Matar makaho 3

 


Page 3️⃣




"Basai ka saya abinci ba, akwai kayan abinci, ruwa nake so, asaya da bread sai kayan meya" cike da kuzari ganin na masa magana, a taushashe sabanin jiya, ya Mike ya fita, Yana fita, ya laluba aljuhunsa Aiko Allah yasa,Yana da gudan dari biyu da dari, na cinikin mangoron sa na jiya, da safe da Yan change ya hada ya fita tsakar gidan, sai ji yayi an saka ihu da shewa, daga mata har matasan samarin, ana ga ango ga ango, wanda Koh tantama babu,duk wanda yaji yasan na raini wayo ne, da shikiyanci kasanciwar ya Saba da irin wannan tozarci na Yan gidansu, sai abin Bai  damunsa Sam, wuce warsa waji yayi, ya fita kofar gida, dayake bakin titi ne gidan nasu, yasa shi sayuwa a bakin kofar gidan, Bai jima ba dayake safiya ne, yaji Mai ruwa na bugawa kiransa yayi  duka ya saya,  ya hadasa da yaron makwantansu, ya nuna Masa kofar amarya, shi kuma ya shiga shagon haladu, sayan bread na dari Mai kyau ya hada da Lipton na goma, da sugan  hamsin, ya karasa table in gwanja yasai kayan meya ya hada ya kamo hanyan gida ,



Mai ruwa ya shigo da yaro "na tashi na fitar da randana, na roba Mai girma sosai irin Mai cin jarka Sha biyar innan, Mai ruwa na Gama juyewa, Yana shigowa ya biya kudin ruwan,  ya ajimin laidan cefenen "dauka nayi nawuce kitchen", shi kuma ya fita, "kitchen na shiga kome an jiramin kuma ba laifi kitchen din ya dauki Rabin kayan da akai mini, gas na kunna na dauko dankalin turawa na fere na daura a tukunya, kwai na fasa na zuba kayan hadi na aji a gefe,  kettle na ruwan zafi, naso daurawa Amma ba nepa dole na daura bojuwa, ( tukunya) a dayan Kan gas in na zuba kayan kamshi da Lipton na rufe, naji" buruntun bude kofa lekawa nayi nagansa rike da Ghana must go na kaya madaidaici na kayansa ya shigo da lalube' ya fada cikin dakin  yaje ya aje sai gasa ya fitoh yana lalube cikin Dan tausayin sa, wanda bansan Ina dashi ba, "nace maikake nema ne" ?   cikin sanyin halinsa yace bokati, "na mike na dauko masa" sabon boket, da kwandon soso, na kayana da soso sabo da sabulu, na wanka Mai sada  na akwatina," hada a kwandon na Mika Masa" ya karba cikin lalube ya lalubi kwandon yace La!! ai Ina da soso  harda sabulu barshi kawai "cikin Jin haushi nace na sani ai na baka kayi dasu" Bai Musa ba ya karba yaje ya zuba ruwa a bokatin ya cika, da lalube ya shiga ban daki, ya ajiye ya dawo ya lalubi inda ya aji butar da yayi alwalan, asuba ya dauka ya cika ruwa ya wuce bayin, 


"Cikin kankanin lokaci na hada breakfast, Mai kyau na soyayyen dankali da kwai tie ga bread a gefe naji daki na dauko kazar dana Gama zagi jiya nazo na juye a kwando na makala gudun karya rube, da rana nayi meya dashi' na fada dakin na kakkabe gado na jira filon Kan kujira, na share dakin na fesa turarukan daki, na fitoh na share baranda na hada da kasar kofar duk da ban taba share kasa ba,  sai dai tayis Koh seminti haka na lallaba na share,  Ina gamawa" Yana fituwa a wanka daure da zani, tsoho a kwankwaso hannunsa dauke da kayan sa daya cire, a boket Yana lalube ya dibe ruwa ya zuba a boket in, ya jika kayan ya mayar bayan gida ya aje, ya fito Ya shiga dakin, "na ibi ruwa Nima na shiga Wanka da soso da towel na  Ina fituwa na fada dakin, ban Damu ba, tunda ba kallo yakeye ba" "Ina shiga na gansa zaune a kasa ya chanja Kaya zuwa jallabiya fari duk da yasha ruwa jallabiyan, Amma a wanke tas, 

"na shiga na bude akwatina na dauki Kaya, rigane dogo na material Mai kyau  da tsantse, NASA na hada da hula fari na fita waji na shanya towel in a igiya da kayan da na cire samun kar suye tsami,  na shiga kitchen na dauko abincin na fada daki da  plet na zuzzuba karyawan na Mika Masa" "na ibi nawa nayi Bismillah Muka fara ci" babu Mai magana a tsakanin mu tunda yasa, abincin nan a bakinsa yake godiya wa Allah a zuciyan sa, daya mallaka Masa sumayya amasayin Mata, tunda zata iyya dafa Abu ta basa yaci Wanda rabon da adafa abasa tun kafun ummarsa tabar duniya shiyake sayawa kansa, abinci she yake nemawa kansa, 


 "muna tsaka dacin abinci naji an banko kofar shashin mu an shigo, ba sallama aka daga Mana labule dukkan mu dagowa mukayi don ganin wani ishanshen ne, haka sabanin shida Banga mamaki a fuskar Saba sai dai alamu sun nuna baiji Dadin hakan  ba, ya kurawa kofar ido Kamar Mai kallo yanda nayi sakake Ina kallon kofa cike da mamaki....... 


💃🏼💃🏼Yan free books💃🏼💃🏼Naga comments naku naji dadin karfafa mini gwuwa 


Mom Abba 

Umme 

Nafisa voice note

Dr humaira 


Da sauran su


🪀My WhatsApp number

08084453785

[9/27, 4:10 PM] +234 806 983 1049: 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯 *

             ~ Na ~


 🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃


✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa 👌

Free book🤧

No comments