Matar makaho 34-35

 


Page3️⃣4️⃣&3️⃣5️⃣     




Al'ameen ne, Sumayya ta gani zaune ya zuba tagumi Koh abincin Bai d'and'ana ba.


Cikin mamaki ta karaso cikin dakin"yayan Khadija lafiya kuwa"? tace tana matsowa kusa dashi  


Firgigit ya dawo hayyacinsa,  Sumayya har kun Gama kwalliyar?


"Eh mun gama,Naga bakaci abincin kaba Allah dai yasa lfy Koh" ta Kara tambayar sa.  


Lafiya Sumayya jiranki nake  in kuka Gama saimuci"ya Bata Amsa


Da mamaki sumayya ke kallonsa"banace kaci ba"? 


Sumayya na kasaci ne, kece Kika nema Kika dafa Taya zanyi na rigaki ci bayan ke kina ta faman aiki.


"Karka Kara fad'amin irin wannan magana daga yau"


Don me?ya tambaye ta


"Saboda duk abinda na baka ni gani nake kamar kaika bani mukeci banason Kara Jin irin maganar nan,Ina zaune itdakai ne badon kome ba sai don Allah,rufin asirin ka nawa ne nawa nakane"ta fada tana kallonsa


Shikenan Sumayya nagode,


"Bana bukatar godiyan ka ka gode Allah"tace tana matsowa kusa da abincin budewa tayi tasa shukali"Bismillah muci"tace tana iba 


Toh yace Yana laluben nasa shukalin


Abinci sukaci Amma cikinsu Babu Mai magana kowa Yana cin abinci ne,bare Hajiya sumy 


Suna Gama cin abincin Al'ameen ne ya tattara Kwanukan yafita dasu waje 


Sumayya Kam wanka ta shiga,tana fita tayi Alwala,kayan bacci tasa ta kwanta 


Al'ameen Jin ta kwanta yasa shima fita wajen ruwa ya Iba yayi wanka.kamar yanda yazamo musu Al'ada wankan dare kafun su kwanta,Yana fitowa ban d'akin kofar shashen su ya rufe,ya shigo d'akin,rufewa yayi a hankali yake takawa Yana laluben gadon harya iso, Hawa gadon yayi ya kwanta a hankali,


Sumayya Kam mamakine ya kamata ganin sa a hakan Sannan yahau gadon ma Bai Saba Mata yanda yake Mata ba, watoh son mannuwa kusa da ita.


A hankali ta mirgina kusa dashi hannu tasa ta Kama NASA hannun"yayan Khadija"


Cikin sanyin halinsan nan ya amsa mata, na'am.


"Menene yake damunka ne Wai" ?


Ba kome Sumayya me Kika gani?ya tambaye ta Yana Mai dagota ya d'aurata a jikinsa gabaki d'aya



"Ba kome, yauwa nace kanada National ID card ne"?


Sai dai voters card bani da National ID card


"Ok shima zaiyi Daman inason na bude account a bank ne kasan banzo da details nawa ba"


Toh shikenan Allah ya kaimu goben saina baki 


"Zaka rakani bank in? Koh naje da kaina"ta fada tana gyara kwanciyar ta akansa 


Duk yanda Kika gani goben ne Zaki bank in Koh yaushe?


"Sai na Gama lallen da akayi booking innan"


Toh shikenan Allah ya kaimu saina rakaki,in khadija taji sauki Kuma sai kuje tare kinsan me?ya tambaye Sumayya


"Ah ah"


Khadija na son zuwa bank Kamar me haka lokacin kudin covid 19 ta dameni Wai sai naje mun bude account muma,mun cika Koh zamu samu kudi,Amma da mukaje bank hanani Shiga sukayi security Wai ba'a bara a banki,Kuma su tsaya su saurare mu sunki Haka suka kuramu waje.


Sosai naji maganar ta tabamin rai"aiko Insha Allah da ita zani taga bank,Amma kaima fa Dole zamuje tare tunda account Kai za'a budewa ba niba.


Toh Allah ya nuna Mana yace Yana zura hannunsa a cikin rigan bacci dake jikinta


Jin hannunsa a riganta unexpected yasa ta zabura sai Kuma ta koma ta kwanta a hankali ta lumshe ido Jin abinda yake Mata da hannunsa a cikin riga"kasan me"?


Ah ah ya Bata Amsa


"Nikam Ina ga Zan Saida laptop Ina da waya"


Akan me Zaki saidasu toh?


"Saboda Banga amfanin suba inba kallo ba me nake dasu shiyasa Zan sayar"tace. Tana taimaka Masa ganin Yana kokarin zare rigar Tata


Umm umm Sumayya waike bazaki ringa d'aukar kwalliya kina sawa a media ba Koh Allah zaisa asamu location naki Kinga ai sai afi saninki sosai a Jala


"Kasan ba kowa keson  asa hotonsa a social media ba shiyasa ban fara posted ba,Nima nayi wannan tunanin"


Eh ai tambayan su zakinayi Zaki d'aura hotonsu kiyi Tallah Amma fa Yan Mata banda matan aure, insun Amince shikinan,tunda wasu da yawa in sunyi kwalliyar ma post suke.


"Gaskiya ne Amma waya fad'a maka ana d'aura kwalliya a online?

Kuma ya akayi kasan ana Post"?Sumayya ta tambaye sa tana kakkama Masa gashin kai Jin wani magic dake bin jikinta a sanadin abinda yake Mata


Uhmmm ai inaji ana Hira koma ni lokacin da na makance ma waya tayi araha a hannun kowa ba,Kamar yanzun


Washhhh toh,uhmm tace tana zillewa daga kansa ta sauka a gefe.


Jin ta zame yasa ya bita shima, tana kwanciya ya kwanta akanta rumfa ya Mata da kirjinsa,ya had'a fuskarsa da Tata fuskar yayi Yana tsintsinar bakinta,dake kamshi 


"Wayyo ka sauka nauye"tace tana mutsu mutsu tana damke damtsen hannunsa


Shagwaba Koh bafa nauyina na d'aura miki ba


"Nidai ka sauka,kawai tsoro nakeji"


Tsoron me?ko ni dodone?ya tambaye ta Yana Mai Kara matsota garesa


"Ka sauka"


Naki,yace Yana Kara Danna kansa akanta


"Nifa bacci nakeji kaji muye bacci"


Nikam banajin bacci


"Nikam ai inaji Koh"?


Sai kiye ai na hanaki ne?


"Amma ai ka tokareni"


Shuru ya Mata yaki kulata sai bidirinsa yake a kanta jifa jifa tana taimaka Masa 


Jin abin NASA ya fara yawa yasa ta fashe Masa da kuka


A tsorace ya mike a kanta sauka yayi gefe cikin tsoro,yake tambayar ta,ke Sumayya menene,Yana tattabata yaji Koh lfy


Saura kad'an dariya ya kubucewa Sumayya Jin yanda duk ya tsorata dagajin kukanta kawai,ta rasa ma wani irin namiji ne Mai shegen tsoro haka


"Toh ba Kaine ba nace maka inajin bacci sai matseni kake"ta fada da muryar kuka tana kallonsa tana Masa gwalo ganin yanda sai zazzare ido yake kamar kace kittt ya ruga


Shine abinda ya saki kuka?


"Eh Mana"


Toh Yi hakuri kwanta toh.


Dariyace ta subuce mata Jin abinda yace Yana kwanciya a gefenta baima mannu kusa da itaba



Cikin mamaki ya Tashi zaune Jin tana dariya, Sumayya Anya lfy kuwa daga kuka saiki koma dariya?


Shuru tayi gudun karya harbo jirginta"babu kawai ji nayi kamar jakulkule ake mini a ciki"


Shuru yayi baice kome ba illah rufe ido da yayi Yana nazarin Rayuwa yau Wai shine da Mata,Ashe haka zama da mace yakeda Dadi duk halinda kake ciki muddin ka samu mace na gari ka Gama samun Jin dadi,duk halinda namiji zai shiga mundin dare yayi zata ga tayi kokarin kauda damuwar tasa Koh Bata cireba,zatayi iyya bakin kokarin ta taga ta d'auke Masa hankali


Jin yanda Sumayya keta motse yasa shi kiranta, Sumayya!!


"Na'am"ta amsa tana gyara kwanciya


Bakiyi bacci ba?


"Umm banyi ba"


Saboda me?


"Haka kawai"


Jin Amsar da ta basa yasa a hankali ya matso gareta,lumshe ido tayi Jin yanda tsikar jikinta ke tashi,Jin gashin kirjinsa na goguwa da bayan ta


Hannu yasa a hankali ya Kama waist inta d'an zabura tayi kad'an,yasa hannu ya maidata,watoh kukan shugwaba Koh?


"Bawani shugwaba,Kuma ni ba shagwabebbiya bace atoh"


Shugwabebbiyace Mana ai duk lukutaye akwai shagwaba


"Waye lukutar"?ta tambaye sa tana juyowa suka fuskanci juna


Daga Sumayya har Al'ameen wani yanayi sukaji a tare da junan su sosai kusancin su yayi yawa akwance da suken nan


Kece Mana, lukuta kiga nan naki fa Kato,yace Yana Kama Mata bombs,

Hannu tasa ta buge Masa hannu"ai naka yafi nawa girma"


Zare ido yayi Kamar tana ganinsa,ai Dana shiga uku ai,sai wando Mai shape za'ana dinka min.


Hhhhh Sumayya ta Kama dariya "Wai wando Mai shape waya ganka kana tafiya kana murgud'asu a cikin jallabiya"ta karasa maganar da kamo hannunsa dake Kan kirjinta don wallahih kirjin zafi yake Mata 


Shi Karan kansa Al'ameen abin sai da ya basa dariya,Amma yakiye, murmushi kawai yayi,Jin ta Kama Masa hannu kafarsa ya daura Mata akan kafa.


Kokarin mikewa ta fara har lokacin hannunsa na rike a nata Wai don karya taba Mata inda bataso


Jin tana kokarin tashi yasa sa tambayar ta,Ina Zaki Kuma dare fa yayi.


"Rigata nake nema"


Kiye me dashi?


"Me ake da riga"


 Sawa, ya Bata Amsa


"Nima sawan zanyi"


Nikam gaskiya banso kawai mu k'wanta haka.


"Jikinka Koh nawa?wato mu k'wanta haka ka karasani ba"


Sorry zafi yake mikine?


"Eh Mana duk ka mammasa mini jiki"


Amma ai kinji Dadi


"Banjiba"ta basa amsa tana mikewa zaune


Ai da sauri yasa hannu ya rike Tata hannun,yana kwance  Bai tashi ba,kiyi hakuri mu k'wanta haka ba abinda Zan sake Miki.


"Ai kasan bakyau kwana ba Kaya"


Menene a jikinki Koh tsirara kike yanzun?


"Rigan fa"


Ai nace bazan miki kome ba yace Yana jawota jikinsa matseta yayi a hankali ya jawo blanket inda ke Kan kadon ya rufe jikinsu.


***********


Washe gari Kamar kullum bayan Al'ameen ya dawo sallan asuba, sunnah TV Sumayya ta kunna musu daga ita harshi in suna kwance suna sauraron wa'azi.


Sai wajen 7:3pm Sumayya ta mike shara tayi yayan Khadija ya Mata wanke wanke, ruwan zafi ta jona abuta,Yana tafasa ta juye a boker tasawa yayan Khadija nasa, ta shiga ban dakin


 tana fita yayan Khadija ma wanka ya Shiga.


Vayan sun Gama shiryawa kudi ta mika masa 1k"ka sai Mana egg's guda biyar sai bread na 500 Mai kyau ka hada Mana da butter "


Karban kudin yayi,ya fita.


Bayan ya sayo k'wai da bread, soya k'wai in Sumayya tayi ta hada musu cornflakes ga tie,jira musu tayi a kasan cafet,kamo hannunsa tayi suka zauna a kasa, bubude abincin tayi"karbi shukalinka"


Toh yace Ya karba shukalin ,tattaba plates in yayi Jin plate biyu ne ga bowl d'aya ga cups biyu,wannene abincin nawa Naga Kwanukan da yawa?


Duka zakaci d'ayan soyayyen k'wai ne d'ayan bread ne da butter a jikinsa sai Kuma bowl na cornflakes,sai cups na tie"nace Ina tura Masa plate in k'wai a gabansa"kaci kwai sai kana Had'awa da tie ga bread"


Shikam Al'ameen ya kasa magana Wai karyawane da abinci Kala uku shi Al'ameen,ganin Al'ameen bai fara ci ba ita har tayi Rabin cup na tie inta yasa ta aje kofin,hannu tasa a cikin k'wai in ta yagi babba ta tura Masa a baki


Shikam Jin abinci a bakinsa da Kuma yatsarta sai faman tura Masa take yasa sa cizon yasan kad'an,


Ai Kara ta sake hade da yarfa hannun nata"wayyo yatsana jini jini yake na bunu tace tana duba hannun".


Da mamaki Al'ameen yace jinii ma Sumayya?


"Eh gashi shikinan ya gusuramin yatsa"


Mu gani


"Bazaka gani ba sai kace idone da kai"


Toh muji.


Bazakaji ba din,tace tana daukar kofin shayen ta


Jin tayi Shuru yasa sa gutsurar bread Mai butter,Wai zai Bata itama d'ayar hannun nasa yasa ya lalubo fuskarta,Jin fuskar Tata yasa ya fara lalubar bakinta da hannunsa


"Kasan Allah Inka samin hannun hagunka a bakina ba"tace ganin Yana ta tattaba Mata baki da hannun nasa


Kayya abinci Zan baki,yafada Yana Mika Mata gutsuren bread inda ke hannun damansa a baki,


Rufe bakin tayi Taki budewa.


Shikam sai goga Mata bread in yake a lebe gashi duk butter ya Bata Mata fuska


"Kanata Bata mini fuska da butter"tace bayan ta rike hannunsa


Toh ba kinki bude bakin ba sai kokari nake,


Kaga kaci abincin kan, ka barni naci nawa,tace Masa tana goge fuskar ta 


Toh ki bare na baki wanann kawai kinji


Ganin yanda ya nace Mata yasa ta bude bakin Yana saka Mata bread in da sauri ta datse hakorin ta,Wai don ta cije yatsarsa shima abin mamaki da sauri taga ya cire hannunsa kafun ma hakorinta ya Sauka akan yatsar,Yana dariya


Ai Daman nasan saikince Zaki Rama shiyasa Nima nayi taka tsamtsam da yatsana.


Shuru ta Masa Bata tanka masa ba.


Haushi ya shigane bakutuwa?


Kara ta sake tayi kansa "nice bakutuwa"


Jin ta hafto, yasashi Kare kansa, hannu yasa ya tare fuskarsa.


Ganin haka sai abin yayi mugun Bata dariya waishi harga Allah tunani yake wani abin zata Masa haryana tare fuska.


Jin shuru baiji tayi Masa kome ba yasashi fara laluben ta Aiko ya jita a kusa dashi,da sauri ya rikota, sorry kinji


"Ni......shuru tayi Bata karasa ba Jin sallama a kofarsu amsawa tayi ta mike kaci abincin kafun na dawo"


Toh yace Yana saka hannunsa ya d'auki cup inda ta aje masa...


Sumayya tana fita taga wata budurwa irin classic innan zata Kai kusan sa'ar ta kyakkyawace Amma baka Tasha kwalliya tana rataye da school back "sannuki da zuwa"tace Mata tana shimfid'a musu darduma"Bismillah ki zauna"


Yauwa Ina kwana?bakuwar tace tana zama akan sallayar


"Lafiya ykk ya gida"?


Lafiya Alhamdulillah,ya aiki?


Lafiya klau,Ina zuwa Sumayya tace tana mikewa d'akin ta shiga ta hada cornflakes da ruwa  Daya a fijrij ta hada a tire ta kawowa bakuwarBismillalahih ka  abin Kari ba nauye Kam"tace tana ajemata a gaba


La d'awainiyane haka Allah dakin barsa yanzun na fitoh gida zanje school ne ma nace bara na biyu dai ta gidanki


"Allah sarki Amma dai ki saka Koh albarkane yafi dai kikici bazanji Dadi ba"


Shikenan bara dai NASA albarkan tunda kin Masa tace tana iban cornflakes in da shukali uku tayi tace Alhamdulillah


"Badai harkin koshi ba"?


Alhamdulillah wallahih ya isheni,suna na kamila Ina zaune a unguwan gadi,Daman nazone wajen ki in Babu damuwa inason zan fara Training in make-up,Naga wanda kika ma kanwata a auren Asma'u shine nace tamin kwatancen gidanki  inyaso sai nazo inji.


"Toh gaskiya ni bana koyarda make-up saboda bani da shago sai gidana Kinga Kuma Ina da ayyuka yau da gobe"tace Mata tana tunanin ta yarda ne Koh karna yarda


Ba damuwa sister Nima Ina zuwa school Kinga saiki bani time inda zanna zuwa Koh ki ban number ki duk lokacin da kike free sai ki kirani Koh Kika samu Yan make-up.


"Shikenan yanzun dai ki bare Inna ma mijina magaa in ya Amince xakiji daga gareni"


Ok ba damuwa saiki bani contact naki Koh in ba damuwa sannan nawane kudin da Zan biyaki Kinga Inna koma Koh yaushe Kika kirani saina tawo dasu


Toh, make-up dai kashi kashine sanann yanayin kwakwalwar mutum wata a wata D'aya zata koye make-up wata biyu wata fiye da uku ma Bata iyya ba so ni bansan ya yanayin d'aukar kwalliyarki ba Amma dai inso samune wata uku kina koya"


Ok yanzun wata ukun nawa ne kudina


"50k Koh wani wata kudinki na wata uku 150k kenan"


Wai habba sister kudin nan yayi yawa Mana dubu dari da hamsin,


Gaskiya kenan Kinga a cikin kudin Zan Saya make-up kit sabo duka,saboda bazaiyu Ina baki na aikina kina koya dashi ba, sanan infa kika iyya a kwana uku Zaki iyya samun sama da kudinda Kika biya na koyo"


Hakane Kam Amma dai ki duba ki rage mini kinsan baban mu yace in zaiyu nida kanwata zai biyawa.


"Shikenan Zan rage dubu goma"


ok shikenan an gode saina jiki


Shikenan bara na baki number,daidai lokacin Al'ameen ya fito d'akin hannunsa rike da cup inda yasha shaye


What?? wa nake ganin nan Kamar  Muhammad Al'ameen Yusuf bakuwar tace tana zare ido


A matukar razane har bakin sa na rawa yace kamilaaaaa...........




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉



🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* 


🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da*  *gyara* 


🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* 


🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* 


🍀 *Na tsunguno(habil)* 

🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,

🍀 *Na d'aki(halud Al'oud)* 

 

 *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼


🍀🍀🍀 *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* 


🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* 


Contact them vie

🪀08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

🧑‍🦯MATAR MAKAHO   🧑‍🦯  

             ~ NA ~

🍃Rukayya ibrahim🍃


✨Tsokaci wanna shine novlel na farko Koh da z a ga mistake ko typing error Amin afuwa👌 


Free book🤧

 

  *🍀wanann  shafin sadaukarwa ne gareki haj Aisha Ahmad Allah yabar kaina🍀*

  

No comments