Matar makaho 11

 





Page 1️⃣1️⃣

Bayan fitar Ammar Khadija ta kirga kudin dubu goma ne,Mika min tayi, Aunty ga kudin


"Ajjye Khadija in yayanki yazo ki basa tunda shike fama da zirga zirgan asibiti" toh Aunty ta bani Amsa tana aje kudin a cikin ak'watin Kayana,


Al'ameen na fita daga asibiti da kafa ya koma har gida Dayake akwai sanda in Kuma yazo titi sai ya Kama yara su tsallakar dashi Yana Isa unguwan su(sintali) wajen shagunan bakin titi ta inda yake sai da mangoro a bakin su,


Shagon malam shu'aibu ya fara zuwa don shine yafi masu shagunan abin arziki sosai alayin da sallama a bakinsa ya shiga shagon,


Assalamu alaikum malam shu'aibu


Waalaikumu salam Mai mangoro ne?


Eh nine malam shu'aibu barka da jama'a


Barka dai lafiya Kam Naga yau tun safe danazo bude shago Naga hulbairon ka a rufe dazun na aiki yaron gidana ya karbo mini yako yake fadamin baka nan?


Eh wallahih malam shu'aibu iyalina ne ba lfy jiya na kaita asibiti,


Allah sarki ya jikin nata?


Da sauki Daman nace bara nazo ka taimaka mini da kudi dubu hamsin za'a Mata aikine appendix ya kumbura a cikin ta don Allah ka taima kamin,


Kutt lallai ma a karnin nan da kowa ke takai takai Ina Zan iyya daukan kudi har 50k na baka da sunan bashi, bayan anyi operation in Ina zaka samu kudina ka biyani, gaskiya bazan boye maka ba ni nan Koh biyar bazan iyya baka ba banaji ance Yar masu kudi aka aura maka ba me yasa danginta bazasu Mata jinya ba tunda sunsan baka dashi Daman suka baka ita


Shikinan malam shu'aibu na gode, ya fada Yana fita ba tare da ya basa amsar tambayar Saba,


D'ayan shagon Al'ameen ya shiga  shagon gwanja bayan sun gaisa shima ya rokesa Koh zai samu bashin kudi


Amma Kai dai wallahih D'an rainin wayo ne ya Ina Saida kayan Miya zakace na baka dubu hamsin duk kayan shagon nan aka sayar Ina zaiyi dubu hamsin,


Haka yayita bin shagunan makwantansa Amma ba Wanda ya basa Koh sisi wasu kamma da bakar magana suke binsa dashi,


A haka ya iso shagon Haladu shima yace baidashi,. Wajen bairon mangoron sa yaje ya bude ya tataba mangoron rabi duk sun lalace saboda yini da sukayi a rana Kuma a rufe, zabe masu kyau yayi Yana,

D'auka yana sawa  a k'wando ya shiga shagon Haladu dashi, Yana cewa,


 don Allah Haladu Koh zaka sayar mini da mangoro na zanje na zauna a asibiti  na kwana biyu daidai Matata taji sauki 



Gaskiya bazan iyya sayar maka ba sai dai na saya kawai na sayar Nima na samu D'an riba,


Ba damuwa Al'ameen yace Masa


.....Nawane mangoron?


D'ari takwas da hansim


.....Zan baka dari biyar  don Naga wasu sunyi laushi?


Ba damuwa Allah ya saka musu albarka


......Ameen


Kudin Haladu ya basa ya karba gida ya shiga ya bude kofar,


 da yake ya karbi key a hannun Khadija wanka yayi ya saka kayansa Jin ana  Kiran la'asar yayi Alwala ya lalube takalmin Sumayya ya fita dashi a hannunsa, masallaci ya tafi yayi sallah ya wuce asibiti duk zuciyansa ba Dadi ya rasa wajen wa zai tinkara da zancen kudi,, yasan Koh mutuwa zaiyi Yan gidansu bazasu taimaka Masa ba bare Sumayya matar sa,



***Muna nan da Khadija har la'asar sallah mukayi dukan mu nurse tazo ta mayar mini da laidar ruwan a hannu na,


Na kwanta baccine ya dauken nabar Khadija na zaune,


Ya iso asibitin da sallama ya shigo dakin Khadija ta amsa masa.


Sannu yaya ka dawo?


Eh Khadija


Toh yaya ka samu kudin?


Wallahih Khadija sai addu'a naira 500 ne kadai na samu


Amma yaya ya kamata ka sanar da Aunty gaskiya don wallahih Yaya Ina Jin tsoro kaga ance appendix in ya kumbura fa tunda Allah Bai baka ikon samu ba, ka fada Mata ita sai ta biya?


Toh Khadija wallahih inajin kunya a matsayina na mijinta na kasa biya Mata kudin operation don samun lfyr ta,


Habba Yaya karfa ka manta Allah yaga zuciyar ka baka dashine Kuma ba abin kunya bane tunda itama tasan baka dashi,


Suna cikin Hira na farka a gigice Jin wani irin mahaukacin ciwon ciki ya tasarmin " Innalilahih wainnailaihir rajuun wayyo Allah na cikina"


Subhanallah Sumayya cikin ne Al'ameen Daya Mike cikin tsananin tashin hankali yake lalubarta ,


Khadija ma da saurin ta ta iso ni,sannu Aunty take fada idon ta ya jika da hawaye


*****Nikam.na kasa Bata amsa kuka kawai nake hankali tashe


Khadija tashi kije ki Kira doctor eiiii sauri 


Toh yaya tace tana mikewa da saurin ta


Al'ameen Kam hannun Sumayya ya Kama sai sannu yake Mata a hakan likita yazo ya sameta a halinnan


Da sauri shida nurse suka rufu a kanta tare da K'ura Khadija da Al'ameen waje,allurai sukai Mata harda na bacci lokaci daya bacci ya dauke ta,


Khadija da Al'ameen na tsaye a  bakin kofa likita ya fitoh ya kira su zuwa office,


Malam Al'ameen majinyaciyar ka tana cikin condition Mai muni ya kamata ka samo kudin aiki nan da awa uku ba wallahih kome zai iyya faruwa,


 Innalilahih wainnailaihir rajuun kawai suke fada,


Suka mike zuka fita a office in Khadija Kam kuka ta fara abin Yama Al'ameen yawa ta Ina zai fara anya zai yafewa kansa kuwa in yar mutane ta mutu ata dalilin rashin kudin aikin da Bai samo ba,


Yaya ya kamata Aunty tasan abinda ke faruwa muje ka fada mata ta Kama hannunsa sukayi dakin 


Suna shiga suka samu Sumayya na bacci ..........


Yaya Ammar innan yazo baka nan  ya bawa Aunty kudi Amma Taki karba tace na baka 


Allah sarki Ammar yazo ne?


Eh yaya kana fita Yana shiga, yace ma Wai Daman Yaso kuyi sallama tafiya ne ya kamasa, na gaggawa,


Allah sarki, Allah ya saka Masa da alkhari Yan kiyaye sa aduk inda yake,


Ameen yaya


 Khadija Miko min kudin na hada da dari biyar in hannu na naje na Basu Koh zasu mata daidai a Nemo sauran su bimu bashi,


Uhmm lallai yaya kadai San asibiti bata ma matum aiki ba tare da kudi bak'oh?


 Khadija bara dai naje na gwada Koh Allah zaisa a dace tunda kinga hour uku aka bamu kuma yanzun bacci take, bara naje na dawo ya fada Yana karban kudin da khadijar ke mika Masa,



Yana fita yaje wajen biyan kudi, 


don Allah Dan uwa kayi hakuri ga dubu goma da dari bayar a fara mata aikin in yaso za'a cikita muku daga baya Dan Allah ku taimaka min matatace ba lfy kuma hour 3 aka bani ake son mata operation?


Amma Kai *makahon* nan Ina ga baka zuwa asibiti ne taima?


Ina zuwa ranka shi Dade sai dai ban taba kawo majinyaci irin wannan ba


Toh gaskiya ka gannin nan Koh biyar naci a cikin kudin da nake karba wallahih Sai an daure ni


Kuma anan in baka biya kudiba wallahih baza'a Mata aiki ba Koh mutuwa zatayi gwara kaje ka Nemo duk in da kudi ya shiga ya fita shawara nake baka,Amma zance a taimaka maka toh hadai asibiti ba



Shikam tsabar damuwa har jiri yakeji yana ibansa ,a rayuwar yanzun in baka dashi kana ji kana gani harka mutu indai baka da kudin jinya ba Mai taimakon ka, zama yayi a bakin barandan pharmacy in yayi shuru cikin tashin hankali da alhini,



Bayan fitar Al'ameen khadija na zaune har lokaci hawaye baibar zuba ba sai ta gogi wani ya zuba, har  hour 1 yayanta Bai dawo ba,


*** A hankali nabude idona na sauke akan Khadija dake ta hawaye ido harya kumbura abinka da farin fata fuska tayi ja" khadija lafiya kuwa meya faru Naga kina kuka"??


Babu Aunty Daman na tsorata ne danaga cikin ki ya Tashi Ashe haka kike fama da Jin jiki sannu,


Murmushi nayi "haba Khadija Menene na kuka baki ga naji dauki ba" 


Toh Aunty,


"Yauwa khadija nikam likita ya fadi abinda ke damuna ne, Koh yake sani ciwon cikin nan"?


Kafun ta bude baki ma sai ga doctor ya shigo,Wai har yanzun baku samo kudin aikin ba Koh bakuji condition inda nace muku tana ciki ba Wai ina MAKAHON yake ne?


"Doctor ban gane mikake nufi ba" nace ina kallon sa?


Au baku fada mata bane? Yana kallon khadija alamar tambaya


Eh doctor bata sani ba khadija ta bashi Amsa,,


"Wai meke faruwa ne kun sani a duhu" waza'a ma aiki??


Kece appendix ya kumbura sosai tun jiya na sanar dasu Amma haryau shuru Basu biya kudiba yanzun haka  hour 3 na Basu su kawo kudin Dan kina bukatan aiki  gaggawa Amma an share hour 1  shuru, Banga alaman zasu biya ba


Da mamaki nake kallon khadija"yanzun khadija Ina fama da wannan babbar matsala irin wannan Amma kuke mini Wasa da rayuwa Ina da kudin da Zan iyya biya ba bandashi ba"


Kiye hakuri Aunty Daman Yaya ne yace shi yake son biya


" Koh ance lallai sai yayanki ne ya wajaba ya biya ai ni Karan kaina nasan Bai dashi don Bai biya ba ai bazai  zama wani abu na daban ba" menene riban ya fita yana neman bashi alhalin Ina da kudi"??


Kiye hakuri Aunty,ta fada jikinta a sanye ganin Raina ya baci


"Nawane akace kudin aikin"?


......50k ne


"Khadija tashi ki dauki key kije gida ki dauko mini jakana  wani yellow a cikin whtdp nawa ki dauko mini jakan akwai kudi a ciki"


Toh Aunty ta fada tana mikewa daukan key in tayi a jakan kayana ki hadamin da wayata ki dauko darduma babba da filo, ga kayan da nacire ma kikai mini gida kisa a basket in bayan kofa"


"Kihau nepep   ya kaiki kofar gida ki shiga in kin dauko kudin saiki shiga ya dawo dake ki basa 1k ya d'auki kudinsa karfa kice Zaki tafi da kafa"??


Toh Aunty ta d'auki  kayan nawa ta fita  a dakin, doctor Kam Dan kallo ya zama Daman tun da ya ganni yake ganin alamun Jin Dadi a tare Dani Amma abinda ya daure masa Kai mutanen da suka kawo ni asibitin abin yana bashi,mamaki harda Nurses Amma basuga fuskar tambaya ba


**komawa nayi na kwanta shima doctor fita yayi

 


Tsabar rudewa Khadija Koh yayanta Bata Lura dashi ba akan baranda ta wuce,


Shikam ganin lokaci na wucewa yasa ya Tashi ya shigo dakin,da sallama a bakin sa,


**Amsa Masa nayi Ina kallon sa yazo ya zauna a kujiran gefena,


 Sumayya,yakira sunana


"Na'am" na amsa Masa 


Kiye hakuri Sumayya na kasa kula dake wallahih nayi iyya kokari na Amma ban samu kudin ba Daman appendix ne ke damunki Kuma ya kumbura, shine ake son Miki aiki kuma........


**Da nayi niyar rufesa da matsifa Amma sai jikina yayi sanyi Jin bayanin da yake mini" ban bare ya karasa ba na katse sa"ba kome, me amfanin Ina dashi kaje kana,.. baran attaimaka maka kazo ka biya mini kudin aiki"? Karka sake mini irin wannan banaso duk abin da zai taso a waje na Koh Khadija Koh Kai, in baka dashi  karka sake zuwa gun wani da sunan ya taimaka maka indai abin baifi karfina ba pls"


Kiye hakuri insha Allah bazan sake ba,


**Shuru na Masa

Jin Bata amsa ba ya sashi yin shuru



Khadija na Isa gida ta samu jama'a na cike a kofar gidan dam alamu dai wani  abinne ya furu don harda motar police ga jama'an unguwan makil...............


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉



🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa* 


🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da*  *gyara* 


🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace* 


🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE* 


🍀 *Na tsunguno(habil)* 

🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )

🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,

🍀 *Na d'aki(halud Al'oud)* 

 

 *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼


🍀🍀🍀 *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa* 


🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria* 


Contact them vie

🪀08028827241 or 09033791049

IG @umsadincense







🪀my WhatsApp number

     08084453785


🪀My WhatsApp number

     08084453785

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯 

             ~ Na ~


 🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃


✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwa 👌

Free book 🤧


No comments