Matar makaho 54-55

 


Page5⃣4⃣&5⃣5⃣




Akan ibada don naga d'an changen rayuwa da kuka samu haryasa kuna sanyi da ibadan koh, toh bari kuji irin wannan daman makiyan ku suke jira sumu ku mai gabaki d'aya in kukayi sake da ibadah toh tabbas zasuga bayan ku sarkin yawa yafi sarkin karfi, watan da muka shiga   wata ne mai Albarka ni'ima da falala ku dukufa wajen neman tsari da kariya a wajen mahaliccin mu.


Sake baki sumayya tayi tana kallon matar da bata santa bama gashi dare ne ba nepa bare ta mata kallon sap"malama wani irin magana ne haka sannan suwaye makiyan mu"?


Baki bukatar ji nidai na fad'a miki tace tana fita a kofar


Sumayya kam kamar doluwa haka ta kuma sai bin hanyar da matar ta fita kawai take tana Al'ajabi"yayan khadija kaji wani magana kuwa"?


Uhmm sumayya  maganar matan nan koh bamu gaskata ba, Amma tunda ibadah tace toh mu dage koh ba makiyi Addu'a makamin mumini ne 


"Gaskiya ne" sumayya tace duk jikinta yayi sanyi sosai abincin ma kasa cigaba daci tayi


Al'ameen dake cin abinci tsayawa yayi jin sumayya shuru hannu yasa ya tabata sumayya yadai?


"Uhmm babu kome kawai dai ina mamaki ne"


Mamakin me kuma? inna matan nan ne ai ba abin mamaki bane don duniya da fad'i kika san menene Alakarta da su kedai mu rike ibadah hannu bibiyu insha Allah ba Abinda zamu gani sai Alkhari kici Abinci pls?


Toh tace tana cigaba dacin abincin"yayan khadija me zan dafa mana na sahur"?


Me kike so?


"Uhmm  aikai na tambaya koh"?


Nima saina tambaye ki


"Toh ai mata ke tambayar miji abinda za'a dafa"


Au yanzun kam an yarda ni mijine kenan?


"Oho dai nikam ka fad'a mini abinda zan dafa so nake mu kwanta da wuri samun mu tashi da wuri"


Ki mana tuwon shinkafa miyan shuwaka 


"Nama koh kifi"?


Duk wanda ya dace ki saka


"Ok" kawai tace tana tashi kitchen ta shiga ta barshi zaune akan taburma


Girki sumayya tayi sai kusan 10:30 ta kammala aikin girki juyewa tayi a kula takai d'aki tayi tatan kamu da khadija ta karbo mata a inji tana gamawa tattara taburman tayi, ta rufe kofar su zuwa lokacin Al'ameen yayi bacci tuntuni itama kwanciyar tayi bata tashesa ba don bacci takeji itama


Misalin karfe 1:30am Al'ameen ya farka jin sumayya ajikinsa yasa sa tata bata, sumayya!! sumayya!!


"Menene"?


Ki tashi mana


"asuba yayi ne"?


Baiyi ba sallah zamuyi tashi maza kinji


"Uhum"tace tana mikewa sauka tayi akan gadon ta kamo hannunsa suka fitoh waje bayan ta kunna hasken wayan ta Alwala sukayi suka tada sallah


Sai karfe uku suka sallame sosai suka dukufa suna Addu'an neman tsari wajen mahallincin mu da neman gafaran sa


3:41 sumayya ta d'auko musu tuwon ta bude da zafin sa kamar yanzun akayi zuba musu tayi sukayi sahur  basu koma bacci ba sai data cika ruwan randa a laida fari ta d'add'aure ta cika firij nata bayan asuba suka koma bacci


Dayake Cikin Ramadan ba'acika sayan kaya da safe ba sai yamma yasa Al'ameen yabiye wa sumayya suka cigaba da bacci basu suka tashi ba sai kusan 9 Al'ameen ya tafi masallaci tafsiri sumayya ma  islamiyar unguwan taje  wata babbar malama ke tafsir wa matan aure a ciki 


  sai bayan Azahar Al'ameen ya fita shago,  sumayya kam sallah tayi ta shiga kitchen abinci ta dafa dankali ne da kwai ta soya sai ruwan tie ta musu macaroni da miya duk ta zuzzuba  a kula ta zuba wasu goggo ma a manyan kula guda biyu,  kiran yaro tayi ya kira mata khadija bayan ta dama kunu cikin bokatin penti fari babba, wanka ta shiga kafun ta fitoh saiga khadija ta shigo bayan sun gaisa ta bata boket in da cups na roba wanda ta saya jiya ta had'a mata takai masallaci sadaka sai ruwan da tasa da asuba a firij  sunyi guda shima boket ta cika ta d'aurawa Almajiri yabi khadija 


Rarra bawa khadija tayi a masallaci sosai jama'a ke sawa abin Albarka don koh masu kudin unguwan basa kawo kome a azumi sai talakawa ke kokarin ciyar da masu azumi (Allah ya kyauta)


Bayan khadija ta dawo da bokata yen, kulan abinci sumayya ta bata ta kaima goggo suyi bud'a baki


Al'ameen ne ya had'a kankana da dabino sai sweet milo, yasa a laida biyu ya rike a hannunsa barin shagari yayi a shago hade da basa kudi yasai abin bud'a baki shima 


Gidan goggo ya wuce ya bata laida d'aya ya kamo hanyar gida


Tun akan hanya ake ta masa godiyan kunu da kankara sosai yayi mamaki wani kunu kuma amma baiyi magana ba amsa musu yayi ya shiga gida daidai lokacin aka kira sallan mangari ba


Assalamu Alaikum


"Wa'alaikumu salam"


Jin bakin sumayya cike da abinci ta amsa sallamar yasa sa da mamaki yace toh yau koh jira babu hajiya har an kai loma?


"Ai a azumin nan ba jira kaji in gaya maka ana kiran sallah sai ci yaushe zan jiraka kuma"


Uhmm yayi kyau yace yana zama akan dakalin da take, mika mata laidan yayi ganin yau koh karba batayi ba sai jin karan shukali kawai yake


Amsa tayi ta bude dabino ne guda biyar ta damka masa a hannu sai ruwan shayi a kofi


Karba yayi ya bude baki da addu'a bayan yaci dabinon ruwa ya kurba kawai yayi Alwala ya tafi masallaci 


Sumayya kam sai da ciki ya d'auka kafun ta zakud'a itama sallar tayi bayan ya dawo masallaci shima yaci nasa Abincin sauran kayan marmari da ya rage ta saka a firij 


Da misalin karfe 11 bayan ta gama aikace aikacen girkin asuba yake tambayar ta akan kankara da kunu


"Yanzun don zanyi aikin lada saina fad'a maka yayan khadija watan azumi ne fa" 


Allah ya karbi ibadun mu


"Ameen, FATAN MU(next novel)kenan insha Allah"


Ta bangaren kamila Alhamdulilah jiki yayi sauki sosai harma an sallame ta sai dai fa fatar hannu kam ba kamar nada ba 

Yau dai gidan kawarta ta nufa

Assalamu Alaikum

Wa'alaikumu salam wanake gani anan koh dai idanuna ne kemin gezo lallai kamila duniya ashe ana iyya tunawa damu 


Ke matsalar ki kenan Harira daga mutum yazo gunki koh wajen zama baki bani ba kin kama mini korafi


Ai dole na miki kamila tun auren ki na sake saki a idanu na? koh wayarki na daina samu sai dai inji a gari kinzo kin koma yar buru uba har zaki ce ban baki mazauni ba


Yanzun dai kiyi hakuri ki zauna wata magana ce ta kawo ni


Aikam sai ta kawo ki badai kika kawo kanki ba 


Kee habba don Allah jarabar ta isa haka 


Naji meke tafe dake kamila


Yauwa zancen dai na muhammad ne


Wani muhammad in?


Ki jiki da wani banzan tambaya muhammad nawa nake dashine wai


Nidai nasan tsohon mijinki dai ba muhammad bane 


MAKAHO...


Kwal uba yanzun kuma tsohon zuma aka koma


Ai daman tafi magani, ke Harira kinsan meya kashe min aure?


Ah ah 


Toh rashin biyamin bukata ne bayayi, don bana gamsuwa shiyasa na kashe aure na don ni yanzun duniya kaf  in dai zan samu namiji gwarzo ba ruwa na da talauci koh kyau kin gannin nan don nabisu banga da kyau ba


Amma ke dai kamila akwai shirme kece miki akai shi Al'ameen in jarabebbe ne kamar ki?


Hhh habba Harira ido fa ba mudu bane amma yasan kema 


Hhhh shegiya ta faso gari, ta karasa maganar da bawa kamila hannu suka tafa, toh yanzun me kike so ayi ne 


Yauwa MAKAHO fa aure yayi kuma wata yar iska ya aura family shugaba


😳shugaba fa kikace?


Eh nima nayi mamaki auren nan yar iska in kika ganta sai gaban ki ya fad'i tsabar kyau


Kema dai kamila aikin san zuriyan gidan daman kyawawane sai dai na wani yafi na wani


Gaskiya ne in gaya miki wai dana gama bibiyar muhammad na tataro kome nasa na samu cikeken bayani akansu shinefa naje da sunan koyan kwalliya wajen ta yar iska kinga duka da suka mini karshe ma acid inda zani makaranta dashi zamu shiga lab zuciya ya ebeni na d'auko zan watsa ma yar banza kawai in gaya miki abin mamaki muhammad ya zabi matar sa akaina da kansa ya hankad'a ni har acid ya zube a hannuna, ta karasa maganar da nunawa Harira hannun


Cap  wani mataki Dad ya d'auka akansa?


Ai ban fad'a masa gaskiya ba cewa nayi ita ta zuba mini


Aiko kinyi wauta 


Ai ma abin ba inda yaje don  bata kamu ba


Kema ai kinsan bazata kamun ba, yanzun dai me kike so ayi


Yauwa Harira wajen malaman nan naki nake so ki kaini akan maganar nan


Hhhh yar iska ba kullum fad'a kike mini akan malamai ba angaya miki ana zama hakane ai kikace zaki zauna haka toh bone ya sameki


Gaskiya kam don akansa babu abinda bazan aikata ba ke so nake inga koh kaunar ganin sumayya baya so yaji kaf duniya ba wanda yaki jini irin ta,  ba wanda yake so irina


Shegiya ba kome tashima kiga bara na d'auko mayafi muyi gaba kinsan har kauyen mutum biyu ne in bamu tafi yanzun ba sai kuma gobe saboda hanya ba kyau ga dare


Amma harira haka zaki tafi naga mai gidan baya nan gashi yara daga su sai yar aiki


Kee waya gaya miki sai na jira sa ai wallahi sai abinda nace 


Uhmm kai nima fa za'ayi tafiyar nan naku dani


Amma dai kin taho da kudi kam koh ?


Karkiji kome akwai kudi akwai mota sai ki tukamu tunda ke kika san hanya


Ok muje


  haka kamila da Harira suka d'auki hanyar mutum biyu wajen boka a watan azumi koh tsoron Allah babu


Sai la'asar suka isa cikin mutum biyu dole tasa suka faka motar su a bakin titi suka hau machine mai kafa biyu zuwa ciki cikin kauyen bayan sun iso ma sai da suka tsallake ruwa


Wani dutse ne baki kiren hayaki na fita akai tunda suka nufo wajen wani irin wari ne yake bugan hancin su da sauri kamila ta tushe hancin ta 


Cikin gaggawa Harira ta buge hannun,  kamila ke kamila ki rufa mana asiri kar muje ciki a haka kin tushe hanci wani irin iskanci ne wannan?


Amma Harira baki jin wari da doyi na tashi ne?


Ina ji amma rufe hancin ki daidai yake da rasa aikin ki 


Kamar ya?


Kamar haka tace tana kama hannun ta su koma baya


Ke Harira menene haka?


Bakin ce baki gane ba shine zan ganar dake


Yi hakuri muje


Haka suka nufi cikin kokon kamila kamar zata  mutu tsabar wari ai bata gama ganin tashin hankali ba sai data shiga kokon taga tashin hankali mutum ne a zaune kamar an sassaka sa jikinsa duk kuraje sunyi ruwa sun cika sai doyi yake dagashe sai fata kawai ya d'aura a Gabansa ga gashin kansa sa tsitsige kamar shaid'an gashi jikin kokon kadangaru ne sunfi dubu a mamman ne koh ta ina bazama kaga jikin kokon ba tsabar yawansu gasu a shure waje d'aya


Kai ku dakata ku dakata nace,  yafad'a da muryarsa mai amoi gata  muryar yar irin jarirai cikin tsawa yayi maganar 


Sosai kamila ta razana da gudu tayi hanyar fita 


Karki kuskura ki fita a nan ba tare da an gama da bukatun ki ba Tabbas zaki sami Muhammad MAKAHO.......


Aijin ya ambace zata samu muhammad yasa ta dawo da sauri jiki na rawa ta tsunguna kamar yanda Harira tayi 


Kallon ta bokan yayi sannan ya rufe idonsa yana wani irin magan ganun tsibbo na d'an wani lokaci kafun ya bude idanunsa kallon cikin kwaryar yayi nad'an wani lokaci kafun ya d'aga ido yana kallon kamila


Tabbas zaki samu muhammad amma fa rabasu da sumayya babban Had'ari ne saboda kaddarar su a manne take dana juna akwai makiya sama dake idanunsu kullum na kansu sannan asirin dake yawo akansu yafi wanda kike so a saka musu Amma akwai mafita d'aya


Jiki na rawa kamila tace kamar ya kenan Allah gafarta malam


Wani irin  tsawa ya daka mata,  keee ba'a kira mana Allah Anan kinsan akwai sane kika zo neman biyan bukata wajen mu(Wa iyyazubillah)


Tuba take na kan dutse sabuwa ce Amata afuwa


Ammata Harira amma ta kiyaye nan bama son shirme


Zan...z..nkiyaye..takara sa maganar cikin tsoro harga Allah mutumin razana ta yake


Yanzun ana tsaka da ibadan watan Azumi kuma sun tsaya dakyau wajen ibadah basu bada wani kofa da Za'a kawo musu farmaki ba sai dai akwai dama,  nan da sati biyu zata Fara jini mundin tayi sake da ibadah zamu farmata 


Kamar ya malam?kamila ta tambaye sa


Ranan juma'a 17 ga azumi da misalin karfe 1 na rana zata fara jini a lokacin zuwa kwana biyar kina da daman da maganin zai cita mundin tayi sakaci da ibadan da suke yanzun


Ok toh malam ni yanzun wani mataki koh ince wani aiki d'aya za'a mini


Akaf asirin da za'a musu don ganin yakita,  bazaici ba don an musu bakin asiri na zama tare da juna abu d'aya zan miki shine Ama sumayya kurciya tabar kasan gabaki d'aya ta manta da NIGERIA a rayuwar ta kwata kwata da rayuwar da tayi a ciki, 

Wannan damar xaki samu na auren muhammad, duk da hakan zai batawa wasu shirin su da suka dade sunayi


Na Amince wallahi na yarda ayi mata koma menene


Shikenan zaki kawo bakar tinkiya da jan tatabara sai rakuma biyar masu ciki


Malam ina zan samu wa'innan abubuwan sai dai in b

Da hali na bada kudin sai a nema asaya


Ba damuwa ki kawo


Nawa ne?


Bama yanke kudi biya kawai ake 


Kudi kamila ta basa kusan 500k 


Kije ki dawo gobe in mun had'a aiki sai kizo ki karba


Toh mungode 


Fita sukayi da Harira sosai taji dadin jin za'a mata maganin yar iska 


**************

Sosai sumayya da Al'ameen suka dage da ibada sallan dare ga sadaka duk yamma sai sumayya tayi kunu da kankara shi kuma muhammad yayi sadakar lemo ma Almajirai koh dabino


Khadija kam haryau basu kara haduwa da Ammar ba bata kuma san shiya bude ma yayanta shago ba taci gana da zuwa makaranta har azumi yakai 17  sumayya batayi sakaci da ibada ba kwanciya da Alwala in Muhammad ya tashi da dadare yana tada ta itama ta zauna tana lazimi sosai suke ibada Awatan koh bacci yanzun basu da lokacin sa sai bayan asuba


Ta bagaren kamila sun koma wajen boka washe gari a idanunsu ya kamo wata katuwar mujiya ya fade mata ciki layoyin da ya rubuta sunan sumayya ya saka ma mujiyar a cikin da Allura da zare yasaka ya dinke cikinta ya baiwa kamila tayi ta kula da ita a keji ta mata jinya nan da kwana 16 ranan da sumayya zata fara Al'ada kenan kuma ana son karta sake azumi daga ranan sai randa sumayya ta fara Jini saita saketa da tsakar dare tana mai Ambaton sunan sumayyar kafun gobe da safe zataji kyakkyawar lbr 


Duk da kamila na tsoron mujiya Amma dayake shaid'an ya buga mata ganga haka ta cici  a kwando tayi jalingo


Yau aka kai azumi 20 a daren ranan sumayya ta samu tsarki bayan isha'i tayi wanka


Al'ameen kam bayan ya dawo daga Ashan kwanciyan sa yayi don yau Tahajjud zasu shiyasa yake son kwantawa da wuri


Sumayya kam abincin asuba tayi sai kusan 9:39  ta kwanta 


Da misalin karfe 12:10 Al'ameen ya farka  Tada sumayya yayi sukayi Alwala kaya suka chanja daga na bacci zuwa  jallabiya ita kuma tasa dogon riga sai hijab sallaya ya d'auka suka rufe kofar suka fita


Gidan goggo suka wuce don khadija tayi ta rokon su zata bisu itama bayan sun isa sumayya ce ta shiga gidan da sallama jin shuru yasa ta buga kofar d'akin khadija 


tashe tayi Itama Alwalan tayi suka fita a gidan


Haka su uku suka kama hanya koh ina ka wuce group group ne na Al'umma musulmai suna tafiya manyan masallatai kamar rana ne ba dare ba


Sumayya da khadija da Al'ameen da kafa suka taka har macilin babban masallacin juma'a na Dr Ibrahim jalo jalingo 


Sai 3 aka tashi Ana fifita a masallacin,  ture ture tsabar yawan jama'a cunkoson ne yaraba sumayya da khadija 


Bayan khadija ta fitoh daker  tsaya tayi tana dube duben sumayya Amma bata ganta ba A haka ta fitoh bakin SINTALI GIOBAL ta tsaya saiga yayan ta don daman sunyi agun zasu hadu in An tashi 


Bayan isarsa da mamaki jin muryar khadija kad'ai banda sumayya ya tambaye ta,  ke khadija ina Aunty taki?


Wallahi yaya banganta ba tunda muka..............


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 08146017245  *hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata  na maman haidar*

*Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah* 


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


 *1 Gumbar kankana da ayu* 🍀🍀

2 *Gumbar ayu zallah* 🍀🍀

3 *Gumbar Madara da kwakwa*🍀🍀

4 *Kaza mekwai* 🍀🍀

5 *Zabo me zuma*🍀🍀

6 *Kaza me allurai🍀🍀 sahihiyar mallaka ba boka ba malam*🍀🍀

7 *Kwallin idonka inadona*🍀🍀🍀

8 *Tauwadar mata*🍀🍀🍀

9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*

10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice  gwada wnnn*

11 *Maganin nono. Sahihi* 

12 *Maganin hips and bobbs* 

13 *hodar. Ni I'ma koramar mata*

14 *nakasan Mara babban sirri*

15 *kafi jijjibi*

16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*

17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata* 

18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai  Babu magana*


 

 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

*Maman haidar Bata tsaya anan ba*

*takawomuku hadaddan sabulun  gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata  gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo  kudai kunemeta awannan number*   08146017245

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧 


No comments