Furar Danko Book 02 Page 25

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗





           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣5️⃣




.......Sai kawai ya miƙe zuwa jikin window ya ƙurama waje idanu yana kallon shuke-shuken fruits da ganyayyakinsu ke sake ƙawata ƙamshin wajen. Da ƙyar ya iya samu ya dai-daita kansa a wajen har Ummita ta shigo ɗauke da zam-zam mai haɗe da zuma a ɗan wani kofi da ƙaramin spoon. Tana ajiyewa bata zauna ba ta fice. Nannauyar ajiyar zuciya ya sake sauke a karo na babu adadi da takowa ya dawo gaban gadon, komawa yay ya zauna a inda ya tashi tare da amsar yaron data janye a jikinta tana gyara riga. Amsarshi yayi yana goge masa baki, ita kuma sai ta miƙe masa ɗan cup ɗin. Cikin ɗan tura baki a ranta tana faɗin (Kaima ka ɗan ɗana wahalar da nake ci a kansa)

      A mamakinta babu musu ya amsa. Kamar kuma dama can wanda ya saba da rainon cikin nutsuwarsa ya ɗibo ruwan zam-zam ɗin mai haɗe da zuma ya zubama yaron a baki kaɗan sai gashi yana ɗan motsa bakin da yamutsa fuska. Hakkanne ya saka Smart sakin murmushi har ya ɗago ya kalli Lulu da itama dai kallon nasu take yi. Kauda idanun nata tai ta maida kan bowl ɗin namanta ta fara ci. Cikin ɗage gira ya ce, “Wannan dai ƙwaɗayinki ne ya gado Madam”.

      Da sauri ta ce, “Wa ɗin? ALLAH ya sawwaka mi muka haɗa da shi da zai gado ni, haɗuwa a duniya rabuwa a cikinta”. Sosai maganar tata ta bashi dariya, amma sai baiyi ba yay murmushi kaɗan yana girgiza kansa. Ganin yasha sosai ya goge masa baki ya gyara masa kwanciya a ɗan gadonsa. Lulu ya kama tana kallonsu, amma yana juyowa ta kauda kanta gefe. Kusa da ita ya koma ya zauna gaf, batare da yayi magana ba ya amshi tsinken da take cin naman ya tsira shima ya kai bakinsa, sake tsiro wani ya kai mata baki, idanunta ta zuba masa batare data buɗe bakin ba, shima kallon nata yake a yanayin kasala, dan haka ya ɗan lumshe nasa idanun da kaɗa mata kansa alamar ta amsa. Kamar mai jin ciwo akan lips ɗin ta motsa su da ƙyar shi kuma ya saka mata naman. A kusan tare suka sauke nannauyar ajiyar zuciya su duka. Da ga haka ya cigaba da bata yana ci, sun ci kamar lauma uku a bazata ya jeho mata tambayar da ta sakata ɗan daburcewa, amma jarumar taku sai ta dake abinta.

       “Mi yasa kika zaɓi yin rainon cikin nan ke kaɗai batare da ni ba?”.

      Cikin basarwar nan tata da son dakewa batare data kallesa ba ta ce, “Miye haɗina da kai da zamuyi rainon ciki tare?”.

              “Mai ciki da abunsa har ace miye haɗinsa da cikin. Serious banji daɗin haka ba Mawaddat. Naso ace Ni ne da kaina na kula da ke tamkar ƙwai a cokali a wannan gaɓar. Ban taɓa fuskantar minene ainahin ƙunci ba sai da na waiga babu ke a duniyata, nasan har yanzu zuciyarki na baki na aikata miki abinda ya faru a wancan ranar bisa son zuciya. Ko kaɗan ba haka bane, dan ina son kasancewa da ke basai na baki komai ba ai, domin ke ɗin halalina ce, mizai sa saina wahalar da kaina ta hanyar gusar miki da hankali kamar wani matsoraci. Kin taɓa ganin Aliyu Hydar a matsayin KURE ba ZAKI ba?”. Harararsa tai, sai dai ta kasa cewa komai, shima sai ya ɗan murmusa kaɗan da cigaba da bata naman yana faɗin, “Duk abinda ya faru a wannan ranar Ahmad ne ya ƙullasa bada sani na ba, sai dai karki damu zan rama miki ai kinji ƴar ƙanwata”.

        Cikin suɓutar baki da harararsa akan ƙanwarsa daya kirata tana waro idanu ta ce, “Ahmad fa? Taya zan yarda hakane?. Sannan akan Maryam ɗin? Zaka rama?” 

    “To mata tafi mata ne? Shi ya jawo mata ai. Duk da dai ni ya biyani tunda ban wahala a banza ba ga AA Mawashi na a kusa da ni”. Karan farko tai kamar zata saki murmushi sai kuma ta hararesa ta ɗan taɓe baki da faɗin, “Sai ka shirya amsa hakan a gaban alƙali ai. Dan sai an bimin kadin hakkina na fyaɗe”.

           “Shima alƙalin koroki zaiyi da ga gabansa ai. Nidai yanzu nace magana ta wuce kawai, Aima Abbien AA afuwa bazai sake yin fyaɗe ba”.

       “Humm” ta faɗa tana mai lumshe idanunta. Shima sai ya zuba mata nasa kawai yana kallonta cike da shauƙi. Cikin motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Ke ƙyaƙyƙyawa ce Mawaddatan'warahmah”.

     Da sauri ta buɗe idanun nata a daburce, dan yanda ya furta kalmar sai taji kamar ya haɗa da jinin jikinta ne ya zuƙe har ma da numfashi, kafin ta samu damar cewa komai Usman yay sallama. Amsa masa yay yana mai dafe goshinsa da faɗin, “Gaskiya baka iya zuwa ba”. 

       Ƙaramar dariya Lulu tai tana kauda kai, shi kuma ya harareta da bashi izinin shigowa bayan ya miƙa mata mayafin da ke ajiye gefenta da faɗin, “ALLAH yasa ma ba haka kike zama min a gabansa ba yana kallemin kayana”. Yanda yay maganar cikin ɓata fuska ya sakata sake sakin murmushi, cike da neman tunzurashi ta ce, “Mi kuma ya rage bayan shine mai karɓar haih....”

       “Mtsoww! Shut up!”. 

     Ya faɗa a hasale yana balla mata harara fuska a gimtse. Dai-dai nan Usman ɗin ya ƙarasa shigowa, sama-sama ya bashi hannu suka gaisa, kafin ya ɗan juya yama Lulu tambayoyi game da yanayin jikinta. Ta tabbatar masa da Alhmdllh bata jin komai. Shima hamdalar yay yana ɗan duban Smart da murmushi, “Oga zamu iya wucewa masauki ko anan zaka kwana ka taya Madam jego? Dan itama lokacin barcinta yayi”.

       “Kaga dana ɓarke ɗinkin sai ku tara min jama'arku na likitoci kenan”. Smart ya bashi amsa da ɗan barkwanci duk da da gaske maganar Lulu ta sosa masa zuciya amma ya danne.

     Ƙaramar dariya Usman yay da faɗin, “Ai kai oga ne zamu ɗaga maka ƙafa kodan Son ɗina AA”.

      Murmushi Smart ya sake yi kawai bai ce komai ba. Usman kuma ya matsa ga Lulu ya mata allura da duk sauran abinda ya dace sukai mata sallama, gaba Usman yay ya barsa. Ganin yanda Smart ɗin ya raka bayansa da kallo mai kama da harara  yasa Lulu saurin faɗin, “Nifa wasa nake maka kada ka ƙullacin bawan ALLAH bayan ƙoƙarin sa a kammu. Kana dai ganin a yanda yay min allura ma cike da taka tsantsan”.

      Ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da ɗan lumshe idanunsa da launinsu har ya canja. Batare da yace mata komai ba a karo na biyu ya ƙarasa gareta ya rungumeta tsam-tsam a jikinsa ta yanda dai bai taɓa mata ciwo ba. Su dukansu babu wanda bai sauke ajiyar zuciya ba, yayinda Smart ya shiga laluben lips nata. Da sauri ta janye jikinta saboda jiyo takun tahowa, shima sai ya miƙe dan dai-dai nan Ammah tai sallama. Gaban gadon Babyn ya koma tare da kama hannayensa ya fara tofa masa addu'oi. Har saida ya kammala sannan ya ɗago yana kallon Ammah da ke taimakawa Lulu ta kwanta yanda zataji daɗi. Sun ƙara haɗa ido da Lulun ta kauda kai shima ya kauda da ɗan salon taɓe baki yana wani lumshe idanunsa.....



       *_NIGERIA_*


     Sosai jikin Dada ya ruɗe a safiyar yau dan haka hankalin ƴaƴanta a tashe yake matuƙa. Cikin ƙanƙanin lokaci aka shirya mata barin ƙasar. Baba Garko na Abuja a lokacin Uncle Khamil ya kira shi a ruɗe yana sanar masa zai tafi Kano jikin Dada ya tashi sosai. Duk da ya ji damuwa a ransa sai ya danne cikin nuna halin ko'in kula ya ce, “ALLAH ya bata lafiya” ya kashe wayar abinsa. Abinda Baban yay ya sake tada hankalin yaran. Dan sun sake tabbatar da har yanzu ransa a ɓace yake akan mahaifiyar tasu. Haka suka shirya wasu a cikinsu suka wuce da ita gwiwa a sage. Wanda aka bari a gida kuma suka bita da addu'a kafin suma subi bayansu da ga baya. Matansu kam addu'a suke ALLAH yasa da ga can ta wuce ko zasu huta da samun sukunin zama da mazajensu cikin ƴanci kamar kowacce mace a gidan aurenta. Dan gaskiya surukar tasu ta musu kane-kane a cikin rayuwar aurarrakin nasu....


        (To mudai munce ALLAH ya baki lafiya Dadansy).


       __________★


    Duk da zuciyarta a dagule take da wannan tafiya ta mijinta da kishiyarta da tafi tsana fiye da kowa a rayuwarta ta wani fannin hakan ya taimaketa, dan ta samu damar aiwatar da mugayen nufinta akan wanda suke wa taƙamar da tinƙaho. Saboda tayi alƙawarin kofa komanta zai ƙare ita sai taga bayan Smart da uwarsa. A haka ma dan bata san ainahin abinda ya kaisu UK ɗin ba kenan. Hankalin aunty amarya ya tashi da ganin kai-kawon da Umma ke yi, dan haka kawai zuciyarta ke ayyana mata kai-kawon bana banza bane ba. Su dukansu sun jima suna zargin Umma akan shige-shigen gidajen malamai. Dan a wasu lokutan sukan kasa gane kan mijin nasu ta koma sai ita kaɗai ce madubin dubawarsa. Sai sun dage da addu'a abin yay sauƙi kafin ta sake masa sabon aike. Wannan dalilin yasa a yanzu ɗin ma Aunty Amarya ta shiga damuwa. Sai dai ta rasa dawa zatayi maganar dan Mama ita ba gane kanta ake ba wasu lokutan sai a hankali ce. Ga shi su Maryam basa nan. Ganin abin nata cigaba da alamomi masu yawa ta ɗaga waya tai kiran aunty Bilkisu akan tazo dan ALLAH idan ta samu lokaci. Da sauri Aunty Bilkisu ta tabbatar mata da gatanan zuwa. 

          Da yamma ko sai gata, sai dai ta nuna kamar daga wani waje take ta biyo gaishesu. Sama-sama Mama da Umma suka amsa mata gaisuwarta, dan suna cike da takaici da kishin tafiyar Abba da Ammah. Aunty Bilkisu bata nuna ta damu ba ta shiga ɗakin aunty Amarya abinta. Tsakanin aunty Bilkisu da aunty Amarya suna abune kamar ƙawaye, duk da aunty Bilkisun ta girmeta kaɗan, bayan sun gaisa babu ɓata lokaci suka shiga tattauna abinda ya tara su. Sosai hankalin Aunty Bilkisu ya tashi da bayanin aunty Amarya, duk sai ta rikice. Cikin kwantar da hankali aunty amarya ta ce, “Bilkisu dan ALLAH karki ruɗa kanki, mu nutsu muyi tunanin abinda ya dace, dan kinga dai bawai tabbas garemu ba zargi ne”.

        “Aunty wannan ai ya wuce zargi tunda har kinji tana ambatar sunan Hydar ɗin da matarsa. Wlhy nikam al'amarin Umma ya fara bani tsoro a gidan nan. Ko kin san kwanan nan sai da taje ta kaima kishiyata gulmar Ammah da har ta kaimu da yin faɗa. Alhaji ne ya tausheni da kar nazo gida na faɗa kamar zaimin kuka. Kuma ya tabbatar min da ai ta daɗe tana kai musu gwabsona dana Ammah kawai dai yanzu ne ALLAH ya tona asirinta. Akan wannan rigimar yanzu haka uwargidana na gidansu ya mata saki ɗaya”.

            “Innalillahi. Itako Umman Hannatu mi take son zama ne? Wlhy al'amarin ta na bani mamaki”.

      “Dolene abinta yake bada mamaki ai Aunty, ki duba fa yanda ta tada hankalinta a gidan nan tunda taji Hydar na ƙasar waje. Ni wlhy zuciyata ma har ta fara zarginta akan matsalar da yayta samun nan a baya. Kawai dai dan Ammah tace kar nayi magana ne”.

          “Eh ai tabakin Yayar gara a barta, ita da kanta halinta zai tsangwameta kowa ya shaida. Amma yanzu idan akaji a bakin wani a cikinmu za'a ɗauka sharrin kishi ne kawai. Kin san kuma Yaya ita komai nata a nutse ne bata son gaggawa. Shiyyasa yanzu ma kikaga na nemoki dan kota dawo bana son na fara mata maganar, duk da nasan zata fahimce ni”.

       “Hakane Aunty, yanzu to yaya zamuyi?”.

      “Addu'a zamu dage da ita, mu kuma saka a cigaba dama Aliyu shima har sanda su Yaya zasu dawo miji nata shawaran”.

    Aunty Bilkisu ta gamsu da shawaran aunty Amaryan, dan haka suka cigaba da tattaunawa. Bata bar gidan ba sai bayan sallar magrib........✍️


      _Network kaje dan kanka. Na barka da ƙarfen da ake maƙalaka ehe🥱🥱🚴_.




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments