Furar Danko Book 02 Page 20

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗





           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣0️⃣




.........Ji Uncle Yousuf keyi kamar yay ta  kuka, ga wani jin zafi da takaicin Dada da Alh. Sulaiman na cimasa zuciya. Sai sake kallo Jaririn yake a hotuna harda ɗan gajeren vedion. Uncle Yousuf ya rungume Daddy jikinsa na tsuma. Babu wanda ransa ke hango masa kamar Smart a yayinda zaiji wannan labari mai cike da al'ajabi da mamaki. Dan koda Dada ta sanar musu samuwar ciki da kasancewarsa basu faɗa masa ba saboda yana kan gaɓar da kwanciyar hankali yafi buƙata, ga shi su kuma ba sanin inda zasu samo Lulun sukai ba a lokacin balle su ƙarfafa shi.

      “Yaya yanzu yaushe zata dawo gida? Dan tana buƙatar kulawa a yanzu sosai”.

     “Ya sake kwashe musu passport ɗinsu ne shiyyasa, amma ina kan ƙoƙarina na son ganin an dai daita musu komai sun baro ƙasar. Sai dai ba Nigeria nake so ta dawo ba, dan ina son nai amfani da wannan damar ne wajen ɗaure Sulaiman da jijiyoyin kansa sannan na ɓata abinda na gyara akan Mawaddat.”

               “Wannan tunani ne mai ƙyau Yaya, inaga kawai ta wuce wajen mijinta to”.

         “Zan so hakan Yousuf, sai dai zai iya zama matsala. A yanzu yaron yana a wata gaɓa ne da kowa zai iya kai masa hari ya kumayi tasiri a kansa cikin sauƙi. Bai kamata mu bada gudunmawar maida shi baya ba bayan al'amura sun ɗakko hanyar warware wa. Su Sulaiman shu'umai ne ta yanda komai zasu iya aikatawa. Sannan suna huɗɗa da manyan ƴan iskan duniya a fagen cinikayyar kayan shaye-shaye. Wannan babbar dama ce a hannunsu da akowane ƙasa mutum yake, ko wane irin matsayi ya taka zasu iya ƙulla masa. Abinda kawai ya dace muyi yanzu shine mu rufe bakunan mu ruf zuwa wani lokaci, amma mahaifinsa da mahaifiyarsa su san da wannan haihuwar. Shima kuma na aika a sanar masa yanzu hakan. Daga iya mu huɗun nan kar kowa yasan inda Mawaddat take Please”.

        “Na fahimceka ƙwarai da gaske Yaya. Kuma insha ALLAHU a yanzu bakai kaɗaine zakai wannan aikin ba. Ni da kai ne zamuyisa dan na fara ji a jikina Sukailan ne ya koyama Mawaddat shaye-shaye”.

     Sosai Daddy yaji daɗi da farin ciki, duk da yana tsoron kar a cutar masa da ɗan ƙanin nasa ɗaya tilo kuma. Amma ya bar komai a hannun UBANGIJI, sannan idanunsa a buɗe suke a yanzu kam kowane irin ƙalu bale ya shirya masa. Zancen Alh. Sulaiman ne ya koyama Lulu shaye-shaye kuma shima kansa yana wannan tunanin, a yanzu haka kuma yana kan bincike ne sosai har ma da yanda akai Nanny ɗin Lulun ta mutu duk zuciyarsa na masa zargin Sulaiman. sai dai a yanzu bai cema Uncle Yousuf ɗin komai akan hakan ba....


        *_CANADA_*


    Sosai Alhaji Sulaiman da ya iso Canada yau ɗin nan ke a cikin tashin hankali. Dan duk iya bincikensa yayi amma babu Usman babu su Lulu. Har asibitin da aka kaima Lulun cs yaje sai suka ce masa su basuyi wata theatre wa mai sunan ba. Neman haukace musu yayi, daga ƙarshe akasa security fiddashi tare da warning ɗinsa mai ƙarfi na in ya sake dawowa yay musu hayaniya zasu saka jami'an tsaro kamashi. Baya haɗa sabga da jami'an tsaro ko'a Nigeria, dan kun san mai kaza a aljihu baya jimirin ass. Balle ya samu labarin mahaifinsa ya saka a bincika a nemo inda yake tun kusan wata uku da suka wuce. Shiyyasa ma yaƙi zama waje guda yaƙi kuma shiga Nigeria kwata-kwata duk da labarin da ya samu har na sakin mahaifiyarsa Dada da Baba Garkon yayi. Yana tsaka da kasancewa a haukacensan saƙo ya iso masa. A birkice ya saka hannu a littafin ɗan saƙon, tun kafin ya koma cikin gida ya buɗe, inda ya fara cin karo da hotunan ƙyaƙyƙyawan jariri har kala uku. Hoton ƙarshe da ke ɗauke da rubutu ya juya cikin tsumar jiki. *_Zakaran da ALLAH ya nufa da cara, ko ana mazuru ana shaho sai yayi. Aliyu Aliyu Mika'il Mawashi ya iso duniya lafiya_*

      “What!!” Ya faɗa cikin bugawar ƙirji da rawar hannu. Sai kawai ya saki wani irin ihu mai ƙaraji tare da yin watsi da hotunan. “Usmaann!!” ya sake ambata da ƙarfi. Sai kuma ya ƙyalƙyale da wata irin dariya mai ƙona zuciya, tare da faɗin, “Yaro baka san wuta ba sai ka taka. Ka taro babban match ɗin da kaf family naka basu isa zamar maka defenders ba. Sai na tarwatsa rayuwarka ta inda zaka dawwama dana sanin yaudara ta da ka shirya yi. Yarinyar kuma da hannunka zaka maidota gareni”. Da ga haka ya fisgi rigar sanyinsa da ke a hanger ya fice gidan.....


       

  *_NIGERIA_*

    

        Tun randa taji Smart baya Nigeria ta kasa zaune ta kasa tsaye, ko kaɗan zuciyarta da gangar jikinta sun gagara hutawa. Ba ita kaɗai ba, hatta ƴaƴanta ta cusa musu hassada da ƙyashin da ya ingizasu fara bibiyar al'amuran Smart har suka gano irin cigaban da yake samu a yanzu haka, duk da dai a farko dariya suka fara da ganin Smart ɗin ai a ƙaramin team yake ma. Sai dai kuma a hakan ma dai UBANGIJI sake bayyana shi yake ga duniya a bisa kowane matakin nasara koda akwai ƙalubale a cikinsa. Abu na biyu yanda Abba ya fara jiƙewa a ƙanƙanin lokaci, dan bai iya ɓoye alkairin da Smart ɗin ke turo masa. Duk da ba wasu maƙudan kuɗi bane na tashin hankali, sai dai suna riƙesa ta yanda a yanzu haka baima fita kasuwa sai yaran. Duk da aikin da Malam Na-zuru ya sake mata a kan Smart ɗin hankalinta ya kasa kwanciyar jiran nashin kaɗai. Tuni sun bazama ga wasu malaman harma da bokayan babu inda Hajiya Naqiba bata zuwar mata. Wani lokacin kuma suje tare ma. 

        Ammah ce ta fara fuskantar al'amarin na Umma a randa ta kamata tana bizne abu a bayan windown ta ga sunan Smart tana kira. Hankalin Ammah ya tashi matuƙa a wannan ranar, amma bata yarda Umma ta ganta ba harta kammala. Bayan barinta wajen tai kiran ƙanwarta Gwaggo Sa'adah ta sanar mata komai cikin tashin hankali. Gwaggo Sa'adah ta kwantar mata da hankali akan tana zuwa, sai dai karsu taɓa abinda Umman ta bizne tunda akwai jinin Smart a jikinsu. Gwaggo Sa'adah ce tazo da wani almajirinta, inda cikin hikima ya tone abinda Umman ta bizne ɗin. Layune da wasu sirkulle a kwalba an ɗaure. Koda aka kunce layun abinda ke rubuce a ciki su dukansu ya daga hankalinsu. Amma sai almajirin nan ya ce su kwanatat da hankalinsu addu'a tafi gaban komai ai. In sha ALLAH tunda an farga da wuri babu abinda zai faru, zai je da su ya lalata. Gwaggo Sa'adah taso a ajiye a nunama Abban. Amma sai Ammah tace a'a a ƙyaleta a rufa mata asiri idan halintane zata ƙara ai har Abban ya gani da kansa wataran. Har Gwaggo Sa'adah taji haushi sai kuma da ga baya ta fahimci hikimar Ammah.


      Tunda ga faruwar wannan al'amari Ammah ta sake dagewa da addu'a akan ƴaƴanta gaba ɗaya. Tare da sadaka akoda yaushe. Duk inda taga maraya tana ƙoƙarin taimaka masa. Suma yaran kullum cikin ƙara ƙarafafasu take da ibada har Smart. A duk sanda sukai waya sai ta sake nusar da shi. Alhmdllh yana fahimtar ta sosai, kuma dama baya sakaci akan ibadarsa duk da wataran gajiya kan hanashi iya tashi sallar daren daya sabama kansa yanzu. Amma a koda yaushe bakinsa bai rabo da ambaton ALLAH.


     Yau ma kamar kullum gidan yana ruɗe da hayaniyar yara da jikoki kasancewar juma'a ce ta ƙarshen wata. Dan an sakko massalacin kenan sai ga Abdull ya shigo yana sanarma Ammah Abbah yace a bada ruwa anyi baƙi. Kasancewar itace da girki babu wanda ya damu. Ta haɗa ruwa harda zoɓon da Maryam tayi domin zuwan Ahmad ɗinta kasancewar duk juma'a yake zuwa hira bayan sallar la'asar (Kun san fa Ahmad da Maryam an jone🥱). Har Abdull zai wuce Ammah ta sake dakatar da shi, dan tunda taga Abbah ya aiko a amshi ruwa da alama baƙin masu muhimmanci ne. Masar da tayi matsayin abincin rana ta zuba ta ce Asma'u ta ɗauka ta bisa da shi. 

         Sosai Uncle Yousuf ya tsirama Asma'u da ta kai har ƙasa tana gaishesu idanu, dan sosai tana kama da Smart, sai dai kawai dan shi namiji ne ita mace, ta kuma fishi haske sosai. Murmushi yayi domin tuna wani abu. Daddy na lure da shi sai dai baice komai ba har Asma'un ta fita. Mikewa Abba yay da nufin barinsu suci abinci, amma sai Daddy ya ce yayi zamansa ai ruwama kawai ya wadar. Ɓata rai Abba yay da faɗin, “Saboda abincin namu ba irin naku bane Alhaji Isma'il?”.

      Cikin ɗan daburcewa Daddy yace, “Wlhy ba haka bane Malam Mika'il. Amma aimana afuwa bara muci.” dariya suka ɗanyi cikin barkwanci, da ga haka suka shiga buɗe abincin, ganin masa tasha manshanu ga lafiyayyen zoɓo bama su san sanda suka shiga cin ba har sai da suka tada abincin tas. Daddy na tsokanar Uncle Yousuf ne ya cinye, shima yana tsokanarsa shine ya cinye. Shi dai Abba dariya yake musu cike da sha'awar wannan zuminci tamkar wasu abokai. Bayan sun kammala Uncle Yousuf yace ya kamata Ammah tazo dan suji miya kawosu a tare. Abbah ya jinjina kansa cikin gamsuwa, sannan ya ɗaga waya yay kiran Ammah. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gata, tayi mamakin ganin ashe baƙin su Uncle Yousuf ne, amma sai batace komai ba ta zauna suka gaisa cikin girmama juna. Uncle Yousuf ya zaro hotuna a aljihunsa ya miƙama Abbah. Amsa yay yana murmushi, sai dai yana kallon jinjirin dake a hoto sai da zuciyarsa ta harba. Dan haka ya ɗago da sauri ya na duban Ammah data tsira masa ido, sai kuma ya dubi su Daddyn da ke kallonsa da murmushi. Itama dai Ammah gabanta ne ya faɗi lokacin da taga abinda ke jikin hoton, muryarta na rawa ta ɗago tana kallon Abbah. Abban Salim wannan ai Hydar ne yana jinjiri, sai dai ban san sanda aka ɗauki hoton ba gaskiya, dan kayama na manta da su.”

      Daddy da ya kasa riƙe dariyarsa ne yay gyaran murya, dan haka suka dubeshi su duka har Uncle Yousuf dake danne tasa dariyar shima. Daddy ya ce, “Anya Aliyu ne? Kudai sake kallon hoton Malam Mika'il”.

       Kallon juna Ammah da Abba suka sake yi, sai kuma suka sake maida hankalinsu a hotunan. Abba ne ya sake cewa, “Gaskiya Aliy ne a hotunan nan Alhaji Isma'il. Ba mu da muka haifesa ba ma, duk wanda zaka tambaya in har yasan Aliy yana jariri wannan amsar zai baka”. Ammah dake jinjina kai tace, “Wannan gaskiya ne Abban Salim. Dan Hydar ne yana jariri”.

        “Wannan jinin Aliyu Hydar ne a yau ba Aliyu yana jinjiri ba”. Cewar Uncle Yousuf cikin murmushi. Cikin haɗa baki Abbah da Ammah sukace, “Jinin Aliyu! Tayaya?”.

       “Ta hanyar matarsa Baba. ALLAH ya albarkaci matar Aliyu da haihuwa jiya, wannan shine albarkar da ALLAH ya azurtamu da ita mu da ku da shi”.

       A hankali hawaye suka ziraroma Ammah da jikinta har yake tsuma.  Muryarta na rawa ta ce,.......✍️




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments