Matar makaho 50-51

 


Page5⃣0⃣&5⃣1⃣




Lafiya daman nazo akan maganar make-up inne,  naji shuru baki kirani ba inna kira ba'a picking call in.


"Ok toh ai na zaci koh kina da fahimta ne, ki gane me nake nufi"


Kamar ya sumayya ban gane ba?


"Ok toh kamila bara na miki gwari gwari, bazan koyar ba"


Akan me? bayan kince sai mijinki ya yarda kuma a gabanki yace ya Amince.


"Eh ya amince nima haka yace mini sai dai ni ban Amince dake ba har kizo gidana kina kare mini tanadi"


Kamar ya bangane ba me kike nufi?zanzo gidan ki in kare miki tanadi?ina ma gidan yake bare


"Hhhhh hayyeeee nanayeeee ashe gidan ba yanda yake akazo cin moriyan masu shi"


Ke sumayya nafiki rashin mutunci don naga baki dashi ya daga abin Arziki sai tsiya ya biyo baya matsalanka da matsiyaci kenan bai gaji arziki ba



"Ehhhhhh yariya tsiyama waje ya samu ki kalleni da kyau daga ni har mijina kinga Alamun yunwa a tare damu, kuma ki kallen sama da kasa koh uwar ubanki bataci arzikin da naci ba harta mutu ke uwarki data aure ubanki har yanzun bataci arzikin danake ciba.


A'uzu sumayya wani rin , zagine haka kar in sake jin kin tanka mata shige ki wuce d'aki, don Allah kamila kiyi hakuri


Kutt ni kike xagi? ai kamila super tayi da jakarta tayo kan sumayya da mugun sauri 


"Sumayya da gudu tayi kitchen tabarya ta rarumo ta rike"don uwarki kizo yau saina rusa miki kai shegeya harni zakima bariki kizo mini da yaudara da sunan koyan kwalliya"


Ai da sauri kamila taja birki, in ba tsoro ba ki aje abinda ke hannunki yau saina nuna miki true colour na. 



"Shegeya akan me zan aje nasan dame kikazo kizo kima mijina asara a banza "


Shammatar sumayya kamila tayi tana magana,  da sauri tayi kanta gadan gadan da kwalba a hannu


Ai ji kawai tayi Al'ameeen ya hankad'ata gefe, don duk abinda suke hankalinsa na kansu, keee kamila kin isa kizo har gida kice zaki bugarmin mata kimin asara akan me? Ke kin kini na samu mai zama dani shine zaki bugeta


Wayyyo nashiga uku na lalace wayyo hannu na innalilahih kun kasheni, kamila ke ihun nan tana rike da hannunta wanda Acid ya zube mata akai 


"Subahanallah daman abinda kike da niyar watsa mini kenan Algunguma shegeya, aikokin watsa min bashine yake nufin karewar auren mu ba tunda ba idone dashi ba bare yaga yanda na koma"


Sumayya meke faruwa ne haka meya sami hannun nata naji kina cewa zata zuba miki


Kamila kam ihu take kamar ranta zai fita


Ihun kamila shiya jawo da hankalin jama'ar gidan kofar su Al'ameen,  da sauri daga maza har mata yara da manya suka nufi kofar donjin ba'asi


"Ruwan Acid tayi niyar watsa mini Allah yasa ka shureta shine ya zube a hannunta hannun sai d'ayewa yake"


Subahanallah Al'ameen yace yana nufar inda kamila take, kee kamila tashi muje asibiti tashi tashi yau an bonu



Kaiii karka kuskura ka taba ta kaji na fad'a maka,  keee Kinsan su waye a gidan nan har kika iyya d'aukar Acid zaki zo ki zubawa mutum a cikin gidan Adara? kutumar  uba iro yace yana nufar kamila


Salame ce ta Lailayo Ashar ta maka, Ci ubanta dan uwarta(wa'iyyazu billah) koh dabban gidan Adara bama bari aci zalinsa bare mutum 


Ai kafun Al'ameen yace wani abu tuni iro ya fara wanke fuskar kamila da ruwan maruka ji kawai kake kauuu kauuuu kauuuu



Ihun kamila ke tashi yanda kasan ranta zai fita bugunta suke tana kokarin gudu wasu su kamo ta, Al'ameen karan kansa hankalin sa ya tashi  da kukan ta kamila keyi duk yanda yaso kwatarta abin yaci tura karshe ma salman turesa yayi saura kad'an ya fad'i sumayya ta taro sa


Jama'ar kofar gida su suka shigo gidan jin kukar mace kamar me, shigowa sukayi ganin abinda ke faruwa yasa su rugawa a guje suka kwace kamila


Ai kamila na ganin ta tsira da wani irin matsifeffen gudu ta falla waje kamar walkiya ga hannu duk ya d'aye fatar


Bayan gudun kamila suwaiba ce ta d'auki jakar kamilar, Kai Allah ya mini ga jaka mai azaban kyau maybe ma harda cash a ciki, takara sa maganar da fita a kofar 



Bayan fitar jama'a  a kofar Al'ameen rai a bace ya fara magana sumayya yanzun kin kyauta fisabilillahi daga abin arziki saiki kama zagin yarinya 


"Ok watoh laifina kake gani kenan na zagi budurwan ka koh"?


Waike sumayya meye haka duk wacece ummulkaba'isin wannan matsifar tun farko me yasa zaki zageta akan wani dalili yanzun mutuncin kine ashar koh zamanki a gidan nan ne kika koya, ni fad'a nake miki a matsayina na mijinki ba saurayin kamila ba, yana karasa maganar yayi d'aki ya barta tsayi kamar an dasa ta


Sai yanzun sumayya tayi data sanin biyewa kamila koh yaushe kamila tazo gidan saita had'ata fad'a da mijin ta ina bazai yuba, kitchen in ta shiga taci gaba da ayyukan ta, don batason basa hakuri yanzun ganin ransa ya baci sosai



Da misalin karfe 11:20 saiga yan koyan  make-up inta sunzo a waje suka zauna ta shinfid'a musu taburma suka fara training don yau kwanan su biyu da fara koyo



Jin d'uriyar jiniyar motar yan sanda sukaji ya tsaya a kofar gida, ba'a wani jima ba saiga matan yan sanda sun shigo gidan har kofar su sumayya


Sallama dai...


"Yauwa sannunku da zuwa lfy"?


Lafiya ba lau ba don duk wanda yagan mu baiga lfy ba, wacece sumayya?


"Ikon Allah nice wani abinne ya faru"?


In munje station zakiji dalili, shige muje d'ayar yar sandan tace tana kokarin kama hannun sumayya


Da sauri sumayya ta fizge hannunta tare dama police in kallon banza, babu inda zani wallahi akan me banyi kome ba Awani ce za'a tafi dani



Babu wanda zai tafimin da mata ba tare da sanin laifinta ba, Al'ameen da yafitoh d'aki da sauri yake fad'a musu haka


Kai ka iyye bakinka fa kasan a gabansu wa kake babu ruwan mu da makantar ka wallahi koya maka hankali zamuyi.


Sannu uwar sa koya masa hankali na rantse kika tabamin miji ubanki za'a taba,  station ne dai baza......


Bata karasa ba taji saukar mare tasss a fuska police in ta tsinketa dashi ai kafun ta sauke hannunta Al'ameen ya watsa mata rabonta itama duk da ba'a fuska ya saita ba amma ta maru kam 


Kutturu hukuma ka mara yau daga kai har matar taka sai munga gatan ku a jala yau innan, waya tayi wasu mazan yan sanda biyu suka shigo aka rufuwa Al'ameen da sumayya da karfin cin tuwo za'ayi waje dasu Al'ameen kam anfa kasa tafiya dashi sai kokuwa suke, yau sunga ikon Allah kama MAKAHO ya gagare su  sumayya kam an fita da ita waje bayan ta sanya hijab 


Ammar ne yayi packing mota da sauri ganin yanda jama'a suka cika kofar gidan ga sumayya an tisata a gaba cikin sassarfa ya karaso wajen yana tambayar ba'asi ganinsa da daula yasa police in saura ransa suka masa bayanin sunzo kama sumayya ne Al'ameen ya mari police


Cikin gidan Ammar ya shiga da mamaki yake kallon Al'ameen dake ta fama da police da sauri ya karaso wajen hannun Al'ameen ya kama ya rike hade da kiran sunan sa


Tsayawa da kokuwar yayi, Ammar kaine?


Eh wai meke faruwa ne,  meka musu?  


Wallahi ba musan me muka musu ba daga zuwa wai zasu tafi da sumayya na tambayi dalili wai sai munje office insu kajifa.


Gaskiya ne Al'ameen ba'a fad'awa mutum laifinsa sai a station kazo muje ba abinda zai faru mundin kaine da gaskiya 


Binsa Al'ameeen yayi police kam  sai hararan Al'ameen suke da kitsima irin dukan da zaisha a hannunsu in ya shiga cell


Alfarma Ammar ya nema a barsu sumayya su shiga motar sa inyaso sai police  shigo ciki


Bayan an isa station kenan officer ya had'asu da iyayen kamila a office insa sannan ya kalli sumayya, an kawo mana karanki  kinyi kokarin zubawa wata Acid  a fuska Allah ya kiyaye ta,  ya zube a hannu bayan haka baki barta ba kika mata duka yanzun haka tana kwance a police clinic don haka zamu rikeki anan don iyyayenta zasu kai kara kotu


Amma dai yallaboi kafun a kamata ai sai an tambaye ita sumayyar ba'asi itama aji tata jawabin sannan kamila ta kawo shaida ku kuma saiku kamata ku rufe,  Amma daga fad'a muku magana kuma sai ku rufe mutun ba bincike haka ake Hukunci?Ammar ne ke maganar yana nuna officer in


Toh kai kuma malam asuwa har zaka nuna mini abinda ya dace nayi koh kafini sanin doka ne?


Ban fika sani ba haka zalika bazan barka ka rufe baiwar Allah ba dalili ba akan me?


Kai malam dakata kasan a gaban wa kake kuwa? d'aya daga cikin police in yake Tambaya Ammar 


Koma waye ne shi,  nadai gama magana sumayya fad'a musu menene Ainahin abinda ya faru


Sumayya ba tsoro ta bayyana gaskiyar hakika nin abinda ya wanzu tsakaninsu da kamila


Kuna daiji koh asalima kamilar ce bata da gaskiya koh a hukunce wanda yazo ya sameka har cikin gidan ka kuma yajaka da fad'a kome akai masa shiya kai kansa, sannan a maganar nan ba ruwan sumayya haka zalika Al'ameen bada niya ya zubar da acid in a jikinta ba haka zalika itace take kokarin cutar masa da mata kunga kenan duka wannan abinda ya faru ba ruwan sumayya da Al'ameen duka, kuma jama'ar gidan ne suka mata basu ba ya karasa jawabin yana bin officer in da kallo



Kaima ai yanzun gashi ka yanke hukunci ba tare da bincike ba menene hujjar ka? nace wa kamila ce taje da acid in,  baban kamila ya tambayi Ammar


Ku tura d'aya daga cikin yaran ku officer aje a d'auko goran acid in Allah dai yasa sumayya baki taba bako?


"Eh yana nan ata gefen kitchen a kasa"


Ok aje a d'auko saiku saka a gwada yatsun hannun wanda aka gani  a kai wannnan ma ai hujjane koh?


Wai kai a matsayinka nawaye har zakana bamu order kai waye?


Hannu Ammar yasa a Aljuhu ya zaro ID card nasa ya nuna 


Ai da sauri duka police inda ke wajen suka kame tare da sara masa


A gaskiya station nan yana bukatar gyara tunda bakusan aikin kuba A matsayin ku na hukuma masu kare hakkin wa'inda aka zalunta shine zaku zamo masu tauye masu rauni ku aje hujja akan masu kudi, Ammar ya karasa maganar da tsantsan bacin rai 


Don Allah sir kayi Hakuri wallahi kuskure aka samu Shiyasa kuma duba da irin rauni dake jikin ita yarinyar da aka ma dukan shiyasa muka d'auki matakin gaggawa officern  ke magana cikin magiya


Mtwss Ammar yaja tsaki hade da rufesu da fad'a sosai, muje koh muhammad, yace yana kamo hannun Al'ameen


"Ina da magana yallaboi"


Wace magana kuma sumayya bayan an kashe case, Al'ameen ya karasa maganar da kamo hannun sumayya su tafi



Ah ah Al'ameen ka barta muji meke tafe da ita.


Ah ah Ammar mu tafi kawai yafi


Sumayya yi maganar ki, Ammar yace bai saurare Al'ameen ba


"Yauwa so nake Amana iyyaka da kamila Amata iyyaka da mijina Arubuta  a ajiye don ban yarda da ita ba wanda yayi niyar zubama acid wata rana zai dabama wuka"


Keee ki iyye bakin ki yar tamu yar daba'ce? da zata daba miki wuka wallahi karki kuskura ki kara jefin yarmu  da mummunan kazafi, 


Kallon d'an sandar Ammar yayi 


Da sauri yace an gama sir, ku kuma daga yau ku jama yarku kunne karta kuskura muji koh mu gani tsakanin ta da sumayya koh muhammad


Suna Fita a station in motar sa suka hau sumayya a baya Muhammad a gaba da Ammar


Don Allah kuyi hakuri da abinda ya faru sannan ke sumayya gaskiya banji dadin abinda ya faru ba yara irinsu kamila da basusan kwaba  babu Alkhari rigima dasu .


"Gaskiya ne Ammar ni karan kaina danasan wannan fad'ar zata kai ga haka daban fara ma tanka kamila ba"


Allah ya kiyaye na gaba


"Ameen"


Al'ameen kam kala baice ba shuru ya musu fuskar nan a hade don yau sumayya ta kular dashi tunda yake police basu taba kamasa ba yau ta janyo har station ya shiga😆 kad'an ya rage bai shiga cell ba


Suna isa kofar gidan Ammar yayi packing sumayya ce ta sauka tayi cikin gida abinta


Ammar kam maida kallonsa yayi akan Al'ameen dake kokarin sauka a motar, abokina kayi hakuri don Allah kasan halin mata kuma duk da bansan ainahin abinda yake tsakanin ku da kamila ba na fahimci kishine kawai ke damun sumayya,  kuma koh wace mace iyya abinda zata kwatanta kenan


Ba kome Ammar amma wallahi naji haushi sosai yau innan gashi sumayya  harda Ashar


Hakuri zakayi sai kuma ka mata fad'a a siyasa karkace zaka d'aga jijiyoyin wuya,  mata sha'aninsu sai su


Ba kome Ammar nagode da taimakon ka gareni ashe kai police ne?


Eh muhammad


Amma babba koh naga suna baka girma


Eh, wani aiki kake ne muhammad? kullum nazo a gida nake samun ka badai bara kake bako irin yanda wasu keyi?


Ah ah ammar ina sana'a bana bara 


Sana'ar me?


Mongoro, abakin titi


Amma meyasa kullum bana ganin ka a wajen sana'ar,  inna zo?


Shuru Al'ameen yayi yanajin kamar ya fad'i  gaskiya kamar karya fad'a, a hankali yace jarin nawane ya karye don mangoro yayi Araha yanzun ba ciniki shiyasa bana fita


Toh dame kake ciyar da iyalin kuma?


Had'a fuska Al'ameen yayi jin Ammar na masa tambaya kamar ya masa sata


Kayi hakuri muhammad ina ta tambayar ka Abinda bai maka dadi ba


Ah ah ba kome,  daman ita ke kwalliya da lalle tana mana cefene da sauran abin bukata.


Gaskiya hakan bai dace ba Al'ameen ace kana namiji mace ke d'awainiya dakai ya kamata ka samu ka dogara da kanka, zan baka jari kamar na 300k  sai ka kama shagon haya tunda azumi yazo kaga zama afi ciniki kayan narmari  cikin azumi ga kankana ga lemo ga sweet milo harda dabino saika had'a, kana saidawa kaga saika kula da matar ka,  ita kuma kudin da take samu saita  kashewa kanta da kanwar taka hakan zaifi maka mutunci a wajen mace koh bata maka gori ba, koh bata nuna wani abinba Amma dai inka kasance kaike ciyar da ita kimarka daban yake a idon ta


Ammar ni......


Da sauri Ammar  ya tare numfashin sa kaje kayi shawara da matar taka yanzun dai bana son jin kome bayan kwana biyu xan dawo inji Amsar ka eh koh Ah ah kawai nake bukata. 


Shikenan nagode, Al'ameen yace yana fita a motar 


Ta bangaren kamila kam da bacin rai iyayen ta suka shigo cikin clinic in tana kwance akan gado inda kasan wance tayi Accident haka ta koma gwanin tausayi sai kawarta dake gefe a zaune 


Amma dai ke kamila bakijin bari ba saida namiki tsakani da yaron nan ba shine tsabar rashin zuciya kika ibi kafa kika tafi gidansa harda zuwa watsama matar sa acid kamila?


Nifa mama wallahi bani bace itace ta d'auko zata watsa mini


Uban me ya kaiki gidan ta?


Koyan kwalliya naje


Kwalliyar ubanki?dabani na haifeki ba sai ki gayamin wannan zance na d'auka yarinyar da bata jiran kanta.


Habba Rabi da wanne zataji ne da ciwon da ke cinta koh da fad'anki? babanta ya fad'a 


Fita mamar kamila tayi,

Kamila tambayar baban ta tayi ya aka kare a station


Bai boye mata kome ba ya fad'a mata, tare da fita a d'akin


Kamila tun farko saida na fad'a miki karki fara abinda bazaki iyya ba matar Al'ameen ba wawuya bace kamar yanda kike zatoh mace mai shikara 26 koh 25 kema kinsan bazaki nuna mata tawaye ba shiyasa nace kibi abin ta bayan gida.


Wani banzan kallo kamila tama kawar ta, kinsan Allah sadika sai sumayya tayi dana sanin sanin muhammad saina dasa mata bakin cikin da yafi wanda nake ciki,  muhammad kuma nawa ne tunda nayi aure nasan dadin abin kinga yanzun na gane ba kyau koh ido ne jin dadin aure ba keda kanki kinsan Al'ameen  zaije duk inda ake so, 

Don haka yanzun ma jira nake naji sauki mai gabaki d'aya zan musu.


Me kike nufi?


Uhmm ba sun mini iyyaka da su ba toh Malamai zan shi.............



🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 08146017245  *hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata  na maman haidar*

*Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah* 


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


 *1 Gumbar kankana da ayu* 🍀🍀

2 *Gumbar ayu zallah* 🍀🍀

3 *Gumbar Madara da kwakwa*🍀🍀

4 *Kaza mekwai* 🍀🍀

5 *Zabo me zuma*🍀🍀

6 *Kaza me allurai🍀🍀 sahihiyar mallaka ba boka ba malam*🍀🍀

7 *Kwallin idonka inadona*🍀🍀🍀

8 *Tauwadar mata*🍀🍀🍀

9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*

10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice  gwada wnnn*

11 *Maganin nono. Sahihi* 

12 *Maganin hips and bobbs* 

13 *hodar. Ni I'ma koramar mata*

14 *nakasan Mara babban sirri*

15 *kafi jijjibi*

16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*

17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata* 

18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai  Babu magana*


 

 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

*Maman haidar Bata tsaya anan ba*

*takawomuku hadaddan sabulun  gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata  gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo  kudai kunemeta awannan number*   08146017245

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧                    

No comments