Matar makaho 48-49

 


Page 4⃣8⃣&4⃣9⃣




Da karfi khadija ta watsar da kayan hannunta tsungunawa tayi jikinta na bari ta kama kai, gabaki d'aya ta gama sadakar wa yaukam sai Ta Allah


Cikin zafin nama da haushi mai motar ya fitoh da fad'a fad'a,kee wace irin wawuyace wai kina tafiya koh ganin gabanki bakyayi da yanzun na kadeki fa baki jawo mini matsala ba gashi yanzun kinsa na buge keke napep innan da sai dai me zan buge? nosense kawai stupid 


Khadija kam har yanzun bata dawo daidai ba ga kuma tsawar da ake buga mata, d'aga kanta tayi tana kallon mutumin don Allah kayi hakuri wallahi bangan ka bane


Da mamaki mutumin ke kallon ta sai kuma yayi murmushi,  ke bakece kanwar Al'ameen ba?


Eh.....eh..nice


Murmushi kawai yayi hade da dukawa a tsakar titin yana tattara mata kayanta,saiki taso ai inba so kike wani motar tabi ta kanki ba


Khadija kam cikin had'a fuska don sai yanzun takejin haushin zagin da ya mata, mikewa kawai tayi ta koma gefen titin 


Kizo ki shiga mota na kaiki gida?


Bazan hauba, kuma ka bani  kayana nikam.


Kinji haushine khadija?


Da mamaki take kallonsa toh a ina ya santa gashi itama tun d'azun sai tunanin inda tasan wannan fuskar take


Ke yar Kauye bar kallona 


Naki dainawa kuma miko mini kayana, ta karasa maganar da kai hannu zata karbi laidodinta


Da sauri ya kauce hade da cewa,  ke khadija  nifa yau gidan yayanki zaki kaini yau kusan wata biyu ina sintiri a sintali kowa na tambaya Al'ameen mijin sumayya sai ace ba'a gane saba yau ma Allah ne yasa zamu hadu shiyasa na biyo ta bakin kasuwa.


Aikuwa bazan nuna maka ba,  ba zagina kake ba


Yi hakuri haushi naji Shiyasa yanzun muje ki nuna mini gidan yayan naki 


Gaskiya ni yanzun gida zan koma ba gidan yaya ba sauri nake 


iyeee nace ki nunamin gidan da nafi wata biyu ina nema shine zaki wanice kina sauri


Kaga malam ni yanzun ma haka gidan na fitoh gaskiya bazan koma ba saidai nama kwatance


Toh shikenan yi mini, kuma ga kayanki karki shiga motar inkin ga dama


Oho maka dai, inka tsallaka titin nan  sai ka mike kaga lungun shan  kana shiga zakaga babban titi da yayi barade ka tambaye masu shagunan wajen,  gidan Adara za'a nuna maka saika aike yaro kofar MAKAHO 



Ok toh shikenan naji, yace yana komawa wajen mai keken biyansa yayi asaran da ya masa, ya shiga motarsa yaja 


Khadija kam da ido ta bisa ta kasa tuna inda tasan bawan Allah nan Amma tabbas akwai inda ta sansa.


**************

"Yayan khadija gaskiya nifa yau bazanyi girki ba wallahi na gaji wanka zanyi na kwanta "


Kidaiyi wanka amma banda kwanciya kinsan bakyau bacci bayan la'asar koh?


"Gaskiya ne amma dai zan d'an taba kafun goshin mangariba saika tashe ni"


In ance abu ba kyau sumayya ki gujesa don Allah kidai kwantan koh waya koh TV ki kallah Amma banda bacci kam.


"Toh shikenan akwai kudi a purse nawa anjima ka sayo mana abinci"


Ah ah zan dafa...


"Zaka dafa kuma yayan khadija, kaji mini kaudi"🤕


Nine mai kaudi?😳


"Eh man in ba kaudi ba ina kai ina girki,  salon kaje ka kone koh ka yanke ba"


Amma dai wallahi sumayya kin gama raina mini wayo me kika maidani ne wai?


"Sorry toh me zaka iyya girkawa"


Oho.....


"Yi hakuri mana wasa fa nake maka"


Ba wani, ya karasa maganar yana zama a bakin dakalin


"Banace kayi hakuri ba,  habba danejo Am heedee Am buddi Am yafannam lee"ta karasa wakar da kamo hannunsa ta nufi kitchen in dashi


Kinga sakeni nafa fasa girkin bara kiji karma ki kama mini wani waka wai ma tsaya ke bafulatana ne daman?


"Bororoje ce ba bafulatana ba, kuma girki sai kayi ehen"


Ke wai ana girkin dole ne?


"Yau sai kayi ai duk wanda yayi niyar aikin lada sayya karasa"


Toh nace na fasa koh


"Nikuma nace sai kayi" ta karasa maganar da dokarasa akan kujeran kitchen in 


Kin zama yayi inta dosana sa saiya cije"wai kai kam menene haka kasan Allah yau saikayi girkin nan"


Zama yayi ba yanda ya iyya


"Me ka iyya girkawa"?


Me kikeso na girka miki?


"Iyeee lallai ma watoh am bani zabi kenan irin ga k'wareren nan"


Eh fad'a mini me zan girka miki?


"Waken gembun jiyan nan zaka girka"


Ah ah gaskiya banda shi don nidai ban iyya ba,  don ni ba d'an gembu bane.


"Hhhhh bakar magana koh"?


Kema Aishi kika fad'amin 


"Shikenan yanzun me ka iyya dafawa maganar gaskiya nafa gaji da tsayuwa kwanciya nake son nayi fa"


Doya na iyya soyawa da indomie, kwai, harda taliya dafa duka sai Tie


"Doya Da k'wai ka iyya soyawa ko daban daban"?


Soyayyen doya,kwai ma soyawa na iyya, da dafawa


"Ok sai ka soya mana doyan da salt daban saika soya kwai shima daban akwai yaji a roba ka hada mana da ruwan bunu"


Sannu hajiya,😒 yace yana kokarin lalubar bojuwa(tukunya)


"Waye hajiyan kadaiji dashi"bojuwan sumayya ta wanke ta d'aura akan hot plate tasa masa mai Amma bata kunna ba Albasa ta yanka a ciki, doya ta d'auko da kwai tarugu Albasa lawashi maggi gishiri ta aje masa  a kusa dashi koh wanne a roba koh tire koh gwangwa ninsa ruwa ta iba a boket tasa kofi ta aje masa duka don ya huta da tashi koma ransa innan" ga kome a  zaune  Allah yasa yayi dadi"tace tana fita a kitchen in


Baiyi magana ba kawai wuka ya d'auka yafara feran doyan


Ruwa sumayya ta iba tayi wanka kaya tasa ta kwanta duk da Al'ameen ya hanata amma baccin tuni ya sace ta


Al'ameen na tsaka da feran doya yaji salaman yaro, amsa masa yayi


Wai ana sallama da MAKAHO


Inji wa?


Nima ban sansa ba yace dai in masa sallama dakai


Ok kaje kace masa ina zuwa


Toh, yace yana fita a kofar


Tashi Al'ameen yayi ya wanke hannun sa ya shiga d'akin, sumayya!ya kira sunanta jin shuru bata amsa ba sai numfashin ta dake sauka akai akai, girgiza kai kawai yayi ya d'auki sabon riga da wando da sumayya ta sai masa ya saka ya cire 3quiter dake jikinsa, waje ya fita yana mamakin waye yazo gunsa yau haka 



Waje ya fita yana tattaba jikin ginin kofar gidan don jin ina mai sallama dashin ya tsaya jin baiji  motsen saba ya sakasa, kara maimaita sallamar


Wa'alaikumu salam Al'ameen 


Laiiiiii wana kejin muryarsa kamar Ammar?


Baka mantani ba Al'ameen ka rike sunana baka manta ba.


Habba Ammar wanda ya maka hallaci irin wanda kamin ai ba mutumin da zaka manta dashi bane


Hakane Ya mai jikin?


Da sauki sosai Ammar, ya aiki ya gida?


Lafiya kasan yau kusan wata biyu da dawowa na ina zuwa unguwan nan ban gane kaba wallahi har Hospital in na koma sukace ai an mata tiyata ma har an sallame ku tuntuni


Eh kam satin mu d'aya aka sallame muma tuni.


Allah sarki yamai  jikin toh?


Da sauki fa sosai kamar ma ba'a taba yanka taba, na barka a tsaye muje bakin dakali


Ok toh in ba damuwa naga dakalin da rana kazo mu shiga cikin mota mana?


Tsakake Al'ameen yayi yana nazari kutt anya zai yarda ya shiga motar mutun da bai sansa ba(lokacin da ya taimake ka ka sansa ne) Am daman ina d'an aikine a gida nama manta na d'aura  tukunya 


Murmushi Ammar yayi watoh har yanzun Al'ameen bai yarda dashi ba kenan, toh ba kome nima bara na wuce naga yamma tayi sai na sake zuwa


Toh shikenan nagode da ziyara Ammar


Toh aje a cigaba da aiki mijin hajiya hhhhh


Hhh Ammar kenan, ya fad'a yana mikama Ammar hannu sukayi musabaha a karo na biyu 


Bayan tafiyar Ammar cikin gida Al'ameen ya wuce yana tunane tunane sai kuma yaji bai kyauta ba da Ammar nason cutar dashi da randa ya d'auke sa da sumayya ya cuce su, ta wani bangaren kuma sai yaji gwara masa hakan babu ruwansa da mutanen duniya sai mutunci yanzun bai yarda da kowa ba haka zalika tsoron shiga mota ne dashi tunda masu mota suka makantar dashi, kauda tunanin yayi  ya cigaba da aikinsa,  daya ya gama fere doyan ya zuba a roba wankewa yayi ya tsame a kwando ya zuba gishiri kunna hot plate in yayi ya kama Aiki.



Bayan kammala girkin Al'ameen juyewa yayi a kula ruwan shayi koma a flask wanka yayi yashiga d'akin, har lokacin sumayya bacci take, hawa yayi kan gadon  a hankali ya kamota d'agata yayi cak yayi waje da ita ajeta yayi a kan dakali 


Ido sumayya ta ware jinta a sama kafun ma ta gama nazartar inda take taji an ajeta a dakali"menene haka"?


Mangariba ake kira baccin ya isa haka, watoh bakiji bakisan baccin mangariba akwai matsala bako


"Baccin kwasheni yayi ai"


Sai kiyi Alwala nikam na tafi masallaci, bai saurare abinda zatace ba ya fita abinsa


Itama samayya Alwala tayi ta shiga d'aki...


Bayan sallan isha Al'ameen ne ya shigo kofar su,  kitchen ya wuce ya d'auko kulan da 🍽 ya shige d'aki


Sumayya dake kwance fuskarta sanye da glass ta d'aura system inta akan cikinta tana daddan nawa,d'ago kanta dake kan fillo tayi tana bin Al'ameen da kallo ganinsa d'auke da kula sosai tayi mamaki matuka, don ita harma ta manta da zancen zaiyi girki" ikon Allah wai da gaske kake kayi girki"?


Idanunki zai nuna miki, yana magana yana fita a d'akin bayan ya aje kulan hannun sa da plate da shukula, sai kuma gashi ya dawo dauke da flask da cups,  ajewa yayi a hankali akan cafet ya zuzzuba doyan da kwai sai yaji a gefen plate ya tsiyaye tie a kofuna 


Itakam sumayya sai ido kalala take kallonsa dashi"wai duk wannan kaika soya"?


Eh man bakin raina ni ba an gaya miki in mutum baida ido shikenan sai akace bazai iyya abinda masu ido keyi ba, ai harma yafi namasu ido muna iyyawa


"Ah ah kwadai kwatanta Amma badai yafi ba malam"


Au karya zan miki kenan?


"Bance ba,ina nawa doyan naga ka zuba plate d'aya"?


Eh namu ne yau tare zamuci a plate d'aya


Sumayya batayi magana ba sauka kawai tayi akan kujeran hannu kawai tasa ta fara cin doyan " kai maggi yayi yawa"


Kiji tsorin Allah fa sumayya


"Toh da tsoron ka zanji"


Amma dai k'wan nan babu maggin da yaji inba sharri ba


"Nikam naji,  k'wan maggi ga Albasa doyan kuma bai soyu ba,  tie in kuma sugar baiji ba"😕


Hannu yasa ya d'auke plate in gabanta da cup in tie in ya rike a hannunsa


"Yaya haka kuma"?


Ki miko mini kudi inje in sai miki abinci amma badai wannan zakici ba kowa ma ya hakura Almajiri zan kira na bawa, karasa maganar yayi yana shirin fita a d'akin 


Da sauri sumayya ta biyosa hade da kamo rigansa"dan Allah yayan khadija ka aje abincin mana waikai bakasan wasa bane?wasa fa nake maka"


Wasa koh?toh ni da gaske nake kuma sakar min riga karki yaga


"Habba don Allah yaga riga sai kace wata mai farashunan mayu"


Toh waya sani


"Yasan me"?


Sakarmin riga hajiya


"Ayya ka bani abincin mana wallahi wasa nake doya yayi d'adi haka tie ma k'wai innan inda kasan dafin Turai"


Mika mata plate in yayi shima ya koma ya zauna abinci suka cigaba daci


Bayan sun kammala ci yaukam ita ta d'auki kwanuka, bayan ta kaisu waje brush tayi shikam Aswakin sa  ya d'auka ya goge bakinsa d'akin suka koma kayan bacci sumayya ta saka rigane da wando cotton mai laushi da socks na sanyi a kafarta,  jin an fara yayyafi yasa Al'ameen fita waje ya tattare musu ruwa 

 shima kayan baccin sa da sumayya ta sai masa ya yasa


Sumayya gado tahau iyafis ta d'auka ta jona da wayan ta ta manna a kunne tana kallon film a ciki 


Shima bayan ya gama shiryawa d'akin ya rufe ya hau kan gadon, tattaba kan gadon yake har yaji ya tabota kwanciya yayi kusa da ita yasa hannu ya zame hular kanta 


Hannu tasa ta cire kunne d'ayan ta makala masa a kunne 


Kwanciya yayi akan filon da take gabaki d'aya ya nutsu yana sauraron abinda ke kunnensa, sai kuma yasa hannu ya taba sumayya hade da kiranta, sumayya!


"Na'am"


Uhmm Amma wannan indi'an film ne koh?


"Eh..ya akayi ka gane"?


Muryansu mana duk da Turanci suke magana amma dai sai kiji suna maganar sari koh bauta


"Gaskiya ne kasan sunan film in"?


Ah ah


"this is fate,  watoh kaddarar Rayuwa na Arewa 24"


Oh film in karam koh?


"Eh shine ma ke magana yanzun"


Ai da sauri ya zare abin kunnesa tare da sa hannu ya zare na sumayya, kinsan Allah bazaki kalli film innan ba


"Ikon Allah akam me bazan kalla ba"?


Nidai kawai bazaki kalla bane.


"Toh me kakeso na gani"?


Wani film banda wannan


"Uhmm nikam gaskiya shi nakeson kallo" tace hade da karban abinta ta mayar kunne


Da sauri ya fizgo abin gabaki d'aya ya had'a da system in yana  kokarin sauka akan gadon


Da sauri sumayya ta cakumosa baya hade da kokarin karban system in


Duk yanda taso kwatar abinta abin yaci tura duk inda tayi saiya zillar da hannunsa karshe ma hakura tayi takoma gefe tana maida numfashi


Tashi yayi jin ta kwanta,  zuwa yayi ya aje system in akan kujera, ya dawo ya kwanta abinsa 


Ganin ya aje yasa ta saurin mikewa zaune cikin azarbabi take kokarin sauka ta gefen kadon a hankali, tana sauka saboda matsen d'akin yasa dole saita biyo ta bangarensa kafun taje kan kujera, a hankali take tafiya


Shikam tun tashinta zaune da saukarta duk a kunnensa shuru kawai yayi yana son ganin gudun ruwanta


Tazo daidai dashi har zata gifta a bazata kawai taji ya fisgota baya ta fad'a kansa


Kokarin tashi take,  ya sake maidata, wai sumayya meyasa ne bakijin bari sam


"Me nayi kuma"?


Yanzun ina zaki?


"Waje zan fita"


Me zakiyi a wajen?


"Fitsari mana koh an hana fitane in aka kulle kofa"


Jin amsar da ta basa ya saka hannu ya mannata da jikinsa sosai kamar zai maidata ciki


Karan shagwaba ta sake da karfi"wayyo"


Ke menene haka saikin tara mini jama'ane


"Toh ba kaine ka matseni ba"


Toh ai ke ince bakiji koh kad'an kannan naki taurine dashi fa


Eh naji kaina taurine dashi kuma ni ka sakeni fit.........


Bai bari ta karasa ba kawai ya manna bakinsa da nata sosai yake kissing inta yana dad'a matsota garesa kamar zai maidata ciki 


A hankali tasa hannu ta kama kansa da karfi ta danke gashin kansa masu yawa sosai, hade da ajiyar zuciya


Washhh ashhh kawai Al'ameen yace bayan ya zame bakinsa a nata,  hannu yasa ya kamo hannunta data rike masa gashi ya d'aura a kirjinsa, da sauri ya maida bakinsa cikin nata


Sosai yau sumayya da Al'ameen suka farantawa junansu duk da tafiya tayi nisa sumayya ta copsa Shi kuma Al'ameen tsoro.


 *RANAN MONDAY* 

Yaune fa hajiya khadin Goggo zata makaranta jiya koh baccin kirki bata iyya ba, da sassafe ta tashi tayi wanke wanke shara kafun 6:00 har tayi wanka dumamen da goggo ta duma shi taci, uniform nata tasa fari kal wando da hijab harda riga duka farare ne socks ta saka fari ta d'aura bakin d'an kwali(kallabi)ta zura hijab,  sandal inta da Aunty ta tasai mata kala biyu d'aya 👟 ne d'aya sandal,  👟in ta d'auka bakine shima don a dokar makarantar baki da fari suke so,  tasa a kafarta sai agogo shima baki turare ta fisa fuskar nan washe kamar gonan Auduga takema goggo sallama hade da d'aukar school back nata shima baki mai kyau, ta fita a gidan


Sumayya da Al'ameen ne a kitchen suna girkin karyawa kamar kullum yauma hakan take watoh ana aiki ana fad'a


Assalamu Alaikum


"Wa'alaikumus sallam, yan makaranta"


Kai Aunty ina kwana?


"Lafiya khadija harkin shirya gaskiya ne Allah yasa hakan ya d'aure banda littin"


Ameen Aunty, ina kwana yaya?


Lafiya khadija harkin shirya?


Eh yaya na shirya


D'aki sumayya ta shiga naira 200 ta d'auko sai drinks d'aya da goran faro d'aya ta fitoh "ungo khadija wannan kudi yayanki ne ya bada na baki koda zaki zo ya fita ashe da rabon zaku hadu ma kihau keke sauran d'arin saiki rike a hannunki  ga wannan kuma kisa  a school back naki kinji,  banda kawayen banza banda abota da maza kinga makaranta ne da Christian sukafi yawa sosai kuma benchi d'aya ake had'a maza da mata don haka babu ruwan ki da yaran Christian abinda ya kaiki shi zakiyi kinji ki maida hankalin ki akan abinda ya kaiki Allah ya tsare mana ke"


Hannu khadija tasa ta karbi kudin da drinks in hade dama sumayya godiya, yaya na tafi


Al'ameen kam ya rasa ma me zaice da sumayya sumayya Alkhari ce garesa matar rufin asiri, toh khadija saikin dawo kindaiji abinda Auntin ki tace miki koh?


Eh yaya..


Adawo lfy


Bayan fitar khadija sumayya kam kitchen ta koma taci gaba da aikin ta Al'ameen na tayata


Assalamu Alaikum


"Wa'alaikumu salam" sumayya ta amsa tana fita a cikin kitchen in da sauri jin muryar wance ke sallamar


Aiko itace da mamaki sumayya ta bita da kallo,   

 Al'ameen ma da sauri ya fitoh a kitchen in jin muryar me sallamar


"Lafiya" sumayya ta tambaye ta


Eh lafiya daman n................




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sayanzunshi da gyara* 😉



🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* 


🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da*  *gyara* 


🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* 


🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* 


🍀 *Na tsunguno(habil)* 

🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,

🍀 *Na d'aki(halud Al'oud)* 

 

 *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼


🍀🍀🍀 *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* 


🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* 


Contact them vie

🪀08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense



🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧                       


 *HAPPY INDEPENDENT DAY* 🇳🇬

No comments