Sakayyah Book 2 Page 5

 

 






        Na



*Aysha Aliyu Garkuwa*



 



 



Runtse idanunsa yayi da karfi, tare dasa hannunsa duka biyu
ya matse kansa, sabida yadda ya fara jin 
kansa yana juyawa tare da sarawa, yayin da kalaman Hajja Nana ke dukan
tsakiyar ƙoƙon kansa yana ratsa ƙwaƙwalwar kansa tare da jin suna ratsa
kunnuwansa suna yawo tamkar yanda aradu ke yawo asararin samaniya, baki ɗaya
idanunsa sun juye sun kaɗa sunyi Jawur, kab ilahirin jikinsa rawa yake
kar-kar-kar tamkar mazari cikin wani irin sauri zuciyarsa ke bugawa da kaso
Cassa'in da tara cikin ɗari, tana mai wanzar da jini litter-litter a cikin
dukkan daƙiƙu yana watsashi wa jijiyoyin jikinsa.



Hakan yasa tuni rigarsa ta fara jikewa da zufa, duda yanayin
garin Gembila da ba'a musu zafi.



Sai ga tashin hankali ya sashi tsats-tsafo zufa sabida yadda
zuciyarsa ke bugawa da Masifaffen ƙarfi yayin da numfashinsa ke fusga tamkar
zai bar ganganar jikinsa, cikin tsanananin tashin hankali da wani irin
masifaffen juyi da kansa keyi ya ƙara matse kansa da hannu bibbiyu, da ƙyar ya
iya daga ƙafarsa ya sauka daga barandar ya nufi side ɗinsa yana tafiya tare
tangaɗi tamkar ɗan maye yayin da kuma jiri ke ɗibarsa.



 



Yana cikin tafiya tamkar zai faɗi ya tsinkayo muryar Innayi
cikin tsananin fushi da takaici cikin zafin zuciya tace.



“Zaki sha mamaki kuwa.



Hajja Nana zan nuna miki ƙarfin iko da isan ɗan shegen da
kike faɗi. Zaki gane kinyi kuskure ambatonsa da wannan sunan da yafi ƙarfinsa.
Auren nan kuma da izinin Ubangiji tamkar anyi sa angama ma, in dai wannan auren
nen kika tashi ki kace zaki yaƙesa sannan kika ce zaki hana toki sa. Aranki
anyishi an ɗaura shi angama domin ke dai baki isa ki haramta abinda Allah ya
halastaba wlh muddin ina raye toh in Sha Allah kamar ma anyi auren nan an gama
zan shayar dake mamaki”.



Wani irin kallon rainin hankali me ɗauke da zafin zuciya
Hajja Nana tabi Innayi dashi.



Ita kuwa Innayi. Cikin fushi ta cigaba da cewa.



“Babu wani mahaluki na duniya daya isa ya hana wannan ɗaurin
Auren sai Ubangiji daya halicci sammai da ƙassai. idan har kinga wannan Auren
bai kasance ba to daga Rabbus Sanawati ne amma ba daga ke Hajja Nana mai kaɗa
kai kamar Ƙadangariya ba”.



Wuhuhu ina wuta Hjja na ta faɗa ciki.



Cikin fushi da hatsala Hajja Nana dake ƙoƙarin fita ta tsaya
tare da juyawa ta kalleta sai kuma tayi murmushi tare da gyara tsayuwar ta kana
tace.



“Wani ƙarfin iko ko kuma isa. Ɗan shege ke dashi? Ai sai dai
kuje kunemi watsatstsiya ƴar gaba da Fatiha ku Aura masa, amma dai ba jikata
dake da asali da tushe ba  zuri'ata tayi
miki nisa sai dai hange daga nesa?”.



Afusace Innayi da Idanunta suka kaɗa tamkar garwashi tace.



“Tabbas zaki ga isa da kuma ƙarfin Iko irin na ɗan shegen da
kike faɗa agaban idanunki za'a ɗaura Aurensa da Khausar sannan ya ɗauketa su
tafi ke babu yanda kika iya, zakisha mmkin ganin tushensa daya girmi tunaninki
ya kuma zarta zatonki. domin ke ba kowa bace a kansa,  Allah ya wadaran aminiyar da bata mutunta
amintaka, kin kasance mara ɗa'a da sanin ya kamata!”.



Ita kuwa Hajja Nana mugun kallo ta watsawa Innayi tare da
nuna kanta da tsaya kana tace.



”Ni kika faɗawa haka?”.



 



Kai Innayi ta gyaɗa cikin tsawa tace.



“An faɗa miki wacece ke?Ko kina tunanin nan ma Jauro yaya ne
da kike baza ikon ki da mulkinki kina kaɗa kai uwa ƙadangaruwa, kina abinda
kika ga dama? to a hir ɗinki ki sani kece kika shigo muhalli na toh ki sani duk
da cewa mu muke neman aure a ƙarƙashin ku ba za ki taka muba in barkiba domin
mace bata bada Aure dan haka ki ficemin agidana”.



Wani irin dogon tsaki taja kana tace.



“Ko da baki ce in fice miki agida ba dole zan fita, amma
kisa Aranki badai.



 Ɗai shegen jikanki da
tsarkakakkiyar jikata su haɗa Aure ba”.



Tana faɗin hakan



ta ida ficewa daga ɗakin amma still Idanunta na cikin dakin
tace.



“Dama ace ansan tushe ansan asalinku sannan ansan jikan ki
tsarka kekkene wanda aka haifa ta sunna, to ba komai amma jikanki da yake
Najasa wanda aka haifa ta hanyar ƙazanta ba zaiyu abashi auren jikata ba, zaki
ga ƙarfin Ikona da isata sannan kuma da Izzata akan al'amarin auren nan”.



Innayi da zuciyarta ke wani irin tafarfasa tace.



“Toh mu zuba mu gani kada ki fasa idan har ke kin cika mai
karfin iko da Izzah”.



Ƙwaffa Hajja Nana tayi tare da sauƙa daga barandar ta juya
fuuuu kamar zata tashi sama ta nufi waje.



 



 Moddibo kuwa  yana shiga falonsa ya maida ƙofar ya rufe,
kana ya zame tare da zama aƙasan daɓas ya jingina bayansa da jikin ƙofan Falon
lokaci ɗaya yashiga kokuwa da numfashinsa dake ƙoƙarin ɗauke wa.



 Atake wani irin azabebben
kuka mai gunji ya kufce masa cikin raunin murya da tsantsar tashin hankali ya
shiga furta.



_“Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha Ya
wadud³ ya zul'arshil Majeed ya fa'alillima yurid As'aluka bi izzatil lati
layura wa mulki kallazi la yurad Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n_”.



Cikin wani irin tashin hankali ya cigaba da karanta duk wata
addu'a da tazo bakinsa.



 Kana wani  azabebben kuka mai sa rawan jiki ya sake
kufce masa lokaci ɗaya wani masifaffen zazzaɓi ya rufe sa cikin kiɗima ya fara
zantukan zuci. Aransa yace.



Innalillahi Wa'inna ilahi rajiu'n. Shin wannan wace irin
Masifa ce? wani irin rayuwa ce take fukantoni! sannan inane tushena.



Ko-ko dai da gaske ne kalmar wannan matar gskyace, cewa bani
da asali.”



Sai kuma ya rumtse idanunsa da ɗan karen ƙarfi.



Tare da fara ƙanana mgn a saman lips dinsa dake tsuma.



“Hahhhh da ƙamshin gaskiya acikin kalaman matar nanfa, domin
da inada tushe da asali da tuni Innayi ta kaini garesu sannan ta nuna min
tushena shin da gskene kenan bata hanyar aure sunnanr Manzon Allah Sallallahu
alaihi Wasallama aka samar da niba Yah salam.”



Sai kuma ya fara mgn cikin rawan murya.



 “Ya Ubangiji Allah
kada kasa zargina da zatona na tsawon shekaru ya tabbata ta wajen furucin
wannan matar.”



Ya ida mgnar tare da kife kansa bisa guiwowinsa.



Domin shi akaran kansa ya daɗe yana tunanin wataƙil shi ɗan
shegene shiyasa Innayi bata taɓa faɗa masa Asalinsa ba kuma bai taɓa ganin wani
saba dangi na gefen uwa ko uba, ya kuwa san bazai taɓa yiwuwa ace kab duniya
bayi da wani ɗan uwa ko ƴar uwa da za'ace nase sai dai in har shi ɗin ɗan
Shegen ne, shiyasa Akullum yake tsoron tambayarta wanene shi domin kada yaji
abinda zai tarwatsa masa ƙwaƙwalwarsa da kuma lissafin sa sabida tsoron hakanne
yasa baya bincike kan tushensa sabida shi kansa ya fara zargan lamarin.



Lumshe Idanunsa yayi hakan ne ya bawa hawayen ciki damar
kwaranyowa da masifar zafi suka zubo masa, cikin ransa yace dama nasani dole
irin wannan ranan zai zo ranan da wasu mutane zasu fuskance mu gaba da gaba su
tuhumi nagartata. sannan su kirani da shege idan har basu samu gamsasshiyar
amsaba. Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.



 



Hajja Nana kuwa Afusace ta fita daga gida tare da buga
Murfin gate din tana zuwa ta buɗe motar tashiga tana wani irin huci na tsananin
ɓacin rai da takaici kallon Baffa Jimeta tayi kana tace.



“Mu tafi baki ɗaya mutanen cikin wannan garin basu da
hankali basu san abinda suke yiba”.



Cikin sanyin murya Baffa Jimeta yace.



“Subhanallah Hajja Nana kada kice haka kada kiyiwa baki ɗaya
mutanen garin nan kuɗin goro sam hakan be cancantu ba”.



Harara ta watsa masa kana cikin fushi tace.



“Rufe min baki kaja mota mutafi bana son maganar banza”.



Kai ya gyaɗa kana yayiwa motar key suka bar kofar gidan kai
tsaye hanyar Jauro yaya suka nufa.



 



Anutse Malam Liman ya juya tare da kallonta kana cikin
sanyin murya yace.



“Kiyi haƙuri Hajja Nana ita rayuwar nan na duniya komai sai
da haƙuri ake fuskantar sa, abinda fa hakuri bai warware saba tofa rashin
haƙuri ba zai warware saba, dan Allah ki kwantar da hankalin ki koma menene
Khausar tayi yarinya ce bazaki sa shi amizani da zai tayar miki da hankali har
haka ba”.



Cikin sauri Hajja Nana data tsirawa madubi ido ta juya ta
kallesa kana cikin fushi tace.



“Wai Ni Khausar zata dubi tsabar Idona tace bata son Aliyu”.



Anutse Baffa Jimeta dake driving ya dan juya tare da
kallonta kana cikin sanyin murya yace.



“Toh Hajja Nana menene aciki dan Khausar tace batason Aliyu
ainima kaina bazan yiwa Khausar auren dole ba, duk da cewa Aliyu ya kasance ɗana
amma bazan tauyeta in Aura mata shi adole ba tunda bata son shi”.



Afusace Hajja Nana ta buga masa tsawa tare da faɗin.



“Rufe min baki me kake nufi kenan?”.



Ahankali ya sassauta muryarsa cike da girmamawa yace.



“Hajja Nana kiyi haƙuri ki gafarceni Idan har abinda zan faɗa
zai ɓata miki rai, amma abinda nake nufi a aura mata wanda take so.”



Sheƙeƙe Hajja Nana ke Kallonsa da Idanunta dake cike da
Masifa cike da iko da kuma Izza tace.



“Wannan ne kuma baku isaba ba'a haifi wanda ya isa ya
ƙaddamar da wannan abin ba”.



 



Ajiyar zuciya Baffa Jimeta ya sauƙe tare da kallon Baffa
Liman daya tsirawa titi idanu kana ya sake sassauta muryarsa tare da cewa.



“Dan Allah Hajja Nana ki gafarceni Ayiwa yarinya abinda take
so”.



 



“Bafa ku isa ba”.



Ta faɗa a taƙaice.



Kai Baffa Jimeta ya gyaɗa batare da yace Uffan ba ya cigaba
da Driving.



Ahankali Malam Liman ya sauƙe Ajiyar tare da juyawa ya
fuskanci Hajja Nana da kyau kana yace.



“Adda Hajja to dan tace batason Aliyu shine hankalin ki ya
tashi haka?”.



Sake baki Hajja Nana tayi tare da cewa.



“Au don ne ma kake cewa, wato baka ɗauki abinda muhimmanci
ba, wannan ɗin bai kai hankalina ya tashi bane?Sannan ma wanda tace tana so ɗin
dama ace mutum me tushe ne da asali to ai da sauƙi”.



Dogon numfashi Malam Liman yaja tare da sauƙewa kana yace.



“Toh waye ne tace tana son din ne?”.



Dogon tsaki Hajja Nana taja tare da yin ƙwaffa kana tace.



“Wai wani Malamin Makarantar sune, Moddibo ne ko Momodu
ne  ohon mata, wannan yaron dai da Malam
Arɗo yaje dashi Jauro yaya ashekarun baya sannan akwanakin baya muka je muka
sameshi agidan Malam Arɗon tofa wai shi take so”.



Jinjina kai Malam Liman yayi alamun ya gane.



Ita kuwa cike da takaici ta cigaba da cewa.



“Toh Jikan wannan Ƙawar tawa Innare, kuma sanin kanku ne
tunda nasha baku labari cewa babu wanda yasan asalinsu, sannan babu wanda yasan
tushen su a iya binciken da nayi a iya sanin su da nayi muke zuwa Makka tare
yaron nan ɗan shegene”.



Cikin sauri Baffa Jimeta dake Driving ya juya ya kalleta jin
furucin daya fito daga bakinta.



 



Harara ta galla masa kana ta cigaba da faɗin.



“Ɗan shegene bashi da asali ɗane da aka haifeshi ta hanyar
zina ta ƙazantacciyar hanya, shin taya zamu haɗa alaƙar aure dashi kalen ya
lalata mana sunan zuri'a asamu abin faɗa aciki.



 



Girgiza kai Malam Liman yayi kana ahankali ya juya da
fuskarsa gareta ya fuskanceta sosai yace.



Um-uhum kiyi haƙuri Addah Hajja kada ranki ya ɓaci”.



Girgiza kai tayi tana huci tace.



“Ai dole raina ya ɓaci Liman”.



 Gyara Alkyabbar sa
yayi kana yace.



“Dan Allah kiyi haƙuri amma kada ki sake aibanta yaron,
domin koda maganar ki hakan take, sam bai da ceba duk da cewa kin bada hujjarki
akan cewa shi shegene, tofa koda ya kasance shegen ba laifinsa bane, laifin
Iyayensa ne da suka haifesa ta hanyar zina”.



Tallafe kunci Hajja Nana tayi tare da tsira masa ido babu
keftawa, Malam Liman kuwa cikin sanyin murya da son nusar da ita ya cigaba da
cewa.



“Sannan babu inda Shari'a ta hana Auren wanda aka haifesa ta
hanyar zina.



  Shari'a bata haramta
Aurensa da Khausar ba, bai haramta ba a musulunci sai dai idan har akwai wani
na ƙasu atare dashi wanda yake aikatawa shine zai zama lalura, sannan dan Allah
irin wa'annan kalaman idan zaki furta su ki rinƙa tauna su saboda suna da
nauyi”.



 



Atsawace ta kallesa kana tace.



“Liman Karka fara yimin wannan wa'aze wa'azen'kan nan masu
sauya ra'ayi mutum”.



Cike da ladabi malam Liman ya sunkuyar da kansa ƙasa kana
yace.



“Dole ne in fara yimi ki wa'azi, domin kada ki faɗa cikin
furucin da zai kaiki ga fushin Ubangiji”.



Salati ta rafka tare da riƙe haɓa kana tace.



“Ikon mai duka Fadar gaskiyar ne zesa in fada cikin fushin
Ubangiji, ko kuma yana da Uban ne ai tun yana jariri yana cikin tsumma da ka
gani kasan cewa ƴarta ce ko ɗanta ya haifo shege ya kawo mata shiyasa ta gudu
dashi saboda abin kunya yau tsawon shekara talatin harda ɗoriya kenan bata da
wata ƙawa sama dani amma koni bansan tushen suba, bansan asalinsu ba sannan
bansan daga ina suke ba”.



Girgiza kai Malam Liman yayi kana yace.



“Kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki amma. Duk da haka
Addah Hajja baki da hujjar shegan tasa”.



Cikin sanyi ya cigaba da yi mata nasiyya yana nuna mata
kuskuren abinda take amma firrr Hajja Nana taƙi sauraronsa. Baffa Jimeta kuwa
Uffan bai sake cewa ba har sukayi nisa da tafiya.



 



Ɓangaren Moddibo kuwa wani irin zazzafan zazzaɓi mai zafin
gaskene ya lulluɓe sa wanda gaba ɗaya ilahirin jikinsa ke rawa.



Innayi dake tsaye ɗaki ma baki ɗaya jikinta rawa yake  sai Safa da marwa take daga ƙarshe ta zame ta
zauna kana ta fashe da kuka cur-cur-cur tamkar ƙaramar yarinya cikin Muryan
kuka tace.



“Bansani ba Aliyu bansan wannan abin zai zame maka tabo ba
acikin al'amuran kaba, bansan zai zame maka na ƙasu da kuma abin nunawa acikin
al'amuran kaba Aliyu”.



Cikin tsanananin tashin hankali da tarin damuwa take
maganganu tana zubar da hawaye.



 



Acan ɓangaren Abba kuwa bayan sun gama waya da Moddibo
number Malam Ahmad yayi dearling jin yayi Picking yasa yayi gyaran murya tare
da sallama kana suka gaisa bayan sun gaisa Abba ya sauƙe ajiyar zuciya tare da
gyara zamansa kana cikin sanyin murya yace.



“Dan Allah Malam idan anyi sallar La'asar ko zan samu
ganinka?”.



Cikin daddataku yace.



“Toh badamuwa Insha Allah zanzo, Allah dai yasa lafiya?”.



Jinjina kai Abba yayi tare da faɗin.



“Eh babu komai Allah ya kawo ka lafiya”.



Bayan Malam Ahmad ya katse kiran ya juya ya kalli Ummi dake
gefensa kan 2sitter sai kuma Asma'u da Bashir dake kan 3sitter cikin sanyin
murya yace.



“Abban Jameelu ne ya kirani”.



Cikin alamun damuwa Ummi tace.



“Lafiya kuwa!?".



Kai ya gyaɗa tare da cewa.



“Lafiya lau”.



Girgiza kai tayi hawaye na taruwa akwarmin Idanunta tace.



“Ka dai ƙara tabbayarsa”.



Ganin bata gamsu bane yace.



“Toh bari in tambayan”.



Ya ida maganar tare da dearling number Abba.



Abba na ɗagawa Malam Ahmad yayi Sallama kana yace.



“Dama na faɗawa Fatima gashi-gashi yanda mu kayi to amma
tace wai dan Allah meyake faruwa lafiya kuwa?”.



Kai Abba ya gyaɗa cikin sanyin murya da tarin damuwa yace.



“Eh lafiya lau dama ina so ne kuɗaɗen da suka haɗa na motar
ta data saida da kuma na Sarƙoƙinta tunda ga yanda Ubangiji ya ƙaddara to shine
kuɗin nake so kazo in baka su sai ka maida mata su, sannan kayi mata bayani
tare da kwantar mata da hankali”.



Kai Malam Ahmad ya gyaɗa tare da faɗin.



“Toh shikenan bari zan faɗa mata”.



 



Ahankali ya juya ya kalli Ummi bayan ya katse kiran kana ya
mata bayanin duk yanda sukayi.



Cikin rauni ta sunkuyar da kanta hawaye na kwaranya daga
Idanunta Shar-shar-shar suna zuba akuncinta cike da tausayawa suke kallonta
musamman Asma'u lokaci ɗaya itama Idanunta suka fara zubar da ƙwalla.



Asanyaye Ummi ta ɗago kanta tare da kallon Malam Ahmad
Muryanta na rawa tace.



“Kace masa bana son Kuɗin Na yafe me zanyi da kuɗin da suka
kasa ceto min Jameel me zanyi dasu?.



Me zanyi da duk wani kayan ƙawa bana so bana ɓuƙatar su
nayafe su duniya da lahira bana ƙaunarsu”.



Anutse Malam Ahmad ya girgiza mata kai cikin rarrashi yace.



“Kada kice haka Fatima kiyi haƙuri Jameelu addu'a zaki yi
masa, kuɗin nan kada kice ba zaki karɓaba, idan har kika ce ba zaki karɓa ba
zaki sake saka Mahaifinsa cikin damuwa da tashin hankali aransa”.



Kai ta girgiza tare da miƙewa ta nufi Bedroom ɗinta still
hawaye na bin kuncinta.



Asma'u kuwa kife kanta da jikin cushin tayi tare da fashewa
da sassayan kuka me gunji cikin sauri Bashir ya ɗagota tare da share mata
hawaye cikin sanyin murya yace.



“Asma'u Yah Jameel baya ɓuƙatar kukan mu addu'ar mu kawai
yake buƙata, dan Allah ki daina yi masa kuka kinji, na tabbata Yah Jameel baya
son wannan kukan”.



Kai ta gyaɗa masa still hawaye na bin fuskarta tace.



“Bashir ya zanyi idan na tuna Yah Jameel ya barmu bari na
har abada nakan ji zafi da ƙuna acikin zuciyata, nakan ji raɗaɗi mai zafin
gaske nakanji.



 Tamkar zuciyata zata
fashe”.



Cikin sanyin murya Bashir yace.



“Toh ya zamuyi da hukuncin Ubangiji Asma'u haka Allah ya
tsara Yah Jameel ba zaiyi tsawon rai ba, koda ace basu sace sa sun kashe ba na
tabbata ba zai wuce wannan kwanakin ba mu dai kawai addu'ar mu yake buƙata a
hankali kuma waɗanda suka aikata masa hakan zasuga SAKAYYAH mabayyaniya addu'a
kawai zakiyi ta masa kinji”.



Jinjina kai tayi kana tace.



“Inayi kuma zan cigaba da har ƙarshen rayuwata da izinin
Ubangiji”.



 



Ummi nashiga Bedroom ta zaune gefen gado tare da fashewa da
kuka Malam Ahmad na shiga cikin daƙin ya zauna gefenta kana ya sanya hannunsa
tare da janyota ya mannata da jikinsa cikin sanyin murya yace.



“Kiyi hakuri ki daina kuka Fatima, ki yiwa Jameelu addu'a
Ubangiji ya masa rahma sannan madadin kice ba zaki karɓi kuɗin nan ba ki sake
sakawa mahaifinsa damuwa to ki karɓa”.



Cikin rauni Ummi ta sake manna kanta da ka fadarsa kana ta
cigaba da sheshsheƙan kuka.



 



Tafin hannunta Malam Ahmad ya damƙe acikin nasa kana ya
cigaba da cewa.



“Idan yaso idan kika amshi kuɗin sai kiyi amfani dasu wajen
yiwa Jameelu Sadaƙatul Jariya.



Kamar Gina Masallaci, Ko kuma gidan marayu, Ko Asibiti,ko
makarantar addini, ko kuma yin Bohorle rijiya da dai sauransu da nufin Allah ya
kai ladan garesa kinji ko Fatima kada ki butulcewa Ubangiji”.



Ajiyar zuciya ta sauƙe kana yace.



“Kada kice ba zaki karɓa ba Ubangiji shi yabamu Jameelu,
sannan kuma shi ya ɗauke Jameelu bamu da abinda zamu yiwa Jameelu sama da
addu'a shine kaɗai soyayyar daza mu nuna masa amma idan kika bar kuɗin ya
mahaifinsa zaiyi dasu?”.



Jinjina kai Ummi tayi cike da gamsuwa kana tace.



“Shike nan insha Allah zanyi yanda kace Allah yajiƙan
Jameelu Allah ya gafarta tamasa Ubangiji ya jaddada rahma agaresa”.



Malam Ahmad na share mata hawaye ya amsa da.



“Ameen”.



 



Ɓangaren Hajiya Lami kuwa zaune take afalonta cikin sanyi
Samira ta fito daga Bedroom ta zauna gefenta tare da tsira mata idanu.



Kallonta Hajiya Lami dake riƙe da wayarta tayi kana tace.



“Lafiya kuwa Samira?”.



Girgiza kai Samira tayi cikin sanyin murya tace.



“Mommy cikina ke ciwo”.



Ahankali Hajiya Lami ta ajiye wayarta tare da tsira mata Ido
kana tace.



“Meke damunki ne kwanan nan kina yawan complain din cikin ki
yana ciwo”.



Rau-rau tayi da ido still Muryanta na rawa tace.



“Mommy nikam wannan ciwon cikin ya fara damuna,



 duk fa lokacin daya
Murɗa Mommy wani farin ruwa ne yake fito min ta gaba na.



 Mommy har saina sa
Path agabana kamar mai yin period kuma ba jini bane kawai ruwa ne yake fito min
mai ƙarni da masifar wari”.



Zare ido Hajiya Lami tayi tare da cewa.



“Ruwa kuma?,Ni Lami wani irin ruwa kenan?”.



Cikin rawan murya Samira tace.



“Ruwane kamar Sparm yake fita sannan da yawa da yauƙi yake
fita Mommy ga wari da ƙarnin Masifa yanzu bakya jin ƙarnin da na matsoki”.



Da sauri ta jujjuya mata kai alamun a'a.



Ita kuwa Samira cike da damuwa taci gaba da cewa.



“Nifa idan na sunkuyar da kaina ƙasa ƙarnin da warin
nakeji”.



 



Girgiza kai Hajiya Lami tayi tare da haɗiye wani abu mai
masifar ɗaci kana ta kalli Samira tare da cewa.



“A'a Samira nikam ban jiba. Amma tun yaushe ya fara miki
haka?”.



Kallonta Samira tayi tare da faɗin.



“Yafi kwana biyar idan naji cikina ya Murɗa ya Murɗa, sai
wannan abin ya zubo da fari ya fara zubowa kaɗan-kaɗan, to amma yanzu ya fara
zubowa dayawa, sannan ciwon cikin yana ƙaruwa baki daya hankalina ya tashi
Mommy!”.



Cikin sauri Hajiya Lami tace.



“To bari zan shirya Inje wajen boka Kar'uzu in Faɗa masa
halin da ake ciki”.



Suna cikin magana suka ji ƙaran buɗe Bedroom ɗin Abban
Samira.



 



Ganinsa yasa Hajiya Lami wayancewa da faɗin.



“Eh Samira Insha Allah Idan Daddy ki ya bari zanje induba
Aminan Hajiya Bunayya dake fama da ciwon ciki”.



Cikin nutsuwar Kamilin Dattijo dake cike da kamala da
nutsuwa ya ƙaraso cikin falon tare da kallon Hajiya Lami cike da dattako yace.



“Ayyah Subhanallah lallai dai naji kuna maganar ciwon ciki
ashe Amina ce ba lafiya Allah ya sawwaƙa”.



Da sauri Hajia Lami tace.



“Amin dai”.



Shi kuwa yana gwara zaman hular kansa yaci gaba da cewa.



“Shiyasa na kwana biyu ban gantaba ashe ba lafiya ne?”.



Kai Hajiya Lami ta gyar'ɗa tare da cewa.



“Eh wallahi dama so nake idan ka fito zanje in dubata Idan
ka amince”.



Jinjina kai yayi kana yace.



“Ayyah to ba matsala ki Gaishe su”.



 



Acan gidan Lamiɗo kuwa Hajiya Bunayya na shiga falonta ta
kalli Amina dake zaune kan 2sitter gyara zama Amina tayi tare da cewa.



“Mommy wai ɗazu hayaniyar me nake jine ina waya da Uncle
Naseer ne yana gaya min tsarin ginin gidansa da ake gyarawa a cikin Abuja yace
min in anyi aure zamu zauna a nan na wata ɗaya zuwa biyu kafin mu tafi India,
shiyasa ban fito ba”.



Cikin jin dadi tace.



“Alhamdullah kice dai abu yanata kankama”.



Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.



“ Eh Ummah Amman Hayaniyar me akayi ɗazun”.



Taɓe baki Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.



“Ooo Kakar Khausar ce kuma yau tazo tana ta bala'i, banma
san bala'in da take ba na dai ji tana cewa Khausar bata da kunya zata kalli
tsabar idonta tace batason mijin da ta zaɓa mata tana da wanda take so, to
bansan ya ake ciki ba dai. Ni dai tsoro na kaddai Nasseru take so?”.



Gyara zama Amina tayi tare da Girgiza kai kana tace.



“Ba dai Uncle Naseer ba Dan 
ko magana bata mishi, sai in shi ya mata, shima kuma baya mata magana
sosai da nace masa bana so.



Sai dai ko ina wani can daban wayasan mata”.



Cikin jin daɗi Hajia Bunayya tace.



“Ato da sauƙi”.



Ita ko Amina gyara zama tayi tare da cewa.



“Uncle Naseer Kam yanzu ma wayar da muke yine, ya hanani
fita.



Kuma cewa yayi anfara hada kayan lefe sannan kuma idan an
tashi da kayan lefe da kayan gishi da goro da sadaki da kayan rufi duk za ahaɗa
rana ɗaya za akawo”.



Murmushi Hajiya Bunayya tayi tare da Jinjina kai.



Ajiyar zuciya Amina tayi kana ta cigaba da cewa.



“Kuma yace nan da wata ɗaya za'a ɗaura Auren mu sannan ana
gama bikin a Abuja  zamu tare baza mu
wuce wata biyu ba in yayi yawa ne uku zamu wuce India sannan zai nema min
admission In cigaba da karatuna”.



Dariya Hajiya Bunayya tayi tare da ran gaɗa guɗa kana tace.



“Alhamdulillah burina ya cika haka nake son ji da ace mun na
cewa batun wannan yaron Jameel gashi ƴan Kidnapping sun kashesa a wofi”.



Kai Amina ta gyaɗa tare da cewa.



“Ai dai kam Umma Allah ya rufa mnaasa asiri da na nacewa
batun Malam Jameel da yanzu na zama matar Mamaci ina takaba”.



Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa tare da faɗin.



“Aikam Allah ya tsareki yaje can Allah ya jikansa da Rahma”.



Cikin sanyin murya Amina tace.



“Ameen dai tun da yana da kirki Allah ya jikansa Allah yasa
ya huta amma dai na kama dahir dana kama Uncle Naseer”.



Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.



“Kin kama dahir kam”.



Asiya ce da bata cika shiga mgnar suba, tunda Hajia Bunayyah
tace mata zata tsine mata in tana damunta da batunsuji tsoron Allah, a hankali
ta ninke hijabin da tayi salla dashi tare da miƙewa ta fito falo tana maiyi
musu addu'ar shiriya.



Ita kuwa Amina da baki ta nunata.



Shashar uwa sai dariya tayi.



Suna cikin hiran wayar Hajiya Bunayya ya hau ruri tana
dubawa taga Hajiya Lami cikin sauri tayi Picking tare da kaiwa Kunnenta Hajiya
Lami najin tayi Picking batare da tayi Sallama ba  ta fara kora mata jawabin abinda Samira ta faɗa
mata.



 



Zare ido tayi cike da damuwa tace.



“Subhanallah toh Meyesa haka?”.



Cike da damuwa Hajiya Lami tace.



“Ban saniba amma ki shirya da daddare bayan sallar Isha'i ki
rakani”.



Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa tare da cewa.



“Toh nima zanje dama in Faɗa masa maganar Amina don tuni
anfara hada kayan lefe, Gishiri, Goro, kayan rufi, da sadaki duk lokaci ɗaya
za'a kawo kinga hankali ya kwanta”.



Jinjina kai Hajiya Lami tayi tare da faɗin.



“A hankali ya kwanta kam bari sai nazo ɗin dai”.



Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa kana tace.



“Toh sai kinzo ba komai ki kwantar da hankalin ki”.



 



Aɓangaren Innayi kuwa har maghariba bata ji motsin Moddibo
ba sosai hankalinta ya sake tashi.



 Wunin ranan yini tayi
tana kuka wanda lokaci ɗaya zazzaɓi ya kamata baki daya tunaninta ya ta allaka
akan idan ta mutu ya Moddibo zai kasance awannan gari ya zaiyi.



Wasa-wasa har aka Idar da maghariba da Isha'i har misalin
goma ba Moddibo ba labarinsa cikin sanyin jiki da tashin hankali ta miƙe ta
nufi sashen sa tun kafin ta ƙarasa hawa barandar ta jiyo sheshsheƙan kukan sa
cikin sauri ta ƙarasa hawa barandar tare da Murɗa Kofar falon tashiga kan
Sallaya ta hangosa yayi Sujjada yana sheshsheƙa.



 



Cikin sauri ta zauna gefensa Muryanta na rawa tace.



“Subhanallah haba, Aliyu!, Haba Aliyu!!. Meyesa haka Aliyu
ka ɗauki dangana mana kuka shine abinda zakayi ta raka Jameelu dashi arayuwar
ka wannan soyayya itace zaka nunawa Jameelu kenan?”.



Anutse ya ɗago daga Sujjada tare da yin tahiya  kana yayi sallama yana sheshsheƙa kana ya
daga hannunsa biyu sama cikin raunin murya yace.



“Ya Allah Ubangiji kasa mafarki nake, Allah kasa in farka
daga wannan hautsinennen mafarkin da nakeyi”.



Ahankali Innayi ta matsa kusa dashi tare da Kallonsa cikin
sanyin murya tace.



“Haba Aliyu Meyesa kakeyi yin haka? ka kwantar da hankalin
ka babu abinda ya gagari lamarin Ubangiji”.



Domin Ita batasan cewa yaji maganar da sukayi da Hajja Nana
ba.



Ahankali ya ɗago idanunsa da suke kada sukayi jawur tamkar
garwashi cike da mamaki take kallon yanda idanunsa suka sauya launi Muryanta na
rawa tace.



“Aliyu lafiyar ka kuwa?”.



Kai ya Girgiza tare da cewa.



“Bakomai”.



Ya faɗa tare da lumshe Idanunsa domin ya rasa ta yaya zai
fara tambayarta shin inane asalinsa shin waye mahaifinsa su waye ne tushensa,
yanaso ya tamyan amma ya najin tsoro da fargaba da taraddadin ya tambaye, ya
zama cewa kalaman da Hajja Nana ta faɗa da kuma zarginsa na tsawon shekaru ya
zama gaskiya hakan yasa yaji tsoron tambayarta kamar yadda ya saba, haka ya
meda tambayar cikin ransa, sunkuyar da kansa ƙasa yayi.



Innayi kuwa cikin sanyin murya ta cigaba da rarrashin sa
domin duk azatonta mutuwar Jameel ya tuna cikin rarrashi ta cigaba da cewa.



“Aliyu kayi haƙuri kowa da irin ƙaddarar da Ubangiji yake
masa Addu'a zamu masa”.



Sunkuyar da kai Moddibo yayi hawaye ya cigaba da kwaranya
daga Idanunsa.



 



Innayi kuwa cikin sanyin murya ta cigaba da cewa.



“Kada kayi kuka Aliyu ko wani irin matsala ka shiga arayuwar
duniya kada ka butulcewa Ubangiji da irin wannan kukan, babu abinda zai kawo
maka banda tashin hankali da damuwa”.



Ta ida maganar tana zubda zafafan hawaye, kukan abubuwa biyu
ne suke haɗe mata alokaci ɗaya kalaman Hajja Nana da kuma halin da taga Moddibo
aciki yayi masifar ɗaga mata hankali.



Anutse Moddibo yasanya tafin hannunsa yashiga share hawayen
fuskarsa muryarsa na rawa yace.



“Toh shikenan Innayi nayi shiru dan Allah kema ki daina kuka
Ubangiji Allah yarufa mana asiri”.



Cikin muryan kuka tace.



“Ameen ya Allah”.



Miƙewa tayi tare da fita ba daɗewa ta dawo hannunta riƙe da
Warmers din abinci ta ajiye masa agabansa kana tace.



“Gashi kaci abinci”.



Kai ya Girgiza kana yace.



“A'a Innayi bazan ciba aƙoshe nake”.



Jinjina kai tayi tare da miƙewa ta dawo hannunta riƙe da
wani bowl dake ɗauke da Fruit ta ajiye masa kana tace.



“Toh kaci wannan”.



Kai ya gyaɗa kana ya fara ci ahankali.



Ganin ya fara ci yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa.



“Toh sai da safe”.



Sannan ta fice domin bata da nutsuwa atare da ita.



 



Washe gari Da safe Ganin Moddibo bai zoba yasa Abba yashiga
motarsa kai tsaye gidansu Moddibo ya nufa yana isa yayi Parking ya fito daga
bakin gate ɗin farko ya tsaya yayi sallama Innayi dake Alwalan sallar Walha ta
miƙe bayan ta ida ta nufi ƙofar tare da amsa masa Sallamar.



Bayan sun gaisa Abba ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.



“Dama Moddibo ne nake son ganinsa kuma bai zoba”.



Cikin sanyin murya Innayi tace.



“Hmm Moddibo ai jiya wuni yayi aɗaki yana kuka babu inda ya
fita”.



Cike da alhini Abba yace.



“Subhanallah ni kuwa dama al'farma nazo nema Aliyu yamin
taimako”.



ya ida mgnar cikin alamun neman al'farmar.



Haka yasa Innayi ta ɗan juyo ta kalleshi da kyau kana a
hankali tace.



“Alhji Bashir ai ka wuce haka, kawai Umarni zakiywa Aliyu,
kamar yadda kakeyiwa Jameelu da izinin UBANGIJI kuma zai cika maka umarninki.
Aliyu ɗan ka ne, kadama kacemin komai kawai ka bashi umarni yamaka duk abinda
kakeso ni kam na amince duniya da ƙiyama”.



Cikin jin daɗi kara da kawaicinta gareshi yace.



“Nagode da mutuntaka Allah ya bar zumunci”.



Amin tace tare da juyawa



tayi gaba.



Abba na bin bayanta zuwa falon Moddibo tsaye Abba ya gansa
afalon yana ƙoƙarin fita.



Cike da ladabi yace.



“Ha'a Abba kazo ne?”.



Kai Abba ya gyaɗa kana yace.



“Eh naga shiru-shiru Aliyu ba kazo ba tun jiya”.



 



Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da faɗin.



“Eh dama yanzu nake shirin fita zan biya ta gidan Ummi
sannan na ƙara so wajenka”.



Ahankali Abba yace.



“Allah sarki to zamu tafi tare”.



Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.



“Toh”,Sannan suka fita.



 



Cikin sanyi da



disesshiyar murya yace



“Abba na rasa ta ya zan gayawa Innayi batun



tafiyar nanfa”.



Juyowa Abba ya ɗan yi



ya kalleshi na second uku kana yace.



“Munyi mgnar da Innayi tace, babu matsala duk abinda ya dace
in saka kayi min ta amince”.



Cike da mamakin amincewar tan yace.



“Ta yarda”.



Ka Abba ya gyaɗa mishi yana mai ci gaba da tuƙi.



 



Acan gidan Lamiɗo kuwa 
tun bayan tafiyar Hajja Nana Mommy ta fita sabgar Khausar da zaran ta
gifta gefen da Mommy take Mommy zata kawar da kanta tare da dauke Idanunta
akanta kana Uffan bata ce mata ba ko  da
safe da Mommy ke haɗa breakfast Khausar na shiga da niyyar tayata ta batare da
tace mata Uffan ba ta nuna mata hanyar fita cikin rauni tace.



“Dan Allah Mommy kiyi haƙuri na tuba”.



Cikin fushi Mommy ta nuna mata hanyar fita ba tare da tace
komai ba.



Da gudu Khausar ta juya tare da nufar Bedroom ɗinta tana
shiga ta faɗa kan gado tare da fashewa da matsanancin kuka.



Haiydar ne yashigo falon jin sheshsheƙan Kukan ta a Bedroom
yasa ya nufi Bedroom Cike da kulawa yace.



“Adda Khausi Meye sameki?”.



Ɗago Idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye tayi tare da
Kallonsa tace.



“Haiydar Mommy fushi take dani”.



Cike da Mamaki yace.



“Fushi kuma? to me kika mata?”.



 



Kai ta girgiza still tana kuka tace.



“Nima ban sani ba amma Mommy fushi take dani”.



Ajiyar zuciya Haiydar ya sauke tare da cewa.



“Toh Addah Khausi 
muje kibata haƙuri kinji ko?”.



Nunfashi me zafi ta fesar tare da Kallonsa kana tace.



“Haiydar Ina tsoro”.



Kai ya Girgiza tare da sassauta muryarsa yace.



“Toh idan baki bata haƙuri ba so kike tayi ta fushi dake?”.



Be jira cewar ta ba ya riƙo tsintsiyar hannunta suka fita,
ganin Mommy bata falon yasa suka nufi kichen still Nan ma bata nan kai tsaye
Bedroom ɗinta suka nufa zaune suka sameta abakin gado da alamar bata daɗe da
fitowa daga wanka ba ta gama shiryawa tana ɗaure yalwataccen sumar kanta da
Ribont.



Tsugunna wa Haiydar yayi agabanta tare da jan hannun Khausar
itama ta tsugunna cikin sanyin murya da neman yafiya Haiydar yace.



“Ayyah Mommy dan Allah kiyi haƙuri Addah Khausi tace kinyi
fushi da ita tun jiya bakya mata magana”.



Kallonsu Mommy tayi tare da kawar da kanta gefe Khausar kuwa
da hawaye ke kwaranya daga Idanunta yayin da kanta ke ƙasa.



Miƙewa Mommy tayi kana ta cigaba da shirinta  ba tare data tanka suba ta ɗauki turare ta
feshe jikinta.



Cikin sanyi Haiydar ya mike tare da ƙarasawa gaban Dressing
mirrow ya durƙusa kana Cike da ladabi yace.



“Dan Allah Mommy kiyi haƙuri Idan akwai abinda tayi miki mu
baki haƙuri”.



Banza Mommy tayi dasu ta cigaba da shirinta.



 



Cikin raunin murya da tsanananin tashin hankali Khausar ta
shiga Girgiza kanta tana sakin kuka, kana Idanunta na zubar da hawaye Shar-shar
muryanta na rawa tace.



“Dan Allah Mommy kiyi haƙuri ki yafemin, kinsan fushinki
masifa ce agareni”.



Uffan Mommy bata ceba ta koma bakin gado ta zauna cikin
sanyi jiki Haiydar da Khausar suka bita da rarrafe suka durƙusa a gabanta, ido
ta zuba Khausar tana kallon yadda take kuka,



Ita kuwa  Khausar ta
kasa ɗago kanta, sai hawaye dake cigaba da zuba shar-shar.



Cikin muryar dake nuna ɓacin rai Mommy tace.



“Toh Kuma kukan me kike yi bayan kinyi abinda ranki keso.



Ai dariya ya kamata kiyi tunda har kin kai matsayin zaɓawa
kanki miji, kin iya fetsare idanu gaban manya kice ke ga wanda kikeso. kin
jamin tashin hankali da zagi awajen kakarki”.



Haiydar kam ido ya zubawa Mommy don bai taɓa ganin tsananin ɓacin
ranta irin na yau ba.



Mommy kuwa cikin fushi ta cigaba da cewa.



“Tsohuwar da kinsan ba kirki da kara bane da ita, ta fita
tsakiyar gida tana min ihu da haushi tana tara min mutane,  Kina sane da cewa duk abinda kika yi laifinsa
kaina yake dawowa, sannan duk abinda kikayi Ni bansan dashi ba bansan yaushe
kika tsara ba ban isa ki gaya min sirrinki mu biyuba sai kin bari a tsakiyar
mutane”.



Ajiyar zuciya Haiydar ya sauƙe tare da cewa.



“Dan Allah Mommy me tayi miki ne?”.



Cike da ɓacin rai Mommy ta kalli Khausar kana tace.



“Ai ita tasani ta faɗa maka me tayi”.



Ahankali Haiydar ya juya tare da kallon Khausar yace.



“Addah Khausi me kikayi?”.



Kallon Mommy Khausar tayi Muryanta na rawa tace.



“Dan Allah Mommy kiyi haƙuri?”.



Girgiza kai Mommy tayi babu walwala atare da ita tace.



“Toh me kike nufi da kalmar da kika faɗa?



Kince ba kyason Naseer na gamsu domin Ni kaina bana son
Naseer tunda nasan abinda ke tafiya, sannan na fahimci yanzu Ameena yake so”.



Kuka kawai Khausar keyi Allah ne kaɗai yasan me take ji
aranta.



Mommy ta cigaba da cewa.



“To amma shi Aliyu Meye lefinsa ɗan uwanki ne sannan zai
riƙe da amana da gaskiya kamar yadda ya riƙe yar uwarki. Baffanki bazai bari ya
to zarta kiba sannan kinzo min da wata magana wai Moddibo kike so ko kunya baki
jiba”.



Ahankali Khausar ta ɗago kanta kana ta rumtse idanunta dake
zubar da hawaye Muryanta na rawa tace.



“Mommy dan Allah kiyi haƙuri abar batun Yah Aliyu ayi batun
Aurena dashi Mommy wlh ni Moddibo nake...!



 



 



 

No comments