Matar makaho 64-65

 


Page6⃣4⃣&6⃣5⃣




Mafarki yake koh gaske, da idanun sa yake kallon duniya, wanda rabon sa daya gani yanzun ana neman shekara 13, Allahu Akbar Tsarki ya tabbata ga Allah, Alhamdulilah Alhamdulilah, shine abinda yake maimaitawa


Mikewa yayi da sauri yana bin koh ida da kallo, kamar wani dolo, shi ganin abin yake kamar mafarki ne, an jima zaici gaba da ganin duhu,sai bin wajen yake kamar daji, haka ya ringa takawa a hankali yana tafiya cike da Al'ajabin abinda ke faruwa yau dashi,  shine da kallo?


Hango gonaki yayi a shimfide, gwanin sha'awa na kayan labbu, ga kogi babba yana gudana da gudu yayi saitin kogin da saurinsa ya shiga ruwan, don wallahi azababben kishi yake ji, ai yana shiga kogin ya tsoma hannun sa cikin ruwan ya iba yasha, ya sake tsoma wa ya iba yasha, kamar wasa yaji ruwa yana jansa daga bakin gaba, har tsakiya sai kokari yake ya fitoh amma ina abin yaci tura, salati ya fara yana innalilahi, wasa wasa ruwa ya fara nitsar dashi sai kokowa yake da ruwan, duk  kokarin sa na fita, abu ya gagara, daman shi ba ruwa ya iyya ba, ina makaho ina rafi, koh lokacin tasowar sa baiyi yayin bin yara kogi ba.


Sosai ruwa ya hadiye sa har wuya, sai kokari yake Amma ruwan yafi karfinsa, zuwa wani lokaci, shuuuuuuuu yaji ya burme cikin ruwa,  da sauri yayi tsalle yafitar da kansa, sai kuma yaji ya sake komawa, kamar wasa Al'ameen ya fara shan ruwa, sannu sannu har yaji ruwan yaci karfinsa, tun yana gani dishi dishi har yaji bayanan , 


Gid'ado ne tsaye da shanun sa, daya koro bakin gaba susha ruwa, kamar wasa yaga shanukan sa, na kuka a bakin gaba, Alamu dai wani abin suka gani.


Da sauri ya karaso wajen don yayi tunanin kada ne, koh wani mugun abu, tsayawa yayi turus yana bin abinda yake gani shida dabbobin sa, mutum ne, kwance baya motse kamar gawa, da sauri ya kad'a shanunsa har ya juya zai tafi don gudu rigima, daman ba shiri suke da manoma ba kar ace shiya kashesa, ya shiga uku.


Sai kuma ya sake dawowa, haka kawai yaji hankalin sa bai kwanta da tafiya yabar gawan ba, nade kafar fantalelen wandon sa, na kiwo yayi ya shiga ruwan, jawo Al'ameen yayi, kiiiiiiiiii ya fitar dashi a ruwan, ajesa yayi a kan tabon bakin kogi. 


Kurawa fuskar Al'ameen ido gid'ado yayi tabbas wannan ba kabila bane, duk da fuskar tayi irin na fulani,Amma ba fulani husul  bane, kyaun sanan akwai mix,ganin Hakan yasaka sa ciccibar Al'ameen, ya d'aura a bayan wuyansa yayi Rugan su dashi.


Tun daga mahadin rugan su ake binsa da kallo, ganinsa d'auke da gawa a wuya, kowa ya tare sa, cemai yake shima a ruwa ya gansa, sosai wasu ke zagin sa meye na kawo musu gawa salon ya jaza musu bala'i,  Amma shi sam bai damu ba tafiyar sa kawai yake.


Isarsa gida ya tarar da mahaifinsa zaune a gindin bishiyar tsada a tsakar gidan su, sai innar sa dake gindin murhu tana girki. 


Assalamu Alaikum


Waalaikum.......sai kuma ta dakata, bata ma karasa amsa sallamar ba, hadde yan boni, gid'ado dun dume, miyiyata do ha bahoma?(me nake ganin nan a bayan ka)


Shuru yayi yana kallon ta, ganin yanda gabaki d'aya tabi ta gigice, bappan sa dake zaune a gindin bishiya ne, yayi saurin tasowa jin abinda inna kece wa.


Gid'ado d'obo?bappan sa ya tambaya, yana nuna Al'ameen dake kafadar gidado. 


Bappa, kuyi hakuri bara na sauke sa sai in muku bayani, duk cikin fulanci suke maganar.


Wani irin mu kwantar da hankali?kawai ka ciccibo mutum baya motse a kafad'ar ka, ka shigo mana ruga akan me?


Don Allah inna a wad'a muyal, nima ganin sa nayi a bakin gaba, alamu dai ruwane ya jasa,  koh aka yardashi, gidado yace yana kallon matarsa data fitoh daga d'aki, d'auke da tsohon ciki tana nufosu.


Kwantar dashi gid'ado, in yaso koh sallah Amasa tunda naga kamar musulmi ne, bappa yace.


Sauke sa gidado yayi, sosai bappa ya kurawa fuskar muhammad ido, yana nazari sai kuma ya d'aga ido yakalli gidado, Ai ohmayai(ai bai mutu ba)suma yayi.


Da sauri gidado ya kara maimaitawa suma bappa?


eh, yi sauri ka d'auko mini kwaryar magani a bukka, yana maganar yana dukawa kusa da muhammad, danne masa ciki ya farayi, take ruwa ya fara fita, ta bakin sa duk da baiyi motse ba, amma dai ruwan na fita sosai,  bappa ya mammatse masa ciki.


Matar gidado kam kujera ta samu ta zauna a hankali daker, sai ga gid'ado ya fitoh bukan bappa, da sauri ya ajewa bappa magani a gefe, bappa da lenki mai.


Maganin bappa ya d'auka a kwarya, yana shashafa ma Al'ameen a fuska, da wuya yana masa Tofi,yana gamawa ya d'aga ido ya kalli gidado, husumo ayara ha sudu(ka daukesa ka kaisa d'aki)


Wai bappan gidado ban gane a d'auke sa akai sa d'aki ba, yadaga ganin mutum bamusan daga ina ba, mugune koh nagari?kawai mu d'auko mu aje a cikin gidan mu, ni gaskiya ban yarda ba.


Talatu kena bani mamaki wallahi, yanzun ace mutun baya cikin hayyacin sa, ina kikeso mu kaisa?


Koma ina a kaisa, amma dai gaskiya banda cikin gidan nan, taima ma mugune.


Koh mugune, mu Allah zai dubi zuciyar mu, insha allah bazai basa ikon cutar damu ba,  bare ma wannan yaro baiyi kama da mugu ba,  daga ka gansa kasan akwai jinin fulani a jikin sa.


Lantana matar gidado kam, mikewa tayi ta shiga d'aki ganin fad'an bappa da inna baya karewa in gari ya waye .


Kai gidado d'auke sa ka kaisa d'akin kusa da gindin murhu.


Toh bappa, yace yana ciccibar sa yakai d'aki,  shanu kansa dake binsa a baya tunda ya d'auko Al'ameen har gida, suya kama ya d'ad'aure a turke.......


**************************

Ta bangaren sumayya yau satin ta d'aya a Hospital, har da kwana d'aya, Amma jikin dai za'ace Alhamdulilah, da sauki kad'an duk da baiyi kwari ba, sosai likitoti ke kula da ita,  hatta Dr tana iyya bakin kokarin ta, ganin sumayya ta samu lafiya, Amma taki kwantar da hankalin ta sam.


Khadija ma yau sati guda, rabon ta da makaranta,suna faman jinyan sumayya,  Goggo ke zama a asibiti, ita kuma ke musu girki a gida ta kawo musu, duk da sumayya baci take ba, sai yan aikace aikacen gida duk ita keyi.


Kamar yau ma, khadija ce ta kammala girki a kofar sumayya, zuzzubawa tayi a kula, tasa a kwando ga flask a hannun ta, ta fitoh gidan Adara, tsallaka titi tayi ta nufi shagon yayan ta, shagari ta samu zaune yayi tagumi gabaki d'aya yaron ya shiga damuwa ainu na b'atan Al'ameen, duk da shike kula da shagon yanzun, amma sai yanajin shagon kwata kwata baya masa dadi.


Assalamu alaikum.


Wa'alaikumu salam, khadija zaki wuce hospital in kenan harkin shirya?


Eh na gama girki.


Ok yace yana mikewa, laida ya d'auko ya zuzzuba ayaba da kankana mai yawa, ya  rufe shagon, kwandon hanun khadija ya kamar ba, ya bar mata flask in yana rike da laidan kayan marmarin a d'aya hannun, suka kama hanyar  FMC da kafa, don shagari duk da muhammad baya nan, amma baya masa Almubazza ranci da kudi, asalima tattalin sa na yanzun yafi nada, hatta kudin asibiti duk Abinda aka bukata shiyake biya, ya hana sumayya kashe koh sisi.


Sunzo sharan kwanan doruwa, kawai suka ga anyi packing moter a gabansu, khadija kam koh duban motar batayi ba, kokarin kaucewa take ta gefe, ta wuce abinta, dayake shagari bai wani waye Ammar ba, yasa bai ma saurare saba yabi bayan khadija.


Ke yar kauye, mai tafiya bata kallon gaban ta.


Da sauri khadija ta d'ago jin muryar Ammar,ina kwana?tace.


Kin Amsawa yayi ya dubeta, ina zaku kuma da abinci haka.


Asibiti, ta basa Amsa.


Waye ba lafiya?


Aunty sumayya .


Subhanallah, yayan naki nacan ne?nima yau na dawo da asuba, shine nace bara na biyo gunsa.


Shuru khadija tayi bata basa Amsa ba, sai kaucewa da tayi taci gaba da tafiya.


Da sauri ya fitoh a motar, yabi bayan ta, keee ba magana nake miki bane?kina tafiya?


Kala batace ba, tana ta tafiyar ta.


Hannun ta Ammar ya rike, da sauri ta juyo tana kallon sa, sakemin hannu?


Naki na saken, ina miki magana kina manna mini hauka, ina wasa dake?


Kuka khadija ta sake masa da karfi, ai da sauri Ammar ya sake mata hannu, ya juya yana kallon shagari, dake tsaye yana kallon su, fuskar sa A hade, haka kawai yaji ya tsani Ammar, ganin yanda ya wani rikewa khadija hannu.


Kai meke faruwa ne?Ammar ya tambaye sa.


Fuska a hade yace, An sace oga ne shiyasa daka mata maganar, ina yayan ta,  take kuka.


Sai a lokacin Ammar ya gane shagari, watoh shine wanda muhammad yace zai d'auko su zauna a shago, abu na biyu daya basa mamaki kuma wai an sace muhammad, sai kace kaza, ban gane an sace saba?


Eh an sace sa, haka kawai wasu a mota sukazo suka d'auke sa, a bakin titi


Tsabar razana har tuntube yayi, yau kwana nawa kenan?


Sati d'aya.


Amma har sati d'aya, police basu d'auki wani kakkauran mataki ba?mutum ya bata kamar wani kaza koh d'uriyan sa babu?


Koh report bamu shigar ba, Shagari ya basa Amsa.


What?? ba'a kai kara ba, akan me?


Sumayya na asibiti, ni kuma tsoro nake ji,  shiyasa ba wanda yakai.


Amma ai koh baku kaiba, nasan labari zaije wa yan sanda, tunda kuna kusa da station, yaci su subibiye Lamarin.


Shuru suka, masa.


Ku shiga muje asibitin, yace yana karban flask in da khadija ta dongorar,  yasa a mota.


Shagari ma shiga yayi ya zauna a gaba, har lokaci tana tsungune a kasa, hannu kawai Ammar yasa ya fizgota, ya jefa a bayan motar, ya zagaya driver sit ya zauna, yaja motar suka nufi Hospital.


Suna shiga hospital in, dashi da shagari ne suka d'auko kula da flask, harda laidan,  khadija kam an kaikaya mata inda yake mata kaikayi, kuka har lokacin yinsa take, duk yanda shagari keta bata baki tayi shuru,  amma ina. 


Keeee wallahi in na sake jin koh tarinki, a asibitin nan saina saba miki, banason shirme tun d'azun, sai cika min kunne kike nayi shuru,  yanzun mun shigo asibitin ma bazaki rufe bakin bane? saikin tara mana jama'a.


Shuru khadija tayi, harga Allah wannan Ammar in kamar mai Aljanu haka yake, zafi zafi sanyi sanyi.


Shagari kam gaba ya kara, dayake yasan d'akin da sumayya take, bai saurare tahowar suba, yayi tafiyar sa,  yana maijin haushi a ransa.


Shiya fara shigowa d'akin, da sallama.


Amsa masa sumayya tayi, wance ke zaune daga ita sai dogon rigan kanti, kanta koh d'ankwali babu, tana zaune a bakin gadon, rike da wayarta, hawaye nabin kumatun ta.


Ina wuni Aunty,  ya jiki?


Kai kawai ta d'aga masa, ta mika hannu ta d'auki d'an kwalinta, dake gefen gadon ta yafa a kanta.


Zama shagari yayi yana bin d'akin da kallo,  ganin baiga goggo ba.


Assalamu alaikum, Ammar ne yayi sallama a bakin kofar d'akin.


Amsa masa shagari yayi, ba tare da ya d'ago yaga bakin kofar ba.


itama sumayya bata d'ago ba, sanin wake sallamar, don ta shaida mai muryar.


Shigowa Ammar yayi, idanun sa ya sauka akan sumaya, dake zaune gabaki d'aya ta chanja, ta rame sosai sai haske data kara a yan kwanakin nan, har yayi yawa,tayi fari kamar ka tabata jini ya fitoh.


A hankali ya tako har inda take, hannu yasa ya amshe wayar, sai a lokacin sumayya ta d'ago ta dube sa, hade da mika masa hannu,  Alamun ya bata wayar ta.


Matsawa yayi gefe, ya kurawa screen in wayar ta ido, hoton tane da suka d'auka, ita da muhammad ranan sallah a gidan su.


Sumayya ya kamata kima kanki fad'a, wannan abinda kike kara cutar dakan ki kike,  kuka bashi ne magani ba, koh mafita, kin zauna kina kuka, gaki ba lafiya bane dake, ki dubi yanda kika koma fisabililahi.


Gaya mata kam D'an nan, haka nake fama da ita, bansan me take gani a wayar nan ba, ta tura khadija ta d'auko mata, shikenan tamai dashi madubi, tana kallo tana kuka, goggo data fitoh a toilet na d'akin ne take maganar.


Hoton mijin tane a ciki mama, Ammar yace yana latsa wayar sumayya, dake hannun sa.


Au shiyasa take kuka?/lalle sumayya baki jiran kanki, kiga yanda kika zama gabaki d'aya kin koma, kashi da rai sai haske da kike tayi kamar mai ciwon far d'aya.


Kyaleta mama,  hotunan duka zan goge.


Kuka sumayya ta sake, jin abinda Ammar yace wai zai goge hoton muhammad a wayar ta"ka bani wayata karka goge na rokeka don Allah"


Ah ah bafa zan baki ba, in gaya miki,  tunda zaki tasa wayar a gaba kina kallo kina kuka.


"Allah nayi Alkawari zan daina" tana magana tana kuka


Toh yanzun me kike in ba kukar ba?


Don Allah ka bata wayar ta, sai kuka take tana maka magiya, kana wani ja mata rai, khadija ce tayi maganar cikin jin haushi ganin iyayin da yake ma Auntin ta.


Wani kallo Ammar ya watsa mata, jin maganar da take masa kamar sa'arta.


Bata sake magana ba, aje abincin tayi tana kallon sumayya, in zuba miki Aunty?


"Ah ah banaci"


Wani irin bakici?sumayya yau kwanan mu tara a asibiti, abinci kirki baki ciba ya za'ayi kiyi lafiya.


Shuru sumayya tayi, ta koma ta kwanta bata kara magana ba, don ta fahimci bazasu gane abinda ke damun ta ba.


Ammar kam kallon khadija yayi ya sake kallon, Goggo,meke damunta , sukace mama?


Damuwa ce d'an nan, hawan jinine ya kamata, maimakon ta nutsu ta samu lafiya, Amma ina sai kara kwantar dakan ta take A gado.


Allah ya bata lafiya,  in ba damuwa mama,  ina so zan fara bincike akan case in batar Al'ameen, in muna bukatar cikekken bayani zan tuntube ku.


Ba kome yaro mun gode, Allah ya saka sai dai ban gane kaba?


Abokin muhammad ne.


Au koh dai kaine Ammar, da yake sanar dani ka bude masa shago?ai munga abin Arziki Allah ya biya ka.


Ameeen mama.


Sai a lokacin shagari da khadija, suka san Ammar ne ya bude ma Al'ameen shago.


Fita Ammar yayi bai bawa sumayya wayar taba, ita ma bata sake magana ba.


Ta bangaren Al'ameen kam har dare bai dawo hayyacin sa ba, gidado yayi ta zuwa dubasa yafi a kirga Amma shuru.


 sai da gari ya waye, ya farka jujjuyawa yayi sai kuma ya bude idanun sa,  da sauri ya koma baya da mamaki, ganin yarinya budurwa zaune a gaban sa kyakky.................🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀





🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯 

             ~ Na ~


 🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃

No comments