Furar Danko Book 02 Page 23

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗





           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣3️⃣




.........*_CANADA_*


       Kwanaki Uku kenan da mata cs ɗin, amma Alhamdullah da alamun fara samun lafiya tattare da ita kasancewar bata da ƙan jiki, sai dai kuma Lulu akwai raki. Mahaifiyar Usman da yake kira da Mamy tazo tana tare da su tun shekaran jiya. Hakan yasa take sake ƙara samun kulawa ita da jinjirinta. Ga Ummita na iya ƙoƙarinta itama tako wane fanni. Hakama Usman da Dr Lameer. Tayi mamaki matuƙa da ganin ɗunbin kayan baby da Mamy ta kawoma Aliyu ƙarami. Sai dai yanda matar ke kulawa da su cikin haba-haba ya sa Lulu kasa cewa komai akan hakan. Duk da wannan gata da kulawar da take samu wajen abokan arziƙi zuciyarta a cinkushe take da rashin ahalinta ko guda ɗaya a kusa da ita. Hatta shi kansa uban tafiyar yakan zo mata a rai, duk da a duk sanda yazo ɗin takan yamutse fuskar cikin nuna halin ko'in kula. Sai dai hakan babu alamar zai turesa a ran nata, dan data dubi ɗan jaririn nata zuciyarta kan harba mata, balle kuma idan tana shayar da shi takan zuba masa idanu da tafiya cikin tunani mai zurfin gaske akan al'amarin mahaifinsa. Kasancewar Mamy babbar mace ta jima da hango halin da Lulun ke a ciki, amma bata cewa komai saboda lokacin cewar bai isa ba...


      A ranar da su Lulu ke cika kwanaki biyar da zuwan baƙon duniya su Abba da Daddy suka iso ƙasar Canada, tafiyar da tai masifar tada hankalin su Ummah dan Abba yace musu zasuje duba Smart ne zuwa ƙasar England. Jidali iya jidali rasar su Aunty Amarya sun gani wajen Ummah, dan su Asma'u ma basa gidan Ammah catai su tafi gidan yayunsu har sai sun dawo su dawo. Dan haka suka tafi gidan Aunty Bilkisu da shirin idan suka mata kwana biyu sai su koma gidan Hawwah itama su mata kwana biyu. Babu irin zagin da Ammah bata sha ba ranar har maƙwafta sai da suka shigo, inda mutane da yawa suka fara fassara al'amarin Umman da hassada. Dan sukam basu ga wani abin tada jijiyar wuya a nan ɗin ba...


     Oho su Ammah ma basu san tana yi ba, dan suna can a hanya hankalinsu kwance. Ƙasar England su Abba suka fara yada zango wajen Smart. Wanda zuwan nasu yazo masa a bazata sosai, dan sam Uncle Yousuf bai sanar masa ba. Tsabar farin ciki baima san lokacin da ya rungume Ammah ba. Turesa tai cikin jin nauyi da faɗin, “Kajimin ja'irin yaro abinda ka koya a ƙasar turawan kenan kuma?”. Cikin dariya da shagwaɓa Smart ya ce, “Ammah nafayi missing ɗinki ne, ALLAH sai nake ganin kamar mafarki nakeyi”. Tsinguli ta kai masa da faɗin, “Bari na tabbatar maka idonka biyu”. 

     “Ouch!” ya faɗa cikin turɓune fuska yana kallon Abba a marairaice. Abba ya riƙo masa hannu yana hararar Ammah. Daddy da Uncle Yousuf dai dariya sukeyi, dan basu taɓa zaton Aliyun taɓararre bane a wajen iyayen nasa sai yau. Smart ya gaishe da Daddy cikin girmamawa, Uncle Yousuf kam ai baida maraba da aboki duk da yanzu ana ƴar kunyar surukuta kaɗan-kaɗan. Sosai mazaunin Smart ɗin ya ƙayatar da su Ammah, suka shiga godiya ga UBANGIJI a zukatansu da mamakin wannan rahama ta UBANGIJI. Sunci sun sha daga abincin da Smart ya tanada musu a cikin ƙanƙanin lokaci, dan abinci ne na ƴan Nigeria. Bayan kowa yaci ya ƙoshi suka ɗan tattauna, sosai zaman ya sanyaya ran Smart, inda ya fahimci surukinsa sosai a yanzu ya kuma sakko daga fushin daya tafi. Sun tafi zuwa masauki aka bar masa Ammah da Abbah nan. Hakan ya musu daɗi su duka, dan sun sami damar tattauna abinda ya shafesu sosai shi da iyayen nasa. Inda ya ƙara warware musu cigaban da ya samu da wanda yake fatan samu anan gaba. Ƴan uwansa kaf bai manta da kowa ba sai da ya tambaya, har maƙwafta da abokan arziƙi. Ranar dai ansha hira, dan duk rashin yawan maganar Ammah da Smart yau dai sun sha hira abinsu kamar suyita kasancewa a haka suke ji...


       Washe gari da yamma suka wuce Canada har da Smart dake jin wani irin faɗuwar gaba lokaci-lokaci, yakanyi sauri ya ambaci sunan ALLAH. Wannan ziyara tazo ma Lulu a bazatar bazata. Dan bata san wainar da ake toyawa ba sai kawai ganin Usman tai da baƙi. Lokacin da suka shigo tana toilet ne ita da Mamy dake gasa mata jikinta da towel kamar dai yanda ake cikakken wankan jego a Nigeria duk da Lulu tasha maganin da ya dace Mamy bata barta ba kullum sai ta mata safe da yamma ita da ɗan jinjiri. 

        A hankali take tafiya Mamy biye da ita, tayi fayau da ita sai haske data ƙara da wani cikar ido irin na jego dan tana samun kulawa sosai irin ta malam bahaushe a wajen Mammy duk da cs akai mata. Alhamdullah kumburin ciki da tai duk ya saɓe amma baza'a kirata ramammiya ba kai tsaye. Sanye take cikin doguwar riga mara nauyi dake a buɗe sosai saboda yanayin inda aka yanka ta. Baya tai zata faɗi saboda firgicin ganin abinda idanunta suka gane mata, sai da Mamy ta riƙota tana faɗin, “Mawaddat yi a hankali kinji”. Daga lips ɗin Lulu har zuwa jikinta rawa yake yi, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo tun daga kan Daddynta har zuwa mutum na ƙarshe da ke tsaye ya ɗan jingina abango da harɗe ƙafafunsa waje guda. Sanye yake cikin Suit milk da sukai masifar masa ƙyau da fitar da cikar haiba da kamalar da ya ƙara, ga wani irin ƙamshi mai sanyi da daɗin shaƙa, gaba ɗaya ya canja da ga Smart na Nigeria zuwa wani baƙin bature mai aji a yanzu. Yanda yay tsaiwar ƙasaita da harɗe ƙafafunsa waje guda idanunsa a waya yana daƙila kamar baya a wajen saika rantse ba shine ke zumuɗin azo ba fiye da kowa. Sai da Mamy ta ambaci sunan Lulu ne ya ɗan ɗago idanun nasa a hankali da take kira na macizai kamar zai lumshesu sai kuma ya zuba mata su cikin shammata da bazata. 

       Wani irin girgiza zuciyarta tayi ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri. Rashin mafita ya sata juyawa cikin tsumar jiki ta basu baya tana mai rumtse idanunta da masifar ƙarfi. Ammah ce ta taka a hankali zuwa gareta, cikin tausayawa da ƙauna ta kira sunanta. Kasa juyowa Lulu tayi sai jikinta da ke ƙara ƙarfin rawa. Riƙo hannunta Ammah tayi ta juyo da ita a hankali, sai kaiwa ta faɗa jikin Ammahn ta rungumeta tsam-tsam tare da sakin kuka mai tsuma zuciya.         

         A hankali Smart ya sauke idanun nasa ƙasa yana wani irin haɗiyar zuciya da sauri-sauri. Dai-dai nan Ummita ta shigo ɗakin da sallama bayanta goye da baƙon duniya dake barci. Turus tai tana kallonsu itama cikin tsoro da mamaki, yayinda su kuma suka zubama jinjirin bayanta ido. Uncle Yousuf ne yay ƙarfin halin mata nunin ta kunto yaron. Sai ta kalli Mamy. Kai Mamy ta jinjina mata alamar ta kuntosa babu matsala, dan haka ta ɗan saki ajiyar zuciya tare da kunto yaron ta miƙama Uncle Yousuf ɗin. Kamar ko ya sani sai ga idanu ya ɗan buɗe yana motsa baki alamar neman abinci. Dariya Uncle Yousuf ya saki da faɗin, “Oh oh Aliyu dai kawai ne anan babu wani banbanci wlhy sai na shekaru”. Yay maganar yana ƙarasawa gaban Abba da Daddy cikin sassarfa. A hankali Smart da idanunsa ke kan yaron ko ƙyaftawa babu tun shigowar Ummita ya wani lumshe idanun da suka kaɗa a hankali yana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Jin al'amarin yake kamar a mafarki, shi Aliyu Hydar ne da ɗa na mutum matsayin mallakinsa a wannan duniyar. Ya arrahaman ALLAH mai alkairi. Furucin Lulu da ke faɗin, Ammah nayi kewarku cikin kuka ya sashi buɗe idanun nasa ya zuba musu su. Murmushi Ammah da ke sharema Lulu hawaye takeyi, kafin ta kama hannunta ta ƙarasa da ita a saman gadon da take jiyyar. Dai-dai nan Abbah ya ƙarasa da Jinjirin ga Smart, nannauyar ajiyar zuciya Smart ya ja tare da fesarwa, sai yaji ma duk ya sake daburcewa. Fahimtar hakan da Abbah yay ne ya sashi sakin ƙaramar dariya da sake miƙa masa yaron. A hankali ya miƙa hannayensa duk biyu Abba ya saka masa yaron a ciki, sai da yay masa kallon kusan sakanni goma kafin ya matsar dashi saman ƙirjinsa ya rungume tsam-tsam dai ga hawaye sharrrr. Uncle Yousuf dake murmushi ne ya ƙaraso gareshi, cikin tsokana ya ce, “A'a ƙanina kaga zauna karka zube mana a ƙasa majiyatan su sake ƙaruwa kuma”.

      Furucin Uncle Yousuf ɗin ya sata sake ɗago idanu a karo na biyu ta kallesa, sai akai sa'a shima ita ɗin yake kallo har yanzu yaron na'a rungume jikinsa sai dai ya share hawayen. Harara ta balla masa da ɗauke kanta tana tura baki. Sai ya samu kansa da sakin murmushi yana wani ƙasa-ƙasa da idanu shima. Ammah da ke ankare da su su duka ta ce, “Babana zo mana naga sabon uba dana sake yi, danni kam kai da Mawaddat kun zama Kakannina yanzu kam tunda kun haifa mini Babana”.

         A hankali ya tako gaban Ammah cikin yanayin nan nasa na nutsuwa da kasancewa jarumin namiji tsayayye. Maimakon ya miƙama Ammah babyn sai ya kai zaune a  kujerar gaban gadon kusan da Mawaddat da hankalinta ke kan Uncle Yousuf da ke mata magana ƙasa-ƙasa.....


        Bayan an gaggasa Lulu ta gama ma Daddy da Uncle Yousuf shagwaɓa da koke-kokenta suma sukai mata faɗa akan barin ɗakin mijinta tabi Dada. Ta basu haƙuri da amsar kuskurenta. Sunji daɗin nuna nadamar tata kuwa a gaban kowa. Duk alkairin Ummita da Mamy da Usman gareta bata ɓoye ba. Su Abba sukai musu godiya sosai da wannan karamci duk da akwai sannaya tsakanin mahaifin Usman ɗin da Daddy. Bayan komai ya natsa an fahimci juna Usman yay ma su Abba jagora zuwa masauki, har lokacin kuma bakin Lulu da Smart bai saɓa ba, sai dai ƴar satar kallon juna, koda yake ma shike satar kallon nata, itako tayi biris kamar ta ma manta da shi a ɗakin take nunawa. Baiji komai a ransa ba game da hakan dan halinta kuma ai sai dai ya bama wani labari yanzu. Lulu akwai jan aji, koda wasa bata yarda ta zama a ƙasa ba akan al'amarinta. Lokacin da zasu wuce Usman ya ce ai shi Smart a barshi anan tare zasu wuce gida, suje su ya fara kaisu masauki sai ya dawo ya samesa. Mamy da Ammah kam dama tuni sun fice zuwa ɗayan ɗakin gidan. Itama Ummita sai ta zare jikinta cikin dabara wai bari ta wanke kayan baby data jiƙa ɗazun. Harara Lulu data fara tsarguwa da wannan ƴar zare jikin da ake ɗai-ɗai tabi Ummita da shi, sai dai batace komai ba dan Ummitan ta fita tana mata dariya...........✍️



       *_😂Kar naji wani yace komai kuma ehe. Musamman ma dangi dangi Smart ɗinnan. 🙈Koda yake akwai su aunty fa🚴🚴_*

     




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments