Matar makaho 38-39

 Page 3️⃣8️⃣&3️⃣9️⃣  


"Ni Kaya na saya" ta basa amsa


Wani irin Kaya kenan?

sannan Ina Kayana?




"Nina yarda kayayyakin ka duka sabo na sai maka Naga nakan sun kode,Amma kayi hakuri bazan sake ba" tace tana Kama hannunsa dake kokarin zare jallabiyan jikinsa


Sumayya akan me Zaki sayamin Kaya bazaki fad'a mini ba saboda bani da ido saiki zo ki musanya mini,kamar wani yaro.


"Kayi hakuri kaga yanda jallabiyar nan ta karbe ka kuwa yayan khadija" tace ta ja maza zip in gaban jallabiyar,hade da d'aukar Turare ta fisa Masa,vayan ya shafa Mai 


Nagode Allah ya miki albarka ya hanani Miki butulci a rayuwa Sumayya


"Ameen" tace tana jera abincin karyawan, Bismillah ta Masa suka fara ci cikin kwanciyar hankali


Bayan sun  Gama cin abinci  tattara Kwanukan yayi yakai waje,bayan ya ajeye, d'akin yadawo 


"Toh yayan khadija wacece kamila"Sumayya ta tambaye sa 


Nifa nayi Miki Alkawari ,ai basai kin Kara tambaya taba nida kaina Zan fad'a Miki kome Daya shafe kamila.


"Uhmm ba Dole na tambaya ba tunda sai jamin Rai kake yaufa da wure na Gama aiki Amma sai wani sham kamshi kake"


Nasha kamshin, kema saiki Rama.


"Wallahih ka Gama iyya jarabanka bazan biye maka ba sai naji lbrn nan ehen"


Toh zoki zauna a kusa Dani samun lbrn yafi Dadi,yace Yana zama akan kujera


Saboda tsabar sonjin lbr yasa Sumayya mikewa da sauri tazo Kan kujeran ta xauna kusa dashi


Hannu yasa ya matsota jikinsa a hankali ya rungume ta a jikinsa cikin sanyin hallintarsa murya a sanyaye yace Sumayya!


"Na'am yayan khadija"


Yau Zan baki labarin kamila Amma saikin ji labarina Nima kafun ki gane lbrn kamila dakyau.


"Yauwa Aiko Ina sonjin lbrn ka da dangan takarka da gidan ADARA duk da Ina tunanin dangin mahaifinkane Amma halayenku sun banbanta,hakan matsayinka da khadija a gidan nan na fahimci a kaskance kuke ba Kamar sauran Yan gidan ba"


Duk xakiji insha Allah Koh Nima Zan samu amsar dalilin auren mu Wanda har yau bansan dalili ba.


"Wai kana nufin ba Kaine kace kana Sona ba,aka aura maka ni "?ta tambaye sa cikin zare ido. 


Nima ban sani ba Sumayya bansan dalilin auren muba Amma koma menene inaji a jikina insha Allah haduwar mu dake alkhari ce

 

"Insha Allah insha Allah yayan khadija" tace tana share  hawaye Daya gangaro mata


Gyara zama Al'ameen Yayi a hankali ya fara magana................


 *Shikaru Talatin da biyar da suka wuce baya* 🕢

Malam Yusuf sumul, shine cikekken sunansa da aka Sansa dashi matashine Dan shikara 35,Yusuf mutum ne Mai Hakuri addini ga kawaici baid'auki duniya da zafi ba,Yana da tsananin zurfin ciki duk yanda zaka zauna dashi bazaka taba fahimtar wani abu a tattare dashi ba shiyasa ba Wanda yasan shid'an inane Koh daga Ina yake, duk da kowa ya gansa Kuma yaji yanayin hausar sa da maganar sa Dole yasan cewa ba D'an kasa bane .


Alhaji Rabi'u ubangari. Wanda akafi sani da ubangari,maikacin gonnati ne Kuma Mai rufin asiri sosai,Yana da Mata biyu.


shine Mai gidan Yusuf, saboda tsananin hankali da nitsuwar yusuf yasa ya d'aukesa Kamar D'an gida ya basa d'aki a cikin gidansa,Yusuf na Masa aikace aikace kamar zuwa kasuwa wanki da gugan kayan yaransa da NASA na kansa Yana Kai kananun yaransa makaranta ya dawo dasu,


Yaran ubangari guda biyar ne sai yaran Yan uwansa maza biyu Mata hudu,kenan yara goma Sha D'aya ne a gidan ubangari

Zainab Fatima Auwalu lukman Nasir,sune yaran ubangari na cikinsa


Haidar Umar khairat munira safara'u murja sune yaran Yan uwansa Dayake rikewa


Yusuf da ubangari akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninsu duk da baisan Yusuf ba Amma da zuciya d'aya yake zaune dashi ganin tsawon shikaru Bai taba nuna wani mugun halinsa Wanda mutane zasuye Allah wadai dashi ba.


Yaran gidan na basa girmansa kasancewar duk yaran gidan ya fisu a shikaru,yanajin dadin zaman gidan sosai don tun kafun Alhaji yayi aure suke tare har Allah yasa yayi aure 



Yaran suna ganin girman Yusuf saboda yanda mahaifin su ke tare tashi hakan yasa suke kiransa da bappa yusufa


Zaman Yusuf a gidan ya fara gunduran sane bayan girman Yar Alhaji Rabi'u ubangari zainab,wance Allah ya diga Mata son yusuf Mai tsanani duk da a lokacin tana da shikaru 14 yayin da Yusuf keda shikara 35    


Tun tana boyewa har abin ya gagara ta tinkare Yusuf da maganar.


Sosai Yusuf ya ja Mata kunne akan zancen kuma ya tabbatar Mata shi bazai aureta ba donshi a matsayin diyarsa,ya d'auketa duk yanda tayi kokarin ganin tashawo Kan Yusuf abin ya gagara,taso fad'awa  mahaifyarta zancen tanason Yusuf Amma khairat Yar bappanta ta hanata saboda tasan mundin maman zainab tasan zancen daker zainab ta aure Yusuf.




 ADARA FAMILY HOUSE haifafun jalingo ne tun iyaye da kakanni anan gidan Adara suka tashi don duk fad'in sintali ba gida Mai dumbin tarihi da shikarun mazauna ciki irin family ADARA tun husul sai chanje chanjen gini da ake in zamani ya shude,

Tun husul ma haka suke mutane ne masu masifan tsiya ga fad'a kamar ahlin dambe shiyasa aka musu lakabi da ADARA  


Aishan ADARA  d'aya ce daga cikin yaran gidan adara ,macece Mai matsifa na bugawa a jarida duk yanda kaga mala'in yaran gidan ADARA Aisha ta damasu ta shanye saboda tsananin masifarta yasa Koh saurayi Bata dashi don a lokacin abin kunyane mace takai shikara 20 batayi aure ba Amma Aisha shikarunta 20 Koh saurayi Bata dashi saboda tsananin tsoronta da maza keye 

Gidan ADARA tun asali haka yake har wa yanzun.


Aishan ADARA na Saida Dan wake a bakin kasuwan main market na jalingo


Sun hadu da Yusuf ne lokacin da yaje kasuwa sayayyan kayan Miyan gidan ubangidansa,ya saye danwaken ta by mistake robanta ya fashe a hannunsa,


Ba karamin bala'i Aishan ADARA ta sauke Masa ma kwando kwando da Kuma uzzurawa saiya biyata robanta 


Yusuf Kam ba karamin mamaki yasha ba ganin irin bala'in da Mai danwake ke Masa akan robanda Bai wuce sule biyar ba sai bala'i take Masa Kamar ya Mata Satan jari


Sosai Yusuf yaji haushi kala baice Mata ba ya Kama hanya Yana tafiya itakam sai binsa take sayya Biya robanta


Yusuf kam yasha Alwashin bazai biya ba ganin jarabanda take Masa haka tayita binsa harya Gama cefenen ya Kama hanyar gida bayan ya tare machine.



Duk jaraban Aishan ADARA yau taga iyyakarta don ba zagi ba duka da Mannin hauka Yusuf ya rabu da ita


Bayan dawowar Yusuf gida Sam ya rasa sukuni,tunanin Mai danwake Kam ya hanasa sukuni Sam


Ta bangaren Aishan ADARA ma hakane Sam bayan tafiyar kyakkyawar mutumin da Bata Sansa ba  gabaki daya ya hanata sakat a tsawon shikarun ta Bata taba bi takan soyayya ba Amma wannan Karo tayi tuntuben so a bakin titi Wanda Bata San inda zata sake ganinsa ba



Bayan sati biyu Sam Yusuf ya kasa sukuni ya kasa hakuri sosai Y'an kwanakin nan ya gane meke d'awainiya dashi,sai a lokacin yaji tausayin zainab Ashe haka takeji yake wulakanta ta,


Farga bansa d'ayane kar yaje gareta da soyayya ta tsigalesa don Tabbas daga ganinta Yar bala'i ce sosai Abu na biyu Kuma asalinsa kar rashin sanin danginsa yasa a hanasa auren ta.


A hankali Yusuf ya fara zuwa gun Aishan ADARA cin danwake Wasa Wasa harya kasance ba ranan da baya zuwa ci haka ba ranan da basa fad'a a tsakaninsu kafun su rabu ,har shakuwa yazo ya shiga tsakaninsu Mai tsanani Wanda a zahiri kowa son junane ke d'awainiya dashi,Amma ya kasa sanar da D'an uwansa


A hankali Yusuf ya fahimci masifar Aisha a tarbiyan gidansu  yake a Hankali ya Soma nutsar da ita sosai yake nuna Mata abin Bai dace ma Abu kamar Wasa Aishan ADARA ta nutsu sosai sai dai fa har lokacin in ka tabota zaka Sha bala'i sai dai in abinda ba ruwantane Bata Shiga haka zalika ta daina dambe da kowa,abin harya fara bawa jama'a mamaki sauyawan ta


Lokaci da Yusuf ya bayyana ma Aisha soyayyarsa gareta Babu wani jinkiri ta amsa sosai  suke zuba love


Yusuf ya samu Alhaji akan maganar Aisha ba karamin murna alhajin yayi ba dayaji Yusuf ya samu wance yake so don burinsa kenan,ya tambaye Yusuf danginsa don maganar aure Dole ana bukatan dangi na jini


Hankalin Yusuf ya Tashi matuka don har kwanciya yayi a gadon asibiti Akan zancen danginsa da Alhaji ya matsa Masa akai


Karshe dai fa ubangari yaga abin fa nayine yasa sa hakura da tambayar Yusuf shi yashiga maganar auren Yusuf


Da yake ubangari ya jima tare da Yusuf kowa gani yake kamar Yan uwane hakan yasa ba dogon zance aka basa auren Aisha don Suma sun Matsu tayi aure ganin ta girma a gida


Ta bangaren zainab Yar ubangari Kam in hankalin ta yayi dubu ya Tashi tayi kuka tayi kuka Kamar zatayi hauka Amma khairat ta taka Mata birki tare da Mata alkawarin sai Yusuf ya aureta amma tabare ayi auren taga matakin da zata d'aukar Mata


Bayan auren Yusuf sumul da Aishan ADARA, Alhaji yaki yarda Yusuf ya Kama gidan haya a gidansa sukaci gaba da zama, soyayya suke shimfid'a wa Mai tsafta sosai Aisha ta nutsu suna zaune da yaran ubangari da matansa  lfy Sam bata nuna musu Yar Hali  sai daifa basa shiri da zainab ganin kallon banza da take mata


Sai Bayan shikara uku da auren Aishan ADARA da Yusuf kafun Allah ya baiwa Aisha ciki sosai sukayi farinciki da wannan cikin da Allah ya azurtasu,sukaci gaba da rainon cikin cikin farin ciki


Bayan Aisha ta haihuwa sun samu d'a namiji Mai matukar Kama da mahaifinsa Kamar an tsaga Kara,  mahaifinsa yasa Masa suna muhammad.

Mahaifiyarsa na kiransa Al'ameen.


Da sauri Sumayya ta d'aga ido tana kallon Al'ameen dake Bata lbr"kana nufin kace mini gidan n........"


Bai bare ta karasa ba ya girgiza Mata Kai Yana Kara kwantar ta ita a jikinsa,ki aje tambayoyin ki Inna Gama saiki tambaya


Kai kawai ta gyad'a Masa 


Ya cigaba.....har lokacin zainab Bata saduda da soyayyar Yusuf ba don a lokacin ta kammala secondary school nata,Amma Taki aure Dole yasa babanta nema Mata wani makarantan gaba da secondary taci gaba 


Bayan haihuwa Al'ameen da shikara uku Aisha ta Kara haihuwar wani da namiji yaci sunan Salim, tun daga lokacin Aisha Bata sake samun ciki ba,sukaci gaba da kula da yaransu don a lokacin Alhaji ya budewa Yusuf shago yabar aikace aikacen gida basuda wata matsala sai na d'ansu Salim Wanda ke fama da mummunan ciwon zuciya,duk bayan wata D'aya sai sunga likita Kuma sai anci kudi.


A hakan rayuwa tayita tafiya yau Dadi gobe akasinsa Al'ameen da Salim suna matukar samun kula daga iyayen su suna Isa shiga makaranta aka sakasu yarane da suka shagu da junansu matika Kamar wasu tagwaye Dayake Salim nada gaban girma tuni ya tsara da yayansa har lokacin Aisha Bata San cewa Yusuf ba Dan uwan Alhaji bane duk da tana yawan tambayan sa labarin Yan uwansa Amma Yusuf daga tayi tambar saiya hau hada Mata fuska


Bayan wasu shikaru lokacin Al'ameen nada shikara 11 Salim nada shikara 8 a duniya. Aisha na d'auke da karamin ciki.


wata ranan juma'a da zuriyan yusuf bazasu taba mantawa da ranan b a tsawon rayuwansu ba har Abada ciwon bazaibar  zukatan su ba


Da misalin karfe bakwai na dare yusuf ya dawo gida,Yana kokarin shiga shashen su sai ga khairat taresa tayi cikin kuka Wai zainab ba lfy  tana dakinta Alhaji yace yaje su kaita asibiti


Da gudu yusuf ya bi bayan kairan zuwa shashen Yan matan gidan,shiya fara Shiga d'akin Yana shiga khairat taja kofar ta rufe kofar ta waje da makulli.


Yusuf na shiga d'akin ya ware ido ganin zainab ba Kaya daga ita sai d'aurin kirji a zaune akan gado


Tambayar ta yusuf ya farayi, zainab menene haka Kuma ki nemi riga ki saka yace Yana Mai kokarin bude kofar


Dariya zainab ta sake hade da furta wallahih kaji na rantse maka Yusuf tunda ka hofantar da soyayya ta kasa kafa ka shureta Nima saina jazamaka bala'i inda zaisa ka aureni Dole wannan itace kad'ai abinda zanyi na mallakeka,ka 'dauka Koh shurun da nayi na hakurane?

Ah ah wallahih ban hakura ba tanadi nake maka.


Subhanallah shine abinda yusuf ya furta cikin gigita, zainab Ashe bakida hankali wani irin shirmene haka


Hauka zakace ba shirme ba tabasa amsa tana matsowa garesa hade da fizgo kwalar rigansa ta yaga sosai tana ihu


Sosai yusuf ya razana ya Shiga kokarin k'wace kansa



Khairat Kam tana rufe d'akin ta tsaya kamar minutes biyu kafun ta fara rafka salati a tsakar gidan wayyo jama'a wani zaima zainab fyade a d'akinta yanzun nazo shiga kawai naji kofa a rufe zainab nata kuka ku kawo d'auki


Da gudu Yan gidan harda Aisha  da makwanta Dayake darene ga madalisa a kofar gidan  suka ruga da gudu zuwa d'akin zainab da suke Jin kukanta na tashi har lokacin


Jin kofar a rufe yasa matasan samarin unguwan suka dauko katon itace suka bugawa kofar take kofar ta balle,cikin mamaki tsoro Al'ajabi suka zubawa d'akin ido ganin abinda ke faruwa kamar a mafarki y................




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉



🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* 


🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da*  *gyara* 


🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* 


🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* 


🍀 *Na tsunguno(habil)* 

🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,

🍀 *Na d'aki(halud Al'oud)* 

 

 *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼


🍀🍀🍀 *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* 


🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* 


Contact them vie

🪀08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧  


🏵️Wannan shafin nakune🏵️

Ummu Muhammad 🍀

Zainab mansur🍀

Surayya🍀


No comments