Matar makaho 30-31

 


Page3️⃣0️⃣&3️⃣1️⃣

Ji kawai nayi ya rumgume ni ta baya,




zare ido nayi jinsa shima ba riga,mannani yayi da jikin kofar shi koma ya rumgume ni sosai ya d'aura kansa a kafad'ata


"Wai menene haka don Allah" ?


Dadi ne,ya Bata Amsa


"Dad'au matau"    


Jin Amsar da ta Bashi yasa ya juyo da ita da karbi ya rungume ta


Ware ido nayi jina sukutum a kirjinsa dukan mu ba riga


"Wayyo Allah meye haka" 


Mele,shima ya Rama


"Nikam.ka sakeni"   


Bakinsu ya hada,a hankali yake kissing in lips nata na sama


Bansan garin Yaya ba Koh yaushe ba na tsinci kaina da Kama lips nashi na kasa Nima na shiga tsotsa


Jin ta Kama Masa lips yasa a hankali ya zame bakinsa cikin nata,ai da sauri yaji ta kamo kansa ta sake maisa bakinsa cikin nata 


Sosai suka shiga farantawa junan su Rai ,


ba zatoh Koh tsammani   muka zube a kasan cafet,nice a sama shi koma a kasa,


da sauri ya birkitota kasa Yana lalube da D'an kokarinsa zai zame Mata wandon baccin da ke jikinta


Da sauri na Kama hannunsa Jin aika aikan da yake so yayi


Don Allah ki bari musamu nutsuwa


"Nidai wallahih ah ah"


Please kinji


Kokarin mikewa na fara a jikinsa,


Da sauri ya kamota,Ina Zaki


"Anafa Kiran sallah"   


Sakinta yayi Jin da gaske Kiran Assalatu ake


Mikewa nayi a hankali daga jikinsa Jin ya sake ni,"d'akin ba haske fa"

 

Ki kunna glop Mana


"Bana gani" 


Ok bara na lalubo glop in


"Toh,Ina rigana"?


Bara na kunna wutan sai ki duba,yace Yana mikewa daga kasan cafet


Mikewa yayi Yana lalube ya Isa wajen makunnen NEPA ya kunna


D'akin ya gauraye da haske,da sauri na rufe kirjina da hannu sai koma nayi tsaki tunawa da nayi bama gani yake ba


Menene kike tsaki kuma?


"Banga rigana ba"


Riga Koh vest?


"Oho"


Wai kikam wace irin matane Mai tsewa


"Green in Mata ka aura"


Toh Green Sumayya,mu fita kar ashiga sallah?


"Kai ka fita Mana Koh na d'aureka ne"


Toh Green sumy


Lalle mutumin nan ya Raina mini wayo,ji kawai nayi ya kamo mini hannu Yana kokarin fita Dani a d'akin cikin lalube


"Ban saka rigaba ka sakeni Mana pls"


Sakin ta yayi Jin Wai Bata da rigan da gaske


Bayan fitar shi rigana na d'auka na fitoh Jin harya kammala Alwala ya wuce masallaci


Bayan idar da sallah dukan mu bacci muka koma 


Misalin karfe 7:00 na safe aka doka Mana sallama a kofar d'aki,bude ido nayi a hankali ganin Yana kokarin sauka a gadon yasa na gyara kwanciya


Amsa musu yayi ya zura jallabiyar sa ya fitoh,


Ina kwana yayan Khadija?


Lafiya Alhamdulillah


Gun Aunty Sumayya mukazo,Yan matan sukace


Ok,bara na kirata yace Yana komawa d'akin


Hawa gadon yayi,ya yaye blanket inda ta rufu 


"Menene"?


Baki kikaye,Kamar Yan lallen ne fa


"Gaskiya bazan tashi ba suje su dawo anjima"


Ah ah Sumayya wulakanci ba kyau ki lallaba dai ki tashi kinji Green sumy


"Wallahih Inka sake fad'amin sunan nan Mai rabani da Kai sai Allah"


Me Zaki mini ai Babu abinda Zaki mini sai abinda Allah yaso


"Hmm" kawai nace na mike,fitowa nayi na shimfid'a musu darduma muka gaisa Yan matane guda biyu Amma ba kawaye bane,

"ban fa Saya lalle jiya ba bansamu D'an aika ba gashi 8:00 ake bude kasuwa Koh zaku karba kuje ku sayo"?


Eh Daman mu biyu mukace bara muzo kafun a Gama Mana kafun sauran su karaso,ba damuwa a bamu kudin bara muje mu sayo in 


"Ok bara na kawo muku kudin"dakin na shiga na d'auko musu kudin,suna fita wanka nayi na kimtsa kofata yayan Khadija ya ibo Mana ruwa,


Shinkafa da wake dafa duka na dafa Mana direct harda na Rana 


Bayan mun karya fita yayi, ni Kuma muka fara lalle,

Sai kusan 3 na karasawa matan lallen su dukansu su bakwai kowa hannu hannu na Masa ja da baki,sai kwalliyar walima 


Gaskiya yauma ba laifi na damka kudi Mai tsoka sosai..


Naso.muyi cefene Amma yau khadija batazo ba ni koma ba fita nake ba bare na aiki yaro


Yayan Khadija Kam Yana fita yaje ya bude mangoron sa duk sun rube haka ya zubar dasu don Koh ya bude ba Saya za'a yi ba haka yayita zama har yamma don yasan tabbas Sumayya zata sama musu na abinci Amma yanajin kunya ace kullum ita ke ciyar dashi 


Haka yayita zama sai mangari ba ya mike bayan yaje masallaci ya kamo hanyar gida jiki a sabule


Bayan sallar mangari ba ruwa na Ina na shiga wanka


Yana shiga gidan da sallama ya shigo kofar Jin shuru Bata Amsa ba ya zata Koh tana d'aki ne,ruwa ya Iba ya shiga ban d'akin


Goga soso nake a zaune kawai naji mutum ya shigo bayan gidan


A matukar tsorace na kwana Kara,"wayyooo"


Shikam zuciya D'aya ya shiga bandakin Bai d'auka tana ciki ba shiyasa ihun yazo Masa unexpected,yasa ya gigice, Sam Bai d'auka dalilin shigarsa bane yasata ihun,d'auka  yayi Koh wani mummunan abune ya same ta


Subhanallah Sumayya lafiya? yade?

yace Yana matsowa inda yaji ihun nata


"Wallahih Inka zo inda nake saina kwara maka  ruwan nan",nace cikin tsawa Ina d'aukar bokatin ruwan wanka na in,damuwa na kawai na ja towel inda na makala a saman kofar band'akin,na d'aura


Sai yanzun ya gane dalilin ihun nata,manna Mata hauka kawai yayi ya Kama cire riga


"Wallahi ka fita a toilet innan na ratse Zan kwara maka ruwan nan",duk tabi ta rikice


Ikon Allah waini idone Dani bare na kalli abinda kike boye wan


Kuturu,kawai nace,Ina daga boket in ruwan ganin Yana matsowa inda nake


Jii kawai yayi shaaaaaaaa Sumayya ta kwarara Masa ruwa,Bai d'auka da gaske take zata kwara Masa ruwan ba,


Nikam ganin Yana ta faman sharte ruwan fuskar sa yasa,na ruga zanyi waje da gudu Koh Kaya bansa ba ,


Ai.jin gudunta yasa ya bita shima da gudun 


Ina kokarin fita a band'akin kawai naji ya jawoni ciki, Allah yasa Ina kusa ta towel jawosa nayi a hannusa


Wallahih Sumayya baki Isa ba ki kwaramin ruwa Kuma ki.gudu


Ganin fa na shiga hannu,inda Allah yasoni ma na d'aura towel in"don Allah kayi hakuri yayan Khadija kuskure ne"


Kuskure ai baki isaba kinji na rantse


Kuka na fara ganinsa in yaci serious,Babu Wasa a fuskarsa da gaske yake b barina zaiyi naci bulus ba

"To Kayi hakuri"


Naki,ke Inna Miki Abu ai baki hakura


"Wallahih inayi kaji yayan khadija"


Bazanfa hakura ba malama


To me koma Zan maka Koh dukana zakayi ne?


Ah ah wanka Zaki mini


"Wanka"😳?


Eh Kinga Daman ba gani nake ba kullum.bayana baya fita


"Nima ai bana ganin bayana kuma ni ban iyya ma manya wanka ba"


Ah ah kina kallo Mana,Kuma Zaki koya


"Wallahih ni banason irin abinnan,  nace maka ka sakeni kanaji fa ana Kiran isha'i Kuma sai magana kake sani a bayan gida kasan ba kyau fa"


Tsakanin nida ke waya fara magana a ban d'akin nan tunda ba idone Dani ba, ba kallo Miki abin zanyi ba me na ihu harda kwara mini ruwa🤥


"Toh kayi hakuri kaji yayan Khadija wallahih mantawa nayi baka kallo"


Da gaske kina mantawa bana gani?


"Eh sosai ma,ai ba kowa.ke.ganinka yasan baka kallo ba"nace don ya barni


Ok wayo Zaki mini kenan harda wani yabona toh naki wayon in Kinga na barki kin fita toh kin zabi Daya a cikin ukun nan,

Koh ki wanke mini baya

Koh ki wanke mini Kai

Koh ki haske mini gemu


Lallai mutumin nan yaga wajen baccina nice ma Zan wanke Masa baya Kai Koh aski,


Toh Zan maka aski Amma sai gobe kasan yanzun dare ne bazaiyi kyau ba gashi ba NEPA Kai Kuma bakada shaver"


Kinyi Alkawari Zaki aske mini gobe?


"Eh"


Toh wanke mini


"Toh,ka sake mini hannu Mana saika zauna na wanke maka"


Na sakeki ki gudu


"Allah bazan gudu ba"


Ban yarda ba


Yace Yana Jan hannuta,ya zauna akan kujiran hannunsa na rike da nata


"Toh a hakan Zan wanke maka Kai kana rike da hannuna"


Ai Inna sakeki nasan guduwa zakiye


"Allah bazan guduba"


Toh tunda kikace Allah na sakeki,yace Yana sake Mata hannu


"Ina abin wanke Kai in"?


Gashe yace Yasa hannu a k'wandon soson nasa ya d'auko guntun soda,gashi nan


"Kana nufin da soda Zan wanke maka Kai"?


Eh man ba Yana kunfa da cire datti ba


"Uhmm Ina zuwa",nace Ina kokarin nufar kofar band'akin


Kinye alkawari fa Zaki wanke mini,shine kike son gudu


"Abu Zan d'auko na dawo"


Toh yace Yana kokarin cire jikekken rigansa


Ina fita a band'akin na shiga d'aki bude akwatina nayi na d'auko Abubuwan wanke gashi, na Mata masu kyau da shaver,na dawo ban d'akin wayata na kunna na jinginasa da jikin gini matsowa  nayi inda yake zaune daga shi Sai wando dogo na jeans


Rangwafawa nayi na fara wanke Masa gashinsa sosai na zuzzuba Masa Abubuwan wanke Kai gashinsa mai yawa irin na Fulani,sosai ya fita nasa Masa Abubuwan laushin gashi cikin Yan minutes gashinsa yayi masifar kyau, shaver da na d'auko na saka Masa a fuska zan aske Masa gemu


Ke sumayya ragewa fa zakiye ba askewa ba 


"Na sani ai"nace Ina gyara Masa gashin gemun


Ina Gamawa nace NASA"ka duba Koh yayi"


Ina Naga idon dubawa sai dai na taba,ya Bata Amsa Yana tana fuskar sa, gaskiya kin iyya gyaran fuska


"Uhmm kasan me"?


ah ah saikin fada


"Ai.......ban karasa ba Jin ana kokarin shiga masallaci sallan isha'i yasa ban karasa maganar da nakeson Yi ba,

"kaYi sauri ka kwara ruwa ana shiga sallah"Ina maganar na fita a band'akin


Jin fitarta yayi wanka shap shap ya tafi masallaci


Yana fita ruwan wanka na Kuma ibo wa na Shiga band'aki,Ina wanka inata tunanin shin yau meke damuna ne Abubuwan da suka faru sai bani mamaki suke


Ina fita na shiga d'aki bayan nayi Alwala sallan nayi na kwanta akan kujira don yau ba karamin gajiya nayi ba don Koh girkin dare bansamu nayi ba gashi inason zuwa gidan Goggo Amina na duba Kan khadija yau kwata kwata ban ganta ba


Sai kusan 8 ya shigo d'akin, Sumayya kin kwanta ne?


"Eh Amma idanuna biyu"


Jin muryar ta saitin kujira,yasa ya nufo inda take 


Ina kallonsa harya ido wajen kujiran Yana kokarin zama mini akan kafafu da sauri na mike zaune na nade kafafun nawa"yanzun zama mini zakaye akan kafafu daban d'aga ba ka karyamin kasusuwa Koh me"?


Au kafarki nagun ne?ya  tamaya 


"Kaji nace maka Ina kwance sannan kazo zaka zauna akujiran"

Sanann yanzun kana tambaya ta Ina kwance ne"


Sorry yace Yana zama a inda ta d'aga kafartata, Sumayya!!


Na'am


Sumayya Ina Mai baki hakuri nasan tabbas band'auke Miki nauyin da ya rataya akaina a matsayina na mijinki b Ina Mai neman afuwanki wallahih Sumayya bani dashine shiyasa yau kwana biyu ban baki kome ba



"Ba kome ai nasan baka dashin ne sannan ni don na samu na sai Mana abinda zamuci ai ba kome wata Rana Allah zai baka kaima sauka sai mana"nace Ina kallonsa


Nagode Sumayya Allah ya saka mini da alkhari


"Ameeeeeen Daman jiranka nake kazo muje mu duba jikin khadija kasan yau ban samu zama ba tun safe"


Amma bakin gaji ba ki bari gobe Mana sai muje


 "ah ah  muje dai, gobe ma akwai masu zuwa kwalliyar bud'an Kai dana dinner har dare Ina busy"


Ok toh yace Yana mikewa


Hijjab nawa har kasa na d'auka nasa da karamin purse


D'aukar sandar sa yayi ya tsaya Yana jiranta a kofar d'akin


"Yau fa bazaka tafi da sandar nan ba atoh"


Akan me?


"Akan zaka fita Dani"


Ke asuwa?


"Asu masu ido" nace Ina kamo hannunsa ba musu  ya aje sandar


Tsaya na rufe kofar, yace


Sake Masa hannun nayi ya rufe mana kofar,Yana rufewa sake kama Masa hannun nayi Muka fita a shashen mu 


Tsakar gidan kaman ba dare ba duk jama'ar gidan na zazaune wasu a taburma wasu a kujira,nidai ganinsu baisa na sake hannunsa ba


Ke fasuma Wai me kika ganine a tare da miskini kike zaune dashi kamar auren tsafi,d'aya daga cikin Yan gidan Tama Sumayya gogar zana 


Ai toh auren tsafinne Mana inba haka ba mutun da arziki ya zabi Talauci,fasuma ta bata amsa..


Nikam ban tanka musu ba Donna fahimci Yan gidan nan sai shiriyar Allah don mutum Kam sai wani ikon Allah,tunda mutuwar inno Bai saka sun tsakaita da dambe da cacar baki ba ai hukuma ma bazata iyya dasu ba, kamar yanda Al'ameen yace


Waje muka fita,Ina rike da hannunsa muna tafiya,duk.inda muka wuce sai an bimu da kallo bare ga mazan unguwan da Basu sanni ba suna Daijin kwatance a bakin matansu,duk.madalisan da Muka wuce bin mu ake da kallo ga hasken sola ya haska Koh Ina, a hakan har muka shigo layin su Goggo Amina, na saima Khadija kankana da lemo,

da sallama a bakina na shiga gidan,don shi yace bazai shiga ba sai ammasa iso


"Assalamu alaikum"


Waalaikumu salam barka dai Sumayya sannu da zuwa Goggo Amina ta fad'a tana shimfid'a mini taburma


"Yauwa Goggo Ina wunin ku"


"Lafiya Alhamdulillah Sumayya kece da Daren nan"


Eh Goggo tare muka taho na fad'a Ina sunkuyar da Kai,(Wai kunya🤥)


Shine ya tsaya a waje ai aikin muhammad kenan kamar gidan bakonsa ne,kice ya shigo


"Toh Goggo" nace na koma kofar gida


"Ka shigo"nace Ina juyawa


Toh kin hanani rike sanda sanna kin tafi kin barni


"Yanzun bazaka iyya shiga da kanka ba"?


Eh bazan iyya ba


Uhmm kawai nace na Kama hannunsa da yake dare ne koma ba NEPA sai da muka kusa isa kusa da Goggo na sake Masa hnnu,

Zama nayi a taburman shi Kuma ya zauna a kujira,


Goggon Ina wuni?


Lafiya Muhammad hala kunzo duba khadija ne?


"Eh wallahih Goggo shuru yau najita bata zoba shine muka taho mu duba Koh kan nata ne har yanzun"?


Wallahih Sumayya ta fad'amin abinda ya faru,zaman gidan mu sai hakuri kuma.ku Kara hakuri kinji kome zai wuce


"Ba kome gaggo"


Aiko khadija kam.na kwance a d'aki yau Koh fita batayi ba Kai na ciwo ga zazzabi duka,Daman khadija akwai raki ku shiga ku duba ta,inji Goggo


Mikewa mukayi, muka shiga d'akin

Khadija ce a kwance tana bacci,


Fita mukaye don bamu tashe taba 


"Toh Goggo zamu tafi ga wannan ba yawa Allah ya Bata lfy wannan Kuma 5k ne yayanta ya bani Wai na baki koh gobe saita je asibiti"nace Ina aje laidan da na shigo dashi,hade da mikawa Goggo kudin


Wai Al'ameen d'awainiyane har haka daka bare Koh chemist taje goben sun Kara Mata wasu magani Koh na 200 ma


Al'ameen Kam mamakine ya kamasa yaushi ya samu kudi har 5k da zai bawa khadija,Amma Sumayya tace in jisa,


"Goggo taje asibitin dai zaifi tunda jiya chemist in ta fara zuwa ba'a dace ba"na fada Ina taka kafar yayan Khadija Jin yayi shuru baice kome ba


Am am gaskiya ne Goggo ki karbi kudin inyaso taje asibitin


Amma kudin yayi yawa ai muhammad


Ba wani yawa Goggo In change ya rage ku rike zai D'an rage muku wasu Abubuwan 


Kai Amma mungode muhammad, Sumayya Allah ya saka 


"Ameeeeeen" har muna hada baki dashi


Fita mukaye daga gidan Goggo Amina kafun na rike Masa hannu


Jin tayi hanyar titi ba hanyar gida ba yasa yace Mata Sumayya Ina zamuje koma bafa nan bane hanyar?


Sai da Kai zanyi nace Ina tare keke napep............



🏵️🏵️ *Gaisuwa na musamman da fatan Alkhari ga special FAN'S na MATAR MAKAHO Naga sakonku, Allah yabar kauna,Ina godiya* 🏵️🏵️



🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉



🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* 


🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da*  *gyara* 


🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* 


🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* 


🍀 *Na tsunguno(habil)* 

🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,

🍀 *Na d'aki(halud Al'oud)* 

 

 *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼


🍀🍀🍀 *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* 


🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* 


 *Contact them vie* 

🪀08028827241 or 09033791049

 *IG @umsadincense*



🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧 

No comments