Matar makaho 46-47

 


Page 4⃣6⃣&4⃣7⃣  

Wai yarinyar tana d'auke da ciki shiyasa sukeso na rufa musu asiri na aure ta





Sosai nayi mamaki kuma zuciya ta takasa Aminta akan zancen cikine kawai ba, tunda yaran masu kudi da yawa suna cikin shege Amma ba'a  bawa talakawa saini MAKAHO sam nakasa yarda.


Dana matsawa bappa da tambaya ma cemin yayi koh naki koh naso sati mai zuwa d'aurin aure 


Harga Allah banso auren ba sam,  don inaji a jikina ba batun ciki bane, imma cikin ne taya za'ayi  a d'aura aure da ciki a jikin budurwan kenan, koh an zubar?karshe fa akafi karfine kafun sati d'aya  ba wanda   baisan zancen auren mu ba saidai sam ba wanda yasan dalili kuma duk wanda yaji batun auren saiya digawa auren ayar tambaya


Amma ke sumayya menene dalilinki na aure na?


"Auren ka,   ina ma na sanka kajimin mutumi fa" ?ta fad'a cikin kuka sosai abin ya mata zafi watoh bayan auren kaskanci da akaso mata har b'atata akayi a wajen mijin don aga abinda yafi wanda suka sata😭muni


Sumayya nifa tambaya  kawai nayi kuma abinda nayita gujema kenan,  kika ga nake gudun fad'a  miki gaskiyar abinda na sani, ya karasa maganar da kara rungumarta jikinsa


"Shikenan yanzun koh inada cikin sai ka yarda ka zauna dani" ?


Indai har cikin babu a jikinki koda kin tabayene  zan zauna dake a hakan ma naji dadi ai, na samu mata


Kuka sumayya ta sake sakewa watoh duk zaman da suke da Al'ameen na kokonto ne  tayi ciki koh batayi ba kai wai meta tsarewa dangin mahaifintane, na mahaifiyarta kamma bata sansu ba bare 


Kiyi shuru sumayya mundin bakece kika gaji da zama dani ba ni bazan taba juya miki baya ba a duniya,  bayan khadija da ke sai goggo bayan ku banida mutanen da suke sona  tsakani da Allah, ke kuma kin nuna mini tsantsar hallaci a rayuwa, don wata koh da gaske tayi ciki aka aura matani bazatayi hakurin zama dani ba bare ta taso cikin kudi yanzun kuma tana fama da rashi harsai ta nemi na kanta


Da sauri sumayya ta rufe masa baki cikin kuka tace"karka kara fad'ar haka banaso nima a yanzun kaine kad'ai Garkuwa ta kaine bangon da zan jingina ya rikeni, insha Allah  kome zai wuce kamar ba'ayi ba.


Allah yasa toh yanzun ya maganar kamilar?


"Bazan koya mata ba gaskiya kartazo tana shigewa mijina don yanzun kai ba tsaranta bane"


Yanzun shikenan saboda ni saiki rasa makudan kudi haka?


"Wani makudan kudi kuma bayan jiya ma na samu mutum uku da zasu fara zuwa, shiyasa yau zamu fita dakai muje bank zan bude Account maganar kudin  koyar,  shiyasa zan bude Account transfer zasu mini ta bank kuma yaran manya ne sosai fa, inaga anya ma bazan bude shago ba"?



toh Allah ya bada sa'a,  Amma banda maganar shago kam banyarda ba matar aure da shago kamar wata inyamura.


"Ayya koh a shagunan kofar gida saina kama d'aya tunda bakin titi ne"


Sumayya ban Amince ba, yace yana tashi akanta hade da karban eirps in hannunta ya mayar kunnensa kawai ya kwanta


Ganin ya kwanta yasata tashi ta d'auko musu karyawa jejjerawa tayi, ganin bai sauko ba yasa a hankali tahau kan gadon  agadon bayansa ta kwanta luf ta lumshe idanunta "breakfast is ready"


Shuru taji bai amsa ba Amma dai yasa hannu ya tabata,hannun ta buge hade da cire masa abinda yasa a kunnen san ta makala a kunnenta  wakar umar m shareef ke tashi a ciki


Jin ta cire masa yasa sa mikewa da sauri ya Amshi abin a kunnenta, wakar dadi tamin don Allah ki maida mini, ya fad'a mata yana mai mika mata wayar hannun nasa jin wakar ta chanja


Hhh"waikai kam anya ka taba saka eirps a kunnenka kuwa"?ta karasa maganar da sauka akan gadon


Da sauri shima ya sauko had'e da cewa wallahi kamar kin sani inadai jin ana zancen sa Amma ni bantaba sawa ba ashe da dadi


"Hhh toh zauna kaci abinci sai na baka bluetooth harda wa'azi da karatun qur'ani zakaji a ciki ba waka kawai ba"


Menene bluetooth kuma, banda na waya?


"Baka san ana posted a waya ba? toh ai yakamata kasan bluetooth da mp"


Nasan mp mana,  bluetooth ne bansani ba saina tura abu a waya inaji anacewa kai bude bluetooth naka na tura maka waka koh vedio.


"Kayi kokari wannan kuma na yayi ne a kunne zaka makala ba tare da igiya kamar eirps ba ka gane"


Eh na gane..yace yana zama


Abincin sumayya ta zuba musu mika masa tayi bayan ta damka masa shukali a hannu, wai nikam me kika maidani ne? an gaya miki bazan iyya d'aukar shukalin bane?


"Waya sani koh abincin ma saina fara baka"


Kwafa yayi kawai ya fara ci


Suna tsaka da karyawa sukaji sallamar khadija amsa mata sumayya tayi hade da bata izinin shigowa


Khadija bataso shigaba ganin yayanta na d'akin,  Amma ba yanda ta iyya haka ta shigo, ina kwana Aunty?


"Lafiya khadija ya goggo"?


Tana lafiya ina kwana yaya, tana maganar tana kokarin zama 


Lafiya khadija...ya Amsa mata


" khadija matso  muci" sumayya tace wa khadija


Ah ah Aunty nagode, daman takarduna ne na kawo miki duka kamar yanda kika bukata.


"Lallai ma khadija bansan yaushe zanna baki abu kisa hannu ki karba ba tare da kin mini filako ba"tace tana mikawa khadija plate na abincin data zuba mata sabo


Ba musu khadija ta karba 


"Yayan khadija"


Na'am sumayya..


Inaso zamu fita da khadija, zanje na sama mata makaranta tunda yanzun muna first time bazamu sha wahalar samun aji ba, Amma yakace ka Amince koh yaya"


Sumayya bazance miki kume ba sai dai nace Allah ya biyaki, tabbas yau zaki cikamin d'aya daga cikin buru kana dana so cikawa amma kana naka Allah na nasa.


Aunty makaranta zaki sani😳??khadija ta tambaya cikin zare ido fuska a washe


"Insha Allah kanwata zaki shiga makaranta yau yau ma amma wani school kikeson shiga"?


Koh wanne ma aunty nagode kin gama min kome arayuwa tunda zaki sani a makaranta bani da wani zabi koh wanne ki sani.


Matsalata dake kenan khadija in mutum yace kaza sai kice kaza, yanzun ni in baki fad'amin makarantar da kike soba ina zansan makarantan da ya dace ki shiga"


Nidai aunty na baki zabi 


"Shikenan bari yayanki ya zaba miki"


Da sauri Al'ameen yace, nikam ba ruwana tsakanin ku nida ba idone dani ba ina nasan makarantu inba na gw'annati tada ba


"Shikenan yanzun Art kikeso koh science"?


Aunty science nakeso.


"Shikenan sai muje GSSSJ ina ga makarantar tafi inganci a harkan science"


Kai Aunty tsadane fa da school in kuma ga kudin registration mai yawa gashi wai sai anye Attitude test kafun abawa mutum gurbin karatu.


Khadija kenan indai kin yarda da kanki Attitude test bazai baki tsoro ba maganan tsadan registration, kuma ai kyaunsa yasa kudin yayi yawa,  duk da makarantar goverment ne"?


Gaskiya ne sumayya kinsan koh lokacin mu ba makarantar da ta kaita inganci kyau da doka kuma sai wane da wane ne a ciki a kaf Taraba  daga goverment har private Amma yanzun xamani ya chanja saidai a sata a lissafin goverment school mafi inganci


"Yauwa bara na tashi in shirya kaima sai muje dakai yayan khadija zan bude account a bank da voter's card naka"


Nikam gaskiya ba inda zani tunda khadija tazo da National ID card nata sai a bude miki babban Account kawai.


"Kace kawai bazaka ba shikenan"sumayya tace tana mikewa,kaya ta fitar zata saka ganin haka yasa khadija fita a d'akin ta bata waje


Nifa kawai zuwanne banji shiyasa nace kije da khadija


"Toh zamuje daga nan saina wuce bank in,  nama manta ban fad'a maka ba nayi posted na vedio n make-up da lalle harda photos yanzun haka next week za'ayi bikin yar kanwar Deputy Govnor an bani kwangilan musu lalle da make-up kawaye kawai da Amarya"


Duk sunzo gidan nan?Al'ameen ya tambaya da mamaki


"Ah ah a online fa muka gama kome har balance na fad'a musu yanzun ma jiran Amaryar take na tura mata account numbar na"


Wow Allah abin godiya Amma dai sunan ki da suka ganine yasaka su baki aikin hala?


"Wani irin suna kuma?toh ni ban ma saka sunana ba wani sunan na saka"


Wani suna kenan?


"Basai kaji ba" tace tana yafa gyalenda ta d'auko sai jaka da takalmi data rike a hannu zata fita a d'akin sai kuma ta sake juyowa ta kallesa jin tambayar da ya mata


Sumayya baki bani bluetooth in ba?


"Ikon Allah"tace hade da nufar cikin kayanta,  Allah yasa ma tayi charge insa, makala masa tayi a kunne ta saita da wayanta," waka zan saka maka koh wa'azi"?


Waka....


Wakar ta kunna masa"ga wajen da zaka taba ta gefe in zaka danna next koh back koh stop koh play"tana fad'a tana kama hannunsa tana nuna masa gun 


Eh na fahimta, saikin dawo


"Allah yasa zanbi kasuwa duka me zan saya maka"?


Kasuwa kuma sumayya?


"Eh mana koh bakason naje? na saima khadija uniform ne da kuma d'an cefene nakeso na mana na sati uku kafun a fara azumi"



Saikun dawo Allah ya kiyaye hanya 


"Ameen baka fad'a mini abinda zan sai maka ba"


Am waken Gembu(Red beans)nakeso inkin iyya dafawa yanda suke innan asa tarugun Gembu(yellow pepper) da ice fish, irin dafin.



"Hhhh eyeee  kaima har kasan hadin dadi haka bansani ba"


Allah inason abincin sosai...


"Shikenan zan saya maka sai mun dawo"


Allah yasa...


Ameen, sumayya tace tana fita a d'aki,  suka nufi kofar gidan da khadija



Sunje makarantan kuma Alhamdulilah khadija ta samu gurbin karatu a makarantar science bayan interview da aka mata don an riga anyi Attitude test tun bayan sati uku, sun bawa khadija class,  sumayya ta biya kudin kome atake aka mata registration aka bata su  textbook,  notebook , da  tarkacen kayan makaranta su rigan sanyi rigan house socks vaji da sauran abubuwa


Bayan sun bar makarantar yau kam duk wanda yaga khadija koh ba'a fad'a masa ba yasan tana cikin farin ciki sosai  bank sukaje sumayya tasa aka budewa khadija Account .


Kasuwa suka wuce tasai ma khadija uniform jaka da takalmi don sune kawai ba'a basu ba, a kasuwar ta baiwa tailor ya d'inka musu kala ukune jibi khadija zatazo ta karba Turare ta saima khadija da mayuka masu kyau sai Dutsen guga karami na wuta.


Cefene tayi mai yawa sosai ta sai harda su drinks,  doya, dankalin hausa,  harda na turawa,  vegetables,  kai abubuwa sosai sumayya ta saiya saida kudin hannunta ya kare na machine kawai ya rage musu da d'an abinda baza'a rasa ba


Bayan sun dawo gida da sallama, suka shiga gabaki d'aya dan dazon yan gidan suka bisu da ido ga kaya niki niki kamar masu kaura suka wuce suka shiga kofar ga yara na rirrike da laidodi


Wa'alaikumus sallam,  sannun ku da hanya Al'ameen yace yana cire hannunsa daga cikin kwanukan da yake wankewa


"Yauwa yayan khadija" sumayya tace tana bin kofar da kallo ganin kayansu daya wanke ga randa a cike da ruwa Alamu dai jido yayi


Yaran na sauke kayan sumayya 10 10 ta basu da murna suka karba kowa na jin dadi suka fita


Sallah khadija da sumayya sukayi kafun suka baje cefenen suna dubawa, khadija kam ganin yanda sumayya ta loda mata kayan sayayyanta a gabanta kuka kawai ta sake tana rungumar sumayya,yanzun aunty duka wannan nawane? yaya kaga kayan kuwa wai duka nawa😅, tana fad'a tana kamo hannun yayanta ta d'aura akan damin kayayyakin abin ma abin dariya da tausayi


Shima karan kansa Al'ameen yayi  mamakin kayan, sumayya abubuwan nan basuyi yawa ba kinje kin kashe kudi da yawa haka sumayya kina ga ba aiki nake fita ba bazaki tattala kudinki ba sai kina fashaka haka.


"Allah zai kawo kuma maganar baka aiki bazai hana nayi walwala ba kaima insha Allah kafun d'aya ga azumi zaka daina zaman gidan nan"


Allah yasa Amma dai sumayya kayan yayi yawa


Babu wani yawa yar fa makaranta ce sai da guga da wanki da gyara, kema khadija duk safiya kina zuwa kafun ki tafi makaranta kizo ki karya,ki karbi kudin tara dana keke kinsan sunce sai 2 ake tashi kuma ana dukan letti


Toh Aunty amma zanna karyawa a gida saina zo na karbi na kudin.


"Shikenan monday zaki fara zuwa jibi,  kije ki karbi uniform in ki gobe ki goge,  gata sai school"😃


Hhh hakane Aunty in tafi da kayan naje na nunawa  goggo kona barshi Anan?


"Ai yanzun kayanki ne ki tafi dashi"


Toh aunty tace tana rungumar kayanta ta fita


Khadija na tsananin farin ciki yau wanda rabon dana gansa har na manta, Al'ameen ya fad'a yana lalubar hannun  sumayya ya kama


"Insha Allah zaka yita ganin sa yanzun harka gaji"


Allah yasa,  kema Allah  ya biyaki


"Ameen,  na sai maka waken Amma na gaji gaskiya bazan iyya dafawa yanzun ba kasan sa da wahalar nuna"


Shikenan sumayya Allah ya kaimu goben


"Ameen", tace tana d'aukar wayanta dake neman agaji"Assalamu Alaikum"


Shuru tad'anyi sai kuma yaji tace "toh bara na tura miki ta WhatsApp"


"Ok shikenan", tace tana aje wayan


"Kasan waya kira"?


Ah ah ...


"Yar kanwar deputy ne waina tura account number"


Toh Allah ya bada sa'a


Ameen, bara na tura musu


Tashi Al'ameen kam yayi yaje ya cigaba da wanke wanken sa


 sumayya kam Account numbar ta tura musu koh minutes 10 ba'ayi ba taji Alert kudine ya shigo account in khadija dayake da layinta aka bude account in.....



Khadija kam na fita a gidan yayanta da kaya niki niki sai sauri take kamar zata fad'i damuwarta kawai taga ta isa gida ta nunawa goggo abin Alkhari data samu, bata hankalta ba tazo tsallaka titi koh ganin gabanta batayi, ji kawai tayi jama'a na illalilahi keeee kalli gabanki


Ai jiii kawai kake kiiiiiiiiiiiii kauuuuuuuuu.............




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉



🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* 


🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da*  *gyara* 


🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* 


🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* 


🍀 *Na tsunguno(habil)* 

🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,

🍀 *Na d'aki(halud Al'oud)* 

 

 *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼


🍀🍀🍀 *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* 


🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* 


Contact them vie

🪀08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense



🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧                       


No comments