Sakayyah Book 2 Page 13

 

   *GARKUWAR
MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 13*



 






           Na



*Aysha Aliyu Garkuwa*



 



 



Tallah !! Tallah !!



 



Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga
Allah) wacce  ta nishadantar daku a
littafin ta mai suna *Kanwata* , yau ta sake dawo muku Domin tallata muku
Littafin mai Suna ( Rai Daya Jan Zaki) 
littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin
ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba  Hausawa sukace Gani yakori ji.



 



Farashin wannan littafin Naira Dari biyar ne 500 kacal  postin biyu a arana  banda ranar Juma'a .



Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka
(09069080725 ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa
juna lokaci.



Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam
first bank



Turo shaidar biya akan wannan 09069080725 sai najiku.



 



Jalaludeen kuwa cikin rauni ya É—ago idanunsa wanda suka zama
tamkar garwashin wuta, saboda yanda sukayi ja-jawur yayin da baki É—aya ilahirin
jikinsa ke rawa kar-kar tamkar wanda aka jona masa Shorking kuka yake mai shiga
jiki tare da ratsa zuciyar duk wani mai imani daya saurara.



Da sauri Moddibo ya ƙara sa kusa dashi gefenshi ya zauna
cike da matsanancin rauni da kuma famewar mikin dake zuciyarsa na rashin J É—insa
ya shiga rera wani irin raunataccen kuka tamkar ransa zai fita, kukan wanda bai
samu yayi shi ba a lokacin rasuwar, baka jin sautin komai acikin É—akin, face
Shesh-sheÆ™an kukan su dake cigaba da 
wanzuwa aƙalla sun ɗauki kimanin minti goma sha biyar suna kuka batare
da wani yayi yunƙurin rarrashin ɗan uwansa ba.



Cikin dauriya da ƙoƙarin son hana kansa kuka kana da
shesh-sheƙa Jalaludeen ya ɗago tafin hannunsa mai masifar sanyi tamkar wanda
aka ciro acikin dusan ƙanƙara ya manna aƙirjin Moddibo daya ke jiyo bugun
zuciyarsa, cikin rauni yace.



“Kayi haÆ™uri Mouley haÆ™iÆ™a munyi rashi mai girma.



Munyi rashi mafi ciwo azuciyarmu. Kayi haƙuri Aliyu kaya
femin tsawon lokaci baka ganni ba ina cikin haramine! shiyasa baka ganniba”.



Lumshe idanu Moddibo yayi wasu hawaye masu masifar zafi suka
zubo akuncinsa yayin da sanyin tafin hannu Jalaludden ke ratsa zuciyarsa
Jalaludden kuwa cikin raunatacciyar murya ya cigaba da faÉ—in.



“Saboda na shiga inayin I'itiÆ™afi tsawon lokacin nan shiyasa
kuma koda na fito munyi tafiya nida Kakana munje ƙasar Sin shiyasa baka ganni
ba bansan Jameelu yashiga wannan hali ba bansan Jameelu ya rasuba Mouley”.



Sai kuma ya fesar da numfashi mai zafi tare da cigaba da faÉ—in.



“Sai jiya Juma'a ne naje Taraba domin kai muku ziyara,
kasancewar na daÉ—e ba muyi magana ba yasa na shirya muku Surprised sai dai
kawai ku ganni, toh ina isa gidan innayi na nufa, naje gidan Innayi na samu
babu kowa sai na wuce gidan Ummi”.



Kallonsa kawai Moddibo keyi hawaye na cigaba da silala daga
idanunsa.



 



Cikin rauni Jalaludden yace.



“Acan na samu Innayi suna hiran. Jameel ya rasu kuma na
tsinkayi cewa kana ƙasar Morocco, nazo ƙasar Morocco na bibiyi al'amarin ka har
na gane cewa kana cikin Fadar Rabat!”.



Kuka ne yaci karfinsa cikin kuka kamar ƙaramin yaro ya
cigaba da cewa.



“Mouley munyi rashi.



Jameel ya tafi ya barmu 
Allah yajiÆ™an Jameel Allah yayi mishi rahma!”.



 



Cikin sanyin murya Moddibo yace.



“Amin Ya Allah. Amman nayi mamaki rashin jinka Jalaladdeen
ina ka shiga, tsawon lokaci ba É—uriyarka. Na shiga matsanancin damuwa Jameel É—ina
ya É“ace tsawon lokaci, bamu sameshi ba.



Naso ace kana kusa damu kayi mana amfani fiye da amfanin da
kayi mana abaya ka faÉ—a mana inda J.yake”.



Kai Jalaludden ya girgiza still hawaye na kwaranya daga
idanunsa ya riƙe hannun Moddibo kana yace.



“Bana kusa Aliyu, sannan kuma koda ina kusa muma kanmu
jinnu. Ubangiji bai sanar damu gaibu ba Aliyu,



da ace Allah ya sanar damu ilimin gaibu ko a inda nake zan
iya sani da zan faÉ—a maka, amma Allah bai sanar damu gaibu ba.



Sanin gaibu sai Allah kaÉ—ai bansan haka zai faru da Jameel
ba.”



Numfashi Moddibo ya fesar kana ya dafe goshinsa da hannunsa
na dama tare da faÉ—in.



“Tabbas munyi rashi mafi girma ban taÉ“a sanin ya É—aci da
zafin mutuwa yake azahiri ba har sai da na rasa J É—ina, mutuwar J mutuwa ce da
bazan taɓa mancewa ba. Sannan bazan daina jin zafi da raɗaɗinsa ba har sai
ranar dana koma ga Ubangiji na!”.



Kai Jalaludden ya gyaÉ—a kana yace.



“Sosai ma kuwa Aliyu, amman haÆ™uri zamuyi, domin babu abinda
Jameel yafi buÆ™ata agaremu yanzu face addu'a addu'ar mu”.



Kai Moddibo ya jinjina tare da cewa.



“Zan cigaba da yiwa J É—ina addu'ar samun rahamar ubangiji
har zuwa numfashina na Æ™arshe”.



Haka suka kwana suka yini suna hira.



 



Washe gari da safe koda Sarki Youseef Mouley da Didi suka
shiga wajen Moddibo suna tare da Jalaludden sai dai su basu da ikon ganinsa
kasancewar bai bayyana musu kansa ba,



 ko Moddibo ba ma
asiffar mutum yazo masa wanda sukayi karatu dashi.



Bayan fitansu ya kalli Moddibo yace.



“Kana kama da Mahaifinka”.



Da mamaki Moddibo ke kallonsa kafin ahankali yace.



“Mahaifina ko?”.



Kai Jalaludden ya gyaÉ—a Fuskarsa É—auke da murmushi yace.



“Eh Mahaifinka mana, shin ban taÉ“a faÉ—a maka cewa kai ba É—an
Nigeria bane, har kaita dariya kana tambayata to kai É—an ina bane?”.



Kai Moddibo ya jinjina tuni lokacin suna Jami'atul Madina
bayan sun fito daga darasi suna shan shayi Jalaludden ke sanar masa.



Still da murmushi afuskarsa ya cigaba da faÉ—in.



“Har kace min kai É—an ina ne nace kai É—an Morocco ne,  kace ba haka bane.



Amma ni nasan hakane saboda nayi bincike ne akan Innayinka
na kuma fahimci haka”.



Zazzafan ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe cikin tsira masa
idanu yace.



“Kenan kana nufin nan Æ™asatace?”.



Murmushi Jalaludden yayi ta gyaÉ—a masa kai kana yace.



“Sosai ma kuwa Æ™asar kane, tsatsonkane, Mahaifarkane.
Wa'annan kuma Mahaifanka ne”.



Cikin girmamawa lamuran Ubangji mabuwayi gagara misali
Moddibo yace.



“Ya Salam shin taya akayi wanna al'amarin yakasance ya akayi
abin ya faru a haka, abin ne yazo min tamkar amafarkaina na yau da kullum”.



Gyara zama Jalaludden yayi tare da faÉ—in.



“Kada kayi mamaki,Ka cire al'ajabi da mamaki acikin lamarin
Ubangji ya wuce mamaki. Kai dai kawai kayi godiya ga Allah”.



Ahankali Moddibo ya motsa laɓɓansayace.



“Alhamdulillah Allah kulli halin”.



 



Kai Jalaludden ya jinjina haka suka cigaba da hira kafin
daga bisani Jalaludden ya kalli Moddibo da murmushi afuskarsa yace.



“Sannan kuma akwai al'amarin da naje na samu ranan juma'a ya
kasance amma bazan faÉ—a maka ba sai ka ganin da idonka”.



Ware idanu Moddibo yayi kana ya langwaɓar da kai tare da
cewa.



“Jalaluddeen nawa dan Allah ka faÉ—a min mana”.



Ƴar dariya Jalaludden yayi wanda ya bayyanar da fararen
haƙoransa yace.



“Ok naje na samu Ummi ta shiga damuwa sosai akan tsawon
kwana uku kenan tana kiran wayar ka amma bai shiga har Abban Jameel yazo da
kanshi dan Maganar dana samu suna tattaunawa da Innayi kenan”.



Lumshe idanu Moddibo yayi yasan dole hakan zai kasance
rashin jinsa awaya zai É—aga musu hankali musamman Innayi da Ummi shima Abba sai
dai kawai yayi dauriyar maza.



 



Da murmushi Jalaludden ya cigaba da cewa.



“Ya faÉ—awa Innayi shima ya kira wayarka baya shiga tsawon
kwana uku kenan, amma kuma Innayi sai dariya take tana ce musu kada su damu
kawai afara shirin kawo maka”...



Sai kuma yayi shiru tare da yin mgnar zuci. Alhamdulillah
gwara da ban faÉ—a masa ba saboda naji suna faÉ—in cewa Moddibo bai san anyi masa
Aure ba..



 



ÆŠan ware idanu Moddibo yace.



“Ana shirin kawo min me?”.



BuÉ—e hannu Jalaludden yayi kana yace.



“Kai dai ana shiri kawai abinda naji sun faÉ—a kenan”.



Langwaɓar da kai Moddibo yayi cikin Muryansa mai cike da
sanyi yace.



“Kai dai Jalaludden baza ka faÉ—a min ba kawai”.



Kai Jalaludden ya girgiza kana yace.



“Um-um iya abinda naji kenan, kasan na faÉ—a maka bansan
gaibu ba Allah ne kaÉ—ai mafi sanin gaibu”.



Kai Moddibo ya jinjina cikin gamsuwa da maganarsa yace.



“Toh shikenan”.



 



Washe gari Litinin ya kama kwanan Moddibo biyar kenan acikin
Masarautar Mouley.



Misalin ƙarfe tara na safe Moddibo ne zaune acikin
tangamemen Falon kamar yanda ya saba ko yaushe yaji an buɗe ƙofar falon anutse
ya ɗaga kyawawan idanunsa tare da kallon ƙofar.



Idanunsa suka sauƙa akan.



 Didi da Sarki Youseef
Mouley sai wani kyakykyawan Matashi mai masifar kama dashi kallo É—aya ya masa
ya fahimci shine Ibraahim ƙaninsa ne da Didi ke yawan bashi labarinsa duba da
kamannin dake tsakanin su. Sai kuma Lalla Khadijah da Lalla Hafsat, sai Æ´ar
auta Rahama.



Ibraahim kuwa yalwataccen murmushi ya sakar masa domin shi
yakasance mutum ne mai fara'a da son Mutane kana da abin dariya



 



Suna haɗa ido da Moddibo ya ƙara fara'ar fuskarsa kana ya
tafi cikin sassarfa ya rungumeshi yana mai jin farin ciki da nutsuwa agaba É—aya
ilahirin jikinsa cike da shauƙi ya ɗago kansa kana yace.



“Yaya zance maka? Ko kuma Usaini? ko kuma Hassan É—ina?”.



Moddibo kuwa lokaci ɗaya ya tsinci kansa da ƙaunar yaron
aransa rungumesa yayi kana cikin É—an sakin fuska yace.



“Koma me ka kirani dashi zan amsa”.



Sai kuma suka sake rungume juna yayin da ƙaunar junansu ke
ratsa ko wani lungu da saƙon dake jikinsu...



Cikin tsanananin so da ƙauna Lalla Khadijah tace.



“Kai Ibraahim ka sakeshi haka mana”.



Kalla Hafsat dake ruggume da É—iyarta ce tayi dariya tare da
zama tana kiciniyar bawa baby nono, tace.



“Ai dai kam ya maÆ™aleshi kamar ya fimu sonshi”.



Didi da Abualeey kam kallonsu kawai suke cike da jin daÉ—i
mata misaltawa.



Rahama kuwa cikin tura baki ta harari Ibrahim cikin yanayin
tsamar saƙo-da saƙo tace.



“Ai shi haka yake ga yadda ya maÆ™aleshi kamar shine auta”.



Cikin jin daÉ—i Abualeey yace.



“Toh mu zauna dai kafin ai ta yiwa Ibraahim Æ™orafi”.



Shiko Ibraahim signal yayiwa Rahama tare da cewa.



“Ai shi nawane ni kaÉ—ai ba dama cewa kike nine bani da É—an
uwaba toh Allah ya dawo min da Æ´aÆ´ana dama yafi Yayunki kyau”.



Lalla Khadijah ce ta ɗan zuggure ƙayarsa.



ÆŠan tsalle yayi tare da



É—ago kansa ya kallin Moddibo kana yace.



“Kaga abinda suke minko ko Yah Aleey”.



Murmushi Modibbo yayi tare da É—an janye jikinshi gefe yana
mai kallonsu ɗaya bayan ɗaya yakejin sonsu da ƙaunarsu na ratsa mishi zuciya.



Shi kuwa Ibraahim baki ya É—an tura tare da cewa.



“Kayi haÆ™uri É—an uwana”.



 



“A kan me?”. Modibbo ya jefa mishi tambayar.



da sauri yace.



“Sabida rashin dawowata da wuri, sabida ranar da kazo ranar
na tafi Turkiyya dan daga nan muke kai musu dabino, toh nike wakiltan lamarin,
koda Lalla Hafsat ta gaya min ji nayi kamar inyi fiffige in dawo gashi naga dan
ban dawo da wuriba kamar kafi sonsu a kaina”.



Dariya sukayi baki daya.



Sai kuma duk suka tsagaita tare da zubawa Modibbo ido ganin
yadda yake dariya tare da shafa kan Ibraahim dan ganinshi yake kamar Bashir.



Didi kuwa da su Kalla Hafsat murmushi dukeyi ganin yadda ya
jawo Ibraahim ya ruggumeshi yana mai cewa.



“Waya ce maka nafi sonsu, suda zasu koma gidajensu su barmu
tare”.



Cikin dariya yayi musu gwala.



Rahama kuwa É—an rawa tayi tare da faÉ—in.



“Ni dai muna tare”.



Shi kuwa Ibraahim



juyowa ya kalli Didi da Abualeey tare da cewa.



“Dan Allah Didi ku aurar da ita ta bar mana gida mu
sake".



Baki ta tura tare da cewa.



“Ba ruwanka da ni”.



 



Didin kuwa fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi ta kallin
Æ´aÆ´an nata dake zaune reras agabanta kana tace.



“Alhamadullah Allah na gode maka da ka cika min farin cikin
ahlina”.



Kai Abualeey ya jinjina tare da faÉ—in.



“Masha Allah”.



Ibraahim kuwa



janye hannunsa dake cikin na Modibbo yayi kana ya juya tare
da kallon Alƙibla yayi Sujudur Shukur.



Kana ya É—ago tare da komawa gefen Moddibo ya zauna still
fuskarsa ɗauke da ƙayateccen murmushi ya kalli Sarki Youseef Mouley tare da faɗin.



“Abualeey Addu'ar mu ta karÉ“u Ubangiji ya dawo mana da Yah
Aliyu alokacin da bamuyi zato ba sannan ba muyi tsammani ba sai nake ji kamar
gaba É—aya burikana na duniya aka gama cika min dan ganin É—an Uwana kuma gudan
jina”.



Kai Sarki Youseef Mouley ya gyaÉ—a kana yace.



“Tabbas kuwa domin babu abinda ya gagari Ubangji Allah da
kansa yace mu roÆ™eshu zai amsa mana. Domin shi addu'a ba'a gaggawa dashi”.



Moddibo kuwa cike da tsananin so da ƙaunarsu dake ratsa ko
wani magudanan jinin jikinsa yace.



“Tabbas kuÉ—in kun kasance min. Garkuwa ne atare dani ina jin
ajikina babu abinda zanyi face godiya ga Allah daya haÉ—ani daku kafin na koma
garesa”.



Haka suka cigaba da hira tsawon lokaci ganin suna shirin
tafiya yasa Moddibo ya sunkuyar da kansa ƙasa kana yace.



“Ayyah Abba dan Allah Ina bukatar wayoyina akawo min su”.



Murmushi Sarki Youseef Mouley yayi kana yace.



“Kada ka damu za'a kawo maka wayoyinka dan suna hannu na”.



Cikin sauri da mamaki Moddibo ya kallesa tare da faÉ—in.



“Abba toh a taimaka min dasu Ummi, Innayi, da Abba zasu
nemini, musamman ma Innayina zata shiga damuwar rashin jina?”.



Kai Sarki Youseef Mouley ya girgiza kana yace.



“Kada ka damu In sha Allah babu komai rashin É—aukar wayar
yana da muhimmanci, da amfanin da zaiyi Kankane yace kada a É—auki wayar shiyasa
ma ban kawo maka ba”.



A ladabce Moddibo yace



“Abba zasu shiga damuwa saboda zasuji tsoro kada abinda ya
faru da Jameel nima ya faru dani”.



Cike da kulawa Sarki Youseef Mouley yace.



“Wanene Jameelun naka?”.



Idanunsa ya lumshe tare da buÉ—ewa kana yace.



“Ai wannan Dr Jameel É—in dana biyo, da fari ina bibiyarshi a
zatona J nane sabida tsananin kamar da sukayi”.



Nan ya shiga basu labarin Jameel da duk abinda ya faru
dashi.



Ya É—aura da faÉ—in.



“Shiyasa lokacin da naga wannan Dr Jameel baki É—aya na É—auka
cewa Jameelu na ne saboda kamanninsu yayi yawa, hatta maganarsu, tafiyarsu,
muryar su babu abinda ya raba su sai dai É—abi'unsu ya samu bambanci dana
Jameelu na”.



Cikin raunin murya da tunowa da Jameelunsa ya basu cikekken
tarihin abotarsu.



Sosai suma suka tausayawa masa tare da yiwa Jameelun fatan
samun rahamar Ubangji kana ya cigaba da faÉ—a musu cewa aikine ya kawo sa
kamfanin Baban Jameelu.



Cikin fesar da numfashi Ibraahim yace.



“Allah sarki Yah Jameel Allah ya gafarta masa”.



Cikin sanyi Moddibo yace



“Ameen ya hayyu ya Æ™ayyum”.



Lalla Khadijah ce ta gyara zama tare da fuskatarsa kana a
mutunci tace.



“Da fari dai kaga iya mu yamune cikin mahaifiyarmu da wasu
daga cikin amintattun fadane, suka san da isowarka wacce dole labarin ya bazu
cikin FaÉ—a, to Alhamdulillah zan haÉ—a taro na musamman damon gabatarda kai a
tsakiyar family'nka wato zuriyar sarki Aliyu Mouley, wanda zuriyace ta tun
kakannin Abbanmu da kuma kakanninmu, mu da kuma iyayenmu da Æ´an bappanayenmu
dama goggoninmu, in Sha Allah zayi tarone na musamman dan dan haka ka shirya
fuskatarta idanu mabanmanta. Alhamdulillah na gamsu da nitsuwarka zuwa yau kuma
na fahimci kasan komai na tsarin al'adunmu da nake mamakin yadda akayi ka
sansu”.



Da sauri Kalla Hafsat tace.



“Ke kuwa Lalla Khadijah ya za'ayi ya rayu da jakadiya kiyi
tunanin akwai wata al'adar da bazai saniba”.



Murmushi Modibbo yayi domin shi dai innayi bata taɓa
alaƙantashi da labarin fadaba, sai dai yasan komai na fadar ne a cikin
mafarkansa.



Abualeey ne ya gyara zama tare da cewa.



“Zuwa yanzu mun gama shiryawa komai na taron”.



Haka dai sukaci gaba da tattauna lamurran.



 



Washe gari ranan Asabar misalin ƙarfe uku na yamma Jirginsu
Innayi yayi landing a _Rabat Sale international airport_.



 



Suna sauƙa a airport motocine na alfarma guda biyar suka zo ɗaukar
su bisa jagoranci Dr Ahmad abokin Abban Jameel.



Mota ta farko Dr Ahmad ke driving yayin da Abban Jameel ke
gefensa daga can baya kuma Innayi ce tare da Hajja Nana da kuma Khausar.



Motar dake bima sa kuwa Ummi ce da Hajiya Bunayya sai kuma
ƙanwar Momyn Khausar Aunty Hajara, sai Haiydar da yake gaba gefen direba.



Yayin da mota ta uku kuwa Asiya, Asma'u ce tare da Dija. Sai
Aunty Ruƙayya ƙawar Mommy



Motar dake bayansa kuwa Baffa Jimeta ne da matarsa Hajiya
Umma, kana da Babbar Ƴar sa mai suna Aunty Hawwa .



Yayin da motocin ke tafiya ajere cikin nutsuwa bisa Jagoranci
Dr Ahmad



Bayan sun shiga cikin gari sun nufi unguwar Ben slimane,
cikin sauƙe numfashi Innayi ta fesar da numfashi tare da buɗe Idanunta ta kalli
cikin garin da tsarukan da kuma gine-gine suka sauya alamar garin ya sake samun
cigaba fiye da da.



Cikin sanyayyar murya me cike da kewa da kuma bege ta kalli
Dr Ahmad dake driving kana tace.



“Mubi ta unguwar El'gara sai mu É“ullo ta cikin Ben Ahmad dan
Masarautar Rabat zamu nufa”



Cikin wani amintacciyar murmushi Abban Jameel ya juya ya
kalleta kana yace.



“Kai tsaye kuma?”.



Kai ta jinjina kana tace.



“Eh can zamu nufa shine abinda yafi da cewa”



Still Idanunsa na kanta yace.



“Amma da ya kamata mu fara isa masauÆ™i mu huta tukunna!”.



Numfashi ta fesar tare da faÉ—in.



“A'a ai acan ya dace muyi hutun”.



Kai ya jinjina tare da faÉ—in.



“Toh shikenan”.



Shi kuwa Dr Ahmad juya akalar motar yayi, kana suma saura
suma mara mishi baya.



Nan suka ci-gaba da tafiya cikin nutsuwa still motocinsu na
jere.



 



 Suna isa Æ™ofan Gate
na farkon Masarautar Rabat ganin motoci ajere yasa cikin Sauri Hadiman dake
bakin gate ɗin mutum biyar suka miƙe biyu suka tsa gefen damar motan biyu gefen
hagun motar kana É—aya ya tsaya agaba.



Cikin nutsuwa da yanayin jikin girma Innayi ta sanya hannu
ta buɗe murfin motar kana ta fito yayin hannunta ke riƙe da wani abu kamar
murfi kolbar Vaselin sai dai bisa ga alamu ginannene kana anyi sa da hatimin
Masarautar.



Wanda ke kusa da ita ta miƙawa.



Karɓa yayi ya duba kana yayi saurin kallon fuskarta sai kuma
ya juya ya miƙawa na gefensa shima ya karɓa ya duba.



Da wani irin sauri suka ɗaura hannunsu asaman ƙirjinsu kana
suka sunkuyar da kansu alamar girmamawa.



Kai ta jinjina musu.



Kana cikin sassarfa suka juya tare da buÉ—e musu Gate É—aya
daga cikinsu ya tsaya abakin Gate yayin da sauran huÉ—un suka marawa moticin baya
cikin sassarfa suna isa Gate na biyu É—aya daga cikin masu binsu yayi saurin buÉ—e
musu Gate É—in suka shiga kai tsaye har harabar fadar suka isa,  suna isa sukayi Parking atare.



 



Acan motarsu Hajiya 
Bunayya kuwa Haiydar  wani irin
zazzafan ajiyar zuciya ta sauƙe mai nuni da zallan mamaki kana ta kalli gabas
da yamma kudu da Arewa wani irin daular duniya da suka shiga wanda ya kamata
akirasa da Aljannar duniya cike da al'ajabi ta maida idanunta kan Ummi kana
tace.



“Toh nan kuma ina muka zo haka”.



Lallausan murmushi Ummi ta sakar mata kana tace.



“Nan gidansu Moddibo muka zo gidan Mahaifinsa”.



Dariyar sheƙiyanci Hajiya Bunayya ta saki tace.



“Kai lallai wannan ta tsuniya yawa ne dashi nan É—in ne
gidansu Moddibo?”.



Kai Ummi ta jinjina tare da faÉ—in.



“Toh ki zuba ido ki gani”.



Baki ta taɓe tare da yiwa Ummi wani kallo kana tace.



“CaÉ“ amma Ummin Jameel banyi zaton haka daga gareki ba da
girmanki”.



Ta ida maganar tare da ƙyalƙyalewa da dariya ita baki ɗaya
ma maganar dariya yake bata yo ai ko amafarki Moddibo bai isa ya kasance jinin
wannan ahali ba mutumin da ake kyautata zaton É—an shegene.



Ummi kuwa da mamaki ta kalli yanda take dariya kana tace.



“Kina mamaki ne?”.



Hajiya Bunayya kuwa cikin taɓe baki tace.



“Sosai ma kuwa ai ba mamaki ba harda Al'ajabi na haÉ—a Moddibo
fa”.



Sai ta kuma fashewa da dariyar sheƙiyanci data tuna wai Ummi
tace nan gidansu Moddibo ne.



Kai kawai Ummi ta girgiza batare da tace Uffan ba tana mai
bin baki É—aya ilahirin gidan da kallo.



 



Acan Motarsu Asma'u kuwa cikin zumuÉ—i da ganin tsantsan kyawu
da tsaruwan gidan Dija tace.



“Ehyeh”.



Asiya ma kallon coumpund ɗin tayi cike da shauƙi tace.



“Wowwww Masha Allah kaga wani daular duniya”.



Asma'u kuwa dogon numfashi taja tare da fesar wa tare da faÉ—in.



“Toh Masha Allah wannan al'amari da ban mamaki yake”.



Motocin kuwa re ras suka tsaya.



Fadawan dake tsaye bakin Fadar kuwa cikin sauri suka nufo
motocin wanda aƙalla sun kai biyar isowarsu yayi dai-dai da fitowar Innayi daga
motar.



Sarkin ƙofane idanunsa suka sauƙa akanta cikin sauri ya
mutsi-stika Idanunsa kana ya sake kallonta sama da ƙasa cikin al'ajabi da
mamaki tu'ajubi yace.



“Innare Jakadiyar Gimbiya RuÆ™ayya?”.



Murmushi Innayi tayi kana ta gyaÉ—a masa kai tare da faÉ—in.



“Eh”.



Duk da yawan shekaru kuwa sun gane juna



Cikin wani irin sauri ya juya tare da nufar cikin Fada yana
shiga ya durƙusa agaban Sarki duk da cewa yana tare da mutane na hannun damansa
suna tattauna akan al'amarin Moddibo da yanda zasu bayyanar dashi a Masarauta
ga yan uwansa.



Ganin yanda ya gurfana ne yasa Sarkin zagi cewa.



“Hattara dai Sarkin Ƙofa, mene tafe da kai?”.



Cikin rawan murya tare da tsantsan farin ciki yace.



“Al'amarine mai girmane yake tafe dani”.



Duk idanu mutanen Fadan suka zuba masa ganin yanda fuskarsa
ke É—auke da tarin zumuÉ—in isar da labarin.



Sarkin Fada kuwa cike da kulawa yace.



“Shin wannan wani al'amari ne?”.



Aƙage Sarkin ƙofa ya sake risinar da kansa kana yace.



“Ina so abani izini ne nayiwa Innare Tsohuwar Jakadiyar
Gimbiya RuÆ™ayya iso wacce ta É“ace tare da Alieeyu tsawon shekara talatin”.



Wani irin murmushi Sarki Youseef Mouley ya saki mai cike da
zallan farin ciki da jin daÉ—i acikin ransa yace.



Alhamdulillah ta amsa kiranmu kenan lallai wannan ya nuna ta
riƙe mana ɗanmu da amana da aminci bata kuma wofintar da al'amuran sa ba tana
bibiye dashi, yanzu tsawon kwanaki biyar bataji labarinsane ta bibiyi al'amarin
sa gashi ta nufo nan ne kuma da yaƙinin cewa tabbas daya shigo ƙasar nan zai
dawo Mahaifarsa.



Afili kuma murmushi ya sakarwa Sarkin Ƙofa kana cike da
nutsuwa da kamala kana da ƙasaita irin na sarauta ya masa alama da hannu ta
shigo...



 



Cikin sauri Sarkin Ƙofa ya miƙe kana ya fita kallin Innayi
dake tsaye jikin mota yayi tare da faÉ—in.



“Bismillah”.



Innayi kuwa juyawa tayi tare da kallon su Abban Jameel kana
tace.



“Ku É—an yi haÆ™uri ina zuwa”.



Su kuwa baki É—aya cike da É—umbin mamaki suke kallonta.



Cikin sauƙe numfashi Hajja Nana ta gyaɗa kai tare da cewa.



“Toh mu dai munfi karfin saiduwa, koda an kawo mu nan da
za'a sayar damu ne bazamu saiduba”.



Sai kuma ta juya ta kalli Khausar dake zaune gefenta wacce
idanunta suka kumbura sukayi ja jawur gashin idanu suka jiƙe yayin da suka ƙara
tsayi kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar tasha kuka tamkar mai isarta cikin taɓe
baki tace.



“Toh kuma kukan me kikayi tunda, ai burinki ya cika, ba dai
auren wanda ba'asa asalinsa ba, ai gashi dai kinga kuma wata duniyar da aka
kawo mu, ko mai za'a ce mana ko mai za'a mana kuma oho domin wannan al'amari
dai yafi kama da almara”.



KhausarMouleey ya jinjina tare da faÉ—in.



“Ai nan Fada ce mai mutunci da karrama baÆ™o”.



Sake sunkuyar da kanta tayi kana tace.



“Ranka ya daÉ—e baÆ™in suna da yawa”.



Murmushi yayi tare da cewa.



“Koda ace baÆ™i É—aya Yan yanki da kuke kika É—ebo ba zasu rasa
muhalli acikin wannan Masarautar tamu ba”.



Lallausan murmushi ta saki tare da jinjina kai kana tace.



“Toh abani jagora wanda zai kai mu masauÆ™in baÆ™in namu.



Kai ya jinjina kana yace.



“Toh shikenan babu damuwa”.



Kallon Jakadiyar sa yayi tare da faÉ—in.



“Jakadiya Bismillah akai su sashen Yamma a saman za'a
sauÆ™i”.



Bi'ana saman inda Modibbo yake kenan



Sake sunkuyar da kai Innayi tayi tare da faÉ—in.



“Ranka ya daÉ—e Akwai maza tare kuma damu mata”.



“Baki da matsala”.



Ya faɗa tare da kallon Sarkin Ƙofa kana yace.



“Kai kuma ka kai Mazan Ƙofan Gabas”.



Kai ya gyaÉ—a cike da girmamawa yace.



“Toh”.



Kana suka fice yayin da Jakadiya ta yiwa Innayi, Hajja Nana,
Ummi, Hajiya Bunayya, Asma'u, Asiya, Dija, Khausar, Aunty Hawwa  da Hajja Umma Baki daya bayan Jakadiya suka
bi tayi musu Jagora.



   Yayin da Abban
Jameel, Baffa Jimeta, Lamiɗo, Haiydar suka bi bayan Sarkin ƙofa wani babban
Hanya suka bi kana suka hau Upstairs



Suna haura wa saiga wasu Ƙofofi biyu ɗaya aɓarin dama ɗaya aɓarin
hagu Jakadiya takai su Innayi ƙofar dama yayin da Su Abban Jameel aka kaisu
ƙofan hagu ta can gefen yamma wanda bata cikin falon da Modibbo yakeba suka ɓula
ba sai dai in zadu sauƙo in sunbi ta ƙofar tsaki ta cikin falon zasu bulla...



 



Jakadiya kuwa tana fita daga masauƙin su Innayi kai tsaye ɗakin
Didi ta nufa tana shiga falon ta zube agaban Didi tare da faÉ—in.



“Albishir”.



Fuska É—auke da murmushi Didi tace.



“Goro”.



Sake risinar da kai Jakadiya tayi kana tace.



“Fari ko Ja?”.



Still Didi na murmushi tace.



“Faro soll Dan Æ™walele”.



Washe baki Jakadiya tayi tare da cewa.



“Toh Innare na cikin Fadar Masarautar Mouley ta iso tare da
al'umma baki, daga cikinsu akwai masu tarin kamala da Alkunya kana tazo mana da
kyakykyawan furanni masu haska gida”.



Didi kuwa cikin matsanancin farin ciki da jin daɗi ta miƙe
kana tace.



“Masha Allah Alhamdulillah ta ina take, muje ki kaini
gareta”.



Kai Jakadiya ta girgiza cike da ladabi tace.



“Amma da kiyi haÆ™uri ki koma ki zauna yanzu dai, farko a
fara Marabtansu da abubuwan motsa baki saboda sun É—ebo hanya sannan asanar da
hadimai afara yi musu girki na musamman domin maraba”.



Cike da gamsuwa Didi ta jinjina kai kana ta kalli Hadimanta
dake durƙushe ƙasa tace.



“Maza kuje É“angaren Hadiman dake Kichen kuce maza ashirya
abinci na alfarma yanzu”.



Cike da ladabi suka amsa kana suka fita.



  Didi kuwa cikin wani
irin farin ciki da annashuwa kana da jinjina girma da mutuntaka irin na Innayi
ta kalli Jakadiya tare da faÉ—in.



“Maza ashirya musu drinks, Fruits, Snack's,da É—an gashshen
nama sannan akwai nono mai sanyi da kwakwa ahaÉ—a musu”.



Ta ƙare mgnar tare da kallon Lalla Khadijah sai kuma tace.



“Khadija keda Hafsat ku jagoranci aikin”.



Kai suka jinjina kana atake suka haÉ—a suka kai sashen su
Innayi da kuma sashen su Abban Jameel...



 



Acan É“angaren su Hajiya Bunayya kuwa tunda tashiga
tangamemen Falon da yaji komai na more rayuwa take kallon komai cikin ƙunan
zuciya mamaki da kuma tarin takaici....



Innayi kuwa suna zama ta kamo hannun Khausar  da har zuwa lokacin take shesh-sheÆ™an kuka
kana ta riƙo Asma'u yayin da Ummi ke biye dasu suka nufi ɗaya daga cikin ɗakin
da yake  3bedrooms ne.



Ƙofar da shine na tsakiya suka shiga.



Suna shiga ta saki sassayyan numfashi tare da sakin hannun
Khausar sai kuma ta zaunar da ita gefen gadon kana ta juya ta fita.



Fitanta yayi daidai da shigowar Hadimai mata suka shigo da
Fruits suka ajiye cike da girmamawa suka gaishesu kana suka ce...



Gimbiya tace ayi muku sannu da zuwa sannan ga abubuwan motsa
baki kuci kafin ta iso.



Godiya sukayi kana sukuma suka fice ba daÉ—ewa suka sake dawo
wasu hannunsu riƙe da drinks,wasu Snack's wasu dambun dabbi da soyayyu.



Yayin da Lalla Khadijah da Lalla Hafsat ke riƙe da wasu
Bowls manya da yaji Kindirmo da kwakwa da ayaba suka ajiye.



Cikin tsura musu ido Innayi ta kalli Lalla Khadijah kana ta
juyo ta kalli Lalla Hafsat.



Sai kuma ta saki murmushi gani sun ruggumeta cikin bege da
kewarsu Innayi tace.



“Allah mai iko da buwaya Khadijah kune kuka girma haka”.



Sai kuma ta kalli Lalla Hafsat dake faÉ—in.



“Innayi ashe dai rai kanga rai, baki wani canza ba”.



Cikin mamaki dai Hajja Nana Hajia Bunayyah da dukkan su suka
zuba masu ido.



Gaisawa sukayi bayan sun zauna.



Cikin kula  Lalla
Khadijah tace.



“Hafsat muje ko, mu barsu susha ruwa".



Kai Hafsat ta gyaÉ—a kana suka juya suka tafi hadimansu na
taka musu.



 



Kana acan É“angaren su LamiÉ—o suma haka aka kai musu.



Cikin sauƙe numfashi Baffa Jimeta ya kalli Abban Jameel
bayan fitar Hadiman kana yace.



“Toh Alh Bashir wannan al'amari dai da ban mamaki da kuma É—aure
kai yake toh shi wannan yaro na rasa tantance inda al'amarinsa ya nufa”.



Murmushi Abban Jameel 
kana ya yace.



“Nan shine gidansu Modibbo kamar yadda kakarsa ta labarta
min shi É—an wannan ahlin ne, gidansu ne kuma tsatso kuma jigo sannan kuma
tushen sa mahaifarsa kenan”.



Kai Baffa Jimeta ya gyaÉ—a cike da gamsuwa yace.



“Ikon Allah wannan al'ajabi da yawa yake,ita kuma daga
wannan ƙasa ta tashi ta koma Nigeria har Lungunmun can taje ta zauna dashi.



 wannan wani irin
al'amari ne yasa ta ficewa daga nan ta koma can”.



Zazzafan ajiyar zuciya Abban Jameel ya sauƙe kana ya gyara
zamansa tare da cewa.



“Al'amarine mai girma mai kuma ban mamaki”.



 



Numfashi LamiÉ—o ya fesar wanda tunda aka fara magana bai ce
komai ba ya muskuta kana yace.



“Ai wato sha'ani 
Masarauta sai ahankali idan bakayi Sa'a ba sai a saubata maka rayuwa! A
banza”.



Abban Jameel na taunar Inabi yace.



“Hakanne ma yaso kasancewa shiyasa ta gudu da Moddibo domin
tseratar da rayuwarsa”.



Baffa Jimeta na kurɓan drinks Mai sanyi yace.



“Allah mai iko”.



Daga nan kuma sai suka rufe maganar tare da cin kayan
maƙulashen da aka kawo musu bayan sun gamane Dr Ahmad da sauran masu jan
motocin suka sakkamesu suka tafi.



 



ÆŠaya daga cikin Hadiman dake sashin ne ya shigo cike da
ladabi ya kallesu kana yace.



“Ga banÉ—aki sannan ga É—akuna akwai duk wani abin buÆ™ata da
zaku buÆ™ace”.



Murmushi LamiÉ—o yayi kana yace.



“Mumgode”



Daga haka ya juya ya fice.



 



Bayan awa É—aya, sun ci sun sha Hajiya Bunayya ta kalli Hajja
Nana dake goge baki da Tissue tace.



“Wannan al'amari dai da É—ure kai yake”.



Cikin taɓe baki Hajja Nana tace.



“Toh Ni dai fatana dai Allah yasa basayar damu akazo yi ba
ehee”.



Dariya mai sauti Innayi ta sanya ganin yanda Hajja ke magana
tsakaninta da Allah cike da kamala tace.



“Babu Sai dawa sai karramawa wanda gadon mune, kuma ma in
banda abinki a saidaku a nemi me, ki dai dubafa duk wata É“ukata da É—an Adam
yake dashi muna dashi a masarautarmu”.



Ummi kam murmushi kawai take, dan talura Hajja Nana da
innayi har yanzu ba'a shiryaba.



 



Suna cikin haka sukaji sallama, tare da ganin jagorancin
Hadiman Didi



Cike da zaƙuwa ta tashigo tare da Jakadiyar ta da kuma Kakar
Moddibo Niyna sai kuma su Rahama bakinsu É—auke da sallama.



Innayi na ganin Didi tayi saurin miƙewa tare da durƙusawa
agabanta kana ta sunkuyar da kanta ƙasa batare da tace Uffan ba.



  Didi kuwa cikin
yalwataccen farin ciki ta tsugunna tare da sanya hannunta akafaÉ—ar Innayi kana
ta É—agota ta tsayar da ita suna fuskar juna, sai kuma kawai ta ruggumeta tare
da faÉ—in.



“Kin gama min komai Innayi kiyi min duk kan abinda É—an Adam
zai yiwa abokin zamansa na halacci, daga yau na Æ´an taki kin tashi daga Baiwa
kin zama Æ´a Æ´an tacciya kuma Uwa amintacciya kuma kamila kuma cikekkiyar
jakadar sarki mai jirangado”.



Dariya mai sauti Innayi ta sanya wanda ke nuni da zallan
farin ciki kana tace



“Alhamdulillah Nagode wa Allah ina tahowa zuciyata na
tsinkewa ina tunanin shin ya rayuwa ta kasance shin ana raye ko kuma anbar
duniya zuciyata ta cika da fargaba”.



Baki É—aya mutanen falon kallonsu suke cike da tsantsar
mamaki musamman Hajiya Bunayya da wani irin zufan hasada ke fita agoshinta.



Innayi kuwa cike da annashuwa ta cigaba da faÉ—in.



“Amma Alhamdulillah nayi katari da Youseef akan karagar
mulki kana kema nayi katarin dake acikin shigar Gimbiyya amma banga Ubangida
naba Sarki Muhammad Aliyu Mouley”.



Kai Jakadiya ta girgiza kana tace.



“Allah yayiwa Sarki Muhammad rasuwa yanzu É—anki ne Youseef
akan Mulki”.



Cikin sanyi Innayi tace.



“Allah sarki, Sarki Muhammad Mouleey. Ubangji Allah yajiÆ™an
sa da Rahma”.



Amin suka amsa a tare,



Ita kuwa innayi juyawa tayi tare da kallonsu Hajja Nana da
suka zubo musu idanu sai kuma ta maida idanunta kan Didi tace.



“Yanzu dai idan na fahimta Moddibona Aliyuna shine Yariman
Masarautar nan? kuma Sarki Mai Jiran gado?”.



Yalwataccen murmushi Didi ta Saki kana tace.



“Tabbas kuwa shine É—a Namiji babba A masarautar nan kuma É—a
Mai jiran gado Ahamdulillah kuma ya dawo alokacin da Masarauta ke jiranshi”.



Kai Jakadiya ta jinjina kana tace.



“Sosai kam”.



Didi kuwa cike da nutsuwa ta nufi kujeran dake tsakiyarsu
kana ta zauna murmushi ta sakar musu da lallausan murmushi tare da faÉ—in.



“JaÉ“É“ama MoÉ—on”.



Ga Mamakinsu sai sukaji tayi musu magana cikin Harshen
Fullanci.



 Cikin yanayin mamaki
Hajja Nana tace.



“Allah bauÉ—o be Fulfulde voli, kamar da fulatanci kike yi
mgn fa ko?”.



Murmushi ta saki kana tace.



“Sosai ma kuwa Asalina Bafulatanar Adamawa ce ni É—uyace ga
Sarkin JoÉ—ah Sheiykh Jabeer”.



Kai Hajja Nana ta jinjina kana tace.



“Ai kuwa lallai gashi Yaren da kike mana dashi ya tabbatar mana
da hakan”.



Wani irin zufa mai kamar tafasasshen ruwan zafine ke
tsats-tsafowa Hajiya Bunayya abaki É—aya ilahirin jikinta acikin ranta take mgn
kamar zautacciya.



“Toh shin Me hakan yake nufi, kenan haka nufin Khausar tayi
katari ta tsinci dami a akala? Ko shegiyar yarinyar da wayo kamar dala, ko dai
dama ita tasan Modibbo É—an manya ne, kaji shegiyar yarinya da iya bada kafa,
yoh da na sani ai wlh shi Amina zata aura.



Ashe Samira da abinda ta hanga.”



Gaba É—aya tayi kasake ta tafi dogon tunanin.



Ƙanwar Mommy Aunty Hajara. cike da farin ciki tace.



“Khausar Lelelwal asheko da gaske Lelelwal É—ince ke”.



Murmushi Aunty Ruƙayya tayi kana tace.



“Tabbas kuwa abu yayi yadda ran masoya ke so.   Dama wani hanin ga Allah Baiwa ce”.



Hira suka cigaba dayi cike da farin ciki da mutunta juna saɓanin
Hajiya Bunayya dake cikin tashin hankali da ƙunan zuciya.



 



 Acan É“angaren su
Abban Jameel kuwa Sarki Youseef Mouley da Sheik Jabeer ne suka nufi masauƙin
su.



Sheikh LamiÉ—o na kallon Sheikh Jabeer ya faÉ—aÉ—a murmushin
fuskarsa cike da kamala yace.



“Allah nhokke sabugo Sarkin JoÉ—a kana shagaban Æ™ungiyar
TABITAL POOLAKU, da mi yetti Allah da kansa ne a nan?”.



Kai Sheykh Jabeer ya jinjina kana cike da girmamawa yace.



“Ikon Allah Allah yayi mun haÉ—u kenan?”.



Murmushi Lamido yayi tare da zamewa gefensa dan shi kansa
yasan idan ana batun sarauta toh in su Sheiykh Jabeer na kusa shi dole a ƙasa
zai zauna.



Shi kuwa Sheykh Jabeer cikin kamala da kulawa yace.



“Ikon Allah sai kuma muka haÉ—u anan, amma yanzu dai ku huta
in Allah ya kaimu gobe sai muji meke tafe daku?”.



Cikin gamsu Lamido da Abban Jameel sukace to.



Su kuwa daga nan suka fice...



 



Acan É“angaren su Didi ma Sallama suka yiwa su Innayi tare da
faÉ—in su huta gobe zasu ci gaba da tattaunawa Godiya sukayi musu kana suka
fice.



Washe gari da safe misalin ƙarfe 9:00am Innayi, Hajja Nana,
Jakadiya Sheikh Jabeer, Sarki Youseef Mouley, Galadima, Waziri,  Didi Abban Jameel, Ummi, Baffa Jimeta LamiÉ—o
jakadiyarta zaune suke wuri na musamman kuma keɓantaccen palon Abualeey wato
sarki Youseef Mouley kenan. yayin da baki daya idanunsu ke kan Innayi.



Innayi kuwa cikin sauƙe numfashi ta cigaba da basu labarin
tun randa ta tafi da Modibbo ta wuce Nigeria dashi kana ta nufi Taraba yankin
Gembulan sabida sanin yanki fulanine domin Didi na bata labarin, kuma ta iya
fulatanci tun a lokacin domin Modibbo shine É—a na shida a wurin iyayensa daga
Khadijah da Hafsat sai da akayi ya'ya uku maza duk basa gama arba'in ake
nemansu a rasa sai bayan kwanaki sai a tsinci gawarsu. A wannan lokacin kuma
Khadijah da Hafsat sunyi girma da bazasu mance kamannin innayi ba shiyasa sunka
ganeta.



Fesar da numfashi innayi tayi kana taci gaba da labarta
musu, yanda ta rayu da Moddibo yanda ya taso da yanda yayi karatu, da irin
Æ™alubalen daya fuskanta, da amintakarsa da Jameel  har zuwa mutuwar M Jameel da kuma dalilin
zuwansa Morocco da kuma irin ƙalubale da baƙaƙen magana da kuma hantara da suka
samu awajen mutane kana ta É—ora kuma da wasiyyar da M Jameel ya bar musu akan
Modibbo, haÉ—in da basu labarin Khausar da dole in dai za'a bada labarin Modibbo
da Jameel toh dole cikaton na uku Khausar ce.



Didi Kam lumshe idanunta tayi wani abin idan taji tayi
murmushi wani ta zubda hawaye saboda tausayin halin da É—an ta yakasance cikin
na rashin aminisa da kuma rashin su a kusa dashi da ya zame masa sanadin da ake
shegantashi.



Cikin sanyin murya tace.



“Allah sarki É—ana Jameel Allah baiyi zamu ganka ba bare muyi
maka godiyar kekkyawar amintakarka da gudan jinin, sai dai Alhamdulillah Innayi
tunda Jameel bai mutu da rashin sanin iyayen amininsa, in Sha Allah mukuwa  zamu kasance mashinyi mishi addu'a a tsawon
rayuwarmu. Ummin Jameel Ngd MATUƘA Abban Jameel babu abinda zance daku sai
addu'a. tabbas Aliyu na kuma yaga jarrabawar rayuwa wanda nasan ya samu darussan
rayuwa masu tarin yawa acikinsu  Innayi
na gode kinyi min halarcin da bazan taɓa mantawa ba kin tseratar da rayuwar ɗana
alokacin da ake neman hallakasa kamar yadda akayi ta hallaka yan uwansa da suka
gabata”.



Murmushi Innayi tayi kana tace.



“Wannan yiwa kai ne sannan babu godiya tsakanin mu domin kin
cancanci fiye da haka sabida matsayin uwa kika riƙeni ba Hadimarkiba, shiyasa
nima nayi miki abinda zan iya yiwa Æ´aÆ´ana na cikina”.



Kai Didi ta jinjina tare da juyowa ta kalli Ummin Jameel
dake sharce hawaye cikin sanyi tace.



“Ummin Jameel kada kiyi kuka ga Aliyu na in Sha Allah ya
ishemu nidake baki É—aya”.



Cikin gamsuwa  Ummu
tace.



“In sha Allah kuwa”.



Innayi kuma gyara zamanta tayi tare da cewa.



“Toh Alhamdulillah bayan ta howarsa  nan.



Muka gama mgnar komai akan Khausar da bai sani ba. toh Alhamdulillah
dama acikin labarin dana baku na faÉ—a muku wasiyyar da amininsa Jameel ya bari
toh Alhamdulillah a makkoni biyu da suka gabata an Aura masa Khausar”.



Cikin wani irin Didi ta kalli innayi tare da cewa.



“Aliyun akayiwa aure!”.



Da sauri innayi ta gyaɗa mata kai kana tayi ƙasa da kanta.



Sai kuma innayi tayi saurin É—ago kanta jin Didina faÉ—in.



“A....!



 



Ba editing kam



 



*Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn,
masu cewa wai sun goda suga number'n nayine, ko kuma a'a bari dai in na shirya
zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuÉ—in bai cikaba tukun sai sun cika, ko
kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh in ba iyayiba ai duk nisan state da
kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen wajema.
Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba ku daina
min mgnar ku bari sai kun shirya,kada kizo ki É“ata min lokaci a banza, wlh ni
na tsani harkar karanta, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuÉ—in kaya
ga account no ga numberta ai sai ki biya kawai kafin kimin mgn. Tunda dai ga
alamominshi da duk illar da yakeyi na faɗi in kina dashi faƙat in babu kada ki
wani zo kice min bayani dan ko kinzo iya bayanin da zan miki kenan*



Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin
gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin.
Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya,
melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. BuÉ—ewar gaba,
domin har budurwa infection na iya buÉ—ata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi
al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin
wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma
saduwa, da dai sauran abubudann ban 
lissafa. Sune manyan alamomin infection.



Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman
kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari
kiji illolin infection wato cutar sanyi.



Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin
kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi
bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiÉ—a ta
lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya,
zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk
tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki
nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.



KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA
BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya
dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da
zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki
magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau,  duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji
sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta
gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai
kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic
infection ne yar uwa.



INFECTION set É—inmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara,
Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar
komai Maganin na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk
nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi,
cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da
maganin set É—in na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki
ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da
mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da
shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai
sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a
jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita
miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin
garin yasa ina raba rabin set É—in in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set É—in
10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz
bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuÉ—inki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP
NUMBER'N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi
Available ko yau kika tura kuÉ—inki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko
sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na
mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki
shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR
MA'AURATA.

No comments