Tabarmar Kashi Book 2 Page 16

 


* TABARMAR KASHI_*


Book 02 Page 16








Ko a fuska ba zaka taba zaton karantar tata yake ba,har zuwa lokacin da maji ta magantu


"'Ki saki ilkinki dani khadijatu,ina jinki ne tamkar moha da nadeeya,ke yanzun diyata ce halak malak,zan iya raba kowacce damuwa tawa da sirrina dake" garamin murmushi ta saki tana jinjina kai. Tabe baki yayi kadan yana matsawa gefe daga gaban kwanukan alamar ya qoshi,duk wadan nan abubuwan gani yakeyi kawai salo ne irin na mata wanda kaidinsu ba qarami bane,sai yanzu ya karanci dalilin da ya sanya dukkansu ta tafi da hankalinsu,cikin ransa yake gulmarta,ta wani sadda kai qasa,tamkar ba itace wannan mara kunyar ba me shegen tsiwa dake iya yarfa masa maganar da duk duniya ba macen data isa ta gaya masa bayan maji


"Ban baku kowacce gudunmawa ba ko?" Maji ta fada tana murmushi,a nutse toufeeq ya waiwaya ya dubeta


"Wacce iri maji?"


"Ta aurenku mana" kasa cewa komai yayi,don baisan wacce gudunmawa kuma maji keson bayarwa ba bayan dukka abinda tayi da uwar kudaden data kashe,tamkar zaiyi auren fari ne ko kuma auren autarta nadeeya takeyi. Wani envelope ta ciro ta ajjiye a tsakaninsu


"Maldives, turkey Malaysia,su sajjad ya zaba muku as Honey moon destination" bashi

daya ba,hatta da sãahar sai da taji gabanta

ya fadi,yayin da toufeeq din yaji abun gazo

masa a mugun ba zata,yayi imanin akwai

gudunmawar sajjad a zancan,tunda yafi

kowa sanin abinda ke gabansu,duka duka

da niyyar yij sati hudu kacal wato wata guda

yazo,amma gaddarar da baisan da faruwarta

ba ta rigeshi har yayi watanni biyu. Bayajin zai

iyayin wannan tafiyar da yarinyar,ya dauketa

duk inda suka shiga suna tare idanuwa a

kansu,dauriyarsa ta qare don haka a tausashe

.ya hada envelope din da hannun maji ya riqe

cikin nasa hannun


"Indai bakiyi booking ba sannan baki biya

kudaden ba ki zaremu a ciki please maji,na

tara ayyuka da yawa da suke jirana,inason na

idasu cikin watan nan" idanu ta sanya masa

sosai tana kallonsa tare da gasgata zarginta


"Moha,sabon aure fa kayi,akwai Cabinda

yakai iyalinka muhimmanci?" Kai ya girgiza a

tausashe


"Ba haka nake nufi ba maji,koma inane kikeso taje din zata je,amma a yimin uzuri na kammala ayyukan gaba na,zan biya da kudina na kaita ko ina ne ma indai yawo ne,amma kinga tun yanzun bai kamata nabar ayyukana na tafi ba" ran sãahar ya dan sosu,indai yawo ne wato gata shanshani wadda bata taba hawa jirgi ba.


"Shikenan,amma wannan tafiyar bata soku ba,koma wanne aiki ne ka kammalashi nan da watanni biyu kacal zaku tafin, daga nan inason ku sauka a Algeria"


"In sha Allah" ya fada yana lumshe idanu yana jin nutsuwa na saukar masa ta yadda yayi nasarar soke tafiyar ba tare da wani dogon turanci ba,yasan ya taki sa'a ne kawai,amma maji har yau tana nan a yadda ya santa tun yana da gananun shekaru.


A nutse ya bude fararen idanun nasa,baisan yadda akayi ba suka sauka saman fuskarta.

Tsaf ta gama fahimtar manufarsa ta soke tafiyar,koda baiyi hakan ba ita sai tasan yadda ta bulowa maganar ta rushe,don ko dogon zama ba zata iya yi dashi ba bare doguwar tafiya ta satittika,idan kowa baisan me ya dawo da ita gidan ba,ita da shi duka sai sun sani. Cikin jikinta tai idanun nasa saman fuskarta,wani abu ne da ita kanta batasan ta yadda yake faruwa ba,a duk sanda yake kallonta sai taji a jikinta,tun haduwarsu ta farko. Nata kewayayyun idanun masu cikar eye lashes ta daga,sai suka hadu guri daya da nasa,sai ya basar yana shirin kau da kallonsa,saidai kuma hararar data watsa masa ya sanyashi kasa aiwatar da hakan. Take ransa ya sosu,mamaki kuma ya cikashi. Ita ba abinda ta iya daga tsaki sai harara?,me yasa ta maidashi kamar sa'anta,da gaske dai ya fuskanci sai yayi maganinta ya saita zamanta.

Tarko ya sanya mata da idanun nasa,saidai tunda ta harareshin bata sake waiwayowa sashensa ba,hasalima ta maida hankalinta kan maji dake magana da ita qasa qasa.


Migewa yayi cikin nutsuwar nan tasa yana ware hannun rigarsa da nufin fita yabar musu dakin,saboda yadda maji din ke magana da ita kamae bataso yaji ne. knocking qofar akayi,maji dake gab da säahar wadda kanta ke a sunkuye tace


"A shigo" A hankali aka murda handle din gofar aka turo aka shigo tare da sallama.


Ba maji kawai ba,hatta toufeeq yayi mamaki qwarai da ganin mahaifinsa dr mahmud kai tsaye cikin dakin. Tsakanin toufeeq da sãahar ne kadai aka amsa sallamar banda maji da ta dauke kanta gefe kamar bata ga shigowarsa ba,ta kuma tsuke fuskarta,wannan kyakkyawan murmushin dake saman fuskarta ya bace bat. Sanye yake da wani irin yadin cashmere da aka yiwa dinkin manya,riga da wando 'yar ciki me dogon hannu,sai wata a sama kamar gown ta maza me gajeran hannu

Tun daga rigar cikin wandon da kuma gown din aikin hannu na sarauta aka zauna aka zuba masa me matugar daukan hankali da masifar tsada,saman kansa hular dara ce maroon color. Ya sake fitowa sak mahmud din data sani shekarun baya da suka shude,matashin saurayin da ya zuba tashen kyau da farinjinin

'yammata wanda take da imanin a yanzu shi toufeeq ya debo,abu daya ya dakushe wannan a wancan lokacin,akwai wadatar kunya me tarin yawa ga 'yammatan wancan qarnin ba kamar yanzu ba.


Gurin zama toufeeq ke gyara masa,amma dukka idanunsa da hankalinsa suna kan majin,wadda ita dinma babu abinda ya sauya daga gareta tsahon shekaru ashirin da bakwai da suka shude sai shekaru kawai da suka dan nuna kansu kadan.



* HAJIVA OARAMA_*



Tunda gari ya waye bata zauna ba,sai data tabbatar an kammala shirya breakfast na alfarma a babban dining din dake sassanta,bayan an kimtsa ko ina ta tabbatar komai yayi yadda ya kamata sannan ta shiga wanka ta shirya kanta cikin wani Swarovski lace dake ta fidda walwalin Swarovski crystal dake manne a kowanne pattern na lace din.



Ta riga ta sani ma,koda bata fadi ba kamar wancan auren nasa,a nan zasuyi breakfast shida matarsa kafin ya shiga kowanne sashe na gidan,don haka ta shirya ta koma falo ta dauki wayarta tare da saka me aikinta ta canza mata channel tanata dakon shigowarsu. Tun tana chart a wayarta don rage lokaci har ta gama lissafe lissafenta ta maida hankalinta ga tv tana dan bibiyar program din da akeyi din.

Sannu sannu ta fahimci lokaci yana tafiya,ta duba wayarta ko zata ga kiran toufeeq amma babu komai,mamaki yadan kamata,to me yake faruwa? aure dai ba na soyayya bane bare tace itace ta hanasu fitowa. Zuciyarta nata yi mata kokwanto ko yana wajen uwarshi?to amma batajin hakan zata faru,saboda sam babu wannan sabon a tsakaninsu,hasalima yaushe rabonsa da ita da har zai iya wuceta ita ya tafi gurinta? har ta dauki wayar zata kira taji alamun bude gate din gidan,dai dai shigowar 'yar aikinta,sai ta maida dubanta kanta


"Waye ya shigo?"


"Boss ne" ta amsa mata cikin girma mawa,maida wayar tayi ta ajiye ta fasa kiran toufeeq din,don tayi amanna nan din Dr jarman zai fara shigowa,kuma dole toufeeq din ya biyoshi.


Duk bayan minti daya sai ta kalli agogo amma bataji shigowar yayan nata ba kamar yadda ya saba yi a duk sanda ya kawo ziyara gidan,duk da cewa abune mawuyaci ka ganshi a gidan. Zuwa lokacin haqurinta ya gaza,ta kasa jurewa,sal ta miqe tsaye tana gyara daurin dankwalinta hadi da qwalawa me aikinta kira tace ta rigo mata wayarta ta biyota da ita.


Tabbas Dr jarma ne ya shigo,don ga galla gallan motocinsa da vake amfani dasu nan guda hudun a fake a parking lot na gidan.


Abun ya sake daure mata kaita maida dubanta ga sassansu fadeela. Gabanta ne taji yadan fadi,saboda jikinta ya gama bata yana can,don son tabbatarwa saita nufi sashen kawai kai tsaye.


A parlor din farko ta samu baaba ramatu tana qarasa kintsa dan abinda bai gama gyaruwa ba a sashen, kasancewar yadda tsafta ta ratsa kowa cikin gidan harta da ma'aikata maza da mata,basa barin koda tsinke a waje bare qura


"Yaaya ya shigo?" Ta tambayi baaba ramatu kai tsaye


"Eh suna ciki"


"Shi da wa?" Ta tambayeta fuskarta adan

yamutse


"Toufeeq amarya da alhaji sai hajiya maji"


"Danqari" ta furta har yana furucin nata yana fitowa fili. Daga kai baaba ramatu tayi ta kalleta,suka hada ido,sai hajiya qaraman ta basar kamar ba ita tayi maganar ba,ta sanya kai ga hanyar da zata kaita qaramin falon sassan gidan wanda daga can sai hallway na bedrooms dinsu. Kai baaba ramatu ta girgiza


"Allah ya kyauta" ta furta qasa qasa taci gaba da aikinta, zuciyarta cike fal da mamakin dabi'un fauziyyan da har yau suka gaza sauyawa.

Ganin idanun TOUFEEQ da sãahar dake a mazaunin suruka yanzu a gurinta shine kadai abinda ya sanya ta gaidashi da harshen larabci a taqaice,kamar yadda suka saba shekarun baya da suka shude. Wannan abunne yayi masa mugun fami hadi da tuna masa wani lokaci can baya. Majin ta mige zata fice tana

cewa "'dan kun gama Khadija ki sameni a falo mu qarasa ko?"


"Da kinyi haquri kin koma kin zauna akwai maganar da zamuyi" Dr jarma din ya fada a tausashe,wanda shi kansa baisan da haka yayi maganar ba. Cak hajiya qarama ta tsaya tana jin qirjinta yana bugun uku uku,sautin da yayanta yayi magana da maji din a yanzu,wani tsohon sauti ne da yake mata amfani dashi a shekarun baya idan yana son lallashinta.

Wai meye yake faruwa ne?,sannan wacce magana ce da yau yayan nata ya hada iyalinsa,harda bare aurowar jiya amma ita babu ita aciki? koma meye za'a tattauna din ba zata iya Jurewa a tattauna ba tare da ita ba. Sai data dorawa fuskarta fara'ar dole sannan ta buda qofar dakin hade da yin sallama. Maii itace ta farko da idanunsu suka fara haduwa waje daya. Dauke kai maji din tayi kamar yadda ta yiwa dr jarma din da a yanxun ma ya samu nasarar dawo da ita ya zaunar duk saboda idanun mutum biyun dai,toufeeq da SÄAHAR

Sam bata ko gaunar jin muryar fauziyya a rayuwarta bare ganin gilmawarta,itace silar da har yanzu take zaune ba tare da wata gagarumar katangar dake qara cikasa daraja da kimar diya mace ba wato AURE,ko tuna abubuwan da fauziyya tayi mata a rayuwa batason yi,amma duk da haka tana godiya ga

Allah da ya bata wasu damarmakin,duk da wasu sun subuce mata,amma still har yanzu tana rige da lambar mutum ta farko data zamewa fauzivya qadangaren bakin tulu,tsare tsarenta suketa tafiyar wahainiya,wasunsu ma su gurgunce ba tare da sun cimma gaci ba


"Ashe duk kuna nan,abun na ahali ne,ko mu koma?" Ta fada da sigar tambaya.


"A'ah,qaraso mana,you are the part of duk tattaunawar da za'a yi din" dr jarma ha fada yana fidda gyara zamansa,har yanzu idonsa na kan maji din wadda ta baiwa banza ajiyarsu shida 'yaruwar tasa.


Guri ta samu ta zauna a tsakaninsu,a sanann majin ji tayi kamar ta miqe ta fice a wajen,to amma kuma yin hakan kamar bada qofa ne ga fauziyya,so far kuma ita din tana jin a shirye take akan sake maido yaranta ilkinta,wanann na daya daga cikin boyayyun dalilan da yasa batabi ayarin family dinta da sukazo biki sun koma tare ba.


Kamar yadda suka saba toufeeq ya gaidata,tayi gogarin gagaro murmushi


"'Lafiya lau ango,idonka kenan?" Gaisuwar da sãahar ta migo ita ta katse tuhumar da take masa ta sigar tambaya a fakaice. Wani irin shu'umin kallo tayi mata,tadan kada qafarta kadan


"Amarsu,lafiya ya kwanan baqunta?,koda yake

ma ai 'yar gida ce na manta" ta furta tana sakin wani murmushi me dauke da ma'anoni da dama,gasan ranta kuma zuciyarta ke

sake cika da alwashi da algawura iri iri akan sãahar din,sai ta biya baqincikin da ta sanya ta kwana dashi a jiya sanadiyyar maida mata maaganganun da tayi. Maida dubanta tayi ga

yayan nata Dr jarma tana gaidashi.

[16/09, 7:18 pm] +234 703 451 7171: *HUGUMA*

No comments