Budurcina 5

 




*🕊️BUDURCINA!🕊️*

Love, romance, sympathetic, and erotic story.


2023/2024 New Hausa Novel

Written by 

      *Aunty Aysha Mamanteddy*




          Free page 5


*In the next 3 free page shafin kyauta na wannan littafin zai ƙare , wato a page 8 shafin ƙyauta na labarin zai ƙare , ga masu buƙatar cigaban labarin Budurcina regular payment ₦300...Vip payment ₦600... Special payment ₦1000 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan kuma Vtu transfer ne sai ki tura ta Wannan number 09061466409*


Hade fuska Audi mai Shayi yayi yana mutsike idanun sa da suka yi jajir na tsaban wuyar itacen tukunyar shayin nasa da yake ji , ga itacen wahalar su yake sha sai zuba uban hayaƙi suke yi , gyefe guda kuma ga tarin Almajirai masu jiran idan an saya shayin nasa an sha a rage su dauka . Bangare guda kuma ga Phania wacce ta narke masa fuska tamkar mutuniyar kirki tana basa Haƙuri kuma sarai yasan halin ta , inshallahu ko ya rabu da ita tace ba zata yi faɗa ba sai anyi da ita da Almajiran nan . Kullum girma take yi amma ganin kan ta take tamkar yarinya yar sheƙaru goma , duk da kusan zata kai Shekaru 14 a yanzu . 


Ke Phania ɓace mun da Gani sanin halin ki ne yasa Ni nace ki tafi ki bani wuri . Audi ya kuma katse Phania yana zuba mazurai . A'a haba Audi , Meye akayi akai Ragowar shayin Kofi dai ? Muryar Ɗaya daga customers din Audi ya katse Shi , wanda jin haka yasa Audi Kallon Malam Bello yana fadin “ Wallahi Phania bata ji , kullum sai tazo wurin nan ,kuma sai tayi Tsokana anyi dambe take jin dadi ,tamkar ba mace ba ” . 


Ayya ba itace ƴar gidan malam Ummaru ba ? ,Kaga zuba mata shayin na kofi ɗaya sai ka cire anan . Kallon Malam Bello mai kanti Phania tayi tana Wangale masa baki cike da jin dadi ta hau murna da tsalle tana fadin “ Na gode sosai Malam Bello mai kanti , Allah yakaro dadin masu sayayya . Kallon ta Malam Bello yayi yana sakin mata Murmushi kamin yayi magana ne Audi mai Shayi ya katse su da dangwara mata shayin a leda yana cewa “ Amshi jeki abin ki ” . 


To . Ta furta tamkar babu komai a ranta , sai da ta riƙe ledar shayin ta fara yin nesa da su Audi ne sannan ta ɗaga murya iya ƙarfin ta tana cewa “ Na gode Malam Bello mai kanti, kai kuma Audi inshallahu sai gobe ka wayi gari babu kowa da zai zo sayan shayin nan naka , bani ka hana da Umma na ba . Sai kuma gashi ALLAH ya bani .


Kuji mun yar ba ubun yarinya ,dama bana faɗa maku ba ? , Ai haka take .  Muryar Audi ya katse su yayin da Phania ta zunduma tana rugawa da Gudu . Dariya jama'ar wurin aka sanya wasu na cewa “ Ƙuruci dangin hauka kenan yaro man kaza” . 


Umma Umma...!! Muryar Phania gaba ɗaya ya gama karaɗe cikin gidan tana ƙwaɗa kiran sunan Umma . Wani irin kallo Rahmatu tabi ta dashi dake Aikin talgen tuwo , kana ta caɓe baki tana cigaba da daurare roba . Sam Phania bata bi ta kan matan gidan da wasu ke Hidimar Alwalar Magriba ba , cikin Ɗakin Umman ta ta nufa kai tsaye tana kutsa kai babu sallama don babu wanda yayi mata koyi da tayi hakan . 


Wani irin ajiyar zuciya ta sauke tana sakin Murmushi kana ta kalli Inda Umma ke zaune jingine da bangon yanda ta bar ta. Umma na Alhamdulillah zamu ce , yau zamu sha Shayi , ba zaki kwana da yunwa ba irin na jiya . Uban wane ya baki shayin Satowa kika yi kenan ?. 


Muryar Rahmatu ya katse ta wanda ta banko dakin , a tsaye don ita Haushin Phania da uwar ta take ji Tamkar ta kashe su ta huta , na biyu ga Irin abun da ta furta gami da yar ta Inna . Sata...! 


Phania ta furta tana mikewa tare da aje ledar shayin a gyefen Umman nata . Eh satan kudin kika yi kika sayo kenan ? Don ban ga uban da ya baki ba ?. Ko kuwa Uwar taki dake kwance tare da cutar shashi ne ta baki kudi kike nufi? Ko kuwa Uban ki da yake can zaman majalisa babu sana'a bare aikin yi sai zaman banza ?.


Wani irin kuka Phania ta fashe dashi mai daga Hankali da gunji wani irin tsuma take yi na masifa wanda jin hakan yasa Matan gidan dake waje saurin shigowa dakin.  Cikin wani irin ihu Phania ta dauki tafasasshen Ruwan shayin da yake cikin ledoji biyu tana nufar Fuskar Rahmatu dashi , jikake shaƙƙƙ.........Ta wanke ta dashi duka . A wani irin ihun azaba Rahmatu ta fara salallami don bata yi zaton hakan daga Phania ba . 


Ihu Phania ta kuma sakawa tana rarumar komai na wurin tare da nufo Rahmatu dashi , hakan yasa matan gidan darewa suna ficewa da gudu ciki har da ita Rahmatun dake fadin “ Phania kashe Ni zaki yi ?. Ita kuwa Phania ihu take iya iyawan ta tana faɗin “ Umma ta zaki zagar mun ? ,Mene tayi Miki? Me umma ta tayi Miki ? Yau sai na rama ma Umma na . Maganan take yi cike da zallar hauta da kuma nuna zafin soyayya ga Umman nata tare da jin tsananin ƙiyayyar Matar Uban nata Wato Rahmatu . Taɓarya Phania ta ɗauko tana nufo Rahmatu dashi kana tace “ Me yasa zaki zo inda Umma ta take kina mata hayaniya? Me yasa zaki zagi Umma ta? Ko me nayi Miki kiyi mun mana . Wani irin duka Phania taji an mata ta bayan Wuyan ta wanda sai da ta ɗauke wuta ji kake “ Fauuuuu” .  Wani irin duhu ta gani ,jin ta da ganin ta duka sun ɗauke a lokaci guda , kusan mintuna biyu tana a haka kana ta fara jin Masifar Mahaifin nata yana zage ta ta uwa ta uba . Nayi nadamar haihuwar ki Phania, ke bakya kaɗai ba har ta Uwar ki tun da na Aure ta naƙi gaba naƙi baya , yanzu Wacce take rufa mun Asiri tsawon shekaru kike son kashemun ita ? Kullum baki da ɗabi'a sai baƙa? Yau zanci uban ki a cikin Gidan nan, sai naga mai goya Miki baya . Yana maganan tamkar wanda aka saukar masa da Aljanun ifiritu gaba ɗaya a zauce yake tun da Phania ta taɓa masa matar so wato Rahmatu . 


Baba...!


Phania ta kira sunan sa a hankali idanun ta na tafiyar da hawaye , jan majina tayi kana tace “ Baba Umma ta zaga kuma tace mun nayi sata , kuma banyi ba ”. Zanci uban ki ne ...! Yau sai naga jini na tsiyaya a jikin Phania, Idan ba satan kika yi ba wake baki kuɗin? Gantali kika fara ? . Kasa magana Phania tayi yana kallon Mahaifin nata dake tsalle yana jawo wayar inji , ita kuwa tsayawa tayi babu tsoro dama haka take da wannan kangarewar ba dai ta gudu ba ko tsoro ko kuwa mene zata aika ta . Bata da tsoro ko kaɗan ga girgiwa.  Muryar Malam Ummaru ne ya katse su yana cewa “ Ai dama na faɗa Miki Sai tayi karuwanci muna nan dake zaki gani ,wannan yarinyar tun tana ƙaramar ta jinin harijai take dashi , in banda iskanci menene hadin ta da almajirai maza , yanzu har wurin mai Shayi ta koma zuwa . 


Sakin baki Phania tayi tana kallon Mahaifin nata , kama cike da Yarinta tace “ Au dama Baba kasan ba satowa nayi ba , shine kuma ka yarda da  Rahmatu tayi maganan ?. 


Cikin doka Tsawa yana daga malunmalun ya furta “ Na yarda nace na yarda dan Uwar ki , Rahmatu da kike ganin ta ko Wuƙa tace na danna Miki a wuya na kashe ki zan kashe ki na huta da dauko mun Magana da kike yi , don da zama da Rayuwa da irin ki gumma ban haihu ba . Baba nice fa kadai yar ka ko ka manta ne ? Inna yar Rahmatu ce , ba kai ka haife ta ba ,mahaifin........ Shegiya yarinya ƙonanniya ba ilimin boko bana addini sai na zaro zance tauuuuuuuuuu kaji ya zuba mata Bulalan Injin da ƙarfi wanda sai da Phania ta kusa Shiɗewa don azaba . 


Ganin haka yasa Wasu matan gidan kecewa da Dariya ciki har da Mubashshira don dama duk sun gaji da halin Phania da tijaran da take masu , idan tana cikin gidan nan basu da sakat Magana a hankali suke yin shi , a cewan ta babu mai zarran ɗaga murya umman ta Bata da lapiya don haka dole ne ayi shiru . Su da yaran su kullum shiru ² zaka gan su basu da walwala sai idan Phania bata nan . 


Wayyo Umma na...Baba zaka kashe Ni , baba zafi wayyo .! Duke yar banza...!! Muryar Rahmatu ya katse su tana Dada ingiza masa Phania wacce yake mata duka tamkar zai kai ta lahira . 


Luba ce ta mike daga gindin rijiyar da take ,duk abin da suke yi tun daga fari shigowar Phania a idanun ta . Zaf³ ta iso inda Malam Ummaru ke jibgar Phania kana ta kai hannun ta tana ficncikar ta daga gare sa . Amma gaskiya Sai kayi nadama a rayuwar ka malam Ummaru.! Wallahi wannan Abin da kake yi ma Wannan yarinya da Umman ta Atika zalunci ne , kuma ka tuna da ALLAH . 


Furucin da Luba tayi kenan tana Ƙwatar Phania wacce ta ruga da gudu tana shigewa ɗakin Umman ta cikin wani irin matsanancin kuka . Ina ruwan ki yar ki ko ya ta.? Muryar Baba Ya katse ta . Wani irin kallo Luba tayi masa kana ta kalli Rahmatu dake Gyefe tana ja masu tsaki . 


Kasan nasan Komai, tamkar idona aka yi , Rayuwar ka dana Umman Phania haka shigowar Rahmatu don haka ko da yake yar kace , wallahi ba zan iya ganin zalunci nayi shiru ba . Kwana nawa baka basu ci baka basu sha , yarinya tun tana yar shekaru 7 take baran abincin da zasu ci , har yanzu bata huta ba , sannan kuma bin ta da jifan ta da munanan kalamai . Kai ba zance maka yatsu da yawa ba , don yar taka itake nan gata nan Phania bayan ita kuma baka da kowa , ke kuma Rahmatu kina da yara a Gidan mijin ki , ki sani duk abin da kika yi za'a yi mana ki . Ni wannan tunasarwa ce . 


Ai da sai ki tafi masallatai ne ki saka lasifika ba'a anan ba , aikin banza aikin Wofi . Daga tsawatarwa Shikenn sai Kice ina azabtar da Yarinya? Duk abin da nake mawa Phania a gidan nan ba'a gani?. Ai Shikenn wallahi da Allah .... Rahmatu take maganan tana matso hawaye na makirci tare da kallon malam Ummaru dake ta zuba mazurai , kaga idan Phania kashe ki zata yi kar ka kara mata magana , idan na mutu sai a kaini makwancina hankalin ta ya kwanta .


Kaman Wani gaula ya fara rawar baki yana cewa “ A'a sai dai ita ta mutu ko uwar ta ,don kece me amfani a rayuwa ta , su kuma basu da wani Amfani a nawa Rayuwar.  


Haka dai gidan har wuraren isha'i babu daɗi , shiru kake ji tun bayan faruwar al'amarin , ita kuwa Phania ko alwala bata saka umman nata tayi ba sai kuka kawai da take yi , Damuwar ta shayin ta zubar sannan kuma Umma babu abincin da zata ci . Juyawa tayi tana kallon inda Umma take cikin duhu don ko Arziƙin fitila basu da , a haka suke kwana su tashi ita ta manta rabon da taga gilmawar fitila da Dare a cikin ɗakin nan nasu.  Saurin muskutawa tayi tana miƙewa tare da cewa “ Umma na ki kwantar da hankalin ki , Phania tana cikin koshin lafiya, yanzu Zanje na samo Miki abincin da zaki ci . Ba tare da ta jira jin na bakin Umman nata ba ,don tasan ba magana take ji ko tayi ba , nan take ta fice daga Dakin tana barin cikin gidan baki daya . 

**

Ƙwance take tayi luf a saman bisa ƙayataccen Gadon nata ,wanda komai nasa ke dauke da kala mai haske na baby wato Pink colour, tun daga Blanket zuwa Bedsheet sune aka rufa Wannan haɗaɗden gadon da shi . Idanun ta a lumshe suke amma saman idanun nata da Fuskar ta wani irin fankacecen gilashi ta sanya fari mai haske da ya sauko har wurin Kuncin ta . A hankali take saka hannun ta cikin wani roba ƙarami dake ɗauke da Choco cream cheese tana kaiwa bakin ta a hankali , wani irin murmushi take saki ita kaɗai kana naga Ta ware kyawawan idanun ta tana sauke su bisa Wani katon frame dake jikin gaban gadon nata da ta saka . Haɗe laɓɓan ta tayi tana kai kiss Uhmm💋. Yaushe zaka dawo gare mu .? Yaushe zamu ganka ? Yaushe zaka Aure Ni...? I really miss Yhu Akhy Deeyaan....Ta ƙare maganan tana kai hannun ta tare da shafa Hoton wani kyaƙyƙyawar matashin Saurayi wanda ban tsaya kare masa kallo ba , don kyawunsa ya Girgiza alkamina, amma maji a gaba . Barka da huta Miss Lele . Muryar Ma'aikaciyar Lele ne ya katse Ta , wanda jin hakan yasa Lele jan Dan tsaki tana yatsine fuska kana tace “ Shareefa matsa mun ƙafa na , yanzu na dawo daga Exercise. 


Ƙasa tayi da ƙafanta guda daya na bangaren dama , don haka lele take tamkar Namiji ko don yanayin cikin gidan ne yake a haka to ga dai ya nan . Kunsan Ezdaan Estate maza da mata ne ba sai mun dawo baya ba.  Komai nasu tare suke yin shi ,basu san banbancin wannan mace ne ko namiji ba su duka kallon daya suke ma juna . Musanman su Lele deeja sai su kwana a dakin cousins din nasu da yayyun su . Wannan shine taƙaitaccen labarin halin da gidan Ezdaan ke ciki . 

**

Raɓe² take yi cikin wannan Uban dare da ya fara nisa sam Ta rasa inda zata nufa don ta nemo ma Umma Abun da zata ci.  Rintse ido tayi tana zama gyefen wani gida kana ta rafka uban tagumi . Tana zaune Ustaz Abdullahi yazo wucewa wato mai gidan . Ke yarinya me kike yi anan Wurin haka ? Tashi maza tafi gida . Yayi mata Maganan a lokaci daya.  Kallon sa Phania tayi kana tace “ Tom don Allah bawan Allah kai taimaka mun da kuɗi ” . Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un....yana wani kama jan Salallami irin na ustazan nan da nairan su ba zasu baka ba , duk nacin ka sai kayi haƙuri yana kai hannu tare da jan dogon Gyemun ƙasan wuyan shi . 


Zamani yakai haka ..? Hasbunallah... hasbunallah... hasbunallah....!!! Ya furta kalmar har kusan sau uku . Ke maza tafi gida ,idan kinje gida Kice ma iyayen ki su kara kulawa dake sosai.  Amma Ni a yanzu ina da kudu amma ina da iyali . Kallon shi Phania tayi tana kauda kan ta , tare da cigaba da zaman ta a wurin , ganin haka yasa Ustaz juyawa Yana shigewa cikin gidan sa . Bayan shigar sa ne Phania ta Juyo maganan sa na dawo mata , ina da kudi amma ina da iyali . Hummmm wani gwauron Numfashi ta sauke kana ta mike cikin sauri tana cewa " Bara sai na roƙi iyalin naka sai ka bani . 


Assalamu alaikum ya habibati....! Muryar Malam Abdullahi ya katse Amaryar nasa Nafisa Wacce ta fito cikin sauri daga daki ana karairaya da wannan daren , sai baza ƙamshi ake yi na amare . Amin wa'alaikassalam ya Habibi😍 barka da Dawowa...tayi maganan tana nufo shi , miƙa mata baƙar ledar hannun sa yayi yana Wani irin Faɗaɗa Fara'ar sa tare da Kai hannun sa yana Ɗaurawa Bisa kan ta , sai kuma daga bisani ya rungume ta suna furta " Mashaallh Alhamdulillah" .

Billahil azeem Ina son ki Nafisat. Wangale baki Phania tayi ganin Ustaz da Matar nasa a haka a tsakar gida , wannan yasa ta saurin furta “ Malam Abdullahi kai ne a haka ? , Wannan ne kuke yi ai iskanci ne wannan kai fa kake faɗa a wurin tafsir ” . Cikin wani irin sauri Malam Abdullahi ya janye daga jikin Nafisat yana furta La'ilaha'illahu , Wai wannan yarinya meye haka ne ? Ina iyayen ki ? Me kike so...? . Kallon sa Phania tayi kana tace “ zan rufa maka Asiri ba zan faɗa ma kowa ba , amma kasani na ganka da idona kana yin abun da bashi da kyau , don haka Ka bani kudin nan na jikin ka na tafi . Kudi kuma , mene zakiyi da kudi da kankantar shekarun ki .?


Umma ta .! 


Ta furta idanun ta na ciko da Ƙwallah , kana ta cigaba da cewa “ Umma ta ce babu lapiya, kuma ina son taci Abinci idan nayi kudi nan gaba zan kaita asibiti yanzu dai ka fara taimakona da kuɗin hannun ka . Cike da naci irin na wanda baya banbaruwa ustaz Abdullahi yace “ A'a A'a ....Ni talaka ne Allah ya sani . Baki da labarin Ƙungiyar DYHJ .? Suna taimaka ma marasa lapiya duk girman cuta , ke har ƙasar Nigeria ake fita da mutum ba kudin sa babu na dangin sa . 


Kallon sa Phania tayi baki sake tana mmkkn hali irin na malam Abdullahi, motsa ɗan ƙaramin bakin ta tayi tana furta “Kaman ya ya ? , Ban gane ba , gwamnati ne ?” .


A'a ba gwamnati bane Ƙungiya ce ta taimako na wani Matashin Balarabe ne ko Bature to dai ban san takamamman Bature ne ba ko Balarabe , amma naga hoton sa bai kama da yan Nigeria ba , Bama anan Afrika yake ba .Sunan Ƙungiyar ta arewacin najeriya da ya buɗe DYHJ , amma yana can....faɗa mun da Sauri malam Abdullahi,yana ina ne ...............!



*Hummmm free page zai ƙare a page 8 maza hanzarta wurin mallakar taki  ....shin Ya al'amarin zai kasance da Phania? Wanni kungiyar ce DYHJ...??? kar ku manta regular payment ₦300 Vip payment ₦600 SPC payment ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*


Bhuzuwa empire

*AYYUKAN BUXUWA EMPIRE 08139762831*

1.munayin aikin bakar mallaka wacce muke kira bita zai zai , amma sai mun yi istihara mun bin cika Zuciyar ki .


2. Munayin aikin haihuwa ga wacce bata samun haihuwa inshallah da kinzo taskar empire za'a haske da buwaya na mai sama'u .


3. Munayin aikin bakar firraku wacce duk wacce a kai mashi sun rabu kenan har abada.


4. Munayin aikin da idan mijinki na biye biyen mata kina iya kimasa mallakar gabansa ki gama dashi , shi da wata mace sai ido. Wannan mazinata ake yi mawa ,idan kin san kina da kishiya da cutarwa . Na iya wanda mazan su ke bin matan banza a waje ake mawa .


5. Munayin aikin dafa'i na zallar Ayar ALLAH .


6. Munayin aikin farin jini a duk inda kk ko kuma na samari .


7. Munayin mallakar  wajen a aikinku ko na office wannan na ma'aikata ne .


8. Munayin aikin aljannu musanman wanda aljani ya takura masa ko ya hanashi aure ko samun samari ko saurayin da yazo yau gobe ba zai dawo ba. Ko ya hana zaman gidan Aure . 


9. Munayin aikin budi akan kasuwanci .


10. Munayin aiki a kan miji idan baya maka kyauta ko baya kula da kai da yara tare da ɗaukar hidimar ka . Maza taho Taskar empire kisha mamaki . 


Sannan  duk macen da takeso a zautar mata da mijin ta a kanta a mallake mata shi sai yanda tayi to akwai wani aiki da nasomayinsa wanda nake aikawa da turaren gari garii idan ki kayi amfani dashi komai nashi sai kinsani haka kuma komeye kike so sai ya baki. Amma sai mun duba zuciyar ki idan babu cutarwa .


*WhatsApp or call*

 *08139762831*


Mata masu bukatar kaya da'a wato mgnn mata masu aiki da rubutu ko wanda ba mai aiki ba available maza ku garzayo gurin *Buxuwa empire* domin jin dadinku ma'aurata akan number ta dai wanda kuka sani gashi *08139762831*

Masu bukatar shuumin humra komai ya haɗa subhanallah wannan humra tayi wlh wlh wlh duk wacce tayi amfani da wannan humra mijinta wata ya mace ta burgesa an gama kuma , sannan da na farin jini mai kyaun gaske wanda ake haska tauraronki mata ku garxayo wajen *buxuwa empire* domin kuji dadin ku ku kuma godiya ga ALLAH


*BHUZUWA EMPIRE*

*08139762831*

Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce  ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* *kaikajawa kanka ,  Rai daya janzaki, yau na sake dawowa domin  muku Domin tallata muku Littafaina mai Suna *(RUDANI )* Da kuma *Makauniyar Shari'a*  littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba  Hausawa sukace Gani yakori ji.


Karku Manta  *Makauniyar Shari'a* sabon littafi ne mai bibiyar Ma'anar sunan sa.


RUDANI littafine mai cike da Rudani da ban Al'ajabi , duk wacce kika fi buƙata zaki biya kudin sa Naira ɗari biyar kacal.


Farashin kowannen su Naira Dari biyar ne 500 kacal  

Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (09069080725 ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci.

Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank

Turo shaidar biya akan wannan 09069080725 sai najiku.


    *Mamanteddy*

No comments