Matar makaho 16-17

 Page1️⃣6️⃣&1️⃣7️⃣

Shigowa d'akin nayi cikin hanzari na karasa kusa da abie na banyi wata wata ba na rungume sa na fashe da kuka maicin Rai,,,,





Ji kawai nayi momy ta dakawa abie tsawa,


Kai Abdulsalam mainace maka akan yarinyar nan?,


Ai da sauri Naga Abie ya hankad'ani a jikinsa ya mike tsaye cikin wani irin hada fuska Wanda. Bansan abiena dashi ba Naga ya mike cikin hargage yake magana Sumayya fita a dakin nan banason ganin ki banace Miki bake bani ba Koh bance ki zauna a dakin kiba,


"Abie Kai nazo gani don Allah Abie Koh kowa zai juyamin baya Kai karka Bari a rabamu don Allah Abie," nace Ina fashewa da kuka,


Waye uban naki?? keh daga yau niba ubanki bane bansan wata y'a Sumayya ba kaf zuriyan shugaba babu yarinya Mai suna Sumayya ki fita a gidan nan da zuriyan mu bake bani Koh mutuwa nayi banason ganinki akan gawata,yace idanunsa na taruwa da hawaye daga Gani dai maganar fatar bakine bana zuciya ba,


"Amma abie menene nai maka da har zaka yanke dukkan alakar ka Dani har haka atunani na Koh kashe mutum nayi bazaka yanke alaka Dani ba abie ka rabani da mahaifiyata tun bansan kaina ba yanzun Kuma ka sallamawa duniya ni" wa nake dashi in ba kaiba kaf duniya nan abie why Abie why"😭😭?? 


Nafada Ina kallonsa gani nayi hawaye nabin fuskar sa,ya daga ido Yana kallon momy,


Toh munafuki kallon me kake mini,Ke Kuma wuce ka sata a  gaba tabar Mana cikin gida yanzun,


Nikam mutuwar tsaye nayi nashiga uku yaushe abie ya zama haka zaushe ya koma  yaron momy,abie da na  sani ne kuwa kafun na bar gidan nan Koh maganar banxa momy Bata Isa tamin a gabansa ba bare yau har tana basa umurni  ya koreni,


Ban farga ba naji an janii kiiiiiii!!! Anyi hanyar steps Dani,


Cikin mamaki nake kallon abie yau ni yake ja Kamar wata saniya zai koreni a gidan sa lallai fa,


Jana yake tayi har Muka sauko falo abin gwanin tausayi,nikam kuka nake Kamar Raina zai fita gabaki d'aya naji duniya tamin zafi,

Ganin abie ya nufi kofar fita falo Dani yasa Khadija tasowa ta biyomu a baya Yan falonka da ido suka bimu wasu na dariya ganin yanda uba ke fincikar yarsa 


Fincike hannuna nayi na dawo cikin falon na tsaya a gaban babuji  (kanin babana) " babuji abani ducument Ina, Ina bukatar su,"



Don ubanki lokacin da uwarki ta haife ki da results ta haifiki ne,,,,,



Don haka baza'a bayar ba koma bara ma kiji daga yau Koh a kasuwa ne karki sake hada sunanki da family shugaba,


"K'warai  kayi gaskiya babuji ba'a haifini da results ba Amma da kudin ubana na same su in Kuma hassadace yasa kuka k'wace karfa ku manta arziki nufin Allah ne in Allah ya tsaga da rabonka  sai kayi arziki ruwa da iska Koh guguwa bazai Hanaka samuba",


"Ba karatu bane kadai abinda ke sa bawa arziki rabonsa baya wuce kansa"


"Baiwa ta jarina"sannan wannan tsinannen gidan naku wallahih ku rubuta ku aje sai yafi muku prison ganin..................


Tassss naji saukar wani azabebben Mari  a kumatu na Wanda yasani sumar wucen gadi,ba kowa bane yamin Marin nan sai sahabi yaron babuji,


Ke karamar Yar iska watoh kema harkin zama Yar bariki irin mutanen gidan da kike Koh zakizo nan ki gwada Mana kin falle toh baki Isa ba ki tsaya kina gayama ubana magana in barki ya fada Yana fincikata juyawa nayi Ina kallon abie Wanda ke tsaye kansa a duke,


 Bai tsaya aku Ina Dani ba har Saida ya dangana da get turani yayi waje Yana ma Mai gadi warning daga yau in ya sake barin Mai Kama Dani ya shigo gidan nan a bakin aikin sa,Yana fadan haka ya juya abinsa yayi cikin gida, ya dauko jakana da takalmi ya watso mini a jiki,


Baba buzune ya fitoh yazo inda nake zaune tunda ya jefoni ban matsa ba mamaki tsoro da kuma wani irin tsana naji ya tsargan mini na family mu duka ban cire kowa ba, aciki nayi alkawari daga yau na yanke duk wata alaka da shugaba family house,


Kayi hakuri yaro haka rayuwa take kaji,

 kayi zaman auren ka ka rike mijinka Allah zai baka mafita kaji hajiya Sumayya,kayita addu'a kaima Allah ya tsareka gidan nan yanzun sai abinda matar babanka yace,

ya fada cikin tausayi,nidai Ina duke dakai sai kuka nake inda Allah ya Soni ma unguwan mu ba irin sintali bane nan kowa na cikin gidan sa Babu mutane a waje,


Jin ana kamani anason mikar Dani yasa na daga kaina Khadija ce wance bansan yaushi ta fitoh ba ,Ashe tun Marin da aka kwada mini ta ruga tayi waje tazo ta Saya,...



*******""""


Banyi musu ba na nike tsaye Kayana ta hau karkade mini nidai sai kuka nake Kamar zararriya gashi bamuda Koh sisi da zamu tare abin Hawa ya kaimu gida gashi Koh a gidan  ma bani da kudin da Zan biyasa Kuma banda tabbacin yayan Khadija na dashi, yasa na Kama tafiya da kafa Ina kuka,


Dukawa Khadija tayi ta dauki jakana Dana Bari,sai hakuri take bani Amma nai Mata banza a haka muka fara fasa hanya,


Mota na gani Tasha gaban mu tayi packing Abdul ne ya fitoh a ciki ya nufe mu,


 don Allah Sumayya kiye hakuri da abinda kikaje Kika tarar a gida wallahih yanzun gidan mu sai addu'a abin sai gaba gaba yake, Kuma na rasa me yasa duk gidan mu ke suka tsana,


*****Kala bance Masa ba don shima wani tsanar sa nakeji a Raina Sam yanzun naji banason ahalina kwata kwata na yanke duk wata alaka dasu daga yau Kamar yanda Suma suka yanke Dani,


***Kaucewa nayi na fara tafiya bance Masa kala ba,


Biyo ni ya sake Yi Yana mini magiya, Sumayya don Allah badon ni ba kizo ki hau na kaiki gidanki Kinga yamma yayi bazaki samu Keke napep ba anjima anan,


Wallahih Abdul Ina Ganin kimarka Inka kuskura ka kaini bango Zan maka abinda bazaka manta Dani ba Kai asuwa zakazo ka tsaya kana bani umurni wallahih daga yau Babu ni Babu Kai Koh a hanya ban sanka ba na tsaneku mugaye kawai azzalumai wallahih ku jira karshin ku,



Habba Sumayya menene laifina in sun Bata Miki ni meyasa Zaki had'a Dani,..


"Ai Wanda suka Bata mini su waye ne a gunka"?na tambaye sa Ina kallon sa ido cikin ido,


Iyayen  mune da Yan uwan mu,ya bani Amsa,


"Iyayen kadai da Yan uwanka daga yau bana D'aya daga cikin family shugaba  in baka sani ba ka sani yanzun ka fita harka ta "


Sumayya kada bacin Rai yasa ki ringa furta maganganu da Basu dace ba,



"Na furta Abdul Koh kaima dukana zakayi" na fada Ina wuce sa


Shikam mamaki ne yake son kashesa Anya Sumayya da ya sani ce wannan shuru shurun ashe haka take ganin bazata yarda tahau motarba yasa ya zare kudi a Aljuhunsa ya mikawa Khadija gashi Yan Mata kuhau Keke Koh ya fada Yana duban Khadija,..


"Wallahih Khadija Kika karbi kudin nan sai na nuna Miki true colour na"


Khadija Kam ta tsorata da sauri tayi gaba kamar yanda taga nayi,


Muka barsa a tsaye kamar gunki,



Tafiya muke har lokacin hawaye baibar zuba a. Idanuna ba wani irin zafi nakeji a Raina a haka muka ringa fasa unguwa unguwa muna wucewa tafiyarda tunda nake. Bantaba yin irinsa ba yau shi nake kafafuna duk sun kumbura na rashin sabo, Amma yanda zuciya ke cina Bai bare naji wahalar ba, Khadija kam Koh a jikinta,



Har mangariba yayi bamu ma kusa Isa sintali ba


   Aunty Koh zamu tare kekene in munje gida Yaya ya biya Kinga fa mangariba yayi ga hadari sosai? Khadija tace


Kala bance Mata ba tafiya kawai na cigaba dayi don nasan Koh na hau munje bazamu samu kudi ba tunda cinikin nasa duka ya hada ya bani Ina zai samu wasu dari da hamsin,


Tafiya mukaci gaba dayi ga yunwa don rabona da abinci tun ruwan shayen safe Amma bacin Rai baisa naji ba har aka Kira Isha adaidai lokacin aka fara yayafi sai ruwa ya sauko Kamar da bakin k'warya ganin mun iso bakin kasuwa yasa ban tsaya wani labewa ruwa ya dauke ba tunda dare ne Babu Wanda zai gane mu gashi NEPA sun dauke a haka ruwa na dukan mu muka shiga sintali hanyar gidana muka nufa tun daga nesa Muka hangesa 



Al'ameen ne a tsaye a kofar gida ruwa na dukansa daga ka gansa kaga Wanda hankalin sa yake tashe,


Muna Isa Khadija ce ta fara Masa magana nikam cikin gidan na nufa don bana bukatar Jin kome,


Yaya ya Naga kana tsaye a cikin ruwa haka gashi duk ka jika lafiya Kam?


Ina Naga lfy Khadija baku dawo ba Ina Aunty take Allah dai yasa Yan gidan su basuce bazata dawo ba wallahih naji tsoro Khadija karsuce zasu rabamu?



Hhhh habba Yaya bafa wani abu da zai rabaka da matarka insha Allah sai mutuwa Kama daina mugun tunani irin wannan,


maganan dadewa Kuma abin hawane bamu Bamu ba da wure, shiyasa naso ma mu kwana Amma Aunty tace mu dawo kar hankalin ka ya Tashi(Tamar karya don ya kwantar da hankalin sa)


Shap in kuka kwana ai nashiga uku kenan ,


Amma me yasa baku Kama hanya da wure ba kuka bare sai yamma kuka fitoh,gashi ruwa ya muku duka,


..Kai Yaya abinci fa muka tsaya muka ci,

Yauwa Yaya kasan me yau ran aunty a bace yake don Allah ka bita. A hankali inda Hali ma karka Mata magana yanzun ka Bare sai da safe ka Mata magana in ma kaga change a tare da ita ka Mata uzuri,


Meya faru Khadija?


Ba kome Yaya kawai dai sun D'an samu matsala da yaran gidansu ne sai Randa ya baci,



Bai yarda ba don yasan halin Khadija akwai surutu akwai boye abinda ba'a sata fada ba,shiyasa kawai ya shanja zancen,


Toh khadija muje ciki in ruwan ya tsakai ta sai na raka ki gida


Ah ah Yaya dare yayi fa yanzun ana neman 8:00 na dare nikam Zan koma Goggo zatayi fada,


Muje na rakaki gida  sai nama  Goggo bayanin dalilin jimawar ki karta Miki fada,


toh yaya,ta fada tana Kama hannunsa suka nufi layin su Goggo Amina,


Nikam Ina shiga cikin gidan da yake ana ruwa ba kowa a tsakar gida shashen mu na nufa,aje jakana da  takalmi nayi a baranda na kwabe lufayar jikina da yajika jakaf da ruwa na makala a igiya,

 dakin na shiga nadau towel na daura na zame  dogon wando da NASA   da under wear na makala a igiyar kofa ,


Kitchen na shiga na kunna gas na daura bojuwa (tukunya) na zuba ruwa a ciki,boket na dauko na ibi ruwa a Randa na tsaya a cikin kitchen in ruwan na tafasa na juye a boket in daidai yanda zanyi wanka na dauki boket in nayi bandaki,wanka nayi  na fitoh,har lokacin ruwa ake Alwala nayi,jakana na dauka a baranda na shiga dakin,


 Jin dis dis Kamar panfo yazo daukewa yasa na lalube  wayata  a jaka na haska dakin idona ya sauka akan kujiran da yayan khadija ke k'wanciya  ya jika jakaf da ruwa  saitin wajen na yoyo fita waje nayi da sauri na d'auko baf nazo na tare ruwan,kaya na dauka na bacci na saka da hula harda socks don wani irin sanyi nakeji har cikin k'ashina sallaya na shinfida na Tada sallah mangariba da Isha nayi shafa'i da wutire ,


blanket na dauko nahau gadon na lullubu abina na kwanta da wani irin ciwon Kai da zazzabi nakeji gashi kafafuna sai zuge suke mini nama rasa meke mini Dadi 


Al'ameen suna tafiya da Khadija Chan dai Khadija ta kasa hakuri tace ,Yaya nikam na tambaye ka Mana?


Allah yasa na sani dija,


Kai Yaya ni banason dijan nan ai sunan tsofine,


Toh hadixa Ina jinki,



Habba yaya ta fada tana hada fuska,


Sorry toh kanwata Ina jinki


Yauwa Yaya nikam Aina ka hadu da Aunty Sumayyan ne harkace kana Sonta?


....Dam dam haka gabansa ke bugawa , Khadija meyasa Kika mini wannan tambayar,?



Ba kome Yaya kawai na tambaye Kane ,


Ah ah Khadija fad'amin gaskiya nasan baki tambayar Abu banza,


Am Yaya Naga baka taba bani lbrn kana da budurwa ba kawai sai naji Wai kayi aure za'a kawo Amarya,


Toh Khadija ke abokina ne da saina fada Miki Ina da budurwa,

 auren Kuma yazone a bazata ban dauka iyayen ta zasu bani ita lokaci d'aya ba, 


Amma yaya kaga gidansu aunty kuwa Mai azaban kyau ga Yan gayu k'yawawa  a gidan Kuma Aunty ma kyakkyawa fa Yaya toh ma  Ina kake zuwa daga Tashar kayan marmari sai wajen sana'ar ka Ina kaga aunty har kuka fara soyayya?


Ikon Allah Khadija Wai tambayar nan Kam na lfy kin sani a gaba da tambaya sai kace wani sa'anki ,


Kayi hakuri Yaya dai dai lokacin suna iso kofar gidan Goggo Amina,


Muje Khadija na rakaki cikin gidan nama Goggo bayanin dalilin yin darenki ,


Toh Yaya ,



shiga sukayi cikin gidan tare,


Goggo Amina ce ta amsa sallaman tasu tana fama da icce a runfar girkin ta


Isa sukayi ya gaishe da ta Yamata bayanin dalilin yin Daren Khadija,..


Wallahih Muhammad Nima sai da na tura yaro yajimin lfy Khadija har dare Bata dawo ba ga aikin dare da tace zata dawo ta Kama mini, ya dawo yace min ba kowa a shashen ku,


Kiyi hakuri Goggo, Basu dawo ba sai yanzun Al'ameen yace Yana mike wa,


Ba kome muhammad  shine ka tasata a gaba a ruwan nan Maimakon ku bare Sai ya tsakaita,


Goggo Nima haka nace Mata Amma tace Zaki Mata Holo itakam sai gidan Goggo shine na rakota


Gggo ruwan da yawansa bansan karfe nawa zai dauke ba  shiyasa nace gwara na dawo

 

Hakane Kam  da gaskiyar ki Khadija


Toh sai da safe, Goggo


Allah bamu alkhari


Ameen suka amsa ita da Khadija shikam fita yayi ya Kama  hanyar gida,


Ina kwance Amma ba bacci nake ba tunani kawai na fada  nayi zugum gabaki daya gari yamin zafi,


daidai lokacin ya shigo kofar duk ya jike Daman jallabiya ne a jikinsa ,,


 hauro wa dakalin  Yayi ya zare jallabiyar sa ya aje a cikin boket in wanka dakin ya shigo daga shi Sai gajirin wando, da sallama a bakinsa


Ina kwance cikin duhu don na kashe hasken wayana naji buruntu ana kokarin shigowa dakin  don ni Sam banji sallamar ba, hasken wayata na kunna me Zan gani yayan Khadija ba Kaya, murd'adden damtsen hannunsa naci Karo a waje ga fafad'an kirjinsa mai cike da yalwan gashi,baki sitik kwance akan farar fatarsa kafarsa farare tas sai gashi ke kwance a lallausar fatar kafar tasa ai bansan lokacin da na k'wala ihu ba na dirko a saman gadon,na Kama hanyar waje don ni sai ma gani nake kamar ba wando a jikinsa don ajike wandon yake tsabar birkita hanyar kofa na nufa zanfita na bar Masa dakin,


Jin ihunta sai ya birkitasa ya dauka Koh wani abune ya sameta Jin ihun take  akai akai hakan yasa ya gigice shima ya fara neman hanyar kofa cikin lalube,da D'an saurin sa Jin itama kofar ta nufo tana  ihu har lokacin,


Ji kake gauuuu! sun garu da juna a kofa daga shi har ita ihu suka saka a tare, sai kawai suka kuma zubuwa ji kake timmmmmmm............


 *Gobe Monday Ina da jarabawa bazakuga update ba fan's* 🏃‍♀️


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉



🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* 


🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da*  *gyara* 


🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* 


🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* 


🍀 *Na tsunguno(habil)* 

🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,

🍀 *Na d'aki(halud Al'oud)* 

 

 *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼


🍀🍀🍀 *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* 


🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* 


Contact them vie

🪀08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧     

No comments