Matar makaho 44-45

 


Page 4️⃣4️⃣&4️⃣5️⃣

Al'ameen ne ya yanke jiki ya Fad'i,sosai mutumin ya rikice yahau salati cikin kidema 





Hayaniyar sa shiya matashe samarin dake kwana a d'akunan kofar gida,Suma dai sosai mutuwar Salim ta shigesu ruwa aka watsawa Al'ameen Amma Ina Koh farfadowa baiyi ba Dole tasa wasu daga cikin matasan d'aukar sa zuwa asibiti


Usman makwancinsu shiya d'auki gawar Salim zuwa gidansa  


Washe gari agidan malam Usman aka shirya salim.


Al'ameen dake asibiti kam Yana farfadowa da asuba ya tashi hankalin kowa sai ya dawo ankai Salim tare dashi


Haka aka kamasa g'wanin tausayi zuwa gidan malam usman,Yana shiga gida aka Kaisa Kan gawar D'an uwansa a hankali ya zauna Kan cafet in hannu yasa Yana lalube ya bude gawan jikinsa na bare yasa hannu ya shafa fuskar Dan uwansa murya na rawa hawaye nabin kuncinsa yake ma D'an uwansa Addu'a


Salim sosai ya samu jama'a kamar me don duk wanda yasansa, kuma yaji mutuwarsa  yazo,tare da Al'ameen aka kai D'an uwansa kabari. 


Bayan mutuwar Salim sosai kewa da kad'aici ke damun Al'ameen Koh bacci baya iyya wa saboda kewan D'an uwansa shikenan yanzun baida abokin Hira baida Wanda zai fad'awa damuwar sa baida Wanda zai kwana tare dashi sai Yar kanwarsa khadija ita Kuma mace ce          


Mai gidan Salim shiya bawa Al'ameen kudi Ya sari mangoro Koh a bakin kofar gidane ya fara saidawa don Bai dace Yana tsallake titi kullum zuwa kasuwa zaman shago ba


Ba musu Al'ameen ya karbi kudin yad'an fara business dashi,Kuma Allah yasama abin Albarka Yana samun na abinci da biyawa Khadija D'an hidindimun makaranta



Zancen kamila Kam baiyi fushi ba duk da Bata Masa ta'aziyar D'an uwansa ba haka ya sake Kama Khadija don lokacin ta d'anye wayo sukaje gidansu kamila.


Kamila ce tsaye da kawayen ta a waje tare da wasu samari uku A bakin mota


Al'ameen suna Isa kofar gidansu kamila,yaji hayaniyar maganar mutane Kamar harda ta kamila hakan yasa cikin murna yau dai zasu gana,  tunda ya jima Yana zuwa baya samun ganin ta


Da saurinsa yace wa Khadija suye wajen da Yake jin muryan mutane


Ba musu Khadija na rike da sandar sa suka nufi wajen, Assalamu alaikum


Waalaikumu salam D'aya daga cikin samarin  ya Amsa Masa


Ina wunin ku, Al'ameen ya gaidasu


Lafiya samarin suka amsa d'ayan ya zare kudi a Aljuhunsa Yana mikawa Khadija,ungo Yan mata


Khadija Kam kin karba tayi don bata Saba bara ba koma yayanta ya hanata roko Koh karban abin hannun Wanda Bata sani ba


Karba Mana yarinya D'aya daga cikin kawayen kamila ta fad'a don Bata San Al'ameen ba


Yayana ya hanani karban kudin Wanda ban sani ba, Khadija ta fad'a musu tana noke kafad'a


Da mamaki samarin ke kallon su Al'ameen mutum ya fitoh bara abasa yace bazai karba ba,toh lfy meya kawo ku gun mu inba bara ba


Am don Allah Ina da tambaya ne? Al'ameen yace


Allah yasa mun sani


Yauwa Kamar muryan kamila nakeji d'azun a cikin ku?


Eh ganinan lfy?kamila ta basa Amsa


Lafiya kamila in ba damuwa inason magana dake ne


Ina jinka,tace tana Masa kallon banza


Don Allah mu koma gefe


Kai MAKAHO akan me zaku kebe da matar da Zan aura Kai asuwa d'aya  daga cikin samarin yace


Wani abune ya cake zuciyar Al'ameen shikenan kamilar ma ya rasata shikam yaushe zai samu farin ciki ne duk mai kokarin faranta Masa wata Rana gudu yake ya barsa 


Kamila aure zakiyi?yace Yana kokarin faduwa tsaban shock


Eh aure zanyi Koh kana da matsala da hakan ne


Kamila Ina Alkawarin mu?


Alkawari kana nufin na aure ka kana MAKAHO Kuma talaka da wanne zanji da ciyar dakai Koh da ciyar da yaranka Koh da maka jakora Koh d'awainiya?Zan dai iyya auren ka a Talaka Amma banda kana MAKAHO kam.


Sosai zuciyar Al'ameen ta tsinke 


Dariya matasan da Y'an Matan suka sake na shekeyanci,Kai kamila bakida mutunci wallahi 😒 soyayya ce fa saikuje kusha love da lalube D'aya daga cin Yan matan ta fad'a tana dariya


Budurwar da ke gefe sanye da hijab itace kad'ai Bata ma Al'ameen tozarci ba


Kama hannun Khadija taye hade tacewa Al'ameen su tafe 


A hankali Al'ameen ke tafiya Kamar k'wai ya fashe Masa a ciki Bai d'auka Koh nakasa zaisa kamila gudunsa ba Koda kowa zai gujesa 


Suna sharan kwanan nayin,  kawar kamila ta dube Al'ameen,kaga bawan Allah don Allah Ina Mai rokon alfarma a gareka shine ka rabu da kamila Koda itace autar Mata ka barta duniyace ai Koda zata rabu dakai bada tuzarci Koh kushen halitta ba Amma ita Bata dube hakan ba y

Ta wulakanta ka kaima ka barta bari na har Abada,Kaye hakuri Allah Yana tare da musu hakure.


Insha Allah baiwar Allah na rabu da kamila Nima na hakura da ita Allah ya had'a kowa da rabonsa,


Ameen ta basa amsa tana Mai komawa layinsu tabarsa tsaye da Khadija


Wannan shine Ranar da Al'ameen  ya fita a Rayuwan kamila.


Bayan wasu shekaru karatu ya fara zama sai da kudi, a hakan yake ta faman ganin Khadija tayi karatu Koh ba kome zata tallah fawa kanta,  Amma Ina kudi ya gagara don yanzun mangoron ma sai a hankali Bai wuce a Rana yayi cinikin 200 Koh kasa da hakan. Gashi a ciki Kuma yake ciwa cikinsa hakan yasa karatun Khadija tsayawa iyya Junior.


 *An dawo labari* ...........

Khadija Kam kuka take kaman me,haka ma Sumayya Allah sarki Ashe haka rayuwar wa'innan bayin Allah yake, tasu kaddarar kenan,a cikin Yan watanni nan da mahaifinta ya juya mata baya taji kamar tafi kowa matsala,ashe itakam ma in an had'a kaddarar ta dana Muhammad nata ba kome bane tunda har tayi karatu ta tashi cikin kudi da lfyr ta Amma shifa ga maraici ga kuncin rayuwa da Talauci.


D'aga ido tayi tana kallon Al'ameen dake zaune a kujera fuska tayi ja"yayan khadija baka bani lbrn auren mu ba"?ta tambaye sa


Khadija tashi ki tafi kinji kukan ya isa haka, Al'ameen yace batare da ya amsawa Sumayya tambayar taba 


Mikewa Khadija tayi zata fita a d'akin cikin kuka abin  g'wanin tausaye"Khadija"Sumayya ta Kira sunan ta


Na'am Aunty


"Khadija kiyi hakuri kome na rayuwan duniya Mai karewane Sannan Yana da iyyaka  kinji"?


Toh Aunty tace tana share hawayenta


"Ki d'auki doyan nan ki tafi dashi gobe da safe  sauki kawo mini ducuments naki kinji Khadija"


Toh Aunty kawai tace tana d'auki laidan doyan ta fita


"Yayan khadija na tambaye ka shine kaci no   face"


Sumayya nagaji wallahih ki barni nad'an huta Mana waima me zakiye da ducuments in Khadija ne?


"Oho ba'a sani ba Ina maka magana kana tambaya ta Nima naki fad'an"


Shuru  ya Mata tare da lumshe idanunsa 


Itakam ganin ya Mata shuru tasan dai akwai abinda bayason fad'a matane,tashi taye a hankali ta Isa garesa faduwa tayi a kansa  da gangan


Washhhh yace yana gyara Mata kwanciya


"Don Allah ka fad'amin Mana"


Kinga Sumayya nifa banason na fad'a Miki abinda zaizo Yana d'aga Miki hankali.


"Allah bazan d'aga hankalina ba kawai ka fad'a mini"


Ok toh shikenan Amma sai da dare Zan fad'a Miki


"Gaskiya Nina gaji da abinda kake minin nan wani irin sai dare Kuma Wannan ai Jan Raine"


Banace Zan fad'a ba ki barni Mana zuwa Daren in ban fad'a Miki ba saiki Tuhume ni


"Uhmm toh yanzun me zakayi"?


Bacci,ya  Amsa mata


"Bacci a hakan"?


Eh.....


Tashi Sumayya tayi taje ta d'aura abincin dare ta barsa a d'akin


Bayan fitarta sosai yake tunani akan ya fad'a matane Koh karya fad'a Mata karshe dai ya yanke shawaran ya fad'a matan kawai 


Bayan isha'i Sumayya ce da Al'ameen kwance akan gado Sumayya taye matashe da cinyar Al'ameen sunfi minutes 20 a haka,tunda sukaci abincin dare sukayi sallah, suke a haka Amma Al'ameen baice mata kome akan labarin  ba abin sosai ya dame ta Amma ta danne tunda yace zai fad'a zata barsa ya fad'an da kansa.


Sumayya!!ya Kira sunanta Yana Mai shafa gashin kanta mai tsawo da kamshi


"Na'am"ta amsa Masa


Sumayya banso fad'a Miki dalilin auren mu ga ganin cewa kece kikafi kowa sanin hakikanin gaskiya don bana tunanin har yanzun ana cikin zamanin da za'a ma mace aure batare da tasan miji Koh miji ya santa ba.


"Me kake nufi"? Sumayya ta tambaye sa fuskar ta a hade Jin abinda yake fad'a Mata


Yanzun masifa Zaki mini Koh Jin lbr zakiyi? 


"Aiba labarin kake bani ba sukata kake"Sumayya tace,tana kokarin sauka a gadon


Sorry toh, yace Yana kamota


"Nikam ka sake ni "


Kin saketan yayi yana rungume da abarsa, naki sakin kin in kajimin mata fa


"Allah ni ka sakeni nace maka"tace tana kokarin xame kanta a jikinsa


Fushi kikayi ne Gimbiya?


" waye Gimbiyar"?


Sumayya mana.


"Gimbiyar wa"?


Al'ameen...


Uhmmm kawai tace bata kara magana ba


Kinga na miki Alkawari, zan fad'a miki gaskiyan abinda na sani akan auren mu?


"Nima nafasa ji yau sai gobe"ta fad'a tana mai sa  hannu ta d'auko wayarta dake gefen filo,  airp  inda ke makale a jikin wayar ta manna a kanne


Sai magana yake baiji ta amsa  masa ba hannu yasa yana tattaba ta, Gimbiya ina magana kin mini shuru


Duk da sumayya taji Al'ameen ya taba ta Amma taki koh sauraransa 


Shikam gane fushi take yasa sa dagota sama  daga jikinsa ya jefata gefen gadon


Ihu sumayya ta sake bawai zafi taji ba don laushin katifar dana blanket bazai bari taji zafi ba tsorata kawai tayi don bata tsammaci hakan ba" wayyo wuyana ya karye"  


Nashiga uku sumayya inga wuyan da gaske kinji zafi dan Allah kiyi hakuri ban dauka zakiji zafi ba, yace yana matsowa kusa da ita


Sumayya kam langobewa tayi wai wuya ya bugu"wayyo wuyata shikenan ya kasheni jama'i


Don Allah kiyi shuru muga wuyan wallahi bada niya nayi ba 


Sumayya kam kara lafewa tayi jin ya cicibeta ya daura  a cinya kamar wata baby


Sannu sumayya koh muje asibiti ne?


"Nidai goyona nakeso kayi"ta karasa maganar da make murya


Jikinsa na rawa yace, toh... toh... hau,  yana dukawa a kan gadon 


"Nika d'agani bazan iyya tashi zaune ba"


Cicibar sumayya yayi ya goya haka ya ringa lalube yana zaga d'aki zuwa baranda da ita sai kusan 10:00 sumayya taji gyangyadi kafun tace masa, " ka kwantar da ni bacci nake ji"


Ai da sauri bawan Allah yayi d'aki da ita da lalube ya shimfid'ata a gadon duk ya gama gajiya ba kad'an ba shiyasa daya samu taye bacci ba karamin dadi yaji ba gudun fitina ma koh  tabata bayyi ba a gefe ya kwanta yanata tunanin wuyan sumayya don harga Allah ya d'auka da gaske ne



Da asuba ma hakan take sashi tayi ya d'auketa har waje tayi alwala ya dawo da ita d'aki kafun ya tafi masallaci.


Misalin karfe 9:12 na safe Al'ameen ne ke bacci  a d'aki bayan dawowar sa sallan asuba


Sumayya data gama aikinta a nitse tayi girki duka don bata tashesa ba saida ta gama harda wanka tayi kafun a Hankali tashigo d'akin  wayanta ta d'auka ta danna play in waka ta kara volume,  ta saka Eirps   kunnen Al'ameen ta mannawa


Ai kam yana cikin baccinsa yaji abu tibbbtibb ga waka kamar a kwakwalwarsa, da sauri ya mike zaune hade da furta, innalilahi sumayya wuyank........sai kuma yayi shuru jin dariyan sumayy a kusa dashi


Hannu yasa sosai ya damkota kwantar da ita yayi a gefensa yahau kanta sosai yayi lamo yana daidaita bugun zuciyarsa har lokacin abin na kunnensa


"Wayyo menene haka"?


Shikam koh jinta bayayi, sai dad'a lumshe idonsa yake jin wakar da ke tashi a kunnensa sosai yatafi dashi 


Da sauri sumayya ta zare eirps in jin sai magana take baya kulata


Da sauri ya bude ido, tare da kamo hannunta data cire masa abin kunnensa, mena cirewa? wakarfa bai kareba


"Inata magana kamin banxa badole na cire ba"


Toh mekike son na miki kenan guda daya? tunda jiya ma ai magana nake miki kika saka abinnan a kunnenki kika manna mini nima,  duk wai akan maganar jiyanne kiketa fushi koh?


Shuru sumayya tayi


Dalilin auren mu.......

nidai bazance Miki nasan kome akan auren mu ba illah dai bazan manta ba wata Rana wani mutum yazo ya sameni agun sana'a ta yasai Mangoro ya tafi bayan kwana biyu Kuma sai gashi ya dawo Amma baifita a motarsa ba aika yaro yayi ya kirani nakai masa mangoro bayan naje ne yace na Shiga motarsa,  Yana da magana Dani,ni kuma naji tsoro gudun kar Amaimaita na baya(Randa aka makantar dashi) shiyasa naki Shiga motar duk yanda yayi Dani ki nayi,karshe dai agun mukayi magana,Kamar haka


Ni sunana mamman Ina da yarinya Naga hankalinka da nutsuwarka shine nayi maka kwad'ayin Koh zaka Amince in baka auren ta?


Sosai naji mamaki nida bana gani ad'auki yar Mai mota sukutum a bani gani Talaka haka kawai sainaji Raina Bai Kama zancen ba, shiyasa nace Masa bana bukata batare da Kuma sauraransa ba nayi tafiya ta


Bayan sati D'aya kawai bappa sulaiman yakirani Wai za'a mini aure,sosai abin yaban mamaki za'a mini aure kuma kamar mace,bappa aure Kuma Kamar Yaya?na tambaye sa


Kamar yanda kaji bappa sulaiman ya bani Amsa


Duk Azana Yar gidan nan za'a bani Amma bappa yace Wai Yar shugaba family ne tunda naji haka kawai nasan lallai wannan aure mai dalili ne ba auren Angani anaso ba,da farko naso nunawa bappa illan auren nan Amma ya murza ido yace sai anyi daga karshe ma cemin Yaya Wai yarinyar tanada Wanda zata aura matsala aka samu bayan anyi test shine aka samu tana d'auke da c................





🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉



🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* 


🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da*  *gyara* 


🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* 


🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* 


🍀 *Na tsunguno(habil)* 

🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,

🍀 *Na d'aki(halud Al'oud)* 

 

 *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼


🍀🍀🍀 *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* 


🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* 


Contact them vie

🪀08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense



🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧 

No comments