Tabarmar Kashi book 2 page 72

 "HUGUMA*



•TABARMAR KASHI_*



Book 02 Page 72



Awa daya da wasu mintuna daya daga cikin nurses din dake labour room din suka fito.


"Hajiya d'iyarku ta sauka, amma bazan fadi abinda aka samu ba sai an bani goron albishir" ta fada tana murmushi


Caaa sukayo mata,har abun ya bata dariya yadda taga suna zumudi. Tun kafin maji taji abinda aka samu ta balle jakarta ta fidda rafas na 'yan 100 sabbi kar ta migawa nurse din


"Sauka lafiyar ma da kikace tayi ya wadatar,ga goron albishir dinki" fuskarta ce ta fadada sosai da fara'a tana juya kudin,kafin ta sake cewa komai afifa ta bude tata iakar ta ciro 'van dari biyar biyar ta damqa mata

"Kun samu 'yan samari mazaje" nurse din tayi saurin fada tana rige kudin cikin farincikin tagomashin da ta samu a yau din.


Baaba ramatu ce ta rangada guda cikin tsantsar farinciki


"'Ma sha Allah,alhamdulillah" ta rufe da fadin hakan.

Cikin ganganin lokaci gurin ya kaure da hayaniyar farinciki. Sai sannan aka fara cigiyar toufeeq. Murmushi.Sajjad ya saki


"Oga fa inajin yana masallaci, bari na duboshi" ya fadi yana miqewa ya fice daga gurin.


Sanda sajjad din ya shigo yana zaman tahiya na garshe. Ya zauna daga gefansa har ya sallame, cikin fargaba ya waiwayo yana dubansa, amma murmushin da ya gani saman fuskar sajjad din ya sassauta tsoronsa


"'Yallabai anata qiyamullaili ko? sai kazo to ta babies sun iso”

"Really?" Ya fada yana fidda ido


"Ahaf, kai dai ka tanadi goron albishir dina" ya fada yana migewa. Ai kafin sajjad yakai bakin qofa har ya riskeshi ya ma wuceshi.


Cikin wata irin sassarfa yake takawa,wani farinciki da karsashi suna ratsashi. Duka basu a veranda din, sai hayaniyar su da yake jiyowa daga dakin hutu.


A nurse ya bude gofar dakin, tashin farko idanunsa suka sauka kan fuskarta. Tana zaune sosai abinta saman gadon tana kurbar tea me zafi da kauri, sam ba zakace itace tasha wannan gwagwarmayar ba. Wani irin sassanyan farinciki ne yake ratsa kowacce gaba ta jikinta, tun daga ainihin zuciyarta har zuwa kan fuskarta.

A sace take kallon yaran, tana tasbihu ga ubangijin da ya maidata vara biyun data barar bayan ya maida mata su sai ya sauya musu da nagartaccen uba na gwarai,wanda zasuyi alfahari da fitowa ta tsatsonsa. Komai na duniya idan ubangiji yayi akwai hikima a ciki, haka siddan baya hukunta komai ba tare da dalili ba. A sannan taji babu dadi matuga game da rasa cikinta har taji kamar duk duniya ita daya ke cikin qunci da takurar zuciya,ashe duka ubangiji ya hukunta hakan ne saboda tanadin sauyi mafi alkhairin da yayi mata.

Qamshinsa shine ya fara janye hankalinta,duk da jama'ar dake dakin amma hakan bai hanata shanshano shi ba. Daga kai tayi, idanunsu suka gauraya da na juna,sai ya lumshe mata nasa idanun yana sakar mata wani tattausan murmushi gami da hada hannunsa yay! mata jiniina. Kai ta sunkuyar tana jin nauyinsa data tuna abinda ya faru awannin dazu,sai shima ya kau da kan nashi ya fara takowa cikin dakin bakinsa dauke da sallama.


Hankali kuma sai yayo kansa,kowa yana qoqarin masa barka yana amshewa yau dai duk yadda yakai ga turbune fuska lafiyayyen murmushin nan nasa yaqi boyuwa,a haka har ya qarasa gaban gadonta.


Kuiera nadeeya ta bashi, sai ya jawota gaban gadon ya dora gafarsa kawai akai, fili yake da bugata su bashi,saboda kyakkyawar runguma ce yake gain tafi dacewa da ita. Idanunsa cikin nata yana jin kamar zasu narke su zama abu guda. Cikin hikimar manya maji da baaba ramatu suka mige zasu fice, abinda ya sanya nadeeya fadeela anty farheen da anty samreen suma bin bayansu. Afifa ce dake cikin babban mayafi tana baiwa baby nono ita da sajjad basu fita din ba. A gefansu nadeeya ta jere yaran tana cewa


"Maji din ta fita ai, saiki sake ki qare wa kayanki kallo antyN" ta fadi cikin dariyar tokana tana yin gofa da sauri gudun kada toufeeq din yakai masga.


Hannunsa ya mige ya rige tafin hannunta cikin nashi yana ci gaba da yi mata wannan tattausan kallon


"Yanzu Madam kishi kadai dama ya isa tayar da naquda har a haihu?" Ya fadi cikin salon tsokana kadan. Kai ta langabe tana kallonsa tana kuma satar kallon afifa,ta tabbatar idan afifa taji ta shiga uku da tsokana.


Murmushi ya sake mata yana kanne mata ido d'aya.


"Idan nace sannunki Allah yayi miki albarka batayi kadan ba?" Kai ta gyada cikin murmushi tana kallonsa itama


"Ida nace na gode qwarai, Allah ya sanya mahaifanki cikin aljanna madaukakiya shima baiyi kadan ba?" Nan ma kai ta jinjina tana murmushi zuciyarta cike fal da mahaukaciyar soyayyarsa,sai ta motsa bakinta a hankali itama


"Dukkan wadannan kalmomi naka masu tarin tsada da daraja ne"


"Kamar vadda kike da tsada da darajar da bansan

adadinta ba a idanuna, bude idanunki mu kalli tsarabar

da kika kawomin a tare" ya fadi yana miga hannunsa

cikin takatsantsan da kulawa ya soma bude fuskokin

varan

"Yes!, ma sha Allah, Allah banyi wahalar banza ba" ya fadi

kansa tsaye yana ma mantawa dasu sajjad dake dakin.

Da sauri saahar ta rufe bakinta saboda kunya,sai sajjad

din ya tattara towel din ahlam yana cewa

"Oya let's go, muje ki garasa bata ko cikin mota ne" ai da

gudun tsiya afifan ta rungume diyarta suna ficewa kada

ayi barin zance a gabanta

"Ai da kunyi zamanku" toufeeq ya fadiwa sajjad cikin

gatse sai sajjad din ya gyalgyale da dariya baiko waiwayo

ba

"Bestienkin nan da sajjad original 'yan sanya ido ne" yayi

maganar sanda ya Sanya hannu yana gogarin daukar

babyn ya zauna a gurin

"Ko yaushe gana fadi min muna basu mamaki, basu taba

tsammanin soyayya zatayi mana mummunan kamu har

haka ba"


"Sai gashi tayi mana kamu me kyau harda result" ya furta yana sake bude fuskar dayan baby din, suna nannade cikin wasu lausasan shawl farare gal masu ratsin blue a jiki


Har wani lumshe ido yakeyi sanda yake kallon fuskar varan


"Na yarda ni din jarumi ne, duka vara na ahalina suke daukowa,kiyi haquri ina miki fatan nasara a gaba" kukan shagwaba ta sakar masa, sai ya saki dariya sosai kaman ba MUHAMMAD TAUFEEQ JARMA ba


"Eh, next time ina expecting baby girls twins, zan tayaki addu'ar samun masu kama dake, don nima ina kwadayin* nayita kallon kyakkyawar fuskar nan ta cika kowacce kusurwa ta gida na" sai ya sunkuya a tausashe yayi

U kissing dinsu su duka sannan ya juya kunnuwansu yayi musu khuduba “Muhammad da Mahmud" ya fadi yana kallonta. Farinciki ne sosar ya ratsata, tabbas taji dadin wannan zabin nasa,dama tun asali sunaye ne masu asali


"Allah ya raya dr girema da dr jarma" ta furta a hankali Ameen,let me hug you please ko zan samu sassaucin abinda nakeli na farinciki a zuciyata" ba musu ta bude masa hannayenta,yayi mata kyakkyawar runguma yana sauke ajiyar zuciya idanunsa akan yaran.


Awanni shida kacal aka rubuta mata sallama cikin aminci da goshin lafiya. Tunda yaji maji na zancan tafiya da ita ta kula da ita ya kasa ya tsare. Koda aka rubuta sallamar sai daya kwashesu ya kaisu motarsa sannan ya gaya musu batun sallamar, kafin maji ta ankara tuni motarsa ta dauki hanyar gidansa, don ko kadan bazai iva jumurin rashinsu a kusa ba. Yanzunne yakejin kansa a cikakken magidanci,wanda ya hada dukkan wata falala da farinciki na rayuwa.


Hakanan maji ta gama salatinta ta haqura


"Muhammad ya maidani kakarsa Allah da gaske" haka tayiya mita tana fada. Nadeeya na gefe tana dariya


"Maji, shifa yaa moha har yanzun farin shiga ne,sai yanzu yasan meye dadin family ki bar masa matarsa da yaransa"


"Allah baiko isa ba, dole na gyara diyata, idan yaso su garata,amma dai yara shima yasan bashi kadai ke dasu ba"


"Ah lallai maji akwai kallo kenan,nan gaba kwashesu zakiyi"


"Zasu haifa wasu in sha Allah" ta fadi, don har ga Allah a son ranta ma su koma gidanta da zama.


Wani irin alheri albarka da farinjini yaran sukazo dashi,yadda gidan yake cika kullum saika dauka suna akeyi kullum. Saahar sai yanzu ta sake amanna da gasken gaske 'ya'ya rahama ne,da gaske haihuwa wata falala da baiwa ce daga ubangiji,wani irin budi da alkhairi ita kanta take gani tako ina. Gadan gadan ake shirya I katafaren suna, duk wani taro na biki da basuyi ba toufeeg ya shirya fansheshi a ranar sunan,ya tsara walima ta musamman shi da abokansa, haka bangaren mata da zasuyi nasu cikin yalwatacciyar harabar gidan.


Zafafabiyar

No comments