Tabarmar Kashi Book 2 Page 41

 



Book 02 Page 41








Sosai zuciyar maji tayi wani irin nauyi,girman kaidai da dabi'ar fauziyya maras kyau tana ratsata,saidai kuma

ta tuna da wata magana guda daya na cewa

MURMUSHINKA GUDA DAYA TAK NA IYA SANYA

FADUWAR GABA GA MAQIYINKA don haka fa waiwayo tana dubanta da murmushi saman fuskarta


"Kin riga da kin makara,saboda bana tunanin lokacin da za'a rubuta littafin qaddarata kina gurin,na tabbatar da cewa kedin baki da matsayi a wajen Allah da kike da qarfin ikon canza qaddarata,na rigaki tsayawa a gaban Allah,na kuma rigaki ambatonsa" dariya fauziyya ta saki


"To sannu sufiya". Kasa ci gaba da tsaiwa maji tayi a kitchen din,ta juya ta fice a hankali, zuciyarta cike da mamakin wanne abu ta aikatawa fauziyya haka data cancanci irin wannan sakamakon?.


Ranar hatta da yaran basu wuni gurinta ba,sun wuni gurin fauziyya ne tana nan nan da su, sakamakon a ranar mahmud yana gida,saidai yadan fita ya dawo. Fauziyya ita tayi girkin rana da dare, kamar yadda tayi girkin dare,a lokacin idan ka shigo gidan zakayi tsammanin itace matar gidan idan ba kasan cewa matar gidan shifa bace.


Tana daga daki tana sauraren dabdalarsu, yadda suka wuni suka kai kawo haka ta wuni kwance a daki. Sai bayan magariba lokacin da mahmud din yake zaune a parlor suna kallo da yara fauziyya ta shirya komai saman tray ta shigo dashi falon


"Yaaya,don Allah kayi magana da maji,tayi haquri ta tashi taci abinci, yau duka bataci komai ba" dubanta yayi yana jin tausayin fauziyyan yana kama zuciyarsa tare da kallon kyawun halayenta


"Ke kamar baki da zuciya?,kamar baki damu da abinda ta aikata miki ba?,har yanxu fa bandage ne a kanki fa na abinda ta aikata miki" cike da kissa da kisisina tayi gas da kanta


"Bazan manta kyatatawarta a kaina ba,shi yasa bazan iya fushi da ita ba" Numfashi yaja sannan yace 


"Ni dai bazanje ba,idan kuma ke zaki iya bismillah".

Hawayen da suka wanke mata fuska ta share,duk abinda suke tattaunawa a tsakaninsu tana jinsu. Zuciyarta ta gama amanna da cewa abinda fauziyya ta shirya aiwatarwa a kanta me girma ne, abu guda ne zai zame mata garkuwa tsakaninta da ita shine addu'a. Bata ko marmarin gain fuskarta,don haka salin alin kafin ma ta kai ga shigo mata daki ta miqe ta murza key ta koma ta kwanta. Tana jinta sanda take knocking da magyar ta bude, zallar kukan dake cin zuciyarta ya hanata koda qwaqwaran motsi. Fauziyyan da koda wasa bata tana kama mata aiki ba koda ciwo zai kayar da ita, fauziyyan da sautin INA KWANA da sunan sun kwana gida daya bai taba hadata da ita ba,fauziyya da bawai ta girka ba,wanda ita ta girka dinma qoqari take ta juye ta cinye, amma wai yau saboda zallar kissa ita ke biyota daki da abinci?.


"Ki gyaleta,ta hadiyi baqar zuciyarta ta mutu ita kadai" shine abinda mahmud ya fada yana sake qufula, tare da garin yarda da dukkan maganganun da fauziyya ta gaya masa.


Har dare ya raba tana kwance tana kuka,sanda agogo ya nuna mata qarfe uku na dare ta yiwa kanta fada,ta sauka daga saman gadon ta bude gofarta a hankali ta fito bandakin dake tsakanin dakunanta guda biyu dake manne da parlor. Ta kammala alwalar tana shirin fitowa mahmud ya shigo. Cikin sanyin jiki da karyewar zuciya take kallonsa, amma sai ya dauke kansa gefe ya rabata ya shige bandakin yana turo mata qofa.


Da qyar ta qarasa dakinta, ta zube saman abun sallar tana bude sabon shafin kuka,abin ya fara wuce tunaninta,ko a lokacin da Mahmud din ke ganiyar karayar arziqinsa wani abu makamancin wannan bai taba hadasu ba,ko da yaushe cikin gogarin kwantar masa da hankali take tare kuma da yin amfani da dukkan abinda take dashi saboda aci gaba da tafiyar da hidimar gidan yadda aka saba.


Sallar data kwana tana yi ita ta sanya sassauci cikin zuciyarta,a washegarin kuma ta tashi da wata irin dakiya tawakkali tare da qarfin zuciya,ta sameshi a tsakar gida yana bawa fauziyyan kudin cefane a madadinta. Ko a fuska bata nuna masa komai ba,ta tsugunna cikin girmamawa ta gaidashi yadda ta saba,yana fiffisgewa ya amsa mata,sai itama fauziyya ta rusuna tana gaidata.


Kallo daya tak tayi mata ta dauke kai, don abun na fauziyya yanzu ya daina bata mamaki, abu daya fa sani, tabbas akwai mummunan qudurin data sanya a ranta.


Mai hali inji hausawa sukace baya fasawa,yana fita ta baje kolin rashin mutuncinta,ta cika gidan da waqe waqe tana kuma bin kowacce waqa sau da qafa cikin daga sauti. Yaran kuwa gaba daya ta tattarowa maji din su ita tabi lafiyar katifa abinta. Bata waiwayesu sai data ga la'asar tayi,lokacin ta fito ya dora girkin dare,ta kuma fara kiran sunan yaran tana hilatarsu, har suka kai ga fitowa,ta tattarasu tana jansu da wasa tana kuma aikin abincin dare.


Cikin kwanakin gaba daya gidanta ya koma kamar ba nata ba,bata dats cewa sai abinda fauziyya ta fada,baya aiwatar da komai sai abinda tace masa. Fadin irin tsananin damuwar da maji ta shiga a lokacin batà baki ne,a sannan tana ji har cikin ranta, inama ace fauziyya ba ganwar miji bace kishiya ce,ba shakka inda kishiya ce koda abun zaiyi mata ciwo bai kai kamar haka ba.


Tun asali rayuwarta da Mahmud rayuwa ce ta soyayya da qaunar juna da kowa ya shaida da hakan,ko yaya ka zauna dasu zaka fahimci hakan,wannan ya

Sanya suke bawa mutane da yawa sha'awa, haihuwar

Muhammad da ta nadeeya ba abinda ta sauya game da yadda suke bawa junansu kulawa,koda kuwa bayan karayar arziqin Mahmud jarma din wanna kyakkyawar dangantakar bata canza ba. Asalin maji ta fito daga babban family a qasar Algeria,family ne na masu da shi,a sannan tana da kadarori, haka ta dinga dagasu daya bayan daya tana saidawa tana kula da Mahmud gidansa da yaranta,ko sau daya bata bari ya shiga damuwa ba game da abinda zasuci ko su sha,ko kuma karatun Muhammad ba. Har zuwa sanda riqon fauziyya ya dawo hannunsu.


Batasan me ake ciki ba,tashin farko kawai ta yiwa rayuwarsu katsalandan,ganin kusan duk wani decision shifa ke yankewa,a hannunta taga yayanta yana karbar kudin duk wata hidima tasa,ba shi ba,hatta ita idan tana da bugatar abu a hannunsa zaice ta yiwa shifa magana ta karba a waienta.wannan vasa sannu a hankali ta dauki dukkan karantsana na duniya ta dorawa shifa,tana ganin ta mallake yayanta ne kawai sai abinda tace, tare da tunanin duk wata hidima da akeyi cikin gidan da kudin yayanta ne, kawai don bashi da katabus ne babu yadda zaiyi shi yasa ake juyashi haka.

Duk wata wahala tare da fadi tashin aikin mahmud tare da shifa akayi, ta qarar da kudi masu dimbin yawa kafin tabbatuwar samun aikinsa a wani babban company. Gabanin ya samu aikin kullum maganarsa itace


"Allah ya bani abinda zan kyautata miki nima, Allah ya bani damar mayar miki da halaccin da kika yimin a yanzun da bani da mahaifiya kece makwafinta a gurina,in sha Allah sai kinfi kowa jin dadi na shifa,bazan manta wannan halaccin naki ba" sau tari yana maganar ne a gaban fauziyya,idan yana irin wannan maganar tashi take ta basu guri, saidai ga dukkan me hankali a lokacin idan ya kalleta zai fahimci yadda zuciyarta ke suya a gasan qirjinta. Shifa kam takanyi murmushi ne kawai


"Nisful hayaat,ban baka wani abu nawa wai don ka maidamin koda kwatankwacinsa ba bare ninkinsa,da kai da kaya duka mallakar wuya ne" kai yake girgizawa


"Na sani,amma kada ki manta,komai naki ya qare,fili biyu ne kawai ya rage miki da gida guda daya"


"'Kaci halak malak fa"tace dashi tana murmushi.


Dukka wadannan algawura da alwashi sun tashi a

banza daga lokacin da fauziyya ta yiwa zuciyarta saqa

da mugun zare


"Mu biyu kacal nahaifiyarmu ta haifa,bazan taba bari wata mace da ta sameshi daga sama ta fini cin

moriyarsa ba" fauziyya ta fada sanda take tsaye a gaban  madubi tana gayawa kanta da kanta.


Dukka wadannan alqawura da burika a sannu

suka bi ruwa suka kuma shafe daga tunani da kwanyar

mahmud. Lokacin da ya kamata ace rayuwa ta koma musu dai dai maji da kusan ita taci wahalar komai sai ta

koma 'yar kallo daga gefe,wasu abubuwan saidai taji

daga fauziyya cikin waqe da habaici. A yanzu ta zama

tamkar uwarsa,da ita yake shawara,kuma duk abinda

tace ya zauna kenan. Kamfanin da suka bashi aiki sun

hada masa da kyautar gida da mota kamar yadda ya

shaidawa maji zasu bashin kafin tabbatuwar

al'amarin,saidai koda suka bayar din a bakin fauziyya ta

fara ji,ranar suna hira cikin falonta tana daga daki, ta fito

zata wankewa nadeeya jikinta fauziyyan tace 


"Maji, kinji abin arziqi ko?, kamfani sun bawa yaaya gida da mota,zamu tashi daga nan in sha Allahu,ki tayashi murna" wani abune ya tsaya nata a wuya,al'amurinsu ya zama abun tsoro, saboda tako ina babu lamari na hankali a ciki,wai ita matarsa mafi kusanci da shi,a yau ta zama


'yar kallo,labarin da za'a ji a bakinsa yau ita takeji a bakin wani


"Allah ya sanya alkhairi" kawai tace dasu tana ficewa abinta. Har taje ta dawo suna zaune a gurin, tana gyarawa nadeeyar jikinta sai gashi ya shigo. Sau daya tak ta kalleshi ta kauda kanta,saboda zuwa yanzu ta sallamashi,abu daya ne yake bata nutsuwar ruhi addu'ar da takeyi,ta rame sosai a lokacin saboda tsananin damuwar da take ciki da abubuwan da take ga suna faruwa,gidanta a yanzun bata jin nata ne sam. 


Akwai alamun jikinsa ya sanyaya kadan sai ya tako ciki

"Wai ke me yake damunki? ‚gaba daya kin canza hali?" Ya fada yana kallonta,qasan ransa yana jin damuwa ne tarin yawa,amma kuma wani sashe na zuciyarsa najin ba komai bane muddin fauziyya tana cikin farinciki da walwala


"Me yake damunki nace?,kin sake sabbin baqaqen halaye shifa" abun yayi mata ciwo sosai,wato itace ma ta sake sabbin halaye baqaqe


"Ba komai" ta bashi ams tana daga nadeeya don saka mata riga


"Ai shikenan,sai kije kiyita yi tunda haka kika zaba" ya. bata amsa yanason fita a dakin amma kuma sai ya kasa fitar,ya samu guri ya zauna,har ta gama shirya yarinyar ta kwantar da ita,ta gyarawa toufeeq shima tasa kwanciyar,saboda tun lokacin da abun ya soma faruwa ya raba daki da ita,itama bata sake nemansa ba,tunda taje sau daya yayi mata korar kare


"Don Allah idan ka gama ka fita zan rufe qofata" ta fada da sassanyan muryarta


"Korata ma kike shifa?" Yadda ya tambayeta a yau din da tausasawa sai ya sanya hawaye sauka daga idanunta,daga nan kuma ta fashe masa da kuka sosai harda shashsheda.


Kasa rarrashinta yayi yadda suka saba a baya,yana zaune ya zuba mata ido yana jin zuciyarsa tana gonewa,a cikin ruhinsa yana jin shifa bata cancanci haka ba,amma kuma bazai taba iya daina abinda yakeyi ba,shifa tayi masa abinda uwa mahaifiya cs kawai zata yi hakan wa d'anta. Sai data ci ta cinye don kanta sannan ya qaraso gareta. Miji da mata sai Allah, a nan ya samu hadin kanta,abinda shi kansa ya jima bai nemeta dashi-ba. Bayan komai ya kammala cikin hikima da kwantar da kai ta soma masa magana akan matsalar da suke fuskanta su  dukansu

*HUGUMA*


No comments