Matar makaho 68-69

 


Page6⃣8⃣&6⃣9⃣

Da mamaki take kallonsa"kaine da daren nan?





Kala Ammar baice ba, mika mata goran dake hannunsa d'auke da kunun aya.


Da sauri sumayya ta karba, ta fara kokarin budewa jikin ta har rawa yake.


Sumayya ki tashi ki tafi daki mana, yanzun fa 3:30 na asuba amma kinzo nan kin wani zauna kamar turmin tsakar gida, kina wani bude gora, sha zakiyi anan?don Allah tashi muje na rakaki ciki.


Shuru sumayya tayi taki tashi kafa goran tayi a baki zata sha, da sauri ya fizge goran, kinsan Allah in bazaki bi abinda nake so ba, in ban koma da kunun nan ba.


Da sauri ta mike tsaye, sai kuma ta juya tana kallon sa "toh ka bani mana"?


Mika mata yayi, yayi gaba tana binsa a baya har suka iso block in da take, goggo ne da khadija tsaye a kofar d'akin sun zuba musu ido, juyawa Ammar yayi zaima sumayya magana, kawai ya ganta tsaye da gora a hannu babu kunu, da mamaki yace  kuttt ke sumayya tafiya kike kina sha koh me naga gora ba kome?


Shuru tayi sai kuma ta bata fuska, guda d'aya fa ka kawo mini, ina ma laifin takwas.


Takwas???goggo da Ammar harda khadija suka hada baki wajen tambayar ta.


Sumayya kinsan gora d'ayan nan ma, a ina na samosa bayan likita ya kirani yace khadija taje ta same sa, akan kinason kunu?


Kunya nema ya kama sumayya, a hankali ta wuce d'akin goggo da ido ta bita tana kintsima abu  a ranta .


D'akin sumayya ta shiga rike da goran, ajewa tayi ta kwanta abinta a take bacci ya d'auke ta.


Ammar ma tafiyar sa yayi, khadija da goggo ma duk komawa sukayi suka kwanta.


Da asuba bayan sunyi sallah, sosai sumayya ta uzura ma khadija Akan kunun aya, haka khadija tun asuba taje bakin get ta zauna har saida masu tallah suka fara fitowa, bata samu kunu ba sai 8:00 na safe, ta sayawa sumayya gora uku.


Tana shigowa ta samu sumayya zaune a bakin d'akin, koh magani takisha duk yanda nurse sukayi da ita taki, koh ruwa tace an daina saka mata kenan Alamu dai yau da rigima ta tashi.


Tun daga nesa sumayya ta hango khadija mikewa tayi da sauri ta nufeta, "habba khadija zuwa sayan kunun ne, saikije ki zauna"?


Yi hakuri Aunty wallahi masu kunun ne basu bude ba saida na jirasu.


Karban kunun sumayya tayi ta nufi d'akin zama tayi, takama sha.


Khadija kam.kwanuka ta tsina da kayan sumayya masu datti, zata koma gida.


"khadija inkin koma gida kibi wajen shagari,  ya baki dabino, da kudi kisai min aya rabin kwano, da sugar da kwakwa flavour kimin kunun aya,  kisa a firij in zaki taho saiki zomin dashi"


Tab Aradu Aunty ban iyya kunun aya ba.


"Baki iyya bafa kikace khadija"?sumayya tace tana kallon goggo, dake ta binta da kallo tunda gari ya waye.


Kauda kai tayi tama khadija bayanin yanda zata had'a kunun, dayake baida wahala yasa khadija ganewa.


Tana zuwa kamar yanda sumayya tace hakan tayi shagari dubu biyu ya bata, taje tayiwa sumayya sayaya har change ya rage, kunun ta dama mata tasa a firij kafun la'asar yayi sanyi haka ta jidi kunun a gora kusan 6 ta kaima sumayya hospital sauran ta barsu a firij.


Yau sosai jikin sumayya yayi sauki kamar ba ita ba, da yamma da Ammar yazo likita ya basu discharge,Ammar da khadija ne suke tattara kayayyaki suna kaiwa mota.


Sumayya ce tsaye a jikin motar Ammar, sanyi take da riga da siket na atamfa sai hijab mai corona, sosai kayan ya karbeta gashi tayi wani irin fari tayi fresh sosai, idanun nan nata sun kara fitowa sosai saboda kumburin da kasan idon yayi kamar mai ciwon ido,  saidai kwayar idon ya kara haske, rike take da goran kunun ta da ya rage kuda d'aya a hannu duk da basha take ba a lokacin.


Tun daga nesa yake kare mata kallo,  shikaran kansa ya rasa wani irin ciwo ne haka,  duk wanda ya santa, ramar da tayi ne kad'ai shaidan bata da lafiya.


Ganin ta d'ago yasa sa kauda fuska, kamar ba ita yake kallo ba, boot ya bude ya saka akwatin hannun sa, ya tsaya yana jiran khadija ta karaso da tata jakar, tana zuwa ya rufe boot in .


Shiga baya sumayya da goggo sukayi, dole tasa khadija shiga gaba, Amma yaja motar suka cillah.


Gidan mai Ammar ya shiga zaisha mai yayi packing,ana loda masa mai A hankali ya sace kallo sumayya, gani yayi gabaki d'aya ta maida hankalin ta gefen glass inda take,  alamu dai wani abin take kallo.


Juyawa yayi yaga wata yar Christian ne zaune a tsallaken titi tana gashin masara, bayan an gama zuba masa mai jan motar yayi daidai wajen mai masara gasheshen,  ya mika mata 500, ta saka masa.


Da sauri mai masara ta mike daman ta gaggasasu suna zaune, jimbo ta d'auko tazo ta zuba musu masara guda goma, Hamsin hamsin ne, karba yayi ya aje a mota.


Suna shiga sintali gidan goggo suka bi ya ajeta, masara ya d'auko kuda hudu ya bata Amma taki karba.


Gida ya wuce dasu sumayya, dayake goggo tace khadija tabi sumayya gidan ta tana ibe mata kewa.


Yana packing sumayya kam fita tayi, tayi cikin gida, tana bude kofar su a hankali ta zubawa kofar ido, hawaye na cika mata ido"nayi kewanka yanda ya kamata mijina, nayi kewanka so tarin yawa, don Allah ka dawo, kamin Alkawari bazaka taba barina ba,  saidai in nine na gaji da zama da kai, gashi sun rabamu, bansan halinda kake ciki ba,  "tana maganar tana hawaye sosai taji kewar mijinta.


Toh Allah yayi dare gari ya waye, Ammar daya shigo da akwati a hannunsa da laida yace.


Matsa masa sumayya tayi ta zauna akan dakali tayi tagumi, mika mata laidan masara Ammar yayi


Ba musu sumayya ta karba, a Hankali kamar wance aka sakata dole tace "thank you for everything" tace tana zaro guda d'aya ta b'amb'are tana ci, 


Da mamaki Ammar ke kallon ta jin yau ta masa godiya, amma dai baice kome ba ya juya yayi waje. 


d'aga ido tayi tana kallon Ammar ganin ya dawo, don a zatonta yawuce kenan, da sauri ta mike tsaye tana murmushi har hakoran makkar ta suka bayyana tare da fararen hakoran ta, ganin manyan elagement in hoton su,  da Ammar ya fitar a boro.


"Wow masha Allah,  kamar kasan abinda ke raina akan hoton nan kenan, ka kwashe mini waya" tayi maganar tana karban hotunan a hannun sa tana kallo.


Hotuna ne guda biyar, d'aya ita da mijinta,  sai kuma d'ayan ita kad'ai, d'ayan shima shi kad'ai, sai d'aya kuma shi da ita da khadija, d'ayan kuma su da kannen Ammar ne, sosai hotunan yayi kyau, abinka da hotuna daukar iphone da background.


Yanzun kam kin daina jin haushina kenan koh?


"Eh na daina jin haushin ka, tunda har kamin wannan"tana magana tana nuna hotunan.


Hannu yasa a Aljuhunsa, ya fitar da wayar ta zai mika mata, Amma wayam yaga bata.


Sumayya kam ganin khadija ta bude kofar d'akin yasa ta saurin shiga, wai zata bubbuga hotunan a jikin gini, sake fitowa tayi tunawa da tayi bata da kusa.


Sumayya ga wayar ki, yace yana mika mata wayar, kimin Alkawarin mundin kika manna wannan hotunan duk lokacin da kika gani Addu'a zaki masa Allah ya kubutar dashi ba kuka ba.


" insha Allah"tace tana karban wayan.


Kallon khadija Ammar yayi, kee muje na samo kusa na baki ki kawo mata.


Murgud'a baki khadija tayi, wallahi ta tsane yace mata kee innan , haka dai ta bishi a baya.


Ba'a jima ba khadija ta dawowa da sumayya da kusa, bubuga hotunan tayi a d'akin ta.


Har dare sumayya masaran nan ta ringa ci inta shake tasha kunu a firij, Abinci ma khadija daidai bakinta ta dafa, sumayya kwance take akan gado hannunta rike da masara tana b'amb'ara tanaci, suna kallo da khadija dake zaune akan kujera.


A haka sumayya tayi bacci da masara a hannu, tsakar dare ma data farka wanke baki kawai tayi ta gwaguye masara ta koma ta kwanta.


Washe gari khadija ta koma makaranta, ganin jikin sumayya da sauki sosai, ta mata wanke wanke da shara, breakfask ma taliya ta dafa laida d'aya taci ta rufe sauran, don sumayya tun asuba ta karya da masara.....


*****************

Washe gari kamar yanda bappa ya fad'a haka muhammad yayi maganin sa, yana gamawa ya fitoh kenan ya samu matar gidado ta fitoh zatayi wanke wanke da tsohon ciki, hanata yayi da kansa ya wanke kwanukar ya jido musu ruwa ya ciccika randuna.


Suna karyawa yabi gidado kiwo, basu dawo ba sai yamma, kayan sa kala biyu da jallabiyar da yazo dashi da wanda gidado ya basa, ya had'a ya wanke, ya shanya, wanka yayi ya fitoh wajen kofar gidan ya zauna yana bin garin da kallo.


Tun daga nesa data sauko a machine ta hangosa kara sauri tayi, bako.. bako...bakon nigeria, tun bata karaso ba take kwala masa kira, sai washe baki take irin dai yanda mutanen kauye kiye in sunga bako(mutanen kauye akwai d'aukaka bako kam)


Yajita sarai Amma ya mata banza, harta karaso inda yake d'auke da robobin nonon ta, bako ina kwana?au ina wuni.


Lafiya yace yana basar wa don Wallahi yarinyar ta fara isarsa.


Kasan me bako? Bata jira amsar saba tacigaba, ai in gaya maka ina zuwa birni nayi kawa yar gayu, harna mata tadin ka, gashi tace tana mika masa abu.


Juyawa yayi kawai ya kalleta, ya sake kauda fuska, jin tace masa gashi, menene wannan?


Uhmm abune na saya maka, ka bude ka gani.


Ba musu ya bude abin, ai baisan sanda dariya ya kwace masa ba, bread ne wani yanka kamar na ashirin, gaskiya karbi kayanki ni baxanci ba babu ruwa na,  tunda kudin nonon inna kika saya dashi.


Don Allah kai hakuri kaci, in ba haka ba inna dukata zatayi na kashe mata kudi.


Gaskiya bazanci ba sai dai na aje miki, in zaki fita kizo ki Amsa.


Shikenan in zanje kallon shadi gobe saina karba


Shadi? Gobe bazakije tallah bane?


Eh gobe a........


Bata karasa ba taji dundu a bayanta mai masifar zafi dimmmm, saida ta wantsala gefe, daga muhammad har indo zaro ido sukayi sai kuma suka dubi wanda yayi wa indo dundu..........

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


Kuyi manage na page innan wallahi yau typing nayi by mistake ya goge😥😥da yamma.


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯 

             ~ Na ~


No comments