Matar makaho 24-25

 


Page2️⃣4️⃣&2️⃣5️⃣   

Karasawa tayi kusa dashi, Assalamu alaikum





Waalaikumu salam khadija


Na'am yaya, lfy Kam na ganka haka a zaune, a Rana gashi sai zufa kake


Lafiya khadija wallahih Ina cikin damuwa ne, tun safe na fita nabar Aunty ki Koh karyawa batayi ba gashi har ana neman la'asar banyi cinikin Koh biyar ba


Yaya gaskiya ya kamata ka shanja sana'a yanzun mangoro yayi a raha ba lallai bane kana cini ki sosai


Gaskiya ne khadija Nima Yanzun so nake na sare lemo in gwada na gani Amma bani da jarin,


Toh Yaya Allah dai ya Bud'a maka kaji kabar saka kanka a tunani kaje ka jawa kanka ciwo a banza


Allah yasa khadija


Yauwa gashe Aunty ta bani abinci na kawo maka


Abinci kuma?ai na ta samu kudi har taye cefene?


Ina Zan sani Yaya nidai data kirani saita aike ni kasuwa(ta Masa karya karyace Sumayya batajin maganar sa)


Koh dai kayanta ta sayar ne khadija?


Kai.yaya bana tunanin haka fa,ga abincin kaci pls kaji yayana sannan ka tashi a ranan nan ka koma Gefen shagon Haladu ka zauna


Toh khadija,yace   Yana karbar kulan da take hannunta, 

khadija Turaren wa Kika saka ne naji kina kamshi?


Hh wayyo yayana lalle ne Aunty ta mini, yanzun ma kwalliya zata mini Inna koma


Lalle Kuma khadija kuma yake kamshi?


Eh Yaya Turare aka saka sai aka kwaba dashi


Inta Miki kwalliyar Ina zakije?



Kamun Asma'u Mana Yaya ka manta


Ban manta ba sha'afa nayi khadija, Amma ya za'a yi bani da kudin machine in da Zan baki fa


Yaya za'a d'auke mu a mota gidansu Amarya,kasan yaufa zansha kyau,ta fada cikin farin ciki, zanje sai mu tafi tare...


Sai kin dawo Allah ya tsare mini ke kanwata,yace yanajin wani Annashuwa, kanwarsa na farin ciki Kuma Sumayya ce sanadi, gaskiya Sumayya Rahama ce Allah ya masa,daya basa ita


Ameen Yaya,tace tana tafiya


Bayan fitar khadija wanka nayi na chanja Kaya wando nasa da riga t-shirt   na kwanta akan kujira Ina jiranta,


Assalamu alaikum Aunty na dawo Aunty


"Waalaikumu salam khadija kiyi Alwala sai kizo mu fara make-up in Kinga Koh an Kira Sallah sai kiye kawai"


Toh Aunty, tace tana iban ruwa  Alwala tayi ta shigo d'akin 


Make-up kit nawa dana aje a cikin drawer na d'auko budesa nayi babbane ba abinda babu na make-up a ciki,zama nayi na tsarawa khadija makeover,

Kai Masha Allah duk Wanda yaga khadija mundin ba mugun sani ya Mata ba bazai taba zato Koh tsammanin ita bace heavy make-up na Mata irin na Amare, amaren ma sai agun dinner,"khadija muyi sallah sai kisa Kaya Koh"


Toh Aunty, tace sai murmushi take


Bayan mun iddar da sallah


Less in na Bata ta saka black ne Mai ratsin pink, gel na samata a gashi na d'aura Mata dankwali Mai ubansu,

sarka da d'ankunne warwaro, zube, na Bata dukansu golden colour,takalmi pink, gyale da purse black,Kai duk Wanda yaga khadija a yau Koh shakka bazaiyi ba zaice Amarya ce, Ina Gama shiryata


Tsayawa tayi tana kallon kanta a mirror, kamar taga abin tsoro, Innalilahih Aunty nice na koma haka? Aunty Kinga yanda na koma kamar ba ni ba,ta fada hawaye na cika Mata ido 


"Kece khadija ki share hawayen nan karya Bata Miki kwalliya kinji maza share"


Toh Aunty,tace tana goge hawayen ta


Wayata Kiran iPhone na d'auko"tsaya Khadija na Miki hoto"nace Ina gyara Mata gyelenta


Tsayawa tayi,Aunty ta ta Mata hotona harda video  sosai tayi kyau


"A Ina za'ayi kamun ne"?


A Taraba hotel ne,Wai ta hanyar government house


"Hhh ba Taraba hotel ba, Taraba motel ake cewa sannan Bata government house bane,hanyar ne Amma ta Amazon yake "


Au nikam Ina Zan sani Aunty ba zuwa nake ba, kawai nima naji jiya ana fad'ane


"Ga 200 ki hau machine kije kinji ki dawo da wure fa khadija karki Kai mangariba"na fada Ina Mika Mata kudin


Ki bare Aunty mota za'a kawo a gidansu amarya zai d'auke kawaye


"Aikam yau  a motar zaki,maza ki hanzarta Amma ki.karbi kudin Incase


Toh aunty sai na dawo,tace tana fita a d'akin 


"Toh khadija Allah ya dawo dake lfy"


Ameen, khadija na fita a kofar shashen yayanta, duk Yan gidan suna zaune a tsakar gida daga maza har Mata,ido suka bita dashe kureeeee suna mamakin bakuwar nan Sam tun safe suke zaune Amma basuga wucewar taba,baki a tsake suka bi khadija da ido harta fita,


Khadija Kam duk tabi ta tsargu don Sam tunda take da wayonta Bata taba kwalliya irin na yau ba har kofar gida ta fita duk masu shaguna suka bita da ido suna mamakin Wannan kyakkyawar meya shigo da ita gidan Adara,

Amma wasu basa mamaki in sun tuna MATAR MAKAHO fa Yar manya ce Kamar yanda aka saigunta musu, Kuma sun rasa dalilin auren nan Basu mamaki yake,mutum talaka miskini,a d'auki lafiyayye ya abasa Kuma Yar masu kudi,masu kudin ma zuriyan shugaba,abin nan na mugun Basu mamaki,Amma Basu da halin sani


Khadija Kam ganin ido caaaa akanta yasa ta ruga gida da gudu ta koma kofar Sumayya


"Kee khadija lfy meya faru Naga kin shigo kofa Koh sallama Babu Kamar an koroki"


Aunty duk inda na wuce bina fa ake da ido,ni gaskiya tsoro nake ji


"Kai khadija akwai wauta,don ana kallonki saiki kame jikinki ki nuna musu kauyanci,ai dakewa zakiye kici bom"


"Koh gun kamu kikaje neman kujira zakiyi ki zauna abinki karki kuskura kicewa kowa kome Wanda ya gaidake ki amsa Wanda Bai Miki magana ba karki Masa kinji"


Toh Aunty,tace tana fita


Sai yanzun Yan gidan suka gane ta cikin mamaki Iro yace,buran uba muna d irin wannan kayan a gida Amma ace har yanzun banyi aure ba aradun Allah Naga Mata


Kutumar ubanka iro D'an iska watoh kaga kasa ya rufe idon uwarka shine bare ka karya alkawarin da mukayi akan auren ka da salame,watoh munafurcine kullum akace ka fitoh a muku aure,sai kace baka da kudi,

 ah ah sai kayi gini ashe iskancine,baba lami tace


Kinga baba lami wallahih kibini a hankali Daman ni har yanzun haushin ku nakeji,

Aini ba shege bane dazan aure kanwar Wanda tayi sanadin mutuwar inno na ba,

Koh inno ne ta dawo nasan bazata yafe mini ba Inna aure yarki, iro yace 


Kai karamin D'an Tasha wallahih karka kuskura, kace zaka zagarmin uwa inba haka ba naci ubanka a gidan nan, manu ya fada,babban yaron Inna asabe


Inka fasa shege kake,iro yace Yana huci


Ai Bai Gama rufe baki ba manu ya shakumosa suka hau dambe


Duk yanda matasan ke ta kokarin rabasu abin ya faskara abinka da tamben maza,

Mazan ma masu zuciya


Hatta iyayensu maza an Kira Amma duk sunki rabuwa sai an rabasu an Kama D'aya sai D'aya ya fizge ya shakumo D'aya Inka shiga tsakani duka ya sauka akan ka


Abin da yafi karfin Yan unguwan police aka Kira,suka zo suka kwashe su,inda sabo an Saba da ganin fiye da hakama agidan Adara




*******************

Bayan fitar khadija kwanciya nayi don yau dai naji na gaji da cin cimar mu tunda inada sauran 2k Kuma akwai kayan Miya da yawa,don haka yaudai zanci wani abin special


Duk abinda ke faruwa Ina kwance Ina jinsu sai dai.bansan ainahin abinda ya had'asu ba"garin kallon fad'a a kasheni a banxa " nace Ina gyara kwanciya na


sai kusan 5:30 Al'ameen ya koma gida kwata kwata naira 30 yayi ciniki Sam yau Kam sai a hankali,ya shigo gidan jiki a sanyaye hannunsa d'auke da kwandon kwanuka,bakinsa dauke da sallama


"Waalaikumu salam,sai yanzun"nace masa


Eh Sumayya yau inne ba kasuwa shiyasa ban dawo Koh da Rana ba


"Toh Allah ya bada kasuwa gobe"


Ameen yace Yana aje Kwanukan a mawanki,Mika Mata talatin in yayi


"Ka rike kawai agunka"


Ok yace,boket ya d'auka ya ibi ruwa, band'aki ya shiga yayi wanka Yana fitowa yayi Alwala,daidai lokacin aka Kira mangari ba, masallaci ya wuce


"Sallan mangariba,nayi wanka Nima zani na d'auka fille D'aya na had'a da t-shirt sai hulan bacci, Jin ana kukarin shiga sallan isha'i,

Ina da Alwala hijab kawai nasa na Tada sallah,


7:40 Al'ameen ya shigo d'akin bakinsa d'auke da sallama


Amsa Masa nayi"yauwa jiranka nake ka dawo daman"nace Ina mikewa


Toh Allah dai yasa lfy?yace


"Kasan inda ake Saida tsire"?


Tsire Kuma Sumayya?


Eh "tsire de"


Hmm eh na sani a tsallaken titi akwai Mai nama, kusa damai shayi


Yauwa karbi kudin nan 2k ne ka sai Mana tsiren 1500 sai Kuma  ka sama Mana drinks Mai Dadi guda biyu yau Dadi zamuci gaskiya"

sai ka sai  Madara bornviter da sugar in change ya rage kasai bread Nokia Ina da ruwan zafi a flasks,sai mu karya dashe gobe da safe"


A Ina Kika samu kudin nan? haka Sumayya don khadija tace mini ba kayanki Kika sayarba 


Sosai naji Ina Kara kaunar Khadija yarinya Mai hankali hartasan ta rufa mini asiri agun D'an uwanta,

Amma ni bazan Masa karya ba"uhmm uhmm nidai gaskiya bazan maka karya ba Turarena na sayar"


Amma Sumayya banace ki daina Saida kayanki ba ,ni ban Kara Miki ba, Bai kamata in rage Miki ba


"Habba ya Ina da abinda Zan sayar na saka abakin salati saina zauna da yunwa tsakani da Allah fa, yau baka samu kome ba da haka Zan zauna tun safiya har warhaka banci kome ba kenan"na fada Ina Bata Rai


Ganin Kamar taji haushi sai ya sassauta murya,toh Yi hakuri kawo kudin naje na saya Miki


Mika Masa nayi bance kome Ba


Lalubar kudin yayi harya rike,ya fita


Baifi hour 1 ba ya dawo lokacin Ina kallo a d'aki 


Shigowa yayi da sallama


Amsa Masa nayi,Ina karban laidodi Daya ke mika mini, karba nayi, na mike waje na fita na d'auko plates da cups harda flasks na shigo d'akin,

bude laidan tsiren na zuzzuba a plate,Goran pineapple juice in Mai sanyi na juye Mana a cup,d'aukan NASA nayi na Mika masa,"gashi naka"


karba yayi hade da Mata godiya,a hankali yasa hannunsa a cikin plate in ya dauki Naman da Bismillah yasaka a bakinsa

,lumshe ido yayi,rabonsa da yaci tsire tun  lokacin da mahaifinsa kenan,bazai manta ba shike sayo musu duk dare, lokacin ma ba'a haifi Khadija ba


Nima cin namana nake Ina korawa da drinks ba karamin Dadi naji ba kai.talauci ba kyau talaka sai yafi wata baici nama ba,

Ashe haka talakawa keji,tabbas badon jarabawar da Allah ya jarabceta ba bazata taba sanin rayuwan Talauci haka yake ba Alhamdulillah Alah kulli halim


Daga ni harshi duk nacin mu bamu iyya cinye namarnan ba, sai da muka rage wani,nikam har zafi hakorina naji yake mini kafun na aje Naman don yau cin yunwa na masa,sabanin da, da nake ma nama cin kwad'ayi kawai


Jin ta aje plate nata yasashe magana,sumy Wai harkin cinye ne ga nawa ki Kara wallahih na kasa cinye wa,


"Kutt bazanci sauran abinda kaci ba,Kuma nima ga nawa ban ciny.........


Bai bare ta Gama magana ba taji ya fizgota sosai suka zube akan gado kanta yahau cikin gaggawa ya hada bakin su waje D'aya y'awonsa ya juye Mata a baki


Ware ido nayi Jin y'awonsa cike a bakina so nake na zubar Amma ba Hali har lokacin bakin mu a hade,ji nayi kamar numfashina xai d'auke ai da sauri na had'iye Ina rumtsa idanuna


Jin ta had'iye yasa a hankali ya kamo harshen ta sosai yake tsotsarta cikin zafi zafi..


Fizge bakina nayi,"don Allah ka Bari banason abinda kake minin nan"na fada Ina ta kukarin turesa a kaina



Ni Kuma inaso,ya Bata Amsa,Yana Kai hannunsa, akan t-shirt nata Yana kokarin cirewa


Ai bansan lokacin da na Kama kokarin fizgo kaina ba ganin da gaske fa mutumin nan riga zai cire mini


Jin ta isheshe da fizge fizge shima ya biye Mata inya d'aga riga sai yaji ta jawo rigan kasa,inya cire hannu D'aya sai tasa d'ayan


Tambe muka fara sosai abin dariya abin haushi,daga ni harshi mun jikkata sosai Amma ba Wanda yayi niyar barwa Dan uwansa dama


ni naki yarda ya cire mini riga shi Kuma yaki yarda ya hakura,


Hannu yasa da karfi ya fizge zanin jikinta,


Gwalalo ido nayi jina ba zani,wani yunkuruwa nayi da karfin gaske Zan mike zaune 


Cikin  zafi nama ya maidata kwance  Yana Kara Hawa kanta,



daidai lokacin mukaji sallama na muryoyin Yan Mata a kofar mu....,.....



🌾 *Juma'at Mubarak* 🌾


 


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉



🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* 


🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da*  *gyara* 


🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* 


🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* 


🍀 *Na tsunguno(habil)* 

🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

🍀 *Turaren turara jiki after birth* 

🍀 *Na d'aki(halud Al'oud)* 

 

 *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼


🍀🍀🍀 *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* 


🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* 


Contact them vie

🪀08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧 


No comments