AGIDANA Complete Hausa Novel

 

[10/27, 10:33 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: *A GIDANA*


In the name of Allah the most Beneficent the most merciful.

Praise be to Allah lord of the words.




The beneficent the Merciful.

Master of the Day of judgement.

Alone we worship;Alone we ask for help.

Show us the straight way

The way of those on whom Thou has bestowed the Grace, those whose portion

Is not wrath, and who do not go astray.


   Gaisuwa tare da jinjina da fatan alkairi gareku daukacin masoyana, ina mika sakon gaisuwa gareku, dafatan kowa yana lafiya, musulmai da suka rigamu gidan gaskiya Allah ya jikansu, mu da muke da rai Allah ya sa mu gama da duniya lafiya, masu ciki Allah ya saukesu lafiya, wadanda ke neman haihuwa Allah ya basu, masu neman aikin yi Allah ya taimakesu yasa su samu Ameen suma Ameen.

_Oh ina fatan me karatu yayi saurin cewa Ameen..... lol duk da nasan ke ko kai ka fada.........._


  Dafatan za'amin uzurin jina shiru da akai😄


_Sai dai dan Allah inaso mai karatu yamin uzuri akan wannan littafin bazan samu damar yin posting kullum ba saboda wasu dalilai._


Nagode🥰


🍀 *A GIDANA*🍀


*_Na Ayusher Muhd_*


*Shafi na Farko*


Da sauri ta gama shafa hoda sannan ta dau dankwalinta ta daura, agoggo ta kalla sannan ta jawo jakarta da sauri, ta bude wardrobe ta dauko mayafinta ta rike a hannu ta fito.


Kitchen ta nufa dan tasan yana ciki, tana shiga ya juyo ya kalleta yace "Honey an fito?"


Rugumeshi ta matso tai tace "Yau wani irin bacci ne ya kammani dakyar ma bude idona."


Murmushi ya mata sannan ya sumbaci kuncinta yace "your tea."


Dauka tai ta kalleshi sannan ta sumbaceshi itama tace "Thanks love."


"Kin manta ni zan kaiki?"

"Oh! Ashe fa na sallameshi."


Kai ya girgiza yace "Honey a rage fada, dan Allah drivers nawa kika kora?"


"Ka zauna zani da kaina." Ta fada tare da juyowa, da sauri ya riko hannunta yace "na manta sune basaji."


Harararsa tai tace "wato ni uwar fada ko?"


"Nooo inji wa? Yanzu na dau mataki?"


Murmushi tai tace "ni ka bari na tafi da kaina yafi sauki."


Key dinsa ya dauko wanda ke saman fridge yace "muje."


Falo suka fito hannunsu rike da juna, Goggo suka gani zaune tana kallo a falan.


Kusa da ita ta karasa tace "Goggo ina kwanan mu?"


Goggo ta kalleta tace "ni jiya mantawa kikai kince zaki bani kudin anko?"


"Oh na manta, amma ni Goggo wai wani anko ne ku manya daku?"


Fuska ta hade tace "ba sai kin fadamin magana ba, in bazaki bani ba kawai kice bazaki ban ba, fadar maganar na menene?"


Kallan agogo tai ganin lokaci na wucewa tace "zan bashi sai ya kawo miki."


Da sauri tai gaba "ke wlh Goggo, ina laifin ki bari sai ta dawo? Bayan na fiki bukatar kudi yanzu."


Harara ta maka mai tace "wannan damuwarka ce, kuma wlh ka kawon kudina yanda aka baka."


Binta yai da gudu, tana tsaye gaban motarshi yai saurin bude mata sannan ya zagaya ya shiga gun driver.


Yana zama ya tada motar yaja suka bar gidan.


Mai gadin daya bude ta kalla tace "zan turama kudi kaba mai gadi nashi naga wata yazo karshe, sai kaba Goggo na ankon, dan ko tambayarta ban ba nawa ne."


Yai saurin cewa to, kallansa tai tace "ka cinye kudinka ne?"


Kallanta yai sannan yadan sosa keya, ajiyr zuciya tai sannan tace "zan turoma dan dama anyi albashi, sai dai Honey plz adan rage kashe kudi."


Kallar tausayi yai yace " sry Honey."


Murmushi tai ta riko hannunsa da hannunta dayan hannun koma ta dan kurbi tea dinta sannan ta sakeshi ta zuge jakarta ta dauko wasu takardu tana dubawa.


Kallanta yai yace "in kaka nustu kina aiki you look soo......"


Kallan data masa ne yasashi yin dariya ba tare da ya karasa ba, tace "Honey a nemo wani driver din."


Ajiyar zuciya yai yace "wannan karan bari muga wanda zamu samo wata nawa zaiyi."


Kallansa tai tace "zaka fara ko? Wannan sai ya shekara 2 zuwa 3"


Dariya yasa yace "muna fata, amma indai wannan Honey dince hmmm."


Takardun hannunta ta cigaba da dubawa hakan yasashi yin shiru.


Suna isa yai parking, kallansa tai tace "bari na turama yanzu yanda zaka cirar mata nata dana mai gadin."


Yace to.


Nan ta dau waya ta tura mai kudi sannan ta dau jakarta ta fito, harta kusa shiga taji ya kirata, juyowa tai ya taho da sauri rike da tea dinta ya mika mata, thanks ta fada tare da nuna cup din alama ta amsa ta gode.


Ciki ta shiga, tana shiga cikin bakin kofar ta hade fuska tamau, duk inda ta wuce gaisheta sukeyi tana amsawa tana wucewa.


Tana shiga office dinta ta ajiye jakarta da tea din sannan ta juyo ta fito, gun program din ta fara shiga, kallan masu aikin gun tai wadanda ke kokarin ganin komai ya tafi daidai tai tace " acanza wannan background din is too light."


Da sauri yace "okay."


Kallan jikin camera's din tai kafin tace "meye hakan? Sau nawa zance a rage contrasts din nan?"


Da sauri yace "am sorry, yanzu zan gyara."


Dan ajiyar zuciya tai sannan ta duduba hasken light din gun sai da ta tabbatar komai yayi ta kalli agoggo sannan tace "is live so you have to be extra careful."


Da sauri sukace okay.


*********


  Da sauri ya fito daga soronsa ya fita waje, dan yanda ake kwalla sallama sannan daga jin muryar ya fahimci wanene.


Dan dattijon na ganinsa ya murtuke fuska tamau ya kalleshi rai a bace yace "Khalid karka batamin rai kar kuma ka bata min lokaci bani kudina."


Khalid ne ya kalleshi yace "Malam Mamman dan Allah kayi hakuri, ga dubu daya dazun nan aka biyani kudin fenti, gobe insha Allah......."


Dubu dayar ya amsa yace "karfa ka maidani dan iska, nan nan ubanka yai hatsari kazo kamar zakai min kuka na ara maka dubu goma ka kaishi asibiti yau wata hudu kenan amma haryanzu dubu biyar ka bani da wannan ta yau kenan, nifa shi yasa banasan harka da matsiyata wlh, ubanka yaki barinka kai aikin noma wai shi a dole sai kayi boko, to dakagama bokon uban me ka tsinana? Uban me kake dashi? Dubu goma ta gagareka biya a wata hudu? To wlh ni bazan dauki iskanci ba."


Khalid yace "kayi hakuri insha Allah zuwa karshen watan nan zan hada maka."


Tsaki yaja sannan ya wuce yana tafe yana masifa.


Shiru khalid yai sannan ya wuce ciki.


Mahaifiyarsa na tsaye a tsakar gida yana shigowa ta matso tace "Malam Mamman ne ko?"


Murmushi yai yace "eh amma bakomai Umma, ina Asiya? Ta biya kudin makarantar dana bata jiya?"


Tace "ta biya, haryanzu ba labari?"


Yace "Karki damu Umma insha Allah zan samu aiki."

Idanunta ne suka ciciko tace "shekara 4 kenan da gama karatunka, sai dai haryau babu labari sai uban wahalar siyan form kake kana zuwa yin jarabawa."


Murmushi yai sannan ya danyi gaba yace "kiyi tamin addu'a, lokaci ne."


Kallan tausayi tamai, ciki ya shiga inda mahaifinsa ke kwance ba lafiya, saboda hatsarin motar dayai wanda yasa kafarsa daya ta samu matsala, ya dade yana sana'ar tokin mota sai dai lokaci daya tsautsayi ya hau kanshi komai ya zama labari.


  Kusa dashi yaje yace "Abba kanasan wani abu ne? Dan zan wuce gun sana'ar mu ne."


Hannunsa ya riko yace "Allah ya taimaka, in inasan wani abu zan sanar da mamanka."


To saina dawo.

Abinda ya fada kenan ya mike.


Abba yace "adawo lafiya Khalid."


Fitowa yai daga dakin ya kalli Umma yace "na wuce."


Wayarsa ce tai kara ya dauka da sauri, Salmanu! Ya?"


"Kana ina?"

  "Ina danbatta ya akai?"


Salmanu yace "zaka samu zuwa kano yanzu? Dan wlh wani aiki ne muka samu gidan akwai maiko, kai sauri kazo."


Da sauri Khalid yace "turomin address din gani nan zuwa."


Nan ya kashe wayar yao waje da sauri.


Jakarsa kawai ya dauka a soro ya fita, yana zuwa ya samu mota ya hau ya nufi kano.


**********


A bangaren Adamu kuwa yana ajiyeta yai wata yar kara tare da duba account dinsa, gani kudi yasashi yar taka karamar rawa daga zaune, da sauri ya juya kan mota ya nufi Atm, yana zuwa yaciri kudin Goggo da za’a bata dana mai gadi, sannan ya ciri dubo goma yasa a aljihu, kida ya saka a motar yana tafe yana kada kai, yau akwai jin dadi a majalisa.


  Jin dadin yanayi yasashi kawai yai ta dan yawo a gari, nishadi kawai yakeyi ji yake duk duniya ba wanda ya kaishi jin dadi.


Tsayawa yai yana kallan wanda ke kokarin tsalaka titi.


Fuskar sa ya kara kallo sai dai ya tsallaka titi, da sauri yaja mota ya nufi gefen titi yana binshi.


  Horn din motar dayajine ya sashi dakatawa, juyowa yai cikin mamaki dan dai ba tare hanya yai ba.


Juyawa yai zai cigaba da tafiyar sa yaji ance “Danbatta.”


Cikin mamaki ya juyo, bai gane mai maganar ba hakan yasa ya dan matso kadan.


Hannu ya daga mai tare da nunashi yace “Danbatta kaine wlh.”


Khalid ya kalleshi yanzu kam ya ganeshi cikin mamaki yace “Adam?”


Dariya Adam yai yace “Danbatta cinye duu daga ina haka?”


Yace “daga danbatta saukata kenan.”


Shigo na karasa dakai.


Kallansa yace “karka damu yanzu zan nemi taxi ko bus.”


Dariyar dake neman kofcemai ya kara dannewa yace “shigo dalla.”


Ganin suna bata lokaci yasashi zagayowa ya shiga.


Adam ya kalleshi yace “ikon Allah, kwaro ashe da raban zan ganka.”


Ran Khalid yadan soso sai dai bai nuna ba yace “inasu Zakar?”


“Suna nan lfy, sai dai duk yanzu kowa hidimar gabansa yakeyi, kasan yanzu Zakar yana aiki a kaduna, Mansir kuma yana aiki a Abuja.”


Khalid yai yake “masha Allah.”


Adamu ya kara kallan jikinsa yace “kwaro ya? Kaifa? An fara aiki? A wani asibitin ko babban company?”


Khalid ya kalleshi yace “me kake nufi?”


Adamu yai dariya yace “me nake nufi kuwa? Kawai dai naga ne kai jarabawarka bazata wahalar dakai ba, duk fa shekararmu kai kadai ne ka fita da A class kaga kuwa ai kai sai babban company.”


  Adamu ransa ya baci, kallansa yai yace “ai ba wannan bane hujja komai lokaci ne.”


Kai ya jinjina yace “haka.”


Sannan ya ja mota, shiru sukai kafin Adamu yace “yanzu dai ba aiki kenan kake san cewa ko me?”


“Eh.”

“Oh Allah kenan yanda kaci karatu waya taba kawo haka?”

Kallansa yai yace “saukeni anan, anan zan sauka.”


Nan?


Khalid yace “eh.”


Adam yai parking sannan yace “to ya? Ko na samoma aiki? Dan ni bana aiki kasan ni banasan wahala sannan jarabawa ta ma dai to, sai a hankali, sai dai matata akwai kudi, tana neman driver ko kana sha’awa na samoma?”


Kallanshi Khalid yai cikin mamaki, Adam yace “ya? Baka yarda bane? Wlh bana aiki, sai dai ta ko ina a jiki nake.”


Khalid yace “ba laifi.”


Har ya bude motar zai sauka Adam ya zaro kudi yace “ga wannan.”


Khalid ya kalleshi yace “no, karka damu.”


“Na manta ashe Mr Right ne, nasan bazaka amsa ba, amma ga numberta in kanasan aikin kamin magana.”


Numbersa ya rubuta a jikin paper ya bashi.


Khalid ya amsa kawai ya fita rai a bace.


Adam yana ganin ya fita ya tuntsire da wata muguwar dariya, da sauri ya kira Zakari.


Nan ya fesa mai, ya kira Mansir shima ya fesa mai.


Dariya kam yashata har cikinsa sai daya amsa, sai a lokacin ya tuna ashefa baici abincin safe ba......


Khalid kam yana sauka ya nemi taxi ya karasa inda zaije.


 

*Ayusher Muhd🏌🏻‍♀*

[10/27, 10:33 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀 *A GIDANA*🍀


Haske Writers Association💡


Shafi na biyu


Wattpad/@AyusherMohd.


******


  Khalid yana sauka ya wuce inda Salmanu yamai kwatance, ganin anata aiki agun yasa ya gane ya iso, da sauri yasa hannu ya dauko wayarsa ya kirashi.


Jiki a sanyaye Salmanu ya daga yace "Khalid!"


"Na iso, kana ina?"


Salmanu yace "bari nazo." Ya kashe wayar.

Bai jima ba sai ga shi nan ya fito, Khalid na ganinsa ya matsa gun da sauri yace "ya? Har an fara?"


Cikin rashin jin dadi Salmanu yace "Khalid kayi hakuri wai mutanen da sukeso sun isa, ma fada musu akwai sauran daya da zai karaso yanzu sunce wai a'a iya mutum biyar zasu dauka."


Murmushi yai tare da dan dafashi yace "bakomai, shiyasa duk kai wani iri?"


Kallansa yai yace "Allah duk abin ne yaban haushi, gashi ni kuma wlh kudin nakeso kasan ina tara lefe da wlh na barma kayi."


Khalid yai dariya yace "Just forget, kaidai yanzu ka shiga kayi aikinka, kafin kai laifi."


Salmanu ya dauko dari biyu yace "gashi dan Allah na asarar mota dana saka."


"Kai ka sani? Ko na sa kaina?"


Salmanu yace "ni na saka wlh."


Khalid ya zare hannunsa daga kafadarsa yace "Good luck ni nayi nan."


Yai gaba ya barshi rike da dari biyun, Salmanu ya bishi da kallo a ransa yana jin haushin wannan lamari na kasarmu, bazai manta yanda Khalid yai karatu a makaranta ba, duk wani abu da za'ai a faculty's dinsu, shine yake wakiltarsu, shine yi musu tutorials da sauransu amma dan bashida hanya gashi nan ko karamin teaching ya kasa samu.


Khalid kam yana tafe yana tunanin kalaman Adam, ba shakka ransa ya sosu da yanda ya mai magana, dan duk wanda ya kalleshi ya kalli yanayinsa yasan yanayine na dauriya da wahala, amma wai tambayarsa yakeyi wai wani company din yake aiki?

Murmushin takaici yai tare da sa hannu a aljihunsa, dauramai dari uku.


Ajiyar zuciya yai dan wata yunwa da yakeji gashi kuma kudin motar komawa ma yamai kadan.


Mezai danyi yadan samu kudin da zaici abinci ya kara kudin mota?


*********

"Duka duka anan muka kawo karshen shirin mu na Yammacin mu a Yau, sai mun hadu daku a shiri na gaba.


Ni Zainab Aliyu Tahir nake cewa mu huta lafiya."


Ana dauke camera daga kanta ta shiga bubuga kafadarta saboda dan gajiyar datai, kallanta staffs din gun sukai sukace "Hajiya akoda yaushe ke ta dabance, in kina shiri gaba daya komai tsayawa yakeyi, mu kanmu rasa wayar da zamu dauka da texts din da zamu karanta mukeyo."


Kallan mai maganar tai tace "kuma sannunku da kokari."


Ruwan dake gabanta ta dauka ta sha sannan ta mike tace "Ina Ramla?"


Bata nan, dazu kuma tana nan a tsaye.


"A ce mata ta sameni a office."

Ta fada tare da wucewa.


Zama tai a office dinta tare da daukan wasu takardu tana dubawa.


Knocking din datajine yasa tace "shigo."

Ramla ta shigo cikin yanayin tsoro dan ta tabbatar laifi tai, ko kofar bata maida ta rufe ba ta watso mata takardun dake hannunta.

Gaban Ramla ya fadi ta kalleta a tsorace.


"Me kika dauki media?"

Murya na rawa tace "media? Aunty Zee?"


Fuska ta daure sosai, tace "ya akai kika samu aiki a nan?"


Bakinta na rawa tace "munyi interview......"


Bashi nake tambayarki ba, kallanta tai a tsorace tace "munzo munyi audition...."


"Kin min shiru ko sai ranki ya baci? Karatun aikin jarida kikai ko me?"

Da sauri tace "shinai."


"Then uban me kika rubutamin?"


Idanunta ne ya ciciko tace "binciken da kikace naje nai...."


Ki koma kije ki sake report din nan sannan don't expect me in sake kiranki na miki bayani, ma tabbatar kinsan halina kinji me nakeyi in har nama mutum magana."


Hawaye ne suka zubo mata tace "insha Allah."

Haka ta tsugunna ta shiga kwashe takardunta, tana gamawa ta fita tana hawaye.


Zainab ta dansa hannu akanta dake dan sara mata, agoggo ta kalla, ta kusa tashi, nan ta dau waya ta kira Adam.


********


Shikam Adam yana rabuwa da Khalid ya wuce majalisarsu ta yan zaman kashe wando, suka sha hira da gulma, akai ta fasamai kai akan yanda ba cas ba as sai jin dadin rayuwa da yakeyi.


Dariya yasa sosai yace "nifa dama can ba mutum bane mai san wahala dan dai Allah bai bani dama bane, shiyasa yanzu da Allah yaban dama nake morar jin dadi na."


Nazifi ya kalleshi yace "wai da gaske kake ma ka nemi aikin kuwa?"

Yace "tab ai ko form ban taba siya ba, itadai ta dauka samune banyi ba."


Nazifi yace "Shegen aikai Allah ya maka baiwar sanin yanda zaka so kanka."


Adamu yace "kasan Ita akwai san bin abu yanda ya kamata, danace tasa a nemomin aiki fa cewa wai corruption ne."


Nazifi yace "ai shiyasa nakejin haushin yar iskar Kubran nan, sai anyi magana tace batada kudi, ni wlh haushi take bani, da alama aure zan sake wlh, kuma Hajiya zan nema nima."


Wata muguwar dariya Adam ya saki yace "tab amma lalai kai dan mugun san banza ne, irinsu Zee dita an fada maka sunada yawa ne??"

Nazifi yace "mudai yau mijin Hajiya dan Allah ka dubemu mu dan tauna mai yaji yaji."


Nan ya zaro dubu biyo aka siyo musu balango suka ci suka kora da lemo, sannan ya mike ya nufi gida.


Goggo na zaune tanata kallo tana dariyar ta ya shigo.

Tana ganinshi ta mike tace " Ina ka tsaya ne?"


Kallanta yai sannan ya kalli Tv yace "wai Goggo dan Allah bakya gajiya ke da kallo ne? Kullum kina gaban kujera kina kallo."


Tace "wannan ba damuwarka bane, sannan in na zauna a dakin ma me zanyi? Ba gwara nai kallo na debe kewa ba, ni ba wannan ba, bani kudina."


"Wai nawane ankon? Ai baki fadi kudin ba."


Kallansa tai tace "ban san fa iya shege ce maka akai bansan me nake ba? Ni bani kudina bansan jan magana."


Dubu biyar ya zaro ya mika mata yace "gashinan, amma wlh nasan ankon nan baifi dubu 3 ba."


Amsa tai sannan tace "wai ni Adamu wannan kudinka ne?"

"Na matata ne."

Komawa tai ta zauna tace "daga baya kenan, kudi ba naka ba sai bin ba'asi, wannan da kaine ma kake aikin kila ba ci zanyi ba."


Wucewa ciki yai ya kwanta, kan kace me bacci yayi gaba dashi.


Baccinsa yasha sosai, dan wayar Zainab ce ta tasheshi.


Yana ganin sunanta ya kalli agoggo sannan ya mike zaune.


"Honey kana ina?"


Cikin maganar bacci yace "ina gida na sha bacci ne."

Tace "nakusa  tashi inka samu driver din ka turoshi yazo ya dauken."


Da sauri yace "yanzu zanzo, bansamu ba tukunna."


Kashe wayar tai sannan ta duba laptop din dake gabanta, tana gamawa ta fara hada kayanta.


Adam kam suna gama magana ya sauko daga kan gado, da sauri ya dau key zai fita yaji fitsari, nan ya koma toilet yai sannan ya fito ko Goggo baima magana ba wacce ke zaune tana kallo tana cin abinci.


Da sauri ya shiga mota ya ja ya fita, dole na nemo driver bazan iya yawon nan ba, tuno da Khalid dayai ne yasashi yin dogon tsaki, ya akai ban amshi number shi ba? Ai da masifa da sai na sashi yin aikin nan.


Yana isa ya kirata a waya.

Nan tai sallama dasu ta fito.


Tana shiga ya kalleta cikin kulawa yace "Ayya Honey da alama kin gaji."


Murmushi tai tace "kawai dai fadan da ake sanine yake sani gajiya."


Hannunta ya riko ya sa akan kuncinsa yace "nasan duk wanda yaga shirin ki na yau zai ce waccece wannan? Ni kuma da ina gun zanyi saurin cewa My Wife, da magana ne."


Yanzu kam dariya tadanyi sannan ta zare hannunta tace "Honey."


Yace "kinga gashi harna saki kin ware."


Murmushi tai sannan tace "as always."


Mota ya tada dannan ya juya suka hau kan titi, kallanta yai yace "Honey zaki iya tuna Kwaro? Cinye du?"


Kallansa tai tace "wanda kake yawan labarinsa? Wanda ya maidaku hoto?"


Da sauri yace "shi shi, ai na fada miki komai malamai sai dai suce shi ko?" Tace "eh, ya akai?"


Wata dariya ya sheka yace "kinsan yau na ganshi?"


Kallan mamaki tamai tace how?


Cikin zumudi yace "a hanya, kin ganshi?" Ha ha ha unbelievable wai bai samu aiki ba, sannan kina kallanshi kamar talakan kauyen."


Kallansa tai yanda yaketa dariya tace "lalai Honey to menene na dariya?"


Kallanta yai yace "can you imagine?"


Tace "a yanayin kasarmu sosai, saboda mutane nawa ne suka dace suka cancanta a basu aiki amma suna nan ba labari?"


Dariya yake sosai yana cewa "ban taba kawowa ba wlh."


Kallan mamaki take mai, dan haryanzu bataga abin dariya ba.


Da kyar ya gama dariyar sannan yace "ai naji haushi wlh ban amshi number shi ba."


Kallansa tai batace komai ba.

Yace "namai rayin aikin driver dinki ai, wayyo Allah ubangiji yasa ya amsa."


"Driver?" Ta fada tana kallansa, yace "eh."


Wani murmushi tai sannan tace "baka tunanin u hurt his pride?"


Yace "taimakon sa zanyi ai, dayaje yana neman abinyi ga aiki a gida?"


Kanta tasa jikin window dan ta kasa fahimtar me yake nufi.


Adam ya jawo hannunta yace "me? Bakyaso?"


Tace "no, kawai dai ina ganin kamar bai kamata ba, abokinka ne fa?"


Ganin yanda ta dau lamarin yasa yai saurin canza maganarsa yace "na san bai kamata ba, amma bansan yands zanyi na taimakeshi ba, kins gani nima fama nake da neman aikin nan."


Murmushi tai tace "na fahimta yanzu, amma dai still da baka mai zancen ba, ba lalai ya fahimci dalilinka ba."


Hakane kuma, gashi banda numbersa.


Tace "kawai dai Allah yasa yai calling dinka back sai ka nusar dashi."


Kai ya jinjina sannan yace "Thanks."


Dame?


"Komai ma."

Murmushi sukama juna.


***************


Khalid kam mariri ya shiga yaje gun masu ruwa ya amsa kura akan zai biyasu duk kaiwa daya, haka yai tayi ya hada dubu daya ya nemi abinci yaci yahau mota ya koma gida.


Yana shiga danbatta ya tsaya yasai lemon fata ya wuce gida.


Suna zaune a tsakar gida Asiya na alawar madara da take kaiwa makaranta ya shigo.


Yana tafe su Asif na binsa a baya shi da Amir, wanda ya kamosu daga wajen wasan kwallo.


Bayan sun gaisa da Umma ne ta kalleshi tace "an dace?"


Yace "naje wlh wai sun cika, amma insha Allah........."


  Umma ce tai ajiyar zuciya ta kalli Abba dake zaune yayi shiru, tace "Khalid bayanda za'ai mu samu ko dubu uku ne?"


Kallanta yai yace "wani abu ya faru ne? Tace "dazu daka fita Amir yana wasa ya bige Abbanka aka fama ciwon sai da muka kira mota muka kaishi chemist aka gyara, gashi bashin gun Karima naci, ka santa."


  Kallan Abba yai ya matsa da sauri yace "Abba ya jikin?"


Abba ya share kwallarsa yace "Khalid kayi hakuri inata karama nauyi."


Da sauri khalid yace "ko kadan Abba."


Umma dake share hawayenta itama tace "Khalid gashi yau ba komai a gidan, kokon dana saida shi na mana abincin rana dashi."


Kuka ne yadan kwace mata, hankalinsa ya tashi, gata tana kuka ga Abba ma na hawaye, Asiya ma daurewa kawai tai amma sai da kwalla suka zubo mata.


Bai san sanda yace "Umma na samu aiki."


Da sauri ta kalleshi Abba ma ya kalleshi yace "Da gaske? A ina?"


Idanu ya runtse, me yace? Me ya kaishi?


Umma ta kalleshi tace "nasan wasa kakeyi, wannan lamari dame yai kama? Sai bani jari kake yana karyewa, duk wahalar da kakesha haryanzu........"


Da sauri ya zaro takardar dake aljihunsa yace "kingani number wanda ya daukeni ne, matarsa ce take neman mai tuka mata mota shine yakeso in amshi aikin."


Matarsa? Abba ya fada yana kallansa, sannan yacigaba "kana ganin abinda ya sameni a aikin tukin mota banaso kaima ka gadoni."


Asiya ce da sauri tace "Alhamdulila yaya indai har driver suke nema  da alama sunada kudi kenan? Nawa zasu dinga biyanka? A ina zaka zauna tunda dai nasan a kano ne."


Yace "to Hajiyar tambaya."


Umma ce ta kalli Abba tace "shekararka nawa kana aikin? Ai tsautsayine da kaddara."


Sannan ta cigaba "kai Alhamdulila."


Khalid ya kallesu dan baisan me zaice ba......


Ni kaina jinai bansan me zance ba....lol


*Ayusher ce*

[10/27, 10:33 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀*A GIDANA*🍀


Haske Writers Association💡


Shafi na uku


Wattpad/@AyusherMohd.


Khalid na shiga dakinsa ya zauna abakin gadansa ya dafe kansa yana kallan number dake hannunsa, ajihar zuciya kawai yai dan baimasan tuno abinda ya faru.

Kirim ya maka kanshi akan gadon dan takici.


********


Cikin bacci taji hannunsa a cikin rigarta, juyowa tai ta kalleshi.


Kara matsowa yai yace "kin gaji ko?"


Murmushi tamai duk da dai ba gani yake ba saboda duhun dakin, sannan ta kai bakinta cikin nata........


Bayan sunyi wanka ne ta kalli agoggo, karfe 2 na dare kasancewar gobe asabar yasa bata damu ba, zuwa yai ya kwanta kusa da ita, sun danyi shiru kafin ta nisa ta kalleshi cikin kulawa tace "Ko muje asibiti?"


Shima juyowa yao saitin da take kallansa yace "kin matso ne?"


Kai tadan girgiza kadan tace " i feel like kamar yin planing din danai farkon auran mu ne yake neman ja min matsala, sannan ina tunanin ko ba kaiba nasan Goggo nasan ganin jikanta."


Jawota yai jikinsa yace "karki wani damu, ni ba abinda yake damuna, let's try slowly."


Murmushi tamai sannan ta kura mai ido, a koda yaushe wadan nan kalan nasa ne yake sa take ganin duk abinda tamai bata fadi ba, tana sanshi sannan tana san a sota, shiyasa ko yan uwanta sunyi maganar rashin aikinshi abin bai damunta.


  Iska ya hura mata yace "kallan fa?"

Murmushi ta dake mai sannan ta sumbaci goshinsa a hankali cikin rada tace am touched.


Kallan juna sukai a hankali sukai murmushi, bacci ne ya daukesu suna yar hira sama sama.


Yau da yake asabar ce basu tashi ba bayan sunyi sallar asuba sai karfe goma sha daya.


Sha dayan ma ahi ya fara tashi, yana shiga toilet ta bude idanunta, agoggon wayarta ta kalla sannan taga sako ya shigo mata.


Tana karantawa ya fito, kallansa tai tace "Honey wai anjima su Nusaiba da Nabila zasuzo, dama tun shekaranjiya sukace zasu tambayi Dady ko zai barsu."


Kallanta yai yace "yau din nan?"


Tace "Hmm kana tsoro ne?"


Dariya yasa yace "bari na dauko Panadol na ajiye kusa da ni."


Itama dariya tai tace " Mutanen Goggo."


Mikewa tai ta shiga toilet, zama yai a bakin gado yana kallan wayarsa, Khalid please ka kirani ko text kamin.....


Tana fitowa suka fito falo tare, Goggo na zaune tana shan shayi tana kallo suka fito, gaisheta tai sannan tace "Goggo anjima su Nusaiba zasuzo."


Da sauri ta kalleta tace "har an kuma yin wani hutun?"

Adam ya kalleta yace "wace tambaya ce wannan Goggo?"


Kallan Zainab tai wacce ke kallanta cikin rashin fahimta sai tai saurin wayancewa tace "ah wai nagane kamar basu dade da zuwa waccan hutun ba, ko da yake kwanakin yanzu ai ba wuya."


Zainab ta fahimceta sai dai dauke kai tai daga manufarta ta barshi a yanda take nufi da cewa "lokaci yanzu ai ba wuya."


Goggo tai dariya tace "yan dambe mutane na."


Itadai Zainab batace komai ba ta wuce kitchen.


Adam ne ya kalli Goggo yace "Ko ba kyasan suzo ai bakya nuna haka ba."


Wani kallo tamai tace "kaima so kake suzo? Yaran da suna zuwa ba nutsuwa a gidan nan, fada sai suyi kusan sai hudu a rana daya."


Mikewa yai yace "kedai Goggo kallanki ne bakyasan su tare miki tv da kallab india da korea, na fa sani."


Bata kulashi ba ta cigaba da cin breadin ta.


Kitchen ya nufa ya tadda ita tana fere dankali.

Yasan halinta tunda yaga bata kulashi ba harya shigo kitchen din to batasan a mata magana a wannan lokacin.


***********


Yau tun safe duk wanda yazo siyan koko sai Umma ta fadamai ai ya samu dan karamin aiki a cikin garin kano, badai wani aiki bane sosai amma babbar mace Hajiya zai dinga tukawa.


  Yana daga cikin daki yaji ana mai Allah ya sanya alkairi, a lokacin yana zaune yana duba result din wani test da sukaje sukai, jin yanda matar ke mai Allah ya sanya alkairi ne yasashi mikewa, tana fita ya shigo cikin gidan, Umma na zaune tana dama koko, sai daya gaisheta sannan yace "Umma badai harkin fara fadawa mutane na samu aikin tuki ba?"


Cikin farinciki tace "yanzu Salamatu tazo takemin zancen Salmanu na hada lefe shine nake mata zancen? Da wani abu ne?"


Dan huci yai kafin yace "ai da kin bari na soma aikin sai ki fada musu, in abu yazo da tsautsayi fa?"


Cikin tashin hankali tace "akwai matsala ne?"


Ganin yanda tai yasa yai saurin cewa "a'a kawai dai da kin bari sai dana fara."


Umma tace "ai salamatu da Karima kwai na fadawa."

A ransa yace ai su kadai bakinsu radio ne, amma a fili baice komai ba.


Gun Abba ya shiga wanda ke kwance, Abba yace "yanzu dama zan sa a kiraka, dan taimaka ka kaini bayan gida."


Nan Khalid ya dagashi suka nufi toilet, sai daya gama sannan ya kirashi suka fito.


Abba yai dariya yace "ai wasa wasa wannan dabarar ta bature ta taimaka, yanzu kaga da bandakinmu na da ne sai dai in san yanda zanyi, ga kafa daya babu gashi kuma tsugunno ake, kaga kuwa wannan dakasa aka sa mana na zama ai yafi."


Murmushi kawai yai baice komai ba, sai da Abba ya zauna sannan yace mai "Khalid!"

"Naam Abba."


Ya kalleshi fuskarsa cikin kulawa yace "ka fahimci mahaifiyarka, tsabar zumudi ne yasa ta kasa yin shiru."


Khalid yace "na sani Abba."


Dan dariya Abba yai yace "yaushe zaka fara aikin?"


Yace "hmm."


Abba ya kalleshi yace "akwai matsala ne?"


Shiru yai yana kallan Abban, yana san sanar mai gaskiya sai dai yana tsoron yanda zasu kara shiga damuwa tun balle in sukaji matar abokinsa wanda sukai makaranta tare ne ya tabbatar sai sunji ba dadi, hakan yasa kawai yace "a'a anjima zanji sanda zan fara."


Abba ya saki fuska cikin jin dadi yace "Allah yayi albarka yasa a fara a sa'a, duk da ina tsoronka da tukin mota sai dai ina fatan ka fara dashi a hankali kuma ka cigaba da duba aikin yi, yanda kake da jarabawa mai kyau din nan banda dai kasarmu ta zama abinda ta zama ai aiki kam bai kamata ka rasa ba."


  Khalid yace "Amin Abba insha Allah lokacin da za'a samu aikin zai zo."


Abba yace "haka ne, Allah yasa a dace."


Amin yace sannan ya mike ya fara gyara mai zaman sa.


Umma ce ta kirashi ya fito ya dau abincinsa ya shiga daki.


Shiru yai a cikin dakin ya zubawa koko da kosan ido yana tunanin mafita, takardar dake rike a hannunsa ta number waye Adam yake ta bi da kallo.


Yanzu ya samu ya biya kudin makarantarsu Asiya, nan gaba kadan zai sake biyan wani tunda rabi yake badawa a farko sai ya cika rabin daga baya, ga bashi, ga hidimomin gida, ga jikin Abba, idanunsa ya runste saboda yana ganin zaben abinyi a wannan lokacin sam ba nashi bane.


Abincin yaci yana gamawa ya dau wayarsa ya kira Salmanu, ya kuna kanon ne?

Salmanu yace eh wlh, ai naji haushi da baka samu aikin nan ba, gashi haryanzu ba wani labari."


Khalid yace "bakomai ai aiki lafiya."


Ya kashe wayar yi shiru yana kallan wayarsa, mikewa yai da sauri ya shiga cikin gida yai wanka, yana gamawa ya fita waje dan ganin abinyi, ya bari akan in dai har yamma bai samu wani abu ba to fa lalai zai kira Adam.


*******


Karfe biyar na yamma tanata girki, Goggo ta shigo kitchen din tace "dame za'a tayaki? Naga yau sai girke girke kikeyi."


Tace "barshi wlh Goggo ai na ma gama."


Goggo tace "to ki bar wanke wanken nayi."


Zainab tace "su Nusaiba in sun huta sayi."


Kamar da wasa tana rufe baki taji karar bude gate, da sauri ta dauraye hannunta dan dama duk ta juye abincin a flask, ta nufi falo cikin tsananin farin ciki.


Goggo ta kalleta tace "goben nan za'a jiku kina musu fada."


Tana bude kofar waje ta hangosu suna fito da akwatinsu daga mota.


N square abinda ta fada kenan suka waigo ai suna ganint suka bar akwatin suka nufota da gudu suka rungumeta.


Cikin farinciki tace "Welcome."


Dagowa sukai suna dariya Nabila tace "kai wasa wasa Allah Aunty na gaji, tafiya taki karewa."


Nusaiba tace "har wani tafiya taki karewa banda uban baccin da kika maka a hanya."


"Yaushe nai baccin? Dan na rufe ido shine......"


Da sauri tace "zaky fara ne?" Ta fada cikin hade rai, sun san halinta akwai fara'a da wasa da dariya amma fa in taso, sannan in ta birkice to fa ba kanta.


Da sauri suka guntse bakinsu sannan suka jawo akwatin da kayan da suka taho mata dashi suka nufi ciki.


  Goggo tana falo suka shigo, "oyoyo oyoyo ga mutanen nawa sun iso."


Nusaiba tace "Goggo."


Goggo ta kara ware fuska tace "lale lale maraban inji larabawa."


Nabila tasa dariya tace "Marhaba suke cewa Goggo, yau kuma garin larabawa muka nufa?"


Zainab tace "koma me suke cewa tunda kin gane na miye wannan dogon sharhin.


Gate aka sake bude wa wanda yasasu juyawa, Nabila tace "Ya Adam na yawo......."


Kallan da Zainab ta mata ne yasa tai gum.


Shiga da jakakkunan nasu sukai dakin da suke kwana, suna fitowa ya shigo shida Dauda driver wanda ya kawo su Nusaiba.


Yana shigowa yace "My headache kuna ina??"


Fitowa sukau daga daki, Nabila tace "bayan munyi fushi, kasan zamuzo ka fita."


Dariya yai yace "ai yanzun nan na fita nima ko Honey?"


Ya fada yana kallan Zainab, tace "ko yanzu ya fita ko dazu ya fita meye naku a ciki?"


Goggo ta kalleshi cikin takaici, ya bari kowa ya rainashi, kallan Goggo yai sannan ya dauke kai dan ya gane wani abin bai mata dadi ba.


Zama sukai bayan sunyi sallar da ta riskesu a hanya aka fara cin abinci.


*********


Khalid ne ya dawo gida bayan yawon daya sha a garin na dan batta, can ya samu jiran shago yadanyi aka biyashi, shiru yai a cikin daki kawai ya gama yanke shawara zai fara wannan aikin sai dai sai yaji abubuwa guda biyu, na farko shi bashida gun da zai zauna a kano sai abu na biyu baisan aikin da za'a kankantar dashi.


Yana cikin tunanin nan bai fargaba kawai yaji ance Hello!


Shiru yai daga can bangaren Adam dake zaune ana hira ya mike yai daki ya kara cewa "Hello!"


Khalid ya daure yace "is me Khalid Danbatta."


Cikin mamaki Adam ya kalli wayar sannan ya kara karata a kunne yace "who?"


"Khalid Usman Danbatta."


*Ayusher Muhd*

[10/27, 10:33 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀


Haske Writers Association💡


Shafi na hudu


Wattpad/@AyusherMohd.




  Adam cikin mamaki yace "Khalid!"

"Eh nine." Adam ya zauna a bakin gado yace "ya gida khalid? Inatajin ba dadi dama ban amshi numberka ba."


"Is okay, maganar aikin nan."

Idanu Adam ya zaro kamar yai dan ihu amma sai yace "eh tana nan? Kana so ne?"

Khalid ya matse hannunsa saboda jin ba dadi da yakeyi, yace "eh, sai dai zan fara duba inda zan zauna da albashi da sanin yanayin lokacin aikin da sauransu."


Adam da sauri yace "kar kaji komai, ai kawai in dai ka shirya kazo gobe saboda litinin tanada aiki, ba wani matsala."


Cikin mamaki Khalid yace "ba matsala kamar ya?"


"Eh in kazo goben ma tattauna, amma ba wani abun ka kirani gobe in xaka taho zan turo ma da address, abinda kawai yace kenan ya kashe wayar da sauri." Wata irin kara ya saki wanda su kansu dake falon sai da sukajishi.


Zainab ta miki da sauri ta nufi cikin dakin, yana ganinta ya maida fuskarsa, cikin mamaki ta kalleshi tace "Honey lafiya?"


Murmushi yai sannan yace "bakomai dama munyi waya da Kwaro ne shine yace zai fara aikin."

"Kwaro?" Ta tambaya cikin mamaki.


Kin mantashi?

"Ohh friend dinka?"

Da sauri yace "eh."

Kallan mamaki tamai ta matso kusa dashi tace "wai da gaske abokinka ne zai zama driver na?"


Hannu yasa ya jawota ta zauna kan cinyarsa yace "neman aiki yake sosai, da alama yana cikin wani hali, kinga ba dadi na cemai kar yai bayan ya kirani akan yana san aikin."


Idanunsa ta kalla sannan tace "amma gani nake bai dace na kamar."


Karki damu, a yanda kike din nan ma nasan ba dadewa zaiyi ba zaku rabu, dan banaji zaku jitu da halayensa."


  Wani irin murmushi tai sannan tace "kasan haka kace yazo?"


Karkace kai yai yace "I feel bad for him."


Shiru tai kawai batace komai ba, ajiyar zuciya yai kamar wanda yake cikin wani halin wanda yasata kallanshi, yace "matsala daya, banaso ya dinga kalleminke, shiyasa nake neman manya magidanta."


Harararsa tai cikin wasa tace " banda wanda akemin a tv?"

Ahhhh, ya dafa kai sannan ya kwanta akan gado yace "shikenan ni an gama duk kallemin matata."


Mikewa tai tace " zolayar ta motsa kenan?"


Mikewa yai shima yana dariya yace "gobe zaizo, sai dai bansan ko yanada gun zama ba."


Da sauri ta kalleshi tace "sai ya nema ai wannan ba damuwa ta bace."


Dariya yai yace "bari dai yazo goben muji."


******


A bangaren Khalid kuwa yana kashe waya yai shiru yana maimaita kalaman Adam, kafin ya mike ya nufi cikin gida dan sanar dasu Umma tafiyar fa gobe ce.


Umma na zaune akan tabarma kusa da Abba, suna hira.


Yana shigowa tsakar gidan Umma tace "Khalid dan halak, muna maganarka sai kaga."


Murmushi yai sannan ya karaso yana cewa "Su Amir ba'a dawo ba?"


Tace "ba dadewa zaka jisu, dan lokacin tashin nasu yayi ai.


Zama yai daga gefe yace "Abba ya jikin?"

Abba cikin sakin fuska yace "kasani yau inajin wani karfi, duk da ba sana'ar da nake fatan kayi bane ka samu a kalla dai nasan zaka samu abinda zaka taimaka mana ka taimaki kanka har a hankali kazo kai aure, wannan tunanin yasa naji yau jikin nawa garau."


Kallansa kawai yai sannan ya dan murmusa duk da abin bai kai kasan ransa ba, Umma ce tai saurin cefewa da cewa "Nikam kasan yar gidan kyauta?"


Ya fahimci me take nufi sarai amma sai cewa "Zahriyya datai aure?"


"A'a Habiba wacce ta gama makarantar secondary bana."


Yace "ohh wannan yarinyar? Badai harta gama makaranta ba?"


Umma tace "ta gama wlh shiyasa dama nace......."


Eheeem ya isa haka nan, abinda Abba yace kenan wanda ya sata yin shiru.


Abba ya kalli Khalid yace "ko zaka zauna a gidan kawunka Idris? In har gurin zama zai wahalar dakai a kanon?"


Kallan Abba yai sai dai shikam baisan zaman gidan nan sam, shiyasa lokacin da yake makarantar Buk duk abin duniya ya dameshi shi yasa ya koma cikin hostel yake dan zaman wani shagon ana biyansa ga kuma wanda Abban yake turamai ya samu yake biyan na hostel dan sam baya san gidan nan basu da tarbiyya ko kadan, sai dai a lokacin cema Abba yai kawai yafisan can saboda karatun dare.


Abba ya kalleshi yace "ya akai? Bakasan can din ne?"


Khalid yace "a'a bari goben in naje muka gama zan shiga can din."


Umma tace "ah gobe ne? Da wuri haka?"


Yace "yanzu mukai waya dashi, sai dai ban sani ba ko in naje goben zan dawo ko kuma sai juma'a bandai sani ba sai naje can din."


Abba yace "masha Allah ba laifi ai."


Khalid yai shiru kafin yace "Abba!"

Abba ya kalleshi cikin kulawa, yace "na fadawa Salmanu zaizo da yamma ya dauki laptop dina, zai saida ita in yaso sai ya baku kudin a samu a rage wasu abubuwan kafin Allah ya kawo yanda za......."


Katseshi Abba yaida cewa "a'a kul, na fada maka ba tun yau ba in har ba kudi ka samu zaka sai wata ba karna kuskura naga ka saidata, bayan duk abin karatunka a ciki kakeyi, sannan kace zaka sai data?"


Khalid ya kalli Umma wanda itama bata yadda da shawarar ba, zaiyi magana su Amir suka shigo da gudu.


"Kun daina gudun nan ko kuwa?"


Da sauri suka daina dan sun san halinshi.


Asiya na biye dasu, duk saida suka gaishesu da gida, Asiya tace "Yaya! Ya salmanu na sallama dakai."


Khalid ya mike yai waje.


  A yanda yaga Salmanu ne yasa hankalinsa ya tashi, Salmanu na ganinsa ya matso kusa dashi, idanunsa sunyi jaa da alama ma har hawaye sun zubar, Khalid cikin mamaki dan bai taba ganinsa haka ba yace "Salmanu menene? Meya faru?"


Da alama baima san ta inda zai fara magana bane dan duk a rikice yake.


Khalid ne yasa hannu biyu ya riko kafadarsa ya girgizashi yace "Salmanu? Menene? Rasuwa akai?"


Salmanu ya zubamai ido kamar wanda baya hayyacinsa yace "Wai ansa auran Nazifa dazu."


Gaba daya ya kasa fahimta yace "bangane ansa ranarta ba, ba dakai aka saba kenan ko me?"


Salmanu wasu zafaffan hawaye ne auka zubo mai yace "Khalid kwana biyu dama duk bansan meke damun Nazifa ba da mamanta, har yayenta ma, dan duk sanda naje zasucemin ko bata nan, ko tai bacci, ni duk ban kawo komai a raina ba saboda duk garin nan kowa shaida ne akan yanda muke san juna, yarinyar nan tun tana primary....."


Khalid yace "na sani nasan wannan, ni bangane an sa rana ba."


Salmanu ya goge kwallarsa yace "kanar yanda kaji din nan haka yanzu ina dawowa daga kano aka fadamin, ina zuwa gidansu yayanta yake fadamin, wai Alhaji Badamasi."


Khalid ya fahimci kwanan zancen, wato sunga kudi, sai dai ba'ama Salmanu hallaci ba, kusan shekara kenan yana ta faman hada lefe dan so yake ya mata lefe na fitar kunya amma ynzu a mai haka,m? Bayan tun tana primary hartakai secondary komai shi yake mata, hatta provision in zata koma skul shi yake mata.


Ran Khalid yakai matuka gun baci wanda takaici ya kamashi yace "yanzu wani irin cin mutunci ne wannan?"


Salmanu ya kalleshi cikin karayar zuciya yace "taya zan iya rayuwa ba Nazifa?"


Haka ya juya dan yace yana san kadaicewa y tafi, Khalid yabi bayansa da kallo, shi yasa fa shi sam harkar soyayyarnan bata gabansa, karshe ma shi bai yarda da ita ba.


Haka ya shiga daki yana hada kaya cikin takaici.


***********

Wajen karfe 11:30


  "Wallahi bazanyi wanke wanke ba sai dai ke kiyi ni shara zanyi."


"To ni bazanyi wanke wanken ba nima shara nakeso."


Fadansu ne ya sa Zainab ta farka dan cikin bacci taji ana fada.


Mikewa tai ta kalli Adam wanda da alama baijisu ba,  fitowa tai suna tsaye a falo suna fada Goggo na zaune tana kallo ko kulasu batai ba, hankalin ta ma sam baya kansu.


Zainab na rufe kofa suka juyo sauri suka kalleta, kallansu tai tace "mekenan?"


Nusaiba tace "Aunty......."

Ku wuce duk kuyi komai tare, wai sai yaushe zaku girma da fada ne?"


Nabila zatai magana, Zainab ta kalleta.

Da sauri sukai shiru, kitchen suka nufa kowa fuska a hade.


Zainab ta kalli Goggo tace "Goggo kina kallansu amma bazaki hanasu ba?"


Goggo ta kalleta tace "ni? Ina na isa? Ai ni ba a bakin komai nake ba a gidan nan, yara sunzo gidanki ai sun fini iko da gidan."


Zainab kallanta kawai take sai dai kalaman sun bata bata rai sosai, tace "Goggo me yasa wani sa'in in kina magana sai ma dinga gani kamar magana kike fadamin?"


Goggo ta mike tace "magana? A ina? Bayani kawai na miki, sai dai in ke kika fassara, ni ina na isa na fada miki magana?"


Zainab zatai magana, kawai ta fasa dan ta kula ranta ne zai baci, in kuma ranta yabaci to lallai da matsala, juyawa tai kawai ta shiga ciki.


Goggo ta bita da kallo tace "wannan da badan mune a karkashinki ba wlh da kece a kasana dasai na koya miki yanda ake lallaba uwar miji."


Tai tsaki sannan ta zauna ta cigaba da kallanta tana dariya.


Zainab kam daki ta wuce, wayarta ta dauka missed calls ta gani kala kala daga gun aikinta, da sauri ta kirasu, nan aka sanar da ita air advertising din da suka dade suna nema ne ya taso, sannan an kammala musu website din da suka sa a canza musu,tazo suyi meeting.


Da sauri ta shiga toilet tai wanka ta fito, ta hau shiryawa


********


Khalid kam karfe goma yai sallama da gida bayan ya samu a daren jiya ya saida wayarsa ya nemi karama mara internet, yaba su Umma kudin saboda lamari sannan ya bada dubu biyu a kara ba masu bashi, da wannan yai sallama dasu akan zaije ya dawo a yau in ya samu hali.


Har ya shiga mota yana tunanin abinda akawa Salmanu wanda ya bata mai rai matuka.


Address din da Adamu ya turomai jiya da yamma ya dinga dubawa  ganin ya kusa isa gidan yasa ya kirashi a waya.


*****


Adam na bacci yaji motsinta a toilet, ohh cikin layin bacci ya duba wayarsa, mikewa yai ganin yasha bacci, yana zama wayar Khalid na shigowa.


Da sauri ya dauka yace "kwaro!"


Khalid yace "Adam gani nan na kusa isowa, in nace gidan Journalist kawai shikenan?"


Adam yace "eh sai ka iso."


Da sauri ya kashe ya mike daga kan gado, fitowatai daga toilet da sauri ta kalleshi a tsaye tace "ka tashi?"


Yace "eh, tace "taimaka plz ina shiryawa ka dan dubamin email din nan."

Ta dau wayarta tana mikamai, amsa yai yace "gun aiki zaki?"


Tace "eh."


Amsar wayar yai ana karanta mata, da sauri take sa kayan, tana gamawa ta gyara fuskarta, daidai nan ya gama ta amsa tace "thanks Honey."


Kiss tamai sannan tace "i have to drive shiyasa nace ka karantamin tun anan, sai nai tunani a hanya."


Yana kokarin sanar da ita Khalid din yanzu zaizo ta dau jaka ta fita da sauri, biyota yai yana cewa "Honey dama......."


Kallansa tai tace "kar ka damu zan samu abinci naci acan, tnz."


Da sauri ta wuce kitchen, ta kalli Nusaiba da Nabila tace "Allah yasa naji labarin kunyi fada."


Baki suka rufe, tare da cewa "adawo lfy."


Da sauri ta fito ta kalli Goggo tace "Goggo na tafi."

Tace "yau fa lahadi."


Tana tafe tana cewa "abu ne ya taso mu director's ne kawai zamuyi meeting."


"Darastas??? Me kenan?"

Adam ya girgiza kai yai waje.


Tana fitowa waje shi kuma yana turo kofar gate din.


Kallansa tai sannan shima ya kalleta.


Adam da ya fito ne ya kalleshi shima.


Fuska dauke da mamaki tace "Who?"


Khalid zaiyi magana Adam ya dawo gabanta yace "Khalid ne." Khalid? Cikin mamaki ta kalli Adam, da sauri cikin magana mara sauti yace cinye duu... kwaro."


Key din hannunta ta cilla mai ya cafe tace "drive."


Khalid ya kalleta cikin rashin fahimta, wucewa tai cikin mota ta bude kawai ta shiga.


*Ayusher Muhd*

[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀 *A GIDANA* 🍀


*Haske Writers Association*💡


*Shafi na biyar*


Wattpad/@AyusherMohd.


Khalid ya kalli Adam wanda ya gunste dariyarsa,daga cikin mota tai knocking din glass din motar, tana rike da tablet dinta tana duduba abubuwan da sukai discussing waccen meeting din, Adam ya kalli Khalid yace "sai kun dawo ma tattauna.


Ya shige ciki da sauri, Khalid ya nufi jikin motar sannan ya bude mazaunin gaba ya shiga tare da tada motar.


Bai mata magana ba itama haka batabi ta kanshi ba, mai gadi ne ya bude gate suka fita, suna fita daga gidan yaja gefen titi yai parking.


Sunyi minti biyar a haka saboda ita dube dubenta kawai takeyi, ganin shiru kamar ba'a tafiya yasa ta dago ta kalli waje, cikin mamaki ta kalleshi tace "ya naga ba'a tafiya?"


Bai juyo ba yace "bansan ina zamu ba."

"Ai sai ka tambaya, saboda sauri nakeyi."

Shiru yai baice komai ba wanda hakan yasata dan jin haushi tace " muje Gamji Tv station."


"Bansan inda yake ba."


Da sauri ta kalli agoggo taga tana bukatar hanzari.

kallansa tai sannan ta bude motar da sauri ta dawo inda yake a zaune.


Kallanta yai itama ta kalleshi tace "am sorry but sauri nake kwatance bazai yiwu ba, can you please go that side?" Ta fada tana nuna mai dayan gun.


Fitowa yai ya zagaya sannan ta zauna a gun, da gudu taja motar, tana kallan agoggo.


Juyawa yai ya maida kanshi waje yana kallan hanya, sai dai kasan ransa gaba daya tunani yakeyi, wani irin aiki ne wannan? Ba'ai bayani? Salman ne ya fado masa, dan tsaki yai wanda shikanshi baisan yayi ba.


Karaf a kunnenta, kallansa tai cikin mamaki gani tai hankalinsa ma bai kanta, tsakin na menene? Ta fada a cikin ranta, wanda abin ya dan mata zafi, dan bata fahimci me tai ba balle a mata tsaki haka.


Gaban Gamji tv tai parking, fitowa tai kawai ta bude baya ta dauko kayanta dake baya, kallansa tai tace " bansan ko zan dade ba, in nai 1hr ban fito ba ka koma gida in na gama zan kora Adam sai yama magana."


Ta juya kawai ta shige cikin building, mamaki ne ya kamashi ya kwantar da kansa akan kujera, idsnunsa ya rufe a hankali.


Wayarsa yaji tana kara ya zarota a cikin aljihunsa, ganin Abba ne yasa ya daga da sauri.


Bayan sun sake gaisawa Abba yace "munji baka kira ba ko baka isa bane?"


Yace "na isa dazu."

"Kaje gidan?" 

Eh kawai yace tare da saurin cewa "ya jikin?"

Abba ya fahimci baisan maganar da alama ko ba shi kadai bane hakan yasa yace "da sauki, anjima mayi waya." Ya kashe wayar, Khalid yai shiru yana kallan wayar dan to baisan me zai cema Abba ba in ya tambayeshi ko ya ake ciki? Bayan shi kansa baisan ya ake cikin ba.


  Yana nan a zaune yana yan tunaninsa jefi jefi yana kallan agoggon wayarsa.


*******


Zainab tana shiga ta wuce office din meeting dinsu, suna zaune suna tattaunawa ta shiga.


Tana shiga ta samu guri ta zauna, dan daga director din sai ita a matsayi, tana zama ta amshi takardun proposal din da akai accepting tana dudubawa, nan ta shiga bayani tare da kawo yanda za'a cin ma manufar, gaba daya kowa yayi shiru yana sauraran jawabinta, har ta kammala sannan tace "ya suke gani?"


Nan kowa yai naam da abinda ta kawo dan dama indai agun harkar aikinta ne ko director din da ita ya dogara saboda tsabar sanin aikinta datai da kuma darajashi datai, nan suka gama taron akan abinda tace shi za'ai, ta mike zata fita ne director din ya mata magana.


Dawowa tai ta zauna tare da kallansa.

"Zainab naji Ramla tayi laifi ayi hakuri a sassauta mata."


Kallansa tai idanunta tsam tace "ni director kai ka kawota ne?"


Da sauri yace "ni kuma? Interview taci aka bata aiki."


Murmushi tai kafin tace "banajin ranar danai interview naganta a ciki, kafi kowa sanin inada rike mutum duk yanda naima interview zan ganeka balle wanda yaci."


Director yai dariya cikin zolaya yace " yo inbanda abinki dani fa akai interview din nan akai audition duk nasan wadanda sukaci sai dai kin manta ta ne."


Murmushi ta sakeyi dan ta fahimci neman karewa yake da alama shi ya kawo ta ko daga sama dashi ne.

Tace "Ah Alhamdulilah tunda dai ba yarinyar ka bace."


Ransa ya sosu da maganar me take nufi da yarinya? Sai dai ba yanda ya iya da Zainab saboda itace ta kawo cigaban da suke dashi yanzu, itace ta jajirce ta maida gidan tv dinsu ya zama abinda ya zama, inba ita yasan komai ya wargaje, amma da badan haka ba da.......

Kallansa tai tace "maganar Ramla ka cireta daga mai dauko rahoto dan inba haka ba zan koreta da kaina, ka maida ita wani bangaren."

Bata jira amsarsa ba tace "zan wuce inba wani abin."


"To shikenan zan duba inda ta dace." Abinda ya iya fada kenan, ta mike ta fito daga office din, tana rufe kofa tai dan ajiyar zuciya na takaici, haka kawai ga mutanen da sukaci ta bada list dinsu a kan su sukaci amma tazo ta tadda a cikin mutum goma da kana dauka mutum hudu ne kadai aka ba aikin ragowar shidan ba ci sukai ba aka basu, gwada su biyar din ma sunyi interviewe faduwa sukai amma ita wannan Ramlan ba wanda ta ganta sai ranar first day din sabon ma'aikatan."




Agoggon hannunta ta kalla, hawanta kusan biyu kenan ta san ya tafi, hakan yasa ta shiga office dinta tare da kiran number Adam.


Shikam Adam tana fita ya shiga yai wanka ya tafi majalisa, suna zaune suna hira wayarta ta shigo.


Mikewa yai ya matsa gefe, yana ji suna tsokanansa yaran Hajiya zata bada aike ne?


"Honey kin taho ne?"


Tace "a'a kayima Abokinka magana ya dawo ya daukeni."


Cikin rashin fahimta yace "ya dawo ne?"


"Kana ina?" Tambayar data jefeshi da ita kenan, sam batasan majalisa dan tasan gulma kawai akeyi, cewa yai "naje siyoma Goggo maganin zafi ne."


Ayya, to bari na kira Nabila.


Kashe wayar tai ta kira Nabila, mamaki ne ya kamata da Nabila tace mata ba'a bataji alamar shigowar mota ba, harta kara dubawa tace ba motarta a gidan.

Wayarta ta daga ta kara kiran Adam tace "baya gida fa."


Adam yace "inata kiran wayarsa kuma a kashe."


Fitowa harabar gun tai inda suke ajiye motoci amma bata ganshi ba, cikin bacin rai tacema Adam badai ya gudu da motar ba?


Shiru Adam yai yana nazari, bafa haka khalid yake ba ya tabbatar sai dai san rai irin na dan Adam sai cewa yai "ah haba?"


Zainab cikin dan zafin rai tace "badai bakasan halinshi ba?"


Shiru Adam yai duk da yasan ba halinshi bane amma sai cewa yai "na sani amma kinsan mutanen yanzu in aka rabu sai su can........"


Kashe wayarta tai saboda yanda taji ranta ya baci matuka, sam batasan in ranta ya baci ta cigaba da magana dan zata iya fadan abinda bai dace ba wanda daga baya zai iya sata dana sani.


Rai a bace ta fito wajen station din, ranta yakai matuka gun baci, tabbas sai tasa an nemo mutumin nan duk inda ya shiga kuwa.


  Tana fita taga motarta a gefen station din, tsaya tai cikin mamaki sannan ta karasa gun tana kallan motar.


Yana zaune a mazaunin driver yana dadana wayarsa.


Kai ta juya gefe tare da jin ba dadi na zargin datai ba tare da ta bincika ba.


Juyawa tai ta zagaya inda take zama sannan tai knocking din glass din, madannin bude motar ya danna ta bude ta shiga, baice komai ba tana zama ya tada mota suka hau kan hanya.


Shiru tai batace komai ba sai dadana tab dinta takeyi, shikam ko juyowa baiyi ba tukinsa kawai yakeyi.


**********


Adam kam tana kashe waya yai shiru cikin mamaki yace meke faruwa? Ba yanda za'ai khalid ya gudu, to ina ya shiga?


Da sauri ya musu sallama sannan ya ja motarsa ya nufi station dinsu.


Yana isa ya shiga ciki, yana shiga ya hadu da wani wanda yana ganinshi ya ganeshi matsowa yai ya gaisheshi, Adam yace "Zainab fa?"


"Ta tafi dazu."


Kai ya jinjina sannan ya juya tare da kiranta a waya.


Tana zaune cikin mota ya kirata.


"Honey Kina ina? Nazo bakyanan."


A hankali tace "ina hanya, kaje ina?"


Yace "nazo daukanki mana."


Da sauri tace " na sameshi a waje ai mun taho."


Sai data fada ta kalleshi kadan, karya gane zargin da sukamai.


Shikam baimasan metake yi ba, jitai yace "left or right?"


Kallan hanya tai sannan tace left, tace "Honey sry ka taho gida."


Kashe wayar yai yana cewa "nimadai kwai soko ko me nake anan?"


  Yana shiga mota ya tuna karyar dayai da sauri ya kira Goggo, itakam tana zaune tana kallo batamasan yana kira ba.


Haushi ya kamashi ya cilla wayar kujerar dake gefensa matsalar Goggo kenan, tana can tana tainannan kallanta batamasan yana kira ba.


******


Khalid left or right? Abinda kawai yake ce mata kenan in yaga ya kasa gane inda suka biyo dazu, suna shiga cikin harabar gidan ta fito tana kokarin shiga ciki.


Mamaki ya kamashi yace "Excuse me."


Tsayawa tai tare da juyowa sannan ta nuna kanta alamar ni?


Yeah.


Haka yace mata wanda yasa ta kara kallansa batace komai ba.


Kallanta yai yace "lokaci na wucewa inada abubuwan da zanyi sorting a yau din nan, and it seems like bakida niyyar yimin bayanin yanda aiki na yake da abubuwan da ya kamata nayi da sauransu.


  "Am sorry amma you have to told me saboda insan abinda ya kamata nai kafin dare yai, ba'a gari nake ba, inasan komawa."


Gaba daya jitai ma ta rasa bakin magana, yau take ganin ikon Allah, yana mata magana kamar itace take aiki a karkashinsa?


Sannan Excuse me?


Meya dauketa?

Ko dan tana matar abokinsa yana tunanin wulakantata?

Harda tana tausayinsa tana ganin Adam yaci zarafinsa ashe shima dan rainin wayau ne?


"Excuse me, naji kinyi shiru."


Excuse me? Again?????


  Ranta ya baci, kallansa tai cikin bacin rai sai dai yanda yake kallanta da jiran tamai magana yasata juya kanta abokin Adam ne, cool down.....


Bude kofar da akai ne yasa ta kalli kofar, Nusaiba ce ta fito da gudu ta rungumeta, kallan Khalid wanda ke tsaye ta tsaya tana yi, Zainab ta zare ta sannan ta kalleshi tace " bari Adam ya karaso sai kuyi magana."


Haka kawai tace ta shige ciki.


*Ayusher Muhd*

[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀*A GIDANA*🍀


*Haske Writers Association*💡


Shafi na shida


Wattpad/@AyusherMohd.


   Duk yanda yaso karya nuna bacin ransa amma wannan lokacin ya kasa, mekenan? Dan yana neman abinyi shine zai zama wulakantace? Ai ta tsaya taji mezaice.


  Zainab kam tana shiga ta tsaya a jikin kofa sannan tace was i mean? To mezance? Yanata wani cemin excuse me, ko suna nane hakan ai sai haka, juyawa tai taga bataga Nusaiba ba.


Nusaiba kam tsayawa tai cak ta kasa dauke ido daga kansa, can ta hangota zaune kusa dashi ta sa kanta a kafadarsa tana bacci.


Sam baima kula da ita ba sai dayaji an bude kofar, Zainab ta kalleta tace “me kike anan?”

Gaba daya Nusaiba batama san tana yi ba, jin magana ne yasa ya kalli gun, sai yanzu ya kula da yarinyar dake tsaye agun.

Zainab ta kalleta sannan ta kalli inda take kallo, hada ido suke wanda Khalid yai saurin kauda kansa, Zainab tasa hannu ta juyo da ita saitinta tace “lafiya?”


Nusaiba tace “Aunty kamar mafarki nake ko?”


Kallanta tai sannan tace “mafarki anan?”


Nusaiba ta daga kai tana wani irin murmushi, Zainab ta ja hannunta suka shiga ciki.


Khalid waya ya dauko ya kira number Adam, Daga can Adam yana tafe yana shan kidansa, parking yai a gaban wani shago ya shiga ciki, shago ne dayake ta ganinsa satin nan da alama ba’a dade da budeshi ba.

Shiga yai yana kallan kayan dake cikin shagon, shago ne na kayan sawa, na mata dana maza.


Haryana kokarin fita yaga wani takalmi, wanda ya dau hankalinsa, dawowa yai da sauri ya daga takalmin, duba size din da yake sakawa yi ya nufo gun biya yana kokarin bada kudin ta nufo gun rike da wata riga ahannunta, abaya ce rigar, duk rigar jikinta tayi kacha kacha.


  Mikama mai biyan kudin tai, kallanta yai sannan ya kalli Adam yace “dubu goma ne.”


Adam ya mikamai katinsa ya biya, hankalinsa a kwance.


Haryadanyi gaba yaji yana cemata “dubu biyu.”


Kallansa tai tace “malam dan Allah kabarmun dubu daya da dari biyar wlh jakata aka sacemin duk kayana dana taho dashi, dubu biyun nan dake jakata su kadai gareni.”


Kallanta yai yace “kiyi hakuri hajiya amma ba shagona bane.


Harzaj juya ya dawo ya mika katinsa, ba tare dayace komai ba, mai shagon ya kalleshi yace zaka biya?

Adam ya juya kai, nan ya sa pin dinsa ya biya ya juya yai gaba.


Da sauri ta biyoshi tana cewa “Malam! Malam!”


Adam sai dayaje gaban mota ya juyo matsowa tai da sauri tace “nagode, ka taimakeni, zuwa na kenan garin kano aka sacemin kayana gaba daya........”


Wayarshi datai kara ita ta katseta? Daukan wayar yai ya shiga mota ya ja yai gaba.


Khalid ya?


Daga can Khalid yace “Adam dan Allah kana ina?”


“Ganinan a hanya yanzu zan karaso.”


Khalid yai ajiyar zuciya baice komai ba.


“Wani abin ya faru ne?”

Ya fada a ransa yana cewa yasa ai Khalid bazai taba jurar halin Zainab ba wannan aikin nasu ya basu wata daya in anyi nisa.


“No sai kazo.”

Adam yace okay, ya kashe wayarsa, yana tafe yana shan kidansa, hankalinsa a kwance, tunowa dayai da Goggo ne yasashi kara sauri, yasan kila ma ta fada, mai yakaishi tsayawa a shagon can? Sam yama manta abinda ke gabansa.


*******


Zainab kam suna shiga ciki ta makama Nusaiba harara tace “kin gama mafarkin?”


Nusaiba ta kalleta ta matso kusa da ita kamar zata shige cikinta tace “Aunty wanene dan Allah?”


Zainab ta kalleta tace “wa?”


Nusaiba ta kalli window tana nuna mata Khalid dake tsaye yana waya.


Zainab tace “menene damuwarki dashi?”


Kara rike ta tai tace “Aunty dan Allah ina gama secondary ku aurar dani, ku bani shi.”


Kallan mamaki Zainab ta mata  kafin ta girgiza kai tace “Nusaiba da alama kin samu matsala.”


Tai ciki tana cewa “ina Nabila?”


Tana daki, Zainab ta wuce cikin dakin nasu.


Nabila na zaune akan gado tanajin an bude kofar ta boye abinda ke hannunta da sauri.


Zainab ta maida kofar ta rufe sannan ta nufo inda take, Nabila ta kalleta tace “Aunty kin dawo?”


Zainab ta matso bayanta tasa hannu ta zaro abinda ta boye, littafi ne na makaranta ta bude cikin litaffin tare da girgizashi.


Hoto ne ya fadi daga cikin littafi, Zainab zata dauka Nabila tai saurin daukewa ta boye.


Mika mata hannu Zainab tai tace “Bani.”


Nabila ta kalleta idanunta suka ciciko, Zainab ta hade rai tace “bakiji ba?”


Jiki a sanyaye Nabila ta mika mata hoton, tana amsa ta juya baya hoton, sai dai me? Gaba daya yanayin fuskarta ne ya canza, idanunta suka canza, a hankali ta dago ta kalli Nabila wacce hawaye suka zubo mata.


Zainab ta zauna kusa da ita, ta zuba mata ido cikin tausayawa.

Nabila ta share hawayenta tace “Aunty.”


Zainab ta sa hannu ta karasa goge mata hawayen sannan ta kalleta tace “badai haka kikeyia makarantar ba?”


Kai ta girgiza da sauri alamar a’a sannan tace “na dade Allah banyi ba.”

Zainab tai murmushin yake tace “kafin mutanen gidan wu gane, ki tashi ki ware, ina mai bakin tsiwar tawa take ne? Ina mara hakurin nan da neman fada yakene?”


Nabila tasa dariya tace “kai Aunty.”


Zainab tace ba haka bane?


Nabila tana dariya ta mike tai waje.


Shiru Zainab tai a dakin, tare da kara kallan hoton hannunta, raunin datake boyewa nata kar a sani shine ya nemi tasowa, hannunta ne ya fara rawa da sauri ta mike tare da bude windown dakin dan tasha iska saboda zuciyarta tayi nauyi.


Wani nannauyan ajiyar zuciya ta saki tare da kallan waje, Daga can gefe ta hangoshi tsaye yana waya, Excuse me! Excuse me!


Abinda ta tuno kenan, ko baka san sunana ba ai sai kawai kai maganar da kakesan yi Excuse me din na menene? Taja dan gajeran tsaki tana neman zuge window din taga ya kalli gefe, sai kuma taga ya dan daga hannu kadan ba wani alamar sakin fuska hannun dai yadan daga.


Da sauri ta fito daga dakin ta nugi falo, Nusaiba!


Abinda ta fada kenan, Nusaiba ta kalleta da sauri, sannan ta zuge labulen windown.


Zainab ta kalleta, da sauri ta boye a bayan labule tace “Aunty gaisheshi kawai nai.”


Nabila wacce tana fitowa kitchen tai ta zubo abinci tace “karyane kafeshi tai da ido wanda inaji daga nan sai daya kware.”


Zainab duk yanda taso ta hade rai sai datai dariya tace “ruwa yakesha kenan?”


Nabila tace “eh mana.”


Nusaiba ta sa dariya harda faduwa tace “Kanwa uwar hadi, wlh andaiji jiki.”


Nabila ta kalli Zainab tace “Aunty wanene?”


Zainab tace “oh bakimasan me ake cewa ba kike shiga abinda bai shafeki ba, ni ina Goggo ne?”


Nabila tace “ta tafi siyo anko wai ita da kawayenta........” ta karasa maganar tana dariya.


Nusaiba ma dariya tasa tace “wai anko, ina Goggo ina anko?”


“Meye naku a ciki? Kunga ku kiyayeni da wannan bakin naku.”


Jin karar gate ne yasa Nusaiba ta bude labule, Oh Uncle, ko ina yaje?


Hala majalisa, Nabila ta fada tare da zama.


Shiru Zainab tai tana tunanin abinda yace mata, ciki ta wuce kawai ta shiga daki, alwala tai kawai ta sa hijab ta tada sallah.


*****

  Adam na parking ya matso gun Khalid dake jiransa, hannu ya mikamai suka gaisa yace “Kwaro ya?”


Khalid yace “Adam please ka daina kirana da haka.”


Dariya Adam yai yace “To Kwaran danbatta shikenan?”


Khalid ya fahimci rainin wayau ne shiyasa bai tankashi ba yace “so nake naji me da me zandinga yi saboda in san yanda zan tsara komai.”


Tsara komai? Kaida kazo aiki? Abinda Adam y fara kenan a ransa amma a fili yai dariya yace “da farko dai sai kayi hakuri dan Hajiyar akwai fada kamar.....” yamai rada a kunne, wanda nima banjisu ba.


Sannan ya dago yace “ abu na biyu gaskiya aiki ne ya ganka saboda journalists ce babba wacce kuma take uwar aiki wato agoggo kenan, dan ko na kasa da ita sun kawo report na abinda suka dauko wani abin bata yarda dashi harsai taje da kanta ta gani, ta tantance, sannan sau da dama takan je gurin da kanta dan rashin yarda da aikinsu, tafisan ayi a gabanta.


To kaga duk wannan lamari kaine zaka dinga jelar kaiwa da dawowa, sannan sukan tafi wani garin dan dauko rahoto ko kuma meeting nasu na yan gidan tv da sauransu.


Abu na karshe tana fita karfe bakwai da rabi na safe ta dawo karfe shida na yamma, sannan daga gun aikin tana yawo sosai.”


Khalid ya kalleshi sannan yace “ nagane, weekend fa kamar yau?”

Adam yai dariya yace ai kai bakada hutu dan wannan bansan kai na nawa bane a wadanda ta kora wani da kanshi ma yake gudu saboda wahala.


Khalid ya kalleshi yace “ni ba wannan bane damuwata, abu daya nakeso in fada, zan fara aikin nan ina naiman nawa aikin, da zarar na samu aiki zanyi resigning.”


Adam yana dariya yace “bakimai sai dai fa karka manta neman aiki yanzu a kasarnan sai da hanya, waya sani ko in ka daure Hajiya ta nemar ma.”


Ba karamin sosa mai zuciya wannan kalaman sukai ba, murmushi yai yace “ni Adam wani aiki kake ne? Naga har weekend kamar kaima kana aiki?”


Ran Adam ya baci wanda ya bayyana a fuskarsa, kallansa yai yace “menene?”


Khalid yace “bakomai kawai dai tambaya nai naji kamar rannan kacemin kai matarkace mai kudin ko? Ita take baka, haka dai kamar naji, amma sai nake tantama dan nasan yanda kake da san kai abu da kanka kamar bazaka yarda ka zama mijin Hajiya ba.”


Fuskar Adam ta murtuke sosai yace “me kakesan cewa ?”


Khalid yai dariya yace “me zance kawai cewa zanyi ko dayake mijin Hajiyar ma matsayi ne.”


Adam ya washe baki yana dariya yace “sosai ma dan banaji irinku zasu samu.”


Khalid yace “sosai, bare kuma ni kasan bansan a bani, bari na wuce zanje Cafe ne.”


Adam sam bai fahimci magana ya fadamai ba yace “a ina zaka dinga kwana? Muna da dan daki, ya fada yana nuna wani daki can dake gefe, da sauri Khalid yace “Saida safe.”


Ya mika mai key, haryayi gaba ya dawo yace “Sorry Adam me nene salary dina sannan yaushe za’a dinga bani?

“Am sorry but inasan sani ne dan na san yanda komai yake tafiya.


Adam yace “gobe in kazo zata baka contract din sai ka sa hannu, dan nima bansan yaushe take biyansu ba.”


Khalid ya mika mai hannu sukai sallama ya tafi.


Yana fita yabi kofar gidan da kallo, tabbas dole ya kara zake dantse ya nemi aiki dan bazai iya jurar wannan aikin ba.


*************


Wajen karfe 9 na dare ta shigo dakin yana zaune yana latsa waya ta shigo, kwanciya tai tare da rufe idanunta, kallanta yai yace “tun dazu nakeso kizo muyi magana kiji yanda mukai da Khalid.


Kallansa tai sannan tace “Dazu kaje majalisa ne?”


Da sauri yace “a’a takalmi naje siyowa.”


“Meyasa kamin karya to kace kaje siyoma Goggo magani?”


Yace “Sorry honey lokacin ina bank ne banasan yin doguwar magana.”


Ido ta kuramai, sumbatarta yai yace “banace miki na daina zuwa ba? Ko baki yarda dani ba?”


Murmushi tai ta rungume shi tace “kaima kasan duk duniya kai kadai ne namijin dana yarda dashi.”


Kanta ya shafa yana fada mata yanda sukai da Khalid, kallansa tai tace “Honey are u sure wannan mutumin zai yi? Nifa sam hankalina bai kwanta dashi na, sai naga kamar ma fada yakemin.”


Dariya sosai Adam yai kafin yace “Yau wacece wannan anya Zainab ce?”


Tace “Allah ni yau saura kadan ma na koreshi.”


Adam yace “ba fada yake miki ba haka maganarsa take, kinsan a skul sam bashida friends na kudakud? Duk wanda kika gani dashi to fa morarsa yake, saboda iliminsa ne yasa muke juremai, sai daga baya kowa ya gane haka yanayin maganarsa yake.”


Zainab tadan tabe baki tace “sai kace shi kadai ne bashida friends.”


Adam yace “ke da shi akwai banbanci, ke kece bakyasan friends din, shi kuma mutane ne bazasu iya jurar halinsa ba, kinsan daga farko kowa ya dauka dan mai kudi ne?”


Murmushi tai tace “why?”


Nan ya fara bata labari hartai bacci.


Wajen karfe uku ta farka a zabure, addu’a ta shiga yi ta kalli Adam wanda ke kwance yana bacci, mikewa tai ta fito falo, kofar dakin su Nabila ta bude, suna kwance suna barcinsu wanda hakan ya sata murmushi.


Dauko hoton dazu tai ta zauna a falo tana kallanta? A hankali tai murmushin dayafi kuka ciwo tace “Mamana.....”


Nabila wacce taji sanda aka rufe kofa itace ta bude kofa, kallan Zainab tai da sauri ta taho gunta ta rungumeta.


Zainab ta kalleta tana hawaye ta rike hannun Nabila tace “Nabila ba abinda ake miki?”


Nabila tana kuka tana cewa “kema Aunty kinsan bazan bari ba.”


Zainab ta daga kai tana murmushi tace “na manta My boss ce.”


Nabila tai shiru cikin yanayin damuwa, Zainab ta kalleta tace “Maman Nusaiba na takura miki ne?”


Tace kema kinsan ni, Aunty karki bari Uncle ya miki abinda Dady yama Mama, shi yasa sam nikam banaji zan iya aure har na mutu, Aminiyarta, a kullum......”


Ya akai kika sani?

Tambayar da Zainab ta jefe ta dashi kenan tare da mata kallan zargi.


*Ayusher Muhd.*

[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀 *A GIDANA*🍀


*Na Ayusher Muhd*


*Haske Writers Association*💡


*Shafi na bakwai*


Wattpad/@AyusherMohd.


  Idanunta Zainab ta kalla tace "Nabila!"


Nabila ta mike da sauri tace "ba abinda na sani, kawai dai maganar ce tazomin."


Zainab ta kalleta, da sauri ta shige daki ta maida kofar ta rufe.


Shiru Zainab tai tare da zubama kofar ido, kafin ta mike ta nufi daki, agoggo ta kalla taga karfe 4, computee dinta ta dauka ta koma falo ta zauna.

  Wajen karfe biyar ta mike ta shigo daki ta kalli Adam dake ta baccinsa, kusa dashi ta zauna sannan ta dan tabashi, tace "Honey a daure atashi aje masallaci."


Batare da ya bude idansa ba yace "bacci nakeji, nayi anjima."


Hannu tasa ta jashi ta zaunar dashi akan gadon, a hankali ya bude idanunsa yace "Honey Allah bacci nakeji."


Fuska ta hade tana kallansa batace komai ba.

"Na tashi shikenan?" Ya fada tare da bude idanunsa sosai, sakeshi tai sannan tai murmushi tace "ko kaifa."


Yake ya mata, gira ta daga mai ta nuna mai toilet da ido.


Ajiyar zuciya yai sannan ya mike yai alwala yana fitowa ta mikomai jallabiya ya saka yana ta dan zumbure zumburenshi kai kace yaro ne aka kwacemai alawa.


Fitowa yai daga gidan ya nufi hanyar masallaci.

Suna idar sa sallah shine na farkon mikewa ko addu'a bai tsaya ba ya fito, ganin Nazifi a masallacin yasashi saurin bi ta baya, dan bacci yakeji bashida lokacin tsayawa magana.


  Daga kungun da zai shiga kwanar gidansu yaji motsi, cikin tsananin tsoro ya matsa da sauri tare da zaro wayarsa ya haska fitila yana cewa "waye nan?"


Ganin ana kara buyewa ne yasashi kara matsowa gun yana haska fitilar duk da tsananin tsoron da yakeji.


Yana neman karasawa daf da mai boyewar aka saki kwalin da ake boye fuskar dashi.

A tare suka saki wani kara, yaja da baya da sauri, bayan sun gama karar ne ya haska fitilarsa a tsorace.


Tsayawa yai cak yana kallan ta, haska kansa yai hakan yasa ta gane shi.


Kallanta yai yace "bake bace ta dazu? Me kike anan?"


Kanta ta saukar kasa tace "komai na wa an sace kuma makaranta nazo, gashi bansan kowa ba, banko biya kudin hostel ba.

To me kike anan kina mace?


Bansan ya akai na ganni anan ba, shiru yai yana kallanta kafin yace "bakisan kowa ba a kano?"


Kai ta daga alamar eh, shiru yai yana kallanta kafin yace "to ki koma garinku mana in safiya tayi?"

"Ban isa komawa ba inba haka ba mijin mamanmu dukana zaiyi."


Shiru yai yana kallanta bai fahimceta duka ba, kamar yace ta biyoshi kuma yafi kowa sanin matarsa, da sauri yai gaba bai kara waigowa ba ya shige gida.

Yana shiga yai ajiyar zuciya yace " ashe dai inada tausayi."


Kai ya girgiza da sauri ya shige ciki.


A zaune ya taddata a falo taba kan sallayabga laptop dinta a gefe, da sauri ya wuce daki.

Ta fahimceshi wato kar ta mai magana shiyasa ya shige, yana shiga ya kwanta, kan kace me bacci yayi gaba dashi.


***********


A bangaren Khalid kuwa bayan yabar gidan cafe ya wuce ya duduba aiki, sai wajen magrib sannan ya nufi gidan kawu.


Sam ya tsani zuwa gidan dan yana shiga layin yaci karo da babbar 'yarsa mace, anci uban kwalliya a gaban mota itada saurayinta.

Yi tai kamar bata ganshi ba shima ya dauke kai.


Ji yake kamar karya shiga gidan, ya dade a tsaye a kofar gidan yana tuno bakincikin halayensu daya sha farkon zuwansa, harya juya da niyyar komawa danbatta inyaso da sassafe sai ya dinga fitowa yaji ance "Khalid?"


Juyawa yai, dan ya san wanene, Kawu ina wuni?


Abinda yace kinan yana rusunawa, Kawu ya dafa kafadarsa yace "ina zaka da?"

Muje muje, ya jikin Baban naka?


Da sauki, ai naso kara komawa sai dai bana zama ne nima.


Khalid dai baice komai ba, haka suka shiga ciki inda suka wuc falansa yasa a kira matan nasa.


Su uku ne suka shigo kowa sai yace "khalid yau kaine a nan?"


Bayan ya gaisu ne Amaryar ta kalleshi tace "da alama an dace an samu aiki kenan."


Kawu yai saurin cewa "haba?"

Khalid yai murmushin yake kawai, nan ya zauna sukaci abinci tare bayan sunyi sallah, nan ya fito ya wuce bangaren maza, yaran gidan sam basu da tarbiyya suna ganinshi fa amma kaf dinsu ba wanda yamai magana, kowa harkar gabanshi yakeyi, sai shine yace sannunku, kawai ya wuce dan dakin da yake zama, shi da Annur wanda yake karami ne shekarar sa 15 yanzu, Annur shima baya nan, jikinsa ne yai sanyi badai shima harya shiga sahun su ba?


Ajiye yar jakarsa yai sannan yace "bazan iya zama anan ba, daga gobe gwara na dinga zuwa daga danbatta da safe, kwanciya yai yana jin haushin amsar aikin nan dayai.


********


Haryai bacci baiga Annur ba sai da safe daya tashi ya ganshi yana bacci, tashinsa yai yace "sai a tashi a shirya ko?"


Annur yana mikewa ya rungume Khalid yace "ya Khalid."


Khalid ya tureshi yana dariya yace "mutum dai ya tashi kafin ya makara.


Annur yana dariya yace "jiya kawai na dawo naganka?"


"Kana ina har wajen 11?"


Annur yace "muna can muna hida da friends din mu."


Kamar Khalid zai sake magana sai ya fasa, shiryawa kawai yai ya dau jakarsa da niyyar zai dawo ya fita.


Mota ya hau ya nufi gidan.


  Karfe bakwai da minti takwas tamai a cikin gidan, tsayawa yai a waje suka dan fara hira da mai gadin.


A ciki kuwa Zainab ta gama shiryawa dan dama bata koma bacci ba, tana fitowa daga daki taga goggo ta fito tana murza ido, Zainab ta gaishet tana cewa "Goggo adan dai rage kallan nan, kamar yana yawa."


Tana fada ta nufi kitchen, Goggo tsayawa tai ranta yai mugun baci, harara ta bita dashi tace "wannan yarinya da ace ta hada jini da Ado da bamusan yana zata kareba, to sai kuma kikai sa'a bakuda hadi dashi yar kwal......"


Ganin Zainab ne yasa ta kalleta ta saki dariya tace "Gwara dai ki tafi da ko dan shayin ne, amma ace mutum ko abincin safe baya ci?"


Zainab tace "na wuce."

"To adawo lafiya, dan Allah ki tahomin da goro."


To kawai tace ta fita, tana fita Goggo ta tabe baki tace "a haka dai, an kasa bani jika sai feleke kamar, kamar."


Ta kunna socket ta zauna tana cewa "dole nasha ruwan tea dan sam jiya ranta ya baci dasu Nusaiba suka dafa macaroni, haka tasha kunu ta kwanta."


Zainab na fita ta ganshi suna magana da mai gadi, agoggon hannunta ta kalla, bakwai da ashirin, sam bati tunanin ganinshi ba, ta fitone ta fara aiki a cikin mota kafin ya karaso."


Tsayawa tai a bakin kofar, yana ganinta ya nufo inda take, kusa da ita yaje ya mika mata hannu, kallansa tai tace "no am okay, zan iya dauka."


Ta fada tare da dauke kai, "no ina nufin key."


Da sauri ta kalleshi, haushin kanta ya kamata, rikemin, ta fada tana mikamai tea din, ya amsa ta juya ciki, tana shiga ta fito, mikamai tai ya mika mata tea din sannan ya amsa ya wuce ya bude motar, wani irin kallo tamai sannan ta wuce ta shiga.


Sun fara tafiya taga anzo kwana, kafin yai magana tace "nan zakai."


"Na gane hanyar."

Juya kai tai dan dama batasan ya fara mata zancen left da right din nan ne yasata yin magana dan ba karamin haushi taji jiya ba.


So take ta tsaya ta sai biscuit dan na office dinta sun kare, kallansa tai tace "Excuse me dan gangara gefen titi nan."


Neman gangarawa yake ta kara cewa "Excuse me daga dan can."


Karasawayai yai parking, ta fita daga motar, tana fitar tai murmushin jin dadi tace "kaji ko da dadi."


Shikam sam bai kawo komai ba, harta dawo ta shiga.


A cikin tv station din yai parking, ta kalleshi tace "zaka iya zuwa ka dawo, in ina bukatarka zan nemeka."


Okay.


Shiru sukai sannan ta daure ta mikamai wayarta tace "zan kida Adam in na kusa gamawa."


Okay

Ya kara cewa, fitowa tai ta shiga ciki.


Tana shiga bakin gun ta hade fuska tamau, ko ina ta wuce gaisheta akeyi tana amsawa, kayanta kawai ta ajiye ta dawo ta hau aikinta.


***********


Karfe sha daya ya farka? Mika yai sannan ya fito daga daki, yana tafe yana hamma, a falo yana goggo tana ta maka dariya, kallanta yai ya girgiza kai, ya matso yana cewa "wlh Goggo jin dadinki yayi yawa."


Kallansa tai tace "kai kuma fa? Wai kai dan Allah bakajin kunya? A matsayinka na namiji kullum a gida?"


"Kedai kiyi kallanki dan ni ba kunyar da nakeji, ina wadancan yan rigimar?"


Suna kitchen dan wulakanci sai yanzu suke abincin safe


Dariya ya mata yace "to ai da ke kinyi Goggo ni me kikeyi ne a gidan?"


Tace "amma in basa nan ai inayi, in suna nan kam bazan ma katti abinci ba."


Kai ya girgiza, ya mike yana cewa "Goggo ta tv ni wai kina kallan shirin sirikarki ma?"


Tace "ina kallo mana, ba gwara ni ba kai sai karyar kana kalla bayan haryau bansan a inda kake kallan ba."


*AYUSHER MUHD*

[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀


Haske Writers Association💡


Shafi na takwas


Wattpad/@AyusherMohd.


*********


  Bude kofar tai sannan ta shiga cikin inda ake editing.


Suna ganinta kowa ya zauna daidai, tare da maida hankali kan aikinsa.


Fitowa tai ta bude cikin news room suma gyare gyare sukeyi tana gamawa ta fito, da niyyar wucewa dan ta shirya saboda program dinta.


Tana shiga taga Ramla a zaune tana waya.

Sam bata kula tana bayanta ba sai da Zainab ta karasa gun, Ramla na juyowa sukai ido hudu da Zainab da sauri ta mike daga gun da sauri tare da cewa "Good Morr.."


Kallan da Zainab ta mata ne yasa ta yin shiru, sannan tace "ba laifi dan dama irinku kallo daya mutum dai muku ya fahimta."


Ramla cikin mamaki tace "ya fahimci me?"


Zainab ta mata alama da kai akan ta fita, Ramla idanunta suka ciciko, ta bude baki zatai magana  Zainab ta kalleta wanda hakan yasata yin shiru, hawaye ne suka zubo mata tasa hannunta share sannan ta fita.


Tana rufe kofa Zainab ta dan sauke numfashi kadan cikin takaici, sannan ta wuce ciki.


Ramla kam fitowa tai cikin station din tana dan hawayenta.


Kusa da wata mota ta tsaya ta share hawayenta sannan ta dau waya, bata dade da dialing ba aka daga, daga can ta fashe da kuka tana cewa "Yallabai.....kawai tasa kuka.


Daga cikin mota Khalid dake zaune yana waya da Abbansa ya kalli jikin windown.


Sallama sukai ya kashe tare da rufe idanunsa, kuka ta cigaba dayi tana cewa "Nikam matarnan ta tsaneni wlh, yaufa saura kadan ta kirani karuwa..."


Ta kara sa kuka, haushi ya kama Khalid ya kalli jikin window din gashi ta tsaya jikin kofar ba dama ya fita.


Ta cigaba "ni dai Allah bata sona, wai tsoran Zainab din kake?"


Can kuma ta kara sa kuka, sannan ta kashe wayar, tana kashewa ta kalli madubin jikin motar dan gyara fuskarta.


Kallanta taga anayi, idanunta zato da sauri sannan ta sa hannu dan bude motar, Khalid ya bude motar sannan ya kalleta.


Sai yanzu ta kalli jikin mottt are da take, gabanta ne ya fadi dan tasan motar Zainab, idanunta ne suka fifito ta kalleshi sannan ta danyi yake tace "ashe da mutum a ciki."


Khalid ya fito ya rufe motar yana neman tafiya.


Da sauri tace "kaji me nace?"


Kallanta yai sannan yace "daga ina?"


Ta dan motsa baki sannan tace "kaji daga farko har karshe kenan?"


Juyawa yai bai amsa ba, tai saurin cewa "dan Allah kayi hakuri karka fadawa Assistant director Zainab."


Ta ina zan fada mata? Abinda yake tunani kenan, da sauri tace "dan Allah, karka fada mata."


Juyowa yai ya kalleta, mota ta nuna mai tace "ba motarta bace?"


Sai yanzu ya gane, juyawa kawai yai ya wuce, dan wata irin yunwa yakeji, Ramla ta saki ajiyar zuciya tace "shikenan na gama yawo, you are fired."


**********


  Adam ne yai shiru a falo, Goggo nata waya tana ma mai dinki bayani akan dinkinta, Nabila da Nusaiba na gefe suna dane dane a waya, wata nannauyan ajiyar zuciya yai wanda Goggo tana waya tadan kalleshi, mikewa yai ya fita, bai dade sosai ba sai gashi ya dawo.


Goggo ta kalleshi tace "ina kaje?"


Kallanta yai yace "Goggo!"

Ta kalleshi ya mata nuni da daki.


Mikewa tai ta fito suka nufi daki, tana shiga tace "menene?"


Kallanta yai tare da zama yace "Goggo yarinyar can na bukatar taimako" kallansa tai tace "wace yarinya kenan?"


Labari ya bata na yarinyar sannan yace "Zainab bazata taba bari a taimaketa ba."


Goggo tace "ka sani kazo kana fada? Kai ba ka saki jiki komai sai dai a maka ba."


Yace "wai Goggo ba a dalilina kikejin dadin nan ba? Meyasa komai nazo miki dashi sai ki dinga fadamin magana?"


Goggo tace "to ya kake so ayi? Kafi kowa sanin Zainab, ko kawarta ka taba gani a gidan nan? Daga ita sai kanenta sai ni? Sai dai in kanwa ce dakai amma inba haka ba wa ka isa kawowa gidan nan?"


Shiru yai kafin ya kalleta da sauri yace "Goggo!"


Kallansa tai yace "in mukace mata Sadiya ce fa?"


Cikin mamaki ta kalleshi tace "mene?"


Yace "in muka dan kawota akan Sadiya ce in tai kwana biyu sai mu sallameta, bayan ta gama cike abin makarantarta."


Goggo ta saki baki tana kallansa tace "ne kake cewa?"


Kallanta yai yace "Goggo bakiganta ba haryanzu fa tana waje, abin tausayi."


"Ni wai yaushe ma ka fara tausayi ne? Sannan a ina ka santa balle kasan halinta? In aljana ce fa?"


Wata dariya ya saki yace "wani irin zance kike."


Tace "lalai Adam bakada hankali wasa wasa, kanwarka? To in abu ya tashi Sadiya tazo daga kura fa?"


Yace "lokacin sai musan me zamuce kuma hali ma irin na Zainab ganewa zatai."


Kallansa tai galala kafin tace "ka samu matsala wlh, kuma ni ba ruwana, in da raban garin taimako......"


"Haba Goggo meyasa kike haka ne? Taimako na kwana daya zuwa biyu sai ya zama haka?"


Tace "ni wai yaushe ka zama mai taimako ne?sannan taya zaka shigo da ita?"


Shiru yai kafin can yace "dama yanzu nake tunanin in shigo da ita a boye inyaso intai wanka sai.....".


Shiru yai dan kansa ya kulle, Goggo tace "sai me? Sai na bata kayana tasa?"

Tai maganar cikin gatse, da sauri yace "eh sai ki bata ta saka yanda inta dawo sai nace mata ga Sadiya tazoyin kwana biyu, a yanda take dawowa a gajiye ma ina zata ganeta? Sannan gobe kinga da safe zata sake fita, kinga tana gamawa sai mu sallameta."


Kai zaka biya mata kudin makarantar? Tambayar da Goggo ta jefeshi da ita kenan, kallanta yai sanan yace "Goggo wai meyasa kike haka?"


Tace "to wa zai biya mata? Zainab?"


Yace "in taji Sadiya ce ai zata taimaka."


Goggo ta mike tace "can kai ka sani ba abinda ya dameni, nidai wlh kaja aka ganeka abu ya shafeni ranka ne zai baci."


Adam yai shiru yana kallanta.


  ************


  Zainab na zaune a office tanacin biscuit da juice, badai yana waje ba? Abinda ya fado mata kenan? Mikewa tai bayan ta gama hartayi hanyar waje sai kuma ta koma ta zauna tare da cewa "ai yau dole yaje ya dawo saboda zaman yayi yawa.


Da wannan ta cigaba da aikinta, wajen sallar la'asar taga kiran Director, tana kallan wayar har sai da ta katse, sake kira akai ta kalli wayar sannan ta daga.


Zainab!


Tace "Yallabai ina wuni?"


Daga can ya amsa yana cewa "ya aiki?"

Tace "lfy."


"Ashe Ramla tayi laifi? Ayi hakuri kinsan yaran nan ne wlh sai a hankali."


Tace "saboda haka ka kira?"

Yace "no dama ina san fada miki ne wannan proposal din sunce gobe aje a musu presentation."


Tace "that's nice, zan shirya power point."


Yace "yauwa, sai gobe."


Nan sukai sallama ta kalli wayar sannan ta girgiza ki.


Sai karfe shida ta tashi? Ramla naganinta ta boye, Zainab ta wuce tana kiran Adam, duk da dai jikin ta na bata ya dawo.


Motar ta gani a waje hakan yasa ta nufi gun.


Ba kowa a ciki, hakan yasa ta dan wawaiga, daga gefe ta hangoshi ya nufo gun, da alama zama yai a gun.


  Bude motar yai, ta bude baya ta shiga.


Shiga yai yaja suka fara tafiya.


Shiru suka danyi a motar, tana kallan wayarta, can tace "badai a waje ka zauna ba ko?"


Baiyi tunanin dashi take ba sai dayaji shiru alamar ba waya take ba sannan yace "cafe naje."


Shiru sukai ba wanda ya sake magana har suka kusa isa, daurewa tai tace "gobe daga gun aiki zamu fita zuwa kaduna, in na shiga gun aiki 1hr zanyi a ciki sai mu wuce."


Okay kawai yace suka karasa ciki......


*Ayusher*

[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀


Haske Writers Association💡


Shafi na Tara


Wattpad/@AyusherMohd.


Harta bude kofa zata fita tadan juyo, kallansa tai tace " yanzu zaka wuce?"


Yanzu kam ya juyo yadan kalleta kadan yace "eh zan wuce danbatta ne."


Danbatta?

Ta fada cikin mamaki, juya kansa yai yace "eh."


Fitowa tai batace komai ba, tana neman bude kofa taga an bude da sauri, Nusaiba? Ta fada tana kallanta.


Sam batama kula da ita ba ta wuce gun Khalid da gudu? Yana rataya jakarsa a baya taje kusa dashi tace "Ina wuni?"


Khalid ya kalleta murmushi yai sannan yace "ya gida?"


Tace lfy kalau, ga wannan.

Ta mika mai coke mai sanyi tace ga wannan kasha rana.


Kallanta yai sannan ya amsa, Zainab ta saki baki tana kallan ikon Allah sai jitai an rikota, juyawa tai ta kalli Adam wanda ya sa dariya yace "kwaro da alama kayi kasuwa."


Nusaiba ta rufe ido da sauri, ta juya ciki da gudu, har tafa dan bige Adam dake jikin kofar kadan.


Adam ya kara sa dariya, Zainab ce taja hannunsa suka shiga ciki.

Khalid ya juya ya fita.


Tasha ya wuce kawai ya hau mota ya tafi danbatta.


Bayan magrib ya isa, dukansu na zaune a waje suna cin tuwo sukaji sallama, da gudu su Amir suka tashi suka nufeshi suna cewa Yaya yaya


Khalid ya rungumesu sannan ya shigo ciki, Umma da Abba sunyi zuru suna kallanshi.

Asiya kam mikewa tai ta dauko plate ta ajiye, Khalid ya kalleta yace "yauwa kanwata nagode."


Umma ya gaida sannan ya gaida Abba ya tambayi jikinsa.


Abba ya kalleshi yace "meke faruwa?"


Khalid yace "kawai ina tashi naji gida nake so."


Asiya tasa dariya tace "sai kace dan boarding yaya."


Yace "dama inasan kaiki boarding da alama na kusa."


Dariya tai tace "boarding ina Ss2?"


Abba yace "ban gane ba? Yanzu kana tashi kawai ka taho?"


Yace "eh Abba naga hakan yafi sauki, nawa ma tafiyr take daga kano zuwa danbatta?"


Umma tace "to yanzu ci abinci kai sallah ka huta."

Ta kalli Abba tace "tunda yaga hakan yafi sauki sai ka barshi, sanda yaga bazai iya ba sai yaje can din."


Khalid yace "yauwa Umma."


Abba yai shiru bai kara cewa komai ba, Khalid ne ya zuge jakarsa ya ciro coke din nan yace "ga coke Abba."


Abba ya amsa yana cewa "to nagode."


Nan suka ci abinci, suna gamawa ya mike ya shiga daki.


*********


Fitarsa Sallar isha'i ya hangota a inda ya barta, meke damun yarinyar nan? Wai ba mutanene a unguwar da ba wanda zai taimaka mata?


Wucewa yazoyi tare da dauke kansa kamar bai ganta ba, ji yai ance "bawan Allah."


Gabansa ne ya fadi, ya juyo ya kalleta, tasowa tai daga inda take ta matso kusa dashi tace "ka taimakeni ka bani gun kwana dan Allah, jiya ruwan da akai tsakar dare a kaina ya kare, gashi ko ruwa ban samu nasha ba bare abinci."


Adam yai shiru yana kallanta, idanunta ya kalla duk ya jeme alamar wuya, yace "biyoni."

Nan tabi bayanshi da saurinta.


Shiru yai a bakin kofa gabansa na duka uku uku, cewa yai tsaya anan sannan ya shiga ciki, mai gadi ya kalla yace "Bala duba min ban dakinku ko kunbar fanfo a kunne, naji karar ruwa."


Cikin mamaki Bala yace "fanfo?"


Adam yace "eh duba."


Nan Bala yai hanyar bandaki, da sauri ya mata alama data shigo, ta shigo da sauri.


Adam ya nuna mata wani daki a can gefe, ta nufeshi da sauri.


Tana shiga Bala na fitowa yace "nikam banga komai ba."


Adam yace to kila ba nan gidan bane ya wuce.

Dakin ya shiga ya kunna fitila.


Tana tsaye, dayake dakin ba komai sai katifa katuwa dake kasa.


Adam ya kalleta yace "ki zauna anan zuwa dare zan ce ki shigo ciki."


Kallansa tai tace "zan iya zama? Karna ja wani abin ya faru."

Yace "karki damu zan kawomiki abinci, anjima zaki shiga ciki, ba dadi ne ban sanar asu ba su ganki."


Tace "nagode Allah ya saka da alkairi."

Fitowa yai ya wuce ciki.


Zainab na zaune a falo, Goggo na kan kujera daga gefe suna kallan sautin arewa wato inda Zainab ke aiki, gefe kuma Nusaiba ce da Nabila.


Zainab dake zaune tana cin abinci tna dan kallan tv din ta kalli Nusaiba tace "Wato harda daumin coke kiyi gwaninta dashi?"


Nabila tace "to da Aunty bakisan meta kinkimo zata kaimai ba."


Zainab tace me?


Abinci ta zuba a flask, ta sa coke tasa robar ruwa tasa apple a basket wai zata kaimai yai lunch.


Zainab batasan sanda tai dariy ba tace "sannu matarsa."


Nusaiba tace "Aunty dan Allah ku auramin shi."


Goggo tasa dariya tace "yaro yaro ne, wato wannan zamani ba kunya, wai yarinya ke cewa a mata aure."


Nusaiba zatai magana Adam ya shigo yana cewa "in kina sanshi tsaf zan aura miki shi."


Da sauri tace haba?


Zainab ta dan harareshi tace "karka tunzurata batasan gatse ba."


Tana gama cin abinci ta wuce daki, tana mikewa Goggo tasa cassette, Nabila tace "mu dai Goggo ki bari mu gama kallan shirin da ake."


Adam yai saurin mika ma Nabila remote yace "sa abinda kikeso."


Goggo ta kalleshi fuska a hade, yace "Goggo magana zamuyi." Yai maganar cikin rada.


Mikewa tai ta nufi daki, Nabila na cewa "Goggo fushi kikai?"


Adam yace "bari naje naji."


Nan yai ciki, suna shiga ya zauna kusa da ita yace "Goggo ya zanyi yrinyar tana dakin wajen can."


Kallansa tai galala tace "mene?"


Yace "baki ganta ba wlh duk ta rame."


Goggo tace "to meye damuwa ta?"


"Wai Goggo meyasa kike min haka? Taimakon rai zamuyi, dan Allah ki taimaka ma yarinyar nan.


Tace "naji amma kwana biyu, inta wuce kuma wlh duk abinda ya biyo baya kar ka sa dani."


Yace "ta ina ma zata wuce? Ai tana gamawa zan sallameta."


"Ynzu ya zakayi?"


Yace "idan wadancan rigimanmun sun kwanta zan shigo da ita tai wanka ta kwanta a dakinki, kinga ita da sassafe take fita, to inta dawo sai ince mata tazo."


Goggo ta tabe baki tace "wato kwakwalwarka bata tashi yin banban tunani sai kanasan abu."


Dariya yai yace "Yanzu zan kawo abinci na ajiye anan dakin karda daddare a gane in aka kamani ina zuba abinci."


Tace "can kai ka sani, nidai ka tabbatar randa zani bikin nan na yar kawata kai ka kaini a mota."


Yace "an gama Hajiya Goggo."


Fitowa tai ta dawo falo, shikuma ya wuce daki.


Zainab na ganinshi ta dan matsar da laptop din data kunna tana cewa "gobe kaduna zani."


Kaduna? Ya dada tare da zama kusa da ita, tace "eh wlh zamu presentation."


Ya kwantar da kansa akan cinyarta tasa hannunta acikin gashinsa tana cewa "ko zaka kaini?"


Idanu yadan zaro, yace eyee, dariya tadanyi tace "just joking, harna fadawa abokinka."


Sun danyi hira kafin ya fito falo, yana ganin yaran sun bar falo ya fita ya shigo da yarinyar da ko sunan ta bai sani ba.


Dakin Goggo yai da ita, sannan ya fita, Goggo na zaune a falo tana kallansa har suka wuce ciki, itadai sam hankalinta ya kasa kwanciya da wannan lamari, mikewa tai ta dau abincin da aka zuba tai daki.


Tana zaune a kasa, jikinta duk yai datti, Goggo ta kalleta sannan ta nuna mata toilet da kayan da ta fito dashi, ta juya ta fita.


Adam ya kalleta yace "kiyi wanka kici abinci ki kwanta mayi magana gobe."


Kai ta daga mai alamar to, sannan tace "nagode nagode...."


Hawaye suka zubo mata.


Adam ya juya ya fita....


***********


Tunda tai sallar asuba bata koma ba ta tsaya gyara slide din da zasuyi presenting.

Karfe bakwai ta mike tai mikar gajiya sannan tai wanka ta shirya, Adam na kwance nata sharar baci.


Kayanta ta kwasa ta fito, yana tsaye a waje sanda ta fito, murmushin da batasan dashi bane ya fito, tabbas tanasan mutum taga yasan aikinshi, lalai kasarmu tana cikin wani hali ace masu kwazo da san aiki sune wadanda basuda aikinyi.


Tana shiga yaja suka tafi, ba abinda wani yace a cikinsu har suka isa cikin station din, yana parking tace "yanzu zan fito."


Ba matsala


Abinda yace kenan ya fita.


Ciki ta shiga, tana shiga ta daure fuska sosai, sunyi meeting dinsu sun gama, nan wadanda zaku rakata suka shiga tasu motar sukai gaba akan sai sun hadu acan, dan sun san bata yawo da mutane a motarta.


Zainab na fitowa taji karar text a wayarta, kallan wayar tai ta bude, Wlh Zainab sai naga karshenki, yadda kika koran daga aiki shekara biyu kenan na rasa wani aikin, ni zan zama ajalinki wlh


Tana gama karantawa tai tsaki tare da wucewa ta shiga office dinta, printing dinsu tai sannan ta kara duduba komai ta fito waje.


Mota ta shiga suka dau hanya.


Tun da suka fara tafiya mota ke binsu a baya, Khalid ya kula da hakan sau dai da alama ita bata sani ba tana ta dube dube a tablet.


Daurewa yai yace "tare muke da wadancan?"


Juyawa tai ta kalli bayansu, sannan tace "a'a wadanda muke tare sun wucemu da kusan 20min."


Shiru yai yana kara kallan motar ta glass, kallansa tai tace "menene?"


"Bin mu suke."

Bin mu? Ta maimaita cikin tsoro, text din dazu ne ya fado mata.


Kallanta yai ta glass yace "kinsan su waye?"


Bakinta na rawa tace "a'a"


Tunowa da mai kukan jiya yai, kai ya girgiza da sauri yana cewa may be hanyarce daya.


Jitai yace "bari muyi kamar zamu siya abu muga."


Tace to


Kusa da masu sai da kwan zabi suka tsaya nakan hanya, Khalid ya juya baya, gani yai motar ta tsaya a bayansu kadan, yanzu kam yasan tabbas binsu akeyi, kurawa motar ido yai, maza ne a cikinta kusan guda biyar.


Kallanta yai itama kallansa take, yace "kin ma wasu laifi ne?"

Shiru tai hakan yasa yace "please ki fadamin insan ya zamuyi, ga meeting kina dashi ga wadanan, in muka tsaya biye musu zaki rasa abinda zaki je yi."


Wayarta ta ciro ta bude text din ta nuna mai, karantawa yai sannan yace "kinsan number?"


Tace "a'a amma daga alamun text din cikin mutanen dana kora ne."


Baisan sanda yai wani murmushi ba.


Fuska ta hade tace "meye?"


Yace " seat belt."


Sawa tai tana kallansa haryanzu so take taji murmushin rainin hankalincan na meye."


Ganin bashida niyyar magana yasa tace "tsoro kake?"


Batare da ya juyo ba yace "me nayi da zan tsorata? Mai laifi ai shine da tsoro."


Yana kaiwa nan ya fizgi mota da gudu.........


(Ai nikam jinai motata ta makale, ashe gudu sukai suka barni a baya......)


*Ayusher Muhd.*

[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀


Haske Writers Association💡


Shafi na Goma


Wattpad/@AyusherMohd.


*Excuse me a Zauren BieBie nake? Excuse me nan ne Zauren BieBie?....*

Lol kuna sani Dariya da sarar nan, wannan shafin naku ne duka wadanda ke left da wandanda ke right....One Love


*********


Kanta ne taji yana juyawa yanda yake gudu da motar, ga hanyar sam batada kyau kallansa tai tana san mai magana taga ya ja motar sun shiga wata kwana a Zaria.


Suna yin kwanar yai parking, ya fito daga motar ya rufe sannan ya dawo titi, sai a lokacin motarsu tazo da gudu suka wuce a tunaninsu sun wucesu ne.


Juyowa yai tare da ajiyar zuciya sannan yai dan murmushi dai kace me aikin security.


Karasawa yai jikin mota, ya bude sannan ya shiga juyowa yai ya kalleta, itama shi take kallo tace “fada kukai?”


Fada? Ya fada cikin mamaki sannan yace “ni da banda laifi akan me zanyi fada da wani?”


Fuska ta hade tace “da wa kake kenan?”


Baice komai ba sannan yasa key ya tada motar, idanta ne ya dan fito tace “in kuma basu tafi ba fa?”


Yace “sai muji me suke so.”


Haushi ya kamata batace komai ba, juya motar yai suka koma kan titi, suna fita daga cikin garin Zaria suka tadda motar nan a gefen titi, kallansa tai tace “sune?”


“Me kika musu ne haka?”

Shiru tai batace komai ba sai tsoron abinda zai faru fa take.


Khalid yana zuwa kusa dasu suka hau kan titi tare da nunamai yai parking.

Khalid ya kalleta yace “saura hour nawa?”

A hankali tace 2


Bude kofa yai ya fita, kusa dasu yaje yana neman mika musu hannu suyi musabaha, babba cikinsu ya buge hannunsa yace “matarcan zaka bamu.”

Cikin mamaki Khalid yace “wacc kenan?”


“Karfa ka raina mana hankali ta cikin motar can, ba Zainab Aliyu Tahir bace?”


Khalid ya kallesu yanzu kam ya gane aiki su akai basu mansan ta ba.


Murmushi yai yace “wai dama Zainab kuke nema?”


Eh, bamu ita.


Dariya yai yace “ba ita bace, yayarta ce wannan sunan ta Zarah, baku ganta bane? Zo ku duba ku gani.”


Cikin mamaki suka karasa jikin motar, wanda ganin an nufota yasa gaba daya hankalinta ya gama tashi.


Gani tai Khalid ya bude kofar wanda idanunta suka firfito shikenan ya zo ya bada ita, Adam, Nabila, rayuwata........


Muryar Khalid taji yace “kun ganta?”


Ido suka kura mata dayan ya kalli dayan cikin yaren nufe yake mai magana wai itace? Yace kamar ita kamar ba ita ba.


Khalid yai dariya yace “hala bakwa kallan program dinta ne amma da kuna gani zaku ganeta.”


Shiru sukai suna kara kallanta, Zarah wai sun dauka Zainab ce ke?


Zarah? Me mutumin nan ke shirin yi? Ta fada a ranta cikin mamaki, murmushi yai yace “mun biya ta tv station ne saboda zamu koma kaduna inda muke da zama.”


Shiru sukai suna kara kallan Zainab.


Khalid ya rufe kofar sannan ya kallesu yace “amma me yayarta ta muku?”


Ba mutawa ba aiko mu akai, kasan inda take? Suka fada suna kara kallan pic din da aka turo musu, amma itafa ance yau zata kaduna sannan ya akai kuka hau motar da aka nuna mana tata?”


Khalid yai dariya yace “ita ga wuce da ragowar staff din, saboda tana sauri dan 10 zasuyi meeting din, da tare zamu taho to mu bamu shirya ba.”


Yanzu kam sun dan yarda dan dama hoton ba yanzu tayi shi ba.


Khalid yace “kuyi hakuri dan Allah karku ma yayarta komai, bansan meya faru daku ba.........”

Malam karka soma mana wa’azi whve ka bamu gu, neman halak dinmu muke.


Khalid ya shiga mota yaja ya bar gun.


Zainab ta kalleshi tace “me ya faru? Naga sun barmu mun wuce.”


Shiru yai kafin yace “ i just trick them hope bazasu gane ba har mu isa.”


Ajiyar zuciya tai sannan ta sauke window dinta tare fa shan iska, shiru tai tana tunanin wanda ya aiko a kamata a cikin mutane sama da 8 data kora daga gun aiki daga sanda ta fara zuwa yanzu.


Shiru tai tana tunanin ya akai yasan gana program? Sannan ya akai yasan basu ganeta ba? Ya akai yasan bazasu fahimci ita din bace?


Tadan kuramai ido tana tunanin lamarin.


Kauda kai tai a hankali tace “Thank You.”


kallanta ya danyi ta glass amma baice komai ba, yana tunanin me tama mutane haka?


************


Kusa da Goggo ya zauna a falo cikin rada yace “tana ina Goggo?


Harara ta makamai tace “aika fini sanin inda take.”


Mikewa yai ya nufi dakin goggo, Nabila ta dago ta kalleshi amma bata kawo komai ba.


Kofar dakin ya tura, a hankali saboda yana tsoron kar ya kwankwasa su Nabila dake falo suyi tunanin wani abin.


Tana kwance a kasan katifa daure da zani sai dai zani ya sauko kadan wanda hakan yadan bayyana saman kirjinta, da sauri ya juya baya, sannan ya juya zai fita.


Jiyai ance waye? Ta fada tare da saurin jan bargo ta luluba.


Yace “yahkuri bansan bacci kike ba.”


Ya Adam? Ta fada cikin alamar tambaya, juyowa yai da sauri yace “ya akai kikasan sunana?kin sanni ne?”


Kai ta girgiza da sauri tace “a’a jiya a gun Goggo naji tace “Adamu.”


Ajiyar zuciya yai sannan yace “dama fada miki zanyi daga yau zamanki a gidan nan sunanki Sadiya,sannan gobe zakiji ki gama registration dinki daga nan sai ki koma gida.”


Nagode amma me yasa zan boye sunana?


Yace “matar gidan batasan kina nan ba sannan ba dadi taga na kawoki bayan ban sanki ba.”


A hankali tace “kayi hakuri, sannan nagode Allah ya saka.”


Murmushi yi sannan yace an jima zansa ki fito a matsayin zuwanki kenan ku gaisa da mutan gidan.”


Kai ta daga alamar fahimta, zan shigo miki da abinci, da sauri tace nagode.


Murmushi ya sake yi sannan ya juya ya fita.


Yana isowa falan Goggo tamai wani kallo sannan tace “samin kati a waya ina san kiran mai dinki.”


Ba musu yace to.


Nabila tasa dariya tace “yau basa banba, Uncle baice wai Goggo meyasa katinki ke saurin karewa? Tai maganar cikin kwaikwayon sa.


Dariyar borin kunya yai yace haka nakeyi?

Nusaiba tace “sosai ma.”


Suka sa dariya, Goggo ta kalleshi cikin jin haushi.


********


Sun gama meeting komai ya tafi yanda take so, suna gama sa hannu aka kawo musu abinci, kallan mai ajiye musu abincin tai tace “dan kaima driver na yana waje.”


Okay tace tana gamawa ajiye musu ta dauko take away din da juice ta fito waje, ganin batasan motar ba yasa ta koma ta sanar mata batasan waye ba.


Zainab ta amsa ta fito dashi.


Yana zaune cikin mota yana karanta wani littafi a hanunsa, mikamai tai yana amsa ta juya ciki.


Cikin mamaki ya kalleta yau me ya sameta.


“Ex....Ina magana.”

Baisan dame zai kirata ba.


Hartayi gaba ta juyo ya nuna mata alamar na meye? Tace “an ba kowa ne kaine ba’a gani ba.”

Ta fada ta juya ta koma.


Sai kara jinjina ma Zainab sukeyi, suna kara nuna mata jin dadinsu nayin aikin da ita, daya daga cikin directors din yace “yanda kike workaholic din nan ha mijinki yake?”


Murmushi kawai tai bata ce komai ba, dan duk yanda take da mutum indai aiki ne ya hadasu batasan harkar rayuwarta ya shigo ciki.


Shima jin tayi shiru yasa bai sake cewa komai ba sai suka sako wani hirar.....


*Ayusher Muhd*

[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀


Haske Writers Association💡


Shafi na Goma Sha Daya


Wattpad/@AyusherMohd.


  Su Nabila na shiga daki Adam ya mike da gudu yai dakin Goggo, haushi ya turnuketa ta bishi da wata harara ta kaici tare da cewa "meye hakan?"


Adam ya mata nuni da daki sannan ya ruga, kai ta girgiza tare da jan tsaki na takaici, kwankwasa mata yai a hankali, sannan ya tura, riga take sawa da sauri ya koma ya maida kofar ya rufe yana cewa ni bana tashi zuwa sai tana wani abin?


Karasa sa rigar tai ta bude kofar tana kallanshi fuskarta dauke da murmushi.

Kallanta yai yace "hakuri na bude kina shiryawa."


Tace "bakomai ai masan ba da saninka bane."


Yace "ki dauko jakarki ki fito a matsayin yanzu kika zo."


To tace ta juya da sauri ta dauko jakarta ta fito a gaba ya sata har zuwa falo, har kasa ta tsuguna ta gaida Goggo, Goggo ta kalleta tace "ni kin tabbatar sace miki jaka akai?"


Kallan mamaki tama Goggo sannan ta kalli Adam, da sauri yace "Goggo wai meyasa kike haka ne? Bana fada miki ba?"


Share hawayenta tai tace "kiyi hakuri."


Goggo ta kalleta a haka dai gata mutum sai dai itafa tana mamaki ace kaf garin nan ba wanda ya tausaya mata ba kuma wan.........."


Adam ne yace "Goggo ki sake da ita kar Zainab ta gane wani abin."

Goggo ta maida kanta kan Tv harta fara kallo ta mike ta shiga kitchen ta dauko juice ta zauna tana sha tana kallanta.


Da Adam da mai suna Sadiya wacce ko sunanta na asali bamu sani ba sukai shiru.


Can Adam yace zauna.

Zamanta ta gyara sannan ya kwallawa Nabila kira itada Nusaiba.


Fitowa sukai gaba daya fuskarsu a hade.


Adam yace "Rigimanmun mu ya akai?"


Nusaiba ta turo baki tace "Dady yace gobe zai turo a daukemi."


Wani dadi ne y kama Goggo da Adam, wanda har Goggo bata san sanda tace "masha Allah hakan yayi dai dai."


Nabila ta kalleta tace "Goggo ai ba sai kin nuna murnarki a fili ba mun san dama dadi zakiji."


Goggo ta sa dariya tare da wayancewa tace "ba haka bane, ai zamanku a gidan yafimin dadi, ni da da nake zama ni kadai in Adamu ya fita? Yanzu kuwa kuna nan muna shan hirar mu?"


Nabila dai bata ce komai ba, sai yanzu suka kula da budurwar dake zaune a kasa.


Nabila cikin mamakin tace "wannan kuma fa?"


Adam ya sa dariya yace "Sadiya ce yau tazo daga Kura."


Sadiya? Suka tambaya a tare


Da sauri ya kalli Goggo yana mata nuni datai magana.


Goggo tace "baku san Sadiya ba? Kanwar Adam ce ai mahaifinsu daya."


Kallan Goggo yai cikin mamaki, tace "Sadiya ga kannan Zainab ku gaisa."


Nusaiba ta kalleta tace "amma kinfi Uncle kyau kuma bakwa kama, da alama ke mamanki kikayo."


Murmushi tai, Nabila kam kallanta kawai take amma batace komai ba.


Kallan Goggo tai tace "yau da wake zan dafa wlh."


Goggo tace "da dai ni kike dan kinsan bansan da wake."


Nabila tana dariya tace "sai kisa miya akwai ragowar ta jiya.


Tana yin kitchen Nusaiba ta bita.


Suna shiga Adam ya kalli Goggo yace "Goggo wani mahaifinmu daya?"


Tace "to kana san nace mahaifinka da mahaifiyarta daya bayan bakwa ko yanayi? Sannan in tsautsayi ya kawo Sadiya nan kusa fa?"


Sadiya tazo  nan tai me?


Haka dai ka iya ko kunya ma bakaji, sau nawa tana ce ma zakato kana hanata?


"To wai tazo tai me? Ni kinsan bansan takura."


Goggo tace "can kai ka sani, baka dauki na jininka ba gashi kana kinkimo da titi ai."


Sadiya tai kasa dakai, Adam ya kalli Goggo yace "wai Goggo meyasa kike haka ne?"


Goggo ta dauke kai tana shan juice dinta ta cigaba da kallanta.


Adam sai kokarin jan Sadiya da hira yake dan ta saki jikinta.


************


Bayanta tadan buga saboda ciwon da yake mata, sannan ta mike ta musu sallama, nan kowa ya shiga jinjina mata suka fito ita da staff din da sukazo tare.


Tana saukowa daga kan matatakalar da waje waya ta shigo wayarta, bata dauka ba saboda tana kara yin sallama dasu, suna karasa saukowa ya rage daga ita sai staff dinta ne, babban ya kalleta yace "Hajiya kinyi ba karya wlh."


Murmushi tai tace "sannunku da aiki kuma, thanks to you komai ya tafi normal."


Nan suka yi murmushin jin dadi.


Inda motarta take suka nufa, bakowa a motar hakan yasa ta dan wawaiga, sannan tace "kuje ku hau hanya, maybe ya dan fita ne."


Ah Hajiya bari mu jira ki fara tafiya.


Hira suka dan cigaba dayi jefi jefi take sa musu baki saboda bata fiya san yin hira fa na kasa da ita ba.


Khalid ne ya hangosu daga nesa hakan yasa ya kara hanzari dan isowa, yana karasowa yace "kuyi hakuri nadan je Massalaci ne."


Kallansa tai cikin mamaki, yau meke kanshi harda bada hakuri?


Zatai magana wayarta ta sake kara, nan ta dau wayar sai kuma ta kalli Khalid.


Kallanta yai cikin mamaki, sannan ya kalli wayar hannunta wanda baya iya gani.


Hello, ta fada tare da dan matsawa daga gun su.


"Hajiya Zainab! Wato kin gudu ko?"


Gabanta ne ya fadi tace "wanene?"


Wata muguwar dariya ya saki yace "wanene? Tambaya ma kike?"


Juyowa tai ta kalli Khalid, ganin haka yasa ya matsa kusa da ita, daurewa tai tace "mekake nema da ni ne? Koma wanene in dai har ya sanni na tabbatar yasan bana tsayawa maganar da batada amfani a waya, in kana da abin cewa ka tareni ka fadamin."


Tana kaiwa nan ta kashe wayarta tare da kallansa.

Are you akay?

Abinda yace mata kenan ta daga kai alamar eh, hannu ya mika mata yace muga number.


Mikamai wayar tai ya karanta number sannan ya mika mata sawa yai a wayarsa sannan yace "ko zakibi wadancan ku wuce?"


Cikin mamaki tace "why? Ni bana shiga motar da ba tawa ba."


Yace " i think suna nan kar su kara biyo mu, sannan in mun samu mun wuce dazu yanzo ba abinda zamuce musu da zai sa su yarda."


Shiru tai kafin ta daure tace kai fa?


Zan taho.


Abinda yace mata kenan yai shiru, ganin hkan ne mafita yasa ta nufi gun staff din ta sanar dash zata bisu mamaki ne ya kamasu, duk da ba haka suka so ba dan sun san har su isa kuma bazasu sake ba.


Harta bude mota zata shiga ta juyo ta kalli inda yake, in suka kamashi saboda ita fa?


Anya hakan shine daidai?

Karta ja mai bayan bai san hawa ba baisan sauka ba.


Kayanta ta ajiye a motar sannan ta dawo yana kokarin shiga motar,cikin mamaki ya kalleta.

Tace "ba haka kawai nake korarsu ba, duk wanda na kora yayi abinda bai dace bane, wannan muryarsa tamin kama data Dauda wanda na kora shekara biyu da suka wuce, kamashi nai yana neman lalata yarinyar da tazo neman aiki."


Tana kaiwa nan ta juya harta isa bata juyo ba ta shige motar suka ja suka tafi.


Shiru yai a gun kafin shima a ya shiga.


Sai wajen karfe shida suka isa garin Kano, gidsnta tace a wuce da ita, nan ta nuna musu suka ajiyeta, tana sauka sukai ajiyar zuciya a tare, sannan suka sa dariya.


Ahhh so awkward.


********


Bala ne ya bude mata kallan sa tai bayan sun gaisa tace "Yana hanya, zai karaso."


To Hajiya dama na ganki ne a wata motar."


Murmushi tai dan yanda ya kalleta dama tasan me yake nufi.


Ciki ta shiga, Nabila da Nusaiba ne sai wata a falan.


Mamaki me ya kamasu ganinta ta shigo, Nusaiba ta leka ta window da sauri, ganin ba mota yasa ta kalli Auntyn tata tace "Aunty ya haka?"


Jakarta ta mika mata ta amsa Nabila ta amshi ragowar kayan hannunta, tana cema Nusaiba wato ke in zan fita ko in zan dawo ba mi kike nema ba ko?


Dariya tai tace "ai ke Aunty tawa ce shi kuma, wanda zan aura ne"


Nabila tasa dariya tace " a ina zai aureki bayan baimasan kina yi ba?"


Zainab ta karasa ciki, turus ta tsaya tana kallan abinda ta gani a falan ta, Nabila ta kalla wacce tai saurin cewa "Sadiya ce kanwar su Uncle."


Zainab ta kara kallanta, kasa tai dakai tare da saurin cewa "Aunty Ina wuni?"


Zainab cikin mamaki tace "Sadiya?"


Tace eh nice.


Zainab tai shiru tana kallanta kafin tace "ya kura?"


Sadiya ta kalleta tace "lfy kalau."


Zainab ta kara kallanta anya ita ta gani a bikinta?


Nabila ce ta kalleta tace "Aunty Menene?"


Ciki ta shiga tana duba agoggo tare da cewa "ina Adam?"


  Ya kai Goggo gun mai dinki.


Shiru tai tare da kallan agoggo, gata batada numbershi balle taji halin da suke ciki.


Sadiya ta kara kalla tace "sai naga kamar kin rame."


"Na danyi rashin lafiya ne shiyasa."


Kai ta jinjina alamar fahimta sannan ta dau wayarta ta kira Adam.


Yana ganin kiranta ya gyara murya yace "Honey."


Tace "Honey kun kusa gamawa?"


Yace "yanzu muka iso, kinga Sadiya?"


Tace "Eh na ganta, ka kira Abokinka kaji yana ina?"


Ba tare kuka dawo ba?


Eh ka kirashi in kaji ka fadamin.


To ya ce ta kashe wayar, Nusaiba ta matso da sauri tace "ina Uncle din nawa yaje?"


Wani uncle din naki kike nufi?

Dariya tai tace "to yayana?"


Zainab ta girgiza kai kawai, kallan Sadiya tai wacce tai kasa da kanta.


Taci abinci?


Nabila tace "eh."


Zainab tai ciki, Nabila tabi bayanta.


Juyowa tai tace "lafiya?"


Nabila tace "Aunty kin tabbatar kanwar Uncle ce?"


Zainab cikin mamaki ta kalleta tace " me kike san cewa?"


Nabila tace "kawai na gane basa wani hira."


Zainab tasa dariya tace "kinada matsala Nabila, to in ba kanwarsa bace wacece? Me kika dauki Adam?"


Dariya tai tace "shirman nawa fa?"


Zainab tace "da alama kam, ki cire abin nan a ranki kiyi rayuwarki yanda ya kamata."


Kai ta jinjina sannan tace "Dady yace gobe zamu wuce"


Zainab tace "hutu ya kusa karewa ko?"


Nabila tace eh.


Murmushi sukai a tare Nabila, Zainab tace "a hakan ma na gode, dan in baku zo ba banaji zan dinga ganinki."


Nabila ta matso ta rungume ta, Zainab tai murmushi mai tattare da ma'anoni kala kala.


*Ayusher*

[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀


Haske Writers Association💡


Shafi na Goma Sha Biyu


Wattpad/@AyusherMohd.


  Tana tsaye a dakinta rike da wayarta, tana duba agoggo, anya ta zauna anan bayan abinda yake kokarin faruwa a dalilinta ne?


Sadiya na zaune a falo duk motsin datai idan Nabila akanta, wanda har ta daure tace "Lafiya?"


Nabila tace "lafiya kalau tunani nakeyi."


Sadiya ta dauke kai, yanda tai da kanta ne yasa Nabila ta kalleta har zatai magana sai ta fasa, jin an bude gate ne yasa Zainab ta fito daga dakinta.


Muryar Nusaiba taji tace "ashe Uncle ne."


Nabila tace wani uncle din tunda ke Uncle din naki biyu ne?

Nusaiba ta harareta tare da juyawa ta dawo ta zauna.

Nabila tasa dariya tace "Uncle din Aunty ne kenan, da dayan ne da munga fuskarki tafi haka."


Zainab kam Adam na shigowa bakin kofa tace "Honey dan zo."


Gabansa ne ya fadi, gaban Goggo ma ya fadi, a tare suka kalli Sadiya wacce ke zaune yanda suka barta, kallan Goggo yai wacce ta bugamai kallo ta mai alama da ka gani ko?


Adam ya kalleta yace "inzo?"


Tace "eh"


Sadiya ya kara kallo sannan ya nufi daki, a tsaye take hankalinta a tshe, a bakin kofa ya tsaya tace "shigo mana."


Gabansa na faduwa ya maida kofar sannan ya kalleta yace "lafiya?"


Yi maganar cikinsanhin jiki, kallansa tai tace "meya cema? Yana ina?"


Ajiyar zuciya yai yace "na kira bai dauka ba, amma wai lafiya?"


Tace "sake kira."


Kallanta yai sannan ya hau kiran Khalid, sai data katse ya sake kira sannan Khalid ya daga.


Alama ya mata da an daga sannan yace "Khalid kana ina ne haka? Zai......"


Hannunta ga harde tamai alamar X kenan karya fada, Khalid daga can yace " yanzu zan karaso, ina kan babban layi."


Adam ya kashe tare da kallanta yace "yana hanya, wai meke faruwa ne?"


Kallansa tai kamar zata fadamai sai kuma tai shiru, tace bakomai.


Shiru tai tana kallanshi a ranta tana cewa "honey am sorry, banso kaima ka shiga fargabar da nake ciki, in na san abinda ke faruwa na sanar maka."


  Menene?


Murmushi tai tace "Honey sai naga Sadiya?"

Yace "eh wlh dazu kin fita sai gata, kinsan ta dade tana damuna akan tana san zuwa."


Zainab tace ta kyauta, dama su Nabila zasu tafi gobe da safe sai ta koma dakinsu."


Da sauri yace "ai itama jibi zata tafi, ta zauna agun Goggo."


Fuskarta dauke da mamaki tace "jibi kuma?"


Yace "eh makaranta ta samu anan Northwest ne ko Buk? Shine tazo registration."


Hannu tasa tadan bigi kafadarsa cikin wasa tace "ko kunya wai kake cewa ko nan ko nan, gobe zata registration din kenan?"


Yana dariya yace "eh."


Tace "kuje tare zan turo ma kudi, ka tambayeta nawane kudin."


Kallanta yai cikin jin dadi sannan ya jawota jikinsa yace "Honey na gode sosai."


Murmushi tai tace "Kanwarka ce, da ita da su Nabila daya suke."


Dan huce yai kadan sannan yace "nagode Honey."


Dagowa tai t kalleshi sannan tace " naga bata saki jiki ba, ko dan farkon zuwanta ne?"


Yace "ai dama ita magana bata dameta ba sosai."


Tace "wa?" Sadiyan taka da kake cewa tana damunka da tsinaniyar magana?"


Wata dariya yasa sannan yace "Sadiya kam akwai surutu kila dan bata taba zuwa bane"


Jin karar bude gate ne yasa ta fito daga dakin, Adam ya biyota.


Goggo ce ta kalleshi da sauri dan tana zaune a falo ko kayanta data anso bata je ta ajiye ba data anso.


Ganin yanda ya fito fuska a sake ne yasa tasan ba abinda ya faru, nan ta mike ta nufi daki.


Sadiya Adam ya kalla yace "Sadiya kiyi godiya Auntynki ta biya miki kudin makaranta."


Sadiya ta kalleta tace "Aunty nagode Allah ya saka da alkairi......." hawaye ne suka zubo mata, Zainab zatai magana Nusaiba tai tsale tace "My yaya ya dawo."


Zainab ce ta wuce waje, Adam ya kalleta kawai sannan ya kalli Sadiya dake hawaye ya xauna akan kujerar dake kusa da ita yace "kukan na meye?"


Kallansa tai tana share hawaye tace "na rasa me zance ne."


Murmushi yai yace "to kinyi ya isa haka nan, kai ta daga alamar to.


Duk maganar a hankali yakeyi, dan dama Nabila bata falan yanzu da alama ta shiga daki, ita kuma Nusaiba na jikin window tana kallan Khalid.


Zainab ce ta fito ya rufe motar kenan ya goya jakarsa, juyowar da zaiyi taga gefen bakinshi na jini.


Idanu ta zaro hankali a tashe ta matsa tace "lafiya?"


Kallanta yai,tace "su sukama?"


"No ba wani abun, zan wuce sai gobe da safe in Allah ya kaimu."


Ya mata sallama yana neman wucewa, da sauri tace "meyasa suka dakika bayan ba kaine da kaifi ba?"


Baisan sanda ya juyo ba, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa har ya juya kuma sai ya kara juyowa yace "Ko am sake kiranki karki daga, inso samune ma kiyi blocking din number."


Batace komai ba, sannan yadan murmusa kadan yace "sannan ba dukana akai ba, sai da safe."


Ya fita, yana tafe yana cewa wai ka bari aka dakeka sai kace wani yaro, shiru yai yana tuno abinda ya faru.


Ko garin Zaria bai kai ba ya fahimci suna binshi a baya, hakan yasa ya gangara gefen titi yai parking din motarsa, suka karaso sukai parking kusa dashi.


Fitowa sukai suka zagayeshi ganin ba kowa a motar yasa ransu ya baci.


Babba ne ya kalli Khalid yace "ina take?"


Khalid yace "wa kenan?"


Cikin masifa yace " ina take?"


Khalid yace "wanda ya turoku bai fada muku ba a wannan motar ta taho ba?"


Wannan kalma ta hasala su hakan yasa bai an kara ba yaji an makeshi wanda yasa shi ya fadi, har gefen bakinsa ya fashe.


Dagowa yai rai a bace yace "me kenan?" Wnda ya nausheshin yace "kana tunanin tsoranka mukeyi?"


khalid ya goge gefen bakinsa sannan ya make wanda ya bugeshin, shima gefen bakinsa ya fashe, hannunsa dayamai zafi gun naushin yadan yarfe sannan ya kallesu yace " na kira police na tabbatar sun kusa isowa yanzu, in munje police station ma karasa maganar acan."


Jin zancen police ne ya sa suka kalli hanya da sauri, babban yace "mu zaka rainawa hankali?"


Khalid yai murmushi yace "dan Allah kar ku tafi, dan nafiso muje police station din a dau mataki akan ku."


Cikin yaran nupe dayan ya fara mai magana, anya ma tsaya? In aka kamamu fa an kama

Banza?"


Khalid ya kalli Ogan yace "bani wanda ya aikoku a waya muyi magana dan daga yanda wayarka ke kara tun dazj nasan shine"


Ogan ya kalli Khalid sannan ya zaro wayar yana neman dagawa Khalid ya warce.


Dayake jin ogan yai sanyi yasa bai kwace ba, sai leka titi suke.


Khalid ya daga wayar yana ji akace "kun biya bukatar taku? Na fada muku ai xsku sha romo gans kudi ga na can ciki."


  Khalid yayi mamakin jin wannan kalamai, yace "ohhhh am really sorry amma abinda kake neman yiwa matar aure bazai taba faruwa ba."


Jin haka ne yasa yace "waye kai?"


Khalid yace "wanda yasan daraja da mutuncin mace!"


Waye kai? Uban waye kai?"


"Ka shirya zuwa police station dan yanzu za'a tafi da yaranka, kaga lalatar daka nemi yiwa yarinya sai ya bayyana a idan duniya."


Hankalinsa ya tashi, wanda Khalid ya mikawa Ogan wayar da gudu suka shige mota suka arta a guje.


Ran Khalid ya baci dayaga haryanzu ba alamun yan sandan daya kira, idanu ya rufe tare da yin karamin ajiyar zuciya, nigeria kasata abinda ya fada a fili kenan tare da murmusawa, yanzu da itace aka kama har a gama lahanta mata rayuwa ba wanda zaizo cetanta.


Ransa ba karamin baci yai ba ganin ya dade a gun yan sandan basuzo ba yasa ya juya ya bar gun.


Yana tafe kalaman mutumin nan namai yawo, wani irin rashin imanine wannan? Kai laifi dan an hukuntaka sai ka nemi hanya mafi muni kace dashi zaka rama.


  Wayarsa ce  ta hau kara wanda ya dawo dashi daga tunanin dayai, ganin Adam ne yasa ya daga dan dama so yake ya kirashi.


Adam yace "Khalid ka wuce ne?"


Yace "yanzu zan hau mota naga magrib tayi."


Adam ya kalli Zainab da ta wasie tana dadana tablet dinta yace "ka dawo ka kwana anan dan Allah kaga dare yayi."


Khalid yace "karka damu yanzun nan zakaga na isa gida."


Adam yace "yau dai kadai yanda kasha doguwar tafiyar nan ka zo ka kwana anan."


Yace "to zan wuce gidan kawuna na kwana acan."


Adam yace "shikenan."


Har zasuyi sallama yace "Adam."


Adam yace "naam"


Yadanyi shiru saboda baisan yanda zaiyi yace mai karyabar matarsa ta dinga fita ita kadai ba, daurewa yai yace "ai kun shiga gida kenan ko?"


Dariya tambayar taba Adam yace "eh."


Khalid yace "to shikenan sai da safe."


Nan sukai sallama ya dan sosa kansa na jin haushin yanda yai tambayar.


********


Kallan Zainab Adam yai yace "yace a'a"


Tace "me?"


Yace "kikace wannan abokin naka ya kwana anan mana tunda tafiya mukai doguwa."


Ta sa dariya tace "wai dan nace haka ne ka kirashi? Tab lalai Honey kaima."


Tana kaiwa nan ta mike ta shiga toilet.


Tana rufe kofar tace dan an tausaya ma shine zaka wulakanta mutane? Kai ta tafiya din kafi ruwa gudu.....


Harya kwanta yaji kishir ruwa ta dameshi, mikewa yai ya fito a hankali ya nufi kitchen.


Ruwa ya dauko a fridge ya fara sha, daga gefe yaji kamar a na nufo kitchen din, da yake fitilar wayarsa ya kunna kawai ya haske wanda ke tahowa.


Sanye take da vest dinta sai zani data daura, ganin shigarta ne yasa yai saurin sauke fitilar tare da maida fridge din ya rufe.


Nabila dan haskamin hanys zan fadi dan Allah.


Abinda ta fada kenan cikin sanyin murya.


Adam ya haska mata hanya sai dai bai san sanda yake kara kallanta ba, harta karaso.


Kusa dashi ta tsaya wanda hakan yasa ya haska kansa yace "nine ba nabila ba."


Tace "Yaya baka kwanta ba?"


Yace "na kwanta ruwa naji ina san sha na taso."


Amma ki dinga sa hijab in zaki fito, ko bakiga da maza a gidan ba?


Ta kallesh tace "kai kadaine a gidan yaya, sannan bansan zan ganka ba, ga zafi nakeji, na kuma san kai ba masu halin banza bane."


Murmushi yai yace "hakane."


Sha ruwan zan tafi na kwanta.


Tace to nan ga fara shan ruwa, a zabure tai tsale ta matsa inda yake ta kankameshi kam jikinta na kyarma.


Hankalinsa a tashe yace "Sadiya Sadiya menene?"


Kyarma jikinta kawai yakeyi gashi ta matseshi tsam, da kyar ya banbareta yana jijigata, har yana neman kunna wuta ne yasa ta farfado.


A tsorace yace "lafiya?"


Tace "abu nai?"


Yace "eh yanzu kika kankameni."


Hawaye ne suka shiga zubo mata wanda tausayinta ya kara rufemai zuciyaaaaaaa



☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘

[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀


Haske Writers Association💡


Shafi na Goma Sha Uku


Wattpad/@AyusherMohd.


*Jinjina Gaisuwa tare da Fatan Alkairi a Duk Inda Kuke Billy Galadanci da BillynAbdul....May Allah Always Help and Bless You🥰🥰🥰🥰Much Love*


  Cikin mamaki Adam ya kalleta yanda take hawaye ne ya bashi tausayi, yace "Sadiya?"


Hawayenta ta share tace "Yaya bansan meke damuna ba wannan larura tawa ni kaina na kasa ganeta."


Larura?


Ta kalleshi, zatai magana kenan sukaji alamun bude kofa, da sauri ta ja hannunshi suka bar kitchen din. Store ta turashi, sannan ta shiga tare da barin kofar a bude kadan tana lekawa.

Kuna wutar falan da akai ne yasa ta fahimci wacece, matsowa yai yace " wacece?"


Nunamai Nabila dake kale kalan falan tai, yace "to me muke anan? Laifin me mukai muke boyewa?"


Nabila ta kalla wacce ta shiga kitchen nan ma taga ba kowa, tabbas taji alamun magana tana bacci, ganin bakowa ne yasa ta koma daki, tana rufewa Adam ya kalli Sadiya wacce tace "yaya yahkuri ina tsoron me zatace ne in ta ganmu muna magana tsakar dare mu biyu."


Yace "ni dake a matsayin jini daya muke ko kin manta ne?"


Kanta ta saukar kasa tace "na manta yaya, yahkuri."


Murmushi yai yace "bakomai, jeki kwanta dare yayi sosai."


Kai ta daga alamar to sannan ta juya ta fita, tana fita ya fito ya nufi kitchen ya hau kwankwadar ruwa sannan ya juya ya shige daki ya kwanta.


Sadiya kam a hankali ta shiga dakin, Goggo nata jan uban munsharin bacci, ta kwanta a inda take kwanciya wato kasa.


Shiru tai tana tunani, kafin bacci ya dauketa.


Kamar yanda ta saba karfe bakwai ta gama shiryawa, Adam dake kwance yana bacci ta kalla sannan ta sunkuyo ta sumbaci kuncinsa, bargon ta gyaramai sannan ta dau kayanta ta fito daga dakin.


Sadiya ta gani tana ta wanke wanke tare da gyare gyare a kitchen.


Cikin mamaki tace "Sadiya me kike haka da safen nan?"


Nan ta tsugunna har kasa ta gaisheta, Zainab ta amsa tace "amma ke da zaki kwanta ki huta me kike a nan?"


Murmushi tai tace "Auntu kawai sai na hau kwanciya? Gwara dai na taimaka da wani abin."


Zainab ta fara hada tea dinta tana cewa "da sai ki bari in an tashi amma ba da sassafe haka ba."


Sadiya tai kasa dakai alamar kunya, Zainab cikin jin dadi tace "nagode."


Sadiya tace nice da godiya Aunty.

Zainab ta dau tea dinta ta fita.


A waje ta ganshi yana goge motar, karasawa tai gun, ganin bai ganta ba yasa ta danyi motsi da kafarta.


Khalid ya juyo ya kalleta tare da cewa "oh bansan kin fito ba."


Inda aka bigeshi jiya ta kalla sannan tace "hannuna."

Da sauri ya bude motar sannan ta sasu a ciki, shiga tai ciki ta zauna, sannan ya shiga shima.


Harya tada mota sai ji tai ance "Ina kwana?"


Mamaki ne ya kamata wanda har saida tace "dani kake?"


Baice komai ba ya fita da motar, kallansa tai sannan tace "daga jiya zuwa yau ka canza yanayin da kake kallo na ne?"


Cikin mamaki yace "name kenan?"


Tace "gaisuwar ta mecece? Ko dan abinda ya faru jiya yasa ka fara daukata abar tausayi?"


Jiyai baisan me ma zai ce mata ba hakan yasa yai shiru bai ce komai ba, dauke kai itama tai ta cigaba da dube dubem takardarta.


Yana san yaji ko number ta sake kiranta amma baisan ta yanda zaice ba, hakan yasashi yai shiru, dan jiya baccin dayai kalilan ne, yana ta mamakin wannan lamari, wato dan ankori mai laifi sai ya nemi lalata ma matar aure rayuwa saboda kawai cikar burinsa na daukan fansa? Lalai bata san me mugun nan ya shirya a kanta ba da........"


Jin wayarta na kara ne yasa ya kalleta ta glass din mota, jiyai tace "Nabila!"


Hakan yasa ya maida kansa titi, daga can Nabila tace "wai Aunty harkin tafi?"

Tace "eh da wani abin ne?"


Cikin shagwaba Nabila tace "yaufa zamu tafi."


Oh my Gosh!


Abinda ta fada kenan sannan tacigaba " wajen nawane?"


Tace "bansani ba wlh amma nasan bai wuce rana."


Zainab tace "ba matsala zan dawo lokacin lunch sai muyi sallama na koma."


Nabila tace "okay in naga an kusa lunch da kaina zan kiraki, nasan inkika shiga aiki mantawa zakiyi."


Zainab tai dariya sannan tace "to ki tabbatar kin kira."

Nan sukai sallama ta kashe wayar, harta danyi shiru sai tace "wajen 12:30 zaka dan maidani gida."


Okay!

Abinda yace kenan, shiru tai, har suka isa.


Suna isa ta fita tai ciki, juyawa yai da motar ya nufi police station, duk da dai yasan a banza zashi amma yana fatan y hadu da nagari.


Bayan ya shiga ciki ne ya sanar da su wata number yake so su bincika suga na wanene, officer din ya tambayeshi number wacece? Matarka ce ko mamanka? Ko kuma Yayarka ko kanwarka?


Kallansa yai yace "kanwatace."


Yace "wanene ke kiranta?"


Khalid ya kalleshi cikin jin haushin tambayar ya kai da aka fadama ana san ka taimaka ka nemi me number zaka tambaya wai number waye?


Ganin yanda Khalid ya ke kallansa ne yasa yace "oh ashe fa haka kace ko?"


Ran Khalid ya fara baci, daurewa yai yace "eh ga number."


Sai da ya gama karantawa sannan yace " yauwa meye sunansa ma? Sannan a ina zamu nemeshi?"


Khalid ya kalleshi yace "barshi kawai, dan da alama ba a nan ka dace ba."


Ya juya a kufule ya bar gun, Officer ya bishi da zage yana cewa a gidan uwarka na dace? Dan************


Khalid ya shiga mota rai a bace yaja ya bar gun, waya ya daga ya kira Salmanu, daga can ya daga yace "Khalid."


Khalid yace "Salmanu kasan wani a police station? Number nakeso amin tracking."


Salmanu yace "bansan kowa ba wlh sai yayan waccen."


Khalid yace "wanda suka yaudareka? Basu indai sune."


Nan ya kashe wayar ya juya can tv station din, yana isa ana turomai text na interview yana karantawa ya kifa wayar dan yanzu yama daina sa rai.


**************


  Goggo tana zaune akan kujera tanacin soyayyen dankali da kwai da Nusaiba ta soya musu, tana ci tana kallanta a tv.


Ita kadai ce a falan dansu Nabila na daki suna hada kaya, Sadiya kuma na wanka.


Fitowa yai daga daki yana mika, alamar yanzu ya tashi, Goggo ta kalleshi ta tabe baki tare da shan shayinta ta cigaba da cin dankalinta


Kallanta yai yace "Hajiya Goggo abinci akeci ne?"


Kallansa tai sannan tace "wai kai bakajin kunyar rayuwarka?"


Kallanta yai yace "me kuma nai?"


Tace "kalli karfe nawa? Ka baje kana uban baci kamar kasa, ko kunya ma bakaji."


Agoggo ya kalla karfe sha daya da kwata yace "to wai Goggo menene dan nai bacci? Kemafa kallan ki kike, kici kisha ki kwanta."


Ta harareshi tace "can ta matsema, nidai ina tuna ma ran asabar zaka kaini biki ran lahadi kuma za'ai dinner da daddare."


Wata dariya ya saka kafin yace "wai da gaske dinner din zakuyi?"


Tace "mu kawayen uwar amarya ne meye in munje?"


Yace bakomai Allah ya taimaka.


Tace "waccen magen daka kwaso yaushe zaka kaita makarantar ta gama ta tafi? Nifa kasan bansan a takuramin a dakina."


Yace "Zainab tace ta zauna adakinsu Nabila insun wuce yau."


Goggo ta kalleshi cikin zargi tace "ita da saka sallama gobe meye naka nacewa ta koma can?"


Yace "bani na fadaba Zainab ce tace saboda ke."


Goggo tace "to koma menene ka tabbatar ka sallemeta gobe."


Yace to naji, tana ina?


Tana daki.


Ta cigaba da cin abincinta.

Dakin ya nufa ya kwankwasa, daga ciki ta bude.


Kallanta yai yace "inkinshirya ki fito kici abinci kafin na shirya sai muje."


Tace "kai kaci abinci?"

Yace "ba matsala muje ko acan na samu wani abin."


Tace "to."


Fitowa tai sanye da kayan Goggo wanda sun mata yawa, yace "ina zuwa."


Sa sauri ya nufi dakinsu, Goggo ta bishi da ido.

Yana zuwa ya bude drawer din kayan Zainab, kayan da ta dade batasa ba ya dauko guda biyu sannan ya dawo da sauri  Goggo ta kara binshi da kallo.


A bakin kofa ya tadda ita ya mika mata, kallansa tai tace "na waye?"


Yace "kayan Zainab ne bata sashi saboda ya mata kadan,ki gwada ko zai miki"


Ta amsa idanunta suka ciciko yace "kar ki fara kukan nan naki."


Ta kalleshi tace "Yaya nagode."


Juyawa yai da sauri dan shiryawa.


***********


Bayanta tadan mike saboda dan gajiyar data taso mata sannan ta kalli agoggon hannunta, ganin lokacin ya kusa yasa ta jawo drawer din kusa da ita hoton dake ciki ta ciro, a hankali tasa hannunta ta goge sannan ta kura wa hoton ido, idanunta ne suka fara canza kala da sauri ta maida hoton ta rufe.


Sannan ta mike da dau wayarta.


*************AYUSHER**********

[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀


Haske Writers Association💡


Shafi na Goma Sha Hudu


Wattpad/@AyusherMohd.


*Ayusher Muhd*


Baki Goggo ta saki dataga Sadiya ta fito daga daki sanye da kaya, duk da bata san Zainab da kayan ba amma tasan ina zata samo kaya inba na Zainab ba?

  Sadiya ta matso ta tsuguna a gefen Goggo ta gaisheta, Goggo ta amsa tace “Kin shirya?”

Tace “eh.”

“Tafi da wannan kitchen ki zubo abinci.” Ta mika mata plate din hannunta.

Sadiya ta amsa ta mike ta nufi kitchen, Goggo ta kwafa ta maida kanta kan tv.


Nabila ce tafito daga cikin daki, zama tai akan kujera tare da kallan Goggo tace “Goggo naso ina nan za’ai bikin nan inje rakiya.”


Goggo ta kalleta tace “inkinje wa kika sani?”

Nabila tadan tabe baki tace “ba sai kin fadi haka ba Goggo nima neman magana ce, ko ina nan ba zuwa zan ba.”

Dariya tai tace “nima naso kina nan muje tare wasa nake miki, ai tafiya da dan rakiya yafi dadi.”


Nabila tace “Uhm.”


Goggo ta harareta ta kasan ido a ranta tana cewa wannan yarinya da tsinanen neman magana take.

Adam ne ya fito daga daki yana sa mabalin riga.


Wai harkai wanka ko me?

Goggo ta fada tana kallansa, Nabila ta kalleta tace “to in banda abinki Goggo dakalw yai?”

Goggo ta kifa mata harara tace “Nabila wai meyasa bakinki baya shiru ne?

Nabila ta kalli Adam wanda shima kalaman Goggo sun bata mai tace “Uncle dan Allah ka taimaka ka daumin hoto ka turamin.”

“Hoto? Nawa?”

Alama ta mai da Goggo tace “in zamusha ashoki.”

Adam yai dariya yace “angama, nayi alkawarin turuwa.”


Sadiya ce ta dawo dauke da plate biyu, ajiye daya tai a kusa da Goggo sannan ta ajiye ma Adam a inda yadan fiya zama tace “yaya gashi.”

Ta koma kitchen, daga ciki tace “yaya sugar fa?”

Yace “kadan.” Jim kadan ta fito da cup ta ajiye mai sannan ta zauna.


Yace “godiya nake kanwata.”

“Kanwa?” Goggo ta fada ba tare da ta sani ba.

Nabila ta kalleta tace “Goggo me kike nufi?”

Adam ne ya kalleta da sauri, dariya ta saki tace “dubamin ki gani Nabila, maza basa tashi cewa mace kanwarsu sai ta musu aiki.”


Nabila ta kalli Sadiya wacce tai shiru tana cin abicinta, wai Sadiya bakya magana ne?”

Murmushi tai ta kalleta tace “inayi.”

Nabila ta kalli Adam da Goggo tace “wai haka take? Ni sai naga kamar ba haka ya kamata ‘ya da uwa su dinga yi ba.”


Adam ne ya kwashe da dariya harya kusa kwarewa yace “Baki gansu a daki bane su biyu, sun iya kus kus cikin dare.”


Nabila ta kalleshi sannan ta kalli Goggo wacce itama kallanshi take tace “irin wannan dariya?”

Goggo tace “kuyi ku gama ku wuce lokaci na wucewa.”

Adam ya mike ba tare da ya kara cin komai ba ya dau plate da cup din yai kitchen, ajiyewa yai ya fito yai waje.

Sadiya ta mike itama ba tare da ta karasa ba ta kai kitchen ta dauko hijab ta fito.

Harzata fita Nabila tace “saduwar alkairi.”

A hankali tace “bazamu sameku ba?”

Tace “eh, sai kun dawo.”


Sadiya ta fita, a bakin mota ta tarada Adam ta bude ta shiga shima ya shiga, Nusaiba ce ta fito da gudu tace “Yayanane?”

Nabila dake zaune ta mike tace “Allah ya baki lfy dan wlh bakida ita.”


Cikin masifa tace “ke kika dauranun rashin lafiyar?”

Nabila ta daga kafada tace “kika daurawa kanki dai.”

Cikin masifa Nusaiba tace “ke kuma meye naki a ciki?”

Nabila ta fara hamma tace “ahhh nagaji.”


Ran Nusaiba ya kara baci, Goggo ta kalleta tace “fadan karshe ake mana?”

Nusaiba tace “ai munsan murna kike da tafiyarmu.”

Goggo tace “ni mikon ayaba a kitchen da alama neman magana kikeso.”


Nusaiba ta wuce kitchen ta dawo da ayaba ta mika mata.

Goggo ta amsa ta maida idanta kan tv.


*************


Zainab ce tai knocking din glass din baya, Khalid ya bude motar ta bude ta shiga.

Zama tai sannan ta kalleshi a ranta tace baya gajiya da zama a mota?

Khalid ne ya tada motar sannan yace “muje?”

Tace eh.

Nan ya fara tafiya, shiru sukai a mota kafin wayar Khalid tai ringing, dauka yana a handsfree yace “Salmanu zan kiraka.”

Yana neman kashewa cikin tashin hankali yaji Salmanu yace “Khalid yanzu bayan munyi eaya na fito zanje siyo kunun aya, naga Asiya a hanyar gidanmu.”

Asiya?

Khalid ya tambaya, Salmanu yace eh? Wai tsaytsayi ya samu Abba, da alama bandaki ya shiga ya nemi bin bango da kanshi ya fadi.


Cikin tsananin tashin hankali Khalid yace “yanzu Abban yana ina?”

Ya fada yana neman daukan wayar dan ya kashe handfree din.

Salmanu yace “munje Chemist sunce mu wuce asibiti cikin gaggawa, to gashi munzo asibitin su kuma sun ki karbarmu tukunna.”


Khalid hankali a tashe yace “bari na taho, zanzo yanzu.”


Zainab da tunda aka fara wayar hankalinta ke kan Khalid tana ganin ya ajiye ga kalleshi.

Juyowa yai ya kalleta yace “am soryy bansan ya za’ai ba Abbana ne bashida lafiya da alama dole naje.”

Kai ta daga alamar to sannan tace “amma naji yana cema ba’a karbesu ba.”

Yace “eh zanje inga meza’ai.

Zainab tace “inba damuwa ka kawosu nan asibitin Zaks, mai asibitin matarsa tare mukai makaranta.”


Kallanta yai yace “mungode zanje in abin bai yiwuba sai mu taho nan din, nagode sosai.”

Tace “to ko zaka kaini gida sai ka wuce da motar?”


Kallan mamaki ya mata, kanta ta kawar gefe.

Komawa yai ya zauna daidai sannan ya maida motar titi ya cigaba da tafiya.

Can ya daure yace “ko na maidake station din sai na wuce?”

Tace “a’a zan tafi da kaina, ka wuce.”


Shiru yai yana tunanin halin da Abba yake ciki, yana neman shiga gate tace ya ajiyeta anan, nan yai parking ta fito, harta rufe kofar tai saurin budewa tace “Ohh akwai wani dr Sabir a asibitin Danbatta, ta dauko wayarta tak searching din numbersa sannan ta mika mai wayar tace “ka kirashi zan mai magana yanzu.”


Khalid ya karanta number sannan ya mika mata wayar, kallanta yai tana amsa ta wuce ciki.


Juya kan motar yai ya dau hanyar danbatta.


Zainab na shiga gate ta tsaya ta kira shi, sai da wayar ta kusa katsewa ya daga “Zee?”

Tace “Sabir kana danbatta ne haryanzu?”

Yace “eh nemana kike ne?”

Tace “no abokin mijina ne zai nemeka yanzu plz.”

Yace ok, sanin halinta yasan yanzu zata kashe wayar yai saurin cewa “shikenan?”

Tace “akwai wani abu ne?”


Dariya yai yace “Zee kenan, abinda zakicewa wanda ya soki na shekara da shekaru kenan?”

Tace “nagode da taimako.”

Ta kashe wayar, daga can Sabir ya kalli wayar tare dayin murmushi yace “Zee kenan”


*******


Sai da sukai nisa yace “northwest ce?”


Tace “eh.”

Nan suka dau hanya, kallanta yai kadan yace “dazu Nabila ta tsorata ki ko?”


A hankali tace “eh.”

Yace “haka take, halinsu daya da yayarta sai dai ita akwai bin didigi.”


Sadiya tai murmushi tace “meyeasa basa yarda da mutane?”


Adam ya kalleta yace “karki damu da wannan.”

Tace to.

Sai da suka tsaya suka cire kudi ya bata sannan suka karasa northwest yace “in rakaki ne?”


Da sauri tace “a’a zan je in gama, ko zakaje ka dawo? In ma gama sai ma fadama?”


To kawo wayarki na sa miki numberta, nan ta mika mai yar nokia din nan me touch ya amsa ya saka mata sannan yace “inkin gama ki kirani.”


Harzata fita ta juyo tace “yaya nagode sosai.”


Murmushi yai yace “karki damu.”


Shiru tai tana kallansa, wanda harya tsargu yce “menene?”

Tace “ban taba ganin mutum irinka ba.”

Kansa ya shafa yace “ da gaske.”

Ta daga kai alamar eh, tace “irinka mata ke fatan samu? Aunty tayi dace.”

Kallanta yai yace “haka kike tunani?”

Tace eh.

Yace yau ce rana ta farko da wani ya fadan haka, kowa cewa yake nayi dace.”

Kai ta girgiza da sauri tace “duk da bansan halayen mutane sosai ba amma nasan itace tai dace, itama tanada kirki sosai ina kuma mata godiya.”


Washe baki yai, wayarta ce ta fadi tagun kafarsa, da sauri tasa hannu zata dauka, shima yakai hannu zai dauka hannayensu ne suka hadu, kallanta yai, itama kallansa tai sannan tai kasa dakai tare da dauke hannunta.


Dagowa yai ya mika mata wayar, ta amsa tace “nagode yaya.”


Jeki inkin gama ki kirani.

Tace “nagode.”


Fitowa tai ya juya ya tafi.


Sai da motar ta kure sannan na kalli fuskarta, a hankali naga wani murmushi wanda ya fito daga gefen bakinta, ya sunan murmushin nan? Me yake nufi? Wa tayiwa? Abinda ya ziyarci kaina kenan ganin salaha Sadiya dauke da wannan murmushi yasa naji kaina ya juya........


*********Ayusher*******

[10/27, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀


Haske Writers Association💡


Shafi na Goma Sha Biyar


Wattpad/@AyusherMohd.


*Ayusher Muhd*


Juyawa tai hankalinta a kwance ta shiga makarantar, hannu tasa a jakarta ta dauko wayarta wacce na gani daga mai touch ta koma iphone, baki ma sake ina kallan ikon Allah, number ta danna sannan ta fara waya.

Kana ina?

Kazo ina jiranka a northwest.

Tana kai nan ta kashe wayarta, maimakon ta shiga ciki wucewa tai gefen inda motoci suke ajiye tana dadana waya, batai minti goma ba sai ga wata mota nan mai masifar kyau ta karaso, budewa tai ta shiga sannan yaja suka bargun.

Kallansa tai bayan sun fara tafiya tace "ina abin?"

Nan yasa hannu gefen kujerarsa ya ciro wasu takardu ya mika mata.

Amsa tai tana dubawa sannan tai tsaki sannan tace "tsaya."

Nan ya ja gefen titi ya tsaya, kallanta yai cikin kaguwa yace "Booboo na muje hotel din plz, am in a hurry...." ya fada yana daure hannunsa akan cinyarta.

Doke hannun tai tace "sai yaushe zance ma ka barni na gama abinda yafi komai mahimmanci a rayuwata?"


Kallanta yai jiki a sanyaye yace "kiyi hakuri, amma ya abinda kikeyi?"


"Haushi yasa ma abin baya birgeni, I didn't expect him to be that easy."


Ta kalleshi sannan tasa hannunta a saman goshita ts kwantar da kanta kan kujera, wani kwafa ta saki wanda ya sashi shan jinin jikinsa yace "muje?"

Tace "kaini naci abinci dazu na kasa ci saboda wannan yar iskar yarinyar."


Yace "wacce?"

Tace "Nabila take ko wa? I hate that girl."


Murmushi yai yace "me kikesanci?"


"Kaini Cilantro Restaurant."

Yace okay.


********************


  Zainab ce ta shiga cikin gida bude kofar falo tai, wanda yasa su kallan kofar.

Zainab ce ta shigo a tare sukace Aunty?

Zainab ta kallesu tace "wannan kiran fa? Bakuso dawowa ta bane ko laifi kukamin?"


Dariya Nabila tai tace "munji ba alamar karar gate ne bare na mota."


Da gudu Nabila ta tashi ta bude kofa, ganin ba mota yasa ta juyo da sauri tace "Aunty harya tafi?" Ta fada kamar zatai kuka.

Zainab tace "eh ya wuce yanada abinyi."


Zama tai a kasa dabas kawai ta sa kuka, Zainab cikin mamaki tace "menene?"

Nabila ta girgiza kai tace " malama dan jeki waje kiyi kukan asarar ki, mu dan Allah karki cika mana kunne."

Haushi ya kamata ta taso ta nufo kan Nabila, da gudu Nabila ta mike tai bayan Zainab wacce ta shiga tsakiyar falan.


Zainab ta kalli Nusaiba tace "Nusaiba menene kuma?"


Nabila tana dariya tace " saboda wanda take dakon sanshi baisan tanayi ba, ya tafi batamai sallama ba."


Zainab ta kalli Nusaiba wacce ke kokarin jawo Nabila.

Tace "wai dama da gaske kike? Lalai."

Ta kalli Goggo wacce ke kallansu tana cin cincin."


Nusaiba ta kalla tace "Nusaiba kin wuce kin zauna ko kuwa? Ke kuma in sake jin bakinki."

Ta fada tana kallan Nabila.

Wucewa tai ta zauna, Nabila tai kitchen, Zainab ce ta kalli Goggo tace "Goggo an tashi lfy?"

"Lafiya kalau, sun tafi makarantar."


Zainab tace "oh nama dan sha'afa."

Ta fada tare da wucewa daki, tana bude kofar dakin tace "Nabila."

Nabila data sha ruwa ta taho da sauri ta bita dakin.


Zainab na zaune a bakin gado ta shiga.

Zama tai kusa da ita tace "Aunty!"

Zainab ta juyo gaba daya ta kalleta yanayin fuskarta ne ya canzs zuwa tausayi, Nabila tace "Aunty daina, daina kallo na haka."


Zainab ta kamo hannunta sannan tadanyi murmushi tace "Nabila nagode."


Idanunta ne suka ciko amma fuskarta na kokarin bayyana murmushi tace "karki damu Aunty kedai kiyi kokari ki cigaba da zama cikin farinciki, shikedai ne abinda nake nema kuma na tabbatar Mama da tanada rai abinda zata nema kenan."


Zainab ce tai murmushi tace "sai kace kece babba."

Nabila tai dariya tace "in na nuna miki na girma sai hankalinki yafi kwanciya."


Zainab ta jawota ta rungumeta tace "in wani abu ya faru ki kirani kinji?"


Nabila ta goge kwallarta tace "To Aunty."

Zainab ta dagota tace "Dady fa? Yana nuna miki banbanci?"

Kai ta girgiza tace "bansa a kaina ba bare na gani."

Zainab tai dan ajiyar zuciya tace "in an kusa visiting kimin magana zanzo muku."


"Kin tabbatar? Kinsan zaku hadu da Dady da maman Nusaiba?"

Wannan damuwarsu ce insun gani sa tafi, inata kin zuwa miki saboda banasan kisan meke faruwa amma tunda kinsani banga abinda zai hanani ganinki ba."


Nabila tai dariya tace "Shikenan zan kiraki."


Jakarta ta zuge ta dauko kudi, mika mata tai dubu goma tace ke biyar Nusaiba biyar, Nabila ta amsa tace "mungode."

Zainab tace "in kara miki?"


Nabila tace "a'a abubuwa sun miki yawa, Aunty wai haka zaki cigaba da zama komai kece keyi?"


Murmushi tai tace "yana neman aiki, sannan banajin wani abin dan nayi komai, na tabbatar saboda hallarcin danamai bazai taba cin amana ta ba kamar wani wanda baisan hallacci ba."


Nabila ta sake dariya tace "dukda bansani ba nasan da Dady kike, wai dan Allah meya faru takamaimai."


Zainab ta mike tace " zan fada miki amma ba yanzu ba."


Nabila tadan turo baki tace "shikenan."


Dariya Zainab tai tace "borin ya motsa ne?


Nabila tai dariya itama tace "Aunty Allah ki dinga rufe kitchen dinki lamarin ciye ciyen goggo yayi yawa, ke kina can kina aiki danta na tsinanen bacci da jin dadi ita kuma sai ci da tsinanen kallo."


Zainab ta dan bige kanta kadan tace "wayace miki ana maganar manya haka? Kuma mamar Adam kamar mahaifiyata take."


Nabila tadan tabe baki.


Zainab ce ta mike ta bude drawer dinta, agamfa ta dako irindaya guda biyu da mayafinsu, tace gashi, sannan ta dauko jaka guda biyu suma iri daya.


Nabila tace "yaushe kika siya?"

Dariya tadanyi tace "duk sanda na samu naje siyayya ina siyowa saboda nasan zakuzo."


Nabila cikin jin dadi tace mungode.

Da gudu ta bude kofa tana kiran Nusaiba, man Nusaiba ta zo sukaga kaya suka hau murna.......


Adam kam tun bayan daya ajiyeta jikinsa a sanyaye ya dawo gida, shikansa baisan meya sameshi ba.


********


Gudu yake harya isa Danbatta, yana zuwa ya tada Abba a kwance akan gado a Er amma ba kowa a gunsa sai wata nurse, hankalin Khalid a tashe ya nemi number nan ya kira, Sabir ya dauka ya sanar dashi Zee ce ta bashi number din.

Nan ya ce gashinan zuwa, Umma kuka kawai takeyi, Asiya ma haka, shikam Abba gaba daya da alama baisan waye a kanshi ba sosai, sai jini dake zuba a ta kasan inda akamai aikin, Sabir na zuwa ya sallamesu waje, nan ya fara aikinsa na ganin ya daidaita abinda ke faruwa.


Shikam Khalid na zaune kusa da Umma, Asiya na gefensa.


Salmanu ne yace “bari naje na dawo Khalid.”


Khalid ya mike yace nagode Salmanu.

Nan ya wuce, Umma ce ta kalleshi tace “a ina ka sanshi?”

Yace “wacce nakewa aiki ne taban numbersa ta sanshi ne.”


Umma tace “amma mungode mata da alama mutumiyar arziki ce, Allah ya biyata.”


Khalid yai murmushi a kasan ransa yace “da alama kam.”


Sun dade kafin Dr Sabir ya fito, sanar dasu yai ba matsala sai dai ya samu barci abashi ya huta.”


*********


Shigowa Adam yai Gogo ce kadai a falan tana ta cin cincin dinta, Adam ya kalleta ya zauna a kusa da ita, kallansa tai tace “Sallamar kenan?”


Yace “nayi kina ta kallo ina zakiji.”

Harara ta maka mai tace “kai ka sani, ka kaitan?”

Yace “eh sai ta gama zata kirani.”


“Zadai ta gama yau ta kama gabanta ko?”


“Eh gobe zata tafi.”

Tace “ah to dan ni bansan bikin nan ya tashi tana gidan nan.”

Meyasa?

Tace “tambaya kake? Wayasan me zata sata in ba kowa a gidan? Ita waccen tana aiki, ni ina hidimar biki kai kuma kana can kana uban bacci.”


Dariya yai yace “Goggo kenan.”

Karar shigowar mota sukaji yace “Zainab ce?”

Tace “ita tana daki da yara sai dai mai daukan nasu ne kila.”


Adam ya leka yace “oh shine kuwa.”


Nan ya wuce daki ya sanar dash.


Kayan suka nunamai ya tayasu murna sannan suka fita dan kara shiryawa.

Zainab ta kalleshi, karasowa yai ya rungumeta tsam a jikinsa.

Murmushi tai tace “Honey.”

Yace “Ina sanki Honey harbansan yawan adadinsa ba, nagode da kasancewarki cikin rayuwata.”


Murmushi tai ta dago ta sumbaceshi tace “nima nagode da shigowarka cikin rayuwata.”


Tare suka fito, Zainab tai kitchen, gani tai anyi abinci, murmushi tai ta deba ta zuba ma wanda zai kaisu sannan ta kira Nusaiba ta mikamai, itama ta zuba kadan taci.


Nan su Nabila sukai sallama, suka shiga mota.


Nabila tace “Goggo asha biki lafiya.”

Goggo tai dariya tace “to, kuma kusha makafanta lfy.”


Nan suka kara sallama suka tafi tare da fatan Allah ya saukesu lafiya.


Zainab ta bisu da kallo kafin tace “Honey ajiyeni a office.”

Yace to.

Nan ta shiga suka tafi...........


*******AYUSHER MUHD*********

[10/27, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     ......................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


Shafi na Sha Shida


A hayarsu ne yana tafe sundanyi shiru, kallanta yai yace "Yau Honey ba bacci sosai."

Kallansa tai tace "yanzu na daina ai, waccen zuwan nasu kaga na damu?"

Murmushi yai sannan yace " Dadyn fa? Haryanzu bakwa ko waya?"

Yanayin fuskarta ne ya canza ta juya kanta zuwa jikin window.

Dariya yai yace "sorry Honey bansan ya akai zancen nan ya fito daga bakina ba."


Bata tankamai ba har ya kara cewa "Honey ina Kwaro yaje ne?"

Kallansa tai fuskarta haryanzu ba a sake ba tace "yaje wani guri ne." Ta rasa meyasa ta samu kanta dakin fadamai babanshi ne baida lafiya."

Kafin yace wani abu tace "Sadiya fa?"

Kallanta yai da sauri, tace "menene? Da matsala ne?"

"A'a tana makaranta inta gama zata kirani."

To kawai tace tai shiru, suna zuwa ta sauka ta shiga shiru yai yana kallanta harta shiga ciki.


Office din editing ta fara shiga ta duduba ta wuce office dinta.

Shiru tai akan kujera tana kallan takardun da zata duba, waya ta dauka ta kira ciki, kace tazo.

Nan ta ajiye wayar, Ramlah ce ta kwankwasa, Zainab ta bata izini ta shigo.


A tsorace ta gaisheta, Zainab ta kalleta tace "ina report din danace ki kawon?"

Ramlatu tace "Am sorry yanzu nake karasa editing."


Wani wulakantacen kallo ta mata tace "yanzu kike me?"


Yawo ta hadiya ta kalleta tace "banida lafiya........"

Bakida lafiya?

A tsorace ta daga kai, Zainab ta dau wayarta ta kira director sannan tasa wayar a handsfree tace "Sir wannan wacce bansan ta yanda akai ta samu aiki anan ba."

Daga can cikin rawar jiki yace "Ramlah?"

Tace koma wa sunanta bai damenba sai dai kai da ka kawota inaso ka sanar da ita wannan shine dama na karshe da zan bata, idan harna kara bata aiki batamin zata taradda takardar kora a saman kafarta."


Director ya canza yanayin maganarss yace "Yahkuri Zainab, ni kaina bansan amfaninta ba, kiyi hakuri zan ja mata kunne."

Bata bashi amsa ba ta kashe wayarta, kallanta ti tace "dafatan kinji?"


Ramlatu wace ranta ya gama baci da yanda Director ya wulakantata yasa ta saukar da kanta kasa, Zainab tace "banida damuwa da duk iskancin da zakiyi, am i your mother? Ko nice babanki? Banida hadi dake rayuwarki ce sai dai inzakiyi iskancinki kije kiyi a hotel amma nan gun aiki ne, idan baki kawon report din nan in an hour ba bansan me zai biyo baya ba, Get out."

Ta nuna mata hanyar kofa, Ramlatu tana hawaye ta fita, tana fita ta shige toilet tasa kuka.


Zainab kam tana fita taja tsaki, ranta ya kara baci, wani abu ta hadiya na bakin ciki, maimakon ta duba takardun dake gabanta kwantar da kanta tai tare da rufe idanunta.


Mahaifiyarta ta hango kwance a kasan tiles, ga jini a malale ta kasanta, ita kadai a gida babu kowa, hawayene suka gangaro ta gefen idanunta wanda batabi ta kansu ba, hangota tai a rikice tana kuks ta rasa ta yanda zata taimaki Ummynta, kusa da ita kawai taje tana kuka tare da rike hannunta.

Kuka take sosai, a hankali Ummy tace "Uwata ki dsu wayata ki kira Kamisu driver."


Kalan cikinta wanda taketa murna zata samu kani ko kanwa tai, a tsorace tace "Ummy! Ummy....."

Jinin dake zuba ta kalla da sauri taja wani wahalalen numfashi sannan ta bude idanunta tana hakki.


Bakinta ta shiga motsawa tana kokarin maida kukan dake neman kwance mata ta shiga kokarin yi, da sauri ta jawo takardun dake gabanta ta fara dubawa.


Wayarta ta daga ta kira Sabir, daga can ya amsa yace "Zee!"

Tace "ya? Ya kiraka?"

Eh tun dazu harna gama na dawo office dina, hatsari yai ne?"

I don't know.

Yace "okay, amma meye hadinki dashi? Shine mijin naki?"

Dan karamin tsaki tai tace "kaifa matsalata dakai tambayar abinda baishafeka ba, nagode."

Bata jira mai zaice ba ta kashe wayarta.


Harkarta ta cigaba dayi, sai dai kasan ranta a ciki yake da tausayin mahaifiyarta da kuma tsanar mahaifinta.


•************


Sai yamma lis sannan ta koma northwest ta naka ma Adam kira, yana zaune a majalisa ana hira yaji wayarsa tai kara, mikewa yai da sauri ya matsa sukasa mai dariya Yaran Hajiya ya amsa kira.


Adam yace "kingama?"

"Eh yaya nagama."

Okay bari na taho.

Ya kashe wayar ya musu sallama, da sauri ya fada motarsa ya shiga y nufi makarantar.

Tana bakin inda ya ajiyeta, yana yin parking ta shiga ta zauna, juya kan motar yai suka fara tafiya ba tare da kowa yayi magana ba, can sai da suka danyi nisa tace "Yaya nagode sosai."

Ya kalleta yace "bakomai, kingama ko?"


Tai shiru tare da yin kasa dakai, kallanta ya sakeyi yace "baki gama ba?"

Kai ta daga alamar eh tace "bangama ba yaya, kayi hakuri."

Dariya yadanyi kadan yace "hakurin me? Ki zauna ki karasa a hankali, gobe zaki koma kenan?"

Tace "gobe Friday kuma ko naje ba zan iya gamawa in bazan takurama ba inasan in bari sai Monday."


Adam ya kalleta, kasa tai dakai tace "yaya kayi hakuri."

Da sauri yace "bakomai, kizauna sai monday din."


Shiru suka danyi kafin tace "Yaya kayi hakuri akwai lokutan da zakaga ina abubuwan da basu dace ba dan Allah inkaga haka kayi hakuri kamar yanda nacema rannan inada larura ne wlh wanda nikaina bana sanin abinda na aikata."


Kallan ta yai har yadansa tari yace "aljanu?"


Dariya tai jin yanda yai maganar, tace "a'a ni kaina bansan menene ba, saboda hakan ansha min duka."


Duka? Ya tambaya tare da dan kallanta.

Tana wasa da hannunta tace "eh yaya, kayi hakuri."

Idanunta ne suka ciciko jiyai tausayinta ya kara kamashi, yace "ya isa hakanan bansan yawan kukan nan."


Share hawayenta tai da sauri tace "nadaina, duk abinda bakaso bazan sake yi ba." Tai maganar tana girgiza.

Murmushi ne ya bayyana a fuskarsa yace "to."

Wani dadine ya kamashi a kasan ransa, yau gashi shine yake bada umarni ya saba a komai sai dai shi a bashi.


********

Ganin jikin Abba ya dawo daidai yasa Khalid ya fito yai ma Umma sallama akan sai ya dawo, kallanta yai yace "zan tambaya in za'a iya biyana da wuri inyaso sai na baki saboda yin abinci ga yan kananan kudadanen da ake amfani dasu a asibitin."


Tace "To khaleed, sannu Allah ubangiji ya daukaka ka, ya baka damar da zaka taimakemu."

Yace Ameen.

Asiya ya kalla yace "in na dawo Umma zata koma gida dan haka kije gidansu Salmanu, kafin nan, ko kuma ni nace yazo ya zauna a dakina kafin na dawo."


Umma tace "yazo din yafi sauki sauki."

Yace to, sai na dawo.


Fitowa yai ya dau hanya, bai tabajin dadin aikinsa ba irin yau, a da ya dauki aikin ne akan rashin abinyi, sai dai taimakon data mai yau tabbas yass ya kara girmamata a idansa, haushi ne yadan kamashi da ya tuns ba yanda zaiyi ya kama wannan mutumin.


Haka ya isa station din har lokacin fitowarta yai.

Zainab na fitowa ta hango motarta, karasawa tai ta shiga tare da ajiye kayan dake hannunta.


Khalid ba tare da ya juyo ba ya dan kalleta ta madubi kadan, gaba daya yanayin damuwa ne karara a fuskarta, daurewa yai yace "Nagode sosai da sosai."

Kallansa tai tadanyi murmushin yake tace "is okay."


Shiru yadanyi kafin yace "jikin nashi da sauki."

I know, abinda tace kenan ba tare da dogon nazari ba.

Khalid yace "kin sani?"

Shiru tai cikin waskewa tace "tunda kaje asibiti i will assume that."

Oh yace sannan ya tada motar, shiru tai ta zubawa window ido, yauce rana ta farko dayaga bata aiki a cikin mota, da alama an bata mata raine, ko mutumin nan ne? Abinda ya fado mai kenan, shiru yai yana tunanin yanda zaiyi ya tambayeta, daurewa yai yace "wannan ya sake kira?"


"Wa?"

Daga yanayin tambayarta ya fahimci baisake ba, shikenan.

Jin yace haka yasa ta fahimci yanayin da take, juyawa tai ta dau tab dinta tana dubawa duk da dai ba wani abu take ba amma batasan ya fahimci tana wani halin.


Yana sauketa ta wuce ciki, Goggo na zaune a falo tana waya da alama wannan bikin daya ishemu shi take magana akai, wanda mu kanmu mun kosa asabar tayi wato jibi a gama bikin nan mu huta.


Zainab bata tsaya a falo ba wucewa kawai ciki tai, Goggo ta bita da kallo, Sadiya dake daki a kwance ma batasan ta dawo ba.


Adam ta gani kishingide yana kallo a laptop dinta, yana ganinta ya taso da sauri yace "Honeyyy...."

Ya bude hannayensa alamar rungumeta, hannun tadan ture ta wuce toilet, tana fitowa ta ganshi a inda ta barshi ya shagwabe yace "Honeyyyy...." ya kara bude hannu.


Murmushi tai sannan ta shiga jikinsa ya rungumeta, dagowa tai ta kalleshi sannan ta canza kayanta, yace "Honney su Nabila sun isa?"

Ta kalleshi tace a'a kawai, fitowa falo tai ta nufi kitchen.


Sadiya wacce ta fito dan cin abinci itama suka hadu da Zainab, Kallanta Zainab tai cikin mamakin ganin kayanta a jikinta.

Sadiya ce ta kalleta tace "Aunty menene?"

Zainab tace bakomai, flask din ta rufe ba tare da ta zuba abincin ba, Sadiya ta fahimci me ta gani hakan yasa yace "Aunty nagode Yaya ya ban kaya inji ki."


Zainab ta kalleta kawai tai murmushi ta wuce ciki.


Goggo ta bita da harara tace uwar mijinki na zaune amma ko gaisheta da gida bazakiyi ba, in dazu kin shigo ina waya yanzu fa.


Zainab na shiga ta kalli Adam tace "yaushe ka ba Sadiya kayana ban sani ba?"


Kallanta yai da sauri yace "Honey dama naga zata skul ne batada abinda zata saka shiyasa."

Meyesa baka fadamin ba to? Kafi kowa sanin bazan hana kanwarka abu ba amma at least nasan meke faruwa."


Adam ya jawo hannunta yace "Am sorry Honey, gani nai da abuna da naki dayane."


Shiru tai kafin tace "meyasa in ina cikin wani hali baka taba ganewa harsai na fadama?"


Cikin mamaki yace "'menene?"


Kallansa tai tace "baka kula da yanayi na ba tunda na dawo?"


Murmushi yai yace "ai kin saba wani sa'in haka kike shigowa a gajiye, zo kiga na nuna miki nawa mukaci a ball din da akai yau."


Baki ta bude kamar zatai magana sai ta fasa.


Fitowa tai ta wuce dakinsu Nabila ta rufe, zama tai a kasan carpet ta sa kanta akan cinyoyinta.......


Goggo ta girgiza kai a kufule, Sadiya ce ta kalli Goggo tace "Aunty bata kula damu bane hala."


Goggo tace "ina fa tsabar iya iskanci ne." Taja tsaki.


Zainab tai shiru.....

Abinda ya faru a shekarun baya ne suka dawo mata................


*******

[10/27, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     ......................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


Inalilahi wa ina ilaihi Raji’un yanzu abinda na rubuta jiya wata tacemin irin abinda ya faru da kanwar babanta kenan, Ya Salam, mace sai tai amfani da danka ta cuceka, dan Allah mata mu gyara halayenmu, bawai dan kinasan auran namiji sai kin shiga jikin matarsa kin cutar dasu ba, mata mu yima kanmu fada dan Allah, dama namiji ansanshi da sankai da kuma tunanin ya isa da kuma yanada dama, amma mata mu dinga duba rayuwar ‘ya’yan mu, in har mu munci riba in aka ci riba akan namu ‘ya’yan ya zamuji?


Allah ya sa mu gane Ameen, jin kalaman yarinyar nan ya tadamin hankali, domin su a wannan lokacin kanwar baban nata na nan, abinda ta haifa ya koma ita kuma auren daga baya iyaye rabawa sukai.


Allah ya karemu daga sharrin Zuciya.....

Ameen.

[10/27, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     ......................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*Shafi na Sha Bakwai*


Asalin Labari.......


Zuwaira Muhammad Kabo shine sunan mahaifiyar Zainab, mahaifanta yan garin Kabo ne sai dai aiki ya daukeshi ya kaishi garin Gombe inda ya tare da iyalansa.


Yaransa guda shida, biyu mata uku maza, Zuwaira itace yar fari a gidansu, Zuwaira yarinyace wacce ta taso mai sanyi dan ko kananta neman raina ta sukeyi saboda sanyinta, kaninta mai bi mata a duk sanda aka mata abu shine yake zakewa ya amshi fadan, ko a gidansu bata taba neman kananta suyi aiki, harsai mamanta haushi ya kamata ta sa su yi da kansu.

Alhaji Muhammad Kabo ba mai tulin wadara bane sai dai Allah ya bashi rufin asiri inda yake zaune cikin gidansa hankalinsu a kwance.


A lokacin da Zuwaira ta gama secondary ta fara neman makarantar gaba da secondary Allah ya hadata da Aliyu wanda ya ganta a hanya, da farko bata amince dashi ba saboda tsananin shiru shiru da hakurinta, sai dai ganin yanda yake tsananin santa ne yasa hartake dan tankawa.


Soyayya mai karfi ce ta shiga tsaninsu wanda duk rashin magana irin na Zuwaira sai da kowa ya fahimci tsananin san da takemai.

Haka aka hakura da neman karatunta akan intai aure ta cigaba.

Aliyu yana aiki ne agarin Kaduna inda yake aiki a harkar wuta, wato NEPA, iyayensa yan garin Gombe ne, Aliyu nada babban family sai dai irin zuri'ar nan ne da ba ruwan wani da wani, saboda matan gidansu hudu, kowa da 'ya'yansa, kowa nada san kansa a haka suka taso, kowa baisan taimakan dan uwansa, gashi shima mahaifin bai damu dasu ba sabods yawansu.


Ansa bikin Zuwaira da Aliyu, anyi biki lafiya ta tare a gidanta daya kama haya a garin kaduna.

Zama mai tsafta sukai a tsakaninsu, duk da Aliyu nada saurin fishi da fada sai dai sanyin Zuwaira da hakurinta yasa Zamansu yin tasiri, domin ko ba ita tai abu ba inya fara fada hakuri take bashi, wanda hakan yake sawa dole yai hakuri.


Zuwaira shekararta daya ta haifi danta namiji, sai dai kafin suna Allah ya dauki abinci, ta sake samun ciki a lokacin tana shekara ta biyu da aure, sai dai kafin cikin yai girma ya bare.

Wannan lamari ya tada hankulansu, anyi ta dirka mata magunguna na gargaji tayi tayin na asibiti dan sai datai bari uku Allah ya bata haihuwar Zainab, Zainab ta kasance yarinyar da aka samu dakyar wannan dalili yasa Zuwaira da Aliyu suka dauki san duniya suka sa mata.


Sati biyu da haihuwar Zainab aka karama Aliyu matsayi sannan aka mai transfer zuwa Abuja.

Wannan kamari ya kara musu dadi, farinciki haryana neman yi musu yawa.

Sun koma garin Abuja cikin ni'ima da daukaka, abin al'ajabi shine tunda suka koma Abuja matsayin Aliyu ke karuwa, tun suna gida mai daki biyu suka sai gida makeke mai hawa biyu.


Aliyu na tsananin jin dadin wannan rayuwa da suka tsinci kansu a ciki, sai dai Zuwaira a hankali damuwa ta fara mamayeta ganin har yanzu ko bari bata sake ba ga Zainab har ta shiga primary.


Tunda Zuwaira tazo garin Abuja batada takaimai mai kawa saboda ita dama bamai shige shige bace.

Kamar yadda ta saba in Zainab ta tafi makaranta tagama gyaran gida sai ta daura abinci, tanayi tana dan kallanta ko kuma tana jin radio, wannan rana haka tana girki gefenta dan radio ne tanajin labarai, ganin abincin ya kamalu ne yasa ta kashe miyar sannan ta kwashe shinkafar.

Tana cikin hada cucumber salad wanda aka gama koyawa yanzu a radio taji motsin mota, murmushi tai dan tasan an dawo da Zainab kenan.

Zainab ce ta shigo da gudu har tana neman faduwa, da sauri Zuwaira ta dagata tace "yar gidan Ummy karkije ki fadi."


Cikin tsananin zumudi tace "Ummy an bamu sabuwar Teacher."

"Haba? Yaushe?"


"Hmmm yau din nan."

Dariya Zuwaira tai tace "lalai da alama Zainab na san sabuwar teacher din nan?"


Cikin jin dadi tace "eh sosai sosai, Ummy kizo gobe na nuna miki ita."

Dariya Zuwaira tai tace " abin harya kai haka?"


Tace "eh tana dariya."


Kayanta ta canja taci abinci ta wuce islamiya, tana dawowa Dady na nan, tana shigowa gida kafin tai ko sallama ta ruga tana cewa "Dady yau an banu sabuwar Aunty."

Dady ya kalleta da gudu ta karaso ta hau cinyarsa tana cewa "Dady an bamu sabuwar Aunty."


Dady yasa dariya yace "Ummy ta fadamin, lalai Zainab naji da wannan Auntyn."


Dariya tai tace "gobe kazo muje na kaika ka ganta."

Ummy ta kalleta tace "sankai, akace ni za'a fara kaiwa?"

Dariya sukai nan suka shiga hira har dare yai.


Da safe Zainab ana shiryata ta tubure akan lalai itafa sai Ummy da Dady sun kaita makaranta sunga Auntynta, duk yanda Ummy ke lalabata bata bar kuka ba.

Dady ya dauketa yace "yi shiru yar gidana muje muga Auntyn nan."


Ummy ta zura Hijab dinta suka shiga mota tare, driver ya taho shi kadai dan ya maida Ummy, tunda daga makarantar Dady zai wuce.

Suna isa tana sauka daga cikin taxi, tsallako titi tai Zainab na fitowa cikin murna tace "Ummy gatacan."


Taci gayu sosai kai bakace malamar makaranta bace,  sanye take da doguwar rigar atamfa fitted gown wacce ta zauna mata tsam a jiki, mayafi ta yafa a saman kanta tana rike da takardun ta, ta rataya hand bag dinta.


  Ummy ta kalli Zainab tace "ya isa haka nan inta iso sai ki mata magana."


Dady ne ya karasa fitowa daga mota, daidainan ta karaso, fuskarta a sake take sosai harta karaso gun, cikin fara'a tace "Zee."

Da gudu Zainab ta karasa ta rike hannunta, tare suka karaso gun.

Dady ta kalla sannan ta kalli Ummy, cikin fara'a ta gaisheta, Ummy ta amsa cikin nuna farinciki.

Dady ta gaisar, ya amsa yana cewa "shikenan hankali ya kwanta?"

Fuskarta dauke da tambaya ta kalli Ummy tace me?

Ummy tai dariya tace "tun jiya aka dage sai munzo munga sabuwar Aunty."

Fara'arta ce ta karu sosai ta kalli Zainab, Dady yace "tanada san mutane, sannan da alama kinada saukin kai hakan yasa take sanki sosai."


Murmushi tai tace "bakomai ai da na kowa ne."


Ganin yara duk wanda yazo indai a class dinsu yake zai nufota ne yasa sukai sallama suka tafi.


Ummy ta koma gida shikuma ya wuce gun aiki.


Da daddare suna kwance a daki kamar masu bacci Ummy tace "da ace matar nan zata yadda da ita ta taimakama Zainab da lesson din, naga sam basa shiri da Auntyn da take zuwa yanzu."

Dady ya juyo yace "nayi wannan tunanin dazu nima, toko zaki bita ko zuwa karshen satin nan ne ki tambayeta?"


Ummy cikin gamsuwa tace to.


Sati na zuwa Ummy taje da kanta, ba wani dogon nazari ta amince da hakan wanda yasa Ummy jin dadi.


Sai ya kasance duk asabar da lahadi Aunty Basma na zuwa gida tana koyama Zainab karatu.


Lokacin da abu ya fara faruwa.

A koda yaushe Dady yana zama a gida ranar asabar da lahadi, yana hutawa saboda hidmomi.

Yanda yake jiyo dariyar Zainab daga sama ne yasashi kallan Ummy yace "da alama wannan matar tana san Zainab dayawa."

Ummy tai murmushi tace kana ganin nima yanzu nayi kawa bayan malamar Zainab?


Mikewa yai yace "bari naje naga yanda ake karatun.


Ummy batare da wani abu ba tace ya kamata, mikewa yai ya sauko kasa, bangaren da yake na Zainab ne knda take wasa da kuma inda ake koya mata karatu ya nufa.


Kofar a bude take, yana lekawa yana suna wasan hide and seek, Zainab ta dage tana nemanta.


Tsayawa yai yana kallan ta yana murmushi, Aunty Basma ce tamai alama dayai shiru, Zainab tana neman Aunty ta cafko Dady."


Tana bude ido taga Dady shagwabe fuska tai tace "dady kuma?"

Dariya yai yace "nidin ne sai akai me?"

Dariya sukasa gaba daya, ido ya zubawa Basma wacce ke sanye da riga da skirt na material silk ya kamata dam, ga kanta ba dankwali, maida kallansa yai kan Zainab yace "ayi karatu."

Ya juya, wajen magrib tai sallama akan zata tafi.

Dady yace "bari na saukeki dan zan fita nima."

Ummy tace "Basma ki tsaya ya saukeki."

Kallan Ummy tai tace "ina fita zan samu taxi."


Ummy tace "ga sauki hankali a kwance?"

Godiya tawa Ummy wacce ta dauko mata turare da man shafawa ta bata, tare suka fito dukansu suka mata sallama Dady da Basma suka tafi.


Suna tafe a hanya ake ta famar damunta a waya, kallanta yai yace "ki amsa mana!"

Kallansa tai tace "in amsa ince me?"

Yace "in bakyasan amsawa sai ki kashe wayar."

Juyowa tai ta zubamai ido, yanda take kallansa ne yasa ya gangara gefen titi, kallanta yai yace "menene?"

Tace "bakomai."

Kallan na menene to?

Tace "kawai ina tunanin yanda zanji in nai aurene? Saboda wannan zamanin daga zarar mace ta girma an dinga magana kenan."


"Kinada kyanki ba masoya kika rasa ba meye naki na damuwa?"

Shiru tai batace komai ba............

Tin daga wannan rana lamari ya fara baci tsakanin Dady da Basma, Ummy har ta fara tunanin kamar yanda yake kallanta bai dace ba, sannan irin shigar da takeyi ta fara damun Ummy.


Sai dai taya zatai magana? Matar da bata iya magana duk yanda aka muzguna mata?


Yanda take nunawa Zainab so kuwa inka ganta sai a dauka itace mahaifiyar tata.


Kwatsam wata rana Basma tazo ta dauke kafa, a makaranta ma ta ajiye aikinta, Ummy ta fara damuwa saboda a lokacin kawayene su duk da daurewa take.


Ganin ba labarinta yasa Ummy da Zainab wacce ta dameta da zancen Aunty sukaje har gidanta, a lokacin Dady yayi tafiya saudiya.

Sanda sukaje akace ai batanan tayi tafiya.

Ummy suka fito suka koma gida, Dady na dawowa daga saudiya ya canza gaba daya, ko zama a gida bayayi bare yai wasa da Zainab balle har suyi yar hira da Ummy."


Wannan hali daya tsira ya tada hankalin Ummy gashi a lokacin Allah yaima mahaifiyarta rasuwa, dakyar ya barta taje gombe tai kwana uku, sam yanzu zaman nan baya mata dadi, komai ta tambaya da fada yake amsa mata gashi sai sunyi bacci ma yake dawowa


Rana kwatsam Basma ta aiko mata da katin bikinta.

Ummy tai ta murna ta kirata a waya tana tayata farin ciki.

Ansa biki wata shida a wannan lokaci Zainab tana shekara tara.

Har gida Ummy taje ta tadda anata gyara musu gidansu, ga kayan lefe nan na gani na fada, Basma yanda ta karbesu ne yasa jikin Ummy yai sanyi, yau ko yanda ta saba jan Zainab a jiki batai ba.


Sai dai Ummy ta mata uzuri akan bakin dake gidan ne.


Haka suka koma gida su biyu wanda yanzu haka suke yininshi.


Ana sauran kwana biyu biki Dady ya shigo gida da wuri, murna Ummy tai tayi, sukaci abinci tare y zauna yana duba homework din zainab har lokacin baccinta yai.

Kallan Zuwaira yai fuska a tsuke yace "dama fada miki zan na sai gida a can kusa da gun aiki na."


Cikin farin ciki tace masha Allah, kai Allah ya sanya alheri.

Jibi zan kara aure.

Kafin ta gama rufe baki wannan kalmar ta daki kunnenta.


Kallansa tai da sauri tace "me?"

Yace "aure zanyi sannan nan da kwana biyu za'a daura."


Sake baki tai ta kalleshi, mikewa yai zai wuve daki, da sauri tasa hannu ta riko rigarshi tace "haka ya dace miji ya sanar da matarsa zai kara aure? Haka addini ya koyar? Meyasa wani sa'in san zuciya ke neman mantawa da abinda ya dace?"


Hawaye ne suka zubo mata, ta dago ta kalleshi tace "zan hanaka aure ne bayan kayi niyya? Amma haka ya dace........."


Zuciyarsa ce tadan raunana, da sauri ya dagota ya rungume yace "kiyi hakuri."


Hawaye ne suka shiga zubo mata, sai dai san zuciya irin na namiji wai sai ce mata yai yaje gun wacce zai aura tundazu yakejin sha'awa, haka ya biya bukatarsa tana hawaye......


Dady y canza gaba daya ta kasa gane kanshi har tunani takeyi anya shine mutumin data sani da??????


A ranar bikin basma ya kasance ranar bikinsa hakan yasa Ummy ta aika mata da sako a waya akan bazata samu damar zuwa ba.


Haka ta zauna ita kadai a gida babu mai mata tausar kirji, Zainab a wannan lokaci itama duk ta canza saboda ganin yanda mahaifiyarta take cikin damuwa, ga gida ita kadai.


Tunda aka daura auren Dady bai taka kafa yazo gidansu ba har sai dayai wata biyu, a lokacin Ummy tanata fama da rashin lafiya saboda ciki, wanda ita kanta bata sani ba, ta dauka damuwarta ce yasata shiga wannan hali.


Gaba daya Ummy ta zabge, Zainab duk ta canza itama, inta dawo gida sai dai ta zauna kusa da mahaifiyarta, anan take cin abinci suyi bacci tare, Ummy na kokarin daurewa dan ta nunawa Zainab ba abinda ke damunta.


Sai dai Zainab tun tana daukan wayar Ummy ta kira Dady ana kashewa harma ta hakura ta daina.


Ummy kam ganin amai yaki karewa gashi intai abinci dakyar take iyaci yasa tai tunanin zuwa asibiti.


*******

[10/27, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     ......................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


Page 18


Yau watansa biyu kenan bai tako cikin gidan ba sai dai yana aiko kudi yana kuma sawa akai musu kayan abinci.


Yau Ummy ta tashi da wani irin zazzabi sai amai take kwarawa, da alama dadewar datai bata samu ciki na ga girma shiyasa cikin ke wahalar da ita, tana zaune a falo, dauriya kawai takeyi saboda taga gaba daya hankalin Zainab ya tashi, jin sallama ne yasa Zainab tai tunanin driver ne datace inya dawo zai kai Ummy asibiti.

Tana budewa taga Dadynta, samun kanta tai kawai da fashewa da wani irin kuka.

Tausayinta ne ya kamashi don yana tsananin santa, juyawa tai da sauri ta shiga ciki.

Ya biyota shima cikin hanzari, cikin falo ta tsaya tace "Dady akai Ummy asibiti batada lafiya."


Kallan Ummy yai wacce jin sunan Dady yasata kokartawa ta mike ta kalleshi, nan Dady ya ga duk ta rame ta canza kamani, a hanzarce ya dauketa sukai asibiti su duka.

Anan ne yaji cewar Zuwaira nada juna biyu, aka bata gado akasa mata drip.

Sai dai me? Yana fitowa daga office din dr aka kirashi a waya, Zainab dake tsaye tana jiransa yazo taga yayi hanyar kofa cikin hanzari.

Kafin tai yunkuri har ya fice.

Da gudu ta fito amma ko motarsa babu, haka suka zauna a asibiti har aka sallamesu Dady bai kara ko lekowa ba.

Ummy ganin ta samu sauki ta cire komai a ranta saboda yar ta.

Sosai suke zama suyi hira in ta tafi skul ta zauna taita tunani, gashi ta kasa fada a gidansu, Zainab tun daga wannan rana bata sake daukan waya ta nemi Dady ba haka kuma bata karayima Ummy zancen ta kirashi ko baizo ba.


Haka suka cigaba da rayuwarsu har cikin Ummy ya girma, Zainab murna kamar me akan Ummy zata haifar masu baby.

Zainab na shekara goma sha daya Ummy na wata tara.

Wannan rana ita tafi ko wace rana ciwo a tattare da Zainab, taje makaranta, tana dawowa ta tarada Ummy a yashe a kasan beni gaba daya kasanta jini ne ya mamaye da alama ciwo ne ya kamata tana hanyar saukowa ta mirgina, dan har gefen goshinta a fashe yake.


Gaba daya jikin Zainab rawa ya fara, tama rasa me ya kamata tai, a hankali Ummy ta nemi data kira waya.

Jitai kanta na juyawa ganin jinin dake kasa, sai da Ummy dakyar ta kamo hannunta, firgita tai sannan  ta dauko wayar a falo ta kira Dady, gaba daya ba a hayyacinta take ba, mai makon ya dauka muryar mace taji tace "hello."

Da sauri ta kalli Wayar sannan tace "Dady dady yazo Ummy....."

Kashe wayar akai, ganin yanda Ummy ke numfashi yasa ta fita da gudu ta kora driver dinsu.

Haka aka dau Ummy akai asibiti, ana zuwa aka kaita dakin tiyata, sai dai an cire baby amma jini yaki daina zuba duk yanda sukai yaki tsayuwa.

Ummy tai murmushi dakyar tace a kira Zainab.

Zainab ta shigo gaba daya haryanzu bata hayyacinta, Ummy ta kamo hannunta, Allah ne sai Zainab kadai sukasan me tace mata a wannan lokacin.


Mati driver wanda tsoro ya kamashi yasa yana kaisu asibiti ya nufi saban gidan Dady ya sanar dashi sune suka shigo dakin.


Ganin Ummy a kwance yasa dady ya nufeta jikinsa na bari, Zainab baya kawai tai ta sulale agun.


Dady hankalinsa yai masifar tashi, ya nufi Ummy cikin sauri ya kamo hannunta, wasu hawaye ne suka zubo mai, murmushi tamai da kyar daga wannan murmushin ciwo ya rikice, nan ya shiga kokarin sa mata kalmar shahada, ganin yanayinta yasa ya fita da sauri.

Dr ya kira, sai dai kafin suzo Ummy ta cika.....

Allah yai mana cikawa mai kyau Ameen ya Allah.


Haka Basma ta dawo gidan Ummy da gatan cikinta, kannen Ummy sunzo gaisuwa aka bar kanwar Ummy a gidan wato Sauda, nan ta zauna har akai arba'in itama ta koma saboda iyalanta.


Ansama Yarinyar suna Nabila, satin Ummy biyu da rasuwa Basma ta haifi Nusaiba.

Itama Basma tai kuka sai dai Allah ne kadai yasan kukan da takeyi.

Dady kam sai dayai sati ko kofa bai fita ba.


Haka Zainab ta taso, magana wannan inba ta zama dole ba bata yinta, duk yanda dady yaso su daidaita amma inaaa Zainab gaisuwa kadai ke hadata dashi.

In bata makaranta daki take daukan Nabila ta kula da ita.

Tundaga wannan lokaci Zainab tasa a ranta bazata taba bari Namiji ya zama shine yake da komai ba balle har yai tunanin dole ta zauna dashi, ba kuma zata taba bari mijinta ya wulakantata ba, a da auran ma tace bazatai ba.

Tayi karatu kamar zata kashe kanta dan a makaranta babu ko yarinya daya da take kawatar, saboda taga butulcin dake tattare da yarda da mutum.


Tundaga nan ta zama selfish kanta kawai ta sani bata tunanin kowa, abu in bai shafeta ba ko Nabila ba bata shigarshi.

Zama bai mata dadi ba a gida saboda ko ganin Basma tai da mahaifinta hango mahaifiyarta take a cikin jini.

Haka zainab ta gama karatu na nemi aiki a kano saboda ta bar kusa dasu.


Dady yaso hanata sai dai ba yadda zaiyi dan yasan bai isa ya hanata abinda tai niyya ba, Zainab ta dawo kamo gidan Aunty Saudah wato kanwar mamanta.

Anan ta fara aiki har takai matsayin da take a yanzu.

Ta hadu da Adam ne a wata rana lokacin sunji daukan rahoto, tana sauri saboda bata mata ran da akai, tana parking din mota tazo fita shi kuma ya taho zai wuce.

Bata sani ba ta budo kofar ta bigeshi, Adam wanda yake tafe yana waya ya danyi kara tare da kallanta.

Wani banzan kallo tamai tace "idan zakai wayar soyayya ka dinga kallan gabanka."

Ta rufe mota ta fara tafiya, baki ya saki da sauri yace "Baby zan kiraki."

Gabanta yasha yace "me kikace?"

Kallansa tai tace "kunne biyu gareka sannan baki daya ne dakai, ya kamata jinka yafi maganarka yawa, dan matsa ina sauri ne."


Tafiya tai wanda tabai Adam da baki a bude, kallanta yai sannan ya kalli zabgegiyar motarta a ransa yace "ah kin rika ne, ni ina nan na saki baki ina neman yanda zanyi ga wata wacce da alama ta jiku."


Juyawa yai ya tafi.

Washe gari yana zaune ya saka kwanan shinkafa da wake a gaba, takaicin cin shinkafar ya kamashi yace "Goggo wai dan Allah yaushe zaki mana yar dagedage nifa Allah na gaji dacin fara damai."


Radio dinta ta kashe tace "wato Allah wadan naka ya lalace, kana kwance kamar tsuma sai dai na baka kaci sannan har wai abincin ma sai ka zaba? Bayan duk ka cinye mana dan gadon mu agun dan islan karatun da kake."

Adam yai dariya yace "karki damu na kusa samun aiki ina daga cikin office ina shan sanyin AC mai dadi, gefe kuma ga lemo nan in kurba inci naman kaza."


Goggo ta tabe baki tace "sai ka tashi daga mafarkin da kake ko wallahi tinkiyar can ta cinye."

Da sauri yaja kwanansa gabansa yace "in ta cinye ince me?"

"Ina na sani kaci kazar mana."


Haka ya fito bayan ya gama cin abinci suka tafi gidan abokinsa Ziyad inda suke kallo.


Ana switching din tashar Muryar Arewa Adam ya ganta tana labarai( a lokacin labaran dare take)


Ruwan dayake sha ya feso waje ya zuba mata ido, Ziyad yace "Masoyin Baby soyayyar ta motsa ne?"

Adam ya zuba wa Zainab ido ba tare da yace komai ba.

Haka ya kwana yana juya abin a ransa, ai kam washe gari ya nufi cikin kano, sai dai inda suka hadu jiya bai ganta ba.

Tambayar Station dinsu yai yaje.


Tana tsaye cikin fada tanawa staff din gun fada akan  laifin daukan rahoto yanda ya kamata ta hangoshi ta glass, daga waje ya daga mata hannu.

Fitowa tai cikin mamaki tace "me kake anan?"

"Zuwa nai aban hakurin da ba'a bani ba jiya."


Mamaki ne ya kamata, tace "hakuri?"

Yace "eh in baza'a bani ba aban number waya."

Wani kallan banza tamai ta juya.


Tundaga wannan rana kullum sai Adam yazo station dinsu, tun bata kulashi har yanda yake neman magana yake sata murmusawa.

A hankali ta fara fahimtarsa, ga saukin kai komai tace zaice to, a lokacin Zainab ta fara tunanin wannan ne? Dan dama so take ta samu mijin daya dace ta dawo da Nabila gunta.


Adam yana santa so sosai a iya saninta, wanda har tausayin halin da yake ciki yake damunta, hakan yasa ta nunamai aiki zai samu tunda ko wata biyar basuyi da gama karatu ba.


Soyayya mai karfi ce ta shiga tsakaninsu, Adam kanwarsa daya sunanta Sadiya kamar yadda muka sani, wacce ke zaune agun kanin Goggo, ganin Zainab ta samu wanda takeso yasa ta fara ginin gida.

Adam da kanshi ya dinga zama akan aikin har aka kammala....


Tausayin mahaifiyar sa da za'a bari ita kadai sannan da tunanin aikinta yasa ta nemi su tafi da Goggo.


Haka akai auransu dan ta fadamai abubuwa kadan daga rayuwarta, ya kuma nuna shi zai share mata hawaye.

Ta yarda da Adam tana kuma ganin duk duniya idan har akwai namiji daya dayake santa to lalai Adam ne.

Dady kam gaba daya yai sanyi dan tun mutuwar Ummy gaba daya ya canza, sai dai ba yanda zaiyi ya maida hannun agoggo baya, sosai yake san su dawo daidai da Zainab sai dai itakam inaaa matarsa ma kallo bata isheta ba.


Ta nemi a bata Nabila amma Dady ya bata hakuri akan ta barta anan, sannan Nabilan itama tace tafisa nan saboda Nusaiba.


Ganin karta sawa kannenta rayuwar kuncin da take binne dashi a ranta yasa bata taba tada zancen Ummy ba, Nusaiba da Nabila aka barsu a matsayin duka yayan Basma ne wacce itama dana sani da wulakancin da Dady ya fara mata ya dawo da ita hankalinta.


Haka Zainab ta bar gidan sai dai ko waya bata taba hadata da mahaifinta, sai dai ta tambayeshi a gun Nabila, shima yana tambayar Nabila ya Zainab.


Haka rayuwarsu take Zainab tunda ta fara aiki har wannan rana bata taka ko kofar gidansu ba.


Wannan kenan..........


{Mata wandanda suka sanar dani ta Pc da wadanda suki magana a grp akan auren cin amana da rabasu da mazajensu da akai suma, Allah ubangiji ya kara muku hakuri, ya ba mijinku ikon yin adalci a tsakaninku, ya kuma kareku da karewarsa Ameen.}


Allah yasa mu dace..........


Ayusher Ce🏌🏻‍♀[11/9, 11:19 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     ......................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


Page 19


Wani wahalalen kuka ne ya kubce mata toshe bakinta tai tanayinsa, ta dade a cikin dakin nan ba tare da ko fitila ta kunna ba, a hankalu ta taso ta turo kofar dakin ta fito.


Ba kowa a falan da alama sun shiga yin sallah ne, bangarenta ta wuce tana zuwa itama ta shiga toilet tai alwala.


Adam ne ya shigo tana kokarin tada sallah, Honey?

Juyowa tai ta kalleshi tare da yin murmushi, takowa yai a hankali zuwa inda take sannan yace "menene?"

Kai ta girgiza alamar ba komai, a hankali yasa hannunsa zai dauka a kan fusksrta, kauds fuskarta tai da sauri tace "ka dawo?"

Hannunsa ya maida ya sauke sannan yace "eh."

Hijab din ta karasa sawa sannan ta tada sallah, ta dade tana tasbihi kafin ta mike, kan gadonta hau ta kwanta.


Adam ya kashe laptop din ya matso yace "Honey kuka kikai?"

Bata juyo ba tace "a'a"

Ajiyar zuciya yai sannan ya fara danna mata kafafunta yana cewa "kinci abinci ne?"

Juyowa tai saitinshi a hankali tai wani lalaussn murmushi ta zubamai ido.


Kwanciya yai daf da ita suna kallan juna yace "Honey?"

Uhmmm


Shiru yai yana tunanin kalaman Sadiya, kallan Zainab yai yace "yaushe kika fara sona? Na dade inasan naji."

Murmushi tai har hakoranta suka fito tace "abinda yazo ma kenan?"


Kai ya daga alamar eh shiru tai tana tunani kafin tace "sanda kacemin ka fara sona saboda kudina?"


Dariya yai sosai harda mikewa ya zauna, tace "Da gaske nake."

Tsagaitawa da dariya yai sannan yace "yaushe na fadi haka?"


Tace "ka manta? Zuwanka station dinmu na hudu?"

Fuska ya rufe yana dariya yace "lalai Honey, wai dagaske lokacin kika fara sona?"


Tace "eh"

"Na dauka fa fada zakimin lokacin kinsan a rana kika fara min murmushi?"


Dariya tadanyi tace "am serious lokacin na fara maida hankali kanka, at least u are honest, nasan bazaka taba yaudara ta ba."


Jawota yai ya rungume a jikinsa, murmushi tai tace "kace Sadiya ta koma dakinsu Nabila."


Dagota yai ya kalleta, tace "badai ce mata zakai ta tafi gobe ba ko?"


Shiru yai yana kallanta fuskarsa dauke da nuna jin dadi, tace "ka barta tai 2weeks kaga dai bata taba zuwa ba."


Murmushi yai cikin gamsuwa.......


************


  Fitowa falo yai ya zuba mata abinci, Goggo dake xaune ita ma tana cin abinci ta bishi a harara sannan tace "batada hannu ne?"

Cikin falan ya shigo rike da plate, Sadiya dake zaune tayi shiru ya kalla sannan ya ce "Goggo to nawa ne."

Kaine zaka zubo abinci dan haka? Kadaiji kiki gaba gaba ma a kitchen zan ganka kana tuka tuwo."


Alama yamata datai shiru yana nuna mata Sadiya, baki ta tabe tace "kunya kake ko me?"


Haushi ne ya kamashi ya kalli Sadiya yace "Ki koma Dakinsu Nabila da kwana."

Da sauri ta kalleshi sannan tace "Yaya."

Goggo ya kalla wacce ke zabgamai Harara kamar idanta zai fado yace "badai ni nace ba Zainab ce."


Juyawa yai da sauri, Goggo ta kalleta tace "kikace gobe zaki tafi? Idanunta ne suka ciciko tace "kiyi hakuri Goggo nima goben naso tafiya amma bangama registration dina bane."


Shiru Goggo tai kamar bazatai magana ba ta zuba maga ido sai cewa tai "badai bakyasan tafiya bako?"


Da sauri ta kalleta tace "Goggo!"


A'a inba haka bane bar maganar, karki faramin wannan hawayen.


Sadiya tai kasa dakai tana share hawayen.

Mikewa tai ta dauko yar jakarta tayima Goggo sai da safe ta shiga dakinsu Nabila, tana shiga ta cilar jakar kan gado sannan tabi kofar dakin da harara, wannan mata.... tai kwafa.


Wayarta babba ta dauko ta fara dane danen ta tana chatting.....


Wajen karfe 12 na dare Zainab na bacci yaji wayarsa tai kara alamar text.

Idanunsa ya bude sannan ya jawo wayarsa, Yaya....

Abinda kawai ya gani kenan, number ya kalla, baisanta ba hakan yasa yai duba log din sa, ganin ya kira wayar yasa ya mike da sauri ya fito.


Knocking din dakin Sadiya yai a tsorace yana fatan Allah yasa ba ciwo bane ya kamata har ta kasa rubuta mai text.

Nishi yaji daga ciki wanda ya sashi hanzarin bude kofar, tana kwance da vest a jikinta da skirt din dazu, tanata murkusus akan gado.


Da sauri ya karasa yace "Sadiya lafiya? Meya sameki haka?"


Yai maganar cikin tashin hankali, Bayana yaya bayana zai balle, tana fada tana kuka cikin tsananin ciwo.


Sadiya tashi kisa riga muje asibiti, dan dagowa tai gaba daya rabin kirjinta ya fito, da sauri ya dauke  idansa daga kanta, ya hadiye yawo yace "daure ki tashi muje asibiti."


Mikewa ya nemi yi da sauri ta sa hannu ta kamoshi, juyowa yai da sauri, tace "yaya ka tausayamun."


Yanda idanunta sukai jaa yanayinta duk ya canza ga hawaye datake yi yasa tausayinta ya kamashi? Tace "dan Allah yaya ka bubugamin tsakiyar bayana, dan Allah kafin na mutu."


Baya? Ya fada cikin mamaki, luuu tai da idanunta kamar mai shirin suma ta fara wani farfar da idanunta kamar mai aljanu, Adam baisan sanda ya fara bibaga mata bayan ba.


Can ta saki wani nannauyan ajiyar zuciya, sannan ta rike hannunshi dake bubugawa.


A hankali ya zare hannunsa sannan ya mike tsaye yace "ya daina?"


Ta daga kai tace "nagode Yaya."


Shiru yai yana kallanta, tace "ya akai?"

"Bakomai" yace sannan ya mike da sauri yace "ki huta."

Nagode yaya ta fada tare da kara dagowa kirjinta ya kara bayyana.


Da sauri ya fita daga dakin, yana fita ya furzar da wani iska tare da ajiyar zuciya, shiru yai.


"Ya Adam ina asibiti ciwon baya nane ya tashi."


Shiru yai bayan ya tuno wannan kalmar, da sauri ya girgiza kai tare da komawa dakinsu.


Yana fita Sadiya ta kwanta sosai tare da yin dan tsaki, sannan ta kira saurayinta video call.


*************


A daidai station dinsu yai parking, kallanshi tai kafin ta fita tace "yamai jikin?"

"Da sauki"


Okay, kawai tace tai shiru dan so take taji ko an sallameshi tunda bai fada mata ba ta ina zata kara tambaya?


Harta bude kofa yace "yana asibiti, mungode sosai."


Juyowa tai ta kalleshi sannan tace "to."


Kayanta ta kwasa tai waje.


Tana shiga taga Ramlatu a bakin kofar office dinta, bata ce mata komai ba ta bude ta shiga, knocking tai sannan tadan tura kofar a tsorace.


Zainab na zaune tana duba abu a computer din dake gabanta, tea dinta ta kurba sannan ta kalli Ramlatu kadan.


Shigowa tai jiki a sanyeye tace "Na gama."


Zainab ta mata alama data ajiye ta fita ba tare da ta ce mata komai ba."


Jiki a sanyeye ta ajiye ta fita, waya ce ta shigo ta dauka, director ne yace "ya maganar daukan staffs din nan? Kinsan na fadamiki zamuyi transfer din wasu zuwa kaduna."


Tace "wannan karan ni zan dauki ma'aikata dakaina ranka ya dade, in kuma baka aminceba bazansa baki ba kowa ka kawo."


Haushi ne ya kamashi, dan dai duk wani hanyar samun kudi itace ta kawo musu idea din kuma ita ke wucewa gaba amma da tuni ya kori yar rainin hankalin nan.

Zainab cikin gadara tace "mekace?"

Dariya yasa yace shikenan ai yanda kikace hakan za'ai, tace "zan ware wadanda za'akai kaduna."


"Ha'a shima ke xakiyi? Wannan ki barshi ni xan ware dakaina."


Kamar zata ce a'a sai kuma tace "okay."

Ta kashe wayarta.


Aikinta ta cigaba dayi ta fito tana duduba programs, editing da sauransu.


Khalid dake zaune ne ya kalli wayarsa, fitowa yai ya nufi cafe, yana shiga ya duba aikin da aka turo, shiru yai yana tunanin yaje test din? Dan yasan koyaje ma ba samu zaiyi ba, sai dai kasan ransa na bashi yakimin ya sake gwadawa komai na Allah ne.


Wata babbar mota wacce kallo daya zaka mata kasan ta jika da kudi ne tai parking ata gefensa kadan, da sauri driver din ya zuge glass din mota yace "bawan Allah a aina gidan Tv din Muryar Arewa yake?"


Khalid yace gashi can, ya matso yana nuna musu, driver din yace dan Allah in ba damuwa ko zaka rakamu?"


Am sorry gaba zakai sai kai kwana zakaga sign dinsu.


Mungode.


Ya koma yaja motar.


Mutumin dake zaune a baya ne yai shiru, babban mutum ne, ya rasa meyasa kwanan nan mafarkinta kawai yakeyi, yana tunanin lalai lokacin da zai daidaita tsakaninsu yayi, koda bazata yarda dashi ba yana ganin dolene ya nemi yafiyarta, shiyasa ya nemi su Nabila su dawo dan yana tunanin ganinta, dan mafarkin dayai jiya ya tada mai hankalin sosai wanda yasa yau da dsssafe ya nufo garin na kano.


Sun isa suka tsaya driver din yace "a aika tazo?"


Yace "a'a kabarta ta fito naga sun kuds tashi."


Hango Khalid sukai ya nufo gun, cikin mamaki driver din yace "Ashe anan yake aiki."


Khalid ya wuce ba tare da yace musu komai ba, sai data gama tsara takardar Application na daukan ma'aikata da zasuyi sannan ta fito.


Tana fitowa ta nufi motarta ta shiga, tana rufe kofa driver din nan ya kwankwasa.


Kallansa tai cikin mamaki tace "Mamman?"


Da sauri ya gaisheta yana dariya, Khalid ya kalleshi ya dauke kai.


Mamman yace "Tare muke da Yallabai!"


Yallabai? Tai tambayar jinta banbarakwai.


Yace "eh yau haka kawai yace muzo yanasan magana dake."

Juyawa tai ta kalli motar, sannan tace "in aiki ne ya kawoku ku gams ku tafi Allah ya kiyaye hanya."


Ta rufe kofa tace "muje."


Khalid yaja mota cikin mamakin abinda ke faruwa, suna gaba suna binsu a baya, Khalid yace "koma wanene tunda ya taso yazo ki tsaya ku gaisa ma........"


Cikin fada tace "a matsayinka na wa?"


Mamaki ne ya kamashi ya juyo da sauri yace "me?"


Tace "amatsayinka nawa kake neman sani abu? Aikinka tuka mota kai abinda ya dameka, tunda shi kazo yi."


Wannan kalmar ba karamin batama Khalid rai tai ba, mutuncin abinda tamai ne yasa ya daure sai dai ya juyo ya mata wani kallo.


Tace "me? Dan mahaifina yazo ganina sai ya zama dole sai naje?"


Mahaifi? Abinda ya maimaita kenan, cikin bacin rai yai parking.


A zuciye ya bude mota ya fito ya bude kofar inda take zaune yai wani murmushin bakinciki, ya kauda kai yace "da na dauka nine ban fahimci kyawawan halayenki ba. Tuki nake?"


Ajiye key din hannunsa yai yace "gashi nan, sai ki nemi wani mai tuken, dan banaji zan iya tuka wacce batasan darajar mahaifinta ba."


Ranta ne yakai kololuwa gun baci fitowa tai ta tsaya tace mene?


Bai tanka mata ba sai gaban mota daya bude ya dau jakarsa, kudin aiki na danai zan turama Adam account number dina.


Da sauri tace "Dawo nan."


Kallanta yai rai a bace ya nufi motar dake gefe zai wuce wanda suma sukai parking.

Da sauri Dady ya fito ya tsaya gabansa yace "ya akai?"


Khalid yace "bakomai ina wuni?"


Dady ya amsa sannan yace "naga ka barta a hanya ne."


Kallansa khalid yai tare da yin kasa dakai, Dady cikin sanyin jiki yace "kayi hakuri dan Allah, da alama saboda ni ka ajiyeta, ka tsaya anan zan mata magana, amma dan Allah kar saboda ni ka ajiye aikinka."


Shiru Khalid yai jikinsa yai sanyi, haushin Zainab ya kara kamashi.


Dady yai murmushi yace "na mata laifi ne shiyasa take haka, karka damu."


Khalid yai shiru yana kallan Dady ya nufi motar.


Zainab na ganinshi ta shige cikin mota, zuciyarta cike da al'amari kala kala.


Bude bayan motar ta daya gefen da take zaune yai.


Kanta na jikin window bata juyoba.


Zainab!


Sunanta Dady ya kira wanda yasa idanunta yin rawa suna neman yin rauni.


Zainab!


Juyowa tai cikin fada kasa magana tai sai motsa baki kawai datake yi idanunta suka ciciko....


***************

Goggo ke zaune tana hada jaka, sai zuba kaya take kai kace wani gari zataje.


Sadiya dake gefenta a daki tace "ni goggo sati zakiyi acan ne?"


Sati kuma? Gobe zanje da safe in dawo da yamma sai kuma jibi muje dinner


Sadiya cikin dabara tace "ki kwana acan Goggo kinsan kwana da biki yafi komai dadi."


Goggo ta kalleta tace "da gaske?"

"Ku zauna kusha hira sannan ku shirya daga can kuje dinner kinga da daddare sai ki dawo."


Kallan mamaki Goggo ta mata tace " ke da bakya magana yau bayanin na menene?"


Sadiya tai kasa dakai tai shiru, Goggo ta kalleta tace "ni lalen da yan mata keyi manya bamayi ko?"


Sadiya a ranta tace wannan mata, amma a fili tace "sunayi amma sai dai jaa."


Goggo tace "to ni ina zani ma gidan lalai babba dani."


"Indai lale kikeso na iya sai dai ba sosai ba."


Cikin jin dadi Goggo tace "haba?"


Eh bandai iya sosai ba amma lokacin a gida ina yima Yayata.......

Ta kai karshen maganar cikin wani yanayi na damuwa.


Goggo ta kalleta tace "ya akai ta rasu ne?"


Da sauri Sadiya ta mike tace "Bari na shiga toilet."


Ta fito daga dakin.........


******

Ayusher🏌🏻‍♀

*****

[11/9, 11:19 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     ......................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


Page {20}


  Kallansa ta juyo tasakeyi, idanunta ne suka fara rawa, tausayinta ne ya kamashi yace "Zainab."


Idanunta ta runtse wasu zafaffan hawaye ne suka digo a kasan idanunta ta bude su tare da saukesu akan Dady tace "sai yanzu? Sai yanzu? Kasan sau nawa ina jira akan kazo ka fuskanci yarka kuyi magana?"


Kallan mamaki ya mata, yace "Zainab."


Shiru tai tare da juya kanta jikin window, yace "akoda yaushe ina tunanin samunki muyi magana sai dai ina tunanin karna kara taso miki da mikin da kika samu ya bushe.

Na sani ban kyauta ba na sani abinda nai abu ne na halayen dabobi, sai dai nayi nadamar hakan, bansan meya sameni a lokacin ba, hakan yasa itama wacce ta kawar da hankalina akan matata na bata nata kakkarfan hukuncin wanda har abada bazata sake ba wani shawarar yin abinda tamin ba."


Yanzu kam ta juyo ta kalleshi tace "matar da kuke zaune lafiya tana cikin daula har wani hukunci ka bata daya kai na sa Ummy cikin kunci?"


Shiru yai yana kallanta a ransa yace "na sa an tsaida haihuwa ta har abada sai dai ta zauna da 'ya daya, wannan shine hukuncin ta."

Amma a fili murmushi kawai yai tare da kallanta.


Zainab cikin takaici tace "Ummy harta rasu batasan wannan cin amanar daka mata ba."


Yai shiru jikinshi ya kara sanyi yace "na sani Zainab, ki yafemin abinda na muku."


Yanda ya fadi kalmar ne yasa ta dake tace "Sau nawa kasan ina jiranka a dakinmu akan kazo muyi magana? Sau nawa kasan 'yarka na cikin wani yanayi da take neman taimakon mahaifinta? Sau nawa kasan wannan marainiyar tana kin cin abinci saboda tana tunanin mahaifinta zaizo ya sata taci dole? Sau nawa nake dauke Nabila na shiga da ita daki dan kawai ina fatan Mahaifina zai nemi shigowa? Sau nawa.........."


Muryarta ce tai rauni saboda yanda ta tuno abubuwan datai tayi saboda tanaso Dady yazo gareta suyi magana, ko a skul aka bata mata rai inta shigo a gabanshi zatace bazataci abinci ba ta wuce daki saboda tana fatan ai tasan Dady zai shigo.


Baki ya bude yana kallanta tare da girgiza kai cikin tsananin tausayinta, kenan duk abinda take saboda ya dubeta takeyi?


Hannunta ya kamo yace "Zainab!" Cikin rauni yai maganar wanda kawai tasa kuka........


Shi kanshi hawaye yakeyi, yace "Kiyi hakuri Zainab, ni in naga kina haka tunani nake kawai bakya san zama inda nake ne."


Ta dago idanunta da sukai jaa, tace ko hakan ne a matsayinka na mahaifi bazaka tsawatarmin ba? Ka taba tunanin wannan 'yar taka da batada uwa tana bukatar mahaifinta?


Dady idanunta ne suka kara fitar da kwalla ta tsananin dana sani, yace "Zainab."


Shiru tai kafin tace "kasan dalilina na yin aiki a nesa?"


Kallanta yai da sauri, tace saboda duk yanda nasa rai da zaka tunkareni kaki, hakan yasa na nemi aiki a nesa nasan inkai rashina tabbas zaka neman, yau shekara nawa da aure?"


Inalilahi wa Ina ilaihi Raji'un abinda Dady ya fada kenan cikin tsananin nadama.


Hannunta ta zare sannan ta share hawayenta tace "sai yanzu? Dakayi zamanka da iyalanka da hankalin kowa yacigaba da kwanciya."


Shiru yai dan gaba daya zuciyarshi ta gama karaya baima san me zaice ba, a hankali yace "Kiyi hakuri Zainab bakiyi sa'ar mahaifi ba, me yasa baki sanar dani ba? Ke macece mai fadar ra'ayinki, meyasa baki nunamin ni kike jira a koda yaushe ba?


Shiru sukai kafin can harya dauka bazatai magana ba yaji tace "Ummy."


Kallanta yai yace "Zuwaira?"


Hawayenta ta maida tace "kafin Ummy ta rasu ta riko hannuna tace "Zainab ga kanwarki nan, sannan wannan abin da mahaifinki yakeyi karki sashi a ranki, ba halinsa bane kema kin sani, mutum ne dayafi sanki akan kowa a duniya, na tabbatar zai zo ya sanar dake hakan, kiyi hakuri ki cire komai sannan ni ban rikeshi ba na kuma yafemai."


Tana kaiwa nan tasa kuka tana cewa "Ummy ta dauka da wuri zaka sanar dani, me yasa kadau wannan lokacin?"


Kuka take sosai wanda gaba daya jin kalaman Ummy yasa kansa ya fara wani irin sarawa, shiru sukai a cikin motar ba wanda ya iya cewa komai.


Ganin halin da Dady ya shiga ne yasa Zainab ta kalleshi tace "Dady!"


Kallanta yai kamar baya hayyacinsa, bai iya cewa komai ba sai idanunsa da sukai wani irin jaaaa.


*********


Mamman ne ya kalli Khalid yace "Aiki kake ma Zainab?"

Eh kawai yace.

Mamman yai murmushi yace "da alama baka jin dadin aikin, ko da yake Zainab mai mata aiki sai ya shirya." Yai dariya yace "Allah sarki harna tuno lokacin da Mamanta ke darai, yarinya mai san mutane da fara'a ga saukin kai, komai aka mata batajin haushi ."


Kallansa Khalid yai cikin mamaki, Mamman yai dariya yace "baka yadda bako? Tun bayan rasuwar mahaifiyar ta ne ko? Ahh tun sanda Mai gida yai aure ne ta fara canzawa."


Khalid yai shiru yana tunani, Mamman yace "ahh sorry ina ta ma zuba baka sani ba."


Shiru yai bai tanka ba sai dai yayi shiru yana tunanin kalaman daya zabga mata, da alama akwai abinda ke tsakaninta da babanta.


*********


Sun dade a haka kafin Dady ya dawo hayyacinsa, murmushi yamata ganin yanda hankalinta ya tashi ganin halin a a shiga, yace "kije gida ki huta, zan dawo wani satin."


Tausayinshi ne ya darsu mata wanda tun bayan rasuwar mamanta yauce rana ta farko dataji haka, tace "Abuja zaka wuce?"


Yace "eh"


Kai ta daga alamar to, shiru yai kafin yace "tunda gobe asabar zan kwana a hotel in yaso gobe mu hadu."


Kallansa tai batace komai ba, wayarta ya dauka a gefensa yafara sa numbersa gani yai Dady ya fito a jiki, bai taba tunanin tanada numbersa ba, da sauri Zainab ta amshi wayar, Dady yace "zan kiraki gobe."


Kai ta daga a hankali, fitowa yai daga motar ta bishi da kallo, tana goge fuskarta.


Motarsa ya nufa, Mamman ya bude mai da sauri, Khalid ne ya gaisheshi, Dady cikin jin dadi ya dafashi yace "Nagode sosai, badan ka tsaida ita ba da bansan sanda zamu fahimci matsalar dake tsakanin mu ba."


Khalid yai kasa dakai, Dady yace "kayi hakuri ka cigaba da aikinka."


Khalid yace "Insha Allah."


Har ya fara tafiya Dady yace "Bawan Allah."

Khalid ya juyo, kudi ya zaro mai kauri dan a kalla zaikai dubu goma ya mika ma Khalid, da sauri Khalid yace "nagode amma ka bar kudinka, Allah ya saka da alkairi."


Khalid ya juya ya tafi, Dady ya binshi da kallo cikin gamsuwa da mamakin halayensa.


Khalid na zuwa ya tsaya a jikin kofarta, haryakai hannu zai yi knocking yaga ta sunkuyar da kanta da alama kuka takeyi, hannunsa ya sauke ba tare da ya kwankwasa ba, tadan dade tana kukanta kafin ta share hawayenta, ganin duhu yasa ta kalli jikin window, kofar ta tura, wanda hakan ya bige Khalid.


Juyowa yai da sauri jin an bugeshi, fuska ta hade tace "Oh sry ashe da mutum."


Tsayawa yai yana kallanta dan ya tabbatar da saninta."


Matsawa yai sannan yace "key din."


"Key? Kace in turoma albashinka account?"

Shiru yai baice komai ba, harararsa tai sannan ta dau key din ta cila gun zamansa.


Kallanta yai kamar zai sake magana sai kuma ya fasa, budewa yai ya shiga yaja suka tafi.


Tunda ya fara tafiya tasa kanta a jikin kofar batace komai ba, har ya isa gida.


Jakarsa ya dauka zai fita tace "gobe kazo wajen 2 zaka kaini wani gun."

Okay kawai yace ya fita, ita kuma ta shiga ciki.


Goggo ta gani zaune a falo tana kallo, gefenta kuma plate ne da akaci abinci, hannunta rike da lemo ta bare tana sha.

Sadiya na gurin kafafunta tana mata lale.

Sallama kawai tai tace "Goggo sannu da gida." Tai ciki

Sadiya tace da dawowa.


Baki Goggo ta saki tace "wannan 'ya kwai yar rainin wayau, in tsohuwarkice kya cemin sannu da gida ki tafi?"


Sadiya ce ta juya dan ta dauka da Zainab din take, ganin ba kowa agun yasa ta guntse dariyarta.


Goggo ta harareta tace "ki tabbatar kin gama abinda zakiyi littinin ki tarkata ki bar gidan nan dan wlh in tsautsayi yasa Zainab tasan bamuda hadi dake Allah ne kadai zai kwaceki dake da waccen sokon."


Sadiya dai batace komai ba, ana gama mata lale ta shiga dakin ta.


Wayarta ta dauko tace "Gobe zata tafi gun biki, bansan wannan matar ko zata zauna a gida ba, amma kai ka shigo da yamma, in kaga text dina, in baka gani ba karkazo, kadai rike abinda na ce ma kafada ko?"


Yana dariya yace "ba dole ba, amma ni wai haka zakiyi ta bari........."

Kashe wayarta tai tare da jan tsaki.


Zainab kam tana shiga daki tai sallar magrib ta kwanta akan gado tare da lulube bargo a kanta, shiru tai tana tunani.


Adam ne ya shigo wanda yaje aiken Goggo na siyo mata takalmi.

Yana shigowa ya ganta a baje a falo tasha dauren leda an mata lale.


Baki ya saki yace "Goggo? Meye hakan?"

Ta kifamai kallo tace "meye hakan kamar ya?"


Yace "wai ni Goggo meke damunki dan Allah, biki sai kace bikin 'yarki?"


Hade rai tai tace "kai bansan iskanci, kai kanka kasan ban taba zuwa bikin masu kudi ba sai wannan, na saba biki a kauye ba wani abin arziki, wannan kuwa da muka hadu da ita muka zama kawaye kai kasan yanayin gidansu ai, so kake naje a ganni daban?"


"Lalai Amma duk da hakan abin ai yai yawa."

Tace "abinda yai yawa ya wuce waccen kuliyar daka kawo mana, duk da yau na moreta amma nifa ka dauke 'yan nan, sam ni batamin ba wlh."


Yace "to ai litinin zata tafi."

Harara ta sake mai tace "dauke plate din nan kaban takalmin, matarka dan iskanci ko kallan arziki batamin ba yau."

Ke dai Goggo Allah neman maganarki yayi yawa, ta gaji ne.


Baki ta tabe ta fito da takalmin tana gani.


Adam ne ya kalli dakin da Sadiya take sannan ya wuce dakinsa.


Zainab na kwance cikin bargo ya shiga.


"Honey? Bacci?"

Ya fada yana lekata, idanunta ta rufe tana jin motsinsa.


Murmushi yai sannan ya sake fitowa ya zauna a falo.


*************


Abba ne cikin jin dadi ya kalli Khalid yace "an dawo?"

Eh Abba ya jikin?

Abba yai dariya yace "kana gani kasan Alhamdulila ai, ka mika mana godiyar mu dan Allah."


Umma tace "zan mata wainar gero ka kai mata, dansu masu kudi bansan me sukeso ba."


Wainar gero? Ya maimaita

Umma jiki a sanyaye tace bataci?

Da sauri yace "a'a kiyi sai na kaimata."

Cikin jin dadi tace "to."


********


Yau tun wajen karfw 9 Goggo tai wanka, ta saka doguwar rigar da aka mata, zama tai ta shafa mai tasa hoda da kwalli, jakarta ta zuge sannan ta dauko takalminta ya fito.


Sadiya dake kitchen tana gyarawa taji Goggo tace "ke zo dauran dan kwallin nan."


Sadiya ta taho da sauri, tace "Goggo kinyi kyau."


"Na sani ai, dauran ni."

Ta mika mata, zama tak a falo Sadiya ta daura mata, sannan tace ina Adam?

Banga ya fito ba Goggo.

Tsaki tai tace wannan uban sakalan hala yana can yana asarar.


Kwankwasa kofar dakin ta shiga yi.

Zainab dake zaune tana tura takardar daukan ma'aikata, ya mike.


Goggo ta kalla cikin mamaki, tace "Goggo irin wannan gayu?"

Kan Goggo ya sake fashewa tace "ina wannan lusarin? Yazo ya mikani dan Allah."


Zainab ta kalleshi wanda jin kwankwasawa ne ya sa ya bude ido, murmushi tai tace "bari yazo Goggo, ina kwana?"


Baki tadan tabe tace "sai yanzu?"


Zainab tai dan dariya tace "ban baki kudin gudun mawar bako?"


Da sauri Goggo ta washe baki tace "Eh wlh, ganin abubuwa sun miki yawa ne yasa na kasa tuna miki."


Zainab ta koma ciki ta dauko wallet dinta tace "nawa zaki bata?"


Yanda kika bada, sai dai a can zan kwana.

Mamaki ya kama Zainab sai dai batace komai ba, ganin ba kudi sosai a wallet din yasa tace "bari naba Honey sai ya ciro ki bata dubu ashirin sai ki rike dubu biyar saboda sha'ani.


Ai wani dadi Goggo taji tace "Kai Zainab Allah ya kara miki girma, ya miki albarka, wannan 'ya akwai sanin darajar mutum wlh, ni sai naga ma kamar kin dan canza ko bakya jin dadi ne?


Adam daya fito daga toilet ne ya guntse dariyarsa yace "gaskiya ne Hajiya Goggo taga bugun Abuja zata fara kodaki."


Fuska ta daure tace "kayi shiru anan ko kuwa????"


Sadiya dake tsaye tana jinsu ta tabe baki sannan ta fara tunanin, Zainab zata fita dai ko? In ba haka ba komai nata ya wargaje ai.


**********

Ayusher🏌🏻‍♀

**********

[11/9, 11:19 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     ......................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


Page 21


Goggo ta gyara zaman mayafinta tace "ka fito ko sai ranka ya baci?"

Zainab ce ta fito ta maida kofar dakin tace "bari ya shirya Goggo.


Washe baki ya sakeyi tace "Tunda dai ke kikai magana bari na jirashi."


Kallan takalmin kafarta tai mai irin dan dunduniyar nan ne tace "Goggo zaki iya tafiya da takalmin nan dai ko?"


Haushi ya kama Goggo a ranta tace "tunda ba tsohuwar ki bace dole ki yaban magana, amma a fili dariya tai tace "ba matsala zan iya."


Zainab ta kalli dinkin dake jikinta kai kace dinki yan mata, rigace doguwa amma anmata ado da design da ake yayi, da alama ita tasa mai dinki yi mata irin na 'yan mata.

Goggo ta kalli Sadiya dake tsaye a jikin kitchen, tace "ni hadomin shayi nasha kafin ya gama kalular tasa."

Ta wuce ta zauna akan kujera.

Zainab ta koma cikin daki tana guntse dariyarta.


Tana shiga tasa dariya, Adam da ya sa vest ne ya kalleta yace "Honey ke da Goggo ne ko?"

Da sauri tace "ya akai ka sani?"


Dariya yai shima yace "ke abinda ke saki dariya ai yanada wuya, yau kuwa tunda naga Goggo nasan sai ta saki dariya."


Zainab ta karasa dariyarta tace "kai ni Allah yasa kar 'yan gun bikin su mata dariya."


Adam yace "ah to ita ta sani, amma honey dubu ashirin da kikace a bata na gudun mawa, ai goma ma tayi."


Hade fuska tai tana kallanshi tace "ka cinye kudinka kenan?"


Yace "ban cinye ba."


Tace "ka bata hakan takai, kaga dai yanda suke da uwar amaryar."

Shiru yai yana gyara fuskarsa, tace "nasan tunda ka furta Allah sai ka rage, zan turoma 10k, nima ba kudi a account din.


Wani irin dadi ne ya kamashi ya matso ya fara sumbatarta a fuska ta ko ina.

Kafin ya juya ya fita.


Murmushi ta bishi dashi sannan tai shiru tana tunanin mahaifinta.

Wayarta ta jawo ta duba, ganin bai mata text ba yasa ta ajiye tare da yin ajiyar zuciya.

Laptop dinta ta kara jawowa ta shiga aikinta.


*********


Adam na fitowa Goggo ta bishi da harara tace "kaga dama?"

Yace "inkin gama tashi in kaiki."


Cup din ta mikawa Sadiya sannan tai waje, takai jikin kofa takalmin ya dan gurde kadan, waskewa tai tai saurin fita.


Sai da ya bata kudin duka ta sa a jaka sannan suka nufi gidan biki


********


Wajen karfe 11 wayarta tai karan text da sauri ta dauko wayar, ganin sunan restaurant din da zasu hadu da karfe 3 yasa ta saki murmushi, grand central hotel ya sauka kenan.


Kallan wayarta tai sannan ta cigaba da aikinta, sai 12 ta fito.

Kitchen ta shiga taga komai a gyare, murmushi tai saboda tasan Sadiya ce, nan ta fara yin abinci.

Sadiya dake daki a kwance tana waya ne taji kamshin abinci, yau kuma? Badai ba fita zatai ba?


Shiru tai tana tunani kafin ta dan mike ta fito.

Zainab na kitchen tana ta aiki ta shigo.

"Aunty aiki kike baki kirani ba?"


Zainab ta kalleta tace "wannan ma da kikai ya isa kije ki huta."


Cikin dabara tace "fita zakiyi ne Aunty? Naga ko abincin safe bakici ba."


Zainab tace "eh wlh zan fita anjima kadan shi yasa."


Dadi ne ya kama Sadiya wanda har batasan fuskarta ta bayyana hakan ba.

Sai ji tai Zainab tace " zakiyi wani abin ne?"

Gabanta ne ya fadi, ta kalleta da sauri tace "a'a"

Tana fada ta wuce ta fara yanka albasar da Zainab ta fito dashi.


*********


Umma ta kammala sa wainar a flask sannan ta amshi kulin da Asiya ta daka ta zuba sannan ta rufe.


Asiya ta kalla taci " kinci? Komai yaji?"

Dariya tai tace "Umma komai yaji sau nawa za'ai dandanen nan?"


"To sai me za'a hada mata dashi?"

Bansani ba wlh sai dai ko mu tambayi Yaya me takeso.

Shigowarshi ce tasa suka kalleshi a tare, Khalid ya karaso sannan ya ajiye ledar kwanon abincin daya dawo dashi.


Ya gaida Umma sannan yace "Umma bari nai wanka na wuce,"


Tace to Khalid, amma nikam bayan waina me Hajiyar takeso? Kallan mamaki yama Umma yace" ina zan sani nikuma?"


Ya ja ruwa ya wuce toilet, yana fitowa ya sa kaya ya shigo ya dau ledar flask din yai musu sallama, harya juya Umma tace "wai haka zakai ta sintiri daga kano zuwa nan?"


Yace "bakomai Umma hankalina yafi kwanciya a haka."


Jiki a sanyaye tace "shikenan Allah ya kawo mafita mai kyau."


Khalid yace Ameen sannan ya fita.


Yana zuwa ya hu mota suka dau hnyar kano.


**********


Wani hadaden lace ta dauko wanda ita kanta sau daya ta taba sakashi, lace ne wanda ta saishe mai tsada sosai sannan an mata dinkin ya mata kyau sosai sosai, tana gaban masubi tana kwalliya Adam ya shigo.


Wow gaskiy Honey kinyi kyau ina zaki?


Tace "zan dan fita ne kadan akwai wanda zan gani ne."


Fuska ya hade yace "namiji ne?"


Eh!

Tace tana sa kwalli, ni gaskiya ki canza shiga, juyowa tai ya kalleshi tana dan murmushi tace "nifa dadi na dakai wani sa'in shirirta yanzu ni waxan gani da aurena?"


Xama yai a bakin gadon yace "to ai ni kin min kyau ne dayawa."


Shiru tai tana kallanshi a ranta tana tunanin, Adam duk yanayin da take ciki bayantaba fahimta, abinds yasa gaba kawai ya sani.


Menene?

Kai ta girgiza alamaf a'a sannan tace "ba dadewa xanyi ba Honey, nayi abinci yana kitchen."


Da sauri yace "oh mu biyu ne a gidan?"

Yanda yai maganar ne yasa ta kalleshi tace "eh kai da Sadiya ne, amma nima ba dadewa xan can ba."


Dariyar yake yai yace "eh ba matsala nima bacci zan."


Tace "shikenan, Abokinka yazo?"

Yace "banganshi ba dai."

Okay, kace ya turo account details dinsa kafin watan ya karasa."


Dariya yai sosai wanda har Zainab tace "menene?"


Cikin dariya yace "kai duniya labari, kinsan in na tuno yanda yaran nan yake lashe mu a skul sannan duk wani abu na departments din mu shi ake sawa sai naji dariya tana zuwa min, kinsan dariyar da abokanan mu suke mai?"


Fuss ta hade sosai tace "na wuce."


Fitowa tai, tana bude kofar falo yana bude kofar gate.


Mota ta wuce ta bude da kanta ta shiga ta zauna, wayarta na rike da hannunta.


Karasa yai ya shiga sannan ya kalleta ta glass kafin ya tada motar.


Tace "menene?"


Leda ya juyo ya mika mata, cikin kunyar maganar yace "bansan ko kina ci ba, Umma ce ta dage sai an kawo miki."

Amsa tai tace "Allah sarki, nagode kuwa."


Mamaki me ya kamashi dan bai dauka zata amsa ba.

Shiru yai sannan ya tada motar yace "ina zamu?"


Grand Central Hotel, ta fada tana bude flask din.


Waina? Abinda ta fada a ranta kenan, sannan ta maida flask din ta rufe.


Shiru sukai har sukai nisa, can ta daure tace "hmmm nace aikin gidan tv."


Kasancewar baisan dashi take ba yasa yace "me?"

Shiru tai bata kara magana ba, hakan yasa yasan bada shi take ba, har sai da suka isa sannan yai parking, shiru tai maimakon ta fita, shima shirun yai batare da yace wani abin ba, taya zata ce mai?


Daurewa tai tace "nace site din gun aiki na ka duba in kana sha'awar aikin mu."


Tana kai nan ta bude kofa da sauri ta fita, sai da ta fita ya fahimci me take nufi.


Fitowa yai shima yabi bayanta.


Meye yake bina? Abinda yazo mata kenan, ganin alamarsa datai a bayanta.


Wayart ta dauko ta kira number Dady, ringing day ya dauka tace "nazo ina kasa, yace "ki tsaya a reception yanzu zan sauko."

To tace sannan ta juya ta kalli Khalid.


Kallanta yai shima sannan ya tsaya a inda yake, tace "ina zaka?"

I thought zan rakaki na dawo ne.


Are u my bodyguard?


Kasa amsa mata yai, ta juya tai gaba.


Juyawa yai ya koma mota.


Ita kuma tai ciki.


Yau ce rana ta farko a iya saninta wanda ganin mahaifinta yasata sakin fuska sosai, a da sanda yana zama da ita duk tana yarinya ne bazata iya cewa ga yanda takeji ba amma yau ganin sa yasa tasan tabbas tayi rashin mahaifinta dayawa.


Tare suka shiga gun cin abincin, suna tafe yana tambayarta Adam da nahaifiyarsa........


*********


Ihun da Adam yaji ne yasa ya zaburo da gudu daga daki daya baje yana kallo a laptop, yana jiran bacci ya kwasheshi.


Falo ya fito yana neman ina ne yaji ihun, sake ihun akai wanda ya sa ya nufi kitchen a sukwane.

Sadiya ya gane durkuse a kasa rike da kafarta.


Hankali a tashe ya nufeta, ganin abinci a kasa ya fahimci zubo mata abincin yai tunda ga kafarta nan duk abinci.


Baima san sanda ya rike kafadarta ba ba yana cewa "lafiya? Garin yaya?"


Baya tai ta fadi kasa shi kuma yabita ya fada kanta.


Idanunta ta rufe hankali a tashe ya dago yana kiran sunanta.


Sadiya kam kam ba alamar mosti, da sauri ya kinkimeta yai dakin ta da ita, ya kwantar da ita akan gado, saitin fuskarta ya sako kansa yana bubuga fuskarta.


Jiyai an jawoshi kafin yai auni tasa bakunta cikin nasa.


Kokarin kwacewa ya shiga yi sai dai yanda take mai salo da harshenta a cikin bakinsa yasa gaba daya jikinsa ya gama mutuwa, baisan sanda shima ya fara maida mata ba.


Sun shiga wani yanayi kai kace balle harshensu da kabansu zasuyi tsabar tsotso, juyo da ita ai ya hau samanta suka cigaba da sumbatar juna, a hankali ta kai hannu saman kirjinsa wannan ya sa bude idanunsa.


Gabansa ne yai mugun faduwa, a zabude ya mike ya sauko daga kan gadon yana wani irin hakki, na tsatsar sha'awar dake cinsa."


Kallansa tai ta mike da sauri tace "ba mafarki nake ba dama?"


Hankalinsa a tashe yace "mafarki?"


Tai kasa dakai tana hawaye tace "mafarkin sha'awa, Inalilahi meya faru tsakanin mu yaya?"


Adam a tsorace ya juya yai waje.


Yana fita ta dau wayarta tace "yanzu."


Yace okay.


Ko minti goma ba'ai ba Bala yazo yana knocking.


Adam wanda gaba daya zufa ke karyomai ya fito ya bude kofar, bala yace "dama wani ne ke neman Sadiya."


Cikin mamaki Adam yace "Sadiya? Kuma Sadiya akace?"


Yace "a'a bakuwa akace."


Adam yace "au, wanene?"


Bala yace yana waje.

Kace ya shigo.

Ya fada yana gyara tsayuwarsa a jikin kofar.


Saurayin ne ya shigo cikin shadda da hula, ya gaida Adam sannan yace "naga wata yarinyane jiya ta shigo gidan nan shine na biyota."


Sadiya ta fita ne? Abinda yazo mai kenan.


Mutumin ne ya katseshi yace "dan Allah ina sallama da ita inba damuwa."


Sadiya ce ta fito kafin Adam yai magana sannan tace "Yaya kace ya shigo falo muji meya kawoshi ko?"


Adam ya kalleta gabansa na faduwa, sha'awa na kara taso mai.


Cikin jin haushi yace "ya shigo ina? Kai kayi hakuri ka koma ita bata sha'awar yin zance."


Saurayin zai sake magana Adam ya banka kofa cikin jin haushi sannan ya kalleta rai a bace yace "ke easy ce da ga ganin saurayi sai san ya shigo? Inya shigo ya nemi miki wani abin fa?"


Idanunta ne suka ciciko tace "in yamin ma menene? Ni a wannan lokacin so zanyi ma yamin saboa rashin abinda kake so yafi komai ciwo."


Kallanta Adam yai yace "me kike nufi?"


Hawayenta ta share batace komai ba, yace "kina nufin in saurayin nan ya shigo ya tabaki ba abinda zakiyi?"


Tace "eh, mai zanyi bayan a wannan lokacin abinda nakeso kenan?"


Mamaki ne ya kamashi yace "abinda kikeso?"


Ta kara share hawayenta tace "bantaba kiss da kowa ba sai kai yanzu kasan a wani yanayi nake ciki? Ji nake ko mai gadin can ne zai biyan bukatata zsn amince dashi."


Idanu Adam ya zaro, a tsorace ya juya zai koma daki, hannu tasa ta rikoshi da sauri.


Juyowa yai yace "Sadiya."


Tace "kai ka fara sani dan Allah ko kiss din ka karamin, ji nake kamar zanyi hauka, bantaba jin irin wannan yanayin ba."


Shikanshi sha'awar hakan yake, balle dama vest ne a jikinta duk saman kirjinta sun fito.


Baki ya shiga motsawa zuciyarsa na bugawa da karfi.


Ido ya runtse yana neman danne zuciyarsa amma kafin yai wani tunani ya sake jin bakinta cikin nasa.


Gaba daya jiyai komai yakunce mai balle dayaji wani irin salo wanda har tsakiyar kansa yakejin abim.....................

[11/9, 11:19 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     ......................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*💡 HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡*


*SANARWA TA MUSAMMAN DAGA K'UNGIYAR HASKE WRITERS ASSO.*


*Duka cikin littattafan wadan nan haziqan marubuta da muka soma tsakuro muku su guda biyar*


*LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DA SANYA NUTSUWA,KADA KI BARI AYI BABU KE*


*LITATTAFAN DA MARUBUTANSU SUNE KAMAR HAKA*


💡 *KAMAR DA WASA*


*Daga taskar*

*UMMI AISHA*


💡 *ZAFIN RANA...!*


*Daga taskar*

*AYUSHA MUHAMMAD*


💡 *DOGUWAR HANYA*


*Daga taskar*

*BILLY GALADANCHI*


*SANADIYYA......*

*Daga taskar*

*MAMAN KHADIJA*


💡 *SULTAN MEERAH*


*Daga taskar*


*PHARTY ZAHRA*


*Me buk'atar siyan Book d'aya daga ciki ze biya kud'i Naira 200 kacal, me buqatar uku ze biya 350 kacal, me buqatar 4 ze biya 450 me buqatar 5 kuwa ze biya 500*


*Domin biyan kud'inka kai tsaye turawa wad'an nan acc number kamar haka*


2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis


*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*


*+447894142004*



*Kokuma*


0026971316

Gt Bank

Balkisu musa galadanchi


*Seka tura shaidar tura kud'inka ta wannan lambar*


*07084161619*


*Idan kuma katin wayane dakai seka turawa wannan lambar kai tsaye na MTN ake buk'ata*


*08030811300*


*Zasu sakaku kai tsaye muna godiya sosai tare da mika fatan alkhairi da ga dinbim masoyanmu, me neman wani qarin bayanin kuma ya tuntub'i d'aya daga cikin lambobin dake rubuce a sama kai tsaye.....*


*SHIGA FAGEN NISHADIN NA WATAN NAN KEMA A DAMA DA KE*


_*da abaki labari....*_👉🏽👉🏽👉🏽👉🏽👉🏽👉🏽


{22}


Gaba daya ya gama rikecewa da irin salon da take mai, kan kujera suka fada ciki sali ta zare rigarta, hankalinsa ne ya tashi ya sa bakinsa ya fara tsotsa, a hankali komai ya dawo cikin kwakwalwarsa, da sauri ya hankadeta ya mike.

Zufa ce ta shiga keto mai, cikin tsananin fargaba da tashin hankali ne karara ya bayyana a fuskarsa, kuka Sadiya ta saka tare da kankame jikinta.


Kallanta yai yana maida zuciya tare da komawa jikin bango.


Kuka take sosai, wanda yasa yace “zaman mu anan mu kadai ne da alama shedsn ya dirsa mana wani abin.”

Cikin kuka tace “Yaya meya faru? Ya akai na ke zaune anan ba riga?”


Tashin hankali ne karara ya bayyana a fuskarsa ya juya baya da sauri ganin ta sauke hannunta.


Dakinsa ya shiga cikin hanzari, ya zube a bakin kofa yana maida wani irin numfashi.


Yana komawa dakinta bishi da wani wulakancen kallo a fili tace “komin fansa nazo dauka i can’t let you have me.”

Ta dau vest dinta cikin jin dadi ta dau wayarta dake gefe ta kashe sannan ta shiga daki.

Wayar ta kara danawa tana duba abinda tai da wayar fuskarta a hade cikin jin haushi.

Idanunta ta lumshe sannan a fili tai tsaki tace “Useless”


Kwafa tai sannan tace “am almost there.”


********


  Dady cikin jin dadi ya kalli Zainab cikin hirarsu yace “Amma kuna zaune lafiya ko?”

Tace “eh Dady, Adam mutumin kirki ne sosai muna zaune lafiya da shi da mahaifiyarsa.”


Cikin jin dadi Dady yace “masha Allah, amma Nabila tace kina aiki dayawa.”

Murmushi tai tace “haryanzu baya aiki Dady kaga dolene na dage sosai.”


Shiru Dady yai kafin yace “Amma Zainab kina ganin rayuwa zata tafi a haka? Yana namiji sai dai ki bashi?”


Tace “yana nema insha Allahu zai samu.”


Ido Dady ya zuba mata kafin yace “in samo mai?”


Da sauri tace “Dady in har bazai samu dakanshi ba a barshi, meye amfanin aikin da mutum ya samu bada kokarinshi ba?”


Dady kallanta kawai yake cikin wani yanayi yace “Allah yasa bani na maidake haka ba.”


Kallansa tai jiki a sanyaye tace “ya ya?”


Kai a girgiza cikin wani yanayi yace “komanki kinayinsa cikin isa wanda na tabbatar mijinki da wadanda ke kusa dake suna samun hakan a wata fuska ta daban.”


Shiru tai batace komai ba, murmushi yai yace “a dinga rausana murya in za’ai magana, kinji?”


Kai ta daga a hankali batace komai ba.


Dady yasa aka kawo musu abinci sukaci, kallanta yai cikin kewa yace “kiyi hakuri Zainab, bansan mekike ciki ba duk tsayin shekarun nan.”

Shiru tai batace komai ba, yace “nagode sosai da kika yima kanki tarbiyya na gari, aikin iyaye ne sai dai ke naki mahaifin ya gaza.”


Idanunta ne suka ciko ta dago ta kalleshi, yace “kiyi hakuri, da tun farko na sanar dake kin fadamin abinda mahaifiyarki ta fada miki da yanzu rayuwar mu ta canza.”


Maida kwallarta tai cikin dakiya tace “ka yafemin Dady, duk taurin kai ne irin nawa, dana saki fuska da nemi kebancewa dakai na tabbatar hakan bazata faru ba.”


Shiru yai yana kallanta cikin tausayawa da tsananin kauna, dan san da yake ma Zainab daban ne.


Sun yi hira sosai, kafin yace “zasu wuce saboda dare kar yayi.


Tare suka fito ya rakota har jikin motarta.


Kallanta yai yace “gashi nazo a kuraren lokaci bansan me zan baki ba.”

Dariya tai tace “basai ka ban komai ba dady, hira da fahimtar juna da mukai yafimin komai a duniya, sai dai kayi hakuri amma banajin zan yafewa matarka.”


Kallan Khalid yai wanda ganinsu yasa ya fito daga motarsa.


Dady ya kalleshi sannan ya kalleta yace “A ina kika samoshi? Tun jiya nake yabawa da halayensa duk da ban sanshi sosai ba.”


Dan kallansa tai kadan sannan tace “Abokin Adam ne.”


Cikin mamaki yace “Aboki?”


Tace “eh, tare sukai skul, da alama yayi kokari sosai a skul dinsu aiki me baisamu ba.”


Cikin rashin jin dadi Dady yace “ya gwada cike application na aikin Electricity ko za’a dace.”

Batasan sanda tace “na ce ya gwada aikinmu.”


Dariya dady yai yace “hakan ma is good, nasan Zainab tun tana karama mai tausayi ce, harnaji dadi jin tausayin yana nan bai tafi ba.”


Kasa tai dakai kawai tana dariya.


Kusa da Khalid suka iso, Ya gaisheda Dady, hannu Dady yasa a kafadarsa yace “Nagode, Allah ya taimakeka ya bada sa’a ya kuma daukaka ka.”


Ameen nagode Khalid yace.


Cikin mota ta shiga sukai sallama da Dady sannan Khalid ya shiga suka kama hanya.


Shiru tai gaba daya haushin kanta da yanda tai rayuwa ne ya shiga damunta.


Wayarta ce tai kara alamar shigowar text.

“Ko kinsan mijinki ya salwantar da rayuwar wata saboda ya sameki?”


Ido ta zubawa text din kafin taja wani tsaki, Khalid ne yace “Are you alright?”


Kallansa tai tace “text akamin, bansan meke damun mutane ba.”


Bai tanka mata ba, sai can yai tunanin wannan mutumin, da sauri yai parking bai juyo ba yace “wace number ce?”


Tace “is okay da alama wanine kuma wannan?”


Khalid baisan sanda yace “mutane nawa kika batama rai da........”


Sai kums yai shiru, ranta ne ya baci ta kalleshi tace “har yaushe ka samu hurumin shiga abinda bai shafe ka ba? Ko mutane nawa na batawa rai meye naks s ciki?”


Ransa ne ya baci, ko magana baiyi ba yajs mots ya nufi gidanta, shiru tai bayan ta fadi haka sai kuma tai tunanin kamar bata kyauta ba duba da yanayin shi ya cece ta daga irin wannan matsalar.


Sai dai bata tanka ba ganin yanda ya dame fuska yana tafiya.


Har suka iso gids ba wands ya sake magana, ledar flask dinta ta dauka tace “bari na juye na kawoma flask din.”

Ba matsala na tafi dashi jibi.


Kofa ta bude tace “ka mata godiya.”

Okay kawai yace bai ko kara magana ba, fitowa tai itama rai a bace.

Tana shiga falo tace “Sai kwarewa gun cewa Okay.”


Sai a lokacim ta kalli falan ba kowa a ciki, cikin mamaki ta shiga kitchen ta ajiye sannan ta nufi daki.


Adam ta gani a kwance, ta shiga tace “Honey bacci?”


Jin muryarta yasa gabansa ya kara faduwa, yace “a’a bana dan jin dadi ne.”


Cikin kulawa ta matsa da sauri tasa hannu a saman kansa, jin ba zafi yasa tai ajiyar zuciya tace “Alhamdulila ba zazzabi.”


Kallanta yai sai dai abinds ya faru dazu ke fadi mai.


Mikewa tai tace “ka tashi kasha magani, bari in duba Sadiya.”


Tana shiga taga Sadiya a cikin bargo itama, cikin mamaki ta karasa tace “Sadiya lafiya?”


Sadiya tana hawaye tace “banajin dadi ne Aunty.”


Cikin mamaki tace “ke da yayanki duk ba lafiya?”


Da sauri ta fito ta shiga daki, wayar Adam ta dauka ta kira Khalid, wanda ke bakin titi yana jiran taxi.


Hello Adam!

Zainab tace “am sorry in kana kusa ko zaka taimaka mun zuwa asibiti.”

Okay kawai yace ya kashe wayar, dawowa yai ya kwankwasa.

Budewa tai da sauri tace “nagode.”


Nan ta taso Adam suka fito tana rike dashi, yana karasowa Khalid ya rikeshi ita kuma ta koma ta taso Sadiya.


Adam dake zaune a bayan mota ganin Sadiya yasa gabansa ya fadi, ya dauka shi kadai za’a kai meya kawo ta?”


A kusa da Adam Zainab tasa Sadiya sannan ta bude gaba ta shiga.


Khalid ne wanda ke tsaye har aka sa Sadiya a mota yana kallanta, ina yasan fuskar nan?


Jin Zainab tace muje.


Yasa Khalid ya shiga.


Adam ya juya kanshi gefe, a hankali yace “Honey ciwon fa basai munje asibiti ba.”

Tace “haka da na dauka amma ganin Sadiya ma ba lafiya nasan da abinds kila kuka ci, ya na barku lafiya na dawo duk bakuda lafiya.”


Khalid ne ya fara tafiya hakan yasa motar tai shiru.

Kafa sadiya tasa a tsakiyan kafar Adam, yatsun kafarta ne suka goge gefen kafafunsa.


A zabure ya kalleta sannan ya kalli Zainab.


Kwantar da kanta tai sannan ta lumshe idanunta tana sosa kafafunsa da yatsun tafin kafarsa.


Gaba daya hankalin Adam ya tashi, suna isa asibitin Standard sukai parking.


Zainab ce ta fara fita akan tana zuwa.

Khalid wanda yake nazarin yarinyar dayake gani kamar ya santa, amma ya akai Zainab ta zaunar dasu tare?


Juyowa yai ya kalli Adam wanda yasa kafa ya ture kafar Sadiya da sauri, Khalid cikin mamaki yace “lafiya?”


A tsorace Adam yace “Bakomai.”


Kallanta yai sannan ya kalli Adam yace “wa?”

Cikin sauri Adam yace “kanwatacw Sadiya.”


Sadiya?


Da sauri Adam yace eh.

Khalid ya jinjina kai bayan ya kara kallanta, kanta ta saukar kasa sannan ta gaisheshi a hankali.


Khalid ya fita daga motar ganin kiran Abba.


Ya sanar dashi zaiyi dare sannan ya kashe wayar, dawowa yai jikin motar sai jiyai Adam yace “Sadiya meke damunki? Bakida hankali ne?”


Kuka tasa tace “me nayi kuma yaya? Ni wlh bansan meyasa yanzu kake min fada batare da nasan abinda na aikata ba.”


Zainab yaga ta nufo gun tamai alama daya fito da Adam.


Kofar ya bude, hakan yasa sukai shiru da sauri.


Nan suka shiga, dr ganin ba abinda ke damunsu yasa ta basu paracetamol suka fito.


Khalid ya maidasu gida ya tafi.


**********


“Wallahi Allah an dauken kudina.”


Goggo ta fada tana kokarin nuna cikin jakarta.


Uwar Amarya wato kawar goggo tace “yanzu dan Allah a gidan nan ma sai anyi sata? Wannan wani irin wulakanci ne?”


“Dubu biyar wallahi na taho dasu bayan wanda na baki amma gashi ko biyar babu.” Goggo ta fada cikin bacin rai.


Nan aka fara maganganu, Goggo tace aikam sai kowa ya bude jakarsa ta duba.


Nan ran manyan matan masu kudi dake zaune ya baci, akan dubu biyar kike fadawa kanki magana?


Goggo tace “ai ko dubu daya ne halak dina ne”


Wata ya tabe baki tace ko dubu biyar din aka safe kina da bakin magana ne? Zuwank uban abinda kikaci ai yafi na dubu biyar, komai aka kawo ssi kinci kinsa wani a jaka, wayasan ko garin tusa kayan abinci cikin jakar kika yadda kudin?”


Nan fa ran Goggo ya baci tace “naci din ba dan aci aka dafa ba?”


Ganin haka yasa Uwar Amarya ta jawo Goggo suka fito tana bata hakuri.


Cikin kufula Goggo tace gids zan koma bazan iya wannan wulakancin ba.


🙊🚶🏻‍♀


Ayusher🏌🏻‍♀

[11/9, 11:19 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     ......................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


Kuna ina ne yan Group na Queen Bee? Here is your special page sukutun....lol kullum kuna sani dariya da comment dinku, especially ma🙊 love you soo much.......Ina yinku irin😉


{23}


“Haba Goggo ya zakimin haka? Yanzu inkika koma gida me surikarki zata dauken?”


Goggo ta hade fuska tace “ai ko ban koma ba sai na fada mata, a haka nake shirin hada danki da Nabila?”


Hannunta ta jawo tace “zo muje kigani, yanzu aka kawo pepper chicken bama wanda ya gani, muje na zuba miki.”


Goggo tana tsaye bata motsa ba, yahkuri Goggo zan biyaki kudin Allah.

Sai a sannan Goggo tace “muje kiban na dandana.


********


Kwance yake akan gado yayi shiru gaba daya haryanzu kansa baya aiki, Zainab ta gyara mai bargon tace “sannu!”


Kallanta yai yace “bacci nakeji.”

Kai ta daga alamar to sannan ta mike, bacci ne ya daukeshi.


Tashi tai ta fito ta dau waya ta danna number dady tana kallan wayar.


Daga can taji ance “Zainab!”


Dady kun isa?

Yace “Yanzu na shiga gida.”

To a gaida masu shirin makaranta.

Yace to nagode.


Tana ajiye wayar ta dauko wainar geronta tanaci tana santi.


Cikin farinciki ya shiga cikin gidan.


Basma dake ta jera abinci kan dinning ne ta ajiye ta taho da sauri tace “Dady sannu da zuwa.”


Kallanta yai yace “yauwa.”

Bin bayanshi tai suka shiga daki, yace “su Nabila fa?”

Tace “suna dakinsu.”

Yace “daga gun Zainab nake.”


Kallansa tai gaba daya jikinta a sayaye tace “Ya kukai?”


Yace “mun daidaita matsalarmu.”


Idanunta ne ya ciciko tace “Alhamdulila, Dady haryau bazan daina baka hakuri ba, ka yafemin.”

Yace “na fada miki na yafe miki ai.”

Ta share kwallarta tace “Nagode sosai.”


*********


Tsakar dare cikin baccinshi ya hangoshi yana kusantar Sadiya cikin tsananin shauki, gaba daya mafarkin ya dauka gaske ne dan han nishi yake yi.


Zainab ta bude idanunta cikin tsananin mamaki ta kanshi rub da ciki yana mutsu mutsu, kana gani kasan mafarkin dayake yi.

Wutar dakin ta mike ta kunna ta zuba mai ido.


Idanunsa ya bude, a tsorace ya kalli Zainab dake tsaye a kansa, juyawa yai kawai taga wandan jikinsa adan jike, cikin fargaba tace “Honey!”

Gabansa ne ya hau dukan uku uku tace “Honey in kana san kusantata bazaka tasheni ba? Meyasa a koda yaushe kake sani nakejin bana kyautama?”


Kallanta yai idanunsa sunyi jaa, hannu yasa ya rikota yace “ba haka bane, da alama rashin lafiyar nan ce ta jamin, kin taba gani nayi?”


Shiru tai kawai tana kallansa.


Mikewa yai ya shiga toilet.


Yana shiga ya tsaya a jikin sink tare da kallan kansa a madubi, meke damuna?


Zainab kam tana zaune tana jiransa harya fito, maida ita yai ta kwanta yace “Yahkuri Honey.”


Shiru tai kawai batace komai ba, harbacci ya dauketa.


Duk yanda yaso ya koma bacci ya kasa, hakan yasa ya fito falo ya nufi kitchen dan shan ruwa.


Yana maida kofar ya rufe ya shiga kitchen yasa ruwa.

Yazo komawa ta fito daga daki, yauma sanye take da vest din nan da bayaso, kanta duk ya dan tashi alamar bacci, wani abu ne ya tsirgamai, sam ya kasa dauke idanunsa daga kanta.


Ganin abinda yake ranshi yasa ta tako a hankali zuwa inda yake, juyawa yai zai shiga kawai ta fizo hannunsa ta jashi dakinta.


Kallanta yai yace “meye hakan kuma?”


Tace “yaya dan Allah ko rungume ni kai, sam na kasa bacci wlh.”


Kallanta yai gabansa na faduwa, saboda tsananin sha’awarta dake damunsa, hannunsa ta kamo ta sa a zagayenta ta rungumeshi tsam, wani irin numfashi ya fitar, a hankali ta sumbaci wuyansa sanda gaba daya tasake kwance mai tunanin.


Da sauri ya dago ya kai bakinsa cikin nata, yanda yake mats kiss ke kinsan dama abinda yake nema kenan ido rufe, gaba daya yana nema fita hayyacinsa, hannu yasa cikin vest din ya zare ta, nan hankalinsa ya kara tashi ya shiga hidima, hannu yasa zai zare skirt dinta.


Hannunsa ta rike, ya dago cikin jajayen idanunsa tace “Yaya kar muyi laifi.”


Ta sauke mai hannu taja baya sannsn tace “muyi romance amma kar muyi zina.”


Gaba daya baya cikin hayyacinsa, ta kamo hannunshi ta fito dashi ta rufe komarta.


Kallan kofar yai sha’awa na kara kamashi.


Daki ya nufa da sauri, Zeena na kwance tana bacci taji hannunsa a kasanta.


Farkawa tai ya sauke bukatarsa.


Suna wanka ya hau bacci.


Itakam dan aikinta ta duba sannan tai sallah da addu’oi sannan ta kwanta.


************

Washegari


  Khalid na zaune kusa da Abba sai dai da alama tunani yakeyi.

Abba yace “Khalid lafiya?”



Yace “Abba akwai application din dana ciki na aiki sun turon naje exams sannan wacce nake tukawa mota ma tace na duba site dinsu zasu dauki ma’aikata.”


Cikin jin dadi Abba yace “masha Allah kai ina farinciki, insha Allah wannan karan inaji a jikina za’a dace da izinin Allah.”


Khalid yadanyi murmushi, Abba yace “kai amma matan nan Allah ya biya mata bukatunta ya bata miji ma gari.”


Kallansa Khalid yai yasa dan dariya yace “Sannu Abba, ka manta nacemaka matar abokina ce?”


Abba yai dariya yace “au namanta wlh, to Allah ya kawo ‘ya’ya nagari.”


Khalid yace “Ameen, bari naje na amso abincin rana.”


Nan ya mike ya fito.


Tsaya yai cak dan nesa kadan da wata mota datazo wucewa mace da miji na ciki.


Oh ba ita bace?

Nan ya tuno, ranar daya dawo daga kai Zainab, wata budurwa da saurayi na cikin mota suka tsaidashi.


Saurayin ne ya fito yace “dan Allah kasan gidan Zainab?”


Zainab?

Saurayin ya kalli yarinyar yace “Zainab ko?”

Tace “eh da mijinta Adam, tana aiki a gidan tv.”


Khalid ya nuna musu gidan dan yanzu kam ya fahimta sosai, sannan ya juya.


Shiru yai bayan tunowa dayai yace “in kanwarsa ce meyasa tazo bata kirashi ba? Sannan yanayinsu barashi ne dasu ba yanzu kuma yaga yanayin kwalliyar ta da shigarta ba irinta sanda ya ganta ba”


Da sauri ya girgiza kansa yace “ka sani ko saurayinta ta kawo? Sannan yanzu ma kila dan batada lafiya ne.”


Murmushi yai yace “nizan fadawa Adam kanwarsa ne?”


Da wannan ya wuce gida.


********

Zainab tunda ta tashi Adam baya gidan, waya ta dauka ya kirashi, yace mata yadan fita ne zaije gun Ziyad yazo gari.”


Tace “amma da wuri haka?”


Yace “sorry honey naso jiran sai kin tashi kuma dai ganin baccin yake dawowa yasa na fito.”


Dan dariya tai tace “zakuje gulma ko?”


Dariya yai yace “ai haushinta ma Kwaro baya nan yau da sai na kawo Ziyad ya ganshi, kinganshi nan haryanzu bai yadda ba.”


Zainab cikin dan rashin jin dadi tace “Honey!”


“Shikenan na daina.”

Kashe wayarta tai, sannan ta mike.


A falo taga Sadiya tana gyara falan, tace “Sadiya!”

Gaisheta tai sannan tace “Aunty kin fito?”


Zainab tace “eh, ke da bakida lafiya me makon ki kwanta ki huta me kike anan kuma?”


Murmushi tai tace “bakomai Aunty, Yaya fa?”


“Yadan fita ne gun abokinsa.”


Ayya.


Haka suka karasa gyaran gidan tare Zainab tai musu breakfast sannan ta dau nata ta shiga daki, dan tanada aikinyi.


Wayarta ce tai kara alamar shigowa text ta dauka.


“Badau kin dau maganar dana fada miki wasa ba?”


Ajiye wayar tai tare da sakin yin tsaki tacigaba da aikinta.


**********


Wajen karfe 9 na dare suna gun dinner anata cashewa sai dai su manya sun zama ‘yan kallo, haushi duk ya ishe Goggo daga sun shiga gun rawa sai ace su fita, gaba daya haushi yabi ya isheta, waya ta dauka ta kira Adam.


Cikin masifa tace “kai zoka maidani gida.”


Adam dake hanyar gida shima yace “Ah kungama bikin?”


Tace “tunda na kiraka ai kaima kasan mun gama, tambayar kuma ta meye?”


Adam yace “ganinan zuwa.”


Nan ya juya da kan mota, yana isa ya kirata ta fito ta shiga mota, hannunta rike da jakarta da take away guds hudu.


Kallanta yai bayan ta shiga yace “Goggo yada take away har hudu?”


Tace “nawa daya naka na zainab da waccen kuliyar.”


Dariya yasa yace “Yanzu dama haka ake? Bamuje biki ba sai ki kinkimo mana abin biki?”


Tace “in bazakaci ba kace bakaci, sai ka fadamin magana? Gobe dai zata koma ko?”


Kallanta yai yanayin fuskarsa ya canza yace “dole ma.”


Harararsa tai tace “meye naga fuskarka ta canza? Sannan yau kaine kake cewa dole?”


Adam yai shiru baice komai ba, saboda abinda ke damunshi yasa yabar gidan tun safe, dan sai daya jira ma su Ziyad din.


Suna isa gida ya wuce dakinsu.


Goggo ta takeaway din cikin dan jin haushi tace “gida kamar ba mutane? Itama waccen magen na tabbatar ba bacci take ba.”

Dakinta ta wuce cikin jin haushi.


***********


Duk yanda ya rufe idanunsa hangosu sanda suka shiga hidima yakeyi, da kyar bacci ya daukeshi.


Zainab kam sai data gama aikinta duka sannan ta kwanta.


Da sassafe ta tashi kamar yanda ta saba ta shirya Adam na bacci ta fita.


Tea kawai ta hada ta fito, tana fitowa falo Goggo na kuna socket tare da kallanta.

Zainab ta gaisheta sannan tace “zan wuce.”


Goggo tace “to adawo lafiya.”

Fitowa tai Goggo ta tabe baki tace “a kalla kya tambayeni ai ya biki?”


Mota ta shiga bayan ta ajiye kayanta, suka tafi.


Sai da suka hau hanya yace “ya mai jiki?”

“Ya warke!”

Shiru suka danyi sannan tace “Ya Baban naka?”

Da sauki sosai.


Shiru suka dan sakeyi kafin tace “ka duba?”

“A’a yanzu in na ajiyeki zani cafe.”

“Okay, in zaka wani gun ka dinga tafiya da motar, man motar yayi kasa?”

Dubawa yai sannan yace “eh, ba can ba dai.”


Okay!


Daga nan ba wanda ya sake magana sai da suka isa, kallansa tai tace “ga ledar Umman nan, kace nagode, yayi dadi sosai.”


Baisan sanda murmushi ya bayyana a fuskarsa ba, dan bai taba zata zataci ba.”


Dama yana murmushi? Kayanta ta kwasa tai gaba.


Tana shiga office dinta wani text ya sake shigowa “kin tambayi mijin naki ya musa?”


Cikin kufula ta ajiye wayar.


Khalid na sauketa ya juya ya nufi cafe.


********


Sadiya ta gama shiryawa, ta fito.


Goggo na zaune tana kallo ta gaisheta, kallanta tai tace “kinga dama kin fito?”


Sadiya tai kasa dakai tace “yahkuri Goggo shiryawa nake.”

Ina Adamun yake yazo ya kaiki ki samu ki gama ki kama gabanki.”


Sadiya tace “kiyi hakuri Goggo nasan na takura miki.”


Baki Goggo ta tabe tace “akwai talaway danayo jiya in kinaso.”


Talaway?

Goggo ta murtuke fuska hakan yasa sadiya yin shiru.


Adam ne ya fito, sanye da jalabiya.


Goggo ta kalleshi tace “kayi maza kuci abinka ka kaita, tsinanen lattin nan da kukeyi shiyasa bata samu ta gama.”


Adam yace to.


Haka suka gama suka fito.

Tunda suka shiga mota ba wanda yai wa wani magana, can ta daure tace “Yaya!”


Kallanta yai baice komai ba.

Tace “kayi hakuri ranar na hanaka.......”sai kuma tai shiru, ranar a hayyacinki kike kenan?”


Kallansa tai tace “eh.”


Kunyar abinda yai ya kara kamashi, tacigaba “nasan jiya guduwa kai dan karna ganka, kayi hakuri in na takurama.”


Kallanta yai yace “nine zan baki hakuri.”


A kofar skul dinsu ya ajiyeta ya juya ya tafi, yana tafiya ta kira saurayinta yazo ya dauketa.


Wata irin dariya tasa a cikin mota tace “kai ka ganshi?” Sannan tai tsaki tare da kashe video din datake kallo tace “Kai ina mamakin mema suka gani agun mutumin can.


Kallanta yai fuska a hade yace “nifa gaskiya ko tabaki banasan yanayi.”


Wata banzanr harara tamai tace “bansan iskanci kaikuma, ka kama kanka, kasan akan wannan abin wallahi zaka kama gabanka.”


Da sauri yace “yahkuri.”


Bakin wani shago ta nunamai tace “saman Fanta nasha gaba daya a bushe nakejin bakina.”


Parking yai sannan ya fita.


Khalid daya sai biscuit da ruwan pure water yana kokarin biya mutumin ya matso dauke da fanta guda hudu.

Khalid ne ya kalleshi tabbas shine yace “Salamu Alaikum.”


Kallansa yai bayan ya mikamai hannu, yace “ka sani ne?”

Khalid yace “na dai ganka rannan da wata ka tambayen wani gida.”


Ni? Can sai yai dariya yace “haka kuwa nida Razy ne, Allah sarki mungode fa.”


Khalid ya jinjina kai sannan ya fito.


Yana fitowa ya ganta zaune a cikin mota, Razy? Mekenan?


Takowa yai jikin motar har inda take ya kwankwasa glass din motar.


Budewa tai cikin masifa tace “Malam.........”


Kasa karasawa tai ganin Khalid.


Khalid ya sake kallanta yace “Sadiya?”


Gabanta ne yai wani irin faduwa hankali a tashe ta kalleshi..........


******

Ayusher🏌🏻‍♀

[11/9, 11:19 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     ......................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


{24}


Gabanta ne ya shiga dukan uku uku, nutsuwarta ta tattaro ta kalleshi.

Idanunsa haryanzu yana kanta yana jiran yaji me zatace.

Nutsuwarta ta daidaita sannan ta kalleshi tace "Barka, au ina wuni?"


Khalid yace "Sadiya me kike anan?"


Murmushin yake tamai sannan tace "naje yin registration ne shine naji yunwa nazo nan."


Yanda yake kallanta ne tasan tabbas bai amince ba, idanunta ne suka ciciko tace "Dan uwanane shi bari yazo kaji."


Tana neman sake tambaya ya bude motar ba tare da ya kula da Khalid ba yace "Raziyyah sorry na koma siyo abu ne."


Kafa tasa ta haureshi kallanta yai zai sake magana ya hango mutum a jikin window.


Kallanta yai sannan ya kara cuso kansa dan ganin waye.


Khalid na tsaye yana kallansa, Raziyyah hankalinta ne ya kara tashi ta kalli Khalid zatai magana ya juya ya bar gun.

Kallan Jameel tai cikin takaici ta kwadamai jakar hannunta tai cikin takaici ta bar mota.

Raziyyah lemon fa?


Ko bi takanshi batai ba ta nufi motar Zainab hankalinta a tashe.


Ya tada mota yana neman tafiya kawai ta bude gefen driver ta shiga.


Kallanta Khalid yai cikin mamaki fuskarsa a murtuke yace "Get Out!"

Kallansa tai tace "zan fita amma sai na fadi abinda ke raina."


Khalid bai kalleta ba sai dai yayi shiru.

Hawayenta ta goge tace "Bada wata manufar mukai karya ba na shiga wani haline na neman taimako."


Ganin bashida niyyar kulata tace "shine Ya Adam ya taimakeni, na tabbatar baka tunanin ni nakai kaina gidan a matsayin kanwarsa ko?"


Dan Allah kayi hakuri Wlh bada wata manufa nazo ba.


Shiru tadanyi a ranta tana cewa wannan dan banzan ko uban me ya kawoshi? Gashi da alama bashida yadda.


Khalid ne ya kalleta yace "am in hurry can you get out?"


Wani takaici ne ya kamata, ta share kwallarta sannan ta kalleshi fuskarta ta canza daga alamar tausayin datai tace "badai Zainab kake neman fadawa ba ko?"


Kallanta yai sannan yai murmushi yace "Oh this is your true self?"


Tace "koma menene banaji kanada hurumi a ciki, mijinta ne ya kawoni dan haka duk abinda ya faru tsakaninmu ne banaji mai tuka mota ya isa yai wani abin, kowa ya............"


Yanda ya juyo ya buga mata wani kallo ne yasa tai shiru, kasa karasawa tai gani tai ya bude inda yake zaune yazo kofar datake ya bude ya mata alamar da ta fita.


Mikewa tai cikin kufula ta bar gun.


Khalid yaja yabar gun ransa a bace.


Me Adam yake tunani? Me ya faru harya yaudari matarsa ta aure akan ta?


Raziyya kam ranta ne yi dubu gun bacu, cikin kufula tace "wlh baka isa hanani yin abinda na taso domin shi ba, tarwatsa rayuwar Adam dashi kadai na taso har nakai wannan lokacin.


Jameel ta kalla wanda ya fito yana kallanta.

Karasowa tai cikin jin haushi ta mai wani mugun kallo tace "kunyi magana ne a shagon?"


Yace "Razy shiya tambayeni ni bankawo komai a raina ba wlh."


Kallansa tai tace "bana key din karamin gidan dakai."


Karamin gida? Cikin mamaki ya tambaya, wani banzan kallo tamai yasa hannu ya ciro yace "me zakiyi?"


Amsa tai tace "ka aikon da takardun gidan, na dau kasona."


Kasanki? Cikin mamaki.


Tace "mungama daga yau ni dakai."

Ta juya zata fita, da sauri ya riko hannunta yace "Razy me kike shirin yi? Kinfi kowa sanin bazan iya rayuwa bake ba, sannan sirrinki fa duk na sani."


Juyowa tai ta kalleshi, tace "danka san sirrina sai akai me? Ni wanda na sani naka fa? Na fadama karna sake ganin ko missed call dinka." Tana kaiwa nan ta fita daga motar.


Da gudu y fito yace "in na kawo mana wata mafitar fa? Ni inaga ba lalai sai ta hanyar Adam zaki tarwatsa farincikinsa ba, me zai hana mubi tagun matarsa?"


Kallansa tai tace "koma menene ba ruwanka a ciki."


Adaidaitar datazo wucewa ta shige tai gaba tana maimaita kalaman Jameel, ta hanyar Zainab? Da sauri ta girgiza kai tace mutanen dake karkashinta uban me zasu tsinana.


***************


Haka ya cike application din aikin amma gaba daya hankalinsa na kan abinda ke faruwa, taya Adam zai dauko mace ya kawota?


A haka ya dawo Tv station din.


Lokacin tashinta nayi ta fito rike da kayanta, Ramatu na biye da ita tana bata hakuri tare da cewa "Dan Allah Aunty kiyi hakuri wlh wannan karan ba'a san raina bane, bansan yanda abin yake bane, dan Allah kiyi hakuri, Allah zan sake wani."


Ko kallanta Zainab batai ba, tunda ta fito yake kallansu, ko ba a gun yake ba kana gani Ramatu zakasan rokonta take, kai ya dauke cikin mamakin wannan hali.

Harta shiga mota Ramatu na bata hakuri amma ko kalla batace mata ba.


Kallan Khalid tai jiki a sanyaye sannan ta share kwallar da ta zubo mata, Zainab ce tace "mu wuce."


Shiru yai ba kuma alamar tada mota a tattare dashi.


Kallansa ta sakeyi tace "muje nace."


Kallanta yai sannan yace "magana ake miki, inkin gama sai mu wuce."


Ranta a bace tace "in banida ra'ayi fa?"


Baice komai ba haka kuma bai tada motar ba, Ramatu ce ta zuro report din cikin motar ta window tace "Aunty plz ki duba wannan."


Ta juya tare da cewa Nagode.


Tana tafiya Zainab ta hade fuska tamau tace "Umarnina ba umarni bane ko me kake neman maidani."


Tafiya ya farayi sannan yace garin irin wannan hali gashi can mijinki na miki karya, ya dauka a zuciyarsa yai maganar sai jiyai tace "me kace?"


Kallanta yai ta mirror yace "Sorry."


Wani takaicine ya kara kamata, sorry? Cikin jin haushi tace "Zagi na kai hala?"


Baice komai ba dan baima san me zai ce ba, ranta a bace tace "Banajin zagi sannan bana shakkar abinda wani yake tunani akaina."


Tana kai nan ta dauke kai ta maida kanta jikin tablet dinta.


Khalid baice komai ba suka cigaba da tafiya


**********


Motar Adam ta bude ta shiga, zama tai jiki a sanyaye ta kalleshi.


Bai kalleta ba sai dai ya rasa meyasa yake san ya kalleta.


Atishawa tai tare da sa hannunta kan cinyarsa.


Kallanta yai sai dai yakasa zare hannun nata, cikin kulawa yace "bakyajin dadi ne?"


Kallansa tai idanunta ya ciciko tace "ina tunanin tafiya ne da wannan hade ran da kakemin."


Kallanta yai jikinsa yai sanyi, murmushi tai tare da cewa "bansan me yasameni ba, sai dai da alama na jawoma bakin ciki."


Da sauri yace "A'a Sadiya, nine zan baki hakuri."


Hawayenta ta share tace "kai zan ba hakuri yaya nama kiss bada saninka ba."


Shiru yai ya kasa cewa komai, sai dai gaba daya ganin tana hawaye hasa jikinsa yin sanyi.


Share hawayenta tai tace "can you hug me na karshe?"


Jiyai bazai iya musa mata ba a hankali ya dan matso, jawoshi tai ta rungume tare da sa kuka.


A hankali ya shiga shafa bayanta alamar lalashi, kallan wani a wajen motar tai wanda ke rike da waya da alama hoto yake dauka, Adam ne ya dagota yace "nagode Sadiya, sannan ki yafemin."


Ajiyar zuciya tai sannan ta kalleshi tace "banasan tafiya yaya ka bari na kara sati daya, ba abinda zanma kallan ka kawai nakesan na dinga yi."


Kallanta yai hankalinsa a tashe yace "a ina?"


Tace a gidan Aunty.


Gaba daya hankalinsa ne ya tashi karara yace "A gidana?"


Tace "Gidan Aunty."


Yanda take maganar ne yasashi kallanta cikin mamaki yanda take maganar ba kamar dazu ba.


Kallansa tai tace "am sorry Ya Adam amma bazan iya barinka da gidan ku ba, ko sati sai na kara a ciki."


Baki ya sake yana kallan ikon Allah, anya Sadiya ce?"


Yace "bangane ba."


Tace "kasan yaushe rabona da bacci? Kullum mafarkinka nakeyi, ta ina zan iya tafiya da wannan abin? Kabarni na zauna ko na sati daya ne kafin nan na saita kaina sai na tafi."


Shima gaskiya abinda ke damunsa kenan, ya kasa cireta a ransa, tsantsar sha'awa ce ke yawo dashi.


Hannu tasa akan cinyarsa tace "kaima nasan abinda ke damuna yana damunaka Yaya."


Shiru yai yana kallanta, tace "bamuyi zina ba yaya, junanmu kawai zamu ragewa sha'awa dan Allah ka barni na kara sati."


Samun kansa yai da cewa "ba zina bace?"


Da sauri tace "ai baka kusanceni ba"


Kallanta yai tare da dan fito da harshensa kadan.


Murmushi tai ganin komai na zuwa da sauki, gaba daya wasan ya daina birgeta, anya bazata canza sali ba kuwa? Tabi shawarar Jameel.


To amma Zainab ta ina?


Khalid ne ya fado mata arai, tai dan kwafa ganin irin wulakantata dayai.........


A haka suka isa gida ko kunya Hannunta nakan cinyarsa shi kuma ya kasa cirewa sai dan sanyi da yakeji.


Suna isa gida motarsu Khalid na shigowa.


Khalid yai parking ya zuba mata ido daga cikin mota ba tare da ya fito ba.


Itama kallansa tai sannan ta dauke kai, da sauri ta taho inda Zainab take ta bude mata tace "Aunty sannu da dawowa.


Kallanta tai tace "Sadiya an kammala?"


Cikin jin dadi tace "Eh Aunty na gode sosai."


Khalid yana jinta yanzu kam ya tabbatar yarinyar nan yar banza ce, tasan yasan komai amma ko kallansa batai ba?


Adam ne ya karaso inda Khalid yake, Zainab ta kalleshi tace "Honey!"


Cikin sanyin jiki yace "Honey sannu da dawowa."


Tare suka shiga itada Sadiya.


Khalid ya fito suka gaisa da Khalid, ya amshi account number dinshi, yace "kwaro zan shiga ciki gaba daya banajin daidai."


Khalid ne yace "Sadiya!"


Juyowa Adam yai da sauri yace me?


Khalid yace "a'a kawai ina mamakin girmanta ne, kasan a skul ka taba zuwa da hotonta kai da ita kana tsokanar Ziyd a class akan matar da zaka bashi ce."


Adam cikin tsoro da neman waskewa yace "Oh baka manta ba? Ni na manta anyi haka ma wlh."


Khalid ya kalleshi, Adam yace "ta kara girma da kyau ko?"

Khalid gani yai ma bata lokaci ne sake mai magana kawai ya dau jakarsa da ledar da Zainab ta ajiye dan haushi ko duba cikinta baiba yai sallama da Adam yabar gun....


Suna shiga falo suka taradda Goggo a zaune tana waya da alama cikin fishi take magana.


Yoo dole ki kira ki lalemeni, sanda kuka sa aka hanamu shiga gun rawa fa? Sannan me kika cemin? Cemin kikai mune manya manya, amma meya faru?


Ganin su Zainab yasa tace "na kiraki."


Kallansu tai tace "kun dawo? Ya naganku tare?"


Ta fada tana hararar Sadiya ta gefe.

Zainab ta gaisheta da gida kawai ta wuce ciki.


Kallan banza ta bita dashi tace "kullum a turbune ake dawowa."


Raziyya ta kalleta a ranta tace "ko kunya?"


(Nima nace kema ko kunya? Kina mace🙄 kina abu kamar😒)


**********

Ayusher🏌🏻‍♀[11/11, 10:53 PM] +234 818 247 0922: 🍀A GIDANA🍀

     ......................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


{25}


Duk yanda Khalid yaso yai bacci ya kasa, can ya tashi ya zauna yana nazarin wannan abu dake faruwa, shi kallo daya yana yarinyar nan ya fahimci ba yar arziki bace, ya akai gaba daya idansu ya rufe suka kasa gane wa? Me Adam yake tunani dahar zai kaita gidansa a matsayin kanwarsa? Indai akace kanwarsa kenan mahaifiyarsa da yaji tana gidan itama da ita aka hada baki kenan?


Haka yai ta saka da warwara haryai bacci, ya fito da safe Umma ta nufo asibitin.

A waje suka tsaya suka gaisa tace "zaka wuce?" Yace "eh."

Tace "Jiya nida naji kunya? Matarnan daga kai waina sai data sako min dubu biyu a cikin flask din? Ita haka akeyi? Muna godiya ana sake mana abin alkairi."


Khalid yace "dubu biyu?"

Tace "eh wlh, dama nasan baka sani ba, ka mata godiya dan Allah, ina ma tsoron sake msta wani abin kar ta sake sako wani."


To Umma. Haka yace ya fito.

Ya iso da wuri yana fatan ganin Adam dan jin wannan abin.

Sai dai ba kowa a wajen, Bala ya kalla yace "yaushe Mai gidan yake fitowa?"

Bala yai dariya yace " ai Alhaji sai azahar daka ganshi inhar ba da dalili ba."

Khalid yai shiru tare da shiga ciki, Zainab tana gama shiryawa ta fito ta nufi kitchen, tea dinta ta hada yanda ta saba sannan ta fito falo.


Goggo na zaune tana kallo hannunta rike da cup din tea.

Zainab ta gaisheta, Goggo ta amsa tace "Sadiya yau zata tafi."

Cikin mamaki Zainab tace "yau kuma? Jiya Honey yace zata sake sati daya."

A gidan ubanwa zata sake?

Goggo tai subutan baki gun fadar haka, Zainab fuskarta dauke da mamaki tace "Goggo!"

Murmushi Goggo tai cikin dan dabara tace "a'a gani nai wai ba amfani tanada harkar karatu tazo ta tare anan."


Zainab tace "inya tashi duk yanda kukai ya kirani a waya ina sauri ne."


Goggo ta dan tabe baki a ranta tace ai kullum cikin sauri kike indai kece.


Zainab ce ta fito dauke da kayanta, sannan ta shiga ta ajiye, ta zauna.


Ana fita daga gate din gidan text na shigowa wayarta "A haka in aka ganki sai a dauka kinada nazari amma yanzu na san bakidashi, na fada miki abu kinyi watsi dashi ko?"


Mekenan? Tai maganar a fili.

Khalid ne yace " mutumin rannan ne?"


Ya fada hankalinsa adan tashe, a'a bansan waye wannan ba kuma.

Ta fada tana kallansa, dan parking yai da motar sannan yace "zan iya gani?"


Shiru tai tana nazari, yace "in baki yadda na gani ba shikenan mu tafi kawai."

Mikamai wayar tai batace komai ba.

Tundaga text din farko zuwa na yau ya karanta, sannan yai shiru ya dau number ya mika mata.

Kallansa tai tace "bansan waye wannan ba amma nasan komenene sharri yake shirin yi, nasan Adam nasan abinda zaiyi da wanda bazaiyi ba."


Khalid ne ya kalleta yana tuno waccen rainin wayan da aka mata.

Kallansa tai tace "me? Baka yadda ba? Abokinka ne barshi dai da san jikinsa amma bashi da wata matsala."


Khalid ya juya ya tada mota yace "hakan ake fata."


Kalmar tadan tsaya mata sai dai bata sake tambaya ba, har suka isa.


Tana shiga yai shiru yana nazarin sakon nan da kuma yarinyar nan, tabbas ko za'ace yayi shishigi sai yasan me take a gidan nan.

Number daya dauka ya kira, yayi mamaki dayaji number tana aiki, kenan Zainab bata ko gwada kiran number ba? harta kusa katsewa sannan aka daga.


Hello!

Jin muryar mace ne yasa ya danne zuciyarsa tare da gwada sa'arsa yace "Razy?"

Number tadan kalla, tana mamaki dan sim din a wayarta yake amma ba kowa yasan dashi ba tace "Yes? Waye?"


Khalid mamaki ya kamashi yace "me kike tunani kikeyi?"

Sake kallan number tai sannan tace "waye?"

Kashe wayar yai tare da yin shiru yana tunanin abinda ke faruwa,

Raziyya tai shiru tana kallan wayar, wanene?


********

Goggo Zainab na fita ta nufi dakinsu Zainab.

Budewa tai kai tsaye, Adam na kwance rungume da pillow yana sharar bacci.

Dayan pillow din ta dauka ta makamai, a zabude ya farka, kallanta yai yace "Goggo lafiya? Mekike anan?"


"Me kake nufi da kuliyarcan?"

Me nake nufi kamar ya?

Kace bazata tafi yau ba? Uban me zata zauna tama?

Adam ya kalleta yace "zata tafi amma wai ba yau ba."

Cikin masifa tace "kai bansan iskanci, uban me zata zauna tama? Badai wani abin ya faru tsakaninku ba?"


Goggo tai tambayar a tsorace, kallanta yai yace "me zai faru?"

Yanda ya bada ansar ne ya kara tsoratata tace "kai bansan iskanci, tashi ka sallameta ta tafi, sam hankalina ya kasa kwanciya."


Adam yace 'naji dan Allah jeki."

Fita tai ranta a bace sosai.


******


Juya motar yai ya nufi gidan, daga waje ya ya tsaya sannan ya daga waya ya kira Adam.


Adam dake kwance yana nazarin yanda zai sallameta ne sako ya shigo mai, Yaya dan Allah charge nake so kamin ina kitchen."


Mikewa yai ya fito, Goggo bata falan da alama wanka ta shiga, kitchen ya nufa ya tsaya a bakin kofa tana fere dankali, yace "ya akai wayar taki ba charge? Ko bakida charger ne?"


Hannu tasa bayan ta matso ta jawo rigarsa ya karaso cikin kitchen din, rungumeshi tai tare da sakin wata ajiyar zuciya tace "har hankalina ya kwanta, dazu gaba daya battery na yayi low."


Dagota yai yace "kar Goggo ta fito."


Kiss tamai a baki sannan tai murmushi, duk da gabansa dake faduwa.

Sake mai kiss tai tana neman shiga canciki wayartai kara.

Matsawa yai tareda daukan wayar, yana gyara sautin muryarsa.

Khalid yace "Adam ina waje inba damuwa kazo zamuyi magana."

Adam cikin mamaki yace "magana? Wacce?"

Khalid yace "saika zo."

Adam cikin mamaki yace "Khalid?"

Kallansa tai jin sunan daya ambata, hankalinta a dan tashe tace "Khalid?"

Yace "eh wai magana yakeso muyi."


Yawo ta hadiya sannan tace "kaje ka shirya bari na kai mai ruwa nace kana zuwa."


Kallan mamaki ya mata yace "ruwa?"

Tace "eh wai karyaga ka dade."


To shikenan, ya fada sannan ya wuce daki.

Fitowa tai ta dakko wayarta ta nufi waje.


Khalid dake zaune yana jiran Adam ya hangota ta fito.


Tana zuwa ta bude gaban motarsa ta shiga.

Khalid bai kalleta ba ya dan duba agoggon wayarsa.


Kallansa tai tace "me zaka cewa yaya?"

Bai tanka ta ba sannan bashima da alamar kulata, tace "wai dan Allah kai da kake driver meye naka na shiga hurumin dabe shafeka ba?"


Yanzu kam Khalid ya kalleta, wayarsa ya dauka yai dialing  din  numberta.

Wayarta dake saman skirt dinta ne tai vibration.

Khalid ya kashe sannan ya sake kiranta, kallansa tai hankalinta a tashe, yace "kome kike shirin yi ki dakata dashi, ki koma inda kika fito."


Kallansa tai tace "bazan dakata ba wlh harsai naga rayuwar Adam ta salwanta."


Kallanta yai kamar zai kulata sai kuma ya fasa, dauke kai yai wanda hakan ya sake bata mata rai, kallansa tai tace "Zainab ce ta saka ka bincika? Me kake tunani in na tura mata wannan video din?"


Ta fada bayan ta zaro wayarta ta dana video din, bata nuna mai wayar ba sai dai ga nishi nan na an fada kogi ita da namiji, sannan ta dakko pic din da suke rungume a mota ta nuna mai tace "ko na hada mata da wannan?"


Duk yanda Khalid yaso ya danne abin baisan sanda ya wanka mata mari ba, ransa a matukar bace ya kalleta, itama kallansa tai ranta a bace, zatai magana Adam ya bude kofa cikin mamaki yace "Khalid meta maka zaka mareta?"


Kallansa Khalid yai sannan ya kalleta wacce ta fashe da koka tare da rike hannun Adam, tace "ya zamuyi yaya? Ya san niba kanwarka bace shine ya maren."


Adam ya kalleshi yace "koma menene baikai harka mareta ba, akan wani dalili?"


Kallansa kawai Khalid yake kafin yace "nasan ko a skul kwakwalwarka bataja sosai amma banyi tunanin toshewar kwakwalwarka takai haka ba."


Adam ransa ya baci balle haushin an gwaba mai magana a gaban Sadiya, yace "mene?"


Khalid yace "da nazo muyi magana ne amma yanzu na fahimci maganar batada amfani, ya tada mota tare da jawo kofar motar ya tafi.


Adam baki a sake ya bishi da kallo, yace "sai kace motar ubansa."


Sadiya ce ta kalleshi tace "Ya Adam garin ya ka dakko shi a matsayin driver? Ko Aunty ce ta dakko shi?"


Yace "nine wlh."

Tace "Yaya ina ganin kamar....."

Sai kuma tai shiru, kamar me?"


Kallansa tai tace "ni farkon zuwana dana gansu a mota ma na dauka mata da miji ne, yaya ina ganin kamar akwai abu tsakani.........."


Wani mugun kishi ne ya fito karara a idan Adam, yace "me kike san cewa? Kinsan Zainab kuwa? Tafi karfin tai abind kike tunani."


Ya juya ciki a kufule.

Yana shiga ta daga waya ta kira number "Bash ina san amin photoshop na wasu."

Turo hoton na gani, tace "kai zaka dauki hoton, zan saita lokacin da zan nemeka."


Yace okay.


Kashe wayar tai sannan ta shiga ciki.


Goggo na zaune suka shigo kallanta tai tace "ke zoki hada kayanki ki bar gidan nan in ba gidan tsohonki bane."


Sadiya ta kalleta tace "ba gidan tsoho na bane ba kuma mai fitar dani."

Ta shige daki.


Galala Goggo tai da baki tana kallanta, fuskarta ta girgiza da sauri anya ba mafarki take ba? Meya faru yanzu??


Nace oho 😏


*********


Ran Khalid yakai matuka sosai gun baci, meke faruwa? Wacece yayarta? Shiru yai kafin ya dau waya ya kira Salmanu.

Salmanu dan Allah dan jeka gida, akwai littafin da nake rubuta numbers ka dubomin number wani Ziyad a turon.


Salmanu yace to.


Wajen minti talatin Salmanu ya turo mai, Khalid ya kira number.


Ziyad ya dauka daga can bangaren.


"Khalid ne."


Kwaro? Ziyad yai tambayar cikin mamaki.


Khalid yace "eh, nace dan Allah da Adam yana budurwane kafin yai aure? Watace tace ta santa shine nake so naji ko karya take."


Dariya Ziyad yai yace "saboda haka ka kirani?"


Khalid yace "yahkuri."


Ziyad yace "yana da ita, Baby ni yama sunanta na gaskiya???"


Can yace ahhh Fiddausi, budurwarsa ce sosai, dan tun tana junior akeshan love, waya taba tunanin bazai aureta ba?"


Khalid yace "ohh ba itan bace."

Ziyad yace "ita wannan tana da sikila."


Khalid yace ayya, Ziyad yai dariya yace "ashe driver man ka koma?"

Wata dariya yasa yace "Adam ya fada mana, waya taba tunanin kwaro zai kare a tukin mota?"


Kashe wayar sa Khalid yai sannan yace "Sikila? Fiddausi?


***********

Ayusher ce🏌🏻‍♀

************

[11/13, 7:37 PM] Maman Zara Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀

     ......................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


{26}


Goggo ta mike cikin mamaki ta murda kofar, sai dai tajita a kulle, bubuga kofar tai tace "Ke fito!"


Daga ciki Razy tana jinta batada alamar mikewa, Adam dake daki ne ya fito jin yanda ake buga kofa.


"Goggo lafiya?l


Kallansa tai sannan tace "so nake yarinyar nan ta maimaita metacemin."

Metace?"

Ranta a bace tace "kazo ka tattara yarinyar nan tabar gidan nan ko sai ranka ya baci?"


Kallanta yai yace "zan mata magana gobe ta tafi."


Tsaki tai cikin kuluwa sannan tace "kai dai kam wlh anyi soko, yarinya karama ka kasa sallamarta, naga uban abinda kake rikewa."


Juyawa tai ta koma ta zauna ta dau remote, shiru yai yana nazari kafin ya dau key yai hanyar waje.

Aikin kenan.

Ta fada rai a bace.


Adam na fita ya kira Ziyad, kana ina?

Ziyad yace "ina gida anjima zan tafi."


Nan yace ganinan zuwa.


Gun Ziyad yaje suka fara hira, can cikin hira Ziyad yace "oh ni kwaro ya kiran yana tambayata budurwarka ta da."


Budurwara?


"Eh ka manta? Fiddausi."


Idanu Adam yadan fito dasu dan sam ya manta da ita, sai an dade in ba da wani dalili bama baya tuna ta.


Meyace?

Nan Ziyad ya fadamai yanda sukai.


Adam cikin rashin kulawa ya cigaba da hirarsa.


***********

Washegari.


Sun taho a hanya suna tafe tana waya, daga yanda take wayar zakasan da mahaifinta ne, cikin jin dadi take wayar.


Khalid dake kallan glass din motarsa ta baya yana kara tantance mai motar dake biya dasu, wayarsa ce tadan yi kara, dauka yai a hankali yace "ka dubo?"

Salmanu yace "wanda kace na tambaya baisan gidansu ba shima."


Cikin rashin jin dadi Khalid yace "okay nagode."

Kashe wayar yai sannan ya kara kallan motar bayansu, parking yai yana shan kwana, motar daga dan baya itama tai parking.

Zainab wacce ta gama waya yanzu tace "ina zaka?"

Yace "yanzu zan dawo am sorry."

Fita yai tabishi da kallo tana leken abinda yakeyi.


Knocking din glass din motar yai, Bash daya waske dashan ruwa ya bude yana cewa "Ya akai?"


Khalid ya kalleshi yace "me kake?"


Bash yai dariya yace "ruwa nake sha."


Khalid ya kalli cikin motar sannan ya kalli wayarsa dake gefe camerar wayar a bude take, yace "dan mikon wayar ka."


Bash ya rufe ruwan yace "yanzu bawan Allah haka kawai ina tafiya kace in baka wayata? In baka kayi me?"


Khalid ya kalleshi yace "zaka bani ko sai na kira wacce ta saka?" Ya fadi hakan yana fatan bugar cikinsa.

Bash ya kalleshi yace "Ba ita ta sani ba ni na sa kaina."


Kenan sashi akai? Ita? Wacece kenan? Badai wata kuma Zainab ta sakema Laifi ba?


Daurewa yai ya kalleshi yace "bani wayarka."

Bash yace "wai a kan me zan baka wayata?" Yai maganar yana rike wayarsa.

Khalid ya zagay daya bangaren kafin Bash ya kulle ya shige.


Wayr ya amshe daga hannunsa sannan ya duba calls.

Razy yaga ansa, mamaki ne karara ya bayyana a idan Khalid cikin tsananin mamaki yai saurin duba photo ganin a camera wayar take da alama hoto aka gama dauka.


Zainab ce lokacin da take komarin bude mota, mamaki ne ya kamashi ya kalleshi da sauri yace "me kake shirin yi?"


Bash ya kalleshi yace "me kuwa? Ba abinda nake shirin yi."


Shiru Khalid yai ganin Zainab na zaune yasa ya kalleshi yace "koma me kake shirin yi karka kuskura na kamaka kana bina, inba haka ba duk abinda ya biyo baya kaika sani." Goge hoton yai sannan ya ajiye mai.


Ya bude motar yana tafiya zuwa taso motar yana tunanin meyasa bai goge hoton dake wayar Razy ba? Ko dayake inhar sharrinta ya kai haka ya tabbatar ta ajiye wani hoton a wani gun, meya faru haka? Wacece rayuwarta ta salwanta akan Adam?


Bude motar yai gaba daya yana tunani, Zainab wacce gaba daya tunda ya fita hankalinta ya tashi ne ta kalleshi tace "wanene? Turoshi akai?"


Kallanta yai kadan me kikeyi gidanki ya zama haka?

Ganin baice komai ba yasa tace "Magana nake."


Kallanta ya sakeyi yace "Will you please keep your eyes open?"


Mene?

Ta tambaya cikin bacin rai, makauniya ce ni ko me?


Kallanta yai kamar zai sake magana sai yaga in har baisan komai ba yai magana kamar yana neman raba aure ne.


Ranta a bace tace "uban waye a motar da har zaka fadamin magana?"


Khalid yace "am sorry."

Ya tada motar, bayan yaga waccen motar tabar gun.


Ran Zainab yakai kololuwa gun baci dan bakin ciki ya isheta da har ta kasa magana, wannan dan rainin hankali ita zaicewa makauniya ko me?


Da bakin ciki suka isa gida, yana parking ta fito a zuciye ta wuce ciki, ya sani sarai taji haushin abinda yace "amma garin ya suka bar yarinya karama take juyasu haka?"


Waya ya dauka ya kira number Adam.


Adam ne ya dauka yace "ya akai?"

Yanda yai maganar ne yasa Khalid yace "ka fito." Ya kashe wayar.


Adam ya kalle wayar yace "ka fito?" Sai kace wani danka? Har zai ci gaba da kallan ball dinsa sai kuma ya mike dan yana san jin meya kawo zancen Fiddausi.


Zainab ce ke gaida Goggo da gida fuskarta a hade, kallan Adam tai batace komai ba ta wuce ciki.


Gaban Adam ne ya fadi, meya faru? Honey? Sannu da dawowa.

Yauwa Honey kawai tace ta shiga daki.


Goggo ta tabe baki tace "oh ni!"


Kallan Goggo yai tace "ka gama boyewar? Kasan Allah kazo ka kuri magen nan? Dan gulma yau ko ganinta banyi ba daga kai har ita.


Adam yace "ina zuwa."


Fita yai tace "au kaima ka iya rainin wayan?"


Adam ya fita Khalid na tsaye a waje.


Kusa dashi ya karasa fuskarsa a hade, Khalid ko damuwa dashi baiyi ba ya kalleshi yace "Adam bakada hankali ne?"


"Banda hankali?" Adam ya tambaya ransa a matukar bace.


Khalid ya kare tamke fuska yace "wannan yarinyar daka dauko ka tabbatar ka sallameta yanzun nan in ba so kake ta tarwatsa maka rayuwarka ba gaba daya."


Adam a kufule ya kalli Khalid jinyake kamar ya makeshi, mene? Kai wanene da zakace inyi abu inyi? In taimakeka in baka aiki ka nemi maidani karamin mutun?


Ran Khalid ne ya baci cikin kufula yace "wato kai bakada hankali ko? Banda hauka uban waye zainkawo yarinya gida yacewa matarsa wai kanwarsa ce? Banda hauka da rashin tunani? In kanwarka tazo fa? Taya ma daga ganin yarinya zaka kawota gidanka?"


Adam ne ya dunkule hannunsa cikin kumbura fuska yake kallansa.


Khalid yace "Fiddausi, a ina gidansu yake?"


Fiddausi? Adam ya tambaya.


Khalid yace "ita kadaice ko tanada kanwa?"


Adam ya hade fuska yadan harareshi yace "meya kawo wannan zancen?"


Khalid cikin takaici yace "ban san Fiddausin ba balle nasan kamanninta amma ka tabbatar bata kama da waccen yarinyar?"


Hankalin Adam ne ya tashi ya kalli Khalid da sauri yace "me?"


Khalid yace "bansan wacece ba bakuma ni da masaniya akan meya kawota amma ka bala'in shiga hankalinka, har hotonka rungume ta tana dashi."


Idanun Adam ne suka fifito bakinsa na rawa yace "mene?"


Khalid yamai wani kallo yace "banda rashin tunani taya zaka nemi yin alfasha a gidan auranka? Dan hauka kuma da yarinyar da baka sani ba?"


Adam cikin tsoro yace "banyi zina da ita ba, tace ba zina bane."


Wani kallan takaici Khalid yamai yace "da alama kana bukatar komawa islamiya."


Harya dau jakarsa zai fita yace "a wace unguwa take? Fiddausin nake nufi."

Sunan babanta fa?


Adam baki na rawa yace "Basiru."


Adam hankalinsa a tashe yace "Naibawa suke yar lemo." Yanda yai maganar kadai zaka san hankalinsa baya jikinsa.


Fita Khalid yai ya bar gidan, direct Naibawa ya wuce yar lemo.


Gaba daya hankalin Adam ya gama tashi dan da kyar ya iya takawa zuwa ciki, dakin Sadiya ya bude.


Goggo ta mike da sauri tace "ina zaka?"


Shiga yai ya rufe kofar.


Hankalin Goggo a tashe ta sa bakinta jikin kofar tace "Adam ka fito ko sai kaci gidanku anan gun."


Sadiya dake waya da babbar wayarta shigowar Adam ne yasa ta dan zaro ido.


Kallanta yai yace "Me Khalid yake cemin?"


Mikewa tai tace "me yacema Yaya?"


Ta matso tana neman kamo hannunsa, hannunsa ya matsar sannan yace "hoton me kika dauka?"


Ganin tasan kwanan zancen yasa ta ja baya ta zauna akan gado.


Dama tana jin haushin Bash yace mata bazaiyi abinda ta sashi ba yanzu kuma nan ya bulo? Lalai Kwaro yake ko khalid? To ko kyankyaso ne sai ta saita mai kansa.


Adam ta kalla wanda yace "waccen wayar fa?"


Murmushi tai tace "ahhh am so tired! Na gaji da sa mask din da bai dace da ni ba."


Mask! Ya tambaya yana kallanta.


Fuskarta ta hade tace "me? Yanzu kana so ka koreni ne bayan kaji abinda yace?"


Kallanta Adam yai yanda take magana ne sam kamar ba Sadiyan daya sani ba.


Kallansa tai sannan ta dakko wayarta ta nunamai pic din da video din tace "inka isa kace na bar gidan nan, wlh kana fada ina turawa matarka, tasan wanene kai."


Gaba daya hankalin Adam ne ya tashi.


Mikewa tai ta zo kusa dashi ta sumbace shi, hannu tasa tana yawo dashi kan kirjinsa tace "in maye yaci ya manta uwar da bazata taba mantawa ba."


Gaba daya zufa ce ke zubowa Adam, yace "me kike nemana dashi."


Hannu tasa ta shafi fuskarsa tace "kana iya baccin yanzu? Na tabbatar sha'awa bata barinka kayi sosai."


Adam zufa ke zubo mai gaba daya kansa ya dau wani irin zafi......


Ayusher🏌🏻‍♀

[11/15, 9:44 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     ......................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


{27}


Adam ya kalleta cikin tsoro yace "Sadiya."


"Tsi tsi tsi ni kanka ne baya aiki ko haka Allah ya halliceka? Har a wannan yanayin Sadiya zakace?"


Adam ya matso kusa da ita da sauri ya zube a kasa yace "na sani bake bace dan akwai abubuwa da dama da kike aikatawa ba a hayyacinki ba, taya daga taimako na taimakeki zaki......."


"Taimako?" Wata dariya ta sheke dashi sannan ta sa hannu a wuyansa sumbatar sa tai a bakinsa sannan tace " kule?"


Kallanta yai yaga hoton da aka dauka ta kalleshi tace "in tura mata?"


Da sauri ya mike zai warci wayar, mikamai tai tace "ba sai ka fadi ba."


Adam gaba daya sai ya kasa komai, Goggo dake wajen kofa ne taji kamar kanta baya aiki saboda abinda kunnenta ke juyo mata, baya tai tara dayin kara wayyoooo Allah.


Da sauri Adam ya bude kofa Zainab dake kan Sallaya ta idar da sallah kenan ita ma ta fito.


Zainab ta kalleshi ganin ya fito daga dakin Sadiya, sai dai bata kawo komai ba ta wuce gun Goggo tace "Goggo lafiya? Faduwa kikai?"


Kallan Zainab tai sannan ta kalli Adam tace "wayyo Allah na faduwa nai!"


Sannu, Sadiya ce ta fito ta tsaya a bakin kofa tana kallanta, Adam wanda gaba daya tsoro ya kamashi ya kalli Zainab yace " bari na kaita ciki."


Ta kalli Goggo tace "ba sai munje asibiti ba dai ko?"


Goggo ta zubawa Sadiya ido, kallan Sadiya, Zainab din tai, suna hada ido da Zainab ta fara matsar kwallar tace "sannu Goggona, tsoron matsuwa ma nake."


Adam ne ya taimaketa ta mike sukai daki, sai da taga sun shiga daki sannan ta shiga kitchen ta duba flask, ganin taliya yasa ta zuba a plate ta wuce daki.


Suna shiga daki Goggo ta kwace hannunta sannan ta dada mai wani dundu wanda sai dayai kasa.

Zubewa tai a kasa itama tana kara dukansa tana cewa "wannan wannan ka gama dani ka gama cutata, duk uban kudin dakaci kana makaranta gun sake jarabawa da wahalar da ka samu ban taba jin haushi ba saboda ina ganin ai kayi dacen mata wanda zan fanshe wahalata, yanzu dan hauka ka yadda wannan kuliyar ta kamaka a tafin hannunta."


"Wayyo na shiga uku wannan yaron shi zainkarasani lahira."


Adamu yai shiru yana zube a kasa, idanunsa yana neman kawo ruwa.


Goggo tace tashi ka kirata tazo ta bar gidan nan yanzu kafin rayuwarmu ta kare dan wallahi bazan koma kauye ba kafi kowa sannin matar nan taka in taji ko minti daya bazamu sake a gidan nan ba.


Adam ya mike jiki a sanyeye duk zafin dukan nan bakai zafin abinda ke ransa ba, dan har ga Allah yana san Sadiya a kasan ransa, yana san ya kasance da ita, yaushe yasan yaudararsa take?


Kallanta yai tana zaune akan kujera abinda kullum a kasa take zama yace "kizo inji Goggo."


Wani banzan kallo tamai tace "kace tazo in jini."


Baki ya bude yace "mene?"


Kallansa tai sannan ta nunamai tv, tace "ba a gaban tv take wuni ba? Kace tazo ina kiranta."


Tsayawa yai ya kasa ko motsi.


Zainab ce ta fito deban ruwa, kallansa tai a tsaye sololo.

Matsuwa tai tace "Honey!"


Kallanta yai yace "Hmm."


Ya akai? Jikin Goggon ne?"


Hannunta ya kama da sauri yace "ba shi bane muje."


Dariya tai tace "ruwa zan deba."


Shiga daki zan kawo miki ba'asan ana cin abinci ana tashi."

Murmushi tai cikin jin dadi, Sadiya ce ta kalleta tace "Aunty Yaya na kula dake sosai, irin su Yaya basa cin amanar matansu."


Zainab ta kalli Adam sannan tace "Shiyasa nake ji dashi ai."


Nan ta shiga daki, juyowa yai ya kalleta.


Kallansa tai tace "wuce ka kiramin Goggo ko kuma Allah yanzu na tura."


Juyawa yai sololo ya nufi dakin Goggo ya sanar da ita aiken Sadiya.


Baki ta bude tace "inzo?" Cikin bacin rai ta mike ta nufi falo zatai masifa.


A gaban tv ta ganta tana juna wayarta a jiki.


Cikin zuciya Goggo tace "ke dan ubanki bakiji ina kiranki ba? Yr banza karuwa, wuce ki hada kayanki kafin naci ubanki a gidan nan."


Bata kula Goggo ba sai data gama hadawa remote ta dauka ta zauna a kan kujera sannan ta danna video dinsu, baka gani sosai saboda da alama a jikin tv stand tasa wayar kafin ya ankara sai dai ga muryarshi nan sannan sanda yana tsaye fuskarsa ta fito, ga nishi da alama ya fada.


Jikin Goggo ne ya hau rawa, hotonsu ta bude inda ya rungumeta a mota.


Bakin Goggo na rawa ta kalleta.


Adam kam gaba daya ya sandare kai kace itace ne a gun.


Da sauri Goggo ta kashe socket sannan ta kalleta tace "meya hakan?"


Sadiya tace "in kika kara cemin karuwa ko kuma nabar gidan nan tabbas zaki tsinci wannan abin a wayar sirikarki."


Goggo idanunta ne suka fito cikin takaici ta kara mangare Adam wanda yakeji kamar yai kuka, meye laifina? Daga taimako? Ya fada tare da sa kuka.


Zainab ce ganin bai kawo ruwan ba yasa ta fito.


Kallan mamaki ta musu ganin Goggo da Adam a tsaye carko carko ga Sadiya a zaune, sannan Adam

Sai goge fuskarsa yake kamar mai kuka.


Cikin alamar Zargi tace "lafiya?"


Adam ya juya da sauri ya nufi kofar fita yai waje.


Goggo ce ta kalleta tace "fada nake mai ya nemi aiki wannan zaman ya isa."


Zainab tace "ai yace yana nema, komai sai Allah yayi, sannan shi kinsan baisan aiki irin namu ko na wahala."


Goggo tace "Hmm."


Wucewa tai ta debo ruwanta sannan ta wuce ciki, sai dai sam tana ganin akwai wani abin bayan fadan aiki, haka kawai Adam bazaiyi kuka saboda maganar aiki ba.


Sadiya ce ta kalli Goggo tace "nima bani ruwa nasha."


Wa? Ni?


Sadiya tace "me kike a gidan nan banda kallo? Bani ruwa tun kafin na tura."


Da sauri Goggo tai kitchen ta dauko ruwa kamar mai shirin kuka, yau meke faruwa da ita? Itakam da alama rayuwarta ta kare.


******


Duk yanda ya tambaya bai samu ansar komai ba a Naibawa, ganin haka yasa ya fito, ga dare yayi dole sai gidan Kawu ya nufa.

Shiru yai yana tunanin abinda ke faruwa kafin ya tambayi kansa, ni me nene nawa a ciki? Meye nawa na damuwa? Rayuwarsu ce sun san abinda ya kamata ai ba yara bane su.


Sai dai sam ya kasa bacci sai juye yakeyi, can yace taimakon datai na Abba na zan rama mata.


Da sassafe yana sallar asuba ya kara komawa can, sai dai yanzu ma ba wani labari.


*******


Wajen karfe 11 na dare Adam ya dawo, sum ya shige daki ya tura a hankali, ganin Zainab na bacci yasa ya lalaba ya kwanta cikin takaici da dana sanin abinda ke faruwa wanda tunda ya fita yake dana sani.


Hana kwanciya yaji ta rikoshi, a hankali tace "Honey ka dawo? Ina kaje kai da baka san fitar dare?"


Idanunsa ya runtse cikin takaicin abinda ke faruwa yace "na fita kawai yawo ne."

Murmushi tai tace "nace abokinka yai applying din aikinmu, kai haryanzu baka san aikin zirga zirgar?"


Yace "a'a." Shiru yai saboda gaba daya bai san magana.


Kara kwanciya tai a kafadarsa tace "Honey!"


A hankali yace "Hmm"

Tace "mun shirya da Dady."


Baisan abinda take cewa sosai ba kawai yace "Uhm Hmm."


Mamaki ne ya kamata, matsawa tai daga jikinsa sannan tace "abinda zakace kenan?"


"Me nace?"


Cikin bacin rai tace "bashi."

Jan bargo tai ta kwanta, Hm hm? Wani ya maidata makauniya mijinta kuma tana fadamai abinda ta matso ta fadamai shine zaice Uhm Hm?


Da safe tana tashi ta fita, tayi mamaki dataga yau Goggo bata fito kallo falo ba.


Mota ta shiga fuskarta a hade sosai.


Shikam ko a jikinsa dan gani yake duk matsalar tata ce wani irin rashin kula ne zaice ace bakisan kanwar mijinki ba? Shekara ba daya ba ba biyu ba da aure?


*****


Yau ba wanda yama wani magana har suka kusa isa, haushi ya kara kamata dan ta dauka zai bata hakuri.


Sai da suka kusa isa cikin bacin rai tace "kacemin makauniya sannan bazaka dau lefen ka ba?"


Khalid na tukinsa kamar bazai magana ba sai yace "in bakyasan ace miki haka ki sa ido a Gidanki."


A Gidana? Kai waye da zaka ce na sa ido a gidana?


Khalid yace "niba kowa bane sai dai duk abinda ya faru kisan kece kashi 60 na matsalar."


Ranta a matukar bace tace "da alama ka gaji da aikinka"


Shiru yai bai tanka mata ba.


Haushi ne ya kamata suna isa ta fita ta banko kofar da karfin tsiya.


Binta yai da kallo kafin yai ajiyar zuciya, meyasa yake saurin yin fada in tamai magana?


Sam ya rasa me yasa ransa ke saurin baci da yanayin yanda take magana, bayan yasan a karkashinta yake sannan ta taimakeshi.


Idanunsa ya runtse kafin ya ajiye motar ya fito dan komawa Naibawa.


Yanzun ma baisamu kowa ba yana kokarin juyawa ne ya kalli wayarsa, ganin date din yau ne yasa ya zaro ido da sauri, hannu yasa a kansa cikin dana sani yace "Oh God ashe yaune test din?" Sam ya manta da wanda aka turomai kwanaki.


Cikin rashin jin dadi ya juya, wanni magidancinya gani kamar bazai tambayeshi ba sai yaje gunsa yace "dan Allah bawan Allah kasan wata Fiddausai?"

Fiddausi? Ya tambayeshi.


Khalid yace "eh tanada Sikila sannan mahaifinta sunan mahaiginta Basiru.”


Shiru yai kafin yace “Tanada kanwa Raziya?”


Idanu Khalid ya bude kafin yace “kanwa?”


Mutumin yace “ita?”


Da sauri Khalid yace “eh.”


Mutumin yace “shiyasa baza’a gane ba da kace gidansu Raziya ne zasu gane, ita Fiddausin ai ta dan kwana biyu da rasuwa.”


Kallansa Khalid yai yace “ta rasu?”


Eh baka sani ba?


Idanun Khalid ne suka fito sosai.......


Ni kaina idona sai da suka fito😳🙊


*********

Ayusher🏌🏻‍♀

[11/18, 12:38 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     ......................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{28}


Khalid ya daure tsananin mamakinsa yace "kana nufin kanwarta ce kenan?"


Mutumin ya matso cikin rada da gulma yace "bawan Allah shawara zan baka ka tafi dan mu kanmu yanzu ba wanda yake kula zuri'ar gidansu."


Idanu ya dago ya kalleshi yace "mene?"


Ya kara matsowa har mamaki ya kama Khalid yace "babbar ta rasu, karamar ce Raziyar in santa kake ma ka koma dan....."

Sai kuma yai shiru yace "baruwana jeka kawai."


Khalid ne ya kalleshi, yace "menene dan Allah?"


Kamar zaiyi magana sai yace "ni dai ba ruwana nayi nan." Kafin Khalid ya sake magana yayi gaba."


Duk yanda yaso ya shirya tunanin dake yawo akansa ya kasa hadashi yanda ya kamata, duk da Adam ace ya yaudari yayarta ne ya auri Zainab baici ace taje gidan matarsa daukan fansa ba, to yayar ma ta rasu? Garin ya?


Ganin ya kasa gani komai ga haushin baije test din ba kawai yasashi ya juyo dan takaici.


Zama yai a cikin mota yasa hannunsa akan goshinsa.


Wayarsa ce tai kara alamar text yana dubawa yaga kudi ne yaga ya shigo 20k, ganin sunan Zainab yasa ya fahimci itace.


******


Shiru tai bayan ta dawo office dinta, gaba daya kalaman Khalid ke yawo a kanta suna kara kona mata rai, meyasa ya raina Adam ne?

Wani karamin tsaki taja kafin ta ajiye wayarta data turamai kudi tana cewa in bazai iyaba ya ajiye aikin ai ba dole.


*******


Da kyar takecin soyayyan doya da kwai data gama yanzu, kana kallanta kasan cusawa kawai takeyi bawai dan tanajin dadin sa ba.


Tv din ma dake gabanta tana kallo ne amma yau batajin shaukin kallan yanda ta saba, ajiye zuciya tai tare da shan tea, tana dagowa daga ajiye cup din taga an kashe socket din tv din.

Sannan tazo gabanta tasa hannu ta dauke plate din datake cin abincin.


Goggo ta kalleta, Sadiya tace "zubomin nawa sai ki zo ki dau naki."


Goggo cikin kufula tace "da alama bakisan me ake kira da tarbiyar na gaba ba ko dayake ke da kika zo daga taimako kina neman ruguza........"


Yanda Goggo taga tana kumbura ne yasata yin shiru, bansan tarbiyar ba?

Da sauri Goggo tace "haka nace? Gaskiya bakiji da kyau ba."


Sum sum Goggo ta rabe ta gudu ta wuce kitchen tana cewa "kamar zata daken?"

Abincin ta zubo mata sannan ta fito, gani tai ta saki abincin goggon a kasa, baki Goggo ta saki ta matso da sauri.


Oh zubarwa nai? Bansani ba, ta fada tare da amshe nata.


Daki ta wuce rai a bace, Goggo ta sake baki gaba daya itakam da alama tazama ita ake taimako a gidan ba sadiya ba.


Kallan dakin su Zainab tai rai a bace ta nufi dakin, Adamu na kwance yana bacci rub da ciki, haushi ne ya kara tike ta.

Filo ta dauka ta dada mai, farkawa yai da sauri ya kalleta.

Cikin tsananin takaici da fada tace "har kana iya bacci bayan abinda kaja mana? Ko ince kake neman ja mana? Ka tashi ka kori waccen kedarar ko kuwa?"


Adam ya kalleta yace "wani bacci bayan sai yanzu ne na samu ina ta tunani?"


Baki ta tabe tace "tashi maza ka korerta tun kafin ta kashemu da ran mu."


Mikewa yai ya shigs toilet tsaki tai cikin takaici ta fito.


Adam yana fitowa daga toilet ya nufi kofar dakinta, hannu yasa a jikin kofar sai dai fargaba ya hanashi budewa, dakyar ya daure ya murda kofar tare da turata.


Tana zaune daga ita sai vest sai dai yau vest dinma ta dageta sama duk cikinfa a waje yake, wani abu ya hadiya sannan ya kauda kansa gefe.


Kallansa tai sannan ta dauke kanta ta cigaba da danne dannenta a waya, shiru yai yana nazarin kafin yace "Hmm Sadiya...."


Bata kalleshi ba hakan yasa ya kara tattaro dauriyarsa yace "dan Allah kiyi hakuri kizo ki tafi."


Abincinta kawai takeci kafin ta ajiye plate din ta kalleshi, shakewa nake hadomin tea.


Kamar zai musa sai kuma ya juya, Goggo na zaune yazo ya wuce da tea, yana bata ta kalleshi tace "fita."


Juyawa yai sum sum ya bar dakin.


Goggo ta kalleshi tace "zata tafin?"


A hasale yace "tace na fita, duk ba ke kika ja komai ba? Da kin barni na lalabata ai da ba haka ba, amma duk nunawar da kikai kinji me aka ce ba duk shi ya ja halin da muka shiga ba."


Mene mene? Wato laifina ne kenan? To ai ni na kawota ba dole ba? Ko kunya bakaji, ni Allah yasa ma baka karasa can ba?"


Kallanta yai kawai cikin takaici ya juya yabar gidan ma.


Ranta yakai kololuwa gun baci.


**********


Idanun Khalid a runtse yaji an bude kofar motar, shigowa tai fuska a daure tamau ta zauna, bai kalleta ba shima sannan baice komai ba ya ja motar suka fara tafiya.


"Naga kudi sun shigo dazu? "

Hmm

"Thanks."

Yau har suka isa ba wanda ya tanka, tana isa ta fita daga motar tare da bugo kofa da karfi.


Fitowa yai ya zubawa gidan kallo yana nazarin meke faruwa a cikin gidan nan?

Jakarsa ya dauka ya fita, yana hanyar danbatta ne ya kira Adam sai dai duk yanda ya kirashi bai dauka ba, hakan yasa ya ajiye wayar.


Mamaki ya kama Zainab dataga Goggo bata falan, dakin Goggon ta nufa tana kwance cikin kunar rai.


Zainab ta bude kofar tace "Goggo!"


Goggo ta dago da sauri tace "Zainab kin dawo?"


Jikin ne?


Tai saurin cewa "a'a kawai banajin zaman falan ne, tun azahar na shigo."


Ba karamin mamaki Zainab tai dajin hakan ba, kafin tace "tunda dai lafiya ai Alhamdulila"


Juyawa tai ta fita.


Dakin Sadiya ta kalla, kawai ta nufi daki, budewa tai.


Sadiya dake zaune tana waya, tana ganin Zainab ta gyara zamanta tare da kashe wayar.


Zainab ta kalli yanda take zaune daga vest sai dan wando, daurewa tai tace "Sadiya kina nan ashe?"


Cikin sanyin murya tace "eh yanzu na shigo, da muna hira da Goggo a falo."


Kallanta tai cikin alamar zargi, suna hira? Bayan Goggo tace tun azahar take daki? Sannan ita tunda take ma bata taba ganinsu suna hira ba yanda dai yaci ace uwa da 'ya nayi.


Okay kawai tace ta ja kofar ta koma daki.


Adam yau ma bainan, gashi jiya taji haushin tana mai magana baimassn tanayi ba, kuma haryanzu baiko kira yabata hakuri ba yanda ya saba.


Kayanta ta ajiye ta nufi toilet.


******

Sai wajen goma sha daya yauma Adam ya dawo, tana zaune daram akan gado ta cika ta batse dan bazata dauki wannan halin banzan ba.


Adam ne ya shigo sum sum ya bude kofar daki, ganin Zainab a zaune ne yasa gabanshi ya fadi, baki na rawa yace "Honey!"


Kallansa tai sannan tace "daga ina?"


Yana yar dariyar waskewa ya nufota, hannu tasa ta dakatashi daga tabata tace "daga ina?"


Nadan fita ne neman aiki.

Neman aiki?

Da sauri yace akwai wani baban abokina dayace na kawo takarduna.


Shine sai dare ka dawo? A wani garin suke?


Shiru yai kafin yace "Honey!"

Tace "jiya ma ba sai 11 ka dawo ba?"


"Sorry Honey zan dinga dawowa da wuri."


Matsowa yai ya xauna kusa da ita yace "sorry kinji na daina."


Kai ta daga alama to sannan tace "to."


Kwanciya tai ya zauna a kusa da ita yana shafa bayanta kamar yarinya hartai bacci.


Shiru yai yana tunani, a hankali ya mike ya cire kaya sannan yazo ya kwanta.


Juye kawai yakeyi ya kasa bacci, dazu yana ganin kiran Khalid yaki dauka, tsoro ma yake karya kara jin wani abin.


"Kazo dakina"

Text din daya shigo wayar sa kenan, kallan Zainab yai ganin tana bacci sosai yasa ya mike a hankali ya fito.


Dole yaje ya lalabata ta tafi, da wannan tunanin ya murda kofar dakin.


Tana kwance rub da ciki ya shiga, bata juyo ba tamai  alama dayazo ya zauna a gefenta.


Karasawa yai ya zauna, tadan kalleshi tace "Dan bugamim bayama Yaya."


Kallanta yai sannan yace "ciwon yake?" Kai ta daga alamar eh, shiru yai yana tuno Baby wato Fiddausi wace ke yawan ciwoka ciki kuwa harda ciwon baya wanda yafi matsa mata.


Shiru yai yana kallan Sadiya gabansa na faduwa, tace "bugamim."


Hannu yasa yana buga mata sai dai kalaman Khalid ne ke dawomai, ganin da alama tunani yakeyi yasa ta juyo tare da bude hannayenta.


Kallan kirjinta yai wanda duk rabi a waje yake sannan ya kalli fuskarta, tace "na bata ma rai kwana biyu ko?"


Shiru yai sai dunkule hannunsa dayake yana neman kin amincewa, tace "yahkuri yaya kasan na fadama inada lalura."


Ido ya kura mata yana kokarin danne sha'awar dake taso mai.


Hannu tasa ta jawo rigarsa ya fada kanta, a hankali ta dagoshi ta sa bakinta cikin nasa.


Yanda kasan jira yakeyi nan Adam ya birkice ya na neman fita hayyacinsa.


Sun riga sun shiga wani yanayi, nishi kawai kakeji dan yau har rigar jikinta sai daya cire.


Yoo abinda yake kwana yake yini dashi yau ya samu.


Zainab wacce ke rike da wayarta saboda kiranta da akai ta dauka takejin duk abinda yake faruwa.


Sakar wayarta tai ta fadi kasa, gaba daya jikinta rawa yakeyi neman mikewa take sai dai kafafunta sun kasa daukanta, da kama bango haka ta bi har dakin Sadiya.


Idanunta kumshewa kawai suke kamar mai shirin suma, handa takejin nishin Adam tana tsaye a jikin kofa ne yasa taji gaba daya tana neman zubewa kasa.


Da kyar ta iya sa hannu ta bude kofar.


Adam wanda gaba daya ya zauce da sha'awa har ya fara kokarin aikata aika aika, dan har kayanshi duka da nata ya cire ya cilar.


Tana bude dakin taga abinda ke faruwa kawai ta zube a kasa ta suma.


Adam wanda ana bude kofar ya dago cikin tsananin tashin hankali.


Sadiya kam ko nace Razy ta kalleshi sannan ta kalli Zainab, bataso tarwatsa komai cikin sauri ba sai dai tasan in ta bari waccen dan iskan kyankyasan ya cigaba da shiga abinda bai dameshi ba komai xai wargaje ne ba tare da tayi abinda ta dade shekaru tana jira ba.


Zainab na kalla wace ke sheme kasa a sume.


Goggo wacce ta kasa bacci saboda tsoron abinds kuliya zata aikata yasa ko abinci bataci ba sai yanzu da yunwa ta hanata sukuni ta fito shan dan tea.


Ganin kofar dakin a bude yasa tai ciki.


Zainab ta gani a yashe a bakin kofar a sume.

Ga Adam a kan gado gaba daya ya kame ya kasa ko motsin sa sutura.


Wani kwalelen ihu data saki ne ya razanani, sai da wayata da nake typing ta subuci😨


Hmmmm anzo gurin inji mai tsoron wanka🙊


*****

AYUSHER🏌🏻‍♀

[11/20, 9:16 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{29}


Goggo a rikice ta kalli Zainab, wacce ke sume sannan ta kalli Adam wanda da alama shima suman zaune yai, takaici ne ya kara kamata ganin sa zir ba ko kaya.


Idanu ta runtse cikin tsananin bakin ciki ta kalli Sadiya wacce ke kwance kan filo, tana kallan abinda ke faruwa.


Hankali a tashe ta garzayo kusa da Adam ta tsinkamai wani mari, a gigice ya farfado ya kalleta yace "Goggo!"


"Ka tashi ka sa kaya ko sai na guntile abin?"


Sai a lokacin hankalinsa ya dawo akan abinda ke faruwa, hankalinsa  a matukar tashe ya zabura yaja bargon da Sadiya ta luluba, kallan Zainab yai dake kwance duk jikinsa rawa yake ya kalli Goggo hannu tasa ta hankadashi ya zauna kan gado dabas tace "wannan wannan....."


Sai kuma tai shiru tsabagen tashin hankali da rasa bakin ma magana.


Tama rasa me zatamai ta huce, kallan Zainab tai sannan ta karasa tana neman dagata.


Adam ta kalla tace "kazo ka kamata mun kaita asibiti ko kuwa?"


Gaba daya a rikice ya matso kallansa tai tace wannan ma ina zai iya tuki?


Yau itakan wani mumunan mafarki takeyi haka?


Muryar Sadiya taji tace "in kun fita ku ja min kofar?"


Cikin tsananin kumburin fuska Goggo ta kalleta tace "in kofar gidan ubanki ce sai ki sani na kule tsinaniya mai sufar mayu."


Haka suka fita da Zainab Goggo tace mukaita daki.


Nan sukai daki da ita, kallan Adam tai cikin takaici kawai tasa hannu biyu tana dukanshi ta ko ina, shi kanshi kuka kawai yakeyi yana cewa "dakeni Goggo."


Sai da hannunta taji ya fara xafi sannan ta kalleshi cikin tsananin takaici sannan a zuciye ta fito daga dakin.


Zainab ya kalla, hannunta ya kamo kawai yana kuka, dan shi kansa baisan meya shiga kansa ba, dan ya tabbatar a yanda yajishi dazu da ba kowa ba abinda bazai aikata ba.


Kukan da yake ne ruwan ya diga a kan fuskarta, a hankali yatsun kafarta sukai motsi.


"Honey? Ki yafemin bansan meya shiga jikina ba wlh....."


Wadannan kalaman nasa ne suka doki kunuwanta, kanta taji yayi wani uban sarawa, mumunan a binda ta gani ta tuno.


A zabure da firgici ta bude idanunta tare da jan wani dogon mugun numfashi taja, bakinta da gaba daya jikinta suka hau rawa daga kwance.


Adam dake rude lulube da bargo ne ya kalleta, ganin yanda jikinta ke rawa, ga bakinta ya kara daga mai hankali, hankalinsa ne yai mumunan tashi ya matso yace "Honey Honey."


Gaba daya ya gama tsorata a rikice ya zura riga ya fito dan kiran Goggo.


******


Goggo wace tana ajiye Zainab ta shigo dakin Sadiya cikin tashin hankali da rikecewa ne ta kalli Sadiya dake kwance bayan ta maida kayanta ta kwanta kamar mai bacci.


Goggo ta yaye zanin gadon data luluba dashi tace "kin tashi kin bar gidan nan ko sai na gwaraku da bango kanki ya fashi? "


Sadiya ce ta juyo ta kalleta tace "idan kin isa kenan?"


"In na isa?" Goggo ta tambaya.


Sadiya tace "zan zauna harsai sirikarki ta dawo daga mutuwar wucin gadi datai na bata amsoshin tambayoyim da zata tambayen sannan na fita."


Za kuwa ki farka ki ganki a kabari wlh, wannan yarinya ban taba ganin tsinaniya irin ki ba, wlh ko ki tashi ki bar gidan nan ko kuma wlh ki ziyarci lahira."


Sadiya ta ja zanin gadon tace "ko zan tafi sai da safe ba uban da zai fitar dani a daren nan."


Goggo ta fizgota da hannu tana neman jawota ne Adam ya shigo a rikice yana kiranta.


Saketa tai ta fito da gudu tana cewa "menene?"


"Zai zainab"

A rikice sukai dakin da take, hanyarzu jikinta a rikice yake , hankali a tashe tace "mu tafi asibiti."


Nan suka kinkimeta sukai waje.


Asibitin Standard suka nufa, gaba daya dan Allah yasa gari bai waye bane sam babu motoci a hanya da lalai sai dai wani ikon Allah amma yanda Adam ke tuki, da kyar ya kaisu cikin asibitin.


Zainab gaba daya haryanzu ta kasa saita tunaninta, abinda ta gani ne yake dawo mata kawai ta ko ina jikinta rawa yakeyi.


Haka aka shiga da ita suka kwantar da ita wata nirse tazo dubata.


Adam zaune a waje shida Goggo sunyi tsuru tsuru, Goggo in ta kalleshi sai taji kamar ta rufeshi da duka, shikam sai matsar kwalla yake, can yace "Goggo ya zamuyi?"


Tambaya kake? Tambaya kake? Banda hauka da rashin tunani sau nawa ina fadama ka shiga hankalinka da wannan yarinyar? Tun farko ma uban wa yace ka tsintota?"


Adam ya share kwallar sa yace "na shiga uku Goggo, Zainab bazata taba yafemin ba, Goggo na shiga uku."


Haushi ne ya kara kamata ta runtse idanunta cikin takaici.


Wajen awa daya sannan nurse din ta fito ta kallesu tace "shock ne amma yanzu mun mata allurar baci so in ta tashi muna sa ran komai ya dawo daidai, da alama shock din  data shiga babba ne."


Adam yai shiru yana tausayin abinda zai faru.


Haka sukai Jugum a asibiti, harara kawai Goggo ke zabgamai tana neman mafita da yanda zatai kwacesu, dan itakam im Zainab ta koresu shikenan rayuwarta ta kare dan batasan yanda zata cigaba da rayuwa ba.


Kallan kafarta tai ashe ko takalmi bata sa ba, Adam ta kalla shima haka, tace Allah yasa ka sa wando ba rigar ka zura ba sokon banza."


Kasa yai dakai cikin tsoron halin da suke ciki.


Tunowa datai sun bar Sadiya a can ita kadai ne yasa ta kara shiga wani hali.


Kallan Adam tai tace "inaji dole naje na kuri tsinaniyar can kafin ta farka mu koma ta kulla ma sharri."


A tsorace ya riketa yace "Goggo ki taimaken karki tafi ki barni in Zainab ta tashi banssn yanda zanyi ba."


Cikin takaici ta bige hanunsa tace "kasan kana tsoranta ka aikata?"


Kasa yai dakai cikin tashin hankali, ya zatai da tsinaniyar can?


Haka har gari ya waye suna zaune, sai da Goggo tace "tashi ni kaje kai sallah zan daure in shiga gunta kafin ka dawo."


Mikewa yai yace "in na dawo zan tsaya a waje."


Kallan takaici tamai kawai ta wuce ciki.


A hankali ta bude kofar, sai data tabbatar tana bacci sannan ta shiga.


Zainab dake bacci ta kalla, tabbas tasan akwai tashin hankali mai karfi in Zainab ta farka, lalai ko za'a mutu haka zatai ta bata hakuri, itakam bazata iya rayuwa ba a gidan Zainab ba wlh.


Tana idar da sallah ta fito dan itakam inba korar magen can tai ba bazata taba samun nutsuwa ba.


Adam ta gani xai shigo ita kuma zata fita, da gudu ya karasa yace "Goggo ina zaki?"


Wani banzan kallo tamai tace "ban sani ba."


Tai wucewarta.


Tana fita taga adaidata ta shiga.


******


Karfe bakwai da rabi Khalid ya iso gidan, Bala ne ya kalleshi yace "ranka ya dade basa nan dukansu."


"Basa nan? Lafiya dai ko?


Bala yace "Hajiyarce ba lafiya suna asibiti."


Shiru yai yana tunanin ya tambaya yaji sosai ne? Amma yana ganin ba huruminsa banr hakan yasa ya juya.


Ya juya kenan Goggo na sauka a adaidaita, mai adaidaitan ta kalla tace "in dako ma kudin ka."


Kallanta yai yace "gaskiya Baba kiyi sauri."


Tace to.

Khalid ta kalla cikin alamar tambaya tace "wa?"


Gaisheta yai sannan yace "Khalid ne, wanda ke kaita gun aiki."


Oh matuki?

Yace eh, kafarta ya kalla ba ko takalmi, tace "an fadama batada lfy ko?"


"Eh, Allah ya kara sauki."

Tace amin, sallama ya mata ya juya.


Ciki ta shiga taba Bala kudin adaidaita sannan ta nade hannun rigarta kai kace mai shirin dambe ce ta nufi dakin Sadiya.


Cikin masifa ta bude kofar, a rikice ta kara kallan dakin, ba kowa a ciki sannan bako kayanta a ciki, hankali a tashe ta fara leleka dakunan gidan, sai dai ba ita ba labarinta, sai wayar zainab dake ta kara.


Daukan wayar tai ta dau takalmi ta fito.


Dawowa tai asibitin, a waje taga Adam, yi tai kamar bata ganshi ba tai hanyar ciki.

Da gudu ya taso yace "Goggo kin dawo?"


Tace "uban me kake anan? Kai da zakaje kusa da ita tana tashi ka nemi yafitarta?"


Shiru yai shidai kam yasan Zainab.


A hankali Goggo ta tura kofar daki, ajiye wayar Zainab tai a gefe ta ma Adam alama daya shigo, yana sa kafa cikin dakin Zainab ta mike ta zaune, kai kace mikar da ita akai.


A tare suka kalleta gaba dayansu hankulansu a tashe, kallan asibitin tai, sannan ta kalli Adam wanda ke makale a bakin kofa, Goggo ta kalla idanunta sunyi jaaa sosai ko dan bacci tasha?


Bakinta kawai take motsawa tana san magana amma ji take wani abu ya tokare a kirjinta, har makoshinta."


Ganin maganar bazata yiwu ba ta mike ta zo kusa da Goggo hanyar waje ta nuna mata, da sauri Goggo tace "Zainab kin farfado? Sannu kinji."


Idanunta ta runtse da karfi, Adam ta hango akan gado ba kaya shida Sadiya gaba daya sun fita hayyacinsu.


Da sauri ta bude idanunta, sannan ta nunawa Goggo hanyar waje.


Goggo tace "ya akai? Abu kike so?"


Zainab rai a bace ta kara nuna mata hanyar waje, sarai Goggo ta san me take nufi amma tace "Zainab?"


Bakin kofa ta nufa wanda Adam na ganin ta nufoshi ya zube a kasa yai kneel down tare da daga hannunsa  yace "Honey!" 


Ko kallansa batai ba ta kara kallan Goggo ta nuna mata waje.


Goggo sum sum ta zo ta fice, suna fita ta rufe kofa ta sa key.


Sulalewa tai a jikin kofar ta zauna, gaba daya ta rasa meke faruwa, inama mafarki takeyi? Meke faruwa da rayuwarta.


Wayarta dake kara ta kalla, da kyar ta mike taje ta dauka, ganin gun aike ne yasa ta ajiye har ta katse.


Wayar ta kalla gaba daya ta kasa kuka, ta kasa ko magana, number Dady ta scrolling har tana shirin yin dialling ta tuna abinda tamai akan san zuciya irin tata, Ummy!!!

Abinda zuciyarta ta kira kenan, idanunta ta runtse, Alhakin Dady ne bina Ummy? Ummy Adam.....


Abinda zuciyarta ke fada cikin kukan zuci wanda ta kasa zubar dashi a kwayar idanunta.


Number kanwar mamanta tai scrolling, tunowa da yanda Aunty batajin dadi sosai itama gun mijinta wanda harda bakin cikin hakan yasa ta gaji da zaman gidanta yasa ta ajiye wayar ta kifata.


Nabila! Kina ina??? Rayuwata da alama tazo karshe......


Asibitin ta kalla sannan ta kara daukan wayar, number Khalid ta lalubo tamai text.


"Kace Bala ya dako ma key ka zo ka dauken a asibiti"


Khalid na kokarin shiga cafe ne wannan sakon ya shigo wayarsa, kallan sakon ya sakeyi shidai ya rasa meyasa yake tunanin gagarumin abu ya faru a jiya, daga yanda Zainab uwar san aiki da kuma yaga sirikarta ba takalmi.


Juyawa yai ya koma gidan.


Jin sakonta yasa Bala cikin rashin yadda yace "gaskiya ina tsoro.


Khalid ya nuna mai sakon, Bala yai shiru yana tunani, ganin Khalid abokin Adam ne a cewarsu sannan ga daga yanayin Khalid yana ganin ba mutumin banza bane yasa yai shahada ya dako mai spire key din da take ajiye gunsa.


Khalid ya hau ya nufi asibitin.


"Na iso?"


"Ka shigo ina sama"


Ciki ya shiga, Adam da Goggo na zaune jugum Goggo ji take kamar tasa kafa taita makawa Adam.


Ganin Khalid yasa Adam ya mike da sauri ya nufoshi.


Khalid cikin mamaki  ya kalleshe yace "Adam?"


Adam ya kamo hannunsa yace "Khalid na shiga uku na........"


Adam..

Kiran da Goggo tamai ne yasashi yin shiru, Khalid yai shiru yana kara tabbatar da zarginsa.


Kamar tasan ya iso kawai ta fito ita da nurse, wacce take binta tana ce mata ta dawo ta zauna ko dan rashin maganar da takeyi.


Ko kallansu batai ba har Khalid din tai gaba.


Gaba daya ta canza, kafafunta ba takalmi bako mayafi a jikinta, rigace doguwa zuwa gwiwa ta bacci, da wando, sai hula a kanta.


Da alama halin da take ciki ma baisa tasan abinda ke sanye a jikinta ba.


Juyawa yai ya nufi inda take yace "an baki sallama ne?"


Bata ko kalleshi ba ta sauka har kasa, mota ta nufa ta kalleshi ta mai alama da ya bude.


Yana budewa ta shiga ciki ta zauna.


Kallan Adam da Goggo dake tsaye a bakin kofar asibitin yai sannan ya bude motar ya shiga.


Tafiya suka fara tana kallan motocin dake wucewa, Khalid yai shiru shidai yana tuki amma gaba daya zuciyarshi na tsoron kardai wannan yarinyar tayi wani abin?


Zainab a hankali wani zazzafan hawaye ya zubo mata, tunda ya sako kamar an koro kuka, duk yanda taso ta dane kukan ji tai ta fashe da wani wahalalen kuka mai matukar ratsa zuciya.


Ba karamin tashin hankali Khalid ya fuskanta ba, gefen titi ya gangara, sannan ya ajiye tissue a gefenta ya bude motar ya fita ya tsaya a jikin kofa, sai dai gaba daya jikinsa ya gama yin sanyi, tsananin tausayinta ne ya kamashi.


Kuka take iya karfinta, wanda ni kaina sai danaji hawaye😪


*****

Wai ina Razy ne🙄🙄yasin kafin na kamoki ki dawo yar🙊


Ayusher🏌🏻‍♀

****

[11/22, 5:03 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{20}


Asiya na zaune tana ta mulmula iloka, daga gefenta kuma Abba ne zaune yana jin radio a gefensa, hannunsa rike yake da mafici da alama kuda yake dan kora in suka zo inda yake.


Kallan Asiya yai yace "Kannen naki na gun ball ko?"


Tace "dazu Umma tace na korosu amma Allah Abba suna dawowa da sukaga Yaya bayanan ni bansan ma sanda suka sake fita ba."


"Oh ni yaran nan bansan jaynarsu da kwallo ba, bare yau sun samu dama kuna hutun tsakiyar term."


Dariya tai tace "in lokacin islamiya yai sa dawo ai dole."


Umma ce ta bude labulen dakin tana sallama, Abba ya kalleta ya amsa.

Mayafinta ta cire ta zauna gefensa sai data kalli Asiya dake ta neman kudinta sannan ta kalli Abba tace "yau bakaji dadin da nake ki ba a rayuwar nan."


Abba yai dariya yace "kamar irin kin gama biyan bashin dake kanki duka din nan."


Dariya tai tace "wlh bakaga dana kai musu dubu biyar din nan a dunkule yanda naji wani dadi ba, ai insha Allahu tunda aka fara biyansu yanzun nan zamu gama."


Abba yai dariya yace "ai sai hamdalla."


Umma ta kalleshi tace "ni tun jiya nake san tambaya, dama aikin driver yana kaiwa dubu ashirin?"


Abba yace "eh dama yawanci sha biyar ne, in ka hadu da na gari ya baka ashirin."


Umma cikin jin dadi tace "kai Allah yama matar nan albarka, ina san sake mata waina amma banasan ta kara sa kudi a kwanan, kuma bazan iya sa mata a leda ba."


Abba yace "haka ne kam.

Asiya ya kalla yace "taimaka ki dan ban ruwan can."

Mikewa tai ta mikomai.


*********


Agoggon hannunsa ya kalla, sama da awa daya kenan suna tsaye a gun nan, ta glass ya kalleta, ganin alamar ta dan rage karfin kukan yasa ya bude kofar da take.


Kallansa tai ba tare da tace komai ba, kallanta yai sannan ya bude gun zamansa ya bude jakarsa ya dako ruwa, mika mata yai, kamar bazata amsa ba ganin ruwan dan duri ne bawai na cikin gorar bane.


Kafafunta ta zuro waje sannan ta mika mai hannu, robar ya mika mata ta sake mikamai ta mai alama daya zuba mata, nan ya bude ruwan ya zuba mata a hannu ta wanke fuskarta.


Sai data wanke fuskarta sannan ta kalli jikinta, hankalinta a tashe tai maza ta koma ciki sannan ta bude glass tace "dan bude boot din motar, bansan ko na cire wata yar karamar jaka ba, in tana nan ka bani mayafi a ciki."


Baice komai ba ya bude yai sa'a jakar nanan, da alama wata yar karamar tafiya akai da ita, dakko mata yai sannan ya dawo ya bude mota ya mika mata sannan ya zauna.


Shiru sukai a cikin motar, dan kallanta yai yace "Do you feel better? Mu wuce?"


Kallansa tai itama idanunta sun yi wani irin jaaa wanda ya sashi sauke idanunsa gefe, tace "Do you think i'm pitiful?"


Idanunsa ya dago yace "are you not?"


Kanta ta kawar gefe tace "kaini mu wuce police station."


Da sauri ya juyo ya kalleta yace "muyi me?"


Tace "ko me zanyi meye naka a ciki? Kaini."


Shiru yai kafin yace "bakya tunanin kome ya faru gwara kiji ta bakinsa tukun na? Sannan yarinyar nan fa bakisan dame tazo ba."


Kallanshi tai zuciyarta na sake kuna.


Juyawa yai ya zauna, hawayen da suka zubo mata ta share tace "Kaini gida."


Okay kawai yace ya ja sukai gaba.


Suna isa ta bude motar ta fito, kallansa tai tace "ka tsaya."


Ta wuce ciki.


A falo ta tadda Goggo da Adam sunyi jugum jugum.


Ko kallansu batai ba ta wuce dakin Sadiya direct, sai dai ba kowa a ciki, ba ko kayanta a ciki, Adam wanda Goggo ta sashi ya tsuguna, shine ya kneel down.

Rufo kofar dakin tai sannan ta wuce dakinta ko kallansu  batai ba, takadda ta dauko da biro sannan ta fito falo.


Kallan Adam tai sannan ta ajiye mai takaddar tace "rubuta ka fita!"


Kallanta yai da sauri yace "na rubuta me Honey?"


Hannunta kawai ta dunkule wanda take jin kamar ta wanka mai mari, dan gaba daya kallan Fuskarsa ba karamin daga mata hankali yake ba.


Kallan Goggo tai tace "kice ya rubutan takardata sati uku duka sannan ku hada kayanku ku bar gidan nan cikin awa daya, in ba haka ba kuma wlh yan sanda zan kira, dukanku kunsan halina kunfi kowa sanin abinda zan aikata."


Goggo ta kwalalo ido hankali a tashe tace "Zainab me kike nufi?"


Zainab wacce ta dake tana kokarin hana wani hawayen zubowa gabansu tace "Daga sanda ya kawo karuwarsa cikin gidan nan na tabbatar ya riga ya ajiye igiyar aurena dake hannunsa, yafi kowa sanin bazan kara zama dashi ba, daga sanda kika mara mai baya gun zaman karuwarsa a cikin gidan nan na tabbatar kinsan karshen zamanki a gidan nan yayi."


Adam wanda ya kamo kafafunta ya rike ta kalla tace "rubuta ka fitar min daga gida, in kuma yan sanda kake jira suzo su fitar dakai to.


Ta hankadeshi ta wuce dakinta tasa key.


Adam hankali a tashe yaje bakin kofar da rarrafe, yana kuka "Honey ki taimaki rayuwata kunfi kowa sanin bazan iya rayuwa ba ke ba, Honey!"


Zainab dake zaune a kasa a dakinta, idanunta na zubar da kwalla, mikewa tai tunawa datai ko asuba batai ba gashi azahar har ta nufo, sallah tai ta zauna kawai akan sallayar tana kuka rike da wayarta.


Sunan Dady kawai take kallo a jiki, sannan ta dana kiran wayar Nabila wacce ta san a kashe take amma haka kawai taji tana sannta kira.




*****


Goggo cikin takaici ta matso gaban Adam kamar zata rufeshi da duka sai ta fasa tasa hannu ta dagoshi tace "zonan."


Adam ya kalleta yana kuka kai baka ce namiji bane, Goggo tace "yanzu Adam abinda zakajamin kenan? Banyi sa'ar jin dadi a gareka ba ina farin cikin ina jin dadi ta hanyar matarka yanzu itanma ka ja mana shiga garari?"


Adam yace "Goggo Allah banyi komai da ita ba, nasan nayi laifi daga kawota zuwa sha'awarta amma Allah Goggo abinda kuke tunanin ya faro bai karasa faruwa ba."


Hannu biyu Goggo ta dumamai a baya tace "dan ubanka yanzu da abu ya faru da karya faru meye amfaninsa? Ka manta ayanda muka ganka? Sannan dan dakikanta mai makon ma kana ganinta ka rufe jikinka sai ka tsaya galala, da uban wa yace ka kawo mana tsiya har cikin gidan mu?"


Zubewa tai ta zauna a kasan da yake tace "yau mun shiga uku wannan da zai kasheni da raina."


******


Kallan kan gadansu tai, da sauri ta rufe ido, jitai komai na cikin dakin batasan ganinsa, hatta sallayar datai sallah da sauri ta mike daga kanta daga ta rufe idanta Adam take ganowa da yarinyar daya kira da kanwarsa.


Dakyar ta canza kaya a dakin ko wanka kasa yi tai dan Alwalar ma dakyar tai in ta tuna Adam na shiga toilet din.


Jakarta ta jawo tasa kaya kala biyu ta dauko kayan aikinta ta banko kofa ta fito.


Adam da Goggo na zaune a bakin kofar, suna ganinta suka matso, Adam yace "Honey ki taimaka min wlh wlh ba abinda......."


Yanda ta watsa mai wani kallo ne yasa ya sha jinin jikinsa yai gum.


Goggo ce tai saurin cewa tace "Zainab nasan nina haifi Adam amma yadda na daukeki a raina yafi yanda na dauki Adam, ke kanki kinsan yanda nake sanki."


Zainab ta kalleta tace "ya rubuta?"


Goggo tace "dan Allah Zainab kiyi hakuri."


Zainab wacce ta kalli falan tana tuno yanda Sadiya da Adam da Goggo suka maidata mahaukaciya a gidanta, ta daure tace " zan turo yan sanda ina fita daga gidan nan, in kunso ku rubuta min takardata ku ajiyemin in kuma ba haka ba mu hadu a police station daga nan mu wuce kuto.


Sannan gidan nan yanzu zan sashi a kasuwa ruwanku ne ku zauna ruwanku ne ku fita, motar dana baka na barmaka dan dama kai na saiwa ku kashe kayanku a ciki ku fice min daga gidana, wannan shine uzuri na karshe da zan muku.


Goggo ce ta riko ta da sauri tace "Zainab ki taimaka kiyi hakuri wlh muma cutar mu tai tsinaniyar yarinyar nan."


Adam yana kuka yace "Honey kiyi hakuri dan Allah."


Cikin tsananin masifa ta juyo, kamar zata rufesu da duka  tace "inyi hakuri? Duk wani abu da ya kamata ina maka shi inama, nice shanka, nice tufafinka, kula da mahaifiyarka, komai na rayuwa na dauke maka shi amma ka rasa abinda zaka saka min dashi sai wanan? A gidana? Ka kawota kacemin kanwarka? Na bata gurin zama,  na dauketa kamar yadda na dauki kanwata, ashe karya kake min dakai da mahaifiyarka? Bazan taba yafemuku ba wallahi.

Idan har kunasan zaman lafiyanku ku ficemin daga gida na fada muku."


Ta juya rai a bace ta bar gidan, tana fitowa ta kalli Khalid dake jingine da mota yana nazarin abubuwan dake faruwa, me Adam yama kanwarta haka?

Wayarta yake ta kira anki dauka.


Bala ta kalla ta mai alama yazo, yana zuwa ta kalleshi tace "mutanen ciki zasu fita anjima, yanzu ka kira key walder ya canza min key din kofar nan yanzun nan, sannan kafin dare su barmin gidana, su baka takarda ka ajiyemin, in basu fita ba zuwa dare ka kirani a waya zan turo wadanda zasu fitar dasu.


Ta bude mota ta shiga, kallanta yai, hade rai tai ta shiga ta zauna.


Baice komai ba ya shiga ya zauna shima tace " mu bar gidan."


Yace "okay!"


Yana san tambayarta yarinyar amma baisan shiga abinda ba'a sashi a ciki ba.


Yana tada mota Adam da Goggo na fitowa da sauri, ya dan kalleta ta glass.


Muje!


Shiru yai yana kallan Ada da Goggo, kallanta ya sakeyi.


Please! Abinda ya fito daga bakinta kenan hawaye na gangarowa.


Jan motar yai suka bar gidan.


Tafiya kawai suke batace komai ba shima baice komai ba, ina zani?


Abinda kawai yake zuwa mata kenan, jitai Khalid yace "ina zamu?"


Kallan window tai tace "ina zani?"


Cikin sanyin jiki ya dan kalleta.


Kallansa tai tare da murmushi tace "hotel?"


Yace "Hotel?"


Tace " kaini ko ma inane, inda bazan sake ganinsu da abinda ya dangancesu ba."


Shiru yai baice komai ba, yana tunanin yanda zaiyi da ita.


Wayarta ta dauka ta kira director tace "zata dau hutun sati daya batajin dadi."


Mamaki ya kamashi yace "Zainab sosai ne rashin lafiyar? Kinsan muna bukatarki dayawa."


Ka taba ji na dau hutu? Ko hutuna ina dauka ne na shekara?"


Yace "kiyi hakuri, naji abin ne sama ta ka."


Zan dawo nextweek.

Bata jira amsarsa ba ta kashe wayar.


Shiru tai.


Khalid yace "ina zamu?"


Kanta ta kwantar jikin kofa tana tunani, batasan kasancewa ita kadai a wannan lokacin tana ganin in ta zauna ita kadai lalai ciwon zuciya ne zai kasheta, to ina zata? Wa take dashi? Wayyo rayuwata? Allah nasan ni mai laifice ka dubeni.


Ta karasa tare da rufe idanunta.


Khalid yai shiru yana tunanin yanda zaiyi da ita.


Idanunta a rufe tace "muje Danbatta."


Bai san sanda yai dan burki kadan ba, ya kalleta tare da yin parking yace "danbatta? Bazaki iya zama a gidan mu ba."


Idanunta ta bude sannan ta kalleshi tace "cema nai gidan ku?"


To ina?


Tace "Gidanku."


Yace "mene?"


Da tana tunanin zuwa gun Dr ne dan tasan yayarsa sosai, ta taba zuwa gidanta a danbatta sau daya, sai dai jin kalaman Khalid yasa ta canza tunani.


Kallanta ya sakeyi yace "me zakiyi acan?"


In naje ni zanga mai zanyi.


"Bangane ba, a wani dalilin xaki bar gidanki ki tafi wani gidan?"


Gidana?


Ta tambaya tana kallansa, idanunta suka sake cicikowa, jin sunan kadai ma tada mata hankali yake.


Tace "ba sai ka wulakantani ba, ajiyeni anan ka tafi, zan je inda nake so da kaina."


Shiru yai yana tunanin wannan al'amari.




********


"Yau mun shiga uku, yanzu ya zamuyi?"


Wannan da wannan da.....

Ta kalle Adam wanda yake rabe jikin kujera, tace "yanzu da uban me zamu tsira? Duk ka gama cinye dan gadan mahaifin naka agun tsinanen karatun da bansan me ka karanta ba, sannan yanzu gidan matar taka ma gashi ka mana sanadi."


Adam ya kalleta baice komai ba.


Haushi ya tuke ta yace " yanzu ya zamuyi?"


Adam ya kalleta yace "Goggo Zainab ta gama rabuwa dani kenan har abada, yanda ta tsani mahaifinta akan abinda yai, ni na san yanzu ko zata mutu baxata taba kara zama dani ba, na shiga uku na Goggo."


Goggo a kufule tace "mun shiga uku dai, kasan da aka uban wa ya saka."


Wayyo yau nikam me zan gani rayuwata ta juya min a lokaci daya.


Can tace "Ina tsinaniyar yarinyar nan taje? Wlh ko zan karar da zanin daurawa ta sai na nemota."


Ta karasa da matse kwalla, kanta ke wani irin ciwo.


**********

Ayusher🏌🏻‍♀[11/25, 3:59 PM] Maman Zara Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{31}


  Kallansa tai sannan ta dauke idanta tace " akwai inda zani acan"


Bai tada motar ba sai dai yana nazari, kallansa tai tace "muje!"


Motar ya tada suka fara tafiya, hannunta rike da wayarta tana kallan sunan Dady, can ta danna kira.


Ringing uku aka dauka, sai dai me? Jitai muryar mace, Basma daga can take "Zainab?"


Da sauri Zainab ta kalli wayar wani abu ya tokareta, Basma tace "yahkuri na daga wayar, yanzu ya dawo break daga gun aiki ya shiga toilet ne."


Kashe watarta Zainab tai sannan ta rufe idanunta kamar mai bacci.


Har suka shiga danbatta bata bude idanta ba da alama daga tunane tunane bacci yayi gaba da ita, suna kan titin shiga danbatta ne yace "ina ne unguwar?"


Shiru yaji hakan yasa ya duba mirror din gabar motar, ganin tana bacci yasa yace "Hello!"


Zai sake magana yaga ta farka a zabure, tana Inalilahi wa Inalilahi Raji'un.


Idanunta ta bude a tsorace, tana maida numfashi, Khalid ya gangara gefen titi.


Kallansa tai ta tana jin haushin yanda yake gaminta yanayin da bata san kowa ya sameta a ciki.


Daurewa tai tace "muje."

Yace "inane?"


Kallan garin tai sannan tace "I don't know."


Juyowa yai ya kalleta yace "You don't know?"


"Hmm yafi shekara biyar dana zo i can't remember."


Baisan sanda wata dariyr rainin hankali ba, haushi ya kamashi yace "then ki kira kaninta muji."


Wayarta ta dauka ta kirashi, daga can yace "Zee kece?"


Tace " Sabir Aunty na nan kuwa?"


Aunty Amina?


Eh

Yace "mijinta ya koma Abuja da aiki ya akai?"


Okay shikenan, kafin ya sake magana ta kashe wayarta.


Khalid ta kalla tace "batanan."


Baki yadan bude yana kallanta kafin ya danyi wani abu daga cikin kirjinsa zuwa bakinsa, yace "yanzu ya za'ayi?"


Oho!


Fuskarsa ya hade yace "Then zan iya ajiyeki anan na tafi."


Kallansa tai da sauri sannan ta kalli waje tace "anan?"


Kai ya daga mata alamar eh sannan yace "kina tantama?"


Tace "shikenan, ka barni anan din."


Daurewa yai ya juyo ya kalleta duk fuskarta ta kumbura, idanunta sunyi jaa samansu sun kumbura yace "Am sorry na san ba hurumina bane sai dai yau ma zan sake ciga hurumin da ba nawa ba, wannan zabin kina gani shine ya dace?"


Dagowa tai daga jinginar datai tace "me kake nufi? Ba dai kana so kacemin na cigaba da zama da mijin da na kamashi da mace a cikin gidana ba?"


Gabansa ne ya fadi, abinda ya faru kenan? Yanayin fuskarsa ne ya canza dan ya tausaya mata, kauda kanta tai ganin kallan tausayin da yake mata tace "meye laifina? Kula dashi danai ko kuwa kula da mahaifiyarsa? Meye laifina dan na kula da mijina? A tunanina inayin daidai gwargwadon abinda zan iya bansan menene laifina ba........"

Hawayen da taji suna neman zubo mata ne yasa ta kasa cigaba da maganar, Khalid ne ya kalleta duk da tausayinsa daya kamashi bai hana cemata "kina tunanin duk abinda ya faru baki da laifi kenan?"


Kallansa tai bayan ta dake tace "fadamin menene laifina?"


"Wani irin rashin kula da rayuwar da bataki ba da kikeyi da har za'ace bakisan kanwar mijinki ba? Wannan wace irin rashin kula da gidanki ne?"


Shiru tai tana tunani, tabbas duk matsalar daga nan ta fara, datasanta da duk.....


Dakewa tai tace "Naji wannan ne laifina bayan shi kuma fa?"


Shiru yai yana kallanta kafin yace "komai daya faru rabi naki ne, sannan bakya tunanin gidanku ya kamata kije?"


Fuska ta hade sosai tana kallansa kafin tace " tafi ka barni anan.


Bai kulata ba yaja motar suka cigaba da tafiya itama haushi baisa tace komai ba.


Wayarta ta daga ta kira Bala.


Bala na tsaye a na canza key din gidan wayarta ta shigo, ya gaisheta.

Tace "sun tafi?"

Yace "a'a."


Takardar fa?


Bai nan komai ba.


Shikenan tace ta kashe wayar.


A bakin kofar gidansu yai parking, sannan ya kalleta yace " ki kwana anan gobe na maidake gidanki."


Kin kulashi tai bata kalleshi ba, fita yai daga motar shima ba tare da yace komai ba ya dau jakar ta a booth ya shiga ciki.


Da wani kallo ta bishi tana mamakin hali irin nasa, ko kadan baya burgeta namiji sai tsinanen zafin rai? Ita sam ta tsani namiji mai gadara da neman isa.


Khalid ne ya shiga ciki.


Yana shiga tsakargida yaga Asiya a tsaye tana kiran su Amie su fito su wuce islamiya, kallanta yai tana ganinsa ta matso tana yaya an dawo?


Eh Asiya in zaki wace kiyima bakuwa magana a cikin mota kice ta shigo.


Bakuwa? Mota? Kallanta yai bai amsa ba ya wuce ciki.


Su Amir na ganinsa suka gaisheshi suka fito da gudu suna sa takalmi.


Umma data idar da sallah ne a daki ta fito tace "Khalid? Kaine da ranan nan?"


Zama yai kusa da Abba yana cewa eh wlh.


Kallan Abba yai sannan ya kalli Umma dake kikarin zama, Abba yace "ya akai?"


Dan hannunsa yasa ya shafi keyarsa yace "matar danake ma aiki ne muka taho tare."


A tare sukace "ina?"


Khalid yace "ta samu matsala da mijinta ne shine na kawota nan kafin komai ya warware."


Fuskar Abba dauke da mamaki yace "iyayenta fa?"


Khalid yai dan shiru kafin yace "ba'a kusa suke ba, da alama kuma batada kowa a kusa."


Umma tai shiru kafin tace "kace ta shigo ne?"


Na fadawa Asiya, shiru sukai suna tunannin wannan abu.


Asiya data fito ne ganin mota a kofar gidansu yasa ta nufeta, Amir yace "Ya Asiya motar yaya ce?"


Bata kula su ba ta nufi motar.


Zainab dake ciki ta bude kofar tana kallanta, Asiya ta gaisheta cikin nutsuwa sannan su Amir ma suka gaisheta.

Kanwar sa?

Asiya ta daga kai tace "eh, ya Khalid yace ki shigo."


To, islamiya zaku?


Tace "eh Aunty."


Zainab tana tsaye tana kallansu gar suka wuce tai murmushi tace da alama age mate din su Nabila ce sai dai ta fisu nutsuwa, tunowa tai da fadan da sukeci haka kawai ta samu kanta da murmushi.


Kallan gidan tai bayan tazo jikin kofa ta tsaya, itadai ta kasa shiga ciki.


Abba ne ya kalli Khalid yace "ka shigo da ita bakowa ne zai iya shigowa gidan mutane kai tsaye ba."


Nan Khalid ya mike ya fito.


A waje ya ganta tana ganinshi ta hade rai, shima fuskarsa a hade take yace "ki shiga."


Wucewa gaba tai kai kace gidansu ne, tun daga tsakar gidan take mamakin gidan, gidane dan karami, soro inda dakin Khalid yake sai kofa ta ciki, kana shiga dan madaidaicin tsakargida ne wanda aka sumumteshi tsaf, daga gefe akwai rijiya, sannan bandaki a ta gaban rijiyar.


Daga can kusa da asalin cikin gidan kuma kitchen me a gun, gefen kitchen din kuma inda suke sa murhu ko gawayi.


Sai dai kidan a share yake tsaf, hatta gun wanke wanke an wanke gun tas, duk da ta raina gidan amma ta aminta da tsaftar gidan a haka suka shiga, Umma na tsaye a kan barandar tana ganinta ta fara lale lale da babbar bakuwa.


Zainab ta shigo cikin kunya.


Umma ta nemi data shiga cikin falan, Zainab ta shiga, Abba ne a zaune ta gani kafarsa daya babu yana jingine da bango duk da haka yana ganinta yace "barka da isowa."


Zainab ta zauna ta gaisheshi sannan ta gaida Umma, Khalid dake tsaye ya juya ya bar falan.


Tana ganin yabar falan kunya ta kara kamata, Abba ya kalleta bayan ya amsa gaisuwar yace "ashe abu kuma baiyi dadi ba?"


Kasa tai dakai batace komai ba, yace "bakomai ki zauna anan sai ki kira mahaifinki asan abin yi."


Gudum yin musu yasa kawai tace to.


Umma ce ta nuna mata dakin Asiya nan ta mike ta shiga, gaba daya itakam kunya ma takeyi, ya akai bata tafi hotel ba?


Umma ta shiga ajiye kawo mata abinci, kunya ta kara kama Zainab dole ta mike ta tayata ajiyewa.


Umma ta zauna kusa da ita tace "karki sa komai a ranki kiyi sallah kici abinci ki huta, Allah zai kawo mafita kinji."


Kallan Umma tai haka kawai tunanin Ummy ce a kusa da ita yazo mata, idanuntane suka ciciko a hankali hawaye ya zubo mata.


Umma ta kalli yanda duk idanunta ya kumbura, tausayinta ya kamata tace "yahkuri kinji."


Zainab ta share hawayenta sai dai ta kasa cewa komai, kawai jitai ta nasan Umma ta rungumeta ta rasa me yasa take ganin kamar Ummy ce a gun.


Umma ganin yanda take kallanta yasa ta fahimceta, rungumeta tai tana cewa "bakomai kinji, insha Allahu Allah zai kawo miki mafita duk da bansan me ya faru ba amma nasan ke mace ce ta gari."


Kamar ta tabo Zainab kawai Zainab tasa kuka, wannan kukan jitake kamar a jikin Ummy take yinshi.


Khalid wanda ya fita siyo juice a shagon kusa dasu me ya dawo rike da leda, yana shigowa yani yanda Zainab ke kuka, kusa da Abba kawai ya ajiye ya fita zuciyarsa na tausaya mata.


Wayar Abba ya dauka ya fita Yana fita ya daga waya ya kara kiran Razy.


*****

Ayusher🏌🏻‍♀

[11/25, 3:59 PM] Maman Zara Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{32}



**********


Goggo na zaune tana ta cusa abinci kana ganin kasan cin dole da cin yunwa take ma abinci, Adam na zaune a gefe cikin takaici yace "yanzu Goggo har kinsamu damar dafa indomie kina ci? Muda rayuwarmu take neman shiga garari?"


"Kana sane ko jiya tsinaniyar yarinyar nan bata banni naci abinci ba so kake na muti kafin ma samu ba Zainab hakuri."


Kallanta yai gaba daya duk ya canza, kana ganinsa kasan a birkice yake, yace "Goggo koza'a mutu Zainab bazata taba komawa dani ba, kema kinsani, yanzu akam takardarta wlh sai ta kaimu kotu."


Goggo ta tsame hannunta daga plate din ta kalleshi tace "duk ba kai kaja mana wannan masifar ba."


Da sauri yace "wai kin dane zancen ni naja mana ki nemo mana mafita ko kuwa? Abinda ya faru ya faru amma Sai kara tusawa kikeyi, dana sani ke kanki kinsan nayi, haryanzu bansan uban me ya shiga kaina ba."


Goggo ta kalleshi bayan tasha ruwa tace "nidai mafita daya ce yasin bazan koma kauyeba, kasani tunda kai aure matarka ta dakoni ko da wasa ban sake zuwa can ba, kanina inya ishen da zancen Sadiya nasan abin makaranta kana kallo Zainab ke taimakawa mu tura, mo hanyar ban komaba kuma wlh yanzu bazan koma ba."


Cikin masifa yace "nima cewa nai mu koma? Tambayarki nake yanda zamuyi."


Itama cikin masifa tace "kaina zaka huce? Uban wa yasa ka ja mana?"


Haushi ne ya kamasu duka kowa yai shiru.


Adam ta kalla sannan tace "wai kai da uban me kake da kudin da take baka duk wata?"


Haushi ne ya kamashi bai tanka mata ba.


Goggo ta sake cewa "ko kuma me kale gani idan ka bata takadar sai dai kace mata bazaka bata takardar saki ba harsai ta barma gidan nan."


Kallanta yai da sauri yace "mene?"


Goggo tace "kana gani dai korarmu za'ai nan da awa anjima kaga dai key ake canzawa, kuma wlh tunda ta furta ko za'a mutu sai ka bata takardarta, gwara muma mu cafki gidan, ai harga Allah kaima cutarka kuliyarcan tai."


Shiru yai yana kallanta kafin yace "kina tunanin Zainab zata yadda?"


Tace "karma ta yadda, in bata yadda ba kace mata kuje kuton ai ita idan gari ce aikin gidan tv take mutane dayawa sun santa bazata taba bari sirrinta ya fito duniya ba, kasan yanda take san aikin nan nata."


Kai ya jinjina cikin gamsuwa sannan yace "Goggo Allah banasan rabuwa da Honey."


Yai maganar kamar mai shirin kuka.


Tace "inka kara cemin Honey sai na wankeka da mari shasha shan banza, kai dai wlh banga amfanin ka ba, sam ni na rasa banzan hali da sokon tunaninka."


Adam yai shiru gaba daya hankalinsa ya kasa nutsuwa, wani bangare na zuciyarsa na kwadaitamai abinda Goggo tace.


Goggo ta kalleshi tace "tu ra mata sako a waya, ka fada mata in tanasan takardarta sai ta baka gidan nan."


Da sauri yace "yanzu?"


Tace "da sai yaushe?"


Nan ya dako waya yana kallanta.


••••••••••


Rasy dake kwance Bash na gefenta yana neman kai hannu cikin rigarta ne ta buge hannun sannan ta kalli wayarta dake kara, dagawa tai tace hello.


Khalid yace "Raziyya kinga dama kin daga?"


Nan ta fahimci waye tace "Drivern mota kiran wayar na menene? Na tabbatar banci bashinka ba."


Murmushi yai yace "kin bayyana kanki ko sai naje gidanku na fadawa iyayenki abinda kikeyi?"


Da sauri ta mike tsaye tace "gidan mu?"


Yace "eh kokin dauka bawanda zai san inda gidanku yake?"


Kumbura fuska tai cikin bacin rai, Khalid yace "mu hadu dake gobe a kano, zan kiraki inji inda kike, kada ki kuskura kik'i daga wayarki inba haka ba zan wuce Naibawa yar lemo na fadawa iyayenki abinda kikeyi, Ahhhhhh bansan ya zasuji ba insuka ji, bayan yayarki ta rasu, ina tsoron halin da zasu shiga."


Yana kaiwa nan ya kashe wayar.


Cikin takaici da bacin rai tabi wayar da kallo, a Zuciye ta cillar da wayar kan gado sannan tai wata kara mai karfi tace "Kyankyasan nan......."

Bash ne yasa hannu zai riketa kafa ta sa ta haureshi a matse matsin kafarsa, wani irin kara yasa shima tare da durkushewa a gun.


*********


Umma zama tai a gabanta Zainab Taci abinci sannan ta fito daga dakin bayan taga ta zauna tana hutawa, Zainab tabi bayanta da kallo cikin wani yanayi.


Abba dake falo ne ya kalleta yace "Uwar 'ya an fito?"


Zama tai kusa dashi cikin tausayi tace "da alama batada wanda zata dogara dashi taji dadi."


Kallanta yai yace "kamar ya?"


Kai ta girgiza alamar rashin sani tace "haka kawai nakeji kamar ta dade cikin kewa tana neman wanda zai dubeta."


Shiru Abba yai cikin tausayinta shima.


Zainab ta kalli hoton Ummy a wayarta tai murmushi tare da kwantar da kanta akan dan karamin gadan Asiya, Ummy na!


Ta fada tana shafar hoton, sako ne ya shigo wayarta, kallan sakon tai cikin mamaki ta kara karantashi.


Gaba daya mamaki ne ya kamata, duk da tasan karshen zamanta da Adam yazo amma bata taba tunanin zai nemi bata takardarta bugu daya ba, sannan abinda ya kara bata mamaki wai ta bar mai gidanta?


Wata dariyar bakinciki ta saki tace "Ummy wace rayuwa nai duk tsawon shekaru na???? Me yasa nake gani kamar duk wahalar danasha bata biya min komai ba??"


Umma ce ta turo kofar dakin, Zainab ta kalleta tare da gyara zama, Umma ta ajiye mata ledar juice din tace " badai tunanin kike ba?"


Kallanta tai tana san fada mata abinda ke ranta amma gani take daga ganinta sainta zake???


Kai ta girgiza tace "a'a."


Umma tace "ko nazo mu zauna tare? Dama na fita ne na dauka kina san hutawa."


Zainab tai murmushi tace "zan kwanta ki huta kema."


Nan Umma ta juya tana murmushi.


****


Tana fita Dady ya kirata a waya, kallan wayar tai kafin ta daga.


Daga can yace "Zainab ashe kin kira?"


Murmushi tai tace "eh na kira dazu."


Yahkuri bangani ba sai yanzu dana dau waya zanyi waya ma ga kiranki.


Shiru tai kenan Basma batace mai komai ba ko me?


Tace "dama kira nai mu gaisa ta daga tace kana toilet."


Oh Basma ta daga? Ai bansani ba saboda ina fitowa na taho kila shiyasa bata samu damar fadamin ba."


Zainab tace "bakomai."


Ina aiki ne in na tashi ma kira, kafin ta kara magana

ya kashe wayar da alama aiki yake sosai, sai dai ba karamin sanyi jikin ta yak ba ta kwanta kawai ta rufe idanunta.


😪


***********

Ayusher🏌🏻‍♀

[11/27, 7:28 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{33}


Wajen sallar magrib su Asiya suka dawo, har lokacin Zainab na zaune tana nazarin wannan rainin hankalin, yanzu ne ta tabbatar ma kanta baxata sake kuka akan Adam ba domin kuwa ya nuna mata dama can ba santa yake ba abin hannunta yakeso, duk da tasan hakan kafin auransu amma ita a nata tunanin zaman da sukai yanzu yaci ace tafi abin hannunta daraja agunsa, daga wannan lokaci tayi alkawari hawayenta bazai kara diga akansa ba.


Sallama taji tare da dan turo kofa, amsawa tai tana kallan kofar.


Asiya ce ta shigo har kasa ta tsuguna ta gaisheta, Zainab ta amsa cikin jin dadi sannan tace "kun dawo?"

Eh Aunty

Ta fada tana mikewa, Zainab ta danyi shiru kafin tace "kiyi hakuri bakuwa ta tare miki daki."


Murmushi tai tace "bakomai Aunty."


Kayanta ta dauka ta fita daga dakin, da kallo ta bita tanaji inama su Nabila na nan ta nuna musu mutsuwar yarinyar, haka kawai ta samu kanta dayin murmushi.


Fitowa tai zatai alwala ganin magrib tayi, kunya takeji sosai gani basuda hadi da juna gashi sun amsheta kamar yar su.


Tana bude kofa taga Umma a bakin kofar, dariya sukai a tare, Umma tace "yanzu dama zance ki fito kiyi alwala, ashe kin taso."


Dariya tai batace komai ba, a tare suka fito ta kara gaida Abba sannan suka fito tsakar gida.


Umma ta wuce ta duba miyar dake kan gawayi, shiru Zainab tai tana kallan yanda take gyara wutar, kafin ta wuce dan toilet din, alwala tai sannan ta fito.


Asiya dake shimfida babbar tabarma a kan baranda ne taji tace "Umma yaya ya fita ne?"


"Bansani ba wlh sai dai ki duba dakinsa."


Umma ta kalli Zainab tace "Kin fito?"


Zainab tace eh tare da wucewa ciki, bayan ta ajiye botar.


Bayan Sallar Isha'i tana zaune rike da wayarta tana kara maimaita sakon Adam, Asiya ce ta shigo dauke da tiren abinci ta ajiye mata, sannan ta juya.


"Kazo Danbatta gobe gidansu kwaro, naji yanda zan bar ma gidan."

Haka kawai ta turamai ta ajiye wayar tare da kurawa kwanan gabanta ido  tana tunanu, kauda tunanin komai tai a ranta sannan ta bude kwanan.


Tuwo ne na semovita miyar kubewa danya, murmushi tai tana tuno rabanta da tuwo, dan sam Goggo da Adam basa san tuwo shiyasa ma ba'ayi sai jefi jefi.


Tana cin abincin tana jiyo hirarsu a tsakar gida, jin gaba dayansu ne a wajen yasa idanunta suka dan ciciko tunda take a tsawon rayuwarta bata taba zama da iyayenta da kanenta ba ana hira haka.


Haka ta ci tuwon sosai, jin kunyar sai dai a kawo mata a dauke mata ne yasa ta kwashe kanukan ta fito.


Hira sosai suke ana tsokanar Asiya tana ta rantsuwa, tana ganinta ta mike ta anshi tiren.

Umma ta kalleta tace "Zainab zo ki zauna anan."


Kallan Khalid tai wanda kansa ke kan bare gujiya, wacce sai yanzu ta kula da abinda ake, Umma tace "kin iya ci?"


Kallan gujiyar tai dan bata taba ci ba sai murmushi kawai datai, Abba ne yai dariya yace "da alama bata taba ci ba."


Amir ya sa dariya yace "Abba yanzu a duniya dama akwai wanda bai taba ci ba?" Ya fada yana cin wani.


Asim ya dan ture shi yace "wlh a santi yake wannan da rake ake sha ba'a san tsoyar dazai ba."


Dukansu ne suka sa dariya har ita zainab din wanda ta kaudakai tana dariya.


Takowa tai a hankali ta zauna daga kusa da Asiya, Umma tace "ko a dauko miki pillow?"


Da sauri tace "a'a."


Khalid ne ya kalleta kadan sannan ya dan tura kwanan dan gefensu kadan.


Amir ne ya ja kusa dasu yana cewa Yaya to ita Aunty da kakema Tuki data dawo nan gidan kenan ka daina aikin?"


Abba ne yadan talle mai keya yana cewa "to Barrister uban san jin magana."


Nan suka cigaba da hira ana dariya, Zainab kam gaba daya abin sha'awa yake bata, har sai wajen 9 Khalid ya mike ya koma daki, nan suma suka sake hira kadan kafin suka shiga ciki.


Asiya ta kalla tace "ina zaki?" Ganin ta dau bargo tana neman fita.

Asiya tace "Umma tace na kwana a dakinsu Amir su zasu kwana a falo."


A'a kwanta anan, ta fada tana nuna mata dakin.


Asiya tai murmushi tace "to Aunty."


Bargonta ta shimfida a kasa, ta sa pillow sannan ta fito ta fadawa Umma yanda sukai, ba karamin dadi Umma taji ba.


Can wajen 11 Asiya nata baccinta Zainab tai shiru tana kallan yanda maganin sauro ke ta fitar da hayaki, mikewa tai ta sa hijab dinta ta fito falo a hankali ta fita waje.


Ido ta kurawa sararin samaniya wanda farin wata ya haskashi sosai.


Gefen baranda ta zauna ta zubawa sama ido tana tuno yanda tai rayuwarta da yanda ta wahalar da kanta da mahaifinta akan abinda batada hakki akai, yanzu gashi ita abinda take da hakki akai ma an nuna mata rashin matsayinta.


Tunda ta fito yake kallanta ta jikin window din dakinsa, yana zaune a daki yana karatun littafan daya siyo na aikin gidan tv da zasuje jarabawa, tunda harkar mass yai yana bukatar sani a wannan bangaren.


Haka kawai idanunta suka samu kansu da kallan window din dakin, ganinsa tai ta window, dan dakinsa haske hake tal da kwan wuta.


Mikewa yai ya fito daga dakin sannan ya nufo ta "akwai abinda kikeso ne?"


Kallansa tai bata san sanda tai wani murmushi ba tace "yau ya da magana ba kamar yanda ka saba ba?"


Dan kansa ya juyar gefe baice komai ba, kallansa tai sannan ta nuna mai guri tace "inasan tambayarka abu."


Kallanta yai sannan ya zauna daga gefe tare da kallan gabansa inda rijiya take.


Itama gabanta take kallo tace "wacece yarinyar nan?"

Raziya sunanta.


Raziyya! budurwarsa ce?

No.


Then?


Yayarsa ce budurwarsa.


Kallansa tai da sauri tace "kamar ya?"


Bai kalleta ba haryanzu yace "I don't know the details."


Shiru tai kafin tace "it doesn't matter to me anymore"


Yanzu kam kallanta yai yana mata kallan tambaya, murmushi tai na takaici sannan tace "kana tunanin zan cigaba da asarar rayuwata saboda mutum irinshi?"


  yace "kin tambayi kanki waya maidashi haka?"


Wani kallo tamai tace "Me kake nufi?


Ta tambaya tare da canza fuska, yace "I can't tell, ki duba ki gani da kanki."


Kallansa tai sannan tace "aiki yi ne bai samu ba, ko ni na hanashi samu?"


Samun kansa yai da wata dariya sannan ya mike tsaye yace "Yana nema kenan?"


Shiru tai tana kallanshi, tunda take ta taba jin inda Adam yai applying?


Kallanta ya sake yi sannan yace "Sai da safe."


Da ido ta bishi har ya wuce soro, hannu tasa ta dafa kanta, a hankali ta saki wani murmushin takaici, dan tabbas bata ma taba jin inda yai applying ba, sai dai in ta tambaya yace "yayi bai samu bane."


Haushin kanta ne ya kamata kenan tun ba yanzu bama suka maidata sokowa?


************


Bala ne a tsaye a bakin kofa yace "Goggo ku nake jira zan kule na kwanta."


Adam ta kalla dake gefe a kwance a kasa kamar mara lafiya haushi ya kamata, kafa tasa ta shureshi ya dago yace "wai Goggo meye haka?"


Kwanciya ma kai? Taga sakon?

Wayarsa ya dauka sannan ya kalla, da sauri ya kalli Goggo yace ta gani.


Me tace?


Ta fada tana saukowa.


Nan ya fada mata abinda tace, wata irin dariya tai tace "Alhamdulila dama nasan yarinyar nan yar albarka ce."


Adam ya kalleta yace "Goggo kina ganin hakan ne ya dace?"


Wani banzan kallo tamai tace "da ubanwa yasa ka soma yi?"


Haushi ne ya kamashi ya kalleta zaiyi magana muryar Bala ta kara katseshi "Dan Allah ku fito na rufe."


A zuciye ya mike yaje waje, kallan Bala yai yace "idan baka matsamin daga nan ba sai na koreka daga wannan lokaci."


Bala yace "Hajiya tace......."


Muryar Goggo yaji tace "ita Hajiyar ce tace ka tafi sannan daga gobe gida ya zama namu naga inda zaka cigaba da aiki."


Jikin Bala ne yai sanyi ya koma daki.


******


Washegari da sassafe Goggo ta tashi Adam ya taho danbatta.


Khalid nagun Salmanu suna wani aiki, yana so ya gama ya je kano gun yarinyar nan, yaji meke faruwa ya fadawa Adam a samu su fahimci juna su daidaita.


Duk da yasan ba huruminsa bane amma yana ganin hakan ne ya dace.


Adam sai da tambaya ya isa gidansu Khalid dam ya kira wayarshi a kashe.


Zainab na zaune a daki ko abinci ta kasa ci tana jiran zuwansa dan tasan tabbas da wuri zaizo.


Kamar daga sama taji Amir na fadawa Umma wai wani yazo yana waje, gun Aunty yazo.


Hijab dinta ta zura kawai Umma sai ganinta tai ta fito.


Dariya tai tace "ashe kinaji?"


Tace "eh Umma, ina kwana?"


Umma ta amsa ta gaida Abba.


Umma ce tace "mai gidan ne?"


Zainab tace eh, murmushi Umma tai tace "sai hakuri, nasan kema dole kiso ki koma, zuciyar mace rauni gareta."


Batace komai ba ta taso ta fito.


Adam na tsaye a jikin motarta yana karewa unguwar kallo ta fito.


Kallanta yai sannan yace "Honey!"


Bata ko tankashi ba ta bude mota ta shiga, shima shiga yai ya zauna mamaki ne ya kamashi dayaga ta tada motar taja sun fara tafiya.


Baice komai ba har suka fita dan wajen gari kadan, gefe ta gangara da motar sannan ta juyo ta kalleshi, idanunta ta dan rufe saboda abinda take tunowa, jitai ya kamo hannunta.

Da sauri ta bude ido ta kalleshi, Honey ki yafemin dan Allah, wlh kuskure ne.


Hannunta ta fizge sannan tace "kuskure? Hakane kuskure ne wanda ko wani dan Adam zai iya aikatawa, yanzu bani takardata na baka takardun gidan."


Da sauri ya kalleta yace "wai da gaske kike?"


Tace "kai kana tunanin zan iya zama a gidan daka kwanta da wata? Watan ma ba matarka ba?"


Shiru yai tare da sa kansa kasa, safe ta bude ta dauko papper da biro ta mikamai, tace bani ga takardun gidan a ciki."


Kallanta yai gaba daya jikinsa yai sanyi, yana hawaye ya rubuta saki daya, tace "daya? A haka zan baka gidan?"


Haka ya rubuta saki uku yana hawaye, amsa tai sannan tace "nagode da kyautatawa da amanata daka rike, yanzu na fahimci kula da kai da mahaifiyarka danai ba abinda ya dadeni dashi, ko da yake ance laifinane."


Kai ta jinjina tace "in aka duba dakyau hakan ne, kallansa tai tace "fitarmun daga mota."


Kallanta yai yace "takardun gidan?"


Wata dariya tasa tace "ohh"


Sannan ta sake kallansa ta hade rai tace "Kasan me ake kira da duk yanda akai da jaki sai yaci kara?"


Kallanta yai tare da firfito da idanunsa, tace me? So kake na fadama waye jakin?


Hucin fushi ya fara yi yace "ni kenan?"


Tace "kila."


Haushi ne ya tukeshi yace "Yanzu kina nufin dama ba gidan zaki bamu ba takardarki kike so?"


Dan kai ta kawai sannan tace "kai a naka haukar sai kawai na baka gidana saboda ina tsoronka? In dan saki ne ba ka san zan ita kaika kotu kaban dole ba? Da kai da wanda ya baka shawarar ka koma ka fada mata ta dinga yin tunani kafin ta bada shawara.....Ahhh bansan ko zaku iya tunanin ba dan na fahimci abin kamasal."


Kallansa ta sakeyi tace "fita!"


Adam yatuno basu da inda zasu, kallanta yai yace "Honey ki taimaka wlh bamu da inda zamu, dan Allah ki taimaki rayuwar mu."


Fita!


Honey ki taimaka mana dan All.......


Get Out nace.....

Yanda tai maganar cikin tsawa sai daya sani razana nima, ba Adam kadai daya fita ba nikaina sai da naji ina neman hanyar tafiya🙊🚶🏻‍♀


*****

Ayusher🏌🏻‍♀

[11/29, 2:03 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


_Faty Muktar Allah ubangiji ya jikan Baba ya kai haske kabarinsa, yasa mutuwa ta zama hutu a gareshi Ameen suma Ameen_


{34}


Knocking din motar ya fara cikin tashin hankali, Zainab tana zaune ta zubawa takardar ido, bata taba tunanin wannan lamarin ba, lalai Adam, kallansa tai yanata jijiga kofar motar, zuge glass din tai ta kalleshi, da sauri yace "Honey ki taimaka ki ban takardar dan Allah ki yafemin na tuba wlh, Honey ki taimaki rayuwata dan Allah."


Kallansa kawai takeyi, Honey dan Allah ki yafemin, wlh wlh bansan meya shiga kaina ba.


Daurewa tai tace "ka biyoni inda ka ajiye motarka ka dauka"


Da sauri yace "Honey ki bari mu tafi tare, dan Allah ki tsaya ki........."


Jan motar datai ne tai gaba ya sashi zubewa a kasa wani zazzafan hawaye ne ya zubomai.


Zainab tana zuwa kofar gidan ta ajiye motar a inda ya ajiye, tunanin wanda zataba key dinshi tai sannan tai hanyar ciki, tai sa'a sai ga Amir nan.


Yana ganinta ya karaso da gudu yana cewa "Aunty Umma nata nemanki."


Kallansa tai sannan ta mikamai key tace "Amir ka tsaya a jikin motarnan zakaga wani yazo yana neman key ka bashi wannan."


Amsa yai sannan tai ciki, tana shiga taga Umma a tsaye tana zagaye, Umma!

A hankali ta kirata tana kallanta, da sauri Umma ta taho, itama Zainab ta nufo ta, sai da suka matso kusa da juna sannan Umma tace "Alhamdulila dan na tsorata da akace bakya nan a waje ina tsoron kar wani abu ne ya faru kikai wani gun."


Tsayawa tai tana kallan Umma, ashe haka uwa ke da dadi?

Murmushi ta mata sannan ta nuna mata takardar tace "ya sakeni Umma."


Da sauri Umma ta amsa, da yake ba boko tai ba sai dan wanda Khalid ya nuna mata a gida ta dai dan fahimta gane cikin kokonto da sauri ta kalleta tace "Har Uku?"


Murmushi Zainab ta sakeyi tace "Eh Umma."


Shiru Umma tai tana kallanta, kafin tace "ki shiga ciki ki sanar da mahaifinki."


Kai ta daga sannan tai ciki, Umma ta bita da kallan tausayi sosai dan har sai dataji idanunta sun dan ciko.


Gun Abba ta nufa ta sanar dashi yanda akai, hankalinsa shima ya tashi yace "wannan wani sakaram miji ta samu dahar zaiyi saki uku lokaci daya?"


********


Adam kam yaci uban tafiya yana tafe kamar mara lafiya, dakyar ya iso ga uban yunwa dake damunshi, yana zuwa Amir ya bashi key ya tafi ball dinsa, shiru Adam yai yana kallan gidan data fito dazu, gaba daya ya rasa abinda xaiyi sai dai yasan duk abinda zaice yanzu a banza yake gwara yaje gun Goggo su samo shawara.


Jan motar yai ya fito, a hanya ya tsaya yasai biscuit da juice ya cucusa sannan ya karasa gida.


Bala na tsaye yana kallan Adam dake ta danna mai horn, Bala na kallansa bai ko binta kansa ba yana jin radio dinsa, haushi ne ya kama Adam ya fito a zuciye ya nufi Bala yace "kai Bala ka bude min gate ko sai na ci mutuncin ka?"


Bala cikin maganarsa ta hausar yan niger yace " Hajiya ta kira yanzu tace ku bar mata gida dan haka bazan bude ba."


Adam cikin kofula ya nufoshi, Bala ya kalleshi yace "ka tabbatar zaka iya dukana?"


Kallansa yai kamar zai karasa gunsa sai naga ya bude gate ya shiga, Bala yace "awa biyu na baku ku fito daga gidan nan, dan Hajiya tace inbaku fito ba na dau hukunci da kaina, sannan kunsan mu buzaye ba hakuri, nan da awa biyu yan sanda zasuzo inkunga dama karku fito."


Adam ya wuce ciki, haryaje zai shiga ya dawo da gudu ya zare key din motarsa dan dama ya saba wannan shirman balle in a gidane sau dayawa ma baya rufe motar.


Bala ya bishi da kallan takaici yana tuno abinda suka mai jiya, har fara yake su wuce awa biyun nan dan wlh sai ya rama wulakancinsa.


Adam ne ya shiga falo, Goggo na zaune ta soya dankali da kwai tana ci tana kallan tv, daga bakin kofa ya tsaya ya zuba mata ido, gefe ta hada tea dinta mai kauri.


Kallansa tai tace "Adam ka dawo?"


Kasa mata magana yai sai kallanta kawai da yake, kallansa tai tace "matsalarka kenan sai kai abu kazo kana nadama, kai dai dakai sa'a matarka nasan aikinta in ba haka ba uban wa zai bar ma gida?"


Haryanzu kallanta kawai yake tana cin abincinta tana magana, ganin yaki shigowa ne yasa tace "karka damu duk wanda yai saki da wanda aka saka sai yaji haka nadan wani lokaci amma komai zai warware a hankali, kazo kaci abinci naka na kitchen."


Ganin takaici yaki karewa ne yasa ya matso ya kashe tv din sannan ya kalleta rai a bace.


Kallansa tai tana kurbar tea tana harararsa kafin tace "uban wa yasa ka aikata? Da zaka nemi hucewa akaina?"


Huci ya fara yi yana kallanta, bata tankashi ba dan gani take duk saboda ya saki matarsa ne, abincinta ta cigaba daci, kawai jitai yasa kuka.


Kallansa tai tace "tashi kaje daki kayi abinka ni karka sani a gaba kamar ni na kashe ma aure."


Cikin masifa yace "bake kika kashemin ba amma kinada babban hannu a ciki."


Kallansa tai tace "a ina kenan?"


A zuciye yace "ta kwaci sakinta bata kuma bamu gidan ba, yanzu Bala yace mu fita nan da awa biyu."


Cup din tea din dake hannunta ta yar bata sani ba, tea din ya zube dan har kan cinyarta, ko zafin bataji ba dan ma ba tafashashe bane, Adam ne ya matso yana kuka yace "Goggo ya zamuyi?"


Kallansa kawai take kafin tace "Sakin ka bata kafin ta baka takardun gidan?"


Yace "cewa tai in na bata zata bani."


Baki kawai ta bude tana kallansa, yacigaba to na bata kuma ta koren dan da kafa ma na nufi gidan.


Nawa ka mata?


A hankali yace uku........


Wani wankenken mari yaji ta zabgamai, da sauri ya kalleta, rufeshi tai da duka ta ko ina da hannu biyu, tana dukanshi tana wannan wannan nikam bakin cikinka ne zai kasheni ban taba ganin mutum wanda gaba daya baida lissafi da tunani ba irinka, ka kwashe komai na gadon mu ka cinye a tsinanen karatun da ba abinda ya tsinana mana, kayi aure mun taho nan tunda aka bikinka ko kauye bamu kara zuwa ba sannan yanzu kazo kana cemin ka bada saki uku ba tare da ko daki biyu mun samu inda zamu zauna ba?


Adam kuka kawai yake yana cewa "na dauka zata bani wlh."


Daina dukanshi tai kawai ta fashe da kuka wiwi, Shikenan rayuwarmu ta kare munga ta kanmu."


Adam yana kuka yace "Goggo nanda awa biyu yan sanda zasuzo su koremu."


Kallansa tai kamar ta kara jibgarsa sai dai a wannan lokacin mafita take nema, wayarta ta dauko ta hau kiran Zainab, ta roketa ko dakin waje ne ta taimaka ta barsu su zauna, duk yanda ta kira Zainab bata dauka ba, daga baya ma ce mata akai wayar a kashe take.


Hankalin Goggo ya sake tashi matuka.


Kallan Adam tai da sauri tace "tashi mu hada kaya, duk wani abu mu tattare mu debi rabanmu."


In muka kwashi kayan ina zamu?


Tace "kai ka tafi wani gidan ka kwana ni zani gidan Hajiya bilki na dan kwana biyu sai musan abin yi."


Kallanta yai yace "ni banida inda zani, Ziyad bayanan sannan ko yana nan ma a gidan iyayensa yake kwana anan, Goggo ki taimaka ki tafi dani"'


Wayarta ta dauka ta kira Hajiya bilki sai dai tai rashin sa'a domin bata kasar sunje sari dubai.


Hankali a tashe ta kalli Adam, nan ta sake kiran wata kawarta, ita kuma jin zatazo kwana yasa tace tanada baki, Goggo hankalinta ya tashi nan fa ta shiga kiran duk nambobin kawayenta dana kusa da wadanda ba wani ma shiri suke ba, sai dai duk wanda yaji kwana zatazo sai ya fara kame kame da alama dukansu bamai san tazo kwana.


Hankalinta a tashe tace kafin yan sanda su wulakantamu a unguwar nan ka tashi mu kwashe kaya tunda kunada yar motar nan masan yanda zamuyi.


Haka suka kwashe kaya, Goggo sai data kwashe duk wani fruit da juice na gidan, taso kwasan su dankali Adam yace a ina zaki dafa inkin dauka? Haka ta ajiye amma sai data kinkimi indomie da taliya.


Haka su fito sukai ta lafta kaya a boat din mota a waye, Bala na ganinsu ya fara waya wai da yan sanda yana cewa kuna hanya? To sai kun iso.


Goggo naji suka sake rudewa, haka suka fito Adam najan Goggo tana makalewa dan itakam wannan gida bata san barinsa, suna zuwa gate ta koma ciki da gudu tana kuka.


Falo ta koma ta zauna akan kujera, Bala da Adam ne suka biyota, Bala yace "Goggo kin fito ko sai na radeki?"


Kallansa tai tace "ka radeni amma bazan bar gidan nan ba."


Dariya yai yace "to ki zauna bari su karaso."


Adam ya kalleta yace "Goggo?"


Wani mugun kallo tamai tace "nikam ka ciceni wlh, kai dayin tsiya ni da shiga tashin hankali?"


Adam zaiyi magana sukaji ana bubuga kofa, kallanta yai da sauri yace "gasunan ki fito kafin a toxartamu."


Mikewa tak ya jawota tana tafe tana tirjewa kai kace karamar yarinya ce, a haka suka isa gate, Lokacin Bala ya bude musu.


Kallansu sukai sannan suka kali Bala ogan yace "wad'an nan Hajiyar take nufi?"


Bala yace eh

Kallansu yai yace "kum wuce ko kuwa?"


Haka Adam yaja Goggo ya cusata a mota suka tafi."


Bala ya bisu da harara badan Hajiya tace duk abinda suka dauka karya hana ba ai da sai ya kwashe kayan da suka kwaso.


Suna tafe a hanya goggo na hawaye, daga ta tuno sai ta make Adam.


*******


Khalid kam wanda baisan abinda ake ba daga gun aikinsu da Salmanu ya wuce tasha ya hau kota zuwa kano, yana isa ya kira Razy wacce gaba daya tun jiya take cikin tashin hankali, haka ta daga cikin takaici, Khalid yace kina ina? Ko kina gidanku?


Da sauri tace "ina Tarauni, nan ta sanar dashi inda take."


Haka ya hau adaidaita ya karasa gidan data kwatantamai sannan ya kirata.


Fitowa tai dan tun jiya ta kori Bash ita kadai ce a gidan, a kofa ta ganshi a tsaye, baki tadan tabe ganin ko  mota bashi da ita.


Kallansa tai tace "anan zamuyi maganar?"


Yace "eh"


Kallansa tai tace "ko ka shigo ciki?"


Kallanta yai yace "bana shiga gidan karuwai."


Labanta ta ciza cikin takaici tace "to anan zamuyi maganar?"


eh.


Haushi ne ya kara kamata ta kalleshi rai a bace, jingina yai da bango, tace "ka shigo jikin gate din to banasan sirrina ya fita ne."


Yanzu kam ya dan kalleta sannan ya dan shiga ya tsaya daga jikin gate din.


Kusa dashi taje ta tsaya, kallanta yai yace "Me nene tsakaninki da Adam da har kika lalatamai rayuwa?"


Hannunta ya kalla wanda ke kokarin taba kirjinsa, kallanta yai sannan yai wani murmushi yace "me? Nima seducing dina zakiyi?"


Cikin kallan jan hankali tace "kai ba namiji bane."


Biro ya ciro ya ture hannunta dashi sannan ya kalleta yace "you can't seduce me ko kayanki kika cire a gabana."


Kallansa tai tace "do you have that confidence?"


Kai yadan karkace ya daga mata kadan sannan yace "you are not that attractive bansan ya akai kika jan ra'ayin maza ba, ahhh na tuna suma tunaninsu ba daya yake ba."


Fuskarta ce ta canza, ranta yakai matuka gun baci tace "am not that attractive?"


Yace "badai sun miki karya akan you are ba?"


Yanda take kumbura take hura hanci ne yasa yasan taji haushi sosai kallanta yai yace "fadamin menene tsakaninku?"


"Kai meye tsakaninka da Zainab? Meye naka na shiga abinda bai dameka ba?"


Kallanta yai yace "inje Naibawa?da alama can zan fi jin komai."


Da sauri tace "zan fadama."


Kallanta yai yace "meye tsakaninku?"

Bakimta ta ciza idanunta suka ciko tace "kasan bakar rayuwar da muka fuskanta akansa?"


Kallanta yai baice komai ba, hawayen da suka zubo mata ta goge sannan ta kalleshi idanunta na kara cikowa tace "Abinda ya mana ko rabinshi ban mai ba, mu gaba daya rayuwarmu ya salwantar shifa? Rabashi kawai nai da matarsa."


Kawai? Ya fada yana kallanta, kome ya muku meyasa baki fadamai ya nemi yafiya ba in har bada saninsa bane?"


Yafiya? Ta maimaita sannan tasa wata dariya tace "gun wa? Gun wacce ta rasu? Ko guna? Ko gun iyayen mu?"


Kallanta yai yace "Raziya!"


Yanda ya kirata ne yasa ta zubamai ido, wannan karan shine lokaci na farko data mai kallan mutunci, murmushi tai na takaici sannan tace "Zan fadama yanzu."


Kallanta yai sannan ta sake murmushi ta bude baki zata fara magana..........


*********


Hankali a tashe Dady yace "saki?"


Zainab tace "eh dady yanzu na amshi takardar."


Cikin fada yace "wani irin hauka ne wannan? Taya mutumin da kece wahalarsa zai sakeki ba tare da dogon nazari ba? Me kikai haka?"


Tace "ba abinda namai."


To fadamin meya faru haka? Yanzu zanyi booking flight zan taho gidan nazo na daukeki.


Da sauri tace "inje ina?"


Ki taho nan mana, ina zaki zauna ke kadai kiyi idda?


Tab ai dataje su zauna gida daya da Basma gwara ta zauna ita kadai, da wace fuska zasu kalli juna a gidan? Gasu Nabila basa nan bare su rage musu matslar zaman?


Dady ne ya katseta meya hadaku?"


Shiru tai tana tunani, ta ina zata iya cemai ta kamashi da mace a daki?


Daurewa tai tace ya samu canjin ra'ayi na zuciya ne, sannan nima na gaji da zaman,


Canjin ra'ayi? Gajiya da zama?


Kina gidanki? Zanzo anjima.


Da sauri tace "bana gida Dady."


Cikin mamaki yace "kina ina?"


Ina gidan ina gidan.... can tace "gidansu wannan driver din."


Mamaki ne ya kamashi yace "turon da Address zanzo."


Yana kaiwa nan ya kashe, idanunta ta runtse, Umma ce ta kwankwasa kafin ta shigo.


Zainab ta kalla wacce ke rike da waya, abinci ta ajiye mata sannan ta xauna kusa da ita ta kamo hannunta.


Zainab ce ta kalleta cikin jin dadi tace "Umma!"


Murmushi Umma ta mata tace "bakomai, Allah na tare dake."


Kai ta daga da sauri tace "Umma menene laifina? Dan na kula dasu? Danki yace komai laifinane."


Ta karasa tana hadiye kukanta.


Umma tai murmushi tace "kyale wannan shi dama haka yake fadar magana dan ran mutum ya baci."


"Eh mana haka yake duk sanda yazo sai ya konan rai"


Umma tace "kingani ko? Kyaleshi haka wannan halin nasa yake."


Zainab tace "ga fadar bakar magana ba ruwanshi da yanda mutum zai ji."


Umma Tace "d'a nane amma akwai wannan" ta fada tana dariya, itama dariya Zainab tai kafin tai shiru tana kallan Umma....


*****

Ayusher🏌🏻‍♀

[11/30, 10:26 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{35}


Umma ta zuba mata ido tasan ita kadai tasan me takeji da har komaima fada takeyi, ganin yanda Umma ke kallanta ne yasa tai kasa da ido, a hankali Umma ta sa hannun kan goshinta, zafin dataji ne yasa ta kalleta da sauri, Zainab ta kalleta cikin mamaki sannan tasa hannu a wuyanta, itakam bataji komai ba.


Umma fitowa tai ta wuce gun Abba da sauri, Abba ne ya kalleta yace “Ina yar......”


“Abban Khalid yarinyar nan fa batada lafiya, tsabar zafin abinda ta gani da alama yasa batasan ma meke faruwa da ita ba.”


Cikin mamaki yace “meta gani?”


Shiru tai batace komai ba, murmushi yai yace “nayi shiru tunda sirrinku ne yanzu ya za’ai? Asibiti za’a kaita?”


Khalid ne bansan inda yake ba, nakira wayarshi bata shiga ba, gaba daya hankalin Umma a tashe yake, Abba ne ya miko matw paracetamol a cikin magungunansa yace “ki bata wannan tasha ta kwanta in akai sa’a kiga komai yazo da sauki.”


Amsa tai ta fito da sauri dakin ta shiga Zainab na zaune ta kurawa kasa kallo, jin motsin Umma ne yasa ta kalleta da sauri, Umma ta mika mata magani, amsa tai tasha batare da ta tambayi dalili ba, Umma ta zauna kusa da ita tace “kin fadawa baban naki?”

Kai ta daga ahankali, Umma tai shiru tana kallanta cikin tausayawa.


Juyowa Zainab tai sannan tai murmushin yake tace “Umma abinda na fada miki.......”

Bazan fadawa kowa ba, kai ta girgiza da sauri tace “bashi ba, ko an sani ma magana ta wuce ai, kawai bansan Dady yasan meya faru ne, sannan kiyi hakuri dan yace zaizo.”


Kai Umma ta jinjina tace “dole yazo ai saboda halin da kike ciki, amma meyasa bazaki fadamai ba?”


Idanunta ne suka fara canzawa tace “taya zan fadamai abinda nasan zaizamarmai tabo?”


Umma tai shiru tana kallanta, bata tambayeta dalili ba ita kuma Zainab batace komai ba sai dai a ranta tace tasan tabbas Dady ya sani bazai yafewa kansa ba zaiyi tunanin duk abinda ya faru ne yajawo haka.


********


Taku biyu tai zuwa gaban Khalid, batare da ta juyo ba tace “Adam da Ya Fiddausi ni kaina bansan ya akai suka hadu ba, sai dai tun sanda na dawo daga makarantar kwana take bani labarin saurayin datai, wani irin so suke ma junansu, wanda gaba daya iyayenmu suka maidashi dan gida, a lokacin ina makaranta.

A gidan mu yawanci yake cin abinci saboda karatun da yake a BUK, Yaya na tsananin sansa, dadin dadawa daya ce mata shi AA ne yasa ta kwallafa rai dashi, tanada yawan ciwoka wannan kam kowa yasan saboda ciwonta ne, ga wahalalen ciwon baya da take dashi, akoda yaushe Adam ne ke kula da magungunanta, dan ko yana makaranta in lokacim shan maganinta yai yana kiranta, wani irin soyayya sukema juna wanda ni har mamaki nake in na dawo ta dinga min zancen, sau biyu ina ganinsa sai dai yanda yake nunawa Yaya tsantsar so da kauna yasa ma gaba daya nima na aminta da shi, iyayenmu sun sadaukar da duk wani kauna akanshi, dan akwai sanda yazo gunta cikin tashin hankali saboda bashida kudin biyan kudin makaranta, haka ta sanarwa Baba ba tare da wani kokonto ba suka saida keken dinki Mamanmu aka bashi ya biya.


Sam yanda suka daukeshi kai kace sirikinsu ne, dan shi im ta tashine da an daura musu aure kafin ya gama karatun, Baba ne ya hana a cewarsa hankalinsa zai rabu biyu, gashi yace bayasan tai karatu saboda yanayin lafiyarta, gwara ta xauna shi ya musu, Baba baiso ba sai dai ita Yaya ta nuna hakan takeso dan duk abinda ya fada shi take so.


Haka ya cigaba da karatunsa, duk sanda Baba ya samu kudi burinsa yamai dinki ko ya bashi ya kashe, ni da nake boarding sai nai zuwa nawa amma dakyar Baba ke bani dubu daya da dari biyar a gabana kuma zai ba Yaya dubu hudu-biyar yace taba Adam.


Haka suka share shekara 3 suna cin soyayya mai tsafta dan yasha faduwa jarabawa in bai samu damar biya ba haka Baba zaici bashi a biya mai, hartakai an samu ya kammala karatunsa.


Wata biyar da kammala karatunsa komai ya fara canzawa, dan ko Yaya ta kirashi baya dauka, hankalinta ya tashi, har garinsu ta nike gari taje sai dai randa taje mahaifiyarsa ke fada mata an tafi sa ranar Adam sannan tace ta rufa mata asiri kafin ma wani yaji ta kwashi kafarta ta tafi dan da wacce xai aura.


Dakyar Yaya ta kawo kanta gida, tundaga ranar ciwo ya rufketa, banda kiran wayarsa da kuka ba abinda takeyi, abinci wannan sai ana dura mata takeci.

Baba dakanshi yaje garin sai dai wulakancin da mahaifiyarsa ta masa akan yana musu bakin ciki dan zai auri mai kudi da kuma wanda Adam ya masa akan shi aba Fiddausi hakuri shiyanzu saura wata uku bikinsa gini ma sukeyi na inda zasu zauna.


Haka Baba ya dawo cikin tashin hankali da bakin ciki, Yaya ta shiga tashin hankali ta rame duk ta kanjame ga azababbem ciwom baya da takeyi, a haka ne na kammala karatu na dawo gida.


Ranar daurin auransa........


Hawayenta ta share sannan ta cigaba, ranar da komai na rayuwarmu ya ruguje, Yaya ciwonta ya tashi ga ciwon yunwa da damuwa, munje asibiti akace jininta ya hau sosai sannan zuciyarta ta fara kumbura, haka aka bamu gado aka yanke mana uban kudi zumzurutu da zamu biya, saboda munje asibitin gomnati abu yaki yiwuwa dole muka dawo na kudi.


  A ranar auransa ciwonta ya tashi a asibiti gashi sunce bazasu mana komai ba harsai mun bada rabin kudi tunda haryanzu basuga komai ba.


Haka Baba ya fito ya saida mashin dinshi wanda ba wani kudi ya hada ba, ya daga gidan mu sai dai ba mai siya, Mama tai kuka da kanta ta nufi kauyensu akan yazo saboda sunansa kawai take kira, Mama ta nemi yazo ko na awa daya ne in ta ganshi sai ya koma, sai dai mutumin nan da aka tambayeshi wacece ma sai cewa yai bai taba ganinta ba da alama neman taimako tazo.


Haka Mama ta dawo tana kuka, ga Yaya numfashinta ma ya daina fita daidai, hankalina a tashe na shiga gun likitan na sa gwiwowina a kasa ina neman ya taimaka wa Yaya.


Juyowa tai tana kallansa tace “kasan meyace?”


Bata jira amsarsa ba tace “cewa yai sai na bashi kaina zai taimaketa.”


Haka na fito ina kuka sai dai ganin yanda yaya take ga Mama na kuka a gefenta, ga Baba ya dawo jiki a sanyaye yasa na koma dakin nan.


Hawayenta ta share ta cigaba haka na ba likitan dako sunanshi bansani ba kaina, sai daya biya bukatarsa sannan yazo aka bata gado, sai dai duk sanda zai dubata sai ya kusanceni, haka duk dare banda kuka ba abinda nakeyi, a rana ta uku da kaita asibiti, ciwonta ya tashi sosai, gun likita na nufa yana biya bukatar sa Allah yai ajalin Yaya.


Tana kaiwa nan ta hadiye wani abu daya tsaya mata, Mama tana ganin yaya ta tasu ta fadi a kasa ciwom barin jiki ya kamata, har yau tana nan komai yi mata akeyi.


Takowa tai zuwa inda Khalid yai mutuwar tsaye tai, tace “kanada magana akan abinda na aikata?”


Kallan idanunta dake nuna mikin da aka bude take sannan ta share hawayenta tace “tundaga nan nike ciyar da gidan mu, saboda Baba na gida yana kula da Mama, tun kuma daga sanda na taso da kudirin halaka rayuwarsa dan da wannan kadarin kadai na taso zuwa yanzu”

Tadan ja numfashi sannan tace “in ka gama jin abinda kake san ji ni zan shiga ciki.”


Da sauri ta wuce kafin tajira mai zaice, tana shiga tasa kuka.


Gaba daya Khalid ya kasa ko motsi, saboda abinda yaji bai taba tunanin abin yakai haka ba.

ne ya kamata, sannan ya juya dakyar ya fita daga gidan.


*******


Kanasan cemin tsinaniya dubu ashirin kadai gareka a banki?


Kallanta yai yace “to me nakeyi dazan samu kudi?”


Ranta a bace tace “duk ina uban kudin da matarka take baka? Duk wata dubu saba’in take baka ko ka dauka bansani ba? Kudin da take baka ko ita bata cin rabinsu.”


Kallanta yai yace “ina suke kuwa? Duk na cinye.”


Haushi ya kamata tace “amma wannan wannan ni dai banji dadin haihuwa ba, to yanzu gidan ubanwa kake so mu kwana?”


Inafa na sani mu koma kawai can gidansu kawo shehu.


Kaci gidanku mu koma mu musu uban me bayan kasan yanda muka rabu?


Haushi ya kamashi yace “to sai dai kuwa mu kwana a mota.”


Kallan motar tai sannan tace “in muna bukatar bayan gida fa? Dan ni yanzu ma ji nake.”


Sai kije na kan hanya.


Kwade kansa tai tace “cemaka akai banda mafadi, nidai wlh Adam ka cuceni wannan abu dakai wlh ni ka cuta.” Ta karasa tana murza ido.


Ya kalleta a kufule yace “sai dukana kike kina cewa nina ja miki, amma kinsan hadda ke ko? Dakin tubure sanda zan kawota ai da duk ba haka ba.”


Baki ta saki tana kallanshi tace “kenan laifi nane?”


Bawai naki kadai ba namu ne duka.


Haushi taji tundaga nan bata sake mai magana ba, haka suka sai naman tsire da lemo sukai parking suna ci kowa rai a bace, suna gamawa ta kalli gari tace “yanzu haka zamu kare a titi?”

Kallanta yai yace “ko mu roki babanta? Ko dan daki daya ya sai mana.”


Wani banzan kallo tamai kafin tace kai Addu’a ma karyasa a daureka.


Da sauri ya shafi hannunsa sannan yai shiru, haka suka zauna a mota suna kallan juna kafin Goggo baccinya dauketa yo bata saba zama gum ba badan kallo ko taune taune.


******


Yana tafe gaba daya zuciyarsa ba dadi.


Yana shiga kan layinsu yaga motar datai parking mutumin dake jikinta yana tambaya, Khalid yaje wucewa yaji ance Khalid!


Yana juyowa yaga Dady, mutumin yace “yauwa ga Khalid din ma.”


Da sauri Khalid ya karasa ya gaisheshi.


Dady ya sallami mai motar sannan ya kalleshi ya amsa gaisuwar yana cewa “Allah yayi a hanya zamu dinga haduwa.”


Murmushi Khalid yai, tafiya suka fara Dady yace “Ashe abokinka sakinta yai.”

Da sauri Khalid ya kalleshi, Dady yace “baka sani ba? Saki uku ya mata.”


Idanunsa ya dan runtse cikin takaici wannan haukar na Adam, Dady ya murmusa yace “mungode sosai da taimakom da ka mana, dama tunda na ganka hankalina ya kwanta dakai, ashe raban zaka cecemu ne.”


Da sauri Khalid yce “ba wani abu danai”


Dady ya kalli gidan da Khalid ya tsaya sannan yace “nan ne?”


Khalid yace “eh”


Nan ya shiga yabar dady a waje yana kara kallan gidan.


Umma na tatar koko ya shigo, tana ganinshi ta hade fuska, murmushi yai yace “tuba nake Ummana duk dabansan laifina ba.”


Tace “inata kiranka wayarka a kashe.”


Yace “Yahkuri Ummana, munyi bako.”


Bako? Ya iso kenan?”

Yace “eh ashe kunsan da zuwan.”


Ajiye abin tatar tai ta matsar dashi ta shiga ciki tace “shigo dashi.”


Haka Dady ya shigo ya shiga falo.


Abba dake zaune yana jin radio ya kalla bayan ya zauna, gaisawa sukai cikin girmama juna, Khalid ya ajiye musu ruwa sannan ya dan matsa gefe.


Zainab kam tundataji Umma ta fada mata zuwansa gabanta ke faduwa haka ta dake ta zura hijab ta fito.


Tana fitowa Khalid ya mike ya fito.


Dady ne ya kalleta, Abba yace “Khalid ka bude musu dakinka su shiga ko kuma taimaka min na koma daki na basu guri.”


Dady yace “bakomai wlh ka zauna magana ce wacce kun sani gwara ayi a gabanka.”


Abba ya kalli Khalid yace “Khalid karaso.”


Haka Khalid ya taimaka mai ya shiga daki, Sannan yazo ya fita.


Dady ne ya kalleta yace “Zainab!”


  Kallansa tai tare dayin murmushi bayan sun gaisa ne ta mikamai takarda.


Ransa yayi mugun baci dan bacin ransa ya fito karara ya kalleta yace “wannan wani irin butulci ne?”

Kallansa tai batace komai ba, yacigaba “nasani sarai kin aureshi ne saboda ni, kin samu wanda baya sana’a wanda kuma bashi da burin tabuka komai saboda kina tsoron abinda ya faru da mahaifiyarki, yanzu kin fahimci wayanka baya sai ma komai?”


Idanunta ne sukai jaaa sai dai haryanzu batace komai ba, Dady tausayinta ya kamashi yace “fadamin menene ya jawo sakin nan?”


Kallansa tai tace “yanda manfadama ra’ayinmu ne ya banbanta da juna.” Yanda tai maganar cikin dakewa tayita sai dai Dady ya fahimci tana cikin tashin hankali, hakan yasa yace “tashi mu tafi gida, duk zaman da aka ga kinayi ke kadai ne ma yasa abin yakai haka.”


Gida?


Ta fada da sauri tana kallansa, yace “me? Badai kina tunanin na barki anan bane?”


Kallansa tai tace “Dady kafi kowa sanin yanda nake da matarka wani irin zama zamuyi a gida daya?”


Matata? Matata ba mamanki bace?”


Shiru Zainab tai kafin tace “kayi hakuri Dady amma bazamu iya zama gida daya ba.”


Kallanta yai sannan a hankali yace “taya zaki zo gidan mutanen da baki da hadi dasu kice zaki zauna kiyi iddah a gunsh? In ke kin yarda su ce miki akai sun yarda ko ni ce mike nai na yadda?”


Kallansa tai ta matso kusa dashi sannan ta tsuguna a kasa tace “Dady ka taimaka ka barni anan, inasan zama anan, inaji a jikina hankalina zaifi kwanciya anan.”


Kallanta yai yace “anan gidan?”


Ta fahimci meyake nufi tace “eh, dan Allah dady kamin alfarmar kabarni, nasan Umma bazata hanani ba.”


Shiru yai yana kallanta kafin ya ja nunfashi yace “sai na tambayesh.”


Da sauri tace “na gode Dady ta fada tana share kwallarta.

Dady ya zuba mata ido wai itama tata kaddarar kenen, lalai alhakin Ummy ne ya kamashi, gashinan yarsa na kunsar abinda ya kunsawa yar wani, ita nata ma sakin wulakanci har uku.


Zainab ce takatse tunaninsa tace “Dady ka taimaka ka sanar a gun aikina akan zan dau hutun wata uku, ko kuma kace nayi tafiya gudun kananan maganganu, nima zan tura musu email.”


Kai ya daga alamar fahimta tausayinta na kara kamashi.


Haka ya tambayi Abba da Umma wanda a take suka amince tare da mai alkawarin kula da ita harta gama idarta.


Haka ya fita gaba daya jikinda yai sanyi, Khalid ya nemi ya maidashi Kano a motar Zainab, nan ya amince sai dai suna fita yace Khalid ya kaishi shago zaisai abu, nan fa Dady yahau siyo su Buhun shinkafa, taliya, Marconi, shinkafar turo, indomie, juices ruwa da sauransu, Khalid da sauri yace Dady?


Dady yace “ka taimaka Khalid nima hankalina zaifi kwanciya akalla na taimaka da wani abun, nayi ne dan hankalina ya kwanta, nasan xaka fahimci halin da wannan mahaifin ke ciki.”


Haka suka kai kaya yasa dubu ashirin  a cikin katan din juice, Khalid kansa bai sani ba, haka suka ajiye suka nufi kano.


A hanya sai godiya Dady yakeyi yana jimamin wannan abun.......


******

Ayusher🏌🏻‍♀

[12/1, 9:40 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


There are wounds that never show on the body that are deeper and more hurtful than anything that bleeds.

Laurell K. Hamilton, Mistral's Kiss (Merry Gentry, #5)


{36}


Shiru sukai suna tafiya a hanya gaba daya Khalid na lura da yanayin dady, hankalinsa ba a karamin tashe yake ba kuma da alama bai san barinta acan, dan dai ba yanda zaiyi ne.


Kallansa Khalid yai yace "in bakasan barinta acan mu kuma a dakota."


Kallansa Dady yai sosai yaji dadin maganar dan abinda ke kunshe a ransa kenan sai dai tayaya?

Kallan Khalid yai tare da yin murmushi yace "yauce rana ta farko tunda nake da Zainab dana taba ganin tana san zama a guri kamar gidanku, gidana a zaune kawai take amma sam ba ta sakewa a ciki, gidan kanwar mamanta data zauna kuwa dama kowa yasan ba so take ba tana zaune ne saboda batasan zama a guna, ta ya zan tilasta mata ta taho inda bazata ji dadi ba?"


  Mamaki ne ya kama Khalid dan sosai yana mamakin wannan halin na Dady taya zai zauna komai sai ra'ayin yarsa?


Cewa yai " Amma ni ina ganin nesanta kanta daky da takeyi shiyasa bazata taba sakin jikinta ba, amma in ta zauna cikin yan uwanta dole ta saki jikinta."


Kallan Khalid yai cikin jin dadin kalamansa kafin yace "tsoro na akoda yaushe yanda halin rayuwa yake, ina tsoron ajali na yazo muna wannan zaman."


Labarin Razy ne ya fadomai, da tashin hankalin da suka shiga, ga ita kanta rayuwar da Zainab din ta fuskanta a gidan mijinta, rage gudun motar yai sannan ya kalli inda suke harsunzo kano dan suna daf da shiga kurna.


"Ina ganin ba shawara bace a barta acan, hankalinka bazai taba kwanciya ba, sannan iddah zatai ni ba muharaminta bane, Kuma gidan mu ne dole zan shiga ciki, sannan inada abokai dake zuwa, Abba ma abokansa na zuwa dubashi baza'ace duk sanda wani yazo tana killace a daki ba."


Dady ne ya kalleshi yace "me kake tunani? Zainab bazata taho ba."


Zan ajiyeka a inda kai masauki zan kawota anjima ku wuce tare.


Mamaki sosai ne ya kama Dady yace "kana tunanin zataji maganar ka?"


Khalid baice komai ba ya wuce da Dady, sosai Dady yaji dadin abin nan sai dai sam baisa rai akan zata biyoshi ba, ya daiji dadi sosai a kalla Khalid ya nuna mai shi d'a nagari ne.


Khalid na ajiyeshi ya juya danbatta.


Zainab na zaune a daki Umma na gefenta, ajiye kudin hannunta tai tace "Zainab ki ajiye mai annn duk randa yazo kya bashi, dan bazamu amshi waccen ku amshi wannan ba, waccen din ma a dole muka amsa dan karyaji ba dadi ne."


Zainab ta kalli Umma tace "Allah Umma bakomai dan Allah ki ajiye? Nima bazanji dadi ba in kika ki amsa."


Ajiye mata tai kusa da ita tace "saboda Allah nake zaune dake bawai dan wani abu ba, banasan harkar kudi ta ratsa daga nan in ba'ai wasa ba san zuciya ne zai shiga."


Kallan Umma tai sannan ta daga kai kawai batace komai ba dan rayuwar nan taso ba karamin birgeta take ba.


Zama kusa da ita Umma tai tasa hannu a goshinta tace "masha Allah Zazzabin ya tafi." Ta fada tana kallan Zainab wacce itama ke kallanta.


A tare sukai murmushi Zainab jiki a sanyaye tace "Umma nagode sosai sosai."


Kafadarta ta dafa tace "ki rage sa komai a ranki, Allah baya dorawa bawansa abinda bazai iya ba, duk abinda ya sameki kisa a ranki kaddarace ta Allah sai kiyi fatan sa'ar cin jarabawar."


Kai ta daga ahankali idanunta sun ciciko da hawaye.


Murmushi Umma tai.


A falo ta zauna suna dan taba hira da Abba kasancewar su Asiya dasu Amir duk suna makarantar islamiya.


Jin sallamar Khalid ne yasa Umma ta kalli waje, dayake labulen a dage yake ta amsa tana cewa "har an dawo?"


Karasowa yai yana cewa "eh Umma"


Abba yace "badai gudu kai ba ko?"


Kallan kafar Abba da aka cire yai sannan yace "a hankali muka tafi."


Kallan Abba yai yace "Abba inaganin zamanta anan bazai yiwu ba."


A tare suka kalleshi, ya kalli Abba yace "iddah zatai bai kamata ta zauna inda ba muharammanta ba, sannan hankalin mahaifinta bazai taba kwanciya ba inya barta anan, kuma jikina naban kamar baya jin dadi."


Da sauri Umma tace "meke damunshi?"


Kai Khalid ya daga alamar rashin sani sannan yace "ban sani ba wlh haka dai nakeji."


Umma ta kalleshi zuciyarta duk ba dadi, dan maganar gaskiya tana san zama da yarinyar ta fahimci tana da tabo na rashin uwa ga kuma takaicin namiji.


Abba ne ya kalleta ya sani sarai zuciyarta ba dadi sai dai ya zasuyi? Kallan Khalid yai yace "bari a kirata na mata magana."


Da sauri yace "bari na mata magana."


Kallansa sukai cikin mamaki, shikuwa yasan halinta dan zaman nan da sukai ya tabbata aka mata lagwalagwa ba abinda zai faru.


Knocking din dakin yai, daga ciki tana zaure rike da takardar Adam tace "waye."


Khalid yace "nine."

Mamaki ne ya kamata tace "ya akai?"

Magana zamuyi.


Umma ce ta mike tace "ko na mata magana?"


Khalid ya girgiza kai alamar a'a daga ciki tasa hijab sannan tace "shigo."


Tura kofar yai ya shiga a bakin kofar ya tsaya yace "kizo na kaiki kano, ku wuce da babanki."


Kallansa tai cikin mamaki tace "in wuce ina?"


Gidanku!


Fuska ta hade sosai tace "a matsayinka nawa kenan?"


"Na d'an gidan nan"


Baki ta bude cikin kuluwa da takaici tace "da nace ba d'an gidan nan bane kai?"


Yace "tambayarki haka ta nuna min."


Wata dariyar takaici tai sannan tace "korata kake kenan kome?"


Yace "ba korarki nai ba ina nufin ki bi babanki."


"Nafi karfin ka wulakantani wlh."


Wani mugun kallo tamai ta mike a tsananin zuciya ko kayanta bata dauka ba kawai wayarta da laptop da tab dinta ta dauka ta fito rai a bace.


Kofa ya bude mata alamar hanya, tsayawa tai tana kallansa cikin takaici kafin tai kwafa.


Umma ta gani a tsaye a falo, Umma na ganinta ta matso tace "Zainab."


Zainab tai kasa dakai idanunta suka fara neman rauni, dakewa tai tace "Umma zan wuce."


Tana fada tai hanyar neman fita, da sauri Umma ta rikota sannan ta dago da ita tace "ba korarki mukai ba Zainab, nikaina inasan zamanki anan sai dai ba yanda zanyi."


Kallan Khalid tai kenan shiya kawo wannan maganar?

Abba ta tsuguna tawa sallama sannan ta kalli Umma tace "nagode muku Allah ya saka da alkairi."


Umma ta dauko yar wayarta tace "samin numberki."


Nan Zainab tasawa Umma ta kira wayarta dashi sannan ta kalli Abba tace "Allah ya kara lafiya."


Khalid ta kalla wanda ke tsaye jikin kofar dakin Asiya, wani takaici ne ya kamata ta sake sallama da Abba ta fito.


Umma har tsakar gida ta rakora tana neman fita waje Zainab tace takoma.


Kayan abincin da aka kawo Khalid ya fito dasu, kalan Umma tai tace "Umma ki taimaka ki bar wadan nan dan Allah badan ni ba."


Jikin Umma ne yai sanyi, ta jawo Zainab ta rungume idanunta harda hawaye, Zainab ta share nata da sauri tace "Umma ki taimaka."


Kallan Khalid tai tace ya barsu.


Khalid ne ya fito waje, yana neman bude mota, kallansa tai tace "bani makulina."


Kallanta yai sannan ya kalli motar yace "wazai kaiki?"


"Banaji wannan ya dameka tunda motatace."


Kallanta yai yace "ki bari na kaiki tukun."


"Motarnan tawace sannan jikina ne banaji akwai damuwarka akai, bani."

Ta karasa tare da mikamai hannu,


Bai tanka taba ya shiga motar ya zauna, haushi ya kamata ta bude motar inda yake tace "fito."


Yace "shigo."


Tace "Malam fito ko?"


Yace "Malama shigo ko?"


Jitake kamar ta shakeshi, hankalinta harya kwanta zamanta anan ya koreta kuma yanzu yazo yana wani abu?


Kallanta yai yace "dare nayi."


Ranta a tsananin bace ta bude ta shiga baya yaja suka tafi, har suka isa ba wanda yawa wani magana, kaini gidana.


Kallanta yai yace "kamar......."


Kaini nace, kome zan da rayuwata ba damuwarka bane."


Dauke kai yai yana kaita gidanta ta amshi key sannan ta kalleshi ta wuce ciki.


Bala da gudu ya bude mata tana shiga tama Khalid text "You are Fired."


Yana fita ya gani, kallan gidan yai jiki a sanyaye sannan ya kira Dady ya fadamai.


Dady cikin jin dadi yahau godiya, alokacin ya taho gidan.


Zainab na zaune a falanta ta hade kafafunta tana kallan gida, komai na gidan bataso gani take komai anyi lalata dashi, kankame jikinta tai kawai tasa kuka.


Dady wanda ya shigo ne ya kalleta cikin tausayi, tana ganinshi tasa kuka sosai, tausayinta ne ya kara kamashi yace "tashi mu wuce saboda ba'asan fita."

Kallansa tai tce "Dady anan zan zauna."


Kallanta yai da sauri yace "bazai yiwu ba."


Tace "to kaini gidan Aunty."


Yace "wai akan me bazaki zo mu tafi ba?"


Kallansa tai ta rasa me zatace, tuno da kalaman Khalid tai wai gidan iyayensa ne, Dady yace "mu tafi kinji?"


Idanu ta runtse kafin ta daga kai.


Haka Suka hada kaya suka wuce Abuja, tunda taje gidan magana ba hadasu take da Basma ba, kullum tana daki kamar yanda ta saba, Basma kuma ta rasa yanda zatai ta shawo kanta, Dady ne inyana nan yake kiranta falo shima da Basma su zauna duk da batama Basman magana ko ta mata a kalla tana amsamai in ya sako maganar Basman


Sai dai hakan ba karamin birgeshi yake ba duk da ba san zaman take ba akalla yanzu tana zama a falan in yana nan.


*******


A can bangarensu Goggo kuwa haka suk nufi kauye ganin ba yanda zasuyi dan dakyar goggo tai bacci ranar a cikin mota, gidan kawu shehu sukaje Goggo ta kalli Adam tace "karka fito da kayan tun kafin a tozartamu mu fara shiga tukun"

Haka suka shiga gidan Kawu shehu, matansa biyu da yaransa su goma sha daya, sai Sadiya dasuka barmai.


Yana zaune a kan tabarmar kaba yana ta kankare kaho yaji ana ihun kawu Adam yazo.


Shiga sukai cikin mamaki kowa ke kallansu, makota sai lekowa ake ta kanga, Goggo nasa kafa ta taka kashin kaza, da sauri ta matsa gefe tafara cewa "matsalata da kauye kenan, kaji ko ina......."


Kallan da Kawu Shehu da matansa suka mata ne yasata tai shiru, haka suka zauna, kowa na musu kallan mamaki, Kawu shehu yace "dama kuna raye? Ai mu tuni muka cire tarihinku."


Goggo tace "wato mutuwa kake so muyi ko me?"


Matarsa Delu tace "tunda danki yai aure kika bishi shekara hudu ko kafarki mun gani? Ko falen atamfa kin aiko mana? A matsayinmu na masu rike miki 'ya."


Dariya Goggo tai tace "Adam ina taliyar da muka siyo dako ka shigo da ita."


Kawu shehu ne yace "basai an shigo da ita ba, meya kawoku?"


Adam yace "dama Goggo ce zata dawo nan da zama."


Delu tace "nan ina?

A wani dakin? Bayan mu kanmu gurin kwana wahala yake mana? Ruwa duk ya cinye mana gini?"


Kawu shehu ne yace "ki koma inda kika fito ki zauna nima yara rasa inda zasu kwanta mukeyi, lokacin da zaki tafi danace ki barmana gidanki me kikace? Hanani kikai a gabana kika saidashi ma abokina."


Goggo tasa dariya tace "wasa yakeyi kamar bakusan Adam ba, Sadiya nazo gani, tunda batanan bari mu wuce."


Har sun shiga mota Delu tace "taliyar, nan Adam ya bude mota dole ya cirota aka shiga da ita ciki."


Suka ja suka tafi, haka Goggo suka je kano wajen gidan Zainab Goggo tana kallan gidan tana hawaye, Dakyar suka samu gidan haya daki daya a cikin katan gida mai dakuna kusan goma ban daki daya daga can kasan unguwar gidan Zainab suka zauna, Haka suka saida motarnan Goggo tasai yar mitsilar tv canjin suka sai kayan abinci suka zauna a gida.


Adam kam takaicin rashin mota sam yasa ko fita bayasanyi, wannan lamari na kona mai rai matukar gaske.


Banda fada shida Goggo kullum ba abinda suke a gidan, haka ya nemi majalisa yake zama, kudin mota kam an sashi a gaba sai ciye ciye akeyi kai kace bazai kareba.


Duk gidan nan Goggo batawa kowa mutumci, dan garkame dakinta takeyi saboda batasan yara suzo mata kallo.


*********


Bayan wata uku..........


Wannan lokaci abubuwa da dama sun canza, su Nabila da Nusaiba an dawo, murna agun Zainab baya musaltuwa, Nabila kam taji bakin ciki dan jitai kamar ta je ta kashe Adam duk da batasan me ya mata ba amma haushin wulakanta hallacin Zainab yasata jin takaici matuka.


Su Khalid anyi Jarabawa, Zainab aka turowa takardun tai marking dan sai data turawa director din email akan ita zata dau ma'aikara dakanta, ganin yanda komai nasu yai kasa daga tafiyarta yasa yake lalabata, ta sanar kar wanda yasa suna sai dai ai amfani da numbers hakan yasa sanda tai marking batasan ko wanene na Khalid ba, sai dai akwai takarda daya wanda ita kanta sai datai bincike a google kafin tai marking dinshi saboda tsabar fasahar da aka rubuta ya wuce tunaninta.


Kusan duk kwana biyu sai tayi waya da Umma sosai wannan wayar ke debe mata kewa, har Allah yai ta kammala iddar ta, sannan ta tura ranar interview ga wadanda suka ci sannan tahau shirin dawowa.


Khalid dake zaune cikin shagon dayake aiki ne sako ya shigo mai, baki ya sake sosai dan bai taba yin jarabawa ance yaje interview ba sai wannan, wayar ya kurawa ido yana kallan sakon dan ya kasa gasgata abinda yake gani.......



*****

Ayusher🏌🏻‍♀

[12/3, 3:52 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{37}


  Goggo na zaune adan kucilin falanta da tana kallo, Adam dake kwance a dan mitsilin dakinsu ne yace "Goggo dan Allah rage magana haba, tsakani da Allah kallo da sassafen nan?"


Ranta a bace tace "ka fito ka bar gidan nan ko sai jikinka ya gayama? Ai tun jiya nace ka samo aran yar mota ka kaini gidan Hajiya Bilki."


Komawa yai ya ja bargo baice mata komai ba, haushi ya kamata ta taso ta shigo dakin da karfi ta yaye bargon tace "ko tsinaniya kujera banda ita sai dai na zauna a kasa amma kai ka shige cikin bargo banda uban bacci da yawon banza baka da abinyi."


Cikin kufula yace "koma me nake meya dameki? Ni ki barni da rashin matata dake damuna."


Wani kallan banza tamai tace "har wani rashin matarka? Nawane ragowar kudin mu?"


Kallanta yai yace "wani kudin bayan kin kwacesu?"


Yaushe?


Kallanta yai ya saki baki kafin yace "banasan wasa, wancan satin kikace nawane ragowar kudinmu nace miki dubu dari da ashirin kika ce na kawo miki darin baki yadda dani ba kinji kudin sunyi saurin karewa.


Kanta tadan sosa tace "ina nasa?"


Da sauri ya mike yace "bangane ba."


Hankali a tashe suka fara neman kudi a cikin dakin, hankalin Goggo yayi dubu ya tashi ji take kamar rayuwarta aka gutseri.


Gaba daya kayan dan kayan nasu suka fito dashi waje suna dubawa, sai dai bashi ba labarinsa.


Goggo ta kalli Adam tace “yaushe ka bani?”


Shiru yai yana tunani kafin yace “kamar da safe ne?”


Karya kake wlh, ni baka ban ko ficika ba, bayanda za’ai ka ban makudan kudi nai wazgarere dasu har sati daya bansan inda suke ba.


Gabansa ne ya fadi dan maganar gaskiya ranar ya ciro kudin daga masallaci sai majalisa yaje yana dawowa gida zai bata yaga wayam, kallanta yai yace “ki dai duba Goggo.”


Daga can makotanta ta kalla wadanda kowa ya fito yana kallansu, haushi ya kamata tace “ku kuma me kuke kallo?”


Asabe da dakinta ke kusa da nasu tace “kudai kusan barawon daya dauke a cikin ku dan mu gidan nan ba’a sata.”


Ran Goggo ya baci ta kwashi kaya ta shiga ciki, kallan Adam tai tace “fadamin, uban wa kaba kudin?”


Yace “wai Goggo wa nake dashi da zan ba inba ke ba?”


Zama tai dabas a kasa tace “yanzu ya kake so muyi?”


Yace “nizance haka Goggo yanzu ya zamuyi?”


Takaici ne ya kamata tace “wai uban me ma kake harynzu baka samu aiki ba?”


Ransa ne ya baci ya fita daga gidan, kanta ta rike wanda ke sarawa.


********


Gaba daya sun sa kaya a cikin mota, Nusaiba da Nabila sai murna ake za’abi Zainab.


Zainab dake daki ta kalli dakin, bata taba kawowa zata dawo tai dogon zama a gidan nan ba, duk da wata uku tai amma agunta dogo ne.


Jawo dakin tai ta fito, a falo taga Basma, fuskarta a hade tace “zamu wuce.”


Basma ta matso tace “Dady yace ki kirashi kafin ku wuce.”


To tace batace komai ba daga nan.


Basma tai shiru tanaji suna waya da Dady yana ce mata su tafi da mammab ya dinga kwana a dakin waje kafin asan yanda za’ai dan sam hankalinsa bai kwanta da barinta ita kadai ba, in su Nabila suka taho.


Suna sallama ta kalli Basma tace “mun wuce.”


Da sauri Basma tace “Zainab!”


Tsayawa tai batare da ta kalleta ba, Basma ta dan tako tace “Zainab ki yafemin, sharrin zuciya da sharrin kawaye ne ya sani yin abinda nai, akullum ina danasanin wannan abu, gashi dalilinshi bazan sake haihuwa ba.”


Kallanta tai da sauri, hawayenta ta share tai murmushi tace “hukuncin da Dady yamin kenan”


Gaba daya jikin Zainab ne yai sanyi, tama kasa ko cewa wani abu saboda mamakin wannan zancen.


Basma ta nufi kofa tace “Nusaiba banda fada dake da Nabila.”


Nusaiba ta dan turo baki sannan tace “Mumy mun wuce.”


Haka suka shiga mota Zainab ta shiga Mammab yaja suka tafi, gaba daya jikinta a sanyaye.


*********


Sam Khalid ya kasa gasgata abinda ke faruwa, yana fitowa daga shago ya nufi garage inda suke dan aiki, yana yi yana mamaki, sam zuciyarsa taki amincewa.


Haka ya dawo gida, sai dai sam ya kasa fadawa Umma da Abba, gani yake karsu sa rai azo ba’a dace ba, dan harya gaji da sanar dasu zaije jarabawa sai sun gama sa rai yazo bai samu ba, duk sai yaji ba dadi.


Shiyasa wannan karan ya barma kansa, in haryaje yaga da gaskene aka dace sai ya fada musu, dan ma yanzu hankalinsa ya kwanta ba bashin da ake binsu, duk sun biya, sannan Abba ba laifi in ya rike sanda biyu yana iya dan matsawa daga can zuwa can.


***********


Zufa ce ke karyo mata ta ko’ina, daga yanda take runtse ido zakasan mafarki take mara dadi, jin sautin numfashin Adam da Raziyya ne yasa ta sa hannunta toshe kunenta kafin a hankali ta bude idanunta.


Kwance take a kan gujera a falo, wani abu tadan hadiya tare da kunna fitilar wayarta, duk da Dady da kansa yazo aka kwashe komai aka sa mata sabo na gidan amma ganin komai take kamar yanzu ake yinsa.


Mikewa tai ta kunna watar falan kawai ta dako laptop dinta ta hau aiki, ta shirya abubuwa da dama wanda inta koma za’ai.


Haka tai ta aikinta har asuba tai, sallah tai sannan ta shirya, gadanta ta kalla, duk sanda zata fita yawanci Adam na bacci in bayayi kuwa to yana kitchen yana hada mata tea, wani abu ne mai daci ya zo bakinta hadiye shi tai sannan ta dau jakarta ta fita su Nabila na bacci.


A waje ta tadda Mamman, nan ta gaisheshi suka tafi, a hanya tacemai idan su Nabila sun shirya ka kaisu sumana siyayyar abin gida, yace “to Hajiya.”


Nan suka karasa ta fita tai ciki.


Mutanen dataga sun fara hallara ne tai murmushi tace “is good to be serious.”


Tana shiga station din taga duk staff dinsu a bakin kofa, hadda rike takardar da aka rubuta Welcome back.


Wani irin dadi taji dan dama wata ukun nan kamar mara lafiya tayisu saboda rashin aiki.


Murmushi ne yabayyana a fuskarta nan ta fara amsa gaisuwarsu cikin jin dadi, Head Director ne ya matso yana tafi, yace “barka Zainab yau kamar sallah nake jinta.”

Kallansa tai bayan sun gaisa tace “Yallabai inaji sai mun shiga meeting kafin a fara interview.”


Da sauri yace “an gama Hajiya.”


Nan suka wuce, Ramlatu ta gani ta taho da sauri, kallanta tai da sauri ta gaisheta, Zainab ta amsa sannan sukai ciki.


Sun yi discussing akan abinda zasuyi sannan ta bashi takardun da zaiyi reviewing na abubuwan da za’asuyi nan gaba.


Wani irin dadi yakeji na ganin Zainab balle data kawo abubuwan cigaba yasashi jin wani kwarin gwiwa.


Karfe goma tara daidai ta nufi dakin da za’ai interview kujerar ta ce a tsakiya, tana shiga ta zauna, kallan su tai tace “mu fara?”


Sukace eh,


Kowa ya shigo tana rike da takardar dayai jarabawa da ita, tana mai tambayoyi tana duba takardar, su takwas ne.


  Number 5 aka kira, ba tare da ta dago ba ta shiga duba takardarshi, ganin wannan takardar da ta wahalar da ita ne yasa ta kara dudubawa tana kara bin komai, har ya iso ya zauna.


Rufe takardun tai sannan ta dago dan taganshi.


  Kallansa tai idanunta suka dan fito, tasan ita tace yai Applying amma bata kawo ya ci ba.


Wulakancin da ya mata ta tuno, fuska ta daure sosai, sannan ta kalleshi, shima kallanta yai fuskarsa daidai ba alamar fara’a ba alamar daurewa.


Takardarsa aka miko mata, ta amsa tana duba sunanshi, skul din dayai result dinsa da sauransu.


Kallansa ta sakeyi, H.Director ne yasa dariya yana kallan takardunsa yace “masha Allah, irin wannan cik exams haka.”


Cikin jin dadi ya kalli Zainab yace “Da alama kema abin ya birgeki.”


Fuska ta hade tamau sannan ta kalleshi tare da ajiye biro din hannunta, nan ta fara watso mai tambaya, amsa yake bata yana kallanta, itama idanshi a kansa take mai tambayar.


Dan kai ta dauke bayan duk ya gama bata amsar tambayoyinta sannan tace “ka tabbatar ba satar amsa kai ba?”


Kallanta yai yace “satar amsa?”


Tace “eh from this naga Math ka karanta, then taya ka bada wannan amsar? Ta fada tana circling din takardarsa shafi na biyu.”


Wani dan murmushi yai tare da dan kauda kai kadan, dan ya fahimci da saninta take watsomai tambaya dan yanda ta dinga jero mai tambayoyi yanda yaga suna kallanta ya tabbatar ba haka tawa kowa ba.


Fuska ta hade tace “Murmushin me kake?”


Kallanta yai yace “da wanda yai satar amsa da masu kula da exams hall din har suka bari akai wanene mai laifi?”


Fuska ta kare daurewa tace “kana nufin satar amsar kai?”


Kallan na kusa da ita yai yace “Sir kasan yanda mukai Exams din nan it seems like she is not there.”


Nan ya mata bayani ba yanda za’ai wani yai satar amsa.


Kallan Khalid tai sannan tace “Idan aka baka aiki a news room ya zakai?”


Nan ya cigaba da bata amsoshinta, sai kara mai tambaya take sai da H.Director yace “Zainab ya isa haka wannan tambaya haka.”


Shiru tai tana mai wani kallo, kallansu yai ganin basa kallansa yadan daga mata kafada alamar ko a jikinshi.


Haushi ya kara tukota ta harareshi tare da cewa “next.”


Fita Khalid yai, har ta bude takarda ta kalli kofar inda ya fita sannan ta cigaba, sai da suka gama sannan ta fito.


A inda suke zaune ta ganshi, dauke kai tai ta wuce.


Shima yi yai kamar bai ganta ba yai gaba.


Tana shiga office dinta ta zauna, Malama shigo? D’an Gidan nan?


Haushi ya kara kamata data tuno maganganun daya watsa mata.


Tana zaune Ramlatu ta shigo dasu saboda ana nunu namusu ko ina.


Zainab tana dagowa suka hada ido, daure fuska tai ta maida kanta kan computer din dake gabanta, nan Ramlatu tace musu “wannan itace Director Zainab nasan kunganta agun Interview.”


Nan kowa ya gaisheta, dagowa tai ta kallesu, har Khalid sannan ta amsa tace “Sai kunji daga garemu.”


Nan suka fita, haka suka gama aka sallamesu akan su koma su jira sai an nemesu.


Khalid na fitowa ya runtse ido yana addu’a cikin zuciyarsa, wani irin yanayi yake ciki wanda shi kadai yasan ya yake ji.


Fitowa yai da sauri dan yaje gida ya kai musu labari.


Yana fitowa yaga wata mota tazo ta wuce, yarinyar dake janta kamar Raziyya.


Da sauri ya kara kallan motae sai dai ta riga ta wuce, shiru yai kafin ya juya ya nufi tasha.


  Zainab kam kafadar da Khalid ya daga mata ta tuno wani mugun murmushi ta saki tace “ko a jikinka ko? Let me see in zaka juri wahalar da zan baka.”


Ta saki wani murmushin jin dadi, samun kanta tai cikin nishadi in ta tuno wahalar da zata bashi.


********


Ran Nusaiba a bace ta kalli Nabila tace “wai da gaske Aunty ta koreshi? Nifa Allah saboda shi na dage sai na zo.”


Nabila ta kauda kai tana latsa wayarta tace “aikinyi ne bakidashi wlh, haka a skul kika bi kika ishemu da zancen Ya Khalid kamar kanin Dady.”


Nabila tace “mijina ai yafi kanin Dady a guna.”


Miji? Nabila ta tambaya sannan tace “Allah kanki ba daya ba, da alama kina bukatar ganin likita.”


Ran Nusaiba ya baci tace “sai ki kaini ai.”


Mamman ne yce “ayi hakuri kar ai fada dan Allah.”


Nan kowa ya kauda kai har suka isa Jifatu.


*****


Khalid cikin sauri ya isa gidan, hannunsa rike da ledar ayaba da lemo.


Umma na ta shanyar kayan data wanke ya shigo, cikin jin dadin da ya kasa boyowa yace “Ummana.”


Kallansa tai tare da dan goge hannunta a zaninta tace “Khalid an dawo?”


Cikin jin dadi yace “Umma insha Allahu mun samu aiki.”


Idanun Umma ne suka fifito tace “aiki?” Yanda tai maganar kadai zakasan wani irin yanayi ta shiga mai wuyar fassarawa.


Abba da ya dosanu sandar sa guda biyu yana kokarin fitowa waje ne yce “Aiki Khalid.”


Cikin jin dadi yace “daga Interview nake yanzu.”


Wani irin dadi ne ya kama Umma harda hawayenta.


Fadar irin dadin da suka shiga a wannan lokaci ma wahala ne dan ni kaina nasan Allah ne kadai yasan yanayin da suka shiga duba da irin lokacin daya deba yana gwagwarmayar neman aiki.


(Yan uwa dake neman Aiki irinsu Khalid suma Allah ya dubesu ya basu)



**********


Ayusher🏌🏻‍♀

[12/4, 9:39 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


For you my dear Yan Sauyi members🥰Love you soo much🤝


{38}


Tana zaune tana kade sauran dake ta mata yawo akai, haushi duk ya bi ya isheta na rashin wuta da tun shekaran jiya wutar su ta samu matsala, wani uban tsaki taja data kalli taliya da manjan dake gabanta a roba wanda har yayi sanyi ta kasa ci saboda takaicin sauro.


Kofa ta bude ta hau korar sauran, tanaji makotanta nata hira da shewa a waje, wani uban tsaki ta sake jaa tace “ka rasa uban me suke banda zaman gulma.”


Buta ta dauka zata shiga bandaki, da sauri Asabe ta mike ta warce butarta tace “Tsohuwa wannan butar tawa ce”


Kallanta tai tace “wace tsohuwar?”


Asabe tace “to yarinya wannan butar tawa ce.”


Haushi ya kara tike Goggo ta waiga taga bataga butarta ba tace “to uban waye ya daumin tawa butar?”


Asabe tace “sai ki tambayi na gidan amma ba ni ba.”


Ta ja kafarta ta bar gun, Goggo ta hau neman butarta sai dai bata ganta ba, nan ta matso inda suke hira tace “uban waye ya dau min buta?”


Kande ta mata wani kallo tace “sai ki tambayi yaran da kika kira da danki tunda kinfi kowa sanin ba mai dau miki buta anan.”


Takaici ya kama Goggo ta juya rai a bace, waje ta leka, Adam ta gani suna zaune a kujera suna hira, rai a bace tace “Adamu!”


Kalamta yai yace “Goggo.”


Ka mikon butar nan ko kuwa?

Butar dake gefensu ya kalla sannan ya mike ya dauko ya kawo mata, yana shigowa tace “wuce ciki yanzu zan fito.”


Yace “hira muke.”


Ka wuce ko sai na makeka?


Fuska ya hade ya shiga ciki, taliyar data bari ya jawo ya juya ya hau ci, bayan gida ta tsaya yi hakan yasa ya cinye taliyar kafin ta fito, yana lokar karshe ta bude labulen ta shigo.


Kallansa tai tace “uban wa yace kacimin abinci?”


Yace “au zakici? Gani nai tun dazu kika ajiye shi gashi haryai sanyi.”


Ranta a matukar bace ta karaso tace “ni wai dan Allah yaran nan sai yaushe zakai hankali? Gaba daya ni bantaba ganin mutum wanda bashi da tunani ba irinka, kanyar mana da kudi ka kala min karyar ka bani, yanzu yar dubu ashirin din da muka siyo kayan abinci muke cancanawa kaci naka dazu amma yanzu ka tasa nawa ka handame.”


“Yahkuri Goggo na dauka baci zakiyi ba”

“Ko ba ci zanyi ba ai ka bari nace bazanci ba ko?”


Nadai baki hakuri ya isa haka nan.


Ganin zasu sake fadam da kullum suke ciki yasa ta zauna ta kalleshi tace “yanzu Adam haka zamuyi ta zama? Ga kudi mun cinyesu ga nan da wata biyu za’a amshi kudin haya? Banda wahar rashin abinci da muke neman shiga?


Shiru yai yana kallanta yace “ Goggo na rasa yanda zamuyi duk inda nakai takarduna ko nemana yin jarabawa basayi.”


Goggo ta baza tagumi tace “nikam da alama rayuwarmu tai kusan zuwa karshe.”


Kallanta yai yace “karki damu Goggo ina tunanin zuwa gun Zainab ta taimaka min.”


Wani wulakantacen kallo tamai tace “Zainab? Lalai bakada hankali, inda raban an kulleka daga nan kaga shikenan ni na huta ai.”


Fuska ya hade tace “ni fita ka siyo mana maganin sauro.”


Mikewa yai ya fita rai a bace.


*********


Yau ake aka kira sababbin ma’aikata, tun safe take tunanin yanda zasu kare ita da Khalid dan tana tunanin abinda zatamai ta rama.


Fitowa tai ta nufi inda aka kirata akan isowarsu.


Tana shigowa suka fara gaisheta, kallansu ta hau yi daya bayan daya sai dai me? Gani tai sun cika su takwas ba tare da taga Khalid ba.


Juyowa tai ta kalli Ramatu wacce itace ta taho dasu, tace “su kenan?”


Ramatu tace “eh.”


Kallansu Zainab ta sakeyi, a hankli ta fara takowa daidai inda suke, hartazo kan ta takwas din, mace ce yar gayu taci kwalliya sosai, makeup yaji a fuskarta, tana da kyau sosai ga diri, Zainab ta kalleta daga sama har kasa sannan tace “ya sunan ki?”


Cikin gayu tace “Afreey.”


Afreey? Zainab ta maimaita sannan tace “are you telling me Afreey ne sunanki?”


Da sauri tace “sunana “Safeena Sani amma Afreey ake ce.......”


Kafin ta karasa taga tayi gaba, ranta a matukar bace tai hanyar kofa.


Ramatu ce ta matso da sauri tace “Director ance ke za......”


Kallan data mata ne yasa tai gum, kofar Director ta nufa tasa hannu zatai knocking taji yana waya “ai Ranka ya dade karka damu, zan sata a labaran da takeso, ahhh bakomai mune da godi........”ran Zainab a matukar bace bude kofar Director da karfi.”


Yana ganinta yace “to bari na kira.”


Kashe wayar yai ya kalli Zainab yace “Hajiya kin raba musu aikin?”


Kallansa tai tace “me kake shirin yi?”


Name kenan?


Wacce yarinyar me take anan?


Ohhh Afreey? Am sorry dama yanzu nake shirin fada miki yar kanwar Senate Musa ne, ai kinsan shi ko?”


Wani banzan dariya tai tace “sai a kai ya?”


“Ohh to shine take san aiki a gidan tv shine akin magana, nasan kema zakiji dadi tunda yanzu duk abinda muka je nema zamu iya amfani da ita.”


“Yaran dayai interview a maimakonta fa?”


Wa kenan?


Wani kallo tamai yace “ohhhh yaran da kuka danyi fada? Naga kamar bakya sansa shiyasa nai replacing dinsa da ita, sannan shi na duba maga bashi da wata hanya balle ya dawo yace mun cuceshi.”


Kamar zatai magana kawai ta fasa, gaban desk dinsa ta nufa tasa hannu ta dau biro ta jawo paper.


Kallanta yai yce “karki damu yarinyar akwai hazaka.”


Bata kulashi ba sai data gama rubutunta sannan ta tura mai gabanshi ta ajiye mai biro da karfi.


Kallanta yai da sauri bayan ya kalli takardar yace “wani irin resignation letter? Zainab menene hakan?”


Hannunta ta daura daya akan desk din sannan ta kalleshi tace “kai processing dan na ajiye aikina daga wannam lokacin.”


Hankalinshi a matukar tashe ya dawo ta gabanta yce “Zainab meke faruwa haka? Kinfi kowa sanin duk inda muka kai takarda sai suce dake zasuyi aiki, me kike nufi damu?”


Kallansa tai tace “dama ina da matsayi?”


Wani irin zance ne wannan bayan kina ganin komai sai da amincewarki nake?


Wani irin dariya tai na takaici tace “da amincewa ta? Sanda kake kawo wadanda suka maka ina sani?”


Yace “wai akan Afreey ne? Naga yaran can ba sanshi.......”


Ranta a bace tace “ko na soshi ko karna soshi meye nawa a ciki? Aiki yazo nema ya samu saboda iliminsa? Meya kawo zancen zabi anan? Sannan in maganar zabi ne zan iya sanar dakai, kaf cikin wadanda sukai interview shi ne mutum na farko da na fara tabbatar da gwaxanda da cancantarsa, sannan me? Ka koreshi saboda ka kawo yar uwar wani senate?”


Wannan yrinyar da badan badan ba da......

Kallanta yai yace “to yanzu kiyi hakuri za’amai text yazo kinga sai mu dau mutum 9 kenan.”


Meye dalilin da zaisa mudau 9 bayan 8 mukai?


Da sauri yace “Haba Zainab bazaki daga min kafa ba? Nayi laifi nayadda na dauka sai dai nima ki barta aman.”


Shiru tai kafin tace “naji kasa amai text.”

Tana kaiwa nan taja takardar datai rubutu a jiki ta fita.


Da hararar ya bita yace “yarinya karama ta nemi maidani kaninta.” Kwafa yai sannan ya danna ma secretary dinsa kira.


Yana shigowa ya sanar dashi a kira Khalid.


Komawa office dinta tai ta zauna tare da shan ruwa ta rufe idanunta.


*********


Khalid na garaje wayarsa tai kara dauka yai sai dai yanajin kiran na waye ya fito daga kasan mota da sauri, nan yace gashi nan zuwa.


Da sauri ya nufi gida cikin tsananin farin ciki dan da har jikinsa yai sanyi ganin ba’a kirasu ba.


Wanka yai ya shirya sannan ya shiga ya sanar dasu Umma.


Dadi agunsu Umma kamar me, nan suka hau zabgamai addu’a ya fito ya nufi tasha.


Tayi sallah kenan tana duba wasu takardu taji knocking.


Ramatu ce ta shigo tace “Director suna jira.”


Okay ganinan.


Takardunta ta mika mata tace “yi photocopy din wadannan.


Da sauri ta amsa sannan ta juya, wayarta ta dauka ta kira Nabila.


Nabila  ta dauka tace “Aunty dan Allah anjima muzo?”


Ina?


Gun aikinki, sai mu dawo tare.


Shiru tai kafin tace “shikenan.”

Tana ji suna ihu a tare ita dai ta kashe wayarta ta mike.


Tana bude kofar ta ciki yana bude kofar ta waje.


Kallansa tai sannan ta dauke kai ta kalli ragowar dake gun.


Da sauri Khalid ya karaso, suma suka mimike.


Suka matso inda take, Ramatu ce ta mika musu takardun datai photocopy kowa yadau daya sannan ta kallesu tace “muje”


Nan tai gaba suka bi bayanta zuwa broadcast room.


A lokacin ama gabatar da shiri, haka suka tsaya sukaga yanda ake, nan suka nufi control room, nan ma sukaga yanda akeyi, da yanda ake editing da sauransu.


Sai dasuka gama sannan ta sake yima kowa gwaji dan sai sun gama yimusu training an gwada sosai sannan zata san inda zata sa kowa.


Juyawa tai ta nufi office dinta.


Wani producer ne ya fito daga bakin kofa ya mika ma Khalid flask yace “plz kaima Director Zainab.”


Amsa Khalid yai ya juya ya wuce, Afreey ce ta bishi da wani kallo mai wuyar fassarawa.


Sai da Ramatu ta nuna mai inda zaibi yaje office dinta.


Knocking yai sannan ta bashi izini ya shiga, tana zaune a kan computer desk, ta sa glass tana aiki, bata dago ta kalli wanda ya shigo ba har ya karaso inda take.


A hankali ta dago tare da kallansa, ganin Khalid ne yasa ta maida danta kan abinda take tace “ ya akai?”


Ajiye mata flash din yai a kusa da ita sannan yace “aikoni akai.”


Kallan flash din tai sannan ta kalleshi, shima kallanta yai.


Juyawa yai zai fita,  har yayi taku biyu dai kuma ya tsaya ba tare da ya juyo ba.


Kallansa tai tace “me? Akwai wani abu ne?”


Juyowa yai yce “da akwai amma yanzu babu.”


Zare glass din tai tace “baka da abinda zaka cemin?”


Kallanta ya sakeyi yace “no, I don’t think i have.”


Tace “okay shikenan.”


Glass dinta zata maida yace “da zan tambayeki how have you been? To amma energy din ki da na gani ranar interview yasa nasan bana bukatar tambayar.”


Kallansa tai tace “Masu gida ya gida?”


Yace “Gidan mu normal, ya naku gidan?”


Bata tanka mai ba ta cigaba da aikinta.


Shima bai nemi karin magana ba ya juya ya fita.


Yana fita ya nufi inda ya barsu.


Afreey dake tsaye daga tsakiyar corridor ya kalla, dauke kai yai kamar bai ganta ba, har ya wuceta tace “Khalid!”


Bai juyo ba sai dai yadan tsaya, tace “Khalid!”


Juyowa yai ya kalleta yace “Oh Safeeya!”


Kallansa tai tace “pretending kake baka ganeni ba ko kuma dagaske kake?”


Kallanta yai baice komai ba kawai ya juya yabar gun.


Da kallo ta bishi cikin wani yanayi, waya taba tunani zata tsinci Khalid anan?


Khalid ne ya koma suka cigaba da abinda suke, ransa yayi matukar baci duk juyowar dazaiyi zai ga idan Afreey akansa.




*********


Cikin tsananin murna Nusaiba da Nabila suka shiga mota, kaya iri daya suka saka, sai murna suke yau zasu fita dan sun gaji da zaman gida.


Har suka isa suna hira kai bakace sune masu fada ba.


Mamman ne yace “yau lalai take sallah, haryanzu ba’ai fadan gadan ba?”


Dariya Nabila tai tace “dama can wannan ce uwar neman fada.”


Nusaiba tace “ni ko ke?”


Dariya sukai dukansu Mammab yi parking.


Nabila ce ta kira Zainab, sai data kusa katsewa ta daga, tace “Aunty munzo.”


Ku shigo zan turo a karaso daku.”


Cikin jin dadi suka fito.


Suna isa sukaga wani daga kofa nan suka sanar da inda zasu je, security din yace su jira ya tambayo.


Bai dade ba sai ga wanda zainab ta turo nan, murna kamar me suka taho suna murmushi.


Haka suka shiga ciki.


Kamar da wasa Nusaiba ta hango wani kamar Khalid.


Da sauri ta juyo ta kalli Nabila tce “Nabila duba mun can kamar Uncle dina.”


Uncle dinki? Kanin Mumy?


Haushi ya kamata tace “yaya na to.”


Yaya? Ina kika ga yaya?”


Ran Nusaiba a bace tace “bashi ma.”


Ta dago taga bata ganshi ba, da sauri tabau waige waige.


Nabila ta sa hannu ta jata  tce “inka yaya ne in ma Uncle kya ganshi daga baya.”


Har suka isa Nusaiba bata bar waige ba.


******

Ayusher🏌🏻‍♀

[12/6, 8:36 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


The worst part of holding the memories is not the pain. It's the loneliness of it. Memories need to be shared.

—Lois Lowry


{39}


  Khalid na kammala abinda aka sashi ya mike, ganin masu aikin rana duk sun tattafi yasa yadau jakarsa ya fito.


Office din Zainab ya kalla, a ransa yce “wannan agoggon ko ta tafi?”


Fitowa yai ya sauko kasa, yana fita daga gate yaji ance “Khalid!”


Zabgegiyar mota dake gefensa ya kalla, Afreey ce a cikinta, kansa ya kauda ya cigaba da tafiyarsa, binshi take a hankali tace “Khalid!”


Tsayawa yai ya kalleta yace “Safiyya meke damunki wai?”


Magana nakeso muyi.


Kallanta yai yace “in inada ra’ayi kenan ko?”


Nasan in bakada ra’ayin abu bamai saka canzawa, sai dai dan Allah ka tsaya muyi magana.


Kallanta yai, ya kalli wayar hannunsa yace “minti uku na baki, menene?”


Tana san cewa ya shigo amma tasan bazai taba shiga ba tunda maganar ma daya ta kare.


Kallansa tai tace “ranar........”


Kallan daya mata ne yasa ta yin shiru, kafin tai murmushi tace “nasan duk abinda zan fada bazaka yadda ba, sai dai Allah ranar.......”


Kallanta yai yace “ can you stop talking about that?”


Tace “ka san fatan da nake a koda yaushe akan Allah ya hadani dakai nama bayani?”


It doesn’t matter to me, koma me ya faru a wannan lokacin bashida amfani a gareni kinsan me nake nufi in na fadi haka


Yana kaiwa nan yai gaba, da kallo ta bishi har sai da ya kulle.


********


Nusaiba na shiga ta kalli Zainab tace “Aunty naga wani kamar Uncle a can.”


Ta fada tana nuna mata inda ta ganshi, Uncle? A gidan wa kike da uncle anan?


Nabila ce tasa dariya tace “Kanin Muny ya fara aiki anan ai.”


Kanin ta?


Zainab cikin mamaki ta tambaya.


Nusaiba cikin masifa tacewa “Nabila bansan wulakanci.”


Gwalo Nabila ta mata tai gaba dasauri tana dariya.


Nusaiba ta kalla tace “ waye Uncle?”


Nusaiba tace “Uncle daya miki driver.”


Uncle?


Nusaiba tai kasa dakai wai ita a dole kunya.


Gaba Zainab tai ganin batada lokacin wannan shirmen, mota suka shiga sunara fada Nabila tace “in ba neman suna ba na tabbatar ko a hanya ya ganki bazai ganeki ba.”


Nusaiba tace “in bai ganeni ni ba ni sai na tuna mai ai.”


Wata dariya Nabila ta saki wanda ya kara tunzuro Nusaiba.


Zainab ce ta kallesu tace “ya isheni haka nan, Allah yasa insaki jin bakin wata.”


Nan suka shiru, suna hararar junansu.


**********

Washegari....


Goggo ce ta zazzage lalitarta, naira dari ne a ciki kacal, wani irin ajiyar zuciya ta saki mai ban tausayi, ga wuta amma ko tv bata da niyyar kunnawa, saboda damuwar dake cikin ranta yafi karfin kallo.


Cikin ta ne yai wani irin kara, fitowa tai tsakar gida ta nufi waje.


Sai dai yau Adam baya ma kofar gida, haushi da takaici ya kara kamata, haka taje gun mai shayi ta sai bread na naira hamsin sannan ta koma ta hada tea, ta dau gwangwanin madara ta bude taga ba komai, yaushe suka siyo madarar? Milo ta bude shima taga ba komai, lalai Adam ne ya juye, ranta a tsananin bace ta sa sugar ta shaku ruwan buno da bread.


Zama tai tana tunanin abinyi.


Wayarta ta dauko da sauri tana san kiran Hajiya bilki, sai dai jitai ana ce mata batada kudi, haushi ne ya kara tiketa ta ajiye wayar ta kwanta kamar mara lafiya.


Adam na zaune suna musu a babbar majalisa, soron wani abokinsu suke zuwa susa kallo suyi ta musu ana hira da shewa, kallansu yai yace “wlh Allah da gaske nake.”


Kai malam karka raina mana hankali, wannan ce matar taka.”

Adam ya kalli Zainab dake jikin Tv yace “wlh da gaske nake.”


Dariya suka sheke mai da ita, daya daga cikinsu yace “in har kai mijinta ne to ni dan gidan Dangote ne.”


Adam a hasale ya tashi yace “wai ya zan tayi muku rantsuwa kuki yadda, da na dauko wayata wlh dana nuna muku.”


Kallan jikinsa suka fara yi, wani yace “Malam kai ka maidamu kananan yara in bacci kakeji kai maza kaje ka kwanta.”


Dariya suka sheke mai dashi, ran Allah yai matukar baci ya fito rai a bace, ya shige adaidaita.


Sam baima damu da kayan dake jikinshi ba balle silifas din dake kafarsa.


Kofar tv station din su Zainab yai parking, kallan dan adaidaitar yai yace “bari na shiga na amso ma kudi.”


Ransa a bace yace “Malam bansan wulakanci, bani kudina.”


Adam yace “yanzu zani gun Matata na amso maka.”


Ciki yai da sauri, Security ne ya tareshi yana tambayarsa ina zashi.


Adam yai dariya yace “baka ganeni ba? Mijin Zainab ne Adam.”


Kallansa Security din yai sai yanzu yaga kamar sa amma meye hakan? Ya fada a ransa.


Adam ne yai ciki, duk inda yai kallansa ake ana mamakin waye wannan.


Haka ya shigo duk inda yai kallansa ake suna gulmar shigarsa dan duk sun sanshi.


Kan kace me zance ya yad’u akan mijin Zainab yazo, kamar an koroshi daga daji.


Khalid na zaune yana aikin da aka bashi, zancen yazo mai, cikin mamaki yace “mijinta? Adam?” Wata yar iska ya furzar yana tunanin meya zo yi? Da sauri ya mike ya nufi office dinta.


Zainab na zaune tana tattare takardun da zasu presentation a wani plastic company suna san suyi aiki dasu.


Knocking taji, kallan kofar tai tana tunanin ya kamata ta samu secretary dan dama an bata a farko itace bataso saboda gani take westing din kudin su sukeyi gwara tai abinta da kanta.


Izini ta bada ya tura kofar ya shiga, yana shiga Khalid na shiga corridor din.


Mutane ya gani ana leke ana gulma, juyawa yai ya koma ya zauna.


Tsananin mamaki ne ya kamata har ya shigo bata ce mai komai ba.


Adam yana ganinta yai murmushi yace “Honey!”


Karasowa yai inda take yana cewa “Yaushe raban dana ganki.”


Kallansa tai tsaf sannan tace “Me kake anan?”


Honey wallahi ganinki.......


Fuskarta ce ta canza sosai bacin rai ne ya bayyana a cikinta karara, yatsa ta nuna mai rai a bace tace “don’t you dare call me with that name.”


Tsoro ne ya kamashi, dan yanda yaga yanayinta ya canza gaba daya sai yaji ya kasa magana.


Kallansa tai bayan ta mike tace “Uban me kake min agun aikina?”


Ho....Zainab......


Cikin tsawa da fada tace “me ka daukeni? Wulkantani kazo yi ko mutuncina kazo ci.”


Kai ya shiga girgizawa da sauri yace  “ ba haka bane wlh, bansan ya akai ba na ganni a bakin nan.”


Wani murmushi tai tare da daga gira daya ta bacin rai tace “ka dauka bansan me kazo yi bane? Kazo ne ka ci mutuncina ka nunawa mutane bama tare yadda zan zama abin kwatance da wulakanci a cikin mutane.”


Shiru yai jikinsa duk yai sanyi, tace “ba laifinka bane, kome kai laifina ne da ban sa an kulleka ba bayan abinda ya faru.”


Komawa tai ta zauna tace “fita!”


Juyawa yai jiki a sanyaye kamar an mai duka, haryakai kofa ya juyo yace “Ki taimaka min dana mota.”


Kallansa tai yace “adaidaitar dana shiga ban biya ba.”


Tace “banaji wannan ya dameni, ka fita ko sai na sa an fitar dakai?”


A hankali ya bude kofar ya fita, suna jin an bude kofa yan gulma kowa ya juya, ana kallan yanayinsa kowa da gulma dake cinsa.


Adam na fita suka shigo, daga gefen Khalid suka tsaya suna dariya, wani yace “wannan anya tana bashi abinci ma?”


Dariya wani yai yace “dama duk wanda ya auri wannan ai ya auri rashin kwanciyar hankali”


Afreey dake kefensu tace “mijinta ne?”


Ramatu tace “eh.”


Cikin mamaki Afreey tace “amma yazo a haka?”


Dariya sukai wani yace “ina kwanciyar hankali da alama daren jiya duka tamai.”


Khalid wanda ransa yakai matuka gun baci yana dannewa ji yai wani yace “kai harna tausayamai, wannan da alama ko abinci sai ya tambayeta yake ci.”


Desk dinsa ya daka da karfi wanda yasa kowa kallansa, murmushi ya musu yace “am trying to see how strong i am.”


Kallan mamaki suka mai zasu cigaba da gulmar sukaji yace “Ahhh ni yaushe ma akace za’ai meeting din?”


Ramatu ta kalli agoggo tace “bata fada mana ba, wazai tambayo ta.”


Da sauri kowa ya watse kai kace korarsu akai.


Ramatu ta kalli Khalid tace “ko zaka tambayota?”


Mikewa yai ba musu.


Afreey tai shiru tana tunanin yanayin daya faru a wannan lokacin, tabbas dan a tsaya da maganar ya daki desk, meye nashi a ciki?


Knocking yai, ta bashi izini.


Bata dago ba sai daya maida kofarya rufe.


Dagowa tai ta kalleshi, tace “ya akai?”


Karasowa yai kawai taga yaja kujerar dake gabanta ya zauna.


Sake kallansa tai tace “ya akai?”


Kallanta yai kamar zaiyi magana sai kuma yai shiru, murmushi tai tace “kaganshi?”


Hmmm


Murmushi tai tace “it seems like kowa ya zama busy saboda hakan.”


“Are you okay?”


Kallansa ta sakeyi tadan karkatar dakai kadan tace “ kai da ka saba ganewa sai ka duba ka gani, am i okay?”


Dan matsowa yai yana kallanta, juya kai tai gefe saboda batasan kallan, komawa yai ya zauna yace “you are not.”


Da sauri ta kalleshi tace “mene?”


Yace “then ke kina tunanin u are?”


Tace “sosai, meka daukeni? Kana tunanin karamin abu kamar wannan zai sani damuwa?”


Dan hannunsa yasa ya shafi wuyansa, harararsa tai tace “kana nufin zai sani kenan?”


Yanzu ma baice mata komai ba sai dai ya mata kallan eh.


Haushi ne ya kara kamata ta hade fuska tace “naji ya sani, jeka kacemusu bayan lunch xamuyi  meeting din.


Okay yce sannan ya mike, haushi ne ya kara dan kamata ganin ya mike hankali a kwance tace “mikomin ruwa a fridge.”


Juyowa yai ya kalleta, alama tamai daya miko mata, kallanta yai sannan ya bude fridge ya dauko ya zo gabanta ya ajiye, har ya juya tace “saura cup.”


Kallanta ya sakeyi sannan ya dauko yazo ya ajiye mata, harya sake juyawa tace “ohhh ga wani file can a saman shelf daukomin.”


File? Ya fada yana kallanta, tace “eh.


Dauko mata yai yazo gabanta ya ajiye yana kallanta.


Juyawa yai tace “Ohhhh bana san shan ruwan nan zo ka siyomin fanta a shagon kasan layi.”


Takowa yai yazo inda take, tana guntse dariyarta ta dauko 1000 ta mika mai, amsa yai sannan ya kalleta yana juya kudin sannan ya mika mata.


Kallansa tai tace “na meye?”


Yace “Ohhh bakya san ruwa ya kamata kije ki siyo fanta.”


Fuska ta tsuke tace “kana nufin na fita na siyo?”


Kudinta yakara mika mata yace “ba wannan a cikin aikina.”


Tace “in babu senior dinka a gun aiki tasa ka by right kuma dole kayi.”


Dan ajiyar zuciya yai yace “by right zanyi amma in har bani da abinyi kenan.”


Ya ajiye mata kudin sannan yace “yanzu na fahimci you are okay.”


Kallansa tai tace “Sam baka biyo halin Umma da Abba ba.”


Shima kallanta yai yace “kema baki biyo halin Dady ba.”


Wani kallo tamai tace “bakinka baya rasa abin fad’a ne?”


Yace “in har naki bai rasa ba.”


Hade rai tai tace “ mene?”


Bai bata amsa ba ya juya ya ya fita.


Yana fita ta kalli kofa, sannan ta kalli kudin.


Khalid na fita ya samu kansa da dan murmushin da baisan daga ina ya fito ba.


Afreey dake nesa a tsaye ce ta kalleshi sannan ta tako inda yake.


Kallanta yai bayan ya hade fuska yana neman wucewa.


Tace “menene tsakaninku?”


Kallanta yai kamar zaiyi magana sai  kawai yai gaba.


Shiru tai tana kallan office din Zainab.


********


Adam na fitowa mai Adaidaita ya cakumeshi, yace “ina kudina?”


Adam ya kalleshi yace “dan Allah kayi hakuri yasin ficika bana magani.”


Ficika?


Adam da sauri yace “eh wlh.”


Kallansa yai bayan ya sakeshi ya kalli layin gani mutane ta ko ina yace “ba komai, na yafema kana da yanda zakai ka koma?”


Da sauri Adam yace “a’a.”


Nan Yace “muje na maidaka.”


Godiy Adam ya shiga yi harya shiga motar, suna tafe yanata tunanin abinda Zainab tamai, zuciyarsa duk ba dadi gashi sama da kasa ya nemi Sadiya dan ya ci mutuncinta ya rasa.


Suna zuwa lungun mai adaidaita ya tsaya ya cakumo Adam ya jawoshi waje.


Da sauri Adam yace “Lafiya?”


Naushin daya sakarmai ne yasa shi faduwa kasa, gefen bakinsa ne ya fashe ya kalleshi zaiyi magana ya jawo shi ya kara kaimai wani naushin.


Yazo mai na uku Adam ya mike yafece a guje.......


Ni kaina gudunsa yasa na kasa binsa🥴🚶🏻‍♀


*****

Ayusher🏌🏻‍♀

[12/7, 10:17 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


"Make it a habit to tell people thank you. To express your appreciation, sincerely and without the expectation of anything in return. Truly appreciate those around you, and you'll soon find many others around you. Truly appreciate life and you'll find that you have more of it." —Ralph Marston


{40}


Agoggon dake manne jikin bango ta kalla ajiyar zuciya tai sannan ta tattara takardun dake kan desk dinta sannan ta mike ta fito.


Tasa hannu zata murda kofar taji wani a cikinsu nacewa "kuna tunanin zata iya zuwa? Yanda mijin nan nata ya kunyatata?"


Dariya taji wani na cewa "da alama neman silhu yazo yi, tunda mukaga takai wannan lokacin dakyar ta iya zuwa."


"Yoo ina kunya zata barta tazo."


Khalid na jinsu sai dai baice komai ba, kofa ta bude da iya karfinta.


Kallanta sukai a tare, kallansu tai sannan ta karasa ta zauna.


Takardun hannunta ta watsa jikin dogon table din meeting din.


Dukansu sunyi gum kowa na kallanta, Afreey kam gaba daya hankalinta nakan Khalid wanda ke zaune.


Kallansu tai sannan tace "da alama kun samu abin tattaunawa tunda gashi nayi late amma it seems no one notice that."


Shiru sukai, kallan kowa ta farayi tana tambayarshi abinda yai daga zuwansa har wannan lokacin.


Ganin dukansu sunyi shiru yasa Khalid ya kasa cewa ga abinda yai.


"Bakuyi abinda ya kamata kuyi ba amma kowanenku ya iya shiga maganar da bata dameshi ba?"


Kasa sukai da kansu, haka ta musu bayanin abinda za'ai sannan batare da ta sake tambayar kowa wani abu ba tana gamawa ta hada kayanta ta mike, juyowa tai ta kallesu tace "sannan wanda yazo bani da hadi dashi kamar yanda banida hadi da d'aya daga cikinku."


Gaba daya baki suka sake har ta rufo kofar sannan suka fara kallan juna, Ramlatu ce ta mike ta fito daga meeting room din.

Afreey ta kalli Khalid wanda ke zaune bashi da alamar tashi.


Waya ce tai kara da sauri wani ya daga, Zainab tace "a cikin rookie din nan, kace mutum daya ya fito muje Plastic Company."


Tana kaiwa nan fa kashe wayarta.


Kallansu yai, yace "mutum daya ya shirya zasu fita da Dire......"


Ai kafin ya karasa wadanda ba sababbin dauka ba sun bar gun, Afreey ce tace "me za'ai?"


"Bansani ba tadaice yanzu."


Shiru sukai, wannan yace cikinshi na ciwo wannan yace toilet zaije.


Khalid ne yace "bari naje."


Da sauri Afreey tace "bari ni naje."


Kallanta yai yace "kinyi submitting report dinki ne?"


Kasa tai dakai ya juya ya fita.


Zainab wacce dama da zata taho yau dakanta taja motar saboda tasan akwai inda zata.


Knocking yai ya shiga, kallansa tai sannan ta mike ta dau jakarta batace komai ba tai hanyar kofa.

Ganin haka yasa shima ya fito.


Gaban motarta suka je ta mika mai key sannan ta shiga ta zauna, yayi mamakin data zauna a gaba kenan tasan ba a matsayin driver zai ja ta ba kenan?


Shiga yai suka dau hanya bayan ya tambayeta inda company din yake.


Kallansa tai taga yanda ko magana bai sake yi ba tunda yaji inda zasu, duk da tasan ba magana ce dashi ba amma at least ta dauka zai tambayeta abinda ya faru dazu.


Kallansa tai tace "wannan had'a ran fa?"


Bai kalleta ba yace "ni?"


Ya fad'a tare da dan kallanta, tablet dinta na hannunta tana duba slides na presentation dinta tace "eh"


Baice komai ba ya cigaba da tafiya, kallansa ta sakeyi tace "haushi kaji na had'aku duka na muku fad'a?"


Kallanta yai yanzun ma ba kallanshi take ba, gangarawa gefen titi yai ya juyo ya kalleta kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa.


Itama kallansa tai tace "fadi, ba shi bane?"


Yace "as a director wacce ake respecting kina tunanin dan kin mana fad'a wani abin ne? As we are all your subordinate?"


Tace "then?"


"Ba hurumina bane I don't think inada damar magana."


Murmushi tai tace "kai din? Tun yaushe kake magana akan abinda ba huruminka ba?"


"Hakan ne dalilin dayasa na daina daga dazu."


Dazu? Kenan dan nayi maganar rabuwar aurena da Adam ne ya saka?


Kallanta yai baice komai ba, tace "bakai kace na fada ba?"


Ni? Ya tambaya cikin mamaki, tace "eh muje banasan African time."


Jan motar yai yana cewa "yaushe?"


Tace "dana aikeka ka siyomin abu me ka cemin?"


Bata jira yace wani abu ba ta fara fadamai abubuwan da za'ai fadamai abinda zaiyi agun.


Shima bai kara neman ji ba dan shidai yasan basuyi wannan maganar ba.


Har suka isa bai sake magana ba itama ganin bashi da niyyar magana tana gama mai bayani tai shiru.


******

Kan kace me labari ya karade gaba daya tv station dinsu.


Tunda Ramatu ta fadawa Director Kabir haryanzu bai ce komai ba dan gaba daya hankalinsa ya tashi.


Sai can ya daure yace "me ya rabasu?"


Tace "bansani ba nima."


Shiru yai ransa a matukar bace yace "yanzu in abu ne wanda zai jawo mana matsala da zarar 'yan jarida ko mujalla sunji labari shikenan mun shiga uku."


Hankalinsa a tashe ya kori Ramatu ya dau waya ya kira Zainab.


Tana kokarin shiga company din wayarsa ta shigo, tasan maganar da zai mata, saboda tasan daga sanda ta bude baki tai maganar tafi kowa sanin abinda zai biyo baya, ba abinda ta tsana a rayuwarta irin ta zauna cikin mutane tana yaudararsu, tunda ta dawo daga Abuja take zargin kanta da yaudara da karya tunda duk kowa kallan matar Adam yake mata, mexai faru a sanda wani yaji daga waje? Bata kara jin haushin kanta na boyewa ba sai da sukai magana da Khalid ta fahimci menene aikinta.


  Haka ta wuce ciki bayan ta kashe wayarta.


*********


Goggo na share falo saboda ta kwana biyu ko sharar ma batada lokacin yi saboda damuwa, yaukam tana kwance taketa jin kanshin miyar dage dage, gaba daya yawunta ne ya gama tsinkewa, ganin abin na damunta ne yasa ta mike ta hau shara.


Tana bakin kofa tana kwashewa sai ga Adam.


Tsallakawa yai ya wuce, ta ajiye abin sharar ta kalleshi tace "wai ni sai yaushe zaka dinga sallama in zaka shigo guri ne?"


Karasa wa yai ya zauna akan katifa  yace "ni abinda ke damuna ya isheni dan Allah karki kara mun da wani."


Juyowa tai rai a bace tace "gidan uban wa ka kaimana madara da milo?"


Kallanta yai, da sauri tace "meya sameka?"


Ta fad'a tare da tasowa da sauri zuwa inda yake, kwanciya yai yace "ki bari kawai Goggo saura kadan a halakani, daga shiga adaidaita ba kudi"


Kallansa tai tace "ina kaje? Ki meya kaika shiga mota ba kudi?"


Gun Zainab......


Zainab?


Da sauri ta kalleshi tace "bakada hankali?"


To ya kikeso nayi, ni gaba daya wannan zaman ya isheni, sam abokaina basa darajani, da duk inda naje girmamani ake yanzu ko matsayin magana ta gaskiya ma bani dashi, ni na gaji wlh.


Kallansa tai kamar ta makeshi sai dai kanshin dage dage ya gama sa karfinta ya tafi, tace "wato kaidai wlh ban taba ganin mutum wanda baya nazari irinka ba, ko uban me Zainab ta gani anan harta aura ni bansani ba."


Fuska ya hade yace "koma meta gani shine silar jin dadinki kema."


Mikewa tai tace "ni banida lokacin haukarka, yanzu ka mike ka fita ka nemo mana na abincin rana."


A ina zan nemo? Ko ana rabo a makota ne?


Wani kallan takaici tamai tace "eh duk gidan da ka gani kaje kace kazo amsar rabanka."


Dariya yai jin zafin bakinsa ne yasa yace "Goggo mekila daukeni me?"


Sai na fada? Akai a shashashu ma kaine sarkinsu.


Ransa ne ya baci ya kwanta baice komai ba, tace "billahi lazi tashi zakai kasan yanda zakai muci abinci dan yunwa nakeji kamar me."


Nimafa yunwa nakeji, ina nasan yanda zamuyi?


Sai ka dau kayanka kalai kasuwa ka samo mana kudi.


Tab kayan dana ajiye bansan batasu shine zan siyar?


Tace "dole ka siyar kuwa."


Mikewa yai ya shiga daki ya sauke labule.


******


Khalid shiru yai yana kallan yanda Zainab ke tafiyar da Presentation dinta, shi kuma yana danna mata slides din, gaba dayan mutanen gun sunyi shiru suna jin yanda ta ke watso musu ideas wanda duk wani wanda ke gun tabbas sai yayi sha'awar yi.


Duk tambayoyin da suka jefo mata cikin dabara da jan ra'ayi take basu amsa wannan yasa Chairman din Company din amincewa a take a gun, nan Khalid ya mikamai takardar contract itama ya mika mata daya sukai signing sannan ya amsa yai switching suka sakeyin signing.


Cikin jin dadi Chairman din yace "am looking forward to this project."


Cikin confidence dinta tace "you will never regret your decision."


Nan aka tafa sukai sallama suka fito.


Tana shiga mota ta sha ruwan dake hannunta sannan tasa hannunta akan goshinta ta lumshe idanunta.


Khalid ya shiga yaja, a hankali ta kalli agoggon jikin motar tace "lokacin tashina yayi, bari na ajiyeka na wuce gida."


"Bari na ajiyeki sai na wuce."


Bata musa ba ta dau waya ta turama Director Kabir text na hoton contract din da sukai, sannan tadaura da sauran maganar mayi gobe.


  Ganin contract din da zasu samu uban kudi yasa yace to Allah ya kaimu.


A kofar gidanta yai parking, Bala ya bude ya shiga da ita.


Kallansa tai tace "nagode."


Bakomai, ya bude motar ya fita.


Yana fita daga gate suka gagaisa da Bala sannan ya wuce, yana tafe yana tunanin dole yana bukatar sake dagewa, dan yau ya fahimci bai maida hankali ba ko kadan, duk da ba abinda ya karanta ba kenan anma yasan in ya maida hankali sosai komai mai yiwuwane da izinin Allah.


Zainab har ya fita bata mike daga zaunen da take ba, haka kawai ta samu kanta da jin haushin yanda ya mata, tana ganin shi zai rakata ta dauka yanasan ya mata maganane amma sai ya nuna bashida ra'ayin hakan?


Meye nawa a ciki? Kar ya tambaya din, kowa ya sha xamansa.


Muryar Nabila taji daga gefen ta.


Murmushi tai sannan ta tuna hutunsu ya kusa karewa gashi bata nemi babbar mai aikin da Dady yace ba.


Ahhh da alama tana da abubuwa dayawa a gaba.


*********


Goggo tadan leko, su Asabe ta gani ana tacin shinkafa da dage dage, tace "Asabe nikam kin san waya iya kitso a nan kusa?"


Asabe ta kai loma tace "Karimatu ta iya anan makota take."


Goggo tace "Allah sarki, nagode."


Kallan yaranta dake cin abinci tai tace "oh anatacin abinci ne?"


Asabe tace "eh, ya akai?"


Dariya Goggo tai tace "bakomai, nima inzo in daura dan ganin kunacin abinci ya sani jin yunwa."


Asabe ta kalli yaranta biyu mata dake cin abinci tare, ga danta namiji a gefe wanda ya mike yace "ni nakoshi."


Asabe cikin gatse tace "ko zaki d'ana wannan kafin ki daura? Dan banda wani sai wannan da babangida ya rage."


Ga mamakinta ganin Goggo tai zuruf ta mike tazo ta amsa tana cewa "bari na dan taba, haka kawai yunwa taxomin yanzu."


Asabe ta tabe baki a ranta tace sanda kuke cin tsire a daki, ku soya dankalu ai ko kwaya baki taba ba ko 'ya'yan mu ba.


Ita dai Goggo ta shige daki, tana shiga ta cinye, haushi ya kamata tace "ai da sai ka rage dayawa, na rasa meyasa yara ke da uban ci ina laifin suci kadan, wani sa'in sai ka rasa ina suke kaiwa."


Adam ne ya fito yana neman fita yaganta tana sud'e hannu, da sauri yace "Goggo kinsamo mana abincin ne?"


Kwanon ta turamai tace "eh gashinan ci."


Yace "wannan ai bakomai, ina nawa?"


Wani kallo tamai tace "kasan Allah? Idan baka fita ka saida kayanka ko dako kayi ba, ranka ne zaiyi matukar baci."


Dako?


Yanda yai maganar a zabure yasa tace "to fadamin inba jikinka ba uban me kake dashi."


Dariya yasa yace "nine zanyi dakon? Adam din? Mijin Zainab?"


Mikewa yai yana cewa "zanje indawo ki samarmana abin ci."


Haushi ne ya kamata ko amsa ma bata bashi ba.


Yana fita majalisa suka tsareshi, ina hoton? Nasan ai yanzu ka dako.


Kallansu yai ya zaro wayarsa.


*******

Ayusher🏌🏻‍♀

[12/9, 9:53 PM] Maman Zara Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{41}


  Nuna mana, kallansu yai yace “nawa kuka sa.”


Dariya sukai nan kowa yasa aljihu, yana nuna mai kudin dake aljihunsa, ido suka zubamai suna san ganin hoton.


Bude musu hotonsa wanda sukai shida Zainab bayan auransu kadan, baki suka sake suna kallo, cikin hadara yace “yanzu kun yadda?”


“In kuma a hanya ka ganta kuka d’au hoton fa?”


Cikin bacin rai yce “ to wannan fa?” Nuna musu wanda sukai ya rike kafadarta yai.


Idanuwa suka firfito dashi, cikin mamaki yace “ku bani kudin”


Ba musu haka kowa ya mikamai abinda ke aljihunsa, baki ya washe cikin jin dadin ganin ya hada dubu uku da dari biyar daga nuna hoto.


Kamalu yace “bani wayar na kara gani.”


Mikamai Adam yai tare da hard’e hannu ya zauna yana girgiza kafa irin sarkin nan.


Kamalu ya faki idanunsu ya tura ta whatsapp dinsa, sannan ya mika mai wayar.


Suna rabuwa ya daura hoton a instagram tare da cewa ko kunsan wanene mijin Zainab Aliyu Tahir? Sannan ya daura wani wanda sukai shida Adam.


Ya dan rufe fuskar Adam da hrt emoji kan kace me hoto ya fara yad’uwa a instagrams, whatsapp da kuma facebook, kowa yana san ganin mijin.


Dariya yasa ganin yanda yake ta kara samu followers gashi anata tambayashi ya nunashi.


Kamalu cikin jin dadi ya kara rubuta, ko kun san Zainab da Mijinta basa  zaune a gida d’aya?

Ai kan kace me ta ko ina gulmar abin ake, ko ina ka leka maganar kenan.


Zainab kam batasan me ake ba dan bata whatsapp bare instagrams gwara facebook tana shiga taga labarai, bare su Nabila wanda ta hanasu da kanta acewarta su bari sai sun gama skul.


Da safe ta shirya ta nufi office, sai dai tana shiga taji ana gulmarta, bata wani bi ta kansu ba dan tasan maganar jiya ce suke kara riritata.


Khalid wanda ke rike da wayar Afreey yana kallan hoton data zo nuna mai ya kurawa hoton ido dagowa yai  ya kalleta yace “inada magana dake.”


Kallansa tai sannan ta bi bayansa ba tare da tace komai ba.


D’an dakin da suke cin abinci ya shiga, kallanta yai yace “menene hakan?”


Tace “ina na sani nima, ganinshi nai tun jiya yana yawo shiyasa na nuna ma.”


Idanunta ya kalla sannan ya kauda idansa, dan matsowa tai tace “Khalid tun jiya dana ganshi nake tunanin nasanshi, sai dai na kasa gasgatawa, Ba Adam awala bane?jiya dayazo na ga fuskarsa.”


Kallanta yai, baice komai ba, dariya tai tace “Dagaske Adam ta aura kenan?”


Fuska ya hade yace “Dariyar me take nufi?”


Guntse dariyarta tai tace “ina mamaki ne dan ban taba kawowa Adam bane, yanzun ma na tambaya ne........”


Kallanta yai yace “koma menene aranki karki kuskura ki soma, nasanki sarai nasan akan wani ra’ayi nake ba abinda bazaki iya yi ba.”


Kallansa tai tare da hade fuska tace “shaidar da zakamin kenan?”


Ba haka kike ba?


Kallansa tai tace “kasan shekara nawa nai ina nemanka?”


Wani kallo ya mata tace “Khalid plz ka bani dama na  gyara barnar danai a baya, bansan meye tsakaninku da ita ba amma kai kasan bazan taba hakura da abinda nake so ba, dan haka in har ba abinda nake zargi bane tsakaninku ka bani dama.”


Kallanta yai kawai baisan sanda yasa dariya ba, ya shafi kansa sannan ya kalleta.

Zainab wacce tazo daukan cup ne ta kallesu tacikin glass din kofar, dariyar dataga Khalid  nayi ne yasa ta tsaya tana kallansa, shiru tai kafin ta juya tabar gun.


Khalid ne ya kalli Afreey kamar zaiyi magana kawai ya wuce.


Zainab taje shiga office dinta taji muryar Director Kabir taji yace “Zainab!”


Juyowa tai ta kalleshi, yace “inada magana dake.”


Kallansa tai sannan ta nufo office dinsa, tana shiga ta zauna, kallanta yai sannan ya juya mata da laptop dinta saitinta, kallan hotonta dana Adam tai, sannan ta kalli rubutun kasa, da sauri ta dago ta kalleshi, fuskarsa a hade take, wanda bata taba gani ya hade mata rai ba yace “meya rabaku dashi?”


Kallansa tai tace “kome ya rabani dashi wannan personal matter dina ne.”


Personal? Wannan shine personal? Yai maganar cikin fada.


Kallansa tai tace “me kake nufi? Nina sashi yai kenan ko me?”


Ko ke kika sa shi ko ba ke bace alama ce ta kin kasa controlling dinsa, kinsan daga daren jiya zuwa yanzu mutane nawa ne suka kirani suna tambayata abinda ke faruwa? Akarshe sai wayata na kashe?”


Kallansa tai abin takaici tana kokarin magana taga an kara posting din wajen gidan dasu Adam ke ciki a kasa ansa “ko kunsan nan ne gidan da Zainab ta kori mijinta yake zaune shida mahaifiyarsa? Me kuke tunanin ya mata?”


Comment ne suka fara bayyana ta ko ina, Director Kabir ransa a matukar bace ya rufe laptop din da d’an karfi yace “bazan yadda da abinda zai kawo dakushewar gidan tv din nan ba, dan haka ki gaggauta gyara komai, in ba dan ke nace bama da korar wanda yai zanyi.”


Kallansa tai idanunta suka fara yin jaaa, mikewa tai ta fito ta nufi office dinta ranta a matukar bace, farcenta ta shiga karza dayan farcenta dashi tana tunanin abinyi.


Can yamma bayan la’asar ganin gaba daya yau ta kasa yin komai dan dama haryanzu bata amshi shirinta ba tunda ta dawo, tana so ta gama gyagyara matsalolin su kafin nan.


Wayarta ta dauka ta kalli number Adam, ranta na kara mugun baci, waya ta dauka ta kira staffs room, ana dagawa tace “akira mata Khalid.” Tana kainan ta kashe.


Khalid wanda ya zauna yana harhade takardun da za’ai shiri dasu gobe ne ya kalli Ramatu datace ana kiranshi.


Mikewa yai yazo fita, Afreey ce ta kalleshi fuskarta cike da kishi da takaici, baibi takanta ba ya wuce.


Zainab na zaune akan kujerarta tana kara kallan abinda ke faruwa ta facebook, tare da kokarin bude account na instagram dan ganin abinda ke faruwa sosai.


Knocking Khalid yai sannan ta bashi izini ya shiga.


Kallansa tai bayan ya karaso ciki tace “kana instagram?”


Kallanta yai dan ya fahimci ta gani kenan, shiru yai yana kallanta, sannan ya girgiza kai alamar a’a.


idanunsa ta kalla bayan ta kauda nata idan ne tace “it seems like kaima kaga abinda ke faruwa.”


Uhmm ya fada tare da d’an daga kai


Shiru tai kafin tace “before reporter’s su tare Adam suyi hira dashi i have to do something.”


Kallanta yai yanzu kam baice komai ba, dagowa tai cikin dauriya tace “Bantaba tunanin Adam zaimin haka ba, duk da ynda muka rabu amma atleast na dauka zamu rikema juna sirri.”


Kallansa ta karayi tace “zaka iya dubomin inda yke zama?”


Kai ya daga alamar to, samun kanta tai da jin haushin yanda yaki mata magana bayan yanzu ta ganshi yana dariya da Afreey koda yake dama tasan maza duk daya suke daga sunga mace yar kwalliya magana ta kare.


“Barshi kawai, na kula bakada niyyar yi, just pretend you haven’t heard anything from me, jeka kawai.”


Ga mamakinta gani tai ya juya, cikin kufula tace “tafiyar zakai?”


Juyowa yai yace “I thought that’s what you said?”


Ranta a bace ta mike tace “yaushe ka fara yin abinda nace?”


Bata jira amsarsa ba tace “in magana ce dakai ka fito ka fada, just be your self.”


Shiru yai yana kallanta kafin yace “abinda aka riga aka batashi banaji magana zata gyara shi.”


Zama tai sannan ta Kalleshi  tace “me aka bata?”


“Hotuna sun riga sun shiga wayoyin mutane da dama, sannan kowa a matsayin mijinki yake daukansa, inhar bake zaki........”


Da sauri zatai magana ta zubar da juice din data zuba a cup akan laptop dinta duka ya zube a jiki.


Da sauri ya karaso kusa da ita, zama yai a kujerar da ke gabanta sannan ya ja laptop din.


Da sauri yace “tissue.”


Kallansa tai zatace yana can taga yana miko mata hannu alamar ta bashi.


Kallan tissue din dake kan shelf tai sannan ta kalleshi, d’aga laptop din yai yana kallanta ganin bata da alamar daukowa.


Kallansa tai kamar zatai magana sai kuma ta nufi inda yake.


Ranta a bace ta dauko tana tunanin tunda take an taba sata miko abu? Mikamai tai ta hade fuska sosai.


Baibi ta kanta ba ya amsa ya fara goggewa, sai dai ganin ya shiga ciki yasa ya kalleta yace “inada screwdriver?”


Eh, dan bani.


Kallansa ta sakeyi tace “yana can.”


Kallanta yai yace “taimako fa nake?”


Tace “ko taimako kake a kasa na kake na dauko tissue yanzu sai ka dauko kaima”


Kallanta yai kawai sai taga yasa murmushi, fuska ta daure sosai tace “meye?”


Yace “badai ba’a tava saki dauko abu ba?”


Kauda fuskarta tai ta dan matsa daga kusa dashi tare da zama a d’aya kujerar tace “how do you know?”


Sake murmushi yai yace “rike wannan to, dan inba haka ba wanda ya shiga sake shiga zai.”


Kallansa tai tace “wai sai dai ka sani aiki?”


“Ko na tafi?”


Cikin hade rai ta amsa tare da kauda kai, ina yke?


Tace “can.”


Can ina?


Ya tambaya yana sake kallanta, haushi ya kara kamata tace “dawo ka rike na dauko.”


Da saninsa dan ya gani komawa yai ya amsa ita kuma ta mike fuska a daure ta dauko, da karfi ta ajiye a gabansa.


Yazo dauka ta janye tace “kana san cemin baka ganshi ba?”


“In na ganshi mexaisa na dawo?”


Harararsa tai tace “ya akai nake ji kamar da saninka?”


Hannunsa ya mika mata yace “kin tabbatar ba ra’ayinki bane yasa kike jin hakan?”


Mikamai tai da karfi, amsa yai ya fara kuncewa.


Kallan abinda yake tai sannan tace “karasa maganar ka ta dazu.”


Bai kalleta ba yace “ki sanar da komai da kanki, even though it will get harder at first, amma atleast ba wanda ya isa ya shiga miki bincike tunda kin riga kin rufe bakinsu.”


Nayi wannan tunanin amma in yan jarida suka nemishi suka tambayeshi dalilin rabuwar mu fa kafin nai magana da kaina? Ko kuma suka nemi yarinyar fa?


Dagowa yai yace “Raziyya?”


Ganin yanda ta kauda kai yasa yace “Raziyya bazatace komai ba, am sure dan da dama ba cutar dake tazoyi ba, sannan bazataso tayi abinda iyayenta zasuji ba.”


Wani kallo ta mai sannan tace “da alama kasanta sosai tunda harkasan abinda zatai da wanda bazatai ba, ko da yake wanda ya tsaya yana dariya da wace bai dade da saniba meye bazai ba.”


Kallanta yai duk da bai fahimci kalamanta ba amma yasan magana take gasamai, mikewa tai tana neman komawa daya bangaren, da sauri yace “rikemin wannan.”


Kallansa tai ranta a bace tace “naki na rike.”


“Tunda taimako nake zan iya tashi nima.”


Tace “jeka kafi ruwa gudu.”


Dagowa yai ya kalleta yace “ gaskiya ce bakyaso a fada?”


Gaskiya? Hakan shine gaskiya? Hannunta ta daura akan desk din tace “ace ma gaskiyar kake fada kai baka iya magana cikin sanyi ba?”


Kallanta yai idanunsa na cikin nata yace “na iya.”


“Ni kadai kake ma kenan?” Ta fada tana kallansa


Kallanta ya sake yce “Ummm”


Haushi ya kamata tace “Then why?”


Mika mata keyboards din yai sannan yace “I don’t know.”


Amsa tai ta ajiye akan desk din sannan tace “you don’t know?”


“Hmmm I don’t know why”


Komawa tai daya bangaren ta zauna tare da dauke kanta daga inda yake.


Cigaba da gogewa yai yna cewa “in na samoshi zaiji abinda zaki cemai?”


Shiru tai kafin tace “I don’t know”


Yasani sarai ramawa tai hakan yasa ya kalli agoggo karfe 6 ce ta buga.


Shiru sukai ya karasa gyarawa sannan ya mike yace “zan nemo inda yake, i will send you the address.”


Harya kai bakin kofa ya juyo ya kalleta yace “amsar da kike nema tana gunki, trust your self”


Dagowa tai ta kalleshi, juyawa yai ya fita.


Kofar ta zubawa ido shiru tai tana tunani, meyasa da bata taba neman taimako agun wani duk runtsin da zata shiga kuwa, harsai ta samo yanda zata warware komai, amma yanzu me yasa take san jin ta bakin Khalid?


Kallan screwdriver da tissue din tai sannan ta kalli laptop din.


*****


Yana kokarin fita yaji Afreey tace “sai yanzu ka dawo?”


Juyowa yai ya kalleta cikin mamaki yace “baki tafi ba?”


Kallansa tai tace “kace bakomai tsakaninku.”


Kallanta yai dan baisan sanda ya fadaba kuma baiga dalilin amsawa ba.


Wayarta ta mikamai bani number Adam, kallanta yai yace “kimai me?”


Ince ya maida matarsa.


Ido ya kura mata sannan yace “Please Safiyya, karki soma yin wani abu, I don’t know what you are thinking amma koma meye a ranki i ask you to please stop, in kuma har kikai abinda zai sa mutane shiga matsala saboda ra’ayinki i will never forgive you.”


Yana kaiwa nan ya juya ya fara tafiya, ranta ne ya kara baci tace “in ka aureni ka yafemin.” Ta fada cikin kishi.


*******

Da sauri Raziyya ta mike zaune tana kara kallan hotunan, kafa tasa ta ture hannun Jamil da yake shafa mata mai a daya kafar, cikin takaici tace “bai saketa ba kenan ko me?”


Kallanta Jamil yai yace “na dauka kin tabbatar bazata dauki raini ba?”


Tace “haka na dauketa da alama nice nake mata kallan jaruma.”


Hoton ta kurawa ido ranta a bace tana huce.


Yace “yanzu me zakiyi?”


Tace “kome zanyi sai nayi dan Allah sai auran nan ya rabu.”


Shiru Jamil yai kafin yace “nifa inaga akwai abu a kasa, in ba haka ba me zaisa ta koresu?”


Shiru tai tana tunani kafin tace “fita ka nemomin inda zan sameshi.”


Kallanta yai yace “yanzu?”


Wata muguwar harara tamai tace “dazu”


Mikewa yai da sauri ya fita.


Cikin kuluwa ta cilar da wayarta gefe.


********


Washe gari da safe


Goggo dake tajin dadin kudin da suka samu dan jiya shinkafa da miya tai itama yau kuwa indomie suka dafa da kwai soyayye, ta kalli Adam tace “ashe dai d’an nawa jarumi ne ban taba tunanin daga fita xaka dawomin da makudan kudi ba.”


Cikin isa da mulki ya kai lomar indomie yace “ai ki bari kawai, daga nuna musu hoton auranmu nida Zainab suka cake min kudina.”


Shiru tai tana tunani, karfa abin ya jawowa Zaimab matsala? Sai dai can tace koma menene ai ita taja data bamu gida ai duk da ba haka ba kome ya sameta muma ba hannunmu a ciki.


Kallan Adam tai zatai magana sukaji ana magana a tsakar gida, kallansa tai tace “wanene?”


Loma ya karayi sannan ya leko yace waye?


Kallansa mutumin yai Kamalu yace “shine.”


Adam ya kallesu cikin rashin fahimta, mutumin cikin jin dadi ya mikamai hannu yace “d’an jarida ne ni sunana Aliyu Giss ma’aikacin gidan tv na Farin gani.”


Adam ya kalleshi yace “sai akai me?”


Dan Jaridan yace “muna bukatar yin hira dakai ne in har ka amince zamu baka dubu talatin kudin yin hira dakai.”


Da sauri Adam yace “dubu talatin”


Goggo dake daki ta leko da sauri tace “dubu Talatin?”


Yce “eh.”


Kallan Goggo yai itama ta kalleshi.


Mikamai complimentary card dinsa yai yace “inkayi shawara kamin waya da number nan.”


Adam y amsa hannu na rawa, Aliyu Jiss ya juya ya fita, waya ya daga ya kira wata number yace “Hajiya mungode da taimako.”


Kashe wayar yai cikin jin dadi, dan dama sun dade suna bakin cikin aikin da Zainab take da d’aya gidan tv din wanda sun tabbatar saboda itane suke ta samun cigaba wanda a yanzu su har mantawa ma ake da su.





*******

Ayusher🏌🏻‍♀

[12/11, 9:25 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{42}


  Kamalu ya kalla da sauri bayan ya matso kusa dashi, yace "me ya faru zai ban wannan uban kudin sannan yai hira dani?"


Kamalu yace "Da alama tambayarka yake sanyi akan matarka."


Da sauri ya kalleshi yace "akanta?"

Goggo ta fito da sauri tace "akan Zainab zaiyi hira dashi? Meyake san ji?"


Kamalu da sauri yace "bansani ba nima."


Ganin yanda Goggo ke kallansa yasa yai saurin yin waje.

Kallan su Asabe ta da suka leko, ta kalli Adam tace "wuce ciki."


Shiga yai ya zauna yace "Goggo me kike tunani suke san ji?"


Kallansa tai tace "meke faruwa wai?”


Shiru yai cikin rashin sanin abinda ke faruwa shi kansa yace “bansani ba wlh nima Goggo amma dubu talatin haka kawai?”


Shiru tai tana nazari, kafin ta kwace complementary card din dake hannunsa tasa a lalitarta, da sauri yace “Goggo.”


Tace “ka bari inyi nazari.”


Dan baki ya tabe sannan ya jawo abincinsa ya cigaba daci, shiru Goggo tai tana tunani.


*******


Kashe wayarta Afreey tai sannan ta dawo cikin office ta xauna, producer ne ya shigo ya nemeta data zo ta shiga cikin shirin da za’ai a wannan lokacin.


Kallanta sukai dukansu dan tunda aka daukesu har yau ba wanda ya fara gabatar da wani shiri.


Zainab ce ta mike bayan ta gama nazarinta, office din Director Kabir ta nufa wanda tun shigowarta ya aiko yana kiranta.


Shiga tai bayan an bata izinin shiga sannan taja kujera ta zauna.


Kallanta yai itama ta kalleshi, dauke kai yai yace “kinyi sorting matsalarki?”


Tace “banida wata matsala da zanyi sorting.”


Kallanta yai fuskarsa ta bayyana bacin rai yace “Me kikeso mutane su daukemu? Kinsan kananan maganganun da ake akan ki?”


Kallansa tai ba tare da tace komai ba, ya cigaba “ance kunyi fada hartakai ga saki,  sai dai dayake kece kike rike da auran korarsa kikai ya bar miki gidan, a cewar wasu ma kece kika gaji  da auran kika sakeshi.” Cikin d’an daga sauti yace “me kike so mutane su daukemu a matsayinki na idan gidan tv din nan?”


Itama yanzu fuskarta dauke take karara da bacin rai tace “dan ina aiki anan sai akace ban isa na samu matsala a rayuwarta ba? Meye hadin harkar aiki da rabuwar aure na? Mun rabu ya tafi inda zai zauna sai hakan ya jawo matsala?”


Ransa a bace yace “kinsan ba haka nake nufi ba kema ai.”


Tace “am sorry amma ban fahimci menene hadin aikina da rayuwata ba.”


Takardun hannunta ta turamai gabansa tace “ga wad’an nan ka duba kasa hannu, zanzo na amsa gobe.”


Tana kaiwa nan ta mike ta fita, cikin kuluwa yabi bayanta da ido, ai yanzu tunda dai ta bashi ideas kala kala na yadda zasu cimma manufarsu na kusan shekara hudu zuwa biyar tabbas wannan karan ko da bala’i sai ya koreta, sam ya gaji da yanda kowa yake mai kallan a karkashinta yake kowa kallan wanda baisan komai ba yake, ko meeting suka shiga kowa abinda Zainab tace kawai yake bi ba wanda ya damu da nashi ra’ayin.


Zainab na shiga office dinta ta runtse idanunta tare da kwantar da kanta akan desk dinta, wayarta ta dauka tama Khalid text.

“Ka samu inda yake?”


Ganin ba reply yasa ta maida idanunta ta rufe ranta na kara baci, jin alamar shigowar sako wayarta ne yasa ta bude ido da sauri ta dauka Khalid ne ya mata reply.


“_Ha Ha Ha! Ya kike ji? Gashi kema rayuwa tana neman yin juyi dake?_”


Kallan number tai batama santa ba sai dai murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace “it seems I have alot of enemies” Maida idanunta tai ta rufe cikin kunar zuci.


Khalid kam yana can suna ta aikin editing sam bai kula da wayarsa ba sai wajen lunch da suka gama ne ya fito, yana daukan wayarsa yaga sakonta, har zai mata reply kawai sai ya danna call tare da d’an fitowa daga dan corridor.


Jin bata d’auka bane yasa ya kashe sannan ya koma ciki.


Afreey dake tsaye ne ta bishi da kallo har ya koma, haka kawai jikinta ya bata Zainab yake kira.


Ranta a matukar bace ta fito daga Station din ta shiga motarta.


Waya ta d’auka ta kira Giss, yana d’auka tace “ya kiraka?”

Yace “tun dazu nake jiran kiranshi harynzu bai kira ba.”


“turon Address dinsa.” Haka kawai tace ta kashe wayarta.


A kofar gidansu Adam ta tsaya, kallan unguwar ta shiga yi tare da tabe baki, cikin sa’a sai ga Adam ya fito yana sosa cikin sumarsa, kallo daya tamai ta gane dan ta kara ganinshi sanda yaje gun Zainab.


Horn din motar ta danna sannan ta sauke glass din inda take zaune.


Kallan motar yai cikin santi yake kara kallan motar,yarinyar dake zaune a ciki ya kalla, tasha ado sosai kamar yanda ta saba, sam bai ganeta ba harya karaso, ya cire hannunsa daga kansa tare da dan dafa motar yana kallanta yace “wa kike nema?”


Murmushi ta sakar masa sannan tace “wali walawa baka ganeni bane?”


Kallanta yai cikin mamaki kafin yace “Afreey?”


Murmushi ta sakeyi yanzu kam har hakoranta ne suka bayyana tace “shigo.”


Cikin jin dadi ya bude motar ya shiga ya zauna sannan ya kalleta yace “ikon Allah, Afreey dana ki........”


Jan motar datai ne yasa ya kalleta yace “ina zamu?”


Batace komai ba har sai data bar lungun ta hau kan titi sannan ta ganganra gefen titi tai parking.


Kallansa tai tana murmushi tace “me kake a wannan unguwar?”


Dariya yai yace “me nake kuwa inba zama ba?”


Baki ta tabe tace “Shekaru dayawa.”


Juyowa yai ya kalleta gaba daya yce “Afreey yaushe rabo? Ban taba tunanin zan kara ganinki ba.”


Bai jira tace komai ba yace “Khalid fa? Kin sake ganinshi.”


Kallansa tai tace “me kake tunani?”


Dariya ya saka sosai yace “ai yasin kin ganshi, wai haryanzu dai? Na d’auka ai an wuce gun.”


Murmushi tai tace “wuce gun? Tadan sauke ajiyar zuciya tace “Ahhhh bansan ya zanyi na wuce gun nan ba.”


Dariya ya sakeyi yace “ya akai kika san inda naka?”


Juyowa tai ta zubamai ido, da sauri yace “yahkuri bansan wannan kallan kinsani.”


Murmushi ta sake sannan tace “ina matarka?”


Matata? Kinsan Zainab ne?


Kai ta daga mai alamar eh sannan tace “kun rabu ne gaba daya?”


Shiru yai yana kallanta, tace “taimakonka zanyi”


Taimako?taya?


Tace “ Taimakonka zan ta dawo gareka.”


Zabura yai da sauri yace “taya?”


Kun rabu gaba daya? Uku kai?


Da sauri yace “a’a”

Tace “then?”

Shiru yai yana tuna uku yai, amma ya zaiyi? Shidai wlh auransa yake so.”


Kallanta yai yace “biyu ne, amma taya zaki taimaken.”


Shiru tai tana kallansa tace “Zainab tasan Khalid ne?”


Dariya yasa  nan ya sanar mata ai shi yai recommending dinsa ta daukeshi driver, yana dariya yace “na dade rabona da Khalid ko sanda naje gidansu gun Zainab ban sameshi ba.”


Idanunta zaro tace “bangane ba? Gidansu?”


Dariya yai yace “to uwar kishi taimakonta yai a ranar, Zainab na sona haryanzu ni nasani, bazasu taba jituea da Khalid ba kinsan halayensa ita kuma bazata dauka ba.”


  A ranta tace love bai maida ta ba dai.

A fili tace “ meya rabaku?”


Kallanta yai sannan yace “bazan iya fad’a ba.”


Tace “bai damen ba koma menene, sai dai in har kana san ka dawo da ita sai dai ka d’aura mata laifi ka samu abu kace ita tai maka wannan ne zaisa a fara tausayinka ita kuma mutane zasu fara zagin halayenta, balle dama can mutane dayawa basan halayenta suke ba, kaga hakan zaisa tai tunanin koma maka, dan ta kare aikinta.”


Shiru yai yana nazari kafin yace “ni ba abinda tamin, me zai sa ince tamin?”


“Bakasan ta dawo ma kenan?”


Da sauri yace “ina so mana, sai dai Zainab ina ganin ko za’a kasheta bazata......” shiru yai bai karasa ba.


Kallansa tai tace “To mai zai hana ka fito cikin hira ka zubar da hawaye kana neman ta yafema ku maida auranku? Wannan zaisa mutane tausaya ma kaga za’a fara zaginta in akaga taki maida auranta, wasu zasu fara aibata zaman da take ita kadai wannan zai sa ta dawo ma, na tabbatar yanda takesan aikinta bazataso wani abu yasa ta rasa komai ba.”


Shiru yai yana kallanta yace “Taya zan so a zagi Zainab?”


Fuska ta hade tace “tunda bakasan a zageka sai ka hakura da ita.”


Da sauri yace “wannan ne bazan iya ba”


Enveloped ta mikamai ya amsa tare da budewa, check ne na dubu d’ari, idanu ya zaro cikin tsananin mamaki ya kalleta yace “na meye?”


Tace “Taimakon ka nai sai kaima kai kokarin taimakon kanka, nima duk sanda na nemi taimakonka akan Khalid you have to help me.”


Shiru yai kafin yace “shikenan an gama, nagode sosai Afreey nagode nagode.


Yanda yake mata godiya ne yasa tai shiru tana kalansa, dubu daya ta mika mai tace “ka hau mota.”

Amsa yai ya fito taja motarta ta tafi, baki ya sake yana kallan motar har ta kule.


Wani alheri ne yake faruwa dashi haka? Da alama Allah ne ya dubesu.


Wani irin tsallen dadi yai, ai da kafa ya taka a hanya ya tsaya gun mai balango ya siyo na d’ari biyar ya siyo lemo ya taho gida cikin nishad’in da kai kace talauci aka yanke mai.


Goggo kam mamaki ne ya hanata ma cin balangon sosai, sai kara kallan check din take zuciyarta na kara sanyi, kallan Adam tai tace “shawara ta biyun tafi kaga ai ba mutuncinta kaci bako?”


Da sauri yace “haka na gani, ai gaba daya na rasa farin cikin da nake ciki.”


Dariya suka sa cikin jin dadi, Goggo kam wani irin nishadi takeji, kallansa tai da sauri tare da tsuke fuska tace “ba uku kacemin kayi ba?”


Yace “haka na dauka amma yanzu dana nutsu na tuna biyu nai ranar ma dan bana hayyacina ne.”


Cikin jin dadi tace “haba? Shine baka fad’a min ba? Bari nai maza na fara had’a kayanmu yanda daga an kammala komai mu koma, yan bakin ciki naga yanda zasuyi.”


A tare suka sa dariya, Adam a ransa yace “in na dage biyu nai ai dole ta koma tunda ba aurene da ita na, ko takardar ta dauka sai nace ba ni na rubuta ba.”


Kallan Goggo yai shima yasa dariya cikin jin dadin abinda ya samesu.


Tana kwance akan doguwar kujera har lokacin tashinta yai batama sani ba dan baccin dabatai ba daren jiya shi ne ya dauketa, da yake yau batada amfani ba wanda ya bi ta kanta sai gulmarta kawai da ake.


Khalid kam ganin ya kira sau uku bata dauka ba kawai ya share, lokacin tashinsa nayi ya duba yaga duk yan aikin rana ma sun tafi, mikewa yai ya dau jakarsa yana kokarin fitowa.


Juyawa yao ya kalli office dinta, ganin wutar ta a kunne ne yasa ya nufi office din.


Knocking yai, kamar a mafarki taji knocking, a hankali ta bude idanunta, cikin hanzari ta mike hankali a tashe.


Kallan agoggo tai sannan ta bada izini.

Khalid ne ya bude kofar ya shiga, kallansa tai da sauri ta kauda kanta gefe tana tunanin da alama fuskarta duk tayi abin bacci.


Khalid ne ya kalleta yace “bakyajin dadi ne?”


Bata kalleshi ba tace “I don’t know what’s wrong with me.”


Yana tsaye a gun yace “maganar gidan, nama wanda yai posting din a instagram ya turomin address din.”


Juyowa tai da sauri tace “can you send it to me?”


Wayarsa ya dauko ya tura mata sannan yace “zan wuce.”


Harya juya tace “Ammmm....”


Tsayawa yai sannan a hankali ya juyo ya kalleta, kallansa tai itama sannan tace “Can you help me?”


Yanayin yanda ya canza kallan da yake mata ne yasa ta juya kai, tace “i just feel like Director Kabir akwai abinda zai shirya akai na, i made a mistake dana bashi duka plans din danai, wannan karan they will try to use this against me.”


“But how can they do that? Bayan ba laifinki bane?”


Mikewa tai tare da d’aukan jakarta kusa dashi ta nufo, tace “Dole na nemo abinda zan kwaci kaina dashi, dukansu na saman nan basona suke ba.”


Kallanta yai yace “Do you have to do that?”


Tace “ko na rufe bakin Adam tunda suka san maganar sai sun dinga tuno abubuwa, i know they don’t like me amma banyi zatan wannan abin zai sa suyi tunanin janshi haka ba.”


Kallanta kawai yake baice komai ba, kallansa tai tace “wannan kallan fa? Yanzun ma cewa zakai lefinane?”


“Maybe.”


Takaici ne ya kamata ta bude kofar ta fita, ga mamakinta ganintai ya fito shima kafin ta rufe office din taga yana neman tafiya.


Rufe Office din tai sannan ta taho, yana sauka daga kan steps din dazai sada ka da kasa, jitai yace “Do you ever think about that?”


Itama bata kalleshi ba tace “what?”


Yace “dalilin dayasa dul wanda ke tare dake bai xaune dake zuciya d’aya.”


Kasa daga kafarta tai balle ta sauka, shiru tai batace komai ba wanda hakan ya sashi ya juya ya kalleta.


Ganin yanayinta ne yasa yace “Don’t mind me.” A ransa yace Khalid meke damunka dasan fadan abinda bai dameka ba?


Daurewa tai ta kalleshi tace “can you drop me?”


Baisan sanda yadan murmusa ba yace “a matsayin wa?”

Tace “d’an Umma.”


Murmushi yai yace “then you have to change your tune, in za’a miki abu you have you have to differentiate between favour and order.”


Ita kanta samun kanta tai da murmushi tace “meyasa kake san kamin gyara akan duk abinda nai.”


Kallanta yai a tare sukace “I don’t know.”


Murmushi ya sake ya kalleta tace “i know haka zaka ce.”


Bai ce komai ba ya karasa sauka, itama sauka tai.


Afreey dake zaune cikin mota ta dunkule hannunta tana wani irin hucci na tsananin kishi.


Shiga tai ta zauna a gaba kanta dan kanta ciwo yake da alama baccin datai mai nauyi ne yasata, Khalid yazo shiga yaga Afreey a motarta tana hucci, ido ya zuba mata yana kokarin yin nazari akan ta, Zainab jin shiru yasa ta bude idanunta, ganinsa tai ya zuba ido yana kallan abu, juyawa tai ta kalli inda yake kallo.


Afreey ta hango, kallansa tai sannan ta kalleta.


Fitowa tai daga inda take ta nufi inda yake, bani key din.


Kallanta yai, gani tai ya mika mata ba musu, wani takaici ne ya kamata kawai ta shiga motarta rai a bace taja.


Khalid ne ya nufi inda Afreey take ya bude inda take zaune yace “Safiyya!”


Kallansa tai bakimta na rawa saboda tsananin kishi.


Yace “will you stop that?”


Me?


******


Ayusher🏌🏻‍♀[12/12, 10:00 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


You have come a long way and have won many battles. Whenever you're faced with a difficult or challenging situation, you'll overcome it. Yes, you can.


{43}


Kallanta yai yace "Saboda ni kike aiki anan?"


Kallansa tai itama tace "korata zakai in saboda hakan ne?"


Shiru yai yana dan tuno kadan daga cikin abinda ya faru a Buk yace "Sai yaushe ne zaki nutsu ki kula da rayuwarki? Meyasa bakya tunanin rayuwarki ta nan gaba?"


Zuciyarta cikin kuna tace "Sai yaushe zaka dawo gareni?" Tai maganar idanunta na cicikowa suna neman kawo ruwa.


Wani takaici ne ya kamashi yace "abinda kikeso kenan?"


Hawayenta ta shiga kokarin maidawa tace "bazai yiwu ba?"


Yana kallanta yace "badai ni kike jira na fad'a da kaina ba?"


Wani takaici ne ya kara kamata dauke da wani zafin kishi tace "indai har ni bazan sameka ba to sai dai ka zauna haka, in har bazaka dawo gareniba ba wacce ta isa ta sameka."


Wani mugun kallo ya mata yace "Safiyya wai meke cikin kanki ne?"


Kallansa tai tana hucin kishi, yace "can you please stop? Banasan kisani yimiki kiyayyar da baxata taba gogewa ba."


Ranta a bace ta kauda kanta, kallanta yai sannan cikin takaici ya juya.


Harya isa gida hankalinsa gaba daya ya kasa kwanciya, ya tabbatar Afreey akwai abinda take amma daga gun wa? Taya zaiyi ya taimaki Zainab? Dan baisan me zai ce mata ba in ya ganta a wani hali.


Yana kwance shiru a cikin dakinsa, yana nazarin mafita, abincin daya shigo dashi daga cikin gida ya kalla, yunwar dake damunsa ce yasa ya zauna tare da sa hannu dan cin tuwon dawa miyar kubewa da Umma tai.


Loma d'aya yakai ya fito da idanunsa da sauri, mikewa yai ya saki murmushi yana cewa ya akai banyi wannan tunanin ba?


Da sauri ya tsame hannunsa sannan ya dauko wayarsa, number Zainab ya kira.


Tana kwance a falo, Nabila da Nusaiba nata hada kayan tafiya, laptop dinta ce a gabanta tana dadannawa da alama wani abu take dubawa a ciki.


Kallan wayarta tai dake kara sannan a fili tace "sai yanzu?"


Hararar wayar tai wanda ni kaina harna dauka bazata dauka ba sai kuma naga ta daga da alama ringing din karshe ne kafin kiran ya katse.


Daga can yace "Hello!"


Shiru tai batace komai ba wanda hakan yasa ya kalli wayarsa dan ya dauka ba'a daga ba, ganin alamar ta daga yasa yace "naga kamar bacci kike in kin tashi na kira."


Sauke wayar yai yana jira yaji tayi magana jin takiyi yasa ya kara cewa "hello!"


Murmushi tai sannan tace "na riga na saba da bakar maganarka sannan na gane kanafadan ta ne dan na maida murtani."


"Ummmmmm""


Hade fuska tai tace "ya akai?"


Mikewa tsaye yai yace "ya kike gani in kika amshi aikinki?"


Da sauri tace "you mean?"


Yace "eh, duk abinda suke shirin miki basu isa su miki ba in har kina program dinki, saboda ganin bakya nan zai sa mutane tambayar abinda ke faruwa, waccen karan ance kin yi tafiya ne wanna fa? Hakan zai sa a shiga nemanki, ba hujja garesu ba sannan basu da ikon shiga rayuwarki, tunda sun san hakan, sannan a cikin shirin ki bayyana mutuwar auranki da kanki,  kin riga kin tsoshe abinda zasuyi amfani dashi."


Cikin gamsuwa da abinda yace da jin dadi yasa tace "nima yanzu nake tunanin sauke website dinmu da duk wani program da na saka a youtube"


Shima cikin gamsuwa yace "hakan yayi"


Dan gyara kwanciyar ta tai tace "hmmm"

"Nagode"ta fada a hankali.

Sarai ya jita hakan neya bayyanar da murmushi a fuskarsa.

Can yace "ya zakiyi da Adam?"


Tace "zan je gidan Gobe da rana."


Okay yace suka dan yi shiru, basu taba doguwar waya haka ba dan waya ma bayinta suke ba sai da dalili shiyasa duk suka samu yanayin wani banbarakwai.


Khalid ne yace "shikenan, sai da safe."


Tace "Allah ya tashemu." Tai saurin kashe wayar, shiru tai tana nazari, tabbas shawarar da Khalid ya bata sosai ta gamsu da ita.


Ai mikewa tai ta zauna ta fara harhada abubuwan da zata gabatar a gobe, waya tama daya daga cikin masu dauko rahoto tace "ya turo mata na gobe." Ba musu ya tura mata dan dama sau da dama takan tambaya shiyasa bai kawo komai ba.


Da safe ta shirya tana rufo kofar daki Nabila na fitowa daga nasu dakin hannunta dauke da robar ruwa.


Zainab ta kalleta tace "Hajiyar bacci ya akai kika farka?"


Nabila ta kalleta tace "Allah Aunty zan daina kwana kan gado da Nusaiba kullum da ciwon jiki nake tashi, ta dinga makamin kafa kenan."


Dariya Zainab tai tace "shikenan sai ki koma dakin Goggo."


Hade fuska Nabila tai tace "ni wlh sunansu ma bansan naji an kira." Ta kalli Zainab tace "Aunty haryau bazaki fadan abinda suka miki ba?"


Kusa da ita ta matso ta dafa kafadarta tace "zan wuce Mamman yace sai rana zaku wuce ko?"


Tace "Hmmm kikace zaki kaimu gun Asiya."


Kallanta tai sam ta manta tacewa Umma zata kawosu, gashi har hutu ya kare, ga Dady tasan yanzu zai fara fada akan zamanta ita kadai, next term kuna dawowa zan kaiku.


Hannun Zainab ta kamo, juyowa Zainab tai ta kalleta, a hankli ta sakar mata murmushi.


Nabila ta maida mata tace "jiya kin samu bacci?"


Hmmm ta fada tare da daga mata kai.

Nabila ta saki hannunta tace "karki manta kizo kafin mu tafi."


Kai ta daga sannan ta fita.


Mamman nata goge motoci biyun dake waje dan Dady ya sai mata mota a ciki ma suka dawo.

Kallan Mamman tai ta gaisheshi, da sauri ya karaso yana gaisheta, murmushi tai tace "zan wuce dakaina."


Yace "ki bari na ajiyeki"

"A'a inada inda xani ne daga can."


Ba musu ya mika mata key sannan ya tsaya ya bude mata motar ta shiga sannan ya rufe, jan motar tai ta fita.


******

Khalid ya gama shan tea da Tsame ya dau kajarsa xai fita sai ga Umma.


Kallansa tai tace "ungo wannan ka kaiwa Zainab."


Kallan flask din yai ya amsa tare da budewa, ganin tsame yasa ya rufe yace "Hajiya Umma."


Tace "Allah yasa zata iya ci, sannan kace karta kuskura ta sa komai a kular."


To Umma, jakarsa ya bude ya saka sannan ya shiga yama Abba sallama ya fita.


Zainab na shiga ta wuce fitting room ta shirya sosai, ba tare da ta ma wanda ya amshe da shirin nata magana ba.


Wucewa tai Direct dakin shirye shirye, kawai taja ta zauna.


Nazifi wanda shi yake gabatar da shirin a maimakonta yana shiga ya ganta a hakkimce, yanda yaga alamun fuskarta ne yasa yasan ba wasa, kusa da ita yaje ba musu ya mikamata takardun hannunsa tare da mata barka da cigaba.

sannan ya juya zai tafi.

Nazifi!

Juyowa yai ya kalleta, alama tamai daya zauna, kallanta yai yace "naam?"


Tace "let's do it together."


Da sauri ya kalli gun masu cameras sannan ya kalleta, alama tamai daya zauna.


Da sauri ya zauna tare da dan matse kafafunsa alamar rashin sakewa.


Khalid dake tsaye a gun camera yana ganin abinda ke faruwa, har suka fara gabatar da shirin, sannan ya juya.


Director Kabir dake ta faman hada kan manyan gun aikinsu dan suzo ayi meeting akan Zainab.


Ramlatu ta kirashi ta sanar dashi abimda ke faruwa, ba karamin tashin hankali ya shiga ba.


Cikin hanzari ya juyo tare da sanar dasu su iso suma.


Zuciyarsa fal take da takaici, tare da kara shan alwashin korar Zainab koda zai rasa komai nashi ne kuwa.


Yana isa tana kammala shirinta, daga karshe ne ta mikawa Nazifi takarda bayan an dan tafi nuna rahoto.

Kallanta yai da sauri, tasani sarai mamakin abinda ke jiki yakeyi hakan yasa ta daga mai kai alamar eh.


Ana dawowa daga rahotanni, Nazifi yace "ga shirin namu ya kawo karshe, akwai abinda ke yawan damuna."


Yadanyi dariya ya kalli Zainab yace "gaba daya yanzu zamanin na rasa meke faruwa a ciki, sai kaga mace da namiji anyi auran soyayya mai karfi amma wata uku sai kaji aure ya mutu, me kike tunani yana kawo wannan matsalar?"


Dariya Zainab tai tace "ai ku maza ku za'a tambaya, dan kune masu sakin kaga kune kuka san menene ya ke sa kuke yinsa."


Ta kalleshi tace "ni kaina watan ni hudu da suka gabata nawa auran ya mutu, kaga kuwa kai ne zaka amsa wannan tambayar."


Nazifi yace "Inalilahi bamuda labari, ba dai hutun da kika dauk......


Dariya tai tare da daga kai sannan tace "shi dan adam kowane da nashi kaddarar da Allah yake dauramai shi yasa a koda yaushe muke rokon Allah ya bamu ikon cin jarabawarmu."


Nazifi ya jinjina kai........ nan suka kara tattaunawa akan matsalar aure sannan sukai sallama.


Director Kabir ta kalla wanda ke tsaye a jikin kofa ransa a matukar bace.

itama kallansa tai sannan ta shiga yima Nazifi magana ba tare da ta tanka mai ba.


A zuciya  ya juya.


Yana shiga yaga envelop doguwa akan desk dinsa, budeta yai ransa duk ba dadi, dan ya gama sadaukarwa Zainab ta riga tayi winning ba abinda ya isa yayi.


Abinda ya gani a ciki ne yasa ya zauna akan kujera da sauri yana kara karantawa.


Zainab ta kalli Khalid wanda ke printing, sannan ta wuce.


Tana shiga office dinta ta saki murmushi tare da yin ajiyar zuciya, xama tai ta jawo flask dinta tana kurbar tea tare da duba abubuwan data sauke.


Wayar cikin office dince tai kara hakan yasa ta daga.


Director Zainab ki shigo akwai Emergency meeting nan after lunch .


Okay kawai tace ta ajiye wayar, nazari ta shigayi tana tunanin me za'a tattauna.


Mikewa tai ta dauko key din motarta, ta fito.


Mota ta shiga ta wuce gidan su Adam.


Goggo na zaune tana kallo, yau kamar nela sun san farin cikin da take ciki suka kawo mata wuta, gefe dankali da kwai da suka ci suka koshi ne harda ragewa a gefe, ga kofin shayi nan a gefenta tana kallo tana sha.


Adam ne ya kalleta yace "wai Goggo idanki baya zafi?"


Zafin me?

Kallo mana.


Tsaki tai tace "ni wannan tv din ma ai a dole nake kallo da ita, yo meza'ai da wannan yar fucikar tv din? In na tuno ta gidan Zainab sai maji raina ya baci, duk kai........"


Kallan ta yai sai ta wayance tace "yaushe zaka bank ka tattalo mana kudin?"


Dariya yasa yace "yanzu ma."


Lalitarta ta bude tace "kai inaji tare zamu tsoron baka kudi nake."


Shikenan sai ki shirya.


Zatai magana akai sallama, taran Asabe ne ta bude labule tace "A'a d'an nan ya akai? Ta fada tana dan toshe tv dinta da labule ta dauka abinda yazo kenan.


Yace "ana sallama da Adam ne."


Goggo ta kalli Adam tace "kaji!"


Wata dariya yasa yace "wato Allah yamin farin jini ta ko ina wlh."


Mikewa yai yana kade riga cikin isa da takama.


Yana fita ya ga motar Zainab, idanu ya zaro da sauri ya nufi motar.


Kallansa tai sannan ta budemai yai saurin bude kofar ya shiga cikin tsananin farin ciki mara misaltuwa.


Kallanta yai yace "Honey!"


Kallansa tai ta zubamai ido wanda harya sa ya sosa sumar kansa tace "Bani wayarka."


Da sauri ya mika mata, duk hotunan da sukai tare ta goge sannan ta mikamai.


Kallanta yai yace "me kikai?"


Tace "hotunan mu na goge."

Da sauri ya duba hotunan ko d'aya babu, kallanta yai yace "Honey!"


Da wa kake?


Shiru yai kafin yace " Honey dan Allah bazan yi maganar hoto ba amma dan Allah ki amince mu maida auran mu? Kinji?"


Kallansa kawai take tama rasa me zata cemai, yace "Honey na tuba ki yafemin, Allah nayi laifi amma wlh abinda kike tunani bai faru ba, dan Allah Honey ki........."


Wata irin dariya tasa wanda kana ji kasan ta bakin ciki ce dariya tai sosai dan ni kaina bantaba ganin Zainab na dariya haka ba, cikin dariyar tace "mu maida aure?"


Kai ya daga da sauri.


Kallansa tai sannan tace "yanzu nake nazari iya zaman danai dakai har yai baka taba nuna min jarabawarka ba, dauko takardunka ni da kaina zan samoma aiki."


Kallanta uai kabansa ya shiga faduwa yace "takardu?"


Tace "eh dakosu."


"Zan dauko amma Honey ki am........"


Shiru tai tana kallansa, can tace "Adam haka kake tun dama ko kuma yanzu ne na maidaka haka?"


Cikin rashin fahimta ya kalleta, zuciyarta na kuna tace "wad'an nan dabi'un naka sababbi da nake gani yasa na shiga tunani, dama can haka halayenka suke? Boyewa kai saboda ni ko kuma nice bayan aurena ka koma haka?"


Kallanta yai yanayinsa duk ya canza.


Idanunta ne suka ciciko tace "Wani irin rayuwa mukai nida kai har shekara 4? A kwanakin nan wannan amsar haryanzu na kasa samota."


Cikin sanyin murya yace "Honey!"


Tace "in har kanada imani da tunani ko cewa akai kamin abu zakamin? Bayan abinda ka aikata min? Har sai ka karamin da abinda zai sa na tsaneka har karshen rayuwa ta?"


Kallanta yai hawaye ne suka gangaro mai, itama hawaye ne suka zubo mata tace "na rokeka da Allah Adam ka kyaleni, jiya da kyar nai bacci ina tunanin tambayar da akamin wacce banida amsarta, an tambayen dalilin daya sa duk wanda nake tare dashi baya zaune dani zuciya daya, na dade ina tunanin wani irin shiga hakkinka nai a zaman mu da zaka sakamin da haka.”


Da sauri yace “ba abinda kikamin Honey, ni din ne bazan iya hakuri dake ba.”


Yanayin kallan da takemai ne ya canza tace “da alama kanka ba daya ba Adam, na rokeka da Allah ka barni nai rayuwata, ka barni naji da abinda ke damuna plz.”


Shiru yai baice komai ba, kallansa tai tace “zan wuce, inada meeting.”


Kallanta yai jiki a sanyeye ya fito taja motarta ta tafi.




Ganin time din ya kusa yasa ta kara gudun mota, tana isa ta shiga ciki, wucewa tai gun meeting din tana bude kofar taji gabanta yayi wani irin faduwa, da sauri ta shiga yin addu’a a ranta.


Khalid ne ya kalli Mai maganar, cikin gulma yace “sun shiga meeting da alama akan Director Zainab ne.”


Nazifi ne yace “wai matsalar ta meye? Rayuwartace fa menene dan auranta ya mutu? Ita take da kanta? Ko ita ke san ta kashe auran nata?”


Ramatu cikin fishi tace “ita mutanen data kora saboda rayuwarsu fa?”


Da sauri mutanen gun suka fara bin bayanta, Khalid wanda ke zaune ransa yafara baci matuka.


Afreey ce ta kalleshi cikin kuluwa.


Nazifi yace “dukansu abinda sukai ya shafi aikinsu san kai kawai kuke yi da muna bakin ciki.”




Nima nace haka ne🙄plz ku bat Zee tasha ruwa ya tsirga mata😒


******

Ayusher🏌🏻‍♀

[12/14, 9:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


Always Turn your wounds into wisdom.


*Congrats SURRYHAMS Barka da kammala littafi, Allah ya kara basira da zakin hannu, will miss Khal and Bahi our cute love birds😘*


{44}


Tana kokarin fita daga motarta wayarta tai kara, a hankali ta sa hannu ta dauketa, sunan Swt Sis ne ya bayyana a alan wayar tata, a hankali ta rufe idanunta cikin wani yanayi sannan ta dauka.


Nabila daga can tace "Aunty? Muna ta jiranki."


Cikin wani yanayi mai sanyi tace "Nabila kuyi hakuri bazan samu zuwa ba wlh."

Da sauri Nabila tace "wani abin ya faru ne?"


Tace "bakomai meeting zan shiga yanzu ne, in na fito zan kira Dady."

Jiki a sanyaye Nabila tace "shikenan mu zamu wuce, in kin fito mayi waya."


Kai ta daga kamar tana ganinta tace "shikenan, akwai jakata a daki na ajiye muku kudin skul ki daukar muku."


Mundoge, Aunty dan Allah ki kula da kanki.


Cikin jin dadi tace "to Nabila nagode."

Kashe wayar tai sannan ta zubawa Tv Station din ido tana kara tuno farkon zuwanta da yawan canjin da aka samu daga fara aikinta zuwa yanzu.


Bude kofar motar tai sannan ta fito.


Komawa yai ya xauna a karo na biyu kenan yana zuwa nemanta batanan, haka kawai jikinshi yake bashi ba daidai ba kallan Afreey yai wacce ke zaune tana dane dane a waya, Nazifi ne ya shigo yana cewa "Manya zasu shiga emergency meeting yanzu."


Kallansa Khalid yai, wani daga cikinsu yace "na meye meeting din?"


Nazifi yace "shi ke damuna."


Ramatu ce tace "akan Hajiyar gadara ne ka sani."


Kallanta Khalid yai, juyawa tai ta koma ta zauna cikin jin dadi.


Zainab ce ta tura kofar dakin taron sannan ta shiga.


Duk suna zaune wanda hakan yasa tasan sun gama tattauna abinda zasu ce mata kafin tazo.

Shiga tai ta gaishesu sannan taja kujerarta ta zauna.


Director Kabir ne ya kalleta sannan yace "Zainab munaso mu miki tambayoyi kuma muna fatan jin amsoshi gamsassu daga gareki."


Kallansa tai batace komai ba.

Takarda ya mika mata yace "wanene ya saka law din nan akan duk wanda ya bari harkar personal life dinsa ta shiga cikin aikinsa za'a dau mataki a kansa?"


"Nice" abinda tace kenan ba tare da tai karin bayyani ba.

Yace "yanzu abinda ke faruwa fa menene?"


Tace "banida hadi da abinda kefaruwa, banga dalilin da zaisa a dinga hada rayuwata da wanda banda alaka dashi ba."


Kallan juna sukai, Kabir yace "kenan kina san cemana wannan abin bai shafeki ba?"


Wai akan me za'a dinga jan abinda ba wani abu ba ya zama wani abu? Sau nawa wasu na samu matsalar zaman takewa? Akanta aka fara ko a kanta za'a kare?


Kallansa tai sosai tace "me Adam yai? Me nai? Dan wani ya dau hoton mu ya daura a instagram da facebook ni na daura? Sannan ba aure tsakanina dashi dan ya kama gabansa laifi na ne kenan?"


Murmushi yai yace "hakane, to wani hukunci kike tunanin zakima wanda ya fitarda tambayoyin jarabawarmu yaba wanda yake so yaci?"


Kallansa tai tace "hukuncinsa korar wata shida."

Yace "wanda kuma ya ke da alaka wace bata aure ba tsakanin sa da dan uwan aikinsa fa? Alaka wacce take dauke da ayar tambaya mai karfi fa?"


Kai tsaye tace "korar sa za'ai"


Cikin jinjina kai da gamsuwa ya kalleta batare da ya dauke idanunsa akanta ba yace "menene tsakaninku da saban ma'aikacin da kika dauka Khalid?"


Kallansa tai cikin rashin fahimta tace "wani Khalid din?"


Director Kabir yai wani murmushin jin dadi yana tuno takardar da aka ajiye kai akan kai amfani da Khalid in taki saduda, tabbas akwai abu tsakaninsu, yayi kata driver, a gidansu ma ta xauna da auranta ya mutu sannan yanxu kusan kullum tare suke tafiya."


Menene tsakaninku?


Tace "meye tsakanin mu kuwa?"


Kallansu yai yace "ba abu a tsakaninku ku kika zauna a gidansu?"


Kallansa tai da sauri.


Kallanta ya sakeyi cikin jin dadi yace "Binciken mu ya nuna karatun degree na Maths yai ba yanda za'ai ya rubuta amsoshi masu zafi akan karatun da bai da alaka dashi, in har ba bashi akai ba.

Abu na biyu yaran nan kin nuna baki da alaka dashi kuma mutane uku na tambaya sun nuna kin sanshi, sai a lokacin ma na tuna abinda kikamin akan nayi rejecting din takardarsa ta neman aiki."


Me tama akanshi?


Murmushi yai yace "nan tazo tacimin mutunci akan nacuceshi taya zan hanashi aiki bayan yaci? Har takardar ajiye aikinta ta rubutamun saboda shi."


Kallansa kawai take gaba daya ma tama rasa me ma zatace mai saboda gaba daya bata taba kawo jin abu makamancun haka bama, bata kawo abin nasu har yakai haka ba.


Kabir yace "mu kirashi mu tambayeshi alakarku da sanda kika turamai tambayoyin jarabawar? In har sharri muke miki?"


Kasa magana tai kawai sai kallanshi da take.


Can ya dauke kansa daga kanta yce "ance ma akanshi kika rabu da mijinki."


Idanunta na kansa ita kadai tasan abinda take ji a cikin ranta.

kallansa tai kafin ta saki wani murmushi, kallanta yai yace "in har ba abu tsakaninku kina san wanke laifinki yanzu a kirashi ki koreshi daga aiki da kanki, wannan zai nuna mana tabbas ba abu a tsakaninku."


Farcenta kawai take karzawa yanzu kam ta ma dauke ido daga kansa, kanta na jikin desk din dake gabanta.


Yanzu ne CEO din su yai gyaran murya sannan yace "Zainab ke muke sauraro."


Dagowa tai ta kalleshi idanunta sunyi jaaa, tunowa take da sanda Khalid ya samu aiki Umma ta kirata cikin doki tana fada mata, cikin xuciyarta tace "Ya Allah!"


Samun kanta tai dayin murmushi tace "Duk da nasan kuna san korata ban taba tunanin zaku kaskantar da kanku ku je wannan matakin ba, duk cikinku na san yanda kuke jin haushin ni kadai ce mace a cikinku, na san ynda kuke jin haushin komai ta hanuna akeyi."


Kallan Kabir tai tace "Weldone da kokari, nasan duk wannan abinda kake dan na baka plan din danai wata uku ina shiryawa ne, ba sai kunje wannan matakin ma lalata min mutunci na da shi kansa ba, i will live."


Kallanta sukai da sauri, ta hadiyi wani abu tace "sai dai."


Ta dago ta kallesu daya bayan daya tace "Inaso kusan wani abu, na muku alkawari a wannan indai har inada rai da lafiya a daidai wannan lokacin nan da shekara biyu sai kunyi zaman meeting na neman mafitar yanda zaku gyara matsalar dake faruwa a tv station din nan, na muku alkawari nan da shekara biyu in dai ina da rai inda zan koma aiki sai ya wuce wannan gidan naku daraja da daukaka, zan gani in hakkina da kuka ci zai barku, ko baku ceba banaji zan iya cigaba da aiki daku."


Mikewa tsaye tai tace "Zaman da mukai a wannan wuri yasa na fara tausayin kaina, mijin dana rabu dashi da mahaifina, na yanda na sadaukar da komai akanku na sadaukar da duk wani lokaci na ina faman ganin na daukaka wannan guri, abinci wannan sai nayi da gaske nake ci, sai na tashi tsakar dare na hau aiki duk saboda neman ci gaban mu, bansan sakkayar dazan samu ba kenan."


Director Kabir ne yace "ke mutane nawa kika kora ba tare da hakkinsu ya kamaki ba?"


Kallansa tai ranta a matukar bace tace "duk wadanda na kora fadamin wanda bai aikata babban laifi ba? Sannan cire gurbatatu danai ba shine yasa muka samu ci gaba ba?"


Yace "Kema ai babban laifin kikai."


Kai ta daga cikin takaici tace "hakane ashe babban laifi nai."


Sallama ta musu ta juya, gaba daya shiru sukai, har taje jikin kofa ta dawo tadau maker mai makon tai rubutu a whiteboard din dake meeting room din ta wuce jikin kofa ta rubuta musu resignation letter ta cila maker din ta fita.


Office dinta ta wuce gaba daya ji take kamar zata fadi saboda jirin da takeji.


Hannunta rawa yakeyi sam ta kasa bude kofar, makulin ma ta kasa sashi a jikin kofar.


Khalid daya taho dan ganin ko sun gama ne ya karaso, ganin abinda ke faruwa yasa ya karasa da sauri ya amshi key din.


Kallansa tai idanunta basa gani sosai, yana budewa ta shiga ciki, bayanta yabi da sauri shima yace "Are you okay?"


Juyowa tai ta kalleshi sannan ta kara rufe ido ta bude, murmushi ta kakaro tace "yeah, can you help me?"


Da me?


I need to pack.


Cikin rashin fahimta yace "pack?"


Kai ta daga tace "in an tashi please."


Shiru yai tare da zuba mata ido, tabbas akwai babban abinda ke faruwa da ita kuma tana neman kadaicewa, hakan yasa ya sauke jakarsa ya ciro flask din ya ajiye yace "inji Umma, in an tashi na dawo."


Juyawa yai har yaje kofa ya juyo ya kalleta, tana tsaye haryanzu.


Tana ji ya rufe kofa alamar ya fita ta zube a kasa, gaba daya jikinta ne ya shiga karkarwa, zuciyarta na wani irin kuna.


Wasu zafaffan hawaye ne suka zubo mata, kawai ta fashe da kuka.


Tayi koka har ta gaji.


******

Khalid kam sam ya kasa maida hankali akan aiki, tabbas akwai abinda ke faruwa, menene?


Ramatu ce ta shigo tana dariya, kallan Su tai tace "Hajiyar gadara dai an ajiye aiki."


Da sauri Khalid ya kalleta, yace "aiki?"


Yanda damuwarsa ta fito karara ne yasa Ramatu tace "eh yanzu, ahhh masamu hutu haba kullum cikin takura"


Idanunsa ne suka sauka akan Afreey wacce yaga tana murmushi ta kasa, Nazifi ne yace "ban gane ba? Waya isa ya sata ta ajiye aikinta?"


Ramatu tace "ina na sani?"


Shiru Khalid yai yana tunanin meke faruwa? Adam

Ne? Raziyya ce? Ba shiri ya hau bincike a facebook da instagram sai dai baiga wani sabon posting daya shafeta ba.


Har aka tashi zuciyarsa ta kasa nutsuwa.


******


Jiki a sanyaye Adam ya shigo gida, zama yai a falo akan yar katifarsu yai shiru ya baxa uban tagumi.


Goggo data fito daga bandaki ne ta kalleshi tace "kai kuma fa?"


Kallanta yai ya sauke wata ajiyar zuciya.


Zama tai tare da jawo mai tana shafawa tace "kai fa kayan haushinka yama yawa, meye hakan?"


Kallanta yai yace "Goggo yanzu Zainab ta tafi."


Da sauri tace "Zainab?"


Kai ya daga alamar eh yace " Goggo yaune karo na farko dana taba ji Zainab ta rokeni abu."


Kallanshi tai ta matso tace "komawa takesan yi?"


Kai ya girgiza yace "Rokana tai na kyaleta haka nan."

Hawaye ne ya zubomai ya kalli Goggo yace " Goggo ya zanyi."


Kallansa tai ta koma dabas ta zauna zuciyarta na kuna ta kasa magana itama.


Can tace “ka hakura kenan?” Ido ta kuramai tace “ko ukun kai da gaske?”


Dan kai ya kauda yace “ko ukun nai in na dage biyu nai ai ba yanda za’ai.”


Cikin takaici takai mai bugu, tace “kai dai wlh kaji asara, da alama ka fara hauka, ni anya ma kudin nan da aka baka a takarda na gaske ne?”


Kallanta yai yace “kema kina tunani haka ko?”


Tace “to akan me za’a baka uban kudi ba tare da kayi wani abu ba?”


Yace “nima abinda ke ban mamaki kenan, sannan Afreey fa dama can ba wai kyauta gareta ba.”


Afreey? Meye hakan suna kamar na aljanu?


Dariya yasa yace “ke ina kikasan sunan gayu?”

Tsaki tai tace duk kai kaja mana da kun haihu da Zainab ta isa ta koremu?


Haushine ya kamashi, tace ni tsinaniyar magen ma har yau banganta ba, ta ja mana bala’i tai gaba.


******


Kayanta kawai take ta hadawa, wayarta dake kara ta jawo ganin sunan Dady yasa ta dauka da sauri.


Dady bayan sun gaisa  yace "ashe basu dade da tahowa ba?"


Tace "eh wlh ni suka tsaya jira kuma na shiga meeting."


Yace "kinje gidan Auntyn naki?"


Tace "na kirata a waya tace zata samomin wace zata zauna, haryanzu batace komai ba."


Shiru yai sannan yace " komai dai lafiya ko?"


Hawaye ne suka zubo mata tace "Dady na ajiye aikina yanzu."


Da sauri y mike tsaye yace "meya faru?"


Share kwallar ta tai tace "wani gun zai nema nan gaba daya abin nasu ya baci."


Shiru yai dan yasan tabbas da wani abu, can yace "ki dawo gida, dan dama hankalina ba'a kwance yake da barinki ke kadai ba, in har ba aure kikai ba bazan bari ki cigaba da zama ke kadai ba, in ba so kike a fara miki fassara akan zaman kanki kike ba."


Aure?


Yace "eh shi kadai ne zai sa na barki ki cigaba da zama a kano, tunda har kika ajiye aikinki to ki shirya wani satin zanzo daukanki."


Dady amma......


Kashe wayar sa yai cikin mamaki tabi wayar da kalli, dady ne kuwa? Taya Dadynta zai mata fada haka? Ko ta bakinta bai nemi ji ba?


Aure? Tafiya? Ta ya zata koma bayan yanzu ne take da dalilin zama a kano?


Dady kam yana kashe wayar yai shiru, shikansa mamaki yake yanda yai maganar sai dai yasan dole ne yai haka in ba haka ba baxata taba yadda ta dawo ba shi kuma gaskiya bayasan barinta sam a can ita kadai.


Khalid ne yai knocking a hankali ya shigo.


Kallanta yai, itama kallansa tai.


Shiru yai baisan me zaice mata ba, itama shiru tai dan kanta a cike yake da tunani.


Duk ta hada kayan hakan yasa ta mike tadau box daya matsowa yai ya amsa daga hannunta ya kara dayan akai.


Kallanta yai yace “kofar.”


Karasowa tai ta bude mai kofar, ya fita.


Jakarta ta dauko da flask din Umma.

Kallan staffs din tai duk sun fito kasa suna jiranta.


Wasu harda hawaye wasu kuwa tasan na karya ne, kallan Tv Station din tai tace “in Allah ya yarda nan da shekara biyu sai kun nemi yafiyar abinda kuka min.”



Haka ta shiga musu sallama kafin ta wuce jikin motarta.


*******

Ayusher🏌🏻‍♀

[12/15, 10:11 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


Wannan Page din naku ne Daughter Husaina, Mom Sayyed, Ayshety, Nabeelah Zaggah da Mrs Fahim🤝


{45}


Afreey da tun fitowarsu ta kafe Khalid da ido ganin yanda ya riko boxes din ne yasa ranta ya kara matukar baci, wani irin abu mai daci ne yake taso mata.


Kallanta yai yace "bude booth din."


Ba musu ta bude ya sakasu a ciki ya rufe sannan ya kalleta.

Ganin yanda take kallan tv station din ne yasa yace "muje na ajiyeki."


Kai ta daga sannan ta zagaya zata shiga ciki, Afrrey ce tace "Khalid!"


Yana kokarin bude motar ne yaji kiran, bai juya ba sai dai ya tsaya.


Karasowa tai da sauri tace "ina zaka?"

Ta fada tana kallan Zainab, wani kallo ya watsa mata yace "ke anan zaki kwana?"


Ranta ne ya baci sai dai batasan Zainab ta gane hakan yasa tai murmushi tace "Kai dai Allah Khalid baka rabo da joke, ka sabamin har yasa ma banajin haushi."


Wani kallo ya mata, gani yai idanunta nakan Zainab wacce itama take kallanta, budewa yai ya shiga tare da rufo kofar.


Zainab ta kalla kawai Zainab sai gani tai ta sakar mata wani murmushi, sannan ta bita da harara.


Khalid ne ya sauke glass din inda take hakan yasa bude kawai ta shiga sai dai tana mamakin meke faruwa da yarinyar?


Tana shiga yaja motar suka bar gun, Nazifi ne yace "sun san junane?"


Ramatu tace "ina na sani amma daga yanayinsu ina ga sunsan juna."


Tafiya sukai gaba daya zuciyarsa a dagule take, kasa daurewa yai hakan yasa ya kalli inda take zaune, tana xaune ta rufe idanunta tana tunanin kalaman Dady, daga yanda ya mata magana tasan dole ta shirya, taya zata tafi bayan an gama cucutarta? Shiru tai tana tuno kalaman Director Kabir, bata taba tunanin dan suna san su koreta zasu nemi unnecessary excuse su kawo mata ba, tanaji sun kawo zancen Khalid tasan ta gama zama dasu, sun nuna mata kankantarsu a fili.


Muryar Khalid taji yace "Meya faru? I thought komai yayi working out."


Murmushi tai ba tare da bude idanta ba tace "Na gaji da aiki dasu ne, da alama program din karshe nai bansani ba."


Kallanta yai bude idanunta tai a hankali hakan yasa idanunsu suka hadu, kauda kai yai zuwa kan titi can yace "Ba irinku bane suke cewa sun gaji da aiki, dan a yanda na sanki aikinki shine rayuwarki."


Idanunta na kansa tace "Hakan shine yasani cikin wannan halin, meyasa na dauki aikina komai na rayuwata?"


Dan kallanta yai zaiyi magana yaga wani tsoho na neman tsallaka titi hakan yasa yai tsaya, kallan titi tai ganin da kyar tsohon ke tafiya gashi da alama tsoron mota yake dan in yai gaba sai ya dawo.

Hakan yasa Khalid dan yin parking a gefen titi sannan ya fito da sauri yaje kusa dashi, sai daya gaisheshi sannan ya taimakamai ya tsallaka, tana zaune tana kallansu har ya kaishi ya juyo.


Sam batasan murmushin dake dauke a fuskarta ba, ta rasa meyasa in tana tare da Khalid take san zama mutuniyar kirki wanda ita kanta tasan tanada gibi dayawa na hallayarta.


Yana shigowa ya kalleta yace "am sry na barki."


Kallan baban tai wanda ke ta tafiya tace "ina 'ya'yansa suke suka barshi yake yawo haka shi kadai?"


Bai bada wannan amsar ba dan ba shine a gabanshi ba yace "me ya faru har kika ajiye aikinki?"


Juyowa tai ta kalleshi tace "na fadama ai."


Ido ya kura mata hakan yasa ta maida kanta tana kallan waje, shiru yai yana kallanta.

Ganin bashi da niyyar tafiya tace "ni yunwa nake ji banci komai ba, ga Umma ta aikon da tsame."


Kallanta ya sakeyi cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa "tausayin halin da nake ciki kake ko kuma damuwa da halin da nake ciki kake?"


Juyowa yai gaba daya yana kallanta yace "does it matter?"

Kai ta daga mai tace "eh fadamin."


Kallanta yai yace "Adam ne? Ko Raziyya ce? Taya zaki bari suyi amfani da abinda bake kike da iko akai ba? Sannan duk abin nan meye nasu a ciki?"


Bai jira tace komai ba yace "I have never seen a strong woman like you, akan me kike neman bari a taka ki?"


Murmushi tai tace "Da alama ka samu a ma fada gaba da gaba dadi ne dashi."


Yace "ZAINAB!"


Yauce rana ta farko daya taba kiran sunanta hakan yasa ta kalleshi, yace "meke faruwa?"


Saurin juyawa tai saboda samun kanta datai da nauyin kallansa, idanunta ta rufe tace "bai shafi Adam ba baishafi Yarinyar ba, in fact bai shafi kowa ba, nice kawai na fahimci zama tsakanina dasu ya kare."


Shiru yai sai dai ganin yanayinta yasa yaja sukai gaba, a cikin harabar gidan yai parking, juyowa tai ta kalleshi tace "Nagode."


Ganin baice komai ba yasa tace "bansan ko zamu kara haduwa ba, dan Dady yace xan koma can, please kama Umma godiya, zan kirata a waya."


Baisan meya sameshi ba sai dai gaba daya jin kalamanta yasa jiginsa yin sanyi, ko kalma daya ya kasa furtawa saboda yanda gaba daya yaji.


Murmushi tai tace "zan ba Bala flask din sanda ka samu time ka biyo ka tafi dashi."


Bude motar tai ta fito, cikin sanyin jiki ya fito, boxes din ta kalla ta dau na saman ta bude sannan ta rufe, ta dau na kasan ta mikamai.

Kallanta yai tace "Abubuwan danai ne, da ideas dina da karatun danai da sauransu, i hope zasu taimaka ma."


Amsa yai sannan yace "Thanks."


Dan gefe ta kalla saboda dauriyar tata na neman karewa tace "In fada ma wani abin dariya?"


Kallanta yai ba tare da ya amsa ba, tace " na dade ina tunanin mutanen dake sona na gefe na ta ko ina, hakan yasa akoda yushe nake abuna cikin confidence sai dai daga sanda matsala ta faru tsakanina da Adam na fahimci duk abinda nake tunani ba haka bane, Thanks alot for always been there, Kai maza kai aure kabama Umma jika." Ta karasa tana murmushi wanda suka taho da hawayen da batadan dasu ba.


Da sauri ta dau box din tai ciki, tsayawa yai a gun meke damunsa? Meyasa yake jin wannan yanayi?


Da kyar ya juya ya bar gidan rike da kwalin.


Zainab kam tana shiga tai sallah sannan ta kwanta akan kujera yunwa takeji amma sam ta kasa cin komai, sai wajen magrib ta daure ta shiga kitchen, flask ta bude taga har abinsu su Nabila sunyi kafin su tafi, murmushi tai sannan ta dauko plate ta fito.

Tsamen da Umma ta bata ta juye a plate din sannan ta dau ruwa ta wuce falo.


Samun kanta tai da kunna tv, abinda sai ta dade batai ba, documentary tasa kawai tana kallo tana ci, a fili tace "Abubuwa nawa ne banci ba abincin mu na gargajiya?"


Tana shan ruwa wayarta tai kara, dauka tai a hankali tace "Dady!"


Yace "kin fara hada kayanki?"


Tace "Dady....."


Yace "zanzo gobe da sassafe mu juyo tare, yanzu  ma ji nake kamar nawa Auntynki waya nace ta tura miki wani ku kwana, to dan itama bata dauka waya nane."


Zainab zatai magana taji yana tari, da sauri tace "Dady baka da lafiya ne?"


Cikin tari yace "ki hada kayanki." Ya kashe wayar yana tari.


Basma ce ta mikamai ruwa da sauri amsa yai yasha sannan yace "kiramin Nabila."


Juyawa tai ta fita.


********


Nabila na shigowa ta zauna a gefensa, kallanta yai yace “Yayarki akwai abinda ke damunta ne?”


Kallansa tai sannan tace “Bansan meke faruwa ba amma tun tana nan gidan bata bacci yanda ya kamata, sannan a falo take kwana, sau da dama ko hira muke da Nusaiba bata ma sanin me muke cewa tana tunani.”


Kai ya jinjina sannan yace “shikenan, ki gyara dakinta gobe zata dawo.”


Fuskarta dauke da mamaki tace “gobe?”


Yace “eh.”


Shiru tai yace “jeki.”


Mikewa tai fuskarta dauke da mamaki.


*******


Da sassafe kuwa Dady ya iso Kano haka suka sa Zainab suka kama hanyar Abuja.


Khalid kuwa da kyar yai bacci daren jiya haka kawai ya samu kanshi da juyi shikansa baisan sanda baccin ma ya daukeshi ba.


Da safe ya shirya ya taho kano.


Yasa hannu zai bude kofar ya hango Afreey tayi kofar baya, da sauri yabi bayanta, dan sam baiyadda da ita ba.


Ji yai tace “Giss ya akai?”


Baisan me aka ce ba sai jiyai tace “share Adam din, na samo wata hanyar har na gama abinda nake sanyi.”


Okay shikenan.

Ta kashe wayar, ta juyo zata taho kawai taga Khalid a jingine da bango ya harde hannayensa.


Wayarta ce ta fadi saboda tsabar tsorata da tai, da sauri taja kafafunta baya cikin tsananin tashin hankali.


Wayar data yar ya dauka sannan ya fara takowa zuwa inda take, baya tai tayi har ta isa jikin bango, idanunta a waje tace “Khalid!”


Kallanta yai yace “fadamin me kikai?”


Kallansa tai tace “Khalid!”


Yace “Fadamin.” Yanda ya fadi kalmar ne yasa ta daure tace “koma menai ai kai kaja.”


Naji ni naja ko menene fadamin.


Kallansa tai tace “na tambaya meye tsakaninku ka nuna ba komai, nace ayi amfani dakai gun korarta kuma yayi.”


Hannunsa na hagu ya dunkule da karfi yace “amfani da...... ni?”


Kallansa tai tace “eh, sannan sai jiya naji ashe ta rubuta takardar resigning saboda ba’a daukeka aiki ba, hakan ne yasa aka kiraka daga baya.”


Gaba daya jijiyoyin wuyansa ne suka fito yana kallanta, idanunsa sun kada sosai sunyi jaa.


Yace “kenan kece kika bada gudumawar sallamarta?”


Tace “bansan zata ajiye aikinfa saboda kai ba.”


Idanunsa ya runtse sannan ya bude yace “ke a naki haukar saboda ni ta ajiye?”


To saboda meye?


Murmushi yai yace “saboda ta fahimci hauka da rashin tunanin wanda ya sanar da ai amfani dani, sannan ta fahimci tafi karfin zama da irin su ne.”


Yatsa ya nuna mata yace “kuma wlh........”

Zai sake magana ya tuna kalaman Zainab na cewar gobe zata tafi.


Hankali a tashe ya juya, tace “Khalid ina zaka? Kasan bazasu barka ba insukaga kazo ka tafi.......”


Ai baima san me take cewa ba ya fita waje da gudu.


A titi ya tsaya zuciyarsa na kara cika da takaici tana kara tuno tambayoyin daya mata ashe tambayar tasa ce?


Ganin ba adaidaita kawai yasa ya fara gudu, zufa ne ta shiga ketomai ta ko ina saboda gudun da yake ga hakki saboda yayi gudun dayawa.




Raziyya akan fansar Adam ta shiga rayuwarta ta lalata mata rayuwar auranta, ta wargaza mata farincikinta.


Shikuma yanzu akan mahaukaciyar soyayyar Afreey gashi an kara shiga rayuwarta aikin da take rike dashi wanda da alama shine yasa ta iya juri abinda Adam ya aikata mata harta iya dawowa daidai yanzu shima an wargaza mata.


Tsayawa yai saboda hakin da yakeyi.


Sa’a yai wata adaidaita tazo wucewa ya shige.


Sam gani yai bata gudu suna isa ya sauka tare da sallamarsa.


Bala dake zaune yana cin awara ya kalla yace “Bala!”


Da sauri Baka ya mike yace “Khalid? Kazo amsar flask din ne?”


Kallansa yai yace “tana ciki?”


Hajiya? Ai ta tafi awa daya da suka wuce.


Hannu yasa ya shafi kansa cikin kunar zuci.


**********


A can kuwa su Goggo ansha Aramfa da takalmi kwaskwas shi kansa Adam yasha shadda da hula kai kace wani biki zasu wai duk kwalliyar nan ta zuwa bank ne amso kudi.


Goggo cikin jin dadi tace “mikon jakar tawa.”


Nan ya mika mata yana dariya yace “me zamu fara siyowa?”


Kai dai muje mayi lissafi a hanya.


******

Ayusher🏌🏻‍♀

[12/17, 9:06 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


_Your special page is here my dear fans, much love🥰🥰🥰_


{46}


Bala ne ya fito mai da ledar, amsa yai jiki a sanyaye ya juya yabar gidan.


Wayarsa dake kara tun dazu ya zaro 20 missed calls  ya gani, guda takwas daga Afreey ne ragowar kuma Nazifi ne.

Number Nazifi ya kira, ringing daya ya dauka cikin rada yace "Khalid kana ina?"


Bai jira yace wani abuba yace "kai maza kazo.”


Kashe wayar yai sannan ya shiga adaidaita ya karasa.

Yana shiga yaga ba kowa program room ya nufa anan yagansu a tsaye sun nutsu ana wani program.


Kallan inda ake program din yai, su uku ne agun ciki harda Afreey.


Muryar Nazifi yaji yace "Khalid biyoni."


Bayansa yabi suka shiga editing room, ransa a bace yace "ina kaje?"


Shiru Khalid yai kafin yace "Am sorry."


Nazifi yace "kasan fadan da akamin akanka? Ance bana kula daku? Wannan abinda kai ka jama kanka dan dama na sa sunanka akan masu dauko rahoto yaune amma abinda kai yasa na cirw sunanka nasa wani, dan haka wannan satin duk kayishi a editing room din nan."


Ya juya yai waje.


Juyowa yai ya kallesu sannan ya gaishesu.


Nan ya matsa ya zauna tare da amsar aikinsa.


Afreey kam gaba daya hankalinta nakan Khalid, ana gama shirin ta sauko da sauri ta nufi editing room inda Nazifi yace mata yana can.


Ko kallanta baiyi ba har ta gama wayancewarta na wai tazo ganin yanda ake ne.

Kuda da Khalid taje a hankali tace “Khalid please inasan muyi magana.”


Kallanta yai, sannan yace “kijira lunch time nima inasan magana dake.”


Wani sansanyan Murmushi ta saki tace “nagode Khalid.” Fita tai cikin wani irin yanayi wanda ita kadai tasan yanda take ji.


Ai kam ana tashi lunch ta kirashi a waya, ringing uku ya daga tace “Khalid!”



“Mu hadu a waje.” Abinda yace kenan ya kashe wayar.

Sai dai abinda yaban mamaki wai gani nai hakan yasata jin dadi.


Mikewa tai da sauri ta fita.


Tana tsaye ta zubawa kofar gate dinsu ido tana jiran ganin Khalid, sai murmushi take ita kadai.


Minti goma da tsayuwarta ta hangoshi, cikin wani yanayi ta zubamai ido tana ji kamar ta ruga a guje ta rungumeshi, da alama burinta na shekaru dayawa ya kuda cika.


Har ya iso idanunta na kansa, kallanta yai da sauri ta matso kusa dashi ta “Khalid!”


Cikin idanunta ya kalla yace “Tambaya nake san miki.”


Da sauri ta daga kai alamar tanaji, kallanta yai yace “Me kikeso game dani?”


Tace “Khalid kaima ka sani, auranka kawai nake san yi, ka xama nawa ni kadai.”


Murmushi yai yace “hakane, na tabbatar dama amsar kenan, to menene abu na farko da zai kaimu ga auran da kikeso?”


Idanunta ta zaro cikin wani yanayi, tace “Khalid?”


Kallanta yai yace “me? Kin kasa magana ?”


Shiru tai tana kallansa zuciyarsa na bugawa da karfi saboda tsananin san da take mai.


Kallanta yai yace “ya akai?”


Hawaye ne ya gangaro daga idanunta tace “Khalid bansan wani irin so nake maka ba, ji nake zan iya halaka duk wanda ya shiga tsakaninmu.”


Yace “ai ba sai kin fada ba naga hakan sau biyu kenan, kina hauka da sunan so.”


Kallansa tai tace “hauka?”


“Badai ke a naki haukar soyayya kike min ba?”


Yanayin fuskarta ne ya canza tace “me kake nufi ?”


Yace “inasan inga inkin aureni me zakiyi dani, na farko ko da da kankanin lokaci ban taba sanki ba, na biyu har a wannan lokacin ina mamakin yanda akai taimako ya koma haka, na taimaka miki wanda da alama shi ya maidake haka, na uku ina tunanin me zanyi wanda zan kuntata miki har abada kamar yanda kika kuntatamin da mutane akan wani shirme da kike neman kiranshi da sunan so.”


Gaba daya yanayinta ne ya canza idanunta suka kada sukai jaaa, bakinta na rawa tace “Me ne?”


Yace “me? Kinasan na cigaba?”


Bakinta na rawa tace “Khalid?”


Wani banzan murmushi yai yace “baki taba tunanin me yasa ban taba nuna bacin rai akan abinda kike ba? Ko kinfiso na fito na sanar dake haukar da kike ta isa haka nan? Sannan sai kiyi abu ki sanar dani, wato me zan iya?”


Hawaye ne suka shiga zubo mata idanunta na kansa, tama kasa magana, Khalid ya cigaba “ Badai zaki cigaba da kiran abinda kike a sunan so ba?”


Tace “Khalid kasan yanda nake sa........”


A kufule yace “so? Are you kidding me? Am i your toy? Taya ma zaki nemi bata min suna sannan kice kina so na? Abinda kike tunanin kin ma Zainab ba ita kika ma ba ni kikawa.”


Da wani ido kike san na cigaba da kallan mutane? Sannan kice so? A skul da kika ma Saudah sharri akan tai satar answer da wa kika hada? Cewa kikai ni na bata paper din data shiga dashi, dalilin hakan kinsan tashin hankalin dana shiga a wannan lokacin? Kinsan yanzu zuciya ta tashin hankalin da take ciki? Sannan ki kirashi da so?


Hawayenta ta share tace “amma kasan duk dan ka dawo gareni nai.”


In dawo gareki? Ko a mafarki bana fatan hada hanya dake karshe kenan


Bakinta na rawa tace “to in har bansameka ba kuwa duk duniya sai dai ka zauna kai kadai ba wanda ya isa ya sameka.”


Dariya yai yace “ohhhh is that what you hate the most? Yanzu kinsanar dani abinda ya kamata inyi, nagode da shawara sai na kawo miki IV.” Har ya fara taku biyu ya juyo yace “Ahhhh ko na baki IV din ba gayyatarki nake ba.”


Ya juya ransa a matukar bace.


Zubewa tai tsuguna a gun, bata ma duba yanayin kan hanyar da take ba balle ta duba mutanen dake wucewa.


Kuka kawai take tana tuno kalmar hauka da ya jefeta dashi, tunowa tai farkon haduwarsu randa ya taimaketa randa kuma ta fara sanshi.


Kasancewar ita yar masu shi ce yasa sam banda gadara ba abinda take a makaranta, duk saurayin daya zo mata da sunan so sai ta caba mai maganar da bazai taba mantawa ba, ko juice ne a hannunta sai ta watsa wa mutum, wannan dalili ne yasa yan islan skul din sukai meeting akanta akan zasu kamota su lalatata saga uban abinda take wa wulakanci, sannan dukansu su biyar sai sunyi amfani da ita.


Haka suka hada baki da friend dinta wacce ita kanta haushinta takeji suka sa ta jawota inda suka tsara haduwa can karshen inda ba mutane sai daji daji.


Afreey tunda suke tafiya takema Amrah kawarta magana akan ita haryanzu basu zo inda zasu ba.


Tana nema juyawa tani an cafko ta, a zabure ta kalleshi, gani tai duk mazan sun fito suna wata dariya, a tsorace ta fara kokarin kwace hannunta sai dai hannu yasa ya fizgeta can bayan wani gini da ake yinsa sukai da ita.


Bakinta suka toshe ba damar yin kara, sai ture ture take.

Khalid dake zaune a kangon yana karatu ne yaji suna dariyar mugunta tare da jin dadi.


Daya daga cikinsu ne ya wanka mata mari yace “ni kika zubawa juice a jikina ko? Yau sai na fanshe bakin cikin danasha.


Ya fada tara da jan rigarta daga sama sai data yage.


Kuka kawai take tana tuturesu, jin magana sukai ta bayansu, Khalid na kallansu yana waya “eh suna nan inda nake.”


Okay sir.


Kallan su yai tare da sa wayar a handsfree yace “Eh sir nasa.”

Muryar Discipline master dinsu sukaji yace “dan******kun zo office dina ko sai na kira iyayenku? Duk naji muryarku kar ku kuskura wlh nazo nan dan duk sai na koreku.”


Idanu suka zaro ai a tsorace suka fice daga gun.


Kallanta Khalid yai da sauri ya juya baya ganin rigarta a yage.


Yace “ki tsaya bari na samo abu ki rufe jikinki.”


Har zai fita tace “dan Allah karka tafi, tsoro nake.”


Bai juyo ba ya wuce ciki, sallayarsa ya dauko ya mika mata ta baya, amsa tai tace “nagode.”


Haka ta rufa sallayar suka fito tare, hawayenta kawai take sharewa.


Idanunta ta runtse tana hawaye tunowa da wannan lamari datai.


Yana san ce mata bai taba santa ba? Kome?



******


Bank din Goggo ta kalla cikin jin dadi tace “kaga sai mu samu mu bude wani abu kasuwanci ko tabir na shayi zaka bude?”


Shayi? Wa? Ni? Ya fada yana kallanta.


Tace “a’a mantawa nai nice zan zauna a gun.” Tai maganar cikin gatse.



Dariya yai yace “Goggo tawa, wlh kuma kyau zakiyi.”


Bakin ciki ne ma ya hanata tanka mai, suna shiga suka hau layi duk su biyun.


Har an kusa zuwa kansu Adam yaji an dafashi ta baya.


A tsorace ya juyo, idanunsa ne suka fito sosai yace “Sadiya?”


Razy ta karkatar dakai tace “Adam”


Goggo da sauri ta juyo jin yace “Sadiya.”


Idanu ta zaro a zuciye tasa hannu ta cakumo ta, Jamil ne ya matso da sauri yace “meye hakan?”


Goggo ranta a mugun bace tace “tsinaniyar wanda iyayenta suka tsine mata ai ban taba sa ran zan ganki ba yar banza wlh yau sai kinci ubanki.”


Staffs din bank din ne suka kallesh, Security ne ya matso da sauri yace “Baba meye hakan kike mana anan? In rigima zakuyi ki bari sai kun fita can.


Cashier ne ya kalli Goggo wacce aka zo kanta, Goggo hannunta na jikin Razy ta jata zuwa can.


Shikam Adam gaba daya ya saki baki yana kallan ikon Allah.


Goggo na mike cheque Raziya ta kalleta tace “Yanzu Goggo sai da kika sato cheque din nan?”


Da sauri Goggo ta kalleta tace “an sata din in naki ne.”


Kallan Razy yai yace “sata?”


Goggo ce ya kalleta tace “agun ubanki na sata?”


Adam ne ya matso yace “namu ne wlh, bamu akai.”


Fuskarsa dauke da Zargi cashier din yace “baku akai? Wa?”


Yace “Safiyya nata ne, kawatace a skul.”


Razy ce tai murmushi tace “ta ina kawa zata ba......”

Hankadata da Goggo tai ne yasata yin shiru, Security ne ya taso da sauri ya kallesu.


Cikin xargi yace “ku kira number.”


Nan Security yai gefe dasu, Goggo takaici kamar zatai ihu, Raziyy ta kallesu tace “ni dai na wuce, shaida na bada kuma na isar.”


Goggo a kufule tace “wannan ‘ya Allah ya kwashe miki albarka, kin kashe mai aure dan abin arzikin ma bazaki barmu mu dauka hankalinmu a kwance ba?”


Razy ta tabe baki a ranta tace na barku lafiya.


Adam ta kalla tace “bata dauka ba?”


Kai ya daga sannan ya sake kira.


Afreey dake tsugun ne ta gaji da kiran waya a zuciye ta dau wayar, Adam da sauri yace “Afreey ko zaki samu zuwa nan bank din Zenith? Na kan titi hotoro?

“Inzo inyi me?”


Yace “cheque din da kika bamu ne ake zargin sata mukai.”


Kashe wayarta tai dan haushi ma ta kashe wayar gaba daya.


Hello

Hello

Adam ya shiga fada, Security din ya kalleshi yace “ya?”


Adam yace ta kashe amma wlh ita ta bamu

Duk barayi abinda suke cewa kenen, ku fita ku baku guri.”


Da sauri Adam yace “to baku cheque din.”


Yace “a baku? Kun fita ko sai mun kira police? Ke kuma Baba ki dinga sanin inda ake kawo miki kudi dan gudun sata”


Haka ya korosu daga bank din.


Goggo ji take kamar ta kurma ihu, tana tafiys takalminta ya gurdeta ta kusa faduwa, rai a bace ta cilar da takalmin tai gaba.


Adam na binta a baya, duk taku daya tsinewa Kuliyar nan take.


*********


Dady ne a zaune a falo shi da Zainab, Basma ta ajiye tiren abinci sannan ta fita dan ta fahimci magana zasuyi.


Zainab ce ta kalleshi tace “Dady bakada lafiya ne?”


Kallanta yai yace “meke faruwa? Nasan haka kawai bazaki ajiye aikin nan ba.”


Shiru tai yace “Zainab.”


Nan ta sanar dashi kadan daga cikin abinda ya faru, ransa yayi matukar baci yace “tun zamanki iddah naso yanke wani hukunci amma sai na fasa, naso na bude miki naki gidan tv din na kanki, wannan ne kadai zai sa ki samu nutsuwa sannan shine zaisa ki rage yawan aikin da kikeyi, bazan hanaki aiki ba dan ni kaina ina alfahari da aikinki sai dai aikin yayi yawa.”


Zainab tace “nawa?”


Dady ya daga kai yace “haka nake fata sai dai....”

Yai shiru.

Tace “Dady”


Kallanta yai yace “baxan iya barinki ki fara aikin ba sai kinyi aure.”


Idanu ta zaro tace “aure kuma?”


Yace “sosai, duk inda kika ga mace to tana bukatar kulawar namiji, tun daga sanda aka haifeta Allah yaba mahaifinta hakkin kula da ita har sai tayi aure, bayan tayi aure Allah yaba mijinta hakkin kula da ita, sannan idan ta tsufa hakkin kula da ita ya koma kan d’anta, haka Allah yai mace a karkashin namiji wannan dalili ne yasa in har kinasan na bude miki to lalai ki kawon miji na aura miki, in kuma ba haka ba sai dai ki cigaba da zama a gida ko aiki bazaki kara nema ba.”


Kallansa tai da sauri tace “Dady!”


Yace “akwai d’an abokina wanda matarsa ta dasu, in har kina ganin ba matsala zan turoshi ku gaisa.”


Shiru tai tama rasa tunanin me zatai.


Dady yace “in har kinasan Tv Station tare da daukan fansan abinda aka miki to ki kawon miji, ni kuma na miki alkawarin baki gudun masa ta ko mai dan ganin kin cin ma nasararki.”


Yana kaiwa nan ya jawo abinci ya zuba.


Shiru tai gaba daya kanta ya kulle, miji? Ina ta ganshi? Gashi bataji zata iya sati a zaune ba aiki? Balle taita zama a haka????


********


Hannunsa rike da wayarsa sai juyata yakeyi, number Zainab ce akan alan wayar.


In na kira ince me?


Ajiyar zuciya yai tare da jan bargo.....


******

Ayusher🏌🏻‍♀[12/19, 7:58 PM] Maman Ihsan: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


Obsession is the single most wasteful human activity, because with an obsession you keep coming back and back and back to the same question and never get an answer.


{47}


Afreey na shiga gun aiki  a bakin kofar Kabir ta tsaya, daren jiya ta gama yanke shawarar abinda zatai da hukuncin da zata dauka.


A hankali tai knocking, Secretary dinsa ne ya bata izini bayan ta shigo ta kalleshi tace "gun Director nazo."


Kallanta yai sannan ya mike tare da sanar dashi.

Director Kabir dake zaune yana duba plans din da Zainab ta bari cikin jin dade yake ware wanda yake ganin za'a fara.

Afreey ce ta shiga bayan an mata izini, yna zaune yana duba takardun ya amsa sallamarta.


Harta zauna bai dago ba sai can ya dago ya kalleta yace "oh kece?"


Kai ta daga alamar eh sannan tace "Nice na ajiye ma takardar nan ma.”


Takarda? Ya kalleta kafin yanayinsa ya canza zuwa mamaki yace "kece?"


Kai ta daga tana murmushi tace "nasan in na fada sai ka fi fahimtata."


Fuskarsa haryanzu dauke da mamaki yace "amma ya akai kikasan haka? Sannan haryaushe kikazo da abu zai hadaki da Zainab?shiyasa ban kawoki a raina ba sam.”


Bata bashi wannan amsar ba tace "Zansa Abbina yadau nauyin shiri guda uku."


Baki ya bude cikin mamaki yace "uku?"


Kai ta daga alamar eh sannan tace "zansashi yai signing din 3yrs contract."


Cikin tsananin jin dadi yce "Safiyah! Da gaske?"


"In yau kake so ai signing din zan sanarmai kuyi a yau din nan."


Gaba daya wani irin zumudin jin dadi ne ya kama Kabir, tace "amma da sharadi."


Sharadi? Koma meye fada yanzun nan zan miki menene shi?


"Khalid!”

Tadan numfasa sannan tace “shi nake so ka kora."


Khalid? Waye.......Khalid? Ya sake tambaya.


Tace "eh"


Kallanta yai cikin mamaki yace "a wani hujjar zan koreshi kenan?”


Tace "in anyi amfani dashi an kori Zainab shima za'a iya amfani da ita a koreshi."


Kallanta yi yace "Am sorry sai dai hujjar da kika fada ba naji zatai tassiri."


Cikin mamaki ta kalleshi, murmushi yai yace "Badai kina tunanin shine dalilin dayasa Zainab tabar nan ba?"


Tace "ba shi bane?"


Dariya yasa yana kallanta kafin yace " kin tabbatar zaki sa yadau nauyin shiri uku?"


Kai tsaye ta dauko wayarta ta dannawa babanta kira.


Ringing biyu ya dauka yace "Baby!"


Tace "Abbi taimako mukeso a gun aikin mu, can you please help us?"


Na menene?

Nan ta sanar dashi, kai tsaye yace "shikenan, ki sanar dashi gobe ya samen a office."


Nan ta kashe wayar sannan ta kalli Kabir wanda gaba daya yai shiru dadi ya gama kasheshi, dariya yasa sosai yace "dole a sallameshi, amma me kike gani in kika bari zuwa wani satin? Saboda kar mutane su kawo wani abin ganin an koreshi kai tsaye."


"Shikenan, amma haduwarku da Abbi shima sai wani satin."


Yace "amma yace gobe."


Tai murmushi tace "ina nake da tabbas zaka cika alkawari bayan ka samu abinda kake so?"


Yanayin fuskarsa ne ya canza, mikewa tai ta mai sallama ta fita.


Da kallo ya bita kafin yace "wai ni ta ma magana kamar sa'anta? A kalla nasan nakai sa'an ubanta."


******


Bayan sati daya.......


Gaba daya Zainab ji take kamar batada lafiya, sam komai baya mata dadi hatta abinci a dole take ci.


Ta ina zata iya cigaba da rayuwa a haka? Littafin da take karantawa ta ajiye sannan ta mike tare da shiga toilet.


Alwalar magrib ta dauro sannan tai sallah, kan sallayar ta kwanta tana tunanin abubuwan da suka sameta, tunowa tai farkon fara aikinta, duk uban wahalar datasha?? Mikewa tai zaune zuciyar ta na tafasa da bakin cikin cin mutuncin da aka mata, mijinta ta kamashi a gidanta yana lalata yanzu gun aikin data sadaukar da komai saboda shi gashi abinda suka mata.


Mikewa tai ta fito daga dakin? Saukowa kasa tai gida shiru kamar ba mutane?


Tunda su Nabila suka tafi skul gidan ya koma kamar ba mutane a cikinsa.


Falan Dady ta nufa, yana shan magani tai sallama, kallanta yai tare da amsawa.

Basma ta kwashe maganin daga gun tana kallan Zainab.


Haka ta karasa cikin falan ta xauna daga dan gefensa, bin bayan Basma  tai da kallo idanta ma kanta tace "Dady maganin me kake sha kullum?"


Tv din dake kunne na saudiyya ya kalla sannan yace "Diabetic ne kinsan in ya hadu da hawan jini sai ana kula sosai."


Idanunta ne suka fito tace "sosai ne?" Tai maganar a raunane.


Kallanta yai yana murmushi yace "ba sosai bane, shiyasa da kika tambayen kwanaki ban fada miki ba, a ido kamar mai dauriya amma azahiri akwai iya raki."


Dariya tadanyi, Basma ce ta dawo ta zauna akan kujera tana kallan tv itama.


Dady ya kalli Zainab yace "karki damu ba wani abin bane, kedai ki kula da kanki."


Shiru tai batace komai ba, yace "maganar yaran yazo?"


Kallan Dady tai tace "a'a, ni Dady gaba daya ba aure a harkar rayuwata yanzu, kana ganin abinda ya faru dani.....”


Juya kai yai bai tanka mata ba, tace "Dady in har bazaka budemin tv station ba sai na yi aure to dan Allah ka barni na nemi aiki a wani gun, dan Allah dady."


Juyowa yai ya kalleta, Basma tsam ta mike dan ta fahimci maganar ba tata bace.


Kallan Zainab yai yace "haryanzu baki fahimci me nake ce miki ba?"


"Na fahimta Dady amma ni gaba daya Dady banasan kara hada rayuwata da wani namijin ne."


Shikenan sai ki karasa rayuwarki a cikin gidan nan.


Kallansa tai tace "Dady?"


Kallanta yai yace "in kinga kin bar gidan nan da sunan aiki to tare da mijinki ne, dan haka ki koma ki zauna in dai wannan ne ya kawoki."


Hawaye ne suka zubo mata ta sharesu sannan ta mike tabar gun, yaza'ai Dady ya mata haka?


Da kallo ya bita tare da kallan tv yana tunani, dazu gaisuwar wani abokinsa suka je, shima irin ciwonsa ne ya kasheshi.


Taya zai barta ta fara aiki bayan yasan daga sanda ta fara aiki bazata taba sake tunanin aure ba? In ajalinsa yaxo fa? Ya zatai da rayuwarta? Yan uwansa tun can ba zumunci suke ba saboda yan ubane, yan uwan mahaifiyarta kuwa maza ne su kuma taya zasu kai ta babba da ita cikin iyalansu? Sai dai kanwar Ummy wacce ita kuma matsalolin gidanta sun mata yawa, gaba daya kwanan nan da wannan tunani yake yini yake kwana in ba ta ita ba Nabila fa? Gwara ita da girmanta amma Nabila fa? Haka zasu xauna su biyu a gida kamar 'ya'yan da basuda gata ko me? yasan Basma duk da tana nuna nadamarta a fili ya tabbatar daga sanda ya rasu Nusaiba kawai zata dauka suyi gaba.


Dole me ya matsa mata tai aure ya bude mata gidan tv inyai hakan ne kadai hankalinsa zai kwanta, yasan Nabila tana da gun zama ko bayan ransa, sannan Zainab a darajarta ya barta.


Idanunsa ya dan rufe ya bude sannan ya fara hailala a ransa.


******


Zainab na shiga daki ta zauna a bakin gado zuciyarta na kuna, ina zata iya rayuwa a haka?


Laptop dinta ta dauko ta bude, me zatayi?


A zuciye ta rufeta da karfi sannan ta dafa kanta.


*********


"Yasin bazaka saidamin wannan lace din ba"


Goggo to wai ya kikeso muyi? Duk kinsa na saida nawa kayan ki kawo naki dan Allah.


A tamfa ta cila mai tace "sai dai wannan."


Kallanta yai yana dariya yace "yanzu ke Goggo wani matsiyacin ne zai sai wannan atamfar?"


Matsiyaci?

Bani abata ni ina san kayana.


Mikamata yi yace "Karki damu in muka saida wannan lace din na samo sana'ar da zan fara."


Wani banzan kallo tamai tace "Fadawa wanda baisanka ba amma bani uwarka ba, a gidan ubanwa zaka iya wata sana'a banda ka halaka mana kudi?"


Fuska ya tsuke yace "Ki bari ki gani wannan karan a shirye nake."


Wani kallan banza tamai tace "ya ni sai yaushe zaka amso kudin ne? Ko bacci nake na tuno tsinaniyar nan sai naji na tashi."


Shiru yai shima ransa a bace yace " wai uban me ya kawota bank din ma?"


Ni kake tambaya?


Shiru yai cikin kuluwa.


Goggo tace "yaushe zaka amso mana kudin ne?"


Zan sake kiranta yau dan ko shekaran jiya na kira tana aiki tace inta fito zata kirani kuma naji shiru."


Kirata yanzu.

Ta fada tana mikamai wayarta dake gefen gado.


Amsa yai ya danna number Afreey, harta katse bata dauka ba.


Goggo tace sake.


Nan ya sake kira, yanzun ma kamar zata katse sai kuma ta dauka.


Mikewa tsaye yai fa sauri yace "Afreey, najiki shiru."


Tace "zanzo gidanku in an tashi dan ina san tambayarka abu."


Da sauri yace "to sai kinzo." Jiyai harta kashe ba tare da ta kara magana ba.


Cikin jin dadi ya kalli Goggo yace "tace zatazo anjima."


Cikin wani jin dadi Goggo tasa dariya tace "kai masha Allah, ashe yau shiyasa nai mafarki inacin kaza."


Dariya yai yce "da alama kazar zamuci da daddare."


********


Khalid ne ya kalli Kabir cikin mamaki, yau tun safe yake shiri saboda yau ne zai fara dauko rahoto.


Me kunnensa suke jiye mai?


Kabir ne ya kalleshi rai a bace yace "kana san cemin baka san Giss ba?"


Khalid ya kalli mutanen dake gun sannan ya kalleshi yace ban sanshi ba wallahi, waye shi?


Kabir rai a bace yace "Adam fa? Mijin Zainab? Ka sanshi?"


Yace "Eh, friend dina ne."


Wata banzar dariya yai yace "sannan kacemin ba kai ka sanar da Giss gidansu Adam ba? Ka fadamai abinda ke faruwa tare da neman yaje yai hira dashi?"


Idanu Khalid ya zaro cikin tsananin mamaki yace "nace me?"


Ran Kabir ne ya baci matuka yace "duk cikin mu waye yasan mijinta bayan kai? Kenan sirrin gidan tv din nan kake dauka kana ba abokinka dake aiki a wani gidan tv din, takaicina duk abinda ya faru ashe kaine ka shirya shi.”


Shiru Khalid yai dan yanzu ya fahimci trap ake neman jefashi.


Kabir yace "programs da mukai meeting jiya akan zamu fara ya akai Giss yasan dasu? In ba kai ka bashi ba?"


Khalid ya kalleshi yace "Giss din yace?"


Nazifi ne yace "Director ba halin Khalid bane duk da bansan alakarsu ba amma bazai taba yin haka ba.”


Wani kallo yamai wanda yasashi yin shiru.


Ramatu ce tace "in har sunada alaka a gwada kiran numbersa a wayar sa a gani mana?"


Kallanta yai a lokacin ya tuno dazun nan ta ari wayarshi, wai ta rasa tata tana san kiran wayarta.


Kenan???


Kabir ne yace "ina wayarka?"


Khalid ya kalli Ramatu wacce ta dauke kai gefe, jiki a sanyaye ya mika mai wayar nan ya dauko number Giss wanda suka sa aka turo musu sannan ya sa number a wayar Khalid.


Kallansu yai sannan ya nuna wayar, AGis sunan daya fito kenan a wayar.


Ran Director ya kara harzuka yace "daga can gidan suka turo ka nan?"


Khalid yai shiru, yi magana, me da me ka sanar musu?

Kamar yace agwada a gani ko mun taba waya dashi, sai kuma kawai ya samu kansa da kasa magana.


Shiru Khalid yai kafin Kabir yace "biyoni office."


Ya juya rai a bace.


Nazifi ne ya kalli Agoggo ganin lokacin shirinsu yayi yasa ya juya jiki a sanyaye yana tausayin Khalid, meya kaishi?


Afreey dake zaune ne ta saki wani murmushi a ranta tace Hauka ko? Zan nuna maka babban hauka, idan ka rasa abinyi ka rasa komai naka dole ka dawo gareni.


Suna shiga Director Kabir ya kalli Khalid yace "kanasan ka tafi salin alin ko kana san mu koreka? Kasan bazamu taba barin spy a gun aikin mu ba, a lokacin da ma bazan baka zabi ba sai dai na koreka."


Khalid ne ya kalleshi sannan yace "Nagode da hakan, sannan duk wanda yaci hakkin wani ya zamanto cikin shiri."


Me kace?


Khalid ya mai sallama ya fita.


Hannunsa ya dunkule zuciyarsa na tafasa, bayan abinda ya faru da Zainab ransa ya baci da sam aikin ma ya fita kansa, sai dai ganin yanda Abba da Umma ke alfahari da aikin yasa ya jure komai.


Haka ya shiga ciki ya rubata resignation letter ya kawo mai sannan ya shiga hada kayansa, idanunsa sunyi jaaa.


Nazifi kam yanata fatan ya gama yaji abinda ke faruwa sai dai yana fitowa yaga ba Khalid.


Khalid na fita waje yaji ance "Khalid!"


Juyowa yai ya kalli Afreey, ta karaso inda yake cikin rangwadar ta.


Kallansa tai tace "ya akai haka? Meya faru?"


Kallanta yai yace “Weldone, har na kosa naga inda abinki zai kai."


Tace "au kasan nice?"


Yace "na sani yanzu, saboda bakya iya boye abu."


Kallansa tai tace "ka amince dani yanzu na sa amaidaka gun aikinka.”


Wani murmushin takaici yai kamar zaiyi magana kawai ya juya yai gaba.


Shiru tai tana kallansa, ji take kamar ta ruga ta rungumeshi saboda tsananin san da takemai.


*******


Yamma tanayi ta nufi gun Adam.


Cikin zumudi ya bude motar ya shiga yace "Afreey ina wuni?"


Wani kallo tamai sannan tace "Adam ya akai Khalid yasan matarka?"


Kallanta yai yace "Ni na hadasu ba na fada miki ba?"


Haushi ya kamata tace "Kai wani haukar ne yasa ka ba saurayi tukin matarka?"


Kallanta yai yace "wai menene matsalar ne? Na fada miki ba komai a tsakaninsu."


"Ba komai? Bansan dai matarka ba amma wlh Khalid nasan Zainab."


A zabure ya kalleta wani rikitacen kishi ne ya bayyana a fuskarsa karara yace "mene?"


Tace "haka dai yake kamar yanda na fadama, in har bakasan matarka ta shiga wani hali kaje kuyi sulhu ka maidata in kuma ka hakura da ita ni zan dau nawa matakin."


Ransa a matukar bace yake maimaita sunan Khalid.


Kallan gidan daya fito tai sannan tace "Me kake tunanin yi?"


Kallanta yai yace "Zainab na sona kuma nasan haryanzu tana sona, nasan yanda zanyi na shawo kanta, taya Khalid zai min haka."


Wani kallo tamai tace "kai da wace haukar ce tasa ka kaishi gunta? Sannan kila itama tana sansa."


Da sauri yace "bata sansa, ina halin Zainab ina na Khalid? Halinsu bazai taba zuwa daya ba kema kin sani da Khalid bashida tsatsauran ra'ayi da tuni kunyi aure."


Shiru ti kafin tace "yanzu zaka je ku shirya?"


Shiru yai yana tunanin uku fa yai, ji yai tace "menene?"


Da sauri yace "zanje, ai komenene sai dai ya faru taya ma Khalid zaice yana san Zainab?"


Kallansa tai tace "muje Atm na baka kudi, ka tabbatar ka shawo kan matarka."


Da sauri yace "ai dole ne ma."


*******


Khalid kam ya kasa sanar dasu Umma yabar aikin kullum da safe zau fita ya nufi aikace aikacensa yayi sai yamma likis ya dawo gida wannan ne yasa Umma da Abba basu kawo komai ba.


*****

Yau tunda Zainab ta tashi take jinta kamar mara lafiya, watanta daya kenan a gidan nan daga zama sai kallo, sai dan cin abinci, in taji ta gaji taje kasa ta dan amshi girki, sai ko dan hira kadan shima in Dady na nan.


Sam zaman nan ya isheta daren yau sai juyi take a kan gado, ta ina zata cigaba da wannan zaman?


Agoggo ta kalla wai haryanzu karfe 8 na dare, wayarta ce tai kara a hankali ta sa hannu gefen gado ta daukota.


Ganin sunan Nazifi yasa ta daga, gaisheta yai bayan ta amsa ne yace “Hajiya dan Allah number Khalid nake nema tun lastweek bansamu ba, shine nai tunanin tambayarki.”


Khalid? Ta maimaita.


Yace “eh.”


Tace “wato ba kirana kai kace kayi rashin takurar aiki danake sa ka ba?”


Dariya yai yace “Hajiya bazaki gane aiki yanzu ba ke yanda yake bane, bana san daga miki hankali ne shiya sa ma banyi wannan maganar ba.”


Tace “Taya zaka nemi number Khalid a guna bayan kullum kuna tare?”


Shiru yai kafin yace “ashe bakida labari?”


Labari?


Dan shiru ya kara kadan kafin yace “ai tun sati uku daya wuce zuwa hudu aka koreshi.”


Mikewa tai zaune tace “aka me?”


Nan ya kwashe abinda ya faru ya fada mata, ranta yayi matuka sosai gun baci tace “Director Kabir da alama ya fara zaucewa.”


Nazifi yace “shine nake nemanshi akwai wani yayana dake aiki gidan radio nake san fadamai ko zai gwada.”


Ranta yayi mugun bace tace “bashi basai ka fada mai ba.”


Kashe wayar tai a zuciye ta kira number Khalid.


Yana zaune yna karatun riyadulSalihin, yaga wayarsa na ringing, sunan dake yawo akan allan wayar ya kurawa ido yana kara tabbatar da abinda yake gani, bai taba tunanin ganin kira daga wannan number ba.


Gani yai kiran ya tsinke, sai dai a take ya sake gani wani kiran, hannu yasa a hankali ya daga wayar zuciyarsa na kokonto abinda yake gani dan gani yake shine yake san kira daga number shi yasa yake ganin haka.


Yana dagawa yaji ance “Taya zaka bari su koreka?”


Wani lalausan murmushi ne ya bayyana a fuskarsa yace “taya zaki bari su koreki?”


A kufule tace “ni ai ninaga damar bari.”


Yace “nima ninaga damar bari.”


“Wasa ma ka dau abin?”


Jingina yai da jikin dan gadansa yace “ke zan tambaya”


Tace “wai kai bakin ka baya taba mutuwa?”


“Taya zai mutu bayan mai tambayar nata baya mutuwa?”


Tace “uban waye yace kasan Giss?”


I don’t........

Know? Ta karasa mai, tace “kana tunanin zan yadda da hakan?”


Shiru yai baice komai ba, tace “Umma fa? Sun sani? Naga ko kwana biyu da mukai waya tace kana aiki.”


Yace “na kasa fada musu, bansan yanda zasu dau abin ba.”


Shiru tai zuciyarta na kara tabbatar da abinda take shirin yankewa.

Shiru tadan yi kafin tace “Kana da time?”


“Wani iri?”


“Na zuwa nan garin.”


Shiru yai yana tunani yayi me?


*****

Ayusher🏌🏻‍♀

[12/20, 9:21 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{48}


Bin wayar yai da kallo bayan ya kashe, mikewa yai ya hau kan gado ya dauko littafi daya daga cikin wanda ta bashi yake karantawa, daga nan bacci yai gaba dashi.


  Yau kasancewar Asabar ne yana zaune a gun Abba bayan ya taimaka mai yayi wanka yasa kaya, yana zaune suna dan tattaunawa, Abba ke fadamai labaran dayaji a tashar radio na yanda rayuwar yara kanana ke halaka.


Shiru yai da farko ya fara fahimta sai kuma ya tafi tunani, har Umma ta ajiye abinci bai san ta zo ba.


Sai da Abba yace "Khalid?Khalid?"


Kallan Abba yai da sauri yace "Naam."


Umma ta zauna tace "lafiya?"


Kallan Umma yai sannan ya kalli Abba yai murmushi yace "bakomai, ina tunanin abinda ka fadane, sannan na gano kuskurena na kin daidaita mai laifi irin haka."


Abba yace "wacece?"


Kai Khalid ya dan juya kadan yace "watace."

Kauda zancen yai yace "Asiya su Amir sun fice?"


Tace "wlh dazu ina aiki suka gudu."


Suna gama cin abinci ya shiga wanka, yana zaune a daki yai shiru yana tunani, me Zainab zatace mai?


Mikewa yao ganin ba wannan bane yanxu a gabansa dole ya kawar da babban abinda ya kamata yai.


Kai tsaye yawa su Umma sallama ya wuce ya hau bus zuwa kano, a Naibawa ya sauka, gidansu Raziyya ya nema kai tsaye ya nufi gidan yana fatan dacewa da abida yake shirin yi.


A bakin kofar ya tadda dan dattijon dake ta alwala, tsugunawa yai sai daya idar da alwalarsa sannan ya gaisheshi.


Dattijon ya kalleshi tare da ajiye butar a gefe cikin sakin fuska ya amsa ya daura da cewa "Daga ina??"


Khalid yace "Raziyya nazo nema."


Kallansa yai yace "Raziyya? Ai tun sati uku da suka wuce bata dawo gida ba, kasan ba a garin nan take aiki ba."


Kallan tausayi yamai sannan ya jinjina kai alamar gasmuwa yace "in ba damuwa ina san ka dan bani number dazan sameta."


Kallansa yai cikin yabawa da nustuwarsa yace "to."


Wayarsa yasa hannu ya dauko aljuhunsa sannan ya dan kanne ido yana neman number, can ya mikamai wayar yana cewa "gatanan."


Khalid ya amsa da hannu biyu sannany dau number sannan ya mikamai.


Kallansa yai cikin tausayawa yace "ya mai jikin?"


Da sauki yanayin jikin nata ne sai dai hamdalla, da alama kasan Raziyya sosai, yauce rana ta farko da wani ya tambayi abin cikin gida.


Khalid yai kasa dakai kafin ya dago cikin wani yanayi, kallansa yai yace "da wani abin ne?"


Khalid yace "Ina tunanin in ba damuwa ka kira Raziyya ta dawo gida."


Kallansa yai cikin mamaki yace "ta dawo gida kamar ya?"


Shiru Khalid yai kafin yace "an samu matsala a gun aikinta, sai dai rashin san saku a damuwa yasa ta kasa fada, sai dai ina ganin hakan ba karamin matsala bane ga 'ya mace."


Shiru Dattijon yai duk da yaji rashin dadi sosai dayai na rashin aikin daywace sai dai Khalid gani yai wata yar kwalla ta gangaromai, kallansa yai jiki a sanyaye.


Dattijon yai murmushi yana share kwallarsa yace "nagode dan nan, nagode sosai."


Khalid yai shiru, cigaba yai "yauce rana ta farko kuma da wani yaxo yamin nuni cikin hikima akan abinda ke faruwa, maganar gaskiya na dade nima ina zargin aikinta saboda gulma da zaginmu da ake a unguwa, sai dai ganin ita Raziyya ta nuna min ba hakan bane yasa nake kokarin sawa zuciyata ba hakan bane, yau zan kirata ta dawo insha Allah."


Yadanyi shiru kafin yace "Nagode d'an nan Allah ubangiji yasa ka gama da duniya lafiya, ya daukaka ka ya baka zuri'a ta gari."


Khalid jiyai idanunsa sun ciko a hankali yace "Ameen Baba nagode."


Dattijon ya sake kallansa cikin jin dadi, Khalid yamai sallama ya taso gaba daya jikinsa a sanyaye.


Wayarsa ya kalla, yana tunanin kalaman Zainab, wani dan karamin murmushi ne ya bayyana a fuskarsa, ya daga waya ya kira Salmanu.


Suna gama waya ya kashe, ya hau mota ya koma danbatta.


********


Yau tun safe take duba wayarta sai dai haryanzu bataga sako daga Khalid ba, bata minti biyar sai ta taba wayarta, kara volume na ringing din wayar tai wai incase ko sako ko kora zai shiga bata ji ba.


Ganin har dare yayi ba sako ba waya yasa ranta ya baci, ajiye wayar tai ta kwanta cikin rashin jin dadi.


Bayan tayi sallar asuba tana kokarin kwanciya ta dau wayarta.

Sakon data gani ne yasa murmushi bayyana a fuskarsa.


"Send me the address, zanzo Wednesday."


Nima sai anjima zanyi reply, ta fada tare da kwanciya.


A daren ranar ta nufi falan Dady, yana zaune yana waya ta shiga, Basma na zaune daga gefe tanata kara yanka mai cucumber din da yake ci.


Mika mata tai, Zainab tace "Alhamdulila."


Dady ne ya gama waya sannan ya kalleta, Zainab yanxu nake san kiranki ma ashe kinji dawowata."


Tace "an dawo lafiya?"


Yace Lafiya kalau, ya kalli Basma yace "ya isheni haka Hajiya."


Murmushi tai tace "shi yasa nake yankawa a lokacin yanda in yayi sai a ajiye."


Ruwa yasha yana kallan Zainab yace "tunani nake ke ko yar fita bazaki dinga yi ba haka zakiyi ta zama a gida? Ai ko bin Basma kyayi zuwa siyayya haka."


To kawai tace, kallanta yai yace "ya akai?"


Kallansa tai sannan tace "Dama bako zanyi ranar laraba."


Da sauri ya kalleta tare da gyara zama yace "bako?"


Basma cikin jin dadi tace "masha Allah."


Kallanta Dady yai yace "wanene? Ya akai kika hadu dashi ke da kike gida a kunshe?"


Murmushi tai tace "in yazo zaka ganshi, kaima ka sanshi."


Ni?


Ta daga kai alamar eh, gani Dady ya shiga tunanin waye yasa ta mike ta bar falan, tana hawa sama tai shiru a ranta tace "Sorry Dady wannan ita kadai ce hanyar data rage min."


***********


Mabalan botiran rigarsa ya shiga maidawa, agoggo ya kalla karfe 7 na safe, dole ya fita da wuri.


Fitowa yai, ya nufi hanyar Abuja.


Dady kam yana gun aiki yana kiran Basma akan yazo? Tace "a'a"


Itama tana kitchen ana shirya abinci kala kala dan sai da Dady ya sake sanarwa ayi abinci sosai.


Itakam Zainab batama san hidima suke tayi ba daga cewa zatai bako, tana daki tana tunanin yanda haduwarsu da maganar da zasuyi da Khalid, dan zaman datai dashi ta san halinsa sai dai tana ganin shi kadai ne zai taimaketa a wannan lokacin.


Karfe 2 daidai ya sauka garin Abuja, bai kirata ba duk da tace mai in ya iso zata turo a daukeshi, shi kuma gani yake a wani dalilin akuma wani matsayin za’a zo har a daukeshi?


Baisha wahalar ganewa ba saboda gidan mahaifinta sanane ne a unguwar.


A bakin wani tafkeken gida ya tsaya yana kallan gidan kafin ya nufi gate, knocking yai daga ciki mai gadin ya bude kofar.

Gaisawa sukai da Khalid, ya kalleshi yace “Ammm gun Zainab.....”


Jin abin yai banbarakwai hakan yasa yai shiru, da sauri yace “oh ko kaine bakon da za’ai?”


Kai ya daga, budemai kofa yai ya shigo harabar gidan sannan yace “bari na shiga na tabbatar kaine.”


Khalid yace “bari na kirata.”


Cikin jin dadi yace “yauwa to hakan yayi.”


Kiranta Khalid yai, kallan wayar tai, tunda take zata iya cewa gabanta bai taba faduwa dajin ringing ba sai yau, dauka tai cikin dauriya.


“Ina waje.”


“Okay bari na sauko.”


Jiki a sanyaye ya kashe wayar yana kara kallan gidan, tabbas wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa.


Bata wani dade sosai ba sai gata ta bude kofar waje.


Daga nesa ta kalleshi, haka kawai ta samu kanta da zuba mai ido tana tunanin yaushe rabo?


Dayake dama can ita macece da batada lokacin wahalar dakai da bata lokaci gun kwalliya.

Tadai sa tsadaden lace dinta ta yafa mayafi light purple kalar lace din ta yafa.


Shikam shadda ce a jikinsa kalar madara an mata aiki da kalar ruwan kasa mai turuwa.


A hankali ya fara takawa, zuwa inda take har ya karaso bakin kofar, nan ta koma ciki ya bi bayanta suka shiga ciki.


Bangaren hagu tai dashi inda falan baki yake, shiga yai ya zauna.


Daga dan nesa dashi ta zauna, kallan juna sukai kawai a tare sukai murmushi.


Kallansa tai tace “murmushin na meye?”


Yace “yanda naga kina yi ne yasani.”


Tace “ban taba kawo wani gidan mu bane bawai namiji ko mace ba wannan ne karo na farko shiyasa nakejin abin daban.”


Kallanta yai yana san cewa Adam fa?


Kamar tasan me yake cewa tace “Adam?Dady ne ya kirashi a waya yazo, so karka min dariya.”


Shiru yai bai ce komai ba.


Bari na kira matar gidan ku gaisa.


Ta mike tai ciki, a kitchen ta taddata sun hama hade kayan abincin da Zainab yasata kallanta cikin mamaki, tace “duk wannan na meye?”


Basma tai dariya tace “Na bakon ne, naso tambayarki ko da abinda yake so Dadynki ya hana yace in kika sani cewa zaki sunyi yawa.”


Baki ta bude tana kara kallan jerin abinci da snacks su fruit da juices.


Basma tai dan dariya tace “inje mu gaisa, dadynki yace a kirashi kafin ya tafi shima.”


Sam mamaki ya hanata magana sai gani tai tasa mai aikinsu ta shiga da dishes din.


Kainta girgiza sannan tai ajiyar zuciya ta juya.


Basma ce ta fito cikin fara’a ta kalla Zainab tana dariya.


Ta sani yanzu zata ta kira Dady ta fesa mai, wucewa ciki tai, Khalid na zaune yana kallan ikon Allah ganin sai shigo da abubuwa ake ana jera wa.


Kunya duk ta kama Zainab, har aka gama, kallansa tai shima kallanta yai, idanunta tadan dauke hakan yasashi dauke nashi shima.


Sun danyi shiru kafin ta kalleshi tace “Yanzu ya zakai dasu Umma?”


Tafin hanayensa ya dan hade akan cinyarsa yace “ina tunanin sanar musu amma sai na samu wani aiki, dan na sake applying a gurare dayawa.”


Kallansa tai tace “I doubt it won’t be easy.”


Kallanta yai yace “it wasn’t easy dama.”


Kai ta dan jinjina alamar eh, shiru suka dan sakeyi kafin ya kalleta yace “Yarinyar nan”


“Wacce?”


Ta tambaya kafin ta hade rai tace “meya faru?”


Shiru ydan yi na yan dakiku kafin yace “tayi abinda tai ne saboda daukar fansar abinda Adam yama yayarta, ya rabu da ita saboda ke, in da hali ki yafe mata yarinyar has a difficult life.”


Shiru tai tana kallansa maimakon ta bashi amsar tambayar dayai mata sai jiyai tace “Ya zakai dasu Kabir?”


Kallanta yai yace “ya zanyi?”


Tace “eh I don’t plan to forgive them, sannan in har bai nemi yafiyar abinda ya mana ba banaji hankalina zai kwanta.”


Taya zaki dau matakin?


Shiru tai tana kokarin tattaro dauriyar ta, kallansa tai cikin dakewa kamar wanda gabanta ba faduwa yake ba tace “Dady zai bude min Tv station, sai dai bazai budemin ba sai nayi aure, anda ni yanzu banida plan na auran wani duba da yanayin yanda rayuwata take, bazan iya cigaba da ganin mutum azzalumi kamarsa yana cigaba da yin abinda yaga dama ba.”


So? Ya fada yana kallanta.


Kallansa ta sakeyi tace “i need your help.”


Ni?


Tace “eh me kake gani idan ka aureni?”

Dan yawon bakinta ta hadiya tace “ka aureni muyi aiki a tare a tv station din da Dady zai bude.”


Gaba daya maganar tazo mai sama ta ka dan har yama kasa cewa komai sai kallanta kawai da yake.


Ganin yanda yake kallanta yasa tace “ nasan yanda zakaji abin, amma na duba naga hakan ne kadai mafita daga ni har kai.”


Har ni?


Tace “eh, da farko bakada aiki kabar su Umma da tunanin kanada shi, sannan bakada tabbas din samun aiki nan da shekara uku ma nan gaba, haka zaka cigaba da yi musu karyar kana aiki? Haka zaka cigaba da rayuwarka?”


Samun kansa yai da wani murmushi sannan ya juyo sosai yana kallanta yace “sai na aureki a matsayin jari na?”


Shiru tai kafin tace “jari?”


Yace “Ba hakan bane? In aureki a matsayin me? Wanda kikeso? Wanda kike bukata? Ko wanda kike neman cika burinki dashi?”


Tace “koma menene zaka iya yin tunanin dakaga yama, amma kasan bada wata manufa na fadi hakan ba.”


Yce “okay mu barshi da zuciya daya kika fada, why me?”


Shiru tai kafin tace “kai kadai na yadda dashi.”


Wani murmushi ya sakeyi yace “kinsan halinane? Ta ina zaki yadda dani?”


Kallansa tai batai magana ba sai dai ta fara karzar farcenta.


Kallan hannunta yai sannan yace “kinasan muyi auren karya kenan ko me?”


Kallansa tai cikin dakewa itama tace “in ka fassarashi da karyar kenan.”


“In ban fassara ba fa?”


Ya fada yana kallanta sannan yace “in kuma naji inada wacce nakesan aura fa?”


“Sai ka aureta”


Haka kawai ya samu kansa dajin haushin wannan amsar.


Maimaitata yai yace “sai na aureta?”


Tace “eh, ra’ayinka ne, sannan kai mijin mace hudu ne, ban nemi komai daga gareka ba, let’s work as a partners, sannan nasan kafi kowa kishin kanka bazaka yadda da kudin da wani zai baka ba halak dinka ba, bazan shiga hakkinka ba balle na takura ma ba.”


Wani wahalalen murmushi yai yace “in kuma ban yadda fa?”


Yanayin fuskarta ne ya canza ta kalleshi.


Kallanta yai yace “meyasa kikesan yanke hukunci akan rayuwar wani?”


Rayuwar wani?


Yace “eh, aji ace na yadda munyi aure, in dawo gidanki in zauna in je gun aikin da yake mallakinki, me ya rage min keman?”


Kallansa tai tace “gun aiki daukanka nai kamar yanda nake da damar daukan duk wanda naga dama.”


Yace “Uhm hm”


Tace “wai kai bazaka taba bari ai nasara akan ka ba?”


Dan lebansa na kasa ya lasa kadan yace “bakya tunanin rayuwar da kike neman jefa kanki?”


Tace “ wace rayuwa?”


Taya zaki dauki daukan fansa a maimakon farincikin rayuwarki? Baki taba tunanin yin aure dan farin cikinki ba?”


“Bansan wannan ba, ban kuma nemi abinda ba zan samu ba, na sani ba wanda zai soni a yanda nake, tun daga kan hallayena har zuwa yanda tsarina yake, duk wanda zai aureni da wata manufar zai aureni, that’s why i choose you, ko zaka cuceni kamar yanda kace zakai a kalla nine na zabi ka cucenin sannan a kalla nasan tarbiyyar daka samu bazaka kawo mace cikin gida da sunan kanwarka ba.”


Wasu zaffafan hawaye ne suka zubo mata wanda yasa zuciyarsa yin rauni, wace irin rayuwa ta daura wa kanta?


Sharewa tai tace “kaci abinci Dady da matar gidan sunyi hidima gun shiryashi.”


Shiru yai haryanzu yana kallanta.........


******

Ayusher🏌🏻‍♀

[12/22, 8:58 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


Gaisuwa Batuul Maman🥰 Wish you Allah's Khair and Noor


{49}


Idanu kawai ya zuba mata, ganin yanda yake kallanta yasa tace "menene?"


Wani murmushin takaici yai yace "haka kika dau rayuwar?"


Cikin dakewa tace "eh, ba hakan take ba?”


Kai ya jinjina sannan ya mike tsaye yace "am sorry amma bazan iya yin abinda kikeso ba."


Kallansa tai ta kafeshi da ido cikin wani yanayi na jin haushine  karara cikin idanunta, idanta ya ciciko yana neman kawo kwalla.


Yana kallanta da idanunsa da sukai dan jaa yace “did i hurt your pride?”


Batace komai ba sai dai haryanzu idanunta da kallan da take mai yana bata janyesu ba, yace “nima you hurt my pride.”


Kansa ya dauke saboda rauni da zuciyarsa ta fara yi taya zata zata ce ya aureta da kanta sannan bawai a dalilin komai ba sai akan aikinta? Taya zata.....kanta ta kawar gefe tasa hannu ta tadan maida kwallarta, tace "kaci abincin, a kalla baka wulakantasu ba su."


Juyowa yai ya kalleta, kanta na gefe ya koma ya zaune tare dayin shiru.


Sun danyi shiru na yan dakiku kafin yace "me ya kaiki yin wannan hukuncin mara ma'ana? Taya zaki nemi ruguza rayuwarki saboda daukan fansa?”


Kanta na gefe itama tace "ya bazanyi ba? bayan mutanen can basuda hankali? In ba hauka na kansu ba meye na sako rayuwar aurena a cikin haukarsu? Meye damuwarsu da rayuwata? Aiki nake nayi iya yina ta ya zan yafe musu na hauka da jahilcin da suka nuna karara?”


Bata jira amsarsa ba tace "sannan duba wani hauka na san akoreka da sukai? Taya zasuce ka sanar da wani sirrin cikin gida?"


Kallanta yai yace "akanshi ne kawai?"


Juyowa tai itama tace "kasan wahalar danasha kafin gun ya koma haka?


Idanunsa na kanta yace "I thought ke kika sa kanki?"


Wani takaicine ya kamata ta dau pillow din dake gefenta, kallanta yai yace "ba dai makamin za'ai ba?"


Harararsa tai ta ajiye pillow din a kasa tare da cewa "kaci abinci naga alama in na kara minti biyar anan zuciyata ce zata buga saboda jin bakaken maganganu."


"Ni da kika yaba min bakaken maganganun fa? ince me?"


Kallansa ta sake tace "yaushe? Me nace?"


Kansa ya dauke, mikewa tai ta fita.


Da kallo ya bita cikin tausayawa rayuwarta.


Daga kofa yaji tace “Dady?”


Dady ne ya kalleta yana dariya yace “Zainab? Yana ciki?”


Cikin mamaki tace “naga lokacin tashi baiyi ba.”


Yana dariya yace “sai lokaci yayi? Ai yai dole na fito nazo mu gaisa da sirikina.”


Siriki?

Ta maimaita cikin mamaki, da sauri tace “Dady muje falanka inada magana.”


Kallanta yai yace “mayi daga baya, dan inada meeting, saboda mu gaisa na zo, yanzu zan koma.” Ai kafin ma ta sake magana ya tura kofar glass din.


Khalid ne ya mike tsaye da sauri, Dady ne ya karasa yana kallan Khalid cikin tsananin jin dadi, yace “tunda tacemin nasan bakon jikina ke bani kaine saboda ba kowa dana sani ta bangarenta inba kaiba, ganin kai din ne da gaske ya sani kara jin dadi.” Ya karaso inda Khalid yake cikin tsananin jin dadi.


Khalid ne ya tsuguna a kasa yana gaisheshi.


Dady ya zauna a kasa kusa dashi yana amsawa cikin tsananin farin cikin dani kaina na da dade banganshi a fuskarsa ba.


Khalid ya kalla yace “Zauna sosai.”


Khalid ya zauna samun kansa yai da kunyarsa, Dady ya jawo plate ya mika mai shima ya dau daya, kallan Khalid yai yace “dan zuba mana abinci”


Khalid ya shiga bubudewa yana cikin wani yanayi da bai taba fuskantar kansa ba ko a lokacin yin interview ne kuwa.


Dady kam dadi duk ya hanashi sukuni, Khalid ya kalla yace “shinkafar ta isa haka nan zubamin ganyen dayawa.”


Nan ya ajiye mai, Dady nata matsa kafarsa, Khalid ne ya kalleshi yace “ciwo take?”


Murmushi yai tare da daukan spoon, suka fara cin abinci, shikam dai Khalid ci kawai yake duk jinshi yake daban.


Ganin yanda kafar Dady din ta tashi yasa Khalid yai shiru.


Dady ya sha kunun aya mai sanyi sannan ya kalleshi yana murmushi yace “ba wani abin bane, ciwon sugar ne kasan in muka zauna sosai ko mukai tafiya dayawa sai tadan hau.


Sugar?


Khalid ya maimaita jiki a sanyaye dan yasan yanda ciwon ke da ila, kallansa yai yace “amma ba hawan jini ko?”


Dady yai murmushi, wanda yake nuna akwai.


Cup dinsa ya ajiye gaba daya jikinsa yai sanyi, Dady yana murmushi yace “ Khalid nagode sosai sosai, magana ta gaskiya tun farkon ganinka nai sha’awar dakewarka, jajircewarka da kuma nutsuwarka.

  Nagode sosai da ajiyeta agidanku da kai kafin nazo, zannan nagode sosai dan ta dalilinka ne muka shirya ni da ita.

A koda yaushe ina ma Addu’ar dace wa a rayuwarka, sai kayi hakuri da ita batasan yanda zata nuna jin dadi ko fadar magana yanda ya dace ba, duk laifi nane.

Ita ta raini kanta, har takai wannan matakin shiyasa a koda yaushe bata tunanin halin da dan uwanta zai shiga nata kawai ta sani, nasan zaka gyara mata halayenta, a matsayina na mahaifinta na gaza.”


Hawayensa ya share wanda suka dan gangaro ta kwarmin idansa.


Khalid kansa na kasa baice komai ba sai dai gaba daya jikinsa yayi sanyi, zuciyarsa duk ta karaya.


Dady ne ya cigaba “daga haduwarku da Zainab zuwa yanzu ta canza halaye da dama, duk da kai bazaka gani ba amma mu munsan ta canza wanda ita kanta batasan ta canza ba, shiyasa ina jin tace na san bakon na shiga fatan Allah yasa kaine.”


Yad’anyi ajiyar zuciya yace “nagode sosai da sosai Khalid, ina ji a jikina rayuwar da zatai yanzu bayan ta aureka rayuwace mai tattare da farin ciki da jin dadi, yau tun safe in na tuna hakan sai naji farin ciki.”


Aure? Abinda ya fada a ransa kenan da sauri ya kalli Dady.


Dady ne yai murmushi yace “Nagode sosai Khalid, ina tunanin yaushe kake ganin ya dace muga juna da iyayenka?”


Iyayena? Abinda ya fada kenan? Dady yce “eh, ko yayi wuri?”


Gaba daya Khalid ya rasa me zaice, Dady ne yace “ka duba ka gani, dan matsalar muna bacci muna tashi ne bamu san sanda rayuwarmu zata kare ba, sannan kullum lokacin mu kara tafiya yakeyi, muna rayuwa ne bama duba hakan, duk sanda mukai bacci muka tashi to fa kwana daya daga cikin rayuwarmu ta ragu ne, ya kamata a koda yaushe mu dinga tuna lokacinmu tafiya yake, bansan dogon buri amma ina fatan ganin jikana kafin tawa rayuwar ta kare.”


(Allah yasa mu cika da imani Ameen)


Jikin Khalid ne yai sanyi sosai, me zaice? Ta ina zai iya cewa wani abu a wannan yanayin?


Dady ne ya kalleshi tare da mai murmushi yace “ me kake gani in ka kwana anan? Akwai BQ a ta baya, gobe sai ka koma?”


Khalid yace “ a’a bakomai zan wuce dan anjima.”


Dady yace “to ko musai flight ticket? Dan tafiyar akwai nisa.”


Khalid yai murmushi yace “bakomai zan koma a mota.”


Dady bai musa ba ya jinjina kai yace “ba laifi hakan.” Agoggo ya kalla, yace “dole zan koma office inada meeting nan da 10min, bani number dinka, sannan in ka isa ka sanar damu ka isa lafiya, sanda kuka gaya dace na haduwar sai ku fadamana.”


Amsar wayar yai ya samai sannan ya kira wayarsa ya mika mai.


Dady ya amsa cikin jin dadi ya mike yana cewa “kaci snacks din.”


Khalid ya mike shima yana mai sallama, hannunsa Dady ya kamo wanda hakan yasa Khalid kallansa, Dady cikin jin dadi yace “nagode.”


Juyawa yai ya fita Khalid ya zauna akan kujera tare da sa hannu ya rufe fuskarsa yana tunani abinda ke faruwa.


********


Zainab najin alamar fitowar Dady daga falo ta gangaro da gudu dan dama sallah kawai tai a daki ta fito tana jiransa, sai dai kafin ta sauko ya fice.


Mikewa khalid yai ya dan shiga toilet din dake falan ya kuskure bakinsa sannan ya tada sallah.


Zainab tana ganin ya tafi tai falo da sauri inda Basma take, kallanta tai tace “Hmm Dady yace miki wani abu?”


Tace “a’a wani abin ya faru ne?”


Tace “a’a”


Juyawa tai gaba daya tana san fahimtar meke faruwa ita dai batace ma Dady siriki ba bako tace, yaushe sunan bako ya koma miji? Da wani ido kuma zata sake kallansa? Salan ya kara maka mata wata bakar maganar?


Hannuta tasa tadan dafa goshinta sannan ta nufi falan.


Jin tayi sallama shiru yasa tadan turo kofar, ruku’u yake lokacin, ido ta zubamai haka kawai ta samu kanta da kallansa, a hankali ta dan lumshe idanunta sannan ta tsaya a jikin kofar.


Bayan ya idar ne ya kalli inda take, shi kansa ido ya zuba mata kawai ya samu kansa da mata addu’a samun farin ciki a rayuwarta.


Idanunta ta bude kamar wanda akace ta juyo suka hada ido, da sauri ya janye nasa idan itama ta dauke nata tare da shigowa ciki.


Daga can kujerar farko ta zauna a saman hannun kujerar kallansa tai da idanunta yan madaidaita, ta bude bakinta wanda yake dan karami cikin yanayin burin kunya tace “me Dady ya ce ma?”


Mikewa yai yana nike sallayar yace “abinda kika cemai?”


Juyowa tai tace “abinda nacemai?”


Dan kansa ya karkatar yace “badai cemin zakiyi bakice komai ba?”


Hade fuska tai tace “kaji na musa?”


Kallanta ya sakeyi yana tuno kalaman mahaifinta yace “Hakan kikeso?”


Mefa?


Ki aureni saboda aikinki?


Dakewa tai tace “eh.”


Kai ya jinjina yace “okay, let’s get married.”


Kallansa tai da sauri, wani murmushin takaici ya saki yace “amma karkiyi tunanin na amince saboda wani tunani naki na can daban, sannan na amince saboda mahaifinki ba ke ba, sannan na amince ne saboda ni karan kaina.”


Idanu gaba daya ta zuba mai, yace “aiki? Kiyi aiki har ila masha Allah, sai dai zan sanar dake abu biyu, abu na farko bazanyi aiki a tv station dinki ba in ma harta kama zanyi sai dai nabi sawon masu jarabawa nayi in naci na fara, sannan abu na biyu, gidanki bazan zauna a ciki ba in har kuma na zauna a ciki to zan tambayi nawa ne kudin hayar gidanki, in har naga zan iya shima kenan in ba haka ba sai dai ki hakura da gidan, sannan abu na karshe....”


Shiru yai yana kallanta, wacce itama kallansa take, yace “wannan sai bayan auran zan fada miki.”


Yana kaiwa nan ya dau wayarsa tare da nufota hanyar waje.


Sai daya zo daf da ita tace “Bazaka tabi bari koda wasa ai nasara akanka ba?”


Tsayawa yai ya kallo gefen da take zuciyarshi na kara takaici auren da take neman yi da shi saboda aikinta.


Kallanta yai yace “meyasa kika auri Adam?”


Shiru tai shima bai nemi amsar ta ba yace “ meyasa kika dau aure abin wasan yara?”


Yaushe nace ma haka?


Dan kansa ya juyar kadan tare da dawo dashi inda take yai yace “ inba wasan yara ba kin auri Adam saboda kina san samun mijin da zaki juya wanda bazai nemi hanaki aikinki ba wanda zai zama karkashinki bazai taba yi miki magana akan yawan aikin da kike ba, ba haka bane?”


Bata rai tai matuka bakinta ya shiga rawa, ta kafeshi da ido, yace “ni kuma yanzu kina neman yi dani saboda ba wani wanda kike gani a kusa? Ba haka bane?”


Mikewa tai a zuciye tace “haka nacema?”


Juyowa yai gaba daya yace “ba hakan bane? Ke da kanki kikace saboda aikinki, sannan kika bani damar yin aure sanda naso ba haka bane?”

Zuciyarta ce ta shiga tafasa tana sauketa, tace “ko hakan ne sai ka fadamin ta wannan muryar?”


Murmushi yai yace “oh na manta ashe ke order kika saba badawa bakya san a baki, amma ya zamuyi? Dan nima ba abinda na tsana irin a dinga bani order balle akan rayuwata.”


Cikin kufula tace “In bakayi kace bakayi sai ka fadamin kalamai marasa dadi?”


Ido ya zuba mata, yace “me kike tunani?”


Haushi ne ya kara cikata ji take kamar tai ihu saboda yanda zuciyarta ke tafasa.


Kasa cigaba tai saboda yanayin rauni da zuciyarta tai, kallanta yai shima tashi zuciyar na rauni yace “am sorry in kinji zafi, but ko zan sake maimaitawa abinda zan fada kenan, nagode da karba kirki kimin godiya, zan wuce.”


Tana tsaye har ya fita daga falan, shiru yai bayan ya rufe kofar, na mata tsauri? Abinda ya tambayi kansa kenan, yawon bakinsa ya hadiya sannan ya fita, yaso yace tawa matar babansu magana suyi sallama amma baisan ya sake shiga dan kila sai sun sake wani fadan.


Fita yai kawai ya bar gidan ya nufi tasha.


******


Zainab kam ko kafa daya ta kasa dagawa tana maimaita kalaman Khalid, cikin kufula ta fito tai sama da sauri tana shiga daki ta rufo kofar da key ta kwanta akan gado.


Tunda take a rayuwarta an taba fada mata bakaken kalamai irin na yau?


Meyasa ta cigaba da tsayawa tanajin kalamansa masu kona mata rai? Ai da sai tabar gun.


Idanunta ne suka ciciko kawai ta samu kanta da zubar da kwalla.


(Khalid gaskiya ka kama kanka🙄)


**********


Haka ya shiga mota yana tafe gaba daya zuciyarsa ba dadi, taya zata tunkareshi da aure saboda aikinta? Kenan haka sukai da Adam?


Meyasa take sa aiki a saman aurenta?


Idanunsa ya rufe zuciyarsa duk a dagule.


**********


Wanke kwanuka take a bakin rijiyar amma hankalinta nakan su Asabe dake cin dan wake, cikinta ne yai wani kara, takaici ya kamata wannan tsinaniyar Safiyan ta basu dubu goma tace zata kara musu amma gashi har yau sati daya kenan basuda ko sisi a gidan.


Kallansu Asabe tai wanda suka dauke kai gefe suma suna jin haushin ta, dan sanda sunada kudi haka zasu jiyo kamshin abinci amma ko yar mitsilar roba bata taba san musu ba dan haka itama lokacin ramawarta ne.


Cikin daki ta shiga Adam ta gani a zaune akan katifarsa, rike da waya haushi ya kamata ta kasa kusa dashi ta talle keyarsa.


Dagowa yai da sauri yace “Goggo lafiyarki? Wai ni ya na zama saurayi amma baki da aiki sai makeni?”


Wani banzan kallo tamai tace “saurayi agidan uban wa? Ka tashi ka nemo mana abinci ko sai na saka a gaba nata maka?”


Ina zan nemo?


Tace “nikam mun shiga uku bama zancen abinci ya kamata muyi ba zancen kudin haya ya kamata muyi, jibi kace ko?”


Yace “eh yazakiyi yanzu?”


“Ya zanyi? Da yake ni kadai nake zama ba dole ka fadamin zancen banza ba.”


Kallanta yai yace “to ai ni kinsan bani da hanyar damun kudi.”


Kallansa tai tace “Adam me kake gani in kace wannan Safiya ko Afaro take ta nemoma aiki?”


Kallanta yai, yace “ko?”


Tace “eh mana ba kace Driver din nan take so ba zata iya komai akansa? Ka hada yar dabara kace zaka hadasu a zance kadan cafki rabanka.”


Kai ya jinjina yace “aikam to amma wani irin aiki? Nifa kinsan bansan aikin wahala nafisan na ganni a zaune a gikin makeken office dina ina juyi akan kujera, ga sanyi AC na kadani, in na taso daga mota na wuce gun Matata Zainab na dauko nasara a mora mu dawo......”


Kansa ta sake tallewa tace “kai dai bakada hankali wlh, naga randa hankali zai shiga jikinka.”


Kwanciya yai rigingine yace “Goggo?”


Meye?


Dan Allah Zainab bata hadu ba? Duk da ba fara bace sosai amma ba baka bace can, sannan tanada dan kumarinta dai dai, ga dan tsayinta daidai, ga idanunta yar caras........”


Kamin shiru ko sai na sa muciya nai ta makama? Dan ubanka kasan da hakan kaje kai lalata da wata can kedara? Banda haske me tafi Zainab? Sannan yanzu kazo ka sani a gaba kana min tatsuniya?


Ajiyar zuciya yai, tace “maganar nan dana ma wlh ta tafi da komai na cikina, Adam taimaka ka samo mana ko bread ne mu cucusa, yasin yunwa zatamin illa.”


Kawo lace dinki.


Shiru tai tace “in zani wani gurin in sa me?”


Yace “kisa atamfa dolene sai kinsa wannan?”


Cikin takaici tace “Allah sarki Zainab sai dai kawai naga kudi ko kaya, wannan wannan ni dai ka cuceni wlh.”


Adam yace “kawo lace nidai dan nima yunwa ta gama tattare ni.”


Haka Goggo ta dauko lace din, tana ja Adam na ja haka ya fizge yai waje dashi.


Zama tai cikin takaici da jin haushin rayuwarsu.


******

Ayusher🏌🏻‍♀


*******

[12/23, 9:37 PM] +234 706 813 0709: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


Gaisuwa da Godiya gareki Maman Haneef 🥰ZeeKhalid na gaisuwa🤝

Ina kike Twins din Zainab😉? Tana godiya da zazzafan kaunarki gareta, jiya har rasa bakin magana tai da ina zanzaro mata tsananin kaunar da kike mata🤪Aka Biebie


{50}


Duk yanda yaso yau bacci ya daukeshi ya kasayi sai juyi yake akan dan karamin gadansa, ganin bacci yaki daukansa kawai ya mike ya fara karatun Qur’ani, cikin falalar karatun yaji bacci ya daukeshi.


Yana sallar asuba ya wuce daga can zuwa gun aikin da zasuyi, ya riga kowa zuwa haka ya fara aikin kafin su karaso har sai karfe 1, ya wuce cafe ya dukufa neman aiki, yana gamawa ya wuce shagon dayake zama sai magrib lis ya dawo.


A tsakargida ya tadda su Umma, sunyi dan malele ana zaune ana ci da yaji da manja suna hirarsu.


Yana shiga suka kalleshi cikin kulawa, karasowa yai ya xauna a gefen tabarma yana dariya yace “Umma yau kuma dan malele ake ci?”


“Kai dama ba kwanan ka anan, ga dai shinkafarkacan da wake aci lafiya.” Umma ta fada tana kallan Abba tacigaba “ku dai maza wlh sai a hankali, ni banga me dan malele yai ba.”


Abba ne ya kalli Khalid yana dariya tare da rage sautin radio dinsa yace “ku dai tunda kunaso kuci ni kam da inci abin nan gwara a bani kwadan kanzo.”


Khalid ya dauko kwanan sa da spoon ya zauna yana kallan su Amir da ko magana basayi sai cin abinsu, Asiya ya kalla wacce ta buda yaji dayawa a nata dai shishitun yaji take yace “sannu wannan uban yaji haka?”


Ruwa tasha tace “Yaya yaji.”


Zama yai tare da ajiye ledar bread din daya siyo, ya sa spoon yai shiru tunda yakai loma daya bai sake sa wani ba da alama ya tafi wani tunanin daban.


Umma ce ta kalli Abba, shima ya kalleta sannan suka maida kallansu kan Khalid.


Umma tace “Khalid lafiya?”


Kallansu yai yas murmushi sannan ya dau spoon din ya cigaba da ci.


Sai daya gama yasha ruwa ya shiga dakinsa yai sallah sannan ya dawo, lokacin daga Umma sai Abba a wajen, su Amir anyi bacci da alama Asiya tana daki.


Zama yai sannan ya kalli Abba sannan ya kalli Umma yace “Abba akwai abinda nake san fada muku.”


Hankulansu suka maida kanshi gaba dayansu, shiru yadanyi kafin ya dago yace “Umma me kuke gani in na kawo muku sirika nan kusa?”


Kallan Abba tai tace “sirika?” Da sauri ta sake cewa “aure?”


Dan kansa ya sosa tare da dan kallan Abba.


Dariya Umma tasa cikin jin dadi tace masha Allah, burin mu ya kusa ciki, masha Allah.


Abba cikin jin dadi yace “kayi tunani kyau, a ina take?”


Dan kallansa yai yace “kun santa.”


Mun santa? Suka fada a tare, yace “Zainab.”


Yanayin fuskar Umma ce ta canza tace “Zainab?”


Yace “Umm!”


Abba ne ya kalleta sannan ya kalli Khalid yace “tashi kaje.”


Mikewa Khalid yai cikin rashin fahimtar me Umma take nufi.

Kallanta Abba yai bayan yaga tafiyar Khalid yace “meke faruwa?”

Kallansa tai tace “ina san Zainab har raina kaima ka sani amma Khalid fa bai taba aure ba?”


Ajiyar zuciya Abba yai yace “ku mata kuna da taku matsalar, sai kuso mutum kamar me amma daga ta hadoku da ‘ya’ya sai ku fara canzawa, sam akan ‘ya’yan cikin ku sai ku nemi rufe ido, dan bazawara ce sai akai me? Ko kin manta Annabi da ita ya fara?”


Shiru tai kafin tace “nayi kuskure, nagode daka ganar dani”


Murmushi yai yace “nasan yanda kike san Zainab nasan kuma san da kike ma Khalid ne yasaki tunanin haka amma tunda shi yasan haka yake san auranta sai mumai fatan alkairi.”


Kai ta daga cikin gamsuwa da jin dadi, mikewa tai ta nufi dakin Khalid din.


Yana zauna yana duba wasu takardu dayai printing na wani aiki da zai cike.


Umma ce ta sallama sai daya amsa sannan ta bude labulen, mikewa yai yace “Umma inzo ne?”


Shigowa tai ta zauna a bakin gado tace “Abuja kaje jiyan?”


Kai ya daga mata alamar eh


Kalansa tai cikin jin dadi tace “dazu na katseka akwai abinda kake san sanar damu ko?”


Kallanta yai yana daga xaune a kasa yace “Eh bayan ma dawo ne nama Dady text akan ma dawo shine ya kirani bayan mun gaisa yake cewa na tambayeku lokacin da za’aje gaisuwa, sannan wai in ba damuwa da sa rana ayi a lokaci daya saboda yanayin nisan garin.”


Cikin gamsuwa ta jinjina kai tace “zamuyi magana da Abbanka, amma ya zakayi da abin lefe? Tunda yanaso a sa rana?”


Bakomai insha Allah.


Kai ta jinjina cikin gamsuwa tace “bari naje gun Abban naka.”


Mikewa tai ta fita, shiru yai kafin ya cigaba da abinda yakeyi, yau ma aga gun sallah ya wuce.


********


Dady ne ya kalli Basma yace “Zainab fa?”


Tana daki, bansan meke faruwa ba ko saukowa bata sanyi, sai dai ko abinci tana dauka take komawa, nadai je saman tace ba abinda ke damunta.


Kallan kofa yai sannan ya dau wayarsa ya kirata, tana kwance cikin bargo ta daga, dady yace “Zainab sauko kasa.”

To kawai tace ya kashe.


Mikewa tai kamar mara lafiya ta sa mayafinta akanta, ta sauka kasa.


Dady na zaune shi kadai a falan ta shiga.

Durkusawa tai kusa da inda yake, kallanta yai yace “meye hakan? Ji fuskarki? Ko bakida lafiya ne?”


Kallan Dady tai tana kokarin yin magana dai dai takaici ya hanata.


Kallanta yai yace “ke da Khalid ne? Dan ban taba ganin Zainab ta rasa abin cewa ba.”


Shiru tai kafin ta kalleshi cikin takaici tace “Wai bazai zauna a gidana ba sai dai ya biyani haya, sannan wai aiki ma sai yayi jarabawa ko me?”


Ta fada cikin kuluwa, dan wannan kalmar ko tunota tai sai taji komai nata ya tsaya guri daya.


Kallanta Dady yai kawai bai san sanda ya fashe da dariya ba yana kallanta.


Tace “Dady?”


Dariya yake ya tsagaita yana tunanin yaushe dayai dariya irin haka, yace “ke da cemai kikai ya zauna a gidanki? Sannan yai aiki a kasanki?”


Tace “ba hakan bane ya dace?”


Kallanta yai yace “da me kikaso ya ce miki? To Hajiya naji na gode ko me?”


Shiru tai kafin tace “nasan bazai ce haka ba amma amsarsa ce ban taba zata ba.”


Kallanta yai yace “Jin wannan abu yasa na kara yadda da Khalid, ba shakka shi kike nema a rayuwarki.”


Dady?


Kallanta yai yace “Tashi kije ki ci abinci”


Shiru tai kafin ta mike dan ta kula so yake ta tafi, tana fita ya daga wayarsa ya kira Khalid.


Khalid nahanyar komawa gida wayarsa tai ringing dauka yai ya gaishe da Dady.


Dady ya amsa cikin jin dadi yace “ko kana hanya ne? Naji kamar karar mota?”

Khalid yace “eh amma yanzu zan sauka.”


Dady yace “daga gun aiki?”

Yace “eh.”

“Wani aiki kake yi yanzu?”


“Ina zuwa garage, ina tare shago sannan ina aikin gini.”

Yanda yai maganar da Confidence dinsa yasa Dady jin dadi yace “masha Allah ba laifi, kunyi maganar?”


Yace “eh zan kiraka yanzu in naje gida kuyi magana.”


Cikin gamsuwa yace “Math kai ko?”

Eh

Dady yace “Akwai wani abokina dake aiki a bank, bansan ko da yanda za’ai ba nasan yanada mutane dayawa a banks na nan kano, zan tambayeshi in har ba damuwa daga gunka.”


Shiru Khalid yai dan baisan me zaice ba, Dady yai dariya yace “karka damu ka cancanta ne bawai dan na sanka ba, dan yanada tsauri bazai bari abaka aikiba ba tare da kanada jarabawa mai kyau ba, sannan kasan harkar kasar tamu duk yanda kai in har ba hanya a banza zai tashi, ba tabbatar wahalar dakasha gun karatu bazaka so ta tafi a banza ba.”


Bai jira yace wani abu ba yace “sannan sirri ne tsakanin mu dakai.”


Khalid yace “nagode Dady.”


Murmushi Dady yai yace “sannan na fahimceka taya zakai aiki a kasan matarka? Bayan ita tayi zurfi a aikin? Sannan kai ba abinda ka karanta ba kenan, ta fika sanin komai a fanni, duk wanda yazo kallan wanda ke kasan matarsa zai maka.”


Khalid yai murmushi yace “nagode da fahimta.”


Dady ne yace “maganar lefe dan Allah karkayi”


Khalid yace “dady ayi hakuri abarni nayi, ni nake san yi.”


Shiru dady yai yana kara san yaran a ransa, yace “shikenan tunda kai kake san hakan, in yaso in ta tare sai ka bata, angode sosai.”


Khalid yace “nine da godiya nagode sosai.”


“Ka turo min takardun ka ta email zan turo ma yanzu, inkaje gidan mayi waya da mahaifin naka.”


Khalid yace to angode cikin girmamawa.


Dady yace “sai na jika, in ba damuwa ka kirata.”


Nan sukai sallama, kallan wayar yai maimakon ya kirata kawai sai yai text yace “na dade da isowa lafiya.”


Tana zaune tana cin abinci tai karo da sakon, cikin takaici tace “banaji na tambaya.”


“Au tunda baki tambaya ba na goge maganar.”


Takaici ne ya kara makureta ta kira wayarsa, yana kokarin sauka daga mota ya daga.


Yana dagawa tace “na cikin wayata fa?”


“Sai ki danna delete”


“Cikin takaici tace “banda hannu.”


“Wanda kika kira dashi fa?”


Haushi ne ya tiketa ta kashe wayar, cila ta tai kan gado ta cije lebanta cikin takaici.


Zuciyarta ce tace “kinsan halinsa ai meyasa zuciyarki ta zabe shi?”


Shiru tai tana tunani kafin tace “saboda ni dashi akama laifi? Saboda shikadai nasan bazai cuceni ba? Ya akai nasan hakan?”


Ganin ta rasa amsa kawai ta jigina kanta da gado cikin takaici abubuwan da take kunsa na Khalid.


******


Tundaga wannan rana basu sake ko waya ba itakam fa dukufa sosai gun shirya abubuwan aikin da zata fara, shi kuma yana ta famar neman kudi, har Kawo Idris da yan uwan Abba suka zo garin Abuja, Abba kam ba halin zuwa, duk da yaso zuwa sai dai Dady ne ya hanashi saboda kafarsa.


Su Kawo Idris kam an koma da gulma a baki ganin zabgegen gida da irin uban hidimar da aka shirya musu, Matansu kam sunsha xance kai kace mata ne.

Wani kanin kawo ma cewa yai auren Jari su Khalid kesan yi.


Ansa rana wata biyu saboda Dady yace jan abin bashi da wani amfani tunda dai sun aminta da juna to ai abinda za’ai.


Khalid kam yai kokari dan Dady har fada sai dayamai na bada kudin gaisuwa dubu dari dayai.

Wanda a zahiri yasha wahala matuka kafin ya hada wannan kudi, tun asuba in ya fita aiki sai dare yake dawowa, sannan da weekend ma daina zama yai aiki yake fita, wani sa’in har sai goma yake dawowa gida.


  Zainab kam takaici ya gama isarta na ko sako balle waya ba abinda yake shiga tsakaninsu ga gidansu sai wani shirin biki ake tun balle Dady, sai dai in ta tuna aikinta sai taji komai ya mata daidai dan dama saboda shi take san aure, tunda ta samu ba abinda take nema.


Dady ya sanarwa Abokinsa anyi dace dan takardunsa ya birge Mutumin, cikin jin dadi ya kira abokinsa a Zenith bank ya sanar mai, sannan ya fadawa Dady sai dai ya faro daga kasa dan baisan harkar zallunci.


Dady ya nuna shima hakan yake so.


**********


Kayansu yake cillowa waje, Goggo sai hakuri take bashi, Malam Salau kam ya rufe ido yace “wlh yau sai kum bar gidan nan ko za’a mutu ko kanin ubana bazan barshi har yai wata kusa biyu bai bani ficika ba.”


Goggo tace “kayi hakuri munyi magana da wata tace “zata samomai aiki.”


Wannan damuwarku ce ba tawa ba ni tawa daya ce ku hada kwamutsenku ku barmin gida, banda tsiya ma me kuke dashi daga katifa sai tv, na rasa uban me ake da tv gida ba komai, koma tv din yanzu zan tafi da ita ma rage zafin kudina.”


Adam ne yace “Malam ka shiga hankalinka da ci mana zarafi bafa matsiyata ka samu ba.”


“Yo ai ku da matsiyatan fakirai bakuda maraba.”


Yaja kofar dakin ya garkame da kwado ya fida daga gidan.


Kallan juna sukai tace “Adam ya zamuyi? Haryanzu bata kiraka ba?”


Bata nan ne sunyi tafiya da mahaifinta suna Ko Paris?


“Faras? Ni meya damen da wani Faras? Tazo ta taimakemu mudai dan Allah.


Nikam yau munshiga uku ina zamu nufa.”


Adam yai ajiyar zuciya na takaici.


*******


Dady ne ya kalli Zainab ya mika mata kudin, kallansa tai tace “ duk na meye?”


Gashi nan dai ya kawo, nima sai dana mai fada yayi yawa.


Kallan kudin tai, jikinta ne duk yai sanyi ta amsa.

Dady yace “kinga ana gobe biki su Nabila da Nusaiba zasu dawo.”


Kai kawai ta daga ta mike ta dawo daki.


A hankali ta bude ledar da aka nade kudin dashi, kallan yan dubu daidai din tai mai dasu tai ta rufe ta bude drawer ta ajiye sannan tai shiru, kafin ta jawo laptop dinta ya cigaba da shirye shiryen aikinta da take tayi a kwanakin nan..........


Eheeeeeem🤸🏻‍♂🤸🏻‍♂🤸🏻‍♂

An fa.................


*******

Ayusher🏌🏻‍♀

[12/25, 7:20 PM] Maman Zara: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


........Ahhh na fara lissafoku naga ina neman shanye rabin shafin😆😆


Thanks for the Love🤝

*THE QUEEN BEE (My 🥰🥰🥰)

*ZAUREN BIEBIE (Your Second page💋)*

*HUGUMA CONSERVATION ROOM*

*MASARAUTAR BILLYNABDUL*

*KUNDIN HASKE*


Much Love🤝 Khaleed da Zee na gaisuwa🤸🏻‍♂Goggo kam ta dau list din masu ce ma danta mau kwakwalar 🐟


{51}


Yana zaune a kasa a dakinsa daga shi sai wango dogo, hannunsa rike da rub na aboniki yana shafawa saboda uban aiki dayai kwanakin nan, kullum da ciwon jiki yake kwana.


Sallama yaji a bakin kofa hakan yasa ya amsa tare da sa farar vest din dake gefe yana cewa "Salmanu shigo."


Shigowa Salmanu yai ya kalli hannunsa yana dariya yace "in jikinka baiyi ciwo ba na waye zaiyi?" Yai maganar yana amsar man zafin aboniki da ke hannunsa.


Khaleed ya kalleshi yace  "goben zamu shiga kanon?"


"Eh, kama mutumin magana?"


"Eh tun jiya.”


"amma kanada key din ne?"


"Ta waje zai duba ai."


Salmanu ne ya kalleshi yana dariya yace "tab to daki nawa ne a gidan?"


"Ina na sani kona taba shiga ne?"


Shiru Salmanu yai ya kafe Khalid da ido, Khalid yace "menene kuma?"


Salmanu cikin zargi yace "anya soyayya kuke da ita?"


Cikin waskewa da neman kare kai yace "ji wani zancen banza, kuma nake shirin aurenta?"


Salmanu yace "to abin ne da mamaki, ni ko waya ban taba gani kunayi ba, sannan gashi ka kasa tambayarta daki nawa ne a gidanta?"


Shiru Khalid yai kafin ya kalleshi yace "Nifa so nake gobe mu duba wasu gidajen ba wai waccen ba, dan bazan iya biya ba nama sani sannan ba san zama nake a ciki ba."


Salmanu yace "kai dai ka fiya tsauri wlh meye a ciki dan ka yi a gidan matarka?"


Khalid yai shiru bai ce komai ba, Salmanu ya sake cewa "daga kunyi aure kai da ita ai kun zama daya."


A hankali yace "hmm aikinta ta zama daya dashi dai."

Salmanu yace "mekace?”


Khalid ya dauke kai, su Umma sunyi maganar kudin sunyi yawa ko?"


"A'a dan tasan saboda ba halin yin lefe a yanzu ne yasa na dage sai dana hadasu, so nake yanzu na fara tara kudin gida, inyaso in anyi auren na hada lefen."


Salmanu yai ajiyar zuciya yace "Aiki na gabanka, da alama kafin ka gama komai wannan bayan naka sai ya kusa b'allewa."


Haka suka cigaba da tattauna har ya tafi bayan dare yadanyi.....


Da rana suka shiga cikin kano, mutumin da Dady ya hadasu suka fara nufa gidan Zainab, tundaga wajen gidan yace "gaskiya wannan sai yakai kusan dubu dari biyu duk shekara, nan Khalid yace "akwai wasu mu duba?"


Nan suka shiga motarsa, tafiya kadan sukai suka dan ko minti biyar basuyi ba ya tsaya a wani gida, kallan Khalid yai yace "bansan ko wannan zai ma ba."


Saukowa sukai dukansu suka shiga gidan, saban gida ne dan kana ganinshi zakasan ba wanda ya taba zama a cikinsa, dan karami ne madaidaici.


Kana shiga gate din farfajijiyar gidan ce inda za'a iya ajiye mota biyu amma a matse, mota daya a wadace, sai cikin flat din gidan, babban falo ne a gun marasa hali, sai toilet a cikin falan.

Akwai kofofin guda biyu daga jikin falan, daya daki ne madaidaici dauke da toilet dinsa, inka fito kuma dayar kofar dan corridor ne, daga cikin corridor din kofar store da kitchen ne a hade, in ka fito kuma a kwai wata kofa ta daya dakin.


Khalid kam gidan ya dauki hankalinsa dan karami ne mai kyau da tsari matuka, kallan mutumin yai yace "shi kuma nawa?”


Kallansa yai yace “kaganshi dai sabone, shi dubu dari ne duk shekara.”


Shiru Khalid yai, Salmanu yace “ka dan tambayi me gidan ya dan rage mana”


Waya ya dauka ya dan kira kafin ya kallesu, yace “dubu casa’in da biyar yace in ba haka ba ku barshi.”


Shiru Khalid yai yana lissafi akansa, ya nuna musu wasu gidajen a karshe dai wannan din Khalid ya amince da wannan saban.


A hanya Salmanu yace “ka kaita gida gunsu Umma mana kafin ka tsaya da kafarka.”


Khalid yai shiru aransa yace ta ina zan kaita a yanzu da aikinta kadai ta sani? Ya tabbatar duk yanda su Umma ke santa in sukaga bata damu dashi ba sai aikinta a hankali zuciyarsu zata fara canzawa dan wannan hali ne na dan Adam.


Ya dau hotunan gidan ya tura mata ta waya, yana gani sun tafi ya kashe wayarsa gaba daya ya wuce gun aiki.


*******


A zabure ta mike zaune tna kara zooming din hoton, nan ta shiga danna mai waya amma wayar a

kashe, da sauri ta sauko kasa ta nufi bangaren Dady, yana zaune dan yau asabar yana waya da alama da dan uwansa yake yana sanar dasu biki da kuma rashin taro da Zainab keso.


Yana gamawa ya kalleta yace “Zainab? Lafiya.”


Kallansa tai kamar zatai magana sai samun kanta tai da cewa “bakomai dama maganar rashin taron nazo tunama.”


Nan ta juya daki, zama tai a bakin gado tana kara kallan hotunan, nikam ko na janye ne? Bafa a dole, akan me zan zauna yana juyani yanda yaso? In nan yake san zama sai ya kirani ya fadamin, amma baya turon sako ya kashe wayarsa ba.


Zuciyarta ce tace “wayar da ba amiki bace ta baki haushi ko gidan?”


Cikin takaici ta kifa wayar tare da dafa kai.


******


Wasa wasa abu yazo, gidan Ango ne ake ta hidimar karbar baki, shikam Ango yana can hidimar kwadago.


Yau saura kwana biyu daurin aure suna ta shirin zuwa garin Abuja, dan saboda nisa Dady yace suzo a mota daya ya isa, tunda a massalaci za’a daura auren, anayi da rana yazo ya dau matarsa a motarta su tafi.


Yau Khalid ya samu kira daga bank na Zenith dake kan titin Naibawa, cikin addu’oi yaje interview, bayan sun gama sukace yaje zasu kirashi, haka ya taho cikin tsananin farin ciki da fatan dacewa, yau kuma ha sanar da Abba halin da ake ciki, Abba kam ya tausayamai ganin yanda ya dinga kula dasu sun buda baki sun dauka yana aiki, wanda hakan ne yasa ko maganar kudi sunyi yawa basu mai ba dan sun dauka na aikinsa ne.


Sai dai jin yaje interview yasa ya shiga addu’a yace zai sanar da Umma in dare yayi saboda yawan mutane da suka hallara.


Bangaren Amarya kam har fada sukai da Basma dan kunya tasa tana ta neman jan Zainab a jiki, sai hade hade take kawo mata wanda gaba daya yasa Zainab kuluwa, tun tana amsa ba musu har abin ya fara bata haushi.


Su Nabile da Nusaiba kam murna kamar zai kashesu, dan ma haushinsu ba taro, sunso an sha dinner su cashe, yau tunda suka dawo suka sa Zainab a gaba da tambaya.


Aunty ina kuka hadu?

Aunty a ina yake aiki?

Aunty yaushe kuka fara soyayya?


Zainab kam ko kala batace musu ba, kallan Nabila tai tace “Yaran nan Allah baku da kunya wato yaushe muka fara soyayya?”


Nusaiba tace “Ni wlh ba aurenki yanzu ba takaicina baza’a barmu muje gidanki ba wannan zuwan ni kuma Allah Uncle nake san gani.”


Gaban Zainab ne ya fadi, dan sam ta manta da wannan shiriritar ta Nusaiba, kallanta tai da sauri tace “Da gaske kike wai sanshi kike?”


Nusaiba ta kalleta tare da rufe fuska, Nabila tasa dariya tace “Hauka maganinta Allah”


A zuciye ta dadama Nabila dundu, sannan ta ruga a guje.


Zata bita Zainab ta kamo hannunta, kallanta tai tace “Dagaske take wai?”


Nabila tace “kinga haukar da take a school? Duk littafanta sunanshi ne a jiki.”


Idanu Zainab ta fito dashi, Nabila tace “menene? Kinsan dai shirmene da yarinta, sanda taji sunansu daya da wanda zaki aura bakiga murna ba.0


Zainab ta girgiza kai a hankali tace “bashi ke damuna ba....Nabila....Khalid din da take so ne..”


Tai shiru tana kallan Nabila wacce tace “mene?”


Shiru Zainab tai cikin wani yanayi.


Nabila tace “Khalid da take so?”


Kai ta daga mata shiru Nabila tai kafin tace “yarintace ita ke damunta ai baiko san tanayi ba.”


“Ita nake ji? Tunani za’ai da sanina nai hakan.”


Dariya tai tace “Mamanta?”


Shiru Zainab tai, Nabila tace “shareta jibi in zaizo daukanki zan janyeta daga gidan, in tazo hutu ne dai bansan yanda za’a kare ba.”


“Gwara ki barta ta ganshi yafi sauki akan taje gidan ta ganshi.”


*******


Da yake Dady kudi ya turama Aunth daga kano taje ta mata jere hakan yasa komai yazo da sauki, sai dai Aunty kam ko ita tayi gulmar karamin gidan ganin yanda take da gida da kuma yanda suke da kudi.


Sai dai Dady ne data kira tanawa maganar yace “ba ruwanshi itama kuma ba ruwanta da shiga abin su.”


******


Yau tun duku duku suka shirya tsaf suka dau hanyar Abuja, a gida kuwa ta hada kayanta tsaf, tana murnar barin xaman daki ta koma tai aiki balle yanzu da takejin wani nishadi da ba a kasan wasu zata kasance ba.


Sun iso garin Abuja wajen karfe 11 na safe, sauka ta girma da daraja suka samu a bangaren su Dady, dan ya gayyaci yan uwansa dake nan gari da abokansa.


Haka sukai karin kumallo anan, bayan sun gama cin abinci ne aka kawo motoci sua tafi masallaci da za’a daura auren.


Tana zaune a daki, tana jiyo yan uwan Basma dana Dady suna ta hayaniya a kasa, duk da ance ba taro amma na kusa sun samu sun hallara, itakam tundaga gaisuwa ta dawo dakinta.


Tana zaune cikin material mai yanayin lace, fuskarta dauke da wani hadi na kwai da wata matar kanin Dady tazo ta lafta mata, haushi duk ya bi ya isheta ta mike tana kokarin shiga toilet ta wanke taji an turo kofa bako sallama.


Ta juyo da san yin fada taga Nusaiba da gudu tana hakki, kallanta tai tace “lafiya?”


Nusaiba tana dariya tace “an daura, yanzu Dady ya kira.”


Haushi ne ya kamata ta kalli wayarta, dauka to ta bude bako missed call bare text.


Kallan Nusaiba tai kawai ta wuce toilet ta hau wanke fuska cikin zafin rai take gurza fuskarta, sai dataji zafi ya fara kamata sannan ta cire kaya ta sake wanka.


Tana kokarin sa Atamfa kawai sai ga matar data yabba mata hadin nan, kallanta tai tace “Maman Kulthum kimin hakuri yanzu nai wanka.”


Dariya tai tace “ba na dazu bane, wannan turaruka na kawo miki.”


Amsa tai da sauri dan itakam tana san harkar kamshi, lumshe ido tai tace  “kai kamshin dadi.”


Mika mata dayan tai tace “ki shafa na jiki ne.”


Nagode, ta fada tana kara shinshinawa, juyawa tai ta fita tana dan tabe baki (Allah ya shirya mutanen mu a fuska faran faran a zuciya sai hassada da kyashi🤦🏻‍♀)


***********


Tawagar daurin aure sun dawo suka zauna a falan Dady suna hira, Basma ce ta kalli Nabila tace “Nabila ke da Nusaiba kuzo ku kai snacks din nan.”


Nabila ce ta kalli Nusaiba tace “bashi kawai zan kai.”


Tab ai ni ba kaiwar bane damuwata burina naga ango.


Nabila kamar zata sake magana sai ta fasa, shiru tai suka dau tire din sukai cike.

Sanye suke da kaya irin daya abin sha’awa.


Haka suka shiga suka ajiye, Khalid dake zaune kusa da Dady daga dan gefe ga Salmanu a kusa dashi ta kalla dan yanayin shigarsa kadai zai sa kasan shine Angon.


Sakar tire din kasa tai, da sauri Dady yace “Nusaiba lafiya?”


Jikinta ne ya shiga rawa tana kallan Khalid wanda ya sakar mata murmushi, ya maida kansa kan Nabila yana ganin tsantsar kamarsu da Zainab.


Nabila ta ja hannunta suka fita, suna fita falo ta fizge hannunta ta hau sama da gudu.


Dakin Zainab ta shiga wacce ta gama sa kaya tai sallah tana zaune rike da waya ranta a matukar bace, ai ko mage ka aura ka sanar da ita an daura? Abinda ta fada a ranta kenan cikin takaici.


Nusaiba ta gani ta banko kofa, ta kalleta tace “naga randa za’a dinga sallama in xa’a shigo.”


Nusaiba ta tsaya a kanta tace “Aunty mutumin daya sa babbar riga fara da hula baka shine mijinki?”


“Ina na ganshi dazan san meya....”


Shiru tai data tuna, Nusaiba tace “Khalid din da kika aura Uncle dina ne?”


Zainab tasa hannu ta jawota ta zaunar da ita kusa da ita, Nusaiba hawaye ne ya zubo mata.


Zainab tace “da gaske kike san Khalid?”


Kallanta tai tace “da gaske nake Aunty.”


Zainab tai murmushi tace “shekararki nawa shima Shekararsa nawa? Sannan ra’ayinki ne ke kadai Nusaiba, Allah yayi mijin yayarki ne, bazaki hakura dashi ba?Aunty tayi laifi bata sanar dake tun farko ba, Zaki yafemin?”


Hawaye ne ya shiga zubo mata tace “amma kinsan ina sanshi ai.”


Murmushi tai tace “na sani amma ina zan bari ki hada harkar rayuwarki da mai hali irin nashi?”


Kallanta tai tacigaba “kiyi hakuri har Ki girma Allah ya fito miki da mijinki kinji?”


Baki ya bude kawai ta fashe da kuka.


Nabila dake tsaye a jikin kofa ta kallesu, kai ta girgiza tace “Nusaiba kina fama da hau......”


Harararta Zainab tai, Nusaiba kam kuka kawai takeyi, haka ta bar gun Zainab ta wuce dakin Basma ta kwanta tana ta kuka.


Su kawu Idris wajen karfe d’aya suka taho, Khalid sai da aka watse ya sanar da Dady yanda sukai a gun interview, Dady cikin jin dadi yace “masha Allah, insha Allah za’a dace, nima nan da wata daya nake san zuwa ka rakani na gaida mahaifinka, sannan ina san zuwa muje a duba inda ya dace a bude broadcasting station din.”


Khalid yace “Allah ya kaimu, ya jikin?”


Dady yai murmushi yace “jiki yayi sauki Alhamdulila, ina godiya da gudunmawar samun sauki.”


Khalid yai kasa dakai yana murmushi, yushe zaku wuce?


Tambayar da Dady yamai ne yasa yace “sanda ta gama shiryawa.”


Dady yace “ka kirata kaji sanda ta gama, kar itama ya zama jiranku take.”


Mikewa yai ba musu ya dan fita waje.


“yaushe zaki gama?”


Ha ha ha.... abinda tai kenan tana gama karantawa.

“Ba lokaci.” Ta maidamai murtani ta ajiye wayar tare da zubawa wayar ido cikin takaici.


Ganin ba reply yasa tace “kaji inda dadi.”


Khalid kam dawowa yai ciki ya kalli Dady yai dan kasa dakai yace “minti 30.”


Dady ya kalli Agoggo yace “gwara ku tafi da wuri kam, dan da naso ku tafi a jirgi to amma motar dole sai am kaita daga baya, ga Mamman ya fara girma abubuwan na mai yawa.”


Khalid yace “bakomai wlh.”


Haka Dady yadan basu guri ya nufi dakinsa.


Waya ya daga ya kira Zainab yace tasameshi a daki.


Mikewa tai ta nufi dakin yana zaune akan kujera ta shiga.


Cikin jin dadi yake kallanta har ta durkusa gefensa.


Murmushi yai yace “nanda minti 30 kika ce zaku wuce ko?”


Kallansa tai dan batasan sanda akai hakan ba, jitai Dady yace “nasan saboda kinasan muyi magana kikace hakan.”


Murmushi tai batace komai ba, a ranta tace tanan ka bulo?


Dady ya kalleta yace “Zainab dan Allah ki dubi maraicin ki ki kula da auranki da mutuncin ki? Karki bari aiki da san kanki yafi komai tasiri a rayuwarki, na san Khalid zai kula dake matuka, dan haka kema ki bashi kulawar daya dace, kina gani bai taba aureba amma ya zabeki. Dan haka kiyi kokarin kyautatamai, kinsan bashi dashi amma zuciyrshi a wadace take, dan haka karki zama mai nuna mai rashinsa, kinji?”


To kawai tace dan batasan ma mezatace ba, haka ta taso tai daki tana shiga Nabila na shigowa tace “za’a saukar mata da kaya.”


Haka aka sauka da kaya sannan ta kara gyarawa ta yafa mayafi ta fito, Maman Kulthum ta gyara mata mayafi tadan rufe mata fuska.


Kallan Basma tai tace “Nusaiba fa?”


Tana daki bansan meya faru ba take ta kuka, Nabila tace kila rashin Aunty takeyi.


Dariya sukai aka fita da ita.


Khalid na jikin motar suka fito, bude musu kofa yai aka shiga da ita, Salmanu ya shiga mazaunin driver, shi kuma ya zagaya ya zauna kusa da ita aka rufe motar suka wuce.


Tunda suka dau hanya ba wanda yace ma wani kalla, Salmanu kam mamakin wannan Amarya da Ango din duk ya hanshi sukuni, text tamai ta cikin mayafinta “Zaman nan ya ishen i need my Ipad.”


Yana kallan text din ya dan matso saitin kunnenta cikin rad’a yace “batirin agoggon ya mutu, sai ki kira mu samu shago mu sai wani mu sa mai Hajiya Amarya.”


Ya daga tare da kwantar da kansa jikin kujera ya rufe ido, cikin kuluwa ta rasa abinda zata ce gashi ya matsa, waya ta dauka tace “nice agoggon?”


Kallan text din yai sannan ya maida mata “akwai wani agoggn bayan kene?”


Cikin kuluwa ta kalleshi ta mayafi, kafada ya daga mata sannan ya maida idanunsa ya kulle.


Hannayenta ta damke cikin takaici.....


Nace yanzu aka fara🤪


********


Yanzu Hindu ni kike fadawa haka?


“An fada miki din, in Kinyi zuciya ki kwashi kafarki ki bar mana gida, ni wannan abu ya isheni nan kika wulakantamu saboda ‘yancinki da sirikarki yanzu kuma kinzo kin takura mana.”


Naji kuyi hakuri ku barni na zauna


Shiru tai tana tuno kwanan waje da sukai cikin uban sauro da sanyi, uban wahalar data sha a kano har ta samu yar dari biyu ta karaso kura, gani take ko me za’a mata ai bazata tafi ba, zata jira har yar banzar yarinyar dake Farans ta dawo ta ba Adam aiki duk ta fanshe wulakancin da ake musu.


Adam kam a kano ya zauna yana zaune a soron Kamalu suna lalabawa, yace in Afreey ta dawo zai biyashi kudinshi, dan shikam jira yake ta dawo tamai dabarun da zai maida Zainab (Hauka maganinta Allah)


*********


Wata irin mika tai tare da ajiyar zuciya, sun glass din dake kan fuskarta ta zare ta na janye da akwatinta, murmushi ta saki ta kalli Abbi tare da cewa “Abbi ji nake kamar inyi ihu dan murna.”


Murmushi yai yace “meyasa kika damu da dawowa? Kida naso kiyi wata uku zuwa hudu? In aikinki ne kinsan a ajiye kike.”


Murmushi tai tace “ba aiki bane mijina zan dauka.”


Dariya yai yace “Allah yasa da gaske”


Miji😟? Jama’a ina yake?😳


******

Ayusher🏌🏻‍♀

*******

Tunda nake typing ban taba mai yawan wannan ba, saura kuce nayi kadan🥺su O’O☹

[12/26, 9:22 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


*Hauwa Saleh Allah ya kawo lafiya yasa kaffara ne🤢*

{52}


Idanunsa na rufe baisan sanda bacci yai gaba dashi ba, kwanakin nan kam yana bukatar hutu.


Zainab kam a zaune take kawai sai daddana waya take, har ta gaji tai shiru tanajin wakar Nura M.Inuwa dake tashi a cikin motar.


*****


Dady dake waya ne yace “ka tabbatar bai gane ba?”


“Ina zan bari ya gane? Sannan da alama baisan kan abubuwan ba, shiyasa bai kawo komai ba.”


Murmushi Dady yai yace “nagode sosai.”


Bakomai Alhaji mune da godiya, gashi ka sai gidan marayun nan.”


Nan sukai sallama ya kashe wayar yana murmushi, shiyasa baibi tagun Khalid ba gun hadashi da mai gidajen yabi ta hanyar Abbansa cikin dabara wanda shima ya tabbatar bai kawo komai a ransa ba, tunda basu san kudinsa ba bakuma suzo ba, duk labari kuwa yana zama shirme ne wani sa’in, yasan Khalid a yanzu bazai iya biyan gidan Zainab ba, sanan baisan ya sa jikinsa yin sanyi in har yaji asalin kudin gidanta, shiyasa yai wannan dabarar, ya rage wannan ya rage saban gida ta yanda bazaiyi tunanin komai ba.


*********

Karfe 8 na dare suka iso gidan..


Suna shiga gidan Salmanu ya ajiyesu sannan ya gangara unguwar ya nemi gun mai nama ya siyo kaza da yoghurt, dawowa yai ya dau waya ya kira Khalid.


Acan kuwa cikin daki suka shiga Zainab ta zauna a bakin gado, sannan ta sa hannu tana kokarin zare mayafinta, jin hannun Khalid tai akan hannunta.


Gabanta ne ya fadi, hannunta ya sauke mata sannan ya daga mata mayafin, sannan ya matsa kadan, a hankali ta dago idanunta ta kalleshi, gani tai kansa na kan waya da alama sako yake yi.


A hankali ta shiga yima dakin kallo, Khalid kam ya gama yima Dady da Abba text akan sun iso amma idansa na kan wayar har lokacin, ta gefe yake kallanta yana san sanin yanayin da Zainab zata dau gidan.


“Ina ne toilet?”  Tambayar datai kenan, nuna mata yai da kai hakan yasa ta mike ta nufi toilet din.


Alwala tai bayan ta gama kawai ta samu kanta da tsayawa a bandakin, jin yanayin take daban, da gaske fa yanzu shi mijinta ne ko? Anya bata dauko  ruwan dafa kanta ba?


Khalid ne ya amsa wayarsa dake kara, nan ya fita, tana ji an rufe kofa alamar fita ta fito daga toilet din, shiru tai tana kallan dakin sosai Aunth tayi kokarin gun shirya dakin, farin gado ne sai dai labulayen jikin dakin kalar sarararin samaniya ne,dan karamin dakin yayi kyau, dan karamin carpet din dakun ma kalar labulen ne, yayi kyau kwarai da gaske, kawai dai dakin ne karami a gun masu hali irin su Zainab kenan.


Jin knocking tai sannan ya bude, kallanta yai sannan ya ajiye ledar a drawer din gefen gadon, kallanta yai, ita ma daidai nan ta dago, suna kallan juna ta zare idanta da sauri, tana san cewa abin sallah da hijab amma sam ta kasa, meke damuna? Tambayar da ta shiga yima kanta kenan.


Khalid ne ya wuce toilet din, yana shiga ya saki wani lalausan murmushi, sannan ya dauro alwala ya fito.


Tana nan inda ya barta, ganin yafito ta daure tace “abin sallah.”


Kallan dakin yai yace “bansan inda suka ajiye ba sai dai mu duba.”


Nan ya mike yana dubawa, kallanta yai tana zaune, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa yana bude wardrobe ya ganta a ciki.


Ajiye wa yai, akwatinta ta zuge ta ciro hijab sannan ta shimfida sallayar ta daga hannu zata tada sallah.


Jin hannunsa tai a kugunta saura kiris numfashinta ya dauke dan tafiya yai na wucin gadi, janta baya yai sannan ya dawo ya tsaya a gabanta ya fara tada harama.


Da kyar ta daidaita numfashinta tabi bayansa, sai da suka idar sukai addu’oi sannan ta mike kallanta yai yace “ga abinci can Salmanu ya kawo miko mana.”


Kallansa tai sannan ta kalli ledar, alama ya mata da ta miko da kai, fuska a hade ta nufi gun ledar ta jawota da karfi, kallanta yai yace “ajiye ki zauna.”


Tace “a ina?”


Kallan daya mata ne yasa ta ajiye ta zauna fuska a hade, bude ledar naman yai sannan ya jawo hannunta yasa a ciki, kallansa ta sakeyi cikin wani yanayin da ita kadai ta sani.


Daukan cinya tai tana mamakin ko kunya baya yi ya sakata gaba yana cin abinci.


Itakam da kyar ta ci cinya daya, kallanta yai yace “kunya kike?”


Kunyar wa?


Kallan dakin yai yace “shi nake san ji ganin ba kowa a ciki.”


Shiru tai ta dau wani ta karaci, yana kokarin mikewa aka dauke wutar nepa.


Da sauri tace “mekenan?”


Kallanta yai bai tanka ba ya kunna filitar wayarsa tare da cewa “namanta bansai fitila ba, ko na nemo kendir?”


Tace “dan tada mana generator dan inada aikin yi ma tun jiya naso yi bansamu nustuwa ba.”


Ransa ya sosu ya kalleta yace “banda Generator dan haka sai ki jira aikinki sai sanda suka dawo da wuta, in kin matso ko cikin dare sai ki yanka ki tashi kiyi.”


Hankali a tashe ta kalleshi tace “haka zamu zauna?”


Yace “sosai.”


Da sauri ta mike tace “ina key?”


“Ina zaki?”


“Inje gidana na dauko namu generator din sai na taho da solar in yaso gobe a kira mai hadawa ya sa mana.”


Kallansa tai wanda haryanzu kallanta yake, tace “ina key din?”


Hannu yasa ya zaro mata a aljihunsa, amsa tai ta nufi kofa, komawa yai ya zauna akan gado, yana kallanta sai dataje bakin kofa yace “in kika kuskura kika fita daga kofar dakin nan..” sai kuma yai shiru, juyowa tai ta kalleshi kamar zatai magana taga yanda ya zuba mata ido fuskarsa a murtuke.


Ji tai ta kasa daga kafa, haushin kanta ya kamata tace “to ka taso muje.”


“Naki.”


“To haka zamu zauna?”


Wani kallo ya mata ya dauke kai, takaici ne ya kara rufeta ta tsaya a gun batada alamar dawowa.


Sun fi minti goma a wannan yanayi, kawai ya kalli wayarsa ganin karfe 9 har da rabi, gashi yana da aiki da safe kawai ya mike, kusa da ita yazo batai auni ba taji ya sungumeta.


Shure shure ta fara tana cewa “Khalid meye hakan?”


Kan gado yasauketa, kallansa tai tace “mene...........”

Gani tai ya zagaye ta da jikinsa, numfashinta ne ya shiga fita da sauri da sauri, ta kame kam kamar mara  rai, hannunsa yasa ta zagayenta ya zare pillow bai dago ba yace “pillow zan dauka.” Yai maganar cikin rad’a.


Gaba daya ta kasa maida mai martani saboda yanayin data samu kanta.


Mikewa yai tare da daukan pillow din,  falo yakai sannan ya dawo yai toilet da alama wanka yai, dan taji karar ruwa.

Gani tai ya fito daure da towel a kasansa, ido ta zaro da sauri ta juya baya tare da rufe kanta.


Da sauri ta kwanta ta juya baya, jallabiya yasa sannan ya kalleta yace “asuba fa gari.”


Kallansa tai tace “ina zaka?”


“In kin gama aikin naki kyayi bacci bana iya bacci ana dane dane.”


A zuciye tace “ta ina zan......”


Gani tai ya rufe kofa, haushi ya kamata ta cilo pillow din dake kusa da ita jikin kofar, gani tai an bude kofa, kallan pillow din dake bakin kofa yai, sannan ya mata alama da wayarsa.


Kallanta yai yaga tana wani cika ita a dole an bata mata rai, wayarsa ya dauka, har ya juya daga yanda ya ke ba tare da ya juyo inda take ba ya dau pillow din ya cilla ta baya sannan ya rufe kofar.


Hakoranta ta datse tana ji kamar ta saki ihu.


Wayarta ta dako ta kuna fitila, sannan ta jawo akwatin ta zaro laptop dinta tana fatan da charge, ganin charge full yasata jin wani sanyi, nan ta bude ta sa wifi na wayarta ta fara aikinta, tana yi tana hararar kofa kar kace wanda ake hararar yasan anayi.


Jin yunwa yasa ta jawo ragowar naman nan ta ci stsha yoghurt din, kallan time tai taga sha biyu saura, hamma tai sannan ta mike ta dau wayarta ta nufi falo.


Yana kwance akan kujera ya dugunkune da alama sanyi yakeji.


Harararsa tai sannan ta haske fuskarsa da fitilar a ranta tace “A haka kamar ba shi ba.” ganin yana dan motsi da idanunsa ne yasa tai saurin janye wayar.

Kallansa ta sake, sannan ta juya ciki, harta zauna sai kuma ta kalli bargon dake nade akan gadan.


“Badan halinka ba zan sa ma.” Ta fada tare da daukanshi ta nufi falan.


Yana kwance yana bacci, dan kwanakin nan wani irin baccin gajiya yake da har wani sa’in in ya farka sai yaji yana neman kasa tashi.


Sa mai bargon tai ta juya zata tafi, jitai a hankali ance “Thanks.”


Juyowa tai tace “idanka biyu?”


“No”


“Farkawa kai?”


“Maybe”


Baki sai iya fadan magana, ta fada a hankali, ji tai yace “kin gama na shiga dakin?”


Da sauri tace “a’a”


Tai saurin shiga ciki ta maida kofar ta rufe tana cewa “kaji mun mutum.”


Kaya ta cire sannan ta kwanta, haushi ne ya isheta tace “naga sanda zasu dawo da wutar nan.” Ta karasa da jan tsaki sannan ta kwanta ta dau wani bargon ta luluba.


*********


Wani irin gundun bala yasa tare da saurin daga wayar tsabar ya rikice sai cewa yai “Hajiya Ta Khaleed.”


Murmushi tai tace “Adam ina khaleed yake?”


Dariya yasa yce “bansani ba amma in kin bada umarni a nemo cikin minti ashirin za’a nemoshi.”


Cikin takaici tace “baka sa ido ba kenan? Ka manta nace ka kula da shi da Zainab kafin ma dawo?”


Dariya yasa yace “in banda abinki tana Abuja yana danbatta ina xan iya sa musu ido? Sannan nifa nasan Zainab Allah bazata iya hada harka da Khalid ba.”


Tsaki tai tace “naka shirmen kenan.”


Yace “Allah da gaske nake.”


Tace “ta hada harka dakai Balle Khalid mai cikar zati da haiba? Kana gani yanda na kasa ganin wani namiji a idona bayan shi.”


Haushi ne ya kamashi ya kalli dan jikinsa dayake dogo ne shi jiki ba kiba, yace “ai ba fadin kirji da kyau nake nufi ba hali nake nufi.”


Tsaki tai tace “yo kai halinka har akwai na birgewa?”


Takaici ya kara kamashi yai dariya yace “a nemoshi ne?”


Tace “eh ina san sanin inda yake yanzu.”


To maganar aikin kuma fa?


Tace “yanzu ba wani aiki a kusa dai dai in kura xata maida aniyarta.”


Name??


“Yanda kasa Khalid dina yin driver kaima kazo kamin.”


Mene?


In bakaso sai ka cigaba da yawon da takardun naka muga mai zaka samu.


Yace “Safiyah!”


Tace “me? Yanzu masu first class da second class uppper ma ya suka kare a neman aiki bare kuma su”


Bata jira yace wani abu ba tace “ka nemo min inda yake zuwa dare.”


Ta kashe wayarta.


Cikin takaici da bakin ciki yabi wayar da kallo.


*********

Sai karfe 11 ta farka daga bacci, wani dadi taji gajin fanka na kadawa, mikewa tai ta fito falan, ganin ba kowa a falan yasa ta shiga kallan gidan, kitchen ta nufa, tana cewa “ina yaje shi kuma?”


Ganin a kayan gara da Aunty ta siyo aka ajiye akwai kayan tea kawai ta dau cup tana kokarin kunna gas, sai dai me? Ganin wayar gas din tai a gefe alamar ba cylinder.


Wani hucin takaici ta saki kawai ta dau dibilan ta fito.


Wanka tai sannan ta sa Atamfa riga da skirt ta zauna a jikinta dam, ta zauna a kasa tana ci dibilan din tana duba aikinta na jiya.


Karfe daya ya gama aiki kudin account dinsa ya duba gaba daya dubu takwas ne ya rage mai, shiru yai sannan ya nufi gun masu generator jin tsada yasa ya sai fitila guda uku sannan ya siyo kayan miya da nama ya ya taho gida.


Har ya shigo batama sani ba ta dukufa tana ta aiki, wannan abu ya dan sosa ransa, kallanta yai tana ta aiki, yace “Dan taso.”


Juyowa tai tace “oh ka dawo?”


“Ummm taso.”


“Ahhh aiki........”


Ganin yanda ya maida kofar ya rufe yasa ta harari kofar tace “mutum sai tsinanan isa.”


Fitowa tai ta tsaya a jikin kofar tace “ya akai?”


“Muje.”


Ina?


Gani tai yayi gaba tai ajiyar zuciya tabi bayansa, kitchen ya shiga sannan ya ajiye ledojin hannunsa yace “kinci abinci ne?”


“No dibilan naci”


“Okay yunwa nake ji ki mana abinci.”


Yanzu? Bari na gama abinda nake zuwa d’an anji........


Idanu ya kafeta dashi, tace “zanyi wannan tsari gidan na meye?”


Shiru yai baice komai ba, yasan komai sai a hankali baisan hada abubuwa dayawa.


Kallansa tai tace “dame zanyi girkin? Ba cylinder”


Ga karamin gas mai cylinder nan na siyo.


Kallansa tak tace “bansan ya ake amfani dashi ba.”


“Then sai ki sani daga yanzu.”


Kallansa tai tace “aikuwa indomie zan dafa.”


“Ayya sorry bana cin indomie ko taliya.”


Ido ta zaro tace “mene?”


Kafada ya daga mata yace “Haka.”


Cikin jin haushi tace “me kake so nayi yanzu?”


Karasowa kusa da ita yai, hannu yasa ya dau lighter, daf da ita ya nufa, zuciyarta ta shiga harbawa da sauri, daf suke da juna har suna iya juyo numfashin juna hannunta dake sauke ya bude yasa lighter din sannan a hankali yace “shinkafa da miya? Tuwo da miya?”

Yai dan murmushi yana kallan yanda ta karkato fuska cikin bacin rai tana kallan sa yace “na sani inada sauki gashi na baki zabi sai ki zaba san ranki, na yafe ba sai kin min godiya ba.”


Ya juya, wani irin azababan takaici ne ya kamata, tana kallo ya bar kitchen din.


Lighter din hannunta ta kalla cikin takaici ta cilar da ita kasa sannan tabi bayansa.


Tana zuwa ta ganshi a falo yana dan mikar gajiya, tace “Khalid me kake nufi dani?”


Kallo me alamar tambaya ya mata, tace “munyi aure ne akan aikina akan me zaka sani girki me wahala bayan kasan abu nake?”


Kwanciya yai akan doguwar kujerar ya sa hannu saman goshinsa ya rufe ido, haushi ya turnuketa ji take kamar ta wuce daki.


Sai dai batasan ya akai ba taga ta juya kitchen.


Haka ta shiga aiki ranta a matukar bace.


Nace daga baya kenan🤪


******

Ayusher🏌🏻‍♀

*****

[12/28, 8:59 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{53}


Takaici ne ya kara kamata data kalli dan mitsilin gas din, ita ko ganin irinshi ma bata taba yi ba, haka ta hau kokarin kunawa sannanta fara yin shinkafa da miya, tanayi tana kwafa kai kace in ta gama dukan wanda ya sata zatai.


Haka ta share kusan awa biyu a kitchen saboda haushin fitowa takeyi, ga bakin cikin gas dan mitsili guda daya, tana gamawa ta jujuye a flask sannan ta fito daga kitchen din fuskarta a murtuke tam.


Yana jin motsinta bai bude idanunsa ba yace "ina Abincin?"


A kufule tace "yana kitchen."

Jeki kawo min.


Da sauri ta kalleshi tace "mene?"


Bude idanunsa yai ya juye saitin da take tsaye yace "wuce."


Tace "tab amma Allah kafi kowa iya wulakanci, in dafa ma abincin sannan kawo maka ma sai nayi? Bakada hannu ne?"


"Ina da shi yi ne bazan ba."


"Me kace?"


Neman wucewa daki tai ganin bashida niyar tankawa, yace "bakiji me nace ba?"


Juyowa tai ta kalleshi zuciyarta na wani irin tafasa na bakin ciki, tunda take ta taba kawo wa wani abinci?


Juyawa tai ta dauko tazota dire a gaban shi, yace "plate da spoon sannan ki taho da ruwa."


"Mai aikin ka ce ni?"


Wani kallo ya watsa mata wanda yasata mikewa tana cika tana batsewa taje ta dauko ta ajiye, tana neman juyawa yasa hannu ya rikota, kallansa tai tace "meye kuma?"


Kallan abincin yai ya kalleta, tace "meye?"


Kara kallan abincin yai ya kalleta, tace "badai kokarin cewa kake na zubama ba ko?"

"Haka!"


What?


Serving spoon ya mika mata, ta kafeshi da ido tana huce tace "Hannunka aiki me yake?"


Yace "bani da ra'ayin yi ne."


Ajiye wa tai tace "sai dai karkaci abinci."


Tana kokarin tafiya ya zauna cikin hanzari ya kamo hannunta ya jawota baya ta zauna akan cinyarsa, gabanta ne ya shiga harbawa da sauri da sauri, hannu yasa ya rikota ta gefen cikinta, tana kokarin kwace jikinta dankwalinta ya cire, saitin kunnenta yasa kansa yace "In sake magana?"


Dan juyowa tai gabanta na wani irin harbawa, yanda ta kalli idanunsa ne yasa ta kasa magana, a hankali tace "Amma abincin ma sai na sama?"


Yace "eh, haka nake so kuma dole kiyi."


Dole?


Ya daga kai alamar eh, kokarin kwace kanta ta shigayi, hannu yasa ya juyata tana kallan gefe sannan ya kalli fuskarta yace "in sake magana?"


Harara ta sakar mai cikin takaici idanunta suka ciciko tace "zan sama sakeni."


Saketa yai ta mike kamar zatai kuka haka ta zuba abincin nan, idanu ya zuba mata wani abu na taso mai, ji yake kamar ya kamota ya rungumeta ya lalasheta.


Tana gama zubawa ta kara harararsa tace "Banaji ko sarki yafika mulki."


Ta fada tare da juyawa, ta wuce daki ta banko kofa da karfi."


Murmushi ya saki sannan ya dau abinci yaci, sosai abincin yamai dadi, ga shi dama yunwa yakeji ya cinye wanda ta samai, ya sha ruwa, mikewa yai harzai kirata ta kwashe sai yaga bari yadan bata haka har zai kwashe kwanukan kawai ya barsu a gun.


Fitowa yai ya kalli kofar dakin kawai ya wuce ya fita.


Itakam da tunda ta dawo kwanciya tai a daki cikin takaici, tana jin ya fita ta sake yin kwafa ta mike ta fito.


Kallan kayan abincin tai a falo, mamaki ne ya kamata ta tsaya tana kallan kwanukan kafin tace "Amma mutumin nan ya rainamin wayau wlh."


Haka ta kwasa takai kitchen sannan ta zuba nata, tana kokarin shiga daki kawai taga an dauke wuta.


Wani kululun takaici ne ya kamata, inaaa bazata iya wannan zaman ba, kwana d'aya amma gaba daya tanajinsa kamar wata d'aya.


Waya ta dauka ta kalli number Dady ji take kamar ta kira, amma me? Me zatace? Itafa ta kawo Khalid da kanta, haushi ne ya isheta, ta kalli number Umma, me zatace mata? D'anta yaki bin umarninta? Haushi ne ya kamata kawai ta cila wayar kan gado ta zauna, tana cin abinci tana mita, ya fita bako irin na fita din nan.


Haka ta gamaci tai sallar la'asar ta dan jawo laptop dinta tana duduba plans din da take ta had'awa, awa d'aya da rabi laptop din ta mutu.


Ranta a matukar bace ta rufeta sannan ta zauna a kan gado, ganin ba wani abin birgewa bare nayi yasa ta fito falo ta zauna tai tagumi, nan ma taji zaman ba dadi ta mike ta bude kofar dake cikin falan, toilet ne? Ta fada tare da jawo kofar, kitchen tai tana kara kallan kitchen din, tana ditowa taga wata kofa a ta gefen kitchen, hannu tasa zata bude taji ta a kulle.


Dan kafa tasa tadan buge kofar, zafin dataji ne yasa tad'anyi kara, sannan ta rike kafar ta dawo falo, waya ta dauka ta rasa abinyi kawai ta hau nemo game, abin ma dariya ya bata dan bata taba tsintar kanta cikin irin wannan yanayin ba.


Hart fara game din taji bazata iya ba ta kira Khalid.


Yana gun garage, ya gama aikin wata mota kenan wayarsa tai kara, ya dade yana kallan sunan dake kiransa kafin ya daga.


Baice komai ba itama haushin baice komai ba yasa taki magana.


Sunkai minti daya a haka kafin yace "bye."


A kufule tace "bye?"


Yace "in ke bakida aikinyi ni ina da shi."


"In ni banda aikinyi? Waye ya maidani mara aikin yi in ba kaiba?"


"In mita kika kira zakiyi am sorry am not in the mood"


You are what?


Haka kawai jikinta yabata kashewa zaiyi da sauri tace "sun dauke wuta."


Baisan sanda yai murmushi ba wanda har ita ta jiyo sautin, tace "dariya kamin?"


Maybe?


A hasale tace "ina key dina? Na duba ban gani ba, yana nan a daki sai dai karki manta nike auranki kuma nace kar matata ta kuskura ta fita, kinfi kowa sanin abinda zan aikata." Bai jira tace komai ba ya kashe.


"Me za........."


Jin alamar an kashe wayar yasa tabi wayar da kallo, nashiga uku ni Zainab, me na auro wa kaina a kwana daya ana neman kasheni da raina?


Ajiye wayar tai, kamar zatai kuka ta fita waje tana ganin tsakar gidan, zuciyarta duk ba dadi.


**********


"Sir Am really sorry amma dan Allah karkace bazaka sake renewing din contract din nan ba, ka taimaka mana."


"Kabir kasan takaicin daka bani a watanni hudu da suka wuce? Fad'amin me na samu a watan nin nan?"


Director kabir yace "kayi hakuri zamu gyara matsalar yanzu duk yawanci programs din ne sun rage yin suna ba kamar da ba amma ina da plans sosai."


"In sun dameni kenan, meye amfanin plans ba kwararun masu kula dasu? Kafi kowa sanin sabida Zainab na amince na fara aiki daku, yanzu kuwa banaji zan cigaba."


Zai sake magana ya katseshi yace "ka nemi wani mungode."


Ya kashe wayarsa.


Director kabir ya mike tsaye cikin tashin hankalu dan babban inda suke samun kudi ne in har ya janye to lalai suna cikin tashin hankali.


Dole ya tambayi Afreey ko babanta zaisa baki.


**********


  A hankali ta dau takalmanta tana neman fita kofar gida.


Raziyya!


Cak ta tsaya, sannan ta juyo ta kalli Babanta tace "Baba kati zan siyo."


Dawo, ya fada yana kallanta.


Cikin shagwaba tace "Baba dan Allah ka barni na fita Allah yanzu zam dawo."


Dawo nace ko?


Komawa tai kamar zatai kuka, tai hanyar daki gun mamanta, ta turo baki gaba.


Mahaifinta ya bita da kallo yana mata fatan shiriya tare da godiya ga Allah dayasa ya dau mataki tun da ransa.


********


Tana zaune a tsakar gida ta baza uban tagumi tana kallan yanda Hanne ke ta faman tuka musu tuwon dawa, ga gefe Sadiya yarta ce ke ta wanke kayanta.


Ajiyar zuciya ta saki cikin mugun takaicin wannan rayuwa "Goggo Akuyoyi zasu cinye miki shanyar ki taliyar ki"


Da gudu ta tashi ta bisu, suna tafiya ta zauna agun kamar zatai kuka, yar taliyar mirjin da aka sanmata shine suke so su cinye mata.


Wayarta ta dako a lalitarta, ga bata da kudi ga Adam haryanzu bai ko kirata ya fada mata halin da ake ciki ba, itakam inta kara sati a kauyen nan to lalai ne za'ai asibiti da ita.


********


Gyangyadi ne ya fara daukanta tsabar ta rasa abinyi, tana zaune a falo bayan tayi sallar magrib, tun tana gyangyadi har bacci ya dauketa.


Wajen karfe 8 ya bude kofar ya shiga bakinsa dauke da sallama.


Fitilar wayarta ce a kunne a falan, a hankali ya tako zuwa inda take, kallan kyakyawar fuskarta dake bacci yai, a hankali wani sanyanyan murmushi ya bayyana a fuskarsa.


Ya zubawa fuskarta ido kawai yaga ta bude idanunta a hankali, a kanshi idanunta suka sauka.


Bata tashi daga yanda take dan kishinged'e a hannun kujerar ba tace "ka dawo?"


Sannu da zuwa ake cewa.


Dan baki ta motsa yace "ban taba tunanin kina baccin wuri haka ba."


Dan harararsa tai tace "laifin waye? Ko ni ban taba tunanin ina yi ba"


Kallansa tai tace "Kh......." sai kuma ta kasa karasa fadan sunan haka kawai taji sunan ya mata nauyi, yace "me?"


Tace "bazan iya rayuwa haka ba, Allah."


Kallanta yai yace "kinyi abincin dare?"


Da sauri ta mike zaune tace "me?"


Yace "ba dai mijinki zaki ba abincin rana a matsayin dare ba?"ya fada yana zama a kujerar da take.


Juyowa tai gaba daya tana kallansa tace "kana san cemin bayan abincin rana danama na dare ma daban zan ma?"


Hmm ba haka kikaga anayi ba?


Su da basu da abinyi kenan.


Ohhh ke me abinyi kinfi karfi kenan?ko naki auren da nasu ba d'aya bane?


Kallansa tai tace "Wai dan Allah meke damunka?"


Wani kallo ya mata tace "nama wani abin ne? I feel like kamar da saninka kake sani abu."


Yanzun ma baice komai ba, tace "kafi kowa sanin dalilin auran nan meyasa kakemin haka?"


Wani abu ya had'iya na takaici sannan ya kalleta, mikewa yai ya sa hannu ya fizgota.


Kalansa tai tace "menene kuma?"


Janta yai har daki ya zaunar da ita kan gado sannan ya zauna ya jawo hannunta ya matso da ita daf dashi, har numfashin juna suna ji, idanu ta d'ago wad'anda suka fara yin jaaa tace "me kake shirin yi?"


Idanunsa ya kalleta da su wanda suka nuna bacin rai sosai, hannu yasa a kafadar ta yai baya dasu suka kwanta a gadon zuciyarta na wani irin bugawa da karfi, yanda taga idanunsa ne tsoro ya kamata, ta kanta ya rukufo yace "in nuna miki dalilinki na aurena bashida tasiri a kaina?"


Cikin tsoro tace "daga ni."


In naki fa?


Idanunta ne suka ciciko tace "fadamin me na ma?"


Mikewa yai tare da kallanta, kawai ya juya zai fita.


Da sauri tasa hannu ta kamo rigarsa tace "na gaji bazan iya girki yanzu ba."


Juyowa yai ya kalleta yace "Nikuma nace abincin dare nake so."


Ba akwai shinkafa ba?


Bana san ci.


Ko baka so ka cusa haka ai wani sa'in abinci badan aji dadi ake ci ba, sannan ni na gaji Allah bazan iya rayuwar nan ba, ta ina zan zauna ba wuta ba aiki ni kenan a zaune a gida kamar kayan wanki?kwana dayan nan jinta nake kamar na shekara.


Baisan sanda yai wani murmushi ba yace "in kingaji me zakiyi?"


Kallansa tai kawai taji ta kasa magana, yace "yunwa nake ji."


Ya juya ya fita.


Wani kululun takaici ne ya kamata haka ta fito kamar zatai kuka ta shiga kitchen, ai yasin sai dai kaci macaroni ai bakacd baka cinsa ba, nan ta hau yi randa duk a bace.


Da gudu ya ganta ta fito daga kitchen mamaki ya kamashi, tai daki a guje ta jona charge sannan tasa dariya ita kadai tace "ku taimaken ku bar wutar nan ta kwana dan Allah."


Fitowa tai Khalid ya kalleta yanzu kam ya gane me ta ruga yi, guntse dariyarsa yai balle da yaga ta fito ta make irin ba abinda tai din nan ta wuce, tana gama abincin har zata fito tace "yanzu fa zaice in kaimai?"


Ranta a bace ta dako abincin ta ajiye mai tai daki da sauri.


Da kallo ya bita, sannan ya sake yin murmushi.


Dan bayansa ya mike tare da d'an bunugawa dan ba karamin ciwo yake mai ba, mikewa yai ya bude kofar tana xaune a kasa tana duba abu a laptop dinta gefe ga takardu nan ta baxa da alama aiki take sosai.


Har ya shiga toilet din dakin ya fito bata ko dago ba, kallanta yai yace "kinyi isha'i ne?"


Ba tare da ta dago ba tace "zan yi anjima, ai isha'i ce tana da tsawo."


Kamar zaiyi magana kawai ya juya ya fita, a falo yai sallah sannan yaci abincin.


Shiru yai yad'an kunna tv yana kallan labarai a ransa yace "banaji akwai Amarya da Ango irin mu" sannan yai wani murmushin da shi kadai yasan me yake nufi.


Har karfe tara da rabi yana nan a zaune.


Kafin ya kashe tv din.....


Har ya kwanta yaji sai juye yake ya kasa bacci, gaba d'aya bayansa ciwo yake ga kwanciyar kujerar wahala take mai.


Mikewa yai kawai ya nufi d'aki.


Tana zaune tana rubutu a takard'a, bai ko kulata ba ya hau kan gado ya ja bargo ya luluba ya rufe idanunsa.


D'an dagowa tai jin batajin motsinsa bayan kuma tasan ya shigo.


Ganinsa a kwance yasa tace "anan zaka kwana?"


Eh


Da sauri tace "nifa?"


Ina na sani?


Kallansa tai tace "sorry amma gaskiya bazai yiwu ba."


Bai bude ido ba yace "sorry amma gaskiya bazai yiwu ba."


Baki ta bude tace "waccen kofar dake rufe ta meye?"


D'akina ni na rufe shi.


D'aki?


Shine kake kwance anan?


Bansan hayaniya in zanyi bacci, sannan karki manta bansan karan dane danen keyboards.


Tace "ni kake nufi ma tafi falo kenan?"


Wannan ra'ayinki ne ba nawa ba.


Tace "dan Allah tashi, ko kuma kaban key din dakin."


Baiko kulata ba ya juya baya ya rufe idanunsa.


Wata harara ta nakamai, ji take kamar ta samu bayansa tai ta makamai duka.


Hannu tasa zata rubuta abu a laptop haka kawai ta samu kanta da kasa danna komai, bansan karar keyboards.


Haushin kanta ne ya kamata kawai ta mike ta fito falo, harta zauna kuma ta mike taje kofar dakin ta kalla sannan ta dawo.


Ganin ta ita kadai a falo, yasa taji bazata iya zama ba bawai dan tana tsoro ba dan dai batasaba da gidan ba tukun, dakin ta koma ta dau pillow ta rasa ina zata kwanta, takaicinta daya inta juya ta kalleshi taga yana bacci zuciyarsa d'aya.


Ji take kamar tasa kafa ta tureshi daga kan gadan, wata kwafa tai, har ta kwanta a kasa ta mike ta hau gadan tace "in na barma gadan ma kaci galaba akaina."


Nace na nawa kuma🤪

*********


Ayusher🏌🏻‍♀


*********[1/4, 11:58 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{54}


Wajen karfe biyar ya bude idanunsa jintayai, a hankali ya sa hannu ya dau wayarsa ya dan kuna fitila, tana kwance tana bacci, kallansa yai sannan ya kalleta, dukansu sun bai gefen gadan sun dawo tsakiya, ajiyar zuciya yad'anyi sannan ya mike ya shiga toilet, wanka yai sannan ya dauro alwala ya fito.


Jin motsin watsa ruwa yasa ta farka, wanka da asuba? Badai mafarki yai ba? Abinda yazo mata kenan, can kuma tace "mafarkin wa?"


Tana kwance harya fito, ganin hasken fitilar wayarsa yasa ta rufe ido tare da dan kallansa ta gefen ido.


Ganin saman jikinsa a bayyane yasa tai rufe idanunta cikin faduwar gaba, mai ya shafa sannan yasa kaya, wayarsa ya dauka yace "in kin gama leken kya tashi kiyi sallah."


Ido ta bude daga kwance tace "wai kasan na tashi?"


Bai juyoba yana sa turare yace "zan wuce gun aiki daga can."


Ido ta zaro tace "aiki daga sallar asuba?"


"Eh, kinada sako?"


Cikin mamaki tace "wani irin aiki ne wannan?"


Juyowa yai yace "zan dawo cin abincin rana da na dare, akwai komai?"


Mikrwa tai ta zauna akan gadan tace "ina tambayarka bakace komai ba."


"Dan kin tambayen sai ya zama dole na baki amsa? Ko ni dana tambayeki amsar kika ban kai tsaye?"


Ya karasa maganar yana daukan agogon sa yana sawa.


Shiru tai kafin tace "wani irin aiki kake haka?"


Kallanta yai yace "gini? Zaman shago? Kanikanci?"


Gini? Irin wannan? Ta tambaya tana nuna bangon dake jikin gadan.


Bai tanka taba ya karasa daura agogonsa.


Kallansa tai tace "akan me zakai irin wannan aikin?"


Yanzun ma bai tanka taba ya juya zai fita, da sauri ta sauko tace "meyasa kake irin wannan aikin?"


Juyowa yai ya kalleta, kallansa tai tace "kanikanci? Gini? Taya zakai irin wad'an nan aiyukan kamar wanda bakada yanda zakai?"


Kinasan sani?


Ido ta zubamai tana kallansa, alama ya mata da hannu akan ta matso, kallansa tai kawai ba tare da musu ba ta matsa taje dan so take taji me yake sashi yi.


Dan tsayawa tai kusa dashi hannu yasa ya jawota, kallansa tai ya jawota sosai jikinsu na hade da juna, yana kallanta tana kallansa, tace "Sakeni."


Yace "amsa zan baki."


Tace "sai ka rikeni sannan?"


"Naga aikinki ne kadai a ranki, komai baya zama inba shi ba shiyasa zan sanar dake yanda bazaki manta ba." Cikin magana mai kamar rad'a yai maganar.


Dan yawon bakinta ta had'iya tana kallansa.


Yace "ke meyasa kike aikinki?"


Kallansa tai tace "dan ina so."


Hmmm ya fad'a tare da dan jinjina kai yace "ni kuma dan ya dace."


"Ya dace? Kai aikin gini? Nace muyi aiki tare kaki ka tsaya......."


Kallan daya mata ne yasa tai shiru, saketa yai yace "na wuce."


Kallansa tai har ya bude kofa, tace "ka dau motata mana."


"Motarki kika ce ba tawa ba."


Ya wuce.


Da kallo ta bishi tace "wannan wani irin mutum ne? Ganin duhu ya mamaye ta yasa ta lalubo wayarta ta kunna sannan ta kunna fitilar daya siyo.


Zama tai a bakin gado tana kallan ginin gidan, irin wannan yake?


Jitai gaba daya ranta ya baci, da sauri ta jawo wayarta ya fara checkin din yanda masu gini ke aiki, wani kululun takaici ne ya rufeta ta mike ta shiga toilet, alwala tai sannan tai sallah.


Duk yanda taso bacci ya dauketa ta kasa, inta tuna gini da wani kanikanchi sai taji wani takaici ya rufeta, tsaki kuwa taja shi yafi cikin bucket, ganin ma ta kasa baccin yasa ta mike kawai ta dau wayarta ta kira dady.


Yana shiga office kenan lokacin data kira, gaisawa sukai cikin jin dadi yace "Zainabu."


Tace "Dady dan Allah kama Khalid magana."


Name kenan?


Gini fa yakeyi.


To sai akai me?kece kike yi ko shi?


Shiru tai tambayar kanta tai meye nawa a ciki? Muryar Dady ne ya katseta yace "sana'arsa ce ki daraja masa ita kamar yanda yake daraja abar shi."


Shiru tai kafin tace "Yasu Nabila?"


Yace "tana nan lfy, Nusaiba ce dai ba lafiya, tanata zazzabi tun daren da kika taho."


Shiru tai dan tasan dalilin zazzabin, Dady ne yace "badai wata matsalar ko? Dan ke nakeji."


Tace "nice uwar laifi ba? Wlh Dady dakaga abinda yake min......."


Sai kuma tai shiru, murmushi yai yace "xaman aure kike ai ba wasa ba, dan haka ayi biyayya."


Bafa Gen a gidan, ga wuta sai sunga dama, sannan....." zatai maganar gas taji ta kasa.


Idan Allah ya bashi hali zai saimuku gen din.


Shiru tai dan taga ba amfanin cigaba dan Dady baxai bata gaskiya ba taga alama.


Sun dan sake hira kafin suyi sallama, shiru tai ta fito falo toilet din falan ta kalla kenan jiya anan yai wanka ya wuce?


Kitchen ta shiga ta kalli gas din cikin jin haushi haka ta kunna shi ta hada tea ta fito, shiru tai tana kallan tea din, haka zaiyi aikin bai sha ko tea ba? Oho ai ba yaro bane shi inyaji yunwa ya nema.


********


Aiki tadan fara laptop din ta mutu, wanka tai ta sa riga da skirt na atamfa, harta kwanta zatai dan bacci ta tuna zancen abincin rana.


Tsaki tai sannan ta mike rai a bace ta shiga kitchen, sink ta kala taga ta hada wanke wanke nan ta hau yi da karfi rai a bace, tana gamawa ta kalli kiyar jiya, wata dariya ta saki cikin jin dadi ta daura tukunya, wake ta dafa da shinkafa tace kaci da miya.


Tana fitowa taga azahar tayi.


Kwan wuta ta kalla haryanzu ba wuta? Sallah tai ta zauna ta baza tagumi tana kallan falan, wayarta ta dauko tana dane dane kawai.


********


Khalid ne ya dan mike bayansa sannan yace "kudin yau lokaci na yayi."


Shugaban cikin jin dadi ya mikamai kudinshi yace "gaskiya Khalid kana birgeni da kokarin yin aikinka."


Kallansa Khalid yai yace "akwai inda ake saida gen tsoho?"


Yace "eh kaje kasuwar bata."


Okay nagode, juyawa yai ya wuce bata, yaji dadin ganin ya samu karamin gen a kudi kadan, haka ya siya ya hau adaidaita ya dawo gida.


Bai sanar da ita ya siyo ba kawai ya ajiye shi a waje ya shiga ciki.


Tanata game sanda ya shigo, kallanshi tai tace “ka......”


Wani kallo ya mata, ta hade fuska tace “Sannu da....”


Jin abin tai banbarakwai, bai tanka ta ba ya zauna a kan kujera.


Itama shiru tai sai dai ta ajiye wayar hannunta.


Sunfi minti biyar ba wanda yai ma wani magana, shi kuma ya sa aranshi harsai ta san abinda ya dace, ita kuma haushin yaki amsa mata yasa tai shiru.


Ganin sun kara kwashe wata minti biyar din yasa ta kalleshi, idanunshi baya kanta sai dai hankalinshi na kanta ya kuma san ta kalleshi.


A kufule tace “ai ka amsa min dai.”


Kallanta yai yace “in mijinki ya dawo a zaune kina abinda kike zakice sannu da?”


Ido ta zaro tace “me kake so nama? In tashi in rungumeka ince sannu da?”


“Wannan ma ba laifi bane, sai dai at least ki bada hankali akan dawowar.”


Kauda kai tai tare da hade fuska, bai ko kalleta ba shima yace “bani abinci naci zan koma.”


Kallansa ta sakeyi tace “wai kullum sai na kawoma?”


Magana kikeso na sake?


Fuska ta hade ta mike tsaye ranta a bace tai kitchen, dako abincin tai ta kawo ta ajiye mai, zata mike yace “kin manta?”


Kallansa tai tare da komawa ta dau serving spoon ta zuba kamar zatai kuka take ji, tana gamawa ta mike a kufule tai daki.


Baiko bi ta kanta ba ya fara cin abincin, yana gamawa ya d’au wayarsa ya kira Abba, sun yi hira kafin Abba yaba Umma.


Umma cikin jin dadi tace “ina Zainab? Inata san kira nace bari na d’an sarara.”


Dariya yai yace “tana nan lfy, bakizo kinga gida ba ke da Asiya.”


Zamuzo amma sai wani satin, murmushi yai sannan yace “ina yan ball?”


“Suna nan rashinka yasa sunkara kaimi gun fita.”


Dariya yad’anyi, daidai nan ta fito zata dau wayarta data bari a falo, kallansa tai yana dariya, a ranta tace “kamar gaske.”


Jitai yace “gata ma tana san ku gaisa.”


Kallansa tai tamai alama da hannunta wa?


Mika mata wayar yai, ta karaso ta amsa, ganin Ummata a jiki yasa tai saurin amsa cikin jin dadi tace “Umma!”


Daga can Umma ta saki fuska sosai tace “sirikata”


Zainab samun kanta tai da d’an jin kunya, gaida Umma tai, nan Umma ta shiga tambayanta gida.


Umma can tace “Zan zo ganin gida da sirikata amma yanzu banadan jin dadi sai wani satin.”


Da sauri tace “meya sameki Umma?”


Dariya Umma tai tace “gajiyar biki ce kawai, nake san hutawa.”


Murmushi tai tace “bakomai ki huta, muna nan muna jiranki.”


Nan suka kara hira cikin jin dadi kafin suyi sallama.


Kallanshi tai taga ya daure fuska kamar ba shi ba, wayarsa ta mikamai, amsa yai ba tare da yace mata komai ba ya mike yace “bani ruwa.”


Kallan ruwan tai dake kasanshi, tace “ka dauka mana gashi a gabanka.”


Mikon.


Baki ta saki tana kallanshi, tace da haka kace na baka kasha mana.


Kallanta yai yace “bani nasha.”


Ido ta zaro tace “wai dan Allah haka kake ko yanzu ne kake neman zama haka.”


“Bani”


Mikamai tai kallanta yai kawai taga ya bud’e baki, wai bakan kake nufi nai?


Eh.


Da sauri ta mikamai tace “nan gaba sha ma zakace nai naga alama.”


Ta juya, harzata shiga daki yace “sun kawo wuta?”


Kallansa ta juyo tai ta harareshi, ruwan yasha sannan yace “zan wuce.”


Cikin mamaki tace “daga dawowa?”


Eh na tsaya wani gurine nayi late.”


Shiru tadanyi kafin tace “ina san abu a can gidan.”


Menene?


“A kayanane.”


“In na dawo maje.”


Ya juya.


Da kallo ta bishi tace “kaine agoggon ai ba ni ba.”


Kallan kwanukan tai tace “meye banbancina da mai aiki?”


Haushi ya isheta ta wuce ciki ba tare da ta kwashe ba.


Yana fita ya samu kansa da murmushin yana tuno sanda tace kace na baka mana.


*******


Da sauri ta dau wayar ganin sunan Adam, kafin ta dauka ta katse, hakan yasa tasan flashing ne.


kiransa tai tace “ka nemo inda yake?”


Afreey banda katin da zan kirashi.


Haushi ya kamata ta kashe wayar katin 1k ta tura mai Adam murna harda tsale, nan ya kira Khalid kai tsaye.


Khalid na kokarin shiga shagon wayar Adam ta shigo, dagawa yai dan dama yana nemanshi shima.


Adam yace “Khalid? Ina ka shiga ne? Inata nemanka?”


“Yaushe kake da lokaci akwai inda ya kamata kaje.”


Khalid ya fada ki tsaye, Adam yai dariya yace “Kwaro kai matsala ta dakai kenan komai naka serious, kana ina ne yanzu? Danbatta?”


“No ina kano nayi aure kwana biyu baya.”


Aure?


Adam yai tambayar cikin tsananin tashin hankali, shikenan Afreey ba shi ba samu daga gareta, hankali a tashe yace “kai uban me ya kaika aure bayan kasan da wacce ke jiranka.”


Baiyi mamaki ba dan ya saba da shirman Adam yace “Sorry Abba.”


Adam ya gane magana ya makamai yace “Khalid Afreey kila sai ta kasheni intaji.”


“Yaushe kake da time?”


Ina zamu? Gun Amarya?


A’a ka je Naibawa ka nemi yafiyarsu.


Yanayinsa ne ya canza yace “ina ka tare? Ina san zuwa ziyara.”


Ka tabbatar?


“Menene? Bakasan nunata?”


“Akan me zanyi hakan? Indai kai ka shirya ganinta to.”


Adam yace “Ai dole na nemi ganin matar kwaro.”


Khalid yace “ka samu kaje in har kanasan kwanciyar hankalinka da cigaban rayuwarka.”


“Naji zan duba.”


“Bye inada abinyi.”


Ya fada tare da kashe wayar.


Shiru Adam yai yana tunanin yanda zasu kare in Afreey taji lalai akwai tashin hankali, in kuma bai fada mataba ba shi ba neman d’an abu daga gareta.


*****


Sai magrib ya dawo, yana dawowa ya ga ba kowa a falan, kitchen ya wuce ya ajiye ledar kayan miya da nama da kuma lemon fata daya siyod’aki ya tura, tana zaune tana rubutu a takarda, tana ganin an bude kofar ta kalleshi, ganin yanda ya hade fuska yasa ta mike tace “Sannu da zuwa.” Yanda tai maganar kamar an sa mata goruba a baki ne ya dan bashi dariya sai dai baiyi ta ba yace “yauwa”


Kinyi abincin dare?


“Na tsaya abune in mun dawo nayi.”


Kin tsaya abu?


Eh, kaga, ta matso tana nunamai, dazu wata idea tazomin, me kake tunanin idan na ajiye wacce.”


Ta fada tana nunamai yanda ta tsatsada abin, kallan takardar yai sannan ya jinjina kai yace “kinfini sanin abin indai har kikaga hakan yafi to kiyi amfani dashi.”


Muje?


Ina?


Kace inka dawo zamu.


Alokacin dana dauka zakiyi abincin dare kenan.


Kallan mamaki tamai tace “yanzun ma in mun dawo zanyi ai.”


Wannan ra’ayinki ne, in kin gama tuwon kafin 8 maje.


Ido ta zaro tace “tuwo a daren nan?”


Kallanta yai ya tsare gida, kallansa tai tace “sai kai magana ka hade rai, taya zanyi tuwo a daren nan?”


“Wannan matsalarki ce ba tawa ba.”


Ya fada yana neman wuceta ya shiga ciki, da sauri tasha gabanshi tace “muje in mun dawo musai abu a hanya.”


“Banida ra’ayin yin hakan.”


Ido ta kafeshi dashi ranta a matukar bace, kalanta yai yace “matsa.”


Kin matsawa tai ta kara tare kofar da hannunta, kallanta yai yace “kinasan in nuna miki karfi?”


Taya zakace nai tuwo a daren nan? Bayan kai kace zamu gidana in ka dawo?


Kalanta yai bai ce komai ba, tace “meyasa kake min haka? Menama?” Tai maganar idanunta na cikowa.


Kallanta yai yace “kinsan yanda mace take a gidan mijinta? Kinsan abubuwan da wata macen take a gidan mijinta?”


Su kenan? Ni kasan me yasani...........


Bakinsa yasa kan lebanta ya ciza, itakam gaba daya numfashin ta ya dauke dif?


Kallanta yai yace “kada ki kuskura ki kara fadamin wannan kalmar, in kika sake kuma bansan me zai biyo baya ba”


Yana kaiwa ya matsar da ita ya wuce, har yayi gaba yace “ki wuce kiyi abinci, na ajiye nama da kayan miya a kitchen.”


Toilet ya shiga yana shiga ya furzar da wata iska.


Zainab kam da kyar ta daidaita kanta, shekarata hudu da Adam, ya akai ban taba samun kaina cikin wannan yanayin ba? Shi da yake saurayi? Nida nasan komai?


Samun kanta tai da wucewa kitchen ta daura ruwan tuwo.


Wayyo ni Zee na tuwo🥺


*****

Ayusher🏌🏻‍♀

[1/7, 11:27 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


"The emotion that can break your heart is sometimes"


#OneLove❣


*Gaisuwa yan AYUSHER FANS CLUB🥰*


{55}


Ruwa ya kuna, jin ruwan heater din ba zafi sosai yasa yasan yau ba'a kawo wuta ba.

Wanka yai a toilet din ya fito yasa jallabiya,yasa turare spray na turarensa Lynx sannan ya fito ya nufi waje yana jin mostinta a kitchen, kokarin zuba man daya taho da shi yai ya fara duba wayar gen din.


Karar dayaji ya fito daga ciki ne ya sashi shiga ciki da gudu, kitchen ya shiga, tuwon da take tukawa ne ya zubo mata a hannu ta kone, dagowa tai ta kalleshi idanunta sun ciciko, da sauri ya karaso ya rike hannun fitilar wayarsa ya kara haskawa bayan hasken fitilar kitchen din, ganin yanda gun yai ja yasa ya jata jikin sink ya fara zuba ruwa, kwace hannunta tai sannan ta juya zata koma gun tukin tuwon.


Hannu yasa ya kara riko saman hannunta, ya dawo da ita jikin fanfo hannun ta ta shiga kwacewa, tace "sakeni" tai maganar cikin rawar murya.


Bai kulata ba ya cigaba da zuban ruwan, yana gamawa ya fara mata addu'a a gun ganin ba zuma a gidan dan yaga haka umma keyi, sai yaga inta kone sai ta shafa zuma.


Kara fizge hannunta tai ta fara kokarin komawa gun tuwon.


Kafadarta ya kamo da karfi yace "ki bari mana, so kike ta tashi?"


Wani kallo tamai hawaye suka zubo mata tace "ta tashi din, ba dai tuwo kake so ba?"


Hannu yasa ya rage gas din sosai sannan yasa hannu ya jaa ta zuwa falo, suna zuwa ta kwace hannunta tana neman komawa, kara kamota yai, kallansa tai ta ce "sakeni" tai maganar cikin wani irin rauni.


Naki


Sakeni please ta fada hawaye na gangaro mata, naki nace


Karfi ta fara sawa tana kokarin kwace kanta hakan yasa ya ja ta jikinsa ya rungume, hannu tasa tana kokarin toreshi sai kuma kawai ta fashe da kuka.


Har cikin ransa yake jin kukanta, kuka take sosai hakan yasa gidan ba abinda kake ji sai kukanta da alama ta dade tana tarashi.


Sai datai mai isarta sannan ta dago ta kalleshi idanunsa sunyi jaaa sosai, tace “Bazan iya zaman nan ba Allah.”


Kallanta yai yace "ke yarinyace haryanzu? Shekararki nawa? Har sai yaushe zakisan aure ba wasan yara bane? Haka kikaga iyayenmu na yi?”


Hawaye ne ya gangaro mata tace "haka ake auren? Tunda nazo gidan nan banda aiki me kake sani? Tun asuba in ka fita sai rana sannan kana dawowa abinci kawai kake ci ka fita sai dare, ni kadai a gida kamar mayya? Kwana biyu zuwa uku jinsa nake kamar na shekara, bazan iya ba wlh, gashi kai kullum fada bafa fadan ke ban haushi ba ni da nake yin duk abinda ka sani haushin kaina nakeji, maidani gida dan Allah, na hakura da komai ma.”


Ta karasa maganar tare da kara zubo da hawaye, na tsawalla ne? Nasan bazata gyaru lokaci daya ba, na zafafa mata ne? Daga zuwa? Tambayar da zuciyrsa tamai kenan, amma ita ba yarinya bace sai yaushe zata daidaita kanta?


Dago fuskarta yai yasa hannu yana share mata kwallar.


Hannu tasa ta ture hannunsa tace "nasan ba damuwa kai dani ba ban kuma nemi hakan ba amma a kalla ka dinga........"


Bakinshi da taji cikin nata ne yasata yin shiru, lab'an bakinta ya tsotsa sannan ya kalleta, idanunta ne suka rarage girma tana kallansa cikin wani yanayi, a hankali ta bude baki zata sake magana ya kara sa bakinshi cikin nata, yanzu kam harshenta ya kamo, samun kanta tai da maida mai murtani, jin yanda yake mata salo ne yasa taji kafafunta na neman kasa daukanta, ganin yanda tad'an murguda kafa kad'an ne yasa ya dan turata jikin kujera, har a lokacin bakinsa na cikin nata suna sumbatar juna cikin wani yanayi yoo abinka da me aikin karfi balle an kai lokacin ba a d’ana ba🙊


A hankali ya dago ta ya bude idanunsa da sukai jaaa, itama idanunta ta bude a hankali tana kallansa, a hankali cikin magana mai kamar ta rad'a muryarsa a dan daushashe yace "bakyasan na dinga barinki ke kadai?" Yai tambayar yana kokarin ce mata zan yi kokarin ganin na baki lokaci na.


kallansa tai kawai sai jiyai tace "Ka dauko mana gen din........"


Duk da yasan abinda ke ranta kenan amma a wannan yanayi da yake kokarin fitarda hakkinsa bai kawo zaiji haka ba.


Kallanta yai yace "shine matsalarki kadai?"Yai tambayar cikin wani yanayi da duk wanda yaji zai san yayitane ta rashin jin dadi kalamanta.


Eh ta fad'a kai tsaye.


Wani murmushin takaici yai sannan ya daga ta yace "kiyi aiki har illa masha Allah."


Ya juya ya fita ya koma waje? da kallo ta bishi dan ya tado mata da sha'awar data manta da ita, me ya sameshi? Ko dayake shi me zai saneshi kullum ransa dama a bace yake.


Khalid kam a waje zuciyarshi takai matuka gun baci, hada gen din yai ya sa socket din ya tada, tana jin karar gen ta fito waje cikin jin dadi, ganin wuta ta bayyana yasata kallansa cikin jin dadi matuka.


Ko kallanta baiba ya wuce ciki, biyoshi tai tare da rufe kofa, tace "ashe ka siyo?"


Bai tanka taba ya wuce dakin.


Ganin yanda ya shiga yasa ta juya kitchen, da kyar ta kwashe tuwon saboda hannunta daga ta sashi gun zafi sai taji gun na zafi.


Haka taita duba kitchen din ganin kubewa bushashiya yasa ta kada ta kawo falo.


Daki ta shiga yayi sallar isha'i ya hau kan gado rigingine, ya riga ya taso da abinda bazai iya maidashi ba, na kai ma abincin, ta fada tana saurin matsawa gun laptop tana kokarin zama, ganin yaki motsawa yasa ta matso tace "na kai"

Ta fada tana dan tabashi dan ta dauka ko bacci yake.


Ganin bai motsa ba yasa a ranta tace “ya gaji ne?”


Juyawa tai har zata xauna sai kuma ta kalleshi ganin alamar bacci yake yasa ta cire kaya ta wuce toilet, dan taji duk kanshi abin girki takeyi.


Wanka tai ta daura zani tare da rufa mayafi a saman kanta, bude kofar tai ganin haryanzu yana nan a yanda yake yasa ta fito.


Taku biyu ya dago ganin yana bukatar fita waje, kallanta yai, itama ta kalleshi, sam ta manta yanayin da take tace “ka tashi?”


Wani abu ya hadiya, yana kallanta, ganin yanda idanunsa sukai ne yasa tace “bakajin dadi ne? Ko gajiyaya?”


Baisan tanka ta dan kalamanta na d’azu ba karamin bata mai rai sukai ba, neman dauke idanunsa yai daga kanta.


Mikewa yai rai a bace yana kokarin barin daki, hannu tasa ta riko hannunsa ba tare da tayi shawara da zuciyar ta ba, tace “bakajin dadi ne?”




Kallanta yai kawai ya kwace hannunsa ta dauka fita zai kawai taga an kashe wutar dakin.


Hannu yasa bayan ya dawo ya jawo nata hannun, a hankali ya karasa da ita kan gado yana jin wani abu na kara taso mai.


Mikewa tai kafin tai wani yunkuri ya maidata, Kh.......


Jin bakinsa cikin nata ne yasata yin shiru, wani irin salo yake da shi kansa baisan ya sani ba, a hankali ya kai bakinsa kan wuyanta, wani irin yanayi ta tsinci kanta a ciki wanda tunda tazo duniya bata taba ji ba, hannu yasa a kan zaninta, cikin wani yanayi na rashin karfi ta sa hannu saman hannunsa, idanunta a lumshe.


Hannu yasa ya ture hanun nata ya zare mahafin xanin, sam Khalid ya gama fita hayyacinsa, balle su Zainab wacce aka tsinci kai a wata duniyar da ba’a taba zata ba,  bakinsa yakai...........nai fito a guji, ai takalmi nama sai daga baya na dawo na dauka.


********


Sai da ya kammala sannan nutsuwa ta zo mai, a hankali ya mirgina tare da lumshe idanunsa, Zainab kam bata taba kawo wannan yanayi ba sai dai gaba daya kwakwalwarta ta tafi dan ta manta meya faru a dan lokacin nan, bata san a wani yanayin ta tsinci kanta ba, shekararta 4 da Adam ya akai take jin kamar yau ta fara?


Dagowa yai ya kalleta, ganin idanunta a kansa yasa suka hada ido, da sauri ta dauke nata idon, Khalid duk da hankalinsa ya kwanta amma haushin rashin hakurinsa yake, yaso ya barta da aikinta data aura.


Mikewa yai ya shiga toilet, ya kara yin wani wankan, yana fitowa ya zubama inda take ido, juyowa tai jin motsin ya fito kuma taji shiru, ganin yana kallanta, yasa itama ta zuba mai nata idan, tana san sanin tunani me yake?


Dan hasken dake fitowa daga toilet ne yake dan haske dakin kadan, ganin yaki dauke idanunsa yasa tace “akwai ruwan zafin?”


“Kadan” ya fada tare da wucewa jikin wardrobe, mikewa tai bayan ta gyara zaninta sannan ta fara kokarin saukowa daga kan gado, ta sako kafa daya zata sako dayan tai baya da sauri ya rikota, mikar da ita yai, kallansa ta sakeyi a hankali sannan ta juya.


Hartaje bakin toilet ta juyo ta kalleshi, meya sameshi? Ta tabbatar da dane sai yayi magana, kunya yakeji? Abinka da saurayi tai maganar a ranta gana wanka.


Shiru tai tana tunanin abinda ya faru a d’an lokacin nan.


Murmushi tai ita kadai sannan ta karasa ta fito.


Ganin baya dakin yasa ta fito falo, a kwance ta ganshi baiko ci abincin ba, kuma da alama yayi bacci.


Kallansa tai cikin mamaki, kusa dashi ta matso tace “Abincin fa?” Ta tabashi tana tambayarsa.


“Naci dumame, banaji zan iya cin wani abu ynzu.”


Ido ta zubamai, danta a bace wato ya sata tai abinci sannan yace “bazaici ba?”


A kufule tai ciki, yanajin rufe kofarta, ido ya rufe.


Tana aiki tana masifa haushi ma ya isheta ta rufe laptop din, fitowa tai waje ta shiga duba yanda ake kashe gen din tana kashewa ta wuce ciki kallansa tai a falo a kwance cikin jin haushi tace “inyasan a falo zai kwanta ai ya dauko bargo da pillow.”


Ta wuce ciki harta kwanta taji ta kasa bacci ta dauko ta fito dashi, kusa dashi taje ta samai bargon ta ajiye pillow din ta juya.


Hartai bacci ranta a bace yake.


*******


Ina kudin da Rahinatu tace ta aikon dashi jiya? Naira hamsin?


Goggo ta kalleta tace “Hanne wai dan Allah ni ba yyar mijinki bace zaki sani a gaba da fad’a? Akan ma naira Hamsin?”


Yo ko shi mai gidan ne yacimin hamsin ai naji dalili bare ke kece kika min sirfen? Billahi lazi sai kin biyani hamsin dita.


Goggo tace “zan baki hamsin sau hudu ma amma ki bari Adam yazo.”


Kan bala’i to wlh yau ko za’a mutu sai kin biyan.


Akan tsinanita hamsin kike min masifa?


Tsinaniya? Inyi sirfen in sameta kice tsinaniya?


Yo me akai akai hamsin banda talauci?


Ran Hanne ya kara baci tace “to wlh sai kin biyani in ba haka ba kuma wlh daga yau har kwana biyu bake bacin abinci a gidan nan.”


Sadiya zo ki ban Hamsin naba matarnan.


Sadiya dake sirfe waken alalen siyarwa tace “badai nawa ba kam wlh, kina gani abin aurena nake hadawa.”


Ta juya tana aikinta.


Hanne tace “to wlh ki shirya dakon yunwa.”


Yo a wani abincin? Dumamen tuwo ko saban tuwo?


Koma menene.....

Ta fada tai ciki.


********


Sau uku kenan tana kiran Adam bai dauka ba, kwafa tai tace “zaka san nika wulakanta wlh.”


Adam kam daga yaga kiran Afreey sai yaji hanjin cikinsa na kadawa, gaba daya ya rasa yanda zaiyi, dan ma y saida katin dari takwas a wanda ta turomai aka bashi dari bakwau yaci indomi, da yau kam tsoro da yunwa sai sun halakashi.


Ya zaiyi ya sanar da Afreey wannan labarin?


**********

Ayusher🏌🏻‍♀

**********

[1/7, 11:27 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


“The best and most beautiful things in the world cannot be seen or even touched. They must be felt with the heart”


Helen Keller


{56}


Wajen karfe biyu ya bude idanunsa, jin ba karar gen ga kuma haske kwan wuta ta waje yasa yasan nepa ne, kafafunsa ya sauko dasu daga kan kujerar, gaba daya jikinsa ciwo yake yi.


Daki ya nufa a hankli ya bude dakin, tare da dan haska wayarsa, tana kwance tana bacci, murmushi ne na wani yanayi da yake tausayin kanshi da ita ya bayyana a fuskarsa kafin ya nufi cikin dakin, a hankali ya isa kusa da ita, ya zauna a ta gefenta tare da zubawa fuskarta ido, bacci take kadai ko tana mafarki? Murmushi yai tare da cewa mafarki tana aiki? Yanayin fuskarsa ne ya canza yadan sukunyo yana kallanta cikin wani yanayi da shi kadai yasan me zuciyarsa ke ciki, a hankali ya kai bakinsa kan goshinta ya sumbata tare da dan lumshe idanunsa, sannan ya kalleta ya yace “what should i do with you?” Yai maganar cikin wani irin sanyi murya mai kamar ta rad’a mai ratsa zuciya.


Mikewa yai ya gyara mata bargon sannan yai alwala ya kunna heater ya fito daga dakin, nafiloli yai yasa pillow yai bacci a nan kasan.


Yau kam ya d’an makara dan sai biyar da rabi ma ya farka daga bacci, da sauri ya mike ya shiga toilet din dake falo yai wanka sannan ya nufi daki, tana kwance tana bacci har ya sa kaya, d’an motsi tai bai kalleta ba ya cigaba da shiryawarsa, idanunta ta bude ganin hasken fitila.


Yana gaban madubi yana sa turare, wayarta ta jawo ta duba agoggo sannan tace “yauma da wuri zaka fita?”


“Gaisuwar ki kenan?” Yai tambayar tare da kallanta yana sa agoggo, tace “wai wani irin aiki ne tun safe bai karewa? Kuma irin wannan aikin karfin Allah ni nasan ba wani abu ake baku ba.”


Juyawa yai bai tanka mata ba ya sa mabalen rigarsa sannan ya dau wayarsa, kallanta yai yace “ba saikinyi abinci saboda ni ba, kiyi yanda kikeso.”


Ya juya ya fita, shiru tai, a ranta tace “tausayi na yake?”


Ba tare da wani dogon nazari ba tai sallah sannan ta kwanta, dan baccin awa biyu tai sannan ta mike cikin jin dadin bazatai abinci ba ta gyara dakin tai wanka ta had’o tea ta dauko dubulan tana ci tana aikinta, charge na karewa ta kuna gen ta cigaba da hidimarta, yau ta shirya yin website na gidan Tv dinta da logi, shiyasa ta dukufa sosai a falo tana ta hidima, sai karfe hudu taji gen ya mutu, fitowa waje tai tana dubawa, ganin ba mai yasa ta juye ragowar na jarkar wanda bashi da yawa ta kara kunnawa ta koma ciki.


Tana zama harta dau mouse sai taji yunwa ta kamata, ta mike tai kitchen, ganin tuwon jiya yasa tai shiru ita kadai a kitchen tana tuno abubuwan da suka faru a daren jiya, samun kanta tai da rufe fuskarta tana murmushi, dan ta tabbatar kila kunyarta yake shi yasa ya kasa dawowa cin abinci.


Shiru tai kafin tace “to me zaici?” Ginin kitchen ta kalla haka kawai taji zuciyarta duk ba dadi, jitai bata ma jin cin abincin hakan yasa ta fito daga kitchen din, zama tai a falo, duk yanda taso yanzu tai aikin ta kasa, daga ta tuno yana ta gini sai taji ranta ya baci.


Rufewa tai sannan ta kunna tv bayan tai sallah, abinda ta ganine yasata mikewa ta zauna sosai, ganin masu aikin gini tai ana lafta musu kasa suna dauka, wasu na shafa sumunti, wasu na kankare kasa suna ta faman gyara, jitai gaba daya hankalinta ya tashi abinda Khalid yakeyi kenan?



Waya ta dauko da sauri ta dubo sunansa tana neman kiranshi kawai wayar Aunty ta shigo mata, idanu ta rufe sannan ta dauka.


Aunty daga can tace “Zainab sam baki da kirki, wlh badan ke ‘yar yaya bace ko kallan inda kike bazan karayi ba a rayuwata.”


Zainab tace “me kuma nai?”


Tace “ai ko kudin mahaifinki ne ya turo na miki kayan daki da jere da kuma kayan gara a kalla kya kirani kice sunyi kyau ko basuyi kyau ba, in har bazaki kirani akan gajiyarmu ba.”


Shiru tai Aunty tace “shikenan, Allah ya bada zaman lfy.”


“Ba haka bane banyi tunanin kiran bane, amma komai yayi kyau.”


Kai ta daga kawai tace “shikenan sai anjima” kafin Zainab tai wani abu ta kashe wayar, shiru tai, tana mamakin wannan abu kawai dan bata kira ba sai taji haushi?


******


Karfe biyar da rabi ya dawo, dan ya ajiye aikin zaman shagon, yanzu daga gun gini garaje yake wucewa, yayi sa’a dama store ne ba shi kadai bane ke aiki agun.


Tsayawa yai ya siyo kayan miya, bread da kwai sannan ya taho gida.


Tana zaune a falo yunwa ta isheta yasa ta dumama tuwon tana ci, kallanshi tai bayan ta amsa sallama, tace “yau da wuri haka?”


Harzai mata magana kawai ya fasa ya wuce ciki, kitchen yakai kayan ya ajiye sannan ya wuce daki, da kallo ta bishi tana tunanin gajiyar aiki ce hala? Karar rashin mai gen din ya fara, kafin ya mutu, dan ajiyar zuciya tai bayan ta gama cin abincin ta wuce kitchen ta wanke hannu ta ajiye kwanan ta duba abinda ya siyo sannan tai daki ta sanar mai ba mai.


Jin karar ruwa yasa ta fahimci wanka yake, zama tai a bakin gado, fitowarsa ne yasa ta kalleshi, tana ganin sa daure da towel ga gaba daya saman jikinsa a waje, Khalid irin mazan nan ne masu fadi sannan jikinshi a dan murde yake, wankan dayai yasa gashin kirjinsa sun kwanta, da sauri ta mike ta juya bayanta gabanta na faduwa.


Baiko bi ta kanta ba ya goge jikinsa da karamin towel din da ke hannunsa sannan ya sa jallabiya ya sa turare.


Kokarin fita daga dakin yake tace “naga ka dawo da wuri.”


“Eh da wani abin ne?”


Dan takowa inda yake tai tace “zakaci tuwon?”


Kallanta yai yace “A’a indai kinci shikenan.”


Ya fada tare da fitowa daga dakin, wannan wannan ta fada tana nuna kofa kafin ta daure fuska ta fito.


Yana zaune a falo taje gefe ta zauna ganin wayarsa yake dadanawa yasa ta zauna a kasa inda laptop dinta yake, a kan centre table ta fara duba aikinta, ganin shirun yayi yawa yasa tace “ko zaka kaini gidan?”


“Inkin shirya muje na kaiki.” Ya amsa hankalinsa na kan waya, shiru tai tana tunanin me yake a wayar da ko kallanta baiyi ba?


Mikewa tai ta shiga daki, ta gyara fuskarta ta dauko mayafi da key ta fito.


Haushi ne ya kara kamata ganin har ta isa kusa dashi baiko kalleta ba, sai datace “muje?”


Kallanta yai sannan ya mike yai waje.


Da harara ta bishi sannan tabi bayanshi suka isa gaban mota.


Key ta mikamai ya amsa ya shiga itama ta zagaya ta shiga, shiru tai tana kallanshi samun kanta tai da tuno abubuwan da suka faru a baya a cikin motar, wani murmushi ne ya bayyana a fuskarta, ta kalleshi tana tuno sanda zai tambayeta kwatancen gidanta sai wani left da right yake ce mata, ya wani ce mata excuse me? In zai mata magana, Murmushi tai ita kadai, har suka isa gidan bai tanka ba.


Bala na ganin motarta ya bude cikin hanzari, suna shiga ya taho da gudu yana kwasar gaisuwa.


Bayan sun gaisa ne tai hanyar ciki, ganin Khalid tai a ciki mota bashi ko da alamar fitowa, dawowa tai tace “Muje mana.”


“No jeki fito.”


Ido ta kuramai cikin kuluwa yau tunda ya tashi ko maganar arziki bai mata ba, abinda ya faru daren jiya fa? A banza yake? Kenan duk yanda ya nunamin karya ne? Abinda kawai take rayawa a ranta kenan, yawon bakinta ta had’iya tace “abinda zan dauko nada nauyin bazan iya dauka ba.”


Kallanta yai sannan ya mike, suna shiga tai ciki.


Kallan gidan yai jiyai jikinsa duk yai sanyi, ganin tafkeken falo, da gun dinning a gefe, wanda yake hade da kitchen.


Zama yai akan kujera ta wuce daki ta bar kofar dakin a bude, ganin ta kasa jawo akwatin dake saman wardrobe din ne yasa ta tura kujerar jikin madubi ta hau, ganin ta jawo amma ta kasa dagoshi ta sauko dashi yasa ta sauko ta fito falo.


Kallan Khalid tai tace “dan taimakamin.”


Kallanta yai bai amsa ba kuma bashi da alamar mikewa, kallansa tace “magana nake ma.”


Tambaya ma bata iya ba, abinda zuciyarsa ta fadamai kenan yai ajiyar zuciya.


Kallanta ya sake sannan ya kara dauke kai, wani abu ne ya tokare a mokoshinta a kufule ta juya, karfi tasa ta jawo akwatin, da kyar ta shiga kokarin neman saukewa kawai taji an dageshi daga hannunta, kallan juna sukai kafin ya ajiye a kasa, kallansa take har ya ajiye ya dago tace “kasan zaka tayani meye bazaka amsamin ba?”


Bai kula ta ba ya fara neman juyawa, ranta ne ya kara baci tace “Kayi nadamar aure nane?”


Tsayawa yai ya juyo ya kalleta, idanunta ne suka fara cicikowa tace “akan me yau kwata kwata kaki min maganar kirki? Abu na maka? In haka ne ka fad’amin mana, ai kai ba mai ajiye magana a ransa bane.”


Kallanta yai yadan yi wani mosti da bakinsa, wanda baikai murmushi ba yace “me kikeso in ce miki? Bakya ganin na baki dama ki zauna da aikin da kika aura ne?”


Me yasa taji zafin kalamansa? Bayan hakan take so? Tambayar data wa zuciyarta kenan.


Kallanta yai yace “damar ce bakya san na baki?”


Da gaske kake?


Eh, Na dauka abinda kikeso kenan?


Yai tambayar yana kallanta, murmushi tai tace “ban dauka zaka bani dama haka bane shiyasa, nagode sosai.”


Kai ya daga alamar to sannan yace “karki damu” ya juya ya fita.


Shiru tai a gun meyasa bata farin ciki? Bayan abinda takeso kenan?


Fitowa tai ta nufi kitchen, zare cylinder din jiki tai sannan ta shiga fito da abubuwan abinci wanda ke ciki, yana zaune a falo harta gama.


Kallanshi tai tace “dan tayani.”


Baice komai ba ya dau akwatin ya fita dashi, kallan cylinder din yai yace “do you really need that?”


Tace “eh bansan ya akai Aunty bata sa a ciki ba.”


Bai ce komai ba ya dauka, kallan kayan abincin yai yace “wannan fa?”


Kamar tace Mu tafi dasu sai kuma kawai jikin ta ya bata zaiji haushi, tace “tunanin ba Bala nake.”


Murmushi yai ya dauka ya fito, kallan dayar motar da Dady ya sai mata tai ta kalleshi tace “motar can.”


Kallan motar yai sannan ya kalleta, kamar zata sake magana sai tace “bakomai.”


Wucewa yai ya shiga motar, ta sallami Bala sannan suka fito yana ta godiya.


********


Sai da sukai dan tafiya tace “ko zaka kaini Jifatu? Akwai abinda nake san siya.”


Batama san ya ake tambayar abu ba?


Baice komai ba ya wuce da ita, shiga sukai tare ta dauko mai da take shafawa da abin wanka na shower gel, suna zuwa gun biyan kudi aka buga akace 3000, tana kokarin bada katinta Khalid ya mika nashi, nan aka zara wayarsa ce tai kara akan alert da akai, yana dubawa yaga 1000 ne kadai ya rage a ciki, ajiye wayar yai sannan suka fito.


Haka kawai ta ke jin abin banbarakwai, tunda take bata taba siyan abu an biya mata ba, sai dai ta biya duk abinda ta siya ta kuma biya na wanda sukaje tare, ita ko da Dady ba yawo suke tare ba bale har suje siyayya.”


Suna kokarin shiga mota yaji ance “Kwaro?”


Juyowa yai ya kalleta, Zainab wacce taji muryr mace itama ta juya.


Kallan kallo sukai, yanayin fuskar Zainab ne ya canza tana ma budurwar wani irin kallo.


Ta kusa da ita ta wuce taje kusa da Khalid tace “Ashe zan ganeka?”


Khalid ne ya saki murmushi mai sanyi yace “Safeenah? I never expect to see you here.”


Dariya tai cikin jin dadi tai ajiyar zuciya tace “inalilahi shekaru nawa?”


Shima dariya yai yace “tun a skul.”


Tace “wa?” Tai tambayar tana nuna Zainab da kanta.


My wife, ya fada yana murmushi.


Idanunta zaro tace “me?”


Fuska ya hade yace “ban isa yi bane?”


Dariya tasa tace “bawai baka isa bane, Afreey ta sani?”


Fuska ya hade yace “Zaki fara ko?”


Tace “shekaranjiya muka hadu da ita kuma tana ta zancenka kaga ina zan kawo wannan yanayin?”


Zainab dake tsaye ta ciga ta gama batsewa ta bude mota ta shiga ta zauna tana harararsu, ganin Khalid ma dariya yasa ta karajin wani irin mugun bacin rai.


Safeena ce tace “kuma kun dace amma kamar na santa.”


Murmushi yai yace “na san wannan basai kin fada ba.”


“Oh ni Kwaro ban taba tunanin zakaso wata har kai aure ba, na dauka karatu zaka aura.”


Murmushi yai yace “kefa?”


Horn din motar ne yasa ta kasa magana, kallanta yai yace “Madam ta gaji da jira.”


Oh ni, yau Afreey tazo taga abu, wato Madam ta gaji? Oh ni wannan abu sai kara ban mamaki yake, oh ni Kwaro.


Dariya Khalid yai yace “bye.”

Ya karasa tare da shiga motar, Zainab ya kalla wacce ta cika ta batse, ta murtuke fuska tamau.


Yace “mu tafi?”


Wani banzan kallo tamai ta juya kai, shima ya ja suka tafi, tsayawa yai a gun ‘yan cuwa cuwa yaduba wallet dinsa ganin 300 yasa yasai musu mai suka wuce gida.


Suna isa ta fito daga motar rai a bace tai ciki, tsayawa yai ya zuba mai sannan ya wuce ciki, yana jin cikinsa na karar yunwa, sai dai yasa a ransa dole koma menene ya jure.


Kitchen ya wuce ya gutsiri bread din daya siyo ya dau ruwa ya fito falo yaci ya sha ruwa.


*******


Safeena kam suna rabuwa ta shiga kiran kawayensu na skul tana fada musu Khalid yayi aure, kowa Afreey ya shiga hangowa suna tunanin yanda zasu fada mata.


*******


Nusaiba bazaki tashi kici abinci ba? Wai meke damunki ne?


Kallan Basma tai tace “ni wlh Mumy Uncle nakeso”


Basma tace “banace karki kara maganar nan ba? So kike ran Dadynki ya baci?”


Hawayenta ta share tace “to ni Allah bazan iya hakura ba.”


Idanun Basma ne suka ciko, ta tuno abinda tama Mahaifiyar Zainab da ita kanta Zainab daga koyarwa, share kwallarta tai tace “to sai dai kuwa ki mutu wlh na sake jin maganar nan dukan tsiya zan miki a dakin nan.”


Nusaiba ce ta kalleta tace “Dady zan fadawa tun.......”


Marin da Basma ta wanka mata ne yasata yin shiru, in sake jin maganar banzan nan.


Ta juya ta fita, ba shakka alhakin Ummy dashi zan mutu, tunda ban nemi yafiyarta ba, banama jin tasan nice na kwace mata mijin harta rasu.


Hawayenta ta share cikin wani yanayi......


*********


Yau kam tana tashi taga baya gida, samun kanta tai da jin haushi, kwanciya tai ko dakin ta ki fitowa.


Lalai ma Khalid din nan? Ta fada cikin jin haushi.


Bargo taja ta rufe kanta dashi ta dauko wayarta, gun sako ta bude, me zata ce mai?


Haushi ne ya kamata ta ajiye wayar, ta kara jan bargo tare da yin kwafa.


********


Afreey me kike gani? Ai nasan Babanki dan Albarka ne ba shakka zai dubemu.


Kallan Director Kabir tai tace “badai da gaske kake bako?”


“Haba Afreey kema kinsan ba wasa nake ba, in babanki ya taimakemu wannan karan ba abinda bazan miki ba.”


Wata dariya tai tace “na taba neman abu a gunka? Duk duniya ina da komai danake so abu daya ne ya gagaren wanda shima dole ko da menene sai na mallakeshi, banaji ya shafeka bare ka taimaken.


Ran Director Kabir ne ya baci amma ya ya iya? Daurewa yai yace “ki taimaka ko baki to ya sa a taimakemu dan Allah.”


Zan duba, abinda tace kenan ta fito, tare da hararan kofarsa, wayarta ta dako ta kara kiran Adam, amma sai Kamalu ne ya daga yace mata wai bashi da lafiya.


Kwafa tai ta kashe wayar dole ta je inda yake taji uban me yake boye mata.


Nace Um um dai da dai kin hakura🤪

******

Ayusher🏌🏻‍♀

[1/7, 11:27 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


{57}


Yau kam sam takaici ma ya hanata yin aiki dan in ta tuna wai ya bata dama tai aikinta sai taji ranta ya kara baci, yanzu ma a karo na ba adadi ta mike tsaye a kufule tace "da cewa nai bansan aikina? Kasan haka meyasa ka....." sai kuma ta kasa karasawa ta zauna akan gado cikin takaici, tun dazu take jin yunwa amma bakin ciki ya hanata ma cin abincin sannan dama ita mace ce mai wahalar da cikinta, tana jin yunwa amma in abu na gabanta to ajiyeshi take.


Mikewa tai ganin azahar har tayi tai wanka ta sa turarukanta masu kamshi ta shafa hoda kanta ba dankwali ta nufi kitchen, bread din da aka gutsira ta kalla ta duba taga ba alamar anyi amfani da cup, kenan bread kawai yaci ko me?


Dankali ta fere ta fara soyawa shiru tai tana tunani, are you okay? Abinda kunuwanta suka jiyo mata kenan, tai shiru tana tunani ai Khalid tun kafin ma su fara wata doguwar magana in har tana cikin wani yanayi yake tambayarta hakan, wanda har take mamakin yanda Adam baya gane halin da take ciki amma shi yake ganewa, kenan ya san abin nan da yake mata yana bata mata rai amma ya cigaba? Tana tunani har dankalin ya kone, haushi ne ya kamata kawai ta hada tea tasha a kitchen din, ji tai idanunta sun ciciko, maida kwallarta tai tana tunanin tunda ta taba auran Adam ta taba zama tunani da har xataji tana shirin kuka?


Fitowa tai daga kitchen din kawai ta dau wayarta ta kira Nabila, waya suka shiga yi Nabila na tsokanarta ina Yaya Ango.


Zainab cikin kuluwa tace "ina na sanmasa."


Nabila tai dariya tace "Wai yaushe a gari Aunty ake bari a gida ba ita take bari ba."


Fuska ta daure tace "karki batan rai, dan na gaji da zaman nan wlh, ga rashin wuta, ga mutum sai zafin rai."


Wata irin dariya Nabila tasa wanda tasa Zainab jin haushi tace "dariya kike?"


Nabila ta tsagaita tace "Aunty mamaki nake ban taba ji kina complain akan wani ba shiyasa"


Zainab tai tsaki tace "wannan in na fara zubo miki complain a kansa ai yasin sai muyi awa biyu a waya."


Nabila ta sake dariya tace "da alama Aunty na san Ya Khalid sosai."


Fuska Zainab ta daure tamau kamar tana ganinta tace "abinda yafi so, ce miki akai banda aikinyi?"


"Kinada aikin yi kike samun dama da lokaci na jin haushinsa?"


Zainab tace "ke kika san wannan, Nusaiba fa?"


"Hmm ni ina na san mata, sai wani hade min rai take kamar ni na kar zomon."


Shiru Zainab tai kafin tace "ke kuma uwar rashin hakuri, kiyi hakuri ki dan lalabata harta saki ranta."


Ajiyar zuciya tai kafin tace "zan gwada amma Allah ta kawon wargi zanyi gaba kin sani."


Na sani kiyi hakuri dai, haka suka danyi hira kafin ta kashe, shiru tai tana tunanin abinyi ganin tanata tunani kawai ta mike ta dauko laptop  dinta ta fara aiki, sai la'asar tai sallah sannan ta dafa indomie ta zauna tana ci.


Tana gamawa ko kwanan bata dauke ba ta cigaba da abinda take, sallamar Khalid ce yasa ta dago ta kalleshi tare da amsawa.


Ido ta zubamai ji take kamar ta dade bata ganshi ba, shima kallanta yake yanda tabar kanta a bude da yanda tai zaman nata har jikinsa yaji abin, murmushi tamai shima samun kansa yai da mata sannan ya shiga ciki, daki ya wuce ta bishi da kallo yau ma bashi da niyyar kulatan?


Daki ya wuce ya watsa ruwa saboda gajiyar dayai sannan ya dan zauna akan gadan yana shafa aboniki a bayansa, dan sosai bayansa ke mai zafi, ganin bai fito ba ga charge dinta ya kare yasa ta mike tai dakin.


Ganin sa sanye da wando da farar vest wanda ya daga ta sama yasa ta jawo kofar, shiru tai tana tunani kamar abu taga yanayi, me yake? A hankali tadan tura kofar tadan sa idanta.


Jitai yace "leken me kike?"


Bude kofar tai tace "a ina nai leken?"


Kallanta yai ya rufe man, jin kanshin man zafi yasa tace "me kake?"


Bakomai.


Yai maganar yana maidashi kan madubi.


Haushi ne ya kara kamata dataga yana neman barin dakin, haka ya wuce ta gabanta ranta a matukar baci ta bishi da harara.


Yana kokarin fita daga kofar ta rike rigar sa tace "nice bakasan zama guri daya dani?"


Juyowa yai ya kalleta, tace "ka bar falo ka dawo daki yanzu na shigo dakin ka fita, me kake nufi?"


Kallanta yai ya kalli hannunta data rikeshi, yace "haka kike gani?"


Tace "ba hakan bane?"


Abinda zuciyarki ta raya miki shine daidai a gareki?


Fad'amin ba hakan bane?


"Ba haka bane."


Yai maganar yana kallanta, to menene? Dama ka bani nai aiki?


Hmmm bakyaso?


Ba wai banaso ba amma at least ka dawo yanda na sanka, wannan halin daka faramin yasa ina tunanin abubuwa dayawa.


Zaiyi magana yaji ana buga kofa, kallanta yai yace "bari na duba."


Sakeshi tai zuciyarta na kara hasala, harta juya taji karar text a wayarsa, dauka tai da niyar fitomai da ita, abinda ta gani akan screen din wayar ne yasa yanayinta canzawa.


Idanunta ne suka ciciko, hankali a tashe ta bude wayr ta duba sakon dakyau, bata taba tunanin daukar wayar wani ba bare tunanin bude ta, alert ne na katin dari da aka saka suka turo balance na 900, sam ta kasa dauke idanunta daga kan screen din wayar, jikinta ne ya shiga rawa, tana maimaita 900 a ranta, idanunta ne suka ciciko hawaye suka zubo daga cikinsu ba tare da ta sani ba, jin motsinsa yasa ta ajiye wayar hankalinta a matukar tashe.


Shigowa yai yace "makocinmu ne, bamu kyauta bamu shiga ba yazo mun gaisa yace matarshi za........"


Ganin yanayinta yasa yace "menene?"


Kallansa tai, matsowa kusa da ita yai ya dago fuskarta yace "menene?"


Kwacewa tai da sauri ta shiga cikin toilet, tana shiga ta rufe, shiru yai yana kallan kofar, yana san suyi magana dan kalamanta sun sa jikinsa yin sanyi, da alama abinda yake mata ya mata tsauri ganin lokaci daya komai ya canza mata, samun kansa yai da jin haushin kansa, sai dai baisan meyasa yake hakan ba.


Ganin taki fitowa yasa ya fito falo, Zainab kam tana shiga ta tsaya a jikin kofar ta jingina bayanta gaba daya ta kasa tabbatar da abinda idanunta suka gani, tabbas zero biyu ta gani, kanta ta shiga bugawa a jikin kofar.


Har yai alwala a falo yana jiran ta fito suyi sallah baiga ta fito ba, massalaci ya fita har ya dawo bata fito ba dakin ya shiga sannan ya mike ya kalli toilet din ba alamar fitila ga duhu, buga kofar yai yace “Zainab?”


Jin shiru ya sake cewa “Zainab?”


Nan ma yaji shiru hannu yasa yana kokarin budewa jinshi a kulle ta ciki yasa ya shiga murdawa yana cewa “Zainab! Zainab?”


Bude kofar tai da sauri ya kalleta yace “lafiya?”


Yai tambayar yana duba jikinta, hannunsa tadan ture ta wuce ciki, hijab ta dauka, ta tada sallah ba tare da tace komai ba, shiru yai yana kallanta kafin ya juya ya fita, waje yaje ya kuna gen ya zauna a falo, sai dai gaba daya hankalinsa baya falan yana dakin balle dayaga har a lokacin bata kunna wutar dakin ba.


Ganin ya kasa daurewa ya mike ya nufi cikin daki, kallanta yai wanda hasken waje ya dan haska dakin, tana  zaune a inda tai sallah ta sa kanta cikin kafafunta, hawaye kawai ke zubo mata ta rasa dalilinsu, gaba daya haushin kanta takeji ta ko wani bangare.


A hankali ya taka zuwa inda take ya zauna tare da sa hannu ya dago kanta, kallansa tai idanunsa na kanta yace “bakida lafiya ne?” Yai maganar cikin sanyin murya.


Ummy me nakeyi? Ummy na, Ummy! Abinda zuciyarta ke fada kenan, Kuka kawai ta fashe dashi hankalin Khalid ne ya tashi, kallanta yai yace “menene?”


Baki da lafiya ne? Yai maganar cikin tsananin damuwa.


Kuka kawai take tana tuno a yanzu haka tana da kudi saman da miliyan biyu a account dinta wanda Dady ke sa mata, ga dubu dari tana da shi a cikin dakin nan na kudin gaisuwa daya kawo, tana da gida babba, tana da motoci, tana da fili me take a rayuwarta da har.........


Dagatan da yai ne yasa ta kalleshi, zaunar da ita yai a kan gado, hannayensa yasa akan fuskarta yace “ menene?”


A hankali ta girgiza kanta alamar ba komai


ni ne?


Kallansa tai jikinsa ne yai sanyi yace “ am sorry, am really sorry”


Kai ta shiga girgizawa tana hawaye, goshinsu ya hada hannayensa na kan fuskarta a hankali yace “na sani laifi nane”


  tace “laifinka name?” Tai maganar  hawaye na zubo mata.


“Na komai”


Tunowa tai da abinda tai jiya gen yini yai a kunne, taje jifatu ta kashe mai 3000, ya siyo abubuwan gida na bukata, hawaye ne ya sake zubo mata.


Hannu yasa ya share mata sannan ya jawota jikinsa ya rungume, yace “ya isa haka nan, yaushe kika zama mai raki?”


Dagowa tai ta kalleshu tace “ban sani ba, bansan ya akai na zama mai raki ba.”


Murmushi ya mata mai sanyi a dan jawota cikin sanyi yace “kin zama mai raki but i like it.”


Kallansa tai tace “shiyasa kake shareni?”


Haka kika gani?


Ba hakan bane?


Dam........

  Hannu tasa ta rufe bakinsa tace “ya isheni ba sai ka tisa min ba.”




Murmushi yai, itama tai murmushin karfin hali, cikinshi ne yai kara, kallansa tai tace “bakaci abinci ba?”


In ba’a ban a gidana ba a ina za’a bani?


Shiru tai tana maimaita kalaman a ranta, indomie naci in dafa ma? Karkace nama tuwo plz.


Kin manta nace kiyi duk abinda kikaga shine daidai.


Mikewa tai ta fito dan so take ta kadaice, tana shiga kitchen tai shiru, hawayen da ta rasa dalilin zubarsu ne suke gangaro mata.


Idanunta ta rufe haka ta dafa indomie din, ta fitomai dashi falo, kallansa tai tace “kai na ke ciwo zanyi sallah na kwanta.”


Kallan mamaki ya mata, gani yai kafin yai magana harta wuce ciki.


Laptop da takardunta ya kalla, meke damunta??


Tana sallah ta kwanta, shima harya kwanta a falo ya samu kanshi da mikewa yai ciki, haryai bacci idanta biyu, tayi shiru tana tunanin rayuwa, sai wajen asuba ta samu bacci ya dauketa.


*********


  Suna zaune a cikin office din taro, shugaban gidan tv din ne ya kallesu ranshi a matukar bace yace “kuna san cemin haka zan cigaba da sa kudina yanzu ba riba?”


Kabir yace “Ranka ya dade kadan kara ha......”


Desk din daya daka ne ya sashi yin shiru, kallanshi yai yace “kana tunani kai ba dan kanina bane zan barka ka cigaba da aiki anan? Wlh kaji na fadama bazan dauki wannan asarar ba, da ka san bazaka iya ba uban waye yace ka kori Zainab?”


Fuska ya hade baice komai ba, to Allah kaji na fadama ficikata bazan sa ba, ace gidan tv yanzu banda asara ba abinda nake samu? Kudin biyan ma’aikata ma neman gagarata yake, duk wadanda suka dau nauyin talluka sun ajiye, ka je ka saka mutanen dakaga dama suna shiri yanzu sam ba wanda ma yake kallan tashar to Allah bazan dauka ba kaji na fada ma, inhar naga bazan iya ba saida gidan tv din zan, yana kaiwa nan ya mike yai waje.


Da kallo suka bishi sannan suka kalli Kabir wanda ya cika fam


*******


Adam ne ya kira Goggo, tana zaune tasa dumamen tuwo a gaba ta kasa ci saboda bakin ciki wulakancin da aka mata kafin a bata dan Hanne sai data kare mata cin mutunci.


Ganin kiran Adam yasa ta dauka da sauri tace “Adam ya ya? An dace?”


Yace “ina fa aka dace Goggo bayan muna cikin tashin hankali, Khalid da takeso yai aure.”


Goggo hankali a tashe tace “uban wa yace yai aure? Wannan d’a anyi an banza, garin ya ya ka bari yai aure?”


Ni kya tambayen garin ya ya? Nine babansa? Ni wlh yanzu bansan me zan ce mata bane.


Ka nuna mata baka sani ba, kai maza kasa ta nemarma aiki kafin ta sani.


Cikin jin dadi yace “haka ne Goggona, nagode”


Nan ta kashe wayar tana fatan dacewa.


******


Wajen karfe 10 ta farka, mamaki ne ya kamata dataga tayi bacci dayawa haka, wayarta ta ajiye tana kokarin saukowa taji tayi ringing, d’auka tai da sauri tace “Umma”


Bayan sun gaisa cikin farin ciki Umma tace “na kira Khalid bai dauka ba dama cewa zanyi gobe zamuzo da Asiya.”


Cikin tsananin murna Zainab tace “Allah ya kaimu Umma, karki manta da...”


Umma ce ta katseta tana dariya tace “ina zan manta da wainar geron ki? Kina san wani abin bayan shi?”


A’a Umma.


Umma tace “sai munzo goben.”


Cikin jin dadi sukai sallama.


Murmushi tai na dadi.


*******


Khalid kam a rana yana duba wayarsa yafi sau ashirin yana fatan ganin sako daga Zenith bank, duk da yasan abin na jan dan lokaci amma zuciyarshi ta kasa hakura


Haka ya hau mota ya taho gida.


********

Ayusher🏌🏻‍♀

[1/9, 12:20 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


{58}


Wayarsa ya dauko a cikin mota, yasa hannu zai danna kira akan sunanta kawai yaga kiranta ya shigo, shiru yai yana kallan number murmushi bayyane akan fuskarsa, dagawa yai.


Daga can tace “Umma ta sameka?”


Kai ya girgiza tare da cewa “sallamu Alaikum.”


Kunyar kanta taji dan zumudi yasa ta manta, a hankali ta amsa, yace “yanzu zan kirata.”


Tace “okay dama cema zatai gobe zasuzo.”


Shiyasa zumudi ya sa kika kira?


Har ka gano?


Murmusbi yai yace “akwai abinda kikeso?”


Shiru tai tana tuno kudin da ke account dinsa, yanayinta ne ya canza cikin sanyi tace “a’a”


Ba abinda kike so?


Hmmm ta fada tare da daga kai kamar yana ganinta.


Shikenan sai na dawo.


To tace ta kashe wayar, shiru tai tana tunanin kenan in nashi da kudi ta ina zai ci abinci? Mikewa tai ta wuce kitchen, ganin ba nama yasa tai shiru, sai dai bata zafafa tunani ba ta hau yin jellof din macaroni, dan in ta tuna 00 biyu kacal sai taji idanunta na neman kawo ruwa.


Tana kitchen tana kwashe talliyar, sam bataji alamun shigowarsa ba, shikuma ganin bata falan yasa ya taho kitchen da ajiye nama da kayan miyan daya karo dan yasan dole zata bukata saboda zuwan su Umma.


Ganinta a kitchen tana kwashe abinci yasa shi yin murmushi, ajiye wa yan a hankali sannan ya karasa inda take, hannunsa yasa a ta ratsin cikinta, a tsorace ta juyo dan sam bataji motsi ba, gabanta yayi wani irin faduwa.


Tana juyowa kansu na gwaruwa da juna, wata yar kara ta saki, ya saketa kawai baisan sanda yasa dariya ba.


Zubamai ido tai yana dariya yauce rana ta farko data  taba gani yana dariya haka a kusa da ita, fuska ya canza ganin yanda take kallansa.


Yace “menene?”


Harararsa tai tace “bansan ka iya dariya haka bane.”


Murmushi yai sannan ya matso ya kara kai hannunsa matsen cikinta ya zagayo dasu, wani irin yanayi ne ya ratsata, kansa ya sako ta kan kafadarta yace “me kike?”


Dan juyowa tai tana san bashi amsa sai dai ganinshi daf da ita yasa ta kasa, sumbatar bakinta yai yace “kin gama aikinki ne?”


Juyawa tai ta karasa tana neman daidaita numfashinta sannan tace “ina zanyi raina yana bace?”


Yar ajiyar zuciya yai yace “fadamin nikam menene baya bata miki rai?”


Kallansa tai kadan tace “ni zan fadi hakan.”


Murmushi yai yasa hannu ya juyo da ita sannan ya kara matsewa yace “haka nake?”


Sai na fada?


Ta tambaya tana kallansa, saketa yai sannan yace “bari na watsa ruwa.”


Juyawa yai da sauri tace “inka fito kazo ka ci abinci.”


Da sauri ya juyo ya kalleta, yace “ni kikawa?”


“Wa ya fadama? Abinci ne nima ban ci ba.”


Duk da haka samun kansa yai da kallanta sannan ya juya ya fita.


Yana fita tai ajiyar zuciya ta hau fifita da hannunta, sannan ta dan yi murmushin da bata san dalilinsa ba.


******


Wanka yai ya zauna a kan gado yana dan mike bayansa tare da daukan maganin zafi.


Zainab kam ganin baifito ba yasa ta leka daki, ganinshi yauma kamar jiya yasa ta juya, jitai yace “bakya gajiya da leke?”


Kofar ta bude ta shiga tana dan kallan dakin tace “wai ni nacema leke nake?”


Kanki fa? Ya daina ciwon?


Kallansa tai sannan ta daga kai, kallanta yai shima ya mika mata man zafin dake hannunsa yace “can you help?”


Me kake?


Ta fada tana takowa inda yake, mika mata yai yace “shafan a tsakiyar nan.”


Kallan jikinsa tai da sauri tace “hannunka fa?”


Baya kaiwa.


Hannu yasa ya jawota ta zauna a kusa dashi, juyawa yai ya kwanta akan gadan yana nuna mata.


Kallan bayansa tai sannan ta lakuto a hankali ta fara shafamai, yanda yake dan motsa bayan inta taba gun ne yasa ta fahimci zafi gun yake mai, idanunta ne suka canza, tsananin tausayinsa ne ya shiga ratsa sassan jikinta, cikin yanayi na tsananin tausayi tace “ciwo yake ma?”


Dan juyowa yai yana daga kwance yace “kadan.”


Shiru tai ta kasa ci gaba da shafawa sai idanunta data rufe, hangoshi take yana aiki tukuro a idanunta, jin bata shafawa yasa ya kara dan jiyo da kansa.


Ganin idanunta lumshe tana tunani yasa ya mike zaune, kusa da kunnenta ya matso yace “Do you need me that much?”


Ido ta bude ta ganshi daf da ita, hannu tasa ta hankadashi kan gado tace “wannan fassarar fa?”


Yace “kin tabbatar?”


Da sauri ta mike tace “in ka so ka fito.”


Ta juya falo da sauri, shiru yai sannan ya kalli laptop dinta wanda da alama tadan tabata amma ba sosai ba, charge ne ya kare? Ba mai ne?


Kitchen ta shiga ta bude ledar da ya siyo nama da kayan miya, shiru tai a ranta tana tambayar wannan nawa suke? Kenan 900 din ta ragu kenan? Hankalinta ne ya kara tashi, haka ta kawo abincinsa falo ta koma kitchen dauko nata.


Kaya yasa sannan ya fito, ta ajiye mai abincin a falo, yana kokarin zama ya ga tana neman wucewa da plate dinta wanda ta zuba abinci itama.


Ina zaki?


Ya tambaya yana kallanta, kallansa tai ta kalli abincin, matsowa tai ta dau serving spoon tana neman zubamai, hannunta ya rike, kallansa tai abincinta ya ajiye a kusa dashi sannan yace “zauna.”


Ba musu ta zauna tana kallanshi, yace “me ya sameki jiya?”


Kallansa tai tace “namanta?”


Kin manta?


Hmmm ta fada tare da kallan gefe.


Fork dinta ya sa a plate din sannan ya kalleta.


Kallansa tai tace “badai baka kake san kace nai ba ko?”


In na fadi haka laifi ne?”


Murshi tai zatai magana taga yasa fork dinsa a ciki bai ce mata komai ba.


Kallansa tai yana ci bai ce mata komai ba.


Tsayawa tai kawai tana kallanshi, ganin taki ci yasa ya kalleta yace “sun kawo wuta?”


A’a


“Me kikai yau to?”


“Ka damu ka sani ne?”


“Banaji”


Haushi ya kamata ta harareshi sannan ta janye plate dinta tace “ai wannan abinci nane, kaci naka.”


Kallanta yai kawai baice komai ba, harta mike kuma ta koma ta zauna tace “ai ma ka cinyen nawa sai kaban naka.”


Murmushi yai yace “nawa da naki ba daya bane?”


Kallansa tai cikin wani yanayi, sai kuma tai shiru, mikewa tai ta shiga daki, kudin nan ta dauko dubu 100 ta zuba musu ido tana kallo, mikewa tai ta fito falo.


Ya gama cin nata yana shan ruwa yaga ta dawo, kallanta yai har ta zauna kusa dashi kadan.


Ajiye kudin tai a kusa dashi.


Kallan bakar ledar yai sannan ya kalleta, tace “kudin ka ne daka kawo.”


Kudina?


Ya fada yana kallanta, tace “hmm nina ce muyi aure dan haka bai kamata na amshi kudinka ba.”


Yanayin fuskarsa ne ya canza, bacin rai ne karara ya bayyana a fuskarsa, Zainab tace “ka amsa nagode da ka kawomin a kalla nasan........”


Yanda taga idanunsa sunyi jaaa sosai ne yasa ta kasa cigaba da maganar, mikewa yai kawai taga ya fita waje, shiru tai tasan bazai amsa haka kawai ba amma itakam zuciyarta bazata iya nustuwa ba in ta tuno kudin nan.


Khalid kam ransa yakai kololuwa gun baci, shikadai yasa yanda zuciyarsa ke tafasa, wayarsa dake kara ya daga.


Salmanu


Bayan sun gaisa yace “dan Allah ka dan kaima Umma dubu daya da dari biyar, zan bata gobe in tazo ta baka, nasan kudin hannunta dasu zatai mota.


To shikenan.


Salmanu zai sake magana Khalid ya kashe dan baisan yai magana mai tsayi kar a gane bacin ransa.


Jin ana kiran sallah yasa ya duba gen din ganin akwai dan mai kadan yasa ya tada.


Shigowa yai tana zaune tana cin abincinta gefe kuma ga kudin nan, baiko ce komai ba ya wuce yai alwala.


Fitowa yai ya kalleta yace “in kin gama kiyi alwala muyi sallah.”


Kallansa tai fuskarsa a daure, ruwa tasha ta dauke kwanukan sannan tai alwala, sallah sukai, bayan sunyi addu’oi tace “Kh......”


Kallan daya mata ne yasata yin shiru, mikewa yai ya shiga daki, ya zauna akan gado tare da daga kansa yana neman kwantar da ransa.


Zainab kam tasan bazai amsa da wuri ba amma dalilin fishin ne bata sani ba, har sukai bacci ba wanda ya sake maganac daga zata mai intaga yanayinsa sai tai shiru, haka tai aikinta sunyi sa’a 8 aka kawo wuta, nan ta cigaba , shikam 9 ya kwanta.


Yauma a daki ya kwanta dan kukan datai jiya ya tabashi.


Karfe 4 ya farka, kallanta yai ta matso kusa dashi tana ta baccinta, bargo ya gyara mata sannan ya mike yai wanka yai alwala yasa kaya.


Zama yai kusa da ita, ya sa hannu yadan tabata kadan.


“Tashi kiyi sallah zan wuce.”


Idanunta ta bude, ta kalleshi.


Haryanzu ranka a bace yake?


Kallansa tai tace “okay”


Yai dan shiru kafin yace “ki gyara gidan kafin suzo, sannan ki yi musu abinci.”


Bata amsa ba sai dai ta kalleshi, yace “wajen azahar zan dawo nima”


Kai ta daga kawai batace komai ba.


Kallanta ya sakeyi yace “insunzo ki tabbatar kin musu sannu da zuwa kin kuma gaisheta kafin ku fara magana.”


Idanunta ne kawai a kanshi, yace “sannan kisa mayafi.”


Ajiyar zuciya tai tace “duk ni kadai?”


Hmm sirikarki ce.


Kai ta daga sannan tace “to.”


Mikewa zaiyi ta riko rigarshj, kallanta yai tace “bazaka.......”


Katseta yai yace “na wuce.”


Shiru tai tana kallansa har ya fita.


*******


Haka ta mike tai gyaran gida, dan tunda tazo yaune ta gyara ko ina ta share, bayanta ne taji ya amsa, tab yaushe raban datai shara? Dan dama ita ba gwanar aiki bace.


Haka ta shiga kitchen tasa shinkafa da miya.


Kallan kudin tai a falo, ajiyar zuciya tai sannan ta dauke ta maidashi kan madubi a daki.


Wajen karfe sha biyu da rabi ta gama abinci tai wanka tana shafa mai taji buga kofa.


Da sauri tasa kaya ta dan shafa hoda tasa turare ta fito, hartazo kofa ta koma da gudu ta yafa mayafi.


Sannan ta fito.


Umma ce ta kalli Asiya tace “nan ne kin tabbatar?”


Asiya tai dariya tace “nan ne wlh Umma zuwana biyu fa da Yaya.”


Umma tai murmushi zatai magana sukaji an bude.


Zainab cikin tsananin jin dadi ta tarbi su Umma.


Haka suka shiga ciki tana mata sannu da zuwa.


Umma kam baki yaki rufuwa, sai jin dadi take.


Ciki suka shiga ta tuna kalaman Khalid hakan yasa ta tsuguna ta gaisheta, Umma ta kalleta cikin jin dadi tace “Zainab”


Zainab cikin jin dadi itama tace “Umma sannunku da hanya.”


Hira ce ta barke Umma nata tambayarta zaman kadaici da sauransu, sunyi sallah Asiya ta taimaka mata suka kawo abinci.


Umma ta kalli Zainab tace “kin fadamai munzo?”


Yace “wajen azahar zai taho.”


Umma tai murmushi tace “sai ki kirashi kiji ko ya taho.”


Cikin kunya ta dau waya tadan matsa.


Khalid na ta gyaran wata mota wacce yake sauri ya gama ya taho yaji kiranta ya daga.


Tace “Su Umma sun iso.”


“Okay ganinan zuwa.”


Nan suka kashe wayar, hankalin Umma nakanta, Zainab ta dawo ta zauna tace “Ya jikin Abba?”


Umma tace “da sauki.”


Suna dan hira wanda duk kalamanta Umma na kula dasu, tundaga yanda take kawo abinci, mantawa datai da spoons sai da Asiya ta dauko, ta kawo ruwa ta manta da cup da sauransu.


Khalid sai biyu da kwata ya samu ya iso, Umma tana kallan ba sannu da zuwa ba komai, har ya gaida Umma basu yi magana ba, Umma ta kalleta tace “Ki kawo wa mijinki nashi abincin.”


Kallan Umma tai dan gaba daya ta juye, tace “ai duka na juye Asiya dan dauko plate ya diba.”


Khalid ne yai saurin cewa “ni nace ta hada gaba daya naga haka muka saba a gida.”


Umma ta fahimci kareta yai sai dai batace komai ba, Zainab ya kalla yace “bani plate.”


Mikewa tai ta daukomai, ta ajiye tana neman tashi ya dan maida ita a wayance, baisan Umma duk ta gani ba.


Kodaga yanayin yanda suke magana Umma tasan da matsala, kallan Asiya tai tace “Asiya kwashe kwanukan ki wanke.”


Asiya ta mike ta kwashe tai kitchen dasu.


Umma ta kalli Zainab sannan ta kalli Khalid ta gyara zamanta, harxatai magana tace “Khalid bamu guri.”


Yace “Umma.....”


Sai kuma ya mike yana kallan Zainab yana fatan kar tai baran barama a gaban Umma, dan duk yanda Umma ke santa in taji yanda ta dauki aure da d’anta lalai da matsala.


Jiki a sanyaye yai hanyr daki Umma tace “ka jira zanyi magana dakai, dan dama babbar maganar a kanka ne.”


Baice komaj ba yai ciki.

Kallanta Umma tai tace “ba auren soyayya kukai ba?”


Kallan Umma tai sai dai batace komai ba, Umma tai jinjina kai tace “Koma auren me kukai bashida tasori a wannan lokacin tunda an riga anyi, ke matarsa ce shi kuma mijinki ne, sai dai wani irin zama ne haka Zainab? Ba girmama juna? Ba ganin mutuncin miji? Sannan da alama ma fada kukai daga aure.”


Kallanta Zainab tai idanunta suka dan ciko tace “Umma!”


Umma tace “na sani nasan duk laifin na Khalid ne sai dai a matsayinki na mace ya kamata ki ja mijinki, Khalid dama tun kafin yai aure ni nasan matarsa sai tayi hakuri da halayensa, sam namiji ne mai wani irin ra’ayi da akida da kuma zafin rai.


Sai dai mu da muke iyayensa mu munsan dalilinsa na yin hakan, duk da hali ne nashi amma ya fara wannan halin ne daga sanda ya shiga jami’a.

Khalid ganin yanda mahaifinsa ke fita tun asuba aikin tuki baya dawowa sai can dare wani sa’in ma baya dawowa sai bayan kwana biyu yasa ya slakanta wahalar mahaifinsa da shi, gani yake mahaifinsa na wannan wahalar ne saboda yai karatu hankali a kwance, wanda kuma a zahiri hakan ne, mun daura burin mu akan Khalid.


Tun daga nan baisan komai ba sai karatu gani yake karatu kawai zaiyiya faranta mana, karatu kawai ya sani, baya ko shiga cikin gida gun mu a lokacin ko a makaranta bai taba cemana gashi da wani abokinsa suna hira ko sunje yawo ba, hankalinmu ya fara tashi ganin dan mu na neman tattare duk rayuwarsa akan karatu, lokacin ne muka sa dokar cin abinci tare, sannan dole in yana gida ya fito a yi hira dashi.


Alhamdulila wannan doka da muka sa itace ta maido da zumunci da kaunar junanmu.


Hatsatin mahaifinsa ya sa daga karatu ya koma aiki, dan a lokacin da abin ya faru ya gama karatu, sai kuma gaba daya rayuwarsa ta koma aiki, bashi can bashi can yana ta faman had’a mana kudin da zamuyi rayuwa, komai na rayuwarmu na kansa, shine cinmu shine suturarmu, shine maganin mahaifinsa, karatun kannensa da sauransu.


Umma ta kalli Zainab wacce tai shiru sai kwalla dake zubo mata.....


***

Ayusher🏌🏻‍♀

[1/9, 12:21 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


{59}


Zainab ta kalla ta kamo hannunta wanda hakan yasa ta dago ta kalleta.


Kinsan meyasa nake fada miki hakan?


Shiru Zainab tai sai maida kai kasa datai.

“Ke da shi kun taso rayuwa daban daban, akwai abubuwa dayawa da zakiga basu miki ba a zaman takewarku dashi, Khalid ko bashida lafiya baya taba fadamana, duk kuwa yanda yake jin wahalar ciwo baya taba fadamana, saboda bayasan mu damu, in dai har zai zauna da mutum to baya san ya zama ila ko takura ga wanda yake tare dashi.”


Dan dakatawa tai saboda idanunta dasuka dan ciko, tace “ shi da kanshi bazai taba iya fada ba, wanda hakan zaisa a koda yaushe cikin ko wani hali yake zai cigaba da boyewa.”


Murmushi tai tace “Zainab kuyi hakuri da junanku, shi aure tunda ibada ne dole sai an jure, akwai lokacin sabawa akwai lokacin shiryawa, sai dai kada ya zama in ya hade rai kema zaki hade, ko in yana fishi kema zaki dau fishi, Khalid d’ana ne, sai dai bazan fifita shi saboda ke ba tawa bace, ina fatan zaku kula da junanku ku dau junanku a matsayin abu guda d’aya.”


Kai Zainab ta daga cikin wani yanayin, Umma ta kalleta ta kalli agoggo tace “yima Khalid magana yazo zamu wuce, nabar Abbansu a gida ba babba.”


Zainab na mikewa tace “Asiya.”


Asiya dake tsaye a hanyar kitchen tana jira su gama ne ta shigo.


Umma ta kalleta tace “kingama?”


Eh Umma.


Zainab ce ta tura kofar, yana zaune akan gado hankalinsa na waje, haka kawai hankalinsa yaki kwanciya, mikewa yai ya zo bakin kofa ya tsaya yana tunani.


Tana bude kofa ya sa hannu ya jawota ya maida kofar ya rufe, kallansa tai fuskarta dauke da mamaki.


Shima kallanta yai, hannunta da ya rike da karfi ta kalla sannan tadan murza hannun alamar zafi.


Sassauta rikon yai yace “oh sry, me Umma tace miki?”


Idanunsa ta kalla tace “me kake sanji?”


“Ke nake tsoro kar ki fadi ba daidai ba.”


Harararsa tai tace “Umma na jiranka.”


kai ya dan kauda yace “badai kiyi baran barama ba ko?”


Tace “Umma tace ka fito zasu wuce.”


Kallanta yai sannan ya saketa ya juya zai fita, da sauri tace “ka kaisu a mota.”

Juyowa yai ya kalleta a hankali tace “please.”


Kallanta yai fuskarsa a sake jiyai tace “Kaji?”


Murmushi yai sannan ya kalleta yace “muje tare?”


Kai ta girgiza alamar a’a tace “kaje ka dawo”


Okay yace sannam ya dau key yasa a aljihunsa ya fito.


Da kallo ta bishi wani irin tausayinsa ne ke ratsata gaba daya jikinta, daurewa tai ta fito hannunta dauke da leda data sa ma Asiya atamfa a kayan data dauko a gidanta, da dubu biyu a ciki.


Haka sukai sallama harta cema Umma dan Allah wani hutun Asiya tazo.

Umma tace “shikenan, tunda naga akwai wani dakin ta zo insha Allah.”


Har jikin mota ta rakasu, ta ba Asiya ledar da wayau ta juya bayan taga fitarsu.


Suna fita Umma ta kalli Khalid tace “Khalid!”


Yace “Naam Umma.”


Kallansa tai tace “yaushe mahaifiyarta ta rasu?”


Shiru yai Umma tace “da alama ta dade ba tare da ita ba, dan Allah ka kula da ita, ina tausayinta, duk inda kaga aure yayi kargo to lalai miji ne, in har kaga aure ya tabarbare to miji ne, na san halinka sarai sai dainina fatan zaka canza saboda ita, ka ba rayuwarta mahimmanci, ka bata kulawa wanda ta dace dashi, na tabbatar kana santa, to ka jata a jiki ka fahimtar da ita hakan.”


To Umma abinda yace kenan yana tuno kukan datai ranan.


Umma ta kalleshi tace “ko abinda mijinta ya mata ya isa ta samu farinciki, ina tausayin ta matuka, ina fatan ku ba juna kulawar da kuke bukata, tana bukatar lokacinka, ko yaya ne ka kokarta ka bata.”


Shiru yai haka Umma tai ta dan sanar dashi lamura da hakuri har ya kaisu tasha, dan yaso kaisu ma ta hanashi dubu biyu ya ciro a wallet dinsa ya mika mata yace “kiba Salmanu 1500 daya baki jiya, ya sa hannu a aljuhu, dari biyar ya ciro yace ki kara wannan dubu daya kenan sai kudan lalaba kafin karshen satin nan zan turo kudi.”


Murmushin karfin hali tai tace “Allah ya kawo sanda zaka huta Khalid”


Tai maganar tare da share kwallarta. Murmushi yai yace “bakomai Umma muyi fatan Allah ya sa musu albarka dai.”


Umma tai murmushi tace “haka ne Allah ya musu albarka.”


Kallan Asiya yai yace “yar Umma ba’a baki na yin iloka ba.”


Kallansa tai ta dago leda tace “Aunty!” Tai maganar cikin kama kai na mai laifi.


Umma ta kalleta sannan ta kalleshi.


Asiya tai tsuru tana jiran fada sai jitai yace “kinyi godiya?”


Da sauri ta kalleshi tace “bansan ta ajiye ba sai da ka tada mota.


Inkinje gida ki kira a wayar Umma kiyi godiya.


“Nadauka zaka min fada”


“Auntynki ce yanzu da barece zan miki.”


Murmushi sukai dukansu, nan suka sauka yana ce mata zaizo dan zuwa asibiti karshen wata saboda lokacin Abba ne da zai ga likita.


Nan suka tafi ya juyo, har ya isa gida zuciyarshi sam ba dadi, inya tuna ko sanda mahaifiyarta ta rasu bai sani ba wani haushin kansa ne yake damunsa.


Yana shiga duhun magrib na kawo kai, hannu yasa a aljihu ya tuna ashe bashi da kudi, ga mai jiya ya kare, shiru yai a waje idanunsa sunyi jaa yana tausayin ta, inya tuno gidan mahaifinta da gidanta sai yaji duk ya raina kansa.


Jin ana kiran sallar magrib yasa kawai ya fita ya gangara masallaci.


Zainab kam tunda suka tafi ta shiga daki ta zauna a kasa a lungun gado, kanta ta kwantar a kan gwiwowinta, bazata taba yafema su Kabir ba taji zata yafe musu na abinda suka mata amma Allah bazata yafe musu na korar Khalid ba, jin yanda ya taso cikin karatu da aiki ace aikin daya samu an koreshi saboda ita bazata taba yafe musu ba, dan itakam gani take duk saboda ita ne.


Sam bata damu da daren daya kawo kai ba, waya ta dauka ta duba site din gidan tv din su, ganin yanda abubuwansu ke tafiya ba wani ci gaba sai ma ci baya yasa ta cigaba da karantawa tana duduba shirye shiryensu.


Jin bude kofar dakin ne yasa tadan juyo.


A hankali ya karasa inda take, ya zauna a kasa kusa da ita yai zama irin wanda tai yana kallanta.


Murmushi tai tace “ka dawo?”


Sannu da zuwa!


Au sannu da zuwa, ka kaikus?


Ummm sun wuce, kinyi sallah?


Kallansa tai sannan tadan sa hannu a kafadarta, yace “kinyi?”


Nayi la’asar.


Magrib nake tambaya.


Kai ta dan girgiza tace “ina fashi ko shima sai na fito dala dalla?”


Murmushi ya sa ya matso kusa da kunnenta yace “me yasa baki fadan yau bane?”


Kallansa tai tace “oh ni yaushe ka koma haka wai?”


Dariya yai yace “dazu? Yanzu? Jiya?”


Hannu tasa tadan turashi tace “da alama haka kake tun da”


Hannun data turashi dashi ya rike, yanayin kallan da take mai yake mata ne ya canxa, yanzu kam tausayin junansu suke.


Murmushi mai sanyi ya mata yace “kina shekara nawa Ummy ta rasu?”


Idanunta ne suka ciciko da kwalla tace “da alama bamu san komai game da junan mu ba.” Tai maganar hawaye na gangaro mata tana kokarin yin murmushi.


Hannunsa ya sakalo cikin nata ya sako kansa kan nata kan yace “i am a bad person.”


Idanu ta rufe tace “a’a i am the bad person here.”


Wani abu ya had’iya yace “fadamin yaushe ta rasu?”


Kanta ta zame ta kwantar da kanta akan kafadarsa tace “ina 9 years, sanda ta haifi Nabila.”  Tai maganar cikin rauni.


Hannunsa dayan ya zagayo dashi ya shafi fuskarta yace “bansan tun kina yarinya bane.” Yai maganar cikin rawar murya.


Hannun dake kan fuskarta ta daura nata hannun akai tace “matar Dady teacher dina ce a skul”


Teacher?


Ya tambaya cikin yanayi na mamaki, dagowa tai ta kalleshi cikin duhun dakin tace “hmm nice na kawowa Ummy abinda zai lalata rayuwarta, na kawowa Dady wacce zata shiga rayuwarsa data iyalinsa, na ba Adam damar tarwatsa rayuwarsa, kaima gashi na shiga taka rayuwar ina neman hanaka..........”


Bakinsa dataji cikin nata ne ya sa ta kasa ci gaba da magana sai hawaye dake gudu akan kuncinta, hawaye me yaji ya zubo a fuskarsa, raban dayai hawaye harya manta, saboda sam duk abinda yazo gabansa mutum ne mai jajircewa.


A hankali ya dago bayan sun gama sumbatar juna, hannayensa yasa akan fuskarta ya dago da fuskarta yace “bake bace dalilin dayasa hakan ya faru da Ummy, sannan Adam zuciyarsa ce ta lalatashi ba ke ba, ni kuma nine na shiga rayuwarki ba ke kika shiga tawa ba.”


Hawaye ne ya zubo mata tace “koba ni nai komai ba akanka kam nasan nice” tai maganar hawaye na sake zubo mata.


Jawota jikinsa yai ya rungume tsam cikin wani yanayi, sai data huce sosai sannan ta dago, wayarsa ya kunna, yace “am sorry gobe zan siyo mai.”


Kai ta daga tace “bakomai”


Yace “sannan kudin dana baki na gaisuwa nine nai ra’ayin baki sannan abune daga cikin al’adarmu ta hausa, na kuma yine dan karan kaina, karki kara neman bani abinda na bada a auranki, ki barni naji da.” A ransa ya karasa da rashin lefen da ban miki ba.


Murmushi tai tace “okay”


Fadamin ya Ummy take? Kamarku daya? Yai tambayar yana kwantar da ita akan cinyarsa.


Kallansa tai tace “kamarmu daya, ai kaga bana kama da Dady.”


Inji wa?


Injini.

Ta fada tana dariya, ido ya zuba mata baice komai ba.


Shiru tadanyi harya dauka bazatai magana ba sai kuma tace “Lokacin Ummy da Dady ni kadai ce a gunsu, yanzu abubuwa dayawa bazan iya tunawa ba a abinda ya faru a lokacin, sai dai a kwakwalwata nasan suna tsananin so na, ina kuma jin dadin yanda rayuwata take a wannan lokacin, kafin a kawo Basma sabuwar Aunty skul din mu..............”


Abinda ya faru a baya ta sanar dashi, hawayen dataji na diga akan fuskarta ne yasa ta runtse idanunta zuciyarta na wani irin bugawa da karfi? Hannu tasa akan fuskarsa.


Jin hawayen daga idanunsa yake yasa zuciyarta ta kara rauni, mikewa tai ya jawota jikinsa, ya matseta sosaj, haushin kansa ne ya kamashi, taya zai kira kansa miji bayan baisan komai game da ita ba? Yana mata kallan dan ta taso cikin kudi, tana komai da kanta yasa take ganin komai dole ya tafi yanda take so?


Jin yanda take kuka tana cewa “Kayi hakuri.”


Ya karasa zuciyarshi yin rauni, meyasa take bashi hakuri? Bayan shine zai bata?


Khalid me kake yi????


Wata ajiyar zuciya hai wacce kana jinta kasan wanda yake cikin yanayi na karayar zuciya ne yake yinta.


Zainab ce tace “shiyasa bansan komai ba sai aikina, gani nake shine zai kwatomin darajata, kayi hakuri nayi amfani dakai bansan halin da kake ciki ba kenan.”


Dago da ita yai ya kalleta sosai yace “why me?”


Idanunsa ta kalla, yace “sanda kike neman wanda zaki aura, why me?”


“I don’t know i just feel like in har dakai ne i can do much better”


Gani tai yayi murmushi, sannan ya kalleta yana shafa gefen fuskarta yace “shiyasa bakya san yanda da mutane?”


Ummm gani nake kowa na amince dashi haka zaimun yanda Adam da Dady sukai akan mace.


Nifa?


Dan kanta tadan kwantar kan hannunsa tadan lumshe ido ta bude tace “bansani ba.”


Murmushi yai yace “Umma gulmata ta miki ko?”


Ummm tasan bazaka min da kanka ba.


Murmushi yai yana kallanta, itama murmushi tai tare da kai kanta kasa, hannu yasa ya jata kan cinyarsa yace “kin yadda dani?”


Kallansa tai tace “bansani ba”


Hannayensa yasa ya zagayota yace “in sanar dake?”


Murmushi tai tace “bana sal......”


Iskar daya farzar ne yasata yin dariya, dagata yai ya mike tace “ina zaka?”


Wanka zanyi na tafi masallaci.


Murmushi tai har ya dau towel sai ji tai yace “ko zaki taimaka da......”


Ai bai karasa ba ta mike cikin hanzari ta fita daga dakin garin sauri har kafarta ta buge amma bata nuna ba, murmushi yai sannan ya zauna a bakin gado.


Shiru yai yana tunani, kenan ba dan Umma ta nunamai ba haka zaita daukanta ayanda yaso? Itama haka?


Taya tai rayuwa da abubuwa biyu? Gana uba ga rashin uwa? Sannan miji yazo daga baya? Sannan aikinta?


*********


Duk yanda taso tai bacci ta kasa, screen din wayarta ta bude, hoton Khalid wanda ya dauka ranar graduation dinsu ne akan alan wayar, ajiyr zuciya tai sannan ta kira number Adam.


Adam dake zaune ransa a bace yana kallan su Kamal nacin shinkafa yaje ci yace mai wai gaskiya a’a bazai bashi gun kwana abinci ma ya dinga bashi ba, haushi duk yabi ya isheshi.


Ganin kiran Afreey yasa ya daga ba tare da ya sani ba.


Tace “Adam ka nemo?”


Jin muryarta yasa ya mike tsaye da sauri, yace “naam?”


Tace “dama dubu goma zan baka tunda baka nemo inda Khalid yake ba shi.......”


Wallahi na nemo.


Wani wulakantacen murmushi tai tace “ina ne?”


Ban san ina bane amma tunda munyi waya dashi in na tambayeshi zai fadamin.


In ka nemo ka fadamin sai na tabbatar zan turoma kudin.


Da sauri yace “zuwa zakiyi?”


Wannan ba damuwarka bane.


Me kike gani in na kirashi kikazo inda zamu hadu?


Yai tambayar yana neman sa’ar amincewarta.


Me yake a kano?


Bansani ba nima in mun hadu ma tambayeshi ko?


Shiru tai dan bata yarda da Adam ba amma tace “to ka mai magana sai na jika.”


Ta kashe wayar tare da zubawa hotonsa ido cikin shagwaba tace “Khalid!”


Nace hmmmmm🤢🤢


*******


Bayan yayi sallah ne sukai sa’a nepa suka kawo wuta, cikin jin dadi ta kalleshi sai kuma tasa yar dariya.


Yace “aikin ya tashi ne?”


Tace “Me kake gani zaifi batawa su Kabir rai?”


Akan me?


Kawai da in bude gun aikina daban da kuma in bude in kwashe masu kwazan aikinsu wannan kake gani?


Murmushi yai yace “gashi kin fada.”


Cikin jin dadi ta kalleshi, yau ne ya fara amsa mata akan tambayar aiki da take mai.


Harta dauko laptop suka dauke wuta, kallan Khalid tai kamar zatai kuka.


Yce “sorry zasu dawo dashi.”


Haka ta maida laptop din, tara nayi ya fara hamma.


Kallansa tai ba dole ba yanata uban aiki kullum ba hutu.


******

Ayusher🏌🏻‍♀

[1/9, 12:22 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


{61}


Gaba daya ji tai numfashinta na sarkewa, mai lemo ne ya matso yace “baiwar Allah lafiya?”


Khalid wanda ya shiga mota yaja ya fara tafiya a hankali yana kallan glass din madubinsa ta baya, Zainab a kufule tace “in kasan bakasan barinta meyasa ka taho?”


Kallanta yai yace “am sorry amma sai na dan duba halin da take ciki, kar wani abu ya faru.”


Baki Zainab ta bude cikin mamaki tace “badai fadamin kake zaka koma inda take ba?”


Eh, ya fada tare da dan yin baya da motar, Zainab kam wani mugun kishi ne ya turnuketa, Khalid ne yai parking ya juya yana kallan bayan motar inda Afree take a tsaye mai lemo na mata magana.


Zainab ce ta juya tana kallanta, sanye take da riga english wears rigar takai mata gwiwa, sai wando jeans pencil, ta yane kanta da mayafi.


Wani irin kishi ne ya kara rufeta, Khalid ta kalla wanda ke kallanta sanda ta wuce ta shiga mota ji take kamar zatai hauka.


Juyowa yai sannan yace “kina ganin ba matsala?”


Wata uwar harara ta watsamai tace “in da matsala ka je ka kaita gida mana.”


Okay to ko zaki fara zuwa sai na biyoki?


Tace “mene?”


Gani tai yana neman fita cikin hanzari ta rikoshi tace “da gaske zuwa zakai?”


Eh na dauka mun gama maganar? Ya fada yana kallanta.


Idanunsa ta kalla tace “ka ajiyeni ni matarka ka tafi gun wata?”


Bakya ganin halin da yake ciki? Sannan waye yace min duk sanda naso nai aure?


“Halin da take ciki?ni halin da nake ciki fa?”


Ido ya kura mata hana kallanta, ta kauda kai tace “maganar aure ai ba auranta kai ba.”


“Bari na je gidansu daga can na gabatar da kaina.”


Ya fada tare da juyawa yana neman fita, da sauri ta kara rikeshi tace “wai da gaske kake?”


Kinga alamar wasa a nan?


Tace “maidani gida.” Ta fada cikin raunin murya.


Yace “ke dai kikace naje gidansu yanzu.”


Yaushe na fada?


To meye na hanani?


“Bansani ba amma nidai.......”


Sai kuma tai shiru, murmushi yai ya matso saitin kunenta wanda hakan yasata dan dagowa, yace “fadamin sunana.”


Sunanka?


“Eh, in ba haka ba yanzu na fita na maidata gida.”


Kai ta dauke tace “meyasa ka taho guna kasan hankalinka yana gunta?”


Fadi kona koma gunta ki fada.


Dan baki ta motsa yace “banji ba.”


Ta kara motsa baki, shikenan tunda bazaki fada ba, ya koma ya zauna.


Kai ta juya tana kallan waje ta glass tace “Sweet.”


Murmushi ya saki, ya juya yaga ba motar Afreey agun, ajiyar zuciya yai yana fatan Allah yasa ta cireshi a ranta.


Zainab ya kalla yace “Ur sweet is here.”


Samun kanta tai da jin kunya, murmushi yai sannan yaja suka tafi.


Hade rai tai, hannu yasa ya kamo hannunta, kallansa tai tace “meyasa baka bitan ba?”


Ina zan bita bayan naga bakya so?


Shiru tai tana tunanin shigar da Afreey tai da yanda tai kwalliya, maza irin haka suke so? Meye damuwata da abinda suke so?


Sake sake tai tayi har suka isa.


********


Cikin gidan aka bude musu gate sukai parking ba wai katan gida bane sai dai kana ganinshi kaga gidan dake da rufin asirinsu, a gun talaka kuwa gida ne na masu kudi.


Ledar hannunsa daya dauko ta kalla kallanta yai sannan ya kalli ledar da take kallo, mika mata ledar yai yace “ki rike.”


Amsa tai ta rike.


Bangarenta suka wuce Zainab tai knocking din kofar, daga ciki wata yarinya wacce batakai Asiya ba tazo ta bude.


Cikin tsananin murna tace “oyoyo Aunty.”


Zainab ta kalleta tace “Amira kece kika girma haka?”


Amira ta basu guri suka shiga,


Falo suka shiga, Zainab tace “ina yaran gidan?


Suna islamiyya


Kefa?


“Bana jin dadi ne, Umma na sallah ne”


Zama Khalid yai a kasa, Zainab ta kalleshi tace “ka hau kujera mana.”


Kai Yadan girgiza mata zatai magana Aunty ta fito sanye da hijab tace “ikon Allah, wallahi ban dauka ds gaske kike ba.”


Zainab ta kalleta tace “kai Aunty.”


Zama tai akan kujera tana kallan Khalid tace “lale lale, Ango godiya nake dan nasan Allah Zainab haka kawai bazatacs zatazo ba.”


Gaisheta yai, ta amsa cikin girmamawa yanda taji ya gaisheta cikin girmamawa.


Cikin jin dadi take kallansa sannan ta kalli Zainab wacce ta rasa ina zata zauna, ganin Khalid a kasa.


Tace “Amarya.”


Zainab ta dake ta zauna a saman kujera tana amsa gaisuwar Amira.


Amira dake tsugune ce ta gaida Khalid ya amsa yana tambayar ta makaranta.


Zainab ta mika mata ledar sannan tace “Ajinta nawa yanzu?”


Aunty ta kalleta tace “ko kunya ma tambaya kike?”


Dan dariya tai tace “Rabona da ita na dade.”


Aunty ce ta mike tai kitchen, sai data shiga sannan ta sa Amira ta kira Zainab.


Nan suka hada kayan da aka shirya dominsu, wanda tayi ne tana san ganin ko da gaske take.


Khalid kam zubo yasha yaci samosa guda daya, wayarsa ya dauka ya mata text, ko na barki na dawo da daddare?


Da sauri ta mai reply tace “a’a”


Murmushi yai sannan ya mike, Amira data fito ya kalla yace “Auntynki zata tsaya anan wai sai dare, ko zakima Umma magana zan wuce sai na dawo?”


Juyawa tai ta sanar da Mamanta, Zainab dake zaune mamaki ya kamata yaushe tacemai zata zauna?


Mikewa tai ta fito falo, kallan Aunty yai yace “Aunty na dawo daddare tace tana nan ita.”


Cikin farinciki ta kalli Zainab tace “masha Allah nagode sosai Zainab.”


Zainab tai yake kawai, haka ya fito tabi bayanshi, suna fita waje tace “yaushe nace zan zauna?”


Dazu ko kin manta?


Cikin mamaki tace “A’a fa nace.”


Au haba? Nikam eh na gani.


Tace “ni Allah bansan doguwar hira, ki daure kanwar Ummy ce ita kanta tanasan kadaicewa dake.


Dan baki ta turo yai murmushi yace “sai na dawo.”


Haka tana gani ya shiga mota, ya kalleta yace “ko na kawo miki laptop dinki? Naga suna da wuta.”


Kallansa tai tace “Lalai ma.”


Murmushi ya yace “ki fadi sunan.”


Tace “naki.” Ta juya tai hanyar ciki, jitai yace “bazaki fada ba?”


Da sauri ta wuce ciki tana murmushi.


********


Marin data xuba maine yasashi gigicewa, hankali a tashi ya kalleta yace “Afreey yadaga zuwana zaki wankeni da mari?” Ya fada tare da rike gun.


Cikin hucci take kallansa tace “ni zaka maida yar iska?”


Kamar ya? Haryanzu hannunsa na kan fuskarsa dan yaji abin.


Hannu ta daga tana neman kara mai wani yai baya da sauri yace “Afreey lafiya?”


Cikin tsananin masifa da tashin hankali tace “ta ina? Taya Khalid zai aureta?”


Adam ya kalleta wato taji yayi aure kenan?


Kallan Adam tai tace “uban me kake har hakan ta kasance?”


“Ni kuma? Wai ya kikeso nai da Khalid ne?”


“Fadamin inane gidansa?”


“Ina na sani?”


Haushi ya tuketa tace “ai kasan inda gidan matarka yake, ina ne?”


Adam cikin rashin fahimta yace “gidan matata suke?”


Jakar hannunta ta cillo inda yake ta sameshi kuwa, kallanta yai yace “Afreey lafiya?”


Cikin masifa tace “kana haukar ina Zainab ta auri Khalid?”


Kallanta yai kawai kuma ya bushe da dariya yace “Afreey yunwa kike ji? Wace Zainab din?”


Wani kallo tamai hawaye na zubo mata tace “bakada hankali amma ko? Tun yaushe nace ma akwai abu a tsakaninsu?”


Jin abin yai sama taka kamar irin an mai duka din nan.


Kusa da ita ya matso yace “kina san cemin Honey ce matar Khalid ko me?”


Sai yaushe zaka fahimta? Sau kuma nawa kake san na fada? Da idona fa na gansu.


Baya baya ya fara yi yana girgiza kai alamar a’a, wayarsa ya dauko da sauri ya kira number Goggo.


Goggo kam acan tun jiya take kwance ba lafiya, ita kadai a dan tsukukun dakin da take, yunwa ta gama cinta harta gaji, gayan tuwon dake gefe ta dauka ta hauci, wallahi yau zata bar kauyen nan ko menene sai dai ya faru amma bazata zauna ta mutu ba, dole ya samu ko hamsin ne tasa a waya ta kira Hajiya Bilki ko aikatau ne ta samar mata amma bazata zauna awannam gidan ba.


****


Adam kam duk yanda ya kirata rashin service yasa taki shiga.


Haka ya hakura yana dagowa yaga Afreey bata gun, hankalinshi a tashe ya dannawa Khalid kira.


Khalid na ganin kiran bai daga ba dan yasan dalili shikuma bai san suyi magana ta waya, dan yanasan sashi yaje gidansu Razy abubuwane suka hadarmai yasa ya manta.


******

Acan gidan Aunty kuwa, Zainab batasan sanda ta sake ake ta hira ba, yayin Amira ne suka dawo su Samira.


Kaya suka cire, Samira tasa riga da wando ta fito.


Zainab ce ta kalleta sannan ta shiga daki ta kirata.


Samira ta shigo tana cewa “Aunty gani”

Zainab ta kalli Kayan tana tuno Afreey, sannan tace “kayan jikinki ina ake saida irinsu? Nabila ce take so.”


Samira tace “gasu nan a ko ina, akwai a stores akwai a kasuwani irinsu saban gari.”


Shiru tai dan batasa saban gari ba, amma ta dake tace “zan fadamata”


Haka suka dawo ana hira itadai sai duba waya take.


Khalid kam sai 8 na dare ya taho, wayarsa daya kashe saboda kiran da Afreey keta mai ya kunna.


Texts ne suka fara shigowa.


Kansa yadan dafa sannan yaa Zainab text akan yana hanya.



*****

Ayusher 🏌🏻‍♀

[1/9, 12:22 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


{60}


Yau harya shirya tana bacci, kusa da ita ya nufa ya sunkuyo ya sumbaci goshinta, sannan ya fita, yana tafe yana addu’ar dacewa da aiki dan bai taba jin haushin fita da sassafe da yake ba irjn yau.


Haka ya wuce gun aikin ginin da suka ci karfi dan an kusa kammalashima.


Zainab kam tana ta bacci, wani irin bacci take wanda take jin dadinsa matuka, kamar a mafarki takejin buga gate, idanunta ta bude sannan ta kalli agoggo, a zabure ta mike zaune ta kara kallan wayarta da gaske 11? Wani irin bacci ne hakan?


Jin bugun kofa yasa ta mike toilet take san shiga amma ganin kar wanda ke bugawa yaji haushi yasa ta zura hijab ta fito.


Tana budewa taga matar na kokarin juyawa, jin karar budewa ne yasa ta juyo ta kalleta tace “oh ashe kina nan.”


Zainab ta kalleta cikin rashin fahimta, dariya matar tai tace “Maman Al’amin ce daga nan gidan.” Ta nuna mata makotanta.


Zainab tace “oh Allah sarki.”


Ta fada tana kallanta, Maman Al’amin tace  “bari na shigo mu gaisa dan inata sa rana bansamu na zo ba.”

Jin haka yasa Zainab ta fahimci ciki take san shiga hakan yasa tai gaba da sauri, shigowa tai tana cewa “ba dai bacci kike na tasheki ba?”


Zainab ta kalleta tace “taimako kikai ai.”


Dan dariya tai suka shiga falo, ta zauna sannan suka gaisa cikin mutunci.


“Ina tacewa zanzo gun Amarya mu gaisa amma inata famar hidimar aiki.”


“Masha Allah, a kalla yafi zaman haka.”


Dariya tai tace “duk da agida nakeyi amma sosai nake samu.”


Zainab tadan jinjina kai.


Murmushi tai ta kalli Zainab tace “a kano kike?”


“Eh rabi.” Ta fada tana murmushi.


Maman Al’amin tai dan dariya tace “Allah sarki, ni anan kano nake.”


Bata jira Zainab tace wani abu ba tace “ga wannan, nasan ku amare ba a rabaku da ‘yan abubuwan ku, zan shigo na rasa mai zan kawo miki shine na dauko abinda nake saidawa.”


Ta fada tare da mika mata ledar.


Bude ledar Zainab tai cikin rashin fahimtar menene a ciki ta kara daga robar ruwa wanda aka cika ta da wani abu dark brown, sannan sai kulin garin abu kamar kuka a leda fara, dayan kuma abu ne a dunkule a cikin ledar.


Kallanta tai tace “menene?”


Dariya Maman Al’amin tai tace “haba haba, Amarya kodaga shekarunki ai nasan lokacin auren ne dai baizo da wuri ba, kar kisani dariya taya zaki nuna baki san menene ba?”


Cikin mamaki Zainab tace “na menene? Allah ban sani ba.”


Baki ta bude tace “shekararki nawa?”

Nan da wata biyu zanyi 29, baki ta sake budewa tace “amma baki san wannan ba?”


Eh, abin mahimmanci ne?


Gaba daya kallan mamaki take mata tace “ikon Allah, yanzu yara yan 16 ma sun san kayan mata balle ke?”


Kallanta tai sannan ta kalli cikin ledar, ko irinshi maman Basma ta bata? Amma ita kazace sai su ruwan kankana, wannan kuma daban.


Maman Al’amin ganin da gaske Zainab bata sani ba tace “kiyi kokari ki shanye na ruwan, wannan kuma ki dinga diba kina sawa a nono ko yoghurt kina sha, in kika sha kikaji amfaninsu na miki bayani.


Zainab ta jinjina kai cikin gamsuwa tace “insha Allah, nagode sosai.”


Mikewa tai ta kawo mata ruwa da dubulan dasu alkaki, kadan taci sannan tace zata wuce saboda tana da gyaran Amarya da zatayi.


Zainab ta zuba mata su a leda ta rakota har kofa sannan sukai sallama, komawa ciki tai ta wuce tai wanka ta sa kaya sannan ta shiga kitchen ta daura indomie, wayarta ta dauko sakon Khalid ta gani da alama dazu ya mata.


Kin tashi?


Murmushi tai kamar yana ganinta tace “bayan makara nai, sai fa 11 na tashi.”


11? Dama agoggo ta iya bacci haka?


Nice agoggo?


Murmushi yai sannan ya maida wayar ba tare da ya maida mata ba, Hello?


Nice agoggon?


Haushi ne ya kamata ta ajiye wayar, indomie dinta ga juye ta fito falo tana kallan wayar, har ta cinye baiyi reply ba.


Haushi ya kamata ta juya wayar ta rufeta, kitchen ta shiga ta wanke kwanukan sannan ta kalli ledar, a hankali ta bude robar ruwan ta dan lashi kadan.


Meye wannan?


Ta tambaya tana dan kara kai bakinta kadan ta dan kurba.


Ajiye wa tai ta rufe robar tana cewa “aikam ban iya sha.”


Fitowa tai falo ta dau wayarta, ganin missed call din Khalid yasa ta kirashi da sauri.


Harta katse bai daga ba, ajiyar zuciya tai tace “me kuma nai?”


Jin karar wayar ne yasa ta kalleta, hannu takai zata daga sai kuma ta hau dan kwantar da zuciyarta sai da ta bari tai ringing uku sannan ta daga.


Kina san wani abu ne?


A’a


Okay sai na.......


Kashewa zakai?


Eh da wani abin ne?


A kufule tace “bakomai” kafin ma ya kashe ta kashe.


Fuska ta bata sannan ta tambayi kanta, me nake san ji?


Koma menene a kalla ba kawai ya tambayen ya kashe ba.


Kwan wuta ta kalla suma wadan nan nepan banda rashin mutunci sai yaushe zasu kawo wuta?


Waya ta daga ta kira Nabila suka fara hira, wacce rabin hirar mita take mata akan Khalid ya kira wai kawai ya tambayeta abu yace zai kashe.


Dariya kam Nabila tayishi harsai da cikinta ya kulle, tace “Aunty ni wlh girki nake karkisa na kone.”


Girki? Ta maimaita sannan tace “nabila sai anjima.”


Da sauri ta kashe ta kalli agoggo, karfe 3?


Mikewa tai ta wuce kitchen kamar wacce aka mintsina kawai ta hau yin abinci.


Khalid kam dadi yaji dan yauma da wuri yabar garage gida ya nufo hannunsa dauke da bread, da mai na gen.


Harya shiga falan baiji mostinta ba, hakan yasa ya nufi daki, bata daki sai dai jin karar ruwan flushing daya ji ne yasa yasan tana toilet, murmushi yai sannan ya zauna a bakin gado ya zubawa kofar toilet ido yana jiran ta fita.


Bude kofa tai, sam batasan zata ganshi ba hakan yasa gabanta faduwa, ganin yanda ta tsorata ne yasa ya taso  da sauri, tsoro kikaji?


Kallansa tai sannan ta harareshi tace “ba tsoron kaso bani ba?”


Kallanta ya sake yin ya rike hannunta yana kallan fuskarta.


Samun kanta tai da yin kasa da idanunta, murmushi yai yace “dazu kinji haushi ne?”


Dagowa tai ta kalleshi ta bata fuska tace “ba haushin kaso bani ba?”


Murmushi yai yace “haka ne?”


Ba hakan bane?


Sun kawo miki wuta? Ya tambaya yana zama akan gado.


Kh......


Sai kuma tai shiru, yace “Khalid zaki ce?”


Shiru tai tare da kauda kai, yace “fada gani.”


Kallansa tai tace “Khalid wai me yasa kake san cemin agoggo?” 


Ta fada cikin dakewa.


Khalid?


Kallansa tai sai kuma tai shiru, Khalid? Khalid? Ya maimaita sannan ya mike ya shiga toilet.


Shiru tai tare da binshi da kallo, ko banza na rama, ta maimaita tare da yar dariya.


Kitchen ta wuce ta juye abincin sannan ta dawo falo.


Fitowa yai sanye da yar karamar riga da wando.


Kallan ta yai, ta kalleshi taga ya daure fuska, dariyarta ga guntse har yazo inda take, gani tai ya zauna a kasa inda take ya mika mata man zafin hannunsa.


Kallansa tai ya dago kansa yana kallanta, amsa tai jikinta a sanyaye.


Rigarsa ya daga yace na shafa anan, ya nuna mata kafadarsa.


A hankali ta lakuto tana shafamai gaba daya jikinta yai sanyi, jin yanda take shafawa a hankali yasashi lumshe idanunsa.


A hankali yace “me kike cewa wancan Mutumin?”


Wani mutumin?


Wancan mutumin dai, sunanshi kike kira?


Yanzu kam ta fahimta hakan yasata cewa “meyasa kake sanji?”


Kansa ya sake dagowa yana kallanta yace “in fadamiki?”


Eh!


Hannunta ya riko ya ya juyo tare da dan mikowa yana kallanta, yanayinta ne ya canza, tana kallansa, in fada miki?


Da sauri ta dago man zafin saitin fuskarta tace “ka manta?”


Wani abu ya had’iya yace “ina dai tausayinki amma ai ba dole.....” sai kuma yai shiru tare da yin murmushi.


Zama yai kusa da ita yace “Allah karki kara cemin Khalid.”


To me kake so na cema?


Shima sai na fada miki?


Ahh to zan ce ma K? Tai fadi yanda ake kiran K


Ke? Kin manta keke, ko dayake ki fada nima sai na ce miki Z, ya fadi Zet yana kallanta.


Z? Eh ba K kika ce ba?


Allah bazan yadda kacemin Z ba.


Dariya yai sannan yace “Auntyn ki dake garin nan a wace unguwa take?”


Sharada menene?


Ko zaki kirata ki fada mata zamu je?


Ido ta zaro tace “muje ina?”


Kallanta yai yace “gaisheta, ki kirata kiji in gobe tana nan.”


Baki ta bude tana kallanshi, sai dai samun kanta tai da jin dadi a kasan ranta, tunda take da Adam bai taba ce mata ko Auntynta ta gaida ba, ita dama zumuncin bai dameta ba balle taje, in har taje gidan to lalai haihuwa ce ko biki, bata taba kawo yau ya kamata taje su gaisa ba.


Kallan Khalid tai fuskarta dauke da murmushi ta sauko ta ja plate ta fara zubamai abinci, hannunta dake komarin suba miya ya rike, a hankali ta dago ta kalleshi yace “kinci abinci ne?”


Zanci anjima.


Hannunta ya sake ta suba miyar, zata mike ya sa hannu ya kara riketa, kallansa tai, spoon ya juya mata saitinta ya kalleta ya nuna mata bakinshi.


Tace “dan Allah kaci abincinka.”


Fuska ya daure yace “ashe yau zan kwana da yunwa.”


Cikinka ne fa?


Eh cikin nawa ne zan gani ko an damu shi.


Khalid hooo abinda ta fada a ranta kenan, spoon din ta dauko ta debo ta nufi bakinshi jin abin take wani banbarakwai.


Baki ya bude ta samai, amsa yai yana ci yana kallanta, sai dayaci sosai, ruwa ta dauka ta zuba takai bakinta ta kurba zata sha, amsar cup din yai ya sa hannu a kugunta ya matso da ita dad dashi, ruwan ya sa a bakinsa sannan ya jawota jikinsa ya sa bakinshi cikin nata ya zuba mata ruwan, tana hadiyewa ya shiga yin salo da bakinta.


Gaba daya jitai jikinta ya mutu, yau kam ta dage sai kokarin biyema bakinsa takeyi, jitai wani abu na tsirga mata, kallansa tai da idanunta da suka shanye?


A hankali ya kai bakinsa kusa da kunnenta yace “zan iya jira?”


Hannu tasa ta turashi baya ya dan yi baya jikin kujera.


Mikewa tai da sauri tai kitchen.


Kallan maganin nan tai kawai ta samu kanta da dauka ta dauke numfashi tana sha, sai datasha kusan rabi sannan ta ajiye tana maida numfashi.


Waya ta dauka ta kira Aunty ta sanar da ita sakon Khalid.


Ba karamin mamaki Aunty tai ba dan kasa bata amsa tai sai da Zainab tace “Aunty kina ji?”


Da sauri tace “ina nan sai kunzo.”


********


Washegari.


Karfe hudu ya dawo ta shirya tsaf cikin lace peach anyi ratsin marron da light brown a jiki, dinkin ya amshi jikinta sosai, tayi kyau matuka, tana zaune tana waya da Nazifi akan list da take so ya turo mata, Khalid ne ya gama shiryawa a daki ya fito falo.


Sanye yake cikin shadda sky blue yasa hula dark blue yayi kyau sosai shima, kallansa ta shiga yi tana murmushi.


Muje?


Ya fada yana kallanta, wayarta ta kashe bayan sunyi sallama sannan ta kalleshi tare da mikewa ta yafa mayafinta a kasan kafadarta, kusa da ita ya tako a hankali, yaja mayafin ya maida shi saman kanta.


Idanunsa tadan dago ta kalleshi sannan tai murmushi.


Hannu ya mika maga kallansa tai sannan tasa nata hannun cikin nashi suka fito.


Mota suka shiga ya kalleta yace “me zamu kai?”


Shiru tai kafin tace “basai munkai wani abu ba, ai ta gida ce.”


Bai ce komai ba ya ja motar, sai daya fita sannan ya fito ya rufe gate, shiru tai tana kallanshi harya dawo.


Kallanta yai yace “musai fruit?”


Kamar tace “akwai halin hakan? Sai kuma tai shiru.


Sai da sukai tafiya sosai suna tafe tana bashi labarin yanda ta zauna a gidan, kan titi ya gangara yai parking ganin mai fruit.


Yace “bari na siyo.”


Shiru tai tare da daga kai.


Harta wuce ta dawo baya tana san kara tabbatar da idanunta.


Parking tai kusa da motar dake gun, sannan ta nufeshi.


Mika dari biyar yai ana zubamai fruit din yana tunanin ya isa?


Jiyai ance Khalid?


Kallanta yai sannan ya dauke kai ya maidashi gun lemo da ayaba.


Kusa dashi taje cikin wani irin shauki take kallanshi kallan shigar dayai da yanda yai kyau yasa takeji kamar ya rungume shi.


Kusa dashi taje tace “kasan ina zani?”


Kallanta yai, tace “gunfa Adam zani yanzu ina san jin inda kake.”


Kai ya girgiza cikin kufula sannan yace “hala baki da abinyi ne shiyasa.”


Murmushi tai cikin farin ciki tace “Ka dawo gidan Tv din nan zan musu magana....”


Baiko bi ta kanta ba ya amshi ledar ya juya, kallan Zainab yai ta glass wacce ta cika tai fam, ko daga cikin glass yana ganin tsantsan kishi dake bayyane a fuskarta.


Kallan Afreey yai yace “wuce kije inda zaki please”

Yai maganar sannan ya juya, rigarsa ta kamo wanda hakan yasa Zainab zaro ido, bude kofa tai da sauri tace “Sweet muje in ka gama.”


Ta fada cikin faduwar gaba dan ita kanta batasan me take fada ba.


Afreey ce ta kalleta, cikin rashin fahimta take kallan Khalid, kallanta yai sannan ya nufi inda Zainab take cikin sanyanyan murmushi.


Juyowa yai ya kalli Afreey yace “zo ku agaisa, she is my wifey”


Jakar hannunta ce ta fadi jitai kanta na wani irin juyawa, Khalid ya kalli Zainab sannan ya kalli Afreey yace “Safiya zo ku gaisa.”


Kallansa tai idanunta ne suka fara canzawa, yasan ba zuwa zatai ba hakan yasa ya kalli Zainab yace “muje?”


Kai ta daga da kanshi ya taimaka mata ta shiga motar sannan ya rufe mata motar ya juya ya nufi inda Afreey take, jakar data yar ya dauka ya mika mata yace “da alama tsayuwar ta miki dadi, mu mun wuce”


Ya juya yashiga yaja suka tafi.


Gaba daya kanta ke juyawa, wayarta daje ta zabga kara wanda Adam ke kiranta ya mata karya akan bayannan.


Wani irin ihu ta saki jin da gaske ba mafarki take ba.


Nikam jin ihun nan bansan sanda na arta a guje ba🏃🏻‍♀


*****

Ayusher🏌🏻‍♀[1/10, 9:47 PM] Maman Zara: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*Masoyan Kwaro da Agoggo suna godiya🥰*


{62}


Aunty ce ta shigo daki inda Zainab ta idar da sallar isha’i.


A bakin gado ta zauna ta kalli Zainab cikin jin dadi wanda fuskarta ta kasa boye hakan tace “nagode sosai Zainab, yau bakisan irin farincikin da kika sani ba.”


Zainab dake kallanta tace “kiyi hakuri Aunty yau ma badan Khalid ya sani zuwa ba da haka zan ta cigaba da zama kamar banda kowa.”


Dan ajiyar zuciya tai tace “Da alama kinyi dacen miji na gari, Allah ya baku zaman lafiya mai dorewa.”


Samun kanta tai da cewa Ameen, wanda hakan yasa Aunty murmushi tace “da alama ana san wannan mijin.”


Kallanta tai tana murmushi tace “bansani ba Aunty, bansan ya akw gane ana san mutum ba, na dai san kawai yanzu rayuwata ba daya take dana da ba, inaji kamar bazan iya yini ba tare da shi ba.”


Ta karasa maganar tana sauke kanta kasa, Aunty ta dafa kafadarta tace “Kiyi kokarin faran tamai rai da janshi a jiki, mazajen yanzu ka ja su a jiki ma ya aka kare bare, na tabbatar shi zai nuna miki me nene a ranki.”


Zainab tadan kalleta, Aunty ta dan dafa kafadarta tace “Allah ya kareku dwga sharrin masu sharri, amma anan gidan zaku cigaba da zama?”


Zainab tace “Eh nan yake so.”


“Haka ne, kin kyauta Allah ya kara muku fahimtar Juna.”


Ameen tace sannan ta kalleta tace “Aunty har yanzu baban Amira?”


Murmushi tai na yake tace “yana leko nan sanda ya ga dama kawai dai baya zama ne.”


Shiru Zainab tai tana mata kallan tausayi, Aunty tadan harareta tace “har mun saba ki daina min kallan tausayi.”


Wayar Zainab ce tai kara Aunty ta miko mata ita, ganin Khalid ne yasa tadan juya baya ta dauka “Ur sweet ya iso.”


Kana waje?


Eh


Okay ganinan zuwa.

Kashe wayar tai ta kalleta tace “zamu wuce.”


Kinasan wani abu?


A’a ta fada tana gyara dankwalinta.


“Dama ke kam ta yaushe zakice ma kina san abu? In dai akwai abinda kikeso ki fadamin ko Samira sai na aiko ta kawo miki.”


Zainab ta daga kai sannan ta dau mayafinta ta yafa.


“Dan Abin matan nan na bar ajiyarsu saboda kinga yanda muke zaune da shi, amma in kinaso zansa a kawo miki.”


Tana jinta amma sai tai kamar bataji ba tana kiran Amira, haka suka fito yaran suka rakata har mota.


Suna fita daga gidan ta tsuke fuska, baiko kalleta ba shima ya dauke kai haushi ne ya kamata ganin suna ta tafiya baice komai ba tace “ina kaje da ka gudu?”


Ina kike san naje?


Kallansa tai tace “tambaya da tambaya?”

Amsa da amsa?


Juyowa gaba dayanta tai tace “ba dai....”


Jin ya kamo hannunta ne yasata yin shiru, hannunta ya rike yace “ba dai me?”


Murmushi tadanyi tace “sakeni dare yayi kana tuki da hannu daya.”


Sai kin kira sunana tukun.


Kallansa tai tace “nifa Allah bansan ya akai na samo sunan nan ba.”


Koma ya akai kika samo ni sunan yamin.


Murmushi sukai dukansu, har suka isa gida.


*********

Washegari


A hankali ya bude idanunsa ganinta kwance kusa dashi ne yasashi sakin wani sanyanyan murmushi, hannunsa yasa a gefen fuskarta yana dan shafawa, mostin dayaga tayi ne yasa shi zare hannunsa.


Wayarsa ya dauko yana duba time, yana kokarin sauka yaji ta rikeshi.


Juyowa yai ya kwanta yana kallanta, idanunta ta bude tace “shiri?”


Eh.


Inka tafi sai dare?


Bakya san na fita na dade?


Shiru tadanyi, hannunta ya kamo ya daura akan fuskarsa.


A hankali yace “zan dawo da wuri”


Murmushi tai tace “kadan taimaka min da printing din wasu takardu.”


Okay.


Ya fada kallan juna sukai a hankalu ya matso ya sumbaci bakinta, sannan ya zame gefen kunnenta yace “sai yaushe?”


Murmushi tai tace “kwana 9 nake.”


A zabure ya dago yace “ta me?”


Ta hade rai tace “tara”


Kallanta yai yace “tara? Da gaske kike?”


Eh ya zanyi?


Wani abu ya hadiya kawai ya mike ya nufi toilet, dariya tadanyi sannan taja bargo ta rufe fuskarta, wai Khalid baida kunya dama?


Sako ne ya shigo wayarsa, bata kalli wayarba bare tasa ran dauka tana kwance tana murmushi ita kadai, jiya kwata kwata bata bude laptop dinta ba, anya lafiyar ta kalau kuwa? Kwanan nan aikin ma ba sosai take ba batasan meyasa in tana tare da Khalid mantawa ma take da maganar aiki.”


Kunyar kanta da kanta ne ya kamata ta kara shigewa bargo.


Khalid ne ya fito bayan yai wanka yai alwala.


Kallanta yai yace “kin koma?”


Dan idanun ta ta leko ta kalleshi, zama yai a bakin gado yana shafa mai yace “inata san tambayarki izinki nawa a karatu?”


Karkamin dariya.


Yadan kalleta yace “ba’ai abin arziki ba kenan?”


Tace “tunda na gama primary na daina zuwa.”


( Magana ta gaskiya wannan matsalar tana addabarmu, iya kacin karatunmu na islamiya daga primary ne, da zaran an fara secondary an girma shikenan an daina zuwa islamiya, ana ganin an girmi zuwa islamiya amma bamu girmi karatun boko ba, dan Allah ko ba a je islamiya ba mu dinga kokarin yin tilawa a gida, dan Allah dayawan mu sai mifi wata ko qur’ani bamu bude ba.


Ke da ni da shi da ita dan Allah mu dinga tunawa da Al-Qura’ani muna karantashi ko ya ya ne, in karatu kullum bazai yiwo ba a kalla duk bayan kwana biyu ka karanta.


Allah yasa mu dace Ameen)


  Vest dinsa yasa sannan ya fara sa kaya yace “biyar?”


Tace “a’a”


Kallanta yai yace “badai biyu ba?”


Dan dariya tai tace “goma, biyar kass biyar sama.”


Agoggo yasa ya dau wayarsa ya matso kusa da ita ya nuna mata kuncinsa, dan shiru tai tana kallansa.


Kallanta yai ganin yanda ya kalleta yasa ta fahimci yaji haushi, neman dagawa yai da sauri ta riko wuyan rigarsa ta sumbaceshi a kan labansa.


Tana neman sakeshi ya sa hannu ya kara riketa ya kai bakinshi cikin nata, dagowa yai a hankali yace “Allah kwana tara yamin yawa.”


Jan bargo tai ta rufe fuskarta juyawa yai ya fita.


Sam bai ciro wayarsa ba saboda ganin yadanyi late yana fitowa daga masallaci ya wuce gun aiki.


Yana ta aikin wayarsa tai kara, zarota yai ya duba ganin Abba ne yai saurin dauka suka fara hira.


Sai da sukai sallama sannan yaga sako, budewa yai idanunsa ya zaro yana kara kallan sakon, cikin tsananin farin ciki ya tura sakon wayar Zainab.


Zainab kam bacci kadan tai ta tashi tai wanka sannan ta fara aiki, turamai takardun da zai mata printing tai ta email.


Mikewa tai ta hada tea tana sha tana aiki, shiru tai tana kallan screen samun kanta tai da murmushi.


Ya xaiyi in nace nai wanka?


Fuska ta rufe ita kadai kamar wanda yake gabanta sai murmushi take kai kace albishir aka mata.


Jin sako ya shigo wayarta ne yasa ta dau wayar tana fatan Khalid ne.


Ganin shidin ne yasa ta bude sakon da sauri.


Cikin hanzari ta kira wayarsa, Khalid wanda yai murmushi ganin kiranta ne ya mike yai gefe ya daga wayar.


Zainab cikin farin ciki tace “Yanzu naga text.”


Bari na zo gida.


Yanzu?


Eh


Ya fada batace wani abunba ya kashe wayar ya kalli shugabansu yace “zaije gida sannan daga yau bazai sake zuwa ba dan ya samu aiki.”


Sosai ya tayashi murna dan ya san kwazon Khalid.


Jin Khalid zaizo yasa Zainab ta mike da sauri tai kitchen kawai ta hau shan robar hadin nan da aka bata.


Kunyar kanta ne ya kamata tasa dariya ita kadai tana mamakin me take yi,


Mai zaici?


Indomie ta fara kokarin sawa.


Khalid kam gida ya wuce direct yana bude kofar falo tana fitowa daga kitchen.


Wani murmushi ya mata sannan ya bude hannayensa.


Murmushi tai itama hakoranta suka fito tace “badai nufinka in ruga in rungumeta ba?”


Hade fuska yai yace “idan bakiyi ba kuwa komawa zan.”


Kaifa kace zaka dawo bani nace ka dawo ba.


Ina cikin farin cikin ma bazaki min ba?


Kallansa tai shima idanunsa na kanta, takowa ta fara yi a hankali har tazo inda yake.


Hannu yasa ya jawo ta jikinta ya rungume kawai sai jitai ya dan dagata.


Dariya tasa tana dan dukan bayansa tace “ajiyeni dan Allah.”


Ajiyeta yai ya kalleta kallansa tai tace “Congratulation.”


Thanks dear.


Ya fada yana kallanta, idanu ta dan zubamai, sannan ta kamo hannunsa ta bude tafin hannunsa.


Murmushi yai yace “menene?”


Wad’annan hannaye sunsha wahala


Kallanta yai yana murmushi.


Idanunta ne suka ciciko ta dago tana kallanta cikin magana mai shirin kuka tace “yanzu ka daina aikin ginin.”


Kai ya daga mata fuskarsa a sake, ta kara cewa “ka daina aikin mota?”


Murmushi yai ya daga mata kai.


Sakeshi tai jin zuciyarta na rauni tai kitchen da sauri.


Kallanta yai kafin ya bi bayanta, shiga tai tana sa indomie.


Kusa da ita yazo ya sa hannu ya rungumeta ta baya yace “menene?”


Bata juyo ba tace “bakomai, ya Umma tai?”


Kansa yadan tukufo ya kwantar a bayanta yace “kuka kikai?”


Bata juyo ba tace “bansan meke damuna ba wlh, nifa ina dadewa kafin nai kuka amma yanzu komai sai naji inaaa...”


Sai kuma tai shiru, murmushi yai sannan ya kalli kusa da ita ganin bottle a bude yasa ya kalleta yace “na meye?” Yai maganar yana dauka.


Kwacewa tai da sauri tace “Makociyar mu ce ta bani.”


“Menene? Kikasha kuma?”


Kallansa tai tace “ba sai kaji ba”


Tai maganar tana boyewa a batanta.


Dariya yadanyi yace “kawai daga zuwa ta baki abu sai ki hau sha? Sannan harda kin fadamin?”


Jeka jeka falo ka zauna.


Ta fada tana turashi.


Murmushi yai ya fita.


Falo ya zauna ya dau waya ajiyar zuciya yai ganin uban kiran da Afreey da Adam suke mai.


Number Adam ya kira, ringing daya Adam ya dauka, yace “dan gidanku kana ina? Kana ina nace?”


Yai tambayar cikin zafi da fada kamar wanda ke shirin dukansa.


Khalid yace “kaje Naibawan?”


Uban Naibawa zani ba Naibawa ba, ka yaudareni ka cuceni sannan kace wani nace Naibawa, kana ina?


Khalid yace “mu hadu an jima, a Naibawar daka tsana.”


Bai jira yace wani abu ba ya cigaba “zan turoma da Address din dan nasan ka manta gidan, in mun hadu acan naji me kake san cewa.”


Wayarsa ya kashe sannan ya kalli sakon Afreey kala kala data mai, kansa yadan dafa yana cikin tsananin farnciki amma ana neman sashi tunani.


Kiran Abba ne ya sake shigowa, nan Abba ya kara tayashi murna yace “yaushe zaka fara?”


“Bansani basai gobe suka ce naje.”


Khalid dadi ya hanani rufe baki.


Kace Umma taci abinci kar dadi ya hanata.


Shigowar Zainab falan ne yasa ya kalleta, tare da yin sallama da Abba.


Batai auni ba taji ya jawota kan cinyarsa.


Plate din hannunta ta rike sosai tace “zaka sani bari.”


Kallanta yai yace “tunda Allah yayi yanzu na bar wancan aiki, haka zan zauna na saki a gaba ina kalli har sai kin cika 9 days?”


Tace “to ya kake so nayi? Ka dai san ba’ayi.”


Na sani amma kwana 9 tsakani da Allah?anya Sweet din nan naki zai iya jira?”


Dariyarta ta guntse tace “wai sai wani kiran kanka Sweet kake.”


“In baza’a kirani da hakan ba ni ba sai na kira kaina dashi ba?”


Murmushi tai ta ajiye plate din sannan ta mike yace “Dady na gaidake.”


Kunyi waya ne?


Eh na fadamai an samu aiki.


Murmushi tai, plates din indomie din ya dauka ya kalleta yace “thanks.”


Murmushi tai tana kallansa yana ci, meyasa kwanan nan take jinta kamar wata yar mitsilar yarinya?


Bai kalleta ba sai jitai yace “ni adaina kallo na, abarni da takaici kwana 9.”


Mikewa tai tsam ta dau wayarta tai daki, tana shirin shiga tace “na gama”


Ta shige daki, na gama? Ya maimaita cikin rashin fahimta, da sauri ya kalli kofar dan ya gane.


Jiyai ya koshi da abinci ya mike tsam yai hanyar daki.


*********

  Zazzabin daya rufeta ne yasa Mumy saukowa gun mahaifinta tana sanar dashi halin da Afreey ke ciki, kallanta yai sannan yace “garin ya ya?”


Wlh bansani ba yanzu na shiga naga bata je aiki ba na ganta a kwance.


Mikewa yai ya hau sama inda tafkeken dakinta yake,  tana kwance cikin bargo sai kallan wayarta takeyi.


Abbi ne ya zauna tare da yaye mata bargo, kallansa tai tana hawaye.


Yace “Baby na menene?”


Mikewa tai ta rungumeshi tasa kuka.


Hankalinsa ne ya tashi ya na tambayar menene.


Tace “Abbi bazan iya hakura dashi ba dan Allah ka kwatomin shi.”


Wanene?


Kallanss tai tace “Khalid.”


Ajiyar zuciya yai yace “sau nawa ina miki magana akan wannan talakan yaran? Na dauka tun a makaranta na hanaki?”


Kallansa tai tace “Abbi please.”


Mikewa yai rai a bace ya bar dakin.


Haushi ne ya kamata kawai ta zubo da duk kayan dake kan madubinta.


Abbi na jinta, Mumy na kokarin shiga yace “batta.”


*******


Takardun da aka watsomai ne yasa ya kalleshi yace “Kayi hakuri yaya.”


Ni zaka maida dan iska? Ce maka skai banda abinyi ko me? Ko kuwa ce ma akai kudin da na sa na bude gidan Tv dinan a waje na samosu? Yau zan kira Zainab ta taimaka ta dawo, in kuma har bata yadda ba to zan sai da gidan tv din nan da a gurina yanzu bashida wani amfani.


Kafin Kabir hai magana ya juya ya fita.


Cikin takaici ya ke sakin huci na jin haushi.


Ya zaiyi?


Ya zaiyi?


Nace wa kake tambaya🙄


*******


Da kyar Sadiya ta bata hamsin aka siyo mata kati ta nufi gun network tana komarin kiran Hajiya bilki.


Wayar Adam ce ta shigo dauka tai da sauri tace “Adam an dace?Afir ta samo mana aikin?” Tai tambayar cikin zumudi.


Adam yace “wake zancen aiki rayuwata tana neman karewa an kwacemin mata?”


Mata? A gidan ubanwa kaga mata?


Zaina.....


Kaifa bakada hankali wasa wasa, wato ba neman aiki kake kazo ka daukeni ba can ka cigaba da haukarka.


Goggo Khalid ne fa ya aureta?


Waye Khalid? Inama maganar aiki kana min maganar Zainab.


Khalid fa Goggo abokina driver din nan.


Idanu ta zaro hankali a tashe tace “me?”


Nace mele🙄


******

Ayusher🏌🏻‍♀

[1/11, 11:28 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


{63}


Kofar dakin ya bude, a tsaye ya ganta jikin wardrobe tana duba abu.


Kofar ya maida ya rufe sannan ya ya tako zuwa inda take.


Kallansa tai tace "har ka gama cin abincin?"


Hannu yasa a kugunta ya dan jawota a hankalu yace "ta ina zan iya ci?"


Idanu tadan raba tace "dalili?"


Dan fuska yadan gimtse kadan yana kara jawota jikinsa.


Kikace kin gama.


Ido tadan zaro tace "na gama me?"


Kallan mamaki ya mata yace "me kike nufi?"


Tace "cewa mai ka gama, cin abincinka nake nufi."


Saketa yai fuskarsa a daure yace "ka gama? Haka kika ce kenan?"


Eh da kai mai kake tunani?


Haushi ne ya kuleshi ya kalleta yace "ba sai kinji ba."


Dariyarta ta guntse tace "ina zaka?" Ganin ya juya.


Baiko kalleta ba ya shiga toilet, yana fitowa ya ganta akan gado tana bude wasu takardu, ransa ne ya kara baci ya nufota zai wuce ya koma falo.


Har yadan wuceta yaji an riko rigarsa, bai kalleta ba ya kwace rigarsa zai wuce.


Ji yai ta riko hannunsa, juyowa yai ya kalleta, tace "ina zaka?"


Kin amsa mata yai sai dai kallanta da yai, tace "azahar tayi? Dan wani sa'in banjin kiran sallah da rana, kar na makara banyi sallah ba."


Wani murmushi ya saki yace "are you playing with me?"


Murmushi tai itama ta daga kai tace "eh, sai dai da alama nayi winning."


Baisan sanda ya sake yin wani murmushin ba yace "ramawa kikai kenan?"


Sakeshi tai tana cewa "at least ka sani, me? Zaka ajiyeni kaje gunta? Nima a kalla na rama rabi."


Hannu yasa ya riketa yai baya da ita ta kwanta sannan ya kwanto yace "ba laifi at least for me ina san mace tai kishi na."


Fuska ta hade tana kallansa tace "yaushe nace kishi nake?"


Hannunyasa yana shafa gefen fuskarta yace "inje gunta? Ko in nuna miki kira nawa tamin?"


Wata harara tamai tace "sai ka dawo." Ta dan sa hannu tana neman tureshi, hannunsa ya rike yai baya dashi kan gado sannan yace "fadamin me kika ce dazu?"


Fuska ta daure tace "kaji meye na tambaya?"


Murmushi yai a hankali ya karaso yakai bakinsa cikin nata..............to dai an lula🤪


  Yanda take fitar da numfashi a hankali idanunta a lumshe tana jin wani irin shauki na ratsata, bata taba tunanin abinda ake ji yakai haka ba, ita da Adam iya kaci ayi abu wani sa'in ko minti goma baiyi ake gamawa, dan ita abin ma sam baya kanta daga anyi an wuce gun take shiga wata sabgar.


Jin hannun Khalid ya jawota ya kwantar a kan bayansa yasa ta kwantar da kanta idanunta har yanzu a lumshe suke, tana fitar da numfashi a hankali ta dan ja bargo ta rufesu.


A hankali taji muryarsa yace "ashe shi yasa naji bazan iya cin indomie din ba."


Hannu tasa tadan mintsineshi kadan tace "wai ni haka kake ko yanzu ne ka zama haka?"


Murmushi yai baiyi magana ba, wani irin dadi ne ke ratsa shi.


Zainab kam tuno yanda al'amarin ya kasance dazu tai, dole gobe ta shiga makota gun Maman Al'amin.


Khalid ne taji yace "Ina so zamu hadu da Adam zamuje Naibawa ne."


"Adam? Me zakuyi?"


Tai tambayar cikin mamaki, yace "Gidan su Raziyya ina tsoron kar mahaifiyarta ko mahaifinta wani ya rasu Adam be nemi yafiyarsu ba?"


Me ya musu?


Juyowa yai ta kwanta a kafadarsa, yasa hannu a tata kafadar yana dan shafawa ya fara bata labarin abinda ya faru.


Hawaye ne ya shiga zubo mata yana diga akan kirjinsa, tadan dago ta kalleshi tace "Da alama ni......."


Dan dagowa yai ya sumbaceta hakan yasata yin shiru sai hawaye daya gangaro.


Ya kalleta yace "ba laifinki bane, san zuciya ce ta Adam tasa hakan ya faru, kuma alhakinta ne ke binsa."


Idanu tadan runtse, kallanta yai yace "ki daina dorawa kanki laifin wani, bake kika sanshi yai ba, sannan baki san da ita ba."


Kallansa tai sannan ta daga kai a hankali alamar gamsuwa.


Murmushi yai itama ta saki murmushi........


*************


Masha Allah Khalid anje Zenith an kuma turashi bank na Zenith dake ka titi zoo road wajen Sahad store, duk da daga kasa zai fara amma Alhamdulila shikam dadi yakeji kwarai da gaske.


Zainab kam yau da aiki ta tashi sai data gyara ko ina na gidan ta shige gidan Maman Al'amin, sunyi hira nan taga suna ta hade hade, ana ta hidima, itama ta sai nata ta zauna tana mata bayanin yanda ake amfani dashi.


Zainab kam kunya take in taji Maman Al'amin na mata sharhi, nan ta tambayeta kananan kaya tace "ai gobe ma zata kasuwa."l


Zainab ta ce itama zata kawo kudi a siyo mata, tayi mamaki ganin awanta daya da rabi a gidan ita da sam bata zuwa makota gidan yan uwa ma ya aka kare.


*******^^

Karfe 2 Khalid ya fito, dan sai gobe zai fara aikin full, ga shigar da zasu dinga yi ma a kayyada take.

Ajiyar zuciya yai sannan ya dau wayarsa  ya kira Adam wanda yana kaance cikin bargo takaici ya gama isarsa.


Yana ganin kiransa ya daga jin muryar Khalid yai yace "ka fito mu hadu."


Adam zai yi magana yaji karar katse layi, wani kululun takaici ne ya kamashi, a kufule ya mike yana neman abinda zaisa, ransa bai gama baci ba sai daya ga ba kayan dazaisa a dakin, sai wata riga da wando na jeans haka yasa ya fito.


Aljihunsa ya duba naira hamsin ce dashi, haka ya hau bus yana tafe rai a bace dan bus din an cika ga sai kwaraf kwaraf take.


A titi aka saukeshi ya fara tafiya.


Kusa da gidan ya tsaya rai a bace yana duba Khalid, kenan nama rigashi zuwa ko me?


Daga nesa ya hango Khalid, ji yake kamar ya ruga ya bishi ya danneshi yai ta naushinsa har sai ya ji dalilin daya sashi auran matarsa.


Har Khalid ya iso gun idanun Adam na kansa kamar zai cinyeshi.


Khalid ne ya kalleshi yace "Sorry ban iso da wuri ba."


Adam ne ya karaso kusa dashi ya dunkule hannu yana kallansa rai a tsananin bace yana huci.


Khalid ya kalleshi yace "menene?"


Tambaya kake?


"A'a amsa nake."


Ya fada yana kallan gidansu Razy.


Haushi ya kara tuke Adam ya dan bugi kafadar Khalid yace "banda cin amana ka rasa wanda zaka yaudara sai matata? Hannu ya dunkule ya naushi Khalid wanda sai daya fadi gefen bakinsa ya fashe, wani murmushin jin dadi yai.


Muryar Khalid yaji yace "tunanin me kake?"


Kallansa yai da sauri kenan ba naushin yai ba?


Khalid ne yace "muje?"


Adam a kufule yace "da gaske Honey ka aura?"


Honey? Wa kenan?


Adam ya hade rai sosai yace "Da gaske Zainab ka aura?"


Kallansa yai sannan yasa hadu yadan daki kafadarsa yace "meye naka na tambayar matar wani bayan ba saka akai ba?"


Baijira yace wani abu ba yace "muje."


Adam ji yai kamar yai ihu dan bakin ciki, kofar gidan Khalid yadan buga daga cikin dattijon ya fito ya bude yana tace "waya rufe kofar."


Khalid ya kalla cikin jin dadi yace "oh saurayin nan kaine?"


Khalid yadanyi kasa dakai yana cewa "nine baba."


Cikin farin ciki yace "bismillah."


Nan ya koma ciki Khalid ya kalli Adam sannan yai ciki, shikuma ya bishi rai a bace.


Baba na shiga ya fara kiran Raziyya wacce ke kwance tana daddana waya, bakin cikin gidan duk ya isheta.


Baki ta saki ganin Khalid, kallan Adam tai, shima ya kalleta.


Fuska ta hade tace "me kake anan?" Tai tambayar tana kallan Adam.


Baba ne yace "Ah kinsan shi ne?" Yai tambayar yana cewa "Bismillah kuzo ku zauna."


Khalid ne ya fara zama sannan Adam ya zauna a darare.


Khalid ya ajiye ledar lemo da ayaba daya siyo yace "Ina wuni?"


Baba ya amsa, Adam be ya gaisheshi ya amsa sannan ya kuramai ido yace "kamar na san......."


Muryar Razy ce ta tabbatar da tunaninsa datace "Baba baka ganeshi ba? Kalleshi da kyau."


Shiru Baba yai yace "ya isa haka nan."


Kallan Adam yai yace "me kake anan gidan?"


Adam yai shiru jiki a sanyaye.


Baba yace "me ya kawo ka?"


Adam ne ya kalli Khalid gani yai Khalid din bai ko kallan sa, hakan yasa yace "kuyi hakuri abinda ya faru."


Muyi hakuri? Me dame ka mana?


Adam yai shiru, muryar Baba yaji yace "ka san rayuwar daka jefamu? Kasan halin da muka shiga a tsawon shekarun nan?"


Adam ya kalli Baba jikinsa ne ya fara sanyi.


Baba yai dan gyaran murya yace "mun dauke ka kamar d'a amma ka saka mana da butulci, sai dai kaddara ta riga fata Allah yayi ta wannan hanyar ajalinta zaizo, sai dai mahaifiyarta dake kwance tun faruwar abin, da kanwarta data sadaukar da rayuwarta saboda mu........"


Shiru yadanyi yana kallan kofar dakin da maman take.


Adam kam jiyai idanunsa ya ciciko da kwalla, Baba ya kalleshi yace "idan aka fara cewa da ace bata sanka ba, da ace ka taimaka kazo, da ace da ace da ace...... to magana ta baci dan in abu ya faru ya riga ya faru."


Razy ce ta juya ciki da gudu tasa wani wahalalen kuka wanda su kansu suna jiyo kukanta.


Jin yanda take kuka ne yasa Adam zubar da hawaye, tabbas yanzu ne ya fahimci ya tafka babban laifi, ya dau alhakin su.


Gwiwowinsa yasa a kasa, yace "Baba ka yafemin, dan Allah......." yai maganar murya a raunane.


Baba ya kalli Khalid yace "mun gode sosai, ko dan darajar ka zan yafe masa, sai dai bansan mahaifiyarta da kanwarta ba.


Ni dai ma yafe mai, Allah ya yfe mana gaba daya."


Adam ne ya kara share hawaye yace "nagode sosai."


Khalid ne ya kalli Baba yace "zamu iya ganin ta?"


Eh tana dakincan.


Nan ya rakasu, ganinta yasa Khalid duk dauriyarsa sai da idanunsa suka ciki.


Gaba daya ta rame ta yamushe duk da baisanta ba amma kana ganinta zaka gane.


Tana dan jingine dan tana jin maganarsu a waje, bakinta a dan karkace yake maganar bata yinta yanda ya kamata sai dai tanayi wanda ke zaune da ita zai gane.


Khalid ya gaisheta ta amsa, Adam yasa gwiwowinsa a kasa yana gaisheta.


Tana ganinshi ta fara zubar da kwalla tai saurin kauda kainta.


Adam ya nemi yafiyarta, Baba yace "ki yafe masa tunda ya fahimci laifinsa."


Tadanyi shiru kafin cikin maganar ta tace "Allah ya yafe mana gaba daya, na yafemai."


Kuka Adam yasa yana kara basu hakuri, wanda hakan ya raunana zuciyarsu duka.


Haka suka fito daga dakin, Dakin Razy Baba ya kalla yace "Raziyya fito."


Ya dan murda kofar, jin kofar yai a garkame.


Raziyya? Fito ko?


Kuka kawai takeyi.


Khalid ne ya matso yace "Baba a barta daga baya ya dawo, da alama abin ya dawo mata, in ta dan huce ya dawo."


Baba ya jinjina kai sannan yai ma Khalid godiya.


Adam kam sai kara neman yafiya yake yana godiya har suka fito.


******

Allah ya yafe mana laifukanmu😪


Ameen


*****

Ayusher🏌🏻‍♀

[1/13, 9:20 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


The believers are those who spend in charity during ease and hardship and who restrain their anger and pardon the people, for Allah loves the doers of good.


Surat Ali Imran 3:134


{64}


Ajiyar zuciyar data sakeyi a karo na ba adadi ta sakeyi, wayar ta data rabe gida biyu ta kalla, dan tana jin Zainab tai auri kuma wai drivernta ta saki wayar kasa ta fadi, tagumi ta sake bazawa ta sake yin ajiyar zuciya.


Haka zata cigaba da zama anan damuwa ta mata illa, yanzu taya Zainab zata musu haka?


Tuno abinda Adam yai tai ta baza tagumi dan ba shakka tun daga nan komai ya tarwatse, ajiyar zuciya ta sakeyi, tana tuno yanda tai rayuwa cikin jin dadi da walwala, yanzu gata a wani dan dakin da ake ajiye abincin tumakai, sai shi ta gyara take lalabawa.


Mikewa tai ta fito, tana kallansu suna surfe suna hira, Sadiya na gefe tana ta fama yin abincin saidawa.


Kusa da ita taje tace "Sadiya zuban shinkafar a kwana yunwa nakeji."


Kallanta Sadiya tai tace "Goggo taya zan baki ribar? Kina gani yanda nake ta faman hada kudin nan saboda bikina."


Shikenan karki bani ki bari yunwa ta kasheni.


Ta juya a kufule, da kallo Sadiya ta bita sannan ta dau plate ta dan zuba kadan ta kai mata.


Goggo ta amshi kwanan tace "Sadiya ko zaki taimakan da dari biyar? So nake na koma kano."


Dari biyar? Bandashi gaskiya, haba Goggo yanzu dan Allah bakiji kunyar ma tambayata kudi ba? Ki tafi ki barni a gidan nan banda gori ba abinda naie sha har na dage na fara neman na kaina shine yanzu zakizo ki dauran wahala.


Cikin mamaki Goggo tace "sau nawa ina bada kudi daga can a baki? Sau nawa ina sa Zainab ta ba Adam kudi ya turo miki?"


Shiru tai kafin tace "amma daga baya ai daina turowa kukai."


To ko mun daina dai a kalla ai kinci rabanki kema, dari biyar shine kike fadan magana haka?


Jikin Sadiya ne yai sanyi tace "zan kawo miki anjima."


Ta juya ta fita.


Goggo ta sa hannu tana cin abincin........


*********


Khalid na fitowa ya nufi titi, Adam na binshi a baya, gaba daya jikin Adam yai sanyi har suka isa titi ba wanda yama wa wani magana a cikinsu.


A bakin titi suka tsaya, Adam ya dan matso kusa da Khalid a hankali yace "nagode."


Shiru Khalid yai bai kalleshi ba, Adam ya juya kai cikin kuluwar yanda ya manna mai, jiyai yace "ka san rayuwar da Raziyy tai a asibiti?"


Kallan Khalid yai, wanda idanunsa ke kan titi bai jiyo ba, yace "likitan saboda rashin kudi duk sanda zai duba Firdausi sai yayi amfani da ita, can you imagine how much she suffered?"


Hankalin Adam ne yai matukar tashi yace "wani irin bala'i ne wannan?"


Khalid ya kalleshi yace "a lokacin da kake can kana jin dadin rayuwa a kasan mace, su suna can suna cikin tashin hankali, a lokacin da kake can kana baccin asara su suna can suna zaman makoki, ko da wasa ka taba tunanin kaje ka ga ya suke rayuwar su?"


Adam ne ya hadiyi wani abu yana kallan Khalid, sai yanzu Khalid ya kalleshi yace "ka dawo gobe ka nemi yafiyar ta, dan duk wannan abin dake samunka alhakin su ne ke yawo dakai, nasan dama can kana da naka issue din amma abin bai kai haka ba.


Yana kai nan yaga adaidaita ya tsayar, ganin Adam yai ya nufo adaidaitar, ya kalleshi yace "ina zaka?"


Adam ya kalleshi yace "gidanka."


Kai me?


Kallansa yai yace "Kai kace in na shirya ganinta zaka kaini."


Khalid yai wani murmushi yace "yanzun ka shirya?"


Adam yai shiru.


Khalid ya matsamai ya fara shiga sannan ya shiga suka nufi gidanshi.


A bakin gate din dan karamin gidan suka sauka Khalid ya bashi kudi sannan yai gaba Adam nabinsa a baya.


Kallan gidan yai anan Zainab ke zaune?


Khalid yace "muyi sallah tukun." Ya fada tare da dan gangarawa hanyar masallacin da ake ta kiran sallah."


Sai da sukai sallah sannan suka fito Khalid ya kalleshi yace "yanzu me kakeyi?"


Aiki nake nema.


Aiki? Ina da ina ka ciki?


Adam adan kufule yace "Khalid wai ni kai abokina ne ko babana?"


Khalid ya kalleshi yace "kai ai ba a maganar abokantaka dakai, sai dai ai magana kai tsaye."


Me ka dauken?


Ya tambayeshi yana kallansa, Khalid ya shareshi suka nufi gidan.


Gidan Adam ya kara kallo da gaske nan Zainab take?

Danne tunaninsa yai yabi bayan Khalid.


*******


Zainab kam tana dawowa daga gun Maman Al'amin ta bubude abubuwan da aka bata, tunawa tai tace yawan shan fruit shine zata dinga yi musamman ma kankana da ayaba in ta hadasu ta barkada da madara, murmushi tai ta boyesu a drawer a kitchen sannan ta sa abinci tanayi ita kadai tana murmushi, fitowa tai ta hada turaren wuta ta turara kanta, tana yi tana kunyar kanta, batasan meke damunta ba, ta dade da sanin ana turara jiki dan Aunty tasha yi a gabanta ma amma sam rashin lokaci bai taba sa tayi tunanin yi ba sai yau.


Sai data gama ta fito ta zauna a falo tana duba aikinta, jefi jefi ita kadai sai ta saki murmushi, agoggo ta kalla a karo na uku, haryanzu?


Ta fada a ranta tana kallan wayarta, jin ana kiran sallar magrib yasa ta mike tai alwala, tai sallah, tana nade sallaya taji alamar sallama ana neman shigowa.


Wani irin farin ciki ne ya kamata sallayar ta ajiye ta fito da sauri, daga bakin kofa ta tsaya tana kallanshi.


Shima a bakin kofar ya tsaya yana kallanta, a tare suka sakarwa juna murmushi sannan cikin dan salo da ita kanta bata san tana da shi ba tace "sai yanzu?"


Dan taku biyu yai, ya bar Adam daga gefen kofa ta waje hannu ya bude mata, kafad'a ta noke tace "bayan kayi late dayawa."


Hannu ya kafa nuna mata da kansa, ta kara noke kafada, dan fuska ya hade yace "shikenan."


Ya fada yana neman zama, takowa tai a hankali ta rungumeshi.


Juyowa yai ya kara rungumeta cikin rada a kunne yace "I miss u baby."


Murmushi tai ta kara dan kankameshi.


Kamshin turaren wuta mai sanyi take yi, idanu ya lumshe a hankali yace "do u wanna kill me?"


Tace "in ka mutu wa zai kula dani?"


Tai maganar ne a ranta sam batasan a fili tai ba sai jitai yace "I........"


Dagata yai da sauri yace "bani kadai nake ba, na manta sam."


Kallan mamaki tamai tace "kai da waye?"


Kallanta yai da yake hijab din datai sallah yana jikinta, yace "Adam ne"


Adam? Wani Ad....Adam dai?


Yace "eh"


Me zaiyi anan?


Murmushi yai yace "matar abokinsa zai gani."


Fuska ta daure, yace "Adam."


Juyawa tai yasa hannu ya riko kugunta, matso da ita yai yana kallanta.


Kallansa tai, yace "bakon mijinki ne, tafiya zakiyi baku gaisa ba?"


Daidai nan Adam ya shigo, zuru yai yana kallansu, basu ma san ya shigo ba.


Zainab ce tace "am sorry, bansan me zai cemin ko nace mai bane."


Kome zai ce ko me zakici wannan abu ne daga baya? But at least ku gaisa."


Okay ta fada, sannan ta mai murmushi.


Juyowa tai kawai sukaga Adam a tsaye zuri, kallansa tai duk ya rame yai baki, Khalid ne ya ja hannunta ya zauna sannan ya zaunar da ita kusa dashi, ya kalli Adam yace "Adam zauna mana."


Adam ya zauna a takure, baki na dan rawa yace "Ho......"


Mugun kallon da Khalid yamai ne yasa yace "Zainab!"


Kallansa tai tace "kana lafiya?"


Idanunsa ne suka ciciko yadan takure yace "lafiya kalau ya gida?"


Lafiya ta fada tana kallan Khalid.


Adam ya kara kallansu, ya hadiye wani abu, duk sai yaji ya raina kansa, Khalid ne yace "dan kawo mai ruwa"


Cikin dan rada tace "nayi Abinci."


Murmushi yai yace "thanks dear."


Kallansa tai yace "kawo mana please."


Mikewa tai Adam na zaune na kallan ikon Allah yana ganin Zainab ta tashi ta kawo musu abinci abinda har suka gama zama a shekara 4 da sukai bata taba kawo mai abinci ba, ajiye wa tai sannan ta kalli Adam tace "Goggo fa?"


Yadan daure yace "tana kauye."


Kauye?


Cikin dakewa yace "eh ta koma can kafin na samu aiki."


Kai ga daga Khalid ne ya kalleta, ta koma ta zauna kusa dashi, yace "Baby ko zaki shiga ciki muci abinci tukun?"


Baby? Wa? Ni? Ganin tana ta aune aune ya kanta yasa ya ciro waya yace "kidan samin a charge."


Amsa tai tace "okay ku gama."


Ta wuce daki.


Tana shiga daki ta zauna a bakin gado tare da sa hannu a saitin zuciyarta dake bugawa da sauri, kwanciya tai tasa pillow ta rufe fuskarta, nice baby?


Ahhh wannan Khalid din ko? Ta fada sai kuma tai murmushi,.....


Nace ke kadai dai🤪


A falo kam Khalid ne ya zuba abinci ya kalli Adam yace "Adam Bismillah."


Adam ya kalleshi dan dai yana jin yunwa ne amma yanayin daya samu kanshi a ciki bayaji zaiso cin wani abu.


Haka suka zuba abinci, suna ci Khalid yace "yanzu meye plan dinka?"


Plan? Bandashi ina dai fatan samun aiki.


Ka tabbatar ma ni kana neman aikin?


Kunya ce ta kama Adam ya kalleshi, cikin jin haushin kansa yace "Afreey na tambaya."


Wani kallo yamai yace "meyasa kake so a rayuwarka ka dogara da wani? Bazaka gwada abu da kanka ba sai dai kai tabi kana neman a taimaka ma? Tundaga fara karatunka haryau baka kula komai wani bane yake maka? Haka kake so rayuwarka ta kare?"


Shiru yai jikinsa ya kara mutuwa yace "Khalid kai dani ba daya bane."


Ba wani ni dakai ba daya bane, duk dan Adam daya ake haifarsu, kai dai kasawa kanka ka biye zuciyarka banda san jikinka baka san komai ba."


Shiru yadanyi yanajin rashin Zainab a ransa, ga yazo yaga yanda suke rayuwarsu gaba daya ba kalar tashi ba, jiyai hawaye ya zubo mai.


Khalid ya kalleshi yace "ka zama mai kokarin neman naka wannan zaisa ka rage biye shirmen da zuciyarka ke raya maka a koda yaushe."


Dan shiru sukai Adam ya daure ya kalli Khalid  yace "Khalid da gaske Zainab dina kake aure? Gata dai na ganta naga kamarta amma gaba daya ba ita bace."


Khalid ya kalleshi yace "Wace Zainab dinka?"


Da sauri yace "oh"


Khalid ya dan sha ruwa yace "ka duba ka nemi abinyi, karka dogara da Afreey kasan halinta sarai, in har zata taimaka ma to ko kuwa komenene dole kabi abinda take so, sannan maganar matata bana san menene dalilinka na tambayar matar da ba muharramarka ba."


Adam yai shiru yana cin abincin, har saida suka gama ba wanda ya sake magana, Adam yasha ruwa Khalid ya kalleshi yace "kafin ka samu aiki zaka gwada wanda nai da?"


"Wanene? Zan iya ko wani aiki ne indai ba aikin karfi bane."


Khalid ya kalleshi, kamar zaiyi magana ma sai ya fasa.


Adam yace "kayi shiru."


"Kafi kowa sanin aikin karfi nake to cewa ba aikin karfi ba kana nufin baka so kenan."


Adam yadanyi shiru dan shikam bashi da karfin yin aiki gaskiya.


Mikewa yai ya shiga daki, Zainab na kwance akan gado tana searching a google.


Khalid ne ya kalli wayarta ganin harya shigo bataji ba, hannu yasa ya fizge wayar.


Mikewa gai da sauri tana neman kwacewa.


Dariya yai ya daga wayar sama, hannunsa ta shiga jawowa tana san kamo wayar.


Kafada ya daga mata sannan ya dan karkace kai kadan yana kallanta.


Tace "bani please."


Kai ya daga wayar na sama ya fara karantawa.


Love name to call your husband?


Fuska ta rufe da sauri cikin jin kunya, dariya yai ya kalleta yace "abinda kike nema kenan?"


Fuska ta dauri ta kalleshi tace "Wata ke so shine zan tura mata."


Wata? Wannan? Ya nunata ta cikin madubi.


Tace "ce maka akai nice?"


Mika mata wayar yai yana cewa "in ni ake nemarwa ma na yafe, dan Sweet din nan nakeso, a taimaka a kirani da hakan."


Wayar ta amsa tace "na dauka baka so, tsokana ta kake."


"Ah a taimaka a kirani da sunan nan nidai"


Dan baya ta juya dan haka kawai taji dan kunya, tana mamakin yanda akai wai ita ke kunyar abu in yace, bayan shi sauray.......


Kansa ya sako takan kafadarta dan juyowa tai ta saitin daya sa kansa, kuncinta ya sumbata yace "muje mun gama."


Kai ta daga, sannan ya kalleta, kallansa tai, ya kara kallanta, itama kallansa ta sake cikin rashin fahimta, kallanta yai yana nuna mata gefenta da kansa.


Kallan kan gadan tai, hikab din data cire ta kalla, kallan kanta tai yane yake da mayafi.


Yace "sa"


Dauka tai ta zura suka fito.


Adam tunda suka fito yake kallansu, har suka zauna sannan ya daure ya dauke kai.


Khalid ne ya matsa gefe yana daddana waya alamar ya barsu suyi magana.


Zainab tai murmushi in barinsu za'ai suyi magana ai sai ya tashi.


Kallan Adam tai tace "yanzu a ina kake?"


Ina gidan wani abokina ne ina neman aiki kafin a dace.


A gun wa kake nema?


Dan kallan inda Khalid yake yai sannan yai shiru, kallanshi tai tace "in kansan aikin nepa ka turo takardunka na turawa Dady, amma sai dai ka fara daga can kasa kamar yanda na fadama."


Adam yai shiru,wato dai ko wani aiki sai aikin karfi, harga Allah shikam baisan aikin karfin nan.


Nepa din ma in daga can kasa ne ai yasan wahala suke sha, daurewa yai yace "nagode Zainab zan turo, sannan...."


Ya dan yi shiru yana kallanta, yace "dan Allah Zainab ki yafemin, abinda nazo roka kenan."


Kallansa tai tace "nice zan nemi yafiyarka ka yafemin Adam."


Kai ya gitgiza yana dan share kwala yace "ba abinda kika min nine na miki laifi"


Tace "na yafe maka, kaima ka yafemin."


Cikin dan rawar murya yace "na yafe miki."


Mikewa yai ya kalli Khalid yace "Khalid zan wuce."


Khalid ne ya mike yace "muje na rakaka."


Zainab ta shiga daki a kudin nan ta ciro 10k sai kuma ta rage ta dauko 5k dan tasan halin Adam a kwana daya ma sai ya cinye kudin.


Fitowa tai ta mika mai tace "ka rage wani abin ba yawa."


Harzai amsa sai kuma yace "ta ina zan amshi kudinki?"


Tace "karka damu ba wani abin."


Shiru yadanyi kafin ya amsa, Khalid ne yace "muje?"


Nan suka fito, Adam kam gaba daya jikinsa yayi sanyi, harya hau adaidaita bai ce kala ba, a ciki ma zugum yai.


Khalid kam na komawa gida yaga Zainab na kwashe kwanuka, murmushi yai tana dawowa daga kitchen ya kalleta yace "Baby dan dubamin daki kiban wayata."


Kallansa tadanyi, Khalid fa akwai sa aike, haka ta wuce daki tana shiga ta ganshi shima ya shigo.


Kallansa tai cikin mamaki, matsowa ya farayi yanda taga yanayi da idanunsa ne yasa ta gane nufinsa, kallansa tai tace "sai kace ba wayarka zan dako ma ba."


Ba kirana kikai ba?


Kallansa tai sannan tai yar dariya tace "yaushe akai hakan kenan?"


Yanzu, na tabbatar naji ance Sweet zo kaga.


Baki ta bude tace "har haka nace?"


Kai ya daga yace "sosai dan haka kunnena yaji."


Haka dai kunnenka ke san ji.


Karasowa yai inda take yace "fadamin yanda kunne na ke san ji to."


Tace "Sweet ga wayarka."


Murmushi yai yace "okay, ai kece wayar tawa na gane irin juya maganan nan ne."


Dariya tai tace "oh ni wai dama haka kake? Anya su Umma sun san.........."


Jin ya jawota ne yasata yin shiru, kallansa tai cikin wani yanayi, hannunsa yasa ya riko fuskarta a hankali ya kai bakinsa ya sumbaci saman goshinta, ya sako ya sumbashi karan hancinta, ya sumbaci idanunta dake lumshe, sannan ya sumbaci kucinta.

Idanunsa ya lumshe sannan yakai kan labanta ya sumbata, dagowa yai a hankalu ta bude idanunta, kara kallan bakinta yai sannan ya nufeshi................


********


Afreey tashi kici abinci nace ko?


Bargo ta sake ja tace "banaci."


Afreey wai wani irin abu ne haka? So kike hankalinmu ya tashi?


Cikin kuluwa tace "ki kyaleni banaci, in har kuna so naci abinci ku kawon Khalid."


Tace "mene?"


Bargo ta kara ja ta rufe kanta gaba daya.


Mumy haka ta mike ranta a bace ta fito.


Nace cikin wa?🤪


*************


Yau da safe tana tashi sakon shugaban gun aikinsu Abubakar ta gani, mamaki ne ya kamata dan tambayarta yake sanda take available yana san ya kira akwai maganar da yakeso suyi.


Shiru Zainab tai tana kallan text din, tare da tunanin me yake san yace mata........


^******

Ayusher🏌🏻‍♀

********

[1/14, 10:54 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{65}


  Ganin kira ya shigo cikin wayarta ne yasa ta daga “Assalamu Alaikum Sir”


Daga can Abubakar ya amsa yace “Zainab inata cigiyarki shiru bake ba labari.”


Shiru tai batace komai ba, yace “Zainab me zai haka ki taimaka ki dawo aiki? Wlh akwai matsala rashinki a nan yasa komai na neman tarwatsewa.”


Murmushi tai tace “Yallabai am sorry amma bazan koma ba.”


Yace “na sani an bata miki rai amma kiyi hakuri Zainab ki taimaki gun da kika bunkasa da hannunki karya ruguje.”


Shiru tadanyi kafin tace “An sorry yallabai amma i can’t do that.”


Yana kokarin magana tace “nagode.”


Ta kashe wayar, shiru tai tara da dafa kanta, sannan a hankali tadan sauke ajiyar zuciya.


Rubutun da take a takarda ta cigaba, har sai da azahar tai sannan ta mike tasha tea tai sallah sannan ta sa abinci.


Daki ta shiga dubawa tana neman flash dinta data ba Khalid sanda zai mata printing.


Wandan dayasa jiya ta jawo tana dubawa, takardar data ji a ciki ne yasa ta cirota tana dubawa, list din kayan da zai dinga sawa ne daga sun gama training kenan wani satin zai fara sasu?


Shiru tai tana tunanin kila bashi da ko dubu daya ma ina yaga kudin siyo wadan nan kayayyakin?


Zama tai a bakin gado tana tunani, ya zatai da Khalid?


Ganin tunani na mata yawa yasa kawai ta cigaba da abinda take tana duba abinci.


^**********


Sakon daya shigo wayarsa ne yasa ya kara kallan sakon baya ya gama karantawa.


“Khalid wannan shine magana fa karshe da zan ma in har bakazo ba to lalai zakaji sallahun mutuwa ta gobe.”


Ajiye wayar yai ya rufata ta baya ya cigaba da abinda sukeyi, har sai 5 da suka tashi sannan ya dagota.


Kallan text din ya sake kawai ya danna kira.


Afreey na kwance cikin bargo taga kiran Khalid, cikin sauri ta yays bargo ta daga tace “Khalid!” Tai maganar da sauri cikin zumudi.


Yace “Safiyya sai yaushe zaki daina abu na marasa tunani?”


Cikin mamaki tace “Khalid?”


Yace “Bansan me kika dau kanki kika dau rayuwa ba sai dai daga wannan lokaci zan canza numberta sannan zan sanar dake abu daya, kiyi kokarin daraja rayuwarki da wad’anda ke tare dake, ki nemi wanda ke sanki ki aura wannan shirmen da kike kira da sunan so ba shine so ba, ina miki fatan alkairi.”


Kha....... karar kashe wayar dataji ne yasa tace “khalid! Khalid.....”


Ganin da gaske ya kashe ta shiga sake kiransa sai dai ana tace mata wayar a kashe take, haushi ya isheta ta cilar da wayar.


*******


Khalid kam yana kashe wayar ya fito ya nufi gida.


Zainab na zaune ganin an kawo wuta ta dawo falo, harta fara aiki taji hankalinta nakan kofar waje, tana yi tana kallan time, tv ta kunna ta zauna tana kallan shirin da akeyi, gaba daya shirin dake gudana a gidan tv din ga rainashi, daga masu shirin har yanda shirin ke tafiya, tsaki tai wai a hakan plan dinta ake bi, tasha ga canza ganin ana wani indian film ta tsaya tana kallo, shigowar gate taji a hankali ta mike ta leka kofa, murmushi tai sannan ta koma da sauri ta zauna sai kuma ta girgiza kai tai saurin kwanciya akan kujerar, nan ma taga baiyi ba tai saurin daukan littafin datagama rubutu dazu ta rike wai a dole karatu take.


Khalid ne yadan kwankwasa tare da murda kofar falan, yi tai kamar bataji ba, sallama yai sannan ya kalleta, kallansa tai tadan basar ta amsa sallamar sannan tace “sannu da zuwa.”


Ta cigaba da kallan littafin, kallanta yai sannan ya shigo har ya zauna kusa da ita bata kalleshi ba, sa fuskarsa yai cikin littafin yace “ya naga kamar a juye?”


Kallan littafin tai sam batama san ta yanda ta rike ba saboda hankalinta bai wajen, kallansa tai tace “practicing din karatu a juye nakeyi.”


Practicing? Kai ta daga tace “eh.”


Ohhhh ba laifi amma..... ya jawota jikinsa, kallansa tai ya daure fuska tace “karatu fa nake”


Nima wani karatun zan zuba miki, tadan kauda kai tace “karatu?”


Yace “eh na tabbatar karatuna yafi wannan saurin shiga.”


Kallansa tai tace “shine tunda ka tafi ba ko yar text, balle waya.”


Kallanta yai cikin mamaki wanda hakan yasa tai saurin runtse idanta tare da jin haushin kanta, murmushi Khalid yai mai fadi wanda hakoransa suka fito yace “au fishin kenan?”


Kanta tasa a cinyarsa da sauri cikin jin haushin kanta, murmushi ya sakeyi ya kwanta akan bayanta yace “but i like it, i wish za’a cigaba da yin fushi dani indai akan haka ne.”


Ya dan dago yana cewa “Baby in miki text yanzu?”


Dagowa tai tace “kana gida me.....”

Sai kuma tai shiru tana murmushi ganin tunda ta fara murmushi yakeyi, tace “menene?”


Yace “i just feel like i need it now.”


Tace “me kenan?”


Hannu yasa akan cinyarta yana tahowa dashi, ture hannunshi tai, dariya yai yace “raguwa.”


Wace?


Nidai banfadi suna ba.


Ah to nidai mutum bazaicemin raguwa ba.


A gwada?


Tureshi tai tace “dama nasan juya maganar zakai.”


Yace “tunda kin sani ya akai kika biyemun?”


Dan laban bakinta ta hade sannan ta wadd tace “fanshewa kake yi ne?”


Me?


Ta matso kusa da kunnensa tace “gaurantakar da akai da?”


Ta mike da sauri tana neman guduwa, hannu yasa ya jawota, fadowa kan cinyarsa tai yace “fanshewa kike?”


Kallan sa tace “ni kuma name?”


Bakinsa yakai saitin kunnenta sai yace “na fasa fada.”


Yasa dariya, sauketa yai ya mike yana dariya, tace “fadamin name?”


Ciki ya wuce ya fada toilet, tana biyoshi taga baya dakin.


Shiru tai tana tunani name?


Falo ta dawo ta kashe tv ta kawo kai abinci falan.

Khalid na fitowa faga wanka yasa yar riga da wando ya fito.


Kallan abincin yai sannan yace “Ur sweet na godiya.”


Tace “in Sweet na godiya ya fadamun me yake nufi.”


“Ayya am sorry baby amma da alama Sweet dinki bai shirya sanar dake yanzu ba.”


Fuska ta daure tace “shikenan.”


Zama yai ya kalleta yace “bani abinci.”

Kallansa tai wannan sakalci? Haka ta zuba kai ta sa spoon ya sau spoon din yana cin jellof din shinkafa da wake datai.


Wayarta ta mikomai? Ya amsa yana kallan email din da Adam ya turo na result dinsa, result ne da kana gani kasan wanda yasha dakyar ya wuce, duk da sake jarabawar dayai dayawa.


Kallansa tai tace “Bari na turawa Dady.” Tai maganar tana neman amsar wayar, hannunta ya hade da wayar ya juyo yana kallanta, yace “ba yanzu ba.”


Cikin mamaki tace “jiya nace mai zan tura inya turo.”


Yace “haka kika ce, sai dai daga alamun maganar Adam haryanzu baisan kanshi ba, in har aka nemomai a tsukukun nan mutuncin Dady zai zubar ba komai ba.”


Kallansa tai tace “me kake tunanin yi kenan?”


Ya dan murmusa yace “barshi yai aikin gini danai na wata biyu am sure zai dawo hankalinsa.”


Okay shikenan ta fada cikin gamsuwa.


Abinci ya gama ci yasha ruwa, sai data maida kwanukan sannan ta zauna a dan gefensa, hannu ya nuna mata alamar ta matso, dawowa tai kusa dashi.


Kwanciya yai akan kunjerar ya kwantar da kansa a kan cinyarta, sannan ya sa hannunta acikin sumarsa.


A hankali ta shiga shafawa yana dan lumshe ido, kallansa tai cikin tsantsan san da batasan sanda yai mata kamu haka ba tace “dazu Shugaban gun aikina nada ya kirani.”


Idanunsa yadan bude ya kalleta, nan ta fadamai yanda sukai, kallan idanunta yai yace “kin tabbatar hakan kikeso?”


Kallansa tai tace “ta ina zan manta abinda suka ma?”



Murmushi yai yace “dan bugamin nan.” Ya nuna mata kafarsa.


Matsawa ta shiga yi, tsabar yanda ya aikatu kwanakin nan yasa har yanzu jikinsa ciwo yake.


Can tace “ya zamuyi da kayan da zaka siya?”


Bai kalleta ba yace “zan yi aiki da weekends din nan zan san yanda za’ai insha Allah.”


Shiru tai tana kallansa idanunsmta sukai rau rau tace “Sweet idan naga tanasa ba mijin kyautar abu ya zatayi?”


Yanzun ma bai kalleta ba idanunsa na lumshe yace “indai kyautar batai yawa ba ai bakomai, amma menene?”


Shiru tai wanda hakan yasa ya bude idansa yace “menene?”


Kallansa tai tace “please!” Tai maganar cikin rauni idanunga na digo da hawaye.


Mikewa yai yace “menene?”


Ta kalleshi tace “please ka barni na saima kayan.”


Kallanta yai yace “nace za......”


Rungumeshi tai kam wanda hakan yasa jikinsa yin sanyi, tace “bakasan yanda nakeji ba in ka je gun aikin gini din nan, dan Allah kayi hakuri ka bari nasaima kyautar abu nake san ma amma nasan bazaka taba amsa ba, shiyasa na fadama kar ranka ya baci.”


Ta kara kankameshi, kanta ya shiga shafawa, duk da ba mace bace kai gashi sosai a kallantana da nata daidai gwargwado dan in ta gyara shi yana kwanciya luf.


Dagota yai ya sa hannu yana share mata kwallarta, yace “ana kiran sallah muyi sallah ko?”


Kai ta daga tana kallanshi.


Alwala tai sukai sallah tare, yace ta dauko qur’ani nan tamai karatu yaji, ya mata gyara sannan ya dan daura mata kadan.


***********


Adam kam sai duba waya yake yana jiran sakon Zainab na cewar ta tura komai ya kammala sai dai har dare yai bai ga komai ba, wajen karfe 9 sako ya shigo wayarsa da sauri ya dauka ganin numberce yasa ya bude a dan zuciye.


Number aka turo mai a kasa akasa ka kirashi, namai bayani zakazo gobe, sunanshi Gaddafi.

Sannan kaje gidan su Raziyyan?


Daga Khalid!


Zanzo gobe? Har aikin ya samu?


Shiru yai sannan ya tuna yau yaso zuwa gidansu Raziyyan amma baisamu ya fita ba saboda jiya kasa bacci yai in ya tuno abinda ya faru a gidan Zainab sai yaji sam baccin yaki zuwa.


Jiya itace rana ta farko da ya taba kasa bacci arayuwarsa,


********


Salmanu ne ya shigo bayan an mai izini, hannunsa dauke da bakar leda.


Umma tace “Salmanu sannu da zuwa”


Shigowa yai yana dariya yace “Umma kinjini shiru ko?”


Tace “ai da bakazo yau ba sawa zanyi Asiya ta kiramin kai a waya naji ko lafiya.”


Dariya yai yana karasowa, Abba yace “nikaina nace wannan d’a lafiya?”


Kusa da Abba ya zauna yace “wlh munje dutse ne neman aiki Abba.”


Umma tace “masha Allah, Allah yasa a dace.”


Ameen yace ya ajie ledar gaban Umma yace “Umma ga tsarabar zuwa dutse.”


Budewa taj tana cewa “mungode, Abban Khalid gashi an kawo mana dankalin hausa.”


Mungode sosai.


Asiya ce ta fito gaisheshi tai sannan tai hanyar komawa ciki.


Umma tace “Asiya zo ajiye wannan, yanzu yayanki Salmanu ya kawo.”


Kusa da Umma tazo ta dauka, tana dagowa suka hada ido da Salmanu, murmushi ya mata ta dauka ta ajiye.


Zata koma ciki Umma tace “zo ki kawo mai abinci, Salmanu alale ne nasan kana so.”


Kallan Asiya yai yace “Asiya zubomin alale.”


Ya kalli Umma yace “ashe raban zanci alale ne yasa na rike yunwata.”


Umma tai dariya, kallan Asiya yai harta zubo ta kawo mai sannan ta juya ciki.


*********

Ayusher🏌🏻‍♀

***********

[1/16, 9:58 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{66}


Kwance take akan kirjinsa kamar me bacci, yana dan shafa kafadarta zuwa bayanta.


Shima yana kwance ne sun luluba da bargo, a hankali tace “Dady dazu yamin text yana san jin sanda kake dawowa gida, yana san kiranka.”


Kin fadamai?


Hmm tace kafin tafan yi ajiyar zuciya kadan tace “na san maganar aiki ne, in na fara aiki ya kake gani zamuyi?”


Ba tare da dogon nazari ba yace “kafin ki tafi sai kin gama komai na gida kinyi abinci kin ajiye sannan ki fita”


Da sauri ta dago tace “da safen?”


Yace “eh haka duk mata masu aiki sukeyi.”


Amma ni da nake fita da wuri fa?


“Sai ki tashi tsakar dare.”


Baki ta bude tana kallansa, kallanta yai yace “menene?”


Tace “wani sa’in sai na kasa gane wanene kai”


Kara jawota jikinsa yai yace “so kike nace ki fita aiki sanda kikeso ba tare da kinyi komai ba?”


Tace “ba haka ba amma ta ina zai iya aikin gida nai abinci kafin na fita?”


Kafada yadan daga sannan ya dan sumbaci goshinta yace “zaki iya tunda kina san aikinki kina kuma san Sweet dinki.”


Bata san sanda tasa dariya ba sannan ta kalleshi tace “mekace?”


Yace “kina san aikinki kina kuma san mijinki, ba haka bane?”


Dan ido ta dan kikifta tace “ko haka ne sai ka fada kai tsaye? Sai a bari na fada da kaina.”


Ko baki fada ba jikinki ya fadamin me zai sa na jira sai kin fada?


Dariya ta sake ta sa hannu ta dan tureshi ya dan murgina kadan tace “Allah nikam na rasa irinka.”


Ta juya mai baya tana kunshe dariyarta, juyowa yai ya rungumeta ta baya, hannunsa ya sako saman kirjinta yasa kansa a bayanta yace “Allah in na tuno shekararki hudu da shi sai naji kamar......”


Dan yawon bakinta ta hadiya sannan ta dan lashi kasan lebanta kadan, batace komai ba, shiru yadanyi jiyai tace “kasan meyasa banji haushin yimai magana ba balle harnai tunanin taimakon shi?”


Meyasa? Ya tambaya yana dan kara gyara kansa dake wajen wuyanta.


Juyowa tai suna fuskartar juna, daf suke da juna, tasa hannu akan fuskarsa tana dan shafawa kadan tace “ta hanyarsa na hadu dakai, sannan ta hanyarsa muka kai inda muke yanzu, da ban aureshi ba kila bazan sanka ba, da bai ci amana ta kila bazamu kai wannan stage din ba.”


Tadan yi wani lalausan murmushi tace “shiyasa ko haushinshi banaji.”


A hankali wani murmushi ya bayyana a fuskar Khalid, matso da fuskarsa yai ya sumbaci lebanta yace “That’s why nima nake yafemai duk sanda na tuno hakan.”


A tare sukai murmushi sai kuma ta canza fuska, tace “gwara ni dama haka ka ganni dashi kaifa?”


Nifa?


“Eh yarinyar da har gun aiki a manne kuke kai da ita.”



Wa? Ya tambaya yana kallanta, tayi kicin kicin da fuska yace “wai Safiya?”


Oho koma wa sunanta ni bai damenba.


Murmushi yai yace “Karki tsaneta please yanda ta taso ne yasa take ganin duk abinda take so kamar kayan shago ne da zataje ta siya haka take ji, sannan ni ba komai tsakaninmu da ita, ita tana tunanin so na take ni kuma nasan ba sona take ba, duk sanda hankali ya shigeta am sure zata fahimci hakan.”


Dan baki ta tabe tace “naji da alama kamafi saninta akaina.” Ta karasa maganar tana dan harararsa.


Murmushi yai ya kara kankameta tare da lumshe idanunsa.

A hankali tace “maganar dazu? In fita gobe?”


Murmushi yadanyi idanunsa na rufe yace “abu daya sannan please banda mai tsada.”


Shiru tadanyi tana tunani, itakam ya zatai da Khalid?


A hankali bacci ya daukesu.......


************


  Kabir ne ya kara kiran number a karo na goma sha biyar, yanzun ma harta katse bata dauka ba, Mumy ce ta shigo dakun kawai ta ja akwati ta fara zuba kayan Afreey a ciki.


Afreey dake kwance ce tadan leko kallan Mumy tai cikin mamaki ta mike zaune da sauri tace “Mumy me kikeyi hakan?”


Tace “Gun yayarki zaki tafi yau”


Da sauri tace “yanzun Paris xan tafi? Ban shirya ba?”


Gashinan ina shirya miki ai, sannan in kinje shekara biyu zakiyi acan.


Ido ta zaro ta mike zaune da sauri tace “me kike nufi Mumy?”


Tace “badai taurin kai kike mana akan wani fakiri ba? Mahaifinki ne ya yanke hukuncin nan sannan nima na amince dashi, nan da awa biyu jirgin ku zai tashi.”


Awa biyu? Ta fada tare da mikewa tsaye da sauri ina zata san ma inda yake? Ga ya canza number.


Ranta ne ya baci ta kalli Mumy tace “mumy ki barni plz bansan zuwa wlh.”


Mumy bata kula taba ta cigaba da hada kaya.


Afreey haka ta shirya dan dole Abbi da kanshi yai shirin yi mata rakiya suka tafi kasar Paris suna tafe tana hawaye har jirgi ya tashi bata daina kiran Khalid ba.


*********


Kayanta ta jawo bayan motarsu ta sauka ta nufi gidansu Kamalu, cikinta sai uban karar yunwa yakeyi.


Haka ta isa gidan sai dai Kamalu yace mata Adam ya fita tun safe.


Ganin yanda iyayen Kamalu ke mata wani kallo yasa ta nemi bashin dari biyu agun Kamalu ta nufi gidan Hajiya bilki.


Kallanta sosai mai gadin ya shiga yin dan ya kasa gasgata idanunsa kan Goggo ce.


Sai datace “Nuhu bude min mana.”


Yace “hajiyar bata nan.”


Tace “ina taje?”


Yace “wlh ban sani ba dazu ta fita.”


Bari na shiga na jirata.


Sai dai ki jirata a harabar gidan dan ba kowa a ciki.


Cikin takaici ta wuce harabar gidan ta zauna, sanyi sai busawa yake sai rakubewa takeyi.


Adam kam cikin farinciki ya isa inda mutumin yace su hadu.


Tunda ya iso yaga sunata aikin gini, cikin mamaki yace “oh aikin fad’ad’a gun aikin nepa din sukeyi?”


Haka ya isa can ciki inda mutumin yake yana zaune suna cin abinci shinkafa da wake da suka siya yanzu.


Kallan Adam yai yace “oh harka iso?”


Ya kalleshi cikin mamaki yace “eh amma me kuke anan?”


Ya tambaya yana kallan yanda suke cin shinkafar tundaga yanayin jikinsu.


Gaddafi ya kalleshi yace “kaci abinci ne?”


A’a Adam yace yana kallanshi.


Alama yamai daya zauna, Adam ya zauna ya kalli plate din da aka turo mai, loma daya yaci yace “a ina zan yi aikin? Naga nan kamar ba aikin kuke ba.”


Dariya Gaddafi yai yace “lokacin cin abinci ne daga mun gama zakaga kowa ya d’au harama.”


Cikin rashin fahimta yake cin abincin, kafin ya gama yaga ragowar sun gama kowa ya mike, gani yai suna ta aiki kowa da abinda yakeyi.


Adam ya kalla yace “kai tunda farkon zuwa ne sannan yace baka taba yi ba ka fara da kwaso kasa.”


Shinkafar daya firzo ne yasa ya kalleshe, kallansa yai yace “kasa?”


Gaddafi ya kalli inda ya farzo shinkafar yace “eh ko kafinsan farawa da hada siminti?”


Baki Adam ya bude yana kallansa yace “aikin gini nazo yi?”


Eh da me ka dauka?


Kallansa Adam yai ya mike da sauri zai tafi, sai dai tunawa dayai kudin da Zainab ma ta bashi a biyan bashi ya kare dakyar ya samu na mota yau, yazaiyi ya  koma?


Haka ya nufi gun yashi yana gamawa akasashi hadin siminti, awa biyu jinta ya dingayi kamar wanda ya wuni, jikinsa duk yadau ciwo.


Gun Gaddafi yaje yace kansa na ciwo.

Gaddafi ya duba awa hudu kawai yai yace ga kudinka nayau ya mika mai dubu daya Adam ya kalleshi yace “kullum nai dubu daya zan samu?”


Yace eh, amma kaga Khalid dake aikin mutum biyu dubu biyu yake samu kullum, wani sa’in ma na mutum uku yake.


Baki Adam ya bude shiva Khalid bane bazai kashe kanshi da aiki ba amma dubu daya kullum? Kwana goma dubu goma?

Murmushin jin dadi yai tunda bazai samu waccan ba gwara ya lalaba dama yanata mamaki ace abinda yama Zainab bai dameta ba harta bashi aiki?


Amsa yai ya fito cikin jin dadi.


Har zai hau motar unguwarsu ya canza ya hau ta Naibawa.


Tsayawa yasai lemo da ayaba na dari da hamsin yana tuno Khalid hk yai.


A kofar gidan ya tsaya yana tunani, zata kulashi yau? Yai tambayar jiki a sanyaye sannan yai sallama.


Baba na rubutu da alkalami a alo a waje ya amsa tare da bada izini.


Adam ne ya shigo ya karasa kusa dashi ya tsugunna yana gaisuwa.

Baba wanda tun shigowarshi yake kallansa harya karaso.


Amsawa yai yace “sannu da zuwa.”

Adam yace “yauwa Baba yamai jiki?”

Kallansa yai haryanzu yana jin zafinsa kadan yace “ gun Raziyya kazo?”


Kasa yai dakai yace “Babs ku kara yafemin bansan haukar danai haka ta ruguza rayuwarku ba.”


Kallansa yai yace “Mun yafema dan abinda ya faru yasa na rufe ido na toshe kunena har sai da abokinka ya farkar dani na fahimci lalai nima na tafka babban kuskure, nikaina dana sanin abinda na aikata nakeyi wanda yanzu idan duniya suka gama sani bansan yanda rayuwarta zata kare ba.”


Jikin Adam ne ya sake mutuwa tausayinsu dajin haushin kanshi ya sake kamashi, kwalla ta zubomai yace “kuyi hakuri Baba.”


Murmushi Baba yai ya girgiza kai yana kokarin wanke rubutun yace “duk abinda ya faru laifi nane ina neman Allah ya yfemin, ya bata miji na gari itama.”


Fitowar Raziyya daga bandaki ne yasa ya kalleta, buta ta ajiye ta bugamai wani banzan kallo tana neman wucewa ciki.


Baba ne yace “Raziya dawo nan.”


Dawowa tai inda ya nuna mata fuskarta a daure tamau.


Baba ya mike ya dau rubutun ya nufi dakin mama ya barsu.


Adam ne ya kalleta, cikin dauriya yace “Sa....Au Raziya.”


Bata ko kalleshi ba balle yasa ran zata bashi amsa.


Yacigaba “Raziya ki yafemun dan Allah, nayi kuskure na sani nine silar jifawar rayuwarki haka, amma ki yafemun ba dan halina ba.”


Idanunta ne suka ciko tana kallanshi, a hankali hawaye suka gangaro kan fuskarta.


Daurewa yai yace “kiyi hakuri dan Allah.” Yai maganar cikin rawar murya.


Kallansa tai sannan ta mike, da sauri yace “Raziyya!”


Tsayawa tai batare da ta kalleshi ba, yace “dan Allah kiyi hakuri.”


Daki ta shiga ta rufo kofar yana daga waje yana jin kukanta, sai dai itakam wannan karan kukan tausayin kanta take dan ko yanzu a dole take zaune a gidan nan amma ta riga ta saba da namiji batasan yanda zata kare rayuwarta ba.


Haka ya musu sallama ya fito jiki a sanyaye.


********


Sakonsa data gani ne ya sata sakin murmushi mai sanyi, kallan kayan data amso daga gun Maman Al’amin tai, sannan ta sake karanta sakon.


Baby i miss u.....


Fuska tadan rufe sannan ta kara kallan kayan dake kan kujera wanda ta fita ta siyo yanzu, dan tana dawowa ta tsaya a gidan Maman Al’amin ta amso kayanta.


Murmushi tai sannan ta mike ta shiga dasu daki, budesu ta dingayi tana gwadawa, kunya duk ta rufeta ganin kayan duk kamar kayan ‘yan iskan titi.


Wata riga tasa wacce gaba daya rabin kirjinta a waje yake ga rigar iyakarta gwiwa, da sauri ta hau cirewa tana cewa “ina na isa sa wannan?”


Wayarta ce tai kara ta dauka tare da cewa “Hello Yallabai”


Abubakar yace “Zainab da gaske bazaki dawo ba?”


“eh!” Ta fada kai tsaye, ajiyar zuciya yai yace “na fahimceki shikenan ni kuma zan saida broadcasting station din nan dan dama solution dina kece in har bazaki dawo ba zan sashi a kasuwa.


Cikin sauri tace “ma’aikatan ciki fa?”


Wannan sai su nemi wani aikin dan dama na ba Kabir kwana daya tunda bai samo solution ba yu din nan na koreshi.


Shiru tai kafin tace “wa zaka saidawa?”


Ban sani ba sai wanda yake so naga kuma zai siya yanda nake so.


Shiru tadanyi kafin tace “ka saidamin.”


Fuskarsa dauke da mamaki yace “in saida miki?”


Tace “eh, in har saidawa zakai ka saidamun.”


Shiru yadanyi yace “kizo mu tattauna, kiji ko zaki iya siya.


Okay kasa time ka turon, nan sukai sallama.


Shiru tadanyi, kafin ta kalli kayan, murmushi ta sake, jin fitsari ne yasa ta shiga toilet, tana fitowa ta shiga kitchen tana tafe tana wa kanta dariya tare da cewa “ai baya nan kafin ya dawo na cire.”


Jellof din taliya datai ta zuba ta fito falo tana ci tana duduba abu a laptop dinta, tana gamawa ta cigaba da abinda take ko plate din bata maida ba, jin ta buga mata ba charge yasa tai ajiyar zuciya sannan ta dau plate din zata wuce kitchen.


Karar gate taji, wani murmushi ta saki sam ta manta shigar dake jikinta, dan window ta leka ta sake sakin murmushi tana kallansa har ya kusa bude kofar, kallan kanta tai ido ta zaro sannan tai hanyar daki da sauri, sai dai ko kusa da kofar bata je ba ya bude kofar.


Baki ya saki yana kallanta, idanunsa kuwa ya bude su sosai tun daga kanta yake kallanta, ta tufke gashinta a tsakiyar kai? Sakowa yai rigar kalar ash ce wato kalar ruwan toka, ta zauna dam a jikinta, a hankali ya sauko kasan cinyoyinta dake waje, da alama ma bata jin sanyi.


Wani irin abu ne ya taso mai, a hankali ya fara takowa, jin alamar yana tahowa yasa ta taka kafafunta tai daku da sauri, tana shiga yana turo kofar, kallansa tai ya kalli yanda rigar ta mata ta gaba.


“Wow da alama Baby so kike ki kasheni” ya fada yana dan jingina kansa da jikin kofa.


Kallansa tai sannan ta juya da sauri zata shige toilet, cikin hanzari ya karaso ya kamo kugunta ya jata suka fada kan gado.


Kallansa tai tace “dan Allah barni na cire kayan kunya nake.”


Kunya? Ya tambaya yana kara kallan jikinta yace “ina kunya ana neman zautar dani? An samu hanya?”


Dan idanunta ta juya tace “ni dai karka fassarani, nasan ai basumin kyau ba kamar wata.....” sai kuma tai shiru tana kunyar yanda yake kallanta.


Murmushi yai a hankali yace “i like it, i like it soo much.”


Kunyace ta rufeta ta ja pillow ta rufe fuskarta dashi.


Hannu yasa yana kokarin jan pillow din itama tana kara rikeshi, yana ja ya fizge kallansa tai tace “dagani.”


Um um


Allah nauyi gareka


Dan murginawa kusa da ita yai yace “in nauyi gareni kiyi maza ki koyi yi a sama.”


Baki ta bude da sauri ta dau wani pillow din ta makamai tace “Laaaaa, Allah da alama ba karatu kawai kai a daki ba.”


Dariya yai yace “me nai?”


Tace “Kafi karfina wlh” ta fara kokarin mikewa, riko hannunta yai yace “Baby i miss u.”


Juyowa tai a hankali tana kallanshi, murmushi ya mata, samun kanta tai da kwanciya kusa dashi, hakan yasa suka kwanta a rigingine hannunsu na rike da juna.


Yace “ina kika samo kayan rudani?”


Tace “makota”

“Ahhh lalai na amince da zuwa gunta.”

Murmushi tai tace “I like it.”


Yace “me?”

Tace “inkace you miss me.”


Murmushi yai yadan juyo da fuskarsa yace “in nace I luv you fa?”


Kallansa tai zuciyarta na bugawa da sauri cikin wata murya da ita kanta batasan tana da ita ba tace “i really want to ask you, yaushe ka fara sona?”


Yana kallanta yace “I can’t say, na dai san before ki bar aiki.”


Murmushi tai tace “kenan sanda kaje Abuja ka....” sai kuma tai shiru jin nauyin maganar.


Kai yadan daga mata yace “Umm shiyasa it hurt danaji kina min wani zancen aiki”


Murmushi tai tace “meyasa bakai tunanin me yasa ban nemi kowa ba sai kai?”


Kallanta yai yace “bansan wannan tunanin at that time I feel like zakicemin saboda ni talaka ne.”


Kallansa tai, a hankali ya kai ido kan saman rigarta.


Bakinsa ya sa cikin nata..........


*************


Uwar hamma ta saki sannan tai mika tana kokarin mikewa, kallan Hajiya Bilki dake kanta tai, tace “Bilki kin dawo?”


Hajiya Bilki ta kalleta tace “inalilahi wai da gaske kece? Adama?”


Goggo tai dan yake tace “Bilki nice”


Kallan mamaki ta shiga mata har suka shiga ciki.....


Goggo ta daure tace “Bilki duniya ce ta juya dani nazo dan Allah ko aikatau ki nema min.”


Shiru tai tana kallanta tace “me ya juya haka lokaci daya? Ina sirikarki?”


Shiru tai kafin tace “sun rabu.”


Kuka ta sa mata, Hajiya Bilki tausayinta ya kamata tace “ki kwana anan gobe mayi magana.”


Dadi kamar ya kashe Goggo balle an bata abinci tashi ga falansu ana ta kallo ta rakube a kasa tana yi, har yaran suka kaji suka kwanta tana ta uban kallo, sai da Hajiya Bilki tace su kwanciya ake in dare yayi haka.


Dole ta tafi dan dakin da aka ce ta kwanta, kallan dakin tai tace da Hajiya bilki katan daki take ban amma yau???


Haka ta kwanta.


******


Ayusher🏌🏻‍♀[1/20, 11:47 AM] +234 816 537 8773: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


*Sweet din Baby na gaisuwa 😉😉*


{67}


Kwanciya sukai bayan sunyi sallar asuba alarm dinsa ne ya buga ya bude idanunsa tare da kashewa, a hankali ya janyeta daga jikinsa, har ya cire kaya zai shiga toilet ya kalleta, hannu yasa ya dan tab'ata cikin bacci ta gyara kwanciyarta.


Kara tabata yai yace "Baby tashi."


Idanunta ta bude a hankali ta budesu da kyar cikin bacci tace "ya akai?"


Yace "breakfast."


Idanunta ta maida ta rufe tace "anjima zanci in na tashi."


Yace "bake ba ni."


Idanunta tasake budewa dakyar tace "baga haka kake tafiya."

Yace "hmm haka nake tafiya amma daga jiya na daina, tashi ki samun wani abun kafin na fito daga wanka."


Bata san sanda ta ware idanunta ba tace "yanzu wai zan sama?"


Kai ya daga alamar eh yace "kidan yi sauri kinsan bama late."


Tana kokarin magana ya shiga toilet, tsananin mamaki ne ya rufeta, wayarta ta jawo ta duba time 6:20am? Haka ta mike kamar zatai kuka tai kitchen, tama rasa me ake ci da sassafen Allah, sannan me zatamai kafin ya fito daga wanka? Kwai ta soya ta dafa ruwan tea ta dauko bread ta fito dashi falo, murmushi tai tana tuno yanda Aunty ke tsananin san tea da bread da kwai ashe yau zai mata rana.


Tana ajiye cup yana fitowa, kallansa tai hamma ce ta  zo mata dan bacci takeji sosai, zama yai ta kalleshi, tea din ya hada ya fara sha, kallanta yai yace "kije ki kwanta."


Mikewa tai zata wuce, hannu yasa ya riko hannunta ta koma ta zauna.


Kallanta yai sannan ya nuna mata kuncinsa, murmushi tai sannan tace "bayan an hanani bacci?"


Yace "yanzu aka fara hanaki, dan kullum a gida zan dinga break."


Kallansa tai cikin mamaki tace "a gida?"


Kuncinsa ya kara nuna mata yace "Sweet na jira."


Sumbatarsa tai ya saketa ya cigaba dacin abincinsa, mikewa tai ta wuce ciki ta kwanta, sai dai duk yanda taso tai bacci ta kasa sai juye take, jiya har sha biyu basuyi bacci ba dan bayan sun kwanta hira sukai cikin nishadi da kauna sukai bacci, yau me ya faru haka?


Daki ya shigo ya dau agoggonsa tana kwance tana kallansa, kallanta yai ya sakar mata murmushi sannan ya matso kusa da ita ya sumbaceta a hankali yace "See u baby"


Samun kanta tai da mai murmushi itama, fitowa yai shiru tai a daki a hankali ta sauko ta bude waje ta tsaya a baranda tana jin yanda sanyi ke busawa, hanzu a haka ya fita da kafa?


Shiru tai tana kallan motarta, juyawa tai ciki.


*********


Goggo cikin jin dadi take cin soyayyen dankali da kwai, loma takeyi kai kace bata taba ci ba.


Hajiya Bilki ce ta turo kofar dakin, Goggo tai saurin zuba na hannunta cikin plate din ganin yanda ta cika hannu, kallanta tai tace "Bilki!"

Hajiya Bilki ta na tsaye a jikin kofa ta kalleta tace "inkin gama cin abincin kizo ki tafi."


Kallan ta tai da sauri tace "in tafi ina?"


Murmushi Hajiya Bilki tai tace "ina na sani? Ina fada miki ne bana bukatar mai aiki balle kuma ke dana san hallinki"


Hankalin Goggo ya tashi tace "Bilki na canza yanzu sam ba haka nake ba, ba ruwana wlh ba zan kushe komai ba zan kuma kular miki......"


Katseta tai da cewa "Ko kin canza ko baki canzs ba maganar dai guda daya ce kiyi hakuri ki nemi wani gun."


Goggo ta kalleta tace "yanzu Bilki ina neman alfarma gunki duk yanda muke amma ki kasa min?"


Kallanta tai a kule tace "yanda muke? A yaya muke? Ke da kika sa dana ya fada soyayyar Nabila kikace zaki hadasu aure, yaran nan ya kamu da santa amma dame kika sakamin? Ko cewa nai zaije sai ki fara kame kame, ko duk daga baya kina tunanin ban fahimceki bane?"


Goggo ta kalleta tace "kindai san banda iko akanta ko kin manta kanwar Zainab ce?"


Haushi ya kama Bilki tace "kinsan haka kika kawo mai hotonta?"


Sum sum tai dakai Bilki tace "ni wannan ma abarshi ya wuce ga wannan, ta ajiye mata dubu biyu tace "kiyi na mota, sannan in har baki kara dawowa gidan nan ba zanfi kowa farin ciki xan kuma fahimci kin san darajar kanki."


Ta juya ta fita.


Baki Goggo ta bude tana kallan ikon Allah, wannan dankalin kasa karasa ci tai, ta dau kayanta dake leda ta dau dubu biyun ta fito, tana tambayar 'yarta ma inda Bilkin take suyi sallama amma sam taki ko kulata.


Haka ta fita gaba daya ranta ba dadi, ta koma gidansu Kamalu tana fatan samun Adam.


********

Adam ne ya shirya ai dole ya koma gun aikin nan, dan yama Khalid text ma bai ko mai reply ba, kenan bashida wani zabi.


Ya fito tana tace yana hamma sai jerota yakeyi dan ya saba baccin safe yau kuwa gashi karfe tara wai zai fita.


Yana shawo kwana Goggo na saukowa daga cikin adaidaita, kamar da wasa ya kara kallanta.


Kallansa tai cikin jin dadi tace "Adam!"


Kallanta yai ya karaso yace "Goggo? Me kike anan?"


Kallansa tai tace "da Kamalu baicema nazo ba?"


Kinzo me?

Ya tambaya yana kallan kayanta a leda.


Tace “Adam na gaji da zama a kauye wlh, ga bani da waya gaba daya komai ya tsaya min cak.”


A kufule yace “kina gani nima a dosane nake ina kike so na saki?”


Tace “bazamu rasa na Allah ba.”


Kallanta yai yace “wlh komawa zakiyi yanzu.”


Ina zan koma?


Kauyen kije can ki lalaba kafin Allah ya sa nadan tara, kinsan yanzu aikin da nakeyi ne? Gini fa nakeyi? Duk yanda nake tunda kikaga na dage kema ai sai kiyi hakuri da yanda Allah yai dake.”


Kallansa tai ranta a matukar bace, yace “Allah Goggo komawa zakiyi yanzu.”


Fuskarta ta hade tace “na maka rana dole kamin dare, duk inda nake kai kadai nake tunanin halin da kake amma abinda zaka cemin kenan?”


Yace “Goggo dan Allah ki barni da abinda ke damuwa, idan na tuno abinda nama mutanen can ji nake gaba daya na tsani kaina, ki barni da wannan bazan kuma kara da rokon karaki a gidan mutane ba.”


Lalai Adam ni kake fadawa haka? Akainane bazakai roko ba? Sanda na haifeka tsabar san da na dorama tun kana ciki yasa mahaifinka ya tsokaneni ya sama Adam wai ni Adama kai Adamu, mutane akanka kasan irin zagin dana sha? Na saida duk abubuwa na saboda kai amma haka zaka cemin?


Ransa a matukar bace yace “me na miki? Dan nace kawai Goggo ki koma ki kira ma zauna da kafata? Ke ba abin alfahari bane kiga ina aiki?”


Ido ta zubamai ranta a matukar bace adaidaita ya tara suka shiga, ranta duk a bace, shiru sukai har suka je tasha kallanta yai yace “kiyi hakuri Goggo zanzo da zaran na samu dan kudi.”


Kallansa tai tace “ka aikon da waya.”


Yace “zan aiko da zaran na hada kudi.”


Haka ya shiga mota ranta duk ba dadi, me zata ce ma yan gidan?


Sai da suka tafi sannan ya juya ya tafi gun ginin, kallan gun yai shikam wlh baisan aikin nan amma ya zaiyi? Yanzu Kamalu ma ba magana yake mai sosai ba ya kuma tabbatar ya gaji da zamanshi ne, dole ya shiga ciki.


*******


Har ya iso gate din gidan yana waya da Dady kafin suyi sallama ya kashe wayar.


Zainab wacce ke kwance akan gado rike da wayarta gefe kuna takarda da biro ne tana duba abu a wayarta tana rubutawa a takardar, sam bataji alamar shigowarsa ba, lokaci ta kalla a wayarta taga har shida saura.


Mikewa tai ta fito falo dan shan ruwa, zaune ta ganshi ya jingina kansa da kujera idanunsa a rufe.


Kallansa tai cikin mamaki, sannan ta tako har inda yake, kallansa samun kanta tai da kasa dauke ido daga kansa, idanunsa a rufe yace “Baby in kin gama kallan nawa zan bude ido.”


Kanta ta dauke ds sauri tana cewa “yaushe ka shigo?”


Idanunsa yadan bude sannsn yasa hannu ya jawota ta dan zaune a karkace akan cinyarsa.


Kansa ya kwantar akan kafadarta yace “jira nake ki fito.”


Kallansa tai tace “in ban fito bafa?”


“Nasan zaki fito ma tunda Sweet dinki bai dawo ba, ina kika ga nutsuwa?”


Wani murmushi tai tace “taya akai kasan banda ita?”


Dagowa yai ya kalleta yace “I know it, you don’t have to tell me.”


Wai why are you so confidence?


Kansa ya maida yace “me zai sa na jira sai kin fadi abinda na sani?”


Murmushi tai, kin samu cinya kin ki tashi, gashi ni kuma ina san mikewa.


Kallan mamaki tamai tace “waye ya sani akan cinyar?”


Nine sannan yanzu kuma nace a dagani.


Mikewa tai rai a bace, ta daure fuska tamau, kallanta yai bayan ya mike yace “bari nadan watsa ruwa muyi sallah sai muci abinci”


Kai ta daga kawai fuskarta haryanzu a tsuke, baiko bi takanta ba ya wuce yana murmushi shi kadai.


Haushi ya isheta, kallan atamfar data sa tai tace ko in sa kananan kaya? In kuma nasa ai sai yafi fadam abinda yaso tunda ba dashi ya ganni ba.


Zama tai a bakin kujera, meya sameshi?


Kofar daki aka bude, ya leko kai yace “Baby ina towel dina?”


Dan kallansa tai tace “yana inda ka ajiye.”


Zo ki daukomin.


Banfa dauka.......


Maida kofar yai ya rufe, a kufule ta mike, tana shiga taga towel daure a jikinsa.


Kallansa tai tace “Sweet kace baka ganshi ba?”


Murmushi ya sakar mata yace “so nake kawai naga kinzo.”


Kallansa tai tace “fadamin gaskiya so kake kaga raina ya baci ko?”


Bingo ya akai kika sani?


Baki ta bude tace “dalili?”tai tambayar cikin mamaki.


Sirri nane ni kadai but i like it.


U like it?


Bai bata amsa ba ya shiga toilet yana kokarin rufewa yace “ko za’a tayani wankan?”


Juyawa tai ta fita daga dakin tana ajiyar zuciya, wai meke kan Khalid? Sam baya kunyar fadar abu? Ta dauka shine zai dinga ma jin kunyarta amma yanzu taga alama ita ma ke jin kunyarsa.


*******


  Abincin data ajiye mai ya kalla sannan ya zauna ya kalleta, saukowa tai ta zubamai, ta samai spoon kallanta yai ta kalleshi mamaki ne ya kamata dataga fuskarsa a daure gam.


Mikewa tai ta zauna tana kallan ikon Allah, harya gama cin abincin be ce mata komai ba, ruwa yasha yace “kwashe kwanukan.”


Kwashewa tai gaba daya mamaki ya rufeta, tana dawowa taga ya bar falan.


Daki ta nufa, ganin baya nan ta tsaya a jikin dakin, jin karan gen ne yasa tasan yana waje.


Yana shigowa ya xauna akan kujera baiko kalli inda take ba, gaba daya hankalinta ya tashi, kallansa tai a hankali ta dan zauna daga gefensa tace “menene?”


Kallanta yai yanayin sa gaba daya ta kasa fahimta, tace “menene?”


  Next time in abu ya shafeki ya kuma shafeni ina san jinshi daga bakinki.


Kallan mamaki tamai tace “wani abin nai?”


Murmushi yai.


Kallansa tai ta riko hannunsa tace “Kanasan hankalin Baby ya tashi?”


Kallanta yai sannan ya kalli hannunsa data rike murmushi yai yace “Meyasa baki fadan kina tunanin siyan gidan Tv dincan ba?”


Kallansa tai kana ganin yanayin da fuskarta ta bayyanar zakasan dana sani ne tace “Allah I thought na fadama, sannan abin bai tabbata ba.”


Duk abinda ya shafeki ya kuma shafeni ina san ko ban xama na farko ba ya zama na sani daga bakinki, ni bai zama dole sai na fada miki komai ba but i want you to tell me, zaki iya kiranshi selfishness........


Rungume shi tai wanda hakan yasashi yin shiru, am sorry nayi laifi, amma dan sankai sai kace na fadama kai kuma ba komai ba.


Murmushi yai yace “eh am a man akwai abinda dole ni kadai zan iya rikeshi.”


Dagowa tai tana kallansa tace “selfishness”


Yace “eh dana bakiji nace ki kirashi da hakan ba?”


Dan harararsa tai tace “haushi kaji maganar kajita daga gun Dady?”


Yace “a’a matsayina da yardar da kikamin nake san na duba.”


Murmhshi tai tace “Allah bansan yanda zanyi dakai ba.”


Ta fada tana dan matsawa, kara jawota yai yace “akwai matsala kenan”


Tame? Ta tambaya tana dan yin baya a kan kujera ganin yanda yake kwantowa.


Sai da suka karasa jikin kujera sannan ya nufi fuskarta kamar mai shirin sumbata dan harta rufe idanunta sai jitai yace “saboda ke kadaice a yanzu kike da yanda zakiyi dani.”


Ido ta bude ta kalleshi, murmushi yai yace “yau ke nakeso kiyi.”


Ya fada yana dan motsa bakinsa, kallansa tai tace ka danne ni.


Baki gane yaran ba kenan?


Dan sumbatar lebansa tai tace “gashinan nayi.”


Kallanta yai dan yanda ya kankance ido yana kallanta har ya bata kunya tace “menene kuma?”


Yace “ina tunanin yanda zanyi dake ne.”


Dariya tai tace “yanda zakai dani?”


Yace “eh”


Mikewa yai ya zauna yace “Dady yace cikin weekend din nan zaizo, zakuje gun Abubakar din.”


Zamuje dai bazaka rakani ba?


Eh ya fada kai tsaye.


Tace “ba ko yar kara?”


Yace “so kike nace eh?”


Dan fuska ta kauda, murmushi yai yace “am sorry amma no.” Ya karasa maganar da murmushi.


Shiru tai jin kansa tai akan kafadarta ya kwanta sannan ya jasu suka jingina da kujerar, ya sa hannunsa ya zagayo da ita ta cikinta.


Idanu ta lumshe a hankali.


*******


Ayusher🏌🏻‍♀


********

[1/20, 11:47 AM] +234 816 537 8773: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{68}


Alhamdulila Dady ya zo an sai broadcasting station, sunje danbatta Khalid ya kai Abba asibiti dan kwana ma sukai a can sai washegari suka dawo, ba karamin dadi Khalid yaji ba dayaji Salmanu yacemai yar gida yake san ayi, sai dai Khalid yace mai tunda tana shirin fara exams na waec da neco ya bari sai ta gama.


Sun dawo kano cikin kewa da jiran lokacin hutu dan Asiya tazo dan itama tasan su Nabila zasuzo.


*******


Yau wata biyu da sati biyu da aure, sati uku kenan da fara aikinta.


Khalid ne ya fito daga wanka harya gama shiryawa bata shigo dakin ba, sanye yake cikin suit wanda a koda yaushe inya saka kyansa da kyan zatinsa ke kara fitowa agoggonsa ya daura a ahannunsa sannan ya dau jakarsa ta aiki da wayarsa ya fito daga dakin.


Abincinsa ya gani a falo hakan yasa kawai ya zauna ya bude, soyayyiyar indomie ce, kadan yaci dan tun daren jiya yake jin cikinsa a cunkushe.

Daga waje yaji tada mota hakan yasa yasan tana waje, tea ya hada yadan kurba, yana sha yana kallan gidan mikewa yai ya dau plates da cup din ya wuce kitchen, kallan kitchen din yai ga kwanukan datai amfani dasu nan a sink, ajiyewa yai kawai ya fito.


Tana gani ya fito ta fito daga cikin motarta tace “Sweet kai nake ta jira sauri nake yi.”


Ko kallanta baiyi ba yacigaba da sa takalminsa, da sauri ta tuno hakan yasa tace “Oh ina kwana?”


Ta fada tana tahowa inda yake.


Bai kalleta ba sai dai ya amsa gaisuwarta.


Hannunsa tadan riko tace “muje?”


Kallanta yai yace “ina?”


“Gun aiki na akiyeka na wuce”

Dan kallanta yai yace “no ki wuce.”


Tace “dan Allah Sweet ka daina min haka kazo mu wuce tare plz”


Hannunsa ya dan zare yace “sai na dawo.”


Ya fito daga gidan bayan ya bude mata gate, bin bayansa da kallo tai sannan tai ajiyar zuciya agoggo ta kalla sannan ta juya cikin sauri ta shiga mota, tana kallansa yana tafiyarsa, haka ta wuceshi ta tafi gun aikinta.


Gaba daya komai ya cabe mata dan tana aikatuwa saboda komai na gun ya durkushe sai faman saita komai takeyi, meeting ta wuce direct ranta a matukar bace take magana, tana gamawa ta fito ta wuce office dinta, tea dinta tasha sannan ta fito tana duduba abinda akeyi.


Sai data tabbatar komai na tafiya yanda takeso sannan ta koma office dinta ta cigaba da aikinta.


Secretary dinta ce ta shigo tace “Hajiya ta gama yin aikin.”


Kallanta tai tace “tabi duk wanda zai dauko rahoto yanzu ta taimaka musu da aikin rike kaya.”


Kallanta tai cikin mamaki ganin yanda kullum Ramlatu a wahala take karewa, Zainab tace “menene? Kice in bazata iya ba tabar aikin.”


Haka ta juya ta sanar mata, Ramlatu tace “to” sannan ta juya.


Kanta tadan dafa dake mata ciwo sannan ta kalli wayarta, kan sunan Sweet ta bude ta zubawa sunan ido ajiyar zuciya tai sannan ta kifa wayar ga cigaba da aikinta.


Sai yamma lis sannan ya dawo, yauma ya rigata dawowa, yanda ya tafi dama haka ya dawo yaga gidan, yana tunanin raban da gidan nan yaga shara yakai sati biyu, kitchen ya shiga shiru yai, tunanin gyarawa dakansa yai sai kuma yai tunanin daga sanda ya fara ya tabbatar bazata sake yi da kanta ba.


Juyawa yai ya shiga toilet yai wanka, akan gado ya dan mike yana waya da Salmanu.


Suna sallama yaji shigowar motarta, kayanta ta kwaso ta shigo ciki, ajiyewa tai a falo sannan ta shiga daki, yana zaune yana dane dane a waya kallansa tai tace “Sweet ka dawo?”


Eh kawai yace ba tare da ya kalleta ba, kallansa tai sannan ta matso ta zauna dan kusa dashi tace “sai yaushe zaka dinga kallona in ina ma magana?”


Kallanta yai yace “dan matsa zan wuce masallaci.”


Jiki a sanyaye ta mike ya sauko ya fito ya wuce masallaci.


Kanta tadan shafa sannan ta shiga toilet, wanka tai sannan ta sa kayan bacci sai datai sallah sannan ta fito falo, gen aka tada dayake ya canzo musu gen karshen watan daya wuce.


Zama tai ta jawo takardun ta tana dudubawa, Khalid ne ya shigo baiko kalli inda take ba yai hanyar daki.


“Sweet abinci fa?”


Sai nayi isha’i yace kawai ya wuce ciki.


Shiru tai ganin ta kasa maida hankalinta kan abinda takeyi hannunta tasa a gefen kanta tana dan murzawa tana cigaba da abinda takeyi.


Har ya fito zai fita masallaci sallar isha’i tana nan yanda ya barta tana ta hidima.


Kallo daya yama inda take ya wuce, sai dayaje kofa ta lura ya fito da kallo ta bishi ganin ya wuce bai ko bita kanta ba.


Idanu ta rufe sati daya kenan da canzawar Khalid sam yanzu ko magana baya bari suke mai tsawo, ita kuma ga abubuwa sun cude mata bata san ya zatai ba.


Tana nan tana tunani harya dawo, mikewa tai tana kallansa, zama yai akan kujera a falan ta wuce kitchen ta kawo mai abinci sannan ta zubamai, zama tai kusa da inda ta ajiye abincin tace “ko na baka?”


Kallanta yai yace “kina da time din?”


Kallan takardunta tai tace “oh am sry.”


Mikamai tai ya kalleta jiyai wani abu ya tsayamai a wuya, ruwa ya kurba sannan ya dan ci abincin kadan dan haryanzu cikinsa bai ware ba, mikewa yai ya maidashi kitchen ya kara kallan kitchen din kawai ya wuce daki.


Tana nan a zaune dai sai 11 ma tai sallah, ta danci abinci sannan ta kara komawa ta zauna sai karfe 1 ta kashe komai ta shiga daki.


Khalid ta kalla dake kwance yana bacci, kusa dashi taje ta sa hannu ta ratsin cikinsa ta keantar da kanta kusa da kanshi, tabashin datai ne yasa ya dan farka.


Sha’awa ke cinta kwanan nan dan harmamakin kanta takeyi duk sanda zata kwanta sai taji Khalid take bukata, shiru tai tana tunanin yanda da ya nuna mata kulawa, a haka har bacci ya dauketa.

juyowa yai tare da dan haskata, bacci take hankalinta a kwance.


Ido ya zuba maga kafin ya juya ya koma baccinsa.


Karfe biyar da rabi ta farka, ganin baya dakin ba kuma ya toilet yasa ta fito falo da sauri, zaune ta ganshi akan sallaya yana karatun alqur’ani.


Ruwan shinkafa ta saka sannan ta dawo falo inda yake, kusa dashi ta zauna ta dan sa kanta akan kafadarsa.


Ganin ya rufe qur’anin yasa tace “Sweet me kake tunani yau in muka dawo mu taho tare muyi siyayyar abinda babu a gida?”


No kimin list zan taho dashi in na dawo.


Kallansa tai tace “wai haka zamu cigaba da zama?l


Yanayin muryarta ne ya canza cikin rauni ta cigaba da ba haka kake ba meyasa lokaci daya kake neman canzamin? Bayan kasaba min da kai?in nama wani abin ka fadamin please amma ka daina nisanta kanka dani.


Kallanta yai kallan dayasa tasha jinin jikinta, yace “ni haryanzu Zainab yarinyace yar shekara 10?”


Kallansa tai tace “Sweet”


Idanunsa yadan runtse yace “i just don’t know what to do next, na gaji da miki uzuri na kuma gaji da nuna kamar raina bai baci ba.”


Cikin shakka tace “me nai?”


Yace “haryanzu tambaya kike?”


Tace “in ban tambaya ba ta ina zan sani? Gaba daya kasa na rasa yanda xanyi bansan menama ba amma duk ka canzamin.”


Kallanta yai yace “indai wacce ke gabana yar shekara 10 ce zan dane komai na sanar da ita.”


Kallansa tai bakinta na rawa tace “Ka san bansan......”


Katseta yai cikin zafi yace “can you please stop saying that? Komai kice baki sani ba? A koda yaushe ina miki uzurin rashin sanin abu sai yaushe ne zakisan abinda ya dace dake? Naji laifinane danai tunanin san da kikemin zai canzaki, sai dai da alama san da kikemin bai kai rabin wanda kike ma aikinki ba, nabaki dama kiyi yanda kikeso harzuwa sanda limit dina na hakuri dake zai kare daga lokacin kuma....”


Hannu tasa ta rufe mai baki, tana kallan kwayar idanunsa hawaye na zubowa kuncinta.


Idanu ya runtse, ganin yanda hawaye ke zubo mata, ganin ya kasa jurewa ne yasa hannu ya jawota jikinsa.


Cikin kuka tace “Am sorry, na sani tunda na koma aiki na kasa baka mahimmanci kamar da amma Allah komai nakeyi kana raina abubuwan ne sun.......”


Muryarta ce ta sarke saboda kukan dake neman kwace mata, bayanta kawai yake shafawa dan ba shikadai ne matsalar da suke fuskanta ba.


Dagota yai yana share mata hawayenta, hannunsa dake kan fuskarta ta rike tace “am sorry.”


Kallanta yai yace “ban hanaki aikinki ba but at least respect your marriage, na sani naso kaina in nace ina san ki bani full attention dinki sai dai in kina cikin gida i need your attention, bakisan meke going dani ba, bakisan a ya na dawo ba, bakisan wani hali nake ciki ba, kawai aikin da kikeyi shine abinda ke gabanki, wani irin so ne da zama da muke?”


Wasu hawayen ne suka digo saman hannunsa tace “kayi hakuri na daina, nima please ka daina janye jikinka daga gareni.”


Shiru yai yana kallanta, ba ruwa kika sa ba?


Da sauri ta mike ta shiga kitchen, kusa dashi ta dawo tana murmushi tace “kasan yaushe raban dana taho naga idanka akaina?”


Ko ban kalleki ta ido ba ina ganinki.


Kusa dashi ta zauna ta kamo hannunsa tace “Please ka dawo Sweet din dana sani.”


Yaushe raban da a share gidan nan?


Kallansa tai tare da dan sauke ido kasa tana kallan falan, duk da ba datti yai sosai ba amma kana gani kasan an dade bai ga kulawa ba.

kitchen fa?


Kallansa tai cikin jin kunya tace “Na na....” sai kuma tai shiru, yace “toilet fa?”


Sweet abubuwa sun min yawa wlh.


Kallanta yai yace “kina tunanin akanki mata suka fara aiki? In har bazaki iya ba zan taimaka na samo mai min.”


Mai aiki zaka samo mana?


Tai maganar kai tsaye, yace “a’a wace zata kula dani nake nema.”


Wani mugun kallo tamai tace “mata kake nufi?”


Yace “eh tunda kin auri aikinki ni zan auri mai kula.........”


Katseshi tai tace “naji ai ba cewa nai banda hannun yi ba.”


Oh I thought hannunki na aiki ne kawai.


Kallansa tai tace “da can da nakeyi fa?”


Da can yaushe?


Tadan kauda kai tace “kafin na fara aiki.”


Mikewa yai yana neman shiga daki, mikewa tai ta bishi ta rungumeshi ta baya.


Tsayawa yai yana jin abu na tsirgamai, tace “Ko sunana baka kira ba.”cikin sanyi tai maganar


Dan murmushi yai sannan ya juyo da ita murmushi yai yana kallanta, dan ido ta juya kadan sannan ta dago dakanta ta sumbaci bakinsa.


Kallansa tai tace “I miss you.”


Murmushi ya sake tana neman sakeshi ya sa hannu ya rikota, yace “haka ake missing?”


Kallansa tai tace “eh mana.”


Jeki rage gas kizo na fada miki wani abu.


Sakeshi tai ta shiga cikin kitchen, kallan kitchen din tai me takeyi tabar kitchen din ta haka? Ita da batasan kazanta?


Dole Khalid ransa ya baci, zuma ta dauko tadan diga kadan a auduga sannan ta riga almiskh ta dan yi matsi dashi na dan minti biyu sannan ta cire ta fito.


Yana zaune a kujera ta dawo, hannu ya mika mata ta karaso ya jawota jikinsa, kallansa tai tana murmushi, yace “kafin mu fita aiki mu dinga gyara ko ina? Zan tayaki da gyara gado.”


Zama tai akan cinyarsa tace “am sorry bansan me nakeyi har abin yakai haka ba, sannan gyaran gado ai ba aiki bane.”


To ko bakyaso?


Cikin dan shagwaba tace “ina so, amma Allah karka sakemin zancen wata mai taimako.”


In har kema kin ajiye aiki a office kin ba mijinki kulawa a gida.


Dan kwanciya tai akan jikinsa dagota yai yakai bakinshi cikin nata, yau kam anji jiki dan an dade ba’a gamu ba abin ba’a cewa komai.


Saboda lokacin aiki ya kusa tare sukai wanka tana fitowa ta wuce kitchen ta fara gyarawa, tana fitowa taga ya gyara daki, kallansa tai harya shirya, tace “thanks.”


Murmushi yai sannan yace “Thank god mun shirya abin bai zo ba.”


Kallansa tai sannan a ranta tace oh ya haka? Ya kamata yazo tun last week.


Kallanta yai tana sa kaya yace “menene?”


Kai ta girgiza tace “bakomai.”


Fitowa sukai tare suka sha tea da bread da butter, suka fito.


Sai dadi takeji kana ganin fuskarsu zakasan suna cikin farin ciki tun balle Zainab fuskarta wasai sai murmushi take.


Kallansa tai tace “please!”


Yace “no kije plz karki late.”


Ka manta nice shugaba inada damar yin late please mu tafi tare.


Murmushi yai ya matso kusa da kunnenta yace “bakyasan rabuwa dani?”


Murmushi tai tace “yanzun ma baza’a barni na fada ba?”


Haryanzu kansa na kusa da kunnenta yace “dazu an nunamin anyi missing dina sosai.”


Dadinta nima nasan anyi.


Kallanta yai yace “inyeee”


Tace “me? Kana mamaki? Ai naga alama nima daina shiru ya kamata nai”


A tare sukai murmushi ta ja hannunshi jikin mota ta sake cewa “please.” Tai maganar cikin jan ra’ayi.


Haka suka shiga a tare dadi ya kamata suka fito.


**********


  Sai yaushe zaka daina zuwa?


Kallanta yai yace “ungo.”


Ya mika mata leda, kallan ledar tai tace “menene?”


Kara mika mata yai, amsa tai ta bude, magungunan da Mama ke sha ne a ciki.


Kallansa tai tace “na meye?”


Yace “shekaranjiya naji Baba na cewa zai siyo, ki bashi wannan.”


Dan harararsa tai tace “waya saka?”


Murmushi yadanyi yace “shima laifi ne?”


Juyawa tai zata wuce.


Yace “Raziyya!”


Tsayawa tai a inda take sannan tadan juyo kadan, yace “dan Allah ki yafemin, yau zuwana na 12 kenan.”


Kallansa tai tace “na dauka a zuwanka na 5 na cema na yafema.”


Yace “naji wannan amma nasan baikai zuciya ba.”


Kallansa tai batace komai ba, murmushi yake yai yace “shikenan.”


Dan maganin dake leda ta daga tace “angode.”


Ta wuce, murmushi ya saki yabita da kallo harta shiga cikin gida.


Yana tafe a hanya mazan dake gabanshi yana ji suna gulmar Su Raziya, jikinshi ne ya sake yin sanyi dayaji dayan yace “ah dama ta ina namiji zai gama amfani da mace yace zai aureta?”


Dariya dayan yai yace “gatanan a jibge a gidan duk wadanda suka dana ba wanda ya kawo tayi.”


Ransa ne ya kara baci haka ya wucesu ya wuce gun aikinsa.


Babban shagon da yake zaman jira ya shiga, yana aiki yana tunani, murmushi yai ganin sakon Khalid dayace “In ka gama dawowa hankalinka ka min magana na fada mata.”


Reply yamai yace “Hankalin nawa bace wa yai?”


“Oh na dauka haka kacemin.”


“Haka kace?” Ya tura yana dariya yai sannan ya cigaba da aikinsa.


Sai shida ya taso a hanya ya tsaya yasai bread da kayan tea dan sachet sannan ya wuce gida.


Dan karamin dakin daya kama.


**********


Tana zaune a cikin dan kitchen din tana ta murza gyada, sai uban gumi takeyi tana yin mai.


Kafadarta ce ta shiga amsawa, ta saki wata uwar hamma sannan ta dan gutsiri gwaibar dake gefenta.


Hanne ce ta kalleta ta dan tabe baki dan tana kishin yanda Adam ya turo mata kudi ta fara sana’ar man gyadar nan.


Goggo ce ta gama ta fito tana mika, jaraba ta fada tare da daukan wayar.


Kin gama?


Na gama, wai Adam haka zaka sani a gaba kullum sai kaji abinda nai?


Kudina na baki kike aiki dashi ko kinsan wahalar danasha kafin na samesu?


Daukan hotunan na yau na gani.


Wata uban kwafa tai sannan ta dau hoton tace “in Umaru yazo ya turama.”


Yace “eh zan fadamai.”


Cikin takaici ta kashe wayarta, kwafa ta sakeyi gaba daya ta kasa gane kan Adam dan har tunani take Adam dinta ne wai?


Nace duba dai🤪


*****

Ayusher🏌🏻‍♀[1/21, 10:19 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


“It is not a lack of love, but a lack of friendship that makes unhappy marriages.”


{69}

Bayan Kwana biyu....


Lokacin lunch time dinsu ne yai, Khalid ya zaro wayarsa dake cikin dan safe din desk dinsa, murmushi yai akan sunan Zainab wanda a jikin alan wayar aka rubuta Babylove, wani sansanyan murmushi ya sake bayan wayar ta fara ringing, ganin harta katse bata dauka ba yasa ya ajiye wayar.


Sako ne ya shigo wayarsa, dauka yai ganin Nazifi ne yasa ya bude.


“Khalid in da hali zaka iya zuwa plx?”


Hankalinsa ne ya tashi dan ya tabbatar abin ya shafi Zainab, fitowa yai ya hau adaidaita sai dai gani yake kamar bata gudu saboda hankalinsa dake tashe.


Yana isa Station din nasu ya kira Nazifi, da sauri Nazifi ya fito ya sameshi, Khalid cikin tashin hankalin daya kasa boyuwa yace “Nazifi ya akai?”


Nazifi yace “in ba damuwa ko zaka shiga ciki?”


Me ya faru da ita?


Nazifi ya kalleshi yace “ita da directors da producers ne, ta sasu a meeting room tun safe ta koma office dinta ta zauna”


What?


Nazifi yadan girgiza kai kadan yace bansan me ya faru ba.


Cikin hanzari Khalid ya shiga ciki, office dinta ya wuce direct tana zaune tana ta aikinta sanye take da glass saboda yawan kallan screen yasa take sawa.


Secretary dinta na kokarin sanar da zuwansa Nazifi ya girgiza mata kai, Khalid na shiga ta kalleshi tace “waye?”


Yace oganta.


Oganta? Sai kuma tai dariya tace “ohhh na gane.”


Zainab ta dago zatai magana jin shiru bayan kuma an shigo.


Ganin Khalid yasa cikin mamaki ta zare glass dinta, murmushi ya sakar mata sannan ya nufi inda take.


Mikewa tai tace “Sweet me kake a.....”


Rungumetan dayai ne ya sata yin shiru a hankali ta dago tana kallansa, fuskarta yadan taba yace “ya isa haka nan, okay?”


Tace “me?”


“Na sani haryanzu kina jin haushinsu saboda abinda ya faru da ne, kin nuna musu matsayinki ya isa haka nan”


Kallansa tai tace “Allah saboda kai ne ban koresh ba duk ba abinda suka sani sai zaman kashe wando da gulma”


Yace “i know amma in kin duba manya ne su sannan  sunada iyalai, zaki iya korarsu amma a hankali sannan ki sanarda kowa 2years before saboda ya shirya.”


Fuska tadan hade tana kallansa tace “dan Allah ka dawo nan da aiki, canfa wahala kawai kake sha.”


Harararta yai yace “me suke a meeting room din?”


Tadan kauda kai tace “punishment na basu na aiki, dan nasan ko zasu kwana acan bazasu iya samo mafitarba.”


Ohhhhh ya fada yana hada goshinsu.


Murmushi tai tace “naji zan ce su barshi.”


Ummmm thanks.


Saketa yai yace “zan koma.”


Dan rikeshi tai tana dai jujuya kai, murmushi yai sannan ya sumbaceta ya juya ya fita.


Nazifi ta kira ta bashi izinin su barshi sannan tacemai ya shirya tana so ya rakata yin signing din contract da zasuyi da masu company na detergent.


Nan ya juya cikin jin dadi.


Tare suka fito driver dinta na gun aiki ne ya shiga motar Nazifi ya zauna a gaba ita kuma ta zauna a baya tana tambayarsa abu yana bata amsa har suka isa.


C.E.O din na jin isowarta ya kalli magidancin dake durkushe gabanshi yace “tashi ka fita dan Allah, bana san in samu matsala ta harkar business dina.”


Kabir ne ya kalleshi yace “ka taimaka ka fadawa abokinka ya dauken aiki a gidan Tv dinsa, inada experience sosai akan harkar.”


Zainab ganin haryanzu ba’a basu izini ba yasa ta watsama secretary dinsa kallo, nan ta juya ta kara shiga, daidai nan Kabir ya mike saboda jin yacemai ya tashi ya fita kafin yasa a koreshi.


Haka ya fito jiki a sanyaye, idanu suka hada, kallansa ta sakeyi sosai, tadan shafi saman kanta tana kara kallansa.


Da kyar yace “Zainab?”


Wani kallo tamai sannan ta mike ba tare da ta kulashi ba ta nufi hanyar ciki.


Bakinsa na rawa yace “Zainab?”


Kofar ta bude, CEO din ya taso da sauri yace “Hajiya barka da zuwa.”


Kallansu yai da sauri, Zainab ta kalleshi tana murmushi tace “Yallabai barka.”


Kabir na tsaye kamar hoto aka rufe kofar, kasa ko daga kafarsa yai sai da secretary din yace “in baka fita ba zan kira security.


Kabir haka yaja kafarsa dakyar yabar gun.


*******


Karfe Biyar da rabi Khalid ya dawo, tsayawa yai ya siyo ‘yan abubuwan bukata sannan ya karaso gida, ya san bata nan hakan yasa ya wuce kitchen ya ajiyesu, murmushi yai ganin kitchen din a gyare, yana fitowa ya wuce toilet yai wanka tare da alwala, yana fitowa tana turo kofar dakin.


Salama tai kamar mai shirin yin kuka, amsawa yai yana goge jikinsa da karamin towel yace “An dawo?”


Kusa dashi tazo tace “Allah kaina ciwo.” Tai maganar tana zama akan gado.


Kallanta yai sannan yace “kinsha Magani?”


Kai ta girgiza mai alamar a’a tana neman kwantar da kanta akan pillow, da sauri yasa hannu ya tare kan nata.


Kallansa tai tadan lumshe ido, maida ta yai ta zauna daidai yace “magrib ta kusa karki kwanta.”


Hannu tasa ta riko hannunshi tasa a kanta tace “kama min kaina.”


Stress ne ya miki yawa, kiyi kokarin rage aiki kina barin na kasa dake suna yin nasu aikin, amma komai kice sai kinyi da kanki ko sai kin duba da kanki abin zai miki yawa.


“Ka dawo gurina ka tayani in ka damu dani.”


Murmushi yai ya dau mai yana shafawa baice komai ba.


Kan kafadarsa ta kwantar da kanta tace “nima zanyi magana.”


Uhm ina ji.


Tace “Sweet please daga yanzu duk abinda nai karka dinga dauremin fuska kaki kalona ko kuma kaki kulani, please ka dinga fadamin.”


Dan juyowa yai hakan yasa fuskarsu tai daf da juna, dan kansa ya kwantar kadan saman kanta.


Tace “nima zaka iya daukan magana ta selfishness amma banasan zamanmu ya cigaba in nama abu ka dinga dauremin fuska ba tare da na sani ba, Allah baka san yanda nakeji bane.”


Kusa da kunnenta ya kai bakinsa yace “a ina kika samo point din?”


Dan dago da kanta tai saboda abinda ya dan ratsata, bugemai fuska tai hakan yasa yai dan kara kadan, da sauri ta mike tace “na bige ka sosai?”


Hancinsa ya rike yace “da saninki ko?”


Ni da kaina ke ciwo ina zan bugashi da sanina?


Da zafi? Ta tambaya tana dan neman zare hannunsa.


Ina budewa jini zaki gani.


Ido ta zaro tace “sosai ne?”


Hannunsa ya sake yana murmushi, harararsa tai sannan ta mike.


Hannunsa ya sakalo ta kugunta yasa kansa akan kasan bayanta cikin sanyin murya yace “dazu dan ban zo ba me kike shirin yi musu?”


Shiru tadanyi, yace “umm?”


Tace “sai sanda da tashi in basuyi abinda nake so ba, duk da manyane ai basusan aikinsu ba, tunda abinda nace suyi akan aikinsu ne kaga ba wai ramuwa nai ta hanyar da basuda mafita ba.”


Dan dagawa yai ya juyota saitinshi yace “ya isa haka nan kinji?”


Kallansa tai saboda yanda yai maganar ta sigar lalashi, tace “uhm na kyalesu amma in suka cigaba da yin abinda bai daceba zanyi replacing dinsu.”


Kai ya daga mata, tace “maganar dazu baka ban amsa ba.”


Tai maganar cikin dan salo.


Saketa yai ya mike ya dau farar vest dinsa yasa yace “shikenan.”


Tace “in ka sake min fa?”


Yace “in na sake zan ma kaina hukunci.”


Murmushi tai tace “ka bari ni nai hukunci.”


No ni zanyi da kaina.


Fadamin wani iri zakai?


Ummm ya ce tare da zura riga yace “kamar na hana kaina shan ruwa na awa uku?


Baki ta bude tace “shine hukuncin?”


Turare ya fesa sannan yace “da alama kanki ya daina ciwo.”


Tace “Allah yanayi kawai dai ba kamar da bane.”


“To kiyi alwala muyi sallah sai kisha magani.”


Kallansa tai sannan ta wuce toilet, shiru tai tana kara dubawa haryanzu fa ba abinda yazo, kwana 10 kenan, meke faruwa? Dan jiya ta duba taga stress ma nasa period yai late amma ai nata ya wuce 7 days.


Alwala tai ta fito sukai sallah, shiru tai akan sallaya taba tunani, ganin haka yace “akwai paracetamol a gidan?”


Kallansa tai tare da girgizamai kai alamar a’a.


Mikewa yai yace “bari na siyo.”


Shiru tai dan ba paracetamol take bukata ba test take san yi, ba kuma tasan ta fadamai karyasa rai akan abinda ba haka ba, ta ina ma zata samu ciki? Bayan shekararta 4 da Adam ko bari bata taba yi ba? Gwara da farko tasan tai planning amma daga baya tana so amma ba alamarshi.


Yana fita ta dau waya tana duba abinda ke sa period yaki zuwa har tsawon 10days, sai dai duk inda ta duba zancen test ne gaba in har negative ne to sai ta duba ragowar matsalolin.


Mikewa tai ta fito falo tadan zauna a kasa, ta jawo laptop dinta tana duba wasu report da za’ai program dinsu gobe.


Kofar da Khalid ya bude ne yasa ta kalleshi, mika mata ledar yai ta amsa ta mike tai kitchen, hadiyan maganin tai sannan ta dauko abincinsu ta fito.


Kallanta yai harta kawo ta ajiye yace “ke da bakida lafiya?”


Murmushi kawai tai batace komai ba, zubawa yai da kansa, yace “yaushe zaki dan share dakincan? Naga an kusa hutu su Nabila na zuwa.”


Kallansa tai tace “sai yanzu za’a budeshi?”


Dan kansa ya shafa yana dariya yace “ai saboda ke na rufeshi, haka kawai nasan in dashi shareni zakiyi ki koma daki daya kina aikinki.”


Ahhhh d’an Umman nan


Murmushi yai sannan yace “taho muci abinci.”


Harzatace bari na gama sai kuma ta fasa, mikewa tai ta matso ta zauna sukaci tare, yana shan ruwa tace “Sweet ko mu koma can gidan in sunzo hutu? Nan kamar zai dan matsemana, dan Asiya ma zatazo, nasan su Amir ma nasan zuwa.”


Kallanta yai yace “hardasu Amir?”


Tace “basu sukace ba nice dai naga hakan, tunda ga Nabila da Asiya nasan zasu kula dasu.”


Shiru yai yana dan nazari, tadan sa hannu kan cinyarsa tace “sati biyu ne in suka tafi sai mu dawo.”


Kallanta yai yace “Nusaiba fa?”


Shiru tadanyi tare da kallansa tana neman abin cewa.


Yace “naga tare suke zuwa.”


Cikin saurin magana dan karya gane tace “ita a dole sanka takeyi fushi take dani nasan ba zuwa zatai ba.”


Kallanta yai kawai ya sa dariya yace “sannu wannan maganar fa?”


Tace “wace?”


Murmushi yai yace “yarintace ke damunta in ta dawo ki hadani da ita a waya.”


Da sauri tace “me zakace mata?”


Dan gefen kunnensa ya sosa yace “yayanta zai mata fada?”


Aww ta fada tana dan jin kunyar kanta.


Har suka kwanta tana tunanin wannan lamari ko wani abun ne ya sameta? Bada menopause din data karanta yana hana period ba shine da ita ba? Ai bata girma ba batakai 50 ba, sai kuma tai ajiyar zuciya cikin damuwa, karfe biyar da rabi ta farka.


Tana tashi ta wuce kitchen miyarta ta duba ganin akwai ragowa yasa ta daura ruwa akan tukunya sannan ta fara wanke wanke, tana gamawa ta sa mai ta hau dan fere dankali.


Khalid dake kwance tun fitarta ya farka, mikewa yai ya gyara dakin tas sannan ya shiga toilet yai wanka tare da alwala, yana fitowa ta shigo dakin itama ta shiga wanka.


Cikin sauri tai wankan ta fito sannan ta sa kaya, falo ta fito inda ya dan gyara throw pillows din.


Tsintsiya ta dauko yana kallanta ta fara shara, cikin sauri ta gama, break dinsa ta kawo mai ta dau flask din tea dinta ta hada, tana fitowa daga kitchen ta kalli agoggo gani bakwai saura minti biyar yasa tai hanyar daki.


Khalid ne yace “Baby.”


Naam ta fada tare da kallansa.


Alama ya mata da hannu, hakan yasa ta nufoshi alama ya mata data zauna kusa dashi zama tai tana kallansa.


Fork dinsa yasa a gabanta yace “ci”


Cikin shakka tace “gishiri yayi yawa?”


Ci ya maimaita yana kallanta.


Tace “sorry ina sauri ne bansani ba.”


Kallanta yai ya kalli abincin, hakan yasa ta debo tai spoon daya, kallansa tai da sauri tace “ba abinda yai ko bakina ne?”


Yace “no ci, karki kara fita bakici abinci ba, wannan shan shayin ya isa haka nan.”


Wuyanta ta dan shafa sannan tadanci.


Yauma tare suka fito sai dai yau bai bita ba a titi ya sauka haka ta tafi zuciyarta duk ba dadi.


*******


Yau su Nabila aka dawo hutu zuciyar nan fal take da zumudin zata gun Aunty, dan sam wannan term din haka tayishi ba dadi saboda Nusaiba haryanzu a kule take da ita, da batada kawaye amma wannan term din sai datai friends dayawa.


Abin nasu ma sai ya koma gasa, in Nusaiba taga Nabila da kawaye biyu itama sai ta nemo nata kawayen biyu, haka sukai ta wannan shirmen har sukai hutu.


********


Zainab kam yau tun safe takejinta ba daidai ba, ga abubuwa sunsha kanta ta kasa ma samun nutsuwan zuwa gun likita, ga tsoron yin test takeyi saboda tasan ba ciki bane.


Dayake yau asabar tana kwance har karfe 11, Khalid ne ya shigo cikin dakin, ya zauna kusa da ita yace “lafiya kuwa?”


Kallansa tai tace “bakomai gaba daya karfine bandashi tun jiya.”


Mikar da ita zaune yai yace “muje asibiti?”


Kai tadan girgiza tace “ko mu bari sai gobe?”


A’a muje yau.


Shiru tai tana kallansa, kallanta yai shima yace “me kike tsoro?”


Shiru tai tana kallansa yanzun ma.


Are you that scared? Kar suce miki ciki ne?”


Kallansa tai da sauri tace “ya akai ka san abinda ke raina?”


Dan yake yai yace “tun yaushe ya kamata period dinki yazo baizo ba? Kusan 3-4weeks kenan taya bazan gane ba?”


Kanta ta sunkuyar, yace “bakyasan haihuwa?”


Kallansa tai da sauri, yace “kina dana sanin bakiyi planning ba abi yazo da haka?”


Hannunta ta fixge daga hannunsa tana kallanshi, yace “ba haka bane?”


Ranta a bace tace “wani zance kale yi haka?”


Yace “ke kike sani yin wadannan tunanukan, nasan shekarun da kukai da Adam na yadda bakyasan wani abu ya kawo miki cikas a aikinki, shiyasa ban ce miki komai ba haryanzu.”


Ido ta zubamai jitai hawaye ya gangaro mata, a kufule taja bargo ta koma ta kwanta.


Baby? Ya fada yana neman juyo da ita, ganin taki juyowa yasa ya dan rukufo kanta yace “meye hakan?”


Kallansa tai tace “taya zaka fadan kalaman nan?”


Yace “tunanin dayazomin kenan nake fada miki.”


Tace “ka san sau nawa nake fatan samun ciki? Kasan yanzu tsoron kar inje acemin ba shi bane shine ya hanani zuwa? Ka san yanda nake ji.......”


Muryarta ce ta sarke, dagota yai ya rungumeta yace “am sorry baby.”


Zare jikinta tai tana kallansa, yace “ya isa haka nan”


Tace “ran laraba dady yace zasuzo, in mun fita zuwa asibitin sai na kira Nusaiban.”


Kai ya daga alamar to, tace “zamu koma can din?”


Muje mu dawo tukun.


Kai ta daga alamar to tace “amma Allah naji haushi.”


Yace “na sani, sry”


Tana shiga toilet zuciyarta ta fara tashi saboda kamshin sabulun, jin amai ne yasa Khalid shiga toilet din da sauri, amai take sosai ga ba abincin a cikinta aman sai wahala yake bata.


Bayanta ya shiga dan bugawa har ta gama.


Kallansa tai idanunta sunyi jaa, ruwa ya mika mata ta kuskure baki, dagota yai suka fito yace muje asibitin in kin dawo kyayi wankan.


Kai ta daga mai alamar to sannan suka fito.


A hanya ta kira Nusaiba, har sai data kusa katsewa ta daga murya a dakile tace “Aunty.”


Khalid ya ce “Yaran makaranta an dawo?”


Da sauri ta mike tsaye tace “Uncle?”


Yace “yan makaranta an dawo lafiya?”


Tace “lafiya kalau.”


Yace “yaushe zakizo yayarki tana san ganinku.”


Shiru tadanyi hakan yasa yace “yanzun ma fushi tai nina lalabata taya kina kanwarta bazaki nemeta ba?”


Shiru tasake yi dan batasan me xatace ba, yace “in kinzo lalai sai kin ba yayarki hakuri dan ranta ya baci “


Cikin sakalci tace “nima ai Aunty bata neman ba.”


Inji wa yace miki? Bayan tunda kuma dawo take zumudin xakuxo?”


Tace “da gaske?”


Yace “ki shirya inkunxo kya bata hakuri kinsanta in tai fishi.”


Nusaiba tace “to Uncle zan bata xan hada kayana yau.”


Haka suka kara magana kadan kafin suyi sallama.


Zainab dake kwance a jikin kujera ya kalla, yace “sannu.”


Murmushi tai tace “Thanks da alama Nusaiba xatazo.


Kallanta yai yadanyi murmushi.

**********


Kallan Dr din ta sakeyi bayan anyi test tace “me kikace?”


Tace “Bakiyi test a gida bane?”


Shiru tadanyi kafin tace “Banyi ba.”


Murmushi tai tace “abu harya kau 2mnt ya akai bakiyi ba?”


Shiru Zainab tai, ta bata shawarwari kafin ta fito.


Khalid na ganin ta fito ya taho da sauri yace “ya akai?”

Kallanta yai yaga yanda duk tai wani iri, hanyar waje tai ya bita har suka isa gaban mota.


Budewa tai ta shiga, shiga yai shima yace “Baby?”


Hannunsa ta kamo takai saman cikinta tace “Sweet tace baby ce a ciki.”


Kallanta yai da sauri, idanunta ne suka ciciko tace “I never never.......”


Rungumeta yai hawaye ne suka zubo tace “ a duk sanda nai tunanin baby sai naga kamar na shiga hakkin wanda nake aure saboda bana haihuwa, ban taba yadda da gaske nima Allah zai dubeni ba.”


Tai maganar cikin rauni, shikanshi idanunsa sai da suka dan canza saboda abu biyu na jin dadi da tausayin ta.


Haka suka taho gida hannunta rike cikin nasa.


*******


*******

Ayusher 🏌🏻‍♀

[1/23, 2:26 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


Good luck and tons of best wishes. God bless you in whatever you do. This is my heartiest wish for all of you💖


{70}


Tun a hanya yasai katin waya suna isa gida ya baje a falo ya kira Abba ya sanar musu, dadi kuwa agun Abba da Umma abin ba'a cewa komai, sai da sukai sallama ya kira wayar Dady yana sanar dashi.


Zainab dake kwance kan gado ta saki baki tana kallan ikon Allah, daga cikin wayar tanaji yanda Dady ke nuna matukar farin cikinshi, sai hamdallah yake yana godewa Allah.


Yana kashewa zai kira Salmanu tace "me kakeyi?"


Ya kalleta, cikin mamaki tace "baka kunyar fada?"


Yace "kunyar me?"


Kai ta dan girgiza tace "maza sai a barku"


Kallanta yai yace "dame za'a barmu?"


Ta gyara kwanciyarta tace "bandaice ba kar ace nace."


Dan dariya yai yace "ai kin gama fada."


Idanu ta rufe saboda yanda zuciyarta ke tashi, mikewa tai a hankali yace "ina zaki?"


Komawa tai ta zauna akan kujerar ta kalleshi tace "zamuje can din?"


Shiru yai yana kallanta, hannu tasa akan kafadarsa hakan yasa ya sake kallanta.


Please ta fada cikin sanyi.


Uhmmm ya ce tare da daga kai alamar eh.


Cikin tsananin jin dadi tace "Thanks" tadan kwantar da kanta akan saman kansa.


Murmushi yai yadan shafi fuskarta yace "Dady jin kina da ciki yace gobe su Nabila zasuzo, kenan sai dai mu koma yau."


Gobe? Ta tambaya cikin jin dadi.


Kai ya daga mata, tace "to ko mu hada kaya inyaso zuwa dare sai mu koma?"

Kai ya daga mata alamar eh fuskarsa ta kasa daina murmushi.


*******


Zuwa dare suka koma can Zainab dai har dare ta kasa cin komai kamar wanda aka zigo abin dan gaba daya ta rasa mema ke birgeta, ga uban yunwa wanda ya sa gaba daya karfinta ya tafi.


Bayan sunyi isha'i ne ta zauna akan gado tana ta daura pillow a cinyarta ta daura laptop dinta akai tana duba abu sai dai dishi dishi take ganin rubutun saboda yunwar dake damunta.


Khalid daya fita siyo abubuwan bukata ne ya dawo wajen karfe 9, kitchen yakai sannan ya shigo dakin, kallanta yai yace "tashi muje ki duba wani abu kici."


Kallansa tai tace "Allah bansan cin komai jikina ma duk ba karfi."


Fuska ya dan daure yace "haka kikeso ki wahalar da Babyn tun yanzu?"


Baby? Ta tambaya tana kallansa, tace "wannan kuma fa?" Ta nuna kanta da yatsa.


Dariya yai yana dan sosa cikin kanshi yace "maman baby?"


Tace "maman baby?"


Yace "eh ai yanzu kuma kin girma da sunan."


Fuska ta daure sosai tace "na zama babba ko tsohuwa kake cewa?"


Yace "Hajiya dama ai ke babba ce."


Kai ta kauda tare da dan juya kai saboda yanda yunwa ke galabar da ita.


Ya dan zauna kusa da ita yace "Da kin haihu da wuri na tabbatar da baby na primary hala."


Primary? Yanzu dai cemin kake na zama tsohuwa kenan?


Dariyarsa ya guntse yace "karki damu nima na zama tsohu tunda na baki wata bakwai."


Haushi ne ya kamata tace "ba sai ka tuna min mata sunfi maza saurin girma ba." Tai maganar a kule tare da kauda kai.


Dariya ya danyi sannan ya mike ya sa hannu ya dagota, yace "muje."


Kallansa tai fuskarta haryanzu a daure suka je kitchen, yace "duba abu kici."


Bude fruit din daya siyo tai sannan ta kalleshi ayaba ta dauka sai dai tana barewa taji amai ya taho mata, da sauri ta ajiye tai toilet, a wahale ta gama gaba daya jikinta rawa yake saboda yunwa.


Dagowa tai dakyar ya kalleta sannan ya dan kamota yace "sannu."


Kan gado ta kwanta tana maida numfashi sama sama.


Jiki a sanyaye yace "ko zakisha tea?"


Murmushi tai tare da dan daga kai, abinda ke yawo akanta kuwa ya zatai ga jibi akwai aiki.


Tea ya hado mata ya kalleta yace "tashi kidan sha."


Mikewa tai dan ita kanta yunwar takeji, ta dan kurbi kadan, sai dai duk yanda take san tea yau kam sam ta kasa sha, dakyar tai kurba uku ta girgiza kai jin gaba daya yana neman dawowa, kwanciya tai hakan yasa ya kalleta, tare da gyara mata bargon.


*******


Su Nabila da Nusaiba karfe 2 na rana suka sauka, a lokacin Zainab ta samu tai wanka tana kwance akan gado, Khalid ya kira Umma ya fada mata Zainab ta kasa cin komai, nan Umma tace "kai matsalar ba abinda ka iya, tunda gobe Asiya zata zo zan hado mata su garin kunu ta taho dashi, ita in tana nan ta dinga yi mata."


To shikenan.


Abba ta kalla tana dariya tace "Khalid na ji da matar nan"

Abba ya kalleta yace "da bai ji da ita da ke zaki fara mita."


Dariya tai tace "ni me nacici in inada cikima?"


Kallanta yai yace "hajiyar farau farau."


Dariya tasa sosai tace "na dauka ka manta."


Maganar radio dinsa ya kara yana cewa "ina zan manta bayan an kusa maida mana gida gidan farau farau.


Dariya sukai a tare.


Asiya dake hada kaya a daki ne ta fito jin Umma na kiranta.


Umma ta kalleta tace "dan zo ki dubomin garin kunu naga yawanshi.


Asiya ta dauko mata ta duba sannan tace "dauko garin tuwo nagani."


Nan ta kona ta dauko, Umma nata harhada su guri daya.......


********


Suna saukowa daga cikin mota Nabila ta shiga da gudu tai ciki, Zainab dake kwance kan kujera tana jin shigowar mota ta dan mike zaune, Nabila ce ta bude kofa ta shigo da sauri ta rungumeta.


Zainab tana dariya tace "zaki karyani."


  Nabila ta dan saketa tana dariya tace "Aunty farinciki zai kasheni, Aunty zata haihu."


Tureta Zainab tai tace "wa kike jira ya shigo miki da kayan?"


Au tace sannan ta mike, fita tai taga Nusaiba a tsaya a kusa da akwatunansu tana zabga mata harara.


"Maida wukar Malama na dawo"


Nusaiba tace "karma ki dawo kema kinsan bazan dauki ko tsinkenki ba."


Zuwa tai ta ja nata akwatin da jakar hannunta tace "na sani."


Ciki sukai Mamman na musu dariya, suna shiga falo Nusaiba ta tsaya a jikin kofa tana kallan Zainab.


Zainab ta guntse fuska tana daga zaune tadan jingina saboda batada karfi ko kadan.


Nusaiba ta kalla ta mata alama da hannu akan tazo, a hankali ta tako zuwa inda take ta zauna tana kallanta cikin jin kunya.


Zainab ta jawota ta rungumeta, wanda hakan yasa Nusaiba sa kuka tana cewa "Aunty kiyi hakuri."


Zainab tai murmushi ta dagota tace "ya isa haka nan"


Nabila ta sa dariya tacs "ansha sakalci Auta."


Auta? Nusaiba ta kalleta ranga a bace.


Nabila ta mata gwalo, a kufule Nusaiba takalli Zainab cikin alamar kuka tace "Aunty kinganta ko?"


Murmushi Zainab tai da kyar tace "Nabila ki shiga hankalinki dani wlh."


Nusaiba ta mata gwalo itama.


Khalid ne wanda ya fita sallah ya shigo, Bala na sake gaisheshi.

Ganin Maman a harabar gidan yasa ya karasa da sauri ya mika mai hannu.


Maman ya mikamai shima suka gaisa, cikin jin dadi suka dan hira yana tambayarshi jikin Dady, yace da sauki abin ne dai ba dadi amma Alhamdulila.


Sun dan taba hira kafin Khalid ya shiga ciki.


Ganin ba kowa a falo yasa ya kalli Zainab dake kwance.


Kallansa tai tana murmushi tace "suna sallah."


Kai ya daga alamar to sannan ya zauna kusa da ita yace "yanzu fa? Kin dan sha yoghurt din?"


Nasha dan na kusa shanye robar ma.


Cikin jin dadi yace "good, yanzu kina san cin wani abin?"


Tace "in Nabila ta idar zata dafamin taliya."


Kallanta yai yace "sorry mijinki bai iya komai ba."


Zatai magana wayarta tai kara.


Dauka tai ganin number Basma, mamaki bayyane a fuskarta dan duk da suna da number juna ba waya suke ba.


Kallansa tai kafin ta dauki wayar hakan yasa ya kalli alan wayar.


MATAR GIDA abinda ya gani a jikin wayar kenan, wanda bai san sanda ya kalleta ba.


Dauka tai tare da sawa a kunnenta a hankali tace "Uhm."


Basma tace "Zainab ya jiki?"


Da sauki


Su Nabila sun iso?

Eh

Shiru suka danyi kafin tace "Naji shirmen da Nusaiba tai na mata fada kiyi hakuri, yarintace ke damunta.


Na sani.


Shiru suka sakeyi, tace "Jikin naki sosai ne?"


No


Jin dai wayar taki yiwuwa tace "shikenan Allah ya kara sauki, a gaida mai gidan."


Okay kawai tace ta kashe wayar.


Basma tai murmushi tare da kallan Dady, tace "at least ta daga."


Yace "kin taba kiranta ne?"


Kai ta girgiza alamar "a'a."


Yace "bani ruwa nasha."

Mikewa tai.


*****


Acan gidan Khalid kuwa.


Khalid ne ya kalleta, tasan magana zai mata hakan yasa ta koma ta kwanta akan kujera, yace "meye matar gida?"


Tace "matar gidan dady."

Dan dariya yai yana girgiza kai yace "matar dady dai matsayin uwa take a gunki, balle kun hada jini da 'yarta."


Uwa? Ta maimaita aranta batace komai ba.


Yace "ki canza mata suna ko maman Nusaiba kika sa yafi matar gida, yanzu in Nusaiban ta gani zataji dadi?"


Shiru tai tana kallanshi yace "bazai yiwu ba?"


Kwanciya ta sakeyi tace "bance ba."


Murmushi yai yace "thanks."


Yasa hannunsa akan saman kanta.


fitowarsu Nabila daga daki ne yasa ya kallesu yai saurin sauke hannunsa, fuskarsa dauke da murmushi yadan matsa daga kusa da ita.


Gaisheshi sukai ya amsa Nusaiba sai kasa take dakai.


Nabila yunwa nakeji ta kalli Khalid ce tace "Sweet kaima yunwa kakeji, me zakaci?"


Kallanta yai yace "daga isowarsu kar a sasu aiki dayawa suyi taliyar kawai gaba daya."


tadanyi yaji? Ta tambaya tana kallansa.


Murmushi yai yana kallanta sannan ya daga kai.


Mikewa sukai suka shiga kitchen.


Nabila ce ta kalli Nusaiba tace "Nusaiba mareni in mafarki nakeyi."


Nusaiba tace "mafarki?"


Nabila tace "da gaske Aunty ce a zaune a falan can?"


Nusaiba tasa dariya tace "na dauka ni kadaice nai mamakin abinda na gani."


Oh ni Aunty ce take magana ba yanda ta saba ba? Sannan abinci ma sai ta tambayeshi?


Dariya sukai Nabila tace "Sweet kaima yunwa kake ji me zaka ci?"


Dariya sukai a tare kafin su sa abincin.


Suna gamawa Nabila ta fito tace "Aunty an gama."


Zainab tace "okay bari nazo."


Mamaki ya kara kama ta dan tasan da dane hankalinta a kwance zatace Nabila zubomin.


Mikewa tai ta shiga kitchen ta dau na flask din ta hada ta dau tire din tai daki.


Nusaiba da Nabila suka saki baki suna kallan ikon Allah.


Ajiyewa tai ya mike da sauri yace "ke da baki da lafiya me kikeyi hakan?"


Dan jikinshi tasa kanta tace "kanshin abincin ke damuna tun ana dafawa."


Yace "ki dan daure in kikaci kadan kila kamshin zai tafi."


Dakyar ta iya cin loma hudu duk yanda taso ci kasa wa tai.


Ya kalleta yace "kin sanar dasu gobe bazaki samu zuwa ba?"


Kai ta girgiza tace "zanje"


Wani kallo ya mata yace "a hakan?"


Tace "eh ai zama zanyi ba yawo ba."


Ban yaddaba ba inda zaki cikin yanayin nan.


Hankalinta a tashe ta kalleshi tace "wani yanayi?"


Kallanta yai yanda take toshe hanci ya kalli abincin, ido ta zaro da sauri ta sauke hannunta tana neman sake ci, sai dai kamshin sam ya hanata.


Mikewa tai idanunta sun yi rau rau tace "Allah zan iya."


Kallanta yai yace "wai ina zaki a haka?"


Shiru tai jin kamshin na hawa kanta yasa ta bar dakin da sauri.


********


Tun a falo tai bacci tana kwance suna Nabila na kallo har bacci yai gaba da ita.


Ganin goma tayi bata shigo ba yasa ya fito falo ganinta a kwance tana bacci yasa ya kalli su Nabila yace "yaushe tai bacci?"


Nusaiba tace "tun 9"


Karasowa yai, tabata yadanyi sau dai bacci take sosai ga baccin dama a wahale tayishi saboda yunwa.


Kallansu hai sannan ya daure kawai  ya dauketa yai ciki da ita, Nabila da Nusaiba suka saki baki har ya rufo kofar.

Kwantar da ita yai ya zuba mata ido yana kallan yanda fuskarta tai fayau duk ta fada kwana biyu kacal? Haka abin yake?


******


Alarm dinta ne yai kara 5:30am sam ta manta bata canza ba, mikewa tai ta zauna tare da haska fitilar wayarta.


Khalid tadan haska wanda ke bacci ta dan haska dakin kafin ta fara kokarin saukowa daga kan gadan.


Jitai an rike hannunta.


Kallan Khalid tai yace "bafa zaki aiki a haka ba."


Tace "Sweet Allah in naje zanfi warewa ma."


A'a in naga kin ware sosai gobe kyaje.


Inada meeting 11 bazanyi zirga zirgaba sannan daga naji abin yamin yawa zan dawo gida.


Kallanta yai sannan ya saki hannunta tare da gyara kwanciyarsa.


Komawa tai ta kwanta tana kallan saitinsa tace "kaji?"


Yace "me kikeso nace kuma?"


Tace "naji zan dawo bayan azahar, kaji?"


Kallanta yai kamar zai hanata sai kuma yai tunanin kila ta fi warewa in ta fita dan rungumeta yace "Thanks."


Kwanciyarta tadan gyara kadan tai tace "Sweet na fara tsoron harkar nan, ban dauka abin haka yake ba."


Yace "insha Allahu komai zaiyi sauki."


Murmushi tai kafi ta mike.


Wanka tai dakyar ta fito sannan ya shiga.


Duk abinda takeyi idanunsa na kanta, haka ta shirya tace "break fa?"


Yace "tea da bread kawai zansha." Tasan saboda ya rage mata aiki ne, sannan yana san ganin ko tana da karfin yin aikin.


Dan ya yarda ta warke din yasa ta daure ta ware sosai tai kitchen ta hado mai, amsa yai yana sha yana kallanta.


Sai daya gama yace "kefa?"


Gudun magana yasa tadan sa bread a bakinta, yace "haka zakici?"


Tace "kaima kasha da ruwa ai farkon auranmu."


Murmhshi yai haka tadan ci kadan tai sa'a bataji ya dawo mata sannan lafiya kalau tadanci.


Sai data gama sannan suka fito tare.


Duk yanda baisan shiga motar yaukam bai isa ba saboda yanayin jikinta.


Sauketa yai ya kalleta yace "zanzo na maidake lokacin lunch."


Kai ta daga sannan ta fito, harta shiga yana kallanta kafin ya juya.


********


Zuwan Asiya ba karamin taimaka wa yai ba dan ta iya abubuwan gargajiya wanda hakan yasa Zainab ta samu kwanciyar hankali take cin abinci.


Shakuwa sosai ce ta shiga tsakanin yan matan uku, duk da su biyun sun fiya magana ba kamar Asiya ba wacce magana bata dameta ba sai dai tunda ta hadu dasu ta kasa daina dariya, sosai fadansu ke birgeta ga suyi ta sata cikin fadan kowa nasan ta tare mai.


Khalid na zaune yna waya da Salmanu yace "ba dai cemin zakai ba saboda ni ka kira wayar nan ba?"


Salmanu yai dariya yace "nifa bansan fassara dan kawai nace ya kanwarmu?"


Yace "kadai san bazaka aikeni na kai mata wayar ba ko?"


Dariya Salmanu yai yace "wannan yaya akwai tsauri an hanata waya ance sai ta gama secondary yanzu ka kai mata wayar ma kace bazakai ba?"


Dariya Khalid yai yace "in dai taimaka ma."


Zainab dake kwance yana murmushi, falo ya fito yace "Asiya."


Asiya dake kitchen ta fito da sauri waya ya mika mata ya koma ciki.


Mamaki ne ya kamata ta sa a kunnenta.


Salmanu yace "kanwarmu ashe kin gudu ba sallama."


Nabila ce ta kara kunnenta a jikin wayar Nusaiba ma ta matso hakan yasa Asiya kunya ta shige daki da gudu.


*****

Sosai wannan hutun ya musu dadi Khalid da Zainab sunji dadin zuwansu dan gidan yayi albarka anji dadin zumuncin nan dan ma Zainab nata fama ga Khalid ya sa mata doka 2 take dawowa dole, sai dai hakan ba karamin taimaka mata yake ba saboda tana samu ta huta sosai.


Haka har lafiyarta ta karu, hutu kuma ya kare, dan ma jarabawa zasuyi in suka koma shine karshen term dinsu.


Ganin wahalar da takesha yasa Khalid ya biyama Asiya kudin Waec da Neco a private anan skul din dake kasan layinsu ta dawo nan, kafin ta fita takeyin komai wanda hakan ya sa hankalin Dady kwanciya yai tama Khalid godiya.


********


Mahaifin Xoxo da Allah yamai Rasuwa Allah ya jikansa da Rahama, ragowar musulmai da suka rasu Allah ya jikansu👏🏻


*****

Ayusher🏌🏻‍♀

[1/23, 2:26 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

     .........................


   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


#OneLove❣


{71}


Rayuwa ta ratsa yau da dadi gobe babu a haka cikin Zainab yakai wata takwas wanda daga lokacin dole ta hakura da fita aiki sai dai tai a gida ta tura, da kanta ta sanar da Khalid akan yama Salmanu magana ta samar mai aiki a gun aikinta, shikam cikin murna ya amince da hakan.


Dady kam zumudin jika ya sa kusan kullum sai ya kira, daga kano kuwa Aunty duk bayan sati daya zuwa biyu sai tazo ganinta.


Saboda kammala makarantar dasu Nabila sukai Dady ya turota amma ita kadai saboda yana ganin ba dadi a dinga sa Khalid barin gidanshi saboda su, inyaso in Nabila ta dawo sai itama taje, dayake Asiya ta koma tunda jikin Zainab yai sauki sannan kuma ta kammala jarabawarta.


Nabila sosai take kula da Zainab, a koda yaushe mamakin halayen yayarta takeyi gaba daya yanzu ta canza tun balle akan mijinta a koda yaushe cikin maganarshi take abin na ba Nabila dariya, in ta shiga daki ta kira Nusaiba tana mata gulma, bata damu da saurayi ba sai dai ganin yanda Auntynta ke canza yasa ta fara tunani kula samarin dake santa.


*******


Adam ne ya kalli Raziya dake neman komawa ciki yace "tafiya zakiyi?"


Tace "me zan ma to?"


Murmushi yadanyi yace "magana zamuyi."


Kallansa tai tace "bana san jin shirmenka."


Dan dariya yai yace "Maganar ki ce da abokina Kamal na miki maganarshi kwanaki."


Wani banzan kallo tamai tace "nacema neman kai nake da kaina?"


Bakicemin ba amma haka zaki cigaba da zama?


Kai haka zaka cigaba da zama?


Dariya yai yace "haka nace miki?"


Dan kai ta karkartara tace "kaje kai naka auran ka bar damuwa da auran wadanda bakada alaka dasu."


Ta nufi kofa jitai yace "Raziyya."


Yanda ya kirata ne yasa jikinta yai sanyi, juyowa tai ta kalleshi yace "laifin danama Fiddausi za'a ban dama na wankeshi?"


Kallansa tai yace "me kike tunani game dani?"


Kai? Ta tambaya tana kallansa.


Yace "eh ki amince dani."


Idanu ta zaro tana kallansa, tace "ni?"


Kai ya daga, da sauri ta shige cikin gida tana maimaita maganar sa.


Sau biyu yana dawowa kafin ta amince dashi dan Baba ya amince.


Sai da akasa rana sannan ya ma Khalid magana ya fadawa Zainab ta sanarwa Dady, Khalid yaji dadi sosai jin zai auri Raziya.


Adam kam rayuwa ta canza shi duk da ba babban aiki bane amma a kalla yana iya kula dasu, har dan mashin dinsa ya siya.


Goggo kam taso dawowa birni amma Adam ya hanata yace ta zauna acan ta cigaba da sana'ar man gyada sai dai yana bata kudi iya kokarinsa, haka nan ta hakura wani sa'in in taji yara sun dawo daga gidan kallo sai taji kamar tai ihu ta shiga cikinsu suje tare.


Amma tsoron zagin da za'a mata a kauye yasa dole ta hakura, sai kokarin bada labarin fina finan data kalla a gidan Zainab.


Abin mamaki ma da sam bata manta su ba, dayawa suna kanta in ta fara labari kai kace ita ta tsara ma masu shiryawan.


*********


Sai cika take tana batsewa a cikin daki, Ayaan dake kwance a kan gado ta kalla yanata baccinsa, agoggo ta kalla sannan ta mike ta fito daga dakin.


Nusaiba dake zaune wace tazo da suna tana zaune a kasan carpet tana ya kallan hotunan suna tana ta murmushi ita kadai, ganin yanda Mumynta suka tsaya tare da Zainab aka musu hoto duk da Zainab ta dan kaude kai saboda bata san yi amma itakam dadin hoton.


Zama tai kusa da ita tana kallo itama.


Kallan Nusaiba tai tace "Nusaiba zama haka ba dadi ko?"


Tace "ba dai kamar da Nabila ba amma ai ina dan shiga makota."


Shiru Zainab tai kafin tace "in an barmiki Ayaan zaki iya zama dashi?"


Zaki wani gun ne?


Aiki na, sam aiki a gidan nan hankalina bai kwanciya.


Dariya Nusaiba tai tace "Ya Khalid zai barki?"


Shiru tadanyi sannan ta mike tai kitchen, tsumi tasha sannan ta dan dama na sha da madara.


Daki ta shiga ta bude wardrobe ta dauko riga wata yar karama ta saka, ta dameta sosai tasa skirts three quarter.


Tayi kyau sosai, turaren farar humra ta dauko ta shafa a jikinta, murmushi tai saboda tare da fatan yin sa'a a abinda take shirin nema.


Karfe biyar da rabi ya dawo, yar karamar mota toyota daya siya ya shigo da ita sannan ya shiga ciki.


Nusaiba na kitchen tana abincin dare hakan yasa ba kowa a falan, sai kuka Ayaan dayaji.


Da sauri yai daki, tana zaune tana bashi mama.


Maida kofar yai ya rufe yana murmushi, kallansa tai tace "sannu da zuwa."


Hanayensa ya harde yace "na dauka kina aiki bakiji kukanshi ba." Ya karasa kusa da ita tare da kallan Ayaan.


Murmushi yai sannan ya karbeshi, mikewa tai ta karbeshi, kallanta yai cikin rada tace "bari in kaima Nusaiba shi."


Kaya ya fara cirewa ita kuma ta fito dashi.


Nusaiba ta goyama a baya sannan ta koma daki, zanin data daura saman skirt dinta ta zare.


Kallanta yai yana zaune akan gado da vest da karamin wando yana san shiga wanka, karasowa tai kusa dashi yace "Are you trying to seduce me?"


"eh" tace tare da zama kusa dashi, murmushi yai yace "ahhhh." Ya fada yana kara kallan ta daga sama har kasa.


"Meye na fada tunda ka sani?"


Ohhh sry na janye.


Yai maganar yana jawota jikinsa, dan hannunta ta kwace alamar dan karamun fushi.


Jawota yai yana dariya yace "a ina kika iya fushi haka?"


A gunka?


Dariya yai yace "ni?"


Tace "eh malamin hade rai." Tunawa tai da abinda tazo yi hakan yasa ta dan kwanta a jikinshi.


Dagowa tai ta sa hannu saman fuskarsa tana dan taba labansa a hankali.


Jawota yai sosai ta fado kanshi baya yai wanda hakan yasa ta fada samansa a hankali ta sa bakinta cikin nashi...........


  Kwanciya tai akan kirjinsa tace "Sweet me kake gani in na koma aiki nextweek?"


Murmushi yai dan yana ganinta jikinsa ya bashi abinda take so.


Yace "yanzu ke zaki iya fita aiki ki bar Ayaan?"


Tace "ba dadewa zan dingayi ba, in naje 10am zan dawo 2pm."


Zaki iya?


Ta kalleshi da sauri tace "eh."


Fuska ya daure tare dacewa "ni me kika fi so ne a rayuwarki?"


Kallansa tai tace "so kake nace kai?"


Laifine in naso hakan?


Murmushi tai tana cewa "in kuma nace aikina fa?"


Wani kallo ya mata dariyarta ta guntse tace "ni Sweet kishi kake da aikina?"


Mikewa ya shiga neman yi ta danne shi tana dariya tace "wasa nake, kaima kasan nafisanku kai da Ayaan ai wancan na saba ne ga hankalina ya kasa kwanciya gani nake kamar zasu lalata min komai in bana kusa."


Kai ya daga alamar gamsuwa yace "hakan yayi"


Tace "zaka dawo can muyi aikin tare?"


Murmushi yai yace " Maman Baby magrib zatai"


Dagashi tai yana shirin mikewa tace "Sweet ka kaini toilet please."


Kallanta yai yana dariya yace "in kira Ayaan ya kaiki babanshi bashida karfi."


Haushi ne ya kamata taja pillow din dake gefenta ta cilomai, cafewa yai sannan ya cila mata, makuwa yai akan fuskarta hakan yasa tai kara tare da rike gefen idanta.


Idona.


Hankalin Khalid ne ya tashi ya matsa kusa da ita yace "idanki?"


Mikewa zaune tai tana shishitun jin zafi, muga?

Ya fada yana neman zare hannunta.


Dariya ta kwashe mai dashi tare da zare hannunta.


Wow yaushe kika fara fooling dina?


Dan harshenta ta fito dashi kadan tace "yanzu? Dazu? I can't tell."


Mikewa yai kawai yana murmushi ya shiga toilet.


*******


Ayaan ne yake ta kuka da daddare mikewa tai tana jijigashi, in ta kalli Khalid na bacci sai taji kamar ta tasheshi, wai komai na yaro ita zatai? Falo ta fito tana jijigashi


(Nace Hajiya Baby maman Baby haka abin yake🥴)


Haka taita jijigashi harya koma bacci komawa daki tai, dan ido ya bude kadan yace "Ayaan ne?"


Eh tace sannan ta kwantar dashi, kwanciya tai bacci ya dauketa.


Tana sallar asuba ta shiga kitchen, dankali ta fere tana yi tana hamma, tana soyawa tana kare wanke ragowar kwanukan da tai amfani dasu.


Falo ta fito ta ajiye tana tunanin yanda zatai in Nusaiba ta tafi tunda skul ake nemar musu da zaran sun samu zasu bar nan.


Tana shiga dakin taga Ayaan a hannun Khalid da alama ya tashi.


Zama tai kusa dashi tana sake yin hamma kallanta yai yace "jiya bakiyi bacci sosai bane?"


Tace "Ayaan ne yai ta farkawa, kai kuma kana kwance kanata bacci."


"Sorry nadaiji shi kamar cikin bacci."


"Ahhh maza kuna samun sauki mu haihu sannan kula da yaro duk mune."


Haccin Ayaan yadan taba yace "ai shiyasa aka kiraku Uwa aka kiraku mata."


Mikewa yai yana shiryawa, yana gamawa ya fito falo ta biyoshi dauke da Ayaan a kafadarta tace "In na dawo daga gun aiki Aunty zata dan zo."


Kice baki za'ai akwai abinda kike bukata?


Tace "in akwai zan aiki Nusaiba kasan layi."


Wallet dinsa ya zaro ya ciro 1000 ya ajiye kusa da ita.


Kallan kudin tai kamar tace ya barshi sai dai tasan ransa ne zai baci amma itakam gaba daya ta rasa me zatai gata da kudi ga yanzu kudinta sai karuwa suke amma sam bata isa yin wani abu na gida ba, sai dai kamar kayanta na sawa tana siyo lokaci lokaci duk shima yana siyo mata, hakan yasa tai shawara da Khalid ta fara kai sadaka masallatai da gidan marayu.


**********


Rayuwa ta ratsa, yau da gobe sai Allah, yanzu shekarar Zainab da Khalid biyar da aure, a wannan lokacin abubuwa da yawa sun canza.


Ciki harda auran Asiya da Salmanu da akai shekaru uku da suka wuce, auren Adam da Raziya suma a shekara ukun da ta wuce da yanzu Raziya harda tsohon cikinta.


Adam kam Alhamdulila an dage ko dayake dole ma ya dage dan Raziya bata mai da sauki sam, daga taga yana neman biya abokai zaman majalisa zata tsawatar mai hakan yasa tun yana yi lokaci lokaci yanzu ya daina.


Kallan Adam tai yauma bayan ya dawo daga gun aiki tana mai kallon tuhuma, dariya yai yace "Allah ba inda na tsaya."


Hannunsa ta rike tace "ba cewa nai ka tsaya ba."


Zama yai a dan falan nasu ya dan daga labulen dakin ganin dan karamin dakin dake waje kusa da kitchen a bude, kallansa tai tace "Goggo!"


Tadan kwala mata kira.


Goggo ce ta fito daga dakin, kallansa tai tace "Adam an dawo?"


Ciki mamaki ya kalli Raziyya.


Murmushi tamai tace "kaga na kusa haihuwa ba babba a gidan shiyasa na kirata a waya"


Goggo ya kalla wace duk girma ya kara hawanta, yace "Allah yasa ba sa tv a gaba zakiyi kina kallo har ta haihu a bandaki ba?"


Dariya Goggo tai zatai magana Raziyya tace "ai tana ma daki nan ba koda yaushe zata dinga shigowa ba."


Yawon bakinta Goggo ta hadiya tace "Uhmm"


Raziya ta sake kallo wannan kam sai na lalabata in ba so nake na koma kauye ba.


*******


Karfe biyar saura ta mike ta wuce kitchen tasa abinci, dawowa tai toilet din falo tai wanka sannan ta shiga dakinsu Ayaan da Ayra ta daga Ayaan dake baci ta shiga dashi toilet ta mai wanka sannan ta fito ta tashi Ayra.


Tana fitowa ta wuce dakinsu, Khalid ke shafa musu mai yana sama Ayaan kaya lokacin.


Ayra ta ajiye ta fito kitchen.


Ayra yar shekara biyu ce ta kalli dake shafa mata mai tana zilewa.


Khalid yana dariya yace "Ayra tsaya lokaci na tafiya."


Ayaan ta kalleshi cikin yanayin shagwaba tace "School nake so nima."


Ayaan ne ya mata gwalo yace "ke yarinyace gidan Aunty zaki sai kin kara girma."


Haushi ya kamata, Zainab ce ta dawo dakin ta kalli Ayaan tace "a wuce a ci abinci"


Ayra tasa kuka tace "nima Mumy school nake so."


Naji aje aci abinci.


Fita tai a bakin madubi tana shafa mai tace "Na tambayi school din Ayra jiya sunce zata fara next term."


Necktie dinsa yake sawa yace "shikenan Allah ya kaimu."


Tace "in kawo abincin nan?"


Yace "a'a gama mu fita."


Kallansa tai sannan tadan sumbaci kumcinsa tace "yaushe raban da mu gana?"


Yace "bansan haka abin yake in da yara ba, gaki kullum kin gaji baccin wuri rannan da na tasheku tsakar dare haka kika wuni kina hamma."


Ajiyar zuciya tai tace "mu dinga sasu bacci da wuri?"


Murmushi yai yace "Kin kawo shawara."


Dariya tai ta gama sa kaya suka fito falo.


Khalid ne ya fara cin abincinsa itakam dan dankalin kadan taci tasha tea.


Mikewa tai ta koma daki ta sharo, tana fitowa falo suna gama cin abincin.


Ummy na a wuce asa takalmi.


Ayra tace to.


Fitowa sukai suka Ayra ta shiga motar Zainab shikuma Ayaan ya shiga motar Khalid suka fito daga gidan.


Gidan Asiya tai parking, tana kwankwasawa Asiya ta fito sanye da hijab, Ayra ta tafi da gudu ta rungumeta.


Zainab tace "Asiya sai na dawo."


To Aunty.


Ayra ta kallantace "baki tambayeni kawarki ba?"


Ayra tana dariya cikin maganar suka shiga ciki.


Zainab na isa office dinta Ramlatu ta shigo dauke da uban takardu, ajiyewa tai a gabanta tace "Hajiya ga su na duduba."


Kallansu tai tace "good yanzu, ina Nazifi yake da Salmanu? Su duba gun exams din yanda baza'a samu matsala ba"


Tace "okay na sanarma securities din suma.


Kai ta jinjina tace "well done."


Sakone y shigo wayara.


Zainab dan Allah ki dubi girman Allah d'ana zaizo yin jarabawa karki duba abinda na miki ki koreshi, dan Allah, wallahi rayuwa ta juya mana dakyar na samu ya gama karatu.


Kabir


Kallan Ramlatu tai bayan ta kira number tace "ki samar dashi nafi karfin na hukunta wani saboda laifin mahaifinsa."


Ramlatu ta amsa jin muryar Kabir ta sanar dashi, ya shiga godiya.


Ajiye wayar tai sannan ta juya.


Zainab ta kalleta dan sosai Ramlatu ta shiga hankalinta taba aikinta mahimmaci da rayuwarta.

*******


Khalid na isa makarantar ya riko hannun Ayaan yaji ance "Khalid?"


Juyowa yai Afreey ce ta karaso tace "ikon Allah ashe kai din ne."


Afreey ce ta dan karaso tana kallan Ayaan wanda ke tsananin kama da Khalid.


Murmushi tama yaran, Khalid ya kalleta yace "Safiya."


Tace "ban taba tunanin zan ganka ba."


Murmushi yai yace "Ayaan a wuce ciki, ya fada yana duba agoggon hannunsa, ganin bakwai da ashirin yasa yace "Wani kika kawo?"


Tace "eh yarinyata."


Masha Allah, Allah ya rayata.


Ya fada tare da bude mota.


Kallansa tai tace "aiki?"


Eh.


Murmushi tai tace "Allah ya taimaka yace Ameen."


Mota ya shiga ta kalli motarshi sannan ta shiga katuwar motarta ta bar gun.


Yana fitowa lokacin lunch ya kira Dady ganin missed call.


Basma ce ta dauka bayan sun gaisa tace "Khalid jikin nashi me yadan tashi dama shine zan fadama."


Inalilahi sosai ne?


Tace "a'a kawai dai in da hali dan Allah da weekend kuzo kila inyaga su Ayaan yadan ware."


Ok insha Allah

******


Alhamdulila


Godiya mai tarin yawa gareku masoyana da masoyan wannan littafi, hakkika ima godiya kwarai ga dumbin kaunar da kuka nuna mai.


Nagode kwarai da gaske🤝


Godiya ta musamman gareku masoyana na wattpad masu bin wannan novel🤝


Yan

The Queen Bee

Haske Writer's

Zauren Biebie

Ayusher Fan Club

A Gidana Novel

A Gidana Fans

Masarautar BillynAbdul

Kundin Haske

Zauren Khadeeja Candy

Huguma Conversation Centre

Unity Girls (Sauyi 🥰)


Nagode kwarai ga duk wanda yabi novel din nan da wanda na sani da wanda ban sani.


I wish i can write those names whom always make a long comment on each page🤕na sani kun sani ina godiya kwarai da gaske🤝


Kuskuren da ke ciki Allah ya yafe mana wanda muka fada dai dai Allah ya bamu ladansa


Much Love 💕


*****

Ayusher🏌🏻‍♀

*******

*****

No comments