Matar makaho 62-63

 


Page6⃣2⃣&6⃣3⃣  




Kamo muhammad sukayi, suka d'aga sa sama suka tura a mota sai ihu yake yana ataimake sa, amma ina mutane kowa gudu yake kar a had'a dashi, muhammad naji aka turasa a mota suka ja....


Khadija data tsallake titi, ganin yayan ta yasata tsayawa tana jiransa ya tsallako su karasa gidan tare,kamar a mafarki take ganin abinda ya faru da d'an uwanta, ihu tasa ta ruga a guje ta tsallaka titin kafun ma ta isa garesu tuni sunja motar sunyi gaba, kuka ta sake sosai tana a taimake yayan ta sai a lokacin jama'a suka fara dawowa. 


Sosai surutu ya tashi a unguwan anata bawa khadija hakuri wance ke kuka kamar ana tsikaran  ranta da tsinke, wasu kam maida zancen yanda ya faru suke, khadija dake duke tana kuka taji an dafa ta, d'agowa tayi da sauri tana kallon sa.


Lafiya khadija mai ya faru naga mutane na tare a bakin titi, gaki kina kuka kuma?


Wayyo shagari yayana barayi suka sace,  duk sun rufe fuskar su da mask, tana maganar tana kuka.


Innalilahi wa'inna ilaihi raji'um yanzun fa yabar shago, ya d'auki lemo, yake sanar dani yau bazai fitoh ba na zauna a shagon, saida ya fita naga ashe ya manta bai d'au maganin daya shigo dashi a hannun sa ba, shine na biyo na kawo masa, yana maganar hawaye na zuba, 


Khadija mikewa tayi, har tana ganin jiri jiri shagari yana rike da ita da taimakon sa suka koma gidan goggo, don bazata iyya zuwa gun sumayya ba a halin yanzun da take cikin nan .


Assalamu Alaikum,shagari yayi sallama a kofar gaggo.


Wa'alaikumu salam, lafiya me zan gani meya samu khadijan?


Zaunar da ita shagari yayi a hankali, shima ya zauna akasan koh kujera bai nema ba tsabar tashin hankali, khadija na kuka shi kuma yana hawaye duk da yana namiji Amma b'atan muhammad ya shiga jikin sa.


Kun zauna kuna kuka bazaku fad'amin abinda ya faru ba, gabaki d'aya kunsa raina sai tsinkewa yake?goggo ta fad'a jikin ta na rawa har zani na kuncewa.


Goggo wallahi oga Al'ameen ne, wasu sukazo suka d'auke sa?


Kamar ya suka d'auke sa bangane ba?


Eh ina ga kidnap ne fa.


Kidnappers kuma wani irin yan garkuwa da mutane, kuma muhammad ina yaga kudin da yan garkuwa zasu sansa, sai kuma ta fashe da kuka, na shigesu ni Amina, ya Allah ka taimake wannan bawa naka ka tsaresa a duk inda yake, Albarkacin Annabi da Alkur'ani.


Ameeen goggo, shagari yace yana dafe kansa koh mutuwar mahaifin sa baiji tashin hankali irin  nayau ba koh don baban nasa ya rasu baiyi wayo sosai bane sai Allah.


Goggo Aunty bata sani ba, ina tsoron kar wani yakai mata labari tazo ta d'aga hankalin ta, gwara dai ke, ki sanar da ita goggo.


Hakane khadija ki daina kukan ya isa haka,  addu'a yake bukata ba kuka.


Dole nayi kuka goggo, shikad'ai nake dashi,  nake gani hankali na ya kwanta, yau an waye gari bansan halinda zai shiga ba.


Kiyi hakuri khadija, bara naje gidan yayan naki, na samu sumayya.


Toh goggo, kawai tace tana cigaba da kukan ta, shagari ma mikewa yayi kamar ruwa ya cisa yayi waje.


Ta bangaren sumayya kam bayan fitan muhammad, kwanciya tayi haka kawai takejin faduwar gaba, for no reason, har bacci ya d'auke ta. 


Goggo tunda ta fitoh gidan ta, sai zulumin ta ina zata fara sanar da mace an sace mata miji, amma dai gwara ita ta fad'a mata dataji a wani wajen, tana shiga gidan koh bi takan kofar yan uwan ta batayi ba,cikin kofar sumayya tayi tana kwala sallama.


Sumayya dake tsaka da bacci ne, ta farka jin sallama ake,  Amsa wa tayi, ta sauka a kujeran a hankali tana dingishi don yanzun dai Jikin da sauki tunda, ta shiga ruwan zafi.


"Laaa goggo sannu da zuwa, bismillah goggo ki shigo"


Ah ah sumayya kedai bari zan zauna a wajen,  ban kujera kawai.


Kitchen sumayya ta shiga zata d'aukowa goggo kujera, da ido gaggo ta bita koh ita yarinya ne ta fahimce meke faruwa.


Hawaye ne ya shikawa goggo ido, duk yanda taso daurewa kasawa tayi.


Sumayya kam sosai jikin ta ke rawa, wanda batasan dalili ba, tana ajewa goggo kujeran itama a bakin dakali ta zauna tayi shuru.


Sumayya!!


"Na'am goggo"


Kin dai san a rayuwar d'an Adam tana tafiya ne, tare da jarabawa koh?


"Kwarai kuwa Goggo" tace tana kara gyara zaman ta, don tasan tabbas akwai abinda ke faruwa


Sumayya ina so ki kwantar da hankalin ki,  kuma ki rungume kaddara a yanda tazo miki,  ina son kiyi hakuri da abinda zan sanar dake sumayya, ki kwantar da hankalin ki addu'a kad'ai ya dace kiyi.


"Meya farune goggo"?


Sumayya ki kwantar da hankalin ki, tace ganin sumayya harta mike tsaye jiki na rawa tana kallon ta.


" goggo meya same shi?tabbas nasan abune ya faru dashi, tun d'azun wallahi zuciya ta tsinkewa take"ta karasa maganar da fashewa da kuka.


Sumayya kiyi hakuri wasu da bamu san suwaye ba, suka zo suka tafi dashi,ki kwantar da hankalin ki in ma masu garkuwa ne zamu jira kiransu, insha Allah babu abinda zai f.......


Goggo bata karasa magana ba, dalilin ganim sumayya ta zube tim akasa,da gudu tayi kanta tana girgizata tana kuka. 


Jin kuka akofar sumayya yasa inna asabe lekowa, wanake gani kamar Amina meya samu MATAR MAKAHO kuma?


Wallahi inna muhammad aka sace, shine na sanar da ita kinga sai kawai ta yanke jiki ta fad'i.


Toh ai saiki kamata muje asibiti, ashe abinda modi ya sanar dani gaskiya ne, wai an kama MAKAHO banda haukan kidnopas ina su ina kama nakashashe?koh d'an kudi da aka ga yad'an samune oho.


Inna ki taimaka mini bara na zuba mata ruwa, da gudu goggo tayi d'aki,ruwa ta ibo a firij  tazo ta watsa mata, amma sumayya bata tashi ba, cicibarta sukayi ita da inna asabe zasu fitar da ita waje sai ga khadija.


Innalilahi inna meke faruwa?


Khadija jeki rufe musu kofa kizo mu tafi asibitin kiyi sauri.


Toh goggo tana kuka ta nufi kofar yayan ta,  rufewa sumayya d'aki tayi da kofa tabi bayan su goggo.


FMC suka kai sumayya, suna zuwa aka bata gado,khadija shagon yayan ta ta wuce saboda rashin kudi a hannun su, shagari dubu 10k ya baiwa khadija, yace na cinikin da yayi yaune.


Ta bangaren kamila, bayan yan uwan babanta sunzo aka kaisu sukaga kamila, sosai suka tausaya mata ba kad'an ba, masu magani aka nema kowa yazo ya gwada, abu ba sauki kadangaru fa sunki barin kamila.


Harira taso koma wa jalingo, Amma sam baban kamila yaki, mijin ta yayita kira tun tana masa karya harya gaji yazo da kansa,  yaji ba'asin zaman ta a kauye. 


Sosai yasha mamaki lokacin da baban kamila ya masa bayanin abinda matar sa ta jawowa yarsu, baice kome ba ya juya ya koma jala.


Bayan maman kamila ta farka, tace atafau sai an maida kamila gun nakan dutse, suje su basa hakuri in ma kudi za'a basa a basa, ya bar musu yarinya ta huta.


Anyi yanda za'ayi aja kamila amma an kasa saboda kadangaru sunki daga an tinkaro ta zasu hayayyako ma mutum. 


da aka ga haka sai aka samo bulala ana kora kamila dashi kamar saniya ana mata barazana tana gudu, in zatabi hanyar da bashi suke soba sai wasu su tarota, a haka gwanin tausayi akayi gun nakan dutse da ita,  Amma ina suna zuwa aka ga koh kokon sa yau babu filine shatt ba kome.


Haka suna ji suna gani kamila tayi ta fama da kadangaru, ga watan azumi gashi sun rasa ya zasuyi su dawo da ita jalingo.


Karshe dai  motar akori kura, aka samu aka kora kamila tahau baya, da kadangarun ta mammanne a jikin ta, Aka ja motar sai jalingo.


Sai ayau Harira ta samu dawowa gidan ta,   jikin ta har rawa yake ta shigo gidan, da mamaki ganin mijin ta zaune da yaranta, suna bud'a bakin azumi.


Assalamu Alaikum


Ba tare da ya d'ago ba ya amsa mata,  wa'alaikumu salam.


Rikice wa tayi ta rasa ma me zatayi ta zauna a falon ne, koh ta shiga d'aki, tashi tayi ta shiga d'akin ganin kallon banza da mijin ke mata.


Tana shiga d'akin ya taso ya bita, kee Harira sai yau kika dawo?


Eh sai yau wallahi aka samu aka fitoh da ita.


Yayi kyau karbi wannan,yace yana mika mata takardan dake kan mirrow ta.


Jiki na rawa tace menene wannan baban Amir?


Takandar sakin kine, kije bazan iyya zama dake ba, yanzun ma jira nake ayi sallah aure zanyi.


Saki, aure?


Kwarai ma kuwa na baki nan da awa biyu ki tattara kayan ki kibar mini gida now now...


Don Allah kayi kahuri, baban Amir kayi hakuri na tuba, wallahi bazan sake bin koh mai tofi,  kayi hakuri karka sake ni wallahi bazan iyya koma wa gida a yanzun ba .


Au nan in gidan ubanki ne da bazaki iyya koma wa ba?


Sosai harira tasha mamaki, yau mijin tane ke zagin ubanta, mutumin da koh d'aga ido bayayi ya kalli tsakar idon baban ta tsaban kunyan sa dayake ji.


Koh bazaki fita bane? yace cikin tsawa.


Mikewa tayi ta fara tattara kayan ta, tanayi tana kuka tana dana sanin sanin kamila,  gashe a dalilin neman mata auren wani gata ta kashe auren ta ..


Kamila kam har akayi sallah tana fama da kadangaru, yan unguwan su ba wanda baiji abinda ya faru ba,  wasu suzo gulma wasu suzo musu jaje, mamar ta haukane kawai batayi ba, duk malamin da aka samo abu yaki sam har akayi sallah jiki yaki sauki kadangaru kam basu barta ba.


Ta bangaren muhammad kam, tunda suka sasa a mota sai had'asu da Allah yake, su taimaka su barsa matar sa ba lafiya yanzun ma magani yaje sai mata, sumai hakuri, amma ba wanda ya kulasa, da suka ga surutun sa yayi yawa, gam suka likawa bakinsa.


Shidai yana zaune yanaji sai tafiya ake dashi sosai, kafun yaji motar ta tsaya, d'aya daga cikin sune ya bude masa baki, suka jasa waje aka fitar dashi daga motar, ajesa sukayi a kasa, suka aje masa plate a gaba, 


kai muhammad d'auke abincin gaban kan nan kaci, tafiya ne a gaban mu.


Don Allah kuyi hakuri ku maidani, wallahi matata bata da lafiya na barta koh karyawa batayi ba.


Kai muahmmad banace kaci abincin gaban kaba, koh bakaji bane?


Ai da sauri ya fara cin abincin, jikinsa na bari.


Kasan me mukeso dakai muhammad?


Ah ah sai kun fad'a ya basu amsa abinci cike a  bakin sa, don ya tsorata ainun, tura abinci kawai yake.


An bamu kwangilar kashe ka, Amma mu bazamu iyya kashe ka ba, don shekarun baya mune tsilar makantar ka, wanan karon bazamu iyya d'aukar ranka ba, bakaji ba, baka gani ba, ana buwayan rayuwar ka.


Innalilahi kune daman wa'inda kuka zubamin abu a fuska, na makance?


Ba zuba maka abin bane ya makantar dakai muhammad, tafiya mukai dakai a wancan karon ma.


Toh me nai muku kuma, waya saku?yana maganar yana kuka.


Kai mana shuru,abinda muke so dakai yanzun shine xamu fitar dakai daga NIGERIA,  Bama son ka kara taka kafar ka a wannan kasar, kaje can kayi rayuwar ka, yafi maka Alkhari sama da zaman ka a kasar nan.


Toh don Allah ku bari na d'auki matata da kanwa ta, saimu tafi tare wallahi na muku Alkawari bazamu sake taka nigeria ba.


Kaiiii kana wasa da ranka koh? ana maka gata kana kokarin sa kanka a matsala, an gaya maka koma warka gida yanzun baka bata mana aiki bane, don haka barin kasar nan dakai ya zama dole mundin kana son rayuwa mai tsawo


Don Allah ranka ya d....


Bai bari ya karasa ba yace, rufemin baki wawan banza kawai, kome mata mata  ai akwai mata da yawa a duniya, in sake jin ka am bace Hakuri anan saina sumar dakai nosense.


Shuru muhammad yayi, agun suka kwana washe gari suka kama hanya, wanda shi ba gani yake ba bai san ma ina ake jansa ba.


Lokacin da aka zo tsallaka border da muhammad ana tsallaka nigeria wani irin ihu ya sake yana birgima a cikin motar, ji yake kamar ruwan zafi aka watsa masa, sosai yake salati yana kuka jin jikinsa na tafarfasa. 


Abin mamaki mutanen basu wani damu ba,  kuma abin bai basu mamaki ba, d'aya daga cikin sune ya masa Allauran bacci a take jikin sa ya sake.


Ta bangaren sumayya sai da ta kwana biyu kafun ta dawo hayyacin ta, tunda ta farka sunan muhammad kawai take kira sai kuka,  zaune take akan gadon asibiti An d'aura mata sabon ruwa a hannu, inka ga sumayya saika tausaya mata tsabar rama da tayi, 


Likita ce ta shigo d'akin, sumayya ta kalla ta sake kallon goggo dake zaune a gefe, ga khadija ma zaune tayi tagumi gabaki d'ayan su wujiga wujiga suka koma, abin tausayi.


Sannun ku yamai jikin?


Da sauki likita, goggo ta Amsa mata.


Masha Allah, sumayya kam tana da mijine?


Eh likita tana da miji.


Ok koh zan iyya ganinsa?


Kuka sumayya ta sake mai tsanani, tana dafa kirjinta jin zafin da yake mata.


Subhanallah sumayya ki kula da lafiyar kifa, kina kokarin d'aurawa kanki wani ciwon kuma akan wanda kike dashi.


Dole nayi kuka Dr mijina aka sace shikaran jiya da safe.


Amma kun kai report wajen yan sanda kuwa?


Ah ah waye muke dashi, da zai kai mana report, yan sandan ma in kaje sai sun nemi wani abu agun ka, mu ina muka ga abinda zamu basu.


Duk da haka gwara kukai report yafi, sannan ina son kuban waje zanyi magana da sumayya?


Ba kome likita, goggo tace tana fita, khadija ma tashi tayi tabi goggo har lokacin bata daina kuka ba inta tuna yayan ta.


Sumayya hawan jini kika samu ya kamata, ki nutsu kisa tawakkali a ranki kiyi hakuri insha Allah mijin ki zai dawo.


Dole nayi kuka Dr mijina shine kad'ai farin cikina daya saura mini, sannan a waye gari ban gansa ba dole na shiga damuwa.


Kiyi hakuri, sannan ya kamata kima mahaifiyar ki magana ta ringa xuwa miki da ruwan zafi, kina zama a ciki saboda yanayin jikin ki kinji Allah ya sauwaka.


Ameeen nagode likita, sumayya tace tana kallon likitar bazata wuce sa'arta ba koh ta bata yan tsiraran shekaru.



Ta bangaren muhammad Sai da sukayi sati suna tafiya a motar, kafun suka iso kasar da suka shirya kaisa.


Suna shiga kasar da suka yanke zasu aje sa, d'aya daga cikinsu ne ya kalli ogansa, oga anya wannan yaron, bazaice zai dawo kasa ba kuwa, ka sansa akwai fahimta ni inso samune mai zai hana a masa yanda zai manta da kome,  na d'an wani lokaci.


Bazai yuba hakkin yaron nan ya mana yawa,  mu barsa haka wannan karon bazan sake cutar da yaron nan ba.


Shikenan oga amma naga hakan ma,  taimakon sa muke son yi, don mun masa hakan ba kome bane.


Gaskiya ne oga, d'aya daga cikin su yace


Kai ban Amince ba ku aje yaron nan mubar kasar nan, kar a kamamu jirgi ma zamu bi,  bada mota zamu koma kamar zuwa ba.


Haka suka aje muhammad suka kara gaba.


Kamar Awa d'aya da tafiyar su muhammad ya farka, A hankali ya motsa hannunsa sai kuma ya fara kokarin bude idanusa a hankali, ya bude su yana kallon sararin samaniya, ai da sauri ya mike zaune, mafarki yake koh gaske jikin sa har rawa yake yasa hannu ya murza idon sa da kyau don kara tabbatar wa kansa abinda yake gani, gaskiya ne koh A  mafarki yake...............🍀🍀🍀🍀🍀



🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯 

No comments