Matar makaho 56-57

 


Page5⃣6⃣&5⃣7⃣  

Tunda muka fitoh Banganta ba.





Wani irin baki gantaba kuma hauka kike ne khadija koh me?


Wallahi yaya da gaske nake banga Aunty ba.


Nashiga uku ni muhammad, yace yana kamo hannun khadija suka tsallaka titi zuwa cikin masallaci sosai suka dudu ba Amma basu ga koh mai kamada sumayya ba sosai abin ya gigitashi, ke khadija a daidai ina kuka rabune wai?


A kofar fitane fa yaya cunkoso yasa muka rabu.


Jingina kawai yayi da jikin ginin masallacin shikam dai ya shiga ukun sa ina sumayyar ta shiga ne wai?


Yaya koh dai aunty gida ta koma ne?


Wani irin gida kuma khadija bayan saida nace ku jirani a global xaki wanice ta koma gida nadai san sumayya bazata koma gida ba

 

Daga khadija har muhammad hankalin su ya tashi har hankalin yan agaji ya dawo kansu d'aya daga cikin su ya tambaye sa


 malam lafiya naga kana ta zaga masallaci kaje ka dawo,  tun dazun yanzun fa ana neman 4:00 bazaka tafi gida ba ga kanwarka   ma naga kuna ta yawo tun d'azun lfy kam?


Ina fa lfy wallahi ranka ya dade da matata mukazo masallaci amma ban ganta ba gabaki d'aya na gama iyya dubata amma bangan taba


Wace irin magana ce wannan ita matar taka yar yayece koh jaririya da za'a nema a rasa koh hanyar gidane bata sani ba?


Ranka shi dad'e ni nasan bazata koma gida ba tunda nace ta jirani toh tabbas zata jiranin


Kaga malam karkazo ka d'aga mana hankali a wani unguwa kuke ne?


Sintali ne..


Sintali😳A koh B?


Sintali A ne ranka ya dade


Amma dai kai d'an rainin wayo ne ina sintali A ina macilin da bazata iyya komawa da kanta ba kazo kana kokarin daga mana hankali?


Kayi hakuri ranka ya dade 


Na hakura amma ka fita kakama kanwarka kubar masallaci nan ya zakazo da maganar da hankali bazai d'auka ba matar ka ta bata,  ina macilin ina sintali?da bazata koma ba


Kayi hakuri..


Kama gabanka malam?


Haka Al'ameen ya fita kaman k'wai ya fashe masa a ciki 


Da sauri khadija tazo ta kama masa hannu haka suka fito a masallacin gwanin tausayi     

Tsallake titi sukayi suna tafiya Gabaki d'ayansu inka gansu kaga wa'inda basu da nutsuwa gabaki d'aya zuciyar Al'ameen bugawa take kamar ance masa sumayya  zata barsa   


Sunzo daidai titin doruwa kamar daga sama khadija ta hango mace da hijabi tana tsallako titi Allah yasa akwai wutan sola shiya bata daman ganin wance ta tsallakon da karfi ta kwala ma sumayya kira Aunty!!!


Ai da wani irin mugun sauri Al'amesn ke magana, kee kin ganta ne ina sumayyar take tana ina?


Kafun khadija ta basa amsa da  gudu sumayya ta karaso karesu"lafiya har yanzun baku koma gida ba"?


Kee sumayya kina da hankali kuwa banace miki kafun mu shiga masallaci,  kujirani a gidan man sintali ba koh ba haka nace ba,  shine zakisa kafa ki koma gida don tsabar kin raina min wayo gani d'an iska koh?


"Don girman Allah kayi hakuri, wallahi sace mini takalmi akayi shine na tsaya nema na jira mutane suka fifita duk ban gane ba dana fitoh wajen global, nan ma ban ganku ba shine nayi tunanin kun koma gida saina koma nima danaje kuma naga baku dawo ba, shine nabiyo ku"


Don Allah yaya kayi hakuri tsabani aka samu!


Na hakura khadija Amma sumayya karki sake mini haka Am warning you?


"Insha Allah" tace tana kama hannunsa dake cikin na khadija don baizo da sanda ba suka tsallaka titi


Bayan sun isa gida ganin sun kusa makara yasa sumayya hana khadija zuwa gida abincin sahur ta iba mata tuwo ne miyan kifi d'anye suka zauna a waje suna ci 


Al'ameen kam tuwo kawai yakeci  da miya baya cin kifin 


Da mamaki sumayya tace "yayan khadija ya bakacin kifin  gashi mun kusa makara fa"?


Sumayya bazan iyya cin kifi d'anye ba kar kashi ya makale min a wuya


" tarwad'a ne fa"


Nikam ah ah


Hannu sumayya tasa a kwanon miyan ta yago kifi tasa mai a baki"toh bude bakin nasa maka"


Da sauri khadija ta kauda kai kamar bata gansu ba don wallahi sun bata kunya


Al'ameen kam bude baki yayi sumayya sai da ta ciyar dashi kifi har yace ya isheshi kafun ta ci nata


Bayan sunyi sallan asuba khadija ta koma gida Al'ameen kam bacci suka koma suna ramakon na jiya


Yau koh tafsir basu samu zuwa ba saboda baccin dake idanun su har 12:00 suna bacci a d'aki 


Assalamu Alaikum!! wasu yan matane guda hudu ke sallama sunfi minutes 8 suna buga sallama shuru


Al'ameen kamar a mafarki yake jin sallama akai akai mikewa yai hade da amsa musu


Ina kwana?


Lafiya, ya amsa 


Am wajen sumayya mukazo


Ok lafiya kam?


Eh munzo tambayar lallen sallah ne


Ok bara na tada ta


Ah ah ka barta in bata tashi ba inyaso gobe sai mu dawo 


Ok toh Allah ya kaimu 


Ameen,  in ba damuwa inta tashi kace yaran gidan Malam yunusa ne sukazo tambayar Lalle kar wasu suzo su riga mu?


Toh yace yana d'aukar boket bayan sun fita wanka yayi ya shiga dakin dayake yanzun yasan soket in kunna TV  jin an kawo nepa ga fanka na hura d'akin danna soket in yayi daman jiya sunnah  suke kallo aka d'auke, zama yayi yana sauraron wa'azi hannun sa d'auke da calbi yana ja


Sumayya bata tashi ba sai azahar nan ma shiya tashe ta kafun ya tafi masallaci


*******************

Haka rayuwa yayi ta tafiya axumi nata karewa a hankali hankali customers na sumayya suke zuwa tambayar lalle tun sallah saura kwana goma ita karan kanta batasan adadin wa'inda suka tambaye lalle ba ita dai ta amsa zatayi amma suzo da wuri,  sannan tana musu tallan wanda zaiyi kitson sallah kanwar mijinta nayi ai kuwa khadija ma tatara customers sosai, 


kayan sallah ma bana muhammad ne ya d'auke sumayya da khadija har kasuwa sukayi sayayyan sallah duk da sumayya taki yarda ganin tana da wasu zanunuwan a akwatin ta amma ina yace na akwati daban na sallah daban, ba laifi yasai musu kaya itama ta dad'a wasu da kudin ta haka ma khadija ta kara mata har kala biyu bayan wanda ya musu she karan kansa gezena biyu yasaya sumayya ta kara masa biyu duk sunka kai dinki.


Akwana A tashi yau dai saura kwana d'aya sallah kofar sumayya makil da jama'a daga masu kitso harda masu lalle, harda su suwaiban adara yau ana bin layi a kofar, sumayya na hango sanye da riga da wando baki tana ta fama da lalle sai khadija dake ma wata yarinya kitson brazil kulu da bit 


Har yamma mutane ne makil ba ita ta rabu da mutane ba sai kusan goma na dare nan ba hakuri ta basu akan gobe su dawo da asuba


Al'ameen dake d'aki kwance yana lazimi shiya raka khadija gida 


Yau sumayya koh girkin asuba bata samu tayi ba na bud'a bakin ma watace ta mata girki tana ma yarta lalle


Yauma bayan sunje tahajjud suna dawowa ne suka samu tuwo a bakin titi na asuba suka saya,  dashi sukayi sahur


Sumayya suna komawa gida suna sallah ta kwanta ai koh gama d'aukarta bacci baiyi ba tafara jin sallaman mutane ga idonta duk bacci kin tashi tayi Al'ameen ne ya fita ya basu hakuri akan sumayya na bacci Amma haka bayin Allah nan sukaki tafiya taburma suka shimfid'a suka zazzauna🤣suna jiran sumy(masu lalle gaskiya kuna ganin abu a sallah har kwana ana muku a d'aki)


Surutun su shiya hana sumayya komawa bacci haka tanaji tana gani ta kasa bacci dole yasa ta fitoh jin jama'a sai dad'uwa suke


Ai tana fita saiga khadija da tawagar masu kitso sun tasata a gaba😎


Haka suka dukufa suna neman halal nasu, 


Al'ameen fita yayi a d'akin sumayya! yakira sunan ta 


"Na'am"ta amsa tana mai mikewa ta bisa d'akin ganin ya koma


Sumayya zan fita na karbo mana dinki,  maganar zuwa kasuwan fa muna sa ran gobe sallah fa naga bamu shirya kome ba?


"eh kam gaskiya nima naso naje kasuwan nan da kaina amma yanzun ba iyya fita zanyi ba sai dai ku tafi da khadija in yaso sai na rubuta mata list"?


Ok nace na saya mana watanda ne?(naman shanu da ake yankawa a ranan jajeberi ana saidawa a unguwa)


"Ah ah ka saya mana kaji gaskiya tunda sallah ne"


Shinkafa koh tuwo zakiyi?


"Habba tuwo ranan sallah, shinkafa zanyi da miya sai coslow da kaji sanan zanyi masa da miya"


Ok daman so nake ranan sallan nan mu kaiwa gidan su Ammar abinci kuma muje mu gaida iyayen sa sai kuma nayi tunanin kar suce don kudin su yasa muke son rabansu fa?


"Ah ah yayan khadija in zakayi abin Alkhari kayi kawai karma ka bari shaid'an ya saka maka wani tunani daban a ranka kaji"?


Shikenan sumayya Allah ya kaimu goben kinyi lalle kuwa?yana maganar yana kama hannun ta


"Ina naga lalle daga ni har khadija ba lalle ba kitso"


Kai gaskiya nifa an takurani tun sallah saura kwana hudu ban sake cin abincin kiba ki taimaka ki mana girkin sallah da kanki


"Insha Allah la'asar nayi zan sallami kowa wanda ya samu da wanda bai samu ba duk sai suyi  hakuri nima na samu nayi aikin sallah"


Ok kiramin khadijan inkin gama rubuta list in mu tafi


Haka koh akayi sumayya list ta rubuta ta baiwa khadija duk yanda jama'a masu kitso suka ringa roko sai da sumayya ta d'aga khadija suka tafi kasuwa


 dinki suka fara karbowa sai cefenen da sukayi sosai sukayi cefene sai da ya cika bairo.


Bayan khadija ta dawo sumayya tashi tayi ta gyara kajin duk da wasu sunso karba mata Amma taki yarda soya kajin tayi daman guda biyar ya saya ta rabawa mutane d'aya sosai tayi ta ayyukanta wasu kamma ganin aiki take kuma ba karewa zaiyi ba, zuciya kawai sukayi suka tafi abinsu wasu kam kama mata aikin sukayi duk da ta nuna su bari amma kin bari sukayi wasu sun gyara mata tattasai wasu sunkai nika cikin kankanin lokaci ta kammala had'a abubuwan sallan ta miya ma ta soya amma bata sa ruwa ba saboda ba'a tabbatar anga wata ba vegetables ma bata yanka ba tadai sasu a firij ne 


Bayan Ansha ruwa sumayya sallamar mutane tayi wa'inda bata musu ba ta basu hakuri wasu kuma sukace gobe koh jibi zasuzo Amusu


Yau kam saida muhammad ya saya mata matsala 8 tasha tsabar yanda bayanta ke ciwo amma fa gaskiya ta samu kudi bana wasa ba a sallan nan khadija karan kanta kudi ta samu sosai 


Har dare ba'a sanar anga wata ba haka su sumayya suka kwanta da niyar inba'a gani ba zasu tashi da azumi


Aiko hakance ta faru don da asuba ji sukai ana atashi ayi sahur jama'a gobe ba sallah bane😌


Ai yau kam sanin da sumayya tayi ba karamin mutane ne zasu zo ba yasa tana sallan asuba ta tattara boron lallen ta tayi gidan goggo Al'ameen ta bari a d'aki yana bacci tace masa zata saloon gyaran gashi sai tayi lalle tama khadija  


Gidan goggo taje tayiwa khadija lalle ja da baki itama tayiwa kanta sai dai bata ma hannun dama ba manna masa gam tayi khadija tasa mata lalle akai


Lallen su na kamawa ita da khadija saloon suka wuce aka gyara ma khadija gashi don ita kam bata wanke kanta a sefe, kitso khadija ta watsa mata a saloon sai kusan la'asar sumayya suka dawo, kai taga ikon Allah jama'a ne tirem a kofar ta Al'ameen ya rufe kofar d'aki ya fita sukam suna zazzaune a baranda 


 haka ba yanda ta iyya ta hau musu lalle 


Dayake ana da tabbacin gobe sallah ne yasa khadija had'a musu miyan sallah ta d'aura zobo tana gama had'awa ta juye a robobi tasa a firij


muhammad ma ya turo kayan marmari da sumayya tace zata markad'a a blander tayi juice dashi 


Sai dare sosai mutane suka watse ita da khadija suka kai nikan shinkafa bayan sun dawo suka kwaba, yaukam khadija a gidan ta kwana da sumayya a waje yayanta na d'aki


*RANAN SALLAH*

yau take sallah ranar farin ciki ga dukan wani musulmi kowa ka gani fuskar sa d'auke da farin ciki hakan take a wajen su sumayya tun asuba khadija ta fara tuyan masa


 sumayya ma wuta ta hura ta d'aura shinkafa don yau dai ba'a gas koh hot plate za'ayi girki ba


Vegetables inta ta kama yayan kawa su green beans green pepper yellow pepper piece cabbage carrot harda k'wai ta d'aura a wuta ga babban kwalban BAMA a zaune agefe


karfe 7:30 sumayya sun gama girkin sallah, 

manyan kulolin ta masu shegen kyau,  bata taba bude suba sai a ranan mai guda biyar ne ta zuba shinkafa masa coslow miyan ganye da miyan stew sai manyan manyan kofunan zamani ta juye zobo a ciki d'aya kuma mango juice duk sunyi sanyi har suna raba ta sake maidasu firij, wannan na gidansu Ammar kenan,  sauran juyewa tayi a babban kula  haka ma miyar duk d'aki ta shigar dasu sanin halin mutanen gidan 


Wanka tayi ita da khadija suka saka kayansu mai kyau da hijab Al'ameen ma gezena insa sabo ya saka koh sanda sumayya ta hanasa rikewa ita ta kama hannunsa khadija ta rike musu sallaya rufe kofa sukayi lokacin karfe 8:30 sauri suke karsu rasa sallah


Suna fita a gidan sun tsaya a bakin titi amma ba keke koh wani keke suka tare a ciki haka suka fara takawa, kamar hadin baki saiga Ammar ya shawo kwana da motar sa packing yayi a gabasu hade da budewa ya fitoh sanye yake da wani d'anyen yadin shaddane mai kyau sai hula da takalmi agogonsa sai d'aukar ido yake.


Ashe gwara danayi sauri tun d'azun ina ta tunanin bazan same kuba taima ?


Laii Ammar kaine sannu ina kwana?


Lafiya muahmmad barka da sallah.


Ai ba'ayi sallar ba tukum, muhammad ya basa amsa


"Ina kwana"?sumayya tace tana had'a fuska ganin yauma kamar kullum idonsa akanta


Lafiya sumayya muntashi lafiya?


"Lafiya mungode Allah"


Khadija kam kuri tayi tana kallon sa toh a ina tasan bawan allah nan ne kam ta kasa tunawa, a hankali ta ma sumayya magana, aunty nikam a ina kukasan wannan ne?


"Habba khadija kin manta mutumin da yazo asibiti lokacin da za'a mini tiyata ya baki kudi ki ban"


Oh na tuna na tuna Aunty , ina kwana?tana gaida Ammar


 kin amsawa yayi hannun muhammad ya kama muje koh ku shiga mota muyi sauri karmu rasa sallah


Ba musu dukansu motar suka shiga yaja suka kama hanyan masallaci


Allahu Akbar anyi sallah lafiya jama'a kamar kasa suna ta fitoh wa a edi kowa ka gani fuskar sa a washe sai gaisawa ake da juna abin gwanin sha'awa kowa na sanye da sabin kaya sai dai na wani yafi na wani tsada


Bayan su Ammar sun fitoh a cikin cunkoson jama'ar dake masallacin, yaso kaisu muhammad gidan su amma sukace ya maidasu gida zasu d'auko abincin da zasu kai gidan nasu


Ba musu ya mai dasu gida abincin muhammad ya d'auko musu a kula ya fitoh waje dasu juice taburma ya shinfid'a musu ba kyama Ammar ya  zauna sukaci abincin da muhammad sai santi hake don gaskiya abinci ne na kece raini 


Ta bangaren sumayya abinci ta sassaka a kwanuka ta baiwa khadija ta rabawa mutanen gidan ADARA kowa da plate nasa ta zubawa goggo ma ta kai mata tana dawowa sukaci abinci tukum kafun suka sake wanka lokacin azahar yayi sallah sukayi sumayya ta watsawa khadija make-up sosai khadija tayi kyau tana sanye da dogon riga na zani holland mai shegen kyau sai gyele da jaka tare da takalmi hada agogo da su sarka masu azaban tsada sosai sumayya ta kashewa khadija kudi a sallan nan 


Ita kam les tasaka sai mayafin ta babba powder kawai ta shafa sai kwalli da man baki don A matsayin ta na matar aure hakan baidace ba tayi kwalliya ta fita tana d'aukar hankalin maza


Al'ameen ne ya shigo duba su sumayya sun gama shiryawa ne Ammar ya dawo yana jiransu 


"Don Allah yayan khadija ka sake wanka mana ka chanja kayan jikin kan nan"?


Meya samu na jikin nawa?


"Ba kome amma dai ya kamata ka chanja tunda gidan masu kudi zamu gwara mu kece raini"


Kai sumayya kin cika shirme amma dai bara na watsa ruwan shap shap yayi wanka ya fitoh sabon gezena da sumayya ta d'inka masa shiya saka mai tsadane sosai sai takalmi da agogo yau harda glass sumayya ta d'auko tasa masa lias na hannu riga duk ta makala masa,  hannunsa ta kama suka fitoh bayan khadija ta rufe kofar 


Kulolin suka d'auko guda biyar sai jup na juice da zobo duk suka jera a boot na motan Ammar 


Tunda sumayya ta fitoh idon Ammar ya sauka akanta gabaki d'aya ya tatara hankalin sa

Gareta sai kallon ta yake kamar idanunsa zasu zazzago


Sumayya kam tun fitowar ta ta lura da kallon da Ammar ke mata kamar maye duk d'aga ido da zatayi sai sun had'a ido ganin yanda duk yabi ya zuba mata na mujiya yasata juyawa da sauri cikin haushi tayi cikin gida


Khadija dake kokarin shiga motar ganin sumayya tayi cikin gida yasa ta kwala mata kira, aunty sumayya kin manta wani abune?


Sumayya koh juyowa batayi ba tayi shegewar ta ciki 


da sauri Al'ameen ya fita a motar jin khadija tace masa sumayya ta koma cikin gida yabi bayanta..........

 


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 08146017245  *hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata  na maman haidar*

*Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah* 


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


 *1 Gumbar kankana da ayu* 🍀🍀

2 *Gumbar ayu zallah* 🍀🍀

3 *Gumbar Madara da kwakwa*🍀🍀

4 *Kaza mekwai* 🍀🍀

5 *Zabo me zuma*🍀🍀

6 *Kaza me allurai🍀🍀 sahihiyar mallaka ba boka ba malam*🍀🍀

7 *Kwallin idonka inadona*🍀🍀🍀

8 *Tauwadar mata*🍀🍀🍀

9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*

10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice  gwada wnnn*

11 *Maganin nono. Sahihi* 

12 *Maganin hips and bobbs* 

13 *hodar. Ni I'ma koramar mata*

14 *nakasan Mara babban sirri*

15 *kafi jijjibi*

16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*

17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata* 

18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai  Babu magana*


 

 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

*Maman haidar Bata tsaya anan ba*

*takawomuku hadaddan sabulun  gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata  gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo  kudai kunemeta awannan number*   08146017245

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧   


*Wannan page nakune Queen fauzee da ogan ki naga comment naki jiya*😂


No comments