Tabarmar Kashi Book 2 Page 25
Book 02Page 25
"Yanzu ba zaka sanya baki ba ko don a samu hankalin yarinyar nan ya dawo jikinta?" Agogon hannunsa da ya manta bai cire ba ya soma zarewa
"Bana shiga lamarin da ban isa na hadashi ba, daga ke har fauziyya na gaya muku, toufeeq yana da ido so ba sai an tursasashi ba,ko ni bani da ikon bashi umarnin ya auri wance,idan ya gani yanaso bazan hanashi ba" maganar tasa ta tabata sosai, kuma dama fauziyya tana can tana nata yaqin kenan? ya tabbata ta shirya cin amanarta da gaske,iska ta furzar a bakinta tana gangance idanu
"'Wallahi wallahi wallahi tsautsayi yasa ta yimin kan kara sai nayi mata na itace, idan tana tutiya da ita din gwanace ni uwarta ce a wannan fannin, zatasan ni mansura cikakkiyar KARA DA KIYASHI ce daukan mara sani" abinda ta furta kenan qasan ranta, kafin daga bisani muryar dr mahmud ta mamayi kunnenta
"An samu ticket din? na ranar yaushe ne?, alright zanyi managing na jira ranar" sai ya sauke wayar daga kunnensa a hankali yana furta
"Alhamdulillah" yadda fuskarsa ke nuna annuri yaja hankalinta
"'Wacce tafiya ce haka me muhimmanci zakayi?"
"Ni kadai tafiyar ta shafa,so ba wani abu bane na daban" ya fada yana kashe wayarsa. Binsa tayi da kallo,haka kawai taji jikinta bai bata ba,so amma koma inane zatabi diddigin tafiyar har ta san inda zashin. Hannuwanta ta sake tajuya tana ficewa don dauko masa plate din abincin data manta.
Tana saukowa daga stairs din hajiya qarama na shigowa falon,kallon kallo suka yiwa junansu, kafin hajiya garama ta buda baki da qyar tayi sallama. Kamar yadda tayi sallamar da gyar haka mansura ta amsa mata da gyar tare da dauke kanta, tazo zata wuce ta gabanta tamkar batasan da wanzuwarta a wajen ba. Matuga da gaske abun ya daure mata kai,don bata taba kawowa a duniya akwai lokacin da zaizo mansura tayi mata irin wannan abun ba
"Ina yaya yake?"
"Tunda kinsan kan gidan ai kinsan inda zaki sameshi" ta amsa mata da gatse, tunda ta sani aduk sanda tazo gurinsa itace ke shaida mata yazo din
"Idanma da gatse kika fada yanzun zaki ga cikar aikin irin na fauziyya" tana kaiwa nan ta kama stairs din tana hawa,hajiya mansura ta bita da kallon zallar mamaki baki bude.
Ya danyi mamaki da yaji ana knocking,ya miqe ya buda qofar, mamakinsa ya qaru da ganin fauziyya da safen
"Muje falo" yace da ita ha fito ya biyo bayanta. Nan falon saman suka zauna,yana qoqarin zama ta fashe masa da kuka
"Subhanallahi, lafiya me yake faruwa?" Hajiya Mansura da tayi gaggawar dawowa don taji abinda ke faruwa duk da tasan fauziyyan bata taba wata magana me muhimmanci tsakaninta da yayan nata a gabanta ba,ta saci kallon fauziyyan cikin sa'a suka hada idanu
"'Maganace ta ahali yaya,zan samu sarari?" Kai ya jinjina vana karbar plate din daga hannun mansura yana cewa
"Mansura bamu guri"
"Tom" ta fada zuciyarta kamar zata fado daga qirjinta saboda tsananin takaici. Shekara da shekaru har yanzu babu abinda ya sauya a irin wannan abubuwan dake faruwa,a wannan shekarar kadai ta soma gain abinda fauziyya ta nema dr jarma bai bata ba
AURAWA TOUFEEQ HASEENA.
"Me ya faru?" Ya sake tambayarta,sai ta sake sakin hawaye
"Ba shakka yaaya toufeeq ya auro yarinyar da zata rabamu dashi" mamaki ya kamashi
"Kaman yaaya? wai säahar kike nufi?" Kai ta jinjina masa
"Itafa,tun daga lokacin da tazo gidan komai ya canza,shi kansa toufeeq ya sauya,a yanzun ban isa da shi ba,sai abinda tace,hatta da gaisuwa bankai ta shigo ta gaidani ba,saidai idan mun hadu a compound na gidan" Shuru yayi hannunsa saman bakinsa yana mamaki, vasan wanne aure akayi da manufar auren dake zukatansu dukka su biyun,to yaushe hankulansu suka hadu guri guda har suka fara mu'amalar da mutum me taurin kai da kafiya irin toufeeq sahar zata fara juyashi ya soma daukan maganata?
"Yanzun me va faru?" Hawaye sosai ta matso
"Waini yarinyar zata kalla tace daga yau tanamin kashedin babu ni na fadeela, ta soke bata duk wata kulawa da nake bata,ta shiga ta fita ta canza komai har na makarantarta,abinci bata magani,hatta da daukan yarinyar yanzu babu wanda yake da wannan ikon idan ba ita ba,hatta kaita makaranta yanzun ta maidashi wuyanta". Ga mamakinta murmushi ne ya subuce akan fuskarsa yana dan girgiza qafarsa,cikin ransa aminci da gaunar sãahar tana ratsashi
"Banda abinki da rigima irin taki, kefa yanzun kin girma,da meye kikeson kiji? da shekarunki koda kasuwancinki koda kula da fadeela? ina cewa ke sauqinki ne ma,aiki aka rage miki da nauyi ko?" Sosai ta girgiza,amma kuma ba zata saare ba sai taga abinda ya turewa buzu nadi
"Haba yaaya,haba yaaya, ubanta ma nina raineshi bare diyar? ta yaya kawai don an aurota zamu sake mata kula da diyarmu haka sakaka? yadda yanzu duniya ta zama babu gaskiya,sai a hada kai da mutum a cucuka"
"'ah dakata fauziyya,duk ba za'a samu wannan daga sãahar ba ina kyautata mata zato, banda abinki meson naka ai shima naka ne,ki bar musu diyarsu don Allah, ki cire ranki daga wannan qanqanin abun,duka ba damuwa bane"
"Yanzu ba zata tsawatar ba kenan yaaya?" Murmushi ya saki yana girgiza kai
"A'ah ni bazan shiga wanna maganar ba, diyarsu ce, inda ace kina qorafi ne akan nadeeya to itace 'yarki sai kuma inda qarfinta ya qare" Boom ?? taji wani abu cikin kanta,karo na farko data fuskanci haka daga
gurinsa, bai taba ganin hawayenta ba ba tare daya zartar da abinda take muradi ba. A yanzun shurun da tayi ma
kamar bai fuskanci bacin ranta ba,janta ya shiga yi da
hira yana yi mata tayin abinci
"Alhamdulillah na qoshi, zan wuce gida na baro meenal
ita kadai,kasan kuma baquwa ce har yanzu"
"'Gaskiya ne ya kamata tazo tayi kwana biyu su saba da mamarta da yar'uwarta"
"Zatazo" ta amsa masa a taqaice,saboda ta qagauta ta
fita daga cikin gidan ko zata samu damar yin
kyakkyawan tunani akan yarinyar,sai takejin kamar wata masifa ce ke tunkarota.
System ya tura mata da tarin wasu ayyuka da zata
tattara masa bayanan guri guda. A nutse take aikin
tamkar ma bata office din, lokaci lokaci tana ji a jikinta
tamkar yana kallonta ne,amma kuma duk sanda ta daga kan nata don ta tantance sai taga idanunsa yana saman system.
Mintuna goma sha biyar kacal suka rage lokacin
break ya cika,har a lokacin bata motsa ko ina ba tana zaune tana gogarin tattara aikin da ya bata hatta da wayarta ma a kashe take, don batason tayi wani abun ma da magana zata shiga tsakaninsu.
A karo na barkatai ya sake satar kallonta, shi kansa
bazai iya tuna wani abu a rayuwarsa da ya yiwa adadin satar Kallon da yayi mata ba ba tare da shi kansa vasan satar kallon yake ba. Dai dai lokacin data zura hannuwanta ta cikin lafayar ta kuma bayan wuyanta tana gogarin tattare gashin data nannade, santsinsa ya sanya ya ware da kansa yake kuma damunta a wuya. Hakan ya baiwa laffayar damar zamewa, lallausan gashin nata dake da wani irin bagi da daukar idanu ya ware a kafadarta ta hagu. Tana qoqarin mayar da mayafin kira ya shigo ta wayar office din. Ta daga kai zata kalleshi suka hada ido, basarwa yayi cikin shan gamshi va kuma hade rai sosai, don bayason ta fahimci tun ba yanzun ba idanunsa ke kanta
"Kin manta aikinki ne?" Ya fada a dake,har ta dan juya
idanunta zata sauke masa harara sai tayi saurin gyara
kallonta,tayi rolling qwayar idanun tamkar me yin fari.
Wani irin ayalli idanun nata suka bada,a dole ya rusunar da kallon nasa daga kanta. Migewa tayi a nutse ta isar ga wayar ta daga,ta kara a kunnenta tare da yin sallama da nutsatsiyar muryarta me sanyi da taushi. Cak ya tsaya daga singing din da yakeyi sautin yana shigar masa kunne
"Idan kuma namiji ne fa?" Yaji tambayar ta fado a ransa,sai ya rige biron a hannunsa yana juyashi tare da son tsinkayo muryar waye a wayar.
"Ma sha Allah, ina fatan Khadija Muhammad girema ce?"
Mamaki ne qwarai ya kama sãahar, ta yaya za'a yi kira a wayar office office din da ba nata ba amma farat daya a kama sunanta?
"Eh itace"
"Good,na buga dai dai kenan.....kina magana da
Ameesha,ex_wife din mijinki muhammad
toufeeq,maama ga FADEELA" sosai ta gyara tsaiwarta ba tare da tace komai ba
" Zuwa yanzu nasan fes kin fahimci wacece ni din"
"Me kike bugata" garamar dariya ta saki
"Naji dadi dana sameki me saurin fahimta,hakan na nunamin bazan sha wahalar fahimtar dake lokaci yayi na dawowata gida na ba"
"Dashi ya kamata ku garasa wanna maganar" tà gintse ameesha din daga abinda ta kira da soki burtsu a waienta. Waiwayawa tayi gareshi bayan ta dauke wayar daga kunnenta suka hada ido dashi, idanunsa zube fes akan fuskarta yana son ya karanci wani abu. Bata bashi dama ba don dauke kanta tayi, ta qarasa gabansa ta rangwafa daga saman table din tana gyara masa zaman wayar a gabansa,wannan ya baiwa ragowar gashin kanta damar qarasa warwarewa,iskar dake shigowa daga window ta buso masa dukkan gamshin dake magale a jikinsa harda tsarabar shafar gefan fuskarsa. Ido ya lumshe a hankali yana jin yadda zuciyarsa take bada wani sautin bugu, sanda zai bude idon harta ja da baya tana sanya takalmanta ba tare data dubeshi ba tace
"'Baguwa keson magana da kai" bata tsaya sauraronsa ba ta dauki hand bag dinta da wayarta ta fita daga office din.
Kamar zaman jiran ganin me shiga da fita daga office din saima tayi tana fitowa suna hada ido,saita dauke kai tana nufar living room dinsa dake cikin office din. Ta dora hannunta zata murda handle din living room din sai aka budo ainihin gofar da zata sadaka da sashen saima. Sai ta waiwaya tana duban qofar.
Sanye take da wata gown na Vintage clothing, saman kanta lullube da siririn scarf data nadeshi daga kanta zuwa wuyanta kawai,fiye da rabin fuskarta sun glasses ne ya mamayeshi, sai wani rufaffen takalmi me tudu data sanyawa qafarta, daya hannun na maqale da hand bag yar mitsil, daya hannun kuma wani foldable basket ne da aka shirya qananun warmer's masu kyau a ciki. MEENAL YA'AQOUB AJI kenan,sananniya ga duk me ta' ammali da kafofin sada zumunta,wanann dalilin ya sanya saima miqewa tsaye cak suna kallon kallon a tsakaninsu. Koda batace ba tasan gurin toufeeq tazo,don duk wanda ya santa,yasan ita daya ce tallin tal dake wallafa hotunansa kusan koda yaushe saman shafukanta na sada zumunta. Batayi mata kallo na biyu ba ta murda gofar room din ta shige ta barsu suna kallon kallo tsakaninta da saima.
"Madam ina zuwa haka?" Saima ta tambayi meenal cikin gatse. Dawowa tayi da baya tayi qasa da glasses dinta ta qarewa saima kallo,sai ta saki wata dariyar rainin wayo
"Jealousy"' ta fada cikin nishadi sai kuma ta dora
"Zanyi mamaki gwarai idan kikace wai baki sanni ba…
Meenal ta fada cikin izza da jin cewa ta kai ta kawo ta kuma shirya gogawa da kowa akan TOUFEEQ,tasan da saima already tasan kuma zaman me takeyi a gurin…
[22/09, 10:23 am] +234 703 451 7171: *HUGUMA*
* TABARMAR KASHI_*
No comments