Matar makaho 32-33

 


Page3️⃣2️⃣&3️⃣3️⃣  




Keke napep na sayar ban kulasa ba


Hajiya Ina Zaki?Mai napep in ya tambaye Sumayya.


"MEGA restaurant" na basa Amsa


Ok hau muje


Sumayya restaurant Kuma?Koh dai banji daidai bane? Al'ameen ya tambaye ta


"Daidai kaji,yau agun zamuci abincin dare,banyi girki ba"


Sumayya ai akwai wajen Saida abinci Koh round about ana sai dawa basai munje restaurant ba.


"Nidai gun zamu Kuma sai kaje"   


Wai hajiya bazaku hau bane? Koh nayi tafiya tane? ,kun tsaidani Kuna Bata mini lokaci ga dare nayi  


"Yi Hakuri.

 yayan Khadija muje"  nace Ina Kama hannunsa muka shiga keken        


 A MEGA restaurant, Mai keke ya saukesu


Biyansa nayi kudinsa bayan mun sauka,Kama hannunsa nayi muka shiga ciki,


Al'ameen Kam binta kawai yake baida baki ,sai dai yaji sun shiga wani waje Mai mugun sanyi sai Kuma D'an motsen jama'a d'aid'ai ku


Har lokacin Ina rike da hannunsa,D'aya daga cikin kujerun dinning table dake wajen,na nufa ja Masa kujera nayi"ka zauna"nace Ina zama a nawa kujeran


Ok , yanzun cikin inda muke nan shine restaurant in? ya tambaye ta Yana zama


"Eh Mana Hala baka taba zuwa ba"?


Nasan restaurant Amma bana shiga.


"Toh yau ka shiga"


Waiter ne yazo, sannunku da zuwa mega restaurant,ga list nan ka duba abinda za'a kawo muku,yafada Yana mikawa Al'ameen Takardan hannunsa


"Yauwa bani Anan"nace Ina karban list in.

"Me za'a kawo maka"? 


Duk abinda kike so, Al'ameen ya Bata Amsa


"Tamabyar ka fa nayi"


Amsa na b'aki 


"Ok toh a kawo maka tuwo Koh shinkafa Koh doya"?


Aban doya 


Ok,mikawa waiter in nayi hade da basa amsa"ka kawo plate biyu D'aya na doya da miyar kaza,D'aya Kuma fried rice with chicken  yaji vegetable sosai,in Kuna da exotic a had'a mana da ruwa"


Ok ma, an gama,ya karbi takardan in ya wuce


Sosai mutanen restaurant in suka bisu da ido tun shigarsu kowa yake gulman su da ido wasu Kam har kasa hakuri sukaye sunayi da baki,abin mamaki ya Basu ganin matsiyacin MAKAHO Koh suturar arziki Babu a jikinsa,mace Kamar Sumayya tana rike da hannunsa Koh tantama Babu daga ka gansu kasan ma'aurata ne,Amma kallo D'aya zakama Sumayya kasan ba karamar classic bane 


Bayan an kawo Mana abincin,tura Masa nayi nasa a gabansa shukali na Mika Masa"ungo shukalinka abinci na gaban ka"


Abinci muka faraci a nitse idon mutane na Kan mu sosai har abin ya takurani


Sumayya!!


"Na'am"


Nikam wajen nan akwai mutane sosai ne?


"Eh akwai Amma ba sosai ba kasan yanzun dare ne"


Amma dai kallon mu suke koh?


Mamakine ya kamani Amma na maze, "ah ah ba Wanda ke kallon mu kowa harkar gabansa yake,Amma meyasa ka tambaya"


Jikina ya bani ana kallo nane tunda muka shigon nan


"Aiko ba Wanda ke kallon mu",na basa amsa


Taima ke kike kallona.


"Akan me Zan kalleka Kuma"😒?


Waya sani Koh kyau na Miki,Kinga dogon hanci


"Ina abin yake bare a yabasa"


Abinci muke ci muna Hira har muka Gama Amma dukan mu bamu cinye duka ba,

list aka akawo mana,na duba kudin mu dubu 3,800 ne, bude Purse nayi nabiya kudin, ordern ice cream nayi aka Mana takeaway a laida



Mamakine ya Kama Al'ameen yanzun abincin da sukacin nan shine 3800 ,ai cefenen dubu uku da dari takwas zai musu wata ma suna dafawa.


Suna fitowa a restaurant in ganin titi ba napep yasa Sumayya duba wayar ta


Karfe 10:3 na dare ne,"asaifa mun jima a wajen nan 8 fa Muka bar gida"


Gaskiya Kam Kuma bana majin dirin machine sai mototi


"Ba machine Kam sai dai mu taka da kafa"na basa amsa Ina Kama hannunsa muna tafiya inda Allah ya somu ma tsakanin sintali da mega ba nisa sosai 



"Nikam azumi saura wata nawane"?


Saura sati nawa dai?ya Bata Amsa


"Satitika kenan baikai wata ba?Ashe shiyasa aketa aure aure"


Gaskiya Kam saura sati uku da kwana hudu


Lalle kam,"kasan yanzun haka gobe, za'a yi bud'an kan Amarya da yamma,sai ayi fitan Angonci duka,da dare Kuma dinner,Kuma nice duka Zan musu kwalliya, shiyasa nake son in Allah ya kaimu gobe sai ka nemo mini yaro yaje Mana kasuwa Ina son Gama girki da wure"


Yaro Kuma wani yaro.kike ga Zan iyya aika a unguwan mun nan har kasuwa ,sai dai naje kawai tunda khadija ba lfy.


"Toh Allah ya kaimu,ni chemist ma nakeson mu shiga nasai maganin gajiya,Amma dare yayi"


Ah ah Sumayya da kankantan shikarunki karki Bata shi dashan maganguna, don kina aikin gajiya,in Kika riga Kika saba,toh zai biki Koh yaushe kikaye aiki sai kinsha 



"Gaskiya ne Amma wallahih bayana ya tokare ni sosai,gashi yanzun ma sai tafiya muke da kafa"


Da kafa suka taka har sintali suna tafiya suna Hira,Dayake gidan Adara ba'a rufesa Koh karfe d'ayan dare ne yasa suka samu kofa a bude,


Shigan su, suka shige shashen su bakin su d'auke da sallama


Al'ameen ne ya bude d'akin 


Muna isa ruwa na iba duk yanda nake tsoron toilet in dare yayi Amma zafin da nakeji Bai barni naji tsoron ba,

band'akin na shiga na kwara ruwan na fito,

d'akin na shiga.


Al'ameen na zaune a Kan kujera Yana jiran Sumayya ta fito shima ya shiga Wanka don yaukam ba NEPA an d'auke


"Assalamu alaikum"nace Ina shigowa d'akin


Waalaikumu salam, gaskiya yau Kam Alhamdulillah akwai.zafi Kam


"Gaskiya ni a waje ma zanyi shimfid'a yanzun"


Ok.bara nayi wanka daidai kinyi shimfid'ar?yace Yana fita a d'akin ban d'aki ya shiga bayan ya ibi ruwan shima


Yayan khadija na fita na saka.kayana saboda zafin da ake have vest na saka ,da wandon bacci fankalele shara shara har kasa,kayan shinfid'a na fitar na shinfid'a mana darduma a baranda na shinfid'a zanin gado da filoluka, kwanciya nayi a gefe tsabar gajiya Koh hula ban saka ba,bayana sai damuna yake koh bacci na kasa.


Yana fitowa d'akin ya shiga 3quiter yasa Koh riga baisa ba ya rufe kofar, ya nufi inda yake kyautata zaton agun ta musu shimfid'a



Ina kwance Ina kallonsa harya matso inda nake kwance hannu yasa ya tattaba shimfid'ar sai Kuma ya fara laluben Kan shinfid'ar  bayan ya xauna.


Jin ya tabata yasashe Hawa Kan shinfidar kwanciya yayi a Gefen pillow n da ta d'aura kanta akai


"Bakaji pillow da na aje maka bane"


Naji Mana Amma a naki nakeson kwanciya


"Kaga ka rabu Dani jikina ciwo yake mini"


Hannu kawai naji yasa a bayana Yana mammatsa mini baya,naso hanasa amma Jin yanda message in ke kauda tsamin da bayana yake mini yasa nayi Shuru


Yana ta mamatse Mata baya da kafa duka har yaji tayi bacci, gyara Mata kwanciya yayi,daga kefuwarda tayi shima ya kwanta a Gefen ta bacci ya d'aukesa.


Misalin karfe biyu na dare ya farka Jin iska na kad'awa ga kamshin kasa na tashi bude ido yayi sosai, ya mike zaune hannu yasa ya taba Sumayya Aiko tana kwance Koh juyawa Bata sake ba tun gyarata da yayi, Sumayya!! Sumayya!!



"Ummmm menene"nace cikin magagin bacci don harga Allah yau dai baccin gajiya nake



Ana iska ga hadari,ki tashi mu shiga d'aki


"Da wani idon kaga hadarin ni wallahih ka barni nayi bacci",na fada Ina gyara kwanciya


Sumayya ruwane fa da gaske


Shuru na Masa abina na koma bacci 


Jin Taki tashi yasa ya mike key ya d'auka ya bude d'akin, d'aukarta yayi a hannu a hankali yake tafiya Yana lalube harya shiga da ita d'akin,Kan gado ya haura ya kwantar da ita,Jin an Soma yayafi da sauri ya fitoh a d'akin shimfid'ar su ya tattara ya Kai d'aki randar robansu ya zubar da ruwan ya hada da bokataye ya jejjera a bakin baranda,daidai lokacin aka fara ruwa sosai Kamar me .


Alwala yayi ya shiga d'akin sallaya ya d'auka ya shimfid'a wa yayi ya Tada kabbara,lafilfilu yake har kusan karfe uku na dare kafun ya kwanta shima a gefenta 



 *Washe gari*

Kamar kullum yaukam da safe kudi na basa yasai Mana manya manyan gongomin Madara da bornviter  na sai suga Rabin kwano Lipton kwali d'aya na had'a da cornflakes,dashi muka karya ya fita



Al'ameen kam yasan baida abinda zaiyi haka ya fita yaje ya zauna a bakin titi ya rasa mafita Allah ya gani Yana iyya bakin kokarinsa wajen niman abinda zai rufawa kansa asiri,Amma abin yaki yasan kome na Allah ne Kuma Bai manta dashi ba a hakan ma yana kara godewa Allah tunda Sumayya nada rufin asiri da ace Bata sana'a a war yanzun da kayan abincin ta ya fara karewa baisan yanda zaiyi ba.



***********

Khadija ce ta shigo bayan sallan azahar lokacin Ina kanwa matan da suka zo make-up, Assalamu alaikum


"Waalaikumu salam" dukan mu muka amsa Mata


"Ah ah khadin Goggo idonki kenan"?nace Ina kallonta sanye take da atamfar dana Bata riga da zani sai gyle da takalmi harda jaka sai laida Mai tambarin asibiti a hannunta sosai tayi kyau fuskarta tayi fayau alamu dai batajin dadi,abinka da farin fata


Wallahih Aunty na fitoh asibitine nace bara dai nashigo yau Goggo takece mini kun shigo da dare Ina bacci.


"Eh wallahih mun shigo da yayanki nace abarki kawai kar a tasheki"


Allah sarki,tace tana gaida matan dake zazaune suna jiran na Gama wa Wanda

 nakema make-up 


"Khadija ki shiga d'aki Mana akwai NEPA ki jona kittle akwai kayan shayi asaman freezer"


Aunty bazan iyya shaba bakina ba dadi Sam shiyasa koh abincin dare ban iyya ciba Haka karyawa ma.


Ah ah khadija dadai kin daure kinsha shayin Daya fi Amma ace bakinki ba Dadi saiki kicin abinci,ai ko magani in ba abinci baya aiki,D'aya daga cikin customers nawa ta fad'a


"Gaskiya ne  khadija,ki shiga in kinsha saiki kwanta ki huta"


Toh Aunty tace tana shiga d'akin, kittle in ta d'auko ta zuba ruwa ta jona,shayi ta hada kad'an ta iyya Sha ta balle maganin Tasha  kwanciya taye  lokaci D'aya bacci ya d'auke ta



Sai kusan 4:30 na Kamala wa sauran kwalliyansu Daman Amarya tun 3 na yamma na Gama Mata saboda bud'an Kai,


Gaskiya yau  na damki rabona mutane kusan goma nama makeup heavy make-up

Simple make-up

Light make-up

Duk yau ba Wanda banyi ba sosai na samu kudi 50k yau na damka nan ma banyi na dinner ba kenan.


Misalin karfe biyar khadija ta mike zata wuce gida Aunty nikam Zan wuce sai gobe 


"Toh khadija Allah ya Kara lafiya ga wannan ki D'an samu abinda kike bukata ki Saya dashi" nace Ina Mika Mata 10k


 Aunty ki barshi kawai d'awainiyar tayi yawa jiyama fa Goggo tace mini kun kawo Mana 5k naje asibiti danaje in ma,Ina saurayin da nace Miki yazo guna?


"Eh na tuna har kikace bazaki fita ba"na Bata Amsa


Ashe Dr ne Ina zuwa na gansa shine ya sayo mini magani  kyauta,


"Allah sarki, Allah ya saka Masa da alkhari"


Ameen Aunty


"Wancan yayan kine ya baki wannan Kuma nawane,ki karba khadija kid'an Saya Abubuwan da baki dasu"


Gaskiya Aunty nagode Allah ya saka da alkhari,tasa hannu ta karbi kudin


"Ameen khadija"


Yauwa aunty nace Koh Zaki aje mini tunda Naga azumi ya kusa Inna tashi zuwa kasuwa saina karba naje na sai kaya,samun na samu dinki da wure?


"Ah ah khadija insha Allah, Allah zai Bud'a Mana har yayanki ya sai Miki kayan Sallah, wannan dai ki sai Abubuwan bukata irinsu kananan Kaya da mayuka Turare pad omo sabulu ke dai irin Abubuwan bukatar Yan Mata haka"


Toh shikinan Aunty Daman bani da kananan Kaya sai na saya pant biyu Brz sai vest shima biyu Amma na gwanjo Zan Saya aunty sauran chanjen, Ina materials da ake yayi yanzun ana yankawa a dinka dogayen riguna dasu?


"Eh khadija"na gane su 


Yauwa yadi d'aya dari uku su Zan Saya kala biyar na dinka 


"Gaskiya khadija kinye tunani Mai kyau kema saiki samu na chanjawa kwana biyu"


Toh Aunty Zan tafi nagode Allah ya Karo customers


"Ameen khadija yanzun ma wasu na zuwa da dare maganar dinner aike alkhari ce tunda sanadin ki nake samun kudin"


Ah ah Aunty Allah ne ya tsaga da rabonki , shiyasa kike ci


"Hakane Kam khadija" nace Ina shiga kitchen da sauri nake na d'aura Mana abincin da zamuci


Bayan fitar khadija girki na Gama na juye Mana a kula,sai goshin mangari ba yayan Khadija ya dawo


Sumayya sannu da gida?


"Yauwa sannu yayan Khadija sai yanzun"


Eh wallahih ya aiki?


"Lafiya klau" nace Ina kallon sa ganin Kamar a cikin damuwa yake


D'azun Bashir wani makwancin mu ke tambaya ta Wai MATAR sace taji labarin Wai kina lalle ke kikama Asma'u na aure shine Wai yake tambaya ta zata samu lalle gobe,make-up jibi da Rana?

nace ya bari saina tambaye ki inyaso in mun hadu a masallaci anjima na fad'a Masa amsar ki.


"Lallen me za'a ma MATAR tasa"?


Suna ne haihuwa tayi jibi suna


"Gaskiya nifa bazanje home service ba,in mutum nason lalle Koh kwalliya yazo ya same ni a gidana"


Amfa Sumayya haihuwa ne ya za'a yi mace maijego tazo lalle gidanki?


"Wallahih yayan Khadija ni raini ne banaso a rayuwa na kar mutun yaga kaje Masa lalle ya Raina ka" 


Kai Sumayya ba wani raini ai sana'a ce ta kaiki ba maula ba,ki daure kije ki Mata kinji?


"Shikenan Allah ya kaimu goben Amma bansan gidansu ba da yamma ta tura yaro yazo ya kaini"


Sumayya har yamma?ya tambaye ta


"Eh man saina Gama aikina,Koh so kake na tafi da safene,jibine fa sunan"


Toh shikenan Allah ya kaimu yace Yana mikewa ,ruwa ya ibo a boket ya shiga bandaki


Muna idar da sallan mangariba Koh abinci bamu ciba Yan make-up na dinner suka zo su biyar ne dukansu harda Amarya heavy make-up suke so,Dole tasa na hakura dacin nawa zuba Masa nayi na d'auko Masa ruwa a freezer na jira Masa,a d'aki na fitoh waje,don ni bana saka baki a dakina Sam kowa ya zauna a waje kawai


Sai da yaye isha'i kafun ya shigo gidan, gaisawa sukaye da customers nawa,don na fahimci yanzun mutane na ganin kirmansa tunda kofarsa suka shigo


"Abincin ka na d'aki yayan Khadija"nace Masa ganin ya nufi d'akin kar yaje ya zubar da abincin tunda a kasa na jira.


Toh yace Mata Yana shiga d'akin


Make-up na Amarya na fara, Gamawa ta biyani akazo aka d'auketa saura hudun ma duk na Gama musu kafun 9:00,kudin da suka bani 25k Inna hada Dana d'azun kusan dubu saba'in na samu kenan Alhamdulillah yau kawai na tashi da kudi dubu sittin da biyar in aka cire 10k Dana bawa khadija


Wani tunanine ya fado mini akan kudin, murmushi kawai nayi na nufi d'akin

Ina bude labulin idona ya sauka Akan plate inda nasama yayan Khadija abinci nakai dubana garesa da mamaki ganinsa a..............





 *My Real and special Fan'S* 


 *Princess* 🏵️

 *Maryam najibu* 🏵️

 *Mummy*🏵️ 

 *Shamsiyya Gombe* 🏵️

 *Ummu na'eem*🏵️ 

 *Faeexetion* 🏵️

 *Zainab*🏵️ 

 *Bebi* 🏵️

 *Maman khairat*🏵️ 

 *Oum Abdullahi*🏵️ 

 *UMSAD INCENSE* 🏵️

 *Ummul husnah*🏵️ 


 *Duk Naga comments naku Allah ya bar kauna Nima Ina yinku* 🏵️🏵️



🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉



🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* 


🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da*  *gyara* 


🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* 


🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* 


🍀 *Na tsunguno(habil)* 

🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,

🍀 *Na d'aki(halud Al'oud)* 

 

 *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼


🍀🍀🍀 *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* 


🍀🍀🍀 *Suna  bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* 


Contact them vie

🪀08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense



🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧     


🍀 *Wannan shafin  sadaukarwa ne gareki haj j Aisha Ahmad Allah yabar kauna* 🍀

No comments