Matar makaho 12

 


Page 1️⃣2️⃣




Cikin tashin hankali Khadija ta nufi kofar gidan tana isa taga an fitoh da inno Akan kadon asibiti da ake daukan gawa Koh Mara lfy tana kwance Koh motse batayi aka shigar da ita Ambulance sai su Inna asabe da baba lami suke ta rusan kuka Kamar ana yankasu,


Khadija Kam iyya rudewa ta rude ganin Yan matan gidan duka kuka suke harda wasu mazan ma


Bappa Dayyabu da bappa sulaiman harda kawu  tafawa suka shiga motar Yan sanda da gani dai abin Case ne babba 


Ta rasa wama zata tambaya ga Goggo Amina sai kuka take ,


Ganin lokaci na tafiya tasan yanzun bazata samu amsar tambayar taba yasa ta wuce kofar yayan ta shanyar kayan dazun da safe takai d'akin jakar ta dauka da Abubuwan da ta lissafa Mata duka,ta rufe kofar  tayi kofar gida


Da sauri ta fita daga gidan ganin har yanzun jama'a na tare Tam,


Hospital ta wuce direct tana isa dakin ta baiwa Sumayya jakar,


Budewa nayi na zaro kudi  50k  na mikawa yayan khadija "ga kudin ka dau takardan khadija ta rakaka kuje ku biya"


...Toh Al'ameen yace  Yana laluben kudin ya karba hade da zaro dubu goma da dari biyar in safiya da Khadija ta basa ya hada da dari biyar in mangoron sa,ki cire dubu goma da dari biyar a cikin kudin sai na hada Dana wajena na ciki ta na biya,


"Ka bar na wajen Kan ai ba'a sallame niba zasu bukace  mu Sai wasu abubuwan irin su hand gloves Koh ruwa da allurai duka ai bamu Gama kashe kudi ba ba iyya aikin bane kawai ka rike kudin a gunka,"


Toh khadija Tashi mu tafi 


Toh yaya, ta basa amsa


**Fita sukayi nikam zuciyata tsinkewa ya ringayi da fargaba gani nake kamar bazan rayu ba,


Waya ta da khadija ta kawo mini na dauka number abie na Kira Amma Bai dauka ba,


Sake Kira nayi harna fidda tsammani naji  ya dauka cikin sanyin jiki na Masa sallama"assalamu alaikum abie"


Waalaikumu salam ke lafiya?


Lafiya Alhamdulillah abie Daman na kiraka ne nace maka za'a mini operation yau don Allah Abie in nayi maka ba daidai ba kayi hakuri abie ka yafe mini bansan Inna shiga operation room  xan fita da Rai Koh a mace ah ah shiyasa na kiraka naji muryarka abie ka samin albarka Koh xanga nasara a rayuwa ta Dan Allah"


Keeeeeee!!!! ce Miki akayi  in za'a ma mutum tiyata mutuwa yake ne kin wani kirani kina fadamin Zaki mutu ki mutum Mana keee!!!! bara ma na fada Miki daga yau karki sake kirana!!!!


 wallahih, tunda na aurar dake ki barni na huta mana,


***Hawaye ne keben fuskata Wai meke faruwa da rayuwa nane haka,,


Yanzun mahaifina in ma ya juyamin baya,


ganin shigowar Al'ameen da Khadija yasani share hawayen,


"Khadija kin biya"?


Eh Aunty.... Sunce 7:00 na dare za'a shiga operation room in,


"Toh bara nayi sallah mangariba Koh kafun Azo a dauke  ni" na fada zuciya takaraya sosai wallahih,


Shima masallaci ya tafi nida Khadija mukayi Sallah muna idarwa na sakasu suci abincin da ya rage tun safe Basu sake saka kome a cikin su tun karyawan safe na taliya da wake,,


Daker suka iyyaci Amma kadan nikam na kasaci tsabar fargaba,


Karfe bakwai akazo za'a dauke ni,


*** Da kafata na fitoh nurse suka sakani a gaba har nayi nisa Al'ameen ya k'wala mini Kira tsayawa nayi ya iso inda nake lalubar hannuna yayi ya rike cikin damuwa sosai nasan daurewa yake,


Sumayya insha Allah Zaki fitoh cikin nasara kinji ki cire tsoro a ranki kinji Allah ne ya jarabceki Kuma insha Allah shizai baki lfy kinji,


"Kukane ya k'wace mini yau wa'innan bayin Allah sune gatana a yau bani da kowa a kusa Dani sai su dame Zan biya su babu, Allah ne kawai xai biyasu" rungumar sa nayi cikin kuka nake  cemai "insha Allah insha Allah"


Lokaci fa na wuce wa ki shige mu tafi Naji muryan Nurse 


***Sakensa nayi na rungumi khadija wance tun tuni kuka take, 


***Na juya Ina tafiya a hankali Kamar wance k'wai ya fashewa a ciki sudai suna bin mu a baya har Muka Isa kofar operation room aka dakatar dasu tare da nuna musu su koma Kan kujirun d'ayan block in su zauna...... 



Bayan da Al'ameen baiyi ba Khadija ta koma gida taje ta kwanta Amma Taki tace anan zata kwana sai da ya nuna Mata Jan ido kafun ta yarda zata tafi 500 ya Bata ta hau nepep sauran change ta rike a hannun ta ,,,

. godiya ta Mar sosai ,ta dauki kula ta fita,.....




Zama Al'ameen yayi agun har akayi Kiran isha'i yaje yayi sallah yanata Addu'a Allah ya yasa aiyi aiki a sa'a ya Bata lfy(muma mukace Ameen) 


Bayan wasu hours Sumayya aka fitar akan gado tare da kayan tiyata da hulan duka Koh motse batayi aka kaita dakin da ake aje,wa'inda akama tiyata Basu farfado ba shima binsu yayi har dakin ya shiga sun dauke ta sun daura akan gadon dakin,


 kujira ya samu  a Gefen gadon ya zauna ganin an shanja musu daki ba dakin emergency bane tashi yayi yaje ya tattara kayansu na dakin emergency ya dawo dashi dakin da take yanzun, zama yayi a Kan kujira,


Har dare yayi sosai Bata farka ba,  sai karfe 2 na dare ta farka tana fizge fizge bakin ta dauke da salati tana ambatan sunan abie yayi hakuri karya gujita itama,,


Abirkice ya mike Yana kakamata ganin irin girgiza da take ya tsorata da sauri ya k'wala ma nurse inda ke dakin a zazzaune Kira ganin inyace zai tashi Sumayya zata iyya raunana kanta,


Da gudu suka yi kanta suka kakamata surutai tayita Yi Akan Abie da salati sai Shan anjima kadan Sumayya ta koma bacci,


Likita lafiya kam meke faruwa ne da Matata?ya fada hankalin sa a mugun tashe,


Ka kwantar da hankalinka ana samun haka Daman in dai mutun zai farfado sai yayi ta sambatu,..


Toh doctor yace Yana komawa Kan kujiran ya zauna hannunta ya laluba ya rike yanajin wani irin tsoro a ransa,


Har asuba Yana zaune sai da yaji ana Kiran sallah kafun. Ya Mike ya fita yaje yayi ya dawo  ya cigaba da zama...



Khadija Taki fadawa yayanta abinda ta gani a gidansu gudun kada hankalin sa ya tashi ta Sansa da saurin birkice wa gashi Yana fama da Sumayya tazo ta Kara Masa da wani Kuma,



Keke napep tahau  ta wuce a kofar gidan su Goggo Amina ta sauka ta biyasa kudinsa ta shiga gida da sallama. ......


Goggo Amina ta samu  zaune sai rusan kuka take Kamar wance ake yanka namar jikinta,


Da sauri ta karaso gareta cikin tashin hankali tana cewa Goggo Amina lfy menene ya farune wallahih tunda na tafi hankali na yaki k'wanciya?


Wallahih Khadija kedai ki bare kawai mutanen gidan mu sun dawo kashe junansu,


Kamarya Goggo ban gane ba?


Toh dazun bayan la'asar iro ya dawo daga aiki yazo zaici abincin ranan sa ashe suwaiba( yar baba lami) ta dauka taci shine da yazo dauka yaga babu yake tambayan inno ya abincin sa babu  a kula shine fati tace masa suwaiba ne taci, 


Tashin sa ba wani tunani ya zaro wayan wuta ainahin na bol ya zuba mata ita kuma da taji zafi tana ihu ta zari tabarya zata muka Masa,


Inno Kuma ganin za'a bugawa iron ta tabarya tazo zata k'wace kawai tabarya ya sauka a kanta,shine fa Kika ga ta mike Koh motse batayi, 


Ni tsorona ma yanda naga Kan Bai fitar da jini ba kinsan akwai babban hatsari ka bugu irin wannan ace jini Bai fitoh ba,



Shine iro ganin inno a yashe a kasa yaje ya ibo Yan sanda akazo aka tafi da suwaiba, gabaki daya gida ya hargitse su bappa nayinku duk sun bisu station wasu suna asibiti har hanzun ba'a San takamammen halinda inno ke ciki ba mutuwa Koh rayuwa😭😭😭 wayyo ni Aminatu,


ta fada tana sake rushewa da kuka ita dai Khadija Allah ya kiyaye na gaba tace ta Mike taje ta ajiye kulan Sumayya a kitchen sai gobe zataje kofarta da safe,wanka tayi, tayi isha'i ta kwanta don batajin yunwa taci a asibiti,haka tayita juyawa Amma bacci yaki daukan ta tashi tayi ta Kama lafilfilu tana nemawa Aunty Sumayyan ta lfy da nasaran aiki sai 1 ta kwanta


Bangaren Al'ameen bayan sallan asuba har lokacin yana zaune Dayake dakin da suke yanzun babban falo ne Mai dauke da majinyata masu yawa wa'inda aka ma operation shiyasa Basu kadai bane a dakin,


 sosai Yan dakin ke mamakin MAKAHON nan shin baida Yan uwane da zasu kula da wannan Mara lfy sai MAKAHO chap lallai Kam kowa gulma na cinsa( Niko nace gulma zai karku bazakuji kome ba) 



Tun asuba Khadija ta farka Bata koma. Bacci ba wanke wanken Goggo Amina ta fara ta hada harda kulan  aunty ta duka ta wanke tayi shara tana Gamawa ta daura dumame ganin yau Goggo Kamar Mara lfy haka da tashi ,tana Gamawa ta dauki key sai gidan yayan ta,


Yauma sai da tayi shara ta daura ruwan zafi Yana tafasa ta juye a flasks ta dafa indomie da kwai lokacin karfe 7:30 wanka tayi tasa kayan ta data dauko a gidan Goggon ta tadau abincin tayi hanyar FMC



****Da misalin karfe bakwai na safe na bude idona Wanda nakejin Kamar an zuba mini barkono a ciki a hankali na sauke k'wayan idanuna a kansa a zaune yake ya tasani a gaba Kamar wani Mai kallo yayi tagumi kallo daya zaka Masa kasan a cikin zullumi yake sosai.......




🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin Koh kinsan mace sai da kamshi da* 😉


🍀🍀🍀🍀 *Turaren  Suna d'ayane Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin*


🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da gyara*


🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*


🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*


🍀 *Na tsunguno (habil)*

🍀 *Na jiki (kwalaccam) (khumraBlack & while*)

🍀 *Turaren turara jiki after birth*

🍀 *Na d'aki (halud Al'oud)*


 *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼 💃🏼


🍀 *Suna bada kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*


 *Contact them vie*

08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense


[9/19, 4:45 PM] +234 813 343 4840: 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

 🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯      

               ~ Na ~

 

 🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌

free book 🤧   

No comments