Matar makaho 22-23

 Page2️⃣2️⃣&2️⃣3️⃣ 

Yau da Matata Zan kwana gaskiya





Da mamaki nake kallonsa"waye matarka"?


Ga tanan ya fada Yana kwanciya Da ita a jikinsa 


"Wai menene haka ka matseni fa" nace Ina kukarin tashi a jikinsa


Fuska ta ya hada da tasa fuskar har hancin su na gogan na juna,


Karan in TV nan Kam kyakkyawa ne shiyasa yake burgeki?


Ikon Allah yanzun Kam na gane inda mutumin nan ya dosa, maganan Karan innan ya damesa"mummuna ne kamar Kai"na basa amsa,har lokacin Ina kwance a jikinsa don karfe ya saka mini sosai


Murmushi yayi a hankali yake goga Mata gashin gemunsa  a Gefen fuskarta


Wani  Abu nakeji sosai  a tare dani"Kai me haka"?


"Kana goga mini gonan ciyawa a fuskata Koh so kake ya garceni ni" 


Kinji Dadi kenan?


Kuma ni ba mummuna bane sai dai kece mummuna


Hhhh shap ai in fada maka "Kai mummuna ne sosai gaka bak'i,gajere, Mai guntun hanci, ga tumbi"


Wannan Karo Kam dariya ya kamayi don sosai yake cikin nishadi, ganin ya samu abokiyar Hira 


Farine ni, Kuma hancina dogone Ina da ido bakina irin na khadijata fuskata dogone  Mai dauke da gashin gemu Mai yawa haka na kaima, akwai tabon sallah a goshina,ya Bata Amsa yana Kai hannunsa kanta ya zame hularda ta saka a hankali ya Kama gashinta da khadija ta kitsa Mata har gadon baya,

Da Ina Tara gashi sai yafi naki yawa


"Kutt wallahih bazaifi ba duk ma Wanda ya farfada maka haka kamannin ka yake  kawai zaginka yayi Amma ba wani yanda na fadan nan dai haka kake"


Dariya kawai yayi sai Kuma yace,

Da ace ban taba ganin kaina a madubi ba dayau kinyi Dani don d'auka zanyi da gaske hakan nake


"Au Daman ka taba kallone kafun ka makance"?


Shikarata 18 na zama MAKAHO Kinga ai zuwa yanzun kamannin Bai sauyaba


"Ya sauya kam gashi harda tumbi kayi"na fada Ina murmushi haka kawai na tsinci kaina cikin farin ciki yau na samu abokin Hira Wanda rabon da nayi harna manta sai in khadija tazo


Cikin hanzari ya birkitota zuwa kasa shi kuma ya koma Saman ta,


Zaro ido nayi cikin Al'ajabi da tsoro bakina har rawa yake"yayan khadija me haka wayyo kirjina nauyi ka d'agani"


Ina da tumbi Koh Babu kinsan ba gani nake ba shiyasa na saka Miki tumbin don kiji akwai Koh Babu


"Wayyo Allah cikina kirjina nauyi ka sauka a kaina wallahih baka da tumbi washhhh numfashina xai d'auke"


Jin yanda duk tabi ta gigice yasa a hankali ya d'aga nauyinsa akanta Amma Bai sauka ba,


"Ashhhhh toh ka sauka a kaina Mana"


Shuru yayi yaki magana yanajin ta sai masifa take, ya sauka a kanta ya Mata banza don yanzun Sam baicika Jin shakkarta ba Kamar da


"Ina Jin fitsari"


Yayi shuru don yasan ba fitsarin zatayi ba muddin ya saketa guduwa zatayi


"Koh bakaji bane, ya matseni fa"


Kiyi anan kawai, ya Bata Amsa


Ganin ya manna mini hauka yasa nayi shuru ganin da gaske fa ba sauka zaiyi a kaina ba bare akan gadon,ganin baida niyar yimin kome yasa hankali na ya kwanta har kusan 1 na dare idanun mu biyu daga karshe dai bacci barawo yayi gaba Dani,


Jin saukar numfashin ta ya tabbata tayi bacci a hankali shima ya ringajin bacci na d'aukarsa zamewa yayi ya kwanta a gefe ya dagota ya d'aurata a kansa ya lumshe idanunsa har yaji babushi,


Kiran farko na Assalatu shiya sauka akan kunne na a hankali na bude idanuna na,masu cike da bacci jina ajikin mutum yasani tunawa Ashe fa jiya tare muka kwanta zame jikina nayi a hankali Zan mike


Jin tana zame jikinta a nashe ya sakasa bude ido sai alokacin yaji Kiran sallah ake


Daga ni harshe waje mukayi na ibi ruwa a buta na aje Masa"ga ruwan Alwala kar a shiga sallah baka Kama Alwala ba ka rasa jam'i"Na fad'a Wai karya tuna wani abu, don yau na iba Masa ruwan Alwala



Butan ya d'auka Alwala yayi ya tafi massalaci sai tunanin abinda zasu karya yake baida Koh sisi Kuma inya bude Mangoro da safe ma ba ciniki yake ba kwana biyu nan,   amfiya D'an Saya da rana Koh yamma


Alwala nayi na shiga d'aki,

 Ina iddar da sallah na kwanta a Kan sallayan don harga Allah bacci nakeji jiya ban kwanta da wure ba


Gida ya shigo don ya rasa mafita Sam baisan me zayi ba,a Ina zai samo musu na karyawa tsoro yake kar hakurin Ta ya Kare wata Rana ta guje sa, da sallama ya shigo d'akin Jin Bata amsa ba yasa ya fara laluben ta akan gado Amma Bai jita ba ya sauka Yanata tattaba kujira a tunaninsa Koh tana jinsa kin amsawa tayi, 

Sumayya!! Sumayya!! ya kirata baki biyu Amma shuru,hankalin sa a tashe ya shiga tattaba kome na d'akin Yana nemanta hardai yajita a kwance akasan cafet,sosai hankalinsa ya kwanta shi Karan kansa ya rasa meke damunsa akan Sumayya Sam baida jarumta akan lamarin ta, Koh  don ta kasance mutum na farko dake da kusanci dashi a duniyarsa ta yanzun ne oho,hannu yasa a hankali ya cicibeta Yana lalube harya Isa bakin gado kwantar da ita yayi,ya fita waje,boket ya d'auko ruwa ya ringa ja a rijiya harya cika Randa ya wanke kwanuka harda shara yayi Amma dai sharan Koh na yara albarka saboda kwata kwata batayi kyau ba (sharan Mara ido)



Yana Gamawa d'akin ya shigo  da lalube ya isa Kan gadon Hawa yayi,hannu yasa ya fara tataba ta Yana neman fuskarta har hannunsa ya sauka akan kirjinta 


Waro ido nayi Ina kallonsa Jin yaki cire hannunsa a kirjina yasa na buge hannun"me haka don Allah"?


Da nayi me?ya sake tambayar ta


"Ai kafini sani waima menene kake ta faman laluba ta  Ina bacci"


Nidai bansan kome ba tunda ba gani nake ba nadai San na taba Abu mai laushi Amma bansan kome Nene ba,ya Bata Amsa


Lallai mutumin nan ya Raina mini wayo ai Koh Bai taba kallo ba a rayuwar sa yasan meya taba bare harya Kai 18 Yana kallo,jin rainin wayone ma ban sake magana ba


Kin tashi lfy?


"Lafiya Alhamdulillah"


Uhmm Sumayya Zan fita, Koh zan samu na karyawa anjima Zan dawa insha Allah ban kwana da kudi ba


"Sai ka dawo" nace Masa Ina sauka a Kan gadon don wallahih yunwa nakeji ba kadan ba


Allah ya yasa,Yace Yana  fita a d'akin harya bude kofar shashen zai fita yaji Sumayya na kiransa tsayawa yayi 



"Am Daman nace in ka fita pls ka tura yaro ya kiramin khadija"Ina magana Ina bin kofar da kallo da mamaki 


Toh,yace mini zai juya


"Wai waye yayi aikin nan duka haka"?na fada Ina murmushi ganin sharan Kamar wata yarinya Yar 3 ce tayi 


Nine na Miki aiki yau dai ki huta


"Aiko naji Dadi na" nace Masa don na gane so yake ya burgeni 😌


Da gaske?ya tambaye ta


"Sosai ma,ka tafi Mana samun mu samu na karyawan ka tsaya surutu yanzun ana neman 8:10 na safe"


Ok.toh sai na dawo


"Yauwa"



Yana fita a kofar gida ya aiki yaro gidan Goggo Amina ya Kira Khadija



Nikam tsintsiya na d'auka na sake share kofar na gyara d'aki sosai kwana biyu nan. Nake jina a sake sosai 


Khadija ce ta shigo bakinta dauke da sallama,

Assalamu alaikum


"Waalaikumu salam"khadin Goggo


Kai Aunty ni banso sunan fa nasan a bakin Yaya kikaji duk shike Bata mini suna


"Toh khadin Yaya"


Aunty ai khadin ne banaso


"Toh khadija shikenan"?


Eh Aunty Ina kwana ?


"Lafiya khadija ya goggo"


Lafiya Alhamdulillah,tace tana zama a bakin dakali


"Wai ni khadija ya Fulani Dance in dai su kawayen Amarya jiya an rabashe kenan"?


Shuru tayi sai Kuma Naga hawaye ya cika idanunta..


Da mamaki nake kallonta "Khadija me ya faru kuma daga tambaya sai kuka wani abin na Miki"?


Aunty don Allah nida yayana muna da wani abin kyemane a jikin mu, da mutane ke wulakanta mu Koh saboda mun kasance Marayu ne, Koh Kuma don Yaya baya kallo ne, ta fada tana fashewa da kuka


"Subhanallah khadija meyasa Kika Fadin irin wannan kalaman haka"


Dole na fada Aunty kaf unguwan nan yayana baida aboki Sam ba Wanda keson rabarsa gani ake Kamar Inka jashi a jiki zai zama maka kaya, Amma wallahih Aunty yayana baida zuciyan kwad'ayi kullun so yake yaga ya neme na kansa Amma duk da haka in Kinga yayana na Hira toh ta miskinai ne irinsa Amma bayansu ba Mai son Koh Hira da yaya, shiyasa har kullum nake mamakin auren ki,


Ni Karan kaina mujiyace a cikin kawaye, me laifin mu aunty mu muka d'aurawa Kan mu Talauci ne Koh akwai Wanda yafi karfin maraici ne?


"Gaskiya Babu khadija Amma meya faru ne haka"?

Na tambaye ta idanuna na cika da hawaye tabbas khadija Allah ne ya tsare ta a irin zamanin da muke cikin nan yanda Yan Mata suka baci da son kyelekyele Amma ita ta kauda fuska ta cire buri a ranta ta zauna a matsayin da Allah ya d'aurata,samun irin khadija kalilan ne a yanzun yarinya Mai hakuri


Aunty Kinga wulakancin da kawayen Amarya suka mini jiya a wajen bikin nan? ta fada tana kuka


"Ah ah khadija me suka Miki"


Aunty' Wai daga zuwana naje na tsaya agun da kawaye ke tsaye kawai Ina zuwa suka mimmike suka  koma wani wajen  Wai kunya suke kar abokan ango suganni a cikin kawaye za'a Raina class nasu,kinsan ma Aunty me yafi Bata mini Rai?


"Ah ah khadija"


Wai Aunty danaga duk sun watse saina koma cikin mutane na tsaya kawai kowa na tsaya kusa dashe sai ya Kama matsawa Wai kar ace tare Dani yazo, don ban saka kayan Fulani ba koma banyi ado ba


Sosai naji wani irin haushi kamar zai kashe ni


Aunty bazan sake zuwa bikin kowa ba daga yau


"Yau me za'a yi"?


Kamu,ta bani Amsa


"Zaki je bikin nan khadija har a Gama dake za'a Gama insha Allah"


Aunty ni bazan sake zuwa ba a wulakanta ni,don Yaya yace Koh mutun baida kudi in dai ya rike mutuncin sa bazai wulakanta ba


"Ki kwantar da hankalinki insha Allah bazasu sake wulakanta kiba" na fada Ina Mai Jin tausayin baiwar Allah nan


D'aki na shiga na barta tana kuka akwatina na bude Kaya na d'auka Atamfa da les masu azaban kyau a dinke sai Turare na d'auka guda D'aya na fitoh a d'akin dasu a hannuna 


"Khadija rike kayan nan Naga kamar akwai tailoli a tsallaken titi ki Kai musu wa'innan kayan su rage Miki yayi daidan ki yanzun in Kika fita,

wannan Turare Kuma kasuwa nakeso ki Kai shagunan masu Turare Koh zasu Saya kudin sa 20k ne Amma Koh 10k Kika samu Koh kasa dashe ki karba kawai"


Aunty ba Yaya yace ki daina Saida kayanki ba?


"Khadija Zan zauna da yunwa ne Ina da abinda Zan tsayar naci a cikina sai na zauna"


Gaskiya ne Aunty Amma fa Yan kasuwa bazasu Saya ba don yanzun Suma tsoron sayan kayan hannu suke karsu Saya na sata,sai dai akwai wata Mata dillaliya ta bayan kasuwa sai na Kai Mata don ance itakam Koh kayan satane Saya take don Yar rikici ce sosai


"Yauwa khadija Allah yasa ta Saya wannan kayan in kin fita ki fara kaisu shagunan dinki"


Aunty wazaki bawa kayan Kuma ai Naga daidan kine naji kince a maidashe daidai na?


"Ina ruwan Ki,nidai tashi kije mini aika na,

 sannan in ta Saya Turaren ki shiga kasuwa ki sai Gam bak'i Mai kyau ki hada da Turaren lalle,sajan,tsamiyan kanti, ki sai bakin lalle guda biyu shima"


Aunty lalle zakije ne?


"Kai Khadija banson tambaya ki sai mini kayan Miya duka,in kin dawo ki biya tailan kudinsa ki karbi kayan Saiki saimin doya soyayye  a bakin titi na karya"


Toh Aunty tace ta karbi kayan tasa a laida ta fita


D'aki na shiga Ina ta tunanin halin rayuwa da khadija ke ciki


Sai karfe 10 khadija ta dawo kayan na bubbude na Bata ta gwada Aiko yayi Mata daidai jikinta sosai kayan ya karbe ta,doyan na bude Mana mukaci tare


Kam in na manna a tire na kwaba Jan lalle, "khadija zoki zauna na Miki lalle"nace  Mata Ina zama akan dakali


Aunty Daman ni Zaki ma lallen ne har Kika Saida Turaren ki Mai tsada a naira 5k?


"Khadija bazan d'auki wulakanci ba Sam insha Allah yau saikin fi Amaryar kyau bama kawayen ba" 


Daman kin iyya lalle ne Aunty?ta fada tana zama


"Sosai ma khadija ai lokacin da nake primary school innaje makaranta sai nayita zana flower lalle a takanda na Inna dawo gida sai ummie na tace zata buge ni sai abie ya k'waceni  yace bazata bugeni ba ai batasan Koh baiwar da Allah ya mini ba kenan,

sai ya sai mini takkadar lalle daban duk lokacin da zanyi Zane saina dawo makaranta sai ya bani takardar na zana, lokacin da na Gama primary sai ya sai k'wallon dayes ya baiwa Mai aikin mu ta dafa mini da lalle,sai nayi mole na zuba a ciki,abie ke saimin hydrogen Ina ma yaran gidan mu lalle harda yaran makwanta,

harna girma Ina lalle duk yaran gidan mu da aka aurar Mata Ninake musu lallen aure da make-up haka kawaye na da Yan unguwan mu sosai nake Alfahari da lalle khadija"nace Ina manna Mata Gam a gafa


Kenan Aunty kina sana'an lalle da kwalliya?


"Ban taba yin lalle kudi ba Koh make-up khadija don ba abinda na nema na rasa a rayuwa a lokacin"


Allah sarki, tace 


Lalle na tsarawa khadija sosai bak'i da ja sai bayan azahar Muka Gama, tunda nake da khadija ban taba ganin farin cikin  Dana gani a lokacin da na Gama Mata lalle ba bini bini saita duba lallen tayi murmushi


"Wai nikam khadija baki taba lalle bane"


Aunty Kenan Koh a sallah bana lallle in Kinga nayi lalle toh gaggo ne ta mini yabe


"Toh yaukam kinyi design na flower"nace Ina mikewa


 sallah Mukayi kafun Muka girka abincin Rana har lokacin yayan Khadija Bai dawo ba,


Sai biyu da rabi na Gama abinci zuba Mana nayi mukaci har lokacin fuskar khadija na d'auke da murmushi 


***Nima sai naji Ina cikin farin ciki ganinta tana walwala


"Khadija ga abincin yayanki kikai Masa"


Toh Aunty ta d'auki kulan tana kukarin fita,"yauwa khadija in kinje ki dawo da wure samun mu fara make-up in da wure"


Toh Aunty nagode,tace tana fita,cikin farin ciki duk Wanda ya ganta yau yasan Bata da wata damuwa


Tun daga nesa ta hango yayanta a zaune g'wanin tausayi sai zufa yake................




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉



🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* 


🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da*  *gyara* 


🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* 


🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* 


🍀 *Na tsunguno(habil)* 

🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,

🍀 *Na d'aki(halud Al'oud)* 

 

 *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼


🍀🍀🍀 *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* 


🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* 


Contact them vie

🪀08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧     

No comments