Matar makaho 36-37

 





Page 3️⃣6️⃣&3️⃣7️⃣




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃


✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa 👌

free book 🤧     


Page 3️⃣6️⃣&3️⃣7️⃣

Kamila kice Koh dai Mai irin muryar tane, Al'ameen yace cikin d'unbin mamaki


Ikon Allah Ashe da rabon za'a sake ganin juna Muhammad,kamila tace tana me Kara kallon Al'ameen


Wallahih fa kamila yace Yana isowa kusa dasu sumayyar


Oh duniya Muhammad Daman a unguwan nan kake?


Anan nake kamila,ya bayan rabuwa ya maigidan ki da yara?


Jiki a sanyaye kamila tace,hmm muhammad mijikam aure ya kare, yara Kuma Allah Bai kawo ba tukum.


Allah ya kawo masu albarka


Ameen Muhammad,Amma nayi mamaki wallahih wannan ce matar ka,ta fad'a jikinta na Kara sanyi tunawa da abinda ya faru a shikarun baya da suka wuce


Eh kamila matatace sunanta Sumayya


Masha Allah gaskiya matakam tabar kalla Masha Allah wallahih gata kyakkyawa son kowa kin Wanda ya rasa,tace tana kallon Sumayya har lokacin


Haka Allah yake abinsa sai ya baka abinda baka taba tunani Koh tsammani ba, shiyasa duk abinda bawa ya samu a rayuwa rabonsa ne ba Mai hanasa muddin Allah ya basa


Gaskiya ne muhammad,Aiko shikenan Daman kwalliya nazo tambaya Allah dai yasa madam in zaka barta ta koya mini,tace tana Mai Al'ajabin Rayuwa


su kamila kenan yaushe Kika dawo Jala ne?


Shap aini na jima a Jala, Amma Dad nawa transfer mun dawo nan


Allah sarki toh ya gidan naku da aiki?


Gida Alhamdulillah aiki Kam Babu sai karatu.


Karatu Kuma,kamila?


Eh Mana ai kasan bayan rabuwar mu aure nayi sai karatun ya tsaya sai yanzun na samu na Shiga TSU 


Gaskiya ne Allah ya bada sa'a..


Ameen, muhammad Kai ya lbrn karatun?


Kai kamila wani karatu Kuma makaho talaka zaiyi ba kudi ba ido ya fad'a Mata maganar cikin murmushi


Sosai taji wani abu ya Tukare Mata makoshi Jin kalaman da ya fad'a ya tuna Mata da kuskuren da ta tafka a rayuwar ta tabbas Al'ameen Mai hakuri ne da wanine haduwarsu yanzun bazai ma saurare taba


Cikin sanyin jiki tace,toh nikam Zan tafi Sumayya saina jiki Koh,ta fad'a tana kallon Sumayya dake zaune a Kan darduma


Sumayya Kam ba karamin haushi taji ba Kamar ta tashi ta Basu waje, Amma saita maze gudun karta bada kanta agun kamila,"yauwa"kawai tace tana kallon kamila dake Shirin fita a kofar


Sumayya! Al'ameen ya Kira sunan ta


Kin amsawa tayi Tamar kunnen uwar shegu


Sumayya Koh kin tashi a wajen ne?


Nan ma Sumayya kin amsa Masa tayi.


D'aki ya shiga a zatonsa ta koma d'akin ne Amma ya Gama laluben ta bai jita ba


Sumayya Kam na zaune duk haushi ya Gama kasheta Jin yanda Al'ameen ke wani sake baki Yana Hira da Yar banzar bazawaran (Kai Sumayya harda zagi)

Ji kawai tayi Al'ameen ya rungume ta a zaune da take


"Menene"tace tana zame jikinta a nasa


"Me yasa kika ki amsa mini bayan kinji Ina kiranki,yace Yana Kara lafewa a bayanta


"Oho Kuma ka sakeni"


Meye Kuma nayi Miki haka hajiya


"Bansani ba nika sakeni nace maka"


Habba bakutuwa


"Ka sakeni fa"


Green sum......


Sumayya Bata bari ya karasa ba kawai ta dasa Masa hakoranta a hannunsa D'aya zagayo dashi Kan kirjinta


Washhhh Allah na yatsata,yace Yana yarfa yatsar don harga Allah da gaske Sumayya ta cijesa,ni Kika ciza?


"Eh din kuma,ka sakeni nikam"


Wai menene Kam?


"Bansani ba"


Karki sani Kuma kamila zata fara zuwa make-up gobe nace Mata na, Amince kamar yanda Kika Bata umurni,yace ya na son gane dalilin fushin nata Koh saboda kamilane, don shidai lfy suka rabu kafun ta fitoh waje


"Bazan Yi ba ai ba'a dole karta kuskura tazo mini gida don kurinta zanyi"


Kishi kike da ita?


"Akan me zanyi kishi da ita kuma" samayya tace tana Jin bugun zuciyarta na karuwa


Akan mijinki,Mana


"Ina mijin yake"


Au bakisan inda yake ba?


"Eh ban sani ba saika sanar dani"


Jin abinda Sumayya tace yasa Al'ameen zabura da karfi ya fizgota jikinsa ya juyarda ita suna fuskantar juna,kikace in sanar dake Ina mijin yake? Sumayya ni kike fadawa wannan magana saboda Ina miskini Kuma kina ciyar dani,ya fada ransa a matukar bace


Sosai Sumayya ta razana harga Allah batasan maganar ta fita ba Sam ita Karan kanta bazatace ga abinda ya harzukata ba yanzun yanzun nan


Tambayar ki nake Sumayya saboda kina ciyardani? Koh saboda bana gani shine kike wulakantamin aure?


Sosai ta Shiga rud'ani Bata d'auka Al'ameen da ta sani yanada irin wannan fuskar ba"Kayi hakuri"tace tana zame damtsen ta a hannunsa D'aya damke


Kala baice ba mikewa kawai yayi ya d'auke sandarsa da ciny'ayyen takalmin sa yafita


Bayan fitar Al'ameen sosai Sumayya ta Shiga Dana sani,tabbas magana zarar budu inta fitoh Bata komawa,da tasan haka zai Bata Masa Rai da Bata fara ba


Mikewa tayi ta Shiga d'aki ta kwanta sosai zuciyarta ke Mata zafi 



Bangaren Al'ameen Kam bayan fitarsa gida Tashan kayan marmari ya nufa, duk yanda yaso ya samu bashin Kaya abin ya gagara haka yayita yawo Amma shuru Bai samu kome ba ,tabbas irin wannan yake gudu Sam bayason mace  ace ita ke ciyar da miji,Sam maganar Sumayya Ada Baya Masa ciwo Amma yanzun yaji wani irin ciwo akan maganar sosai,sanann ya Mata hakan ne don ta kiyaye gaba in zata Masa magana ta ringa taunawa,ya fahimci kishine kawai ke d'awainiya da ita 


Jin ana Kiran azahar yasa Sumayya mikewa sallah tayi ta d'aura shinkafa da wake,zubawa tayi a flasks don itakam Sam bazata iyyacin kome ba yanda take Jin tsananin damuwan nan,gashi batasan Ina Al'ameen ya Shiga ba,har yanzun Bai dawo ba 



Har yamma Al'ameen shuru Bai dawo ba duk inda hankali Sumayya yake ya Tashi sosai ta Shiga damuwa matar Bashir data ma alkawarin lalle day uku tana Aiko yaro karshe ma Sumayya tace yaron yace Mata bazata samu zuwa ba


"ya Allah ka dawo mini dashi lfy"tace tana zabga tagumi



Sai bayan Isha'i Daya idar da Sallah Aljuhunsa ba kome yanda ya fita haka ya dawo Koh abinci Bai Karaci ba bayan na karyawa,da sallama ya shigo d'aki


Sumayya dake cikin dogon tunani tana zaune akan sallaya Koh hijab Bata cireba , da sauri ta amsa"waalaikumu salam yayan khadija lfy kuwa baka dawo ba sai yanzun"tace tana isowa garesa


Uhmm sai yanzun, kawai yace Mata Yana k'wabe rigansa,jallabiya ya d'auko a cikin kayansa ya fitoh waje Bai Kara Mata magana ba


Baki a sake Sumayya ta Bisa da kallon mamaki harya fita,ta koma ta zube a jikin kujera hawaye na cika Mata ido,ta Shiga uku sauran hope natan Daya saura shine shima yake kokarin juya Mata baya Wai meke faruwa da itane me yasa duk Wanda zai sota daga baya sai ya kaurace Mata,kuka kawai ta sake "nikam na Shiga uku"tace tana cigaba da kukanta, Al'ameen Bai taba fushi da itaba sai yau menene Bata Masa ba Abaya Bai taba fushi ba sai yau daya ga kamila.


Al'ameen Kam wanka ya Shiga Yana fita yaji muryar Sumayya kasa kasa tana kuka da sauri ya aje kayanda ya cire,Wanda yaso wankewa Amma baida omo.

D'akin ya shiga Amma saiya maze ya kwanta akan kujera Bai kulata ba 


Sumayya Kam Jin yanda Koh damuwa baiyi da kukan da yaji take ba yasa a hankali cikin muryar kuka tace"yayan khadija ga abincin ka"ta fada tana mikewa ta dauko a saman freezer


Na gode Amma bazanci ba yace, ba tare da ya Koh motsa a inda yake ba



Kuka kawai Sumayya ta sake kamar ana yankata"nikam na shiga uku tunfa safe banci kome ba bayan karyawa saboda Ina jiranka ka dawo Amma shine ka dawo kace bazaka ci ba"


Na hanaki cine ai ban hanaki ba kici Mana ni indai nace bazanci ba


"Wayyo Allah na ni Sumayya Yaya zanyi da Raina ne"


Da na Miki me?


"Kaci abincin toh kaji"


Ah ah naci ai 


"Waya baka kudi ka saya"


Ai Ina da sana'a Koh?


"Nidai don Allah Kayi hakuri kaci kaji"


A matsayina nawa Kika damu da sai naci abincin ki?ya tambaye ta


"A matsayinka na"......


Sai Kuma tayi shuru tana kallonsa


Uhmm ,kawai yace Yana lumshe idanunsa so yake ya kitsema wannan baiwar Allah Koh Amafarkine Yana son kallonta, tunda ya makance Bai tanajin yanason kallo ba irin haduwarsa da Sumayya sosai yakeson ganinta da idanunsa 


"Wa.....i mi...jin..a.."tace cikin eeii eiiina


Waine ma kenan?


"Mi..ji...na"


Sumayya!ya Kira sunanta


"Na'am"


Meya Bata Miki Rai d'azun?


"Babu"


Akwai Kam?


"Babu"tace hawaye nabin kumatunta


Nine Koh kamila?ya Kara tambayarta


"Koh D'aya"


Ki fadamin gaskiya wannan shine kad'ai zaisa na hakuri.


"Kaine"


Me nayi Miki har zakina fad'amin magana irin Wannan


"Toh ba Kaine ba"


Nine me?


Kaketa Mata dariya harda wani.....sai kuma tayi shuru Jin subutar baki da tayi


Shikam murmushi ne ya subuce Masa hade da wani irin farin ciki tunda Sumayya na kishinsa,Kuma duk inda akwai kishi akwai alamun so,

sai Kuma akace ki gaggaya min magana?


"Kaye hakuri don Allah"tace tana mikewa a hankali ta matso garesa fadawa tayi kansa da karfi ta sake kuka


Rumtsa idanunsa yayi Jin saukan hawayen ta a kirjinsa tamkar ruwan guduma haka yajisu, Sumayya!ya Kira sunan ta Yana Mai Kara matseta a jikinsa


"Na'am"ta amsa Masa hade da cusa kanta a kirjinsa ji take Kamar numfashin ta zai d'auke


Sumayya na hakura Amma karki sake mini Wasa da aure kinji banaso.


"Wallahih bazan sake ba"


Allah yasa,yace Yana shafa rigan jikinta

Sumayya wannan ba kayanda kikasa da safe ba?


"Shine" Ta basa Amsa


Miya hanaki wanka? sai tsami kike ma,ya fada hade da shafa Mata baya


"Damuwa ne ya hanani,Kuma ni bana tsami"


Bagashi  ba sai tsami kike, yace Yan sunsunar wuyanta,dake tsananin kamshin Turaren ta


"Zakaci abincin na baka"?ta tambaye sa cikin damuwa


A koshe nake ki bare sai da safe sai naci.


"Nidai ban yarda ba wallahih Koh kaci saikaci nawa"


Toh zanci,kije kiye wanka ki wanke tsami kisa Kaya 


"Bayan na Gama sai muyi me"?


Saina karbi hakkina,ya Bata Amsa shima


"Niii..... niii.. Babu ruwana,abinci nake nufi"


Ai kema abinci ne,ya Bata Amsa


"Wacece kamila"?


Uhmmm abinda ya hanaki sukuni kenan?


"Nidai ka fad'amin kawai malam"


Toh malama bakutuwa kije kiyi wanka sai kizo kici abinci sai mu k'wanta da safe saina fad'a miki,.


"Har gobe kuma"tace tana hada fuska


Eh na gaji bacci nakeji yanzun yace Yana cire Mata riga


"Bacci Kuma kake kwabeni"?


wanka zakiy i,ya Bata Amsa hade da karasa cire Mata rigan

 

Wanka Sumayya ta Shiga tana fitowa lokacin karfe 8:00 dai dai, shiga d'akin tayi Kaya tasa,tana Gamawa ta jawo abincin "yayan khadija muci abinci"


Sumayya kici nikam na koshi saiki  dumamin da safe.


"Ni wallahih ban yarda ba,toh bakace ka hakura ba Koh baka hakuran bane" tace tana hawaye


Tabbas ko yaki Koh yaso Sumayya ce rufin asirin sa inba itaba bashida wajen da zaici abinci tunda ba kudi Koh sana'a bane dashi,sauka yayi ya matso Yana lalube ya zauna shukali Sumayya ta Mika masa,ya karba suka faracin abincin



Koh minutes uku basuyi ba sukaji sallaman yaro a kofarsu,


"Kai wallahih nifa na gaji habba matan nan bazata samu lallen nan ba"


Wace Mata Sumayya kardai kice min matar Bashir baki je kin Mata lallen ba?da mamaki yake tambayar ta


"Nikam banje ba"


Saboda me?


"Saboda baka dawo ba,Kuma ni yanzun dare yayi"


Amma sumy gobe nefa sunan Kuma baki je kin Mata ba,sannan yanzun Kuma kice kin fasa,baxataji d'adi ba in Kama mutum Alkawari Yana da kyau ka cika Kinga na riga nace wa Bashir zakizo kima matar sa lalle bazaiji Dadi ba in Kika ke zuwa Kuma gobe suna.


Hakane kam, Sumayya tace tana fitowa waje


Ina wuni Aunty?yaron ke gaida Sumayya


"Lafiya ya mamarka"?


Lafiya aunty Wai inji mamana inzo in fada Miki Wai don Allah kiye hakuri kizo ki Mata lalle ta nemi me lalle Bata samu ba


Toh shikenan bara na d'auko hijabina, Sumayya tace tana shiga d'akin


"Yayan khadija zanje lallen saina dawo ga abincin ka karasa ci"tace tana d'aukar hijab nata da jakan lalle   purse ta bude 50k ta d'auka,zata fita a d'akin


Toh baki karasa cin abincin ba?


"Ah Ah Alhamdulillah kaci kaikam nikam sai nadawo"


Sumayya muje na rakaki kinji?yace Yana mikewa


"Ah ah ga yaro zamu tafi tare,sai dai kazo ka d'auke ni anjima"


Kamar karfe nawa?


"Kana da agogone"?


Oho,nikam ki fad'amin.


"Yanzun 8:12 zuwa 10:00 sai kazo ka d'auke ni"


Toh shikenan yace Yana zama,d'aukar abincin yayi ya cigaba da ci


Sumayya Kam fita tayi da yaron,sai da sukazo kusa da titin first bank taga shagunan a bude kamar Rana ga wuta ako ina,"tsaya Kai mu Shiga shagon nan"  tace ma yaron tana Kama hannunsa suka tsallaka titi,shagon ta shiga"excuse me"tace ganin Mai shagon inyamurine


Yes ma barka da zuwa shigo ciki customer ki duba Kaya


Da mamaki sumayya ke kallonsa Ashe ya iyya hausa,yauwa "sannunka,Kaya nake so"


Ok wani iri?


"Jallabiyoyi"


Ok ki shigo gasunan kizo ki zaba Wanda ya miki,yace Yana zazzaro Mata jallabiyoyi sunfi kala goma


Guda uku sumayyaa ta zaba masu masifan kyau fari da baki Mai maiko sosai da hula sai Kuma Mai aiki ruwan sararen samaniya,takalmi ta sai Masa Mai kyau na tambarin Adidas silifas ne,sai t-shirt da 3quiter sai Jean's,sosai Sumayya Tama Al'ameen sayayya harda Turare na maza ta sai Masa da abin haske Kai da gemu,sai kusan 9:26 suka je gidan Matan da zatama lalle 


Lalle Sumayya ta Mata baki da ja, Al'ameen tun 10 yazo Amma Basu Gama ba,ya zauna Yana jiranta a kofar gidan


Suna Gama lallen Sumayya ta karbi kudinta laidan da ta aje a kulle a gefe na kayan da ta saima Al'ameen ta saba,waje ta nufa


Tana fita taga yayan khadija a zaune


"Yayan khadija mu tafi Koh"tace Masa


Kun gama?


"Eh mun Gama"


Ok yace Yana mikewa tafiya suke shuru,can dai Al'ameen ya kasa hakuri Jin yanda yakejin motsen laida a hannun Sumayya


Sumayya nikam laidan menene a hannunki Kato haka don nasan dai laida kananu basa Kara haka?


"Abu na saya"ta basa amsa


Kala baice ba suka cigaba da tafiya har suka Isa gida,Dayake sunyi wanka dazun yasa Kaya kawai suka chanja 


Yauma kwanciya sukayi tare bayan Al'ameen ya Gama kwsan rabonsa


Washe gari da safe bayan Al'ameen ya tafi masallaci, Ghana must go nasa ta bude Daman jiya ta kirga kayan jallabiya ukune sai wando da riga D'aya sai 3quiter D'aya sai armless D'aya sai gajeren wando biyu vest D'aya, kwasosu tayi ta juye a basket na dattin kayanta,sabbin kayanda ta suyo jiya ta mayar cikin bakkon ta shirye Kamar yanda kayan suke a kirge sauran Kuma ta aje sai Randa ya wanke kayansa biyu masu dattin saita musanya Masa,


 Vaseline insa da ya kusa karewa ta juye a laida daukar manda ta siyo Masa tayi ta diga a cikin gongomin kamar yanda baseline insa yake, Haka ma tamasa da sabulu


Sai 6:30 Al'ameen ya shigo gidan


Sumayya Kam ganin ya shigo d'akin da sauri ta d'auki takalmin sa ciny'ayyen ta saka Masa sabo,ta dawo d'akin,kudi  ta basa 2k yasai musu dankalin turawa boket D'aya sai k'wai guda biyar,


Fita yayi a d'akin bayan ya karbi kudin yazo ya zura takalminsa,sai Kuma ya cire da sauri,ya ringa laluben bakin dakalin Amma wayam baiji takalminsa ba


Sumayya!!ya k'wala Mata Kira


"Na'am"Sumayya ta amsa tana fita a d'akin itama


Sumayya Banga takalmina ba pls ki duba mini Mana?


"Ba gashinan a gefenka ba" tace tana kallonsa


Wannan ba nawa bane


"Nawa kenan?kadaisan banda takalmi irin wannan soson"?


Amma ni sai inaji Kamar ba nawa bane,nawa fa da laushi sosai ya kode


"Toh wannan in fa",ta tambaye sa tana mamakin fahimta irin nasa


Kamar sabo sabo,


"Hhhh lalle zaka tafi da kafa kenan tunda dai ga takalminka kace Wai ba naka ba"


Sumayya bafa Wasa nake ba Wannan ba takalmina bane 


"Nidai naka na gani atoh"tace tana komawa d'akin


Al'ameen Kam ba yanda ya iya Haka ya saka takalmin Amma har ransa yanaji ba nasa bane.


Bayan fitar Al'ameen Sumayya aikace aikacen ta na gida ta Gama ta d'aura ruwan zafi a kittle.


Al'ameen Kam bakin kasuwa  yaje ya musu sayaya ya kamo hanyar gida



Bayan Al'ameen ya dawo Sumayya ta soya dankali da k'wai sai ta hada musu tie, rufewa tayi ganin Al'ameen ya Shiga wanka


Al'ameen aban d'aki mamakine ya kamasa Jin sabulunsa na kamshi ,Amma baiyi magana ba bayan ya fitoh, d'aki ya Shiga a hankali ya bude bakkon sa jallabiya D'aya ya zare a ciki ya zaro gajeren wando da vest.


Sumayya na zaune akan kujeran tana kallonsa saka wando yayi da vest sai Kuma taga ya tsaya Yana tattaba vest in,Amma baiyi magana ba ya d'auki jallabiyar yasa,sai Kuma ya juye kayan bakkon duka a cafet Yana tattabasu.


 Sumayya!ya kirata


"Na'am"tace tana kallonsa


Sumayya wa'innan ba Kayana bane?


"Akan me zakace haka"


Sumayya wa'innan Sabine kijifa kayan kamshin sabbin Kaya suke bama Turare ba kiji da karfi fa kayan ba masu laushi irin nawa  bane?


"Nidai naka na gani"


Sumayya me Kika sayo jiya da naji laida na kayo kayo a hannunki?


"Ina ruwanka"ta basa Amsa


Indai baki fad'amin gaskiya ba toh bazan fad'a Miki wacece kamila, menene hadin mu da ita ba


Tabe fuska Sumayya tayi "Gaskiya n................


                  




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉



🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* 


🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da*  *gyara* 


🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* 


🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* 


🍀 *Na tsunguno(habil)* 

🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,

🍀 *Na d'aki(halud Al'oud)* 

 

 *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼


🍀🍀🍀 *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* 


🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* 


Contact them vie

🪀08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

        👨‍🦯MATAR MAKAHO👨‍🦯

              ~ Na ~

   🍃Rukayya Ibrahim🍃

No comments