Tabarmar Kashi Book 2 Page 51

 "HUGUMA


• TABARMAR KASHI*

Book 02 Page 51









Lokacin da aka fito da ita tana bacci. Afifa so tayi ta rude, toufeeq din ya riga yasan situation din da afifan ke ciki, don haka ya yiwa sajjad din alama na ya jata yabar gurin da ita.



*********Sannu a hankali ta dinga bude idanunta da taji sun dan mata nauyi ga kuma hasken da ya cikasu. Yana zaune a gabanta hannunsa cikin nata,ko motsi baya yi da idanunsa bare hannun nasa dake dame da nata.


A nutse ya miga hannunsa zuwa saman goshinta don tabbatar da farkawarta. Dumin hannunsa dake saman goshin nata ya sakata dauke idanunta daga kan maji dake zaune gefe daya saman kujera ta dawo dashi kansa. Sarqewa idanunsun sukayi cikin na juna,ta dan zuba masa ido tanason tabbatar da shi dinne?, har yanzu akwai fushin nan saman fuskarsa ko kuma yayi qaura?.


Hawaye ne suka fara tsatstsafowa idanunta,idonsa ya lumshe sannan ya bude yana girgiza mata kai alamar a'ah dai dai lokacin maji ta dawo da dubanta kansu,ta matso a nutse tana fadin


"Ta farka ne?"


"Eh" ya amsawa maii din. Qogarin zame hannunta daga nashi takeyi saboda gain maji a wajen, amma saidai bashi da niyyar motsawa daga wajen ma bare ya bari ta zame hannun nata.


"Sannu d'iyata" maji ta fada cikin kulawa. Kai ta gyada mata sannan ta motsa bakinta a hankali


"Yauwa" ta amsa mata,dai dai lokacin likitan ya shigo, bayansa afifa ne ita da sajjad. Dukkansu kayan data gani a jikinsu a daxun yanzu basu bane ba,da alama ta dauki wasu awanni kenan tana bacci ba tare da tasan abinda yake faruwa ba.


Sannu suka yiwa likitan, afifa ta matso tayi mata sannu sannan suka juya dukka suna fita saboda bawa likitan damar dubata, banda toufeeq da ya gara matse hannunsa cikin nata.


Wannan karon cikin harshen turanci likitan yake masa bayani


"'Ina mai baka haguri, ta samu bari na ciki dan sati hudu"


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati, wa'akhlifni khairan minha" ya furta yana runtse idanunsa.


Har cikin saman kansa ya dinga jin wani abu, sai ya kasa ci gaba da tsaiwar,ya koma a hankali ya zauna saman kujerar yana ci gaba da rige hannunta,kana ya sauke idanunsa a kanta.


Tunda likitan ya fadi maganar taji kamar an sauke mata dutse mai nauyi a girjinta

"Anya tana rabon ganin qwanta a duniya?" Tambayar data yiwa kanta kenan,tana jin numfashinta kamar yana mata wahalar shaqa.


"Akwai abinda yadan raunata qarfin mahaifarta,don haka tana da dan rauni,wanda cikakken motsi ko zirga zirga me yawa,ko kuma razana suna iya kawo mata miscarriage" idanunsa ya mayar kan likitan,yana jin zuciyarsa na quna


"Yanzu sai yaushe zata iya sake conceiving?" Maganar ta sanya likitan dagowa ya dubeshi tare da sakin qaramin murmushi


"Kada ka damu yallabai, indai za'a kula da ita yadda ya kamata, maida wani babyn bazai zama abu me wahala ba"


Magunguna ya rubuta cikin file din sannan ya ajiye yana qara masa was bayanai sannan ya juya ya fita. Ya barshi cikin wani irin yanayi,ya dinga ji kamar laifinsa ne, kamar shi yayi sakacin da cikin ya fita,amma bai sani ba ba shakka inda yasan akwai ajiyarsa tattare da ita ko sama da gasa zasu hade bazai bari tayi tafiyar ba. Shi daya yasan yadda Allah ya jarabceshi da son tara zuri'a,musamman a yanzun a yadda yake,Allah yayi masa dukkan wata ni'ima da sutura ta rayuwa.


Idanunsa ya dauke daga kan likitan a nutse ya maida saman fuskarta dake a runtse wani abu me masifar garfi yana sake fusgarsa a kanta. Duk da idamunta a kulle suke, duk da a gadon asibiti take amma hakan bai hana bayyanar kyan siffarta ba.


Sosai ya zubawa gefan idonta ido yana son tantance hawaye takeyi?,ya gani kuwa dai dai?. Yatsansa ya sanya ya dangwali hawayen,ya tabbatar sune, abinda ya sanyashi tashi cak daga kujerar da yake zaune a kai ya koma gefan gadon saitin kanta.


Cikin taushi ya daga kanta ya dora saman cinvarsa, sannan ya sanya tattausan tafin hannunsa ya fara dauke mata hawayen. Saukar hannun nasa saman fuskarta ya sanya ta dakata da kukan saboda yadda ta jita kwance saman jikinsa. Sai da ya gama tas sanann ya sunkuya da kansa saman fuskarta,sai ya zamana kamar yayi mata rumfa. Cikin muryarsa me taushi da kuma wani irin deepness yace


"Kema kina bugatar sa ko?" Yayi mata tambayar da sai da taji kamar zata nutse a gurin. Sake sassauta muryarsa yayi


"me yasa ya tafi a irin wannan lokaci? ya tafi ya barmu da kewa me yawa ni da mommy dinsa,we missed him a lot, but karki damu,kiyi goqari ki warke da wuri, nay algawarin zanyi replacing wani very soon in sha Allah" kasa jurewa tayi duk da idanunta suna a bude ne, saita mirgina kanta daya sashen tana sake lumshe idanunta.


Tsaye tayi daga bakin qofar ICU din, inda aka

kwantar da fadeela,wadda a qalla zata iya kaiwa gobe ko jibi tana bacci saboda allurar baccin da sukayi mata,suka saka mata na'urar ventilator saboda ta taimaka mata wajen yin bacci da kyau.


Duk lokacin data kalli fadeelan sai taji zuciyarta ta

tsinke sosai, tsoron Allah yana sake kamata,tare da

tabbatar da cewa lallai dan adam ba'a bakin komai yakeba. Haka kawai cikin jikinta takejin zargin hajiya qarama me garfi akan ciwon fadeela,har yanzu kunnuwanta suna iya jiye mata fadan da take a dazu cikin wayar jarma bayan ya kirata don ya gaya mata ta aikawa mansura a kira company din nan suyi gyaran sashensa irin wanda sukeyi duk shekara, daga nan ya shaida mata suna Germany tare da sãahar da fadeela harma da toufeeq da nadeeva an yiwa fadeela aiki.


Saura qiris ta zame ta fadi saman marbles na

kitchen din da take tsaye a ciki a sannan, don sai data

dafa me aikinta sannan ta samu guri ta zauna zuciyarta na wani irin rawa kamar zata tsinke daga qirjinta


"Yaaya? yanzu har rashin muhimmanci na yakai kowa da kowa ya tafi gurin aikin ciwon fadeela amma banda

ni? bayan nice nafi cancanta da naje?"


"Nima daga qasar da naje na samu visa na wuto, bansan me yake faruwa ba"


"Amma yaaya ina cikin gidan nan, har yaushe aka yanke. shawarar yin hakan ba tare da na sani ba?"


"Wannan kuma ki jira danki yazo sai yayi miki bayani, don hukuncin surukarki ne,ita ta tsara hakan, ban sani ba ko da saninsa ne koma meve dai anvi aikin successfully inji likita, farfadowarta kadai muke jira"


"Turgashi!" Ta fadi cikin matsanancin tashin hankali


"Ita har waye yaaya da zatayi kutse a rayuwarmu? har ta isa tayi hukunci cikin rayuwar 'yarmu?, to wallahi ka shaida mata ta kuka da kanta, muddin daya daga cikin matsalolin da akan iya gamuwa da su sanadin surgery din nan ya samu fadeela to la shakka sai nayi shari'a da ita,sai na daureta wallahi, akwai visa ta ta garmany dana taba yi, batayi expire ba,ina nan tafe nan da kwanaki uku in sha Allah" ya zuwa yanzu haka kawai Dr mahmud yakeji ya fara qosawa da damuwa da matsalolin fauziyya


"Sai kin iso. kawai vace da ita vaja jan garamin tsaki.

Hayaniyar da tayi masa cikin waya yaji tana bata ransa, ya waiwava va dubi maji dake zaune a gefansa cikin mota.


Ko a fuska bata nuna taji komai ba, duk kuwa da yasan

bata yadda za'a yi tace bata ji din ba saboda handsfree ya saka,amma yadda ta nuna din sai ya garyata maka hakan. Ajiyar zuciya kawai ya saki,shi kadai yasan irin rudanin da yake ciki, tunda me afkuwa ta afku suka baro.


Algeria ko sau daya bai gara ganin murmushinta ba.

Sallamar Dr mahmud jarma din ta sanyata

motsawa kadan,ta kuma amsa ba tare data juyo ba.

Gefanta ya garaso ya aza hannunsa daura da nata,sai kawai ta cire nata hannun ta fara takawa tana barin gurin.


Kamar ya kirata sai kuma ya fasa, gudun kada ayi

abun kunya gaban surukai,ya maida kansa ga fadeelan

vana ci gaba da yi mata addu'a,don shi kansa yayi

matuqar damuwa, kasancewarta tilon jika a gurinsa.


******* Kusan minti guda cif yayi yana kallonta daga nesa zuciyarsa tana narkewa. Kwata kwata bata zauna ta samu cikakken hutun da likita ya bugata ba daga gareta, tunda har taji zata iya migewa taqi zama,sai zirga zirga da takeyi tsakanin ICU din zuwa dakin da aka bata, tsahon kwanakin ukun duka ta tashi hankalinta,ta dorawa kanta laifin komai da komai har da rashin farkawar fadeela akan lokaci.


A hankali taji an rungumeta ta baya, sannan cikin

taushi ya sanya hannunsa va hannuwansa saman ruwan cikinta ya sake jawota cikin jikinsa sosai. Kansa ya dora saman kafadarsa,cin taushi ya soma mata magana a kunne me kama da rada


"Damuwarki tana ciremin kowanne karsashi daga raina"


hannunsa ya sanya ya juyo da ita suna fuskantar juna,ya miga yatsansa yana dauke ruwan hawayen dake layi saman kuncinta


"Karki sake kuka we'll figure this out together, she will be fine in sha Allah,don't blame your self" qas tayi da

fuskarta wasu sabbin hawayen na saukowa,sai kawai ya bude girinsa ya sanyata a ciki,ya kuma rungumeta tsam yana shafa bayanta a hankali idanunsa kan fuskar fadeela da ta dan kumbura kamanninta suka dan jirkita kadan.


"Toufeeg" yaji an kira sunansa daga bayansa. Dukkansukoda basu waiwaya ba sunsan me muryar. Motsawa säahar tayi kadan da nufin janye jikinta


"Don't move" ya furta can gasan magoshinsa, idanunsa a lumshe yana ci gaba da shafa bayanta. Bata sake motsawar ba kamar yadda ya buqata,hakanan bai juya ba shi dinma, har zuwa sanda ta iso gabansu


Hajiya qarama ce, cikin shigar nan tata da ko yaushe take nuna tsananin alfaharin da take dashi,izza da kuma nuna isa


Toufeeq.…...au lallabata kakeyi ma?,na tsammaci zanzo na samu kana hukuntata da mafi tsananin hukunci? yarinyar da take shirin yi maka sanadin rasa tilon 'yarta saboda shegen shishshigi da rawar gafarta? ko an gaya mata mu bamusan hanyar germany din bane da zata kwaso gafafunta ta kawo mana yarinya uwa duniya? gashi har yanzu bata farka ba? waye ya sani ma ko cinikin qodarta kota qwaqwalwar tata tayi mana"


"Stop" ya furta cikin gautsi da bacin rai,yana jin kamar ya juya ya wanke mata fuska da mari,saidai a yanayin da ake ciki yanzu bayason yace mata komai,lokaci kawai yake jira. Sai a sannan ya bude idonsa kan fuskar sãahar wadda ta daga kanta daga qirjinsa tana duban awayar idanunsa cikin damuwa da razanin kalaman hajiya qaramar.


Hannunsa ya dora saman kanta kamar qaramar varinya


"Banason wannan tsoron, banason wannan firgitar,tun yanzu nakeson ki ajiyeta, da irin wannan abun naki kikayi mana asarar baby". Wata nutsuwa taji tana saukar mata da kalamansa dake nuna ko daya zancan annamimiyar matar baiyi tasiri a ransa ba.


"Asarar wanne babyn bayan fadeela?" Tayi masa

tambayar adan rude. Kai tsaye ya waiwaya,karon farko

tunda ta iso ya dubi qwayar idonta kai tsaye


"She had miscarriage, cikina dake jikinta ya bare"

mummunar faduwar gabanta yayi wanda sai data jishi

har tsakiyar kanta,me yake shirin faruwa tana toshe wata barakar wata barakar tana kunno kai? yanzu har tayi saken da wata macen da ba meenal dinta ba zata dauki cikin toufeeq?. Kafin ta sake cewa wani abu ya dauke idonsa daga gurinta


"Ko zaki matsa daga nan gurin, saboda basa bugatar

hayaniya da tarin tarkacen mutane" dubansa tayi a

mamakance a karo na biyu, Ita toufeeq yake kira da tarin tarkace?, koda yake tayi masa uzuri yana cikin dimuwar rashin farkawar fadeela,to amma kuma idanunta suna nuna mata canzawar mu'amala tsakaninsa da yariyar, yaushe hakan ta kasance? indai hakanne kenan aikinta ya sake linkuwa?,kenan wani dogon zangon zata ci muddin hakan ya tabbata kafin cikar muradinta?.


Shuru ne va ratsa gurin bayan ta juya ta bar gurin

cikin wasi wasi. Ci gaba yayi da boyeta a qirjinsa, saboda weakness din da yake hanga tattare da ita bayason ganinsa, she's strong enough,tayi abinda dukka dangin fadeela suka gaza yi mata,bai kamata ta karaya haka ba.


"Subhanal malikil guddus" taji ya furta yana sakinta daga jikinsa. Daga kanta tayi da sauri ta kalleshi,sai kuma ta maida dubanta ga inda yake kalla.

No comments