace "I can't, na gaya miki I can't".
Raina a bace na koma cikin gida. Why is he so stubborn? Amma ina zuwa gida na tarar inna ta na tsarawa Murjanatu dalilin rigimar mu ni da Sadauki, sai ta juyo tana kallona tace "why are you so stubborn?" Nace "ni? Au nice ma mai taurin kan bashi ba?" Inna tace "ke ce fa. Kuma ke zakiyi wa kanki, dan ni bazan goyi bayan yayi ta zama yana jiranki ba har zuwa sanda zaku gama rigingimun ku wadanda babu rana. Ke fa kece baki da gaskiya, shi waye yace ya daukar masa kudi? Ita kuma Subay'a ai ba'a kanta aka fara rufe uba ba, wasu ma uban nasu mutuwa yake yi ya bar su kuma haka suke hakura. Wadansu ma basu san iyayen nasu ba uwa da uba gabaki daya. Kowa da kaddarar sa".
Ni dai bance mata komai ba saboda nasan ba fahimta ta zata yi ba. Sai naga ta saka mayafin ta tace mana ta tafi unguwa. Sai bayan ta tafi sai sannan na zauna nayi wa Murjanatu bayanin irin yadda Sadauki intentionally ya shirya wa Saghir trap din daya kai shi prison. Maimakon inga ta fahimce ni sai naga tayi dariya tace "kadan da aikin yaya na wallahi, Aliyu Haidar sadaukin sadaukai" na bude baki ina kallonta da mamaki "wato ke burge ki yayi ko?" Tace "waye yace ya daukar masa kudi? Ai kamar yadda ya fada ne shi ba shi yayi forcing hannunsa ba, ba kuma bindiga ya saka masa a kai ba, ya dai haka masa rami amma shi yayi deciding ya dauka dan haka shi ya jefa kansa cikin ramin".
Sai dare sannan Inna ta dawo daga unguwar tata. Lokacin kwanciya bacci yayi muka je muka kwanta ni da Murjanatu dan tun zuwanta na mayar da Subay'a dakin su Inna. Muna kwance Murjanatu tana ta chatting da sisters dinta da samarinta. Na dauki wayata ina ta jujjuyawa a hannu na. Sam bana jin dadin rabuwar da mukayi da Sadauki dazu, amma kuma banji dadin abinda ya gaya min ba akan wai ina son fito da Saghir ne saboda ina so sa. Zuciyata tana son in kira shi in ji muryarsa kuma in bashi hakuri amma kuma wani barin yana nuna min cewa shi me yasa ba zai kira ni ba? Na ajiye wayar nayi tsaki na kwanta na juya bayana, kusan awa daya ina kwance babu bacci babu dalilinsa, har Murjanatu ta gama yin wayoyinta da chatting dinta naji tayi addu'a ta kwanta. Sai na kuma dauko wayata na nemo number dinsa nayi dialing a raina ina cewa ba lallai ne ta shiga ba, amma sai ta shiga din, bugu dayakuma ya dauka sai kuma muka yi shiru gabaki daga muna sauraron numfashin juna.
Nace "I tot ba zaka dauka ba" yayi ajjiya zuciya yace "ni na isa. Bayan kin hana ni bacci" nace "ta yaya zan hana ka bacci ina miles away from you" yace "yes, miles away but so close" sai na lumshe ido na ina jin dadi a raina, naji duk bacin raina yana gushe wa zuciyata tayi fes. Nayi murmushi nace "ko?" Yace "ke ma kin sani ai, ko sai na maimaita miki. Haliman nan dai ita ce a kirjin Aliyu. Itace a jininsa ita ce a tsokar jikinsa. Bana jin akwai abinda zakiyi min in ki daukan wayarki" a hankali nace "kayi hakuri. Na bata maka rai na sani amma tawa zuciyar tafi bakanta a kan taka" yace "nima na bata miki ai. I shouldn't have said what I said about Saghir. Matsalata ina kishinki da yawa Diyam" nace "Amma ka yarda cewa bana sonsa kai nake so?" Yayi dariya yace "kara fada min inji?"
Mun jima muna hira har credit din yawa ta ya kare. Sai ya kira muka cigaba. Yana ta bani labarin rayuwar sa a Canada da University din da yayi. Sanyin da naji gari yayi yasa na fahimci dare ya ja sosai. Da kyar nayi masa sallama. "Zaka je office fa gobe" sannan dai yayi min sallama ya kashe. Ina yin addu'a ko minti daya ban kara ba nayi bacci.
Da safe Murjanatu ta tashi tana ta jera hamma. "An hana ni bacci jiya da I love You I Love You" na jefa mata pillow nace "zaki koma kwana a palo" tayi dariya tace "wai su yaya Aliyu an iya soyayya. Lallai in na koma gida akwai labari" sai na tambayeta in tana ganin Papa zai amince, ta bata rai tace "why not?" Nace "ni na taba aure. Aliyu kuma bai taba yi ba" tace "and so what?" Bazan iya miki describing Papa ba, but duk randa kuka hadu you will feel ashamed in kika tuna cewa kinyi min wannan tambayar".
Ranar ma inna ta sake fita unguwa. And I stated to suspect something. Har yamma bata dawo ba, a lokacin ne kuma Sadauki yazo. Na bude masa palon da yake a matsayin na baki muka zauna a ciki. Sai a lokacin na samu courage din yi masa tambayar da take raina nace "Sadauki baka gaya min labarin yaya ladi ba" yayi murmushi yace "sai yanzu kika tuna da ita? Na gaya mata ai nace kin manta da ita gashi kuma kin kwace mata miji" na zaro ido nace "tana raye? Tana ina? I tot ta rasu ne kuma bana son tuno maka da old painful memory, you are already bitter ba sai na kara maa wani ciwon ba" yace "tana nan. Tana damagun gurin wata cousin dinta. Bayan na tafi Canada ta tafi can ita kuma, kuma tunda na dawo taki dawowa gurina tana can sai dai inje in ganta, one day zamu je tare as a couple" na ture maganar gefe nace "baka kuma fada min ba, tuwo na na ranar nan, ka ci? Na jima ina son inji ko kaci ko baka ci ba" sai naga ya bata rai kamar ba zaiyi magana ba sannan yace "naci, sai da safe amma. I drove throughout the night"
Muna cikin hira aka kira shi da kamar ba zai dauka ba kuma sai ya dauka yana cewa "Inna ce" naji sun gaisa sai yace "ina gidan ma. Okay bara in fito sai inzo" na yi masa alamar tambaya da hannuna sai yace "Inna ce tace inje in same ta a gidan Kawu Isa" ina jin haka nasan magana tace, amma ya inna zata yi min haka bayan mun gama magana da ita na roke ta kar ta shiga maganar?
Sai dare inna ta dawo. Bata ce min komai ba sai ta shiga harkokin ta nima kuma ban tambaye ta ba amma sai na kira Sadauki na tambayeshi. Ya kukayi a gidan Kawu Isan?" Yace "babu komai. In tayi tsami zakiji ne ai" amma ni kuma ai bana son tayi tsamin. Nafi so in samu maganar a fresh dinta yadda zan iya tackling dinta. Amma Sadauki yaki gaya min.
Da weekend Murjanatu ta koma gida. Sai naji duk babu dadi saboda na saba da ita a kwanakin da tayi a tare damu. Bayan tafiyar Murjanatu kamar yadda nayi wa Subay'a alkawari na shirya ta muka tafi central prison gurin Saghir. Amma sai da muka samu ganin sa sannan nayi nadamar zuwa gurin cos it really broke my heart to see him a wannan condition din. Ya rame sosai fatarsa tayi baki ta lalace. Yayi datti. Uniform dinsa na prisoners wandon ya yage daga gwuiwa. Sai na tuno wancan Saghir din dan gayu mai iya daukar wanka da kwalliya yana kyalli kamar tarwada.
Ya dauki Subay'a ya daga ta sama ya rungume a jikinsa irin yadda yakeyi mata a gida. Sai ta kankame shi tana cewa "Daddy ka dawo gida gurin mu dan Allah" ya sauke ta yana lakuce mata hanci yace "Daddy zai dawo gida kinji princess, ki ringa yiwa Daddy addu'a kullum in kika yi sallah" sai ya juyo yana kallona yace "look at you. Kinyi wata kiba kamar wata Hajiya. Me Inna take baki kike ci ne?"
Sun jima suna hira shida yarsa, tana bashi labarin sabuwar makarantar ta da sababbin kawayenta. Sai da zamu taho yace "Diyam ya labarin alkawarin mu? Wannan alkawarin da kika yi min shi kadai ne yake keeping dina going a gurin nan. The hope that one day zan fita shi yasa har yanzu banyi loosing sanity dina ba".
Na dauka Subay'a zatayi kuka amma sai naga bata yi ba. Muna zuwa gida tace min "Daddy yace zaki saka uncle Sadauki ya fito dashi ko?" Nace "mommy da uncle Sadauki zasuyi iyakacin kokarin su, amma sai kinyi min alkawarin kin daina maganar, ba zaki kara yiwa kowa maganar ba kuma ba zaki kara yin kuka ba".
Da yammacin ranar nayi baki. Kawu Isa aunty Fatima da Mama. Ina ganinsu naji hankalina ya tashi dan nayi guessing maganar data kawo su. Basu jima da zama ba sai ga Sadauki shima yazo, naji haushinsa for not telling me abinda ake shiryawa. A gaishe su, shima ya gaishe su sannan sai na gaishe shi sama sama.
Kawu Isa ya fara magana. "Diyam innarki ta same ni da maganar ki da yaron nan. Tace yazo yana neman aurenki amma ke kin dauko wasu sharadai marasa tushe kin gindaya masa. Menene dalilinki nayin hakan?" Na dago kai ina son hada ido da Sadauki amma ya sunkuyar da kansa. Na fahimci lallai ni ake jira inyi magana amma kuma ban fahimci me ake so ince din ba. Shin wai su basa ganin abinda nake gani? Sai dai na fahimci akwai banbanci a tsakani na dasu, su basu san gadar zaren da Sadauki ya saka wa Saghir ba, su basu san maganar siyan gida da motar Saghir da Sadauki yayi dan ya taimaka wa Kabir wajen guduwa da kudin da Saghir ya sata ba. Nace "ni ba cewa nayi bazan aure shi ba Kawu. Ni cewa nayi ya yafewa Saghir kuma ya taimaka masa yayi clearing case din drugs dinsa" Mama ta kara da cewa "Sannan kuma ya bashi aiki ko?" Sadauki yayi sauri ya dago kai ya kalle ni, shi baisan da wannan part din ba ma. Nayi niyya ne sai Saghir ya fito sannan zan gabatar masa da wannan kudirin. Na dauke kaina daga kallonsa yayinda Kawu Isa ya rufe ni da fada ta inda yake shiga bata nan yake fita ba. Ni mamaki yake bani sosai musamman saboda nasan ba wai dan zumunci yake yin wannan abin ba, yana yi ne dan ya batawa Alhaji Babba rai kuma dan ya tabbatar da zaman Saghir a prison saboda abinda yayi wa suwaiba. Sai na tambayi kaina "anya kuwa akwai family din daya kai namu lalacewa?"
Sai daya gama yi min fadan sannan yace "kuma yaron nan yana iyakacin kokarin sa gurin ganin an fito da Saghir, jiya ma sai da muka je tare dashi har ofishin commissioner of police, kuma sun gaya mana suna iyakacin kokarin su akan maganar amma akwai rudani a cikin maganar sosai. Sunce zai fito amma sai ya dauki lokaci" Ya juya yana kallon Sadauki yace "shekara nawa ma suka ce mana?" Sadauki yayi gyaran murya yace "drug case is complicated. Kamar five years haka zuwa sama. Amma zai fito".
Mama tace "to alhamdulillah. Wanda ake tunanin ya tafi kenan kuma aka zo aka samu sassaucin da har za'a saka ran fitowarsa? Ai babu abinda zamuyi sai godiya ga Allah. Kai kuma Sadauki Allah ya biya ka" suka ce ameen. Aunty Fatima tace "ai wannan commissioner Ahmad Muhammad yana kokari sosai" suka ci-gaba da hirarrakin su yayinda ni kuma hankali na ya tafi wani gurin daban.
"Ahmad Muhammad" a ina nasan wannan sunan? Na dago kai muka hada ido da Sadauki sai na tuno inda nasan sunan and everything become clear to me. Ahmad Muhammad shine babban abokin Sadauki wanda suka taba zuwa min visiting makaranta tare, Ahmad Muhammad da yace bashi da buri irin yaga ya zama commissioner of police dan ya kama yan iskan gari ya rufe su a cell. That Ahmad Muhammad. Sai na tuno da kamun Saghir na farko, lokacin da aka je bail dinsa akace wai commissioner yace kar a bada bail dinsa. Sai nayi realising cewa Sadauki yana playing Kawu Isa ne, wato ya dauke shi ya kaishi office din abokin sa sun hadu sun ninke shi a bai bai da maganar cewa suna iyakacin kokarin su bayan kuma babu wani kokarin da suke yi. And I realized with a sinking feeling that Sadauki bashi da niyyar fito da Saghir.
"Ahmad Muhammad" na maimaita a fili. Duk suka juyo suna kallona sai muka hada ido da Sadauki a take kuma na fahimci cewa ya gane cewa na gane abokin sa ne. Nace "shekara biyar ko? Allah ya nuna mana shekara biyar din. Kawu kuyi hakuri kuyi min afuwa ku barni in tafi karatu, kafin shekara biyar din na dawo insha Allah. A lokacin in Saghir din ya fito sai ayi maganar auren".
Gaba-daya suka yo kaina da fada, har bama na jin abinda suke cewa ni kuwa na sunkuyar da kaina. Su basu san cewa decision din yafi yi min zafi a kansu ba amma dole ce ra saka ni. Sadauki bashi da niyyar fito Saghir bana jin kyma zai fito dashi ko da kuwa bayan na aure shi dinne. Option dina daya a lokacin shine inyi relying da son da yake min in hana shi cikar burinsa na aure na har sai ya warware daurin dayi da hannunsa.
Fada suke tayi min har saida Sadauki ya koma basu hakuri, inna kamar zata dake ni tana cewa "ya fasa auren naki to, aurensa zaiyi ya rabu dake. Yarinya sai shegen taurin kai" Aunty Fatima tace "ikon Allah, wai kamar ba Diyam din da take ta kuka an raba ta da Sadauki ba ce ba, yanzu kuma ita ake cewa ta auri Sadauki tana ki"
Ni kuma bana son in bayyana musu gaskiyar laifuffukan Sadauki saboda bana son in bata shi a wajensu. Gwara ni in dauki laifin shi kuma ya zauna fes.
Washegari da safe Sadauki ya kira ni a waya. Da kamar ba zan dauka ba kuma sai na dauka dan inji me zai ce min sai yace "Oxford din ce kenan" na danyi tunani. I need a break gaskiya, from Sadauki and from my family. Maybe in nayi nesa da Sadauki zaifi tabbatar wa cewa da gaske nake maybe rashina yayi breaking dinsa. Sadauki loves me, and that love shi nake relying on. Nace "Yes, Oxford din ce" ya danyi shiru sannan yace "na gaya miki tuntuni, I can't do abinda kike fada. Ki bar maganar Saghir, he deserves halin da yake ciki" nace "deserves? Sadauki Allah ne fa kadai yasan waye yayi deserving kaza wate baiyi ba, Allah ne kadai yake judging mutane akan laifuffukan su ba wai mu bil'adama masu tarin laifuffuka ba, Saghir yayi laifuffuka na sani, Alhaji Babba ma haka, amma Allah shi zaiyi judging dinsu bamu ba. Me yasa ba zamu zamanto masu yafiya ba saboda muma Allah ya yafe mana?" Sai yace "Allah yana judging wadansu ta hanyar wadansu. Wanne department din za'ayi miki applying for?" Nayi shiru. I had been thinking about that for years na kasa tsayar da shawara sai a ranar da Saghir ya bani takarda ta, a ranar da na samu freedom dina, a ranar ne na yanke shawarar abinda zan karanta. Law.
"Law" na fada masa. Yace "wow. But why law" nace "nayi tunani, kusan duk abinda ya same ni a rayuwa, tun daga auren dolen da akayi min har zamana a gidan sa da rabuwar mu ta farko da karbar Subay'a da yayi da farko. Duk wadannan sun faru ne saboda abu guda daya. Saboda rashin sanin yancin kaina da banyi ba. Alhaji Babba a both musulunci da kuma a dokar kasa bashi da right din yi min auren dole. Ko da mahaifin daya haife ni ne bashi da wannan right din sai dai zan iya yi masa biyayya dan in samu lada amma ina da option din cewa 'no'. Zaman da nayi a gidan Saghir, wahalhalun da nasha wadanda suka yi kokarin lalata both rayuwata ta duniya da kuma ta lahira duk sun faru ne a saboda bansan yancin kai na ba balle in nemi rabuwa da Saghir, both matsayi na na musulma da kuma matsayina na yar Nigeria sun bani yancin zabin wanda nake so in zauna dashi a matsayin mijina, na tuna rabuwar mu ta farko lokacin da ya dauke Subay'a ya tafi da ita da irin halin dana tsinci kaina a ciki saboda rashinta, shima wannan duk ya faru ne saboda bansan yancina ba, ba kuma ni da courage din fighting for my right dan shari'a ni ta bawa rikon ƴata, ko da mutuwa nayi rikon Subay'a baya hannun Saghir sai dai a bawa Inna, wannan itace Shari'a ta gaskiya. Amma rashin sanin yancin kai da matan hausawan mu suke fama dashi shi yasa ake tauye musu islamic and constitutional rights dinsu"
"Wannan shi yasa nayi deciding in karanta law, dan in samu damar tsayawa duk wata yarinyar da iyayenta ko marikanta zasu tursasa ta gurin auren wanda bata so, dan in tsayawa duk wata matar auren da take zaune da abusive husband kuma take son rabuwa dashi, dan in tsaya in tabbatar iyaye mata sun samu right dinsu da ubangiji da kansa ya basu na karbar rikon yayayensu a lokacin rabuwar aure ko kuma lokacin mutuwar miji. Wannan shine zai zama role dina a society"
Yace "Masha Allah. I am very proud of you Diyam. Kuma ki sani ina tare dake tun daga farko har karshe".
Na fahimci cewa Sadauki shi ko a jikinsa da nayi suspending auren mu nace sai na gama karatu. Shi dai kawai in dai Saghir zai cigaba da zama a prison shikenan. Da nayi kokarin yi masa complain cewa bama so nake tunda bai damu da aurena ko rashin aurena ba sai yace "you have no idea how much I want to marry you. This is just a phase we are going through. Am sure zaki chanja mind dinki along the way, in ma baki chanja ba I will wait har ki gama din ki dawo".
Wato ni ina depending on son da yake yi min cewa zai sauko ya chanja shawara ya fito da Saghir saboda muyi aure shi kuma yana depending on son da nakeyi masa yana saka ran zan sauko in bar maganar Saghir muyi aure. Ni dashi aga wanda zai fasa.
Ya gama nema mana admission, kuma mun samu successfully. Anan na fahimci cewa su ba yearly suke bada admission ba kamar in batches suke yi kuma mu namu session din zai fara ne January. Daga nan kuma sai ya shirya ya tafi yaje yayi one week a can ya dawo yace "all set, an samo muku apartment a kusa da school din an kuma ajiye muku mota saboda zirga-zirga. Abinda ya rage miki shine koyan driving" shi ya koya min, ya ajiye duk harkokinsa yake zuwa yana dauka na muna fita koyon mota kuma cikin kankanin lokaci na iya sosai. Zamu yi ta hirar mu amma da zarar nayi masa maganar Saghir zai dauke wuta in ba hakuri na bayar da kuma to sai dai mu dawo gida ranar ba za'ayi koyon motar ba.
Shi yayi min komai na harkar student's visa, muka je Abuja ni da shi da Asma'u. A embassy na UK na hadu da Judith itama tana neman student's visa, daga gaisawa naji yarinyar ta kwanta min muka yi ta hira har na fahimci scholarship ta samu daga program na African Initiative for Governance kuma session din karatun mu zai fara tare ne. Sai na roki Sadauki ya karbar mana visar tare da ita sannan kuma nace mata in mun hadu a can tazo mu zauna tare a apartment din mu.
Bayan everything ya zama set kuma sai na ji duk jikina yayi sanyi. Naji bana son rabuwa da gida, da Inna da Subay'a da Asma'u. Bana son rabuwa da Sadauki. Inna nasamu wadda har lokacin bata daina fushi dani ba akan kin auren Sadauki, nayi mata bayanin manufa ta akan hakan, na nuna mata nima bawai hakan naso ba sai dai hakan nake ganin shine dai dai, sai ta dan sauko, ta saka min albarka sannan tayi min nasiha a game da zaman da zanyi a can.
Ranar tafiya Sadauki ne yazo ya dauke ni muka tafi airport, su kuma yan rakiya ta suka biyo mu a mota daban. A hanya babu wanda yayi wa wani magana a cikin mu har muka je muka yi packing sai kuma muka ci gaba da zama a motar. Can ya juyo yana kallona yace "can you promise me something?" Nima ina kallonsa nace "what?" Sai kuma yayi shiru kamar ba zai yi magana ba sannan yace cikin rikakkiyar murya "zaki tafi jami'a, Oxford, akwai mutane da yawa a can, maza, and you are very beautiful am sure some of them will ....... God, bazan ma iya fadar kalmar ba" nayi murmushi nace "soyayya? I won't. Nayi maka alkawarin Halima ta Aliyu ce. In ba Aliyu ba kuma to babu wani namiji a gaba na" yayi dan murmushi yace "Allah yasa ki rike alkawarin nan. Dan ni yanzu am not sure about you anymore. Tsoro nake ji. Gani nake anya kuwa zan iya wannan zaman jiran kar inje fa zuciyata ta buga" sai nayi dariya nace "tsoro da girmanka" ya juyo and for the first time ya kama hannuna a cikin nasa ya rike yana kallona yace "let's play a little game da zai making everything easier for everyone. Let's make a bet" na girgiza kaina nace "ni kasan bana son wadannan games din naka fa" yayi dariya yace "tsoro kike ji? Tsoro kike ji kar kiyi failing?" Nace "kaima kasan ko sanda muke games din bana faduwa" yace "yes, kina winning, saboda ina barin ki kiyi winning dan kar kiyi kuka" sai muka fara musun cewa ba barina yake ba ni nake winning da kaina sai yace
"let's do this one mu gani. Yanzu in muka rabu a airport din nan in kika sauka a UK, through out your stay har zuwa sanda zakuyi hutu in dai har kika dauki wayarki kika kirani da kanki then nayi winning and I got to decide whether or not zan saki Saghir. In kuma baki kira ni ba har kukayi hutu kika zo gida then kinyi winning kuma zanyi duk abinda kika ce"
[3/10, 9:37 PM] +234 706 757 8042: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Epidode Sixty Four : A Little Advise
Na dan tsaya ina kallonsa ina assessing maganarsa, yana kallona with a broad smile a fuskarsa, na dauke kai ina lissafi, yes it will make everything easy amma anya zan iya kuwa? Not talking to him for months bayan a yanzu bana iya kwana daya ba tare dana yi magana dashi ba? But the result is really worth it, amma kuma in na fadi fa? In na kira shi fa?.
Na sake kallonsa naga har yanzu ni yake kallo yana murmushi with an unreadable expression a fuskarsa. Na girgiza kaina, it is too risky gaskiya. Sai ya langwabe kai gefe kamar abin tausayi, yana robbing palm dinsa a nawa yace "Please Diyam, shekara biyar tayi yawa. Ba kya tausayina wai ke?" Nayi saurin zare hannuna daga nasa ina yarfarwa kamar wadda wuta ta kona saboda wani blood rush da naji ya taso daga hannun nawa cikin seconds ya zagaye duk jikina. Cikin sarkewar murya nace "okay, okay. Na yarda. It is a deal" ya lumshe idonsa ya bude yana kallon yadda nake yarfe hannuna sai ya miko min nasa hannun yace "let's shake on that" na boye nawa hannun a cikin hijab dina nace "nace na yarda ai, no need to shake kuma" ya daga gira yace "tsoro kike ji?" Sai na dauki handbag dina nace masa "goodbye Aliyu" yayi murmushi yace "till we meet again Halima".
Na fita da sauri daga motar ina harhada hanya, but I felt as if gangar jikina ce ta fito ta bar zuciyata a cikin motar. Nayi kokarin calming down kafin in karasa inda Asma'u take jirana rike da sobbing Subay'a. Na durkusa na rungume ta ina jin tafiyar duk ta fita daga zuciyata, tausayinta naje ji sosai zata zauna without uwa da uba kuma bayan duk suna raye. Sai da muka je bakin departure hall sannan na juya na kalli inda motar Sadauki take, har yanzu yana nan a zaune, bana iya hangoshi amma ina hango duhunsa. A smiled at him, waved my hand sannan na shige.
Murjanatu ce ta tare ni a airport a Oxford. Muka tafi gida tare da ita, sannan washegari ita ta fara kaini school duk da dai itama bakuwar ce amma kasancewar ta fini wayewa da sanin kan al'amurra sai ya kasance ita tayi guiding dina har na kammala duk abinda ake bukata cikin nasara. I tot about Sadauki alot, tun a jirgi nake nadamar taking wannan bet din nasa but what is done has already been done, sai kuma naja damarar ganin cewa nayi winning dan mu samu nutsuwa gabaki daya ni dashi. Nasan shima burinsa shine yaci, kuma yana ganin kamar zaici din saboda yana ganin rauni na, and I decided to show him am strong. At first abin da wahala, musamman in naga kiransa ya shigo sai inji kamar in dauka amma nasan halinsa in na dauka zai iya cewa duk is part of the deal dan haka kiran nasa ma bana dauka. And it really hurts. Kullum babu fashi zai kira ni first thing in the morning, sannan ina dawowa daga school zai sake kira sai dai in naki dauka ya kira Murjanatu ya tambaye ta lafiyar mu ko kuma in muna bukatar wani abu. Kudi kuwa kamar ruwa haka ya sakar mana su, ina so in masa complain ince kudin sunyi yawa amma ina tsoron kar yace yayi winning.
Most of the times in suna waya da Murjanatu sai in yi ta straining kunnena wai dan in jiyo muryarsa, wani lokacin kuma shi da kansa zai ce ta saka a handsfree yayi ta yi min magana amma sai in ki yin maganar duk a tsoron kar yace yayi winning "please Diyam, please, please kiyi min magana" amma na daure na cije na cigaba da ignoring dinsa hoping wannan ta zama karshen wahala ta. Gani nake yi taimaka wa Saghir da nake so yayi shine zai gyara image dinsa a gurin family dina, kuma ina hopping hakan ya zamanto sanadiyyar daidaituwar al'amura a cikin family din. And Subay'a. Ina so in aure na ya kasance Sadauki Subay'a ta rike shi a matsayin uba ba wai matsayin enemy ba, wannan shine zai tabbatar da zaman lafiya a tsakani na da shi. Sannan taimaka Saghir zaiyi softening heart dinsa ya zamanto mai yafiya ga wanda ya munana masa sannan mai tausayi ga na kasa dashi, wannan kuma zai kara kusantashi da mahaliccin mu. Dan haka ni a ganina duk abinda nake yi ina yinsa ne domin Sadauki.
And then he tricked me into calling him and also found out about Bassam. And now he is angry. Nasan kishi yakeyi dan nasan yana da kishi sosai, ni kuma har cikin zuciyata ba wai ina kula Bassam bane saboda wata alaka ta soyayya, na fara kula shi saboda in goge haushina da yake ji, and we became friends, sai kuma na lura cewa shi Bassam din ya fara developing feelings for me wannan shi yasa nayi deciding in yanke alakar mu tun kafin abin yayi nisa but the decision was made late, dan already Sadauki yasan maganar Bassam ba kuma na son yazo yayi wani abinda ba dai dai ba. Ban kashe wata wutar ba bana son a kunno min wata.
Wannan ne yasa na yanke shawarar bawa Bassam labari ne dan ya fahimci dalilin yanke alaka ta dashi, dan yasan waye Sadauki da kuma alaka ta dashi, sannan kuma ina hoping labari na zai taimaka masa wajen solving family issue dinsa kuma maybe zai iya bani shawarar yadda zan bullowa crises din Sadauki da Saghir.
(Now, some people need to re-read episodes 1-10. Diyam is in love with wanda yake kiranta. Kuma ba labari take bawa Bassam ba, she is going over the story a kanta kafin ta bashi. Lol)
Bassam yace "ina jinki. Ina so inji labarin naki" ta dauke idonta daga kallon ruwan da yake tsiri a fountain, sai ta samu kanta da yin murmushi ganin yadda ya nutsu yana kallonta, tace "ba labari ne mai dadi sosai ba, and get your hanky ready cos you might cry at some point" yayi murmushi amma baice komai ba sai ta bashi labarin ta in summary, asalinta, soyayyar su da Sadauki, mutuwar su Baffa, aurenta da Saghir da yadda sukayi rayuwar auren tsahon shekaru, dawowar Sadauki cikin rayuwarta da kuma mutuwar aurenta ta farko data biyu. Ta bashi labarin a takaice but without missing all the main points da zasu saka ya gane manufarta sosai. Sai kuma ta gaya masa winning din da Sadauki yayi da kuma text din da yayi mata dazu akan Bassam din. Tana bashi labarin yana yi mata tambayoyi a gurin
Baiyi kukan ba kamar yadda ta tsokane shi da, amma idonsa yayi ja fuskarsa ta nuna bacin ransa akan abinda ya faru da ita, abinda bai taba tsammanin yana faruwa a kasar sa har a yanzu ba. Ya kuma jinjinawa jarumtarta dan he can't even imagine a girl of 14 years going through what she went through.
But his heart breaks daya fahimci karfin soyayyar da take tsakanin ta da Sadauki. Yes, da gaske ya fara jinta a zuciyarsa har yana hoping alakarsu will lead to something da zai fitar da khausar daga zuciyarsa. But daga labarin ta ya fahimci cewa cigaba da rike soyayyar ta a ransa will be a wrong move. She is already in love, deeply in love with someone else, just like Khausar.
Ta katse masa tunanin sa ta hanyar cewa "ina fatan ka fahimci duk abinda nake so ka fahimta" ya gyada kai yace "na gane, sosai. Kuma bana jin da akwai wata kalma da zan iya furta miki wadda zata nuna how sorry I am akan abinda kika yi passing through a rayuwarki. It was unfortunate. Kuma bazan iya misalta miki how happy and how important I feel right now da har kika zaunar dani kika bani wannan labarin. Naji dadi sosai, na karu sosai, nayi wa rayuwa kallon da ada ban taba yi mata irinsa ba" tace "thank you, thank you for understanding Bassam" ya sake murmushi yace "nine da godiya, you have no idea how this is going to change my life. My family, I have been taking them for granted duk da irin kauna da kulawar da suka yi kokarin gina min rayuwata a kai, a lokacin dani nayi watsi da supportive family dina nayi kokarin rusa zumuncin dake tsakanin mu saboda budurwar da bama ta sona a lokacin ke kuma kike against mutumin da ya ke miki soyayya ta gaskiya irin aliyu saboda family din da suka yi everything possible dan ganin sun rusa rayuwar ki. You truly are an angel. I now understand the real value of my family, kuma zanyi iyakacin kokari na inga na gyara kuskure na. And like you said, story dinki ya kara nuna min ma'anar true love, it is not feelings like I said. It is much more than that, true love means sacrifice. Kayi sacrificing happiness dinka dan wanda kake so yaji dadi, ka sa farin cikin wanda kake so a sama da naka. Na koyi wannan daga Aliyun ki kuma nima zanyi applying dinsa a case dina da khausar, ina sonta dan haka zan dora happiness dinta a saman nawa, happiness dinta kuma shine kasancewa tare da wanda take so. Am going to let them be, and hope to find my one true love nima watarana".
Tayi murmushi tana jin tausayinsa a ranta, tasan so tasan zafinsa dan haka tasan decision din nasa is not an easy one. But it is for the best.
Tayi ajjiyar zuciya tare da gyara zamanta tace "to saura ni. Ina so inji menene view dinka a game da sharadin dana kafawa Sadauki" ya girgiza kai yace "ni a fahimta ta, daga ke har Aliyu kuna kan gaskiyar kune, dan haka sharadin da kika kafa masa from your point of view dai dai ne. But where you are wrong is on the approach, hanyar da kike bi wajen ganin yayi abinda kike so ne ba tayi dai dai ba. Mu maza a yadda Allah ya halicce mu shine bama son ake directing din mu, do this, do that. Wannan hikima ce ta ubangiji sai ya saka mu as heads of the family mata kuma yace kuyi submitting to us. Amma inda hikimar take shine indai mace tabi namiji sau da kafa yi nayi bari na bari to zata juya shi ba tare da shi yasan tana juya shi din ba. Musamman ace idan yana sonta. Duk mijin da zaki ji ance mijin tace to shi bai san ma yana yin abinda mutane suke tsegumin ba. Irin son da Aliyu yake miki if you submit to him ba fito da Saghir kadai ba, in yana da dama zai iya fito da duk mutanen prison for you".
Ta jinjina maganar sa, Mama ta taba fada mata something similar to this, tace in ta nuna wa Sadauki soyayya zaiyi duk abinda tace but ita a ganinta ai tayi ta fada masa tana maimaita masa cewa tana sonsa kuma gashi nan har yanzu baiyi abinda take so din ba. Sai tace "yanzu me kake ganin ya kamata inyi?" Ya daga kafada yace "Marry him. Aurensa kawai zakiyi to make him feel loved, pamper him, take good care of him, ki tabbatar masa da cewa you are his and his alone kuma ki daina o da mentioning sunan Saghir then shi da kansa zai dubi yarinyar da take tsakani ya sake shi ba tare da kin furta hakan ba".
Ayi hakuri da wannan. A kuma yi hakuri da jina shiru kwana biyu, abubuwa ne suka cushe min but insha Allah in komai ya warware za'a cigaba da jina akan kari.
[3/12, 1:05 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Sixty Five: The Unbreakable Love
Ta tsaya tana kallon sa for some seconds. Sai kuma tayi murmushi very brightly sannan tayi dariya, shima dariyar yayi and they laughed together sannan tace "thank you Bassam. Nagode sosai" yace "no, thank you. Nine da godiya" wayarsa tayi kara ya dauko ta yana duba prayer alarm dinsa, lokacin magrib yayi. Suka mike a tare sannan suka jera suna tafiya suka bar garden din, taking their steps together kamar yadda suka shigo but unlike yadda suka shigo kowa rai a bace yanzu da zasu fita kowa a cikinsu murmushi yake yi. A bakin kofa ya tsaya yace "wait a minute, naji kince Umar Mustapha Abatcha, Umar Abatchan dana sani kike nufi ko kuma wani daban?" Tayi murmushi tace "shi din dai da ka sani, do you know him personally?" Ya girgiza kai yace "sunanshi dai na sani. But the son, ya taba zuwa gidan mu ones. Last year lokacin auren Ya Ameen Daddyn mu ya gayyaci father din sai bai samu damar zuwa ba but he sent the son to represent him. Ko gaisawa ba muyi ba amma zanso mu gaisa wata rana" Diyam tace "am sure shima zai so haduwa da kai" sai kuma tayi murmushi ta kara da "idan ya huce".
Yayi murmushi yana kallonta yace "goodbye Halima" tayi murmushi tace "see you soon Sadiq". Sai ta juya ta tafi shi kuma ya tsaya yana kallon bayanta, sai kuma yayi murmushi yana girgiza kansa yana tunanin irony din rayuwa.
Duk wanda ya shigo rayuwarka da akwai dalilin shigowarsa, some enter your life to teach you a lesson, some to take lessons from you, some enter to help you and some to accept a help from you. Duk wanda ka hadu dashi to ya shigo rayuwar ka ne for a reason. Da akwai point din da zaka hadu da mutum akwai kuma point din da zaka rabu dashi bawai lallai dan bakwason juna ba sai dan role dinku to each other ya kare. The only person that will stay from start to finish in your life is YOU and YOU are the only person responsible for your happiness.
People are not perfect, nobody is, so if you truly love a person you just have to accept him/her the way s/he is, accept both the good and the bad sides of them and together you can bring out the best in each other.
Ya juya da sauri ya koma cikin hotel din sannan ya hau zuwa dakinsa. Yana zuwa ya fara gabatar da sallah sannan ya jawo jakarsa ya fara zuba kayansa a ciki. It is time for a change a rayuwarsa, Nigeria zai tafi ya gyara rayuwarsa but before that he have to pay a visit to his Aunt first, yasan haduwarsu ba zatayi masa dadi ba but dole yayi clearing mess din da yayi creating da kansa.
Diyam tana zuwa gida itama sallar ta gabatar sannan ta tsaya a gaban mudubi tana practicing yadda zata fuskanci Sadauki gobe. Tasan akwai battle a tsakanin su dan ta tabbatar da daurarriyar fuska zai sauko daga jirgi. Sai ta fara making faces a mudubi tana zabar wacce zata fi melting frozen heart dinsa. Ta gwada fuskar tausayi, ta gwada fuskar shagwaba ta kuma gwada serious face amma duk sai taga basu yi mata ba. Ta binciko kaya tana zaben wadanda zata saka saka suma kuma taga duk basu yi mata ba, ta tuna ranar nan a Kano da Murjanatu tayi mata kwalliya ya yaba sosai dan haka gobe ma zata saka ta tayi mata. And she is going to wear dogon hijab kamar yadda yake so.
Ta ajiye kayan ta fita da sauri zuwa dakin Murjanatu, ta tarar da ita tana waya sai ta tsaya har ta gama sannan tace "Murjanatu Please zo ki taya ni zaben kayan da zan zaka" Murjanatu ta ajiye wayar tana kallonta, sai kuma tayi murmushi tace "kayan da zaki saka yaushe? Biki zaki je?" Diyam ta harare ta tace "kakan biki ba biki ba. Malama ni fa yayarki ce kuma am ordering you to do something for me" Murjanatu ta hade hannayenta tace "to babbar yaya tuba nake yi, tunda yaya na za'ayi wa kwalliya dole in tashi".
Haka sukayi spending the night preparing. Har takalmi da sarka sai da aka ware. Sannan suka yi plan din abincin da zasu dafa masa. Tuwo dai yafi so miyar yauki amma basu san inda zasu samo ingredients din ba dan haka Diyam ta yanke shawarar dafa masa farin couscous garnished with vegetables sannan kuma suyi masa farfesun kifi sai kuma suyi pepper meat. Drink tasan yana son kunun aya amma bata da aya dan haka zata yi masa banana smoothie.
Ta kira shi da niyyar tambayarsa sanda jirgin su zai sauka amma kamar yadda tayi tunani sai yaki picking, tayi masa text babu reply. Ta saka Murjanatu ta kira shi itama yaki dagawa duk sai taji babu dadi, shi wannan zuciyar tasa ce problem dinsa, yana da saurin hawa amma kuma yana da saurin saukowa dan haka ta shirya sauko dashi goben in yazo.
Ta lura Murjanatu duk ta daga hankalinta sai ta zaunar da ita tace "kar ki wani damu kanki da fushinsa, zai sauko na gaya miki ki barni da shi kawai" Murjanatu tace "baki san halinsa ba, zai iya raba ni da makarantar nan fa wallahi. Akwai abinda ya taba yi min a gida Canada akan wani saurayi na an gaya masa bad abubuwa akan sa sai yace min kar in kara kula shi ni kuma na cigaba da kulashin. Ashe yasa a saka masa ido a kaina sai gashi an tura masa da videon mu tare a gurin cin abinci. Ba wani abin muke ba kawai muna hirar mu muna dariya. Akan haka ya karbe wayata kuma yayi grounding dina a gida for three months ko kofar gida bana fita. Papa da Mama kuma suka biye masa yanzu ma kuma nasan duk abinda yace biye masa zasuyi" Diyam tace "ba zai ce komai ba, ki barni dashi".
Suka duba suka tabbatar suna da abubuwan da suke bukata, abinda basu da shi kuma sai sukayi order online da niyyar a kawo musu da sassafe. Sai kuma suka shiga website din airport suka duba flights schedules na gobe, anan suka ga time din da jirgi zai sauka from Nigeria. Sai yamma. Wannan yasa suka yi baccinsu sosai sannan suka tashi a tsakane suka yi komai tare har da Judith itama ta taya su, suka ci abincin su sannan suka yi wanka aka zauna kuma yin kwalliya a shafa wancan a goga wannan a ja wancan suna ta rigima har aka gama sannan aka yi dressing aka kuma bi da turare. Murjanatu ce ta dauko hijab da kanta ta bawa Diyam tace "gwara ki saka tun kafin yayi ball damu tun daga airport har gida".
Tare suka tafi airport din a mota, suka bar Judith a gida tana gyara musu gidan. A hanya duk sukayi shiru kowa tana lissafe lissafen ta sannan Diyam tace "Murjanatu a tunanin ki ta yaya Aliyu yasan ina kula Bassam?" Murjanatu ta daga kafada tace "yaya Aliyu ne fa, ya iya bincike ta karkashin kasa I guess wani ya saka ya saka masa ido akan mu. The guy might have saw you two together and reported to him" Diyam tayi shiru tana tunani, she will have to talk to him about that, hakan kamar rashin yarda ne. Murjanatu ta katse mata tunanin ta ta hanyar cewa "there is nothing between the two of you, is there?" Diyam ta harare ta tace "in kina son shi just say so, sai in hada ku" Murjanatu ta tabe baki tace "bai yi min ba, he is definitely not my type. Daga ganin sa nasan lady's man ne, Allah kadai yasan yawan yammatan sa" Diyam tayi dariya tace "wai dama kura tana iya cewa da kare maye? Ke ma Allah ne kadai yasan yawan samarinki" Murjanatu ta yi murmushi ta fara bata labarin new catch din da tayi a school last week.
Suna tsaye suna jira jirgin ya iso, Diyam tana ta jujjuya hannun ta feeling nervous dan bata san da wacce zai zo ba sannan kuma ga zuciyarta da take neman betraying dinta saboda dokan tuwa da tayi gurin son ganinsa after almost three months of not seeing him. And then suddenly sai idonta ya sauka a kansa, yayi kyau sosai fuskarsa tayi fes gashinsa na fulani da sajensa sun kwanta lufluf suna daukan ido. The freshness of his dark skin alone zai tabbatar maka da cewa he is taking good care of his body, yanayin takunsa kuma da posture dinsa sun nuna yawan ziyarar da yake kaiwa gym. Their eyes locked, and everything in her stopped except bugun zuciyarta da yayi doubling. He walk straight to gabanta ya tsaya one hand inside pocket, his expression unreadable yace "hello Madam".
Ta bude baki zatayi magana amma sai taji duk rehearsal din da tayi na abinda zata ce masa ya gudu ya barta. Yayi mata kwarjini da yawa, and the fact that he called her madam have added to that. Sai ya dauke idonsa daga kanta ya mayar da dubansa kan Murjanatu da take kusa da ita tana mishi murmushin dole, suna hada ido tace "sannu da zuwa yaya, ya flight din?" "Fine" yace mata in short sannan ya zagaye su yayi hanyar fita, Murjanatu taja hannun Diyam da sauri suka bishi a baya. Suna fita suka ga cab tayi packing a gabansa Murjanatu tayi saurin cewa "ga mota munzo da ita fa" ya juyo yana kallon Diyam yace "thank you" sai ya shige suka ja suka barsu a wajen.
Murjanatu ta juyo tana kallon Diyam tace "you kept quiet, me yasa zaki yi shiru?" Diyam tace "he called me Madam. Kin san kuwa yadda nake jin haushi in yace min Madam?" Murjanatu tayi dariya tace "to menene na jin haushi? In yace miki Madam sai kice masa Sir, ba shi kenan ba? Now we have to follow him kuma" suka shiga mota suka bi bayan cab din data dauke shi but sai suka ga sunyi wata hanyar daban ba hanyar gidan su ba, Diyam zata yi magana Murjanatu tace "gidan Papa zashi. Inda muke sauka in munzo gari" sai Diyam ta juya kan motar suka yi hanyar gidansu. Murjanatu tace "ba binsa zamuyi ba?" Diyam tace "we cooked for him, dole kuma yaci abincin da muka dafa".
Suna zuwa gidan Murjanatu ta shiga ta hado kan girkin da suka yi masa ta jera a babban basket sannan ta dawo motar suka kama hanyar wajen gari inda anan ne gidan yake. Suna packing Diyam ta tsaya tana kallon gidan a ranta tace "wow, da gaske dai Umar Mustapha Abatcha ne ya haifi Sadauki" ba mutane a gidan sai security daya bude musu gate suka shigo, amma komai na gidan tsaf yake daga alama ana zuwa aba gyaran gidan akan kari. Kofar da suka hango a bude suka dosa, suka shiga wani palo madaidaici Diyam tana iyakacin kokarinta na ganin bata yi kauyanci ba. A kan dining suka hango shi yana zaune yana kallon kofar da suka shigo. He kept his eyes on them har suka karaso Murjanatu ta ajiye basket din hannunta ta gaishe shi ya amsa tare da tambayarta karatu, sai kuma tace da Diyam bara taje ta dubo wani abu a cikin gidan.
Sai data fita sannan Diyam ta dauke idonta daga kansa ta sauke kan wata baturiya sanye da apron da hular cooks tana ta jera abinci akan dining table din gabansa. Diyam ta tako ta karaso gurin tana kallon baturiyar tace "thank you, I will take it from here" sai matar ta juya tana kallon Sadauki shi kuma ya yi mata alamar ta tafi da hannunsa sai ta juya ta bar gurin. Diyam tabi bayanta da kallo tana jin haushinta ba tare da matar tayi mata komai ba. Sai kuma ta fara tattare abincin kan table din tana ajiyewa gefe sannan ta dauko basket din da suka shigo dashi ta dora akan table din ta fito da abincin ciki ta jejjera sannan ta jawo kujera kusa dashi ta zauna. Tunda ta fara yayi folding hannayensa yake kallonta har ta gama ta zauna sannan ta jawo plate gabanta tace "banyi maka tuwon da kake so ba saboda bani da kayan hadi. Amma nayi maka something da nake tunanin zaka so" still idonsa akanta yace "how is he" ta gane maganar da yake amma sai ta cigaba da hada abincin ta, carelessly tace "how is who?" Sai ta debo abincin a spoon ta kawo bakinsa tace "ha" and she saw his lips curved in a smile amma sai ya juya fuskarsa gefe kar ta gani sai ta sake bin bakinsa da spoon din tace "ha muga ni" sai ya langwabar da kai sannan a hankali ya bude mata bakin ta saka masa abincin a ciki sai ta zauna tana kallon sa with wide opened eyes shi kuma yana taunawa a hankali sannan tace "please tell me yayi dadi. I spent hours ina shirya maka abincin nan kamar yadda nayi spending hour ina yi maka kwalliya amma gashi nan ko yaba wa ba kayi ba" ta karashe maganar kamar zata yi kuka.
A hankali yace "waye yace miki ban yaba ba?" Ta turo baki tace "you called me Madam, kuma kaki shiga mota ta" ya danyi murmushin daya tsaya a iyakacin idonsa yace "to ba Madam din bace ba ke?" Tace "I am not Madam, in ka kara gaya min kuma nima Sir zan ke ce maka" and his smile widen to his lips. Ta sake dauko wata lomar ta kuma cewa "ha" ya bude ta saka masa yana ci ya kuma cewa "how is he?" Ta gyara fuskarta zuwa serious one tace "kana magana akan Bassam ko?" Ya daga kafada yace "bansan sunansa ba and I don't want to know" tace "he was fine as of yesterday, bansan ya yake yau ba. Kamar yadda bansan me yasa kake wani tunani akan sa ba. He is just my friend, department din mu daya muna lectures tare and he is a Nigerian" ya bata fuska yace "shi yasa kuke cin abinci tare?"
Ta saka masa wata lomar a baki sannan tace "and how do you know that? Wani ka saka yake spying on me? Baka yarda dani ba?" Yace "babu wanda na saka yayi spying on you. Akwai mutumin da muka yi harkar admission da registration dinku tare. He saw your pictures then. A lokacin kuma na gaya masa ke matata ce then he saw you with that boy and thought ya kamata in sani. I told him bake bace ba cos I thought you would never do it sai ya tura min da picture of you two together" ta ajiye spoon din hannunta tana kallon yadda fuskarsa take nuna bacin rai, yace "do you like him?" Ta dafe kanta tace "I just told you, Bassam is my friend. Na bashi labarin ka ma na gaya masa zaka zo yau kuma har cewa yayi zai so ku hadu. There is nothing there. Please stop looking for something that isn't there" she saw him relax a little yana kallonta yace "he is handsome" tace "really? Ni ban gani ba. He may be one of the thousands of stars in the sky amma ni duk bana ganinsu, only one star shines brightly a ido na, you. Kai kadai nake gani a matsayin mai kyau sauran duk dusudusu nake ganin su. You are the only star in my sky".
And he smiled. This time genuine smile yayi mata ya lumshe idonsa ya bude yace "I always remember that night duk sanda naga starry sky" ta sunkuyar da kanta kasa tace "me too".
Sai ya saka dogayen fingers dinsa guda biyu ya dago fuskarta yana kallon cikin idonta yace "feed me" ta hadiye wani abu a makogwaron ta amma taji yaki tafiya, sai ta yi sauri ta dauke idonta daga cikin nasa ta dauki spoon with shaking hand ta cigaba da bashi abinci. Bai kuma magana ba sai ido daya tsare ta dasu har sai da ta tabbatar ya koshi sannan ta bashi drink ya sha sai kuma yace "thank you, this is the best food I have tasted for a while. Ko kuma yadda aka bani abincin ne ya saka naji yafi kowanne dadi?"
Sai kuma ta danji kunya ta rufe fuskarta da bakin hijab dinta, suddenly sai taji babu abinda take so irin ta kuma jin wannan kalmar daga bakinsa but as her husband yadda zata ji dadi fiye da na yanzu kuma ta samu lada mai yawa.
Sai ta zame daga kujerar da take zaune ta durkusa a gabansa tana kallon yadda yake kallonta da mamaki tace "Aliyu Umar Abatcha. Will you do me the honor of marrying me?"
Please, duk wanda Allah ya bawa ikon karanta wannan page din ina barar a karanta min surorin Falaq da Nas. Da niyyar Allah ya gina mana katangar tsari tsakanin mu da duk wanda yake neman mu da sharri, Allah kuma ya tabbatar mana da alkhairi tsakanin mu da duk mai neman mu da alkhairi. Allah yayi mana jagora kar ya barmu da iyawar mu dan mu ba zamu iya ba. Allah ya tabbatar mana da alkhairi a kasar mu baki daya.
Nagode
[3/14, 10:49 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Sixty Six: The Unbreakable Love 2
Naga adduoin ku, nagode sosai.
For two seconds ya zauna yana kallonta da tsantsar mamaki a fuskarsa sai kuma yayi sauri ya mike tsaye ya kamo hannayenta duk biyun ya mikar da ita tsaye yana kallonta tana murmushin ganin duk yadda yabi ya rude sai yace cikin saurin murya "No! No".
Ta bude ido da mamaki tace "no?" Sai ya saki hannunta da sauri ya dafe kansa yace "ba wannan no din ba, I mean no karki durkusa please, karki bata kayanki" ya fada yana ciwo hanky da sauri ya kama goge mata hijab dinta, sai daya dago sannan ta daga gira tace "so? Yes ne ko No?" Maimakon ya bata amsa sai ya dora goshinsa a kafadarta, tana jin yadda ya sauke wata nannauyar ajjiyar zuciya wadda tasa hawaye ya gangaro daga idon Diyam sannan yace can kasan makoshinsa "Yes Diyam. Of cause I will marry you. You have no idea how much I want to marry you"
Murjanatu ta bude kofa ta shigo, sai kuma ta tsaya tana kallon su sannan tace "wrong room. Ba nan zan shigo ba" sai ta kalli kofa tace "Na'am!" Ta juyo tace "they are calling me so I gotta go" sai ta juya da sauri ta fita. Diyam tayi dariya tana share kwallar idonta tace "she is funny. Babu wanda yake kiranta" ya danyi dariyar da Diyam taji vibration dinta a kirjinta yace "kika sani ko aljanun gidan ne suke kiranta?"
Ta dan matsa baya forcing him to raise his head from her shoulder. Sai ya kalle ta da idon da suka fara chanja color yace "yaushe kika chanja shawara kuma? What about Saghir? Kin fasa fitar dashi din?" Ta zauna a kujera tayi dagumi but fuskarta da murmushi tace "you won the bet, I can't continue to deny myself freedom. Nayi kokari ai ko?" Ta fada da sanyin murya. Ya zauna opposite dinta yace "Subay'a fa?" Tace "in muka yi aure Subay'a ta zama yarka. And I trust you will do everything in your power to make your daughter happy" ya gyada kai yace "you bet. She is going to be the happiest girl ever".
Matar dazu ce ta shigo ta fara gyaran dining table sannan ta zo gurin su tana tambayar Sadauki in akwai abinda yake bukata in babu tana son tafiya. Ya sallameta ta tafi ya juyo yana kallon Diyam da take bin bayan matar da harara yayi murmushi yace "what?" Tace "fire her. Ita da wannan secretary din taka ta Kano" ya bude ido da mamaki yace "why?" Ta turo baki "ni bana son su" yayi dariya yana shafa kansa yace "and you accuse me of being heartless" ta bude hannu tace "sai ka basu wani aikin ai. Kai kuma ka samu maza suke yi maka irin wadannan aiyukan" yayi tagumi da hannu daya yana kallonta yace "yarinyar nan anya kuwa Baffa bada A'isha yayi miki huduba ba? Kishinki yayi yawa. Yanzu suna min aiki kince ba kya so, so tell me idan kuma kika gan mu tare muna cin abinci a cafeteria mai zaki yi? Hmm?" Ta gane inda ya dosa sai tayi saurin cewa "kayi hakuri, an gama ba za'a kuma sakewa ba" bai ce komai ba sai kallonta da yake tayi fuskarsa da murmushi. Ta jawo fuskar hijab dinta ta rufe fuskarta tace "ni kunya kake saka ni in kana kallona" sai ya koma ya jingina a jikin kujerar yace "kinsan tunanin me nake yi?" Ta bude fuskar ta tace "no" yace "tunani nake yi in koma airport a yau in koma Nigeria, gobe inga Kawu Isa jibi a daura mana aure in dawo gurin amaryata a jibin" tayi saurin mayar da fuskarta ta rufe tace "kai dan Allah. Ka dai bani lokaci in shirya dai ko?" Yace "wacce shiryawa kuma? Nasan a gida zasu ce zasu shirya wani abu amma koma menene sai dai su jira sai bayan na tare da amarya ta" sai ta mike da sauri tayi hanyar waje tana hada hanya tace "sai dai ka tare kai kadai" ya biyo bayanta yana cewa "dama ai ni kadai nake tarewa ta kullum on my empty cold bed, it is about time I get some warmth" ta karasa kofar da sauri tana hoping ba irin ta office dinsa bace ba. Tana murdawa taji ta bude ta fita tana raba idon inda zata hango Murjanatu, sai gashi nan ya fito shima ya rufe kofar ya jingina da jikin kofar ya harde hannayensa da kafafuwansa yace "run run little girl. Duk inda zaki je you will come back here" ya fada yana nuna kirjinsa yace "cos that's where you belong. A heart belongs to the chest".
Ta juya suka hada ido, feeling like yau ta fara ganin sa. She couldn't help but look at chest din daya nuna, very broad and very strong, sai taji babu abinda take so irin ta jita a gurin feeling the warmth and the strength that she so much miss. Ta hadiye wani abu tare da saurin girgiza kanta a kokarin ta na goge image din daga kanta tace masa "uhmmm. Lokacin Sallah. Murjanatu" yayi mata murmushin gefen baki sai ya nuna mata wata kofa da hannu" ta juya da sauri ta tafi can. Sai data bude kofar ta shiga sannan ta rufo kofar ta jingina da jikinta ta yi ajjiyar zuciya. Sai kuma tayi murmushi tana girgiza kanta.
Daga gefenta taji ance "hmmm. Wato da can anaso ana kaiwa kasuwa akeyi ko?" Ta juyo ta harari Murjanatu tace "ke nifa yayarki ce, bana son rashin kunya". Anan tare sukayi sallah tare sannan suka fita Murjanatu tana zagayawa da ita gidan Diyam tana ta kashe kwarkwatar idonta. Komai na gidan abin kallo ne, exact lissafin da Diyam take yi na abinda ake cewa aljannar duniya. Suna cikin zagayen suka hadu dashi, yace da Murjanatu "thank you Fanna, zaki iya komawa daki" ta turo baki tana buga kafa amma yana yi mata wani kallo ta juya ta koma. Diyam tace "kai kuwa ka barta mana mu karasa" yace "a gabanta zanyi hira dake? Kina sone ma ta raina ni kenan" suka jera suka cigaba da tafiya tare, but ba kallon gida sukeyi ba hirar su kawai suke yi suna jin dadin iskar da take kadasu.
Ta rungume hannunta tana jin sanyi amma bata son nunawa dan tana jin dadin hirar da yake yi mata, sai ya cire top dinsa ya saka mata, ya cigaba da bata labarin irin yadda ya yi ta kokarin ganin ta kira shi dan yayi wining amma taki. Yace "har halucination fa nake yi. In wani ya kira ni sai inga kamar ke. It was hectic. I almost lost it" tayi murmushi tace "kasan me? Wani lokacin sawa nake Murjanatu ta saka min kai a handsfree" ta fada tana rufe fuskarta, yace "laaa ila, that was cheating" ta bude fuskarta tana hararar sa tace "har zaka yi maganar cheating?" Yayi dariya yace "bature yace 'nothing is fair in love and war".
A lokacin suka kai karshen gidan sai suka juyo suna retracing steps dinsu sai yace "sanda zaku taho Papa cewa yayi ku zauna a nan gidan, but sai na nuna masa cewa yayi nisa zaku ke shan wahalar transportation. But ni personally ba wai dan haka na samo muku wancan gidan ba, ni a ganina you are my responsibility kuma nan ba gida na bane ba bana son matar gidan ko sauran siblings dina suzo gidan suyi miki wani kallo, gwara can nawa ne babu mai daga miki kai" tayi murmushi tace "bansan sauran ba amma Murjanatu tana da kirki sosai" ya gyada kai yace "tana da kirki, suma duk basu da problem amma hausawa sunce maganin kar ayi kar a fara".
Sai da sukayi sallar isha sannan suka bar gidan. Zuciyoyin su tas kamar takarda. Suna zuwa gida sukayi wanka suka yi shirin kwanciya saboda duk sun gaji. Diyam ta kwanta tana bitar maganganun su da Sadauki. Yes, ta karbi shawarar Bassam, Sadauki baya son tana maganar Saghir dan haka ta daina amma bawai ta bar maganar bane ba, zata jira taga if he will come around and do the right thing da kansa.
Watarta tayi kara ta dauka tana murmushi. Bai gaji da hirar ba kenan. Ta dauka da sallama yace "so nake in taho nan kin yarda?" Tace "nan kuma? Me zaka yi anan din?" Yace "hira zan yi miki kadai" tace "to kayi min a wayar mana, ai ina jinka a haka" yace "nafi son inke ganin ki as ina miki maganar. Nafi son in yi miki joke kiyi min murmushi in gani. Nafi son in tsokane ki ki harare ni in gani. Nafi son in fada miki sweet sweet words inga kin rufe fuskarki kina jin kunyata" sai taja abin rufa ta rufe fuskarta. Tace "ni dai kar kazo zuwa zakayi kayi ta sakani jin kunya" sai kuma tace "amma bada gaske kake ba zancen daurin aure jibi ba ko?" Yace "in da zan samu yadda nake so da ko gobe nema ina so. But nasan ba zan samu ba, Papa zai ce abokansa da sauran mutanen sa, Mama zata ce zasuyi biki, and you, I want you to have all the wedding things da baki samu ba ada. So, I will wait. Kinsan ni am a patient bird. Yanzu ki gaya min duk abubuwan da kike so for the wedding" ta lumshe ido tana tunanin childhood dreams dinta, but those are only dreams kuma yanzu sun zama past, dan haka tace "ni bana son komai fa. Sai dai ko in kai kana son wani abu" yace "ni ke nake so. I want only you, and that's the only thing that matters" taji ta tamkar tana narkewa tana shigewa cikin katifar da take kwance. Is it possible to love someone this much?
Suka cigaba da hirarsu mai ratsa zuciya, tana bashi labarin makaranta da yadda tayi adapting, shima yana bata labarin lokacin da yake tasa makarantar. She told him about Bassam abinda ya hada su da yadda rayuwar su ta kasance tare but sai taki gaya masa cewa Bassam ya fara sonta. She told him yace ya taba ganinsa yaje daurin auren brother dinsa. Sai a lokacin yace "Abuja? Last year you said?" Tace "eh" ya danyi tunani yace "naje daurin auren gidan sarki. Maybe can yake". Sai da yaji alamar ta fara jin bacci sannan yace "kiyi addu'a ki rufe idonki. I will talk to you sai kinyi bacci saboda ina son kiyi mafarki na"
Took my hand, Touched my heart, Held me close. You were always there, By my side. Night and day, Through it all. Baby, come what may.
Swept away on a wave of emotion, Oh, we're caught in the eye of the storm. And whenever you smile, I can hardly believe that you're mine, Believe that you're mine.
This love is unbreakable. It's unmistakable. And each time I look in your eyes, I know why.This love is untouchable. A feeling my heart just can't deny. Each time I look in your eyes, Oh, baby, I know why This love is unbreakable.
Shared the laughter, Shared the tears. We both know We'll go on from here. 'Cause together we are strong. In my arms: That's where you belong.
I've been touched by the hands of an angel. I've been blessed by the power of love. And whenever you smile, I can hardly believe that you're mine.
This love is unbreakable. Through fire and flame. When all this is over, Our love still remains.
This love is unbreakable. (Lyrics by Westlife)
Washegari Sunday, Diyam tayi baccin safenta sosai sannan ta tashi. Tana mikewa ta jawo wayarta ta tura masa message cewa tana gayyatarsa breakfast. Ta fita ta tarar duk su Murjanatu suma babu wanda ya tashi dan haka ta zarce kitchen ta fara shirya abinci. Tana cikin aikin Judith ta shigo suka cigaba tare har suka kammala sannan ta tafi ta tashi Murjanatu ita kuma ta shiga tayi wanka ta shirya sannan suka fito kusan a tare da Murjanatu. A palo suka hadu suka baje kayan breakfast suna yi sai gashi ya shigo. Suka gaishe shi gaba-daya ya amsa da sakakkiyar fuska tana bude warmers din gurin. "Me aka shirya mana ne?" Murjanatu ta tashi tana serving dinsa yayinda Judith tayi musu sallama ta fita. Ya jingina da kujera yana shan tea yana kallon Diyam yace "kin yi kyau sosai" ta sunkuyar da kanta tace "thank you".
Ranar wuni sukayi tare, ya dauke su a motar Diyam suka fita yawon zaga gari. Sai dare suka gama suka dawo gida ya ajiye su shi kuma ya tafi da motar. A daren Diyam ta kira Inna dan rabon da suyi waya tun sanda ta kira ta suna tare da Bassam. Inna ta dauka suka gaisa suka kuma gaisa da Asma'u da Subay'a. Sannan Inna ta karba tace mata "ya bakon naku?" Diyam tace "lafiya lau Inna" Inna tace "ya gaya miki abinda yayi? Naji bakiyi mana magana ba" Diyam taji gabanta ya fadi, me kuma yayi? Sai ta dake tace "me yayi kuma Inna? Ni bai gaya min komai ba" Inna tace "nasan dama bai gaya miki ba, na dauka zai gaya miki yanzu da yazo. Ya kwashe dabbobin nan daga gidan Alhaji Babba ya mayar dasu bayan gari tun kusan sati biyu da suka wuce. An buge katangar tsakiyar gidan Alhaji yace ya bar masa gurin kyauta".
Ga breakfast, ayi enjoying tare da oga.
[3/17, 12:15 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Sixty Seven: The Inheritance
Diyam ta ajiye wayar tana tunani, sati biyu da suka wuce Inna tace anyi relocating gidan gonar, sati biyu da suka wuce lokacin Sadauki bai ma yi winning bet dinsu ba. This means yayi abinda yayi ne on his own account ba wai dan yayi winning bet din ba. Shin hakan yana nufin Saghir yana da hope?
Washegari Sadauki ya koma Nigeria. A airport Diyam ta marairaice masa kamar zatayi kuka shi kuma ya rikice. "Ki taho mu tafi. Sai ki dawo next week" tace "school kuma fa?" Yace "share school din nan, ai baku fara exams ba" sai ta tuna sanda yake hanata zuwa islamiyya, tace "so kake ayi min bulalar fashi ko?" Yace "waye zaiyi miki bulalar? Gaya min shi in fara yi masa tun kafin yayi miki" tayi dariya kawai tana tuno jibgar da ta sha a gurin Saghir, sai tace "ni yanzu mai duka na ai sai dai ruwan sama, ruwan saman ma sai na tsaya" yayi kasa da murya yace "in kin tsaya din ma I will shield you from it, like an umbrella" sai ta tuno sanda Inna ta kama su suna saukowa daga sama tazo zata dake su ya kare ta shi akayi ta dukan sa. He had been shielding her all his life. Ya katse mata tunanin ta ta hanyar langwabe kai yace "Please kizo mu tafi" ta makale kafada tace "naki, sai dai ka zauna anan" yace "ai kinsan maganar da zata mayar dani Nigeria. So nake fa ayi lokacin hutun ku sai mu dawo tare" ta rufe fuskarta da hannunta tana murmushi, sai kuma tace "Inna ta gaya min zancen Alhaji Babba. An gode madallah Allah ya kara arziki" yace "ameen" sai kuma ya dauke kansa gefe kamar yana tunani yace "ina yammatan gidan? Su Murja kawarki wadanda kika yi min maganar su rannan akan har yanzu basuyi aure ba?" Diyam tace "suna nan. Muna waya da Murja ma. Wani abin ne?" Yace "ya maganar auren nasu" tace "suna jira dai. Last wayar da muka yi tace min zata tura saurayinta gurin Baba Sa'idu (mijin anty Fatima)" yace "idan kun sake waya kice mata zakiyi musu kayan daki, ita da sisters dinta" ta bude baki tana kallon sa yace "ke ba yayarsu bace ba, ke zakiyi musu kayan daki ai" ya dauke kai yace "in place of their brother".
A kano bayan Sadauki yaje gurin Mama yaje ya gaya mata sun daidaita da Diyam, sai kuma ya nemi shawarar ta akan abinda ya dace yayi next. Sai ta nuna jin dadin ta sosai tace "ko ku fa, ai hakan yafi muku akan wannan zaman jiran da da kuka ce zaku yi" ya shafa kai yana murmushi. Tace "to yanzu abinda za'ayi shine zanje ni da kaina in samu Alhaji Babba, in yaso sai ya fadi ranar da za'a je a same su kai kuma sai ka fada a can gida sai su zo" yace "da nayi tunanin ko Kawu Isa, saboda kar a samu matsala da Alhaji Babba" Mama ta girgiza kai tace "babu matsala insha Allah. Shine Babba dan haka dole a bashi girman sa in ya karba shikenan in bai karba ba in yaso sai a je wani gurin a nema" suna cikin maganar sai Mukhtar yazo, suka yi hannu da Sadauki, Sadauki yace "ka yar dani Mukhtar, ko nema na bakayi" Mukhtar yayi dariya yace "ai ka zama yallabai ne yanzu, ka zama hukuma sai da lallashi" Sadauki yayi murmushi yace "sharri zaka yi min kenan ko? Zan samu time zaka ganni har gidanka".
A Oxford da Diyam taje school sai taji babu dadi saboda ganin seat din Bassam empty. But sai taji dadi dan hakan yana nufin ya tafi gida kenan, ya tafi yaje ya gyara tsakanin sa da family dinsa. She just hope ba zai dade sosai ba saboda kar karatunsa ya samu matsala.
Kamar yadda Mama tayi alkawari, washegarin da Sadauki yaje ya same ta sai ta tafi gidan Alhaji Babba. As usual, bata ji dadin yadda ta samu gidan ba duk da dai a yanzu matan gidan sun fara yan sana'o'i, Hajiya Babba tana siyar da ruwan sanyi, lemo da kankara. Hajiya Yalwati kuma tana yin snacks, da wannan sana'ar suke kokarin ciyar da kansu da yayansu dan Alhaji Babba har yanzu kusan dashi da babu duk daya a gidan sai ma jigilar asibiti da suke tayi dashi, shi bai mutu ba shi kuma bai cigaba da rayuwa normal ba.
Taje suka gaisa da matan gidan sannan ta tafi dakin Alhaji. Yana nan har yanzu a dakin da Inna ta zauna bai koma part dinsa ba duk kuwa da cewa Sadauki ya saka an gyara part din tas batan an kwashe kajin. Ta gaishe shi ya tashi daga kwancen da yake ya amsa mata yana tambayarta lafiyar family dinta, kafin ta gabatar masa da abinda ya kawo ta sai cewa yayi "Hafsa ina Diyam, har yanzu bata zo gari ba?" Mama tace "bata zo ba. Basu samu hutu ba ai" ya mayar da kansa ya kwantar yace "Diyam yarinyar kirki ce mai son zumunci. Fatima ta gaya min abinda tayi wai taki auren shi wannan yaron da take ta nacin so tace lallai sai ya fito da Saghir tukunna zara aure shi. Banyi tsammanin haka ba, na dauka in ta juya bayanta ta bar Saghir a prison ba zata sake waigen inda yake ba, na dauka in ta samu cigaba a rayuwa ba zata sake tunanin halin da muke ciki ba. Ina so inga Diyam Hafsa, ina son in roki gafarar ta tun kafin lokaci na ya kare a duniya. Ina kuma son in roki gafarar Saghir. Ko ma menene Saghir ya zama ko ma menene Saghir yayi ko ake zargin yayi to laifi nane, nine na lalata rayuwar dana mafi soyuwa a zuciyata duk a tunanin soyayya ce nake nuna masa. Ina sane, ina sane da duk abinda Saghir yake yi nasan yana yi din amma sai in rufe idona in nuna tamkar ba zaiyi dinba saboda ina so in gaya wa kaina cewa ba zaiyi din ba. Banyi nadama a bisa tarbiyyar da nayi wa Saghir ba sai da na je gidan yari na ganshi tukunna" yayi shiru yana kokarin saisaita muryarsa saboda kukan da yaji yana neman ya kwace masa. Mama ta fara bashi hakuri "sai hakuri Alhaji, komai mukaddari ne komai rubutacce ne" yace "haka ne, amma komai yana da sila. Silar lalacewar Saghir kuma shine rashin tarbiyyar dani da mahaifiyar sa muka gaza bashi. Ba kuma mu tashi ganin sakamakon abin ba sai da ya zama babu abinda zamu iya yi akai. Bani da yadda zanyi in fito da Saghir daga inda yake, bani da kudi ko hanyar samun kudin da zan biya yaron nan kudinsa sannan bani da karfi na jiki dana aljihu da zan samo wannan yaron daya lika masa wadannan kwayoyi"
Yayi shiru yana tunani sannan yace "Hafsa, idan kunyi waya da Diyam ki nemar min gafararta dan ban tabbatar da zanyi tsahon ran ganin ta in roke ta da kaina ba, sannan kuma ki ce ina rokon alfarmarta akan ta janye waccan maganar ta kin cikawa kanta burin zuciyarta na auren Sadauki, ta aure shi indai tana sonsa, shi kuma ruwansa ne ya yafe wa Saghir ko kuma yaki yafe masa wannan zabin sa ne".
Sai Mama taji dadi, dan haka sai ta rufe maganar sasantawar da aka samu tsakanin Sadauki da Diyam dan tana son alhajin ya ji dadi a ransa ya dauka tamkar shi ya sasanta su din, dan haka ta ki shigar masa da maganar auren da niyyar sai bayan kwana biyu sai ta dawo ta sake shigar masa da maganar. Ta kuma yi masa alkawarin kiran Diyam ta gaya mata sakonsa.
Sai dai tana mike wa sai ga Kawu Isa ya shigo dakin hannunsa rike da jariri. Ya wuce ta yaje chinyar Alhaji Babba ya ajiye masa yace "ga sakon Saghir nan. Nayi masa huduba da sunanka dan haka ina yi maka murna ka samu takwara" ya juya da sauri ya wuce Mama ba tare da ya kula mai take cewa ba ya fita. Ta juyo ta dawo gaban Alhaji tana kallon jaririn da take kwance kan cinyarsa yana ta jujjuya kai da alama abincinsa yake nema. Ko ba'a yi mata bayani ba ra fahimci cewa Suwaiba ce ta haihu kuma wannan shine dan gaba da fatihar data haifawa Saghir. Ta saka hannu ta shafi kan yaron tana kallon fuskarsa mai kama data Subay'a. Tace "Allah yayi maka albarka" Alhaji ya dago kansa daga kallon yaron shima yace "ameen. Ki kira min Hajiya Saratu a ciki". Ga dai jika nan namiji Alhaji da Hajiya sun samu amma kuma shege.
Kafin Mama ta baro gidan sai data yi ta zarya zuwa gidan Kawu Isa akan ayi hakuri a mayar da yaron nan hannun uwarsa amma Kawu Isa yace sam bai san wannan maganar ba "ba zata shayar dashi ba" ya fada ya kuma maimaita wa. Ko samun ganin Suwaiba Mama bata yi ba, daga baya ma ta tabbatar bata gidan dan haka ta hakura amma tace "yaron dai jikan mune gabaki daya, kuma shi bashi ne yayi laifi ba dan haka bai kamata a hukunta shi akan laifin dashi bai san ma sanda aka aikata shi ba. Rashin shayar dashi ba zai goge cewa Suwaiba ce ta haife shi ba".
Sai taje ta siyo baby formula da feeder ta dawo ta kawo wa Hajiya Babba. Ta tarar da ita ta goya dan jaririn da ya rare baki yana ta kwarara kuka. Ta mika mata tayi mata barka sannan ta koma tayi wa Alhaji sallama, sai yace "ki turo min Amina dan Allah" daga haka sukayi sallama.
Bata koma gida ba kuwa sai da ta je gurin Inna, ta fada mata duk yadda sukayi da Sadauki da kuma yadda suka yi da Alhaji da kuma abinda ya faru a gidan alhajin. Inna duk ta tayar da hankalinta nan take washegari ta dauki kudi ta shirya ita da Asma'u da Subay'a taje tayo siyayyar kayan babies sukaje gidan Alhaji Babba, ta kaiwa Hajiya Babba ta kuma yi mata barka ta dauki yaron da yasha madarar sa yana ta baccinsa tayi masa addu'a sannan taje gurin Alhaji.
Bayan sun gaisa yace mata "Amina idan kun yarda ke da yayanki ina so za'a zo a raba gadon usuman" Inna ta kalle shi da mamaki tace "wanne irin rabon gado kuma Alhaji?" Yace "an raba ne? Ai har yau ba'a raba ba. Kuma taba kudin da nayi ne ya haddasa min duk masifun da suka same ni. Tun da na shigo kano na fara neman kudi nake samun sa'a da nasara a rayuwata ban taba cin karo asara ba sai dana bi son zuciyata na taba kudin gadon nan. Kuma har yau ban biya ba, wannan shi yasa duk abinda nake dashi bashi da albarka, duk harkar neman kudi bana tarar da komai a ciki sai asara. Wannan kuma a duniya ne kadai, idan har ban biya ba to azaba tana can tana jirana a lahira. Na sani sarai, ina sane da duk abinda nakeyi son zuciyata kawai nake bi shi yasa na kasa gyarawa amma yanzu alhamdulillah rayuwa ta bani wata sabuwar damar gyara kurakurai na guda biyu. Zan fitar da hakkin usuman da yake kaina sannan kuma zan gyara kuskure na na tarbiyyar Saghir akan wannan yaron da aka haifa masa".
Inna tace "mu ai Alhaji mun riga mun yafe maka rabon mu ni da yara da yake cikin abinda ka dauka, shima kuma Sadauki yace ya yafe kason mahaifiyarsa, sannan kuma ai kaima da sauran yan'uwa kuma da rabo a ciki sannan....." Yace "muna dashi, hardo yana dashi, hatta yaya ladi mahaifiyar Zainab tana dashi. Yanzu bayan mutuwar hardo matar daya aura kafin rasuwarsa tana dashi. Mutanen da suke da hakki suna da yawa, wannan yafiyar ba zata sauke min nauyin nan ba".
Tayi shiru tana lissafa maganar sa, sai yace "ina so azo ayi rabon gadon a bisa ka'ida. Zan bayar da complete kudin dana dauka, sai ayi wa gidan da kuke ciki kudi sannan a raba a bisa tsarin da addini ya tsara a bawa kowa rabonsa ko zan samu rayuwa ta dan sassauta min kafin in bar duniya kuma in samu sassauci a lahira" tayi tagumi tace "to a ina zaka samu kudin nan Alhaji?" Yayi murmushi yace "nan gidan da muke ciki shine kadai abinda ya rage min a duniya. Shi zan siyar. Kollere zan koma in cigaba da rikon sarautar da hardo ya mutu ya bari muka ki karba. Sauran abinda yayi min saura kuma sai in samu sana'ar yi a can wadda zata rike min iyalina a can din".
Inna ta girgiza kai tace "ba zai kai ga haka bama Alhaji, insha Allah ba zai kai ga haka ba".
Wasa wasa abu ya tabbata. Inna ta kira Diyam da Sadauki ta gaya musu abinda duk ake ciki, farko Diyam ta nuna rashin yardarta amma sai inna ta gaya mata cewa hakan shine dai dai "shima marigayin wannan wani sauke nauyi ne akayi masa". Aka yiwa gidan Baffa kudi, a take Sadauki ya siya. Aka kuma yiwa gidan Alhaji Babba kudi aka siyar, ana siyarwa Diyam ta aiko da kudi tace a kama musu ko rent ne su zauna kafin komai ya zama settled. Sannan Alhaji Babba ya ware kudin garejin Baffa daya siyar aka hada da kudin gidan Baffa aka raba kudin cash, kowa aka danka masa nasa a hannunsa hatta amaryar da hardo yayi kafin rasuwarsa sai da aka fitar mata da nata a cikin kason Hardo aka aika mata dashi har Kollere.
Babu yadda Alhaji Babba baiyi ba akan son komawa Kollere amma yaya da yan uwa suka saka shi a gaba akan lallai ba zai koma ba. Dole ya zauna a gidan da Diyam ta aiko da kudi aka kama masa haya a unguwar Jaeen, suka koma gabaki daya shida iyalinsa. A lokacin ne kuma Diyam daga can ta aiko da kudurinta na son yiwa kannen Saghir su hudu wadanda suka isa aure kayan daki. Sai Alhaji Babba yace "ku gaya mata tazo sai a hada auren tare da nata".
A bangaren Sadauki, yana ta son ya tunawa Mama da maganar da suka yi amma kunyar ta yakeji, sai yayi ta cewa Diyam wai ita ta kira Mama ta tuna mata, tayi dariya tace "wato nice marar kunya ko? To babu ruwana, tunda kaji tayi shiru tana da dalilinta".
Sorry for keeping you guys waiting. Biki things. Enjoy your week.
[3/18, 11:02 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Sixty Eight : Save the Date
Yace "eh nasan tana da dalilin ta shi yasa ni kuma na kasa zuwa in tuna mata. Am just scared Diyam, tsoro nake yi kar a sake hana min ke a karo na biyu. Bansan me zanyi ba wannan karon" tace "babu wanda zai hana mu juna Aliyu. In har kaga ba'ayi ba to kuwa tabbas Allah bai rubuta za'ayi ba. Waliyai na ne su amma basu kadai bane waliyai na in sunki zamu iya zuwa Kollere mu......" Yace "no, no Diyam. Ba su kadai ne waliyan ki ba amma sune shakikan Baffa, kamar yadda kika fada haka ne Baffa zaiji dadi idan muka sasanta tsakanin mu da su. Kuma ni ba zanzo in zama sanadiyyar rabuwarki da yanuwanki ba but am not going to give you up, not now not ever. Dan haka zamu jira in ta kai ga cewa ni zan kuma durkusawa Alhaji Babba zan durkusa din" sai ya dan yi dariya yace "the table have been turning so past yanzu kuma na dawo ni nake nema a gurinsa" ta taya shi dariyar sannan tace "in lokacin durkusawar yazo, call me sai mu durkusa tare ni da kai because we are in this together".
Washegari sai ga wayar Mama. Ta gayawa Diyam duk abinda sukayi da Alhaji Babba tace "na bashi wannan damar ne saboda naga yadda yayi nadamar abinda yayi, so nake ya nemi Sadauki da kansa ya gyara kuskuren da yayi da kansa. Yanzu yace yana so kizo gari dan yana son neman yafiyarki, sannan kuma yace kice da Sadauki ya turo, in yaso sai a hada dana su Murja ayi gabadaya"
Diyam ta lumshe idonta tana jin wani irin farin ciki marar misaltuwa a zuciyarta wanda har sai daya saka hawaye ya taru a idon ta. Mama tace "kinyi shiru kuma, me zance masa?" Ta dan goge hawayen idonta tana jin zuciyarta fari kal kamar takarda, rabon data ji wannan feeling din tun Baffa yana da rai, tun tana carefree teenager, tun lokacin da Sadauki yake zuwa gurinta a school suyi ta bayyana wa junansu abinda yake zukatan su.
Amma sai taji kunyar Mama tace "mun kusa fara exams yanzu Mama, ba zan iya tahowa gida ba amma muna yin hutu zan taho sai in samu alhajin, duk da dai ni na riga na yafe masa tuntuni" Mama tace "to Allah ya bada sa'a. Maganar Sadaukin fa?" Diyam tace "duk yadda akayi Mama" Mama tace "ki gaya masa ya tura gurin Alhaji Babba, sai asa rana tare daba su murjan. Yaushe kuke so a saka?" Diyam ta sake yin shiru sai da Mama ta maimaita sannan tace "duk sanda aka ce dai dai ne" Mama tace "in aka saka lokacin hutun ku ai yayi ko?" Diyam ta sake yin shiru tana murmushi amma a ranta tana lissafa kwana nawa ya rage ayi hutun.Mama tace "shikenan tunda ba zakiyi magana ba, shi bara in kira shi in tambayeshi" s
Suna yin sallama Diyam tayi saurin kiran Sadauki ta gaya masa yadda sukayi da Mama, yace "tare dana su Murja kika ce?" Tace "eh, haka tace min" ya girgiza kai yace "I don't like that. Nafi son ranar bikinki ya kasance all about you not you and someone else, nafi son in an ganki ace 'ga amaryar can' kar ace 'ga daya daga cikin amaren nan' nafi son ki samu cikakkiyar kulawa daga kowa ba wai ki samu divided attention ba. Dan haka zan gaya mata ayi nasu first, later in an huta sai ayi namu"
Tun da ya fara magana take murmushi har sai daya gama sannan tace "I don't need attention din mutane, attention dinka nake so, in nayi kwalliya ban damu da a yaba ko ayi comparing dina da wasu ba as long as kai ka yaba as long as a gurinka babu wadda ta kai ni. Besides, ni ba biki zanyi ba, daurin aure kawai za'a hada da nasu, ni a gida zanyi zamana kawai sai wanda ya shigo aka gaisa kawai shikenan. Ban damu da having a big wedding ba as long as kaine angon that's all that matters, tunda nasan a gurinka zan samu more than abinda na samu a wancan auren" a can kasan makogwaron sa yace "more of what?" Tace "everything" yace "like?" Tace "caring" yace "and?" Tace "tunda nace everything ai ina nufin everything ko? Sai na lissafa maka?" Yayi dariya yace "so nake ki fada da bakin ki, yadda in lokacin yayi zan tuna miki cewa ke nema da kanki" ta bata rai tace "abinda kake nufi fa ni ba shi nake nufi ba, we are not talking about the same thing" yace "zaki sha kwana ko? To gaya min ni abinda nake nufi" tace "ni ban san me kake nufi ba fa" yace "to in baki sani ba ya akayi kika san ba abu daya muke nufi ni da ke ba?" Tayi rolling eyes dinta tace "good night Aliyu" yace "ashe tsoro na kike ji tunda zaki gudu, ki tsaya mana" tace "ba tsoro nake ji ba bacci nake ji, ina da school gobe" yace "hmmm okay, Allah ya tashe mu lafiya, but I will still demand to know that 'everything' da kika fada, ko ba gobe ba ko watarana I will get the words out of you".
Suna gama wayar Sadauki ya ajiye phone din yana kallonta, sai kuma yayi murmushi sannan ya lumshe idonsa ya kwantar da kansa a bayan kujerar office dinsa yana dan jujjuya wa a hankali. Sai kuma ya mike zaune sosai ya jawo system dinsa yana duba calendar, yasan ranar dasu Diyam zasu fara exams ya kuma san ranar da zasu gama sannan yasan ranar da zasu koma school, sai ya duba dates din da suke tsakanin hutunsu da komawar su school yana neman weekend mai perfect date for their wedding, sai idonsa ya sauka akan date din, his birthday. Ya dafe kansa yana fadada murmushin sa. He is going to have a perfect birthday gift for his 30th birthday.
Mama ta kira shi kamar yadda tace zatayi, ta kuma maimaita masa abinda already Diyam ta gaya masa sai ta tambaye shi shima akan date, sai ya maimaita mata abinda Diyam tace mata "duk sanda aka saka dai-dai ne Mama" ta tabe baki tace "ai shikenan, idan manyan sunzo ayi magana dasu".
Washegari ya hau jirgi daga kano zuwa Maiduguri ya samu Alhaji Babagana wanda yake kani ne a gurin Papa kuma shine dai wanda shekaru goma da suka wuce yazo ya nema masa auren Diyam aka hana shi. Yanzu ma shi zai sake dawowa tare da Alhaji Bukar su karasa abinda suka fara. Nan take shi kuma ya kira Papa ya gaya masa sannan ya bashi izinin ya dauki sauran yan'uwa suje su hadu da Alhaji Bukar suyi duk abinda ya dace. Sai da suka gama wayar sannan Sadauki ya gaya masa date din da ya keso a saka. Sai shi kuma ya tambaye shi "kana ganin ba za'a samu matsala ba? Kar azo ayi irin ta wancan karon" Sadauki yace "babu matsala in sha Allah, tunda wannan karon ai sune da kansu suka nemi azo din".
Daga Maiduguri sai yayi branching a Yobe yaje damagun gurin yaya ladi wadda take zaune a gidan cousin dinta da Sadauki ya gyara musu shi tas ya zuba musu kayayyakin more rayuwa kuma ya daukar musu yan aikin da zasu ke kula dasu. Bayan sun gaisa ta gama loda masa tuwo da fura sai ya sanar mata da duk abinda ake ciki, yana maganar yana murmushi. Sai ta rike baki tace "Diyam din dai Aliyu?" Ya dago kai yana kallon ta yace "Diyam din dai. Ko kina kishi ne?" Ta tabe baki tace "ni dai daka hakura da Diyam din nan da nafi jin dadi, kazo ga yammata nan birjik ka zaba ka darje in ma hudu kake so a tsakanin yau da gobe sai a samo maka su amma kai ka nace sai yarinyar da yan'uwanta suka wulakanta ka, suka wulakanta mahaifiyar ka, suka wulakanta ni kakarka?" Ya daga kafada yace "ita nake so, ita ma kuma tana sona kuma in anyi auren da ita zan zauna bada yan'uwanta ba" Hajiya Dije, cousin din Yaya Ladi tace "amma duk da haka Aliyu, ko bayan anyi auren ne ya kamata ka samu budurwa ka kara da ita" sai ya mike tsaye yana daukan hularsa a hannu fuskarsa da murmushi yace "kar ku damu, bayan anyi auren da sayi daya zan dawo nan sai in aure ku duk ku biyun a rana daya" yaya ladi ta tabe baki dan tasan shirishitar da maganar yake yi, tace "to ai shikenan, uwarka ma haka nayi ta fama har sai dana hakura" ya durkusa a gabanta yace "kisa mana albarka kawai ke dai. Kiyi mana fatan alheri" ta dafa kansa tace "Allah ya sanya alkhairi a ciki, Allah ya baku zaman lafiya ya kuma kade duk wata fitina da zata taso sannan ya baku zuri'a mai albarka" yayi kyakykyawan murmushi yace "yanzu kika yi magana. Karki manta, ke ce uwargida ran gida a gurina, ita kuma amarya ta sannan kuma zuciyata".
A gidan Baffa aka sauki bakin da suka zo daga Maiduguri, aka bude musu part din Baffa inda Inna ta zauna da, Mama tazo da yammatan ta suka hadu suka shirya musu abinci mai rai da lafiya wanda duk da kasancewar su masu hannu da shuni amma sun tabbatar cewa an karrama su. Sannan Alhaji Babba yazo, Kawu Isa ma yazo sannan abban su Rumaisa shima yazo suka zauna suna ta hira ta wasan fulani da barebari suna ta dariya kamar sun saba. Sai a lokacin ne su Alhaji Babba suka san asalin waye mahaifin Sadauki, jin hakan ba karamin girgiza su yayi ba, ba kuma karamin nadama ya saka musu ba. Lallai rashin sani yafi dare duhu, wanne irin gorin arziki ne basu yi wa Sadauki ba? Wanne irin wulakanci ne basu yi masa ba shida mahaifiyar sa?
Sai da suka nutsa sannan Alhaji Bukar ya gabatar musu da dalilin zuwan su cewa suna nemawa dansu Aliyu Umar Abatcha auren yarsu Halima Usman Kollere, sai Kawu Isa ya gyara masa yace "dan mu dai. Sadauki ai dan mu ne kamar yadda Halima take yar mu. Ku kawai zuwa kuka yi dan ku tunatar damu akan abinda ya kamata muyi tuntuni amma kuma son zuciya da kuma rabo ya hanamu aikatawa sai yanzu da Allah ya sake dawo mana da damar" Alhaji Babba yace "mun bawa Aliyu auren Halima. Duk sanda kuka shirya sai ku dawo a saka rana" Alhaji Babagana ya jawo yar jakar daya shigo da ita ya ajiye a gaban Alhaji Babba yace "a shirye muka zo. Kuma munzo da ranar mu amincewar ku kawai muke nema" sai ya fadi ranar da Sadauki ya gaya masa, yace "lokacin yarinyar tana hutu" babu musu kowa ya amince da hakan, sannan suka sake gaisawa yanzu kuma a matsayin surukai. Sai kuma Alhaji Babba ya roki gafarar su a bisa abinda yayi musu wancan zuwan. Su kuma suka yafe cikin sigar tsokana dan mayar da abin wasa.
Bayan tafiyar bakin ne aka kirawo Inna da Mama da suke cikin gida suka zo akayi musu bayanin abinda ya faru da kuma ranar da aka tsayar. Alhaji Babba ya mikawa Mama jakar da aka bashi yace "ga abinda suka kawo" Mama ta bude sai ta dago kai tana girgiza wa tace "wannan kudin sunyi yawa, albarkar aure ake bukata ai bawai yawan kudi ba" Kawu Isa yace "nima dai naso ince haka, amma sai naga tunda bani suka mikawa ba gwara inyi shiru" Inna tace "ai duk daya ne babu bambanci, suma kuma nasan sun mika masa ne saboda shine Babba" Abban Rumaisa ya kalli Alhaji Babba yaga yadda yayi da fuskar abin tausayi kamar wanda yayi laifi sai yace "tunda an riga an karba ai ina ganin shikenan. Albarka kuma sai muyi ta saka musu ita mu kuma tayi musu addu'a shikenan". Sai Kawu Isa ya tashi yayi musu sallama tare da fatan alkhairi sannan ya tafi.
Ana isar da sako gurin Sadauki ya turawa Diyam message
"save the date. 25th August"
[3/20, 10:04 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: DIYAM
By
Maman Maama
Episode Sixty Nine: Mrs Abatcha
Assalamu alaikum
Naga votes dinku, kuma kamar yadda nayi tsammani kusan 99% sun goyi bayan a fito da Saghir. Inda aka samu rabuwar kai shine akan lokacin da za'a fito dashi, kafin biki ko bayan biki. I followed the majority kamar yadda nayi alkawari amma na rubuta in such a way that suma minority din zasu samu satisfaction.
Thank you.
We are almost done insha Allah.
Ta lumshe idonta tare da jingina kanta da jikin kujerar da take zaune akai tana murmushi mai sauti wanda yafi kama da dariya. Murjanatu da take zaune kusa da ita tana cin abinci ta dakata da abinda takeyi tana kallon Diyam sai ta bude ido tace "what? Menene ya faru kike dariya ke kadai?" Diyam ta daina dariyar da take yi amma bata ce komai ba sai Murjanatu ta warce wayar daga hannunta ta karanta message din nan take ta mike tana tsalle tana kiran Judith, Judith tana fitowa tayi mata bayanin cewa auren Diyam za'ayi sai itama ta kama murna suna rawa a tsakiyar palon, Diyam tana zaune tana kallon su a ranta tana jin kamar ta tashi suyi rawar tare amma sai ta hana kanta.
Sai da suka gama tsallen murnar su sannan Murjanatu ta zauna tana haki ta jawo phone dinta, Diyam ta bude ido tace "hey, me zakiyi?" Murjanatu tace "su Adama zan gaya wa" Diyam tace "ai za'a gaya musu a can, ki barsu kawai saji a can" Murjanatu tace "yanzu su Adaman ma kunyarsu kike ji? To Papa zan gayawa ma, in ce masa gaki nan kin saka waya a gaba kina ta dariya kin kasa rufe baki kina murna zaki auri dansa" nan da nan Diyam ta mike ta murde hannun Murjanatu ta karbe wayarta ta tafi daki tana cewa "nayi seizing phone dinki, bazan baki ba sai anyi hutu".
Tana shiga dakin Murjanatu ta dauki tata phone din ta kira Sa'adatu wadda a lokacin suna tare da Falmata sai suka kira Adama da taje school a lokacin suka hada conference call sannan Murjanatu ta basu labarin abinda yake faruwa. Duk sunyi murna sosai musamman da yake wannan shine biki na farko da za'ayi a gidan su. Sa'adatu tace "oh su yaya Aliyu za'ayi aure, I wonder ta yaya suke magana da Diyam din da wannan turbunanniyar fuskar tasa" Murjanatu tayi dariya tace "wallahi in kunga dariyar da yakeyi mata ko, zaku dauka chanja shi akayi gaba ki dayan sa" sun jima suna hirarrakin su sannan suka lissafa kwanakin da ya rage kafin bikin sai kuma suka fara tsare-tsaren events din da zasu shirya. Sai da suka gama Murjanatu tace "Allah yasa ya yarda, zamu iya gama shirya komai yace shi ba za'a yi wa matarsa kwalliya a shiga da ita cikin mutane ba, kishi ne dashi kamar me".
Sai da suka gama Murjanatu ta dauki wayar ta kai wa Diyam har daki ta mika mata tace "thank you for letting me use your phone" sai ta ajiye ta fita da sauri tana dariya. Diyam ta dauki phone din ta duba numbers din da Murjanatu ta kira, sai tayi murmushi tana mamakin zumunci irin na wadannan mutanen, sam basa nunawa Aliyu yan ubanci ko dan akwai wayewa sosai a tare da su?
Daga gida ma Mama ta kira Diyam ta yi mata bayanin duk halin da ake ciki, sai kuma ta umarce ta data kira Rumaisa suyi shirye shiryen abinda zasu yi kafin tazo gidan.
Sanda sukayi waya da Sadauki kuma sai yace mata "guess what? Na sayi fili zan yi gini" tayi dariya tana rike baki yace "au, dariya ma na baki ko?" Tace "I tot zaka sayi gida ne kawai, ko kuma ma ka riga ka siya" yace "hmmm, nima na dauka zan siya gidan ne, but then an opportunity presents itself to me, na saka a nemo min gida sai dillalin ya gaya min akwai wani fili ma in ina so, sai na bincika na gano ashe fili na ne, filin mune Diyam da Baffa ya siya mana zamu gina gidan mu, all these years ba'a gina shiba har sai daya dawo hannun mu. And now I hired wani construction company da aka bani labarin sa a Abuja 'Moon Construction Company' sunce zasu gama komai within a month. Ina ganin ai yayi ko? Tunda muna da kusan watanni biyu nan gaba"
Diyam taji dadi a ranta tana jinjina hikima irin ta ubangiji. Tace "yayi sosai ma" yace "zasu turo min samples na building plans dinsu, sai mu zaba ni dake sannan sai su fara" sun jima suna hirarrakin su sannan suka yi sallama suka ajiye wayar. Sai ya cigaba da zama hannunsa rike da phone din yana kallon hotonsu shi da ita da yake kan screen din wayar, a Oxford suka dauka sanda yaje, selfie ne yayi musu suna tsaye a gaban motarta shi yana murmushi ita kuma ta turo baki tana hararar sa. Yayi murmushi saboda ya manta me yayi mata a lokacin take hararar sa kuma yasan itama kanta in da zai tambayeta ta manta. Ya saka babban dan yatsansa a hankali ya shafa fuskarta a jikin hoton sai kuma yayi sliding din hoton sama ya nemo number din one of his lawyers ya kira "barrister akwai maganar da nake so zamu yi Please, lets meet in my office in an jima. Okay, thank you".
Diyam har ta fara sabawa da rashin Bassam a school, duk da dai kullum in ta kalli empty kujerar kusa da ita sai taji babu dadi. Sai a lokacin tayi nadamar rashin exchange din numbers da basu yi ba at least da yanzu ta kira shi tasan halin da yake ciki. And then one day, suna gab da fara exams din su sai gashi ya shigo ana tsakiyar lecture. Yayi ignoring lecturer din da yake masa kallon yazo late yana distracting din class sai ya wuce empty seat din kusa da ita ya zauna ya juyo yayi mata murmushi sannan suka mayar da hankalinsu kan lecture din da ake yi. Sai da aka gama lecturer din ya fita sannan Diyam tace masa "welcome back prince Sadiq" ya juyo yana kallon ta da mamaki dan shi dai ba zai iya tuna sanda ya gaya mata daga inda yake ba, yace "Prince? Yaushe na gaya miki haka?" Tace "ba ka gaya min ba, Aliyu told me" yace "shi din ya akayi ya sani?" Tace "okay, ba direct ya gaya min ba, kace ka taba ganinsa a gurin daurin auren yayanka a abuja last year, shi kuma yace daurin auren da yaje abuja last year na jikan sarkin Abuja ne, so, in yayanka ya kasance jikan sarki to kuwa kaima jikan sarkin ne, ko ba haka ne ba?" Ya dauke kai yace "an baki A1 a fannin bincike" tayi dariya tace "tell me everything. Dame da me ya faru? I hope komai ya warware yanzu and you are back to your old self again"
Yace "well, bayan mun rabu naje gurin aunty Hafsat but she refused to see me. Nayi iyakacin kokari na amma abin yaci tura but sai na ci sa'a uncle Zayed ya dawo, dama yayi tafiya ne lokacin da muka samu sabani dan haka bai ma san abinda ya faru ba, I explained everything to him kuma na dauki laifina sai ya saka ni a gaba muka tafi Nigeria tare" ya danyi dariya yace "ba karamin taimako na Allah yayi ba da muka je tare dashi, da maybe in Daddy ya fara jibgata sai na kwanta a asibiti" Diyam tayi dariya tace "anya kuwa bakayi girma da duka ba?" Yace "not to my Daddy, ba ruwansa da girma na wallahi dukan tsiya zaiyi min Mami kuma ba zata hana shi ba. But Allah ya taimake ni Uncle Zayed ya shiga maganar, and my grandparents too, sai komai yazo da sauki musamman tunda na karbi laifina kuma na bada hakuri. And now Ya Ameen ne ya dawo dani tare da wife dinsa Humairah itama zata fara karatu. She is an artist, yana so ne ta samu qualifications din kawai" suka yi shiru Diyam tana tunanin ina ma dai itama nata family din zasu zama irin haka in ɗa yayi wa wani family member laifi sai iyayensa su danne son da suke yi masa su hukunta shi har ya zamanto su ake bawa hakuri ma.
Bassam ya cigaba da cewa "Mommy, my grandma, tace wai in zabi budurwa a cikin cousins dina in place of khausar, but nace mata ta barsu duk na gode, saboda duk wadda na zaba din za'a iya forcing dinta dan a faranta min and I don't want to end up like Saghir dinki, in zauna da matar da bata so na, so I decided zan jira, rayuwar ai yanzu ta fara ko? Zan jira har Allah ya hada ni soulmate dina da zata soni kamar yadda kike son Aliyun ki" ya karashe da sigar tsokana. Ita kuma tayi murmushi tace "ka lallaba ni in baka kanwata" yace "wacce kanwar?" tace "Murjanatu" ya daga hannu yace "no, no, no. Thank you so much but no. Wannan yarinyar samarinta sun kai cikin container".
Suna tare har aka tashi. A lokacin ne ta bashi labarin itama cigaban da aka samu a nata bangaren, ya taya ta murna sosai da sosai sannan shima ya tambaye ta game da shirye-shiryen da take yi. Ta daga kafada tace "ba fa abinda zanyi ni, ina naga friends din ma da zan shiryawa event. Nasan dai Inna zata yi taron yan uwa da abokan arziki and that will be all" Bassam yayi shiru yana kallon ta sannan yace "kinsan wani abu? Matar yayana dana gaya miki mun taho tare zata fara school itama, zan hada ki da ita ina tunanin you two will like each other. Zaku iya zama friends" Diyam tace "no, ni bana son friendship da yayan masu kudi" yayi murmushi yace "babanta ba mai kudi bane ba, mai rufin asiri ne. Kuma bafulatana ce irin ki" tace "in babanta ba mai kudi bane ba ai mijinta mai kudi ne" Bassam yace "that makes the two of you" sai ta sunkuyar da kanta tana murmushi, the mare thought of Sadauki as her husband yana saka ta murmusawa.
Suna rabuwa da Bassam ta kira Sadauki ta bashi labarin dawowar Bassam. Wannan shine dai dai saboda boye boye shi yake kawo zargi in a relationship.
Kamar wasa sai ga Bassam ya kawo wa Diyam Humairah har gida. Sai Diyam taga cewa ashe duk abinda take tunani a game da Humairah ba haka bane ba, na farko she is young, dan Diyam tana ganinta ta san cewa ta girme ta. Ko kuma dan tana da baby face ne? Da suka zauna suka fara hira sai ta fahimci tana da saukin kai sosai da kuma addini. Ta karbi babyn da yake hannun Humairah tana yaba kyawunsa tace "masha Allah, ya sunansa?" Humairah tace "Abubakar, Ayman ake ce masa" Diyam tayi murmushi tana tuna mitar da Bassam ya taba yi akan cycling suna daya within a family. Amma ai honor ne ko? Kowa yana burin ya haihu yayi wa iyayensa takwara.
Nan da nan Diyam ta dauko zani ta goya Ayman, tana tuna sanda Subay'a take jaririya. Wannan yasa Humairah ta kara sakin jikinta saboda hausawa sunce mai ɗa wawa ne. Sun jima suna hira, suka yi hirar similarities dinsu sannan suka yi hirar differences dinsu, a take kowacce a cikin su ta fahimci cewa tayi kawa.
Tare suka shirya abinci sannan suka zauna suka ci a plate daya, suna cikin ci Murjanatu ta shigo tayi joining dinsu itama. A nan ne take bawa Humairah labarin cewa an kusa auren Diyam da yayanta, sai kuma hirar ta koma kan hidindimun aure da kuma zamantakewa ta aure har sai da Murjanatu ta mike tace "wannan hirar tafi karfina kar kuje ku kona ni tun kafin in tafasa".
Komai ya tafi normal har Diyam ta kammala exams dinta, a cikin lokacin sau biyu Sadauki yana zuwa Oxford Diyam tana koro shi Nigeria saboda tace karatu yake hanata yi in dai yana can din. A dole ya hakura ya dawo Nigeria amma da sharadin cewa kullum zasuyi video call sau biyu.
Ranar da zata dawo Nigeria Sadauki ne yace zaije ya dauko ta, amma sai ya gaya wa Asma'u ta shirya Subay'a su tafi tare. Subay'a kam murna take tayi ta kasa rufe bakinta saboda farin cikin zata ga mommyn ta, dan haka bata damu bama da wate zasu tafi tare dashi. Shi ya fito da kansa ya bude mata kofar mota ta shiga sannan ya zagaya ya zauna yana tsokanar ta "Subis yanzu duk wannan kwalliyar ta mommy ce? Dama ashe kin iya kwalliya haka shine ni ba kya yi min sai mommy ko?" Ta sunkuyar da kanta tace "bani nayi ba ai, aunty Asma'u ce tayi min" yace "to gaya min, me kika tanadarwa mommy?" Ta bude hannu tace "babu komai, ai ni bani da kudi" yace "to me kike so ki siya mata" tayi shiru sannan tace "sweets" yayi murmushi "wato kin san ta da shan sweet ko?" Sai tayi shiru bata ce komai ba. Yace "kina so in kai ki ki siyo mata?" Ta gyada kai kawai, sai yace "a'a, in dai kina so to sai kinyi magana da baki ba da kai ba. In kuma baki yi ba bazan siya miki ba" tace "ina so" yace "to sai kin fadi sunana tukunna. Ya sunana" a hankali tace "uncle Aliyu" yayi murmushi ya shafa kanta yace "good girl".
Suka biya ta mall suka ciko leda da kayan zaki sannan suka karasa airport. A airport din sai yaga duk walwalar data fara dazu ta ragu, tayi shiru kamar mai shirin yin kuka, sai ya durkusa a gabanta yace "menene kuma? Ba kya murnar ganin Mommy? Ko in kira ta a waya ince mata ta koma ba kya son zuwanta?" Sai tayi sauri ta girgiza kai, yace "to me kike so?" Tace "rannan da muka zo nan da mommy, sai police suka zo suka tafi da Daddy na kuma har yanzu basu dawo min dashi ba" sai hawaye suka zubo daga idonta ta dago tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta ta sake cewa "mommy tace zaka fito min dashi ko?" Ya saka hannu ya share mata hawayen fuskarta yace "daddyn ki zai fito little girl. I promise you" sai kuma yayi murmushi yace "amma sai kinyi min wani alkawari, promise me daga yau mun zama friends" ya fada yana mika mata dan karamin finger dinsa, ta goge hawayen fuskarta ta saka nata karamin finger din a ciki sannan ta gyada kai tana murmushi. Ya daga ta masa ya dora ta akan kafadarsa yace "now, let's wait for your mommy".
Diyam tana fitowa ta hango su, and seeing them smiling together ya saka taji wani irin joy a zuciyarta marar misaltuwa, tana kallonsa ya sauke Subay'a kasa ita kuma ta taho da gudu gurinta sai ta durkusa ta bude mata hannayenta ta shige zuwa kirjinta ta rungume ta taba ajjiyar zuciyar dadi, ta dago fuskarta tayi kissing goshinta tace "I miss you so much little girl" Subay'a tace "I miss you too mommy". Ya karaso ya tsaya a kansu yace "na gane matsayi na" ta mike tana kokarin daukan Subay'a yace "ke! Careful kar kisa a daga min biki" ta harare shi tace "wato bikinka ne a gaban ka ko?" Yace "a yanzu, yes" Subay'a tace "uncle bikinka za'ayi?" Ta fara tsalle, "zanje gidan ka inga amaryarka" ya daga ta sama yace "karki damu, kece yar zaman daki".
Daga airport basu yi cikin gari ba sai suka dauki wata hanya daban. Diyam tace "ina zamu je?" Bai kalleta ba yace "kawunan ku zanje in siyar" tayi dariya "ni kaina yafi karfin babarbare ya siyar" ya kalleta yace "siya na nawa kuma? Sai ya kalli Subay'a ta mirror yace "kinci sa'a we have company" ta murguda masa baki, yace "ki cigaba, ba dai rashin kunya ba, akwai ranar kin dillanci".
Titin bypass suka hau sannan suka shiga unguwa uku, suka sauka daga babban titi suka shiga wani layi sannan yayi packing a gaban wani gida yace "Mrs Abatcha, welcome to your home" ta bude vaki tana kallon gidan sa yake gabanta sannan tace "wow" yayi murmushi yace "shall we?" Kafin ta bada amsa Subay'a ta bude motar ta fita da sauri tana cewa "uncle gidanka ne wannan?" Ya fito yana cewa "gidan mu ne princess, ni da mommyn ki da ke" sai ta kwasa a guje ta kama gate din tana cewa "Mommy ki kira inna kice ta aiko min da kayana" Diyam da Sadauki suka yi dariya a tare.
Malam iliyasu ya fito yana bude musu gate. Diyam ta kalleshi sannan ta kalli Sadauki shi kuma ya daga mata kafada yana murmushi. Sai ta juya tana amsa gaisuwar da malam iliyasu yake yi mata amma bata ce masa komai ba sannan suka taka da kafa suka shiga gidan. Tsayawa bayyana tsari da kyawun gidan zai tsawaita labarin mu amma dai tabbas Moon construction company sun kure adakar su a wannan gidan. Daki daki suka bi a nutse Sadauki yana yi mata bayanin komai kuma tana neman gyaranta in akwai amma ita bata jin akwai wani gyara da za'ayi a wannan tsararren gidan. Bayan sun gama sun fito ne suka zagaya baya gurin wani dan karamin gurin shakatawa mai lullube da grass carpet da kuma madaidaicin swimming pool mai dan karen kyau wanda ganinsa kawai ya isa ya saka mutum yaji yana son yin wanka. Suka zauna a wasu daga kuherun gurin ita kuma Subay'a ta bazama tana zagaya gurin a kuje. Diyam tace "amma gidan nan yayi kyau, irin sosai din nan fa" yayi murmushi yace "am glad you like it. It will be our Kano home insha Allah. Zamu yi wani a Maiduguri saboda muke sauka in munje, and for Oxford we have to get a bigger apartment dan wanda kuke ciki yanzu yayi mana kadan".
Sai ta dauko wasu takardu ya mika mata sannan ya gyara zama yana kallonta. Ta karanta ta kuma karantawa, ta fahimci cewa wata yarjejeniya ce signed by Aliyu Umar Abatcha cewa ya yafewa Saghir Muhammad Kollere kudaden sa daya satar masa. Akwai saka hannun lawyers dinsa, akwai saka hannun alkalin da yayi waccan shari'ar sannan akwai saka hannun Saghir. A kasan inda Saghir ya saka hannun ya rubuta "thank you".
Ta dago da sauri tana kallon Sadauki, sai kuma ta kasa magana. Yaushe Sadauki yayi wannan shawarar? Shin hakan yana nufin Saghir ya fito ko kuwa bai fito ba?
Jin bata ce komai ba yasa yace "lokacin da Saghir ya fada min wannan maganar a kanki ba rufe shi nayi niyyar yi ba, zuciyata abinda take gaya min shine in kama shi inyi ta dukansa har sai ya daina numfashi sannan in kaishi daji in ajiye shi dabbobi su cinye shi da rai" ya danyi dariya ganin kallon da take yi masa yace "babu irin imagination din da bana yi that's why I decided to set a trap for him and luck him up, a hakan zaiyi paying for what he did and he will be out of my reach yadda bazan yi masa lahanin da duk zamuyi dana sani ba. I didn't know his friend will set him up for drugs. Niyyata shine a lokacin da naji zuciyata tayi sauki a kansa sai in yafe masa ya fito but as fate have it ba wannan ne kadai case dinsa ba, so, har yanzu yana can kamar yadda alkali ya fada har sai an samu nasarar kama abokin nasa kuma sai abokin ya karbi laifin shi ya bashi ajjiyar drugs din" Diyam ta gyada kanta tana kallon Subay'a da take wasa a can nesa dasu sannan take murya can kasa "thank you. Mun gode Allah ya kara arziki" baice komai ba shima yana kallon Subay'a sai zuwa can yace "zanyi kokarin ganin ya fito, dan Subay'a taji dadi. But bazan bashi aiki ba kamar yadda kika bukata daga farko, ruwansa ne yayi hankali ruwansa ne kuma yayi akasin hakan. Na riga nayi magana da Ahmad, duk da dai kamar baya goyon bayan fito da Saghir din but yace zai taimaka min, matsalar shine su iyayen Kabir din sunki vada goyon baya su fadi inda dan nasu yake" ya juyo yana kallonta yace "naso ya fito kafin auren mu, naso yazo ayi dashi dan anan ne zan tabbatar da nadamarsa ko akasin hakan. But it is beyond me dan haka sai bayan
[3/22, 10:25 PM] +234 703 589 5826: ❤ DIYAM ❤
By
Maman Maama
Episodes Seventy & Seventy One : The Wedding
The chance of you dying with COVID-19 is 1% while the chance of you dying anywhere anytime by any means by Allah's wish is 100%. Wanne ya kamata muji tsoro? Corona virus ko Allah? Then why the panic bayan mun yadda da kaddara munsan komai rubutacce ne?
Mafita kawai shine mu koma ga Allah mu rungumi Alqur'ani da Azkar, mu yawaita istigfari sannan kuma mu bi dokokin da ma'aikatan lafiya suka kafa.
Idan Allah ya riga ya rubuta cewa Corona virus itace sanadin mu muna rokon Allah ya karbi shahadar mu (mutuwar annoba shahada ce), idan kuma ba ita bace ba Allah ya bamu rayuwa mai albarka ya dawwamar damu cikin imani Ameen. Allah kuma ya kyautata karshen mu.
Diyam...............
Diyam taji dadi sosai a ranta. Tabbas ko da Sadauki bai fito da Saghir ba to kuwa yafe masa ma da yayi ya nuna cewa his stone hard heart is now soft. Yanzu ya yi part dinsa ya rage nasa kuma ya taimaka wa Saghir ko yaki duk ganin damarsa ne, taimakon yana da kyau sosai musamman saboda xuri'ar da aka riga aka hada, amma kuma ba wajibi bane ba. Dan haka ba zata sake yi masa magana ko kokarin tursasa shi zuwa haka ba dan in yayi din ya zamanto niyyarsa ta kyautata.
Tayi masa kyakykyawan murmushi tace "hakan ma mun gode sosai, Allah ya bar zumunci" yace "Ameen, Mrs Abatcha" ta harare shi, "bana so" yace "okay, madam kike so?" Ta mike tsaye kamar zata yi kuka "bana so wallahi" ya mike shima yana mata dariya "gaya min to, me yasa ba kya so?" Tace "sai in ji na zama kamar wata katuwar ƙedara, wai Madam" yayi dariya sosai yana matsowa kusa da ita yace "to me kike so ince miki?" Ta juya ido tace "Diyam" yace "Sadiyam" tayi masa gwalo tace "sholoki" sai ta bar gurin da sauri ta tafi gurin Subay'a tana waigensa. Ya daga murya yace "zan kama ki ne ai, not now but on the 25th" bata waigo ta kalleshi ba but she blushed.
Wayarsa tayi kara ya duba sannan ya taho gurinsu yana cewa "time off, Inna ta gaji da jira tasa yar asama ta kira mu" Diyam ta mike straight tana cewa "Allah sarki inna ta, nima nayi missing dinta sosai" ta mika masa takardun hannunta suka tafi Subay'a tana ta fushi wai ita ta dauka sunzo kenan.
A kofar gida ya ajiye su yace bazai shiga ba. Subay'a ta fita da gudu tana ta dokin bawa Asma'u labarin sabon gidan da suka je. Diyam ta yi masa sallama zata fita kenan sai ya miko mata wani card ta karba tana dubawa taga credit card ne sai yace "ki dauki kudin da zaki bukata a ciki, ki kuma dauki na su Murja da kika yiwa alkawari" kafin tayi masa godiya sai yace "birth year din ki shine pin din" ta gyada kai tana murmushi, ta sake bude baki zata yi godiya yace "bana son ji. Ko ki fita ko kuma in tafi dake kuma bazan dawo dake ba sai dai a biyo ki da kayan ki".
Bata san tayi missing inna har haka ba sai da ta ganta tukunna, ta tafi da sauri ta rungume ta tana dariya, itama innar dariyar take yi amma sai ta ture ta tana cewa "kar ki karya ni" Asma'u ma ta kankame ta tana cewa "nayi missing dinki, sosai Adda ta" Diyam ta kalleta tace "oh, Asma'u kin kara girma fa. Inna wannan ai itama kamata yayi a hada bikinta da nasu Murja" Asma'u ta fara buga kafa tana cewa "shikenan zaki kunto min ruwa, dama inna kiris take jira ta dawo kaina" ta karashe maganar tana tafiya daki. Inna ta bita da kallo tana cewa "yayanki ne ya daure miki gindi ai, daga ke har shi kun tsaya kuna ruwan ido amma ace yarinya kamar ki har yanzu bata da saurayi?" Diyam dai tana tayi musu dariya saboda ta fahimci wanne yayan ake nufi, shi har yanzu kallon Asma'u yake kamar wata jaririya.
Diyam ta lura da chanji a gidan su, an bude part din Ummah an kwashe kayan ciki sannan an gyara shi amma ba'a zuba komai a ciki ba. Ta shiga daki tayi wanka ta shirya tayi sallah sannan ta dawo palo suka zauna cin abinci da Inna, Asma'u da Subay'a da take ta zuba mata hira tana kokarin bata labarin duk abinda akayi a gidan sanda bata nan. Sai Diyam taji tamkar gidan yafi ko ina dadin zama.
Bayan ta kwana biyu ta huta sai shirya da niyyar zagaya gidajen yan uwa ta gaishe su. Inna tace "sai kiyi musu sallama kuma dan ba lallai ne ki sake samun zuwa gurin su ba". Tare da Asma'u suka fita, gidan Alhaji Babba suka fara zuwa, wannan shine zuwan Diyam gidan na farko kuma taji dadin yadda taga gidan, ba kamar dai nasu nada ba amma kuma basa cikin kuntata. Babban abinda ya kara mata jin dadi shine ganin Alhaji Babba ya chanja sosai ya samu nutsuwa fuskarsa ta saki ta rage nuna damuwa. At last ya daina blaming makiya da sauran al'umma for his misfortune. Da fara'a sosai ya amsa gaisuwar tata har da tsokanar ta da cewa "munji ki shiru har ina tunanin ko sai dai kawai mu daura auren anan in yaso angon ya biki can?" Ta rufe fuskarta tana jin kunyarsa. Sai kuma yayi mata godiyar kudin haya data biya masa sannan ya dora da bayanin neman yafiya a bisa abubuwan rashin adalcin da yayi mata. Ta katse shi da sauri "Alhaji ni na yafe ai, tuntuni na yafe muku tun ma kafin mu rabu da Saghir. Komai ya wuce sai fatan Allah ya kara gyara mana zumuncin mu" yace "ameen" ya dora da "ina son kuma ki sake yi min godiya gurin yaron nan Aliyu. Satin daya wuce naje na gano Saghir kuma ya gaya min abinda yayi masa, ya gaya min ya yafe masa kudaden daya daukar masa" ya fada yana dauke hawaye da babban yatsan sa. "Kudade masu yawa amma yace ya bar masa su. Kuma yace min ya hada shi da lauyoyinsa zasu taimaka masa akan maganar kwayoyin nan. Allah ya saka masa da alkhairi, Allah yaji kan mahaifiyarsa, matar da har ta mutu Allah bai bamu ikon neman yafiyarta ba".
Ta shiga dakin Hajiya ta dauki Muhammad, kyakykyawan yaro har ya warware yana ta shan madarar sa. Sai kuma ta shiga dakin Hajiya yalwati inda acan ne tafi dadewa suna ta hira da Murja da sauran yammatan, suna ta competition gurin farantawa Diyam.
A gidan Kawu Isa shima ya karbe ta sosai shi da iyalinsa. Sun jima suna hira yana tayi mata nasiha a game da aure, sai taga kamar wani chance ne ta samu na kokarin gyara tsakanin su da Alhaji Babba. Tace "Kawu, mu kuwa zamu ji dadi idan komai ya wuce tsakanin ka da Alhaji, kune iyayen mu, ta yaya zamuyi zumunci idan ku ba kwa yi?" Sai ya girgiza kansa yace "uwata shi zumunci yi min ne inyi maka, shi Alhaji Babba son kansa da son dansa ne ya jawo igiyar zumuncin sa da mutane duk ta gutsire. Ni fa wai kyautata wa ce na yiwa yaron nan na dauki yarinyar nan nace na bashi ita a daura musu aure saboda in gyara zumuncin da nayi tunanin kamar ya samu baraka, amma kinga sakayyar da ya saka min dashi. Dana je gurin uban na gaya masa ga abinda dansa yayi maimakon ya nuna alhinin sa kuma ya kira yaron nan ya nuna masa laifinsa sai ya shafawa idonsa toka yace shi ba dansa ne yayi ba, ko tambayar yaron ma fa baiyi ba. Yanzu gashi nan ya ga sakayya ai. Ni kuma gashi an barni da yarinya, ni ina ganin na kaita Kollere ta haihu a can ina tunanin kamar na rufe maganar ashe duk jama'a kowa ya sani. Jiya jiyan nan na fito daga masallacin unguwa naji ana maganar. Yanzu waye zai aureta da wannan tambarin? Menene makomar rayuwarta dana zuri'ar da zasu fito daga gareta?" Diyam tayi shiru tana tunani sai tace "Yanzu Kawu zaka hakura idan Saghir ya fito ya auri Suwaiba? Suka bude sabuwar rayuwa suka kuma rike dansu? Zaka yafe masa ka dawo da zumuncin ka da Alhaji?" Yayi shiru yana dan jujjuya kafa sai yace "yaushe Saghir din zai fito?" Diyam tace "very soon, insha Allah" sai yace "Allah ya fito dashi lafiya, abinda zasu yi shida mahaifinsa idan ya fito din shine zai zama tubalin cigaban alaka a tsakanin mu".
A cikin gidan sai Diyam taga bata ji dadin ganin Suwaiba ba duk ta rame, duk da cewa ita mai kiba ce amma yanzu duk ta sirance, farin ma ya ragu amma sai Diyam ta danganta hakan da haihuwar da tayi. Sai da Diyam tazo tafiya sannan Suwaiba ta biyo ta da niyyar rakata sai tace "Diyam kinga Jawad a gidan Alhaji?" Diyam ta gyada kai tana kallon ta, sai tayi murmushi kawai, anan Diyam ta fahimci problem din Suwaiba, kewar jaririnta take yi, sai tace "Diyam naga abban mu ya sakar miki fuska, dan Allah ko zakiyi masa magana ya karbo min Jawad" Diyam tayi shiru bata ce mata komai ba saboda ita dai ba zata iya wannan rashin kunyar ba. Sai dai kuma ta tausayawa Suwaiba saboda tasan zafin rabuwa da ɗa musamman ma wannan da yake dan jaririn da ko nono ba'a barta ta bashi ba. But hausawa sunce idan bera da sata to kuwa daddawa ma tabbas da warinta. Tabbas Saghir yayi laifi amma kuma itama Suwaiba da akwai nata laifin da har ta bari dadin bakinsa da kyawun fuskarsa suka rude ta ta bude masa kafafuwanta yayi mata ciki. Abinda ta shuka ne itama take girba.
Sai Diyam tayi tunani akan lalacewar zumuncin zamani. Babban dalili a fahimtarta shine son kan mu da muke dashi da kuma nuna son yayan mu a fili. Yes, an sani kowa yana son dansa amma hausawa sunce kaso naka ne duniya ta kishi ka kuma ki naka duniya ta so shi. Duba misalin uwa in ta kama danta tana duka idan yayi laifi, sai kuga mutane sun tafi da gudu sun karbe shi a hannunta suna bata hakuri suna kuma lallashinsa. Amma idan da ace zaiyi laifin ta goyi bayansa ta nuna cewa ba laifi yayi ba sai kuga mutane suna yi musu tsinuwa daga ita har shi. Daga nan kuma zasu fara ja baya dasu, zasu yanke zumunci dasu, in yayi laifin ma babu mai kwabar sa babu mai hana shi. Wannan tsarin na daga ni sai yayana shine tsarin daya tarwatsa zumunci.
A gidan Mama suka kai har dare. Diyam ta tambayeta shawara akan kayan dakin da zata yiwa su Murja, shin ta siya musu kayan ne ko kuma ta basu kudi kowa ya siya da kansa? Sai Mama tace "ina ganin ki sai musu furnitures, sai kuma ki basu kudin da zasu sai sauran kayayyakin anfaninsu tunda kowa da irin taste din ta" nan suka yanke shawarar irin kayan da za'a siya da kuma adadin kudin da za'a basu. Sannan Mama tace "to ke kuma fa? Menene naki shirin?" Diyam ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannayenta. Mama tace "ba kunya zaki tsaya ji ba fa, magana zaki yi sosai. Dan ba kya gari ne da tuntuni ya kamata a fara yi miki gyaran jiki da sauran abubuwa. Amma tunda kin dawo yanzu zamu fara insha Allah. Kinga akwai tsumin Maman Fareeda shine gatan da ake yiwa ko wacce amaryar da za'ayi aurenta a yanzu, ko matan auren ma zasu iya amfani dashi, very pure and natural babu algus. Ga number dinta nan zan baki ki kirata kiyi order zata kawo miki har gida kiyi ta sha kuma sai ki ajiye number din daga baya ma kya cigaba da karba" ta karantowa Diyam number din kamar haka "07033742833".
Sai kuma ta nemi Diyam ta sanarwa da Sadauki cewa zasu zo ganin gida ita da Aunty Fatima dan su san yawan kayan da za'a siyo. Amma da daddare da Diyam tana waya da Sadauki ta gaya masa sai yayi dariya yace "wanne kayan za'a siyo? Ki ce musu suyi hakuri nayi musu shigar sauri har na bayar da order kayan gida gabaki daya, za'a sa komai da komai, sai dai in an gama sakawa sai suzo su gani in akwai gyara suyi mana" da Diyam ta gayawa inna sai ta kama fada "wannan wanne irin abu ne? To wannan kudin da suka kawo a cikin jaka kuma me zamuyi dashi?"
Rumaisa tazo har gida suna maganar gyaran jiki da Diyam. Tace "akwai Hajiya Hannatu Sokoto, mutuniyar Sokoto ce amma ta zauna a sudan dan haka ta iya gyaran jiki sosai kuma duk kayan ta ma daga sudan take zuwa da abinta, nima wata matar abokin abban Najma (babynta) ce take bani labarin ta, aikinta akwai tsada dan matan manyan mutane kadai suke iya hiring dinta amma kuma fa akwai kyau dan saita mayar dake tamkar jaririya, Sadauki kuwa in ya shigo hannun ki to kuwa ya kade har ganyensa" ta karashe maganar tana dariya. Diyam ta dungure ta, sai kuma tace "to kisa a hada ni da ita mana" Rumaisa ta harare ta tace "au, na dauka ai ba kya so".
Tunda aka hada Diyam da Hannatu Sokoto shikenan komai ya chanja mata, matar ta karbi kudade da yawa a gurin Diyam amma fa tana fara aiki akanta, Diyam tasan cewa she is worth it. Kullum sai tazo kuma kullum da kalar gyaran da take yi wa Diyam. Tun daga kan gashin kanta zuwa faratan yan yatsun hannayenta da kafafuwanta babu abinda gyaran bai shafa ba. Yau a shafe ta da wancan a wanke da wannan gobe a saka ta tsugunna akan wancan turaren jibi kuma a bata wannan ace ta liƙa ta kuma yi tsarki da wancan. Gata kuma a jika ta gabaki dayanta a wanke ta. Har bakin Diyam sai da akayi masa gyara na musamman yadda zai bada wani sihirtaccen kamshi. Ga kuma tsumin maman fareeda (07033742833) da Diyam ta kira aka kawo mata shi har gida, wanda tana sha sau daya ta tabbatar wannan bana wasa bane ba dan haka tayi wa number din kyakykyawan ajiya dan gaba.
A gefe guda kuma tayi dinkuna na fitar biki. Duk da dai ita har yanzu tana nan akan bakanta na cewa ba zata yi taro ba, wanda inna zata yi kawai ya wadatar.
Sadauki kuma a nasa bangaren baya samun zama sam. Kullum yana cikin zirga-zirga tsakanin Maiduguri da Kano. Family dinsa duk sun taho daga Canada suna Maiduguri suna nasu shirin. Kamar yadda Murjanatu ta fada, lokacin da suka gabatar masa da jerin events din da suke son yi na biki sai yace "no, kuyi parties dinku ku kadai amma ni ba za'a fitar min da mata ana tallata ta a duniya ba" duk suka juya suna kallon Murjanatu ita kuma ta daga kafada tace "I told you so". Abinda kawai Sadauki ya yarda za'ayi shine wushe-wushe, wanda yake bikin al'ada na kanuri. Sai mother's eve da Mama zata yi washegarin kai amarya dan a nuna wa yan uwa amarya itama kuma ta san su.
On impulse Diyam ta kira Humairah, matar yayan Bassam ta tuna mata zancen bikinta. "Ban sani ba ko zaki samu zuwa?" Humairah tace "what are you talking about? Zan zo mana, ai ina lissafe da lokacin dama already na tambaya har an barni ma. Insha Allah kwana ma zanyi tare dani za'a kai ki gidan Mr Abatcha" sun jima suna hira sannan suka yi sallama. Ana bugo kati Diyam ta sake tura mata, sannan kuma ta tura mata na daurin aure tace "ki nunawa Bassam ko zai samu damar zuwa".
Satin biki yazo, su Mama sunje sunga gidan Diyam kuma babu abinda suka gyara saboda babu abin gyarawar, sai dawowa da sukayi suna rike baki suna bada labarin aljannar duniyar da suka gani. Mama tace "har Subay'a anyi mata dakinta, da set din gadonta da komai na bukatar ta". Ranar talata Diyam tayi baki, Sa'adatu, Falmata, Fanna da Adama gabaki dayan su da akwatinan su "tunda yaki yarda muyi dinner da luncheon da bridal shower da cocktail party gwara mu dawo gidan su amaryar mu zauna muyi ta kallonta" inji Murjanatu tana turo baki. Diyam tayi murmushi tana taryen su with open arms, da alama shi kansa yayan nasu bai san da zuwan su ba tunda bai gaya mata ba. A ranar ne sauran sisters din Sadauki suka fara ganin Diyam a zahiri, gashi kuma dama tasha gyara sai abun yayi musu duka biyu. Adama tace "gaskiya pictures basa yi miki adalci Diyam, you are much more beautiful in person" Murjanatu ta kama hannunta tana shafawa tace "what's the secret? So kike ki kashe min yaya na ko?".
Part din Ummah Inna tasa aka shirya musu aka yi musu shimfidu aka saka musu duk abubuwan bukata sannan aka kai musu kayansu can suka sauka. Sai Diyam itama ta koma can tare da Subay'a da Asma'u suka barwa Inna da yan uwanta da suka fara zuwa daga Kollere part dinta. Wasa wasa sai ga gida yana kara cika. Kusan duk wanda yazo daga Kollere sai yace a nan zai sauka, da Asma'u ta tambayi wata mai yasa basa tafiya gidan Alhaji Babba shi da yake auren yaya hudu? sai tace "haba yar nan, kowa ai yana son dan maiko maiko ko?" Jin haka yasa Inna ta aikawa da Hajiya yalwati kudi da kayan abinci tace saboda baki.
Kamun amare (su Murja) an saka shi ranar Alhamis, juma'a kuma angwaye sun shirya dinner su da amaren su da kawayen amare. Assabar za'ayi daurin aure, wanda shine za'a hada dana Diyam, Alhaji Babba ya bawa Kawu Isa waliccin yaran duk su hudun shi kuma zaiyi waliccin Diyam. Ranar assabar din ne kuma za'ayi yini sannan da daddare akai amare.
A bangaren Diyam kuma babu kamu, babu dinner, sai wushe-wushe ranar friday sai daurin aure assabar da safe sannan inna tayi yinin ta anan gida da daddare kuma akai amarya. But, ranar laraba sai ga mutane daga Maiduguri wai sunzo kawo kudin cin-cin, aka tarye su sosai aka kuma karrama su amma kuma akayi ta mamakin wannan al'ada ta cin cin. Mama tace "to yanzu cin cin din zamu zo mu soya ko kuma me?".
Alhamis da safe Hannatu Sokoto tayi wa Diyam kunshi ja da baki mai dan karen kyau, sannan kuma tayi mata kitso shuku kanana kanana, duk a cikin aikinta ne. Da yamma Diyam ta shirya tayi simple kwalliyarta cikin atamfa riga da plain zani ta dauki in-laws dinta suka tafi gidan aunty Fatima inda a can ne za'ayi kamun wadancan amaren. Amma Diyam tana zuwa sai kallo ya koma sama, kowa ya kalle ta sai ya sake waigo wa "wai Diyam ce wannan?" "Diyam ke ce kuwa?" Har sai data gaji dan haka kafin a gama ma ta gudo ta dawo gida. Tun a daren Sadauki ya gaya mata zasuyi baki washegari.
Washegari Friday, da wuri Humairah tazo gidan, hakan ba karamin faranta ran Diyam yayi ba. Suka hadu da Rumaisa, Rufaida, su Murjanatu da kuma Asma'u. A ranar Kasusu (yan uwan ango) suka zo gari, gidan Alhaji Bukar suka sauka, daga nan kuma suka taho gidan su Diyam kawo kayan gaisuwar uwar amarya. Set guda akayo wa Inna na kaya tamkar wanda aka hado mata lefe, sai kuma kayan kunshi iri iri wadansu ma ko sunan su su Inna basu taba ji ba. Su kuma anan gidan suka hada musu goma sha tara ta arziki na nau ikan kayan ciye ciye, fura da nono kam ba'a maganar ta saboda tambarin su na fulani, sai gurasa ita kuma shedar su kanawa ne, sai kuma sauran abinciccika da kala kalar nama da drinks har sai da suka ci suka bari suka kuma yi takeaway. Da zasu tafi suke tsokanar su Sa'adatu "wato dan kunyi yaya shine kuka tare anan? To sai ku bita har gidan mijin kuyi mata zaman daki" Asma'u tayi saurin cewa "nice yar zaman daki ai".
Daga nan kuma sai aka fara shirye-shiryen wushe-wushe (bangajiya). A gurin taro na Meena event center anyi decorating gurin da traditional costume na barebari. Falmata, wadda take registered beautician ita ce ta zauna ta tsarawa Diyam kwalliya sannan suka nannade ta da flowery laffaya mai kalolin red and blue. Su kuma yammatan duk sunyi kwalliyar blue shadda da akayiwa dinkin riga three quarters da skirt, sai kuma suka yafa jan mayafi. Duk abinda suke yi Diyam tana jin sune kawai, amma ita hankalinta yafi tafiya ne akan murnar yau zata ga Sadauki, dan rabonta da ganin sa tun ranar Monday daya tafi Maiduguri zai taya Papa shirye shiryen saukar bakinsa da zasu zo daurin aure.
Bayan magrib motoci suka zo akayi ta diban mutane ana kai su, kowa cewa yake yi zaije saboda kowa yana son yaga wannan al'ada ta barebari sannan kuma kowa yana son cin dadi. Lol
Sai da aka gama kwasar mutane saura Diyam da yammatan ta sannan Sadauki yazo daukan ta. Aka kawo kuma wata motar da zata dauki kawayenta. Ya kira ta yace ta fito su tafi, ai kuwa duk su fanna suka taho rakiya da kuma tsegumi. Suka hango motar daya zo da ita, tun daga motar suka fahimci cewa yau a shiryen sa yake, Al- Mustapha ne a seat din driver, kuma dama yana daga cikin samarin Murjanatu dan haka ta bude seat din kusa dashi ta zauna. Diyam kuma aka bude mata baya inda Sadauki yake zaune ta shiga ta zauna kusa dashi aka rufe kofar. Adama ta zagaya side din da yake tayi knocking window, ya sauke glass yana kallon ta yace "ya akayi?" Tace "yaya Aliyu dan Allah in shigo? In zauna a tsakiyar ku kaga waccan motar kamar ba zata ishe mu ba" ta karashe maganar tana kokarin yin dariya, bai ce mata komai ba sai tayi winding up glass din yana murmushi yace "yaran nan so suke su mayar dani kakan......" Sai kuma maganar ta makale ya kasa kammalawa saboda juyo wa da yayi suka hada ido da Diyam da take kallon sa saboda kyawun da yayi mata ko kuma maybe dan bata saba ganin sa da manyan kaya bane ba?. Bakin sa ya motsa a hankali amma Diyam bata ji mai yace ba, sai ta tambayeshi. Yace "tasbihi nake yi ga Allah, mahaliccin kyawawan surori" ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannunta sai yabi hannun da kallo, idanunsa suka sauka akan tsararren kunshin da yake kwance akan farar fatarta. Yace "wadda tayi kunshin nan ko nawa aka biya ta taci kudinta" Diyam tayi masa fari da ido tace "harda kitso tayi min" yace "may I see it?" Ta makale kafada tace "not today" yace "gobe ne dai kadai ta rage min. Amma ban sani ba ko zan kai goben? Dan wannan abin da kike min da ido bana jin zai barni in yi bacci yau" dariya suka ji Murjanatu tayi daga gaba, Sadauki ya kalle ta yace "ko kiyi shiru ko kuma a sauke ki ki hau napep" Al-mustapha ya dan waigo yace "amarya, ni ko gaisawa ma ba'a bari munyi dake ba" Sadauki yace "hey! Juya ka kalli gabanka, don't go about looking at something that is not yours" Murjanatu tace "an fara, yau zanga yadda za'ayi wannan taron" Sadauki yace "kinyi shiru ne ko kuma ayi packing ki fita?" Al-Mustapha yace "in ka sauke ta sai dai ka zagayo ka ja motar ka da kanka" Diyam dai tana jinsu tana ta murmushi. Ita kanta tasan tayi kyau kuma tasan yau za'ayi rigima da Sadauki duk kuwa da cewa komai nata a rufe yake fuskarta da hannayenta ne kawai a bude.
Suna packing ya miko mata hannu yana murmushi, ta makale kafada sai ya langwabe kai yace "Please" sai ta saka hannunta a cikin nasa, ya juya hannun sannan ya saka fingers dinsa a tsakankanin nata yana kallon yadda hannayen nasu suka yi kyau sosai together, perfect match for each other, kamar dama a haka aka halicce su.
Suka fita suka jera a tare suka tafi gurin da aka tanada saboda su, Diyam idanuwanta a kasa tana jin tsananin kunyar mutanen gurin. Tun daga bakin mota ake turara su da turaren wuta iri iri masu kamshi kala kala har suka je suka zauna sannan aka sake zagaye su da turarukan wuta. Nan take aka fara gabatar da shagali wanda ita Diyam ba fahimta take yi sosai ba saboda hannun da yake rike da nata kuma tayi dabarar kwacewa ta kasa. Ga kuma idanuwa guda biyu a kanta suna kallon duk wani motsi nata. Ta dan kalle shi tace "hey.......stop looking at me like that" ya daga gira yace "ko? Saboda me? Baki san ni maye bane ba? Ko baki da labari?" tayi murmushi tace "kar ka bari Inna taji ka" yace "am serious fa, kin dauka wasa nake yi ko? Ina tausaya miki ranar da zaki fahimci a inda tawa maitar take" ta sake kokarin karbar hannunta ta kasa. Yace "wannan hannun tunda kika bani shi kuma ya zama nawa, sai sanda nayi niyya zan baki aron sa" ta sake cewa "ni ka daina kallo na" ya bata rai yace "ba fa ke nake kallo ba, lips dinki nake kalla wondering what they taste like" taji kamar zata nutse a gurin, tace "wayyo Ummah".
Anyi rawa sosai, rawar barebari, yan'uwa da abokan Sadauki ne suka fara yi sai kuma na Diyam sukayi joining dinsu suna koya, sai kuma suka koya musu suma irin tasu rawar ta fulani. Amma Diyam ko motawa daga seat dinta Sadauki bai bari tayi ba ballantana ta saka ran yin rawa. Duk wanda yazo gurin su daukan hoto kuwa indai namiji ne to Sadauki zai ce masa "zagayo ta side dina" sai suyi dariya gaba daya. And Diyam wondered, anya kuwa Sadauki zai barta ta koma school?
Sai after 11 suka tashi, shima dan dare yayi ne ba wai dan sun gaji ba. Da kyar Sadauki ya bar Diyam ta shiga gida, shi ji yake kamar su yi ta zama a mota har gari ya waye, gani yake kamar gobe ba zata yi ba.
A ranar duk su biyun babu wanda yayi bacci. Kwanciya suka yi da wayoyinsu a kunnuwansu suna bitar rayuwar su, yarintarsu, rabuwarsu, da kuma sake haduwarsu. Diyam ta bashi labarin sanda take lekensa ta window lokacin da Saghir ya kawo shi gidan su. Yace "ohhhh, ashe shi yasa naji kamar zan fadi, ashe idanuwa ne suka yi min yawa". Sai da dare ya raba sannan suka yi shawarar gabatar da salloli da addu'ar neman alkhairi a cikin sabuwar rayuwar da zasu shiga gobe. A kan sallayinsu suka karasa kwana. Sai da suka yi sallar asuba sannan Diyam ta kwanta, amma kuma ba wai bacci tayi ba likimo kawai tayi tana jin su Humairah dasu Murjanatu suna ta hirarrakin su suna dariya har gari ya waye. Bata tashi ba sai da Hannatu Sokoto ta zo ta tashe ta tana cewa "gwara da kikayi baccin ai, shi bacci yana kara fito da kyawun mutum" sai ta ajiye mata special dahuwar kazar da tayo mata daga gida, ta zauna ta cinye tas sannan ta kora da tsumin maman fareeda (07033742833), tana ci suna hirar su da Humairah suna kuma jiyo hayaniya a tsakar gida maza suna ta shirye-shiryen tafiya daurin aure. A lokacin Bassam ya kira Humairah ya gaya mata ya shigo gari amma ya zarce venue din daurin auren, Alfurqan Mosque.
Kafin ta gama Hannatu Sokoto ta shirya mata ruwan wanka dan haka ta shiga tayi wanka tafito, tana zama a gaban mirror message din Sadauki ya shigo wayarta.
Dear Mrs Abatcha
Alhamdulillah. I am now yours and you are mine.
Signed
Mrs Abatcha
Ai mun gama ko?
[3/24, 10:36 PM] +234 703 589 5826: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Seventy Two & Three : A Perfectly Perfect Night
I was thinking about covid-19. Sai nake ganin da ace al'ummar duniya duk sun sani kuma sun bi umarnin fiyayyen halitta (S.A.W) a inda yake cewa idan annoba tazo guri, wanda yake ciki kar ya fita wanda kuma yake waje kar ya shiga, da an bi haka da cutar bata kai matsayin da take a yanzu ba.
Chinese basu san wannan umarnin na annabi ba, amma mu munsani dan haka me yasa mu ba zamu bi ba dan dakushe yaduwar cutar?
Stay safe
Stay at home
Hannatu Sokoto da muka yi magana a last episode wata member ce ta group dina na WhatsApp, amma bata gyaran jiki, na saka sunanta ne kawai to honor her and for fun.
But Maman Fareeda is real, duk mai so zata iya kiranta.
Ta dora wayar a kirjinta ta lumshe idonta taba jin hawaye yana taruwa a idonta, sai data fahimci da gaske kukan zata yi sai ta mike da sauri zata shiga toilet sai suka hadu da Humairah tana fitowa ita kuma, ta tsaya tana kallon ta tace "wai kuka kike yi?" Sai Diyam taji sauran kukan data rike ya taho gabaki daga, ta juya bayanta tayi facing bango tana kokarin share hawayenta. Humairah ta fara dariya, abinda ya jawo hankalin yammatan da suke dakin suka taso suna tambayar abinda ya faru. Hannatu Sokoto ta shigo lokacin da Diyam take kokarin ture Humairah zata shiga toilet sai Hannatu tace "wai shiga kike so kiyi ki zauna a kan sassanyan tiles kiyi kuka zaki a toilet din? To dakata, bara in kawo miki garwashin wuta in dumama miki tiles din sai ki zauna kiyi ta kukan" duk suka kwashe da dariya, tace "a to, ni ba kukan ne damuwata ba, ni damuwata shine zama a sassanyan guri". Da Diyam taga sun mayar da ita abar tsokana sai ta fice ta bar musu dakin. Daya dakin da yake kusa da inda suke ta shiga, wanda a da shine a matsayin dakin Sadauki sanda suna yara. Ta shiga ta rufe kofa ta jingina a jikin kofar tana kallon dakin da yanzu yaje a gyare tas amma babu komai a cikinsa sai carpet da akwatunan su Murjanatu da aka kawo dakin dan kar wancan ya cika da kaya. Ta rufe idonta hawayen yana cigaba da zarya a kuncinta, hawayen da ita kanta tasan na murna ne ba wai na bakin ciki ba. Sai yau ta tabbatar da cewa ana iya yin kukan dadi.
Ta bide idonta tana tuno lokacin da take shigowa dakin tayiwa Sadauki kaca-kaca dashi, ta yayyaga masa takardun sa ta hargitsa masa shinfidar sa, ko kuma tazo ta kwanta a shimfidar tayi ta baccin ta, amma bai taba ko daga mata murya da sunan fada ba. Da kuma sanda take zuwa ta saka shi a gaba yayi mata homework ko da kuwa shi baiyi nasa ba. She never thought da gaske one day zai zama mijint, duk kuwa da cewa tun kafin tasan ma'anar kalmar miji take cewa shine mijinta.
Anan dakin ta kwanta akan carpet. Ta lumshe idonta sai kuma tayi murmushi tana jin duk sauran problems dinta na rayuwa suna melting away. Ta zama matar Sadauki.
Tana nan kwance Rumaisa tazo gidan, ita ta shigo har dakin ta fita da ita palo sannan suka kafa tsokanar ta wai tayi kukan aure, sai kuma Falmata tayi mata kwalliya ta musamman aka shirya ta cikin tsadadden farin lace din da ta tanada saboda yau wanda tayi musu anko ita da Subay'a. Sannan suka fara daukan pictures, suka dauka anan sannan ta shiga part din Inna can ma suka daddauka da mutane ana ta taya ta murna da kuma yaba kyawun da tayi. Masu selfie nayi a waya, cameraman ma yana yin nasa.
Sai kuma ga sanarwar cewa ango yazo zasuyi pictures da amarya, nan kuma Diyam taji ita duniya babu wanda take kunya kamar Sadauki, ita sam bata dauka zaizo yin wani hoto da ita ba. Sai ta wayance ta koma part din Umma tayi zamanta amma tana jin alamar ya shigo kuma sai ta mike ta tsaya daga bakin kofa tana lekensa, yayi kyau sosai, a idon Diyam sai taga bata taba ganin mutum mai kyau irinsa ba a rayuwar ta, yayi shigar farin yadi kal dashi tun daga hula har zuwa takalmi fuskarsa dauke da annuri wanda yake bayyanar da farin cikin da zuciyarsa take ciki.
Tana kallo ya shiga gurin Inna, da alama gaisheta yaje yayi sai kuma gasu sun fito tare hannunsa rike da Subay'a, suka tsaya a tsakar gida suka yi pictures sai kuma Inna ta sa baki ta kira ta amma sai ta makale taki tafiya, sai Subay'a ta taho part din da sauri "mommy kizo kiga yadda uncle Sadauki yayi kyau, kizo kuyi hoto kafin ya tafi" Sa'adatu tayi dariya tace "chafdi, mai fitar da yaya Aliyu daga gidan nan ba tare da yaga Diyam ba ai babu shi a duniya". Diyam ta kama hannun Subay'a amma kafin tayi magana sai gashi a tsaye a bakin kofa yana kallon ta, tayi saurin sunkuyar da idonta tana mamakin rashin kunya irin ta Sadauki da har ya keto mutane ya taho gurinta. Sai ya tako cikin tafiyar kasaita ya zo har gabanta ya tsaya yace "my wife" sai ta saki hannun Subay'a ta rufe fuskarta da sauri tana murmushi, taji yammatan gurin sun dauki shewa sannan kuma wata mata a tsakar gidan ta rangada guda.
Sai kawai ji tayi ya kama hannunta ya fara jan ta zuwa waje, a dole ta nutsu ta bishi amma fukarta a kasa, ta kasa daga ido ta kalle shi duk da yadda zuciyarta take son ganin cikin idonsa, balle kuma ta kalli sauran jama'ar gurin. A kayi ta hotuna, suna tsaye wannan yazo a dauka wancan ma yazo a dauka har saida aka gama sannan ya kuma jan hannunta zuwa dakin daya dauko ta ya zaunar da ita yace da Murjanatu "kar kuda ya taba ta" sannan ya juya ya fita, sai a lokacin ta dago kanta ta bi bayansa da kallo, tana kallon yadda yake taking steps one after the other.
Sai da ya fita sannan kuma suka zo suka zagaye ta suna tsokana 'mai tsoron miji' 'ta kasa kallon mijinta' 'dama fulani haka kuke?' ita dai bata kula suba sai ta karbi wayar Asma'u wadda ta lura tana ta daukan pictures "kawo inga pictures din da kika dauka" ta bude hotunan da sauri tana scrolling tana neman wanda yafi fitowa sosai har ta samu, sai ta kwanta ta dunkule a guri daya ta zuba wa fuskarsa ido tana murmushi.
Humairah ce ta katse mata daydreaming dinta, tace "Bassam yazo fa, yana waje" sai ta ajiye wayar ta mike da sauri, ta kira Asma'u "akwai bako a waje, ki bude masa dakin baki ki kai shi can, sai kizo ki kai masa abinci da ruwa" sai Asma'u ta saka mayafin ta ta fita, amma kuma wajen a cike take da mutane maza da mata na ta gaggaisawa, sai kawai ta tsaya tana bin su da kallo tana son ta gani ko zata iya gane waye jikan sarkin Abuja a cikin su. Yana cikin mota ya hango ta fito daga gidan da yake tunanin nan ne gidan su Diyam, farko ya dauka Diyam din ce amma kuma yasan Diyam ba zata fito kofar gida cikin mutane ba tunda yau aka daura mata aure, sai kuma ya lura wannan bata kai Diyam maturity ba amma suna kama sosai sai fari da Diyam ta fita. Yana ganin yadda take yamutsa fuska, dafa dukkan alama zata yi tsiwa. Nan sai zuviyar shi ta bashi cewa wannan Asma'u ce, only sister din Diyam. Sai ya bude kofar motar ya fita yana kallon ta, sai yaga ta juyo ta kalle shi kamar wadda aka kira, suka tsaya suna kallon kallo sannan sai yaga ta doso shi. He likes yadda take tafiya, ya tabbatar bashi kadai ba sauran mazan da suke gurin ma ta ja hankalinsu. Ta tsaya dan nesa dashi kadan tace "Bassam?" Ya gyada kai yace "Asma'u ko?" Bata amsa ba sai tace "Adda tace ka shigo ciki" muryarta tayi masa dadi, sautin fulani. Sai ta juya tayi gaba. A zuciyarsa baya son shiga dan shi da a son ransa ne daga gurin daurin auren zai komawarsa dan dai Humairah ta nace sai yazo yayi wa Diyam Allah ya sanya alkhairi "dan ita kazo fa, ai ya kamata ku gaisa ko minti daya ne". Amma yanzu da Asma'u take gabansa tana tafiya sai yaji cewa binta a baya ya zama wajibi a gare shi. Ya zare key din motar ya bita cikin gidan yaga ta tura kofar wani daki kafin a karasa shiga cikin gidan ta ce masa "Bismillah" sai ya shafa kai yana kallonta, shi ai ya dauka tare zasu shiga amma sai yaga ta juya ta shiga cikin gida ta barshi a tsaye. Wannan yasa dole ya shiga dakin ya zauna ya kama daddanna phone dinsa. Amma zuciyarsa tana tunanin ko zata dawo?
Bai jima ba sai gata ta shigo da sallama, tayi masa shimfidar abinci can gefe kadan sannan ta fara jera masa kayan ciye ciye iri iri har ta gama amma shi idanunsa a kanta suke ba wai a kan abinda take yi ba. Itama kuma tana jin idanuwan nasa akanta, dan kada ne ya rage bata yi barin abincin da take shiryawa ba. Sai data gama sannan ta mike, yayi saurin pretending kamar wayarsa yake dannawa tace masa "Bismillah, ga abinci. Adda zata fito ku gaisa" ya ajiye wayar sai kuma yace "thank you. Amma ki zauna mana kafin tazo din ko. Kinga ai sai ki tayani hira ko?" Sai ta dauke kanta, wannan mutumin neman magana yake yi kuma. Shi baisan zuciyarta bugawa take yi da wannan kallon nasa ba? Ga shi ya cika kyau da yawa.
Ta girgiza kai tace "ina yin wani abu ne a cikin gidan" yace "Please, minti uku fa kawai. Kinga ni ban iya cin abinci ni kadai ba" he is a playboy, tayi deciding a zuciyarta, sai ta doshi kofa ba tare da ta kuma ce masa komai ba, har ta daga labule sai taji yace "an a lobbo sanne, Asma'u" sai ta juyo tana kallon sa, bata taba tsammanin bafulatani bane ba, mix din shi yayi yawa. Sai ta samu kanta da yin murmushi tace "miyetti" amma duk da haka bata zauna ba ta fita. Bata shirya yin wasa da zuciyarta ba.
Bai ci abincin ba tunda yaci a reception din da suka wuce daga gurin daurin aure. Aliyu ya gane shi kuma ya karbe shi sosai. Sai ya zuba juice ya sha, sannan ya koma ya zauna ana fatan Asma'u ta biyo yayarta su dawo tare. Amma sai ga Diyam tazo sanye da hijab tare da Humairah, suka gaisa tayi masa godiya shi kuma yayi mata fatan alkhairi sannan yace zai tafi. Yace "Asma'u tazo ta kwashe kayan abincin nan mana" Diyam tace "no, kar ka damu kayi tafiyar ka kawai, an jima za'a kwashe su" yace "a dauke dai yanzun ai sai yafi ko?" Ta tsaya kawai tana kallon sa sai yayi murmushi, ta daga gira tace "Asma'un?" Yace "sallama kawai zamuyi ba wani abu ba, dan Allah ki turo ta" Humairah tace "kar ka damu kani na, har phone number dinta zan karbo maka" yace "kash, shi yasa nake yinki over yayata". Suna shiga ciki Humairah ta kwalla kiran Asma'u "kije kuyi sallama da kani na" sai Asma'u ta tura baki tana kallon Diyam, Diyam ta daga kafada tace "ina ruwa na, in kina son zuwa kije mana" kamar ba zata je ba, sai kuma ta zari mayafi ta tafi.
Bayan sallar azahar sai ga yan kawo lefe. Anan gida ya hargitse gaba daya ashe wai al'adar bare bari ne sai an daura aure ake kawo lefe. Akwatuna akwatuna, ga kuma wasu kayan a jakankuna. Lefen yakunshi akwatunan amarya set biyar, akwatin maman amarya (inna), akwatin kannen maman amarya(innaso), akwatin yan uwan baban amarya (bawaso), sai sisters (Asma'u) sai na kawayen innarta (ya samma soye) sai na matan waliyinta (su Hajiya Babba da yalwati), sai matan kawunnanta (kamu rawaye. Matar kawu isa da kuma su Hajiya Babba again)sai na yan bayarwa (na rabo) sune a jakankuna, sai na wadda tayi mata kiso (Hannatu Sokoto) an bata atampopi da kudi. Tun a kofar gida aka fara nunawa maza tukunna aka shiga dashi cikin gida gurin su Inna. Wannan duk al'ada ce ta barebari. Fulani sai suka tsaya kallo da mamaki, wanda baya kusa ma sai da aka kira shi a waya yazo ya kashe kwarkwatar idonsa masu video coverage suna yi masu dauka a hotuna suna yi.
Diyam kuwa tana cikin daki ta rufe kanta, ita kunyar yan uwan Sadauki take ji gashi taji ance gar da Yaya Ladi da yan'uwanta aka zo. Ana cikin haka sai ga Fauziyya ta shigo gidan tana rarraba idanu, da goyon yarinya a bayanta. Irin yadda gidan ya chanza rake kalla ga kuma uban kayan data gani mutane suna ta gani wanda ko ba'a fada ba tasan lefen Diyam ne. Amma data tuna wanda aka ce shi ya auri Diyam din sai taga wannan ba komai bane ba.
Ta tambaya aka raka ta har dakin da Diyam take. Diyam tana zaune da waya a hannunta tana kallon kiran Sadauki yana shigowa one after the other amma ta kasa dauka. Sai ganin shigowar Fauziyya tayi, ta tare ta da fara'a sosai sai Fauziyya tace "fushi nake yi fa, kin manta dani kuma wayar ki bata shiga kwata kwata" Diyam tace "Allah sarki, ba haka bane ba wallahi. Bana kasar ne ina UK ina karatu" Fauziyya ta gyada kai kawai. Ta tuna lokacin da Saghir ya fita da ita honeymoon America, a lokacin tana jin kamar duk duniya babu ya ita, tana yiwa Diyam dariya a ranta tana ganin cewa Diyam din tayi asara ashe ita asara zata samu. Rayuwa ta juya mata baya gabaki daya, komai ya tsaya mata. Dama a gurin maza take karbar yan kudade tana biyan buƙatar ta yanzu kuma tunda tayi deciding haifar cikin Saghir shikenan ta rasa costumers, bayan ta haihu kuma tana kallon fuskar jaririyar ta taji cewa ta gama yawon ta zubar kenan. Yan uwan Saghir sam basa taimaka mata kuma ta fahimci suma kansu taimakon suke nema, sun dai je sunga baby sanda ta haihu sai kuma Hajiya da take dan kiran ta tana tambayar lafiyar Anisa. Jin dadin ta daya ta samu aikin koyarwa a wata private school anan layin su.
Diyam ta karbi Anisa tace "Masha Allah. Kinga dai yaran nan gaba ki dayan su kamar baban su suke yi". Fauziyya tayi murmushi jin an yabi hasken rayuwarta, tace "ni fa bansan ma zakiyi aure ba, Hajiya Babba ta gaya min ana bikin kannen Saghir shine na shigar musu to a can ne nake ji ashe tare da naki ake yi" Diyam tayi murmushi kawai. Fauziyya tace "Allah ya sanya alkhairi" Diyam tace "ameen".
Ta dauko wayarta a karo na ba adadi tana kallon kiran Sadauki yana shigowa. Sai daya katse sannan tayi murmushi. Sai kuma ga Murjanatu ta shigo ta mika mata waya tace "yaya Aliyu yana kira" Diyam ta ture wayar tayi mata sighing "kunya" sai Murjanatu tayi dariya ta fita tana masa magana. Diyam ta kuma daukan wayarta sai sakon shi ya shigo.
Tunda Sadauki ya fita daga gidan yake kokarin ganin yayi waya da Diyam, yana so yaji muryarta. Da farko mutane ne suka hanashi samun sukunin yin hakan, daga baya kuma da ya samu ya kira sai taki dauka. Yayi yayi amma sai dai tayi ta ringing ta katse ba zata dauka ba. Da farko ya dauka bata kusa da wayar ne dan haka ya kira Murjanatu ya ce ta bata, amma sai taki karba, yana jin Murjanatu tana yi mata dariya sannan tace masa "yaya Aliyu kunyar ka fa take ji wai" sai yayi murmushi ya samu secluded guri ya zauna ya shiga WhatsApp ya tura mata "ke fillo" shiru at first, sai later kuma ta aiko masa da reply na emoji na harara. Yayi dariya shi kadai ya rubuta
"wai da gaske kunyata kike ji? Tun yanzu?"
"Kunya kuma? Wacce irin kunya?"
"Hmmm, really? So tell me, me yasa kika rufe idonki da na shigo gida? Me yasa kika ki yi min magana kuma me yasa kika ki daukan phone dina?"
"Bafa kunyarka nake ji ba. Fushi nake yi"
"Poor me, laifin me nayi?"
"Ba kai bane ba ka hanani rawa a gurin wushe-wushe" (imojin shagwaba)
Dariya "okay, yanzu dai rawa kike so ko?"
"Uhmmmm"
"Shikenan. Kina bina bashin rawa"
"Da gaske?"
"Yes, but just me and you. Tonight."
Tayi logging out da sauri. Feeling very nervous. Ina ma dai za'a daga kai amaryar nan zuwa gobe? Ko jibi?
Babu abinda aka fasa. Magrib tana yi aka saka ta ta sake wani wankan, wannan karon babu kwalliyar da aka yi mata sai atamfar da ta saka blue mai adon pink and white flowers. Sannan aka nada mata laffaya fara mai shara shara da adon blue and pink flowers. Humairah da Murjanatu ne suka shirya ta tsaf, sannan suka kamo hannunta suka taho da ita dakin Inna inda anan iyaye suke, Mama, Inna, Hajiya Rabi (matar Kawu Isa) sai kuma step sisters din su Inna su biyu. Ta zauna a tsakiyar su ta nannade kafafuwanta suka fara yi mata nasiha, idan waccan tayi ta gama sai waccan ta dauka itama tayi nata. Suka gama sannan suka yi doguwar addu'a suka shafa. Lokacin masu daukan amarya suka zo, yaya ladi, Mama (matar baban Sadauki) sai kannen Papa mata su biyu.
Suna zuwa aka fara nuna musu kayan garar da aka hadawa Diyam. Komai da komai na kayan abinci an siya in abundance, ga kuma kayan gara dangin su alkaki, nakiya dubulan, gireba, cincin da sauran su komai a cikin manyan containers. Sai daaka nuna musu kayan suka gani suka saka albarka sannan aka zuba su a mota aka tafi dasu gidan Alhaji Bukar.
Diyam tana jinsu suka zauna suna ta barkwanci dasu Mama, sai taji dadin yadda taji ana magana tsakanin Inna da yaya ladi. Sai da suka gama sannan aka sake feshe ta da turare sannan maman su Murjanatu ta kama hannunta ta mike. A lokacin Subay'a ta shigo "mommy! Mommy wai aunty Asma'u tace tafiya zaki yi ki barni, Mommy ai tare zamu tafi ko?" Mama tayi saurin dauke ta ta fita da ita daga dakin tana ta rusa kuka, wannan shi ya kawo hawaye idon Diyam. Tun sanda za'a kai kayanta gidan Sadauki ta fara hada na Subay'a amma Inna tace "ba ki da hankali. In ma zaki tafi da ita ba yanzu ba. Kuma ke da zaki koma karatu menene amfanin tafiya da ita?"
Ta fara kuka a hankali maman su Murjanatu tana tsokanar ta. Ita kuma tsokanar kara mata jin kunya take yi. A haka suka fita tana jiyo kukan Subay'a suka shiga mota ita da maman su Murjanatu da Mama, almustapha kuma yana driving suka tafi, sannan sauran motocin daukan amarya suka biyo bayan su.
Duk da fuskar ta tana rufe amma tana gane inda suke har suka je, a lokacin ta daina kukan Subay'a, suka fito aka saka ta tayi basmala ta kuma shiga gate din gidan da kafar dama sannan ta sake repeating sanda zata shiga cikin gidan. Tana shiga kamshi ya kaiwa hancinta ziyara, kamshi mai dadi, kamshin Maiduguri.
Sama suka hau da ita suka kaita har cikin bedroom din da yake nata suka zaunar da ita, suka sake yi mata nasiha sannan suka tafi. Sanda Mama zata tafi sai tace "Diyam yau ba zaki rike hannuna kice kar in tafi in barki ba?" Sai Diyam ta samu kanta da yin murmushi tare kuma da jin kunya.
Humairah ce ta fara zuwa tayi mata sallama saboda a daren zata bi flight zuwa Abuja, daga nan kuma mutane suka fara watsewa a hankali gidan ya fara yin shiru. Su Murjanatu, Rumaisa da Asma'u ne karshen tafiya, sai da suka gyara mata duk inda aka bata suka kara tabbatar wa ko ina na gidan yana kamshi sannan suka yi mata sallama. Murjanatu tace "wato ko dan tayin nan ba zaki yi mana ba ko? Irin ki dan ce 'ku zauna ku kwana mana tunda dare yayi?" Diyam ta matsa mata guri tace "Bismillah, zo ki kwanta a kusa dani" Rumaisa tace "har na tausaya miki Murjanatu. Ni dai kunga tafiya ta maigidana yana waje yana jirana tun dazu" Adama tace "kunsan wani abu? Yaya Aliyu fa yana cikin gidan nan duk wannan abin da ake yi. Naje part dinsa naji kofa a rufe kuma an bar key a jiki ta ciki" Murjanatu ta mike da sauri ta dauki handbag dinta "Allah ya bamu alkhairi" duk suka yi mata dariyar ta fiya tsoron Sadauki sannan suka fita gabaki dayan su a tare.
Tunda Diyam taji cewa Sadauki yana cikin gidan sai taji duk nervousness dinta ya dawo. Wayar ta har zamewa take yi daga hannunta tana faduwa kasa. Ta mike daga kan gadon tana karewa dakin kallo sannan ta kalli kanta a madubi kawai sai taga tayi wani irin kyau har kyalli fatarta take yi duk kuwa da cewa babu ko digon kwalliya a fuskarta. Ta gyara zaman laffayar ta sannan ta bude kofar balcony din daya ke cikin bedroom dinta ta fita tana kallon yadda sama tayi tas sannan taurari suka cika ta. Sai tayi murmushi tana jin wani irin farin ciki a zuciyarta sannan ta koma cikin dakin ta murda kofar fita waje ta leka empty corridor sannan ta fita da sanda kamar marar gaskiya ta bude dakin da yake opposite nata taga shima irin nata ne sai girma da wancan dakin yafi wannan sai kuma banbancin colors.
Shirun da gidan yayi ne yasa ta jiyo kamar motsin takun mutum yana tahowa inda take, sai tayi sauri ta karasa shiga cikin dakin ta haye can karshen gado ta rufe fuskarta da laffayar jikinta. Taji an bude kofar corridorn an shigo, sannan heavy footsteps suka taho zuwa dakin da take yayinda bugun zuciyarta ya karu, taji shigowarsa sannan taji kamshinsa.
Ya dan jima a tsaye yana kallonta sannan ya karasa shigowa ya hawo kan gadon ya zauna akan kafafuwansa a gabanta yana kallon fuskarta ta cikin shara sharan laffayar ta sannan murya can kasa yace "Sadiyam"
Ta saka hannayenta da sauri ta kara rufe fuskarta tana murmushi. Sai ya saka nasa hannayen a saman nata yana shafa wa yace "hannayenki suna da kyau, kunshin yayi musu kyau sosai". Tayi sauri ta juya tana kallon side. Sai yayi dariya yace "yanzu ni fuskar matar tawa ba za'a barni in gani ba?" Tace "sai ka biya tukunna" yayi murmushi ya jawo rose flower da ya shigo da ita a soke a bayan wandonsa a jikin rapping din an rubuta "loving you is all I ever know" ya mika mata ta karba da hannun dama, sai kuma ta miko masa hannun hagu tana murmushi, sai ya tuna lokacin da suna yara in ya bata sweet a hannu daya sai ta miko masa daya hannun shima ya bata.
Sai ya saka hannu a aljihu ya dauko chocolate din twix ya saka mata a hannun. Yace "shikenan na biya?" Bata ce komai ba sai ya saka hannu biyu ya bude fuskarta ya sauke laffayar har kafadun ta. Ta dago kai a hankali suka hada ido yayi mata murmushi mai kyau sai ta kuma sunkuyar da idonta kasa itama tana murmushi ta fara bude chocolate din daya bata amma maimakon ta kai bakin ta sai ta kai nasa bakin. Ya rike hannunta a cikin nasa ya juyar dashi zuwa bakin ta ta fara gutsira sannan ya juyo da hannun zuwa nasa bakin shima ya gutsira.
Sai da suka gama cin chocolate din su sannan ya jata suka mike a tare yace "let's pray". Dakin da aka kaita suka koma, shi ya fara shiga toilet yayo alwala sannan itama ta shiga. Sai ya ja musu jam'i a gurin da aka tanada a dakinta musamman dan sallah. Sukayi sallar isha'i tunda duk su biyun basu yi ba, sannan kuma suka yi sallar raka'a biyu ta godiya ga ubangiji a bisa cikar burinsu sannan ya juyo yana kallonta suka fara jero adduoi. Farko sun fara gabatar da godiya ga Allah sannan suka yi salati ga fiyayyen halitta (S.A.W) sai kuma sukayi addu'a ga mahaifansu da suka riga mu gidan gaskiya, Baffa da Ummah, suka roka musu gafara da ragamar ubangiji, sannan kuma suka yi addu'a ga mahaifansu da suke a raye tare da fatan tsahon rai a cikin kyakykyawar rayuwa. Sai kuma sukayi wa kansu addu'a, suka roki tabbatar alkhairin dake cikin auren su sannan suka roki tsari daga sharrin dake cikinsa. Suka yi addu'a ga yayan su, twins da suka rasu da fatan su zamo masu ceton mahaifansu sukayi addu'ar rayuwa mai kyau ga Subay'a sannan sukayi doguwar addu'ar a kan neman zuri'a ta gari mai albarka a tsakanin su.
In Sadauki ya dauko addu'a Diyam tana amsa masa da ameen in ya gaji sai ita kuma ta karba ta cigaba shi kuma yana amsa mata. A haka har suka kammala suka shafa.
Kanta yana kasa tana kallon hannunta amma tasan ita yake kallo duk da bata kallonsa, sai ta murguda masa baki, yace "ni ko?" Ta daga gira. Ya mike tsaye yana cewa "zakiyi bayani ne yarinya" sai ya zauna a kan gado sannan kuma ya tafi da baya ya kwanta rigingine ya lumshe idonsa, tana zaune still a inda ya barta tana kallon sa ya jima a haka sannan ya juyo inda take ya bude idonsa a cikin nata yace "na gama komai ko?" Ta mike tsaye tace "sauranka kaza" yayi kamar zaiyi kuka "Please ni kam a yafe min kazar nan mana. Kinga na gaji fa, ga kuma dare yayi" ta makale kafada tana kallon sa. Ya mike zaune sannan ya mike tsaye yace "shikenan, in na fita waje aka sace ni kar kiyi kuka" ya juya ya fita ya barta ita kadai.
Kayan jikinta ta cire, ta shiga toilet tayi refreshing sannan ta fito ta zauna tana shafa mai me sassanyan kamshi a duk ilahirin jikinta, tana yi tana kallon kofa a tsorace har ta gama ta saka underwears dinta ta kuma saka riga da dogon wando na bacci, rigar a sake take sosai amma ta tsaya ne a saman cibiya, wandon kuma dogo ne har kasa sai dai ya kama saman sosai ya kuma bude sosai daga kasa, sannan ta hau kan gado ta dauko wayarta tana duba pictures. A lokacin ne sakon Sadauki ya shigo wayarta.
"I owe you a dance, da kuma kazar amarci. Meet me in the garden please"
Ta rufe idonta ta bude tana jin kamar zatayi zazzaɓi. Sai kuma ta mike ya dauki hijab ta saka masa turare ta saka sannan ta fita a nutse. Ta sauka kasa ta cikin corridorn daya raba palonsa na kasa da nata, inda anan ne stairs din hawa sama suke kuma anan ne front door da back door na gidan suke. Ta murda back door din ta fita doguwar veranda sannan ta sauka daga kan steps guda uku ta shiga garden. A tsaye ta hango shi, ya chanza dogayen kayan jikinsa zuwa shirt da wandon. Yayi shimfidar karamin carpet akan grass carpet din gurin ya zuba throw pillows akan carpet din sannan ya zagaye shinfidar da candles masu kyalkyali, a gefe kuma ga food warmers guda biyu da fruits da aka yi arranging dinsu a shape din heart. Ya taho ya tarye ta yana murmushi, ya jawo ta zuwa jikinsa ya rungume ta ta baya yana saka fuskarsa a ramin wuyanta yace "ga kaza an siyo, sai me kuma?" Ta juyo tana kallonsa tace "saura rawa ta" yace "with pleasure" sai ya zare hijab din jikinta ya ajiye a gefe ya juyo yana kallonta lokaci daya ya dauke numfashi saboda abinda ya gani, ya sani cewa tana da good figure but bai san cewa it is this good ba, ya jima tsaye yana jin tamkar ya samu paralises ita kuma tana ta sussunne kai, sai ya saka hannunsa na dama a waist dinta ya jawo ta sosai ya hade jikin su, daya hannun kuma yana shafo tun daga kan kananan kitsonta zuwa gadon bayan ta zuwa hips dinta, ta kwantar da kanta a tsakiyar kirjinsa tana jin cewa tamkar a nan ne aka halicceta, ta zagaye shi da hannayenta, tare suka sauke ajjiyar zuciya. Sai ya fara taking steps tare da ita a jikinsa, tamkar jikin nasu guda daya ne, three steps forward, two steps back.
Ta lumshe idonta tana jinta kamar tana floating a cikin iska, kakkarfan jikinsa like a shield to her, his heart beat like a music to her ear. And he sang to her a cikin kunnen ta:
I found a love for me, Darling just dive right in, And follow my lead, Well I found a girl beautiful and sweet, I always knew you will be the someone waiting for me......
'Cause we were just kids when we fell in love, Not knowing what it was, I will not give you up this time....
But darling, just kiss me slow, your heart is all I own, And in your eyes you're holding mine......
Well I found a woman, stronger than anyone I know, She shares my dreams, I hope that someday I'll share her home, I found a love, to carry more than just my secrets, To carry love, to carry children of our own
We are still kids, but we're so in love, Fighting against all odds, I know we'll be alright this time...
Darling, just hold my hand, Be my girl, I'll be your man, I see my future in your eyes
Baby, I'm dancing in the dark, with you between my arms, Barefoot on the grass, listening to our favorite song, When I saw you in that dress, looking so beautiful
I don't deserve this, darling, you look perfect tonight.
Songwriters: Edward Christopher Sheeran.
Lokaci daya ya tsaya, ya saka hannayensa biyu ya dago fuskarta daga kirjinta suna kallon juna for some seconds sannan ya sunkuya a hankali ya dora lips dinsa akan nata. Very slowly at first, very lightly that she hardly felt it, then it grows and it sends shiver data fara tun daga yatsun kafarta zuwa kwakwalwar ta tayi blocking dukkan tunanin ta, and she opens up to him, inviting him further in.
A hankali hannayenta da suke sarke da juna a bayansa suka fara journey upward, daga bayansa zuwa wuyansa sannan zuwa kansa suna kara jawo shi closer, giving him more, accepting more.
[3/26, 10:19 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Seventy Four : The Birthday Gift 2
Ga masu tambayar abinda Bassam ya gayawa Asma'u. Fulatanci ne, amma kunsan kamar kowanne yare fulatanci ma yana da dialect da yawa. Yayi mata magana ne da dialect din fulanin yalleman. Idan bamu manta ba Maimoon mahaifiyar Bassam yar yalleman ce dan haka dialect dinsu ya iya. Abinda yace mata shine "you are so beautiful" ita kuma tace masa "thank you".
Diyam............
Wani irin feeling na emptiness ne ya farkar da Diyam daga bacci. Tana jin tamkar jikinta ne a kwance a kan gadon amma ruhinta is somewhere else. Ta bude idonta a hankali tana kallon bedside lamp din take ajjiye a gefen gadon feeling so lonely tamkar ita kadai ta rage a duniyar. Sai kuma tayi murmushi tana lumshe ido yayin da tayi realizing abinda yasa take jin wannan feeling din shine saboda babu hannayen Sadauki a rungume da ita. Sai ta mike zaune da sauri tana kallon tafkeken bedroom din daya ninka nata a girma, sai kuma tayi sauri taja sheet ta rufe jikinta saboda tunawa da tayi babu komai a jikin nata, ta kama rarraba ido kamar wadda tayi wa sarki karya sannan ta jiyo motsin ruwa daga toilet, sai ta koma da baya ta fada kan gadon tana yar karamar dariya ita kadai kamar sabuwar shiga a gidan tababbu.
But she is not sure ko ta tabu din ne dan bata da tabbas din cewa abinda take feeling yanzu da abinda tayi feeling jiya da daddare is possible. Can it really be this good? Can one night really be worth a lifetime?
It had started with a kiss, a kiss that lasted for like an hour a tunanin Diyam dan lokaci ya tsaya mata ne tamkar yadda tunanin ta ya tsaya. A kiss that loosen up everything na Sadauki, his heart, his brain and his entire body har ya sashi yayi realizing cewa ashe dai shi ba Sadaukin bane ba.
But suddenly sai tayi breaking up the kiss, wai kazar ta zata ci, tana so ne taja ajinta for as long as she can. Ji yayi shi haushin kazar ma yake ji, haushin dukkan kajin duniya yake ji. Ina ma dai bai siyo ba? But dole ya barta ta zauna cin kazarta amma kuma bai fi loma biyu ta samu tayi ba saboda ko da second daya hannunsa bai bar jikinta ba, nema yake yi yayi mata kuka dan haka dole ta hakura da kazar amma sai da yayi alƙawarin biyanta wata.
Ta rufe fuskarta cikin jin kunya sanda ta tuna cewa she lost some of her clothing a garden din, shima kuma haka. Tayi addu'ar Allah yasa ya fita ya dauke musu kar masu aikin gidan su zagaya su gani.
Daga garden suka fara slow journey dinsu zuwa daki, branching a palo wanda ba zata iya tunawa wanne palon bane ba kamar yadda ba zata iya tuna yadda akayi suka shigo dakin ba, amma abinda take da tabbas akai shine she didn't come in with any of her clothing, except for ribbon din data daure kitson kanta dashi.
Ya rikirkice mata ya susuce mata acting as if cinye ta zaiyi gabaki dayanta, burinsa kawai ya samu ya kai inda yake son kaiwa amma ita kuma ta hana shi, making him beg, har sai da ta tabbatar he can no longer take it ita ma kuma haka sannan ta sakar masa.
The first round was wow, and it fused not only their hearts but their souls together. A gurin Sadauki it was mind-blowing and was much more than what he expected. Ya tuna da duk wahalar da yasha kafin ya samu abinda ya samu din, sai yaga cewa ashe bai ma wani sha wahala da yawa ba, ashe prize dinsa yafi wahalar da yasha yawa. He used to call her his heart, yanzu sai yaga cewa that is an understatement, kamar ya rage mata daraja ne dan ita zuciya ai a jikin mutum kawai take, ita kuwa ai ta hada ne da jikinsa da ruhinsa da kuma duk abinda ya mallaka a duniya. And then he called her his world.
A gurin Diyam mamaki abin ya barta a ciki. Dama haka abin yake? Dama haka ake ji? Can this really be possible ko kuma imagination dinta ne kawai. In haka feeling din yake me yasa ita bata taba ji ba sai yau? Bata taba jin koda kashi daya cikin goma na abinda taji yau ba. Duk rayuwar aurenta na baya ba zata taba iya tuna ranar da taje shimfidar mijinta ba tare da hawaye ya zuba daga idanuwanta ba saboda zuciyarta bata son abin. Saboda jikinta baya son abin. With every touch daya taba ta ji take kamar naman jikinta yake yanka and it hurts duk sanda ya kusanceta. Wannan yasa a lokacin take mamakin matan da suke neman mazajensu su makale musu kamar chewing gum saboda ita ta dauka yadda take ji din haka kowacce mace take ji. But now she knows better.
The second round was wow wow, much better than the first, after which bacci mai nauyi ya dauke Sadauki. Sai Diyam ta tashi ta tafi toilet da niyyar tsaftace jikinta, tana jin cinyoyinta kamar tayi tsallen kwado. Ta fara wanka kenan ya murdo kofa ya shigo, tayi saurin rufe idonta ta durkushe a gurin tana jin wata irin kunyarsa wadda dazun duk bata ji ba, ko dan yanzu ta dawo sense dinta? Baice mata komai ba sai ya sunkuya da dagata chalak ya mayar da ita daki ya dora ta a gado daga ita har ruwan jikinta sannan ya dora daga inda ya tsaya tamkar zakin daya kwana bai ci abinci ba, and she found out ita din ma ashe yunwar take ji.
Jin heavy footsteps dinsa ya katse mata tunanin ta, tayi saurin jan abin rufa ta lullube har kanta dan tana jin kamar ba zata iya hada ido dashi ba. Tana jinsa yazo ya tsaya a kanta sai kuma tayi sautin murmushin sa. Ya saka hannu ya gogo ruwa a jikin gashin sa sannan ya daga abin rufar ta ya goga mata a tsakiyar naked bayanta. Ta danyi kara tana matsawa tare da kara chukuikuyewa a guri daya. Ya zauna a bakin gadon yace "ko ki bude rufar nan ko kuma in shigo nima mu lulluba tare" tayi saurin girgiza kanta, yace "to bude in gani" ta sake girgiza kai, yace "Please, fuskarki kawai zan gani" ta fara bubbuga kafafuwanta a kan gadon cikin yana yi na shagwaba sai yace "hmmmm, baki san wannan abin da kike yi tamkar gayyata ta kike yi ba?" Sai ta daina sannan tace "ka tashi ka tafi" yace "ina zani? Dakina ne fa wannan. Ke ki tashi ki tafi" tace "dan Allah ka tashi. Na roke ka" yace "okay zan tashi amma sai naga fuskarki tukunna. Please just a glimpse" kamar ba zata bude ba kuma dai sai ta bude iyakacin fuskarta amma idonta a rufe gam. Ya jima yana kallon fuskarta sai kuma yasa hannu ya shafa doguwar jelar kitsonta and then bai san yadda akayi ba sai ganin fuskarsa yayi akan tata, hannunsa kuma yana cire abin rufar ta. Tayi saurin bude ido tana kwace bakinta daga cikin nasa "kai ba kayi wanka bane ba?" Yace da dasashshiyar murya "ban fita ba, wani wankan zan sake". Sai da kuwa ya sake din. Yana tayar da sallah ta mike ta nannade jikinta da bedsheet sannan ta fita da sauri ta tafi dakinta.
Toilet ta zarce tayi wanka a gaggauce sannan ta fito ta saka doguwar riga da hijab tayi sallah. Tana son ta koma bacci amma kuma yunwa take ji sosai dan jin cikinta take yi kamar anyi mata yasa. Ta duba agogo taga karfe bakwai, a lokacin kira ya shigo wayarta daga Murjanatu. Ta dauka da sallama Murjanatu tace "amarya, wannan saurin daukan waya haka kamar wadda ta kwana ba tayi bacci ba?" Sai kuma ta kyalkyale da dariya. Diyam tayi rolling eyes dinta tace "kina da abin cewa ne ko kuma kirana kikayi saboda credit yayi miki yawa?" Murjanatu ta daina dariyar tace "Mama ce tace in kira ki in tuna miki cewa karfe goma jirgin mu zai tashi, ki shirya zamu biyo mu dauke ki" Diyam ta dafe kanta, shaf ta manta akwai mother's eve da Maman su Murjanatu ta shirya musu yau a Maiduguri. Lallai Sadauki ba karamin formatting kwakwalwar ta yayi ba. Murjanatu tace "kin manta ko?" Diyam tayi saurin cewa "no no no, ban manta ba, baki ji har na tashi na fara shiryawa ba?"........
Ta cire rigar da tayi sallah da ita ta mayar da wata doguwar rigar wadda bata karasa har kasa ba amma ta kama ta tsam-tsam like a second skin. Yadin rigar mai layi layi ne na kalolin black, dark ash, ligh ash da white. Wuyan rigar ya bude sosai har Diyam tayi tunanin ya zama too reveling, wannan yasa maimakon ta daura dan kwalin sai ta nade shi a wuyanta stylishly yadda ya rufe kirjinta. Ta bude kofa ta fito daga dakinta a dai dai lokacin da taji kara kamar ta faduwar wani abu, followed by another sound kamar ana ɓari. Ta dan kara sauri zuwa inda take jiyo sound din sai ta ga daga mini kitchen dinsu ne da yake a sama.
Ta tsaya a bakin kofa leka ciki, abinda ta gani shi ya saka ta rufe bakinta tana hana dariya fitowa. Sadauki ne daga shi sai singlet da short, kusan duk cabinet din kitchen din a bude su ke ga kasan tiles kaca kaca da egg shells da kuma ɓawon dankali, ga mai cikin kasko a kan wuta shi kuma yana tsaye like three meters away from kaskon hannunsa da spatula yana leka cikin man. Sai kuma taga ya dauko wasu bowls guda biyu, daya ruwan kwai ne a ciki kusan rabin crete, dayan kuma danyan dankali ne guda gudan sa. Sai taga ya dauko dankali guda daya ya saka a cikin ruwan kwan sannan ya dauka da spatula ya jefa a cikin man daya riga yayi over heating.
Dariyar da take rikewa ce ta kwace mata lokacin da yayi wani tsalle zuwa karshen kitchen din. Dariyar ta ce ta juyo hankalinsa gurinta. Yayi kamar zai yar da bowl din kwan da take hannunsa amma sai yayi saurin ajiyewa ya taho gurinta yana kallon ta tun daga kasa har zuwa sama. Ta rufe fuskarta cikin jin kunya sannan ta juya masa baya, not realizing cewa ta juyo masa daya daga cikin abinda yake so a jikinta.
Yana zuwa inda take sai ya jawo ta ya hada bayanta da jikinsa, ya saka fuskarsa a wuyanta yana shakar kamshinta mai dadi sannan yace "good morning Sadiyam" bata amsa ba sai yace "wai kunyar ce har yanzu? I tot na cire ta tun jiya ashe da akwai sauranta. Ki gayawa kunyar nan ko ta rabu dake ko kuma inyi maganin ta" ta kara narkewa a jikinsa tana lumshe idonta. Ya kai baki dai dai kunnenta yace "na dauka kunyar ta tafi lokacin da naji kina cewa 'sadauki more please" ya fada yana kwaikwayon muryar ta. Tayi saurin kokarin janye jikinta daga nasa tana bubbuga kafa tace "lahh! Ni wallahi ban fadi haka ba" yana dariya yace "nayi recording fa, in baki yarda ba mu koma dakina in kunna miki kiji" kamar zata yi kuka tace "ni bana son ji, ni ban fada ba" ya dawo da ita jikinsa yace "I had the greatest night of my life yesterday. And I had the greatest birthday gift. Yanzu wish dina guda daya a rayuwa shine every night na sauran rayuwa ta ya cigaba da kasance wa like yesterday night" ta juyo tana facing dinsa tace "lallai ma. To yau ma ba anan zan kwana ba" ya bata rai yace "ban gane ba" ta saka hannu tana gyara masa hannun rigarsa tace "biki zanje" ya sake bata rai "biki kuma? Bikin wa?" Tana murmushin fahimtar ba ita kadai ta manta ba tace "bikin mu ni da kai. Ka manta yau za'ayi event a Maiduguri? Mama har ta saka a kira ni a tuna min karfe goma jirgin mu zai tashi. Kuma nasan ba zan dawo yau ba, maybe sai jibi". Ta fada da yanayin tsokana. Ya kife kansa a kafadarta yace "bara inje in hada kayana nima" ta ture shi tace "ba fa a gayyace ka ba" yace "duk wanda ya gayyaci matata to kuwa tabbas ya gayyace ni. Anywhere you go I will also go".
Ta kalli kaskon da yake kan wuta tace "me kake dafa mana ne?" Ya kalli kaskon shima, har ya manta ma da cewa girki yake yi, sai yace "dankali da kwai" tayi murmushi kawai sai ya dan ja da baya yana kara kallon shigar jikinta, ya daga gira yace "if you want to wear a dress like this, wear it with confidence" sai ya saka hannu ya zare dakwalin da ta rufe wuyanta da kirjinta da shi. Ta danji kunya ta sunne kai a kirjinsa sai shi kuma ya daga ta chak ya dora akan worktop, ta karbi dankwalin a hannun sa ta nada masa shi a nasa wuyan tana dariya, yace "ki zauna anan. Let me cook for you" sai ya koma ya leka cikin man sa, ya juyo yana kallon ta fuskarsa abin tausayi yace "ya kone" tayi dariya shi kuma ya harare ta ya dauko dankalin da ya zama kamar gawayi ya jefa a waste basket ya dawo gurinta ya zagaye ta da hannayensa ya dora kansa a kirjinta yace "ban iya girkin ba. I wanted to cook for you" tace "ka iya mana. Let me tell you what to do. Shi wannan dankalin you boil it first with a little bit of salt, sai ka yayyanka shi a kwance yayi shape din circles, shi kuma kwan sai ka zuba masa attaruhu da albasa da spices, sai ka juye dankalin a cikin kwan ka juya su sosai sannan ka dora frying pan akan wuta ka zuba mai kadan sannan ka juye dankalin da kwan ka soya su together on a very low heat, in side daya yayi ka juya dayan side din shima yayi, shikenan" sai ta sauko taje ta kashe wutar da har yanzu man yake kanta yana konewa. Tace "yanzu bara in hada mana, in ka gani yadda nayi kaga watarana kai ma sai kayi mana" sai ya sake daukanta ya mayar da ita kan worktop yace "you seat here, ni zanyi mana, ai na gane".
Har ya koma gaban cooker din sai kuma ya dawo gurinta yana langwabe kai yace "energy na ya kare. I need a refill" ta turo baki tana magana kasa kasa, yace "me kike cewa?" Tace "bayan yunwa nake ji tun jiya banci komai ba kuma kazar ma baka barni naci ba" yace "to ba nace zan biya ki ba, please" ya fara koma mata Sadaukin jiya, tayi kokarin ture shi "kitchen ne fa" yace "kitchen din waye? Gidan waye? Matar waye?" Ta sake makale kafada sai yace "okay, just a kiss then" ya fada yana kawo fuskarsa kusa da tata, ta saka fingers dinta tana tracing gashin girarsa ta zagayo har zuwa sajen sa, ya lumshe ido sai tayi sauri ta juya fuskarsa side tayi kissing cheek dinsa. Ya bude idonsa ya bata rai ita kuma tana dariya yace "gaskiya ban yarda ba. Ni bana son wannan" ta miko hannunta tace "bani kaya na to tunda baka so" yayi mata murmushin mugunta yace "with pleasure" sannan ya dora lips dinsa akan nata.
Hmmmm. Naga wadannan ba yunwar suke ji da gaske ba, kuma na fahimci basu da niyyar zuwa Maiduguri. Gwara in tafi kar jirgi ya tafi ya barni.
[3/28, 10:13 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Seventy Five : Maiduguri
Diyam bata samu shiryawa ba har sai data ji horn din mota a waje, sannan ta ruga daki da gudu tayi refreshing. Tana cikin saka kaya Murjanatu ta shigo dakin tana kallon ta tace "wai sai yanzu kike shiryawa?" Diyam tace "da wannan complain din da kike yi dama jakar da zan tafi da ita kika dauko min a closet. Na riga na hada kayan da zanyi amfani dasu tun a gida" Murjanatu ta shiga ta fito da karamar jaka a hannun ta, lokacin Diyam har ya dauko hijab dinta tana checking contents din handbag dinta sannan ta kara abinda zata kara tayi zipping dinta ta rataya. Suna saukowa Murjanatu tace "baku da abinci a gidan nan? Ki zubo min dan Allah ko a mota ne sai inci yunwa nake ji" Diyam tace "nima yunwar nake ji, in kin samu nima ina so".
A waje Sadauki ne a tsaye tare da Al-mustapha wanda yake cousin din su Sadauki kuma daya daga cikin maneman Murjanatu suna magana, ya dora jallabiya akan shorts din dake jikinsa. Su Diyam suna fitowa Al-mustapha yazo ya karbi jakar hannun Murjanatu ya je ya saka a mota, Murjanatu tana kallon Sadauki tayi wa Diyam rada tace "baiwar Allah me kika yiwa yaya na? Na ga ya zama fari cikin dare daya. Ko dai man bleaching kika shafa masa?" Diyam tana dariya tace "kakan bleaching ba bleaching ba" amma ita ma sai ta lura fatar Sadaukin tayi haske sosai, wani annuri a kwance a fuskarsa and he seems kamar ya kasa daina murmushi.
Al-mustapha ya dawo suka gaisa da Diyam yana kallon Sadauki, Sadauki ya lura tsokanar sa yake son yi sai yace "to ya isa haka, shiga mota" ya nuna Murjanatu yace "kema shiga, ko a gaban ku zanyi sallama da mata ta?" Almustapha yace "kaji masu mata, muma dai mun kusa zuwa gurin" Sadauki yace "kun kusa, amma baku zo ba. Ka bari sai kazo gurin sannan sai kazo mu jera, amma yanzu kana baya na" duk suka yi dariya, sannan su biyun suka shiga mota.
Ya karaso gaban Diyam yana kallon ta, kanta a kasa tana wasa da fingers dinta, sai ya mika hannu ya kama nata, tace "zamu tafi" yace "Allah ya kiyaye hanya. I will be on the next flight insha Allah. Take care of yourself for me kinji? Sai nazo anjima" tayi murmushi tana gyada kai, sai kuma tayi ɗage on her toes tayi kissing beard dinsa. Ya bude mata kofa, ta shiga sannan ya gyara mata hijab dinta ya manna mata kiss a palm dinta sannan ya rufe mata kofa.
Suna jan mota Murjanatu tace "I will pretend kamar banga komai ba" Diyam ta harare ta tace "to ai dama babu abinda kika gani yarinya. Ni yunwa nake ji wallahi". Suna zuwa airport suka wuce VIP lounge. A can suka tarar dasu Mama already har sun isa, sai a nan Diyam ta samu tayi breakfast kafin su tafi. A lokacin ne kuma ta yi studying maman su Murjanatu sosai, sai ta ga cewa akwai tsantsar ilimi da wayewa a tare da ita wanda Diyam ta fahimci cewa shine dalilin da yasa bata daukan Sadauki a matsayin abin ki sai dai abin so, dan jahilci da rashin aikin yi suna playing role sosai akan wadannan abubuwa.
Kafin 11 na safe sun sauka a Maiduguri. Tun daga yadda akayi musu a airport, tun daga motocin da Diyam taga sun zo daukan su harda motar security, Diyam ta kara tabbatar wa lallai ɗan Umar Mustapha Abatcha ta aura. Gidan da suka je kuwa ba gida bane ba, Diyam ta fahimci kamar wani estate ne amma family estate mai dauke da gidajen kakanni, iyaye da ya'ya. Gidan baban Sadauki a ciki yake, uncles uncles dinsa duk suna ciki, da kuma cousins dinsa da sukayi aure. Ko wanne gida ka gani a cikin estate din abin kallo ne, amma babban abin kallon shine gidan Umar Abatcha, tsarin gidan, motocin da suke gidan, kayan alatun da aka kawata gidan dasu, su suka saka Diyam ta fahimci dalilin da yasa Sadauki baya jin fitar kudi daga aljihunsa dan akwai su din.
Yadda ake tayi mata ya saka take ta jin kunya, abincin da aka sauke su dashi ma takasa ci sai da Murjanatu ta ja ta suka tafi part dinsu su yammatan gidan wanda shi a kansa ma gida guda ne. Murjanatu tana ta tsokanar ta "wallahi in kika ce kunya zaki ringa ji ko? To wallahi a gidan nan sai an kusa mayar dake tababbiya" Diyam tayi murmushi, amma ita tasan ba zata iya cire kunya daga ranta ba kamar yadda ba zata iya cire jini daga jijiyoyin ta ba.
Anan ta samu taci abinci sosai tare da sauran yammatan, sai kuma duk suka yi wanka har ita suka fara shiryawa, ta jawo jakar kayanta zata saka sai Sa'adatu tace "Mama fa ta bayar anyi miki dinkin da zaki saka yau, sai dai ki gwada abinda baiyi ba aje yanzu ayi miki adjusting" Diyam tayi godiya, amma kuma ta so saka nata kayan data tanada musamman saboda yau din sai dai kuma hausawa sunce yaba kyauta tukuici, in bata saka kayan ba Mama ba zata ji dadi ba. Dan haka sai ta yanke shawarar zata saka yanzu in yaso in an jima sai ta saka nata. Aka kawo mata kayan ta saka, komai yayi mata sai hips ne da za'a dan buda mata. Nan take Sa'adatu tayi waya aka zo aka karba kuma suna cikin yin kwalliya sai gashi an dawo dashi. Farar shadda ce da akayi mata wani irin stone work da golden brown stones a gaban rigar da kuma hannayenta, in ka gani zaka dauka aikin sirfani ne amma stones ne kawai aka jera su, Falmata tayi mata dauri mai kyau da dankwalin shaddar sannan ta saka bungles na danyen gold wanda ta dauko daga kayan lefenta, ta saka takalmi ta rike clutch golden brown nan take ta fito a matsayin Mrs Aliyu Abatcha. Bayan suma su Murjanatu sun gama shiryawa sai suka fita babban palon gidan, aka zaunar da Diyam a kan kujera kusa da Mama wadda Diyam tana zama ta rike hannunta tana yaba kyawun da Diyam din tayi.
Already mutane sun fara zuwa gidan, yanuwan Sadauki, kannen babansa mata da matan kawun nan sa, matan abokan babansa, abokan arziki da sauran matan manyan gari. Duk wadda tazo zata zo su gaisa da Mama sannan Diyam ta gaishe ta, Mama kuma tayi introducing dinsu, kuma duk sai sun yaba kyawun Diyam sannan suyi mata wasa saboda kasancewar su barebari ita kuma sai dai tayi murmushi kawai dan ba zata iya mayarwa ba.
Wasa wasa gida ya fara cika, duk girman palon sai Diyam taga mutane suna neman cika shi. Kowa kuma tazo zata kawo mata gift ta karba tayi godiya sannan sai Mama ta saka a shiga dashi ciki. Sai a lokacin ta fahimci ma ashe ba wai anan ne za'ayi taron ba, akwai hall da suke dashi a gidan wanda suke amfani dashi dan gudanar da tarurruka ko kuma family meetings. Sai da akayi la'asar sannan aka fara kai mutane can gurin taron, Diyam kuma ta koma daki dan shiryawa. Tana shiga sallah ta fara yi sannan ta dauko kayan da ta taho dasu ta ajiye akan gado a lokacin da Sa'adatu ta shigo dakin tana kallon kayan tace "wow" Diyam tayi murmushi. Kayan Fulani ne na saki complete set din da abin wuya da hannu da kafa da komai. A gaggauce tayi wanka, sannan ta danci abinci kadan kafin ta shirya tsaf ta fito a cikakkiyar bafulatanar ta. Nan take ta dauki kanta a hoto ta turawa Sadauki wanda tun dazu da suka tare da su Mama yake ta kiranta a waya amma ta kasa daukan wayarsa a gabansu. Yana gani yayo reply
"Diyam, na taba gaya miki kuwa cewa ke din kyakykyawa ce?"
"Really? Ba zan iya tunawa ba. Maybe ka taba fada but not directly"
"To yanzu zan fada directly din. You are very beautiful Halima. Kina da beauty na fuska, na jiki dana zuciya. Ki godewa Allah Diyam dan yayi miki komai"
"Anya kuwa na kaika kyau Aliyu? Ni in ina kallonka har mamakin kyawunka nake yi. Komai naka tamkar kai ka zabar wa kanka. Komai ya dace da komai a fuskarka wadda ita kuma ta dace da jikin ka. Jikinka kuma ya dace da sunanka, Aliyu Sadauki. Strong in the heart and the body.
Imojin heart mai beating
"I love you so much my husband"
"I love you more, my wife".
Dakin taron ya cika sosai da manyan mata, ga makada nan suna ta aikin su mata ana ta cashewa ana barin kudi. Diyam tana zuwa aka saka ta a tsakiyar fage aka fara yi mata ruwan kudin da har sai da ta fara tunanin anya wannan ba almubazzaranci bane ba? Ba'a tashi daga event din ba sai daaka fara kiran magrib.
Karshen gajiya Diyam ta gaji, jikinta gabaki daya ciwo yake yi mata dan haka akan sallayar da tayi magrib anan ta zame ta kwanta sai bacci. Cikin baccin aka zo aka tasheta wai taje su gaisa da matar governor wadda bata samu zuwa dazu ba sai yanzu. Can palon Mama aka kaita ta tarar dasu suna ta hirar su suna dariya, ta gaishe su suka amsa mata da fara'a suka yi ta tsokanar ta tana rufe fuska sannan matar ta dauko wani set din scent burner mai kyau ta bata a matsayin gift sannan tayi musu sallama Mama ta tafi ta raka ta. Bayan Mama ta dawo ne sai kuma ta zauna tana ta yiwa Diyam nasiha da kuma dabaru irin na zaman aure, wadansu maganar sai Diyam taji sunyi mata nauyi da yawa amma kuma duk tana ganewa kuma tana dauka. In dai Sadauki ne, she can and will do anything for him.
Suna tare su Murjanatu suka shigo, sannan aka gabatar musu da abinci suka hadu a dining din Mama suka ci tare sannan suka dawo palo suka cigaba da hira, Diyam tana ta mamakin yadda Mama take yi da yayanta kamar kawayenta. Suna nan tare Sadauki ya shigo, Diyam ta kalleshi sau daya suka hada ido ta sunkuyar da kanta, ya je ya gaida Mama sannan ya samu guri ya zauna yana amsa gaisuwar kannensa, Diyam ma ta gaishe shi ya amsa yana danna phone dinsa, Murjanatu tayi dariya Diyam ta harare ta.
Mama tace "kaje gurin babanka kuwa?" Yace "eh, muna tare dashi ai tunda nazo, sai daya shiga ciki sannan na shigo". Ya turo wa Diyam text "ki taso mu tafi" ta karanta sai ta dago kai ta harare shi. Ya hade hannunsa alamar roko sai ta gyara zamanta yadda bama zata ke kallon sa ba. Sai kawai suka cigaba da hirar su shida Mama, tana bashi labarin taron da irin matan da suka zo da kuma gifts din da Diyam ta samu. Sai yayi mata godiya sosai sannan ya mike tsaye yana cewa "Fanna kawo min abinci daki na Please" Mama tayi sauri tace "wacce Fanna kuma? Mu ai mun yaye ka yanzu. Halima tashi maza ki hada abinci ki bishi ki kai masa" bai ce komai ba yayi hanyar waje sannan ya juyo a wayence yana kallon Diyam, yayi mata gwalo.
Ta tashi ta hada masa duk abinda tasan zai so ta zuba a basket sannan tace da Murjanatu "tashi ki rakani" Murjanatu ta harare ta "kinga in kika fita daga gidan nan ki kalli gabas, gini na farko da kika gani a gurin shine part dinsa" Adama tayi dariya tace " me dakin gabas kenan, shi yasa mu a gidan nan bamu fiye kallon gabas ba sai in zamuyi sallah" Falmata tace "to ai dan kar mu kalla ace harara mukayi" Mama ta jefi Fanna da remote tayi mata magana da barbarci sai ta mike suka fita tare da Diyam.
Suna fita Diyam tace "kun takurawa bawan Allah nan. Mutum mai hakuri da kawaici irinsa, mutumin da ko hannu aka saka masa a baki ba lallai ya ciza ba" Murjanatu tace "waye hakan? Lallai so hana ganin laifi. To in gaya miki saboda muguntar sa kwanan baya sai da ya saka ni Murjanatu na share gidan nan gabaki daya, tun daga sama har kasa" Diyam tayi dariya tace "daga ji wani babban laifi kika yi masa, shi bawan Allah ne mai sanyin zuciya mai kuma hakuri da yafiya idan aka bata masa" a lokacin suka zo kofar part din Sadauki. Murjanatu ta bude kofa ta tsaya a gefe tace "wacce take fadar maganar tafi wacce ake fadawa sanin cewa ba gaskiya take fada ba. Good night friend" Diyam tayi dariya tace "yanzu zan dawo ai" Murjanatu tace "we will see about that".
Ta ajiye abincin a palo tana studying kyawun gurin, sai ta tafi kofar da jikinta ya bata yana ciki tayi knocking ta tura kofa, yana kwance a kan gado da yawa a hannunsa, dakin cike da sanyin ac da kuma kamshin sa, ya ajiye wayar yayi mata murmushi yana folding hannayensa yace "welcome wife" tace "ga abincin" ya dan bara rai "waye yace miki yunwa nake ji? Ni matata nake so" ya karasa maganar yana langwabe kai, ta fara bubbuga kafa a kasa "ni wallahi bacci nake ji, ni wallahi na gaji jikina ciwo yake yi min" ya mike zaune yace "good. Kinga sai inyi miki massage" ya fada yana tattare hannun rigarsa. Ya nuna gefensa akan gadon yace "come and lay down here inyi miki tausa. You will thank me tomorrow". Ta yi kamar zata yi kuka, ya miko mata hannunsa yana kara marairaice wa sai kuma tayi murmushi ta tafi tasa ka nata hannun cikin nasa.
Da safe sai da kowa ya tashi a gidan aka kuma gama komai har breakfast an gama shiryawa amma babu Diyam babu Sadauki babu kuma labarin su. Anyi ta kiran wayoyinsu kuma da suna shiga amma daga baya switched off. Sai da aka zo yin breakfast sannan Papa yace aje a kirawo su, yana son suci abinci tare gabaki dayansu saboda a yau yake son komawa Canada.
Cikin bacci Diyam taji kamar ana knocking kofa, ta bude ido da kyar saboda nauyin bacci, ta hannun Sadauki daga jikinta sannan ta juya tana kallon fuskarsa so deep in his sleep sai kawai ta dulmiya wajen kare masa kallo tana murmushi. Wani bugun kofar da aka sake yi shi ya dawo da ita daga duniyar kallon Sadauki. Ta mike tana gyara kayan jikinta sannan ta dauki hijab dinta ta saka still cikin baccin ta fita palo ta bude kofa. Murjanatu ta gani a tsaye, ta harare ta tace "kika ce min ba kwana zaki yi ba" Diyam tace "wannan ne dalilin da yasa kika dame mu muna bacci? To bara inje in kira wo shi sai ki maimaita a gaban sa" ta daga hannu tace "Papa ne yake kira, in kuma inje in gaya masa kunce kar a dame ku ne to?" Diyam bata ce komai ba ta koma da sauri ta tashi Sadauki ta gaya masa sakon kira sannan ta fita da sauri a ranta tana cewa "wannan wanne irin abin kunya ne nayi ni Halima".
Da sauri Diyam tayi brush ta wanke fuskarta ta chanza kaya sannan suka tafi part din Papa inda anan ake neman nasu. Tana shiga Sadauki shima yana shigowa, fatar idonsa a dan kumbure alamar bacci bai ishe shi ba. Shi ya fara zuwa ya durkusa ya gaida mahaifinsa sai bayan da ya zauna sannan Diyam itama ta karasa for the first time ta gaishe da surukinta. Ya amsa da madaukakiyar fara'a "Halima, ance min jira kinyi kyalliya da kayan fulani, ni kuma sai nace to lallai zamu yi miki zanen barebari dan mu tabbatar miki kin zama tamu yanzu" duk suka yi dariya har Diyam data rufe fuskarta da hijab dinta. Sai data zauna sannan ta samu damar ganin fuskarsa. Sai a lokacin tayi mamakin yadda akayi duk ganin da take yi masa a hotuna bata fahimci suna kama sosai da Sadauki ba sai data gan shi ido da ido tukuna. Bayan shekaru, banbancin fuskarsa data Sadauki shine hancin Sadauki yafi nasa tsaho sai kuma sumar Fulani da Sadaukin yake da ita.
Suna zama masu aiki suka matso suna tambayar kowa abinda za'a zuba masa daga cikin menu, kowa ya fada aka fara saving, Sadauki kuma ya fadi nasa dana Diyam dan yasan ba zata yi magana a gaban su Papa ba.
Sai da suka gama cin abincin sannan Mama ta sake yiwa Diyam barka da zuwa family. Papa kuma ya dora da cewa "ina so Halima ki saka a ranki cewa nan gidan ku ne ba wai gidan surukan ki ba, ki dauke ni a matsayin baban ki ba wai baban Aliyu ba. Saboda baffanki, malam Usman yayi min halaccin da babu wanda ya taba yi min irinsa a duniya. Ya rike min Aliyu tamkar shi ya haife shi dan haka nima zan rike ki tamkar ni na haife ki insha Allah. Wannan shine abinda zanyi in kwatanta abinda Usman yayi min".
"Nasan Aliyu ya baki labarin dana bashi akan rabuwata da mahaifiyar sa amma ban gaya masa dalilin da yasa bayan nayi bincike na gano wanda yake neman halaka su kuma na dauki mataki akan sa ban koma na dawo dashi gida gurina ba. Na barshi ya cigaba da zama a hannun Usman ba tare da yasan nine mahaifinsa ba saboda a lokaci nayi tunanin hakan shine dai dai a gurinsa, maybe I was selfish, but I wanted what is best for my son. Ni mutum ne mai harkoki da yawa wanda ban fiya samun lokacin kaina ba ballantana na iyali na, tarbiyya, nuna soyayya, nuna kulawa ga dan karamin yaro bayan kuma bana tare da mahaifiyar sa ba abu ne da zai samu a gurina ba. Wannan ne yasa na bar shi a hannun Usman da Zainab. Na kuma boye kaina daga gare shi ne saboda ina son ya zama strong, bana son yasan nine mahaifinsa ballantana ya dora wani abu a ransa ko kuma ya raina marikansa. Sai na nemi alfarmar Usman nace ya koya masa neman na kansa tun yana karami. I used to go to the garage duk sanda na samu dama, I used to watch him work, drenched in oil and sweet, na kan ce a raina "good, yanzu zaka san darajar kowacce kwandala da ka samu". Usman kuma bai taba neman ko kwandala daga wajena ba saboda kula da Aliyu, sai lokacin daya kasa samun admission ne ya nemi in taimaka masa ni kuma nace ya barshi ya sha wahala ya samu da kansa, har yayi fushi dani a lokacin yana ganin kamar nayi tsauri da yawa. Amma yanzu gashi naga result din abinda nayi din, Aliyu yayi turning into more than yadda na saka rai. Yes, na bashi kudi nace ya juya, shekaru biyu bayan nan dana bincika sai naga already yayi doubling kudin da na bashi. A yanzu haka bansan adadin me yake dashi ba. Allah ne kadai yasan me ya tsara wa rayuwar sa amma ni ina saka ran cewa this is just the beginning for him. Allah yayi muku albarka gabaki dayan ku, Allah kuma ya baku zaman lafiya da zuriya mai albarka".
Duk suka amsa da ameen. Diyam ta saci kallon Sadauki sai taga kansa a kasa amma fuskarsa tana nuna tsantsar farin ciki. Mama tace "a matsayin wedding gift, Papa and I decided to give you two, Aliyu da Halima, gidan mu na Oxford, mun bar muku shi duniya da lahira. Allah ya baku zaman lafiya" nan take gurin ya kaure da murna, siblings din Sadauki duk suka taho suka ringume Diyam suna taya su murna. Ta gefen idonta taga Sadauki ya durkusa gaban mahaifinsa yana godiya, sai taga ya dago shi ya rungume shi a jikinsa yana bubbuga bayan sa.
[3/30, 10:51 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Seventy Six and seven : Karma
Food for thought: Mun tuna da hadisin da Annabi (SAW) yake mana bayani akan healing power da take cikin habbatus sauda? Sannan da hadisin da yake gaya mana cewa nemon tsami yana maganin cututtukan annoba? Zam zam fa? Mun tuna cewa yana maganin duk wata cuta da aka sha shi da niyyar neman waraka daga gareta? Add that to bin ka'idodin kare ka kai daga wannan cutar, kar ki/ka fita daga gida indai bada wani kwakwkwaran dalili ba, in za'a fita din kuma a saka face mask da hand gloves. A guji taba mutane, doorknobs, railers etc a lokacin da ake waje, kar kuma aci ko a sha wani abu, a kuma guji taba fuska, in an dawo gida kuma a cire kayan da aka fita dasu a shanya su a rana sannan ayi wanka kafin a taba komai na gidan.
Don't forget your morning and afternoon azkar. Insha Allah we will get through this together.
#Don't panic
#Stay safe
#Stay at home
A ranar da yamma su Diyam suka dawo Kano. Tun a jirgi Diyam take ramuwar baccin ta, sai Sadauki ya daga armrest din tsakanin kujerun su ta kwanta ta dora kanta a cinyarsa shi gyara mata hijab dinta ya rufe mata har kafafunta. Sai da zasu sauka sannan ya tashe ta, suna fitowa already daya daga cikin office drivers dinsa yana jiransu ya dauke su ya kaisu gida. A gidan ma Diyam baccin ta ta cigaba, dan sai yau take huce gajiyar biki, Sadauki bai dame ta ba ya batta tayi baccin ta shi kuma yayi musu order ta abinci aka kawo musu har gida saboda ya tabbatar wa kansa cewa bai iya girki ba.
Sati daya bayan tariyar Diyam Asma'u tazo ita da Subay'a, ranar Subay'a kamar zata zuba ruwa a kasa ta sha dan dadi musamman saboda ganin dakin da aka ware a gidan saboda ita. Diyam kuma sai ta dauko gift din data samu a Maiduguri ta ware wadanda take so sannan sauran ta hada da wasu daga cikin kayan lefen ta ta bawa Asma'u tace ta kaiwa Inna a raba wa yan'uwa, cousins dinta duk kowa sai daya samu wani abu. Asma'u kam sai data debi rabonta dama tun kafin a fara tabon. A lokacin ne Diyam ta fahimci cewa Asma'u suna waya da Bassam, she did not comment, idan hakan suke so to ita kam sai dai ta taya su da fatan alkhairi.
Sati biyu bayan bikinsu hutun su Diyam ya kare, ta dauka zasu yi drama da Sadauki akan komawarta amma sai taga shine ma mai taya ta lissafi. Da lokaci ya matso sai taga ya fara hada nasa kayan shima. Tace "aikin fa? In ka bini wa zai kular maka da companyn ka?" Yace "my dear Halima. Kin manta I managed my company for the five years din da nake karatu? Ko kin dauka zan barki tafi ki barni ne?" Tayi dariyar yadda ya fadi maganar kamar wani yaro. Amma kuma tana jin dadi a ranta dan ba karamin faduwar gaba take yi ba a duk lokacin da ta tuna cewa zata koma England school ta bar Sadauki a Nigeria.
Ta zo ta zauna akan cinyarsa ta zagaye wuyansa da hannayenta ta saka fuskarta a wuyansa tana dan bubbaga bayansa tace "kar kayi kuka, bazan tafi in barka ba kaji habibi" ya shafa mararta yace "habibi yana cikin nan gurin a kwance" ta zaro ido tace "ba wani nan" yace "to ni dai banga kinyi period ba" tace "sati biyu ne fa kadai" yace "koma kwana biyu ne, ni ai nasan irin shukar da nayi kuma nake yi so nake inga na fara girbi" ta boye fuskarta a wuyansa tace "kai dan Allah, sai kace wata gona? Ni bani da komai Allah. Kuma ma ai kaga karatu nake yi yanzu ko? Ko so kake in ke faduwa exams dina?" ya dago fuskarta yace "tare zamuyi karatun ai, muna yi kuma muna cigaba da planting seeds din mu, kafin mu gama in Allah ya taimake mu sai mu girbi ko da biyar ne" ta zaro ido "biyar fa kace? Sai kace kaza?" Sukayi dariya tare. Yace "biyar din ma rage miki nayi ai dan kar ki sha wahala da yawa, in za'a bani zabi twins nake so duk shekara. In akayi twin boys sai ayi girls, sai a sake boys a sake girls, kinga a shekara hudu anyi takwas kenan" ta mike da sauri tana cewa "in yaso a shekara ta biyar sai inga an shigo min da amarya ko" ya jawo ta ta fado jikinsa, ya gyara mata zama tana facing dinsa yana tracing jawline dinta da finger dinsa yace "kina so ta mutu ne amaryar saboda bakin ciki? Ko kuma kina so ranar lahira in tashi da shanyayyen barin jiki saboda na kasa adalci? Kina ganin zan iya jera wata dake a zuciyata Halima?" Ta turo baki tace "daɗin baki" yace "au baki na yana da dadi dama? Ai ban sani ba nasan dai naki yana da mugun dadi. Let's taste and find out na waye yafi dadi".
Tafiyar su tazo dai dai da hutun su Subay'a. Dan haka Sadauki yace zasu tafi da ita da Asma'u suyi musu hutu a can kuma su taimaka musu gurin settling a sabon gidan su. Murna gurin Asma'u kamar zata tashi sama dan dadi, Diyam tana kallonta tace "kina murnar zaki je England ne ko kuma kina murnar zaki je gurinsa?" Asma'u tayi saurin yi mata signing akan tayi shiru kar Sadauki yaji. Diyam ta daga murya tace "eh, Bassam da kuke waya dashi Asma'u nace kinga kuwa a can yake karatu, nasan zaku ke haduwa in kinje" Sadauki yayi saurin juyowa daga kallon news yana kallon su yace "Bassam, menene hadin Yar asama da Bassam?" Diyam ta nuna ta tace "gata nan, tayi maka bayani". Asma'u ta fara kame kame tana rarraba ido, ya kalle ta strictly yace "bana son shashanci, idan yana sonki da gaske yazo ya same ni first kafin ya cigaba da neman ki. I know his family, amma shi din zan saka a bincika min halayensa in kuma basu yi min ba kin gama ganin sa kenan. Kinji abinda nace?" da sauri Asma'u ta gyada kai.
Ranar dasu Diyam suka sauka a ranar ne suma su Murjanatu suka zo. Sun taho gabaki dayansu tare da sisters dinta dan su taya su Diyam tarewa a sabon gidan su. Gidan da Diyam taga kamar yayi musu girma dan haka ta saka aka rufe part din matar gida suka zuba kayansu a part din maigida ita da Sadauki. Sai bangaren yara kuma anan Murjanatu zata zauna tare da Judith din da Diyam ta kuma gayyatowa. Daga nan kuma sai gurin ma'aikatan gidan wadanda dama suna nan already, masu kula da tsaftar gidan, masu abinci da masu gadi. A cikin kwana biyu aka gama settling komai, a ranar suna zaune gabaki dayansu matan a palo suna hira sai Sa'adatu take basu labarin abinda Papa ya gaya musu kafin su taho daga Canada, cikin kwaikwayon muryarsa tace "ke Sa'adatu dake Falmata, ku fito da miji ayi muku aure hakanan, tunda naga karatun nan naku ba karewa zaiyi ba" duk suka kwashe da dariyar yadda tayi maganar, Diyam ta harare ta tace "yanzu haka baban nawa yake magana?" Falmata ta bude hannu tace "yanzu fi sabilillahi ni ina naga mijin da zan fitar? Ni ina naga saurayin ma? Samari fa basa kula yayan masu kudi" Murjanatu ta gyara zama tace "basa kula ku dai, ku da kuke musu girman kai, ki zo in koya miki yadda ake jawo hankalin maza" anan Sadauki ya bude kofar bedroom ya fito ya tsaya yana kallon su, duk sunyi tsuru tsuru saboda basu san yana cikin daki ba sai Diyam ce kawai ta sani. Bai ce musu komai ba sai ya dauko wayarsa yayi dialing sannan yace "hello Papa" ya gaishe shi yace "maganar nan da ka yiwa su Sa'adatu, ina ganin a hada harda fanna saboda duk tafi su samari. Okay. Insha Allah. Thank you Papa. Love you too" ya juyo yana kallon fanna yace "ke ma ki fito da naki. Gaba daya guri na zasu fara zuwa First, sai nayi approving sannan zasu je gida" bai sake cewa komai ba ya saka hannayensa a aljihu yayi tafiyar sa.
Murjanatu ta zamo daga kan kujera ta fado kasa tana birgima dramatically, tace "wallahi yau na kuma tabbatar wa yaya Aliyu baya so na" su kuma duk suna tayi mata dariya. Diyam tace "alhamdulillah. Zuciyata fess yau. Karyar tara samari ta kare.
Satin su Sa'adatu daya suka koma. Su kuma su Asma'u sai da sukayi wata daya sai da hutun su ya kare sannan suka koma gida. Washegarin da suka tafi ne da assuba Diyam tana karatun Alkur'ani akan sallaya sai ga Sadauki ya dawo daga masjid. Ya zauna akan gado yana kallonta har ta idar sannan ta mike ta hawo kan gadon ta kwanta tana lulluba yace "ni fa har yanzu banga tazo ba" bata kalle shi ba tace "wacece zata zo? Bakuwa zaka yi?" Ya yaye rufar yace "yau ba zaki yi baccin nan ba sai kin gaya min akwai ko babu" ta fara yi masa shagwaba "ni me zan gaya maka. Ni babu abinda zan gaya maka" ya cire rigar da yaje masjid da ita yayi astriding dinta yace "ko ki gaya min ta lallami da lumana ko kuma ki gaya min in kinji wuya" ta fara dariya, ya sakar mata nauyinsa shima yana dariya, tayi kokarin ture shi ta kasa sai ya rike hannayenta duk biyun da hannunsa daya, yace "akwai ko babu?" Tace "to ni yanzu me kake so ince maka" yace "cewa zaki yi 'sadauki kayi min ciki" ta kwace hannunta da sauri ta rufe fuskarta tace "la ila, wai kai baka jin kunya ne?" Yana dariya yace "ina ji mana, ina jin kunyar mutane amma bana jin kunyar matata" tace "ni dai bazan iya fada ba" yace "to kinga, in akwai ki gyada kanki, in babu ki girgiza kanki" tayi shiru, yace "akwai ko babu?" Ta bude ido tana kwallon sa ta miko masa hannu tace "kawo tukuici" yace "say it, duk abinda kike so, anything" ta rufe hannun tace "in ka kawo tukuici sai kazo a gaya maka" yace "a bani bashi zan biya" ta turo baki "har yau fa baka biya ni bashin kaza ta ba kuma kake neman a kara maka wani bashin?" Ya dafe kai "wannan kaza, wannan kaza. Yanzu duk kajin gidan nan amma ban biya ba?" Tace "waccan special ce" ya mike yana saka rigarsa. "Zan siyo miki kaza yanzu, zan kuma kawo miki tukuicin ki".
Sai daya loda rigunan sanyi a jikinsa saboda sanyin da ake yi a waje, gashi kuma gari bai ko gama wayewa ba amma haka ya fita, da kyar ya samu kazar saboda duk eateries din kusa dasu basu fito ba sai da ya shiga cikin gari sosai sannan ya samu, ya siyo mata chocolates duk wadanda yasan tana so leda guda sannan ya dawo gida.
A gado ya same ta har lokacin ta lulluba tana baccinta. Ya zauna a gaban gadon ya bude ledar gasassun kajin ya yanko cinya daya ya bude fuskarta ya kai naman kusada fuskata, ta motsa idonta sannan ta bude idon cikin nauyin bacci tana kallon naman sai kuma ta kai hannu da sauri zata karba sai ya janye yace "kwadayayyiya. In kina so sai kin fada min abinda nake son ji, akwai ko babu?" Ta tashi zaune ta leko tana kallon naman kajin daya bude ya cika dakin da kamshi ga kuma chocolates din daya zube a kasa suma. Sai ta kalleshi ta gyada kai da sauri ta koma ta kwanta ta rufe fuskarta.
Wannan ciki na Diyam ya sha gata, gayu da soyayya a gurin sabon shiga Sadauki. Rigimar da tayi tunanin zasu yi akan komawarta school basu yi ba sai yanzu akan zuwa school da ciki. "Idan kuma kika fara rashin lafiya a can fa? Ko kuma in kina son ki kwanta ki huta babu gurin kwanciya? In zaki yi amai fa? Ko kuma kina sauri kin makara ki gurde ki fadi" tana dariya tace "baban baby kenan" yace "babies, kar ki rage min daraja mana" tace "okay Baban babies. Wannan cikin fa ba me laulayi bane ba, dame laulayi ne da ni da kaina zan nemi hutu. Ka barni in cigaba da zuwa please kaga yafi inyi ta zama a gida ko?" Amma fir Sadauki yaki, sai yayi enrolling dinta a online classes yadda zata zauna a gida tayi connecting da class dinsu online, duk abinda suke yi ko suke cewa tana ji kuma tana gani a screen din computer dinta, za kuma ta iya yin question a amsa mata, in bata kusa kuma zata iya saving lecture din sanda take free ta bude ta gani. Sai Murjanatu ta koma ita kadai take tafiya school sai Judith, dan ma dai ta samu at last ta koyi driving an kuma bata mota tana zuwa da ita.
Diyam babu abinda take yi sai dai taci ta sha ta kwanta tayi bacci sannan ta kula da mijinta, wanda sun rasa gane a cikinsu waye yafi kula da danuwansa. Kullum tamkar kara wa musu kaunar junansu ake yi. A lokacin ne kuma ya bayyana mata abinda yake shiryawa. "Branch nake so in bude na Abatcha Motors anan kasar, kinga sai inke siyan motocin daga nan ina aikawa dasu Nigeria kuwa zanke siyarwa anan din ma. Tunda muka zo nake processing abin amma saboda kasancewar ni ba dan kasa bane ba sai na kasa samun permit na bude Company, but alhamdulillah yanzu na samu" ya dauko takardar ya nuna mata, ta karba tana karantawa yace "har na sayi fili ma, yanzu zan fara gina gurin tukunna sai in dauki ma'aikata insha Allah" ta rungume shi cikin jin dadi tace "congratulations darling. Allah ya cigaba dayi maka jagora mijina" ya zagayo da ita gabansa yace "ameen. Yanzu problem din shine, bana son harkar bude wannan branch din ta saka ni in kasa saka ido akan wancan, though lafiya lau komai yake tafiya a can din but I need an assistant, someone that I can trust" tayi shiru tana tunani sai tace "Alhaji Bukar bashi da ya'ya? Kayi masa magana mana ya hada ka da mafi aminci a cikin yayansa kaga shima zaiji dadin ka karrama shi" yayi murmushi mai kyau sannan yayi kissing forehead dinta yace "that is one of the reasons I love you, saboda kina da tunani mai kyau. You know what? Kema na baki aiki" ta bata rai tace "wanne aiki kuma bayan wanda already nake dashi?, na matarka?" Yace "you are now my special advisor" tace "duk ka dai part of my job ne as your wife".
Koda yaushe Diyam tana lissafin Saghir a ranta, amma bata taba yiwa Sadauki maganar ba saboda bata son taba masa zuciya, duk kuma sanda suka yi waya da Subay'a sai tayi mata maganar sa, duk da cewa Inna tana yawan kaita ta ganshi. Shima Sadauki bai taba yiwa Diyam maganar Saghir din ba amma shima Subay'a bata barshi gurin tambaya ba.
A lokacin dasu Diyam suka kammala second semester dinsu a lokacin cikinta yana da watanni biyar, a lokacin kuma Sadauki har ya kammala ginin sabon branch din Abatcha Motors. Cikin Diyam ya dan fito kadan amma baiyi girma sosai ba, abinda ya fito sosai shine kyawunta, dan sanda suka fito daga jirgi a malam Aminu Kano international airport ita da Sadauki hannayensu rike dana juna, duk wanda ya kalle su sai ya sake kalla. Gidan Inna suka fara zuwa, a can suka ci abinci suka huta Diyam tana ta jin kunyar cikin jikinta, anan Sadauki ya barta sai dare yazo ya dauke ta duk da tayi ta rokonsa ya barta ta kwana biyu a nan. Yace "ina garin zaki kwana gida? Ki bari in nayi tafiya sai kiyi zauna ko kwana nawa ne kiyi musu".
A week after that, ya dawo daga office sai taga mood dinsa ba shi da kyau, tayi masa sannu da zuwa ya amsa ya zauna akan kujera tare da lunshe idonsa. Ta zauna a hannun kujerar tana shafa fuskarsa tace "wanka ko abinci?" Ya dan bude ido ya kalleta yace "bara in dan huta tukunna" sai ta sauka ta durkusa a gabansa ta cire masa takalmi ta hada da briefcase dinsa ta kai sama ta dawo ta sake zama a gabansa ta cire masa safar kafa ta dora kafafun a kan cinyarta tana mammatsa masa ita, tana jan yatsun kafar. Ya dan janye kafar yana cewa "ke! Chakulkuli fa kike min" ta sake jawo kafar tace "tausa fa nake yi maka, haka ake chakulkulin?" Sai tayi masa chakulkulin gaskiya a tafin kafarsa, Yayi dariya yana tashi zaune sosai ya janye kafarsa, sai ta mike tayi kneel down tana murmushi ta faki idonsa ta saka hannunta cikin rigarsa tayi masa chakulkuli tana cewa "gana gaskiyar nan nayi maka to" ya kama dariya har da zamowa kasa ya jawo ta suka fadi tare, sai shima ya yi mata yana cewa "sai na rama wallahi" ta kama kyalkyata dariya tace "wayyo zan mutu, ka bari wallahi, chakulkuli fa kanin mutuwa ne" ya sake ta ta janye daga jikinsa tana dariya, yace "kinci sa'a bake kadai bace ba" ta murguda masa baki sannan ta dawo kusa da fuskarsa tace "wanne mai tsautsayin ne ya taba min lion dina" ya danyi tsaki yace "mutane, yanayin rayuwa, cin amana. Babu abinda wasu mutanen ba zasuyi saboda kudi ba. Babu wanda ba zasu ci amana ba akan kudi. I don't know mai mutanen mu suka mayar da kudi, abinda zaka iya samu yau gobe ka rasa, abinda zakayi bayani a lahira dalla dallar yadda akayi ka samu" tace "me ya faru?" Yace "Saghir zai fito next week insha Allah" taji dadi har cikin ranta amma sai ta boye ta danyi murmushi tace "alhamdulillah. An samu Kabir din kenan?".
Yace "tun kafin ku koma school ake neman Kabir an kasa kama shi, iyayensa sunki bada hadin kai dan haka ba'a san sanda yake shigowa gari ba ballantana sanda yake fita, nayi nayi abu ya gagara, daga baya ma sai na samu labarin wai ya kwashe iyalansa daga kano sun koma kaduna da zama baki daya. I told Ahmad amma sai yace ba zai iya kama shi a kaduna ba saboda kaduna ba a ikonsa take ba, in dai zai kama shi a can sai yana da arrest motive da zai nuna wa commissioner of police na kaduna, kuma a lokacin babu wani motive na kama kabir tunda zargi kawai akeyi babu shaida. Sai nayi tunani a kan wani abu, Nayi tunanin yadda son kudi ya kai Saghir inda yake a yanzu, na kuma tuna yadda son kudi ya saka abokinsa yayi framing dinsa, sai na tuna maganar hausawa da suke cewa sai hali yazo daya ake abota, da kuma maganar bature da yace birds of the same feathers flock together, sai na saka aka bincika min wanene next friend dinsu su biyun, sai aka hada ni da wani Bashir, kin sanshi?" Diyam ta gyada kai, yace "ranar da muka zo gari na kira shi nace ya same ni a office dina, and he came, na gaya masa abinda Kabir yayi wa Saghir ba kuma nemi ya taimaka mana mu kama Kabir din, farko sai yaki, but then as I expected sai ya fara bargaining, ya fadi kudin da yake so in bashi in ina so ya fada mana sanda Kabir zai shigo gari da kuma inda za'a same shi. I told him in yana so in bashi kudi sai dai yayi making Kabir yayi confessing cewa shi yayi framing Saghir and he agreed. I gave him some money. Yau sai gashi ya dawo, can You believe ge got Kabir drunk ya ringa yi masa questions yana amsawa shi kuma yana recording? It hurts me cewa duniya tayi lalacewar da friend zai iya yiwa friend dinsa haka, but considering abinda shima kabir din yayi sai naga yayi deserving shima ayi betraying dinsa"
"Nayi submitting record din to Ahmad, yanzu zasu iya shiga har Kaduna su kama kabir, and Saghir is coming out latest next week".
Not edited. Ayi hakuri da typos.❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Seventy Eight and Nine : Finale
Sai da Diyam ta gama da Sadauki sannan ta zauna ta kira Inna ta gaya mata labarin zancen fitowar Saghir. Inna tayi murna sosai tace "Allah ya tabbatar da alkhairi, Allah yasa karshen wahalar sa kenan shi kuma Sadauki Allah ya saka masa da alkhairi" Diyam tace "ameen Inna" tace "bari in kira gidan Alhaji Babba inyi masu albishir". A ranar zance ya zagaya family, zuwa washegari yab uwa suka fara kiran Diyam suna confirming "da gaske Saghir zai fito?".
Ranar da aka kama Kabir kuwa Hajiya Babba har gidan Diyam ta zo tayi mata godiya ita da sister dinta, hawaye fal idonta, tana ta bata hakuri dan gane da rashin kyautawar da suka yi mata a baya. Diyam ta cika su da abin arziki kuma ta nuna musu babu komai ai yiwa kai ne. Sun so ganin Sadauki suyi masa godiya amma yaki fitowa yace ace musu babu komai.
Ranar da Saghir zai fito, Friday kenan, a ranar Sadauki yace da Diyam ta shirya tare zasu je. Daga gidan su gidan Inna suka fara zuwa suka dauki Subay'a sannan sannan suka tafi prison din. Suka yi packing a tsallake, Sadauki yace musu su zauna a mota ya shiga shi kadai. Bayan ya tafi Subay'a tace "Mommy nan prison ce ai" Diyam tace "eh" "inda Daddy na yake" "eh" "to Mommy mu shiga mana muhe mu ganshi" "a'a ba shiga zamuyi ba Subay'a" "to Mommy mai uncle ya shiga zaiyi a ciki?" Sai kuma ta bude ido ta ja numfashi tace "zuwa yayi ya fito dashi, dama ya gaya min zai fito dashi, Mommy ki bude min kofa inje gurin su" Diyam ta rike hannunta, sai kuma tayi murmushi tace "Subay'a uncle zuwa yayi ya fito da Daddy, amma kiyi zamanki a mota tunda uncle bai ce ki fito ba, yanzu zaki gansu sun fito tare". Subay'a ta hakura bata fita daga mota ba amma kuma bata zauna ba, in ta leka ta waccan window din sai ta dawo ta leka ta wannan, in kuma taga motsi a bakin kofar gurin sai ta fara tsalle sai taga basu bane ba. Daga baya data gaji sai ta kwanta a backseat tana kuka wai sunki fitowa.
At last sai gasu sun fito. Sadauki ne fara fitowa tare da wadansu mutum biyu wadanda Diyam ta gane a matsayin lawyers dinsa. Sai kuma Saghir ya fito tare da wani wanda ya tsaya yana ta yi masa bayanai har su Sadauki suka karaso mota. Mutanen suka yi masa sallama suka tafi sannan wancan ma yayi wa Saghir sallama ya tafi.
Diyam ta zauna tana kallon shi ta cikin motar. Yayi baki sosai, ya kuma rame sosai, amma wannan kyawun yana nan sai dai babu gayun, kuma shekaru sun fito sosai a fuskarsa harda strings of furfura a gashin sa. Ta gane kayan jikinsa, sune kayan da yake sanye dasu ranar da aka kamashi a airport, she can remember yadda ya fito daga arrivals cikin yana taku dai dai yana jin duniya duk a tafin kafarsa ga kyakykyawar Fauziyya a gefensa but yanzu da ta kalle shi bata ga komai daga cikin characters din wancan Saghir din ba. He looked calm and very different.
Sadauki ne yayi knocking a tagar da Subay'a take, ta dago tana kallonsa sai yace "Subis ga Daddy nan" ta mike da sauri ta kalli kofar prison din, tana hangoshi sai ta kama kokawa da handle din motar sai Diyam ta bude mata central lock tana dariya. Ai kuwa nan take ta bude ta fice daga motar a guje, Diyam ma ta bude ta fito tana cewa "careful Subay'a akwai titi fa". Daga tsallake Saghir ya hango fitowar ta, ya kuma lura da yadda tayo kan titi da gudu dan haka sai shima ya taho da sauri gurin ta zuciyarsa tana bugawa. A tsakiyar titi suka hadu, ya daga ta sama amma sai ya kasa juyi da ita ya sauke ta yana haki yace "kinyi girma Subay'a, Daddy kuma bashi da karfi" sai ta rungume ƙafafuwan sa tana murmushi.
Ya kamo hannunta suka karasa tsallako titin zuwa inda su Diyam suke a tsaye. Unintentionally hannun Diyam ya sauka akan cikinta tana kallon Saghir, sai taga ya kalli cikin sai kuma tayi sauri ta dauke hannun tana sunkuyar da kanta. Yayi murmushin takaici Yace "amarya" sai ta gaishe shi ya amsa yace "a sake min godiya gurin Mr Abatcha. Na goge sosai Allah ya bar zumunci" ta gyada kai a hankali tace ameen tana kallon Sadauki wanda yake ta danne danne a waya kamar baya jin me suke cewa. Sai ta kalli Saghir tace "congratulations. Allah ya kiyaye gaba" daga haka ta bude mota ta koma ciki. Sadauki ya dago kansa yana kallon Saghir ya nuna masa mota yace "Bismillah, sai mu ajiye ka a gida ko?" Sai Saghir ya kalli Diyam, ya hadiye wani daci a ransa ya girgiza kai yace "no, thank you. Kar in takura muku maybe akwai inda zaku je. Bara in hau napep kawai" Sadauki ya daga kafada kawai, sai ya tare masa napep din ya kuma biya kudi sannan ya yi wa mai adaidaitan kwatancen sabon gidan Alhaji Babba, tunda Saghir din bai sani ba.
Saghir yace da Subay'a "zaki bini gidan Alhaji?" Ga mamakin su sai ta kalli su Diyam ta kuma kallonsa sannan ta girgiza kai tace "no, Aunty Asma'u tace yau Uncle Bassam zai zo, kuma na bashi sakon abubuwan da zai taho min dasu in zai zo, ka ga kar yazo bai same ni ba" Sadauki ya bude ido yace "Subis akwai zarar magana sai kace wata babba" Saghir yayi murmushi yana kallon inda Diyam take yace "gado tayi ai". Har adaidaitan zai ja sai Subay'a tace "Daddy zan kawo maka ziyara gidan ka".
In silence suka bar gurin kowa yana lissafe lissafe a zuciyarsa. Sai can sannan Sadauki yace "ba zan bashi aiki ba kamar yadda kika bukata. Bana son drama, nafi sonsa a nesa damu" bata ce komai ba, ya cigaba "amma zanyi masa komari ya samu kudin sa na gurin Kabir" Diyam tayi sauri ta kalle shi tace "kudin ka dai, ai kudinka ne" ya girgiza kai yace "nayi signing takarda cewa na bar masa kudina daya dauka, so legally yanzu kudin sa ne ba nawa ba. I have already talk to my lawyers, za'a siyar da kadarorin Kabir maybe za'a samu part of kudin amma nasan ba za'a samu gaba daya ba" Diyam taji dadi sosai a ranta tana yabawa kyawun zuciyar Sadauki, kamar yadda ya taba fada mata shi fire ne da ice, duk da wadda kazo dashi za'a tarye ka.
Tayi masa godiya sosai sannan yace "kin san wani abu? Ni da Saghir are alot alike" ta bude ido dan ita bata ga hadin su ba bayan kasancewar su musulmai kuma half fulani tace "ta yaya?" Yace "kinga ni da shi duk only sons ne a gurin iyayen mu. Kuma iyayen mu suna son mu sosai sannan sun nuna mana soyayya in their own different ways. Duk kanin mu iyayen mu sun bamu kudi, the only difference is yadda muka yi da kudin da suka bamu. Sannan kuma duk muna sonki" ya fada yana kallon ta, tayi saurin girgiza kanta tace "he doesn't" yace "he does. I saw it in his eyes yanzu da yana kallon ki"
Tayi saurin kawar da maganar ta hanyar cewa "kuma duk ku biyun kuna da kanwa mai suna Murja" yayi dariya yace "ni kanwa ta Murjanatu sunan ta ba Murja ba, kuma ni nafi shi son kanwa ta" tace "ita kuma duk duniya gani take yi kafi kowa kinta" and they laughed together.
*************************
Saghir ya juyo yana kallon Subay'a, yana kallo Sadauki ya kama hannunta ya bude mata kofa ta shiga mota sannan shi kuma ya zagaya ya zauna kusa da pregnant Diyam. Yayi sauri ya rintse idonsa tare da dafe kansa yana jin hawaye yana zuwa idonsa. Bai dauka har yanzu Diyam tana da gurbi a zuciyarsa irin haka ba, ya dauka ba zaiji komai ba inya ganta musamman saboda kokarin da mr Abatcha yayi masa, amma ita zuciya bata da linzami dole ya ja baya dasu ya daina ganinsu, ko kuma abinda yaji din yana da alaka da yadda Diyam din ta zama? Irin kyawu da cikar halittar da tayi? Wai hakan na nufin da ace ya kula da ita tsahon shekarun da suka yi a tare da irin haka zata zama kuma maybe da zata so shi? Lallai gaskiyar hausawa da suka ce tun ranar gini tun ranar zane, shi kuwa nasan ginin ya bushe dole sai dai ya hakura da zanen ko kuma ta sake sabon gini, sabon ginin wata rayuwar.
But with who? Wannan wata tambaya ce for another time. Maganar da Subay'a ta fada ta dawo masa zuciyarsa "zan kawo maka ziyara gidan ka" wanne gidan? Shi fa yanzu ko gidan kansa ba shi da shi, wayake ma maganar gida, shi ko kwandala bashi da ita. Bashi da komai sai freedom dinsa, kuma ya dauki freedom din nasa ya zama another chance at life. Chance din kuma da insha Allah zai yi amfani dashi sosai yadda har sai mutane sunyi mamakinsa. Yadda har sai iyayensa sunyi alfahari da shi. Iyayen da a wancan lokacin ya wofantar ya wulakanta, abinda yake tunanin shine dalilin zuwansa inda yaje ba wai Diyam ba.
Maganar mai napep ce ta dawo dashi hankalinsa, yace "yallabai munzo" ya leko dakansa yana kallon gurin yace "nan ne?" Mai napep yace "nan dai yayi min kwatance, yace jaen layin shago tara, gashi nan kuma har mun kusa fita daga layin tunda mun fara hango diga. Sai dai ka sauka ka tambaya" Saghir ya sauka yana kallon gurin, not that bad. Mai adaidaitan ya miko masa dari biyar yace "dubu biyu ya bani, ga dari biyar ka sha ruwa kai ma" Saghir ya karba harda yi masa godiya sannan ya tafi gurin wasu mutane su uku da ya hango a kasan bishiya ya gaishe su yace "dan Allah tambaya nake yi, gidan Alhaji Babba, bai dade da dawowa unguwar nan ba" duk suka ce basu sani ba, yayi gaba ya cigaba da tambaya amma babu wanda ya sani sai ya juyo ya fara retracing ta inda suka shigo yana yi yana tambaya, ga rana gashi dama jikin sa duk babu karfi.
Da kyar ya samu wanda yace "inda akayi biki watannin baya?" Da sauri Saghir yace "eh" sai aka hada shi da yaro suka koma can inda ya baro, suka je har gaban wani gida sannan yaron ya nuna masa ya juya. Ya tsaya yana kallon gidan, a tsahon rayuwarsa bai taba tsammanin duniya zata yi juyawar da har nan gidan zai koma shine gidan baban shi ba, gidan ma kuma gidan haya, gidan hayar ma kuma Diyam ce ta ke biya masa.
Ya shiga soro yayi sallama, Hajiya ya hango ta fito daga wani guri daya ga kamar kitchen tana amsa sallamar hannunta rike da wuka tana goye da wani yaron da bai sani ba a bayanta. Ta yarda wukar tana kiran sunan Alhaji, Alhaji ya fito, Hajiya yalwati ta fito, sai ga yaran gidan suma sun fito daga wani daki duk suna binsa da ido. Shi ya karasa shigowa, ya tafi gaban mahaifinsa ya durkusa amma sai ya kasa gaishe shi sai kuka ya kwace masa. Alhaji ya sunkuya gabansa ya jawo shi jikinsa ya rungume shi shima yana hawayen yace "bansan yau zasu fito da kai ba Saghir, da ko ba zan iya zuwa da kaina ba da sai in gaya wa mahaifiyarka ta je ko ta tura aje a taho da kai" Saghir ya goge hawayen sa yace "Mr Abatcha ne yaje ai, dashi da Diyam da Subay'a" ya fada yana jin dacin zuciyar dazu yana dawo masa. Alhaji yace "madallah dasu. Allah yayi musu albarka ya jikan Usman".
Nan fa gida ya rude da murnar dawowar Saghir, dan ma yanzu duk yaran babu saura kadan. Hajiya Babba ce ta kama shi ta kaishi daki, Hajiya yalwati kuma ta dora masa ruwan wanka, alhaji kuma ya aika a siyo masa nama da lemo kafin a gama abinci. Babu laifi suna cikin rufin asirin su duk da cewa alhaji har yau bai kuma gwada kasuwanci ba amma matansa suna yan sana'o'in su sannan yayansa mata da suke aikin gwamnati suna kokari gurin taimaka musu sosai, haka ma surukan gidan lokaci zuwa lokaci suna aiko musu da kayan abinci ko kuma suttura.
A dakin Hajiya ya huta, naman da Alhaji ya siyo masa sannan yayi wanka ya chanja kaya zuwa wanda Hajiya ta ajiye masa akan gado. Sai ta kunto yaron bayanta ta mika masa. Kallo daya yayi masa yasan waye, sai kawai ya ajiye shi a gabansa ya sunkuyar da kai, tace "sunan babanku ne dashi, Jawad ake ce masa" yaron ya rarrafa da sauri yabi bayan Hajiya yana kuka alamar bai san shi ba.
Dakin da yake soro, wanda kuma yake da kofa a waje shi dama Alh yasa aka gyara tun sanda yaji labarin dawowar Saghir gida. Aka shimfida carpet aka saka katifa, wardrobe, da kuma standing pan. Nan ne ya koma dakin Saghir.
Kwanan Saghir biyar ya warware, duk da dai babu inda yake fita sai yan'uwa da suke ta zuwa yi masa murna. Inna ma tazo ita da Asma'u da Subay'a, suka kuma bar Subay'a anan tayi weekend tare da mahaifinta da kakannin ta. A ranar ne Alhaji ya kira shi dakinsa. Suka zauna sai ya dauko wata leda ya miko masa, Saghir ya karba ya bude sai yaga kudi a ciki, ya zaro ido "Alhaji kudi ai, kudin menene wannan?" Alhaji yace "kudi na ne, sauran kudin gida na ne da kuma abinda na samu daga gadon Usman, su nake ta ajjiye dasu da niyyar duk ranar da ubangiji ya sake baka dama a rayuwa ya saka ka fito daga prison nima zan sake baka dama in baka su kayi jari" Saghir yayi saurin girgiza kansa hawaye yana bin idonsa yace "Alhaji kar kayi haka, ka bani kudi sau ba adadi ina salwantar wa, kai ma kana bukatar kudin nan alhaji, kana da iyali kaima. Ka rike kudinka alhaji ka kula da kanka da matanka da kanne na" Alhaji yace "da wanne karfin Saghir? Ni ai tawa ta kare, karfi na ya kare, dan haka kai na dora wa wannan nauyin ka juya wannan kudin ka kula da kanka sannan ka kula dani da iyayenka da kannenka, kuma ka cigaba da kula dasu ko bayan rai na ne".
Saghir ya karbi kudin ya rike yana jin nauyi a zuciyarsa "anya kuwa akwai soyayya sama data iyaye?"
Alhaji yace "akwai kuma wata magana da nake so muyi. Ina so ka kawo karshen rashin jituwar da take tsakani na da danuwana, ina son ka auri Suwaiba" ya dago kai yana kallonsa, Alhaji ya gyada kai yace "ta inda ake hawa tanan ake sauka. Tunda kuka bata dan haka ku zaku gyara". Sai Saghir yaji Fauziyya ta fado masa a ransa. Bayan ya bata takardarta sun rabu, daga baya sai ta koma tana gaya masa cewa tana da cikinsa, ta kuma ce zata haifi cikin za kuma ta jira shi as long as bata samu miji ba har ya fito sannan kuma yana da sha'awar mayar da ita. Bayan ta haihu kuma ta kai masa babyn ya gani. And after seeing Subay'a rike da hannun Sadauki, baya jin zai kuma barin wata yar tasa a wani gidan. Dan haka indai Fauziyya bata yi aure ba to sai dai ya hada su ita da Suwaiba.
Wata daya bayan nan Diyam tazo yi musu sallama zata koma Oxford, England. Washegarin zuwanta kuma alert ya shigo masa. Ya bude ido yana kallon kudin cike da mamaki ya tafi da sauri ya nunawa Alhaji. Alhaji yayi murmushi yace "Diyam ta gaya min jiya, kudin da Kabir ya gudu dasu ne aka dawo maka dasu. Zabi kuma ya rage naka kasan me zaka yi dasu".
Abinda Saghir ya fara yi shine ya dauki kudin da Alhaji ya bashi ya sayi gida madaidaici amma me kyau. Ba shine ya tare a gidan ba, Alhaji Babba da iyalin sa ne suka tare. Sai kuma ya sayi karamin fili a kusa da gidan a matsayin nasa "sai in zauna a kusa daku yadda zanfi jin dadin kulawa daku" next sai yaje har gidan Kawu Isa ya durkusa ya bashi hakuri sannan ya nemi ya bashi auren Suwaiba. Sai kuma ya tafi gidan su Fauziyya itama ya nemi auren ta. Amma duk kan su yace sai shekara mai zuwa idan ya samu nutsuwa sosai.
Daga nan sai ya tafi kantin kwari, tsofaffin shagunan Alhaji wadanda wuta ta cinye babu komai sai ginin, shima ginin duk ya mutu an sace kwanukan. Cikin kwanaki kadan ya tayar da ginin su, yayi komai ya saro kayan duk da yasan Alhaji yana siyarwa ada da kuma kayan da yasan zamani ya zo dasu ya zuba a ciki. Sannan ya nemo tsofaffin yaran Alhaji wadanda suke kular masa da shagunan a da ya dawo dasu dan su suka san kan kasuwa, shi kuma ya zauna cikinsu dan shima ya fahimci harkar.
Watanni kadan abubuwa suka warware wa Saghir, ya hada kudin neman aure ya kai gida biyu aka saka masa rana watanni takwas masu zuwa za'ayi duk a tare, sannan kuma ya fara ginin gidan sa a hankali. Gidan da yake da yakinin zai zamanto tushen sabuwar rayuwa a gurin sa.
****************************
A lissafin Sadauki so yayi in sun bar Nigeria su fara tafiya Canada suyi kwana biyu tukunna, amma Diyam ta tubure masa ita bata son zuwa, ya gane abinda yasa bata so, ita kunya take ji ake ganin ta da ciki. Yayi dariya "to wai ke banda abinki, ni fa banga abin kunya anan ba, kowa ma fa yana yi" ta juya masa baya tana kallon Subay'a a cikin swimming pool tace "kuma kawai sai in je gidan inyi ta yawo da ciki suna kallona?" yace "baiwar Allah, idan baki je da ciki ba in kika haihu dai ai dole zasu ganki da dan ko? Ko shima cewa zaki yi ba ke kika haifa ba?" Tace "ai kuwa in naje gidan da baby to har in bar garin ba zan dauke shi ba" ya rike baki "to waye zaiyi feeding dinsa?" Tace "sai ya sha madara" ya kwanta akan camp bed din da yake zaune akai ya rufe ido yace "you are impossible Diyam, ke fulatancin kamar a kanki ya kare" ya sake cewa "kiyi addu'a to, kar a saka bikin su fanna kafin ki haihu, sai muga yadda zakiyi da cikin a gurin biki" tayi saurin cewa "Allah ya kiyaye, insha Allah sai na haihu". Sai ta jawo kujerar da take kai kusa dashi tayi tagumi tana kallon sa, ya bude ido yana kallon ta yace "what?" A hankali tace "I want to kiss you, kuma Subay'a tana kallon mu" yace "ohh, a wannan bangaren kam kin ajiye fulatancin ko?" Sai kuma ta rufe ido tana dariya.
Addu'ar Diyam dai bata karbu ba, dan suna komawa makaranta aka saka ranar bikin su Sa'adatu kuma wata biyu kadai aka saka, meaning cikin Diyam yana da wata takwas kenan za'ayi bikin. A dole Diyam ta taho Maiduguri lokacin bikin da katoton cikinta, Sadauki yana ta yi mata dariya amma sai ta maze da shiga harkokin bikinta sosai ta rike role dinta na matsayin babbar yaya. Da ita akayi shawarar komai, da ita aka sayi komai, wani abun ma in ana nema sai Mama tace azo wajen Diyam.
Su Inna da Mama da Asma'u ma duk sunzo gurin bikin sun kuma Kawo wa amaren gift sosai har sai da Maman su Murjanatu tace "kayan nan anya basu yi yawa ba Amina?"
Aka daura aure aka kai amare gidajen su. Sa'adatu ta auri Aminu an kaita Abuja. Falmata kuma Saifullahi mutumin Kano amma mazaunin Canada dan haka can zasu koma, Fanna kuma ta auri cousin dinta Al-mustapha zasu zauna anan Maiduguri amma zata zauna a gurin su Diyam ta karasa karatun ta.
Bayan su Diyam sun koma England sai hankalinsu kuma ya koma kan haihuwa, Sadauki yana ta rawar kai, duk zuwa asibiti tare suke yi idan kuwa yaga namiji ne zai duba ta sai ya ja abarsa su bar asibitin. Twins ne kamar yadda Sadauki yake ta addu'a. Diyam tayi tunani sai taga cewa ba zata iya tuno yadda haihuwa take ba tunda bata yi labor a haihuwar Subay'a ba, haihuwar twins kuwa ba zata iya tuna yadda abin ya kasance ba dan haka sai ta shiga maternity classes, anan ta fahimci komai ta kuma yi browsing wasu abubuwan ta sake fahimta.
Abinda take tsoro guda daya shine shigar Sadauki gurinta in tana labor, tasan kuma za'a bashi option din shiga kuma tasan zai shiga din. Sannan tasan in dai ya shiga sai ya hargitsa daga ita har me karbar haihuwar kuma in yaga wahalar da ake sha a gurin haihuwa sai sunyi rigima kafin ya barta ta samu wani cikin. Ta kuma san yadda yake son yaya, dan haka ta yanke shawarar yi masa dabara yadda ba zata haihu a gabansa ba saboda ta haifa masa yaya as many as yadda Allah ya basu.
Ranar data fara jin alamar labor da daddare sai taki nunawa Sadauki, da safe kuma sai tayi pretending as if bacci take yi har ya gama shiryawa a hankali dan kar ya tashe ta, ya zo yayi mata kiss ya fita. Sai bayan fitarsa sannan ta tashi ta dauko jakar tafiya asibitin ta wadda already ta riga ta shirya ta ta kuma yi driving kanta zuwa asibitin. Sai da taje suka aunata suka kuma tabbatar mata da cewa haihuwa zata yi sannan suka bata daki suka kuma nemi su kira mijinta amma ta hana su tace sai ta haihu tukuna.
Ta sha wahala ba kadan ba, Sadauki ya sha kira kamar sunan sa zai kare ta kuma yi nadamar kin gaya masa dan da yana kusa ko ganin sa in tayi zata ji dadi. A haka har Allah ya sauke ta lafiya ta haifi namiji first, sai data huta sannan labor ya sake dawowa ta haifi mace. Ana miko mata su taga fuskar babansu amma fatarta, sai dai namijin bai kai macen haske ba.
Sai da aka gama garata aka kuma gyara babies din ta kuma danyi bacci kadan ta huta sannan tace su kira shi. 30 minutes after kiran nasa sai gashi ya shigo asibitin hakan yasa Diyam ta tabbatar da cewa yayi breaking every traffic rule a hanya saboda sanin nisan asibitin daga office dinsa.
A rikice ya bude kofar dakin da aka nuna masa ya shiga. A tsaye ya ganta a gaban window ta juya masa baya. T-shirt dinsa ce a jikinta, wadda ta kawo mata har zuwa rabin cinyarta, gashin kanta a barbaje wani ya sauka a bayanta wasu akan kafadun ta wasu kuma sun zubo kan kirjinta. "Diyam" ya fada cikin sarkewar murya. Ta juyo tana kallonsa, hannunta rike da jariri tana rocking a hankali, fuskarta da faffadan murmushi. Ya karaso cikin sassarfa ya jawo ta jikinsa ya rungume ta yace "don't you ever do that to me again" ta kwantar da kanta akan kirjinsa tace "am sorry my Lion. Bana son in tayar maka da hankali ne" yace "kinsan tashin hankali da naji kuwa? Kinsan da yadda nazo asibitin nan kuwa? I tot karya suke yi min da suka ce lafiyar ki kalau, I tot ba zaki iya haihuwa ba tare da ni ba" tace "I missed you sosai, nayi ta kiran sunanka" ya danyi dariya yana dago fuskarta da hannun sa daya, taji kunya ta mayar da fuskar kasa.
Ta zaunar dashi akan kujerar da take dakin ta mika masa babyn hannunta, ya dan leka cikin diaper dinsa fuskarsa kamar zata yage dan murmushi. Ta dauko dayar da take bacci a kan gadon su ta mika masa itama. Ya rike su hannu bibbiyu inya kalli wannan sai ya juya ya kalli wannan ya kasa tantance wanne yafi kyau a cikin su. Yayi musu addu'a. Tana tsaye a gabansu tana kallon su sai ta fara buga kafa cikin shagwaba, ya dago kai yana kallon ta cikin alamar tambaya sai tace "ni a ina zan zauna, sun tare min gurin zama na" ya daga babies din da sauri yace "zo ki zauna akan cinya" ta tafi ta zauna tana karbar daya, ta rike ta da hannun ta daya dayan hannun kuma ta zagayo wuyansa dashi. Sun jima a haka suna kallon kyautar da Allah yayi musu sannan yace "Baffa ne da Ummah. Baki ga yadda suke ta kokarin rike hannun juna ba?" Diyam tayi dariya tace "babu ruwana sai na gaya wa Inna" yayi murmushi yace "so kike ta biyo ni da muciya?" Sukayi dariya a tare. Sai ta kwantar da kanta a wuyansa shi kuma yayi kissing forehead dinta tare da sauke ajjiyar zuciya. A hankali yace
"ALHAMDULILLAH"
Godiya ta tabbata ga Allah da ya bani ikon kammala wannan littafi lafiya. Allah ya kara salati ga fiyayyen halitta (SAW) Allah kuma yasa muna da rabon ganin sa baki daya.
Godiya ga fans dina wanda na sani da wanda ban sani ba a duk inda suke, alkhairi ya kai muku har dakunan ku, ina sonku sosai da sosai, idan babu ku to kuwa tabbas babu ni.
#MyWattpadpeople, thank you for all the votes, the comments and the encouragement.
#MamanMaamaNovels na Facebook ina godiya da soyayyar da kuke nuna min a duk books dina, ina ji daku sosai mazan ku da matan ku.
#MamanMaamaNovels groups 1,2,3,4,5 na WhatsApp, ina ji daku tamkar nama daya a miya. Allahu ya bar kauna.
The ladies at #Shatuuskingdom, #zaurenBiebeeIsa, #KDM soldiers, #ZeenatNovel, #SameenaAliyuNovels, da sauran groups din da nake ciki da wadanda ma bana ciki, ina godiya kwarai da gaske. Allahu ya bar zumunci.
Zaku sake ji na da wani labarin, amma banan kusa ba, maybe sai 1-1-2021 maybe kuma kafin nan. In kuma babu rabo to Allah ya hada fuskokin mu a aljannatul Firdaus. Allahumma ameen.
Please pray for me a duk sanda labarin mutuwa ta ya riske ku.
ILYSM.
No comments