Matar makaho 52-53

   



 Page5⃣2⃣&5⃣3⃣



Malamai  zan shiga,  ke koh yawo tsirara zanyi don naga bayan sumayya sai nayi


Amma dai kamila baki da imani habba don Allah kin wulakanta bawan Allah ya fita a Rayuwan ki sannan yanzun kice zaki wargaxa masa farin ciki ai wannan baso bane


Wace farin cikin bayan nice farin cikin sa har gobe ina da gurbi a zuciyar sa


Hhh hayya lallai kamila kina da gurbi a zuciyarsa ya hankad'aki akan matar sa koh an gaya miki so na dauwa mane a zuciya? duk mai sonka muddin baka kyautata masa toh fa kamar fure ka shuka baka ban ruwa tum tana bushewa aje aje wata rana zata mutu


Kee sadika na fahimci daman ke yar hassada ce shiyasa kwata kwata tafiyyar mu bata kyau dake


Nidai gaskiya nake fad'a miki kamila kuma gaskiya d'aya ce da wannan haukar ai gwara kije garesa da soyayya koh xai dawo ku daidai ta kinga sai ayi na biyu dake


Ina ma yake fita kullun yana gida,  naje inda akace min yana bude sana'a ma naje Amma shuru bantaba ganin sa ba, kuma ni nafi karfin kishi da sumayya sai dai ta fita tabar min shi


iii in kamila karkije kikai kanki a mahallaka wallahi wani rabon kashe ki zaiyi


Ya kashe ni mana indai akan Al'ameen ne kowa ma ya mutu


Wallahi badai kowa ba,  nidai mai sonki ce zan fad'a miki gaskiya koh kinki koh kinso rabuwa da bayin Allah nan shiyafi miki mutunci Akasinsa kuma bismillah zaki ga.



Bakin ki ya sari d'anyen kashi ba abinda zan gani  sai Alkhari


Ai baki neme Alkharin ba mutumin da keson kashe Auren wasu shine zaiga Alkhari?tace tana

Mikewa tayi ba tare da tajira Amsar kamila ba tayi mata sallama ta fita a asibitin



Sumayya na shiga cikin gidan kofar su ta wuce da mamaki take kallon kadija dake zaune tana rusa kuka"ke khadija lfy"?


Da gudu ta tashi zuwa wajen sumayya rungume ta tayi tana kuka'Aunty ina yaya? ina dawowa daga makaramta ake ce mini wai an tafi dake da yaya,.


"Babu inda akaje damu khadija yayan ki na waje shine  kika kama kuka koh uniform baki cire ba kika zauna haka"


Toh ni Aunty fisabililah yazanyi na cire uniform yayana da Aunty na na station


"Toh gani na dawo ki ibi ruwa kiyi wanka na baki kaya kisa dai dai yayan naki ya shigo"


Toh kawai tace tana d'aukar boket,  wanka tayi sumayya ta bata kayanta ta saka abincin da suka girka na karyawa daba su ciba shi ta ibawa khadija


Khadija na cikin cin abinci sai gashi ya shigo da sallama


Amsa wa khadija tayi hade da gaidashi, yaya  sannu da zuwa


Yauwa khadija ya makarantar


Lafiya yau subject 6 aka mana a rana d'aya Assignment biyu


Masha Allah ki gama ci sai muyi assignment in



Hhh yaya ka iyya ne?


Toh khadija ba nayi secondary ba koh azatan ki duk abinda na koya ya gudu ne?


Yi hakuri yayana


D'akin ya shiga sumayya kam daman tana kitchen


Bayan khadija taci abinci wanke uniform nata tayi ta shanya,school back nata ta d'auko ta bude Assingment ne aka busu na physics sai English,  yaya na gama inzo muyi Assingment in?


Bara na fitoh khadija, 


Toh yaya


Fitowa yayi suka zauna a dakali sumayya na kallon sa yana ma khadija bayanin assingment in  yanda zata fahimta sannan yana fad'a mata Amsa tana rubutawa


Bayan sun kammala gida khadija ta tafi tabar uniform nata a shanye, mikewa yayi ya ibi ruwan wanka ya shiga yana fita yayi Alwala ya wuce masjid


Bayan fitarsa  da ido sumayya ta bisa haka kawai yau taji tana jin shakkarsa sosai abinci ta juye a kula takai d'aki tayi sallah sanin baya dawowa sai bayan isha yasa tayin wanka d'akin ta shiga zani fille da T-shirt ta saka sai hulan bacci. TV ta kunna tana kallo gabaki d'aya yau ta rasa nutsuwar ta gabaki d'aya zuciyarta cike yake da tsoro


Bayan ya dawo sallah abinci ta gabatar masa baiyi magana ba kawai ya zauna ya fara ci 


Itakam taji ba dadi koh fad'ane ya mata akan wannnan shariyan ba karamin damunta yake ba 


Bayan sun kammala cin abincin wanke baki sukayi,  Al'ameen kwanciya yayi a gadon yayi shuru baice mata kome ba


Sumayya dake kwance a gefensa hawaye ne ya cika a idanunta itakam ta shigesu da mutumin nan


Sunfi, minutes 30 a haka baice kome ba itama batayi magana ba Amma kowa yasan d'an uwansa baiyi bacci ba


A hankali sumayya ta matso garesa kwanciya tayi a gabansa sosai ta shige jikinsa


Al'ameen yana jinta kala baice mata na shuru kawai yayi don so yake ya  mata horo ta ruwan sanyi yanda gobe baza tayi

Abinda bayaso ba.


Hannu tasa a hankali ta na cire botur in shirt insa nan ma baiyi magana ba 


"Ni da wannan fushin ai gwara duka da wannan shariyan"


Kala baice mata ba sai kama hannunta dayayi wanda ke yawo a jikinsa 


"Dan Allah ka kulani"


Kinsan Allah sumayya in baki rabu dani ba sai na sauka a gadon na koma kan kujera habba Ana dole ne?


"Kayi hakuri bazan kara bafa"


Sauka yayi niyar yi da sauri ta riko sa hade dasa ihu"wallahi nidai ban yarda ba kayi hakuri toh na tuba"


Fasa saukar yayi ya koma ya kwanta itama kwanciyar tayi a gabansa sosai ta mannu a jikinsa


Haka suka kwana tsakanin su babu shiri sumayya dai na makale da muhammad duk yanda yaso cireta a jikinsa taki


Washe gari haka suka tashi salam  Al'ameen yasha mata mur sosai duk yanda tad'au abin da sauki abu fa ya wuce nan don da gaske muhammad yake


Bayan sun karya ta d'aga ido tana kallon sa"yayan khadija"


Na'am


"Daman maganar make-up inda zan ma yar kanwar Deputy ne saboda tsaro bazasu iyya zuwa ba shine wai naje na musu a gida har kwana biyar ana biki"


Saikin dawo kawai yace yana fita a d'akin


Sosai shariyan Al'ameen ya damu sumayya, haka dai ta lallaba ta shirya tad'au hijab  nata ta saka rufe kofar tayi ta fita.


Bakin titi ta tsaya idonta ya sauka a kan Al'ameen ne zaune a bakin masallaci kusa da masu bara suna hira dasu, kara sowa tayi inda suke bakin ta d'auke da sallama, "Assalamu Alaikum"


Mutanen bakin masallacin gabaki d'aya suka zubawa sumayya ido suna mamakin ina zata, wa'alaikumu salam su Al'ameen suka had'a baki wajen Amsawa shikam cike da mamaki meya kawo sumayya gunsa bayam tace gidan deputy zata, tashi yayi ya matsa gefe


Binsa sumayya tayi  inda ya tsayan ba mutane, itama tsayawar tayi batace kome ba


Lafiya?


"Lafiyar kenan koh laifine in nazo wajen ka"?


Babu laifi...


"so nake ka rakani"


Rakaki ina?da mamaki a fuskar sa 


"Gidan da zanin mana"


Hala baki  gani ne?


"Ah ah ina gani so nake ka rakani"


Bazani ba, yace yana tafiya


Ai da sauri sumayya ta riko rigansa 


Keee menene haka? koh baki ganin a gaban mutane muke ne


"Toh sai me in a gaban mutane muke koh ba mijina na rike ba kuma wallahi in baka shige mun tafi ba saina rungume ka a gabansu"


Uhmm Allah ya kyauta shige mu tafi



Mutumin da ke saida ruwa kusa dasu Al'ameen ne ya dubi abokin sa, Kai Amma yariyar nan bata da kunya har masallaci zatabi miji bata maji kunyar idon mu ba muna zaune? wama yasan dalilin da yasa aka aura masa yarinya kamar  wannan?


Gaskiya ne haruna daga gani idon yarinyar a tsatsaye yake..



Haka sumayya tasa muhammand a gaba har gidan kanwar deputy har falon baki aka kai Al'ameen aka had'asa da abin motsa baki sumayya kuma ta shiga falon matan gidan


Har yamma suna gidan sallah kawai ke d'aga Al'ameen yaje yayi ya dawo  


Sai kusan 5:43 na yamma suka fitoh gida  gaskiya sumayya ta yaba da karamcin y'an gidan don Take Away na abubuwan da aka shirya  na biki aka iba mata" yanzun ina zamu"?


Sama jannati zamu, Al'ameen ya bata Amsa


"Ni kake fad'awa bakar magana"?


Eh an fad'a in ai nafi mai Ashar kuma bakar ma agunki na koya


"Badai aguna ba kuma in kayi tsiya saina gudu na barka ka bata"


Kanki kika ma Asara bani ba.


"Akan me xan ma kaina asara kuma"?


Aikan mijin da kike dambe mana


"Dambe ni banyi dambe akanka ba"


Au habba daman tabaryar ta burgane?


"Ai na razana tane, karka wani zata fad'a nake akanka"


Na nawa kuma.


"Allah ba wani"


Ke kika sabi dai mutum sai taurin kai


"Kamar kai"


Shuru ya mata don ya fahimci sumayya inya biye mata fuskar da ya d'aure bazai san lokacin da zai sake ba.


Keke suka hau suna isa gida ana kiran mangari ba masalaci ya shiga ita kuma ta wuce cikin gida


Bayan ya dawo sallah take Away in ta bude musu donut da kaza rabi sai drinks d'ayan take away in kuma fried rice ne da lafiyayyen naman shanu suna kammala ci, muhammad kam kwanciyan sa yayi


Sumayya TV ta kunna ta koma ta kwanta tana kallo a kwance"yayan khadija"ta kirasa tana kallonsa ganin ya natsu waje d'aya yana tunani, jin bai Amsa ba yasa ta dafa kafad'an sa


Da sauri yace Am Ammar kudin nan basuyi yawa ba, sai kuma da sauri ya fara kame kame don sam subutar baki ne abinda ke zuci shiya fitoh fili


"Wani kudi kuma Waye Ammar"?


Am ba kome.


Akan me zakace ba kome duk kabi kasa kanka a damuwa in ma bashi ake binka bazaka fad'amin na biya ba duk kudin da nake tarawa Wallahi tatali nake maka naga kudin yayi yawa sosai kafun na baka ka kama sana'a mai d'an kauri mu samu murufawa kan mu asiri, amma ina dalili ina dana rufin asiri kabar kanka a rikici"


Ba haka bane sumayya ba'a rikici zansa kaina ba wannan magana ne daban.


"Wace magana kenan?koh bankai naji damuwar kaba"?


Daman Ammar ne ya mini magana jiya zai bani jari dubu d'ari uku na kama shago kafun azumi tunda saura sati biyu ne ga kayan marmari a azumi akwai kasuwa.


"Bazai yuba wani ma Ammar inne d'aya? akan me zaice zai baka kudi tun da baisan zai Taimake kaba sai yanzun"


Sumayya bamu fa dade dashi ba kuma insha Allah ba abinda zai faru


"Gaskiya ban Amince ba ka bari inna gama had'a kudin saina baka kabar masa nasa"


Gaskiya sumayya gwara na karbi nasan kawai na gwada kasuwar tunda ba kyauta yace ba koh bashi saina tambaye sa in kyauta ne ni karan kaina bazan Amince ba Amma in bashine saina karba ke kuma saiki tara kudin ki wata rana zai mini Amfani.


"Yanzun ka zabi karban nasa akan nawa kenan"?


Ni bance ba Amma dai gwara nasan akan bashin tsakanin mata da mijin nan bana sha'awarsa sai in ya  zama dole


"toh ce maka akai bashi nace ne"?


Koma dai yayane kiyi hakuri bazan iyya karba ba


Sumayya juyawa kawai tayi ta kwanta bata kara magana ba  a hankali yasa hannu ya d'agota  kwantar da ita yayi a jikinsa cikin sanyi yake mata magana, don Allah badon niba sumayya ki daina Ashar koh don yaranda zamu haife su tashi da kalami mai kyau a baki banji dadin abinda ya faru ba koh kad'an yau ace anzo an d'auki matata a motar yan sanda wannan ba mutuncin matar aure bane sai in ya zamo mata dole


" insha Allah bazan sake ba"ta karasa maganar da kara kwanciya a jikinsa


Allah yasa...


"Ameen" shuru sukayi dukansu biyu ba wanda ya kara magana a hankali Al'ameen yasa hannu ya yaye hijab da sumayya tasa don yau sanyi ake sosai


"Sanyi fa nake ji"


Nima ai sanyin nakeji kinga nasa abune?


"Ai kai daban ni daban"


Nida ban,  inji wa?


"Sumayya"


Uhmm muyi bacci


"Banaji"


Saboda?


"Sanyi "


Uhmm toh bara na rufeki sai kibar jin sanyin, yana maganar yana hawa kanta


Saboda sabo da hakam yasa bai dame sumayya ba baccin ta kawai ta kamayi bata san ma yaushe yayi nasa ba 



Washe gari Ammar yazo Akan maganar su Al'ameen ya Amince, Tare da tambayar Ammar kyautane koh bashi kai tsaye Ammar yace bashine don ya fahimci muhammand kalansa daban ne mutum ne wanda baison banza damuwar sa kawai ya nemi na kansa


Cikin sati d'aya Ammar ya sama ma muhammad shago mai kyau ta tsallaken first bank kaya ya cika masa makil a shago kama daga mazar kwaila dabino kayan marmari ba wanda babu su dangin Apply duk ba'a barsu a baya ba,yaune Aka kammala had'a shagon kai masha Allah shago kam saidai makiya suji haushi



Muhammad Anya zaka iyya kasuwancin nan babu yaro a kusa dakai kaga yanzun shagon nan babba ne idanun barayi zai sauka akai bare an ganka baka da ido za'a iyya baka d'ari ace dubune, Amma in kana da yaron daka Aminta dashi mai hankali a Unguwan naku sai yazo ku zauna tare kana d'an basa nasa ladan sai inga kamar zaifi?


Gaskiya ne Ammar daman Akwai wani yaro shagari d'an wani makwancin mune daya rasu toh yaron ba boko ba Arabic tunda iyayen sa suka mutu dai abin sai a hankali ba kula dashi ake ba saina d'auko sa yazo mu zauna tare


Amma muhammad yaro irin wannan da ba boko ba arabic bazai cutar dakai ba kasan fa halin yaran yanzun?


Ba kome insha Allah bokon ma iyya secondary ya tsaya arabic in tunda iyayen sa suka rasu ya daina zuwa saboda rashin mafad'i Amma najashi a jiki kaga inda rabo sai kaga Allah ya dad'a nitsar dashi


Haka ne kam sai kaje wajen bappan nasa kuyi magana saika d'auki yaron


Insha Allah Ammar nagode Allah ya tsaka maka da Alkhari ya bani ikon biyan abinda ka bani


Ameen,  ni bara na wuce Allah ya kawo kasuwa 


Ameen, Al'ameen yace yana rufe shagon gida ya nnfa fuskar nan a washe


Bayan ya shigo gidan da sallama lokacin sumayya nama wasu lalle


Amsa masa tayi tana kallon sa ganin sai murmushi yake"yayan khadija lfy"?


Lafiya kun gama lallen ne ?


"Saura hannu d'aya meya faru"?


Babu kome ki gama dai sai muje ki gani


Toh sumayya tace da sauri sauri ta kammala musu don ta kagu taji menene" na gama muje"


Kiye wanka dai kisa kaya da hijab amma daga gama lalle sai fita


"Nidai gaskiya Ah Ah muje inna dawo zanyi"


Hannunta kawai ya kama har ban d'aki ya fitoh ruwa ya iba ya kai mata, kiyi wanka malama


Ba yanda sumayya ta iyya haka tayi wanka ta shirya ya saka ta agaba har shagon sa sosai sumayya tayi mamakin girman shagon da abubuwan da aka zuba masa gwanin sha'awa kai gaskiya "masha Allah waje yayi waje"


Gaskiya ne nima ina ji wajen ba karamin kyau zaiyi ba 


"Ya mayi Amma dai ya kamata kane mi abokin zama saboda tsaro"


Eh munyi magana da Ammar,  gidan su shagari zani koh xa'a amince ya tayani zaman shago


"Gaskiya ne hakan yayi kyau sosai wallahi Allah ya kawo kasuwa"


Ameen, muje ki rakani gidan su shagari


"Toh"sumayya tace tare suka tafi gidan su shagari kuma Alhamdulilah  sun Amince


Cikin sati d'aya ba karamin mamaki yan sintali sukayi ba ganin muhammad da babban shago gashi bai fad'awa kowa kome ba inka tambaye sama sai yace Allah ne ya rufa masa Asiri yayi shuru , sosai yake cefene yanzun kome na gidan sa ya d'aukewa sumayya duk yanda taso hanata yake gashi Allah yasawa abin Albarka Arana d'aya yana cinikin dubu goma gashi Shagari ya kaisa wajen wani mai kayan marmari ya had'asu da dilan yan gembu yanzun masa ordern kaya ake daga gona sai dai kawai ya tura shagari tasha in kaya ya sauka a d'auko masa.


yanzun kam Alhamdulilah sumayya kudi na shigo mata wallahi kowa ya ganta zai zaci daki Ac falo Ac mota AC  office Ac ne tsabar yanda ta dawo tayi kyau tayi fresh sosai har wani yellow yellow tayi yanzun koh tunanin gidan su batayi ita karan kanta tana mamakin yanda take mantawa akwai abie A duniya, wata rana har mamakin kanta take saitaji kamar ta kirasa sai kuma ta fasa


hatta shi muhammad yanzun in ka gansa zaka san kwanciyar hankali ya samu matsunguni.


 ga suturu masu kyau yanzun shima da kudin sa yake sayan kaya ya saka duk ya watsar da tarkacen kayansa hatta khadija yanzun daban ta koma kamar ba khadija ba gata ba yaya ba,  ba Aunty ba


Yaune aka ga watan Ramadan gobe  za'a tashi da azumi sumayya yau da khadija kasuwa suka shiga sosai sumayya ta musu sayayyan azumi kome buhu buhu katon katon ga kaji ka kifi, vegetables daman bata da matsalan fruit

bayan sun dawo kasuwa kowa ka gani fuskar sa a washe Adalilin gobe azumi 


Bayan isha muhammad ne da sumayya suke cin abinci a waje,  zazaune suke akan taburma don yanzun sumayya ta saya 


Assalamu Alaikum


"Wa'alaikumu salam"muhammad da sumayya suka Amsa " sannun ki da zuwa sumayya tace tana tashi,  ta d'aukowa bakuwar kujera don a tunanin ta koh customer ne


Ah ah ba zama nazo ba magana zanyi dake


Ni kuma?sumayya ta maimaita


Eh ke dai,  ina dai kice sumayya Abdulsalam shugaba?


Eh nice


Nazone na shaida miki koh na gargade ki Akan i................



 


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 08146017245  *hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata  na maman haidar*

*Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah* 


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


 *1 Gumbar kankana da ayu* 🍀🍀

2 *Gumbar ayu zallah* 🍀🍀

3 *Gumbar Madara da kwakwa*🍀🍀

4 *Kaza mekwai* 🍀🍀

5 *Zabo me zuma*🍀🍀

6 *Kaza me allurai🍀🍀 sahihiyar mallaka ba boka ba malam*🍀🍀

7 *Kwallin idonka inadona*🍀🍀🍀

8 *Tauwadar mata*🍀🍀🍀

9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*

10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice  gwada wnnn*

11 *Maganin nono. Sahihi* 

12 *Maganin hips and bobbs* 

13 *hodar. Ni I'ma koramar mata*

14 *nakasan Mara babban sirri*

15 *kafi jijjibi*

16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*

17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata* 

18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai  Babu magana*


 

 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

*Maman haidar Bata tsaya anan ba*

*takawomuku hadaddan sabulun  gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata  gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo  kudai kunemeta awannan number*   08146017245

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧                       


No comments