Matar makaho 58-59

 


Page5⃣8⃣&5⃣9⃣ 




Cikin gida yabi sumayya, yana kiranta amma koh juyawa batayi ba, har suka shiga kofar su


Ke sumayya bake jinane, koh me? sai magana nake kin mini banza.


"Na fasa zuwa kaban key na bude d'aki"?


Akan me kika fasa zuwa, koh ince me akai miki, nadai san lafiya muka fitoh?


Ba kome kawai dai na fasa ne, tace tana tunanin ta fad'a masa abinda Ammar ke mata, wani zuciyar kuma ya gargade ta,   kartayi ta jawo wata rigimar kuma abanza.


Ke sumayya koh ba magana nake miki bane, nace menene dalilinki na fasa zuwa ?    


"Nikam nafasa nace maka kuje kawai"?    


Akan wani dalilin?


"Kaina ciwo yaka kuje kawai"


Ai shikenan nima na fasa zuwa, bara nakira, khadijan ta dawo,yakarasa maganar da kokarin juyawa


"Da sauri ta rike masa hannu"nifa ba ina nufin ku fasa zuwa bane,bafa"   


Ni kuma in bakije ba bazanje ba


"Shikenan muje"    


Haka sumayya tanaji tana gani tabi muhammad suka fitoh waje, ido ta d'aga ta kalli Ammar


Sunkuyar dakai Ammar yayi, tunda yaga fitowar su bai sake d'aga ido ya kalleta ba


Shiga motar sumayya tayi,  muhammad ma gaba ta bude masa ya shiga, ita da khadija a baya.


Ammar motan yaja suka cillah titi,sai millionaire sweet khadija kam sai bin gidajen unguwan take da ido, kamar wata wawuya,  tana d'aga ido, suka had'a da Ammar ta mirrow hararanta yayi ya kauda fuska 


A kofar wani makeken gida sukayi packing Ammar ya danna hon, da gudu maigadi yazo ya bude musu get, kusa hancin motarsa yayi zuwa ciki.


Suna packing Ammar ne ya fara budewa ya fita da,sauri ya zagaya ya bude ma muhammad bangaren sa hannunsa ya kama,  yatai maka masa ya sauko


Sumayya ma budewa tayi ta fitoh ta tsaya, tana kallon khadija dake ta kalekale koh fita takasa "khadija menene haka bazaki fitoh bane"?


Da sauri ta fitoh tare da d'an sosa kumatun ta najin kunya.


Cikin gidan suka shiga, sumayya kam, koh d'aga ido batayi ta kalli waje sau biyu ba , gaban ta kawai take kallo, don ita wannan gida baikai ta masa kallon hauka ba


Suna isa kofar falon Ammar yasa hannu ya bude,shiga sukayi bakin su d'auke da sallama


Wa'alaikumu salam oyoyo laleemon bee warugo, wata bakar mata hajiya kyakkyawar gaske, kallo d'aya zaka mata kasan ita ta haifi Ammar,sai wasu yan mata guda biyu,   da saurayi zaiyi sa'an khadija, duk suka mike ganin su sumayya sun shigo cikin falon.


Murmushi d'auke a fuskar muhammad ganin yanda mutanen gidan suka taresu da mutunci,yauwa hajiya jam bandu, noi shumre yan julijam?


Jam sai jam,muhammad?tace tana kallon sumayya dake tsaye, bismillah sumayya on jod'a mana?


Ba musu sumayya tazauna akan d'aya daga cikin kujerun falon Ammar ma waje yanunawa muhammad ya zauna sai khadija da tuni ta dade da zama abinta.


Gaisawa sukayi da hajiya, kannen Ammar suka gaidasu,Kayan ciye ciye aka jera musu a gabansu, dangin nama da kayan ci. 


Ammar ne ya aike kannen sa suka d'auko abincin da suka kawo a motar,sosai mamarsa taji d'adin ziyaran nan, abincin ma atake suka zuzzuba suna ci, sosai hakan yama sumayya dadi ganin basuda wulakanci koh jijidakai sam.


Har yamma suna gidan sosai khadija ta sake sai hira take da yan matan, muhammad ma hira yake da Ammar da Abbas sabanin sumayya da hajiya keta janta da hira, itakam daga eh sai ah ah .


Kai Aunty sumayya tsaya maimuna ta d'auke mu hoton sallah, khadija tace tana matsowa kusa da sumayya don tun d'azun hotona suke d'auka, ba musu sumayya ta mika wayarta iPhone wa maimuna ta dauketa da wayan.


Da mamaki maimuna kanwar Ammar ke kallon wayan, da sumayya ta mika mata,  koh su basu rike waya mai tsadan wannan ba,  sai wannan da yayansu yace rayuwansu abin tausayi, Amma ita bata ga tausayi anan ba mata kamar balarabiya, ga aji, dajiji dakai,  ga sutura mai tsada irin wanda mom in su ke sawa, Karba tayi 


khadija da sumayya suka gyara ta fara d'aukarsu hoto


Ganin maman Ammar tabar falon, yasa sumayya tashi ta kamo hannun Al'ameen ta jashe zuwa d'aya kujeran suka zauna, dafa kafad'arsa tayi "maimuna d'auke mu pls hoton yayi kyau


Ai da gudu khadija ta dawo bayan kujeran ta tsaya, daman 1siter ne Al'ameen azaune akai, sumayya a hannun kujera, ita kuma ta tsaya a bayan kujeran, d'aukarsu hoto maimuna take duk da muhammad ba kallo yake ba, Amma dai hoton yayi kyau, saidai ba camera yake kallo ba 


TikTok maimuna ta shiga ta kunna waka,  tana musu vedio sosai yayi kyau, fa'i ma shiga tayi da Abbas kannen Ammar, duk sun shiga vedio abu da iphone ga background, ba karamin kyau sukayi ba, Ammar ne kawai bai shiga ba.


Sai dare maman Ammar ta barsu suka tafi bayan sunci abincin dare, da suka tashi tafiya turare da zani ta baiwa khadija, sumayya kam sarka mai kyau ta bata fari, sosai sukayi godiya.


Tunda suka kama hanyan dawowa, sumayya ta lura akwai abinda ke damun mijinta,  ganin yanayin sa ya sauya sosai.


Bayan sun dawo gida, har gida Suka raka khadija,ruwa ta iba takai band'aki ganin yanayin Muhammad, kamar ba lafiya, gabaki d'aya yayi laushi kamar bashi ba"yayan khadija nakai maka ruwa, koh zakayi wanka"?


Toh,kawai yace yana mikewa,wankan ya shiga koh towel bai d'auka ba, saida sumayya ta kai masa 


Bayan ya fitoh wanka d'aure yake da towel, daga kagan sa, kasan ba lafiya,a hankali yake tafiya yana dafe da kirjin sa, yashigo d'akin.


 da sauri sumayya ta bisa da kallo,dayake yanzun basa shakkan juna, sosai bakaman daba,yasaka ta tube kaya a dakin, towel nata ta d'aura ta fita, ban d'aki ta shiga tayi wanka,  fitowa tayi ta shiga dakin da mamaki take kallon Al'ameen, ganinsa har lokacin zaune koh kaya baisa ba yayi tagumi.


Al'ameen dake zaune ji kawai yayi sumayya ta kamo hannunsa,A hankali tayi magana "yayan khadija lafiya"?


Janyota kawai yayi gabaki d'ayanta ta fado kansa, a hankali ya sa hannu ya dad'a mannata a jikinsa.


" yayan khadija bansa kaya ba"? 


Na sani sumayya ai naji jikin ki d'aure da towel.


"Meke damunka"?


Zuciya ta ke dokawa da karfi, sumayya inaji a jikina akwai wani babban Al'amari dake tinkaro ni.


" kamar ya"?


Sumayya zuciyar kowa na bugawa, sannan wani sa'in mutun najin zuciyar sa na luguje,  Kamar yaji tsoro,koh baida gaskiya,koh yayi laifi.


"Hakane"


Amma ni wannan bugun zuciyar bana tsoro koh fargaba bane.


"Name kenan, bangane ba"?


Lumshe ido yayi yana kara manna sumayya a jikinsa,irin wannan lugujen na ringaji lokacin da mami na zata bar duniya, Aranan haka na wuni da lugujen zuciya.


Haka ranan da zan makance, ma irin bugun nan na ringa ji, haka ranan da salim zai bar duniya,sumayya inaji a jikina akwai abinda zai faru dani duk da bansan gaibu ba.


"Subahanallah insha Allah ba abinda zai tinkare ka sai Alkhari"


Insha Allah....Sumayya!


"Na'am yayan khadija"


Don Allah sumayya, yau ki bani hakkina, sosai nakejin wani irin matsanacin bukata, tun da yamma.............



Ta bangaren hajiya kami, kamar yanda boka yace, haka ta d'auke mujiya har cikin gidansu, bayan ta saka kejin a buhu, a d'akin ta ta ajesa a karkashin gado, kamar d'a haka take masa jinya, A washe garin ranan da sumayya zata fara period, a daren ranan, Alarm kamila tasaka a wayan ta, da misalin karfe 2 na dare ya tashe ta, mikewa tayi a hankali ta bude kejin zata d'auki mujiya.


Da wani irin mugun sauri taja baya tare da zaro ido.....mujiya ne tayi mushe, bakinta har rawa yake ta d'auki waya, lalubo number Harira tayi, ta kara wayan a kunne


Ta bangaren Harira kam,tana tsaka da baccin ta,don a silent ta saka wayar sam bata san ma, wata kamila na kiranta ba


Jifa kamila tayi da wayan,jin Harira bata d'auka ba 


Washe gari da sassafe koh karyawa,kamila batayi ba ta ciccibi mushen mujiyan nan, tayi gidan Harira,don wallahi ta kudurta A ranta bazai yuba, bazata kashe kudi abanza ba, sai an biyata kudin ta, haka kawai ita ba muhammad ba, ita kudin ta ya tafi


Koh sallama babu ta shigo falon Harira, tana kwala mata kira.


Da sauri mijin harira ya d'ago, yana kallon kamila, lafiya baiwar Allah? 


Lafiyar kenan, ina Harira?


Kafun ma yayi magana, harira ta fitoh daga d'aki cikin mamaki jin muryan kamila da sassafen nan, kamila lafiya?


Lafiyar kenan, kika gannin nan,wallahi kinji na rantse bazanyi asaran kudina ba, kin sanni bani da mutunci tam.


Da sauri Harira ta kamo hannun kamila,  sukayi wani d'aki dake cikin falon, ganin mijinta a zaune a falo, kamila ke kokarin tona mata tsilili


Ke kamila bana son iskanci kinji koh, zaki  zo mini gida da sassafe,agaban mijina kina kokarin zubar mini da mutunci.


Au mijin da kikace kin shanye ne,  har zakiji tsoron yasan wani abu a game dake?


Ji hauka toh don ka asirce, mutum sai akace ka fad'a masa ka masa asiri ?ji mahaukaciya


Ke duk ni ba wannan ba,mujiya ta mutu,  tana boot na mota na,ki wuce mu koma inda muka karbo she, yaban kudina in yasan bai iyya aiki ba, mena karbamin kudi(daman wannan halin kamila ne indai akan kudin tane bata da mutunci)


Ke da sassafe,  koh karyawa banyi bane,  zan kama hanyar mutum biyu,toh baki isa ba,  don uwarki ni, xaki tsaya kina bawa umurni.


Ganin Harira tad'au zafi, daman ita bata iyya fushi ba sam, yi hakuri Harira raina ne ya baci,  don Allah ki taimaka,mu koma wajen mutumin nan.


Ki jirani nayi wanka, na karya saimu tafi?


Ok kawai tace tana zama,abakin gadon d'akin ta zabga tagumi.


Sai kusan 9 suka d'auki hanya, gabaki d'aya kamila sai masifa take, akan malamin bai iyya aiki ba


Bayan sun isa,aje masa kejin mujiyan,  kamila tayi a gabansa 


D'aukar mujiyan yayi ya kakkala, yanka cikinta yayi ya fitar da layan,warwarewa yayi atake,  yaga rubutun sunan sumayya ya kone murus,  kamar wanda aka saka kalanzir da petur aka banga masa, d'aga ido yayi ya kalli kamila.


A gaskiya raba Wa'innan ma'aurata baban matsalane, don asirin da aka musu mundin aka rabasu, xa'a iyya samun matsala aikin wasu warware wa zaiyi,gashi sun rike ibada sosai,koh wajen kofa da Aljan zai kusance su sun tushe sa,makiyansu na tare dasu,  tabbas suka gane akwai mai kokarin bata musu shiri,zasu iyya ganin bayanki don su mutuwa koh Rayuwa,agunsu don cika buri ba kome bane.

Ina mai baki shawara,kamila ki hakura da kokarin rabasu,kidai nemi wani hanya da zaki malleke sa, Amma banda asiri tunda kika ga nayi iyya kokari na ba'a dace ba toh ki hakura.


Wani irin na hakura,sai dai kace baka iyya aiki ba, kuma maganar kudina, Amaida min tunda aiki baici ba.


Keeeeeeee!!!! dakata,  bamason rashin kunya a wajen nan,inba haka ba wallahi zamuyi maganin ki, nan ba wajen shirme bane, kuma kudi inya shigo baya fita


Ganin tana kokarin magana,yasa Harira matse mata baki


Buge hannun Harira kamila tayi,don gabaki d'aya ranta ya gama baci,sosai zuciya ya ibeta,kai bokan banxa, bokan wufe mai karyan aiki,yana cin kudin mutane,wallahi baka isa kace zaka dakeni ka hanani kuka ba,  kudina ne sai ka bani,tunda aiki na baka,  kuma aiki baiyi kyau ba,kai harka isa kace zaka min abinda Allah bai mini ba?


O' kinsan da hakan ne,kikazo guna yau saina nuna miki aikin, nakan dutse gaskiya ne, wani irin maganganu yayi take kadangaru dake manne a jikin kokon,guda goma suka ruga da gudu zuwa jikin kamila, ai kam da sauri suka manne mata a jiki, daman dogon riga da d'an karamin gyele ta yafa, biyar sukayi kasan dogon rigan suka mamakale mata a cinya wasu sukayi cikinta wasu kan breast inta, suka makale wasu kam gashin kanta suka shiga suka kwanta.


Ai wani irin ihuuuu Harira ta sake, da gudu tayi waje, kamila kam wani rin tsalle tayi ta bugu da kasa hade da kurma ihu, tana bawa nakan dutse hakuri,amma ina koh kallon ta baiyi ba,jin kadangarun manne a jikinta,  kamar sun samu jikin gatanga, yasata yarda d'an kwali da takalmi da gyele,da gudu ta ruga tayi waje tana ihu, jinsu sai yagushinta suke, b'anb'arawa tayi da gudu harta wuce, Harira data dade da fita,cikin gari ta fitoh tana ihu tana kokarin kwabe riganta Allah yasa akwai brz da dogon wando 


Ai jama'a salati suka d'auka, ganin kadangaru mammanne,a jikin kamila gashi duk inda ta wuce sai wasu kadangaru dake wajen,sun bita da gudu,ai itama saita kwasa a guje suma suka bita gayya guda a baya 


Duk mai imani inya kalli kamila saiya tausaya mata, wasu kam sai Allah kara suke mata jin tana sambatun, mugun abinda taso aikatawa hakan ya faru da ita


Harira batabi dakan kamila ba,duk tabi ta tsorata motar taja sai jala.


Tana isa gidan su kamila ta wuce direct, tana kuka ta sanar, da iyayen kamila abinda ya faru, sosai hankalinsu ya tashi,  hade da tsinewa Harira,su sunsan yarsu batasan wajen boka ba Harira ne ta kaita


A take suka tasa keyar Hariya zuwa mutum biyu, suna isa ake sanar dasu ai kamila tayi daji,don gudu take kadangaru na binta, da gudu iyayenta suka nausa hanyar da aka nuna musu kamila tabi. 


Kamar wasu zararu haka suka fasa daji, suna neman kamila,Acan gindin wani bishiyan kuka,suka ganta zaune sai ihu take tana kama kadangarun dake jikinta tana hurgarwa,  da gudu zasu dawo su like mata, gabaki d'aya katangaru ne a mammanne a jikinta, wasu suna manne da jikin bishiyan da take kai, saboda basu samu fili ba abin gwanin tausayi gabaki d'aya ta zareeee.


Maman ta kam kwala kara tayi, tayan ke jiki ta fadi, da gudu baban ta yayi wajen da niyar kamo yarsa, duk da kadangarun sun matukar bashi tsoro, amma haka yayi ta maza


Ai kadangarun nan,na kallon baban kamila na tahowa da gudu suka zabura, sukayi kansa 


Ganin kadangaru sun juya garesa,yasa sa b'anb'arawa da gudu yakoma baya,suma koma sukayi inda suke kamar da


Ganin Halin da maman kamila take ciki, yasa Harira da baban kamila,d'aukarta yayi suka fitoh cikin gari da ita,asibitin mutum biyu suka kaita, bayan an bata gado,waya baban kamila yayi ya kira maman sa, da yan uwansa ya sanar dasu abinda ke faruwa, Harira taso fecewa,Amma baban kamila yace ina, kafarsa kafar Harira in Harira taga tabar mutum biyu toh da kamila za'abar garin.............


No comments