Matar makaho 40-41

 


Page4️⃣0️⃣&4️⃣1️⃣    

Yusuf ne kwance akan zainab suna dambe





Salati dumbin Alumman dake wajen suka sake,zainab Kam da sauri ta sake Yusuf ta matsa gefe tana kuka da rawan jiki 


Yusuf Kam ya kasa magana sunkuyar da Kai kawai yayi don bazai iyya hada ido da ubangari ba 


Yusuf Ashe Kai Maci Amana ne Yusuf Ashe Kai mugune Yusuf shiyasa tsawon shikarun nan kake zaune Dani da fuska biyu azzalumi maha'inci   kawai wallahih nayi Dana sanin zama dakai, Allah ya isan mini tunda ka rasa Wanda zakabi sai Yar cikinka,yace hawaye na taruwan Masa a ido,matasan samarin nan basuye wata wata ba suka rufe Yusuf da duka duk yanda yaso musu bayani Basu basa dama ba


Aisha Kam ba karamin shock ta Shiga ba Daman Yusuf ba D'an uwan ubangari bane? shiyasa inta tambaye sa Ahlinsa sai yahau fushi Ashe baida gaskiya ne kwata kwata, Aisha Kam kuka take tana dana sanin Yusuf, ya zubar Mata da mutunci ya ha'ince  ta


Matar ubangari waya ta d'auka ta Kira police lokacin Amma Yusuf jina jina Koh tsayuwa baya iyyayi,ga matan sa da yaransa duk suna kuka, A lokacin yaran basusan me uban yayi ba Amma tabbas sunsan ba lfy


Police na zuwa daker suka k'wace Yusuf ganin ana kokarin kisan kai, lokacin da police suka Kama Yusuf za'a fita dashi cikin tsananin azaba yake rokonsu su barshi yaga MATARSA zai Mata magana.


Ba musu domin tabbas su kansu police a lokacin sunji tausayin sa sosai da sosai,wani ne a cikinsu ya taimaka Masa suka nufi wajen da Aisha ke duke tana kuka


Yusuf na Isa dukawa yayi yasa gwuwarshi a kasa cikin galabaita ya fara magana, Aisha Koh kowa zai yarda akan abinda yafaru don Allah Aisha ke kad'ai  ki yarda Dani, yardan ki kawai nafiso akaf fad'in duniyan nan bayan yardan Allah,don kece abokiyar rayuwa ta in kowa zai juyamin baya ke Kika rungumeni bani da kaito Aisha Ina neman Wannan alfarman. ya karasa maganar hawaye nabin fuskar sa 


Aishan ADARA Kam yau Hali ya motsa jikinta har bare yake cikin kakkauran murya ta mike ,Yusuf Yusuf wallahih nayi Dana sanin haihuwa da Kai Yusuf, nayi Dana sanin auren ka Yusuf ka cuce kanka ka cuceni Yusuf bana bukatar ka a rayuwa ta ni daga yau mijina ya mutu.


Sosai Yusuf ya fashe da kuka maicin Rai Wai waye zai fahimce sane kowa bazai yarda dashi ba kawai don an gansa a d'akin yarinya Babu bincike sai kawai ad'au mataki, me yasa tunani bazaizo musu ba duba da cewa ya rasa inda zai nemi zainab sai a cikin gidansu?


Yunkurin magana yafara ais......,da saure Aisha ta d'aga Masa hannu Yusuf Koh Babu Kai zamu rayu da yarana Koh bakai Zan iyya rayuwa Koh ba Kai rayuwar zata Mana Dadi,Amma zaman ka acikin mu shine kuncinta ka tafi bana bukatarka a yanzun,tace tana Mai kokarin baren wajen.


Da sauri yusuf ya Kama hannun Aisha,bataye wata wata ba ta tsinka Masa Mari.

Da sauri Yusuf ya sake Mata hannu


Da sauri Al'ameen Yayi wajen babansa cikin kuka ya rungume sa,abbajo menene Kaye musu suke dukanka abbajo ga fuskarka duk jini,abbajo muje asibiti a maka treatment kaji abbajon mu ka bawa police hakuri karsu tafi dakai,kuka Yusuf ya sake hade da rungumar d'ansa Dayake Jinsa Kamar bugun numfashin sa, cikin su biyun yafi kaunar Muhammad sosai.


Karka damu muhammad Zan dawo kaji laifin da ba nawa bane aka d'aura mini Wanda duniya kaf ni ake gani da laifin ,Yusuf yace ma d'ansa Yana Mai  d'aukar sarkan dake wuyansa fari Mai azabebben kyau da walkiya ya d'aurawa Al'ameen a wuya, Muhammad ka kula da mamanku da kaninka kaji in mamanku ta haifi mace kace asa Mata khadija Inna mijine asa masa Shitu,Yana fad'a Masa hakan police sukazo suka Tisa keyarsa zuwa cikin mota 


Bayan an tafi da Yusuf, Alhaji ubangari da danginsa Koran Kare sukama Aisha da yaranta,sosai Aisha tayita kuka tana tattara kayanta zubawa tayi a ak'watin karfe ta d'aurawa Al'ameen da salim,suka Kama hanyar sintali.


Gari gabaki d'aya ya d'auka zancen Yusuf yayi kokarin mawa Yar ubangidansa fyade,bayan isar Aisha gidan ADARA zuwa lokacin labari yazo kunnensu Dayake unguwan da suke da sintali ba nisa


Bayan isar Aisha gida ta sake haduwa da wani tashin hankali shine mahaifinta yace sai ta mayarda yaran Yusuf gun danginsa kafun ta zauna musu a gida Dayake mahaifiyar ta tarasu tun kafun auren ta,yasa ba Wanda yayi yunkurin baiwa baban ta hakuri 


Aishan ADARA ta shiga tashin hankali ba kad'an ba na rashin sanin asalin Yusuf abin yayi mugun daga Mata hankali,ta rasa Ina zatasa kanta taji Dadi,don da ta koma gidan ubangari tunda shine waliyin Yusuf ya fad'a Mata inda dangin Yusuf suke Amma rashin mutunci da aka Mata a gidan Koh kyaun gani Babu,karshe dai  wani abokin Yusuf ne Wanda sukaye mutunci sosai ya taimaki Aisha bayan Jin labarin abinda ya faru tabbas shima ya shiga tashin hankali Amma Sam Bai yarda Yusuf ne zai aikata wannan abinba, d'auko Aisha yayi ya Basu d'aki a gidansa duk da MATARSA ta tsani zaman su Aisha Amma ba yanda zata iyya Aisha ta koma gidan abokin Yusuf da zama.


Wannan zaman gidan abokin Yusuf shine mafarin haduwar

 Al'ameen da kamila 


An Kai Yusuf kotu,Amma  bashi da hujjan Kare kansa haka yanaji Yana gani,laifinda ba nasaba aka yanke Masa hukunci.



Bayan Shari'a abubuwa sun ma Aisha yawa na rashin mijinta don abinda zataci  ma gagaransu yake Dole karatun su Al'ameen a private ya gagara ta ciresu ta maidasu Government school, sukaci gaba da zuwa,itakam wankau take Koh daka take sama musu abinda zasuci sosai Aisha take fama da rayuwa ga bakin cikin_ abinda Yusuf ya aikata,ba karamin bakin jini ya shafawa yaransa ba 


Hankalin Aisha Bai Kara tashi ba Saida lokacin komawar Salim asibiti Amma Bata da Koh sisi haka ta d'aukesa sukaje asibitin Amma abin mamaki duk yanda suka Saba da zuwa ganin likita Amma yau kawai da basu da kudin magani haka suka dawo gida kayan sakawarta Aisha ta tattara da kayan dakinta take sayarwa a hakan ta ringa ma Salim jinya da kayyakinta don abokin Yusuf d'aki kawai ya Basu Amma abinci Kam sai dai ta nema musu,


Ta bangaren zainab Kam tayi Dana sani Dana saninda har abada bazata daina yinsu ba sai yanzun take ganin wautarta na biyewa khairat harta aikata wannan mumunan kazafi wa Yusuf gashi abin Bai tsaya iyya Yusuf ba ta raba ma'aurata ta raba uba da yaransa ganin Yusuf da take taji Dadi yanzun Babu shi gashi  Koh samarinta ma yanzun duk sun gujeta a dalilin labarin da suka samu


Zainab rayuwa ta Mata zafi Koh baccin kirki Bata iyya wa taso sanar da iyayenta gaskiya Amma kairat ta kwabeta don hakan zai iyya zubar Mata da mutunci fiye Dana yanzun da take ciki.


Al'ameen da kamila yaran makwanta ne gidansu kamila.na kusa da gidan bala abokin Yusuf,


Kamila dalibar makaranta i private school ne Wanda ke kusa da goverments day da Yusuf ke ciki


Farkon haduwar kamila da Yusuf a hanyar makaranta zai tafi itama zata fita.


Tunda kamila.taga Al'ameen take yawan shige Masa har gidansu take zuwa tun Al'ameen baya kulata hardai ya fara kulata Aisha Karan kanta da farko bataso mu'amalar Al'ameen da kamila ba ganin Al'ameen lokacin shikara biyar ya bawa kamila Amma haka ta barsu ganin karatu Yusuf ke koya Mata kullum insun hadu


Bayan wata uku lokacin cikin Aisha ya Shiga wata bakwai,zuwa lokacin Aisha Bata da kome a dakinta sai taburma sai sarkan wuyan muhammad sai tsummo karansu saboda duk kudin sun Kare akan kudin maganin Salim ga rayuwa dai anata gargarawa



Yau ranan juma'a Al'ameen da Salim sun dawo makaranta bayan sun kara kamila gida don yanzun shakuwane Mai tsanani a tsakanin su wanda in kamila bataga Al'ameen ba zatazo gidansu haka shima, suna zaune dumamen safe da ya rage shine Aisha ta Basu itakam haka ta hakura saboda yau sun tashi bako sisi,zainab ce ta shigo gidan da sallama a bakinta


Aisha ta amsa Mata Dan Sam bata Jin haushin family ubangari don Koh itane abinda Yusuf ya aikata saita Masa fiye da haka


Kallon zainab take Wanda duk tabi ta rame kallo d'aya zaka Mata kasan Bata cikin hayyacinta,bayan  sun gaisa zainab ta d'aga ido tana kallon Aisha Bata San ta Ina zata fara ba yau tayi Alkawarin zata Fad'i gaskiya Koh zata samu sassauci a rayuwan ta 


Hawaye ne ya cika idanun zainab ta bude baki a Hankali tace,maman Muhammad akwai wani magana da zanfada Miki bansan ya Zaki d'auki maganar ba Amma na g'wammaci na karbi Koh wani hukunci akan Wanda nake ciki


Cikin mamaki Aisha kam ke kallon zainab a iyya zamansu da zainab Bata taba ganin ta Mata magana a mutunce ba Kamar yau,toh zainab Allah yasa naji alkhari


Gaskiyan abinda ya faru maman Al'ameen babu ruwan Yusuf aciki,tace tana kallon Aisha


Kamar ya bangane ba zainab?


Eh tabbas Kamar yanda nace , Yusuf Babu ruwansa a ciki nice da khairat Muka had'a kome a tunanin mu Koh in aka Kama Yusuf xai mini fyade babana zai tilastashi ya aure ni Amma ban taba tunanin abinda na aikata ba daidai bane Saida Naga yanda na wargaza muku farin cikin na dasa muku bakin ciki, wallahih maman Al'ameen nayi nadama,Dana biyewa khairat ban tashi nadama ba Saida naji jiya tana Hira da kawarta a waya suna mini dariya, na tsokancin danayi harna yarda da abinda ta gayamin Ashe itama son Yusuf take,ta karasa maganar hawaye ya zuba akan fuskarta


Aishan ADARA Kam daskarewa tayi a zaune itakam wace irin mace ce Mai mantuwa me yasa ta kasa yarda da Yusuf, namijin daya yarda zai rayu da ita Bai damu da tarbiyan gidansu ba Koh halinta ba ya aureta Koda Yusuf Zina yayi hukuncin da ta yanke Masa yayi tsauri,wani irin murdawa mararta yayi na tashin hankali atake jini ya balle Mata durkusawa Aisha tayi tana Kiran sunan Allah.


Da gudu matar Bala dake tsaye tun d'azun tanajin bayanin da zainab keye tazo da gudu,tana kwalawa mijinta Kira da gudu ya fitoh su uku suka ciccibi Aisha zuwa asibiti


Al'ameen Kam Kama hannun Salim yayi suka Kama hanyar gidan ADARA,suna Isa kakansu suka samu a kofar gida suka fad'a Masa mamarsu ba lfy an kaita asibiti, hankali baban Aisha ya Tashi matuka don shi Karan kamshi korinda Yama Aisha na haushin yaran Yusuf ne, Amma Yana son yarsa tura su Salim yayi gidan Amina (Goggo) shi Kuma ya wuce gidan Bala agun ya samu wa'inda ke zaune aka fita da Aisha, aka Masa kwatancen asibitin da aka Kai Aisha


Bayan zuwansa ne yaji labarin abinda ya haddasa ma Aisha nakudar Dole abakin Matar Bala,shima sosai ransa ya baci duk da Bai gamu da zainab a asibitin ba Amma ransa ya matukar baci gida ya koma ya sanar da yaransa da yaran Yan uwansa akan suje su fara d'aukar mataki akan zainab kafun hukuma ta shiga


Ayarin gidan ADARA daga Yan Mata har  zaurawa da  samari sukaye Ayari guda suka fasa unguwa  da kafa suka taka har  gidan ubangari.


Zainab Kam gabaki d'aya ta rasa nutsuwarta Koh zama takasa waje Daya, tunda ta gudo daga hospital karshe dai Saida mamarta ta tambaye ta Koh meke damunta haka? tunda abinnan ya faru ta fahimci walwalar zainab ya d'auke, zainab Kam kin fad'a Mata gaskiya tayi


Suna zaune dukansu a gida dayake yau Friday ne ubangari ya dawo aiki da wure haka Yan makaranta,ji kawai sukaye an bankado get in gidan an shigo ciki kafun ma su gama tantance suwaye ne har kanwar Aisha ta nufi d'akin zainab jawota sukaye har kofar gidan da gudu su ubangari suka Mara musu baya.


 Rufeta da duka ADARA sukaye, saiga khairat tafitob  gida makwantan su, Aiko kamota sukayi suka Had'asu suna jibga duk yanda Yan unguwa da ubangari suke kokarin k'wace zainab da khairat abin ya gagara ganin zasuye kisan kai don zainab ta Suma Amma haka Ayarin gidan Adara Basu daina jibgarta  ba Saida ta farfado da duka


Police aka Kira lokacin unguwan ya cika makil day'an kallo, abinka da Friday kowa na gida,


bayan zuwan police kafun aka samu aka k'wace su zainab anso Kama Yan ADARA Amma Ina abin ya gagara don fad'ane ya kusa zama na police da Yan gidan Adara,ganin jaraba irin na Yan gidan yasa polisawan tambayar musabbabin fad'an don dai sunyi sunyi su bisu station aye kome agun Amma sunki, D'aya daga cikin samarin gidan ne ya nuna zainab,ke don uwarki fada musu meya faru tsakaninki da yusuf mijin Aisha?


Hakika zainab tayi mugun tsorata hakan yasa Bata boye kome ba ta fad'a duk abinda ya faru,atake Alumman suka fara Allah wadai da zainab da khairat ubangari Kam yanke jiki yayi ya Fadi hawan jininsa ya tashi, police ma tafiyarsu sukaye Basu d'auki kowa ba.


Ta bangaren Aisha Kam  ganin tana kokarin rasa Ranta yasa likitoti Mata operation aka cire baby girl bakwaini aka saka a kwalba,Aisha na farfadowa sunan mijinta ta fara Ambata tana sambatu,tunda ta farfado batada magana sai a kaita wajen Yusuf ta nemi gafaransa Amma ba'a barta ta fita a asibitin ba saboda yanayin jikinta Dana baby.


Ta bangaren ubangari ma hakan take jinya ya kwanta har kusan sati baisan inda kansa yake ba abubuwa sun taru sun Masa yawa,Yana Jin sauki kad'an ya Tashi da kafarsa ya koma wajen Alkalin da yayi musu Shari'a,


  An nemi ganin Yusuf don a wankesa a kotu Amma abin tashin hankali shine, Yusuf a Randa aka kaisa prison Bai kwanaba ya fita tare da sa hannun kotsosin kasa


Wannan magana ita tafi ko wace magana tashin hankali agun Aisha don anye iyya bincike an had'a hannu da masu kudin da Yusuf yayi mu'amalan kasuwanci dasu don binciko inda Yusuf yake Koh suwa suka fiddasa 


Duk Wanda aka tuhuma Mai hannun a cire Yusuf magana D'aya yake fad'a baisan Yusuf ba kawai umurni aka basa daga sama


Wannan magana tayi mugun dagawa Aisha hankali atake ta sake kwantawa ciwo Wanda an rasa kansa kullum gaba gaba yake duk abinda babanta ke dashi ya kare a jinyar Aisha da Salim don shima zuwa lokacin zuciyarsa ta fara tashi.


Tsawon wata biyar ana binciken case in Yusuf Amma shuru ba wani cigaba,yau dai jikin Aisha da sauki,bayan Salim da Yusuf sunzo duba mamar tasu ,don yanzun suna zaune a gidan Adara ne 


A hankali ta Kama hannun Al'ameen ta rike cikin nata ta fara magana hawaye nabin Gefen idanunta,Al'ameen ga kaninka nan da Yar uwarka khadija Muhammad ka kula dasu ka zama uba a garesu Koda kowa zai gaji dasu Kai ka zaman musu gata, jagora,Garkuwa,inaji a jikina wata Rana zaka Hadu da mahaifinka,kace Masa ni Aisha Ina neman afuwarsa ya yafe mini Koh Zan samu salama,ka zamo Mai hakuri kamar mahaifinka duk abinda zakaye a rayuwa ka ringa bincike karka yanke hukunci a cikin fushi don karshin sa Dana sanine.


Al'ameen duk da yarone Amma hankalinsa in yayi dubu toh ya tashe in Bai manta ba haka abbajonsa yayi Masa, shikenan ya gudu ya barsu don shi har yanzun baisan takammamen abinda yake faruwa ba,


Mami kema gudu zakiye kamar abbajo ki barmu?yace Yana kuka shida Salim dake kusa dashi


Ah ah Yusuf ba gudu zanye na barku ba inda zanje kowa ma zaije in lokacin sa yayi sanan abbajonka Bai gudu ba wata Rana zai dawo kaji,ga kaninka na kuka ka rarrashesa karka barsa ya zubda hawaye kasan ciwonsa bayason damuwa Koh?ta tambaye sa muryanta na shakewa


Kai muhammad ya gyad'a Mata hade da Kama hannun Salim Yana rarrashensa,


Ji kawai yayi mamin su na wani irin shakuwa hade da Kiran sunan Allah,da sauri ya fita a d'akin yaje Kiran Doctor


Suna shigowa dakin da sauri Muhammad ya matso gareta cikin matukar razana ganin maminsu Bata m................... 

          




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉



🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* 


🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da*  *gyara* 


🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* 


🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* 


🍀 *Na tsunguno(habil)* 

🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,

🍀 *Na d'aki(halud Al'oud)* 

 

 *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼


🍀🍀🍀 *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* 


🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* 


Contact them vie

🪀08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧 


No comments