Matar makaho 66-67

 


Page6⃣6⃣&6⃣7⃣




Kyakkyawa tana sanye da kayan fulani, ga wani kitso manya manya a kanta, ta kura masa ido, da sauri ya mike zaune keee lafiya?ya tambaye ta cikin Al'ajabi.


Wallun hakkiloma, tace masa tana murmushi.


Da mamaki yake kallon ta, kafun ma yayi magana yaga wani saurayi da bazai wuce shekara 21 ba ya shigo d'akin, baki ne kamar yarinyar sai dai yarinyar ta fisa kyau sosai, duk da shima ba mummuna bane.


 laaa ka tashi?yace da sauri yana karaso wa kusa da Al'ameeen.


Al'ameen kam ya cika da mamaki wai inane nan? gashinan a cikin wani daki kamar akurkin kaza, haka yake kallon d'akin, sai dai jin fulatanci a bakin su yasa sa gane fulanine su, duk da gidan Adara fulani ne sai dai sam basa magana da harshen su,  da hausa suke magana sai dai koh yaya ne indai mutum ya zauna a jalingo, zaiji fullaci koh bai iyya maida martani ba bare shida yake zaune a unguwan fulani, shima cikin fullaci yake tambayar su nan inane yake.


Murmushi yaga saurayi yayi, sai kuma ya juya ya kalli yarinyar, indo wai har yanzun baki tafi tallah ba?kinsan in inna tazo ta samu baki wuce ba ranki zai baci koh,fita ki d'auki nonon ki kitafi.


Ba musu ta mike duk da ranta baiso ba, ta fita a d'akin, juyawa gidado yayi yana kallon Al'ameen, sunnu ya jikin naka?duk da fulatanci yake magana.


Sosai Al'ameen yake mamakin wannan Al'amarin, wai garin yayane ma yazo inda yake nan, yanaji gidado nata masa magana amma kala baice ba.


Ganin yaki magana yasa gidado tashi yabar dakin,cikin gida ya shiga yaje ya sanar da bappan sa bakon ya farka, amma baya magana don shi ya d'auka koh wata matsala ce, ya hana muhammad magana.


Al'ameen na zaune kamar gunki yana tunani abubuwan da suka faru dashi, a yan kwana kin nan, sai kuma tunanin sumayya ya fado masa, koh yanzun a wani hali take?lumshe idanunsa yayi yana kiyastata amma yagagara hasko kaman nin ta, yaso ace itace mutum na farko da zai fara gani, bayan dawowar idanun sa.


Gidado da bappa da suka dade da shigowa,  sai magana suke amma Al'ameen baisan ma sunayi ba, dafasa gidado yayi, da sauri ya zabura sai kuma ya d'aga ido yana kallon dattijon dake kusa dashi, ya zuba masa ido, sunkuyar da kansa yayi Amma baiyi magana ba.


Akwai inda yake maka ciwo ne?


A hankali y dago kai ya kalli mutumin, sai kuma ya basa amsa cikin fulatanci kamar yanda yamasa magana, babu abinda yake mini ciwo.


 tashi ka fitoh kayi Alwala ka biya sallan da ake binka, gidado zai kawo maka kaya ka saka da abinci kaci.


Toh kawai Al'ameen yace, yana mikewa tsaye da taimakon gidado ya fitoh a d'akin, kasance war dakin a hanyar kofar gidane , yasa yana fita yaga inna zaune tana gyaran zogale a tsakar gida,  ina kwana?


Mtswww kawai inna Talatu tayi, tacigaba da abinda take ba tare da tabi takan gaisuwar saba.


Sanin halinta yasa gidado d'aukowa Al'ameen buta ya mika masa,shima Al'ameen dayake ya saba ganin abinda yafi na inna yasa bai wani damu ba, don duk Abinda zata masa lafilane in an had'a da rashin mutuncin gidan Adara.


 gidado dakinsa ya shiga, kaya ya d'auko kala uku na fulani, sai nono da matar sa ta dama,ya had'a da dambu ya kaima Al'ameen a d'aki.


Bayan muhammad ya idar da sallah, wanka yayi bayan gidado ya iba masa ruwa a rijiya,  ya chanja kaya, abincin ya bude kasa cin dambu yayi, nono kawai yasha, kad'an duk yabi ya shiga damuwa halinda sumayya da kanwar sa zasu shiga a rashin sa.


Sai bayan muhammad ya gama kimtsawa,  kafun ya mike a hankali ya fitoh a d'akin bappa ne da gidado zaune a gindin bishiya,  sai inna dake zaune a gefen su rike da fifita, karasowa yayi kusa dasu bappa a hankali, ya zauna a gefen su,duk da bansan tayaya nazo nan ba, amma dai nasan taimako na kukayi,  nagode Allah ya saka da Alkhar, yace musu.


Ameeen,bappa da gidado har suna had'a baki suka amsa masa, sai kuma bappa ya kara tambayar sa, yaro garin yaya babba dakai har ruwa ya jaka?koh wani abinne ya faru dakai?


Shiga ruwan nayi zan sha, shine yajani, ya bashi Amsa.


Kai bako ne hala koh?don ruwan mu bayason bako.


Eh ni ban taba zuwa kauyen nan ba, baba


A ina kake?


Jalingo.


Jalingo kuma?inane haka, nidai bantaba jin sunan wannan gari ba, gidado yace da mamaki.


Bappa ma kara tambayar sa yayi inane jalingo kuma?


Muhammad kam sai yanzun ya tuma ashe bafa a kasar NIGERIA yake ba, yanzun toh Amma a ina yake haka, gadai mutane kamar na kasan sa fulanine musujin yare, wani kasane wannan, dan uwa?yayi maganar yana kallon gidado.


Gidado ya juya ya kalli bappa, shima bappan gidadon ya kalla suka had'a ido, sannan suka sake maida kallonsa kan muhammad, Cameroun.


A hankali yace musu ba'a kasar nan nake ba.


Kamar ya ba'a kasar nan kake ba?


Eh baba ba'a nan nake ba, a nigeria nake.


Nigeria, a ta ina kasar take? gidado ya tambaya da mamaki, don shikam baisan wata kasa nigeria ba, murmuahi bappa yayi yana kallon gidado, nigeria ai na sha zuwa, lokacin da muke cikin ganiyar kuruciya, har kasar muke zuwa kiwo tun daga Cameroun, har nigeria.


Wai bappa kasan kasar ne?inji gidado


Sosai ma nasan jahohin kasar,  kai yaro a wani jaha kake?ya tambaye muhammad.


Taraba, ya basa Amsa yana kallon inna dake ta zabga masa harara tun daga inda take.


Allah sarki ai naje jaharma dashi, da gombe harda Adamawa, amma tunda kace a taraba kake kenan ta Gimbu ka shigo kasar cameroun?


Nima ban sani ba baba kawoni akayi.


Kamar ya yaro aka kawo ka, ban gane ba?


Shuru muahmmad yayi yama rasa ta ina zai fara.


Dafasa bappa yayi, kaga yaro ka fad'amin gaskiya, mu bazamu cutar dakai ba sannan haka muke fata agunka.


A hankali muhammad ya gyara zaman sa, ya fara bawa bappa da gidado labarin sa, har Auren sa da sumayya, da batar mahaifin su , har zuwa sanadin zuwarsa kasar nan, ya kara dacewa, sannan baba ina so na koma kasata koh don ganin halinda na tafi nabar mai d'akina a ciki.


A hankali bappa ya d'aga ido yakalli muhammad da kyau, ya sunan ka?


Muhammad Amma anfi sanina da Al'ameen.


Ashe sunan baba nane dakai, Zan fad'a maka gaskiya, akwai asiri a jikin ka har yanzun,  sanan bakai aka ma asirin ba, an ma wasu asirin ne a jikin ka,  anyi amfani da tauraren ka anyi asiri da kai, dole kana bukatar ka zauna ka nutsu, komawar ka gida yanzun matsala ne duba da abinda mutanen da suka kawo ka sukace, zaka bata musu aiki sanan kwangilar kisan kai aka basu, watoh kaga yanzun an daina Amfani da boka, da zahiri ake son ganin bayanka, ka zauna anan zan maka jinya da izinin Allah duk asirin dake jikin ka zai karye, wa'inda akama asirin ma zasu dawo hayyacin su, sannan zan taimaka maka da maganin kariya babu wani asiri da zai sake cinka bi'izinillah,kaima ka dage da Addu'oin neman tsari a wajen Allah, don yawan ibadan ka shiyasa har yanzun basu gama cin nasara akanka ba.


Shuru muhammad yayi amma sam ransa baiso ba, baiso hakan ba, yaso ace ayau innan ya koma gare ta, yaje yaga halinda take ciki ya kalleta da idanun sa, yaga wani irin farin ciki zatayi yau idan taga yana kallo,  amma babu hali, sannan maganar mutumin nan bai kwanta masa ba,  don shi ba mutum bane mai bin maganganu irin wannan na magani magani, aa tsari tsarin nan sam basu ransa.


Ka kwantar da hankalin ka babana, ni magani zan baka don nema maka lafiya, sannan mu sama ma wasu lafiya, domin samun lafiyar ka, warakan wasu ne, karkaji kokonto ni bana aiki da Aljanu koh wani shirka, magani nake bayarwa wanda Alllah ya hure mini sani akan ganyen itatuwa da sassaken su, tunda na ganka nasan Akwai sihiri a jikin ka, Amma inga sarkan da mahaifinka ya baka.


Hannu yasa ya kunce sarkan ya mikawa bappa, kurawa sarkan ido yayi nad'an wani lokaci sai kuma ya mike ya dauko ruwa a kwarya ya saka sarkan, ya zuba magani kad'awa yayi sai kawai ruwan maganin ya zama fari tas, wannan sarka d'ayan biyu ne Amma bazance maka kome ba Akansa, bappa yace.


Shuru Al'ameen yayi sai kuma ya gyada kai a hankali alamun ya amince,ya karbi sarkan ya makala, kamar kwana nawa ne zamuyi baba?


Murmushi bappa yayi sai kuma yace,ka kirani da bappa haka yarana ke kirana, sannan maganin ka bana kwana bane, na wata ne.


Kamar wata nawa kenan bappa?


Kamar wata uku, kuma kasan inka gama magani dole sai kunje cikin cameroun asai da shanu mu baka kudin mota.


Shuru muhammad yayi kamar ya fashe da kuka, yanzun har wata uku yana zaune a wannan  kauyen, ba tare da sumayya ba ai sai kewan ta ya kashe sa, tun lokacin sa baiyi ba, toh nagode bappa Allah ya saka,mikewa yayi a hankali ya nufi kofar da yake hango fili ta waje , alamu dai kofar gida kenan.


 ina zaka?Gidado daya mike yake tambayar sa don ya d'auka tafiya zaiyi 


Waje nake son fita, ya basa Amsa.


Kanason zaga gari ne?


Eh ina so, yace cikin ransa yana dariya wai wannan kauye ne gari.


Toh jirani barana kunce shanu mu fita kiwo, saina nununa maka wajaje, yace yana tafiya tirkensu domin kunce shanun.


Da sauri Al'ameen ya biyo sa wai zai tayasa kuncewa, ai yana saka hannu a kafar shanun da sauri yaja baya, ganin yanda shanun ta hafto kamar zata tunkudesa da kahon sa.


Dariya gidado yayi, kai kaja baya fa shanun nan saimu, yana maganar yana kunce su .


Matsawa muhammad yayi gefe yana kallon gidado yagama kunce su yana kad'asu yayi waje bayan ya karbi guzirin sa a wajen matar sa, muhammad na binsa a baya yana mamaki wai d'an yaron nan ne da mata.


A haka suke tafiya gidado sai hira yake masa,  duk inda suka wuce saiya ringa masa bayani, ga gonan wane, ga shanun su wane, ga kogin kaza a haka har suka nausa daji, wuni sukayi suna yawo sosai Al'ameen ya gaji bayan gidado ya kunce boronsa daya rataya, abinci ne a ciki sai goran ruwa, bayan sunci ne suka kamo hanyar gida basu suka iso ba sai goshin mangari ba, suna isa suka samu har an kira mangariba da sauri sauri gidado ya d'aure shanun suka tafi masallaci.


Sosai jama'ar garin suke bin muhammad da kallo, ganinsa ras dashi kamar ba gawan jiya ba, gashi kyakkyawar bafulatani, suna idar da sallah, gida suka koma suna shiga muhammad yaga yarinyar d'azun da safe zaune a gefe tana cin tuwo, kai koh d'an kwali babu. 


 d'aga ido tayi ta kalli Al'ameen da sauri kuma ta mike, cikin fullaci tace, laa bako kaine ka tashi, ya jikin naka yau sai sauri nake nono na ya kare na dawo gida, Amma bai kare da wuri ba.


Shuru Al'ameen yayi baiyi magana ba, yana nazarin yarinyar kenan khadijar sa zatafi yarinyar nan a yanzun, Allah sarki yaci burin ganin su duk da bai taba tunanin ganin sa zai dawo ba, Amma yaso ganin sa na farko yafara dasu, ganin yanda ta bata fuska alamu dai bataji dadin shurun da ya mata ba, gashi gidado na kusa dashi, yasa a hankali yace eh na tashi.


Washe baki tayi sai kuma da sauri tace, nakai maka abincin ka d'aki bappa yace na kai.


Kai ya fahimce yarinyar nan yar damuwace,  fadi ba'a tambaye taba, kamar ya sata, rijiyar dake tsakar gidan ya nufa jan ruwa yayi a kwalla ya wuce bandaki, bayan ya d'auko kayan da zaisa, bai wani jimaba ya fitoh Alwalan isha yayi jin ana kiran sallah ya wuce masallaci.


Bayan an idar da sallan gida ya nufa a hankali ya shige dakin da aka ware masa, zama yayi akan gadon kaba da aka saka A dakin, ya buga tagumi abin duniya ya dame sa, tunanin matarsa kawai yake, adaidai wannan lokacin ne suke cin abinci, shin itama abincin take cine koh me take yanzun?


Gidado ne ya shigo dakin da sallama.


Amsa masa muhammad yayi, tare da gyara zaman sa.


Har yanxun bakaci abincin ba tsoho?


Da mamaki muhammad ke kallon sa, tsoho kuma?


Eh man tunda ka haifi bappa aikai tsohone, yace yana aje agushin hannunsa.


Murmushi muhammad yayi sai yanzun ya tuna, ashe fa bappa yace sunan baban sa garesa.


Abinci na kawo mu had'a muci, yace yana bubude agushi.


Hannu kawai muhammad yasa a kwanon bawai don yana kwadayin cin abinda ke ciki ba, loma uku yayi ya tsame hannun sa,  da mamaki gidado ke kallon sa, wai harka koshine koh me?


Wallahi gidado bazan iyya ciba, gabaki daya na saba ci da mata na, muna ci muna hira gabaki d'aya yau dai ina jina wani iri.


Hhh dayake kabar hannun wa'inda suka kamaka ba har kana zancen kewa .


Dariya shima muhamad yayi yana kallon gidado, wai ni ya akai nazo gidan kune?


Nine na tsintoka a ruwa, na kawo ka gida.


D'agani kayi koh shanunka ne ya kawo ni?


Nina d'agaka, mana.


Da mamaki Al'ameen yace, kaika d'agani fa kace, yana mamakin yaron nan ne ya dagasa.


Hh ka raina karfina kenan koh?


Shuru yayi sai kuma ya girgiza kai 


Toh kaci abincin mana, in bazaka ciba sai nasa indo ta kawo maka nono.


Kai na koshi, nagode gidado 


Haka gidado  yaci sauran abincin, bayan sun fita waje muhammad ya wanke hannunsa yana kokarin koma wa daki don sam zaman gidan baimai ba, bayason zama a gidan da akwai mata, haka shi kuma yana tsakiyarsu gashi ba'a kewaye dakin sa akayi ba, babana!!!!yaji bappa ya kirasa.


Na'am ya amsa yana nufo bappa, bayan ya zauna ne bappa ya mika masa maganguna,  wannan na hayaki ne wannan na wanka,  yanxun zaka d'auki kwalla ka jika zuwa safiya,  zaka fara amfani sai wannan gadaline zaka,  shiga daki da kanka zaka nika da duste zansa gidado ya kawo maka, ga mai saika zuba gadalin a ciki, kana shafawa safe da rana, sosai bappa ya had'awa muhammad magani karba yayi, yayi godiya.


Kamar yanda bappa yace haka yayi,  ya jika maganin ya had'a nasha, yana gamawa ya shiga ya kwanta abinsa, sai kuma kewar sumayya duk yabi ya cikasa ji yake kamar yayi tsuntsu ya gamsa a nigeria, koh hankalin sa zai kwanta sosai yake kewan gadon su,   kewan jikin ta, abincin ta, fadar su,kamshin ta kome nata kewan sa yake, a haka daker bacci ya d'auke sa.


*********************

sumayya fa jiki ya fara sauki  kad'an duk da ba kwari yayi ba, Amma da sauki, sosai take samun kulawa a wajen mutanen nan guda uku, goggo Ammar da khadija duk da ba kula Ammar take ba, amma kullum sai yazo kuma inzai zo haka zai kawo mata abubuwa, su tsire koh kaza, sai dai su khadija suci, itakam bata iyya ci sam.


Makwanta dayan unguwa, harda yan gidan Adara, sunzo dubata sosai ta cika da mamaki, haka customers nata ma sunzozzo kuma sosai suke rike wani abu in zasuzo, lallai sana'ar mutun nasa aga kimarsa,tunda lokacin da bata sana'a babu wanda ya lekota a asibiti, Amma yanzun kowa zuwa yake yana mata ya jiki, da jajen batar mijin ta, gashi yau satin ta biyu a gado, amma haryau zuwa ake, iyayen Ammar ma sunzo da kannen sa,  baban sa ne kawai baizo ba.


Kamar kullum yauma hakan take, da sallama ya shigo d'akin, hannunsa d'auke da laida jikin laidan duk raba da alamu dai wani abin mai sanyi ne.


Khadija dake gefe ne ta Amsa masa tana tashi daga kan kujeran da take, ta koma gefen gadon ta zauna.


Sumayya dake kwance, koh d'ago kai batayi ta dubesa ba, don tun akan wayanta ta daina bi takan sa.


Sannu hajiya ya jikin?


Shuru ta masa taki magana, sai khadija dake gefen tane takece masa jikin da sauki.


Bude laidan da yazo dashi yayi, goran kunun ayane mai sanyi harda raba a jiki, gashi fari tass, ya mikawa khadija, gashi ki bata koh zata sha?


Kaidai yaya Ammar baka gajiya wallahi,  kullum ka kawo abu baci take ba, amma koh yaushe sai ka saya.


Mom ina cefa tayi kunu, shine nece ta zubamin a gora guda biyar, zan kawowa sumayya tun jiya na aje a firij.


Karba khadija tayi tana kallon sumayya dake kwance tana jinsu, Amma har lokacin bata d'ago ba, Aunty ga kunun aya mai sanyi.


Shuru  tayi sai kuma taji tana jin kwad'ayin sha, mikewa tayi a hankali ta karbi goran.


Tsaya ta tsiyaye miki a kofi, Ammar yace ganin tana kokarin bude marfin.


Koh magana sumayya batayi masa ba, tana bude goron a hankali tasa hancin ta mai tsayi a bakin goron tana tsuntsuna kunun, tare da lumshe ido, kunun sosai yake mata wani irin masifeffen kamshi, dake fita a ciki na aya da dabino.


Habba sumayya menene haka?abinci kike tsuntsunawa hakan bai dace ba, babu kyau fa, yace yana mamakin abinda tayi kamar wata tababbiya.


Kafa goran tayi da bismillah, ta fara sha shatake kamar yar kokowa da sauri sauri, tunda ta kafa goran sai da yayi rabi ta cire a bakinta tana hutawa,kafun ta sake kafa bakin ta akai sai gora ya rage babu kunu.


Ammar da khadija tsakake sukayi suna kallon sumayya, ita da tafi sati biyu ana binta taci abinci, taki sai d'aura mata ruwa ake, duk an bubula mata jiki, Amma yau ba lallama ba banbaki, da kanta tasha kunu har goran faro medium.


Sumayya kam ta kammala da gora d'aya, rike take da gora empty a hannu, tayi shuru amma fa har ranta kari take so, saidai tanajin kunyar tambayar wani,ganin Ammar in baibar d'akin ba.


Bude laidan Ammar yayi ya fitar da wani goran kunu, tashi yayi da kansa ya mika mata, hade da karban empty na goran, ba tare da yayi magana ba ya koma ya zauna.


Ba kunya sumayya ta bude goron ta kama sha, wannan karon kam a hankali take sha tana kurba kad'an kad'an har tayi rabin goran,  kafun ta aje sauran a hankali ta koma ta kwanta.


Ammar mikewa yayi ya kalli khadija, ke tashi muje waje zanyi magana dake, yana maganar yana fita waje.


Tashi khadija tayi tabi bayansa, samunsa tayi tsaye a baranda yana jiran ta, karasowa tayi ta tsaya a gefen sa fuska ba walwala, kamar yanda taga yayi.


Shin yayan ki nada abokan hammaya ne?


Babu yayana baida wani abokin fad'a, asali ma yanda na tashi ban taba ganin yayana yayi koda cacan baki bane da wani.


Ok toh akwai wanda yake nuna masa kii koh kyama haka?


Gaskiya babu.


Ok shikenan kawai, yace yana barin wajen ya nufi packing space, khadija ma cikin d'akin ta koma .


Sumayya kam da tafiyan Ammar koh minutes 30 batayi ba, ta sake mikewa da sauri ta d'auki sauran kunun ayan ta shanye wanda ta rege a gora, kafun dare sumayya ta gama da gora biyar innan tas sai fitsari da take akai akai.


Goggo data dawo karan kanta tasha mamakin kunun da yau sumayya tasha, amma batace kome ba.


Da misalin karfe 2 sumayya ta farka da sauri ta mike zaune, jin wani irin azabebben yunwan kunun aya daya farkar da ita, sauka tayi a gadon ta nufi wajen empty in gorunan,  bubudesu tayi tana kale a marfi tana sha, tsaban yanda take ji kamar bazata iyya bacci ba in bata sha ba.


Da yake asibitin ba'a barin mutane fiye da d'aya da mara lafiya, yasa goggo barin khadija da sumayya a dakin ita ta koma wajen block in ta shimfida taburma ta kwanta, kamar yanda sauran yan uwan majinyata keyi, shiyasa buruntun sumayya, khadija ya tayar mikewa tayi a hankali tana kallon sumayya, Aunty lafiya?


"Khadija kunun ayannan nake so, kuma ya kare"


toh kiyi hakuri Aunty, zuwa da safe sai inje in sai miki, kinga yanzun dare yayi.


Sumayya kam ji take yanzun in bata sha kunun nan ba zata mutu, mikewa tayi ta d'au hijab tanufi kofa.

Aunty ina zaki kuma?

"Neman kunu, ta bata amsa"

A daren nan ina zamu samu wani kunu , don allah ki dawo bara nafita ni naje na saya miki.


Dawowa sumayya tayi ta zauna a bakin gadon, ta d'auki goran kunu tana shinshinawa. 


Fita khadija tayi tun sumayya na tsammanin ganin ta har ta fara gajiya, ta jira kusan awa d'aya bata dawo ba, mikewa kawai tayi ta fita a dakin,ba tare da ta damu ba don yanzun damuwar ta kunu ne, ba dare ba,bakin get ta nufa daga ida sai hijab, data d'aura akan zanin ta sai takalmi koh kudin kunu ma bata d'auka ba a hakan ta nufi get.


Security ne suka tare ta da mamaki, ganin zata fita da uwar daren nan, duk yanda taso su barta, ki sukayi itama  taki koma wa ciki, tana tsaye a bakin get in harta gaji ta koma gefe ta zauna, ta had'a kai da gwuwa.


Tsayawar mutun taji a kanta, da sauri ta d'ago ta dubesa sai kuma ta mike da sauri cikin mamakin ganinsa a wannan lokacin.................🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯 

             ~ Na ~


 🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃


No comments