Matar makaho 14-15

 


Page1️⃣4️⃣&1️⃣5️⃣   




Aunty' inno ta rasu tace tana Kara karfin kukanta,


"Innalilahih wainnailaihir rajuun"   Allah ya jikanta da rahama yasa ta huta" nace 


Ameen Aunty tace tana mikewa tadau hijab inta ta nufi cikin gida,


**Banyi niyar zuwaba saboda jikina Amma ganin mutuwa ne Kuma Abu da  gida babba hakan zai iyya zama abin magana, yasa na mike na fita zuwa cikin gidan, 


Ai ban tashi sanin Yan gidan ba sai da Naga manya da yara Suna kuka harda na tashin hankali kuka suke ba manya ba yara Mai makon a ma mamaci Addu'a sai ihu da kuka nidai Ina zaune a Gefen matan makwanta da suke shishigowa Ina kallon ikon Allah


Al'ameen da wannan sanyin jikin ya iso kofar gida ya tarar da jama'a makil, inno ta rasu mutuwar ta dake sa sosai don alokacin sai da mutuwar mahaifiyar sa ta dawo Masa sabo,ganin yanda iro ke kuka Wanda yasan halin iro ba kome ke tsorata Sa  bama Amma yau kuka yake,


tabbas mutuwar iyaye akwai ciwo,(Allah kajikan iyayen mu)


Ankai inno gidan ta na gaskiya yau har anyi sadakar bakwai gida ya koma kamar yanda yake kowa na sha'aninsa sai yaranta da sukayi sanyi kadan na rashin uwa,


A tsawon satin nan na fahimci yayan Khadija baida aiki haka zaije yayi ta yawo Koh sisi bazai samuba ya dawo Yana kame kame taliya Koh Maggi Koh indomie nake iba  na bawa Khadija takaima masu shago su Saya da araha kafun mu samu na shifenen Miya,..

Duk da Al'ameen baisan Ina Saida garana ba,


karshe dai ajesa nayi nace ya fadamin me ke faruwa, dashine yanzun,duk lokacin da ya zauna baida aiki sai tunani,


Tukum yamin bayanin bashi da jari yaje tashan kayan marmari  sun hanasa bashi duk inda yaje su taimaka Masa sunki,


,"Amma   menace maka in Abu ya taso ta wajenka bance ka ringa fada mini ba"?


Hakane Sumayya Amma ni sai Inga Kamar ni ya dace in bukatar ki ya Tashi ki tambayi ni ba Zan ringa daura Miki nauyi ba,


"Au aini ma nufina bashi Zan baka Amma Ina ni Ina baka kyautar kudi sai dai bashi "


Duk da haka dai Sumayya....


Ban Bari ya karasa maganar Saba na tare sa "na baka bashin ne ka rufawa kanka asiri Koh na rike kudina ka cigaba da yawo ba aiki ga azumi saura wata biyu"


"Kuma bara na gaya maka in azumi yazo kayan Dadi zakana sai min Kuma kamin kayan sallah harda Khadija kaji dai na fada maka"  


Toh shikenan abani yace Yana gyara zama alamun dai baida mafita,


"Ka Bari sai gobe Zan baka"


Washe gari Khadija na tura yaro yace tazo, ba'a jima ba sai gata aikanta nayi   *say* *box* ta Kira mini Daya daga cikin yaran  masu shagunan sai da wayoyi da laptop's suzo tare tace Masa amarya ce ni Kuma ban fara fita ba,


Don nasan in na Bata laptop innan za'a Mata cinikin wulakanci ne kawai Koh ma wani ya Mata wayo ya gudu da laptop in don nasan say box ba irin mutanen da babu a ciki,


Munyi ciniki da Mai sayan system in ganin  yanda Yama laptop in cinikin wulakanci yasa nace na fasa sayar wa,


Buhun flower na dauko a kitchen Daman ban taba bude Saba nace wa Khadija taje gun Haladu tace Masa xai Saya buhun flower Zan Masa sauki,


Bata jima ba ta dawo tace min yace ta kawo flowern ya gani, Bata buhun nayi taje shagon Haladu ta sayar mini shima naira dubu bakwai ya Saya ba yanda na iyya haka na sayar Masa Amma ni Karan kaina nasan ba haka kudin yake ba,


Yayan khadija na baiwa dubu uku yayi jari na rike dubu hudu na D'an Yi sayayyan abin bukata  nayi irin su pad omo sabulu na baiwa Khadija dubu D'aya, tunda har yanzun Basu gyara Mana NEPAn kofar muba  don sun biya ganin mu bamu biya ba sai suka yanke wayar kofar mu Khadija na baiwa dubu daya ta mikawa bappa sulaiman kudin wutan NEPAn mu aranan sukasa aka hada mana wayar aka gyara, na baiwa Khadija dari biyar itama  😉



Haka rayuwa tayi ta tafiya Rana ya wuce sati ya shude yau Dadi gobe Akatsen sa  har Muka cika wata Daya da sati biyu da aure, ba abinda ya taba shiga tsakanin mu Koh da kuwa hada gado ne, in munkwana waje D'aya toh ana zafi munyi kwanan waje ba nepa,


A y'an kwanakin nan na  fara fuskantan matsen rayuwa Wanda ban Saba ba,


Dole sai abinda ya samu zamuci wani sa'in ma in Bai samo kome ba haka zamuci indomie d'anye wani a dafe da ruwa, in ya samu D'an ciniki Kuma muci shinkafa da Mai da yaji,Inda Allah ya sumuma garana Bai kare ba akwai taliya Mai Maggi kefe shinkafa, Amma duk da haka na D'an fada  na chanjin yanayi,  saboda yanzun ya hanani Saida Kayana don har Yan unguwa sun fara gulman ya kasa rikeni Kayana nake sai dawa,maganan har kunnen da yashiga shiyasa ya nuna mini baya so ,


yau na shirya da niyar zuwa gidan Goggo Amina, da gidan mu tunda safe na kammala aikina yau mun Sami kudin kayan shaye mukasha da safe' bayan ya fita na kammala aikina dake na sanar dashi Zan fita gidan Goggo Amina ( marikiyar Khadija ) Zan bi gidan mu d'uka Bai Musa ba saboda mun Riga munyi maganar dashi, dari da hamsin ya bani kudin Keke,


 Khadija zata rakani kasancewar yaune Zan fara fita, unguwa tunda nayi aure bayan asibiti ba inda naje,


Sai goma Khadija tazo lokacin na fitoh wanka, Muka gaisa ta shiga Wanka Dayake tun jiya ta zo ta guge kayanda zatasa d'aya Daga cikin Wanda nake Bata,


Shiryawa nayi cikin lufaya Mai tsada fari Mai Flowers brown NASA riga long sleeve brown NASA takalmi fari na dau jakama fari fuskata ba kome sai powder da man baki, Khadija dake gefe na tsaye baki bude tana kallona,


"Rufe bakin ga guda zai wuce ciki"nace Mata cikin murmushi Mai karawa fuskata kyau,


Hmm Aunty na gaskiya ke Mai kyauce Allah ne kadai yasan dalilin da yasa ya bawa yayana wannan k'yakk'yawar hallintar nan Ina ma Yana kallo yaga yaran da za'a Haifa Masa 😅


Murmushi kawai nayi bance kome ba  don na lura ita ta yara ma take,


" Khadija kiye sauri kisa kaya don Allah na masu na ganni a gidan mufa Naga abie na"


Toh Aunty tace tana saka dogon riganda na taba Bata,tayi shafe shafen ta tana Gama shiryawa, Muka  fita"


Yaune rana na farko Dana taba karewa unguwan sintali kallo unguwa ne da ya hada ruwa biyu masu kudi da talaka wa Yan kasuwa da ma'aikata da masu zaman banxa unguwan nada kyau sosai da fasali,..


Gidan Goggo Amina mukaje da kafa ,


Mun samu tarba Mai kyau ba laifi matar nada kirki sai dai na Lura ita mace ce da Bata shiga abinda Bai shafe taba Sam babu ruwanta,mun D'an jima a gidan kafun Muka Mata sallama na aje Mata laidan Turare Wanda na d'auka a kayan aure na,


ta rakomu har waje Muka tare keke napep ,


Hajiya Ina kukayi? Ya tambaye ni


"Specialist" zaka kaimu,

Ku hau muje yace,


Dukan mu Hawa mukai yaja machine insa muka nufe  unguwan specialist,


Muna shiga unguwan mu  na Masa kwatancen inda zai sauke mu,


"Yana sauke mu na tambayi sa "nawane kudin ka"  


Naira dari da  hamsin kudin ku kubiyu,


Sai a lokacin na tuna dari da hamsin inne a jikina kacal Wanda yayan Khadija ya bani Allah dai yasa abie na gida nasan zamu samu na dawowa don karyan mu taka da kafa daga specialist zuwa sintali,

biyansa nayi muka  nufi kofar gidan mu


Khadija mutuwar tsaye tayi ganin wani irin gida Mai bala'in kyau Wanda Koh a mafarki Bata  taba ganin irin Saba Daman ita ba yawo take ba iyya kacinta kasuwa sai unguwowin kusa da sintali  irin mafindi unguwa gadi da sauran unguwowin kusa da unguwan su,


Amma Bata taba zuwa unguwa Mai nisan nan ba sai dai tanaji a bakin Asma'u sunje unguwan specialist Koh millionaire's sweet in suna Bata lbrn gidajin unguwan sai taga Kamar tatsuniya suke Bata bata taba zaton haka gine ginen unguwan yake ba Wai duka wannan a cikin Jala yake?


***Harna nufe get Amma sai naji Kamar ba Khadija a gefena juyawa nayi me Zan gani Khadija an sake hanci baki ido ana kalle kalle zuwa kawai nayi na jaho hannunta, sai a lokacin ta farga da kauyancin da ta nuna 


Cikin Jin kunya tace Aunty wallahih unguwan nan yayi kiga gidan da zamu shigan nan Kamar aljannan duniya,


Kai Khadija kin cika shirme wallahih mu tafi nikam,


**Get Muka nufa Mai girman gaskiya kamar get In gidan prison haka ma ginin gidan dogayene sosai anyi penti fari get in ma farine k'wank'wasa,makeken kofar get in,nayi


Wani farin buzune ya leko ganina yasa ya washe bakinsa cikin hausar sa da baya fita yake cewa laaa Amarya Kaine hajiya Sumayya wallah nayi kewanka shannu  da zuwa lale lalema barkama lale ya fada Yana bude mini get muka shiga,


Shiga cikin gidan mu ya sake ruda Khadija ganin filin gidan mu filine babban bana Wasa ba  Wanda yakai girman wani karamin unguwa,ga shuke shuke na Flowers ya kewaye gidan Wanda ya kara haska gidan sosai ga parking space babba Mai dauke da mototi na alfarma wanda akalla zasu Kai talatin duk ciki bamai araha,



Nidai Ina rike da hannun Khadija Muka nufi wani  babban part Wanda duk fadin gidan part inne kawai ba wasu Amma daga ganin part in kasan ba karamin duniya bace a ciki ganin shima ginine na gidan sama Mai Hawa uku,babban kofar falon NASA hannun na na bude da sallama a bakine duk da banida tabbacin za'a ji,saboda girman falon,


Khadija Kam mutuwar tsaye ta sake tayi ganin cikin falon gidan mu,


Kusa Kai mukayi cikin falon falone Mai girman gaskiya Wanda ke dauke da kujiru set biyar ga babban plasma na alfarma Kai fadar tsaruwar falon gidan mu Bata lokaci ne na barwa readers su keyasta,


Babban falon gidan mu Yana dauke da d'akuna kusan Sha biyar haka upstairs shima dakuna  goma Sha biyar ne Hawa na uku ma haka,Amma duk yawan d'akunan gidan munan falon mu dayane shine falon kasa, Wanda Koh a Hawa na uku kake kana hango falon,


 d'akunan kasa na samarine sai kakarmu dake zaune dasu a kasan Wai tana saka musu ido injita, dakunan Hawa na biyu na iyaye ne Hawa na uku shine na Yan Mata da d'akunan yaran gidan da sukayi aure maza,suna zaune da iyalansu ,..


duk yanda Zan fasalta muku gidan mu saifa na  rage wani abin,


Kaf gidan mu da colour D'aya aka kawatashi da white colour sai surkin baki Kama daga kujiru labule  Abubuwan da aka kawata gidan kome farine daga sama har kasa abin sai Wanda ya gani,


Jama'ar gidan mu duk Muka samu a falo da yake yau weekend ne ba aiki ba makaranta kowa na zaune wasu na kallo wasu na Danna waya wasu na Danna laptop yara na wasa wasu abinci suke ci ganin mu yasa dukansu barin abinda suke suka zuba Mana ido Kamar yau suka fara ganina,tunda Khadija ce Basu sani ba,


Idanuna ne ya sauka a Kan kakata dake zaune tanacin kefe sai uncle's nawa dake zazaune wasu na cin abinci wasu na Hira wasu na duba takardu,


wani abune ya tsayamin a makoshi Mai kamada Takaici sun aurar Dani Basu damu da rayuwar da nake ashan ba gasuna suna zaunen su Kamar Basu San wata Sumayya da aka bawa MAKAHO ba Basu neme sanin ya rayuwa ta kare ba waima me dalilin auran Dani ne tunda gasu Aunty miemie sun girme ni nesa ba kusa ba Amma saini kadai aka aurar auren ma da MAKAHO ba lafiyaye ba,Koh don anga mahaifiyata Bata gidan ne Kai Koh mahaifiyata Bata gidan ai ubana nanan


Koh da kowa zai nuna Mini kiyayya dada zata sassauta tunda ita ta haifi babana amma Ina abin ba sauki,


"Ina kwana dada,"nace Ina zama a cikin Daya daga cikin kujirun falon,



Toh matan miskinai ne agidan namu yau Koh idonane,?


Ah ah Kaka ba idon ki bane kinsan azumi ya karatoh anzo amsan zakkah ne,


Hhhhhh Kai miemie baki da dama Amarya ce fa tazo ganin gida mutun da gidansu kece yazo karban zakkah,kubra ke fada tana dad'a tunsirewa da dariya


Waiku yaran nan wasu irin Yan iska ne me yasa baku da mutunci shegu kawai ai gwara ita tayi aure Koh?


Keee koh miskini kin samu yazo wajen kine da sunan aure, a cikin ku waye ta samu miskinin na zuwa wajenta,Yaya Abdu ya fada ransa a bace,


Ai itama ba zuwa yayi ba lika Masa akayi,miemie ta basa amsa,..


Rufe mini baki karna ci ubanki Yar iska Abdul yace Yana mikewa,


Ai duk laifin  dadane Sam bansan me yasaba, Dada (kakar mu)  itace babba Amma ita ke sasafo Mana bala'i yaya kabiru yace Yana maijin takicin ahlin gidansu,


Abubakar kanajin abinda shegen yaron Kan nan kabiru yake  shimin mutunci kayi shuru kana kallonsa,,,


Kiye hakuri Dada Kai kabiru zanci kaniyarka fa inka sake shiga abinda ba ruwanka uwarka aka zaga Koh me da zaka saka bakinka a ciki,


Mikewa Kabir da Abdul sukayi sukabar falon,


Ganin yanda aka Mai Dani Kamar kashi ba Wanda yabi ta kaina kowa na Harkan gabansa


Ganin Banga Abie na a cikin falon ba yasa na mike nayi hanyar upstairs na nufi d'akin sa nabar Khadija a falo wance ke rakube Kamar ace kitttt ta ruga,


Bude kofar d'akin nayi nasa kaina na shiga   Abie nane zaune a kasan tiles Yana duke da Kai sai momy (yadikko na) zaune a bakin gado daga Gani dai magana suke..................




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉



🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* 


🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da*  *gyara* 


🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* 


🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* 


🍀 *Na tsunguno(habil)* 

🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,

🍀 *Na d'aki(halud Al'oud)* 

 

 *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼


🍀🍀🍀 *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* 


🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* 


Contact them vie

🪀08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense

[9/19, 4:45 PM] +234 813 343 4840: 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧  


No comments