Matar makaho 7

 





Page7️⃣

*A hankali nakejin sanyin asuba na  ratsani har cikin kashi kowa yasan yanda sanyin asuba yake alokacin zafi,


*Juyi nayi a hankali Amma sai me jina nayi Kamar Abu ya tukare ni, bude ido nayi sosai, me Zan gani ni Sumayya  a kwance rabe-rabe a jikin MAKAHO, ai bansan sa'ilinda da na wantsala gefe ba, kwalbar maganin sauro na buge harya fadi a simintin dakali, ya fashe


Jin Karan fashewan Abu shiya farkar dashi cikin sauri ya mike Yana tambaya ta lfy?


**Nikam na kasa basa amsa toh me zance? cewa zanyi ka tabani Koh Kuna nace ajikinka na farka na ganni *


Cikin Dan daburcewa nake magana" am am Babu fa Daman na tashine ban sani ba na buge kwalba ya fashe"


Bai dai ji Miki ciwo ba ya fada cikin hanzarin karasuwa wajen da yake jiyo muryata,

"Ah ah  banji ciwo ba"

Ok Allah ya kiyaye gaba, 

*Da Amin na amsa *

Daga ni harshi Alwala muka  hanzarta farawa Jin har anyi raka'a daya a masallaci,

Muna kammala Alwala daki ya bude ya cire kayan jikinsa yadau jallabiya ya saka ya,

 

*Nikam hijab kawai na dauka har kasa, sai sallaya biyu nazo na shinfida Mana Jin an sallame sallah a masallaci, 


*Na hau Kan sallaya Daya nayi gyran  murya *


Jin hakan yasa a hankali ya Suma takawa Yana nufo inda yaji nake tsaye ganin ni yake nufuwa yasa" nace ga sallah na shimfida maka tunda Naga baka samu jam'i ba"

Ba musu ya ringa lalube harya Ji kafarsa ya taka wani abu Mai laushi sosai Wanda laushin ya banbanta da cafet in dakin,hakan yasa she gane sallaya ne " Hawa yayi ya saita gabar ya Tada sallah Ina binsa,


Muna idarwa Naga ya Kama karatun Alkur'ani cikin suratul Qafe cikin zazzakar muryarsa Mai dauke da nutsuwa irin na mamilallun maza,da Kai (hadda) 


Nima.mikewa nayi na dauko Qur'an na bude Ina duba ayoyin da yake karantawa,harya Kai karshe ba gargada Koh wani harafi an basa hakkinsa, 


sosai nayi mamaki Amma Dana tuna ido kawai Allah ya jarabcisa  ba zuciya Koh k'wakwalwa bane, ba abin mamaki bane, sai da yakai karshen surah.


*Mukaye azkar sai kusan bakwai na tashi nade sallaya nayi nayi waje,


Duk da akwai NEPA hakan Bai saka na kwanta ba fita waje nayi na tattara Mana shimfidar na mayar daki,

Tsintsiya na dauka na share baranda na fara sharan qasa,


Jin Bata dawo ta kwanta ba Kuma yaji tana shara yasa ya mike yayi waje shima,


Gaidani yaye na amsa ba yabo ba fallasa, takalmin sa ya saka cikin lalube yayi kitchen wajen da yasan Ina Tara kwanuka da bojuwaye yafara tattarawa Yana kawowa mawanki harya Gama kwashewa,

Boket ya dauka. Randa ya wuce a hankali ya dau Moda dake Kan randan da hannu daya ya bude randan da daya hannun sa,  moda ya zura a randa zai ibi ruwa yaji wayam,sai da ya rank'wafa kafun yaji  ruwa,


 hakan ya nuna masa  ruwan Randa saura kadan fasa iban yaye ya dauki boket in ya Kama hanyan fita"


Ganin ya Kama hanyan fitane,yasani tambayr sa" Ina zaka da boket kuma"?

Cikin sanyin sa na halitta yace, ruwan Randa saura kadan Inna iba bazaki samu na aiki ba shiyasa Zan Iba a rijiya"


"Rijiya"? Na sake tambayar sa,

Eh yaban amsa, Kamar Zan hanasa,sai kuma nayi shuru na Kama kwashe shara,


Jin bance kome ba yasa shi cigaba da tsayuwa,

*Ganin yaki tafiya yasani cewa "yakuma ka saya"


Fita yayi, ni Kuma na shiga kitchen na Kama hada breakfast,

Yana fita rijiya ya nufa da lalube harya Isa Dayake rijiyar ba bakwansa bane Yana gane hanya,  ya lalube guga a gyfen rijiya, ya zura hade da Bismillah,

sai da ya Bari na Yan second kad'an kafun ya sake dagawa Jin ta cika yasa yaja, sai da ya cika boket dam kafun ya sunkuce boket da hannu d'aya d'ayar hannun yana lalubar hanya har ya samu ya shigo kofar ya zuba a Randa, 


Ganin wahalan da yasha kafa d'aya ma kafun ya kawo duk rabi ya zube Masa a jiki gashe yafi minti 10 daga rijiya zuwa kofar mu Yana lalube kafun ya gane,


Haka kawai na tsinci kaina da" dakatar dashi ganin Yana kokarin juyawa ya karo


Ka bar iban ruwan nan an.... Ban karasa ba saboda ganin  d'aya Daga cikin yaran gidan budurwa ta shigo ba Koh sallama, tana cewa


Wai inji inno ka Bata d'ari biyu zata sai goro, 

Cikin sanyi yace  yau ban kwana da kudi ba sai naira d'ari d'aya kacal Kuma ita nake son saya Mana kayan miya zamu karya, tayi hakuri zuwa anjima inna fita na samu ciniki Zan bada a kawo mata,


Cikin bala'i take cewa eh lallai watoh matar ka tafi inno kenan, dadin abin munsan auren liki aka maka ba Wai don ka Kai abaka ba, shidai kala baice Mata ba.


Ke Kuma  duk kudin da kike dashi Koh nace gidanku suke dashi sai kin jira D'arin karyawa  mtwss,tana fada tana nunani,


*Ai bansan lokacin da nayi  super ba na saya a gaban ta " keee karki kuskura ki sake sakani a cikin haukarki na jahilci karki yarda  in karta Miki layin rashin mutunci a gidan nan iskancin ku ya tsaya ku wak'u karku kuskura ku sani,

idan takamarku bariki da rashin kunya wallahih ni Zan gyara Miki zama,"


"bace min daga gani" cikin tsawa na karasa maganar,Ina nuna Mata kofa,


Tabbas ta tsorata Dani sosai don Bata dauka Ina da baki haka ba,da saurinta harda tuntube ta fita,


Juyawa nayi na kalle sa Yana tsaye Kamar ruwa yacisa,


Wani abu Mai kamada tausayi-tausayi takaici-takaici ya kamani, ganin kwata kwata na rasa me yasa Yan gidan nan suka Raina Masa wayone oho,


*Daki na shiga na d'au jakana gudan dubu na dauko * fitowa ta yayi daidai da shigowar wata dattijuwar Mata cikin bala'i ta,toh Ina kike karamar Mara kunya, harkin Isa ki shigo gida jiya jiya ki nuna Mana iskanci, Daman tunda Naga yau kwananki uku a gidan nan Koh gaishemu baki zo kinye ba nasan ba banza Kika rasa miji ba Rana tsaka aka lika Masa ke,

* ba tare da na kalle taba nace, 


"Yayan khadija pls ka Bata kudin da ya kwana a aljuhunkan, ba musu ya lalube jallabiyarsa ya d'auka ya Mika mata, fizga tayi tana ta tsababi zadai kaji da munafurcinka, 

*daga ni harshe bamu tanka mataba harta fita,


*Albarkacin girmanta yasa naja bakina bance kome ba,


Jin ta fita yasa na Mika Masa dubu d'ayar "gashi ka sai kayan Miya Mai D'an yawa  Dana shaye ka hada da Kiran Mai ruwa"


cikin sanyi yake cewa, kiye hakuri Sumayya Nike da alhakin daukar nauyinki akaina bazan iyya karban kudin kiba, sannan Ina Mai baki hakuri da abinda Yan gidan mu sukayi Miki,


Bari naje  na karbo kayan miyan da na shaye,


"Da wani kudi Koh ba yanzun naji kace D'arin ne da Kai ba"? 


Eh hakane Amma Zan karbi kayan a shago Inna fita sana'a Allah ya bada kasuwa tunda mak'wancina ne saina Mika Masa Amma ni bazan iyya karban kudinki ba.


"Au ni in cema akaye kyauta na baka ai bashine Inka tashi ka biyani" nace Masa ganin da gaske bashin xai fita ya karba,


D'an Jim yayi sai Kuma ya karba ya fita, kitchen na koma na sauke macaroni ganin ya nuna na juye a kwando,


Wanke wanken da ya Tara na Kama wanke wa da yake babu yawa plt ne biyu sai cup biyu shukali sai bojuwa biyu, kafun ya dawo harna kammala

 Yana dawowa nayi miyan stew da kefe busheshe manya-manya, guda biyu Wanda aka mini caton guda na gara


Wanka yayi ya chanja kaya  ya kwanta a kujiran daki,


Ina Gama girkin na zuba Masa na Kai Masa daki hade da gyran murya na fita 


Wanka nayi  na shiga daki da towel Mai Dan girma na daura yaukam zama nayi na shafa Mai da powder NASA kwalli sai man baki, 


Yana Gama ci ya ibi Kwanukan yakai waje, *Yana fita na ibi Kayana na saka rigane Abaya Mai kyau sosai ya karbi jikina gyelen na  daura a kaina,


Na kurawa kaina ido a madubi bansan lokacin da hawaye ya taru a idanuna ba,


 *Sun Rabani da aikina sun saka mahaifina ya datse mini Account Wanda da gumina na Tara Rabin kudin da ke ciki,sanan

Kaf jalingo su rasa mijin da zasu aura min sai MAKAHON miji Wanda Koh kwalliya nayi baisan nayi ba,  ni Karan kaina ma, sunar Ina matar sa Bai San ya nake ba, in badai muryata yaji ba bazaisan Ina wajen  ba, me nai musu a rayuwa mina tsare musu basa kaunan cigaba na komin kankantarsa, a matsayin su na Yan uwa ga mahaifina. Duk a Raina nake zancen nan hawaye nabin kumatuna,


Kinyi kyau,


*abazata na juya cikin mamaki jin muryansa a dakin wanda bansan yaushe ya shigo ba Yana tsaye idonsa a.......




🪀My WhatsApp number

08084453785

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯 

             ~ Na ~


 🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃


✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa 👌

Free book🤧


No comments