Matar makaho 6

 


Page6️⃣




 shanyan Kayana da sukaye datti harda zanin gado Ashanye a igiya an wanke  harda kayan yayan Khadija (MAKAHO) 


Khadija na gani cikin kitchen, tana aiki,


* a Hankali na daga kafata na Isa kitchen in,


 "Khadija kece akitchen?" da murmushi a fuskarta ta amsa mini da Aunty, Naga har Rana baki tashiba shine na daura Miki Abinci shinkafa da wake miyane ban Gama ba ya kusa,


"Kayan nan fa waya wanke ?"


Nice Aunty ta bani Amsa, *wallahih in banji Dadi ba nayi karya sosai naji yarinyar ta shiga Raina sosai da fara'a nace Mata" gaskiya Khadija nagode wallahih Amma aikin ya Miki yawa da baki wanke Kaya ba,


La Aunty babu yawa fa kayan, ta bani Amsa 


"Khadija tashi muyi Sallah tukum tunda miyar kin daura a wuta"


..Toh Aunty 


Sallah mukayi, na sauke abinci na raba na zuba Masa na hada Kamar jiya,  na Bata ta Kai Masa  " in kin Kaifa ki dawo Khadija"  da toh ta amsa mini,


Tana dawowa na iba Mana nida ita a plt daya, Muka zauna a waje munaci muna Hira cikin hiran nema nakejin ainahin sunan sa a bakin Khadija Ashe   *Al'ameen* ne sunan sa saboda larurar da Allah ya daura Masa shine aka batar da sunan zuwa MAKAHO Kai duniya, 


"Tambayar ta nayi a gidan nan take"?


Ah ah Aunty ni agidan Goggon mu nake ,


"Har wani unguwa ne haka"?


Ta bayan layin nan ne tsakanin mu ba nisa sosai Aunty,


Sosai muke Hira Kamar mun Dade da sabawa,


 "Aikin dare na hanatayi nace ta Huta ni nashiga kitchen nakama girki* 


kin zama tayi dutsen guga ta dauka ta fara gogan kayan da ta shanya duk yanda na hanata sai da ta gogi,



4:10  na yamma tace min zata tafi hanata, nayi sai da na Gama girkin abinci na sata tayi wanka Kayana na Bata cikin dogayen rigunana nakanti na Bata daya Dayake tana da tsawo sosai ya zauna Mata na hada Mata da gyele medium size kalar fulawar rigan,


Sosai kayan ya karbe ta na hada Mata da Mai turare harda powder,man baki, da Jan baki biyu, maskaras da sauran kayayakina da basa cikin set na make-up kit Ina na babata daker ta karba sai godiya take min,


 *nayi nayi taci abinci dare  Amma Taki,zuba Mata nayi a kula Taki karba sai da nace Goggo zata kaiwa kafun ta Amsa ta wace,


Fitar Khadija sai da ta biya wajin yayanta sosai take basa lbrn abin arziki Dana Bata da irin sakar Mata fuska da nayi,


Har cikin ransa yaji dadin  daraja.masa kanwa danayi sosai,


Hatta damuwar da ya fita da ita na safiya ganin yanda yau na tashi da zafi zafina abin ya tsaya Masa a Rai,


Wannan abinda nama Yar uwarsa tilo da yafi so  sai yaji zuciyansa wasai. 


Mangoro ya bata hade da naira dare ta rike a hannunta ya kara Mata nasiya sosai da hakuri A duk inda Allah ya ajita  kafun ta wuce,


*Khadija na fita wanka nayi nasa siket in kanti da t-shirt Mai kyau na daura gyele karami a kaina laptop na.....


Sai kusan shidda ya dawo gida yauma da kwandon sa a hannu, da sallama a bakin sa *amsa Masa nayi, kaina nakan laptop, *


Wanka yayi ya tafi masallaci yauma Bai dawo ba sai Isha waje na fita ganin yau ba NEPA, na fitar Mana da babban darduma na shimfida, 


*abinci na iba masa, nasa nawa na aje  Mana tare da Masa Bismillah zama yayi shima Muka fara ci *


Khadija ta tsanar Dani abin arzikin da kika Bata na gode, naji muryansa cikin sanyi sanyin sanan,


Ba kome wallahih abinda ba yawa,


Jin yanda na Masa magana a mutunce abin sai ya Masa Dadi sosai, mun Gama cin abincin har lokacin NEPA shuru na kasa shiga dakin saboda tsananin zafi da ake yau ga sauro,


Tashi yayi ya fita yaje ya sai Mana maganin sauro, Yana dawowa na karba na kunna,



 kitchen na shiga na yaga caton in indomie, zanyi fifita dashe,


* Wanka na sake shiga tsaban zafin da nake ji Kaya nasa vest sai wando Yale yale dogo har kasa,


Kushin na dauko a daki na zuba akan cafet in na kwanta Ina fifita,Yana zaune a gefe shima ya jingina da jikin gini,


Shuru mukaye dukan mu ba Mai magana,shikam tunani yake azaman da yaye da Sumayya ya fahimci Abubuwa cikin halayan ta,


 in Abu ya Bata Mata Rai, toh kowa ta shafa, in aka faranta Mata kowa zaiga fara'ar ta akwai ta da tsafta akwai iyya girki ga nutsuwa sam.bata da rawan Kai,


*Har Sha biyu bamu shiga ba, ganin dare yayi  ban tashiba ya mike a hankali yaji ya rufe kofar shashen mu, ya dawo ya shiga dakin  ya cire kayan jikinsa yadau wando  iyya gwuiwa sai riga Mara nauye , ya dauko filon kujira ya rufe kofar dakin harda k'wado   key in yasa a cikin filon sa,



Dawowa yayi ya tsaya a gefe cikin sanyin jiki yace "uhmm Daman Naga Kamar baki shiga daki ba kwanan waje zamuyi kenan?


"Eh wallahih Amma tunda akwai maganin sauro"?


Sake tambaya yaye in akwai wani abin kwanciyan a bani,Gefen dardumar na nuna Masa ya kwanta hade da furta" ita dayace" kwanciya yayi tare da Addu'an bacci, a hankali bacci ya dauke sa


*Sai kusan karfe daya kafun bacci ya dauke ni da ker'


Saboda rashin samun bacci da wure da bayi ba shiyasa yau Bai tashi yin sallar dare ba 



*Nikam ban sake sanin kaina ba sai asuba........


Ayi manage ba yawa😩

Masu complain in page na kadan 



No comments